Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

ABULLE ANNOBA COMPLETE HAUSA NOVEL

[8/14, 11:33 AM] Mss Flower: ♀️♀️ *ABULLE ANNOBA COMPLETE HAUSA NOVEL*♀️♀️ (Sanadin neman haihuwa) _Na_ _*Mss Flower*_ _&_ _*Mrs Abdool*_ بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *____________________________________* Yarinya ceh 'yar kimanin shekara goma sha biyu tana tafe tana 'ballar rake, hannunta na hagu na bisa kanta tana susar dan da'kwalin kanta dake d'auke da wani kitso wanda har ya 'bace da wuya ka ke gane kan akwai kitson, tsayawa tayi wajen mai gasa kaza, ta jima tana 'kare ma kajin kallo sanan ta dubi wata dan'kwaleliya jajajur tace "Halliru bani wanan" ta ri'ke 'kugu tana yatsina fuska Idon Halliru daya ciko da 'kwalla ya zubamata yana kallonta "Halliru ko bazaka bani ba ne, na wuce" ta fad'a tana jijjiga 'kugu "A'a Abulle, ni na isa" ya fad'a yana jawo ba'kar leda ga idanuwansa sun cika da 'kwalla, fuskarnan tamau kamar an masa bushara da mutuwa, kar'ba Abulle tayi ta wuce tana shilla ledar "Allah kayi mana maganin wanan annoba" Halliru ya fad'a chan 'kasan ma'koshi Abulle da ta wucesa ta juyo ta tamke fuska sanan tace "Halliru nafa ji ka, ka 'batamin rai wallahi angama cin kazarka a garin nan" ta 'karashe tana juyawa tana tsalle tsalle irin na yara "Abulle Ina yini" cewar wani matashin saurayi har yana d'an rage tsayi "Iya gidan uwarka shi kwanan, hege mai siffar ra'kumi" tana she'kewa da dariya, shi dai bai ce da ita komai ba harta yi wucewarta tana cilla kazarta Zugar samari neh zasu 'kwallon 'kafa suka wucewa ta inda Abulle ke tahowa, ai ko da Abulle ta hangosu sai ta tsaya ta hard'e hannayenta a 'kirji ta jingina jikin bishiya tana jiran 'karasowarsu, har sun gitta ta tace "ku kudawo" Aikuwa nan suka fara dawowa suka zo gabanta kowa na fad'in "Abulle barka da yamma" Idanunta neh ya sauka kan wani saurayi daya murtuke fuska, ai kuwa tace " d'an Talle kai hala dai kashin shanu uwarka taci matsayin abinci kan a haifeka?" "Uwarki dai" d'an Talle ya fad'a, ai nan da nan samarin suka fara matsawa daga kusada shi suna ra'bewa gefe. Dariya Abulle ta kwashe da ita sanan tace " jar uba, dama ance mai cinikin shan zuma, in reshe bai karye dashi ba watarana 'kwarya ta fashe masa, zo nan dan ubanka" ta fad'a tana masa alama da hannu Tsaki d'an Talle yayi ya juya ya fara tafiyarsa, aikuwa taku biyu yayi yajisa timmm a 'kasa sanan wata guguwa tayo baya dashi sai gashi gurfane gaban Abulle, 'kafarta mai uban nauyi kamar ta doki goma ta d'ora bisa 'kafarsa ai saukaji 'bass Kuka d'an Talle ya fara yana 'ko'karin janye sililiyar 'kafar Abulle daga tasa 'kafar amma ya kasa, ya jigata sosae duk ya had'a hawaye da majina sanan Abulle ta d'agasa tace " zaka kuma neh" sanan ta yi jifa dashi jikin bishiya, aikuwa ya rushe da kuka itakuma tayi tafiyarta tana tsalle tsallenta "Abulle an fito, barka da yamma" cewar wani magidanci da keta faman jan akuyarsa tana tirjewa "Lahiya lau Isiyaku, aikuwa akuyan nan zatayi mai" Abulle ta fad'a Cikin in ina idanuwansa na kawo ruwa yace " wallahi kuwa, jiya na kaita asibitin binni aka ceh tanada Corona, shine zan ke'banceta gudun kada ta shafawa mutane" ya fad'a 'kwalla na zubomasa "Allah sarki, ai waraka ma tazo" ta fad'a tana tsalle "Iyyehhh!" Ya fad'a yana 'kwalalo ido "Eh, bari zan ke'bance maka ita a cikina" ta fad'a tana yashe baki "Abulle dan All...." Bai 'karasa tayi masa wani mugun kallo, ai sai ya saki akuyar "Toh Allah bamu alheri, Allah i yaye Corona inta shafeku" ta fad'a sanan ta maida dubanta kan akuya tace " taho muje" aikuwa Akuya ta fara binta zungwi zungwi   "Hansatu!!!" Abulle ta 'kwala kira, ai da sauri wadda aka kira Hansatu ta fito tana d'aura zani, wadda kallo d'aya zaka mata kasan itace mahaifiyar Abulle "Abulle gani" Mahaifiyarta ta fad'a "Hansatu ungo akuya ki yanka, ki fed'e kiyi mana dabge" cewar Abulle "Abulle ina kika samo akuya" Hansatu ta fad'a "Bani akayi" Abulle ta ansa tana janyo wani daro da shinkafar ciki tayi rabin kwano ta d'ora kazarta ta fara ci "Abulle sai dai a jira Malam yazo ya yanka" Hansatu ta fad'a "Hansatu Qur'ani sai kin yankata yanzu" cewar Abulle Aikuwa Hansatu bata kuma 'bata lokaci ba, ta hau jan akuya qiiiiii.......   Mss Flower & Mrs Abdool _MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA SIYAN LITTAFIN NAN_ *NAIRA 300 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA ILMANTUWA* _ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS, SAI KIYI SCREENSHOT KI TURO TA WANAN LAYIN 08167888934. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU❤️❤️❤️ [8/14, 11:33 AM] Mss Flower: ♀️♀️ *ABULLE ANNOBA*♀️♀️ (Sanadin neman haihuwa) _Na_ _*Mss Flower*_ _&_ _*Mrs Abdool*_ بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *____________________________________* *NOTICE!!!* _Bisa ro'kon readers a rage kud'in, toh mun amsa ya dawo *200* sai ku hanzarta kada ayi babu ku_ _MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA SIYAN LITTAFIN NAN_ *NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA ILMANTUWA* _ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU❤️❤️❤️   *02* Hansatu ce sai faman jan akuya take, akuya kam sai tirjewa take tana 'ko'karin kada Hansatu da ta had'a zufa kashar'bam ga hawaye dake d'igo mata Abulle da keta had'ar shinkafa da kaza sai dariya take 'babbakawa kamar ta'babbiya "Hansatu zata tad'iyeki" Abulle ta fad'a tana she'kewa da dariya, aikuwa rufe bakinta keda wuya Hansatu ta fad'i sai ji kake timmmmm "Wayyoni wayyo Allah, Abulle kwi'bina ya karye, dan Allah ki rabani da yankan akuyar nan" ta 'karashe tana 'bere baki da kuka "Hansatu in baki yanka akuyar nan ba, kwarankwatsa kin bar cin nama" ta fad'a tana sakin mahaukaciyar dariya tana buga 'kasa Wata yarinya ce ta shigo gidan a guje tana sosa jikinta, zubewa tayi gaban Abulle tace " ranki ya dad'e yanzu daga gida nake, naji Baba na sanar da Iya wai za'ayi taron malamai ranar juma'a a miki addu'a a rakaki bakin gari" ta 'karashe tana 'kwalla "Ke Bintalo meye na kuka, sai kace iya korar tawa zasuyi, yanzu ki tashi kije ki kiran shi uban naki da mai gari, kice ina jiransu yanzu" Abulle ta fad'a "Angama ranki ya dad'e, yawwa wata ya kusan 'karshe ba kud'i a asusu da za'ayiwa ma'aikata albashi" cewar Bintalo "Haka neh fa, bari nagama da mai gari da ubanki, sai mu fito siyarda maganin mata" Abulle ta fad'a "Angama ranki ya dad'e, bari na 'karasa na isar da sa'konki" tana ficewa "Hansatu bari haka, dawo zauna uwata, ai baki kuka tunda kin haifi Abulle" ta fad'a Hansatu da zufa suka ji'kata kamar an watsa mata 'karamin bokiti ta zauna tana haki, ta jima kafin tace "Abulle dan Allah ki daina saida kayan matan nan, wallahi kina zaluntar mata, ki duba wasu fa basuda kud'in siya, ki tausaya musu" "Allah sarki, Hansatu sai ki min bayani, kema kinasan maganin mata na amma bakida kud'i, bari zan baki in aka daka kyauta" cewar Abulle "Abulle kwarankwatsa ni ba so nake ba, ri'ke abinki Allah kawo kasuwa" Hansatu ta fad'a "Hansatu Qur'ani tunda kika tanka sai kin kar'ba, na matsi zan baki kuma, in bakiyi ba kinsan sauran" Abulle ta fad'a   Mai gari da tawagarsa tunda aka fad'a masa kiran Abulle suka fito, sun kawo dai dai 'kofar gidan Bintalo ta tintsire da dariya tace " yau za'a ci 'kwal uba, ba dai korar Abulle zakuyi ba" Mai gari baya yayi yana tangal tangal aikuwa cikin sa'a babbar riga ta tad'iyesa sai kuwa ya fad'i timmm a 'kasa, bai damu da mummunar fad'uwar da yayi ba ya nufi Bintalo yana cewa " dan darajar Allah waya sanar da Abulle" duk ya rikice "Zakayi bayani ne" Bintalo ta fad'a tana shigewa ciki da gudu. Mai gari da tawagarsa nan kowa ido ya kawo 'kwalla, haka suka kutsa kai cikin gidansu Abulle, Abulle dake hakimce bisa tirmi ta she'ke da dariya tace " ko yanzu zaku koran neh?" Mai gari zubewa yayi 'kwalla ta 'ballemasa yana fad'in " ranki ya dad'e dan Allah kimin rai, wallahi jita jita ce, ba gaskiya ba, kada ki d'auki zigar ma'kiya" ya 'karashe yana ri'ke sililiyar 'kafarta "Jar uba, ka daiyi nadama amma ba sheri aka maka ba" Abulle ta fad'a tana girgiza "Iyyehh, eh nayi nadama" ya fad'a yana fyace majina Sallamar mahaifin Abulle ne yasanya hankulansu ya koma garesa, cikin sauri ya nufi mai gari dake shararar 'kwalla ya zube yana gaishe shi, sanan ya maida dubansa ga Abulle yace " Abulle mai ke faruwa" "Shirin korata daga garinsa ikeyi" ta 'karashe tana yatsina "Wa!!, Ni wallahi ban isa ba" Mai gari ya fad'a yana 'bere baki "Abulle barshi ya tafi dan Allah" Mahaifinta ya fad'a "Isuwalle zaka kar'ba masa hukuncin ne" ta tambaya "Miye hukuncin" Isuwalle ya fad'a "Bulala d'ari ce, aka sosa ta zube" ta fad'a tana jefa agwaluma baki tareda taunewa Mai gari da idonsa ya kawo ruwa har yana tsiyaya yace " Abulle ranar da kika min biyar, kwarankwatsa nayi sati ina jinya, ko fada ban je ba" ya 'karashe da kuka wiiwi "Sharad'i da shawara" Abulle ta fad'a Cikin sauri ya zabura ya 'kara yowa kusada ita daff yace " Ina jinki" "Ka kawo zuma farar sa'ka 'kwarya biyu, ka soyomin zabbi bakwai" ta fad'a "Na amince" ya fad'a yana washe baki Mi'kewa Abulle tayi tana cewa " Bintalo jeki kirawo Kandala mu wuce gidan mai gari mu daka kayan mata" tana wucewarta Karara, ciyawa, da abincin dabbobi had'e da kashin shanu suka samo wanda za'ayi maganin mata .........   Mss Flower $ Mrs Abdool [8/14, 11:33 AM] Mss Flower: ♀️♀️ *ABULLE ANNOBA*♀️♀️ (Sanadin neman haihuwa) _Na_ _*Mss Flower*_ _&_ _*Mrs Abdool*_ بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *____________________________________* *03* Abulle ce ke tafe yayinda zugar yara 'kidaga guda ke biye da ita a baya, basu tsaya ko ina sai gidan mai gari "Abulle mun jima ba'asiya mana lemo ba" cewar Kandala "Ke dan uban bunsurun gidanku ban hanaki fad'in sunana gatsal haka ba" Abulle ta fad'a tana ciza le'be "Allah ya huci zuciyarki Iya Abulle" Kandala ta fad'a idanuna 'kurrr kan Sule mai kayan marmari "Muje a kar'ba" Abulle ta fad'a Tunde Sule yaga basu shiga gidan mai gari ba sun nufo hanyarsa yaketa zufa, idanunsa ya cika da 'kwalla cikin zuciya sai fad'in " Allah kasa zawo ya kamata kan ta 'karaso, kai Isuwalle Allah kwashe maka albarka daka haifo wanan jinnun d'iyar, ni ba na hanata ba, ta turan macizai cikin dare su hanani bacci" 'kwalla na saukomasa "A'a Sule kukan me kakeyi neh" Abulle ta tambaya "Kayana neh sukayi espaya" ya fad'a yana rushewa "Allah sarki, lemon ko ayabar" Abulle ta tambaya "Duka Qur'ani sukayi espaya" ya fad'a yana hawaye "Bari kuka Sule, kai ku taimaka ku kwashe masa ku rage masa aikin zubarwa" Abulle ta fad'a, rufe bakinta da wuya yara suka daka ma kayan marmarinsa wawa, wasu na 'kullewa a zani, wasu d'an kwali wasu suka jawo leda. Sule kuka ya dinga rerawa kashar'bam, chan yayi su'bul da baka yace "Allah ya isa" "Mai kace?" Abulle ta tambaya "Cewa nayi, Allah saka da alheri kun ragen wahala" ya fad'a yana shasheka "Ba damuwa, duk sanda suka kuma espaya ka kirani" ta fad'a tana wucewa yayinda Sule keta tsinemata a zuciya   "Assalamu Alaikum munzo sana'a ba sata ba" Abulle ta 'kwala sallama "Shegiya Annoba, Allah karki ya kar iyayen da suka haifi wanan annobar" cewar wato tsohuwa dake gurza goro bisa tabarma Abulle da ta jita tace " Yagwalgwal ki kiyayeni fa wallahi, tsufa ne yasa nake raga miki" ta 'karashe tana 'kwafa "Kar ki raga dan butar ubanki" cewar Yagwalgwal Abulle kallon kaji dake kiwo tsakar gida tayi tace " ku casamin ita" tana rufe baki, Yagwalgwal ta mi'ke tana 'ko'karin shiga d'aki har ta kusa santsi ya tad'iyota aikuwa aikuwa ta fad'i kifff, kaji kuwa suka yo kanta kusan su sha wani abu suka hau caccakarta, sai ihu take tana tsinema Abulle Jibgegen tirmin gidan mai gari suka d'auko suka had'a karara da kashin shanu da ya bushe suka hau daka baji ba gani, har sai da ya koma gari, cikin kula suka kwashe sanan suka zuba ciyawa da dusar tumaki nan ma suka dake lu'kwi, sanan sukayi zaman 'kulli "Abulle maganin matan neh, ni dayake inada ragowar na satin da ya wuce sai wani satin zan siya" cewar uwargidan mai gari "Allah sarki, ai ba irinsu d'aya ba, sai ki 'kara akan wancan" Abulle ta fad'a tana mi'komata d'auri biyu da na matsi da na sha, hakanan ta kar'ba fuska ba walwala ta kunto jaka hud'u daga zani ta mi'kamata Abulle ce ta bankad'a d'akin amaryar mai gari dake baccin 'karya, hannu Abulle ta d'aga ta nana mata a cinya, ai a kind'ime ta tashi tayi zaman 'yan bori tana sosa wajen da ya kwaile kamar sabuwar 'kuna, cikin hawaye tace "Abulle banida lafiya fa, kuma ciki garan mai gari ma baya tarawa dani kinga maganin ba amfani, ga kuma rashin kud'i" "Allah sarki, toh Allah ya raba lafiya, magani kuma ke yafi cancanta ki amsa kyayi gyaran haihuwa, kud'i kuma kya had'a ki bani da na wani satin" Abulle ta fad'a tana diremata 'kulli biyu sanan tayo waje Yagwalgwal da keta bori a tsakar gida, kaji na caccakarta har sun janye mata zani, yara sai dariya suke mata, itakuwa sai tsinar Abulle da iyayenta take. Sai da zasu fita sanan Abulle ta cewa kaji " kai ku barta haka" Gida gida suke shiga bada maganin mata........   Mss Flower & Mrs Abdool _MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA SIYAN LITTAFIN NAN_ *NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA ILMANTUWA* _ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU❤️❤️❤️ [8/14, 11:33 AM] Mss Flower: ♀️♀️ *ABULLE ANNOBA*♀️♀️ (Sanadin neman haihuwa) _Na_ _*Mss Flower*_ _&_ _*Mrs Abdool*_ بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writters-Association-111719967001810/?reffer=whatsapp 04 Gida gida suke shiga bada maganin mata, Abulle ce agaba taci uwar damara kamar zata dambe, kara gyara Dan Kwalin Kanta tayi wanda ya rune sai tsamin dauda yake, turoshi tayi gaban Goshi irin na yan duniya, Gaba tayi zugar yaran daukeda kayan Matan na biye da ita, gidan kusa da na mai gari suka shiga tareda cewa "salamu alaikum munzo sa'a ba sata ba, jikin matan gidan ne ya hau kerma kamar mazari jin muryar abulle, Kicibus tayi da uwargidan zata cefene Abulle tace "madallah ga naki" tareda miko mata kulli biyu na sha Dana matsi, karba tayi badan ranta naso ba tareda cewa "abulle inada saurafa" "Eh sai ki kara ai, bani nan tafada tareda mika mata hannu" "Abulle banida kudi wallahi wannan kudin cefene ne" cewar uwargidan kamar zatayi kuka "Ke nide dai na bata min lokaci" tafada tareda warce kudin dake hannunta tana turawa cikin Zane, Kada kugu tayi tareda shigewa cikin gidan tana "dije Amarya fito ga naki", Nakurewa DIJE tayi kamar bata nan Don tasan halin Abulle tsab, cikin tsawa Abulle tace "dallah ziko karba acikin canjin uwar gida ai naira dubu ce na karba a hannunta karbi" itama aka mika mata kulli biyu, Fita tayi daga gidan tana wake waken ta irin na kauye, Dije kam tsinuwa tabi Abulle dashi har tafice tabar gidan. Next gidan tashiga shima nan saida Asha daga don since sunada saura Amman tace wallahi sai sun siya haka suka siya badon ransu na soba. Haka tadinga shiga gida gida tana basu magani suna karba wanda basuda kudi kuma suna karbar bashi tareda musu gargadin zuwa na gaba zasu biya. Sai can da yamma liss bayan Abulle tagama siyarda maganin tass don dama ita bata kwantai, ka'idace Kullum sai ta saidoshi, Washe jajayen hakoronta tayi tana kwance zaninta nan kudi suka Watso kirgasu tayi taga dubu ukku ne, gakuma bashin na dubu daya, dubu daya tacire taba zugar yaran dake mata tallah suka karba suna tsalle tareda mata godia, Bintalo ta kalle Abulle, "iya Abulle yaushe za'a kuma yin wani"sai gobe Amman kuzo da wuri "to iya Abulle" suka wuce suna tsalle, Abulle har takama hanyar gida tatuna Idan taje tuwo zata ci kuma gaskiya yunwa take ji, canza akala tayi zuwa gidan mai gari, a zaure ta iske shi zaune da babbar Riga kamar wanzami, wani mugun kallo ta balla mai nan da nan ya zube kasa yana "Allah y taimaki Abulle wallahi daman yanzu nake cewa azo akaimiki zabin nan tinda nasan yanzu kindawo yawon sa'anar yagama tareda sharce zufar dake tsatssafo masa kamar ankama malam a gidan karuwa, Harara ta kuma zabga masa tareda cewa "bani su nan" aguje ya ruga ya dauko kwarya biyu ta farar saka saikuma zabi bakwai, warcewa tayi daga hannunsa tareda kama gaban ta ranta fess, Tana tafiya mai gari yafashe da kukan bakin ciki yana "Allah y tsine ma hansatu da isuwalle duk sune suka ja mana wannan annobar. Wallahi dole mu kashe abulle ina haka bata barin mu muzauna lpia, Gida tashiga ta jawo turmi tazauna tareda kwala ma hansatu kira da gudu ta karaso, turus tayi tareda sakin bakin tana kallon Abulle sai tandar Zuma take, "Ungo wannan soye zakimin yanzun nan Don yunwa nake ji..........   Mss Flower & Mrs Abdool _MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA SIYAN LITTAFIN NAN_ *NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA ILMANTUWA* _ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU❤️❤️❤️ [8/14, 11:34 AM] Mss Flower: ♀️♀️ *ABULLE ANNOBA*♀️♀️ (Sanadin neman haihuwa) _Na_ _*Mss Flower*_ _&_ _*Mrs Abdool*_ بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *____________________________________* 05 Hansatu ce dauke da zabin da Abulle tashigo dasu don yankawa, "Ke hansatu guda ukku zaki yankamin ki ajemin sauran hudun gobe zakimin dabge dasu"Cewar Abulle har lokacin sai tandar Zuma take kamar sabuwar mayya. Guda ukku hansatu ta ware gefe guda, tazuba sauran a wani tsohon keji, nan da nan ta hau yankawa don Abulle tace tayi sauri yunwa takeji,nan ta dafa ruwan zafi tafige tayi tafashe sannan tahau suya, Abulle dake hakimce tana bin hansatu da umurni, zabga wata uwar hamma tayi kamar tsuwar mayyar da ta Kwan bataciba jin kamshin soye yafara gauraye gidan, Isuwalle ne ya kwado uwar sallama tindaga soro, sannan ya karaso cikin gidan, zaune ya iske Abulle kan turmi tana karkada kafa, "isuwalle Dan karbomin lemo a gun idi mai shago", "wani irin lemo kuma Abulle" cewar isuwulle yana kallon ta "Wanda kasani kuma kalar baki nan nake so karda ka karbo wanda bashiba kadeji Mena cemaka" tabashi amsa, Babu yanda ya iya haka yanufi shagon idi, tsayawa yayi bakin shagon don takaici duk ya ishe shi, kamarshi da girman shi ace Yarinyarshi tana aike shi cikin iko da gadara Idan kuma mutum baije ba ta Aiko masa macizai suna shi bacci mtswww duk a zuci isuwalle ke wannan maganar, ganin yana bata lokaci yasa yace "idi Abulle tace kabata lemu baki" Allah sarki Idi jiki na rawa yace "guda nawa" "guda biyu"tace isuwalle yabashi amsa Mika masa yayi harda sakawa a leda sannan ya karba yatafi, yana shiga lokacin kuwa hansatu tagama soye sai kamshi suke, "Juye min a kwanan nan kikawo su nan", haka ko tayi tadire mata su agabanta, "to daukomin yajin nan mai tafarnuwa Wanda zanyi Dangwale tareda plate dinda zan saka miki naki, mikewa hansatu tayi don yin umarnin Abulle, Miko mata ledar isuwulle yayi, tako karbe ba sannu bare nagode, Hansatu mikomata yajin tayi tareda plate din, nan Abulle tazabe kawunan da kafafun tasaka musu "kici keda isuwulle" Isuwulle yace yanzu Abulle Kai zaki bamu, cikeda tsiwa tace "to daka samu ma nabaka koh, Idan baka ci bani" tsinto fukafuki tayi tace hansatu ladan suya, karba tayi suka koma gefe, shima isuwalle saboda tsabar kwadai saida yaci, Abulle kuwa 'kasa takoma don taji Dadin cin naman tabude yajin ta tareda balle robar lemu tanaci tana korawa, saida tacinye su tass ta shanye lemun sannan ta saki wata uwar kara alamun ta koshi, gantsarewa tayi ta narko wata uwar gyatsa irin ta yara marasa tarbiya sannan ta Mike ta karkade bujenta tayi da'ka abinta, Hansatu ce dake wanke wanken kwanukan da Abulle tagama cin abinci ceh ta saki tsaki tana cewa " Allah wadarai" "Ai kece abin Allah wadarai Hansatu, kece sanadin komai tubda ke kika haihota, ni dai tsakanina dake sai dai na ce Allah sakamin" cewar Isuwalle da ke zaune bisa turmi yana tsotsar 'kafafun zabbi "Isuwalle ai kaine musababbin komai, da kan na haifeta wani wula'kanci ne bakamin ba kai da danginka, kai ka tasoni gaba dole kasa na kauce hanya kai da danginka" cewar Hansatu dake mi'kewa "Yarinyar da kika haifa mana yanzu ai gashi tazame mana annoba, tun shekarar data wuce data karya 'kugun Baaba har yanzu Baaba jinya takeyi, sam ta'ki bani fuskar magana da ita duk saboda abinda 'yarki ta jawo, ni dai kin cucan Qur'ani, ga uban ci kamar gara kullum kusan kwano biyu na hatsi take ci, duk ta 'kararmin da kadara, ga ba'kin jini data jawomin a al'umma, duk inda naje zumd'ena akeyi ana ja min Allah ya isa" ya 'karashe yana tura kan zabo baki had'i da sakin kuka "Dallah rufen baki, duk abinda ake maka yayi rabin nawa ne, ina ce..." Hansatu shiru tayi ganin Abulle ta fito daga d'aki tana kallonta "Jar uba! Yau za'a kuma 'yar tsere a gidan nan kenan" ta fad'a tana wage baki saboda hamma "Abulle ni dai bakiji nace komai ba ko?" Cewar Isuwalle domin ranar da akayi 'yar tsere kwanakin baya shiya fad'i kuma shi ya azabtu daren ranar....... Mss Flower & Mrs Abdool _MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA SIYAN LITTAFIN NAN_ *NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA ILMANTUWA* _ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU❤️❤️❤️ [8/14, 11:34 AM] Mss Flower: ♀️♀️ *ABULLE ANNOBA*♀️♀️ (Sanadin neman haihuwa) _Na_ _*Mss Flower*_ _&_ _*Mrs Abdool*_ بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *____________________________________* *07* " Abulle na ro'keki da Allah ki rufan asiri, wallahi 'kashin 'kafata ya turgud'e" cewar Hansatu tana 'bare baki wiwiiii "A dakata to, bari Hansatu ta huta" cewar Abulle tana zama "Abulle 'kafata, wayyo Allah ta turbud'e 'kafata" Hansatu ta 'kara fasa kuka Isuwulle ne ya mi'ke ya nufi Hansatu da keta yarfe hannu tana matsar 'kwalla, 'kafarta ya ri'ke yana 'ko'karin jaa aikuwa ta tsallara ihu tana fad'in " Isuwulle azaba, jaa da kyau, cikata haka" sai sumbatu take tana 'ko'karin janye 'kafarta "Isuwulle ri'ke 'kafar ka ja ta da kyau, matseta sosai kada ka cika" cewar Abulle tana ta d'irka dariya harda hantsilawa Hansatu ba 'karamin kuka tayi ba sanan Abulle tace " yau na rushe 'yar tseren kowa ya huta" ta fad'a tana cigaba da dariyar mugunta, Hansatu tana d'ingisawa ta samu ta d'ora ruwan zafi domin gasa 'kafarta   Abulle zaune bisa tabarma ga kayan kwalliya birjik a kusada ita danginsu jar hoda, kwalli, barbad'a kumatu, ga kanta kile jambaki, ga kuma ba'kar jagira, kwalliya ta rambad'a fuskarnan taji uwar jar hoda, ga ba'kar jagira da aka sha guduma sanan aka bi aka d'iddige fuskar da ba'ki, sanan ta rambad'a jambaki a saman ido da baki, Isuwulle da Hansatu dake gefenta sai kallonta suke kamar sunga sabuwar halitta domin kwalliyar Abulle idan ta tashi yi ta kere ta kowa muni a 'kauyen, madubi ta kalla ta turo baki sanan ta she'ke da dariya tana dad'awa da shewa sanan tace "kai jama'a irin kyau haka, yasin mijin Abulle ya cha'ba" ta fad'a tana mi'kewa "Abulle wane mijin hala, ko sai a dandali zaki fitar da gwanin naki" Isuwulle ya tambaya "A'a Isuwulle ni ai na fidda gwanina tun jiya, yau in aka tashi daga dandali ka sanarma zan wuce gidan mai gari, wallahi kowa ya taru da yaro da babba duk wanda bai je ba zaya sani" Abulle ta fad'a tana karkad'e kayan jikinta "Abulle mi za'ayi a chan ne" Isuwulle ya tambaya "Zan fidda gwanina" ta basa amsa sanan ta wuce tana tsalle, dan'kam ta tadda 'yammatan 'kauyen 'kofar gidansu kowacce ta sha kwalliya da d'amara haka suka kama hanya suna hirarrakinsu har suka 'karasa dandali Bayan samarin da suka tadda sun gaida Abulle aka fara gudanar da gad'a da wasanni, bayan angama ya zamana saura lokacin hira, haka kowa ya ja budurwarsa gefe suna zance banda Abulle da Bintalo dake zaune kan wani dakali suna 'yar hira, chan Abulle ta mi'ke ta dubi Bintalo tace " zo mu zaga mu ga ko za'a samu 'yan iska", Bintalo mi'kewa tayi suka fara zaga 'yammatan da samarin suna ganin abinda sukeyi, idon Abulle ne ya sauka akan wajen ciyayi, gani tayi kamar mutane dan haka suka nufi wajen cikin sand'a "Mati da zafi kake sha fa" cewar wata muryarta kamar zatayi kuka, Mati kam bai kulata ba sai faman matseta yake "Jar ubancan! Dama Dije ke 'yar iska ceh, yau zaku ci ubanku, maza ku fito" cewar Abulle Mati iya rikicewa yayita, hawaye yake ya fara magiya cewa shi hira yakeyi amma Abulle sai d'ure d'uren ashar takeyi ta 'ki sauraronsu "Abulle dan girman Allah kiyi ha'kuri, na rantse da Qur'ani izihi sittin ni ba komai nakewa Dije ba, ai ga tanan a tamba..." Bai 'karashe ba yaji wani gigitaccen mari bisa fuskarsa kamar an maka masa itace mai uban nauyi "Wa zaka maida 'yar iska, ca aka ce maka banganka ba, bare ka tsara, wato ka kama nonuwan yarinya kana sha ita ba shanuwa ba ko kuma kai ba jinjiri ba, salon ka ciremata su ka kasheta, to kwarankwatsa yau sai kaci 'kwal ubanka" ta fad'a tana 'ballo tsumagiya lokacin masu hira duk sun yo caa hankalinsu ya dawo wajensu Abulle "Kai Saminu, Isiyaku ku d'aga min shi" Abulle ta fad'a, Mati ko 'kara sautin kukansa yayi yana magiya amma haka aka d'agashi sama Abulle ta dinga zuba masa bulala, kafin tayi masa goma har ya sume, haka tasa aka bugo tu'ka tu'ka aka kwaranya masa ruwan, yana bud'e ido ta kuma cigaba da sambad'arsa Abulle ko da tagama ta buga uban tsalle tayi girgiza sanan tace " Allah kuma ba ma wani sa'a naga yana 'ko'karin lalata da yarinya ko 'ko'karin tsinke mata nono yaga yanda zanyi dashi a garin nan" ta fad'a tana dariya da buga 'kafa, nan kowa dai yayi tsuru tsuru, Mati kuwa jini duk ya 'bata masa riga gashi baya iya tafiya sai kuka kawai yake "Mai gari ya aikoni, yace na sanar da duk wani saurayi dake dandalin nan da yayi haramar zuwa gida ya shirya cikin ado, ya 'karaso gidansa cikin 'kan'kanin lokaci domin yau Abulle zata fidda miji, wanda bai zo ba zaya had'u da fushinsa da kuma na Abulle" cewar d'an shela dake yawo da lasifika. Nan dukkan samarin suka fara watsewa fuskokinsu da fargaba yayinda 'yammata suka fara 'kus 'kus amma ba batun fiddo zance waje Abulle ceh zaune kan kujera yayinda samari da dattawan 'kauyen sukayi dafifi a 'kofar gidan mai gari kowanne zuciyarsa cikeda zullumi da addu'ar Allah yasa kada Abulle ta za'besa musamman samarin "Abulle ke ake jira ki za'ba, sanan ki saka lokacin auren" Mai gari ya fad'a Dariya Abulle ta she'ke da ita sanan ta fara kallonsu d'aya bayan d'aya chan tace " za'bina shine...........   