Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

TUMFAFIYA 8

 
  1️8️⃣ AL AZIZ,,,,,,,,,,   ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI K ARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,        Allah ya taimakeni ba a wani taru sosai ba a makaranta amma haka nake ganin kamar idon kowa na kaina lokacin suna kallona haka na fito na rufo motana a hankali na tako yadda na saba tafiya a nutse zuwa department din mu.     Akwai mutane saidai ba sosai ba don safiyane sosai lokacin kamar yadda na saba shiga da siriryar sallama haka na shigo na dan gaisa da na kusa da ida na zauna daga haka na zaro takarduna na fara karatu.     Can na tuno da lecture din da ban samu attendedi ba jiyan da rana lokacin da abin ya sameni don dolene na koma gida saboda bana cikin hayacina lokacin.     Dago kai nayi na kalli ta gefena ina fadin don Allah yar uwa jiya an dauki attendaces ne na rana wani iri tayi far da idanu tana fadin ke baki ajine lokacin da aka dauka din.   Kaina girgiza tare da fadin banda lafiya na tafi gida ban samu daukan darasin rana ba jiya din kaita jijiga min tana fadin jandi kina da aiki ga wanan malamin da baijin Allah tana fadan haka ta juya ta barni cikin damuwa.    Har muka fito daga lectures din ina tunanen rashin yin attendance da ban samu yiba don nasan halin lectural din da zafin kai sosai da a hankalina nake ba abinda zaisa na yarda naje gida a lokacin.     Tun daga nisa na hango mutum yana bin motan da kallon mamaki saidai baiyi kama da dan makaranta ba shi don kayan jikinshi da suke kode duba ga yadda yan makaranta ke shigowa cikin kure adaka ko wani lokaci ba mazanba ba mata ba.     A hankali nake takowa cikin mamakin me yake nema a wurin motan daga bayan shi na tsaya ina mai sallama ya juyo yana amsa min tare da fadin ashe kin samu shigowa yau din ?    To yaya jikin naki banda waya naso na karbi layin mahaifiyar ki naji yadda kika kara ji sai rashin waya ya hana hakan saidai ki kula tunda kina da lalura koda kinji wani abu zaki iya nemana ina Science department UG four.    Sake kallon shi nayi ina mamaki a raina dan makarantane wai wanan din dama ashe ga yadda yake nunawa shine wanda ya kaini gida jiya ke nan nan na fara kokarin tuno da abinda ya faru jiya din tabas shine wanda ya tsaya ya kare min mutuncina a jiyan don ummah ta danyi min bayani kamar yadda yai mata shima.   Saida na nunashi da yatsa nace Kaine kaine dama ka taimaka min jiya nagode gida zaki tafine ya fada yana kawar da fuska gefe daya kamar baison kallona.    No mosque zan tafi nayi sallah daga nan saina tafi wurin malamin mu ya shigo jiya bana nan ya dauki attendance kuma baida sauki mutumin.     Wani department kike ya tambaya wanan karon yana kallona apply chemistry nake karantawa na bashi amsa kai tsaye.     Ok department din mu daya ke nan dake idan kina da matsala zaki iya nemana duk da ba wani sani nayi sosai ba kan haka.    Ki dai kula da addua kafin ki fito gida da kuma lokacin da zaki shiga school din don yanzu mutane sun baci sosai.   Saboda haka don Allah idan kinji alama ciwo zai taso ki samu wuri ki dinga natsuwa don jiya badon Allah ya gyara ba zaki iya halaka kanki a motan nan.    Don a yanzu taimako yayi karanci sai gulma dasa ido ga al,umma ana yadawa a duniya don mutane yanzu suna tsoron taimako saboda shiga fitinan jami,an tsaro.     Ki kula sosai saboda kasancewar ki mace don mutane basu da gaskiya yanzu yana kaiwa nan ya dago yace na barki lafiya dama motan nan da na gani nayi mamakin ganin kin shigo kuma school yau duba ga yadda na kaiki gida jiya a wani yanayi can.     