Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

TUMFAFIYA 23

   
  Da kuka wiwi na fado part din ban tsaya ba sai a jikin ummah dake zaune a cikin yanayin damuwa da takaicin hali irin na da namiji da bamu da yadda zamuyi dasu a rayuwa sai zaman hakku ri.    Kalah ummah batace min ba asalima kamar bata san inayi ba a lokaci sai can naji muryan ta tana fadin tun farko na fada maki kibi komai a hankali gidan nan don nima hakkurin nakeyi nakai ga samun ku a yanzu.    Ban san me hjy maimuna ta fadawa Abban ku ba har ya hau haka da zafi kan wanan maganan don ba zanyi tunanen cewa hjy karima bace ta zugashi tunda a gaba data fuskanci rashin gaskiya a cikin maganan suka rikice dasu a wurin .    Jiya kuma hjy maimuna a dakin Alh ta kwana bansan ya sukayi ba sai yau danaje gaisheshi yake min maganan wai tunda yaron nan kike so a turo shi yazo naso fahintar dashi gaskiya ya hauni da fadan hakan.     Don haka komai ma ya faru nasan itace ta kullashi don taga ta wargaje min farin cikina a gidan nan dama kuma a cikin hakan muke da ita kullun.     Salamu alaikum aka fada hjy karimace ke sallama daga kofan ta shigo itama ranta a bace yake lokacin da gani sin kwasa da Abba din kan zancen nawa ke nan.    Au kuka kika tsaya yi kan wanan zancen ke ina kina son yaron dai ba shike nan ba saiki turoshi din kamar yadda ya fada ya bincikeshi don naga an zugashi sosai ya zugu kan zancen.    Za a hana budurwa yin saurayine ko macece zata kira maza zuwa gareta ni wanan maganan banga ya kai wani abin tsayawa a tayar da jijiyon wuya ba hakan nan.    Amma saina fahinci zancen da akwai lauje cikin nadi tun farko so kawai ake aga an kuntatawa wani a wanan zancen sam Alh baiyi tunane ba ta yaya mace zata fada ma zance ka tsaya ka haushi haka ka zauna wai shine gaskiya.     A gaskiya hjy salma kinyi kokarin zama a haka cikin mutanen nan wallahi ni sam ba zan dauki wanan irin rainin wayau ba tunda bana wa yayanta hakan nan ni don me wasu mutanen basa tunanen mutuwansu ne wai ?    Na fahinci komai a gidan nan yanzu don haka mu zuba dani da matan nan zata gane cewa karyan iskaci takeyi a baya yanzu ke zarah ki turo yaron wa Alh muji me zai masa.    Shike nan kuwa ai wuya baya kashe bawa idan kayi hakkuri sai ya zamo maka alheri wata rana idan anyi hakanne don a tozarta mu na roki Allah ya mayar muna dashi alheri a rayuwan mu ummah ta fada.    Insha Allah sai kunyi alfahari da hakan ban son ki nuna sarewa ko gazawa kan wanan zancen a yanzu ki daure din ga duk hukkuncin da zai yankewa yarnan a yanzu ki bita da addua da sadaka hakan ya zama mata alheri a rayuwan ta.    Ina a jikin ummah gurfane na lafe ina jin abinda suke fadi a gaskiya ba zance ban son Ahmed ba da sunan so ba kuma zance bana son shi ba don halinshi dana sani a yanzu na jajircewa rayuwan shi.    Haka kuma har in hakan ne meyasa ake son kashe mu da ran mune mu da mahaifiyar mune idan hakane gara nabarwa mama gidan na huta da wanan ukuban da suke nuna min ita da diyanta zaifi min sauki hakan ma.     A ranan ina kuka na kira Ahmed a cikin tashin hankali na fada mai neman shi da Abba din keyi tunda umurni Abbah ya bani kan yin hakan don haka ya zama dole in kirashi in fada mai hakan.   Shima a rude yake tambayana kome ya faru Abba din ke son ganin shi haka don yasan ba zancen soyayya a tsakanin sai mutunci da girmamawa.    Ban iya mashi bayanin komai ba don banda karfin halin iya magana a lokacin don haka na kashe wayata kawai shima ya shiga tashin hankali irin wanda na shiga din a lokacin.    Don haka da yamma karfe hudu ya fitowa sallah ya shirya ya fito zuwa gidan namu ba tare daya fadawa kowa inda zashi ba don baisan dalilin dayasa Abba din yake neman shi ba.    