Mss Flower & Mrs Abdool   _MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA SIYAN LITTAFIN NAN_ *NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA ILMANTUWA* _ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU❤️❤️❤️ *YAN NIGER NAKU 300F NE KU TUNTU'BI WANAN LAYI DOMIN BIYAN NAKU +22795045822 IDAN KUN BIYA SAI KU TURO SCREENSHOT TA WANAN LAYIN 08167888934*❤️❤️❤️ [8/14, 11:34 AM] Mss Flower: ♀️♀️ *ABULLE ANNOBA*♀️♀️ (Sanadin neman haihuwa) _Na_ _*Mss Flower*_ _&_ _*Mrs Abdool*_ بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *____________________________________* _HEY LOVELIES!! KUYI SAURI KU BIYA DOMIN SAMUN DAMAR SHIGA INDA ZAKU KARANTA ABULLE, DOMIN FREE PAGES NA GAF DA 'KAREWA, KADA KU MANTA ZAKU SHA DARIYA, ZAKU ILMANTU. KU NEMI NAKU TUN KAFIN A BAKU LABARI_ *06* "Kwarankwatsa sai anyi 'yar tseren nan" cewar Abulle tana karkad'a 'kugu "Abulle" cewar Isuwalle da idanunsa suka kawo ruwa " Kada kayi magana, ku jira na samo rake nadawo a fara" Abulle ta fad'a tana ficewa Tafiya take tana dirka tsalle, idan ta cilla 'kafa chan sai ta dire kamar wata 'yar rawar 'be'be, tana ta wa'ke wa'kenta tana tafa hannu. Sa'adu mai mangoro ne ya hangota, suna had'a ido ya zura takalma ya fara tura baron mangoro cikin sauri kafin ta taddosa dan akwai 'yar tazara tsakaninsu "Chalama!! Sa'adu akwai rowa kwarankwatsa, yanzu ko zanyi maganinka" ta 'karashe tana tattare bujenta had'e da gyara murya, ta'kar'karewa tayi tana "Sa'adu mai mangoro tsaya", ai Sa'adu jin ta kirasa sai ya kuma daddagewa ya fara zuba gudu da baro, mangoro na fad'uwa yana d'agosu da 'kafa yana maidawa, yayi gudu mai nisan gaske sanan ya juya ganin Abulle bata bayansa yasanya ya koma 'kar'kashin wata makekiyar bishiyar kuka ya zauna yana haki had'e da maida numfashi, 'yar gorar ruwansa ya d'auko zai sha aikuwa sai yaga ruwa na tashi sama kamar ana zu'kosa ta saman bishiya, cikin kid'ima ya birkita wanda yayi sanadiyyar zubewar mangoronsa a 'kasa, d'aga idanunsa yayi sukayi ido biyu da Abulle tana murmushi Dirkowa tayi daga bishiyar ta ri'ke ha'ba sanan tace " yanzu kai Sa'adu saboda ba'kar rowa shine kayita zabga gudu kada ka bani mangoro biyu zuwa biyar, lallai ka cika uban 'yan rowa" ta 'karashe tana zubewa tana dariya harda birgima "Kiyi ha'kuri Abulle ban lura dake ba ne" ya fad'a idanunsa na kawo ruwa " Bata shafan ba, kai ta shafa" ta 'karashe da karka'be bujenta ta tsinci mangoro biyu daga 'kasa tayi tafiyarta tana tsallenta "Shegiyar yarinya mai zubin aljanu, ashe ma aljanar ce, ni naga ruwa iya sama ziiiiii ashe aljanar na bishiyar, Allah ka yayemana wanan annoba, yanzu ta jamin asarar murtala" ya fad'a yana tsaki, sanan ya nufi mangoronsa da ya zube yana 'ko'karin kwashewa amma da ya kama sai ya koma dutse, haka yayita bin mangoron d'aya bayan d'aya suna komawa duwatsu, zaman 'yan bori yayi ya dinga kuka kamar zai shid'e sa'ilin nan ya mi'ke kamar an tsikaresa ya nufi gidan mai gari yanata kumfar baki a hanya   "Isuwulle ya kamata ayiwa Abulle aure kaga ta zama budurwa, ga kuma duk sa'aninta da tsarar rakinta ansa musu rana, a nema mata miji" cewar Hansatu "Lallai Hansatu sai yau na tabbatar bakida hankali, yanzu uban wa kike tunani zaya auri Abulle, wallahi ko mahaukaci aka ce za'a bawa na tabbata guduwa zaiyi, wai Abulle Annoba suke mata kirari, toh wa zaya kwashi annoba ya kai mahallinsa" ya 'karashe da tsuka "Ai idan kai son zama da ita kake kana wahala a banza sai kayita zama, amma ni nagaji da wahala, azaba, da ba'kin jinin da nayi cikin mutane, bari ta dawo nace ta za'bi miji nasan dai ko yanasonta ko baiso sai ya aureta eheee" Hansatu ta 'kare da murgud'a baki gefe "Nima farincikina ne, Allah ya tabbatar da alheri" Isuwulle ya fad'a "Yanzu naji batu, da kana magana kamar son zama da ita kakeyi" Hansatu ta fad'a "Nadawo, me kuke tattaunawa" Abulle da shigowarta kenan a guje "Magana muke akan auren sa'aninki da za'ayi nan kusa, ke kuma shiru ba wanda ya turo" cewar Isuwulle "Hehehehehe Qur'ani kun bani dariya, wayaga Abulle amarya" ta fad'a tana kwashewa da dariya harda kifewa 'kasa "Abulle baki son auren ne" cewar Hansatu cikeda fargaba "So kai, Hansatu ni ai da sam bani maganar aure ma, ashe fa na zama budurwa" ta 'kara kwashewa da dariya tana hantsilawa "Ai aure shine cikar mace" Isuwulle ya fad'a "Kwarankwatsa za'ayi budiri da auren Abulle, kada ku damu nan kusa za'a sha shagali, nan kusa zan fidda miji" ta fad'a tana murmushi Wani farinciki ne ya 'kara kama iyayen Abulle, cikin zumud'i suka ce "Allah ya kaimu" Abulle ceh ta tattare buje, ta daka uban tsalle tace "za'a fara 'yar tsere, yanzu za'a fara wa'ka kafin a gudanar da wasa kamar yanda aka saba" ta fad'a tana daddagewa tana baya kamar an ri'ke kafafunta sanan ta wage murya " A bada fili fili" "Filiya!!" Suka ta'kar'kare suka amsa fuska kamar kashin shanu "A bada filin wasa" Abulle ta kuma fad'i "Filiya" suka amsa suna matsawa domin bada filin "Duk wanda bai bayar ba" Abulle ta fad'a tana direwa "Filiya" suka amsa suna tafawa "Uwarsa 'yar kamasho ceh" Abulle ta fad'i "Filiya" suka amsa suna 'kara matsawa "Ubansa d'an kamasho ne" ta fad'i tana tafi "Filiya" suka amsa suna watsa mata harara ta 'kasan ido "Daren yau ya kwan da cinnaku" ta 'karashe tana taka rawa "Filiyaaaaa!!!!!!" Dukkansu suka ta'kar'kare iya 'karfinsu suka amsa Abulle dariya ta she'ke da ita sanan tace " kunci wanan, toh a jaaa layi" Nan suka shata layi, suka tsaya 'ki'kam kamar sojoji Abulle ta kallesu tayi murmushi sanan ta fara musu cewa "Mai tsumma", ai sai suka d'aga 'kafar hagu "Mara tsumman" suka d'age 'kafar dama "Mai tsumman, mara tsumman Hansatu ya baki d'aga ba?" Cewar Abulle. Cikin sauri Hansatu ta d'age 'kafa sanan ta makata 'kasa da 'karfi, ai kuwa zafi ya ziyarceta ta dur'kushe tana yarfe hannu ...........   Mss Flower & Mrs Abdool _MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA SIYAN LITTAFIN NAN_ *NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA ILMANTUWA* _ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU❤️❤️❤️ [8/14, 11:40 AM] Mss Flower: ♀️♀️ *ABULLE ANNOBA*♀️♀️ (Sanadin neman haihuwa) _Na_ _*Mss Flower*_ _&_ _*Mrs Abdool*_ بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *____________________________________* _HEY LOVELIES!! KUYI SAURI KU BIYA DOMIN SAMUN DAMAR SHIGA INDA ZAKU KARANTA ABULLE, DOMIN FREE PAGES NA GAF DA 'KAREWA, KADA KU MANTA ZAKU SHA DARIYA, ZAKU ILMANTU. 08 Kyakkyawan saurayine dogo mai kimanin shekaru 32 a duniya, sanye yake cikin suit Dark blue mai mugun kyau, hannunsa na dama daukeda brief case sai dayan hannun kuma daukeda suit din saman, yarage dagashi shi sai long sleeve light blue da butterfly neck tie, Tafe yake cikin sassarfa yana duba time a hannunsa dake makale da kyayyawan agogo, kofar exit din katafariyar asibitin yake tunkara,harya fito yaji ringing din wayarsa, da sauri ya dauka ganin "first love" dauka yayi tareda karawa a kunne, "Hello Mom on my way, wallahi aikine yad'an min yawa shiyasa but in the next 20mins Ina gida" Banji me taceba, kawai yakashe wayar, da sauri yashiga motarsa ya tada yabar harabar asibitin. Mintina ashirin ya iso bakin wani kantamemen gate, horn ya danna da 'karfi daga inda mai gadin yake zaune ya danna remote nan da nan kuwa gate ya zuge, kutsawa yayi, kaitsaye ya perker mortar a inda aka tanada ya bud'e ya fito d'auke da jakarsa, Direct apartment d'in mahaifiyarsa ya tunkara, handle d'in ya murza tareda yin sallama, budurwar dake zaune a falon ta wani amsa masa a da'kile, shi da baima lura da ita ba direct hanyar stairs ya nufa don shiga d'akin mahaifiyarsa, Ahankali cike da yanga ta kirsa tace "Doctor barka da dawowa", tsayawa yayi tareda juyowa sai a lokacin ya lura da akwai mutum a palon, bai ko amsata ba, sai kallon ta yayi sama da 'kasa tana sanye cikin riga da wando damman mu sai wani juya ido take irin na 'yan duniya, tsaki kawai yaja tareda hayewa kan stairs d'in, 'Dakin mahaifiyarsa ya bud'e tareda zama akan cushion d'in d'akin, kana ganin sa kasan a gajiye yake, Kallonsa tayi cike da 'kauna tace "son yau ka dad'e dayawa, tinda dazun Meema tazo tana jiranka" 'Bata ransa yayi yace" Mom is that why u have been calling?, plss mom wai meyasa matan nan suke damuna ne plss su 'kyaleni na huta mana, when it's time zanga wacce nake so da kaina, duk bana son su kar nasake ganin 'kafar kowace shegiya a gidan nan inba haka ba zan mata rashin mutunci, I can't marry such type of gals ba class bare kamun kai, God forbid ma" ya 'karashe maganar ransa a d'an 'bace. Mom itama da abun saddiq yafara damun ta tace "son yaushe ne zaka cikamin burina naganin matarka, its high time fa shekarunka 32 a duniya fa idan ba yanzu ba sai yaushe, I am sick and tired of ur attitude plss enough, kowa baka so then wa zaka aura?!!" itama ta 'karashe maganar ranta na 'kuna, Mi'kewa yayi ya koma kusa da ita yakama mata hannun ta "plss Mom just pray for me kinji koh, so nake na samu yarinya mai tarbiya da hankali wacce zata kula dake, Mom u won't understand it's only u I have am doing this all because of u, meyasa bazaki gane ba kinsan insonki banson na auro wacce zata baki problem kingane koh Mom to plss calm down just pray for me, cos ur prays matters a lot, bazan ta'ba yin abu don na 'bata miki rai ba, kinson banson 'bacin ranki ko yaya ne kiyi ha'kuri ki yafe min kinji Mommy na" ya 'karashe maganar kamar zeyi kuka. Murmushin jin dadi tayi " I know my son kullum Ina maka addua Allah y baka tagari Allah kuma yayi maka albarka" tafad'a tana murmushi tareda saka hannu cikin curly hair d'inshi tana murzawa kamar wani yaro. "Yanzu tashi muje kaci abinci yau favorite d'inka na dafa ma" tafada tana kallonshi tareda 'kara fad'ad'a murmushin fuskar ta Ware idanuwansa yayi "wow really, u are the best Mom ever, I love u so much" ya fad'a cikeda farin ciki yana hugging d'inta, Zamewa tayi, tayi gaba yana biye da ita har suka sauko stairs d'in, kallon falon yayi yaga Meema bata nan it means ta gaji tawuce abunta, Dining yawuce ya zauna, serving d'insa tayi lafiyayyar fried rice da coslow tareda liver souce, ci yayi sosai har ya 'koshi suna fira, kallon ta yayi yace "Mom u are the best cook ever wallahi banta'ba cin abinci mai dad'in naki ba" ya karashe zancen yana kai lomar shinkafa baki, Fashewa tayi da dariya tareda cewa "kaide ci bance kamin santi ba" "Allah Mom Idan zanyi aure sai tazo ta koya kalar girkinki don shi zata rin'ka min" "To naji, maza cinye ka tashi kaje ka dibo 'kanwarka batada lafiya inaga ciwonta ya tashi" "Mom kinsan dai bana zuwa can sasshen saboda Umma banson abubuwan da takeyi" "kayi hakuri kaje saboda Allah ai taimako zakayi" "To shikenan" yafada tareda mi'kewa ya wuce part d'insa, kayan sa yacire ya shiga wanka tareda d'auro alwala don an rigada anyi sallar zuhr a masallatai, agida yayi nashi yasaka jallabiya mara nauyi ya nufi hanyar apartment d'in Umma, Da sallama yashiga falon, amman ba kowa wuce wa sama yayi d'akin Sultana, kwance yaganta ta du'kun'kune da duvet tana rawar sanyi, Da sauri ya yakice duvet d'in yana "Sultana meke damunki?" Ahankali ta bud'e idonta tareda d'an mi'kewa ta jingina da gado cike da 'karfin hali tace "Ya Saddiq ina ta neman lambarka baya zuwa" "Am sorry sis nashiga thearter shiyasa, how are u feeling now?" 'Dan gyada masa kai tayi kawai numfashinta na fita sama sama "Sultana bakijin magana kinsan lalurarki but kina wasa da lafiyar ki gashi baki shan drugs, Ina umma take?" "Tafita tin d'azu", "Kinci abinci?" ya tambayeta, girgiza masa kai tayi, "Toh meyasa?", yasake tambayarta "Yaya banason abincin da aka dafa ne" ta fad'a tana d'an yatsina "Zaki ci fried rice?", gyad'a masa kai tayi yace "toh Ina zuwa" yafita Babu dad'ewa sai gashi tareda plate d'in abinci, taimaka mata yayi taci sosai sannan ya d'auko box d'in magugunnan ta yabata, "Ki huta yanzu Idan kinji wani abu call me kin...." Bai gama magana ba yaji hayaniya daga bakin kofa wanda ko bai juya ba yasan Umma ce, "muryar wani kwarton namiji nake ji a dakin 'yata" juyawa yayi zai fita ta tare shi "wai kai wani irin mara zuciya ne wato harkafara shigomin d'akin 'yata bana nan ko, to ahirr dinka, kar na sake ganin 'kafarka cikin gidannan banzaye masu asiri" Fashewa Sultana tayi da kuka "haba Umma Yaya taimakona yayi fa banda lafiya, wallahi Umma karki kara zagin Yaya meya miki saboda kawai baki son Mom shine zaki had'a dashi?" Rushewa Umma tayi da kuka tana "shikenan Allah y isa tsakanina da Amina wato banda mutanen gidannan dana gari yanzu har 'ya'ya na ma ta asirce su nashiga ukku na lalace wallahi da sake" ta 'karashe da kururuwa Sunkuyar da kai saddiq yayi yana "Allah y baki hakuri Umma" Cikin masifa tace " fice min d'aki tsohon munafiki kawai kamar mutumin kirki sai wani sun sun da kai yakeyi" A hankali ya ra'ba ta gefenta yafita yana girgiza kai, 'Kara fashewa Sultana tayi da kuka, wani mugun kallon Umma ta watsa mata "munafuka kema daya sai kitayi tinda na kori ubanki" tafitana tana banko kofa. "Ai Umma Yayana ne kuma baki isa ki raba mu ba duk duniya banda kamarshi, kuma inasonshi.   *ABULLE POV* "Abulle to kinyi shiru munata sauraronki, ai kwarankwatsa ki fidda duk wanda kikeso a nan, wallahi sai an aura maki, in bayada gida ma ni zan bashi" cewar Mai gari Dariya Abulle ta she'ke da ita sanan ta girgiza kai irin abun na mata dad'i, chan ta mi'ke ta fara tattakawa tayi gaba tayi baya tana 'karewa jama'ar wajen kallo, murmushi ta saki sanan tace " duk 'kauyen nan wa yafi kud'i?" Aikuwa jama'a suka d'aga murya har suna rigegeniyar furta " Mai gari" "Gonakin wa suka fi yawa" Abulle ta kuma wage murya ta tambaya "Mai gari" Jama'a suka dad'a amsawa. Mai gari kam zufa duk ta ji'kashi bai san lokacin daya zamo daga kujera ba "Abulle ai gonar taki ce, ki za'bi miji sai na barmasa" cewar Mai gari Wani kallon zakaci ubanka Abulle tayi masa, sanan ta kuma tambaya " wane ne ya ta'ba zuwa binni?" Ai ko suka kuma d'auka sunan Mai gari "Jama'a to ni Abulle na tsaida Mai gari matsayin mijina, domin shi yafi cancanta ya zama mijin Abulle" ta fad'a tana washe baki Mai gari wasu zufa da hawaye ne suka kuma zubomasa, rarrafawa yayi gabanta, gwiwoyi 'kasa yace " mi zaki yi da tsoho?" "Shine za'bina" Abulle ta fad'a...........   _Few pages to last page, ku garzayo ku biya naku, kada ayi babu ku_   Mss Flower & Mrs Abdool _MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA SIYAN LITTAFIN NAN_ *NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA ILMANTUWA* _ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU❤️❤️❤️ *YAN NIGER NAKU 300F NE KACAL, KU TURAMA WANAN LAYIN +22795045822, SAI KUYI SCREENSHOT ZUWA WANAN LAMBAR 08167888934* [8/14, 11:40 AM] Mss Flower: ♀️♀️ *ABULLE ANNOBA*♀️♀️ (Sanadin neman haihuwa) _Na_ _*Mss Flower*_ _&_ _*Mrs Abdool*_ بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *____________________________________* *12* Mai gari tagumi ya zabga yana tunanin irin azabar da zaya sha, ta lafiya da ta dukiya in akayi auren nan, a kwanakin nan da zazza'bi yake kwana domin Abulle ta sako shi gaba, cikin dare har zabura yakeyi domin mafarkanta ne yake ta yawan yi tun bayan lokacin da ta fiddashi matsayin mijin auranta A 'bangarensu masu dukkan Abulle kuma, bayan tayi ligi ligi dasu aka kwashesu kai tsaye kemis aka wuce dasu Yagwalgwal aka fara dubawa kasancewar ita tsohuwa ce, diresin d'in kanta akai mata inda taji mummunan ciwo, sai ihu take a haka aka saka spirit da uban bandeji aka d'ad'daure kan, Ita kuwa Amarya banda kururuwa babu abinda kakeji nata, likitan chemist d'in na duba ta yace "subhanallah baiwar Allah ya akayi hakan tafaru ne, kinga yanzu cikin nan yasamu matsala saura kadan ya 'karasa 'barewa", wani mahaukacin ihu tasake tareda cewa "shikenan Abulle kin kashe ni, Yagwalgwal Allah ya isa tsakanina dake duk ke kika kawo mana wannan muguwar shawarar gashi yanzu kin ja min asara wayyo ni na bani na lallace" haka take ta maimaitawa cikeda azaba Likitan ne ke ta bata baki yana kiyi ha'kuri don Allah, nan da nan aka firda saura cikin aka mata duk abinda yadace, Ita uwargida bama tasan inda kanta yake ba, saboda mummunar karayar datayi a 'kafa an dai samu an mata d'ori da 'kyar ankuma shafa mata magunguna. Maigari dake zaune cikeda jimami duk duniya ya ishe ya kifa uban tagumi sai zufa yake sharcewa akai akai, Wani matashi ne ya fad'o fadar Mai gari hankalinsa a mugun tashe sai nishi yake, zubewa yayi yana "ranka ya dad'e akwai matsala fa, ga iyalinka can a kemis d'aya tayi karaya d'aya kuma tayi 'bari" Mi'kewa Mai gari yayi a zabure yana "ina kasamu wannan labarin?, suna ina ne?, meya samesu?" ya fad'a zufa na tsatsafo masa saboda tsabar tashin hankali, Matashine yace "ranka ya dad'e ance sunje dukan Abulle ne shine hakan tasame su" Mai gari zaman 'yan bori yayi tareda rushewa da kuka mai cin rai, nashiga ukku na abulle takasheni, saida nace su kiyayi wannan aljanar yarinyar suka 'kiya, ni kaina suna gani biyayya nake mata na zauna lafiya, amman saboda taurin kai shine suka tafi dukan ta yanzu ga irin ta nan" ya 'karashe zancen yana 'kara 'bare baki. "Mai gari yanzu ba lokacin maida zance bane muje tukun kaga halin da suke ciki" cewar saurayin cikin muryar lallashi. Mi'kewa Mai gari yayi yana share 'kwalla tareda cewa muje, taka babbar rigarsa yayi Aiko ta tad'iyeshi ji kake timmm Mai gari a 'kasa, wani kukan yasake saki yana "inalillahi wa innailahi rajiun Abulle kashe ni zakiyi nima" Da 'kyar aka d'aga shi suka nufi chemist d'in, Mai gari shi ya biya kud'in sannan aka tattarosu Yagwalgwal aka nufi gida, Mai gari komawa yayi fada ya zuba uban tagumi yana tunani, "to tinyanzu nafara fuskantar wannan barazanar ai Idan akayi auren ma kila kashe ni zatayi dole akiyin auren nan wallahi ko mai zai faru" mai gari duk a tunaninsa a zuci yake wannan maganar,   A 'bangaren Abulle kuwa ko da ya fad'a mata sonta yake sai ta kece da wata uwar dariya, Mai Indomie kuwa nan da nan idonsa yayi 'kwal da hawaye domin a tunaninsa zata 'ki amincewa da shine. Chan Abulle ta dakata da dariyarta sanan tace " bari nayi nazari akan wanan batu, ko mai ake ciki zaka jini mai kama da ludayi" ta 'karashe tana kwashewa da dariya   *Dr Saddiq POV* Sanye yake cikin suit dinsa baka mai masifar kyau, yafito agaggauce kasancewar yakusa makara, Part din mom din yashiga, yagaishe ta samasama, yajuya zaifata, Kallonsa mom tayi tana "a'a sadiq bazakayi break fast ba zaka fita" mom wallahi nayi latti ne Ina sauri Idan naje zanyi a can" To ubangiji Allah y tsare Allah y taimaka, ameen Ameen mom nagode saina dawo, Murmushi tayi tana daga masa hannu "adawo lpia" Kai tsaye motarsa yashiga, aguje ya isa Asibitin, ko parking bai gama ba yafito kasancewar kiran da ake tamasa akan zaiyi ma wata mata aiki, Fitowa yayi rikeda brief case dinsa ya nufi office nasa cikin sauri nurses dinda ke ta gaishe sa ma saidai kawai yadaga musu hannu ya wuce, Mamakine yakama shi ganin office dinsa a bude, shiga yayi da mamaki cike a fuskar sa yana kallon burdurwar dake kwance kan three sitter dinda ke office din, Cikeda masifa yace " ubanwa yace kishigomi min office without my permission, kina hauka koh, shin bance kar na sake ganin ki a gun aikina ba, ohh I know u want to tarnish my image koh arinka kallona mutumin banza koh, tunda daman already ke duk wanda ya ganki yasan ba mutuniyar kwarai bace daga kallon shigarki, cos a good lady can never dress to tempt a man, c'Mon get out kafin na bude idona" ya daka mata uwar tsawar da nikaina saida na tsorata. Mikewa tayi da sauri ta dauki handbag dinta tayi waje, ganin yanayinsa zai iya maketa, Kwafa yayi tareda saurin canza dressing zuwa na theaterya kwashi kayan aikinsa yafita dasauri ya nufi thearter room......   *Mss Flower* & *Mrs Abdool* _MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA SIYAN LITTAFIN NAN_ *NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA ILMANTUWA* _ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU❤️❤️❤️ [8/14, 11:40 AM] Mss Flower: ♀️♀️ *ABULLE ANNOBA*♀️♀️ (Sanadin neman haihuwa) _Na_ _*Mss Flower*_ _&_ _*Mrs Abdool*_ بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *____________________________________* _INA FARINCIKIN GANIN YANDA KUKE SIYAN WANAN BOOK, INSHA ALLAH SAI KUNYI FARINCIKI DA SIYA. MASU TURO ALERT SUYI SHIRU PLEASE KU DINGA MIN MAGANA TUNDA BA SANINKU NAYI BA, SON SO FISABILILLAH❤️❤️❤️_   *09* *ABULLE POV* "Abulle na ro'keki da Allah ki janye zancen aurena, na fa kusan haihuwar ubanki" cewar Mai gari da zufa tayi masa wanka, idanuwa sunyi tulu tulu kamar an bad'e da barkono "Tsufanka ba shine damuwata ba, kasan shi so baruwansa da tsufa" Abulle ta fad'a tana dariya "Abulle mene ne son" Mai gari ya fad'a yana zare babbar riga domin wani zafi da ya ishesa "A ci abinci mai dad'i, a saka miji aiki yayi yana rawar jiki" Abulle ta fad'a tana 'ko'karin mi'kewa "Kiyiwa Allah ki za'bi saurayi dai dai ke kuyi aure ku kwashi soyayya" Mai gari ya fad'a cikin tausayin kansa "Da kaima zamu kwashi soyayya, kai dai jira daren farko kagani" Abulle ta fad'a tana mi'kewa had'e da dariya mai bayyana jajayen ha'koranta Ko da Abulle ta fice wani ihu Mai gari ya saki yana kuka sosai sanan ya tattare babbar rigarsa yayi cikin gida, zaune ya tadda uwargidan da amaryar had'e da Yagwalgwal suna sauraren radio kasancewar wanan 'kayataccen littafin na _(NAMIJI)_ *GUMBAR DUTSE* ake karantawa, Yagwalgwal ta share 'kwallar idonta ta dubi Mai gari daya zamna bisa tudunka ya rafka tagumi 'kwalla na tsiyaya "Mi yake faruwa, ko kaima kukan littafin kake ne?" ta tambaya, bai amsata ba sai girgiza kai da yayi wasu sabbin hawayen suka zubo masa "Mai gari, haba kai ba 'karamin yaro ba ka zauna kayita kuka, ka fad'amana damuwarka man" cewar uwargida "Nima dai shi nagani Yaya" amaryar ta d'ora "Aure zan 'kara" ya fad'a wasu hawayen masu mugun zafi suna sauko masa "Mai gari ai abin farinciki ne, hala kukan murna kake ne"cewar uwargida bakinta d'auke da fara'a "Wallahi ba'a isa ba, wanan ma ai tozarci ne, du du du yara nawa na juye da za'a min kishiya, wanan ma ai cin fuska ne" cewar amarya tana rushewa da kuka Yagwalgwal kam shewa ta saki had'e da rafsa gud'a sanan tace "Mai gari a 'kara aure, in anyi ta ukun a cike da ta hud'un nan kusa, ai cikar kamalar namiji mata hud'u" ta 'kare da dariya "Yagwalgwal ai ke na kula kin tsanan, duk wani abu da zai 'batan burinki ayi shi, toh wallahi bari tsinanniyar kishiyar ta shigo taga yadda zanci uwar ubanta nan gidan, wallahi in karya ha'kar'karin yarinya ba damuna za yayi ba" ta 'karashe tana wucewa d'aki cikin kuka "Ohoo dai, 'yan ba'kin ciki dole d'ana iyi aure tunda Allah ya hore mar" cewar Yagwalgwal tana afa goro cikin baki "Iya banisan auren nan ba d'iyar arzi'ki ba ceh" Mai gari ya fad'a yana 'bare baki "Mai gari wa aka baka hala" uwargida ta tambaya baki sake ganin yana kuka " *ABULLE ANNOBA*" ya fad'a yana kuma 'bere baki Yagwalgwal wata muguwar hantsilawa tayi aikuwa ta bigi garu (bango) ihu ta sake alamun taji zafin buguwar sanan tace "mi ya kaika neman wanan aljanar, so kake ta 'karasani hala" "Ni kuma ta kasheni da maganin mata" uwargida ta d'ora idanunta na kawo ruwa "Wai wace jarabar ce ta sanyaka nemanta yarinya ko 'kirgan dangi bata fara ba ga 'yammata nan cikakku amma kace wanan annobar kake so" Yagwalgwal ta fad'a tana fyace majina "Iya hauka nake zan nemi aurenta, wallahi ita ta neman" ya 'karashe cikin raunin murya Amarya dake la'be a tagar d'aki ta rafsa gud'a domin tana jinsu ta d'ora da cewa " Ahayyee ras, wayaga Mai gari angon Abulle, Iya Yagwalgwal za'ayi suruka mai hankali" ta 'karashe da she'kewa da dariyar mugunta Mai gari daya fusata ya mi'ke yana 'ko'karin cimmata Cikin sauri Yagwalgwal ta ri'kesa tana cewa " barta namiji baya bugun mace sai sauna, ko dan cikin jikinta ai an 'kyaleta, kuma iskancin da take ai Abullen ba 'kyaleta zatayi ba, dai dai take da kowani shege" cewar Yagwalgwal tana hura hanci "Shine ai" Mai gari ya fad'a yana shigewa d'aki domin ya 'karashe matse ruwan idonsa   "Abulle amma kin iya tsiya, ai labari ya riskeni kin za'bi Mai gari" cewar Hansatu daga shigowar Abulle gidan "Hansatu ni fa banason munafunci, mene ruwanki da gwarzona da har za'a zo a fad'amiki" ta fad'a tana yatsina Hansatu tayi shiru da bakinta sai 'kwalo ido da ta farayi kamar sabuwar mayya "Abulle amma dai bikin ba nan kusa ba ko, domin ban shirya ba" Isuwulle ya fad'a "Chalama!! Isuwulle bikina ai bazaya wuce satittika ba domin kuwa auren nakeso, maganar kaya ka kwantar da hankalinka kwarankwatsa binni zamu da Mai gari iyi mun siyayya" ta fad'a tana zama bisa tabarma tana janyo daron da ake zubamata abinci Isuwulle kam murna tayi masa yawa jin ba shi zayayi kayan d'aki ba sai washe baki yake kamar gonar auduga "Jar uba, Hansatu!!!" Abulle ta 'kwala kira, Hansatu da tashige d'aki tana murnar zata rabuda ala'ka'kai ta fito tana gyara zanin dake 'ko'karin kunce mata "Abulle gani" ta fad'a "Hansatu dan wula'kanci shine zaki ajiyen tuwo malmala bakwai, wanan kwatan cikina ai ba zaya cika ba" ta fad'a tana watsa mata harara "Abulle wallahi shinkafar tuwon ce ta 'kare" Hansatu ta fad'a idonta na kawo ruwa "Ke nawa kika ci?" Abulle ta tambaya " 'Daya da rabi" Hansatu ta fad'a "Kutumelesi shine kika ci har haka, meyasa baki ci rabin ba" Abulle ta fad'a tana watasamata uwar harara "Abulle kiyi ha'kuri nima ba 'koshi nayi ba" Hansatu ta fad'a idanunta rau rau "Hansatu wallahi sai kin daka sakwara da miya agushi" Abulle ta fad'a "Abulle dare fa yayi" Hansatu ta fad'a idanunta na kawo ruwa "Hansatu toh......     *SECOND TO THE LAST PAGE*   _MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA SIYAN LITTAFIN NAN_ *NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA ILMANTUWA* _ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU❤️❤️❤️ [8/14, 11:40 AM] Mss Flower: ♀️♀️ *ABULLE ANNOBA*♀️♀️ (Sanadin neman haihuwa) _Na_ _*Mss Flower*_ _&_ _*Mrs Abdool*_ بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *____________________________________* *10* *ABULLE POV* " hansatu toh yama zaayi naci abinci ba nama, ai wannan labarine" mikewa tayi tareda kada bujenta tayi waje, tafiya tadanyi kasancewar masu kajin dake kusa dasu duk suntashi, tindaga nesa taji wani mahaukacin kamshi na tashi miyau Tahideye tareda karasawa gun mai balangu, gashi kuwa yasha mai sai kyalli yake, Saurin isa tayi wajen tace "a bani balangu" tana kada kugu, "Na nawa" cewar mai balangu, "jar uba Amman kai bakone agarin halan cewar Abulle, "To kwarankwatse ko kazubamin balangu kokuma na Mayar da shege kashin shanu" ta karashe zancen tana huro hanci Mai balangun da dawowarsa kenan da buta a hannu alamun yazagaya jin abinda Abulle tace yace "haba waya isa ya hana Abulle nama, ai ko na dubu kikeso sai akasamiki" mai balangu yafada yana kallon Abulle zuciyarsa fal tsoro, Yanka naman yashiga yi a jarida saida ya yanka mai uban yawa ya bade shi dayaji yasaka abakar leda sannan ya mika mata, "Allah y kiyaye Abulle", "Ameen" tace tareda karba tayi gaba" "Tana tafiya mai balangu yafashe da kuka yana Allah ka kawo mana karshen wannan annobar banji ba banganiba nayi asarar dubu biyu, naman dubu biyu Nasaka mata wallahi, yakarshe yana sharce majina" Kallon kaninsa yayi yace "Dan jakar uba kai Kuma daga zuwa zakamin asarar jalina,wallahi da baka bata ba tsab zata maidashi kashin shanu daga yau Idan wannan aljanar tazo ko me take so kabata shine zaman lpia na" kanajina koh yafada cikeda kunar rai. Abulle data tasa uban balangu tanaci tana dangwala yaji saidata cinye shi tsab sannan tabi da tuwo malmala bakwai ta sha ruwa tamike, tana sakin gyatsa tareda mika tanufi daki....   "Yanzu yagwalgwal kina kallo maigari zai kwaso mana annoba" cewar uwargidan maigari Cikeda da bacin rai yagwalgwal tace "dalla rufamin baki ni banfiki damuwa ba, duk gidannan akwai wadda wannan aljanar yarinyar ta raina sama da nine" yagwalgwal tafada tareda sakin sabon kuka, "Ai yagwalgwal dole musan yanda zamu hana wannan auren inba haka ba babu wanda ya tsira a cikin gidannan dole muci uwar abulle wallahi, bayan wannan ma ai karya ma maigari tattalin arziki zatayi saboda ci kamar gara" fadar uwar gida tana jawo kwanon shinkafa gabanta kasancewar uwar yunwar dake damun ta don rabonda taci abinci tinjiya da mai gari yazo da labarin auren Abulle, Mikewa yagwalgwal tayi tanufi dakin amarya, bakincikine ya turnuketa ganin barcin ta kawai take kwasa, waje taje ta dauko botiki cike da ruwa tana zuwa ta sheka mata, Afirgece ta miki tareda cewa "abulle kimin rai don girman kiyi hakuri," shekewa yagwalgwal tayi da dariya tana "ai ba Abulle bace, tashi dallah jaka kawai, Idan zaki ajiye wannan jakin kishin ki ajiye shi don bashine gabankuba ku nemi hanyar cin uban Abulle shine zancen, Amman saboda hasara shine kike barci, Mikewa tayi jikin ta tsamo tsamo sai rawar sanyi take tabiyo yagwalgwal Numata turmi tayi tace zauna nan, kallon uwargida tayi sannan ta kalli Amarya tace "inada shawara ku saurareni, kunajina kutashi yanzu muje gidansu Abulle muci uwar uban ta kawai Inbahaka ba auren nan ba makawa kuma kunsan bani kadai zanci ubana ba harku don haka kutashi kunsan ance sarkin yawa yafi sarkin karfi" "Yagwalgwal kina ganin wannan shawarar tayi kuwa ni wallahi tsoron Abulle nan nake" cewar amaryar maigari idonta yayi raurau yana shirin kawo ruwa, "Ke dalla ja can matsoraciya ai Abulle don taga Anan tsoronta shiyasa take iskanci dataga dama, dallah kutashi," Mikewa kowace tayi tashiga taciwo uwar damara sukayo waje ya gwalgwal ce gaba matan mai gari na biye da ita, Hankada kofar gidansu Abulle sukayi suka shiga, hansatu suka gani duke tana ma Abulle wanki, Uwar gidan mai gari cikeda balai tace "ke hansatu Ina wannan aljanar diyar taki, saboda raini wai maigari shine gawaninta mu saointane Iye yau zamuga uban da ya tsaya ma Abulle take iskan cin dataga dama...." ta karashe zancen tana girgiza cike da balaie, Yagwalgwal ce ta Dora da " yarinya yar ficika tabi ta addabi kowa ta yau saida akwashe kasusuwan Abulle" itama tana wani huci kamar zakanya, Hansatu ce tafara kwalla tana "Dan Allah kumin rai ku kyalemin Abulle in dan mai gari saita Janye Amman ku kyaleta...." Hansatu bata karasa taga Abulle tsaye tana kallon su, kallon hansatu tayi tace "share hawayen ki uwata ga Abulle nan" Yagwalgwalce tafara matsawa baya ganin idon Abulle yafara canza kala zuwa ja, Amarya kam tuni takai kofa ma, ganin su Ya gwalgwal sunyi gaba yasa itama uwargida tabi bayansu tana "yarinya tajanye ko muyi maganin ta ehe," Har sunkai fita Abulle tayi wani gurnani nan da nan guguwa ta bade gunsu yagwalgwal baka ganin komai sai kura, Banda kururuwa babu abinda ke tashi, can na hango yagwalgwal iska ta wancakalar da ita gefe guda Kanta yabugi garu nan da nan Jini ya balle, Ita kuwa amaryar me gari can talulu saida tayi sama sannan takifo kasa cikinta ya bugi dutse nan da nan tafara burgima tana "wayyo cikina" Banda Jini babu abinda ke malala, Uwargida kuwa haba ai can bayan randa aka lalubota ko magana bata yi sai kafarta dake lilo alamun karaya, Hayaniya tasa makwafta suka cika gidansu Abulle Amman ba mai bakin cewa komai sai ido, wasu maza ne suka kawo ma su ya gwalgwal dauki aka nufi chemis da su, Abulle kam ko ajikinta illa ma fadar mai gari data nufa tana murna, tana zuwa tace atara mata mazan garin, Babu bata lokaci kuwa kowa da kowa ya hallara, kallon bainar jamar tayi tace kusan dalilin wannan kiran gaggawar" hada baki sukayi gun cewa "a'a " to ni Abulle na tsaida ranar Aure na nan da sati mai zuwa nida angona mai gari akan sadaki dubu hansin" takarshe zancen tana Washe jajayen hakoronta Tuntsirewa mai gari yayi akan Kujerar sa yana fashewa da wani Sabon kuka....... *DR SADDIQ POV* Umma ce zaune gaban Abba, "uhmm dande kar ace nayi ma Dan kishiya sharri Dana fadi wani abu amman abun yana damuna Kullum dashi nake kwana" tafada tana share hawayen karya a habar zani Abba ne yace safiya kinga banson haka kifada mana ai saddiq dankine kema Idan kinga yana abu ba dede ba sai ki Kwaba masa "Ina na isa uwarsa ta daure masa gindi yayi son ransa, nayi magana ace na tsane shi saboda ban haife shi" "Yanzu Ina jinki me sadeeq din yayi ne?" "Yanzu Alhaji sai ace sadeeq, kamar danda da ka Haifa kaduba kamalar ka da mutuncinka a garinnan Amman ace sadeeq wai mata yake kwasowa yana kawowa gidannan har da rana tsaka, nayi masa magana yanunamin ban Isa ba shine nace gara nafada maka kayi masa aure kawai shine mafita" tafada tana barkewa da wani Sabon kuka Cikeda kidima Abba yace "wani sadeeq din wai....." *Mrs Abdool* & *Mss flower *   *LAST PAGE*   _MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA SIYAN LITTAFIN NAN_ *NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA ILMANTUWA* _ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU❤️❤️❤️ [8/14, 11:40 AM] Mss Flower: ♀️♀️ *ABULLE ANNOBA*♀️♀️ (Sanadin neman haihuwa) _Na_ _*Mss Flower*_ _&_ _*Mrs Abdool*_ بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *____________________________________* *11* "Abulle na ro'keki kada a sanya wanan biki nan kusa, na rantse da Qur'ani sumuni sittin ban gama shiri ba" cewar Mai gari idanu sun kad'a sunyi jajawur " Mai gari wai ni shirin me zakayi, kayi lefe ghana masigo d'aya sai kayan d'aki da kud'in shagali fa sun wadatar ka bar tada hankalinka kan abinda bai kai ya kawo ba" cewar Abulle tana washe baki "Abulle a d'aga dai dan darajar Allah" Mai gari ya fad'a "Gaskiya aure nakeso dan haka baza'a d'aga ba" ta fad'a tana gaba yayinda ta bar fadar Mai gari jugum jugum Tafiya take tana tsallenta duk inda ta ratsa ana zubewa ana gaisheta ta zagi wanda takeso, ta amsa wanda taga dama, ta ya'bawa wanda tayi ra'ayi magana, har ta kai gidan kallo Mazan da sukayi dafifi suna kallon Indiyan Hausa ganinta ya sanya suka fara matsawa domin ta shige, tana zama aka nuno wani scene inda wani actor yayi kissing actress d'in, nan 'karatan suka hau ihu alamun abun ya musu dad'i, Abulle ce ta yafito wani saurayi dake kusa da ita a d'arare tace " kai meyasa ya cijeta kuma aka saka ihu, ko muguwa ce?" Ta tambaya "A'a budurwarsa ce" ya bata amsa yana sunkuyar da kai "Jar uba! Kuma ya cijeta, wayaga Mai gari ya cizan za'ayi bura uba" ta 'karashe tana she'kewa da dariya, maida kanta tayi kan majigin sai kuma taga macen na dariya abin ya kuma d'aure mata kai ta yafitosa "Kai, wai ya zai cijeta maimakon ta kwad'a masa mari irin na fim d'in ranan sai tayi dariya" ta tambaya "Ba cizo bane, soyayya ceh" ya bata amsa "Hehehe wallahi har na hango ina gantsarawa Mai gari cizo ran da aka d'aura aure" ta fad'a tana she'kewa da dariya Bayan Abulle tagama kallonta ta taho komawa gida, idanunta suka sauka kan Mai Indomie, 'karasawa tayi wajensa "Abulle barka da dare" ya fad'a yana mata wani kallo mai wuyar fassara "Barka dai Jabiru taliya ake ta dafawa?" Ta tambaya "Eh, bari na dafa miki" ya fad'a yana sosa 'keya Murmushi Abulle tayi sanan tace " A'a dama na tsaya mu gaisa ne kawai" ta fad'a tana karkad'e jikinta harta fara tafiya "Abulle!!" Jabiru ya 'kwala mata kira "Iyyehh" ta fad'a tana juyowa, sosa 'keya Jabiru ya farayi chan ya nisa kafin yace " Abulle dama akwai maganar da nakeson yi miki tuntuni Allah bai bani iko, yanzun na kasa daurewa ne nace gara na sanar dake" ya fad'a idanunsa a 'kasa "Jabiru i sauri ka fad'a, kaga hadari ya had'u nan kusa ruwa zai tsinke" ta 'karashe tana kafesa da idanunta manya masu ban tsoro "Abulle dan Allah kada ki d'auki maganar da zafi nakasa dannewa ne, wallahi ba rashin kunya zan miki ba" ya fad'a yana 'kyafta idanu kamar tsohon munafuki "Wayyo Jabiru ka fad'i ko nayi gaba wallahi" ta fad'a tana 'balla masa harara "Abulle wallahi na jima inasonki, I lobiyu wujiga wujiga" ya fad'a yana sunkuyar da kai Abulle kam ri'ke ha'ba tayi sanan tace ....   *Dr Saddiq POV* "Saddiq dai d'anka, wanda kuka nuna ma gata har kuka sangarta shi, nayi ma uwarsa magana amma sai ta nuna ba d'a na bane har da d'orin ba'kin ciki nake mata tunda Allah bai bani d'a namiji ba" ta 'karashe tana sharce hawaye Kid'ima iya kid'ima Abba ya shigeta domin bai san lokacin da ya gyara zama ba, iya saninsa Saddiq mutumin kirki ne bai ta'ba tunanin fuska biyu yake masa ba, nan da nan fuskarsa ta canza alamun ransa ya 'baci dan haka yace " tashi ki kiramin shi Saddiq d'in da mahaifiyarsa" "A'a Alhaji ya za'ayi naje kiransa ka hanamana zaman lafiya, yanda take ta zabga wula'kanci a gidan nan, yanzu ai sai tace had'aku nake sonyi, kawai dai ka bari idan Allah ya nuna maka da idonka" ta 'karashe tana yatsina   "Saddiq wai dan Allah yaushe kake son kayi aure ne, ba fa yaro kake da d'a komawa ba, girma kakeyi amma ace har yanzu ka 'ki tsaida hankalinka waje guda, ga mata dayawa na so ka zama mijinka, ga yaran 'kawayena ma su ma suna sonka, iyayensu har kunyarsu nake ji, fisabilillahi haka zaka dinga kunyatani dai" "Mom haba mana, please ki daina irin wanan maganar insha Allah zanyi aure and you will love ur in law, kinsan wani abu Mom, daga ke sai ita a kyau, nutsuwa da hankalinta sai ya baki mamaki, kawai ki dinga min addu'a" ya 'karashe yana ri'ke hannunta "Yawwa, Allah yayi maka albarka, maganar wai mai aikin da nayi maka, yaushe zaka samo min ne" Mom ta fad'a "Nasanya a bincika idan ansamu insha Allah zaki jini, just ni banason typical 'yar 'kauye ne, kinsan basu cika hankali ba" ya fad'a "Ni dai nafi son yarinya wadda zamu dinga hira da ita" Mom ta fad'a "Ni dai banason su, sun fiye 'kazanta" ya fad'a yana ta'be baki   *Saboda ro'kan wasu mun 'kara free page zuwa 15, wasan bai ma fara dad'i ba, ku garzayo ku nemi naku* _MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA SIYAN LITTAFIN NAN_ *NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA ILMANTUWA* _ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU❤️❤️❤️   *Mss Flower* & *Mrs Abdool* [8/14, 11:40 AM] Mss Flower: ♀️♀️ *ABULLE ANNOBA*♀️♀️ (Sanadin neman haihuwa) _Na_ _*Mss Flower*_ _&_ _*Mrs Abdool*_ بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *____________________________________* *13* *Abulle POV* Zaune take kewaye da su Bintalo dake ta aikin haɗin kayan mata "Bintalo ku haɗesu da kyau yau har na maza zamu sai da" Abulle ta faɗa tana wage baki tana hamma "Wai ni dama Abulle bayan kayan mata har da na maza" Kandala ta tambaya tana riƙe haɓa "Ohoo, in ma babu mun ƙirƙiro da kanmu" Bintalo ta bata amsa Bayan sun gama ƙullin magungunansu ne Bintalo tace " ni wai yau ban ji ɗuriyar mutanen gidan ba, Allah yasa dai lafiya" "Hmmm, bar ƴan baƙin ciki so sukayi su illatani ni ko nayiwa shegu lahani" Abulle ta faɗa tana afa ayar da aka shanya a baka wadda takeda tabbacin ta uwargida ceh domin tana kunun aya na siyarwa dan haka sai da ta cinyeta duk da kuwa ta kusa kwano ta jagalgala wajen da tuƙar ayar "Ahhh lallai sun so a lahantasu, mutum in yaga faɗan da yafi ƙarfinsa ai sai ya maishe shi wasa" cewar Bintalo Yagwalgwal dake ɗaki tana jiyo hirarsu kasancewar ɗakinta da inda suke babu tazara ba ma wanan ba da ƙarfi suke ɗaga murya, chan ƙasan maƙoshi tace "tsinanniya jinin ifiritu, Allah ya kar ki ya kar iyayenki" ai tana rufe baki taji an sakar mata ranƙwashi mai uban zafi " Allah ya isa" ta furta idanuwa sun cika da ƙwalla, ai kuwa taji kamar ana mintsininta a ɗuwawu, ai kuwa tayi wata uwar zabura ido fal ƙwalla ta fara faɗin " inni sa'imin kwarankwatsa na daina, ku dubi tsufana ku min afuwa" ta ƙarashe idonta ƙwal da hawaye Abulle da ke zaune ta kwashe da uwar dariya har tana kifewa, duk ƴammatan suka tsareta da idanu ganin tana ɓaɓɓaka dariya ga Yagwalgwal na ta kururuwa a ɗaka, amma tunawar da sukayi Abulle na da ikon cin uwar mutum dake ƙoli ƙoli da su ma sai suka bar al'ajabi Mai gari ne ya shigo ciki bayan ya kwaɗa sallama tun a zaure, hango dandazon su Abulle ya sa yayi saurin juyawa yana ƙoƙarin komawa "Dawo jannu" cewar Abulle tana washe baki, aiko Mai gari yayi banza da ita ya ɗaga ƙafa ya kai ƙofar soro ta inda zai fice yaji an taɗiye shi aikuwa yayi mummunar faɗuwa kan kace kwabo jini ya ɓalle ta bakinsa, yana ƙoƙarin tashi yaji an figosa ba'a tsaya ko ina ba sai daff da ƙofar shigowa cikin gida, Mai gari da ya gane nufin haka ya miƙe da ƙyar cikin ɗingisawa ya ƙarasa wajen Abulle, leɓe ya haye yayi suntum kamar an hura ƙaramar balan balan Abulle ko da taga leɓensa sai ta sheƙe da uwar dariya tana faɗin "Jannu kaga leɓenka, dama leɓatu aka saka maka" ta ƙarashe tana tafa hannaye Mai gari ga zugi ya ishesa, ga uban haushinta da yake ji ga wani ɗan iskan suna wai Jannu sai abin ya ƙara ɓata masa rai, dan haka ya haɗe girar sama da ta ƙasa wanda ya ƙara bayyana munin da fuskarsa tayi Aikuwa me Abulle zatayi in ba dariya ba, bayan ta gama sai tace "Jannu ɓata ran mai kakeyi haka, fuskarka kamar ta tsohon goggon biri Qur'ani" Mai gari ya ƙara haɗe rai sanan yace " ni sunana Tsalha ba Jannu ba" "Ji sauna sunan Indiya ne na masoya fa" ta faɗa tana murmushi da ya ƙarawa fuskarta dake jagalgale da kwalliya muni *DR SADEEQ POV* Dr saddiq fitowa yayi theater room din yana zufa, yakoma office yazauna tareda dafe Kai sai A lokacin ya tuna da baiyi breakfast ba, yana cikin wannan tunanin yaji wayarsa na ringing, dauka yayi ya kara a kunne tareda sakin sassanyan murmushi kamar yana gabanta, "Mom how are doing" "Am fine son da fatar kaci breakfast koh?" Ta tambayeshi Sosa Kai yayi yace "mom yanzu nafito operation fa, da ban zoba matar zata iya rasa ranta Amman yanzu zanci insha allah" "Saddiq banson kana wasa cikinka kana ji na koh, indai baka son fushina to kaci abinci yanzu" tafada ranta a Dan bace "Insha Allah mom zanci tanks for d care"yafada yana murmushi, Datse wayarta tayi, kallon wayar yayi tareda yin murmushin saida ya bayyana dimples dinsa tareda fararen hakoransa, Ajiye wayar yayi, Ya dauki landline yakira akan kawo masa abinci, yana ajiye wayar yaji knocking Kai tsaye yace come in, wani handsome guy ne yashi go shima dogo ne kamar sadeeq Amman bai kai sadeeq ba, sit yaja yazauna tareda mika ma abokinsa, "Doctor kwana dayawa kaboye tinda nadawo bamu hadu ba" sultan yafa murmushi na bayyana akan fuskar sa, "WAllahi abokina aiki yayi yawa this days" sadeeq yafada yana juyawa akan kujera, Sultan yace "man yajikin sultana wai" Dan tabe baki sadeeq yayi tareda cewa to "saidai ace Alhmdullh kasan yanayin jikin yau lpia gobe babu" "Wai abokina meke damunta ne haka" "Sickle cell ce fa a kasan basu rabuwa da ciwo har Abada, ni wama zai auri sultana ne" yafada da alamun tausayi a fuskar sa, "Wallahi abokina tin sultana na karama nake masifar sonta ba sickler ba ko mecece saina aureta insha allah" yafada da alamun seriousness, Allah ya taimaka Amman bada yawuna bako kafi kowa Sanin halin uwarta Sam Batada kirki, bata nufin mutane da alkhari Sam Ina mata addua da Allah y shiryeta" Ameen sultan yace tareda kauda zancan, "Sadeeq yace "plss sultan inason nasama ma mom mai aiki saboda aikin yamata yawa kuma she's alone,ko zaka tambayi umma Inda tasamu nata sai itama a nemomata, Amman fa banson yan kauye gaskiya sun fiye karanta da rashin kunya kasani" Fashewa da dariya sultan yayi kana yace "to wakakeson yamata aikin ai dole sai kauyawa hakuri zakayi kasamo mata daya, Amman y not kayi wai kaga sai matar tarinka zama da mom kawai" yafada yana kallon sadeeq, "Plss sultan ka kyaleni har yanzu banga wacce tadace dani ba" "Yanzu duk cikin yan matan nan baga wacce kakeso ba to shikenan wallahi zaka kare a bakauyiya kuwa low class ma kade gama ruwan idon" Tsaki sadeeq yaja tareda daukarsa yana tambayar har yanzu breakfast din bai hadu bane, bansan me akace masa ba yana ajiye wayar sai sukaji knocking wata macece tashigo daukeda breakfast din a hannunta gaishe su tayi tareda ajiye abincin tayi gaba, Abinci suka ci suna cigaba da fira, Abba ne ya kalli mom cikin tsananin fushi yana cewa "Ameena kin bani mamaki ashe abinda danki keyi kenan Amman baki taba gayamin ba, saboda ya zubar min da mutunci yake kawo min karuwai cikin gida, to wallahi nabashi 1 Month yafito mata kokuma na aura masa duk wacce raina ya kwanta da ita" Kwalla ne suka taru a idon mom tareda cewa "yanzu Alhaji a ina kasamu wannan zancen haka, yaron nan babu ruwan shi da mata Amman shine zaace yana kawo su har gida" tafada cikin tsananin bakin ciki tana share kwalla "Idan ba haka bane ya nene toh kina kallo yaron nan shekararsa nawa Amman baison maganar aure Sam, Dana nayi zaton aljanace ta aure shi Amman ashe abinda yakeyi kenan, I mean what I said I month nabashi" Abba ya karashe zancen cikin fada sosai Mom da tasan wannan zancan duk Inda yafito daga wajen umma ne Amman ta basar tareda cewa "Alhaji Allah y baka hakuri insha allah zan gayamasa, Amman Idan angayamaka abu daga yanzu karinka Bincike akai Don ba komai bane gaskiya" tana gama fada tafita ta barmasa dakin...... *MRS ABDOOL* & *MSS FLOWER*   _MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA SIYAN LITTAFIN NAN_ *NAIRA 300 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA ILMANTUWA* _ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU❤️❤️❤️ [8/14, 11:43 AM] Mss Flower: *15* *Abulle POV* "Kai ku sauko mana, na rantse da Allah babu zaki, wai banda abun ku in ya shigo garin nan bana ƙwamushe ɗan banza, Hansatu kiyi mana dabge dashi" ta faɗa tana uwar dariya "Amma ke kau anyi muguwa, ji yadda ki sanya hancina ya fashe wataƙila ƙashin bayana ya rabe" Isuwulle ya faɗa yana watsa mata harara Hansatu da ƙyar ta kama katanga ta dirko tana faman haki ga hancinta na yoyon jini "Isuwulle ba wanan ba, nace ko zaka shirya muje farautar zaki jeji gobe" cewar Abulle "Saɓeni ki kaini Abulle, kinga dama ajiyeni gabansa yayi karin kumallo" ya faɗa yana watsa mata harara, da ƙyar ya daddafa ya kai ɗaki yana ɗingisawa, ɗaga labulensa keda wuya ya ga ƙatoton maciji ya fasa kai yana dubansa, cikin azama yayi baya har yana taka rigarsa da dama saura ƙiris ta kai ƙasa aikuwa yayi taga taga cikin sa'a ya dafe diro bai kai ƙasa ba, a firgice ya dubi Abulle dake dariyar mugunta yace " Abulle yanzu maganar da nayi harta ɓata miki kada ki manta ni fa mahaifinki ne" Murguɗa baki tayi sanan ta gyaɗa kai tace " na maka uzuri" Hansatu da take bakin rijiya tana wanke hanci Abulle ta duba tace " Hansatu ina abinci" "Banyi ba" ta bata amsa batareda ta dubeta ba "Kan uba! Dalili" Abulle ta faɗa "Shinkafa ta ƙare ke kuma baki cin tuwo da rana" ta faɗa "Allah sarki yau bara naje na samo mana nama da biredi mu kwashi gara, sannu" Abulle ta faɗa "Na roƙeki kada ki samo mai rai, gara su yanka su feɗe miki a chan sai ki kawo naman a dafa" cewar Isuwulle "Toh ba damuwa" Abulle ta faɗi, har ta doshi ƙofa tayo kwana Hannu ta saka cikin aljihun burgujejen bujenta ta zaro ƙulli biyu tace " Hansatu ga naki maganin matan da nayi alƙawari, ki tabbata kin amfani dashi ko dan Isuwulle ya ƙara sonki" "Abulle ni ai bani son amfani da maganin matan nan wallahi, dama kin bada kawai" cewar Hansatu "Kwarankwatsa sai kinyi amfani dashi dan ke kika nema" cewar Abulle tana ficewa Misalin ƙarfe biyar da arba'in ne kasancewar magaruba ta kusa rufawa ya sanya mutanen ƙauyan ke ta haramar kame dabbobinsu suna nufar gida, wani magidanci mai suna Tanimu da ke bin awakansa ne ya bangaji Abulle garin binsu, ai kuwa da gangan Abulle ta kurma ihu ta tuma a ƙasa tana ya ɓallata Aikuwa Tanimu yayi mugun rikicewa, sai faman haƙuri yake badawa ganin Abulle tayi biris dashi tana ta hantsile hantsilenta sai kuwa shima ya fashe da kuka kamar an aiko masa mutuwar iyayenasa lokaci guda Abulle ta dubeshi da kyau tace " kai dallah bari kuka, ni ai wanda ya bangajeni nakeson ka bani na yanke kan shege ko shegiya" "Abulle kaina zaki datse?" Ya faɗa yana ƙwalalo ido waje "A'a akuyar da ta bangazan, jar uba ko dama kaine ba akuya ba" ya faɗa alamun ɓacin rai "A'a ina ke da gani kinsan ai sai aikin dabbobi, bani ba ne waccan akuyar ce" ya faɗa yana nuna mata wata jinjirar akuya "Toh kasan ni burina in baƙanta wa mugu, dan haka muje gida ka yankan uwarta ai abin zai fi ma muguwa ciwo" ta faɗa "Abul..." bai ƙarasa ba tace "kai Tanimu banison ɓata lokaci in ko fansarta zakayi muje na datse kanka" "A'a, Allah ya baki haƙuri" ya faɗa ido taf hawaye "Na canza shawara jeka gida ka yanka ka feɗe ina tahowa bayanka, zan biya wani waje ne" ta faɗa tana yin gaba gamida fasa dariya Tun daga nesa Ukasha mai biredi ya hangeta aikuwa kan ta ƙaraso yayi maza ya kwashe biredinsa ya tura cikin kwaba ya bar guda bisa teburin, cikin fara'a ya tarbi Abulle yana washe baki " A aha yo ni da nazo karɓar biredi ya zan tadda teburi sumul" ta faɗa baki buɗe "Wallahi kuwa sai guda ne ya rage, da yake ban siyo wani ba tun jiya da ya ƙare" ya faɗa yana dariya "Toh ai shikenan" ta faɗa tana juyawa har ta fara taku ta juyo tace "Ukasha diba cikin kwaba aljannu sun kawo min yanzu ɗebosu duka kada ka rage" Ukasha nan da nan hawaye suka wanke mai fuska, haka ya dinga zaro siƙa siƙan biredi yana ajiyewa. Bayan ya gama Abulle ta kwashe duka cikin ghana masgo ta bar mai biyu wai ladan aiki *DR SADEEQ POV* Zaune yake da jallabi ta zuba ma mom ido, "plss mom meke damunki Naga damuwa a tattare dake" Sauke ajiyar zuciya tayi tareda cewa "sadeeq plss kafito da mata kayi aure lokaci ke tafiya fa ko zan samu sauki nima" Dafe Kai yayi "ohh God mom I told banga warce nake so ba har yanzu , Amman I will make a choice soon insha Allah" To sadeeq don baka samu warce kake so ba shikenan haka zauna kana jamin bakin Jini gun mahaiminka, u should better know what u are doing plss, nagaji da wannan abun, Kai kasani matar nan bata binka da alkahri sai sharri Amman ka kasa gane wa" "Afwan mom insha Allah I will make a choice, is that all?" Ya tambayeta yana sakar mata murmushi, "Ai gara dai inba haka ba abbanka ya hadaka da duk warce yaga dama kuma kasan kadan daga aikinshi kenan ma" "Insha Allah mom Bama zaa Kai ga haka ba" "To Allah ya sa" tafada tana introducing sabon fira, "and maganar yar aiki fa har yanzu baka samo min ba?" "Eh nayi ma sultan magana yama mom nashi magana Inda tasamu nata, cos Naga tasu tanada Dan tsabta,kinsan ni banson kauyawan nan" yafada yana ya mutsa fuska, "Wai Kai narasa gane wani irin mutum ne, to ita din daga ina take inba kauyen ba, kawai tasamu kulune, kuma inba yan kauyen ba suwa zasu maka bauta, nide duk warce tasamu ka dauko min ina so, nagaji da zaman kadaici gashi yarinyar nan sultana da tana shigowa Amman uwarta mai mugun hali tahanata" "To shikenan nizan wuce" yafada yana mikewa had yakai kofa sukayi karo da sultana, Kallonsa tayi tana "yaya Ina wuni" "Lpia Lau sultana ya jikin ki" Turbo baki tayi tareda cewa "bayan ma baka sake zuwa dubani ba" "Am sorry kanwata aikine yamin yawa" "To shikenan" Jin ummanta na kwalla mata kira yasa ta kusa ta gefen a guje tareda cooler dake hannunta ta nufi dakin mom, Sadeeq ne yace "ke ba kiranki akeyi ba" "Wallahi yaya ba abinda zan mata don naje gun mom ne kawai,kuma no banzanje ba" tafada kamar zatayi kuka, Girgiza kansa yayi tareda cewa "Allah y shirye umma" Yanufi part dinsa kenan ya hangota "Kai Ina sultana take, halan ta tafi gun munafukar uwar koh, Ai ni tsakanina da Ameena sai Allah ya isa, haka suhaima kafin tayi aure da kyar na raba ta da Ameena duk tagama sihirce min ya'ya" Ko beyiba yawuce part dinsa don Inda sabo yasa ba da halin umma saida abun nata Kullum gaba yake...... [8/14, 11:43 AM] Mss Flower: ♀️♀️ *ABULLE ANNOBA*♀️♀️ (Sanadin neman haihuwa) _Na_ _*Mss Flower*_ _&_ _*Mrs Abdool*_ بسم الله الرحمن الر حيم *__________________________________* ☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀ FCWA *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *____________________________________* *masoyan Abulle kuyi hakuri da wannan Dan allah, wallahi munada matsalar wuta Kwannan bamu samun damar typing mai yawa, Abulle tace tana gaishe ku son so fisabililah*❤️❤️ *14* *Abulle POV* Da ƙyar su Abulle suka rabu da Mai gari sanan suka wuce gida gida suna saidawa mata da miji magani, Abulle ƙuli biyu ta rage na sha da na matsi, bayan sun kammala sai dawa ta sallami ma'aikatan ta miƙa tayi gida tana ta fara'a kamar gonar auduga Zaune suke jugum jugum kowanne tunanin abin duniya ya ishesu, rabonsu da farinciki da kwanciyar hankali tun haihuwar Abulle "Wallahi nayi kewar rayuwar da mukayi a baya ta farinciki da kwanciyar hankali" cewar Hansatu "Hansatu ba ke kaɗai ba, duniyar nan gabaɗaya ta min zafi wallahi kullum cikin tunanin wace masifar zan haɗu da ita anjima nake" cewar Isuwulle " kaico! Mu kam haihuwa batayi mana rana ba" cewar Hansatu "Wallahi da a yanzu za'a kawon abun da zanyi na rabu da Abulle har abada da ba makawa ko ya kai birnin sin sai na samo shi a ƙas billahilazi" cewar Isuwulle yana jan wani tsakin "Ni kam Mai gida dama inaso na tambayeka, wallahi inason zuwa gida nayi ko kwanakin mako ne daganan in cigita ko za'a samu wani abin karyewar aljannancin yarinyar nan" cewar Hansatu "Lallai Hansatu kin mugun rainamin ajawali da ke tunaninki zaki cigaba da maisheni sauna kina guduwa gida kina barina da wanan ifritun ƴar taki, na dinga hura itace idanuna su koma kamar garwashi dan wuya ga ta ciyarwa gata girki, ga shara ga wanke wanke, ai wallahi in dai zaki ƙafarki ƙafar ƴar ki" ya faɗa yana watsa mata harara "Haba Mai gida kasan na tafi da ita banda ɗibar albarka ba abinda take jawo min, kayi dai haƙuri na kwana biyu nadawo" ta ƙarashe da alamun magiya "Zancen banza" ya faɗa yana kaɗe bujensa yayi gaba Abulle ce ta shigo a guje, zubewa tayi kan yaloluwar tabarmar da suke kai tana haki "Abulle lafiya" suka faɗa suna ƙwalo ido waje domin abinda zaya koro Abulle ba ƙanƙani ba ne Miƙewa tayi a zabure aikuwa ta fara laluban maɓoya ganin haka sai suka ƙara kiɗimewa suna rige rigen shiga ɗaki "Zaki i shigo gari sai ta asa yake ya cire kawuna na mutum bakwai, ya warci hannu da ƙafafu sha biyu" ta faɗa jikinta har rawa yake Ai kan ta rufe baki Hansatu ta daka wani uban tsalle tana nufar ɗaki cikin sa'a Isuwulle shima aikuwa sai sukayi karo nan da nan jini ya ɓalle "Kai zaki yana banke ƙofa ku nemi maɓoya" ta faɗi, rufe bakinta ke da wuya Hansatu ta janyo turmi ta fara ƙoƙarin ɗale katanga, Isuwulle ya durfafi iccen dirimi dake tsakar gidan, ya kusa kai wajen ɓuya wani siririn reshe da ya taka ya karye aikuwa ya faɗo timmmmm, wata iriyar azaba ce ta ziyarce shi nan da nan