Duk wanan bayanin da yakeyi sai kallon fuskanshi nakeyi ina son intuna inda nasan fuskan nasa saidai na kasa tuna hakan saida ya juya zai tafine na tuno ai shine wanan guy din na shagon abinci dana ga anaciwa mutunci har naji haushi matar a raina na taimakeshi.     Kayan jikinshi na kalla duk sun kode saboda tsufa ga takalman kafan shi duk sun kode sunyi wani baki dasu da ganin shi  zagaka gane shi din fakirine na gaske tun daga duba ga yanayin shi kuma a haka yake rayuwa cikin diyan mayan da masu hali bai damu ba.    Wani irin tausayin shi naji ya shigeni lokaci guda sai naji matukar sanyin jiki gashi dai da halin kirki irin wanda ake son samun dan musulmi dashi .     Amma rashin gata yasa ya koma kamar mahaukaci a ciki mutane har wasu na tafiya suna kallo inda muke ganin na tsaya dashi ina magana ashe sam baya shiga harkan kowane a makarantar.  Shine da aka ganmu tare suke mamakin hakan don bai kula kowa shi kadai yake rayuwan shi gashi dai kamar shiya halittawa kanshi kwakwalwan shi don hakane malamai suke ji dashi sosai.    Naje sallah na dade a masallacin zaune kafin na kalli lokaci na fito saidai na kasa zuwa kai korafina wurin wanan malamin don ko naje ance baya duban mutane.    Don hakane na ba kaina shawaran na kyaleshi kawai zaifi min rufin asiri danaje ya tozartani don mutum ne shi mai ji da kanshi da zamani yana amfani da daman da Allah ya bashi yana wullakanta mutane ta hakan.     Ummah tayi kokarin buyewa kowa halinda yarta ke ciki a lokacin ba don komai sai don rsshin yarda da kowa a yanzu tunda ba yan uwane gareta ba a nan sai abokan arziki da dangin miji.     Suma din kuma wasune suke hurdan arziki da ita don sunfi bada karfi a bangaren mama dama haka yake a al,adan yanzu duk inda miji yafi karfi can mutane ke dosa don neman abin duniya da gulma.    Ko wanan maganin da Tani ta karbo mata saita koma tana tsoron amfani dashi don yanzu mutum ba abin saurin yarda bane tsakaninka dashi haka kai tsaye.     Wanan yasa take wasi wasin ko ta mayarwa Tani din da kayantane ta fallafawa ubangiji lamarin su don Allah shine mai yin yadda yaso da bawansa haka kuma bawa baya kaucewa kaddaransa tun rangini ranan zane.     To amma kuma zaman ta da Tani na amana ne don hjy tasha kullace tani din yadda tani tabata gaskiya da amana duk yadda hjy taso taja ra,ayinta.    Amma Tani din taki yarda da hakan har saida hjy ta kulafuci tani din taso ta tasa a kori tani din daga gidan saida ummah ta fahinci me mama ke nufi ta nuna jajircewan ta kan hakan.    Tun lokacin sai gaisuwane da sannu ke hadasu da hjy ddin tana taka tsatsan da lamarin mama din a gidan harta shigo ta fita da yamma tana part din ummah zaune.    Wanan gaskiyan da amana na Tani din yasa ummah kara yarda da lamarinta da har yanzun din ma hankalin ummah din ya kwanta da maganin data kawo wanda ita tsakani da Allah ta amsawa ummah din shi.     Dauka tayi ta kara dubawa kafin ta mike ta fito zuwa kitchen dashi a hannun ta  Tani din tana tsame shikafan data wanke a ruwa taji shigowan ummah din yasata juyowa lokaci guda.    Ummah ce kofa rike da ledan maganin data kawo mata a hannun ta idon tani ya sauka kan ledan gabantane ya fadi take fadin  hjy lafiya dai ko ?     Lafiya Tani ummah ta dan sake murmushi tana takowa cikin kitchen din tana fadin kinga Tani ba zan boye maki ba da farko ban dauki wana maganin da kika kawo min dazun ba.    Amma yanzun nayi tunane na aminta dake Tani duba da yadda mukai sabo da amana kuma a tsakanin mu dake nasan kinyi wanan ne da niyar taimakona nida diyana.    