A iya tunanen da zaiyi kan shawara guda ta yanke zancen shi shine kuma Abba zai mai iyaka dani kan ya rabu mai da diyanshine.    Yanzu in an mai kashedi a kaina anya zai iya daukan hakan a yanzu kuwa yadda ya saba da yarinyar tana daukan shi da mutumci takar dan uwanta najini neshi a gareta yanzu don zarah ta zame mai wani bangare na rayuwan shi yanzu.   Da wanan ire iren tunanen ya kawo har kofan get din gidan namu ya sauka ga mashin ya biya dan achaba kudin ya tafi shi kuma ya kalli gidan yana addua a zuciyarshi da neman kariya daga wurin ubangiji.    Maigadi yaiwa magana don ya bude mashi get din gidan saida maigadin ya kalleshi da kyau duk da yasan shi yana zuwa suna gaisawa kuma yana dan maj ihisani daidai karfin shi kuma maigadin najin dadin hakan.    Yaron arziki kaida kanka kake son ganin Alh yau anya bakayi karanbani ba kuwa ganin Alh fa sai manya ko manyan sai ka amsa sunan ka .    Kai Ahmed din ya daga ya kalli gidan namu cikin second yadawo da kallonshi ga maigadin yana fadin yasan da zuwana don shi yace nazo yau din a daidai wanan lokacin.  To to to aishike nan bari na tashi naje nai maka iso dashi din tunda yasan da zuwanka din ai dama na dauka ko zuwan kankane kayi da sai in baka shawara kawai ka hakura da ganin nasa ka koma inda ka fito zaifi ma sauki.    Ya mike kata kata ya nufi kofan falon Abba din dake dan saye hakan ya nuna ba wanda zai shigo a lokacin gidan saishi da iyalinshi ko wasu shakikai nasa na jikin shi.   Wucewan maigadin yasa Ahmed din kara tsarguwan kanshi duban jikin shi yayi yaga duk da yayi shiri irin wanda bai taba yin irinsa ba a jikin shi amma sai yaji ya raina kanshi a hakan.    Bai dade ba maigadin ya dawo da sauri yana fadin yace kashigo daga ciki yasan da zuwan ka din haka yasa ya dufari inda yaga maigadin yaje duk dabai gama tabbatar dako nan ne hanyar shiga cikin gidan ba yadai sakai ya shiga da sallama a bakin shi .     Sanyi da kamshine sukai mashi maraba da zuwa lokaci guda har saida ya dan lumshe idanun shi kadan don irin abinda yaji bai taba jin irinshi ba a rayuwa.     Sallama yayi cikin muryanshi mai taushi da izza da gadara bai shigo ba saida aka amsa daga ciki tare da bashi izinin shiga falon shiga ciki ta hanyar fadin bissimillah shigo mana ciki .    Yana dan dukar da kai yasa kafa ya shigo falon tare da dan gurfanawa can daga nisa yana fadin ina wuni Abbah shima Abban kai ya dago yana kallon dan matashin saurayin daya baiyana a gaban shi.    Sau daya Ahmed din ya dago kai ya kalli Abba din kwarjinin Abban din yasashi saurin dukar da kanshi kasa da sauri ya fara gaida dattijon dake gaban nashi watau Abbah .    Dan shirune ya biyo bayan hakan tsakanin su bayan gaisuwa kafin Abba ya kawar da shirun da fadin yaya sunan kane yaro Abba ya fada yana kallonshi ?    Ahmed nake ya fada sunan mahaifinka fa Sama,ila ya bada amsa kafin ya kara noke kanshi kasa kamar kunkuru.   Meye hadin ka da yata Abba ya tambayeshi tare da tsureshi da ido yana son jin amsan da zai bashi a lokacin lafin yasan hukuncin yankewa .     Shiru Ahmed din yayi kafin Abba yace dashi bakaji band meye hadinka sa yata zarah ne ?.     Abba wallahi ba komai tsakanina da ita sai alheri mun hadune a makaranta da ita ranan da wani matsala ya faru da ita kowa ya kewayeta yana kallon halinda take ciki na neman taimako.    Naga rashin dacewan hakan tunda mace ce shine na taimaketa har ta dan farfado daga yanayin da take ciki din na fitan hankalinta.    Tun wanan ranan ne hakan yasa muka shaku da juna muke zumunci da ita nake kuma taimaka mata wurin karatu don ina gaba dasu da shekara biyu a school din.   Ka tabbatar wanan ne kawai atsakanin ku  shi kawai na sani tsakanin mu Ahmed ya fada yana kara soke kanshi kasa.    