kuwa ya tsallara ƙara sanan ya miƙe cikin dauriya ya kuma durfafar dirimi, bayan ya haye ne ya fashe da kuka yana faɗin " Allah ka tsinewa wanan zaki" Abulle da ta ɗaga kai taga Hansatu bisa katanga tana ƙwalo idanu tana kallon ƙofa kamar ƙadangare ga jini na zuba daga hanci, mai da dubanta tayi kan Isuwulle da keta kuka yana tsinar zaki, ta fashe da uwar dariya har tana tintsirawa sanan tace " ku sauko tsokanarku nakeyi" *MRS ABDOOL* & *MSS FLOWER*   _MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA SIYAN LITTAFIN NAN_ *NAIRA 300 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA ILMANTUWA* _ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU❤️❤️❤️ [8/14, 11:43 AM] Mss Flower: *16* "Nace inji dai angama gyaran akuyar nan" Abulle ta tambayi Tanimu dake ƙoƙarin rufe ƙofar gida "Iyehhh" ya faɗa yana ƙyafta ido alamar rashin gaskiya "Tanimu hala lafiya naganka kana rufe gida da wuri haka, um ko da wata shafiyo inji ƴan binni, ina akuyata" ta faɗa "Abulle ai akuyar kina barin wajen ta tsere nayi nema amma Qur'ani na zagaye kusan rabin gari babu ɗuriyarta" ya faɗa yana ƙyafta ido haɗe da share ƙwalla "Allah sarki Tanimu, tau bani wata ko ƙarama ce in naje gida Hansatu ta yankan" ta faɗa tana ƙara saɓa bakkonta na biredi "Abulle manyan fa sun mace kwarankwatsa" Tanimu ya faɗa yana share ƙwalla "Wai du ɗinsu?" Ta tambaya tana riƙe haɓa "Wallahi kuwa yau ɗin nan" ya faɗa yana share hawaye da hannun rigarsa "Toh ai shikenan" Abulle ta faɗa tana wucewa abinta harda waƙenta Tanimu cikin murna ya saki ƙofa dan dama saboda ita yake ƙoƙarin rufewa, baki buɗe ya shiga gidan "Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un" shine abinda uwargidansa ta faɗi cikin kururuwa tana aza hannu bisa kai, cikin kiɗima Tanimu da ke zaure ya shigo gidan har yana ƙoƙarin zamewa Suman tsaye yayi ganin yanda akuyoyinsa manyan ke ta zubewa suna faɗuwa a mace, zubewa yayi yana " shikenan ta talautani, Allah na roƙe ka tsine wanan annoba, Abulle Allah ya isa tsakanina da ke" ya faɗa yana fashewa da kuka   "Abulle kin dawo" cewar Hansatu da ta bi bakkon hannun Abulle da ido "I wallahi ga shi na kwaso gajiya kuma ba'a samo naman ba" ta faɗa "Allah ya ƙara" cewar Isuwulle can ƙasan maƙoshi, rufe bakinsa keda wuya cinnaku suka nana masa cizo a ɗuwawu, ihu ya saki yana faɗin "Abulle ubanki fa nake" yana sosa ɗuwawu "Isuwulle ka kiyayeni wallahi, ina ɗaga maka ƙafa amma baka gani" ta faɗa tana ƙwafa "Abulle billahil lazi nabi Allah, nabi annabi, nabi ki, dan Allah kiyi haƙuri" cewar Isuwulle yana miƙewa haɗe da karkaɗe jikinsa "Na haƙura, je ka ɗaura mana ruwan shayi" ta faɗa tana bajewa bisa tabarma Nan da nan ya haɗe rai amma babu yanda ya iya haka ya hau haɗa murhu, ko kafin ya haɗa ya sha wuya ga hayaƙi da ya ishesa haka yayi ta tari har ya sauke tukunya, Hansatu ta kallesa tayi masa gwalo "Ƴar jakar uba, da wa kike hala" ya faɗa yana kallonta "Dani kake Isuwulle" Abulle ta tambaya "A'a da Hansatu nake wallahi" ya faɗa yana zaro ido Biredi ɗai ɗai Abulle ta basu sanan fara cin nata, sai da taci guda biyar sanan tayi gyatsa ta kwanta, ta jima a haka sanan ta ɗago tace "Hansatu bikina wani satin kwarankwatsa haɗe bakin nan na indiyawa ya tsayan a rai, kawai so nake na yiwa Jannu" ta faɗa tana ɓingirewa da dariya, Hansatu kam bata gane kan zancen ba amma hakanan itama ta fara ɓaɓɓaka dariya "Abulle dan Allah wani satin bikinki" Isuwulle ya faɗi hannunsa bisa ɗuwawu yana susa amma bakinsa washe cikin murna "Gaskiya yayi tsayi ma, gobe kaje ka sanar da mai gari bikinmu ya koma nan da kwana uku" ta faɗa "Masha Allah kice jibi za'a saki a lalle" cewar Hansatu tana dariya irin abin na mata kyau "Hansatu nace ko kinyi amfani da maganin da na baki" Abulle ta tambaya tana kashe mata ido guda "Eh fa nayi Aradu" cewar Hansatu tana sosa kai "Isuwulle ya kaji Hansatu to da tayi amfani da maganina" cewar Abulle tana kashe masa ido guda Hansatu da tasan Isuwulle bai san maganar ba tayi caraf tace " Qur'ani maganinki ba dai aiki ba, dan bakiji yanda ya dinga sumbatu ba" Isuwulle ya ɗaga kai ya kalli Hansatu yana son magana, aikuwa ta katse shi da cewa " Isuwullenas" ta kashe mai ido guda Dariya Abulle ta kife da ita tace "Aradu Hansatu da Isuwulle soyayyarku burgeni take" ta faɗi tana miƙewa..... [8/14, 11:43 AM] Mss Flower: *17* Iswullene ya nufi gidan maigari domin isar da sakon maigari, kamar yanda tafada masa haka ya kuwa ya isar akan cewar bikin Abulle ya koma nan da kwana ukku, Hankali maigari yaga tashi Amman ya daure yace "to shikenan gobe na kawo lefen" yayi maganar kuka nason kwace masa, Wucewa isuwulle yayi domin ya koma ya sanar da Abulle, yanda sukayi da maigari ransa fess ko bakomai sun rabu da alakakai, Megari mikewa yayi ya shiga cikin gida domin duba aikin da akema dakin Abulle, yanashiga ya taras da yagwalgwal tsaye da bandejin a kanta tana balla masa harara, Saurin karasowa yayi tareda cewa yagwalgwal lpia kuwa, cikin masifa tace inafa lpia kana neman hadani zama da wanann aljanar ta karasa ni cikin, sai kuma ta fashe da kuka tana wallahi banzan kusada Abulle ga daki ga daki ba sai dai ka maido maryarka Anan kahadasu, KO Karin fahimtar da ita yayi Amman Ina yace masa saidai ya canza mata gida Amman wallahi ko gawarta bata yarda a ajiye kusada Abulle ba balle kuma suyi zama tare, Zaman yan bori yayi tareda kifa uban tagumi tana tunanin abun duniya, don rabonshi da kwanciyar hankali tun ranar da Abulle ta zabeshi a matsayin mijin aure. Abulle ce zaune kan turmi suna fira da Hansatu dake dafa musu danbun marasa mai zogale, "Hansatu kinsan gobe fa jannu zai kawo min lefe" Hansatu da idanunta sukayi jawur kamar garwashi saboda tsabar hayaki tace "waye kuma jannu" Kwashewa da dariya tayi tareda cewa "mijina mai gari mana" Itama Hansatu da murna ta rufeta tace "Kai Alhamdallahi nayi farin ciki Abulle Allah yasa alkhairi" "Ameen" Abulle tafada tareda zabga uwar hamma, WAi Hansatu har yanzu abincin bai kammalu bane, yunwa fa nakeji tin malmalar dumamen danaci guda biyar safe" "Yi hakuri Abulle yanzu zan karasa" "To bari inje in samo kifi wanda zan hada da danbun kinsan na Kwan biyu ban ci kifi ba" "to adawo lpia cewar hansatu" Mikewa Abulle tayi tafita tana tsalle tsallenta har takai runfar hanza, "Barka da zuwa iya Abulle anfito kenan" yafada yana yake wanda yafi kuka zafi, "Barka de hanza kifin ne aketa soyawa" tafada tana sude baki, "Eh wallahi Abulle kinsan kasuwar sai ahankalima, nanawa zaa saka miki" "To Allah ya bada sa'a, Akwai sukunbiya koh don kasan banicin karfasa" "To Abulle jarida ya ciro tareda saka mata zuka zukan kifi guda 10 sannan ya mika mata" "A'a hanza ai sai in karya ka Cire biyu takwas sun isheni ma" "A'a Abulle ai ni nayi niya" "Hanza bazamuyi haka ba Cire ma hudu shi da sun isan kaga manya ne" tafada tareda cewa dadi na da hanza bade kirki ba, "Guda shida yabar mata tareda saka matashi a keda ya mika mata, ki gaida gida Abulle" "To nagode hanza allah y kawo kasuwa" Har tayi nisa taji hanza ya kwalla uban ihuu, da sauri ta dawo taga hanza sai Sai rawar dari yake saboda tsoro ga uban maciji ya fasa masa, da sauri Abulle tace "Kai kama gabanka, hanza yaron kirki ne" nan da maciji yayi gaba, godia hanza yashiga zuba ma Abulle. Abulle nashiga gida ta taras Hansatu har tasauke Danbu tazuba mata a daron ta juye kifin tayi tacire daya taba Hansatu, taciga ba cin kayanta Ko da Abulle ta kammala cin kifinta uwar gyatsa ta saki sanan ta kwanta rigijib bisa tabarmar tana hamma alamun bacci "Abulle yanzu ke da zakiyi aure dole fa ki gyara, kinga gashin kanki ɗin nan ya zama dole ki tsefe shi a fara wankewa domin ba zai wanku rana ɗaya ba, bugu da ƙari sai kin gyara farcenki, kin kuma gyara jikinki da kayan gyara gobe idan na shiga kasuwa zan samo kurkur sai a haɗa da lalle ayi gyaran jiki" cewar Hansatu "Mtswww Hansatu wai na me ne wanan uban gyaran sai kace matan aljanna" Abulle ta faɗa tana tsaki "Abulle ai sai kishiyoyinki da shi kansa aljanin su miki gori" cewar Hansatu "Ba sai in karya ƴan banza ba, Hansatu waye kuma aljanin" Abulle ta faɗa tana banka harara   "Ba Mai gari bane kike cewa aljani" Hansatu ta tambaya "Jar uba! Amma ke dai kin tabbata ƴar ƙauye Jannu ne fa ba aljani ba" ta faɗa tana dariya   "Oho to shi dai Jannun nake nufi" cewar Hansatu tana ɓata ran ance mata ƴar ƙauye "Hansatu yanzu dai gyara kikeso nayi ko" Abulle ta tambaya "Toh shikenan na bar gyaran a hannunki" cewar Abulle   "Yawwa Abulleta yanzu abinda nakeso dake, ki tashi kije ki samo soson kankan ki riƙa wanka dashi" cewar Hansatu   "Chabbb Hansatu kinsan Allah lokacin da nayi wanka dashi bikiga yadda ya karceni ba gara kawai nayi da omo na" cewar Abulle tana dukkan kanta dake ƙaiƙayi "Abulle dama shi gyara sai an jure haƙuri zakiyi, ya kamata yanda zaki auri mai gari ki zama ƴar gayu yanda duk garin nan za'ana kwatance dake" cewar Hansatu "Qur'ani Hansatu inaso, kinga in Mai gari zashi binni ya tafi dani" ta faɗa tana washe bakinta "Ai kuwa dai wallahi" cewar Hansatu itama tana washe baki [8/14, 11:44 AM] Mss Flower: *18*   A kace komai aka saka masa lokaci in har da rai dole ranar ta zagayo, yau ce ta kama ranar da za'a saka Abulle a lalle Matan gari da ƴammata kowa yayi dafifi a gidansu Abulle ya kashe kala, can na hango dafifin ƴan Abulle paid group sunyi zuga cikin shigarsu ta ado da ado, sun sha ankonsu domin har yari da sarƙa anko sukayi, hannunsu riƙe da lalle Abulle ce zaune bisa turmi da ɗan zani sai ƙwalo ido take tana iyayi wai ita a dole amarya, lallen ƴammatan su Bintalo da Kandala suka riƙa shafamata saida suka mulketa ras sanan suka ɗauko kurkur suka mulketa dashi, nan ta koma kamar aljana baka ganin komai sai idanunta da sukayi jawur tana ta ƙwalosu Bayan an wanke Abulle aikuwa tayi yalo sharrr kamar kurkur ɗin, kaya ta sanya atamfarta roba da tasha ɗinkin da yayi mata yawa sai washe jajayen haƙoranta take, Hansatu ma ta haɗe cikin shigarta sabuwa "Abulle kiyi maza ki tafi gidansu Bintalo kinsan ƴan kawo lefe na hanya" cewar Hansatu da keta hidima da baƙi "Wallahi ba inda zani, dani za'a karɓi lefen nan" Abulle ta faɗa tana gyara zama Ba'a wani jima ba ƴan kawo lefe suka shigo, gida ya kaure da guɗa, ghana masgo ce ƴar tsakiya fal kaya Abulle ce ta miƙe ta nufi ghanar ta buɗe, cikin farinciki ta fara washe baki, murya ta taƙarƙare tace "ku ƙirga idan na ɗaga" Ƴan tarbar lefe da ƴan kawo lefe kowa cikinsa taff gulma amma sanin Abulle kowa ya ja baki yayi tsit bayan sun amsa da "to" Atamfa guda ta ɗaga tace "nawa" Suka amsa da "ɗaya" Haka Abulle tayita ɗaga kayan nan har saida aka ƙirga sha biyar sanan ta miƙe tana cewa "wallahi tsaf na haddace komai aka saka mata ta satarmin abu jikinta ya gaya mata" Ƴan biki dai basu ce komai ba sanin zata ci uban wanda ya kawo mata wargi ne, haka suka cigaba da duba lefe suna yabawa da kyansu da yawansu Abulle ko da ta bar wajen ƙatuwar roba ta samu ta ciko da shinkafa ta ƴan biki, ta fara ci kamar ba gobe "Ayiririiiii gobe Abulle an zama amarya a gidan Mai gari, ƴan baƙin ciki da mahassada su mutu" cewar wata mata mai neman gindin zama "Wallahi kuwa, kuma dole a girmamani ayi abinda nakeso" cewar Abulle tana turo ture kaga tsiyarta goshi Bayan ƴan biki sun watse ne Abulle ta jawo kayan lefenta tana ƙara kallo zuciyarta fal farinciki, wani shauƙin ƙaunar Jannu na da ɗa ratsata "Abulle mai zaki bani daga cikin lefen" cewar Hansatu tana washe baki "Haba Hansatu ai dole na baki, ba sai kinyi roƙo ba" cewar Abulle tana ɗauko jambaki kanta kile tana damƙa mata "Abulle wanan fah" cewar Hansatu cikin yaƙe "Baki nayi daga kayan lefen fa" cewar Abulle tana washe baki alamar tayi abin arziƙin nan Hansatu nan da nan fuskarta ta canza amma babu yanda ta iya haka tayi godiya tana miƙewa   Misalin takwas na dare, Abulle ce ke tafiya tana wasa da kara harta ƙaraso wajen Mai gari, a fada ta taddasa suna hira, sosai taga ya faɗa yayi gwanin ban tausayi a fili tace "Allah sarki Jannu bari muyi aure zakayi ƙiba domin zan kula da kai" "Jannu!!!!" Ta kwaɗa kira Mai gari dake kujera tuntsirowa yayi jin mai kiransa, Abulle ƙarasowa tayi ta dubi magidantan dake wajen tace "kai kowa ya tafi zan gana da mijina" ta ƙare tana haɗe rai, basu ƙara sauraron komai ba suka fara ficewa "Jannu" cewar Abulle tana sakin murmushin da ya fito da muninta "Allah yasa lafiya dai" cewar Mai gari yana kallon Abulle data kwashashaɓe wai a dole soyayya "Jannu kaima ka matsu gobe tayi ko" cewar Abulle tana dashare haƙora "Allah ya sawwaƙe" Mai gari ya faɗa yayi tunanin cikin zuciya ne ashe ya fito fili "Jannu mai kace" cewar Abulle tana haɗe rai sosai "Cewa nayi sosai ma, ai na matsu goben tayi" ya faɗa kamar ya fasa ihu "Jannu ka bari kaga yanda zamuyi soyayya irinta Indiyawa" ta faɗa tana murmushi domin ta hango yanda zatayi kissing leɓen Mai gari "Allah ya kaimu" ya faɗa cikin dauriya Abulle zama tayi ta dinga hira yayinda Mai gari banda baƙanta masa rai ba abinda take, burinsa kawai ta tafi ya shiga gida ko ya daina ganinta "Jannu ni zan koma, muje na raka ka ciki" ta faɗa "A'a Abulle bari na rakaki ƙofa dai" ya faɗa yana wage bakin dole Abulle kam dariya ta dingayi domin sai take gani irin na film ɗin India ne sukeyi da Jannu inda kowa yace shi zaiyi rakiya a ƙarshe dai macen ta haƙura a rakata, dalilin da yasa itama ta amince kenan Bayan ya rakata ne har ya juyo ta ƙwalla kira "Jannuuuuu!!", Mai gari a kiɗime ya juyo Dariya Abulle tayi sanan ta hura masa kiss ta tafi da gudu irin dai na Indiya Mai gari ko da yaga ta ɓace tsaki ya ja yana cewa "ashe Abulle bayan iskokai ma tantiriya ce, Allah ya sawwaƙa" ya buga riga ya shige gida Abulle kam cikin farinciki ta koma gida, a tsakar gida ta tadda Hansatu da Isuwulle suna cin tsire da shinkafa, kallonsu tayi ta girgiza kai sanan ta shige ɗaki tana tsalle "Abulle ga shinkafa!" Hansatu ta faɗa tana ɗan ɗaga murya dan Abulle taji "Na ƙoshi, mai zanyi da wata shinkafa bayan Jannu ya cikani da soyayya" ta faɗa tana tsaki   Ranar haka Abulle ta kwana cikin shauƙi, zuciyarta fal farinciki, da ta tuna yanda zatayi kissing Jannu sai ta saki murmushi ..... [8/14, 11:45 AM] Mss Flower: *19*   Tun asuba Abulle ta farka saboda ɗauki, wanka ta salla da sabulun giv sanan ta saka wata koriyar shadda da aka kawo mata a cikin lefe ta baɗe fuskarta da jar hoda, ta sha ɗige ɗigenta na kwalli sanan ta kafta jagira wadda ake kira da guduma, tabi laɓɓanta ta shafesu da jan baki jar kala Janyo kantamemen ɗan kwallinta tayi ta hau naɗin kwakwaro dashi sanan ta feshe kayanta da turaren sure da aka sako a lefe "Masha Allah Abulle ba ƙaramin kyau kikayi ba wallahi tubarkallah" cewar Hansatu cikin jin daɗi ganin yanda Abulle tayi sharrr da ita cikin koriyar shaddarta da kuma kwalliyarta "Hansatu nagode, amma Qur'ani baki ji yadda cikina yake kiran tabahuwa ba, wallahi wani ƙugin yunwa yakeyi" ta faɗa tana hamma "Yanzu ƴan biki zakiji sun fara sallama, azo a ɗaura abincin ɗaurin aure da yini" cewar Hansatu tana ficewa   "Ohhh ni Abulle wai nice yau zan zama amarya, Allah mai iko amaryar ma ta mai gari" ta faɗa tana riƙe haɓa Tana zaune tana tunanin Jannu Bintalo ta kwaɗo sallama "Amarya ba kya laifi, kan uba ni kinga yanda kikayi kyau ne Abulle inata sauri nazo na shiryaki ashe ke kinma cancare abinki" cewar Bintalo tana rafsa guɗa Aikuwa matan dake tsakar gida waɗanda suka fara hallara suma suka hau rafsa guɗa kamar ba gobe nan da nan gida ya cika da hayaniyar farinciki Isuwulle ne ya fito cikin yaluwar shaddarsa, kansa sanye da hula yaluwa itama bakinsa buɗe yanata fara'a "Ayiririiii ga uban amarya iyayen masu gari, Allah yasa alheri za'a ɗauka, Allah ya kauda idon maƙiya a wanan lamarin" wata mata ta faɗa Isuwulle kansa ya fashe ya ƙara dashare haƙora an kirasa da iyayen masu gari, gyara zaman hularsa yayi cikeda burga sanan ya ratsa matan yana tafiya ƙwambo yayi waje dan zuwa wajen ɗaurin aure Misalin ƙarfe goma aka ɗaura auren Zainab (Abulle) Isuwulle da Hamza Akawu (Mai gari) akan sadaki naira dubu ashirin lakadan, ɗaurin auren da ya samu hallartar ɗimbin jama'a daga kowani sashi na ƙauyukan maƙota, bayan an ɗaura uban amarya da ango da tawagarsa suka nufo gidansu amarya domin ƴar ƙwarya ƙwaryar walima da za'ayi Ana cikin kitse cibirin kan Abulle wata ƙanwar Hansatu mai suna Talatu ta shigo ta rafsa guɗa sanan tace "Allah ya nuna mana, an ɗaura auren Abulle da Mai gari ƴan baƙin ciki su mutu, Ayiririiiiii" ta faɗa tana tafawa Abulle fizge kanta tayi ta miƙe kamar zata dambe har zani na kwancewa tace " yanzu an ɗaura auren nawa da Jannu" ta buga wani uban tsalle ta dire "Kai ku min waƙa dole na gwangwaje yau wallahi" cewar Abulle tana, ƴan biki kam da ƙawayenta sukayi shiru suna kallon ikon Allah   Misalin ƙarfe huɗu gidansu Abulle ya kauraye da hayaniya kowa shirin zuwa party yake, chan wani kango ne za'ayi party inda dole aka samo sifiku da za'ayi chasu dasu Misalin ƙarfe biyar amarya ce tafe cikin wani material kalar ja mai duhu, ga gwaggoro da aka ɗaura bisa kanta wanda aka tamke goshinta ram har ya kawo wajen idanuwanta, ta saka takalmanta masu tsini ɗagogwarago tana tafiya amma takalmin na ƙoƙarin kadata dole ta riƙe Bintalo suna tafiya har suka ƙaraso kangon da za'ayi bikin   Waje kam tubarkallah ya cika danƙam da jama'a, chan na hango ƴan Abulle paid group dake najeriya sun haɗe cikin shuɗiyar atamfarsu sunata kwasar rangem data sha naman akuya, daga gefe na hangi ƴar ƙasar cote de voir tana tura zoɓo cikin gida, chan cikin fili kuwa Zahratyyyy da Aysha Humaira ne suke ta ɗirkar rawa ba ji ba gani, chan ƙarshen fili Mrs Abdool ne da Mss flower suna kwashe cincin ɗin ƴan biki da su Bintalo suka ajiye, abin dai sai san barka Fili ya karaɗe da ihu yayinda Abulle amarya ta fito fage ta dinga kwasar shoki, tana haɗawa da shaku shaku, chan uwar gayyar ganin rawar bata kai mata ta tunɓuke gwaggoro ta miƙawa Ameera Madobi dake ɗaure nama cikin zani ajiya yayinda ta dinga timar rawarta baji ba gani, biki kam yayi biki anci rangyam da nama harda cincin ga kuma zoɓo da aka ƙulla gwanin daɗi sai tashi jolly jus yake, haka aka watse kowa nata sam barka   Misalin ƙarfe shida mata suka haɗu aka tafi da Abulle gidan Mai gari, Abulle fara'arta kam kasa ɓoyuwa tayi har aka ajiyeta a ɗakinta Ango Mai gari bai tashi shigowa ba sai wajen goma, hannunsa riƙe da kaza da lemun kwalaba, cikin rashin kuzari yayi sallama ya shigo Miƙewa Abulle tayi ta. ....... [8/14, 11:45 AM] Mss Flower: *20* Abulle mikewa tayi ta Matsa kusada me gari, fuskarta ta cafko tana kokarin hada bakinsu waje daya, kwace fuskar sa yashiga yi yana "Abulle miye hakan wai?" "Haba jannu soyayya ce zan maka fa" tafada har lokacin na jiyo da fuskar sa saitin Tata, lebensa ta cafko ta gasa masa uban cizo mai azabar zafi, Kwacewa yayi yana komawa gefe dafarko ma bai i zafin cizon ba jin wani uban d'oyi daya futo daga bakin Abulle kamar an bude tsohon soakaway, Lokaci guda yaji azababben ciwo ya ziryeshi fashe wa yayi kuka yana sha leben, ganin jini yasa ya kuma rushewa da wani kukan "haba Abulle me namiki zaki cigeni haka" cikin shassekar kuka, Dariya ta k'yalk'yace dashi tana "wallahi jannu nima rannan nagani a wani film akacemin soyayya ce shiyasa namaka" tafada tana jawo ledar kazar daya shigo ita, Tass taciyeta harda kasusuwan tahada ta taune ta daga lemon ta shanye shima sannan takoma gefe tana hararar me gari, "Haba megari shine kasan haka kazar take Da Dan Karen dadi shine kasiyomin kwara daya saboda shegiyar rowa, to kwarankwatsa kaza guda tamin kadan ka tashi ka nemo min wata" tafada tana murguda baki tareda tsotse yatsunta "Abulle Dan allah kiyi hakuri mantawa nayi yanzu fa karfe 12 nadare Ina zanga wasu masu kaji, kimin rai kibari sai gobe" yafada kamar zai fashe da wani kukan, "Ina ruwana da wani dare ai kasan Abulle ce amaryar shine kasiyo guda daya koh" Mararicewa yayi cikeda magiya "don girman kiyi hakuri haba amaryar me gari ai ko dawisu zaki ci sai in nemo miki Amman yanzu dare yayi ai kitausayamin" "To naji Amman da sharadi guda Idan ka yarda" abulle tafada cikeda mulki "Eh naji zanyi ko miye ne wallahi" "Yawwa gobe zaka siyomin zabi guda ukku amin Dabge" tafada tana karkada kafa bisa gado, "Naji Allah yakaimu gobe Amarya" mai gari ya fada cikeda kosawa, Jiyawa tayi ta kwanta nan da nan barci yayi gaba da ita, Megari da shi kadai yasan abinda ke damunshi ya Mike jin sandar girman tamike tayi kikam, kasancewar uban maganin mazan da ya sha dazun rana, Kayansa yafara Cirewa duka ya haye saman gadon yana kokarin Cire ma Abulle kaya, afirgice tafarka ganin maigari tsirara yasa takara firgicewa tana kallon abunsa dake tsaye kamar sanda, "Ihuu tasaki tana me gari daman kaima Dan iska ne bansani?" Saurin toshe mata baki yayi cikin kuka yace "haba Abulle kefe matatace yanzu wallahi Ina cikin wani hali ki taimaka min" yafada yana kara kamota, Mikewa tayi tana neman fita dakin, a guje yamike yarigata ya saka sakata gudun karta tara masa jama'ah, Wallahi nafasa auren tinda daman Kai Dan iska ne, ni ba yar iska bace, Babu kalar majiyar da maigari beyiba ba Amman Abulle tace Sam ita ba yar iska bace, Share kwalla yayi ya maida wandonsa ya koma kasa ya kwanta yana tura abunsa a tsakanin kafafunsa Dan yasamu sauki Amman Ina abu saigaba yake, ranar yanda yaga rana haka yaga dare, Washegari tinda safe tatashi tashiga ta feso wankanta wata jar atamfa ta dauko wacce ake cema matso kaji kunya wato atamfar roba ta buga abunta, kwalliya ta caccaba tacika wannan uban leben da Jan janbaki taff gawata uwar gira ta lafta da baki, haka de tagama ma fuskarta dige dige sannan ta tsikara Dan kwali tayo waje, Turmi tasamu tasaka a tsakar gida tazauna tana karkada kafafu, ya gwalgwal ta kwallama kira daga Inda take, Fitowa tayi tana zabga ma Abulle harara don tasan ba kiran lpia bane wannan, Abulle ta yamutsa fuska tana cewa "yagwalgwal ya banga kin aza girki ba?" Wani kallo tama Abulle irin na kinma raina ni dinnan "Ko danki baigaya miki bancin abincin gayyaba, don Abulle bata cimar banza Dan haka daga yau ke zaki rinka min girki a gidannan" tafada tana hararar yagwalgwal, "Sannan yau shinkafa dafa duka zakimin ta tiya buyi don kawayena su Bintalo zasu zomin yawo" Yagwalgwal ji take kamar tafashe da kuka, Amman ba halin musawa "yanzu yarnan tsofai tsofai dani Amman ni zan miki girki kuma Ina zaki Kai tiya biyu...." zancen ne ya makale ganin mai gari yafito lebensa yayi himmm ya sauya kamanni, Salati yagwalgwal ta rafka tana "lpia meya sameka a lebe haka yayi wannan mugun kunburin" Maigari da daman kyas yakejira yafashe da kuka yana "yagwalgwal zamewa nayi a bayi jiya" Abulle da sai lokacin ta taga lebe maigari yasa ta tuntsire sa uwar dariya harda faduwa kasa tana Angona yanzu da girmanka bakajin kunyar karya, soyyaya ce fa muka sha, ai yau ma zamu sake koh tafada tana kara kwashewa da dariya mai cin rai, Tsayawa tayi da dariyar tace Ina fatar baka mantamin da Zabina ba don uwagidace zatamin Dabge dasu, "Yanzu Abulle da wannan leben kike son nafita kowa yaganni yadingamin dariya" yafada yana sharbar majina "Wannan kuma can ta matse maka" tafada tana kwalla ma Amarya kira, Fitowa tayi tana zunburar baki, "shiga ki gyaramin dakina yanzu" Abulle ta fada, Yagwalgwal tsaki taja tana wannan masifa har Ina, sai tsine ma Abulle take tana kwashe mata albarka bata Kai kofar dakin ta ba wani uban tsantsi yajata jikake jigib tafadi tana kwalla kara ga jini ya balle ta hanci...... [8/14, 11:46 AM] Mss Flower: *22* "Haba Jannu in aka matse zai saki fa ji yanda yayi kamar an aza maka ƙaramin tulu" cewar Abulle tana ƙoƙarin jawo Mai gari Mai gari dake kuka kasharɓam ya fyace majina da hannun rigarsa sanan yace "ni wallahi barmin abuna in ma randa zai zama barshi kawai" ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa "Jannu kai dai wallahi ka fiya raki, bara na gyara maka gado ka hau ka kwanta to" cewar Abulle tana miƙewa Gadon ta kakkaɓe tace "Jannu zo ka kwanta" Mai gari dake jinsa kamar cikin ƙaya ya miƙe da ƙyar ya kwanta bisa gadon yana jan majina *Hours later* Misalin ƙarfe shida da rabi ya farka daga bacci, da salati ya miƙe ganin har anyi la'asar Wani takaici ne ya cikasa ganin Abulle kwance gefensa ta bararraje tana sharɓar bacci, ga wata wawuyar kwanciya da tayi, ga uban munshari da take saki kamar rago ga kuma yawun bacci da ya jiƙa matashin kan "Tirrrr" ya furta yana kyaɓe kumburarren bakinsa haɗe da girgiza kai yana ƙoƙarin miƙewa "Jannuuuu!! Ka tashi" cewar Abulle da ta miƙe tana mutsitsika ido "I" ya faɗa cikeda takaici Ware hannu Abulle tayi tana cewa "Jannu zo ka ɗaukeni toh" tana kyaɓe fuska ita a dole shagwaɓa "Gaskiya ni Abulle banison irin wannan iskancin, kinga dai ni babba ne kuma zaman aure muke yanzu bai kamata muyita sakarci ba" ya faɗa "Jannu haka fa akeyi a film ɗin Indiya" ta faɗa tana turo baki ita dole shagwaɓa "Kinga dai arna ne mukuma musulmai ne ai" ya faɗa yana ficewa domin kallon Abulle baƙanta masa rai yake "Mtswww wallahi dai Jannu baƙauye ne, in abun ya isheni kwarankwatsa barin wannan garin zan, ba gaira ba dalili mutum a haifeshi a ƙauye, iyi aure a ƙauye, i haihu a ƙauye, ya mutu a ƙauye, a binneshi a ƙauye, gaskiya da sake" ta faɗa tana jan tsaki   *Hansatu POV* "Isuwulle sai kaji gidan gwanin daɗi ko, kamar farkon aurenmu kan ku hura wuta sai na haihu" cewar Hansatu bakinta washe "Da kika tashi haihuwar kika haiho wa du gari annoba ba, Allah ka rabani da Abulle duniya da lahira, Allah kasa kada na ƙara ko haɗa hanya da ita" cewar Isuwulle yana ɗaga hannunsa ga hannun rigarsa fantalo "Isuwulle wanan ai ba addu'a ta gari bace, kaine dai uban Abulle dan ba'a sakewa tuwo suna wallahi, dama cewa kayi Allah ya shiryeta" cewar Hansatu "Lallai Hansatu yau na ƙara tabbatar da bakida hankali, tau ciwon hauka nakeyi ne da zanso na ƙara zama da Abulle, insha Allah mun raba hanya, ke ni ko a lahira bansan maƙotaka da ita a aljanna" cewar Isuwulle yana hura hanci "Allah sarki Abulle, wallahi ko ƴar kazar nan da nama da kina nan nasan zan samu yau amma tun tarewarki ko kifi banci ba" cewar Hansatu "Gaskiya ƙwalwarki ta taɓu, sai kije ki dawo da ita toh ta dinga ƙwato miki tana kawo miki" cewar Isuwulle yana harararta "Haba mai gida yanzu ko maƙiyinka ai baka masa fatar mutuwar aure ba bare ɗan cikinka" cewar Hansatu tana rama hararar haɗe da murguɗa baki "Hmmm ke dai kika sani Hansatu, Wallahi kikayi silar mutuwar auren yarinyar nan, kwarankwatsa barin gidan nan zanyi" ya faɗa yana shigewa ɗaki "Mutum sai baƙar zuciya da son jama mutane alkaba'i, Abulle gidan nan wa tafi muzgunawa sama dani da zanyi fatar ta dawo, nan ranan da tasa na hwashe baki sannan tasani ɗalewa katanga ni ba ƙadangaruwa ba saboda shegun ƙarairayinta" cewar Hansatu tana binsa ɗaka   *Abulle POV* Zaune take tsakar gida itada sauran mutanen gidan ana taɓa hira, duk da su a dole sukeyin