Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

TUMFAFIYA 24

  ,,,,,,,
    Wanan labarin na sayar dashi don alredy don haka kada wani yai kasadan juya min shi zuwa audiovisual yin hakan gangancine ga maishi.   Dari biyar ne ki biya don Allah ki karanta a cikin sallama yar uwa don Allah ki biya ki gujewa daukan alhaki a kanki yar uwa.     Kuka nakeyi sosai kamar raina zai fita din maganganun da yake fada min masu tayar da hankali yana kuma kara kashe min jiki da kalaman shi da sunan ban hakkuri a garemu.    Kunnuwana ba zasu iya daukan kalaman shi tun lokacin daya furta zarah dole hakkuri zamuyi da juna don gudun birewa iyayyen ki a kaina dan zaman mu tare zai iya jawo maki matsala da rayuwaka zasu baci.    Don gaskiya Abba ya fadi ni daya nake da maraya ko wani mara uba dayazo duniya don haka kinga banda asalin da zamu iya zama a tare dake har iyayyenki suyi suyi alfahari da hakan don tabon da iyayyena suka shafawa rayuwata.   Dif na kashe wayan saboda cigaba da saurarenshi zai iyasa zuciyana bugawa a lokacin don yadda nake jin kaina haka shima baiyi gigin sake kiran layin nawa ba a lokacin don kukan da yazo mashi.    Kuka yake saboda abu biyu na farko gorin da yasan zan biyo bayanshi dama ako gidanwa yaje neman aure balle irin gidan mu babban gida irin haka da kaddara takaishi ciki.     Shi kanshi yasan duk wanda yaji hakan ba za,a taba bashi gaskiyan hakan daya faru ba don ko driver ya samu a gidan mu yaci a kalleshi a daga mashi hannu.    Balle wai aji yar gidan mune yake nema da aure a lokacin idan ba kaddara ba waya isa yai hakan saiko kaddara din da yanzu aka fake a gareta.     Ya dade a kwance yana kuka shi kadai a dakin kukan nasa yasha bambam danawa domin shi kukan abu biyu yakeyi a lokacin niko ina kukane kan kalaman Abba garemu kadai.    Yayin da shi kuma yake kuka kan irin rayuwan da mahaifan shi suka sakashi cikine don abin fade baiwa mutune kadan yanzu koda abin na a taru a tausayawa mutum ne sai an koma baya ayin gulman mutum a karshe.     Yasan kulba dade dama zai samu irin hakan saidai bai taba tsamanin hakan da wuri ba gareshi sai gashi ya fara fuskantan hakan ga babban mutum kamar Abban mu daya nuna mai kyama ko tsana kan kawai don matsala irin ta iyayyenshi dake binne shekara da shekaru.      Motsinshi da Dije taji na fitowanshi daga dakin ya nufi bandakin yasa ta fitowa tana fadin Amadi kana gidan nan dama ashe ?     Eh kawai ya amsa mata ba tare daya tsaya ba a cikin dakusheshen muryan shi da kuka yasashi narkewa hakan lokaci guda.     Kallon mamaki da zargin ko baida lafiyane ta tsaya take mashi lokaci guda tana tsaye har ya fito ya tsuguna daga can ya samu wuri ya fara alwala a gurguje.    Ya gama ya mike tana fadin abincin ka na nan tun dazun a daki me yuyuwa ma yanzu yayi sanyi don tunda sauran rana nayishi barshi Dije yau banjin yunwa ya fada yana wucewa ba tare daya dan tsaya magana da itaba yadda suka saba idan ya ganta tsaye.    Ya shige dakin shi ya fara sallah komawa Dije tayi dakinta cike da zarginshi a zuciyar ta can taji ya rufo kofan gidan su kafin taji yana rufo kofan dakin nasa kuma haka yasa ta mike ta fito har zuwa kofan shi tana fadin.    