Abban yayi gyaran murya yace ji nan nayi binke nagane cewa duk makarantan nan dakai zarah ke mu,amula fiye da kowa sai kuma kawayen karatun ta mata da maza da kuke zama tare kuyi karatu dasu duk an binciko min hakan.    A yau din nan nasa aka bincika min komai game daka saidai na samu feedback maikyau game da halayeb ka abu dayane ya daure min kai sai zancen mahaifin ka da akace ya barka tun kana shan nono bai kara waiwayo ka ba har yau din nan ?     How do you see kaida baka tare da mahaifinka zakazo wanan irin gidan neman auren yata in baka alhalin kaima kanka baka san mahaifinka ba ?    Ahmed ya lankwashe yan yatsun hannunshi cikin juna a ladabce ya dago kai ya kalli Abba din ya kara dukarda kanshi kasa yace.    Abba saukin abindai bincike ya nunama cewa nidin ba shege bane mahaifina kuma da matsalace tsakanin shi da mahaifiyata da bata bishi zuwa kasansu ba yasashi fushin haka har ya wofitar dani na tashi mara galihu hakan baisa na watsar da tarbiyan da akeson samu ga ko wani daba .    Zancen Zarah kuma ban taba tsayawa da zarah da sunan soyayya ba ko wani abu makamancin hakan a tsakanin mu ba don ko nasan nidin ba dan kowa bane ban kuma kai matsayin da zance zai nemi diya irin zarah ba.     Don hakane alakan mu ya tsaya a iya mutumci kawai a tsakanin mu ba kuma sai don banson zarah din ba don sanin haka a gareni kawai da nayi.     Kallonshi su Abba suka karayi da kyau shida dan uwanshi dake zaune falon a lokacin kafin yayan Abba din yace dashi sana,an me kakeyi a yanzu kuma meka karanta a karatun ka ?    Wanan ma duk bai taso ba a yanzu ai Abba ya fada a dan fusace sai yayan nasa yace ka barshi muji tukuna ai ya kalli Ahmed din don son jin me zai fada masu.    Yace kimiya na karanta sana,a kuma saye da saye da sayarwa nakeyi ina shiga kauye ina sawo hatsi in kawo birni in sayar da sauran yan buga bugan zamani da akeyi.    Tsaya nan ma hakan ya isa mun gamsu da baya nan ka baba sale ya fada yana gyara zaman shi Abbane ya dago yace.    Kai banda abinka da wanan sana,an zaka rike min yata sana,an da ko kudin sabulunta a wata bai kai ba balle zancen sauran bukatan ta na rayuwa.    Kai Ahmed din ya dago ya kalli Abba din dake magana ya sake dukarda kanshi kasa don zuciyar shi dake tausan shi saboda su mahaifan  zarah din ne a lokacin.    Da badon hakan ba yau da suka tayar mai da mikin dake damun zuciyar shi a kullun yana tausan kanshi da hakan yana jajircewa don gudun irin hakan gareshi na tozartawa.     Muryan Abbane daya kira sunan shi ya katseshi Abban ke fadin Ahmed daga yau din nan ina son ka nisanci yata zarah a ko ina don yanzu dai nasan kasan cewa zarah ba sa,arka bace ita.    Karatune kuma kagama kai yanzu din haka banson jin wani mu,amula kuma kota mutunci ya sake shiga tsakaninka da ita nan gaba zaka iya tafiya yanzu.     Kuma kada naji ance ka sake kawo wani abu nan gidan da sunan alheri niko yaushe ina tsaye kan Iyalina ga komai don haka ka nisancesu .     Ga wanan dubu hamsin ne ka kara a jarin ka ka kiyaye don ka zauna lafiya Abban ya fada yana kawar da kanshi gefe cikkn takaici.    Kai Ahmed ya girgiza tare da fadin a,a Abba ka bar kudin ka nagode aikai mahaifine a gareni ko yanzu ka fadakar dani ga abndana manta cewa nidin mai raunine bai kamata na dinga kai kaina inda Allah bai kaini ba.    Ya mike ya tsugunna tare da fadin zan koma nagode kwairai ga hakan yana fadin  haka ya mike ya fice daga falon suka bishi da kallo kowa da abinda yake sakawa a zuciyan shi lokacin.    Baba Salihu ne yace yaron yaron kirkine alama ya nuna hakan gareshi cewa zaiyi mutumci sosai wallahi saidai dan matsalan nan da aka samu kawai shine cikas din.     Kirkin shi bai dameni ba ya rabu min da yata kawai shi nake so a yanzu itama zanyi warning din ta da kakausan murya kan hakan idan ba hakaba ranta zai baci dani sosai a gidan nan kaji na fada maka.    