Don sanin halin rayuwan da muke ciki a gidan nan daba kowa yasan da hakan ba sai yan tsiraru suka sanda hakan a garemu.    Allah sarki hjy yadda kika rikeni nida diyana da yan uwana meye ba zan iya maki ba a rayuwa wallahi Allah jiya na kwana da tunanen uwar dakina a raina don kiri kiri ake son a illanta maki zurian ki nan a gidan nan.    Wanan yasa nayi asubancin zuwa gidan yaron nan na jiya da yai min kwatance shine nayi asubancin zuwa unguwar na kuma gane gidan nasu.    Saidai a lokacin nayi rashin sa, a don shi ya fito zai tafi makaranta a lokacin shine ya hadani da kakarshi ta kaini wurin wani dattiju a nan unguwar tasu.     Ni kuma sai ban boye mai komai na irin matsalan da kuke fuskanta a gidan nan shine yaba da wanan yace a kawo maku kuyi amfani dashi mugu na fili dana boye saidai aniyar shi ta koma mai .    Watau aniya makomiya ke nan yadaice kuyi amfani dashi kamar yadda yace ayi in sha Allah ya wadatar daku saida hjy naga kamar baki yarda dani ba kan hakan ?    Saidai banga laifin hakan ba tunda ba da sanin ki najeni ba amma idan kina wani shakku ga hakan kina iya sa uwar dakina ta binciko maki wanan wurin yaron jiya din tunda suna ganin juna wata kila dashi din a makarantar su.     Haba Tani ba zancen rashin yarda bane ko wani abu yanzu tsakanin mu don mun zama daya daku yanzu ai bake ba ko wani naki bazai cuta min ba a yanzu.     Zuwa nayi ki kara min bayanin yadda zamuyi amfani dasu don dazun sam ban fahinceki ba koda kike min bayanin su a lolacin.     Karban ledan tayi ta warwale ta fara yiwa ummah bayanin yadda akace kafinta dago tana fadin kaidai kada kaiwa wani sheri kadai tsare jikinka yadda ko yayi saidai ya koma kan maishi don ansan asiri gaskiyace tunda yaci Annabawan Allah.     Ina shigowa gidan namu mamace naci karo da ita a waje da alama fita zatayi lokacin mota na fito na rufe na nufi inda suke suna magana da driver gidan mu koshi zai kaita unguwar ban sani ba lokacin.   Fuskana dauke da fara na nufi inda suke din saidai nayi mamakin ganin yadda mama din ta daure min fuska tam babu ko yar fara,a a fuskanta gareni.    Ganin hakan yasa na rage nawa fara,an dake fuskana na karasa ina fadim mama lafiya dai ko ko fita zakiyi ne na tambayeta lokacin ta juyo gareni tana fadin.    Eh zan fitane har kun dawo tana kokatin shiga mota na bita da kallon mamaki daga hakan bata kara juyowa inda nake tsaye ba din sukaja mota suka tafi.     Ajiyan zuciya na sauke tare da juyawa zuwa cikin gidan namu zuciyana da tunanen wanan sauyin da nake gani a gun mama din yanzu.     Da sallama a bakina na shiga part din mu saidai babu kowa a falon mu lokacin haka yasa na wuce zuwa bedroom dina na fara kwabe kayan jikina.     Sauyawa nayi zuwa wani dogon riga kafin na sake fitowa zuwa dakin ummah don na gaida ita kuma tasan na dawo a lokacin ban son ta shigo ta same ni a dakina.     Zan shiga dakin ke nan naji motsinta a falo na juya zuwa falon na sameta a nan ummah na kira sunan ta tajuyo tana fadin ashe kin dawo ke nan to yaya kan naki bai tashi ba acan yau ko ?     A, a ummah saidai nan gefe daya danaji ya daure min kamar zai fara min ciwo din lokacin saina shaka wanan maganin na jiya a masalaci naji ya bari .    Kikuma dinga yin addua kina tofawa ai haka wanan yace min yau da muka hadu dashi a school yau din ma kun hadu ke nan dashi ummah ta tambayeni ?     Eh yazo wurin motana yana duba da mamakin har naji sauki nafito yau makaranta shine yake fadin na kula da jikina da kuma addua don ni mace ce daba don Allah ya kawoshi jiya ba baisan yadda zamuyi ba a wurin.    