Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

TUMFAFIYA 19

 
   Fitowana ke nan daga dakina zuwa falo muryan ummace ke fadin ki dauki kayan abincin nan ki kaiwa su Abban ku a falon shi daga nan ki tambayeshi idan suna bukatan wani abin ki kai masi.   Ja nayi na tsaya a wuri daya ina kallon ummah din dake magana dani lokacin kafin nace da ita ummah wani abincin kuka girka masu a nan kuma ?    Ina su gwaggo sunce an girka masu a gidan hjy ai to Abbah ku yace kada a kawo a nan zamu girka ai kinga ni yaune kawai zan basu abinci daga gobe hjy maimunace zata basu har su bar garin nan don dole nasan dai ya koma zuwa Monday ai.     Badon naso ba na dauki abincin dake a shirye nida Tani muka nufi part din Abba din Tani ta tsaya daga kofa nice na fara shiga da kayan abincin ciki da sallama a bakina.     Suna zaune saman kujera daya zaune a hade jin sallamana yasa Abba ya dan gyara ga yadda suke zaune din na nufi wajen dinning dinshi yace kawo muna nan zaifi.    Na juyo nazo gabansu a kasa na aje saida na aje abinci kafin na dago ina gaida Abba da ina wuni Abba mama kuna lafiya ina ita umman nakune nace tana side dinta na juya wurin matar data kafeni da idanu nace mommy ina wuni ?   Lafiya kalau yan mata wanan mamatace itace na sakawa sunan hjyn mu Abba ya fada na mike nafito na karbi na hannun Tani ta juya ta koma ita.     Na kai gabansu na aje ina jin Abba na mata bayani take fadin wanan na ganta dazun a part dinsu su wa yancan ne ban samu ganin su ba.    A nan na gane sunki yarda data gansu ke nan son nasan suna gidan dai weekend bamu fita zuwa ko ina ki turo min umman taku Abba ya fada.    Na koma na isarwa Ummah da sakon Abba na dibi abinci na koma saman doguwar kujera na zauna na fara ci ina kallo ummah tace kina da dabi,an son zama a nan kici abinci ga wurin cin abinci can ki bari.     Hakan baisa na daga ba naci gaba da kallon da nakeyi din tare da kannena naji ummah tace min dazun da kukaje gidan hjy abinda takewa ke nan ashe ta nuna maku jan ido ga zuwan  ku.     Bansan meya yasa hjy take wanan halin ba haka ko kudin da ku nazo daga gidan mu oho barta kawai na iya fada ai dole tunda tasan gaskiya take takewa duk abinda mutum yayi don kansa ai.     Can naga ummah tamike ta fita ni dai har muka gama kallon mu muka shige ban fito wajen ba ban kuma san lokacin data dawo part din ba don na kai kannena daki na rufo kofan daga ciki data shigone ta rufe kofan.     Washegari misalin tara na safe wayana ya dauki kara ina kwance lokacin ban tashi daga barcin safen da nakeyi ba na lalubo wayan na kara a kunnena bayan na dauka.    Muryan Ahmed naji yana min sallama na karba mai muka gaisa yake fadin badai baki tashi ba har yanzun daga barci ba zarah  ?    Murmushi nayi ina fadin yanzu dai aikatashe ni brother yace manya ke nan har wana  lokacin mutum yana kwance yana barci ?     Nayi murmushi yake fadin  zahar don Allah idan ba damuwa zanzo gidan kune na karbi kudin nan dake hannun ki zamu shiga kauye ne mu sayo wake da gero don azumi daya kawo jiki.    Nayi shawara na sayo su da kudin tunda lokacin sayan su ke nan yanzu nabi wanan riban da zan samu OK na fada kudin suna nan yadda ka bani su ban taba ba ai.   Na sani yace min nazo ba matsala na karba kazo mana idan kazo saika kirani nafito na fada yayi min godiya ya kashe wayanshi a lokacin nima na mike na daga gado inda na boyesu sunan  yadda na barsu na dauko tare da bude wardrobe din na na ciro wani envelop na ciro kudi a ciki na hada dasu na mayar da sauran a ciki.     Bandaki na shiga na kewaya na fito na daura gyale akaina lokacin wayana ya dauki kara wata kila dama yana kusa da unguwar tamuce dama.    Na dauka ina fadin gani fitowa ina daga wajen get ya fada nace ka shigo kawai ciki zan fito yadda nake dagani sai dogon riga da gyalen dana daura a kaina na fito.    Na hangoshi a cikin shiga irin na kauyawa da suke shiga daji da wani hula aja akanshi saidai yana hangoni ya fara cire hulan a kanshi ya nufoni fuskanshi dauke da dan murmushi.     