Banso ka da hakan ba ana cizawa a hura don bamu san me Allah zaiyi nan gaba ba gara ka bita da addua kawai shine mafita nake gani.    Shiru Abban yayi don takaici ya hashi yin magana sai can yace ita kuma shashan daya Aisha wai yaron nan dan kawar uwarta dake Lagos ta lakewa gashi sunja min zubar da mutuncina.    Yau nayiwa uwarshi waya take fada min wai yaron bai yarda da hakan ba yace a barshi ya nemo matarshi idan ya tashi kaga ke nan dama a tsakanin uwayen nasu ne sukeson hadin shi kuma yaki.    Ai kaji matsalan shiyasa nace ko wanan din kabisu sannu don alama ya nuna cewa suna son junan su saida sun kasa gane hakan suka tsaya a mutunci .     Nan dai sukaita tataunawa kan yayan nasu har tsawon wani lokaci kafin Abba din suyi sallama da abokin haihuwan nasa yatafi shi kuma ya fara ganawa da mutanen shi yan maula.    Ahmed ko da kyar yaga ya isa gida dakin shi ya shige ya kwanta don bacin rai don ko Djje bata sanda dawowan shi gidan ba lokacin.    Ba abinda ke masa yawo a rai sai irin maganganun da Abba ya fada mai masu zafi daba wanda ya taba fada mai su a duniya sai yau saidai baiga laifin iyayyen nawa ba don shima yasa  yakai kanshi inda Allah bai kaishi ba lokacin.    Wayan shi yai kara ya dauko yana dubawa sunan zarah mayana ya gani a screen din wayan yaji kamar ya share wayan kada ya dauko don shara din Abban daya kidanya mashi.    Saidai kuma ya kai hannu da zumar dauka wayan ya katse baikai ga dauka ba haka yasa ya juya ya barta  da haskenta na kira kafin can ya sake jin kiran ya koma shigowa again.    Wanan karon bai bari kiran ya katse ba ya daga yana fadin Zarah ya akayine daga bangarena nace bakazo gun Abba din bane halan naji banji komai ba.    Dan murmushi yayi kafin yace nazo mana me kike son ji halan nace abinda yasa yake neman ka din mana brother don bansan me aka fada mashi ba akan mu.    Yace nazo tayi min warning akan kada in kara tsayawa dake ko yaji an gamu tare duk abinda ya biyo baya nina ja yace min.    Haba dai nasan Abba ba zai taba fadin hakan ba ai yace yako fada wallahi don iyakan gaskiyata ke nan na fada maki kinsan ban magana biyu ni ai.    Yanzu Abba din ya fadama hakan don Allah yace kwarai kuwa don Abba yau yai min tuni ga abinda nina manta a rayuwana duk da ba soyayya mukeyi ba naji dadin maganan wani gefe kuma naji zafi.     Don Abba ya fada min jarin hannuna ko sabulun wankanki ba zai saya ba don haka ya yanke duk wani alaka tsakanina dake daga yau kuma ya kafa shedan hakan ga dan uwanshi da muka zauna tare mu uku a falo  naku.     Kashe wayan nawa nayi domn kada yaji sautin kukan da yazo min a lokacin saidai abinda ban sani ba ya riga da yaji ko hakan yasa yai ta kiran layin nawa ban dauka ba.    Don kukan dana rufe kaina  a daki ni kadai a ciki inayi lokacin ina maijin zafin abinda Abba din ya fadawa Ahmed don ma bai fada min duka ba ke nan iya wanan din daya fada min ke nan.    Twelve misscal nasa na daga waya na gani bayan sallah isha,i danayi na dauko wayan ina duba kiran inda na samu sakonshi cewa don Allah in kirashi idan naga sakon shi.    Ban kiba na danna kiran rayin shi ya shiga ya daga ya dauka yana fadin yanzun kin sauko ke nan ko kada wanan maganan ya bata maki rai don Allah.     Ni nasan ke din ko Abba bai fada ba keba sa,ata bace zarah don haka muyi hakkuri mu guji abinda zai iya kai ya komo daga hakan.    Dama ashe ba sona kakeyi da gaskiya ba nafada a cikin wani murya ina sake kuka lokaci guda naci gaba da fadin ni tunda ummah tayi muna adduan daidaituwa a tsakanin mu naji zuciyana ya kwanta da hakan.    Zarah dama kema kina sona ashe kamar yadda nima nake son ki ashe bansan da son juna mukeyi ba sai yau da Abba din yake furta kalman raba tsakanin mu dake.

Post a Comment for "TUMFAFIYA 23"