Gaskiya ya fada addua ya dace bawa ya tsare a kullun don ita kariyace ga mumuni don haka ki kara tsare addua sosai ya fada maki gaskiyan da nima iya nan zan iya fada maki ai.    Ummah wai meya samu mamane naga zata fita ranta a bace ina gaida ita bata tsaya ta amsa min ba tana dauke kai gareni kamar nayi mata wani laifi.    Yanzun nan zata fita da yamman nan haka ban jin nisa zata tafi don bata faye fita haka da yamma ba saidai in wani wuri mai muhinmancin zata tafi hakan yanzu a wanan lokacin.     Amma ai mama bata daure min fuska haka irin yadda tamin yau din nan idan ta dawo anjima zan sameta a part din ta ai na gani..     Kice mata me idan kinje ki barta kawai idan wanan zaikaiki wurinta  saidai idan wani abin zai kaiki gunta ban hana ba amma kada ki mata zancen hakan koda wasa.   Kaina gyada mata alaman amsawa kafin na gyara zama ina tunanen abinda ummah ta fada daga haka mikewa tayi zuwa dakin ta a lokacin kannena suka shigo sun dawo daga islamiya.   Nan nake tar dasu har akai kiran magariba muka watse zuwa sallah ban fito ba sai bayan salllah isha,i da muka fito na samu ummah na waya da Abban mu lokacin naji tana fadin da sauki sosai don yau din ma har taje schoon din ai kuma ba abinda ya faru.    Banji meyace ba tadai miko min wayan na karba a hannunta muryan Abbane ke kiran sunana na karba mashi yake tambayana ya jiki ya karatu na amsa da naji sauki.     Muka dan taba hira yace in ba ummah din waya a lokacin na mike zuwa part din mama da naji dawowanta ana bude mata get ina sallah isha,i a lokacin.     Dukkan su basuyi zaton shigowa na part din ba a wanan lokacin sai ganina kwatsam da sukayi na shigo hakan yasa da sauri naga Aisha tana kokarin boye wani jarka karami dake dauke da wani ruwan rubutu   a bayan .   Nayi kamar banga haka ba lokacin wurin mama na nufa a sake ina fadjn mama ashe kin dawa andawo lafiya ya gajiya ta amsa a cikin dan darare da fadin lafiya tana kawar da kai gareni.   Nan ta barni zaune tankar ba mama ba a ranan yadda ta nuna min din tankar bata san dani ba zaune a wurin ta kama harkan gabanta ta fita batuna ga baki daya.     Saida na gaji da zama na mike nake fadin mama zan tafi dama na shigo na gaida kene don dazun bamu gaisa sosai ba zaki fita.   Ta dan juyo gareni tana fadin OK zaki tafi zarah saida safe ke nan wani irin ba dadi naji a rain haka naja kafana na fice daga part din mama ba tare da kowa ya kulani ba lokacin.    Ina shiga part din duk suna falon a lokacin ummah tana basu wani abu da bansan ko meye ba na daiga yaran na bata fuskansu alama  abin da ake basu baida dadi ke nan a baki.    Kokarin shiga dakina nakeyi a lokacin naji muryan ummah tana fadin maamah oya zo nan ki karbi naki kisha .    Fuska na bata daga inda nake tsaye din ina fadin ummah bana sha a koshe nake na juya zanci gaba da tafiya wanan din ba wani abu bane maganine na ciwon zazzabi kawai.    Ummah oya zoki karba ban son korafi Anty zarah sai kinsha dole ummah tace don maganin ba dadi kuma kanina ya fadi daga gefen ummah inda yake zaune.    Dole nazo na zauna a gaban ummah ta debo maganin a wani silver ta miko min tare da fadin oya yi bissimillah kisha.    Karba nayi ina bissimillah nakai bakina ba dadi abin amma haka na daure nasha maganin kafin ummah ta umurce ni da naci abinci.   Na tsakwara na tashi zuwa lokacin duk jikina ya mutu tashi nayi zuwa dakina ummah ta dubeni tana fadin saida kika je gun maman taku din ke nan ko ?   Kallon ummah nayi a dan shagwabe kafin na gyada kai alaman naje amma ban yi zancen komai da ita ba ai itama din kuma ko kulani batayi har yaranta  

Post a Comment for "TUMFAFIYA 8"