Amadi haka zaka kwanta ba tare da kaci wani abu a cikinka ba ka kwana hakana da yunwa ka fito ko shayi ka fita ka samo kasha son babu ruwan zafi a gidan nan yanzu.      Dije bana iya cin komai jeki kwanta kawai dare yayi yanzu karfe tara saura zakace darene yanzu meke damun kane yau din nan wai ?    Dije ta tambaya daga waje duk da yaji muryanta hakan baisa ya bude kofanba bai kuma bata amsa ba yayi shiru kamar bai cikin dakin a lokacin.     Munaga rasul Dije ta fada ta juya tana cigaba da fadin yaron nan kanshi daya kuwa yau din nan yaro haka kamar wanda yai gamo a hanya Allah ka cecemu ta fada ta koma dakinta.    Gidan yai shiru kowa na part din shi tare da yaran shi don ni tun safe ban leko waje ba ina dakina kwance hjy tsohuwa ce ta shigo tare da wasu jikokinta mata biyu da suka rakota.    A ka,ida dakin ummah takan fara shiga kafin ta koma dakin mama ta zauna har zuwa lokacin da zata bar gidan idan tazo gidan mu.    Saidai hakan bai hana ummah hidima da zuwan nata zata girka mata abinci koda batayi niyar yin girki na musanman ba a ranan zatayi hidima sosai wa hjyn akai mata can falon mama inda zasu zube kowa yaci yasha wani lokacin ma bata sanin tafiyan su saidai taji cewa sun wuce.     Ta shigo bata ko zauna bata ko zauna ba a ranan a tsatsaye suka gaisa da ummah din ta juya ta fita zuwa dakin hjy karima tunda yanzu sun zama su uku a gidan .    A can ma din bata tsaya ba ta fito ta zarce dakin hjy mama a can suka zauna kowa yaci gaba da harkokin shi a part dinshi sai zuwa ranane mama ta aiko wai idan ummah ta gama abinci a kawo wa hjy.     Ummah tace abinci yau banyi girki ba don yaran ma basu zauna ba basu gida komai ban girkaba a part din nan saida yamma zanyi abinci.   Ai ana fadi mama tace zancen banza ke nan ki koma kice mata bata sanda cewa a nan hjy zata wuni bane bata girka mata abinci ba.    Yarinyar ta dawo ta fadawa ummah sakon mama tace jeki kicewa maimuna nace ko ta manta itace da girki yau ne ?     Nan mama ta harzuka wai ita ummah zata aikowa maganan banza har ta aiko mata da wani zancen haka ita ummah ta aika mata da zancen zafi.    Har yakai hjy din ta mike wai zata tafi gida tunda ba a san darajanta ba a gidan Abba din dama inda mama keson akai ke nan Aisha ce ta samu Abba a fslon shi hankali tashe take fada mai abinda ke faruwa a cikin gidan namu.     Mamaki sosai Abba yayi da jin hakan a take ya tarasu a falon shi ranshi bace yake sosai jin cewa wai unmade taki girjawa hjy abinci ga kuma fitina da ya biyo baya.    Har hjy din duk suna falo da matanshi ukun suna shigowa daya bayan daya kusan ummah ce ta shigo a karshe yanayinta kawai zaka kalla kasan bata jin dadin jikinta ko tana cikin damuwa a lokacin.    Wuri ta samu ta zauna kamar yadda kowa yake zaune a falon kafin zuwa can Abba din yace ya akayi har hjy tazon gidan nan ace an rasa wanda zai bata abinci a cikin ku.    Falon ya dauki shiru ya kalli mama kafin ya juya aurin su ummah da hjy karima yace tambayan ku nakeyi fa kun min shiru ?     Ai gata nan a tambayeta don ita ta saba girkawa idan tazo wake nan Abba yace wake nan fa ya tanbayi mama din da tayi magana tace.    Hjy salma na aika a kawowa hjy abinci ta aiko min da maganan banza ta karasa cikin niba ruwana fa don idan mutum yana takama da iya shege ne saimu zuba.    