maganar Abulle ce ta dubesu tace "wai dan Allah uwargida mai kuke da maganin mata ne, na matsin ina ake matsewa dashi" cewar Abulle "Ai gun fitsari ake turawa sai mace ta matse" cewar amarya da ta amshe tana sakin dariya cikin makirci "Allah sarki, to yana aiki kuwa" ta tambaya "Laaa sosai wallahi amarya, barinma wanda kike saidawa" ta ƙare da dariya "Allah mai iko, kinga ni bansan amfaninsa ba ma nake haɗawa nake saidawa ashe yana muku magani" "Wallahi kuwa, in kika gwada sai yanda kikayi da angonki" ta faɗa tana dariya "Aikuwa toh kinga nasamu sana'a zama zanyi na dingayin shi da kyau ina taimaka muku" ta faɗa "Abulle ke fa?" Amarya ta tambaya "Ke bar batuna, Jannu ai yanzun ma sai yanda nayi dashi" cewar Abulle tana yatsina *Wadda ta fitar da wanan littafi Allah saka mata da alheri* "Isuwulle ne aljanin wallahi ba ɗana ba mayya kawai" cewar Yagwalgwal dake bakin ƙofar ɗakinta tana gurza goro "Yagwalgwal ki kiyayen fa wallahi ko na saɓa miki" cewar Abulle "In anƙi fa" Yagwalgwal ta faɗa tana watsa mata yatsunta biyar Ƙwafa Abulle tayi tace "tsohuwa zamu game ne" ..... [8/14, 11:46 AM] Mss Flower: *21* Misalin tara ƙawayen Abulle suka fara zuwa, kafin da rabi ta gota sun cike gida, shewa sai tashi take Abulle komawa tayi ta canzo kaya nan aka aika kiran ƴar asharalle wata mai kiɗin ƙwarya da tayi fice a ƙauyen tazo Isowarta keda wuya aka fara waƙa wadda cikinta duk habaici akewa uwargida ta mai bi mata, hakan kuwa ya ƙara fasa kan Abulle jin yanda ake mata kirari ana kushe abokan zamanta Yagwalgwal ce da jikinta yayi mata tsami ta nufo ƙawayen amarya da dafa duka wadda ta sha daddawa sai tashin ƙamshi take a wani daro Hararar Abulle tayi sanan tace "gashi sauran yunwa" tana ajiye daron gabanta "Koma dai miye mijina ne ya kawo, wallahi kinci sa'a ina ganin darajar tsufanki kwarankwatsa da sai kin bar gidan nan" cewar Abulle tana afa shinkafa a baka Bintalo ganin yanda dafa duka tasha manja tayi ja shar ya sanya tace "Abulle bara na samo mana farantai sai a zuzzuba" tana haɗe miyau "Kawo hannunki" Abulle ta faɗa "Me zaki dashi" cewar Bintalo tana miƙa mata hannun "Gashi ki maida mugun yawu" ta faɗa tana yafa mata shinkafar loma guda a hannu Bintalo haka ta cinye sai siɗe hannu take, Abulle ta juya ta kalli ƙawayenta da suka tsartsareta da idanu, taɓe baki tayi sannan ta muskuta tana juya musu baya, sai da ta cinye abincin tas sannan ta juyo tana zabga gyatsa tana cewa "jama'a ya kuka dakata da rawar ne" "Abulle wallahi yunwa muke ji" cewar Kandala "Allah sarki, tau kuje gida ku ci abinci, nagode Allah ya saka muku da alheri" ta faɗa tana miƙewa Babu yanda suka iya haka suka miƙe suka tafi Misalin ƙarfe biyar Abulle ta rangaɗa sabon wanka ta shirya cikin koriyar shaddar da ta saka ranar ɗaurin aure sanan ta zuba jagira guduma ta kuma rangaɗa kanta kilenta ta aza ture kaga tsiya ta fito tsakar gida Nan ta tadda mutanen gidan suna ta hira abinsu duk da hirartasu ta ta'allaƙa ne akan zaginta da takeyi Turmi ta samu ta zauna ta cake tana yatsine yatsinen fuska ita a dole amarya, dubanta ta kai kan wani yaro ta miƙa masa naira goma ya siyo mata cingam, aikuwa ta wurga baki tana daɗa turo ture kaga tsiyanta gaba tana harare harare tana taunar cingam Jim kaɗan Mai gari ya shigo leɓen nan ya ƙara him, da gudu Abulle ta miƙe ta nufesa haɗe da faɗawa jikinsa Mai gari tsaye yayi yana aiyana tantiranci irin na Abulle, tau ita ba ƙaramar yarinya ba ya zata rungumesa haka kamar wasu ƴan iska amma baida damar cewa wani abu ko hanata Haka Abulle ta maƙalesa tana jansa ɗaki "Jar uba, amma wanan Abulle anyi karuwa ni fa wallahi sam bansan ƴar iska ba ce du tunanina iya jinnu ke gareta" cewar amarya tana riƙe haɓa "Wallahi kuwa, irin haka kuma nan da nan sai kiga ta janye Mai gari" cewar uwargida "Ta janye uwarta dai, ni ɗana wallahi ya sha lahaula tun yana ƙarami" cewar Yagwalgwal tana hararar ƙofar ɗakin   "Jannu kawo na matsa maka leɓen ko zai sace" cewar Abulle "Anya zai sace kuwa in an matsa, zafi fa yakemin in aka matsa abin ai yawa zaiyi" ya faɗa "A'a Jannu zai yi sauƙi" ta faɗa Mai gari da zugi ya ishesa ya turo mata leɓe waje Abulle ta kama ta matse da uban ƙarfi Wani ihu Mai gari ya saki yana kokuwar raba leɓensa da hannun Abulle idanunsa sunyi jage jage da hawaye [8/14, 11:47 AM] Mss Flower: *24* *week later* Abulle ce zaune bisa gadonta itada Bintalo suna cin gyaɗa suna taɓa hira   "Mtswww ni wallahi na gaji da wannan auren ma Bintalo dama banyi ba, ni Jannun ma yanzu haushi yake ban na kula shi bazai taɓa iya soyayya ba" cewar Abulle tana ƙara jan tsaki "Toh yanzu ke Abulle ya zakiyi tunda kin riga kinyi auren sai kiyi haƙuri kawai" cewar Bintalo tana taune gyaɗa haɗe da lumshe ido alamar garɗin na kai mata   Abulle kallonta tayi cikeda takaici ta nana mata duka a cinya sannan tace "uban wa ya gaya miki Abulle zatayi rayuwar takura, ni kinsan Allah yanzu burina bai wuce na ganni a binni ba"   "Abulle toh wai ya zakiyi ne anfa riga an ɗaura auren sannan kuma kije binni wajen wa?" Cewar Bintalo tana harararta ƙasa ƙasa saboda zafin dukan da ta nana mata   "Hmmm wallahi ko ta yane ni fa sai naje binni Bintalo nayi rayuwar ƴan binni" cewar Abulle tana ƙwafa   "Toh ya zakiyi da auren" Bintalo ta tambaya   "Ke wallahi kawai sakina zaiyi ina zan iya wannan banzar rayuwar da baƙauyen nan" cewar Abulle tana turɓune fuska   "Chabbb aikuwa zaki jawo magana, duka yaushe akayi auren" cewar Bintalo tana riƙe haɓa     "Babu mai tankawa gabana sai bayan idona, kinga kuwa bazai damen ba" cewar Abulle tana taɓe baki     "Toh wai ta wace hanya zaki je binnin" cewar Bintalo   "Deluwa mai kai ƴan aiki binni mana, ke bakiga Fatsima ba da taje binni tayi shekara dawowarta ta goge tazama haɗaɗiya, kinga kuwa ai ana mora rayuwa a chan" cewar Abulle   "Ilai kuwa, wallahi yi tafiyarki ki samo ƴan kuɗi, in Allah yasa an dace ma ki samo haɗaɗen mijin da ya iya soyayya kamar sharufkan" cewar Bintalo     "Wallahi kuwa, ni fa ina matuƙar ƙaunar miji ɗan soyayya ko ba komai na sha goyo da ɗauka, ke bakiga Mai gari ba da na haɗe bakinmu zanyi irin na Indiya sai leɓen ya kumbure kamar a kifa jinjirin tulu"     Dariya Bintalo ta kife da ita har tana tuntsirawa sannan tace "jar uba, ashe shiyasa naga kwanaki yanata rufe rufen baki"   "Wallahi kuwa" Abulle ta faɗa tana darawa   "Yanzu Bintalo in kina komawa ki biya gida, ki shaida wa Hansatu da Isuwulle gobe azo kwasar kayana dan gobe zan koma gida"   "Kai Abulle da wuri haka" cewar Bintalo tana dariya   "Wallahi kuwa, ai da zafi zafi ake bugun ƙarfe yau zaya bani sakina" cewar Abulle   "Toh Allah ya kaimu, bara na wuce" cewar Bintalo tana miƙewa   *Hansatu POV* Zaune suke bisa tabarma, suna sharɓar romon kai na rago da burodi itada Isuwulle suna ɗan taɓa hira, kana ganinsu kasan suna cikin nishaɗi domin sai zolayar juna suke suna tuna rayuwarsu ta farinciki da sukayi a baya   Bintalo ce ta faɗo tsakar gidan, da kallo suka bita suna aiyana dacewar abotarsu da ƴarsu domin itama ba hankali ne da ita ba   Dariya Bintalo tayi sannan tace "Hansatu dama Abulle tace na sanar daku gobe kuzo kwashe kayanta wai tagama zaman auren" ta faɗa tana cika bujenta da iska   Wata zabura Hansatu tayi wadda tayi sanadiyyar tuntsirewar kwanon romon da suke sha, kallon Isuwulle daya bar kwanon ya jingina da bango haɗe da zabga tayi sannan tace " kaji abinda ƴar nan tace"   Tsaki ya ja sannan ya miƙe ya bar gidan gabaɗaya     *Abulle POV* Zaune take bakin gado ta caka uban ɗauri, Mai gari ne ya shigo ɗauke da sallama   Kallonsa Abulle tayi ta ɗauke kai tana karkaɗa ƙafa   Mai gari rasa ta cewa yayi shima yasamu waje ya zauna yana kallon yanda taketa cin magani   "Abulle anyi miki wani abun ne?" Ya faɗa ganin taƙi magana     "Ni kawai abinda nake so da kai Malam ka saken dan bazan iya ba" cewar Abulle tana ɗaure fuska   "Abulle lafiya, mai yayi zafi haka?" Cewarsa zuciyarsa ta shiga yanayin da ya kasa tantancewa farinciki ne ko akasin haka   "Kawai sakina zakayi banason tambayoyi" ta faɗa tana watsa masa kallon banza   "Toh Abulle na ....... [8/14, 11:47 AM] Mss Flower: *23* _Da farko dai muna baku haƙuri bisa sha ruwan tsuntsayen da mukeyi, na biyu kuma muna godiya da uzurin da kuke mana❤️❤️❤️_   "Ni Abulle da kike ganina nan kar nake ganinki, wallahi kika nemi yimin tsageranci lallasaki zanyi banza mai ƙashin mundiriɗi, gamewa kuma sai dai ki game da uwarki Hansatu bani ba wallahi" cewar Yagwalgwal tana faman haki   "Um um um, Yagwalgwal ki bar maganar nan" cewar uwargida tana duban Abulle a sace   "Ai wallahi dan taga ana mata shiru ne shiyasa take wanan wulaƙancin, tau ni yanzu uban ƴa zanci babu ruwana wallahi" Yagwalgwal ta faɗa tana hararar Abulle   "Wallahi ina raga miki ne darajar Mai gari dana aura amma ki jirayi randa zan waiwayeki kwarankwatsa sai kinyi rawar alanta tsakar gida" cewar Abulle tana watsa mata harara   "Ohoo dai babu abinda kika isa kiyi ɗiyar aljannu" cewar Yagwalgwal   Abulle ce ta sauke idonta kan Yagwalgwal wanda wani irin jan haske ya fito daga cikinsa mai tsoratarwa, nan da nan kuma ya ɗauke idanunta suka dawo daidai   Yagwalgwal wata zabura tayi har tana tuntsirar da goron da take gurzawa tana faɗin "wa makaru wa makarallah wallahu khairul makirin, innahu sulaimanu wa'inahu bisimillahir rahamanir rahim" duk ta firgice sai ja da baya take   "Yagwalgwal lafiya kuwa" cewar uwargida tana nufo Yagwalgwal da duk ta haukace   "Kwarankwatsa Abulle aljana ce kinga idonta kuwa" cewar Yagwalgwal da ta ɓata zaninta da fitsari   "Yagwalgwal kinyi fitsari fa haba ido biyu da lafiyarki" cewar uwargida   "Amma dai bakida hankali, gara ni fitsari nayi ke kam nasan zakiyi zawayi in kika ga abinda nagani ne" cewar Yagwalgwal dake leƙen Abulle da ke bisa turmi tana cigaba da taunar cingam ɗinta   "Abulle Aljana" cewar Yagwalgwal dake laɓe bayan amarya tana leƙen Abulle     Murmushi Abulle ta saki sanan ta miƙe ta nufi ɗaki     Wucewa uwargida da amarya sukayi nasu ɗakin aka bar Yagwalgwal tana gyaran wajen da tayi fitsari, tana tsaka da gyara taji kamar giftawar wani abu ta bayanta, juyawa tayi taga bata ga kowa ba dan haka ta share ta cigaba da aikinta, ƙara jin motsi tayi ta juya amma babu kowa tsaki taja tana faɗin "koma waye uwar ubansa zana ci"   Rufe bakinta keda wuya taji sanyi na kanannaɗe ƙafarta, duban wajen tayi nan taga wani zabgegen baƙin maciji na kanannaɗe ƙafarta, wata ƙara Yagwalgwal ta saki ta zube a nan somammiya     Dariya Abulle ta tintsire da ita jin ƙarar Yagwalgwal sannan tace "shegiyar tsohuwa zaki kuma ne kiga yadda zanyi dake, naci ƙwal uban Hansatu ma bare ke" ta faɗa tana tafa hannayenta   Misalin bakwai Yagwalgwal ta farfaɗo tana faɗin "dan Allah cikan ƙafata wallahi na tuba bani kuma zagin Abulle Annoba"   Abulle dake gefen tabarma tana tura tsire baki ta ɗago ta kalli Yagwalgwal tace "me kuma nayi miki Yagwalgwal ki bar ƙazafi"   "Uwarki kika min shegiya mai zubin ifiritu" cewar Yagwalgwal dake kuka tana duban ƙafar da taga macijin ya hau     "Hmmm Yagwalgwal ki kiyayen fa" cewar Abulle   "Wallahi na kiyayeki bani kumawa" cewar Yagwalgwal tana jan majina   *jama'a ku bini bashi wallahi banda lafiya* [8/14, 11:48 AM] Mss Flower: *25* "Toh Abulle na sakeki saki ɗaya" cewar Mai gari   "Kai kar ka maidani ƴar iska mana, uku zaka min, tau wai cha aka ce maka hauka nake da zan ƙara dawowa wajenka ai wallahi ni Abulle sai binni " ta faɗa tana murguɗa baki   "Abulle na sakeki saki uku, Allah ya sadamu da alheri" cewar Mai gari yana ƙoƙarin ficewa   "Mai gari tsaya tukunna, ya zaka tafi baka ban kuɗin kashewa ba, zaka sallameni haka hannu rabbana" cewar Abulle tana miƙo mai hannu   "Kuɗin suna ɗakina" ya faɗa yana kallon Abulle da ta tsaresa da ido   "Muje na ɗiba toh, ko kuma jeka kawon dubu ashirin" ta faɗa tana faɗawa gado   "Toh" cewar Mai gari yana ficewa simi simi   Bai jima ba ya dawo ya kawo mata kuɗin, Abulle watsa kuɗin tayi cikin bujenta sannan ta koma gado ta kwanta   *NEXT DAY*   Misalin ƙarfe tara ta fito tsakar gida cikin kwalliyarta tana taunar cingam, bankaɗa ɗakin Yagwalgwal tayi da keta haƙar tuwon masara ɗumame,   Tsaki Yagwalgwal tayi sannan tace "Annobar banza annobar hofi" ta cigaba da cin tuwonta   "Kin ci sa'a ina cikin farinciki na rantse da sai nayi ƙwallon basamude dake" cewar Abulle   "Chan ta matse miki" Yagwalgwal ta faɗa tana cigaba da cin tuwonta   "Toh ni zan tafi, na bar gidan nan sai mun haɗu a hanya kuma" cewar Abulle   Wani zillo Yagwalgwal tayi tana miƙewa sannan ta nufi Abulle tana washe haƙora da wasu sun zuɓe ma tana faɗin "dan Allah yanzu kin tafi" tana kamo hannun Abulle cikin ɗoki son jin abinda zata faɗi     "Ke dallah cikani kar ki ɓatamin kwalliya" cewar Abulle tana hankaɗa Yagwalgwal baya, tura Yagwalgwal keda wuya sai ta bugi garu (bango) nan da nan goshinta ya fashe bayanta yayi mugun buguwa aikuwa ta saki ihu   Uwargida na jin kukan Yagwalgwal ta fito daga ɗaki a guje, miyar yauƙi da yara suka zubar nan tsakar gida ta taka aikuwa sai ta faɗi timmmm, ƙara ta ƙwalla cikin tsananin azaba   Abulle dake kallonsu kowa ya ɓare baki na ta kuka ta sheƙe da dariya sannan tace "shegu masu girman banza" ta tafa haɗe da cewa "ahayyeee ari"   Amarya dake ɗaka ta noƙe cikin bargo jin kukansu abokiyar zamanta da Yagwalgwal ta kuma linkewa cikin bargo   Abulle shigowa tayi ɗakin, chan ta hangota chan ƙuryar ɗaki ta lulluɓe da bargo kamar mai bacci, nufar gadon tayi ta janye bargon, Amarya jin taku sai ta kuma lumshe idonta ta cure kamar alkaki, hannu Abulle ta ɗaga ta nana mata a baya, zumbur ta tashi tana waige waige sai kuma ta aza hannunta bisa bayan ta rushe da kuka   Dariya Abulle ta kuma sheƙewa da ita sannan tace "toh ni na fece, Allah sadamu da alheri"   Abulle ce tafe tana tsalle tsallenta kamar ko yaushe, daidai ƙofar gida suka ci karo da Isuwulle dake ƙoƙarin fitowa da uwar gana masgo a kaa, raba idanu ya farayi sannan ya fara ƙoƙarin raɓewa ta gefenta har ya kusa ficewa daga ƴar harabar gidan Abulle ta damƙosa tana faɗin "Isuwulle ina zaka haka da shiminin kaya"   Ɓata fuska yayi sannan yace "balaguro zanyi"   "Inaa! Isuwulle mu ukun nan ai mutu ka raba takalmin kaza, in tafiya zakayi ai dole mu bika" ta faɗa tana iza ƙeyarsa cikin gidan   Hansatu na hangosa yana zumɓuren baki da kwaɓe fuska ga Abulle bayansa ta sheƙe da dariya tana tafa hannu tana cewa "yau dai haihuwa ta min rana" ta ƙare da sakin guɗa   Isuwulle da ya ƙule sai ya zari takalmi yayi kanta ya hau bugu, nan itama ta samu nasarar damƙar muciya ta yo kansa, ganin nata yafi girma sai ya ga wani kututuren icce da za'a haɗa murhu shima ya ɗauka yayo kanta   Abulle dake kallonsu tana ɗirkar dariya ta girgiza kai haɗe da cewa "........ [8/14, 11:48 AM] Mss Flower: *26* "Kai kudakata da wannan shirmen ni sallama nazo yimuku" cewar Abulle ranta fes, Hansatu jin furucin Abulle yasa tayi saurin yarda muciyar hannunta tana kallon Abulle baki sake, "sallama kamar ya Abulle" shakewa Abulle tayi da dariya harda tafa hannuwa sannan tace ai daga nan sai binni hansatuwa Idan Nadawo Baku gane ni kwarankwatsa, Hansatu tace Abulle binni kuma gun wa, "wa kika sani a binni Abulle kuma Ina Auren naki?" "Nifa ba zuwanayi don ki Ishen da tambayoyi ba Eheee, aure kuma na ya kice ya Dan megari yamin saki ukku na don haka banjin zanya iya kara minti 30 acikin kauyen nan daga nan gidan delewa zani nima takaini aiki binni" tafada tana kwanto habar zaninta tareda ciro budu biyar taba Hansatu, "Hansatu ki aje wannan a gun ki Idan isuwulle bai baki abinci ba sai siya don nasan ba mutunci yacika ba" tafada tana wulla ma isuwulle harara, "toh ni nayi gaba" Abulle tafada tana tafita gidan, Abunka da y'a da uwa duk yanda Abulle ta takura musu sai da taji ba dadi, Kasa Hansatu tayi da Kai tana goge yar kwallan data ziraro mata wani munafukin kallo isuwulle ya buga mata tareda cewa "munafukar banza munafukar wofi kukan uwar me kike daga Allah y raba mu da annoba Idan kuma kaunar nata kike sai kitashi kibita" yafada yana buga uban tsaki tareda shigewa daki. Abulle nafita gidan sukayi cikibus da bintalo kallon Abulle tayi tana cewa "iya Abulle daga ina kuma sai Ina?" Washe jajayen hakoranta tayi tana "ai Abulle kuma sai binni ko kinsha wasa nasa nake" sake baki bintalo tayi tana au Allah wai daman dagaske kike Abulle" tafada cikeda mamaki, kallon kasa kasa Abulle tamata tana cewa "sai ki bari sai kinga Abulle a talabijin kokuma ansauke ni a gibgegiyar mota sannan" tana gama fada tai gaba abinta. A kofar gidan deluwa ta rafka uwar sallama tareda kutsakai tsar gidan, deluwa ta gani zaune tana surfe kujera Taja ta zauna, "A'a abulle yau kice a gidan namu" tafada tana cigaba da surfen ta, "Aikuwa ga Abulle nan daga nan kuma sai birni ba" tafada kanta tsaye Dan zaro ido deluwa tayi tana cewa "Abulle binni kuma gun wa kuma wa zai kaiki" " ke deluwa ki saurareni banson rainin hankali yawwa binni zaki kaini yanzunan Inda kika Kai yara yan aiki" gabanta ne yayi mumannan faduwa Dan tasan ko hauka take bazata fara Kai Abulle aiki birni ba, kafin hali tayi tana cewa "Ai abulle masu aiki sai ance Anaso sannan muke kaiwa Amman yanzu kam babu mai bukatar Dan aiki" tafada tana sharce zufar dake tsatsafo mata, deluwa kwarankwatse bani kwana ko ina sai binni ehe don haka tin cikin laluma kitashi mutafi binni" tafada fuskarta murtuke, mikewa deluwa tayi tashiga daki tareda rafka tagumi tana sharce zufa tunanin ta daya shine Ina zata Kai Abulle gashi mutun daya ne masu bukatar yan aiki Amman Ina zata fara Kai musu Abulle, zabura tayi ta sabi hijab jin Abulle na kwalla mata kira daga waje, fitowa tayi sanye da hijab tace muje mikewa tayi deluwa na gaba Abulle nabiye da ita suka nufi can tashar kauyen dake gaban nasu don nan ne ake hawa motar zuwa garin Kano, Suna isa tasha suka iske wata rubabbaiyar bus wacce batada maraba da kwanko shiga su abulle suka yi shuka hakince a mota, kwamdastane yace "ke ina kudin motar ku ku kawo dubu biyune harara abulle ta zabga masa tana kudin mota kwarantsa ban biya kuma dani zaayi tafiyar,nan ba karamin daru da rigima akayi da Abulle ba kan cewar bata biyan kudin mota, fizgota kwandastan motar yayi ita da deluwa ya watsar a gefen titi suka shisshiga da zumar kama hanya driver ne yashiga yaba mota wuta amman yaji dipp yayi yayi mota taki tashi, kallon kwandasta yayi yana kaga karfen nasara koh lpia lau fa motar nan take amman ji wai taki tashi, jin sanyi sanyi na bin hannun sa yasa yayi saurin kallon hannun wani murdeden maciji yagani bakkirin yana bin hannansa, wata uwar kara yasaki yana fita motar da gudu nan kuwa kowa na motar ya watse kwandasta da garin fita yayi kundunbale yafada akan wani katon dutse nan kansa yafashe yana zubar da jini, Abulle kuwa banda bariyar mugunta babu take a inda kwamdasta ya watsar da ita, kallon driver tayi tanacewa "to kutafi nagani mana" tafada tana gabbabewa da uwar dariya, rarrafowa driver yayi yana ba Abulle hakuri akan Idan tasan da sa hannunta tayi hakuri, cewa tayi zan hakura Amman da sharadi daya "cewa yayi tafadi ko menene zanyi" to Idan ka yarda ni kadai za'a dauka a gaban mota" "eh bakomai naji na yarda" to muje tafada tana yin gaba umarni taba macijin nan kuwa ya kama gabansa ya tafi, abulle ta hakimce gaban mota suka kama hanyar garin Kano, tafiyar awa 4 hudu sukayi har Abulle ta gaji ga uwar yunwa na damunta, Sai bayan laasar sannan suka sauka a tashar Kano napep suka Tara suka ce ya kaisu nasarawa. *Sadeeq pov* "Ooh ni sadeeq tinda mukayi maganar mai aiki ban kara jinka ba" cewar mom tana kallon sadeeq, "mom nafa Bama umman sultan cigiya Idan su samu wata daga inda aka kawo mata nata sai kema akawo miki kuma ko jiya na mata magana kuma tace min tasanar musu indai akasamu zaa kawo miki" cewar sadeeq cikin muryar lallashi, "To shikenan Allah de yasa asamu nan kusa don wallahi nagaji" to ameen mom insha Allah ni zan wuce aiki kar na makara, "ubangiji Allah y bada sa'a, Allah yasa a dawo lpia" mom tafada masa tareda rakashi bakin kofa, "Ameen mommy na" yafada yana murmushi. Yana fita su Abulle na shiga gidan, sai kalle kalle Abulle take, tuntubine tayi saura kadan ta fadi akan sadeeq yayi saurin matsawa tareda jifarta da wani kazamin kallo, cikin fushi yace "ke bakida hankali ne ko baki gani ne kike tafiya kina kalle kalle" zuba masa kwala kwalan idanunta tayi tana kallon sa don bata taba ganin mutum mai kyau irin nasa ba, "deluwa Aljannah kika kawo ni ne daman naji anacewa akwai samari masu kyau can Ai ko gashi nafara gani ikon allah ashe dai inada rabon zuwa aljannar nima tafada tana barkewa da dariya harda tuntsirewa kasa, saurin matsawa sadeeq yayi yana a'uziyya don yaga ma tsorota gaba daya Bama daya kalli fuskar Abulle yayi tunani Aljana yagani mikewa Abulle tayi tana nufoshi, ganin yana ja da baya yasa itama tayi saurin binsa tsere suka fara a tsakar gidan yana "auzubillahi minnashaidanirrajim, lailaha illa anta subahaka inni kuntu minna zalimin" ita kuwa sai babbakar dariya take tana kokarin kama shi, da kyar yasamu yafice gate din yashige mota tareda saka lock tana zuge glass din motar gaba daya yana maida nufashi tareda cewa.......... *It's not free duk wanda yakarmta bai biya ba matsalar sa ce don zamu hade a can, don haka kuji tsoron Allah* ✍ *Mrs Abdool & mss flower* [8/14, 11:49 AM] Mss Flower: *29* Ahankali sadeeq ke Kai breakfast bakinshi ci yake Amman duk abincin baya masa dadi yarasa dalili, kallonsa mom tayi tana cewa "son lafiya dai Naga duk kazama wani iri?" Mom bakomai yafada tareda basarwa, "am son plss tinda Naga yau evening zakaje y not kuje shopping da zainab sai kusiya duk abinda yadace kokuwa" saurin ajiye spoon din hannunsa yayi tareda zaro ido yana mom wallahi yanzu aka kirani emergency zan ma wata theatre I can't make it" ok shikenan Tom sai muje da ita anjima cewar mom tana Kai spoon bakinta, "mom y not kuje keda sultana tinda Naga baki san zuwa ke kadai" to Dan me bazanje da zainab din ba" mom tafada tana kallonsa "mom yanzu sai ki dauki yarinyar nan kutafi kasuwa ta dauko miki magana kin dai San bakauyen mutum" eh toh kuma haka ne fa bari munje da sultana din" tafada tana ture plate din gabanta alamun takoshi. Har sadeeq xai Mike mom tayi gyaran murya tareda cewa "son I have start thinking of enrolling her in skul sbda Naga she's too young ne ko aikin ma sai ahankali zankoya mata koya kagani" eh its a good idea but gaskiya mom akwai aiki a gabanki u have to teach her many things..." bai rufe bakinshiba yaga Abulle tsaye ta zuba masa ido daurewa yayi yana "ke baki gaisuwa bane" dariya ta kwashe dashi harda tafawa tana kokarin matsowa kusa dashi, tsawa ya daka mata lokaci guda yana mikewa, turo baki tayi tana kallon Mom, mom kallon sadeeq tayi tareda daurewa " Sadeeq gaskiya banson haka" zainab zo kici abinci kinji koh mom tafada mata murmushi, takowa tayi ta zauna kusada mom, shiko sadeeq mikewa yayi ya nufi kofa, mom cewa tayi "karka manta kashiga kagaisheda ummunku ta karye" gyada mata Kai yayi yafita. Abulle data saka abinci a gabanta ci kawai take hannu baka hannu kwarya kaf saida ta cinye komai na tebirin tashanye tea Din sannan tasaki uwar gyatsa tana jinginewa jikin kujera, kallon ta kawai mom take cikeda mamakin Inda takai abincin dataci, daurewa tayi tace zainab ban san dabiar nan ji yanda kike cin abinci fa and wannan gyatsar ta mutanen banza ce karki sake yinta kina ji koh Alhmdullh ake cewa" daga Kai tayi mom tace ba daga min Kai zakiyi ba cewa zakiyi toh, toh tace tana kallon Mom, tattara kwanukan nan kikai kitchen gashi can, mikewa tayi takai ta dawo, tv mom ta kunna mata tareda cewa kizauna nan karkije ko ina zanfita Nadawo kinajina koh, toh tace tareda zama tana zuba ma tv manyan idanunta. Sadeeq nafita part din umma yanufa Kai tsaye ya nufi dakin ta kwance ya iske ta da hannunta a daure, kansa a kasa ya gaisheta a dakile ta amsa masa tana cewa "na tabbata da amina ce ta karye ai da bazaka yanzu ba, Amman dayake ni daman baa nuna maka girmana ba baka daukeni a bakin komai gashi sai yanzu kake zuwa, yiyayi kamar baiji maitace ba ya zauna gefen gadon yana mata yajiki, "umma wai ya akayi kika karye ne?" Hmm wallahi Abubakar kunemo malamai ayima gidan nan rukiya don jiya aljanu nayi gamo dasu suka kadani don ma Allan y takaita da bansan abinda zaifaru ba" dariya ce taso kwace ma sadeeq Amman ya daure tareda cewa Allah y sawake yafita da harara tabiahi tana sai kace mutumin kirki. Mom har tafita taji bata natsu ba hakan yasa takoma ta kulle kofar falonta da key sannan suka wuce kasuwa ita da sultana, siyayya mai dinbin yawa sukayi na abubuwan anfani tindaga kan kaya underwear, kayan shafa, kayan wankin Kai,takalma Macline brush da komai dai dasuka dawo biyawa tayi gun tela ta kaimasa dinki tabiyasa sannan suka nufi gida. Kayan suka shiga dasu ciki nan tasaka Abulle a toilet tashiga yimata wanka sabi biyar tama sannan ta wanke mata Kai, shikuma saida aka masa sabi goma sannan don kamar an juye masa tifar yashi, bayan sungama ta mata brush sannan tamata shafa gamida gyara kan sannan tasaka mata wasu yan kanti data siyo mata gamida saka mata turare, sosai Abulle tayi fess abinta kamar ba itaba kallon ta mom tayi tana murmushi tace "kinyi kyau" kallon kanta tayi a madubi ta buga tsalle tana kyalkyatar dariya harda faduwa kasa "kwarankwatsa kamar ba ni ba" daurewa mom tayi tareda harararta lokaci guda ta natsu tana cewa "yi hakuri hajiya mantawa nayi" kidena cemin hajiya mom zaki rinka cemin, sannan daga yau duk abinda namiki shi zaki rinka yi wanka da wanke baki Kullum sau biyu safe da dare sannan ki kirinka saka turare kuma Kina saka wando mace Idan tana zama ba wando maciji ke shige mata, kwalo ido Abulle tayi tace "Allah kuwa nadena" sannan kuma Kullum da safe dani da mutanen gidan zaki rinka cemusu Ina kwana Kina ji na, sai kuma wannan dariya da rantse rantse duk nagaya miki ban so Idan baki dena ba kuma can kauye zaki koma, Aa mama ba sai na koma Bama duk zan dena. [8/14, 11:49 AM] Mss Flower: *28* Haki Sadeeq yake tareda jingina bakin ƙofar, Abulle miƙewa tayi itama ta nufi ƙofar fita falon tana ƙoƙarin turawa ta kasa, faɗi take "dan Allah ɗan aljanna ka buɗe, kwarankwatsa kallonka kawai zanyi" ta ƙarashe tana tura ƙofar da ƙarfin gaske sai ga Sadeeq a ƙasa, cikin sauri ya miƙe ya ranta a nakare yayi ɗaki yana ta adduo'i domin shi bil haqqi yayi zaton Abulle aljana ce, zama yayi bisa king size bed ɗinsa yana maida numfashi gamida karanto duka ayoyin tsarin da suka zo bakinsa Abulle zama tayi kan tantagaryar interlock na tsakar filin tana faɗin "Wallahi wannan bashida mutunci ya tsaya na kallesa kawai amma dan mugun hali sai ya fece" ta ƙare da jan ƙwafa Sadeeq kwanciya yayi bisa gado yana lumshe idonsa, wayarsa ce tayi ƙara ganin Mom ya sanya ya cira, "Sadeeq ya kuma kana shigowa zaka fita ne", shiru yayi sannan yace "wallahi