Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

KyalKyalin Kauna 92

8/19, 9:59 AM] SAFIYYA: Baffa na zaune shi kadai afalo yana yan rubuce rubuce Baba yayi sallama kallon kofan yayi yace "shigo" anatse Baba yashigo yazauna akasa cikeda girmamawa, baffa yace "ya jikin Yasmeen din yaya tace gobe dasafe akace za'a sallamesu ko"? Anatse Baba yace eh' Baffa yace "to Allah ya kara sauki" yayi shiru yacigaba da abinda yakeyi, Baba rasa ta yanda zai farama Baffa magana yayi, da kyar ahankali yace Baffa uhmmmm dama dama"dago kanshi Baffa yayi ya tsare Baba da idanu, ahankali Baba yace Baffa dama inaso ka jagoranci tafiyan mu ne gobe inaso karakani mu maida Yasmeen dakinta, kaga gata da juna biyu yakamata tayi zamanta adakin daganan sai uhmm katayani hakuri" duk wacce takaranta min daidai wani kalan murmushi Baffa yayi tareda girgixa kafa yana kallon baba saikuma chan yace "ni bazaka sani a halin kunya ba lbrahim, kai kadai kaje kayi rashin mutuncin ka kai kadai zakaje ka gyara abinda ka bata ni baza ayi mubawa yaron ba yan uwanshi halin karanta Dani da sauri Baba yace "Baffa dan Allah kayakuri Baffa yadagamai hannu yace "kaga dakata bawai zancen na yakuri bane, tayaya zan kalli makahon tsohon nan dakasa aka kakkama akasa sukai kneeling akasa aka daura bibdigogi akansu Sannan ka Sheka musu rashin mutunci? Koko tayaya kakeso na kalli mijin fatima da saida ka sumar dashi tsabagen dukan dakamai kaman kasami jaki"? Lumshe idanu Baba yayi ahankali Baffa yace "kai bazama kaji kunya ba da full chest naka da rashin mutunci kasa aka kwaso kayan yarinyar nan tsaf ko tsinke baa bari ba yanzu kuma akoma amai da kaya? Haba haba lbrahim kama kanka adalci mana gaskiya badani za'ayi ba, Fateema diyaraka ce kariga ka nunamin haka kome zakayi kayi akanta daidai ne but gaskiya bazan iya kallon iyayen yaron nan da yaron nan ba" gumi ketoma Baba yashiga yi Baba zai kara magana Baffa yadagamai hannu yace "tashi katafi bazan bika ba iya gaskiya ta kenan nagaya maka" Baba jiyayi duniyan tamai zafi wato kowa ya tsame.Hannunshi an barmai komi dan shiyay komi ga Fateema takicin komi a asibiti sai kuka take tana gayama mamanta ita akaita wajen Maheer Baba har wata yar rama yayı yay Zuru zuru, wucewa yayi yana tafiya shi kadai yaje dakin da aka jera kayan Yasmeen din ya tsaya yana kallo tayaya zai fara sa amaida kayan nan? Wih abin da kunya bala'in kunya yakeji kaman ba gobe wucewa tayi yakoma daki ranan har gari yawaye bai runtsa ba kasa fitanta yayi saidai Baffa yaje yadawo dasu Yasmeen. Yasmeen na ganin Baba ta duka agabanshi tafashe da kuka sosai tace Baba dan Allah kada karabani da mijina wlh wlh Baba zan mutu ina bala'in son Maheer, shi kadai nakeso kabani shi kabani komu aduniyan nan Baba an sakeshi dan Allah ku maidani dakin mijina" kowa na gidan kallon yasmeen yake an kasa magana ga bakin yarinya yabude Yasmeen bako kunya, Baffa ne yayi jarumta yace jeki hada kayanki Babanki ze kaiki" dasauri Yasmeen ta tashi tawuce tafita tai dakinta da gudu Baffa yakalli Baba dayakasa motsi yace "gwara ka maida yarinyar nan dakin mijinta tun wuri kadai gani da idanunka" yakalli su Ammi da Yaga yace "kuje ku shishiryata pls" da kyar Baba yace "idan gari yayi duhu zan kaita" hararanshi Ammi tayi duk suka fice sukayi lafiyayyun magunguna aka babbama Yasmeen tasha, Ammi dakanta tamata wani kazan magana batai amai ba sai murna taje zata koma wajen mijinta. Yasmeen tasha Abinda Baba bai sani ba tuni Baffa yaje har gida yabama su Baba hakuri dasu Hamad sosai yace yau Zaa dawo da Yasmeen anjima da daddare har cikin ranshi Maheer yaji dadi, dakanshi duk wacce takaranta min daidai da harafi daya a littafi ban yafe mata ba wlh har abada yakira wani funiture company aka kawo funiture saka shiga gyara side nasu komi dasauri sauri akeyi shima sai murmushi yakeyi dudda bawani zama sukayi agida ba dan anyi inviting nashi to channels new dan amai interview sukaje sai bayan magrib yadawo. Shirya Yasmeen su Ammi sukayi dake bala'in kamshi dan sun mata wankan turare cikin wani pitch lafiya an gyara mata gashi, dudda ta rame but tayi wani irin kyau farida tace "Anty Yasmeen kinyi kyau" murmushi Yasmeen tayi takalli Ammi dake kulle mata lafayan a waist tace "Ammi wai haka"? abada Gyadamata kai Ammi tayi tace "sosai" cikeda jin dadi Yasmeen tace "nasan shima Ya Maheer zaice nayi kyau" dan buge bakinta Ammi tayi kadan tace "ke bakida kunya ko" turoma Ammi baki tayi cikin kunkuni tace "nida mijina" hararanta Ammi tayi tace "mara kunya wuce kitafi Baban ki anjiranki amota" rungume Ammi tayi tsamtsam tace Ammi na ina sonki sosai sosai wlh, zancema mijina yakaina nasaya miki gift kinji" baki Ammi tasaki tana kallon Yasmeen yanda take wani murna za'a kaita gidan Maheer akunyace Yasmeen tajuya tafita mota tashiga Baba da baida karfi yatada motan suka tafi harsukakai gidan baicema Yasmeen uppan ba koda sukakai gidan kasa horn yayi sai tuna abubuwan dayayi yake ranan dayaso gidan da kyar yatara courage Wainolotrey yayi horn aka budemai yashiga ciki yayi parking ya aika mai gadi yaje yayi sallama, baa jimaba Baba yafito cikin mutuntawa yace "kushigo pls ku shigo" binshi Baba dake rike da Yasmeen yayi suka shiga ciki Hamad ne kadai afalo ganin Baba yatashi yabama Baba hannu, Baba yace "jeka kira Maheer Hamad" zama Baba yayi Yasmeen na zaune gefenshi hakanan Taji gabanta yahau faduwa, ba'a wani jimaba Maheer yasauko tareda Hamad yana sanye cikin wani farin yadi anmai dinkin jumper yamai kyau na fitina yana zuba wannan mugun kamshin ijiyan zuciya Yasmeen tasauke gabanta nafaduwa sosai yanzun wannan Hadadden guy din nan ne mijinta, Maheer is huge, ga tsayi, ga broad chest, ga lifiyayyen saje, ga dogon hanci, ga idanu, ga pink lips ga kira Ya Allah! sosai take kallonshi amman ko kallon inda take baiyiba bakaraso cikin falon, tashi Baba yayi ahankali yabama Maheer hannu. [

Post a Comment for "KyalKyalin Kauna 92"