Muka hade muka kara gausawa na mika mai kudin zakace wani takardane yadda ledan suke don yadda na shiryasu a ciki.   A daidai lokacin su Aisha tare da Rukkaiya suka fito daga cikin gidan namu ko su san sunga mutane a wurin basu nuna muna hakan ba.    Daga inda muke yake fadin ina kwanan ku Rukkaiya ta wani kalloshi tasa kai ta wuce mu yace toh ga manya gaisuwan ma sai angadama ake karbawa a gidan ku.     Murmushi nayi nace yanzun kauyen zaka ke nan yace dana bar nan mota nacan mun fara taruwa sai mu daga Allah ya tsare na fada naji karan bude kofan fitowa again.     Mamace ta fito naji gabana ya fadi ras na juya ina gaida ita tayi dan jim kafin ta amsa tana wucewa zuwa wurin motar dasu Aisha suke shiga ko ta shiga baya sukaja suka fice a daidai fitan su naga duk sun kallo mu suna magana.    Yai min sallama shima ya tafi na juya na koma ciki a falo na samu ummah tsaye suna hada abin karyawa ita da Tani nasan sun makara ko kuma aiki yayi masu yawa lokacin.     Ummah ta juyo tana fadin yaushe kika fita daga nan nace yanzu wani ne yazo amsan takarda a wurina nakai mashi .    Amma kinsan Abban ku yana gari kika fita haka ko ai yanzun na fita na bata amsa kizo ki kai kayan nan falo nasan kila sun tashi suna jira yanzu.     Nace to na fara daukan kayan zuwa falon Abban mu nayi sa,a babu kowa a falon har na gama jerawa na juya zan fito naji an bude kofan matar ce ta fito na juya ina gaida ita tace.    Aa kece ashe ina jin mitsine ina ciki na leko nace eh da kara fadin ina kwana ta amsa min cikin murmushi tare da fadin sannu da kokari ki gaida ummah taki kafin na shigo gaida su.    Wanka na fito duk da ina jin zuciyana a wani irin don ba dadi ko farin ciki a zuciyana mai na zauna ina shafawa naji wayata ta dauki ringing na duba Ahmad din ne ya kirani na dauka.     Yayi sallama na amsa ya fara fadin nazo na bude kudin naga sunfi wanda na baki a jiya yawa eh na sani nima bansan me zanyi dasu ba na baka ka kara don naga kana bukata .    Amma zarah hakan zai iya hadani dake don kudi ba ayi mai haka Allah dai ya bada sa,a na fada yace amin yanzu kim aramin dai na kara ke nan nace eh aro din na baka.     Amma kuma ban faye son  kudin wani a cikin sana,ata ba abin dan uwa aibana aani bane na bashi amsan na kashe wayata naci gaba da shirina rana  shigar atampa nayi dinkin riga da buje.    Har na kwanta na mike na nufo waje kitchen na wuce na dauko goran ruwa na fito ido muka hada da amaryan Abba dake zaune a falon ummah tana fitowa daga bedroom din ta.    Matar yar kwalisace sosai don shigarta kawai zai nuna hakan kamar na shareta saidao na daure na sake gaida ita ta amsa itama a cikin fara,a tare da fadin hjy ki bani yar nan taki mu zauna tare da ita Abuja .     Ayi hakan tana karatu a nan ai Dear ya fada min ai a can kuke kuka dawo nan yanzu  wallahi ummh ta fada mun dawo gida saboda yara su saba da yan uwa da al,adun mu na nan din ta fada kamar yadda Abba da mama suka tsarata a lokacin.    Abinda ummah ba ta sani bashi don mama dake son dawowa gida da yaranta a lokacin yasa muma tasa aka dawo damu kusa da ita don kada mu zauna birni suna gida su.    Don dama Abujan tace zata dawo Abban yace bai yarda da hakan ba shine tayi makarkashiya wurin hjy inno kakarmu Abba yasa kowa dawowa gida.    Murmushi matar tayi kafin tace nayi mamaki keda kike da yara kanana haka kika yarda kika dawo nan ba tare da yaranki sun samu wadatattacen ilimi ba kamar yadda yan uwansu suka samu a can su.    Nan ma ai sunayi ba laifi bawa duk baya wuce kadaranshi ai in Allah ya nufa zasu zama wani abu a rayuwa zasu zama din aiko mahaifinsu a nan din yai karatu har ya zama wani abu yau a rayuwan shi.    Hakane Allah ya raya munasu ummah ta amsa da amin sai sukai shiru gaba dayan su don matar ta kula da ummah bata da yawan surutu yasa taja bakinta itama tayi shiru .    