Mom aljana ke bibiyata tun safe", cikin zaro ido Mom tace "ina kaga aljanar", shiru yayi sanan yace "duk inda naje bina take gashi yanzu da na shiga ɗakinki ma na ganta tana kallo harta miƙe ta biyoni" Mom sai a lokacin ta fahimci zancensa sanan tace "kai Sadeeq da wani abu kake, sabuwar mai aikin da aka kawo mana ce kasan mutum daga ƙauye sai haƙuri" Sadeeq shiru yayi yana ƙoƙarin gasgata zancen Mom zuciyarsa na ƙaryatawa, chan dai ya miƙe ya nufi sashen Mom zuciyarsa na bugawa, zaune ya kuma tadda Abulle ƙasan carpet gaban tv ta wage baki da hanci tana kallo Mom dake bisa kujera tayi masa ƴar dariya, gaisheta yayi sannan ya nufi dining ya fara cin abinci, talla aka tafi hakan yasanya Abulle ɗauke kanta gamida jan tsaki, idonta ne ya sauka akan na Sadeeq ai kamar an zungureta ta miƙe ta nufesa, tsayawa tayi ƙiƙam a kansa yayinda ta kafesa da idanuwanta manya Cikin ɓacin rai Sadeeq yace "ke wai mene hakan bakida hankali ko me" ya faɗa yana watsa mata harara Tsaki Abulle ta ja sannan tace "Malam ras nake kwarankwatsa da hankalina kuma ko me zaka ce ba zan daina kallonka ba ɗan rainin hankali da ka gama guje gujen yanzu ai gashi ka dawo ko" ta faɗa tana yatsina fuska Tsaki Sadeeq ya ja ya miƙe daga kujerar cikeda takaici, Abulle rufa masa baya tayi, wajen Mom ya je ya zauna ya riƙe hannunta cikin ƴar shagwaɓa yace "dan Allah ki kori wannan mahaukaciyar zan samo miki wata" Abulle ce ta sheƙe da dariya sanan ta tuma a ƙasa tace "kai kwarankwatsa mai kama da sharufkan ba inda zani, nazo kenan zuwan sojan badaskare, ni wallahi ka bani dariya ji yanda kake shagwaɓa gansamemen ƙato da kai kamar na goye" Sadeeq haɗe girar sama da ta ƙasa yayi sannan yace "wallahi idan baki fita sabgata ba sai ɓallaki a gidan nan" ya ƙarashe yana furzar da iskar baƙin ciki "Jar uba, wallahi mai kama da sharufkan ƙashina tauriƙiƙi nake gaya maka, ƙashina ƙwari ne dashi bai iya karyuwa" ta faɗa tana hamma Tsaki Sadeeq ya ja sanan ya fice daga part ɗin domin kallon Abulle ba ƙaramin ɓata masa rai yake ba Abulle taɓe baki tayi tace "ohoo dai ko banza zan dinga ganinka", Mom ta kalla tace "Hajiya wallahi yunwa nake ji", Mom dubanta tayi tace "buɗe warmer can ki ɗiba", Abulle da ta kula da inda hannun Mom ya nuna ta nufi wajen, plate ta shaƙare ta zauna ta naɗa sannan ta kife bisa carpet ta cigaba da kallonta Misalin takwas da rabi Abulle tayi sallah bayan Mom ta tilasta mata, ɗakin da Mom ta nuna mata ta shiga tana hamma, zubewa tayi akan gadon 6 by 6 ta bararraje tareda washe baki tace "ohhh ni Abulle yau gani a binni bisan gadon laushi, gaskiya an cuci ɗan ƙauye" ta faɗa tana buga ƙafa haɗe da kwashewa da dariya Mom ce ta turo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, murmushi Abulle ta sakar mata tana cewa "Hajiya sannu da zuwa" Murmushi Mom tayi mata sannan tace "Yawwa yarinyata dama magana nakeso muyi, in har kinason zama dani dole ki ringa sallah akan lokaci, sannan ni macece mai son tsafta bani son ƙazanta ko kaɗan, tsafta kuma ina nufin tun daga kan gashin kanki har zuwa yatsun ƙafarki ya zamana a tsaftacce suke sannan sai mu koma gyaran mahalli sam banison ganin waje kaca kaca dan haka ki kiyaye" "Kwarankwatsa zan kiyaye Hajiya in dai zan zauna a nan niko agwagwa kika ce nazama tsabar wanka ai zama zanyi" cewar Abulle tana washe baki "Yawwa kuma banison yawan rantsuwa kamar wannan kwarankwatsa da kike faɗa da kwaratsi da kikeyi dan haka ki kiyaye, zan fi so ma in kika dawo ba mai surutu ba" cewar Mom tana nufar ƙofa "Toh Hajiya za'a kiyaye wallahi, nagode Allah saka da alheri" cewar Abulle tana ɗaga mata hannu. ... [8/14, 11:49 AM] Mss Flower: 27 ".....no wonder banyi azkar ba yau shiyasa nayi gamo" sadeeq yafada tareda sauke ajiyar zuciya, lekawa yayi bayan motarsa kar yaji an cafko shi ganin bakowa yasa yasake jin relieve tareda yin addua sannan Ya tada motar ya nufi gun aiki,Abulle kallon deluwa tayi tana cewa "deluwa yanaga yana gudu kuma inazaije?" Deluwa da kunya da takaici suka cikata tace ya bazai gudu ba Abulle daga mutum kinfara binsa dagudu" mtwss dan rainin wayo nifa burgeni yayi aradu" cewar Abulle tana turo Baki gaba, sharewa deluwa tayi tace "muje ciki toh ai nan ne nakawoki" washe baki Abulle tayi tana "Allah deluwa nan zakibarki aradu akwai cin dadi wannan gida kamar lahira Kai yan binni sun more kwarankwatse shiyasa nace banzama kauye me akeyi a kyauye ga Inda zan caji insha ruwan famfo" deluwa de bata cede ita uffan ba, adede umma tafito zubarda ruwa ta kichen su Abulle kuma zasu wuce jikake shaa tazuba Abulle ruwan wankin shinkafa masu zafi, ihuu Abulle tasaki cikin azaba tana kallon Inda aka zuba mata ruwan, umman kallon Abulle tayi tana "innahu min Suleimana wa inna hu bismillahirrahmanirahim wannan mahaukaciyar fa daga ina ni safiya umman ta daure fuska tana ke dallah fita nan ba psychiatric bane ko bola Dan haka kama gaban ko na kuma sheka miki ruwan zafi in sale miki fatar fuska" tafada cikeda balaie, Abulle da tagama kuluwa huci kawai take daga inda take tsaye, umma kan tajuya zatashige kitchen wani uban tsantsi wanda bata San daga inda yake ba yaja ta jigib tazube a kasa tareda murgude hannu kara tasaki cikeda azaba don tama kasa tashi ga hannunta datake kyauta ta zaton ya karye, fashewa Abulle tayi da dariya mai amsa amo, lokaci guda suka hada ido da Abulle gani tayi idon Abulle yakoma ja kamar jini tana gefanta da wani kallo mai wuyar fassara, langabewa umma tayi ta suma a gun, deluwa kam takasa magana don gaba daya tagama tsorata da alamarin Abulle Allah Allah take takaita ta wuce abunta, a bakin kofar falon mom sukayi sallama bada jimawa ba tazo ta bude kofar, da fara a ta amsa musu tana musu Iso har cikin falon, Abulle da AC ta bugeta dama ga ta jikkankun kaya yasa tafara rawar sanyi daga tsaye, zama sukayi a kasa sukayi gaisuwa cikin mutun tawa tareda tambayar daga ina, deluwa ce tamata bayanin komai daga kuma abinda yakowasu, murna sosai mom tayi tana tambayar wace mai aikin acikin su, deluwa ta nuna Abulle tareda cewa gabata nan, mom da sai alokacin taga halin da Abulle tace ciki tace "subhanallah mesameta haka" deluwa tayi kasa da Kai tace munzo wucewa ne shine wata mata ta watsa mata ruwa" ajiyar zuciya mom tasauke tana cewa "kuyi hakuri Dan Allah muje ki canza kaya" tafada tana kallon Abulle, mom tace ma deluwa "Ina kayan nata ne" deluwa tasake yin kasa da Kai tace "bamuzo kaya da kaya ba" to gashi sadeeq bai nan bare ya samo mata kaya a kasuwa Amman yanzu bari na samo mata ko na sultana ne tasaka tinda wannan sun jike" tafada tana Danna ma sultana kira waya daga upstairs din mom taleko tana cewa "mom bari naje na dauko mata" tafada tareda sauka ta nufi part nasu, mom tace "Amman kina ganin wannan zata iya aiki kuwa Naga kamar yarinya ce" Abulle data dago da zumar yima mom rashin kunya Amman suna hada ido saitaji takasa mom tamata wani mugun kwarjini abunda Abulle bata taba jiba kenan ko akan iyayen ta, saurin cewa tayi "zan iya mana" Dan murmushi mom tayi tana cewa toshikan, deluwa kallon mom tayi tace "hajiya nizanwuce toh" don gaba daya ta kagara tarabu da Abulle, mom tace "tinyanzu kibari akawo Binci mana" A'a dulewa tace nan mom tabata kudi masu yawa sannan ta karbi nombernta akan Idan da matsala zata kira ta, sallama sukayi da deluwa tafita, tana fita Abulle Tabita deluwa tace "Ina zakakuma kije ai nan zaki zauna, kuma Abulle Banda daukar magana nan ba can bane wallahi gurin sojoji zasu kaiki kokuma su yarda a jeji don haka kibi ahankali kiyi zaman ki Anan kuma karki dawo kauye kinji koh Nina wuce saduwar alkhairi" bata jira fadar Abulle ba tayi gaba abunta harda tuntube tana fita gate din gidan tacire tabude Nokia dinta wacce tasha lobari ta Cire SIM din ta jefar a kwata don batason abunda zai kara hadata Abulle bare Idan tayi wani abun akirata. Abulle takoma falon ta zauna tareda zuba tv ido kamar idanun zasu fado kasa mom da shigowarta kenan Abulle ta kalleta tareda cewa "hajiya yunwa nakeji" yi hakuri zaki ci abunci kinjikoh yama sunan kine? Kai tsaye tace Abulle, mom tace zainab kenan ta gyada mata Kai, kiran sultana ne yashigo wayar mom ta daga salami kawai tasaki tareda kallon Abulle tana cewa Ina zuwa, part din umma suka isa suka daga ta da kyar aka yayyafamata ruwa sannan ta farfado ihuu tasake saki takuma sumewa ganin Abulle kawai take gani ta kyar suka samu ta farfado ga hannunta da ya kumbura sosai mai dori aka kira ya tabbatarda karaya ce tayi Anan aka dorata sannan mom ta karbi kayan takoma gun Abulle, Inda tabarta tana zaune tana kallo, mom tace tashi muje ciki koh sai kiyi wanka ki canza kaya, cewa tayi ita taci abinci sannan, kitchen mom din tashiga don zubo mata abinci, Doctor sadeeq tinda yaje asibiti yakasa focussing akan aikinsa Sam duk jiyake jikin sa ba dadi yarasa miye dalili yanke shawarar komawa gida yayi kawai, yana isa gida ya faka motarsa ta fita part din mom dinsa yanada Kai tsaye, murza handle din yayi tareda sallama yashiga Abulle yagani zaune gaban tv da sauki yayi reverse da ni yar komawa yana auziyya itama jin alamar mutum yasa ta juya tana cewa kwarankwatsa shine ta Mike tareda nufar shi, dede mom tafito rikeda plat din abinci a hannunta kallon su tayi tana sadeeq lpia, ai bai jira mai zatace ba yakoma dagudu tareda rufe kofar falon baki daya........... [8/14, 11:49 AM] Mss Flower: *34* Misalin ƙarfe bakwai da rabi bayan sunyi sallar magariba suka ɗauki hanyar zuwa gidan Malam Abulle a mota sai magana takeyi tana faɗin "mai kama da Sharufkan baka cika alƙawari ba fa, ya kamata ace ka bani furgun ɗin da kayi alƙawari" Cikin jin haushi Sadeeq ya dubeta yace "na rantse da Allah kika kuma furtamin kalma guda a nan zan yasar da ke kuma bazaki koma gidanmu ba" Abulle zaro ido tayi tana son furta "daga magana sai cibi ya zama. ..." amma kasancewar kalaman Sadeeq sun shiga ƙoƙon kanta ta ja bakinta tayi shiru   Tafiya sukayi ta minti ashirin sannan suka ƙarasa wani ɗan madaidaicin gida ginin daa a anguwar hotoro, parking yayi sannan ya dubi Abulle yace "jirani" Abulle bata tanka ba ta bisa da harara, yana fita tace "mai kama da tsula biri kawai"leda ta gani ta ɗauka tana buɗewa taga chocolate, farkawa tayi ta fara ci tana faɗin "ko banza naci bati, marowacin banza kawai" Sadeeq bai jima sosai ba ya dawo tareda cewa "ke fito" Abulle fitowa tayi tana cin chocolate ɗin, daidai ƙofar soro sukayi kiciɓus da Malam, wani irin baya ta jaa ta nufi mota zata shige Malam ɗan murmushi yayi yace "Sadeeq jeka shigo da ita, ka riƙeta da kyau" Da mamaki Sadeeq ya koma yace "ke dallah malama fito" Abulle hawaye ne suka fara kwaranya daga idonta tace "dan Allah kada ka kaini wajensa wallahi tsoronsa nakeji, ka maidani wajen Mom" Cikin jin haushi ya saka hannu ya fincikota, haka ya nufi gidan da ita Abulle sai ihu take tana turjewa gamida ƙoƙarin ƙwacewa amma haka Sadeeq ya shigar da ita ciki, suna ƙarasawa ya gurfanar da ita gaban Malam, Wani irin gunjin kuka ta saki ta cure waje ɗaya tana faɗin "dan Allah ku maidani gida banason nan" Malam duban Sadeeq yayi yace "shigar da ita wancan ɗakin" Sadeeq nufarta yayi yana ƙoƙarin riƙeta ta kai masa wani mugun naushi da ya kaisa ga bango ya bigi garu sosai Ihu ta saki tana "dan Allah ku ƙyaleni, ban cutar daku ba ku rabu dani" Malam hannu ya saka ya kamata haka ta miƙe ta bisa salin alin amma bakinta bai daina kwarara ihu ba, tsakar ɗakin ya ajiyeta dake cike da ganyayyakin magani Sadeeq cikin dauriya ya shiga ɗakin shima don ba ƙaramin buguwa yayi ba Abulle chan ƙusurwa ta samu ta zauna ta haɗe kai da gwiwa tana ta faman kuka Malam ne ya dubi Sadeeq yace "jeka amsomin ƙwarya nan tsakar gida wajen mai ɗakina" "Toh" Sadeeq ya furta yayi waje, taddata yayi riƙe da ƙwaryar tana ƙoƙarin shigowa ɗakin Miƙa masa tayi tace "gashi tallabe da hannu biyu sannan karɓi da bismillah" Da bismillah ya amsa da dukkan hannayensa ya shiga ɗakin dashi, miƙawa Malam yayi Malam amsa yayi ya fara karanta adduo'i yana tofawa, gamida ɗauko robar zamzam da yake kusan rabi ya juye a ciki sannan ya nufi Abulle bakinsa bai yanke daga adduo'in da yake ba Abulle ihu ta fara saki mai firgitarwa da yafi na daa tana dukan bangon da ya fara girgiza kamar zai tsage biyu, ganin Malam bai daina matsota ba ta kurma kururuwa tana faɗin "wallahi ka matsoni zan kasheka mai nayi maka ne, wa na cutar ne" Malam bai dakata ba sai ya ƙara ƙaimi wajen ayoyin Allah da yake ambata Abulle ta kalli wata randa dake gefen Sadeeq chan wajen ƙofa ta nunata da hannu nan da nan randar ta tashi sama sannan ta saketa ta tarwatse Sadeeq ba ƙaramin tsorata yayi ba domin bayan film bai taɓa ganin irin wannan abun ba, dan haka sosai ya firgita Malam yana ƙarasawa wajenta ya fara watsa mata ruwan magani yana karatu Abulle wani duka ta fara kaiwa bango nan da nan ɗakin ya fara girgiza ihu na tashi kamar a dokar daji Malam bangon ya watsawa ruwan hakan ya sanya ta dakata taɓasa, zubewa tayi a ƙasan gwiwoyinta tana karkarwa tana cigaba da sakin ihu Malam yafara karanto wasu ayoyin Allah hakan ya sanya ihunta suka lafa Chan kamar an tsikareta ta miƙe ta fara kewaye ɗakin tana ƙyalƙyala dariya mai ƙara Malam ne yace "zo nan ki zauna" yayi mata nuni da kan tabarma Babu musu tazo ta zauna tana cigaba da ɓaɓɓaka dariya idan tayi dayawa sai ta tsagaita ta saki kuka Malam yace "maiyasa zaku addabi wannan ƙanƙanuwar yarinya" Dariya ta sheƙe dashi wanda sai da ɗakin ya amsa sannan tace "tun tana ciki aka mallaka mana ita kuma an zubda jini an binne laya dan haka bazamu taɓa barinta ba" Malam cikin jin haushi ya watsa mata ruwa ya fara karanto ayatul kursiyyu Wani ihu ta kurma tana faɗin "zaka ƙonani azzalumi" Malam bai dakata ba, ya cigaba da karatu yana mata yarfen ruwan magarya da zamzam Wani karaji ta saki ta dirka tsalle sai gata saman ceiling tana ƙyalƙyala dariya Sadeeq bin ceiling ɗin yayi yana kallonta, sosai ya kuma razana dan shi bai taɓa witnessing horror event ba irin wannan, ganin yanda Abulle ta fara wulwulawa kamar fanka tana dariya ya sanya ya zube ƙasa ya maƙalƙale yana karanto adduo'in tsari Malam karatunsa ya ƙara ƙaimi yana cigaba da watsa mata ruwa duk da tana sama Wata girgiza Abulle tayi ta diro ƙasa ta fara kartar bango Malam zaren tabarma ya ɗauka a ƙasa ya nufeta dashi ya ɗaureta dashi Abulle fizge fizge ta farayi amma ta gaza katse zaren dan haka ta cigaba da sakin gunjin kuka tana harbe harbe Malam ya dubi Sadeeq dake rakuɓe yace "Sadeeq muje waje ko" Fita sukayi sannan Malam ya kuma duban Sadeeq da keta rawar ɗari yace "kaje gida yanzu bazaka iya tafiya da ita ba domin muddin ta bar ɗakin nan yanzu babu mai kuma ganinta, insha Allah zata samu sauƙi, gobe kazo da wuri ka kuma ƙaromin zamzam in kana tahowa" Godiya sosai Sadeeq yayiwa Malam sannan ya nufi motarsa zuciyarsa fal tsoron abinda ya gani.... [8/14, 11:49 AM] Mss Flower: *31* Shiru motar har suka ƙarasa gida bata ƙara cewa kanzil bas, yana parking ta ɓalle ƙofar ta fice a guje, Sadeeq girgiza kai yayi yace "wannan yarinya ba hauka kaɗai ta tsaya ba da alama shafar jinnu ce", Abulle faɗawa tayi parlor babu sallama, kiciɓus tayi da Mom dake yawo da kaskon turaren wuta, harara ta watsawa Abulle sannan ta cigaba da aikinta, Abulle ganin haka kuma Mom bata kallonta sai ta murguɗa baki tayi hanyar ɗakin da take, Mom cikeda takaici tace "Zainab zo nan", Abulle ƙarasowa tayi tace "gani" tana soɓaro baki, Mom hararta tayi tace "wai bana gayamiki banason hauka a gidana ba, yanzu abinda kikayi shigowa a guje babu sallama haka musulunci yace meyasa ke bazaki yi hankali ba ne, kuma na tura akaiki makaranta da kika dawo maimakon ki sanar dani sai kika zumɓuro baki kikai hanyar ɗaki, kin kyauta kenan" cewar Mom, Abulle ranta da ya soma ɓaci tace "ai dana shigo ina murna na faɗa miki sai kuma kika harareni shiyasa nayi banza nima", cikin takaici Mom tace "wallahi abinda na faɗa miki dai ki kiyaye in ba haka ba sosai zamu dinga samun saɓani dan banison yarinya mara nutsuwa" cikin ɗan faɗa faɗa, Abulle bata ce komai ta juya ta wuce ɗaki, idanunta sun kaɗa sunyi jawur kamar an watsa mata barkono, Mom girgiza kai tayi tace "Allah ya shiryeki". Wunin ranar haka Abulle tayisa cikin ɗaki sai ɓacin rai da take ji kamar ta kashe mutum, abinci ma kasa ci tayi saboda yanda take jin zuciyarta na tafarfasa kamar ana hura mata wuta, misalin shida ta sakko, zaune ta tadda Mom da Sadeeq idanunsu na kan tv suna kallon sunnah tv, ɗauke kanta tayi daga kansu tayi wucewarta harabar gidan, Mom girgiza kanta kawai tayi batareda tace uffan ba, Abulle zama tayi bisa kujerar cement cikin wata ƴar rumfa tana jin wani zafi a zuciyarta ta rasa na mene, kuka kawai ta fashe dashi kamar an kashe mata iyaye, Umma ce ke tafiya tana amsa waya hannunta ɗaya yana a ɗaure, daidai ta iso wajen Abulle taji kuka, zagayowa tayi ta kalli Abulle data kife kai tace "ke dan ubanki me kike nan, me kika zoyi gidan nan irin yaran ɓarayine ko, to tashi ki fita dan uwarki", Abulle zuciyarta nan da nan ta ƙara tsananta da zafi ji take kamar ana gangamin hura itatuwan wuta amma sai ta share bata tanka mata ba, Umma ce ranta ya ɗan ɓaci ganin tana ma yarinya ƙarama magana amma ta ƙi tanka mata yasa ta nufota, hannunta mai lafiya ta wara ta ɗaka mata dundu a baya, wani irin miƙewa Abulle tayi a zaɓure idanunta sunyi jajajur ta kuma kafe Umma dasu, Umma a tsorace da Abulle ta soma ja baya, wani irin kukan kura Abulle tayi tai cikin Umma da duka, dukanta take cikin ƙarfi, nan da nan Umma ta wage baki tana ihun neman a gaji, Abulle kam taƙi sausauta mata itama sai ƙara take tana cigaba da dukan Umma, Sadeeq da Mom dake kallo ne suka fara jin ihu, a guje suka runtumo, cikin tashin hankali Mom ta nufi Abulle tana ƙoƙarin rabata da Umma amma ina sai ƙara take tana ƙara ƙaimin dukan Umma, Sadeeq ne yaje ya riƙeta tam nan ma sai fizge fizge take amma sai ya riƙeta da dukkan ƙarfinsa bakinsa na karanta adduo'i domin tabbas da gani jinnu ne Abulle ta tada, a parlor ya kwantar da ita tanata fizge fizge tana maganganu marasa kan gado, addu'a ya cigaba da tofa mata da ayoyin Allah har fizge fizgenta ya fara raguwa zuwa chan bacci ya kwasheta, Mom ce ta shigo lokacin ranta duk babu daɗi kallonta Sadeeq yayi yace "ya jikin Umma?", zama Mom tayi tace "da sauƙi amma duk ta kurje mata fata har ta lalata gyaran karayar da aka mata yanzu ake ƙara gyarawa", shiru Sadeeq yayi can kuma ya nisa yace "Allah ya bata lafiya", Mom ce ta kalli Sadeeq tace "ashe iska take shiyasa tayita ɓacin rai ɗazu ba gaira ba dalili, Allah ya sawwaƙa" Misalin takwas na dare Abulle ta buɗa ido, hamma ta saki ta miƙe tayi ɗaki a guje, Mom da kallo ta bita tana addu'ar Allah yasa ba iskar bane basu tafi ba, tana tsaka da tunani Abulle ta sheƙo ciki a guje, dining ta nufa tana dafe ciki, ci ta hau yi kamar babu gobe, tana cikin cin abinci Sadeeq ya shigo kallonsa tayi ta ɗauke kai ta cigaba da tura abincin, tana gamawa ta cika kofi da ruwa sannan ta saki gyatsa, ganin ta ƙoshi yasa ta sauko daga dining ta ƙarasa kusada Mom tace "wallahi Mom da mugun fitsari na tashi ba dan Allah yasa na farka tsaf zan yisa a kwance, sai kuma abin mamaki ina gamawa wata uwar yunwa ta tasomin sai yanzu naji wasai wallahi", Mom ta kalleta tace "toh sannunki ki dai kwanta da wuri kinsan gobe zaki makaranta", Abulle ce ta dubi Sadeeq tace "dan Allah Yaya Sharufkan ka siyomin wanan abun mai yaji da Anty ta saimin bansan yanda akayi suka ƙare ba" ta ƙare tana langaɓar da kai, harara Sadeeq ya watsa mata yace "sai kisa na siyo" ya faɗa yana miƙewa gamida yiwa Mom sai da safe *next day* Misalin bakwai da rabi Abulle ta sakko cikin doguwar rigar kanti da ƴar ƙaramar hijabinta, parlor ta tadda Mom tana zaune bisa kujera tana lazimi, tsugunnawa tayi tace "Mom ina kwana" cikin fara'a Mom ta amsa mata da "lafiya lau, kin shirya ko ƴar albarka", Abulle dubanta ta kai kan dining tace "eh na shirya", Mom tayi murmushi tace "toh acici jeki ci abincin kafin Sadeeq yazo ya kaiki", gyaɗa kai Abulle tayi ta nufi dining, plate biyu ta shaƙare da jellop ɗin couscous ta hau ci ba ji ba gani tana korawa da black tea, tana cikin cin abinci Sadeeq ya shigo, gaida Mom yayi sannan ya kalli Abulle dake hannu baka hannu ƙwarya yace "baƙauya ki hanzarta ni ina sauri", Abulle kalmar ta baƙanta mata dan haka ta ɗago bakinta fal couscous tace "kai kuma mai kama da kirista", Sadeeq cikin fushi ya ɗauki remote ya kwaɗa mata sai kuwa a goshinta, dafewa tayi saboda tsananin zafin da ya ziyarceta, kuka ta fashe dashi tana "Allah ya isa ban yafe ba baƙin mugu", Mom cikeda takaici ta miƙe ta bar wajen saboda maganar gaskiya ita yarinyar duk ta fara sure mata rashin kunyarta yayi yawa, tana shekara tsakanin sha uku ta kalli Sadeeq da yake wajen talatin ta mai irin zagin nan kam ai ba mai tarbiyya bace, a daa tayi niyyar gyara yarinyar tunda ance ɗa na kowa ne amma yanzu yarinyar ta soma fita a ranta, Sadeeq ɗaukar jakarshi yayi zai fice, Abulle dake kuka tayi zumɓur tabi bayansa sai kumbure kumbure take, ganin ya buɗe mota tayi sauri ta shiga, kallonta yayi yace "fitarmin", maƙe kafaɗa tayi tace "bilahillazi bazan fita ba", Sadeeq ganin zata iya ɓata masa lokaci kuma yanada theatre yasa ya fizgi motar a guje, saitin gate na makarantar ya tsaida motar tareda cewa "fita", Abulle ta murguɗa baki tace "ko baka faɗa ba", haka ta ƙarasa cikin makarantar ranta a ɓace, office ɗin principal ta nufa, yana ganinta yace "Zainab kin ƙaraso kenan, ina yayan naki", taɓe baki Abulle tayi tace "ohoo masa ya fece" ta ƙare tana jawo stamp ɗin da taga ya bugawa wata takadda, ɗauka tayi ta dinga bugawa teburin, principal da yake duba takadda ya juyo, cikin tsawa yace "ke dallah ajiye bakida hankali ne", Abulle direwa tayi nan fa wani haushi ya cikata zuciyarta ta hau tafasa, principal ya dubeta yace "taso muje na kaiki ajinku" ya ƙare yana gaba, Abulle binsa tayi lokacin da suka shiga har an fara lesson, wani sit ya nuna mata tsakiyar wasu yara mata yace "jeki zauna", Abulle bata tanka masa ba ta wuce ta zauna batareda ta tanka kowa ba, principal na fita, malamin ya juyo yace "new comer what is ur name", Abulle haɗe rai tayi ta ƙi cewa komai, jin tayi shiru ƴan aji suka kwashe da dariya, dariyar da ta ƙara fusata Abulle sai ta fashe da kuka, haka tayita har period ɗin wannan ta ƙare, haka har aka fita break Abulle kuka take, wadda take loko ce tazo fita babu hanya dole sai Abulle ta gyara, buɗar bakin yarinyar tace "ke ƴar ƙauye matsamin na wuce", Abulle banza tayi da ita, yarinyar ta saka ruler ta ɗan zungureta tace "ke ƴar ƙauye dallah ki matsa", Abulle wani kukan kura tayi ta hau naushin yarinya tana ƙara kan kace kwabo nan jini ya fara kwaranyar ma yarinya daga hanci, ƴan aji suka fara ihu suna faɗin "aljanu aljanu" nan wasu suka garzaya suka kira malamansu, islamic teacher ɗinsu ne ya samu ya raba Abulle da yarinyar da har ta sume, sai ƙara ƙaimi take tana fizge fizge zata ƙara dukanta, staff room aka wuce da ita sai fizge fizge take, malamin addua ya fara mata yana mata karatu, wata iriyar kururuwa ta fara saki ta fara jifa da teburan dake cikin wajen, nan da nan malamai mata suka fara guduwa, sosai Abulle take ihu da kururuwa, da ƙyar wani malamin PHE ɗinsu ya riƙeta ya danneta, malamin islamic ya matuƙar tsorata domin bai taɓa gamuwa da iskokai irin waɗan nan ba, dole ya ajiye karatu ya fara mata adduo'in da zasu lafa... [8/14, 11:49 AM] Mss Flower: *30* *next day* Abulle ce take nufo Mom dake zaune kan doguwar kujera, sanye take da english wears riga da skirt wanda sukayi mata ɗasss a jiki, zubewa tayi ƙasa tana dariya haɗe da cewa "Mom barka da hutawa", Mom ɗagowa tayi daga danna wayar da takeyi tace "lafiya lau, ya kike" tana mai duban Abulle sai a lokacin ta fara hango wani ɓoyayyan kyau na yarinyar, Abulle ce ta ɗora hannu bisa kai ta buga haɗe da sosawa, Mom tace "lafiya dai", Abulle sai da ta gama susa sannan tace "wallahi kaina ƙaiƙayi yake ne" ta faɗa tana kyaɓe baki, "Ayyah bari na kira Sultana naji ranar da zata saloon sai kuje tare a wanke miki kan", ta faɗa tana dannawa layin Sultana kira, cikin sa'a Sultana tace yanzu zata harma ta shirya tanason zuwa kitso, Abulle ƴar ƙaramar telha da Mom ta siyo mata ta saka sannan ta fito haramar gidan tana kalle kalle, dubanta ta kai kan wasu flowers masu ɗaukar ido tace "wai! Gaskiya ƴan binni na mulki, jar uba ni abinda ke ban mamaki ma yanda suke rayuwa kamar baza'a mutu ba bayan dole sai an turbuɗe mutum a ƙasa" tana tsaka da hirarta ta hango kyakyawar budurwa mai ɗan kama da Sadeeq, Abulle ƙuramata ido tayi cikin ranta tana cewa gaskiya dukka ƴan binni kyawawa ne, Sultana murmushi ta sakar mata tana cewa "Zainab ko", Abulle gyaɗe kai tayi tana cewa "ko kice Abulle", Sultana dariya ta saki tana cewa "kinada abin dariya, mene Abulle kuma" ta riƙe hannunta suka fara tafiya tana sakin dariyarta, saloon suka wuce cikin motarta, sosai aka wanke dandaƙwalin kan Abulle da yake cinkushe da amosani, drying akayi mata sannan aka mata streching, sosai gashinta ya miƙe har dokin wuyanta, sai murna take bakinta ya kasa rufuwa tana taɓa kanta, ko da aka gama ma Sultana kitson, super market Sultana ta wuce dasu inda tayi musu siyayyar ƙwalama sosai sannan ta saima kanta mayukan shafawa, Abulle ce ta zumɓuro baki, Sultana kallonta tayi tace "lafiya Zainab naga kin sauya fuska", ƙara turo baki Abulle tayi sannan tace "ni ai baki siyamin man shafawar ba", dariya Sultana tayi tace "ai na manya ne amma bari na ɗaukar miki wannan tender skin ɗin", dariya Abulle tayi tace "shiɗinma yayi amma fa da kike gani na kamar yarinya Qur'ani har aure nayi, gani nayi ban iya zama na fita" ta faɗa tana yatsina baki, Sultana dariya ta kwashe da ita sannan tace "kai wallahi kinada abun dariya, ke ɗin ce kikayi aure", dariya itama Abulle tayi tace "wallahi kuwa ƙila kin haifi kamata ko, yanzu wai ke yaranki nawa", ɗan zaro ido Sultana tayi tace "ni banyi aure ba", buɗar bakin Abulle sai cewa tayi "yanzu haka jibgaga dake baki aure ba, toh shi wannan ɗan girman kan ƙaton na gidanku fa yaransa nawa", harararta cikin wasa Sultana tayi tace "ki daina faɗin kowacce magana, wani kuma ƙato kike magana", shiru Abulle tayi sannan tace "yawwa wani Sadiqu mai kama da ƴan aljanna kuna kama dashi sosai" dariya Sultana ta saki sosai sannan tace "Sadeeq shima bashida aure kuma ki daina ce masa ƙato banaso", taɓe baki Abulle tayi sannan tace "toh Anty", har zasu wuce wajen biya Sultana ta tsaya ta saya bands na gyaran gashi da duwatsu sannan sukayi pay, a mota sai hira suke yayinda Sultana ta fasa musu robar pringles suna ci, Abulle kam sai cin abinci take masa tanata dumamusu goma goma take turawa dan haka ta cinyesa duka, Sultana nata mata dariya da zolayarta har suka ƙarasa gida, side ɗinsu Sultana ta ja Abulle, zaunar da ita tayi ta mata kalba masu kyau da tayima kitson kwalliya da duwatsu, sannan