Wai tsaya hjy maimuna mu zuba din nan da kike fada hannun ki ya rikene kin kasa zubawan ko kayan nauyi kika dauka da kika kasa ajewa ki zuba din.   Kai hjy maimuna kiji tsoron Allah don raini ai kinsan cewa yau kece da girki don kawai ki hanani kwanciyan hankali zakiyi kokarin hadani da hjy ?    Amma kece ai kika saba girka mata idan tazo gidan nan dama mama ta fada amma kinsan sai idan nike da girki har in tazo gidan nan lalai ya zama wajibi na zubawa hjy girki kan .   Kuka tsohuwar ta saka wai an raina mata wayo ana wullakanta ta a gidan danta sai maganganu take sakewa wanda ke nuna aibanta ummah.     Haba haba mama wanan maganan baikai can ba ai maganace da amsanta a zahiri ga maigirki a yau ta kasa girka abinci ta baki ta ya wata zata dauko ta kawo maki alhalin mama a wurinta fa kika sauka da kikazo gidan nan koda ace ba ita bace ya kamata ace ta girka maki tunda kina side dinta hjy karima ta fada.    Wana  naga kina son ki shige mun hanci da kudundune a cikin gidan nan don tun zuwan ki idan zance ya taso sai kiyi kokarin dora min laifin a kaina ?   Eh don gaskiya dayace a fade idan hakan ya taso haba wanan boyar Allah meye laifinta gidan nan kan wanan abubuwan yanzu ?     Kujeku na gode da wanan abinda kukai min din mahaifiyata dani kun nuna min bamu da daraja a idanun ku a, a Alh wanan zance sai idan anso a jashi amma wanan ga gaskiya a fili kowa ya sani .   Akan me zamu bar hjy bamu bata abinci ba don ba wanda zai zata cewa tun shigowanta gidan nan ba a girka mata abinci ba a gin hjy maimuna duk hjy karima ke fadan haka karshe saita mike tsaye tana fadin Allah ya huci zuciyar ku wanan zancen maimunace mai laifin haka ko gaba  kuliya akaje.    Zan tafi don wana  maganan bai shafeni ba ni yanzu kuma naga ba a son gaskiya a cikin zancen don haka na barku lafiya hjy kiyi hakkuri .     Kowa ya bita da ido don ganin yadda tasa kai ta fice daga falon ba tare da Abba ya basu umurnin yin hakan ko nauyi yadda tayi din Abba yaji ya kira sunan ta da karima karki sake ki kara daga kafa a wurin nan.    Alh dole in tafi don naga fadan rashin gaskiya kakesonyi wurin nan a yanzu  don ko gidan kuliya yana son hujja ga sharia ai.   Ta koma ta zauna tana cicika saman kujeran Abba ya kallesu yace ya zama wajibi ga kowan ku daga yanzu duk ranan da hjy tazo gidan nan kowa ya girka mata abinci a kai mata final ku tashi ku ban wuri banson karin wani zance kuma.     Amma mama ta fada ya daga mata hannu yana fadin nace banson wani zance kuma ku fice min zanyi magana da hjy.     Hjy kiyi hakkuri hjy karima ta fada ta fice daga falon sai ummah ta dan zaudo daga saman kujeran da take zaune tace hjy don Allah ki yafe muna munyi kuskure hakan ba zai sake faruwa ba itama ta fice.    Sai mama dake mikewa tana fadin na kula matan nan da sunana tashigo gidan nan wallahi sai nasa tayi nadama  fadowa rayuwata a cikin gidan nan.    Keko kikan fara maganan ki yanzu me kikaji ance dake kan abinda ta fada hjy tsohuwa ta fada sai Abba ya amsa da zandai fada din hjy yanzu ina dadin irin wanan abinda maimuna tayi ai gaskiya karima ta fada yanzu.   Kece da girki a dakin ki kuma hjy take zaune amma kin kasa girka mata abinda zataci don shashanci kuma in anyi magana hjy ki tare kada a fadi.    