Waya Abba ya bugo mata zata gaisa da wasu abokan shi yasa ta mike zuwa falon na Abba tavarwa ummah part dinta duk ina dakina ban fito ba yinin ranan.    Mama ko tana can a family house din suna kwasa dasu gwaggo don takai karan gun hjy saita samu da sanin tsohuwar da aka toshe wa baki da abin arziki akai auren ashe.   Wana  yasa suka hargirse a wurin ta fara fadan bakaken maganganu garesu suma suka shiga ramawa tafito hasale ta juyo zuwa gida.     Dije ce ta leko daga daki sukai arba da akuyanta datayiwa suna da uwargarke da yau uwargarken ta juye ta komawa dije wani abu na daban da Dije ta kasa fassarawa lokacin.     Yauma tun fitan Amadi gidan suke takon saka a tsakanin su dalili kuwa shine  ruwan kasarin da ya kwana Dije ta gyara masu don Amadi yau sakkon fita yayi bai samu tsayawa yadda ya saba gyara masu ba.    Ita kuma ganin ai ruwan baiyi komai ba yasa ta gyara masu shi ta aje tana kokarin juyawa ta bar wurin taji kamar an bangajeta ra dauka wani a bayanta mai karfi yayi mata wanan bangazan .    Allah ya gyara bata kai kasa ba ta juyo taga uwargarke a tsaya tana ture ruwan cikin jarkan da kai hakan bai mata ba tasa kafa kamar mutum ta ture ruwan ya zube a wurin.   Da sauri Dije taja baya a firgice don sai taga kamar ba akuya bace mutum ne ai gabanta don yadda uwar garken ta nuna hasala a fil sai hakan ya ba Dije tsoro ya koma dakinta ta shige sai lekowa takeyi daga cikin dakin tun safe ta kasa fitowa ta dan rage aiyukanta na gida kamar yadda tasaba yi.     Gashi kamar hadin baki yau ba wanda yayi sallama a gidan ita kadaoce a cikin gidan sai dabbobin ta dake kiwonsu inka debe uwar garke dake tsaye tun lokacin bata kwanta ba ta kurawa kofan dakin Dije din ido babu kiftawa.     A daidai lokacin da Dije din ke lekawan ne a yanzu uwargarke din ke kwantawa a makwancinta komawa Dije din tayi baya ta dafe kirjinta tana sauke ajiyan zuciya.   Sai kuma raji shigowan mutum gidan yana sallama da mamaki a fuskanshi yake bin gidan da kallon ganin a yadda ya fita yabar gidan haka ya dawo ya samu gida kamar tun safe Dijen bata leko wajen ba.     Dijeh ya fada da karfi kuma a razane yana sauri zuwa kofan dakinta sai gata ta leko a tsorace don ta sheda shi din ta gani ko wani sukai arba da juna a hakan.    Amadi kaine ashe ta fada kamar a tsorace tana kokarin yunkurawa ta mike tsaye lokacin yace wai lafiya kike kuwa Dije ? Tace balau ba kan ,  kadai huta a san nayi a gidan don ga baki daya duk a firgice nake yau din nan.    Me ke faruwa agidan ne Dije ya sake tambayanta a gagauce, Dije ta dubeshi tace huta dai mayi maganan daga baya barin dan fita in samo muna dan wani abu inciwa cikina ta fada tana jawo tsunman gyalenta daga kofa a rataye.    Tasa kai da sauri ta fice gidan ko kallon inda dabbobin suke batayi ba ta fita da sauri ya bita da kallon mamaki don yadda take jan kafanta mai mata ciwo kamar na dole takeyi lokacin da sauri.     Juyawa yayi wurin dabbobin yana kallon su kafin yabi ko ina na gidan da kallo yasan duk da tsohuwar nada ciwon kafa amma idan yai irin tafiyan nan na sammako ya fita bata barin gida haka da datti saita gyara shi.     Cikin dan lokaci yayi tunane kardai yawan maganan akan uwargarke da tsohuwan keyi ya zamo gaskiya fa shi bai kula ba har wani abu yazo ya samu kakar nashi saidaga baya yayi daya sani akan hakan .   Bin bayan Djje din yayi wace ya samu a tsaye kofan gidan nasu kamar tana tunane Dije ya ambata daga bayan ta cikin murya mai nuna yanayi.     Ta juyo a firgice taga shine ya karsso dab da inda take tsaye yana fadin Dije meye damuwan kine wai  ki fada min don naga kamar a firgice kike yau a gidan.     Duban bayan shi tayi kamar tana duba idan wani na biye dashi lokacin kafin taja hannun shi su taka dan nisa kadan da gidan nasu kafin tace yau uwargarke taso kasheni Amadi.    Kasheki Dije tace kwarai nan ta kwashe komai yadda ya faru ta labarta mashi tare da fadin don haka dole ka sayar da akuyan nan ko mu saketa tabi gari kawai taje duk inda zata.    