ta bama Abulle kayanta tace ta tafi zata shigo anjima, godiya sosai Abulle tayi mata tanata murna ganin yanda kanta ya koma an mai kitso mai kyau, haka ta fito tana ta tsallenta tana murna, a parlor ta tadda Mom da Sadeeq da dawowarsa kenan yana cin abinci, Abulle yadda ledar hannunta tayi ta kwasa a guje wajen Mom tana zare hijabinta tace "ji Mom kaina ya koma na ƴan film da muke gani, kuma Anty ta min kitso har ta jera masa duwatsu" cikin murna, dariya Mom tayi tace "Masha Allah, kinga kuwa kinyi kyau sosai, ashe haka ƴar tawa keda gashi", washe baki Abulle tayi sannan ta nufi Sadeeq dake harararta da durƙusa tana tura masa kanta gamida cewa "ji fa yanda gashina yayi kyau irin na Indiya" ta faɗa tana washe baki, Sadeeq dariya ya tuntsire da ita yana faɗin "shashasha", harararsa tayi sannan ta miƙe ta ɗauko ledarta ta dawo kusada Mom tana fito da kayan da Suhaila ta bata tace "Mom kalli kiga kayan da Anty ta siyamin, kinga wannan abun kwarankwatsa daɗi garai duk da yaji yaji ne dashi" ta faɗa tana nuna mata pringles, dariya Mom tayi ta buɗe mata tana cewa "toh ci abinki", Abulle duban Mom tayi tace "Mom kici kema", Mom girgiza kai tayi tace "bana son flavor ɗin nan", gyaɗa kai Abulle tayi duk da bata fahimci flavor ɗin ba ta hau dumamusar abunta, Sadeeq ne dake kallonta yana yaba ƙauyancinta ya sheƙe da dariya, Abulle ɗagowa tayi ta hararesa tace "wallahi bazan sammaka ba", ɗaure fuska Sadeeq yayi yana miƙewa, taɓe baki Abulle tayi har ya ɓace, Mom ce ta dubeta tace "gobe zan sa a kaiki makaranta", washe baki Abulle tayi tace "Allah ubangiji ya kaimu" *next day* Misalin ƙarfe takwas Abulle ta fito cikin doguwar riga hannunta riƙe da hijab, a parlor ta tadda Mom da Sadeeq, tsugunnawa tayi ta gaidasu, sannan ta ɗebi abinci ta fara ci, bayan taci ne ta ƙoshi ta kwashe kwanukan domin Mom da Sadeeq sun riga sun gama ci dama, Mom ce ta dubeta tace "toh sarauniyar yawo ba ɗan kwali saka hijab ɗinki ku wuce makaranta", dariya Abulle tayi tace "yanzu kuwa Mom", bayan ta saka hijab ne Mom ta dubi Sadeeq tace "har da islamiyya zata dinga tsayawa", Sadeeq cewa yayi "toh" kawai ya miƙe, Abulle binsa tayi har mota, a mota sai faman zuba surutu take ko mai tagani sai ta tanka, Sadeeq da ya fara ƙulewa yace "wallahi idan baki ƙyaleni da surutun banzanki ba zan saukeki a nan", Abulle jin zancensa sai ta kama bakinta bata kuma magana ba har suka ƙarasa makarantar, bayan an mata gwaje gwaje ne principal yace bai san inda zai sata ba dan ko harafin "A" Abulle bata sanshi ba, Sadeeq ne ya roƙi alfarma kan a kaita jss 1 zai samo mata lesson teacher, da ƙyar principal ya amince dan ma yaga ƴa ƴan banki, haka aka biya kuɗin komai na Abulle harda shoes kasancewar komai school take saidawa harda socks kanta, Abulle murna kamar me bakinta yaƙi rufuwa haka suka nufo mota, ko da suka shiga Sadeeq ya dubeta yace "kinga iyayen kuɗin dana kashe akanki ko, toh wallahi muddin kikayi daƙiƙanci sai na maidaki ƙauye gara ma ki maida hankalinki kan karatunki yarinya, zan samo miki wanda zai dinga koya miki bayan an tashi daga makaranta saboda haka ki maida hankali dan kinganni bana asara", Abulle da idonta yayi ƙwal ta gyaɗa kai dan a yanzu ta tsani taji an anbatar mata komawa ƙauye.... [8/14, 11:49 AM] Mss Flower: *33* A gajiye Sadeeq ya dawo, zai shiga part ɗin Mom sai kuma yayi kwana zuwa ɓangarensa Bakin ƙofar shiga parlor yaga uban ruwan kumfa ya taru baiyi aune ba ya jefa ƙafarshi, wani ɓacin rai yaji dan ruwan har ya fallatsarmasa jikin wando, da takalmansa ya shiga, slippers ɗin da yake yawo cikin parlorn ya saka aikuwa ya ji uban ruwa kasancewar slippers ɗin sau ciki ne, tsaki ya ja ya zubda ruwan yana "bari na ɗauko mopper" Ya zira takalmin aikuwa wani santsi ne ya taɗiyesa kasancewar takalmin ƙasansa sumul sumul ne ga kuma ruwan klin da tiles, rimmm Sadeeq ya faɗi, dafe ƙugunsa yayi yana "wannan yarinya anyi mahaukaciya, nima da gangan na sakata aiki ai nasan wawuya ce" haka ya miƙe yana ɗingisawa Carpet ya taka aikuwa yaji ƙafarsa lutsum cikin ruwa, wani irin mugun ɓacin rai ne ya ziyarcesa bai ma bi ta mopper ba ya nufi hanyar waje a fusace, ruwan klin ɗin daya ɗebo a takalmin kuwa suka kuma kwashesa ya zame ya tafi suuuu bai tsaya ba sai wajen tv stand ya bugu da ita, dafe hannunsa daya bugu sosai yayi ya rintse idansa azaba na ratsasa har kwanyarsa, idonsa sun kaɗa sunyi jajajur juyawar da zaiyi idonsa ya sauka kan receiversa dake tsamo tsamo cikin ruwa, saurin ɗagata yayi sai yaga ruwan ta cikinta yake ɗiga, wani malolon baƙin ciki ne ya cikasa, miƙewa yayi cikin dauriya ya bar sashen yana ɗan ɗingisawa har ya ƙarasa sashen Mom Bai taddata a parlor ba dan haka ya wuce ɗakin da yakeda tabbacin na Abulle ne, baisameta nan ba ya dawo na Mom, da sallama ya shiga sai ya taradda Mom tana linke kaya Cikin fushi sai huci yake yace "Mom ina wannan daƙiƙiyar ƴar aikin da kika ɗauko", Mom kallonsa tayi cikeda mamaki sanan tace "ai bata dawo ba tunda ta tafi sashenka, lafiya na ganka a birkice haka" Bai tankata ba ya juya ya fita, sashensa ya koma ya zarce bedroom ɗinsa Kwance ya tadda Abulle sai zuba munshari take tayi ɗai ɗai bisa gadon, hannu ya saka ya fincikota aiko ta mako ƙasa da ƙarfi Cikin tsananin fushi ya hau cewa "dan ubanki bakida hankali zaki min wannan haukan a ɗaki, in bazaki gyara ba ki barshi man amma name zaki lalata min wuri" Abulle da zafin buguwar da tayi ke cinta tace "yanzu Sharufkhan fisabilillahi na gyara maka waje da kyau ka hauni da masifa, kaga baƙar wuyar da naci wajen aikin nan" Cikeda takaici Sadeeq yace "dan uwarki fita, kuma goben nan zaki koma inda kika fito", Abulle dafe kai tayi ta fasa ihu sannan ta fito waje tana ta kuka tana kwarara ihu haka ta ƙarasa har sashen Mom tana faɗin "ya kasheni, wayyoni wayyoni Hansatu ki ceceni" A kiɗime Mom ta sauko tana faɗin "meya faru mai yayi miki" Abulle cikin kuka da shasheka tace "cewa yayi ya tsanan sai ya maidani ƙauye, sanan ya min mugun duka yayita ƙwallo dani yana makani jikin gado ina tunanin ma ya karyamin ƙashin baya, wayyo Allah na" Mom cikin ɓacin rai tace "to ubanme kika masa da zai ce ya tsaneki, wani dalili ne zaisa ya miki wannan dukan" Abulle ta kyaɓe baki tace "wai saboda gyaran bai masa ba kuma nace zan kuma gyarawa amma bai sauraran ba" Cikin fushi Mom ta latsa number sa tace "kazo nan yanzun nan, ina nemanka" bata sauraresa ba ta kashe wayarta Sadeeq haka ya nufo part ɗin har yanzu ransa bai daina tafarfasa ba, zaune ya tadda Abulle kan tantagaryar tiles tanata sheƙa kuka kamar an mata aiken mutuwar iyayenta, tsaki ya ja ya dubi Mom da ta haɗe girar sama da ƙasa yace "Mom kinga yadda wannan daƙiƙiyar yarinyar ta lalatamin ɗaki" Mom cikin fushi tace masa "dakata!! Kai yanzu kana namiji ƙato da kai ka ware ka dinga tamola da wannan ƴar ƙanƙanuwar yarinyar, haba Sadeeq ai ni bantaɓa tsammanin haka daga gareka ba, wannan rashin imanin har ina fisabilillahi", Sadeeq cikeda mamaki yake duban Mom yace "ce miki tayi na daketa", Mom watsa masa kallon banza tayi tace "Ƙarya zata maka ne", girgiza kai yayi yace "Allah ya huci zuciyarki" Mom gyaɗa kai tayi sannan tace "daga rana irinta yau kada ka kuma maimaita shashanci da kayi, zuwa anjima kuma in ka huta kada ka manta zaka kaita wajen Malam", gyaɗa kai kawai yayi zai fice idonsa ya sauka kan Abulle dake masa gwalo.... [8/14, 11:49 AM] Mss Flower: *32* Misalin huɗu Sadeeq ya ƙaraso makarantar dalilin kiran da principal yayi masa, kwance ya samu Abulle a sick bay tanata bacci, principal sosai ya nuna rashin jindaɗi akan abinda iskokan Abulle sukayi, sannan ya nemi Sadeeq da ya kira mahaifin yarinyar da Abulle ta buga ya basa haƙuri, ya kuma ƙara da su tashi tsaye su nema mata magani. Sadeeq ɗaukanta yayi ya sakata a mota sukayi gida, kafin su ƙarasa ta buɗe ido tana ta ƙwalo idanuwa, Sadeeq da ya ganta ta cikin madubi ya watsa mata kallon banza, Abulle tace "dan Allah mai kama da Sharufkhan yaushe aka tashi har kazo ɗaukata", Sadeeq ko kallonta baiyi ba bare ya tanka zancenta haka har suka ƙarasa cikin gida, da gudu Abulle ta kwasa tayi ciki tana kiran "Mom nadawo", Mom dake zaune bisa kujera tana duba newspaper ta ɗago ta kalleta da murmushi kan fuskarta tace "ya makarantar", Abulle zama tayi sanan tace "wallahi bansani ba kawai gani nayi an tashi", da mamaki Mom ta dubeta tace "kamar ya kenan", Sadeeq dake jin hirar tasu yace "ina zata sani tunda ta tada iska ta zane ƴar mutane", Abulle kafesa da ido tayi tana juya kalaman a zuciyarta chan ta taɓe baki tace "ohooo, chan ta matse musu" duban Mom tayi tace "Mom dan Allah kiyi haƙuri nazo miki aiki amma bana yin komai, bari na ci abinci yau kiga aiki a gidan nan kwarankwatsa", Mom murmushi tayi tace "toh ƴar albarka jeki ci abincin" tana miƙewa Sadeeq ya dubi Mom yace "Mom in har bazaki maida yarinyar nan garinsu ba, toh ya zama dole a nema mata magani dan wata rana zata iya kisan kai, kinga yarinyar data daka sai da ta sume saboda wahala, gaba ba'a san mai zatayi ba", Mom jinjina kai tayi tace "yarinyar ce wallahi tausayi take bani shiyasa nake kokontan maidata gida, Sadeeq dan Allah anjima in ka huta ka kaita gidan Mallam Sunusi ya dubata, wanda yayima Sultana gyaran karaya da tayi shekarun baya, ina zaka gane gidan", gyaɗa kai Sadeeq yayi yace "zan gane, Allah yasa a dace dai", da Amin Mom ta amsa masa. Abulle ko da ta gama cin abinci sai ta dubi Mom tace "bara na hau na miki gyaran ɗaki, tasss zan ƙalƙale miki shi" ta faɗa tana ƙoƙarin wucewa, Sadeeq ne yace "ke kin iya gyaran kuwa", Abulle bata tanka ba sai gyaɗa kai da tayi, Sadeeq ya dubeta yace "nima ki gyaramin sashena yanzu, zan ɗan fita kafin nadawo ki gyara da kyau zan taho miki da pringles", Abulle tace "meye furgun ɗin to", Mom dariya tayi, Sadeeq yace "abin nan mai yaji da kikeso", ai wani ihu Abulle ta saka haɗi da daka tsalle tace "yanzu kuwa naka ma zan fara gyarawa muje ka nuna min", Sadeeq cikin jin daɗi yace "yawwa taho muje, Mom sai na dawo", Abulle suna tafiya tana faɗin "ai wallahi wanan furgun ɗin daɗi garesa, ban taɓa cin abu mai daɗi irinsa ba kuma gashi kamar ƙanzo, dan Allah mai kama da Sharufkhan nace wai shi ɗin ƙanzon mene?", Sadeeq ya dubeta yace "ga ɗakin chan, ki gyara da kyau" ya wuce, Abulle harararsa tayi tana faɗi ƙasa ƙasa "ɗan rainin hankali ya faɗan ƙanzon meye ya ƙiya", Abulle ɗakin Sadeeq ta shiga ta ganshi tsaf sai tashin ƙamshi yake, riƙe haɓa tayi tace "ohhh ni Abulle yanzu nan ɗin ba'a gyare yake ba, aikuwa zan masa gyara na ban mamaki", tsintsiya ta ɗauka ta share ko ina tass, sannan ta ciko bokiti da ruwan kumfa, tsintsiya ta sanya ta hau wankin carpet ba ji ba gani, bayan nan tabi parlorn tana wankewa da tsintsiya da ruwan klin, ko da Abulle ta gama sharce ruwan waje sai ta dawo dan ta kunna fankar dake ƙasan carpet ɗin, ta kusa kaiwa ga makunnin wani santsi ya ɗebeta aikuwa tayi muguwar faɗuwa, ta jima tana dafe da ƙugu sannan tace "wai da a ƙauye aka ganni na faɗi da anyi abin kunya", cikin sanɗa da dubara take takawa har ta kai ga makunnin, fanka ta kunna 1 tana faɗin "Allah yasa carpet ɗin ya bushe kan ya dawo", cikin takatsantsan ta kuma haɗo ruwan klin a bokiti da kofi da ɗan tsumma ta nufo wajen kayan kallonsa, receiver ta ɗauka ta tura cikin bokiti tana saɓeta da tsumma sannan ta zaro ta ajiyeta wajenta, kallon tv tayi tace "ke kuma gaki gingima dole ake wankeki a wajenki dan baki iya shiga bokiti",kofin ta saka ta kamfato ruwa ta hau sheƙawa tana gogewa da tsumma kamar tana wankin mota, ta jima sannan ta zube tana haki tace "gaskiya aikin wannan da wuya", miƙewa tayi ta ƙarasa bedroom ɗinsa, duba wajen da yake aje agogonsa tayi dake kan mirror sannan ta ɗebosu, har zata watsasu cikin ruwan omo tace "kai tunda ma basuyi wani dati ba barina gogesu da tsumma in yazo nace na wanke" ta faɗa tana saka tsumma ta hau gogesu sannan ta maida wajensu, toilet ta shiga, idanunta ne ya sauka kan robar shampoo ɗinsa, ɗaukowa tayi tace "ni Abulle ƴan birni sun fiya sanabe, yanzu bayan abin wanke kwanuka wai shi molin firesh harda na wankin bayi" ta ƙarashe tana taɓe baki, buɗewa tayi ta zuba kusan rabi sannan ta zuba ruwa wanke bayin tayi batareda ta ɗauraye ba sannan ta fito ta ɗane gado tana tsalle tana faɗin "jar uba, ohhh wai ni Abulle ƴan binni kuwa zasu shiga aljanna anya ba suna ƙarar da jindaɗinsu bane, ji gado mai laushi haka jama'a" miƙewa tayi ta hau karkaɓe gadon, bayan ta gama kuma ta tuma a kai ta fara bacci..... [8/14, 11:49 AM] Mss Flower: *35* Ko da ya isa gida sanar da Mom halin da ake ciki yayi, bai wani tsaya jan zance ba ya wuce sashensa Daren ranar Sadeeq bai iya baccin kirki ba domin da zarar ya rufe idonsa hoton Abulle cikin yanayin abin tsoro yake gani Misalin takwas ya fito cikin shirinsa, bayan ya gaisa da Mom ya tsakuri abinci, asibiti ya wuce, excuse ya ɗauka ya nufi gidan Malam, a hanya ya tsaya ya sayi zamzam da Malam yace ya taho dashi sannan ya ƙarasa Ko da Sadeeq ya kai ƙofar gidan ƙirjinsa tsananta bugawa yayi domin ba ƙaramin tsorata yayi da lamarin Abulle ba daren jiya, da faɗuwar gaban abinda zai tarar ya kwaɗa sallama "Wa'alaikha salam, shigo ciki Sadeeq" cewar Malam Sadeeq ɗan rintse ido yayi sannan ya shiga cikin gidan, zaune ya tadda Abulle tana cin ƙosai da koko hankali kwance cikin yaran gidan Abulle na ganinsa ta miƙe ta tunkarosa a guje bakinta jage jage da koko Sadeeq ko da ya ganta haka kamar taɓaɓɓiya kuma ta nufosa dan shi iya saninsa hakan bata taɓa shiga tsakaninsa da Abulle ba dan haka sai ya tattare wandonsa gamida jefar da ledar zamzam ɗin hannunsa ya ɗiba a guje Abulle ganin haka itama sai ta daddage ta ƙara ƙaimi wajen gudun tana faɗin "Sharufkhan dan girman Allah ka tsaya abu ɗaya zaka faɗan'' "Wallahi ba zan tsaya ba ku kassarani a banza" cewar Sadeeq da tsabar gudu saura kaɗan ƙafarsa ta kamo ƙeya, bai zame ko ina sai wajen da yayi parking motarsa Cikin hanzari ya zauna ya na maida numfashi Abulle da ta ƙaraso yanzu ta nufi ƙofa tana ƙoƙarin buɗewa amma taji ta rufe, sai ta fara ƙwanƙwasawa Sadeeq ƙofa tana "ka buɗe ko na murɗe ƙofar" sai tai alamun murɗe abu da hannunta   Sadeeq dake kallon bakin ta abinda ya fahimta shine "ka buɗe ko na murɗe wuyanka" aikuwa ya tulo ido waje yana cewa "na rantse bazan buɗe ba ki kassarani, yanda kike juyi kamar fanka jiya nasan tsaf zaki murɗen wuyan bayan ni ba kaza bane, sai dai mu kwana a haka bilahillazi" ya faɗa yana zare mata ido   Malam ne ya fito, nan ya tadda Abulle a bakin mota ga Sadeeq da ya garƙame ƙofa idonsa yayi jajur tsabar firgici Malam ne yaje ƙofar ya ƙwaƙwas, Sadeeq ganin Malam ta ɓangaren da ba nan Abulle ke tsaye ba ya buɗe Malam yace "Sadeeq ya dai naga ka fito da gudu"   Sadeeq duk kunya ta rufesa ya hau sosa ƙeya Malam jansa yayi yana cewa "ai ƙanwar taka ce ba iskokan ba"   Sadeeq jin haka ya sauke ajiyar zuciya duk da har yanzun a tsorace yake da lamarin Abulle dan yau sai duk take basa tsoro   Haka suka shiga gidan Abulle na bayansu tana musu waƙar mai tsumman mara tsumman tana ƙyalƙyala dariya   Malam hannunta ya kama ya shigar da ita ɗakin, zama tayi kan darduma yayinda Sadeeq ya tsaya chan ƙarshen ɗaki saitin Abulle   Malam ruwan magarya da addu'a ya fara haɗawa Sadeeq kam a matuƙar tsorace yake saboda wani kallo da Abulle ke masa tana kashe ido guda tana tuntsirewa da dariya duk ya sha jinin jikinsa   Malam ne ya fara mata yarfin ruwan maganin, wata gigitacciyar ƙara Abulle ta saki ta miƙe tayi cikin Sadeeq   Sadeeq ko da yaga ta tunkaraso a masifar gudu bayada damar kuma guduwa sai ya rintse ido yana jiran ta fizgo ƴan hanjinsa   Abulle ko da ta ƙarasa cikinsa ta ɗora kanta ta hau gogawa tana zabga ihu kamar dai yanda rago keyi   Sadeeq wasu hawaye ne suka fara gangaro masa ya kuma rintse ido yana tunanin yanda Mom zatayi rayuwa babu shi   Malam ne ya ƙaraso wajen yana watsa mata ruwan magani gamida karatun alqur'ani Abulle wani gunjin kuka ta saki ta zube a ƙasa ta fara birgima Sadeeq ko da yaji ta cikasa sai ya buɗe ido, saɗaf yana ƙoƙarin ficewa ta ɗora hannunta bisa ƙafarsa gamida wurgasa ciki Raɓewa yayi jikin bango ko da ta cillasa ciki yana kallon ikon Allah Sosai Malam yakewa Abulle karatu sai faman juyi da nannaɗewa take tana ihu mai saka ƴan hanji rawa   Chan Abulle ta ƙyalƙyale da dariya tace "Malam in har zamu barta sai an tone layar da mahaifiyarta ta binne a ɗakinta tukunna, in ba haka sai dai kayita ƙonamu muna shan wahala mu da ita amma bazamu fita ba!!!" Ta ƙare da kurma ihun da ya sanya ceiling ɗin ɗakin girgiza   Malam banza yayi da batunsu hakan ya sanya ya cigaba da karatunsa Abulle miƙewa tayi ta nufi bango ta hau buga kanta da ƙarfin gaske, jini nan da nan ya fara tsiyayya har ya wanke mata fuska amma bata daina ba Hakan ya sanya Malam dole daina karatunsa ya fara mata adduo'in da zasu lafa   Cikin layi tayo baya, daidai inda Sadeeq yake ta zube a ƙasa sume Malam jinjina kai yayi yace "tabbas akwai al'amari mai girman gaske tareda yarinyar nan dan haka dole muje gidansu a tone layar in ana neman waraka" Girgiza kai kawai Sadeeq ya keyi, bayan sun ɗan tattauna akan matsalar Malam yace zai iya tafiya da Abulle in yaso ranarda suka shirya zuwa garin sai su sanar dashi su tafi   Sadeeq godiya sosai yayiwa Malam sannan yace "insha Allah Malam ai tafiyar bazata wuce jibi ba"   Gyaɗa kai Malam yayi yace "Allah ya kaimu"   "Ameen" Sadeeq ya amsa sannan ya ɗauki Abulle zuwa mota   Ko da suka isa gida, direct sashen Mom ya wuce da ita a hannunsa, kwantar da ita yayi akan kujera sannan ya kira Mom ya sanar mata ya wuce sashensa Misalin biyu da rabi Abulle ta farka, ganin Mom tayi sanye da hijab ta fito daga kitchen A guje ta nufeta ta faɗa jikinta tana "Mom wallahi nayi kewarki, bakiga yanda nake roƙon mai kama da Sharufkan ya kawoni wajenki amma ya ƙiya" ta faɗa tana langaɓe kai Mom ɗan rungume Abulle tayi domin itama sosai tayi kewar yarinyar musamman surutunta da wautarta..... [8/14, 11:50 AM] Mss Flower: *36* *next day* Abulle ce zaune gaban tv ta buɗe ido da hanci tana kallon sponge bob, chan Abulle ta kwashe da dariya ta buga ƙafarta tace "jar uba, ana rainin hankali a nan" Mom da fitowarta kenan tace "Zainab meya faru haka kike ta dariya" "Mom wallahi rainin wayo ne da ƴan film ɗin nan masu zane, ji fa wani wai ya fito daga gidan abarba, kuma yana zubama shuka ruwa ta miƙe tana dariya, yoo wai sun ɗauka mu mahaukata ne da zamu yarda" ta ƙare tana dafe ciki tsabar dariya Mom girgiza kai tayi sannan tace "Zainab tun jiya yayanki yake miki magana amma naga sai kiyi wucewarki" Abulle ƙwalo ido tayi sannan tace "Mom cewa fa yake muje ƙauye kuma ni kwarankwatsa bazan koma zama chan ba" ta ƙare tana murguɗa baki Mom ɗan murmushi tayi ta jinjina kanta sannan tace "Zainab waya gaya miki ƙauye zai maidaki" Abulle taɓe baki tayi sannan tace "ai ko bai faɗa ba nasani" Mom tace "toh yanzu naga gara na shirya muje tare kawai tunda ni kin yarda bazan barki chan ba ko" Abulle washe baki tayi ta hau gyaɗa kai, sannan tace "wallahi ko kamar kinsan na kan ɗan tuna Hansatu" Mom ta dubeta tace "wace Hansatu?" Abulle tace "Innata ce fa" Cikin mamaki Mom tace "mamanki kike kira da haka gatsal" Abulle dai bata ce komai ba sai chan kuma ta dubi Mom tace "wai yaushe zamu je ne" Mom tace "gobe insha Allah" Suna cikin hira Sadeeq ya shigo ɗakin, duban Abulle yayi yace "ke tashi ki bamu wuri zamuyi magana" Abulle turo baki tayi ta ƙara bararrajewa saman carpet ɗin Mom dubanta tayi tace "Zainab jeki ciki kinji minti kaɗan" Gyaɗa kai Abulle tayi sannan ta dubi Sadeeq tace "mai kama da Sharufkan sai anjima" Bai kalleta ba bare tasa ran zai amsa, taɓe baki tayi tana wucewa "Mom yanzu Malam yake sanar dani iskokan Zainab suna ta masa kashedi wai ya fita hurumin da ba nashi ba, yace kuma a haka wai ƙarfinsu ya ragu ne sosai saboda ta bar asalin tushen asirin, so idan ankoma chan zasu iya yin komai amma yace bai yanke ba, in ta faɗi garin insha Allah zai je" Mom ɗan jinjina kai tayi sannan tace "wallahi Sadeeq wannan abu da ban mamaki da ban tsoro, Allah dai ya rabata da waɗan nan bayi nasa" "Amin ya Allah, wallahi Mom da ban tsoro kuma ƙarfinsu na nan ma sai ya baki mamaki wallahi dan ni dai sosai na tsorata" cewar Sadeeq "Allah ya bata lafiya" cewar Mom tana jinjina zancen "Ameen, Mom ki tambayeta sunan garin nasu" cewar Sadeeq "Zainab!!!" Cewar Mom cikin ɗaga murya "Gani nan" cewar Abulle tana fitowa a guje Zama tayi kusada Mom tace "gani nazo" "Yawwa Zainab sunan garin naku zaki sanar damu" Shiru tayi sannan tace "Mom kin daiyi alƙawari zaki kuma tare zamu dawo ko" Gyaɗa kai Mom tayi tace "tabbas" Shiru Abulle tayi tace "zakara muke ƙarƙashin ungogo local government" "Zakara!!" Cewar Sadeeq "Ka san wajen ne?" Mom ta tambaya "A'a amma dai da kwatance ma je, ke ai zaki gane gidanku in mun isa ƙauyen ko" yana kallon Abulle Taɓe baki tayi tace "Ai kaf garinmu babu wanda zaka tambaya Abulle bai sani ba wallahi, ai wallahi anfi girmamani akan mai gari nan birni ne kawai ake min abinda aka ga dama na rasa dalili chan kuwa mutum ya min wallahi uwassa nake ci, macizai da kunamu su susutamin ɗan iska amma a nan ko nai niyya baya aiki" ta ƙare tana kyaɓe baki Mom dariya ta saki jin sakarcin da Abulle ta faɗi yayinda Sadeeq ya zuba mata ido dan ya gasgata dukkan zancenta duk da cikin sakarci take bayanin Sadeeq waya ya ɗauka ya kira Malam ya sanar dashi, nan Malam yace gobe zasuyi sammako su ɗau hanya.... [8/14, 11:50 AM] Mss Flower: *37* *next day* Misalin takwas da rabi dukkansu sun hallara zasu tafi garinsu Abulle, Mom da Abulle suna gidan baya yayinda Sadeeq ke driving zuwa gidan Malam Ko da suka ƙarasa a ƙofa suka gansa yana jiransu, gidan gaba ya shiga suka ɗauki hanya Sunyi tafiya mai ɗan nisa kafin suka ƙarasa cikin ƙauyen Daidai bakin wani rami Sadeeq yayi parking domin ba zai iya wucewa da mota ba Abulle ganinsu cikin garin nan ta fara ɗaga kai, gaba tayi suna binta a baya, sun kawo daidai dandazon matasa dake bakin masallaci wasu na saida mangoro, wasu rake abubuwa dai da dama na baro, suna ganin Abulle suka fara binta suna gaisuwa gamida barka da zuwa amma kowa zuciyarsa babu daɗi domin ba ƙaramin kwanciyar hankali suka samu ba a ƴan kwanakin da bata nan Abulle haka ta dinga hura hanci tana ƙin amsawa Mom ce tace "Zainab jira ni" Abulle tsayawa tayi har Mom ta taddota "Zainab ya naga manya na gaidaki gamida miki sannu da zuwa baki amsawa" cikin mamaki "Rabu dasu munafukai ne babu mai son dawowata" ta faɗa Daidai nan wata tinkiya ta taho a guje mai ita na biye ta bangaji Abulle Abulle ta faɗi ƙasa sannan ta zabga ihu tana faɗin "jar uba daga zuwana har za'a kassarani" Mai tinkiya ko da ya ɗaga kai ya kalli Abulle sai ya zube a ƙasa yana faɗin "dan girman Allah Abulle kiyi haƙuri wallahi bata kula ke ba ce da bazata tunkaroki ba" Abulle ta kyaɓe baki sannan tace "kwarankwatsa sai na ladabtar da tinkiyar nan, ke zo dan uwarki" cewar Abulle tana kallon tinkiya da ta tsaya cin ciyawa Abulle na rufe baki tinkiya ta taho ta tsaya Mom da ta cika da mamaki, tsoro, al'ajabi ta dubi mutumin nan babba dake ta kuka yana durƙushe gaban Abulle tace "Zainab rabu da su mu wuce kinji ko" Abulle turo baki tayi sannan tace "hakanan su ci ɓagas" "Barsu dai nace" Mom ta faɗa Malam ya dubi Abulle yace "hanzarta dan Allah mu kai gidan naku" Haka Abulle ba dan ta so ba tayi gaba Cikin gari kuwa a ƙanƙanin lokaci dawowar Abulle da ƴan birni ta karaɗe garin, nan kowa ya shiga tashin hankali haɗe da wanko ƙafa zuwa sannu da zuwa Mai gari ko da yaji zancen dawowarta baisan lokacin da ya tima a ƙasa ba ya haɗa uban tagumi ƙwalla ta fara tsiyayo masa Ko da suka ƙarasa ƙofar gida tsaye suka tarar da Hansatu da Isuwulle bakin ƙofa, Hansatu na ta washe baki yayinda Isuwulle ya murtuke fuska kamar an aiko masa saƙon mutuwa Da gudu Abulle ta faɗa jikin Hansatu tana faɗin "Hansatu wallahi nayi kewarki" Haka suka shiga cikin gidan, Hansatu ta shimfiɗa masu babbar tabarma suka zazzauna sannan Isuwulle yaje kawo musu ruwan leda, gaisawa Mom da Hansatu sukayi cikin mutuntawa Mom ta dubi Abulle tace "Zainab ɗan bamu waje " Turo baki Abulle tayi sannan ta miƙe Malam ne yayima Hansatu bayanin abinda ya kawosu Hansatu kuka ta fashe dashi daidai nan Isuwulle ya dawo, shima sanar dashi akayi sosai kuma ya girgiza Hansatu cikin kuka tace "wallahi mun cuci kanmu, gajen haƙuri shi ya jawo mana wannan bala'in, tabbas munga ishara Allah ba'a masa wayo dan ko yanda wannan ɗiya ta zamema kowa bala'i cikin garin nan yayi yawa, kowa ya buɗi baki tirrrr yake cewa babu bakin da ke faɗin ƙwarai gameda ita, ga uban baƙin jini da mukayi cikin mutane mu mahaifanta dan dalilinmu ne tazo duniya" cewar Hansatu tana share ƙwalla Mom cikin tausayawa tace "ko zan san labarinku daga farko" Gyaɗa kai Hansatu tayi tace "eh" *Asalin labari* Isuwulle da Hansatu sunyi auren soyayya ne na saurayi da budurwa, rayuwarsu suke cikin so da ƙauna, taltali da girmama juna, abinda ya fara ɗaga musu hankali shine yanda suka share shekaru uku ɓatan wata Hansatu bata taɓa yi ba, tun abun bai wani damunsu harta kai ga sun fara damuwa sosai, abinda ya ƙara ɗaga musu hankali shine yanda dangin Isuwulle suka fara hura wuta akan sai dai ya ƙara aure, haka sukayita kai kukansu ga Allah amma har suka ƙara shekaru biyu babu bayani, suna shekara ta bakwai fa da aure Maman Isuwulle ta samo masa wata bazawara mai ɗa biyu, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin Hansatu yayi ba dalilin nan Isuwulle ya ƙagawa ransa damuwa shima, kwatsam suna zaman majalisa sai wani abokin hirarsu yake bada labarin wani malami da yayi masa aiki wanda ya basa matuƙar mamaki dan cikin kwana guda jal burinsa da buƙatarsa ta biya, sosai zuwa wajen malamin nan ya ɗarsu zuciyar Isuwulle, ko da ya ƙarasa gida baiyi ƙauron baki ba ya sanar da Hansatu, sun jima suna tattaunawa akan zancen kafin nan suka yanke hukuncin amincewa da zuwa, washegari da sasafe suka garzaya wajen wannan mutumi inda yayi musu jagora gun malamin nan, bayan sun je suka zayyana masa damuwarsa nan ya karɓi kuɗin da za'ayi yanka har dubu hamsin, ya basu laya yace su birne tsakiyar ɗakin da suke kwana da magungunan da zasuyi amfani dasu, ko da suka koma gida hakan suka aikata, bayan sati guda kuwa sai ga alamomin ciki sun bayyana jikin Hansatu hakan ya sanya su da dangi tsananin farin ciki, haka sukayita raino da ririta abinda ke cikin, watan Hansatu bakwai da kwanaki da zuwa gun boka ta haife ɗiyarta, murna wajensu ba'a magana, rana suna yarinya taci sunan babar Isuwulle Zainabu dan haka ake kiranta da Abulle, abinda ya fara tada musu hankali shine saurin fushinta ga ƙarfin bala'i dan ta haɗu da yaro duk girmansa ɓaras zata ɓallasa, manya kuwa in sun baƙanta mata in tayi nuni da abu sai abun nan ya cutar da mutum, haka dai sukayita haƙuri wai tunaninsu ta girma abin zaiyi sauƙi amma sai ya