To ai yanzu ga yar gaskiyan nan ta fadakar dakai gaskiyan ko da hakan wanan saurin sanyin hali irim naka har kazo ka sake ta juyama gida daga kai har iyalin ka kuna kallo.    Hjy wanan zancen gaskiyane ta fada wanan itace mai laifi kuma baki son a fadi saiki tare mata to kiyi hankali da karima  da kike gani haka sosai don nasan da tana daga maki kafane akan komai .    Ficewa tayi bata tsaya jin karshem maganan shiba don bai goyi bayanta ta dau fushi dashi tana kulla hjy karima a zuciyar ta don in batayi hankali zata iya kafa gwaunatinta a wurin Abba don irin haka.    Shara ya tashi dashi yana gyaran gida da kone konen da bai samu tsayawa  yayi masu gyaran sallaba a gidan yazo kusa don haka ysu ya tashi da gyare gyaren cikin gidan nasu.    Yazo gurin wanan  tumfafiyan daya fito masu a gefen katangan gidasu din ta cikin gidan nasu mikewa yayi tsaye daga duken da yake ya zubawa tsiron ido yana mamakin saurin girman da dan icen yayi lokaci guda.    Wurin randan ruwansu ya nufa ya fara debo ruwa yana zubawa icen zakace an shuka icen ne ana son yayi girma a lokacin .    Dijece ta fito daga dakinta da niyar tambayanshi ya jikin nasa saidai tana  fitowan idonta yai tozali dashi a wurin tumfafiya ya kura mai idanu kaman yana nazarin tsiron ne.   Amadi kardai kuma cireshi kake sonyi tanan din bayan ka barshi ya girma ya gama hayayyefa a gidan nan koda ka cireshi a nan din indai tumfafiyace komai daren dadewa wata rana sai ya dawo gidan nan kuma .    Ba cireshi zanyi ba ruwa nake zuba mashi don an dade da dauke ruwan sama baya samun ruwa murmushi ta sake tare da fadin kaiya yaro dai yarone .   Kai in banda abinka Amadi kataba jin wanda yaiwa tumfafiya banruwa don ya tofu da kyawo shida keda ruwan Allah a jikinshi ina ruwanshi da wani ruwa can.     Ganin bai kulata ba yaci gaba da harkokin gaban shi yasa Dije din barin wurin ta nufi wurin murhunta don ta hura wuta ta dora masu abin kari a gidan.    Ta gwama dan icen daya saura masu a gidan cikin wuta na karshen take sakawa a murhun mafarkin icen da mutumin dayazo yana mata sallama a na gobe za a fara azumi ya fado mata a rai.    Zubur ta dago daga duken da take ta juyo tana kallon jikin nata dake aiki kafin ta kai kallonta gun uwargarke dake tsaye tana kiwon ta sosai gashin jikinta ya dawo yayi kyau yanzu.    Ta zama cikkakiyar akuyan data koshi da kiwo tayi bulbul da ita a yanzu kodai sai kuma ta kasa fadan abindake kasan zuciyar nata .    Aikin dake gabanta ta fara bayan ta hura wuta ta dauko tukunya ta dora saman murhun ruwa ta debo ta zuba cikin tukunyan daki ta nufa ta dauko Sauran tuwon jiya daya rage masu gidan ta dawo ta zauna tana barewa.    Har lokacin mafalkin na mata yawo a zuciyarta tana kokarin tuno da abinda bakon fuskan cikin mafalinta ya fada a ranan saidai ta kasa gin hakan .    Bata jin zata iya tunawa da abin saidai nan gaba kila muryan Amadine ke fadin yanzu idan mutum yace zai tafi garin mahaifina nawa zai kashe kudin mota Dije ?     Kaita dago tana mashi kallon mamaki don jin abinda ya fada din a lokacin cikin mamaki ta sake tambaysn shi Manbila fa kace Amadi ?

Post a Comment for "TUMFAFIYA 24"