Dan shiru yayi yana kallon tsohuwar kafin yace baki ganin in muyi hakan munyi ganganci Dije akuya nan fa ba zamun takeyi a gidan nan ba yanzun.   Tana zama na amanane a wurin mu yanzu yau idan mun saida ita maishi yazo muce dashi me ke nan ta dawo mun koreta ko ta dawo mun sayar da ita ?     Kiyi hakkuri kizo mu shiga gida zan san abinyi kan hakan me zakayi ta tambayeshi a dan tsorace tana kallon shi don jin me zai fada.    Yace bari dai yanzu koma ciki bari na gangara na sayo maki abinda zakici kafin motan kayana ya iso nan da dan lokaci in zama busy ya fada yana kokarin wucewa.     Ta jawo hannun shi ba zaka barni da wanan abin ba a gida ni kadai kai subbahanallahi ya fada kafin ya dan daga kai yana tunane a wurin na dan lokaci.     Yanzun zo ki zauna ga wuri naje in dawo yanzun nan yana jan hannun ta zuwa wurin dan dutsen dake kofan gidansu a kafe inda wani lokaci suke zama ko masu tafiya su zauna asama su huta akai.    Zama tayi kamar yadda yace din shi ya wuce can inda yan mata ke saida abinci ya sayo mata shimkafa da salad da miya da nama yanka hudu sai ruwa mai sanyi daya riko mata a leda lokacin tare da fantan kwalba.    Ya dawo suka shiga gida tare ya kaita har dakinta ta zauna ya fito ya diban mata ruwan wanke hannu don yasan ba zata ci da cibi ba saida hannu.    Saida ya tabbatar da ta fara cin abincin a galabaice ya mike ya fito sai wurin dabbobin nasu ya tsaya a gaban uwar garke daga daki  inda dije take ta iya hangoshi wurin yana gyara masu wuri.     Ya zubar da ruwan ya dauke roban ya wanke ya share wuri ya zuba masu abinci da ruwa duk a cikin zafin nama da alama yana saurine a lokacin.   Haba uwargarke keda Dije ba hakan tsakani  ku ai karki manta Dije itace farin ciki  gidan nan dani daku duka baki dayan mu gidan ai Dijece gatan mu kin ture ta idan wani abu ya sameta yau duk ya samemu ke na  ai.     Ke kanki ina baki girman ki na babba cikin yan uwa duk wani laifi ko wani abu kece babba ke, ke dauka don haka kibar firgita min Djje don Allah ba lafiya ke ga tsohuwar ba kin sani.    Haba uwar garke bai kamata haka  ba tsakanin ki da Dije sai mutunci ai yanzu kibar mata abin dabo dabo tana firgita dake haka don Allah.    Zaka ce da mutum dan uwanshi yake magana a lokacin yana taba uwargarke magana sai ta mike ta girgiza jikinta kafin ta dona kai a ruwan shan su tana sha .    Bayan ya gama dasu ya dawo zuwa dakin dije daga kofa ya tsaya yana mata magana Dije zanje na duba na gani ko motar kayan mu ta iso na fake don nan nake son a kawo min su gida tunda banda shago a kasuwa yanzu.     To kayi niyya Amadi Allah ya taimaka nima barim je gidan malam Tanimu harka dawo sai in dawo gidan ta fada tana yunkurin tashi tsaye ya dawo ya tsaya yana fadin .    Dije kardai ki dauki wana zancen ki kaiwa makwabta shi suzo su fassara wanan magana  da wani manufa kuma daga baya.    Kinsan yadda mutane suke yanzu balle ana ganin na fara sana,an nan da kudin mutane sai su dauka ai wani hali na daban na farayi yanzu karshe ma sai a camfa gidan nan kiga anzo anki shiga daga karshe azo ana gudun gidan nan kuma.     Hakane fa yanzu lokaci ya canza ai gara daka kwabeni don kan abinda nayi niyar zuwa fadamasu ke nan yanzu inda taimakon da zasuyi min su taimaka min dashi.     Ba abinda zai sake faruwa in sha Allah har inma ta hurhurane Allaj zai muna maganin ta balle yanzu ina batun shigo da kayan nan kinje kin fadi hakan a take zasu camfa min ne kan kudin tsafi nake amfani dasu.     Alhalin kudin mutane ne na aro na kara nake juyawa tace Amadi kudin wa ka anso yace naso maki wanan bayanin kuma sai naga baki cikin hankalin ki yanzu idan na dawo zan fada maki komai in sha Allah.     Nan ya fice ya barta tana zancen zuci ita kadai a gidan har ta dan samu fitowa ta gyara gida saidai tanayi tana kallon inda dabbobin suke har taje ta sakamasu hayaki saboda sanyi a wurin garken nasu.

Post a Comment for "TUMFAFIYA 19"