ci gaba *cigaban labari* [8/14, 11:50 AM] Mss Flower: *38* Sosai Mom, Malam da Sadeeq suka girgiza da jin zancen, haka sukayita jinjina maganar daga bisani Malam yace a nuna masa ɗakin Isuwulle yace "anyi daɓe sai dai a fasa wajen" Malam yace to a fasa ɗin Isuwulle yayi musu jagora ɗakin, Sadeeq ya fara fasawa A guje Abulle ta sheƙo ɗakin ta fizgi gatarin da ke hannun Sadeeq ta wurwura shi waje ya kafe jikin garun katanga Cikin wani yanayi tace "kada ku sake ku gwada tone abinda yayi shekaru nan ne wajen zamansa har abada" tana wani ciccijewa Malam addua ya fara karantawa yana haɗawa da ayoyin Allah sannan yace "Sadeeq jeka ɗauko gatarin can ka cigaba da aikinka" Sadeeq a tsorace ya ƙarasa, duk yanda yayi ƙoƙarin cirowa amma ya kasa dan ya shige ciki sosai Isuwulle ne ya ɗauko wata ƙatuwar guduma ya hau dukan wajen, Malam kuma bai tsaya da addua ba Abulle sai ihu da kururuwa take hakannan kuma ɗakin keta girgiza har ƙasa na zubowa alamun zai rushe Hakan ya sanya Isuwulle ƙara ƙaimi wajen fasawar, ko da ya fasa shafen da ƙyar yake tone ƙasar wajen kasancewar tayi masifar tauri tayi kuma baƙiƙirin saboda tsananin mugun asirin da aka birne, ya jima yana tona kafin ya ganta Malam da bismillah ya cirota nan ɗakin ya ɗauki wani uban ƙugi Abulle barin ɗakin tayi a guje, tsakar gida ta faɗi sai ihu da birgima da gunji take mai tada hankali Malam bai ce komai ba ya kalli jama'ar wajen yace "in da mai jin fitsari yaje yayi ya kawo mana" Hansatu ce ta wuce bayi tayo fitsari cikin kwano ta kawo Karɓa Malam yayi sannan ya ajiye layar dake ta tururin hayaƙi tsakiyar rana ya kwarara mata fitsarin da bismillah Wata ƴar ƙara ƙara ta fara fita wani, ba'a ɗauki mintina ba hayaƙin ya ɓace Ɗiffff suka daina jin ihun Abulle ko da suka juya wajenta, wani uban baƙin hayaƙi curi curi ke fita daga jikinta in yayi sama sai ya baje, ya jima yana fita kafin nan ɗan motsin da take ma ta daina jikinta yayi laƙwas idanunta suka rufe A hargitse Hansatu da ta cika da tsoro tayi kanta tana tambayar Malam mai ya sameta Malam yace " Alhamdulillah insha Allah taji sauƙi, kaita ɗaki ta kwanta yanzu bacci take" Mom da Hansatu suka kamata suka kaita ɗaki, tsakar gida suka dawo sunata al'ajabin abinda suka gani da maida zance Mom ta sanar dasu ƙudurinta na komawa da Abulle nan sukayi na'am da batun domin ko ba komai Mom ta cancanci duk wata alfarma daga garesu tunda ta ceci ƴar su tilo, kuma sun san mutan gari suka san Abulle ta rabuda masu ƙarfi hukuncin da zasu ɗauka sai Allah domin ta matuƙar wahalar da jigatasu Sosai sukayi ma su godiya inda Isuwulle ya dubi Sadeeq yace "yaro in bakada aure gata na baka in kana so ka aura" Zaro ido Mom tayi tace "Zainab ai tayi ƙanƙanta da aure" Hansatu ta riƙe baki tace "haka ta gaya muku, aiko dai ta taɓa aure ma fitowa tayi fa wai ta gaji da auren, toh kai baka isa ka ce ga ra'ayinka ba ta wahalsheka shiyasa muka haƙura ta fito ɗin" Sosai Mom ta ƙara cika da mamaki dan dai Abulle ko kaɗan batayi kama da wadda ta taɓa aure ba dan in mutum yayi komin yarintarsa ya kan rage wani abun A ɓangaren Sadeeq hakanan yaji bai ji daɗin zancen auren nata ba amma dai ya basar Isuwulle ya dubesa yace "in kaga tayi maka ƙanƙanta a ɗaura in yaso sai kuje can kayita rainonta har ta zama ginshimemiya, kaga hankalinku da namu zaifi kwanciya tunda ko ba komai munsan gidan aure ta nufa" Mom ce ta jinjina abun sannan tace "bari na tattauna da mahaifinsa" Sosai sukayi magana da mahaifin Sadeeq, inda ya tambaya wa zai masa wakilci ta sanar dashi Malamin nan na iya yi masa, amincewa yayi domin shi dama mutum ne mai sauƙin kai sosai Sadeeq a ɓangarensa shi dai baya ce yana murna ba haka zalika baya baƙin ciki, shi dai gashinan Mom sanar dasu yanda sukayi da Alhaji tayi, nan fa iyayen Abulle suka dinga murna dan ko bakomai sun san ɗiyarsu tayi dacen miji da gidan mutunci Isuwulle haka ya aika a sanar da Mai gari yazo zasuyi magana Mai gari hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba da jin batun amma babu yanda ya iya haka ya ja tawagarsa zuwa gidansu Abulle Isuwulle bai sanar da su cewa taji sauƙi ba sai dai maganar aurenta da za'a kuma yi Mai gari cikin murna yace "aikuwa dai ta gama iddah tun watan da ya gabata, Allah ya sanya alheri, amma nace birni zata koma ko" Cikin bagu Isuwulle yace "eh ai kasan Abulle dama matar manya ce batayi kama da kai zaman ƙauye ba wallahi" Gyaɗa kai Mai gari yayi yace "hakane" Nan Mai gari ya sanya aka sanar da mutan gari ɗaurin auren Abulle nan da awa biyu da rabi, tareda aikawa gidansa a ɗora abincin ƴan ɗaurin aure, cikin daɗin rai da tunanin ta tafi kenan ya sanya akayita ɓarar da kuɗi wajen shirye shiryen aure kai ka rantse shine ango ko uban amarya.... [8/14, 11:51 AM] Mss Flower: *39* Misalin huɗu bayan an idar da sallar la'asar aka ɗaura auren Sadeeq da Abulle bisa sadaki dubu ɗari, ɗaurin auren da ya samu hallatar sama da rabin mazan ƙauyen Sosai Isuwulle ke murna cikin fariya ya dinga nunawa jama'a mijin ƴar sa, haka suka ɗingumo suka dawo gida Daidai lokacin da suka shigo Abulle da ta farka daga bacci ta fito tana hamma, idanunta ne ya haɗu dana Sadeeq, murmushi ta sake masa tana cewa "su Sharufkan harda yawo aka fita" Sadeeq jefa mata harara yayi itakuma ta taɓe baki tace "ohooo dai" Mom ta dubeta tace "Zainab an tashi" Gyaɗa kai tayi ta ƙarasa kusada ita da Hansatu tace "wallahi sai dai banjin ƙarfin jikina" "Ayyah, zauna kici abinci sai kiyi sallah ki haɗiyi panadol mu wuce" cewar Mom Gyaɗa kai Abulle tayi sannan ta wuce ɗaki, sallah ta farayi sannan ta zauna taci abinci plate guda ma bata iya cinyewa ba Hansatu cikeda mamaki tace "Abulle daron fa duk naki ne" Dariya Mom tayi tace "ina zata iya cinyewa dama dai jinki kawai nayi" Gyaɗa kai Hansatu kawai tayi itadai mamaki ya cikata dan batasan ƴarta da sararawa abinci ba Bayan taci Isuwulle da Hansatu suka sanar da ita auren da suka ɗaura mata Wani uban ihu ta kurma ta faɗa jikin Sadeeq cikin murna tana faɗin "ashe dai zan auri mai kama da Sharufkan nima" Mom girgiza kai tayi tana mamakin yarintar Abulle sannan tace "ke zo ki zauna" Babu musu Abulle ta koma ta zauna, tana ta ƙyaftawa Sadeeq ido shikuma yana zabga mata harara Misalin biyar da rabi suka fara haramar tafiya, wannan karon sosai Abulle taji kewar Hansatu, harda ƙwallarta suka rabu suka kama hanyar komawa cikin gari A mota Mom tace "Allah mai iko mu da muka je da niyyar magani gashi har mata muka samo maka" ta faɗa tana shafa gashin Abulle dake kwance jikinta tana bacci Sadeeq dai bai tanka ba yace "Mom dan dai babu yadda zanyi ne amma ba dan naso ba" Malam yace "dama ai sau tari wani abun da baka so sai ya zame maka alheri, ubangiji ya sanya alkhairi aka ƙulla" "Ameen" Mom da Sadeeq suka amsa Mom tace "nikam Sultana tana ta min maganar wata Fatima ƙawarta yarinyar nitsatsiya ce ya kamata ka aureta dan na yaba da hankalinta tunda bakada zaɓi kai, domin Zainab in zata tare wajenka ma dai sai ta shiga jami'a" Taɓe baki Sadeeq yayi yace "in har ita Fatiman tayi miki na amince, Allah yasa hakane alheri" Da Amin Mom da Malam suka amsa Tafiyar minti arba'in da biyar ce ta kaisu cikin garin Kano, bayan minti kamar sha biyar suka ƙarasa cikin gida bayan sun sauke Malam har gida inda Sadeeq yace gobe zai zo insha Allah Mom ta dubi Sadeeq tace "ɗaukota ka shigo da ita ciki" tayi wucewarta Sadeeq buɗe gidan baya yayi nan yaga sai sakin murmushi takeyi, ɗan murmushi ya saki yana bin dark round cute face ɗinta da kallo ya furta "she is beautiful", idonsa ne ya sauka kan ƴan tsilli tsillin ƙirgan danginta da ya fara pushing kaɗan, taɓe baki yayi yace "nikam kin kin yarinya dayawa, i can't wait, dole nayi sure " ya faɗa yana ɗaukarta in a bridal style Straight ɗakinta ya sauketa sannan ya wuce sashensa dan watsa ruwa, ɗan zama yayi akan gado ya dafe kansa in disbelief yace "wai ni ne yau na auri wannan mahaukaciyar yarinyar" Bayan sallar magriba ya dawo sashen Mom, Mom da ta dafa musu spaghetti jellop ta zuba musu suna ci, suna cikin ci Abulle ta sauko da alamu itama tayi wanka dan ta canza cikin wando da t shirt na jeans, da gudu ta ƙaraso ta zauna ta dubi Mom tace "Allah Mom saboda yunwa cikina har wani ƙuuuuu ƙulululu yakeyi" ta ƙare tana janyo plate Mom da Sadeeq dole sukayi dariya, Sadeeq ya dubi Abulle yace "ke kam ai dole cikinki yayi haka halan a duniya akwai wanda ya fiki ci ne" Ɗaure fuska Abulle tayi sannan ta hararesa ta turo baki tace "naji ɗin" Abulle ta dubi Mom tace "Mom idan na gama zan haɗe kayana harda sababbin na wajenki zaki bani" Mom cikin mamaki tace "kiyi me da su kuma" Abulle tace "ai sashen Sharufkan zan koma tunda munyi aure" Mom cikin mamaki tace "to mara kunya bazaki koma ɗin ba sai daga baya in kin girma" Sadeeq kam sosai yaji kunyar furucin Abulle amma babu yanda ya iya Abulle tace "Mom wai kina nufin sai na zama gingimemiya kamar Anty Sultana" Cikin takaici da gajiyawa da surutunta Mom tace "eh" "Mom to ai shi Sharufkan naga ƙato ne ya isa aure" "Ai yanada mata tafiya tayi kuma zata dawo nan kusa" Mom ta faɗa "Amma Anty Sultana tace bai da aure" cewar Abulle "Yana da shi" Mom ta bata amsa Taɓe baki tayi tace "toh " ta cigaba da lodawa cikinta abinci Bayan ta gama ta dubi Mom tace "Mom yaushe zan koma makaranta ne wai" "Gobe zaki insha Allah, dama Sadeeq ya amso miki uniform ɗinki" cewar Mom Wani ihu Abulle ta saki tana "Mom ina uniform ɗin" Girgiza Mom tayi sannan tace "suna wardrobe ɗina" Da gudu Abulle ta bar wajen tayi ɗakin Mom tana tsalle Mom ta dubi Sadeeq tace "kanada aiki sosai" Sadeeq cikin jin kunya ya sadda kansa ƙasa, Basu jima ba sai ga Abulle ta fito cikin riga da wando black and white sai ƴar guntuwar hijab fara da take daidai kafaɗa sosai kayan sukayi mata kyau suka amsheta, cikin dariya ta ƙaraso tana cewa "Mom kayan sunyi min kyau sosai ko" Cikin fara'a Mom tace "sosai ma kuwa sai kuma ki dage da karatu" Abulle ta tintsire da dariya ta zauna a carpet har da dafe ciki Mom tace "this girl you will never stop amusing me, yanzu mai na dariya haka" Abulle sai da ta ƙara darawa sannan tace "wai fa daa mai kama da Sharufkan yace in banyi ƙoƙari ba ƙauye zai maidani yanzu kam na zama matarsa kinga dole ya ƙyaleni" Mom ɗan ɗaure fuska tayi tace "ai in bakiyi ƙoƙari ba da hannuna zan ɗaukeki na maidaki ƙauyen, shi dama yanada mata ƴar gayu mai ilimi kinga kuwa ba zai damu ba" Abulle ɗan jim tayi sannan tace "nima zanyi karatun" Mom tace "yawwa yanzu tashi kiyi isha'i ki kwanta bacci, dan ki tashi da wuri" Jiki a mace Abulle tayi musu sai da safe sannan ta haye ɗakinta.... [8/14, 11:51 AM] Mss Flower: *41* *3 months later* Lokaci gudu yake, baya jira sai dai a jirasa, sakanni kan koma mintina, mintina su koma awanni, awanni su koma ranaku Abulle ta waye sosai ta goge, bata cika samun lokaci ba dan haka haɗuwarsu da Sadeeq ta kasance kaɗan ce sai in zaya kaita makaranta, sosai kuma ta maida hankali a kan karatunta domin burinta bai wuce itama ta ganta tana turanci ba, a yanzu ta iya jefa words na turanci a cikin zancenta in tana magana, a ɓangaren addini ma sosai take ganewa dan a yanzu tayi izu biyar a cikin alqur'ani mai girma, hadisai tayi kusan talatin cikin arba'una hadith, sosai tayi hankali kasancewar ta haɗu da ƙawa (Amira) yarinya mai nutsuwa da dagewa a kan karatu Yau ta kama ranar asabar kuma ranar da aka ɗaura auren Sadeeq da amaryarsa Fatima, sosai gidan ya taru da ƴan uwa da abokan arziƙi dan taya murna Wunin ranar kuwa Abulle a ɗaki tayi ta kulle ta ciki domin karatun exams take sosai dan on monday zasu fara Misalin shida na dare lokacin ƴan biki sun watse, Mom ce tayi knocking ɗakin da Abulle ke ciki Abulle murmushi tayi da ta buɗe tace "Mom ya hidima" "Alhamdulillah anyi karatun da kyau ko" Mom ta tambaya cikin kulawa "Eh wallahi" Abulle ta faɗa tana hamma Mom tace "toh muje kici abinci" Abulle tace "Mom bari nayi wanka toh" ta faɗa tana juyawa Mom wucewa tayi ta dawo parlor Sai wajen takwas da rabi sannan Abulle ta sauko cikin kayan bacci riga da wando masu kauri Mom da Sadeeq da ke ɗan hira ta kalla, kallon Sadeeq tayi ta galla masa harara Shima hararar ya watsa mata ya girgiza kai sannan ya dubi Mom gamida cewa "Mom zan wuce sai da safenku" Abulle tace "Umma ta gaida Aisha" ta bi bayansa da murguɗe Mom tace "Zainab wai nikam Allah bazaki daina wannan halin ba, Sadeeq fa yayanki ne kuma ko ba komai mijinki ne" Abulle turo baki tayi tace "toh meyasa ya yaudareni ya ƙara aure, dama bashida wani aure wallahi sai yanzu yayi" Mom ta girgiza kai tace "nikam Zainab in na kaiki ɗakin Sadeeq yanzu mai zakiyi ne halan, lokaci na zuwa da zan kaiki wajensa kinji ko yanzu ki dage da karatunki" cewar Mom tana dafata Gyaɗa kai Abulle tayi tace "toh shikenan" ta fara cin abinci Abulle bayan ta gama ɗaki ta koma ta cigaba da karatunta har bacci yayi gaba da ita Washegari da sassafe ta tashi bayan tayi azkar da Mom ta dage kai da fata ta koya mata, karatun alqur'ani tayi sannan ta janyo takaddun bokonta tana dubawa Misalin bakwai Mom ta shigo ɗakinta, da fara'a da jin daɗi tace "Zainab karatu ake tayi haka" Abulle ɗagowa tayi ta kalleta sannan tace "wallahi kuwa Mom, ni yanzu burina kawai na iya turanci sosai kuma nayi ƙoƙari a ajinmu dan kada a rainani" ta ƙarashe tana ɗan langaɓar da kai Mom murmushi tayi tace "insha Allah za kici jarabawarki ai Allah na taimakon wanda ya jajirce, yanzu sakko ki kaima amaryar yayanki abinci" cewar Mom tana ficewa Abulle yatsa tasa a hannu ta ɗan ciza sannan tace "wallahi ba dan Mom bace tace bazan kai ba naga ma nice uwargida, ƴar iskar gardiya ta ƙwacemin mijina" ta faɗa tana yatsina baki Abulle ba dan taso ba ta ɗauki warmers cikin basket ta nufi sashen Sadeeq dasu, babu knocking bare sallama ta banka ƙofar ɗakin, zaune ta tadda amarya Fatima ta ɗora kanta bisa kafaɗar Sadeeq tana zuba shagwaɓa Fatima na ganinta ta janye jikinta ta saki murmushi tana "sannu da zuwa ƙanwata" Wani banzan kallo Abulle ta watsa mata sannan tace "wallahi ni ba ƙanwarki bace, aikin banza a zo gidan mutane a dinga musu iskanci" Sadeeq da takaici ya cikasa ya dubi Abulle yace "ke ajiye ki fita" Ɗan harararsa Abulle tayi tace "wato in fita ku cigaba da iskanci ko, toh wallahi in bakuyi wasa ba sai na faɗa ma Mom" cewar Abulle tana ficewa daga ɗakin Cikin takaici Sadeeq ya girgiza kai ya kamo hannun Fatima yace "kada ki damu da wannan tanada aljanu ne sun ɗan taɓa mata ƙwalwa" Haka Abulle tayita saƙa da warwara kan kwanciya da taga Fatima tayi jikin Sadeeq daga ƙarshe dai ta watsar ta kama karatunta Lokacin abincin rana Mom ma aikenta tayi ta kai, cikin sanɗa ta banka ƙofar parlorn da niyyar ta kama su suna wani abun, sai dai bata tarar da Sadeeq ba sai Fatima dake zaune tana kallon arewa 24 Harara Abulle ta watsa mata ta ajiye flask ɗin abincin ta fara kalle kallen ɗakin tana taɓe baki Fatima cikin murmushi ta dubi Abulle tace "Zainab sannu da zuwa ga waje ki zauna" Harara Abulle ta kuma watsa mata sannan ta buga ƙafa tayi waje tana zumɓure zumɓuren baki Da dare ita ta kuma kai musu abinci nan ma cikin sanɗa tana dakon ko zata gansu suna wani abun amma sai ta tarar wannan karon Sadeeq ne kawai ke parlorn, kallo guda yayi mata ya kauda kansa, dole ta ajiye flask tayi waje ba dan ranta yaso ba. ..... [8/14, 11:51 AM] Mss Flower: *40* *next day* Misalin bakwai da rabi na safe Abulle ta shirya har ta ci abinci, tana jiran Sadeeq dake breakfast Bayan ya gama ya dubi Abulle yace "ki tashi muje" Mom ta dubi Abulle tace "Zainab ki dage ki koyi ko mene aka koya miki, dan kika dawo zaki min bayani in da hali ki zauna a first seat yanda zaki gane komai da kyau" cewar Mom Gyaɗa kai Abulle tayi tace "toh Mom, sai na dawo" Ko da suka ƙarasa makarantar Sadeeq ya dubeta yace "bari na gaya miki gaskiya ni bazan iya zama da macen da batada ilimi ba, so in kinason mu zauna tare dole ki dage a karatunki" Jiki a sanyaye Abulle tace "toh" ta fita daga motar Tana ƙarasawa aji ƴan ajin suka dinga bata waje, seat ɗin gaba da taga ba kowa ta samu ta zauna tana ta cin magani, da sun haɗa ido da wata ko wani ta galla musu harara English teacher ne ya fara shigowa sai dai duk yadda tayi ta gane bata fahimci komai da yake cewa ba har ya fita, yana fita maths teacher ya shigo, wannan karon Abulle ta fahimci abinda akayi sosai sai ɗan abinda ba'a rasa ba, yana fita taji yara sun ɗauki ihun "break time" Abulle ta dubi ta kusada ita dake revising karatun da aka koyar tace "ke wani malamin ba zai shigo ba ne" Yarinyar da ke tsorace da Abulle tace "eh an fita break" Abulle ta kuma cewa "abinda aka koya ɗazu ke kin fahimta ne" Yarinyar tace "eh na fahimta" Abulle tace "to ki koyamin dan ni bangane komai ba barin na farkon" Yarinyar sosai ta shiga koya mata, alhamdulillah kuma Abulle ta fahimta har ta kwatantawa yarinyar tayi mata ƴan gyararrakin da baza'a rasa ba Abulle cikin jin daɗi tace "nagode sunana Zainab, ya sunanki" Yarinyar tace "sunana Amira" Abulle tace "toh mun zama ƙawaye" ta zaro cake guda biyu da chocolate da ɗan ƙaramin kwalbar coke, cake ɗaya da chocolate ta miƙawa Amira Amira tace "laa ki barshi Allah nagode" "A'a ki amsa dan Allah" cewar Abulle Amira amsa tayi tace "thank you " Abulle tace "me kenan kika ce?" Amira tayi ƴar dariya tace "nagode nace" Bayan break basic science teacher ne ya shigo, wannan karon ma Abulle sosai ta gane dan malamin ma yana sirke da Hausa, bayan ya fita malamin computer ya shigo, shima ta gane inda har ta nunawa Amira system ɗin malamin tace "kinga wannan wallahi yayana mai kama da Sharufkan yana da ita" Amira dariya ta saki tace "sunanta system, kuma ba Sharufkan bane Sharukhan ne ko ba jarumin india ba" Gyaɗa kai Abulle tayi tace "shi fa, nagode Amira yau na ƙaru dake sosai wallahi" Ko da aka tashi Amira wucewa gida tayi kasancewar ita bata islamiyya yayinda Abulle ta wuce islamiyya, sosai ajin islamiyyar yafi yi mata daɗi dan anfi magana da Hausa sai ɗan larabci ba kamar da safe ba kowa turanci Bayan an tashi Sadeeq ne yazo ɗaukarta tun kan ta shigo take ta dariya da wage baki, zama tayi tace "mai kama da Sharukhan wallahi na koyi abu dayawa yau ɗin nan" Sadeeq ɗan dubanta yayi jin tace Sharukhan ba Sharufkan ba yace "tabbas ga alama naji ai" Haka suka ƙarasa gida, yana parking ta ɓalle ƙofar tayi ciki a guje, gaisawa sukayi da Mom sannan ta wuce ɗaki ta shirya ta ci abinci Misalin shida sabuwar lesson teacher da Sadeeq ta ƙaraso, sosai sukayi karatu aka kira sallah sukayi suka ɗora, sosai ta koya mata abubuwa sannan suka dandaƙa abinda aka musu aji tun daga bokon har islamiyyar sannan sukayi assignment, bayan nan suka tashi wajen takwas da rabi suka bar ma gobe A gajiye Abulle ta ƙarasa ciki, zubewa tayi kan doguwar kujera tana hamma Mom ta dubeta tace "sannu bayan wahala sai daɗi" Gyaɗa kai Abulle tayi, abinci ta ci ta koma ɗakinta bata wani jima ba bacci yayi gaba da ita.... [8/14, 11:51 AM] Mss Flower: *42* *Monday* Abulle ce zaune bisa dining cikin shirinta na makaranta tana cin abinci Sadeeq ne ya shigo ciki, bayan ya gaida Mom ya dubi Abulle yace "dalla kiyi sauri ina da abunyi" ya faɗa yana watsa mata kallon banza Abulle ɗan taɓe baki tayi tace "ohoo dai dole a jirani" chan ƙasan murya Bayan Abulle ta gama shirinta ta ƙarasa wajen Mom ta ɗan langaɓar da kai tace "dan Allah yau ma ki bani kuɗi ko naira hamsin ce" kamar zatayi kuka Mom tace "Wallahi gashi banda canji amma ɗaukomin jakata na baki five hundred kin dawomin da canji" Sadeeq ne yayi saurin cewa "inada 100 zan bata, taho muje" Abulle fita tayi tana waving ma Mom, ko da ta shiga mota haɗe gira tayi ɗan surutun da ta saba yau tayi shiru sai cika take tana batsewa Sadeeq da yajita shiru sai ya ɗan waiga gefenta yaga ko lafiya, ganin yanda take cin magani sai ta bashi dariya, sosai ya ɗan dara sannan yace "Abulle ya karatun" Ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa tayi tace "kai ne Abullen, kuma meye ruwanka da karatuna naga baka damu dani ba ina zaman zamana ban maka komai ba zaka je ka yimin kishiya wata mai zubin samudawa ma" Sadeeq ɗan zaro ido yayi sannan yace "ai ni bansan kina sona haka ba harda kishi" Ɗan taɓe baki Abulle tayi tace "ai ko bana sonka kai mijina ne" Murmushi yayi yace "bar wannan shiriritar yarinya kinmin ƙanƙanta kinji ko" Taɓe baki tayi tace "chan ta matse maka" "Wai ni ta ina ma zan soki yarinya sai tsiyar bala'i amma kinga matata ta yanzu Masha Allah yarinya mai hankali da nutsuwa duk abinda nakeso shi takeyi bata taɓa ɓata min rai bare mai da min magana" Abulle bata ce komai ba sai kicin kicin da tayi da fuska, ko da suka isa bata tankasa ba sai hannu da ta miƙa kan ya bata kuɗi Cikin rainin hankali yace "ya akai" Murtuke fuska tayi tace "kuɗin" a taƙaice Murmushin rainin wayo yayi sannan yace "ban da su" Nan da nan idon Abulle yayi ƙwal da hawaye, ɗan langaɓar da kai tayi tace "dan Allah" Harararta yayi yace "fita min a mota" Cikin ɓacin rai ta fita tareda banka masa ƙofar motar tayi wucewarta, girgiza kai Sadeeq yayi sannan ya wuce Misalin takwas da rabi aka basu jarabawar farko, sosai exams ɗin tayiwa Abulle sauƙi bayan andawo daga break ma around 11 aka basu paper ta biyu, itama tayi daɗi ba laifi sai dai bata kai ta farko ba Misalin sha biyu da rabi aka tashi, Abulle ce ta dubi Amira tace "dan Allah in kinada hamsin ki aramin na tafi gida gobe na baki" Amira hamsin ɗin break ɗinta ta bata kasancewar dama bata sai komai ba Cikin jindaɗi Abulle ta amsa tareda godiya sannan ta wuce gate Napep ta tare ta faɗa masa sunan anguwar, da ƙyar ya amince zai amshi hamsin kasancewar anguwar ɗari ne kuɗin zuwa hakanma dan ya ganta ƴar makaranta ne, ba wata doguwar tafiya sukayi ba suka kai anguwar Bayan ta sallameshi ta nufi cikin gidan, tsaye taga Sadeeq yana rungume da Fatima a bakin mota alamun fita zaiyi Abulle ko da ta ƙarasa wajensu tsaki ta buga tareda cewa "ƴan iska" hakan ne ya janyo hankalinsu kanta Sadeeq cikeda mamakin yanda ta dawo da kanta ya bita da kallo har ta ɓace ma ganinsa Da sallama ta shiga ɗakin, Mom da mamaki ta ke kallonta dan yanzun Sadeeq ya fita bai ci ace ya ɗaukota ba Kuka Abulle ta fashe dashi ta faɗa jikin Mom tana cewa " Mom bakiga yanda yaci zalina ba yau, ni dai ki dinga bani kuɗin mota na zuwa da dawowa" Mom tace "meya yayi miki ne, bari ya dawo ya sameni, ni da shi ne" Abulle girgiza kai tayi tace "ni dai ki ƙyaleshi dan Allah, in kika yi masa magana Allah kawai yasan mai zai ƙara yi min" Haka Mom tayita lallaɓata sannan tace zata na bata kuɗin mota tana zuwa da dawowa ganin yanda ta dage zata iya Misalin takwas na dare Abulle na kallo Sadeeq ya shigo dan yiwa Mom sai da safe Abulle kallonsa tayi tana ganin zai zauna ta miƙe tayi hanyar ɗakinta dan haushinsa takeji, sosai take masa kallon ɗan iska dan ita kam bata taɓa gani ana haka a garinsu ba, ko mai gari dai data aura baya ruƙunƙumeta haka, sau ɗaya ma ne ta gwada yi masa irin na film hakan kuma ya suntumar masa da leɓe..... [8/14, 11:53 AM] Mss Flower: *43* *2 weeks later* Abulle sanye cikin atamfa doguwar riga sai ƴar ƙaramar hijab, duban Mom dake zaune tayi tace "Mom dan Allah ai kinga nayi ƙoƙari nayi karatu ko har aka gama exams" Mom dariya ta ɗanyi sannan tace "Zainab wai mene ya faru da kika dage kina maimaitawa kike wanan zance?" Abulle ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "wallahi kuwa Mom tsoro nakeji, barin da naga Sharukhan ya dage tare zamu karɓo result ɗin" "Ki daina damuwa, khairan insha Allah zaki ci dayawa, yanda kika sha karatu insha Allah first kikayi" cewar Mom Washe baki Abulle tayi tace "Allah ya amsa amma nafison Amira tayi first" Sadeeq ne ya shigo Fatima na gefensa cikin Abaya, duban Abulle yayi yace "ke taso muje" Batareda ta tanka masa ba ta miƙe tana bin Fatima wadda alamu sun nuna tare zasu fita da mugun kallo Sallama sukayi ma Mom da tayi musu a dawo lafiya sannan suka wuce Fatima da Sadeeq ne gaba suna ɗan taɓa hira yayinda Abulle ke bayansu tana musu daƙuwa Suna isa Fatima ta buɗe gidan gaba da niyyar shiga Abulle ta ƙaraso da sauri ta shige sannan tace "malama nan wajena ne" Da mamaki Fatima ta bita da kallo wadda ranta har ya soma ɓaci dan duk juriyar da takeyi da Abulle abun ya fara isarta, zatayi magana kenan Sadeeq ya katseta da cewa Abulle "ke dallah fito ki koma baya" Abulle ƙin kulasa tayi ta tsuke baki ta kuma ƙi fitowa Haka Sadeeq yayita nanatawa amma ta ƙi kulawa, cikin ƙunar rai ya saka hannu ya fincikota ya iza ƙeyarta waje tareda buɗe gidan baya ya hankaɗata ciki Kuka Abulle ta fashe dashi tana ta faman jero masu Allah ya isa ita ancuceta Sadeeq da Fatima hirarsu suka cigaba batareda sun kulata ba har suka ƙarasa makarantar Parking yayi ya dubi Abulle yace "na baki minti goma kiyi ki amso ki fito" Batareda ta kulasa ba ta fita tana hawaye tareda banka masa ƙofar Sadeeq girgiza kai yayi tareda cewa "Allah ubangiji ya shiryaki" Hirar soyayya suka ɗora shi da Fatima sama da minti talatin sun nutse cikin kogin soyayya sun manta da wata Abulle ma Abulle da ta amso takaddar ko buɗawa batayi ba saboda ɓacin ran da take ji, buɗe motar tayi ta shiga Sadeeq ma jin ta buga ƙofa bata tankasa ba ya sanya yayi banza da ita ya tada motarsa, shopping mall suka zarce, haka suka shiga shi da Fatima su ka bar Abulle a mota, sun jima kuwa sosai dan siyayya sukayi kamar ba gobe sannan suka fito Abulle ta cika tayi fammm sai kumburi take kamar kububuwa hakan ma babu wanda ya tanka mata, har suka ƙarasa gida suna hirarsu ita kuma tana ɓacin rai Yana parking ta kwashi result ɗinta tayi waje da gudu, ko kafin ta ƙarasa kuka ya kufce mata saboda haushin da take ji a ranta Mom da sauri ta miƙe tana tambayarta lafiya, kasa furta komai tayi sai kukan da takeyi harda shasheka Mom ce ta duba result ɗinta ta ga ko batayi ƙoƙari ba take kuka, cikin mamaki ta ɗago tace "Zainab ai kinyi ƙoƙari sosai, ta takwas out of ku ashirin da tara, you have really tried, wallahi nayi matuƙar mamaki ma banyi expecting haka ba, next term sai ki ƙara dagewa" Abulle cikin kuka ta kalli Mom tace "Mom ya tsaneni sai yayita wulaƙantani a gaban matarsa" Mom cikin takaici tace "to ke sau nawa zance ki daina shige masa, ki share batunsa yanzu da kike liƙe masa rainaki kawai zaiyi ne, lokaci zai zo da zai damu dake" Abulle girgiza kai kawai tayi tareda cewa "Mom na fita sabgarsa insha Allah"..... [8/14, 11:53 AM] Mss Flower: *45* Abulle ɗauke kanta tayi daga dubansa cikin basarwa, hira sosai suka sha da Sultana, Mom sai Sadeeq ɗin da ya kan ɗan jefa bakinsa Sultana ce ta dubi Abulle tace "wai ni kin amso ɗinkin dinner ɗin naki?" Abulle ta ɗan taɓe baki sannan tace "wallahi Anty kinga tailor ɗin bashida kirki, da ƙyar nasamu yace gobe nazo na amsa, da jibi ma yace ranar bikin amma nace masa goben zan saka shine yace nazo goben" Sultana miƙewa tayi ta na "toh barka ma tunda kin samu, Allah yasa dai yayi kyau" "Amin, Anty zaki wuce ko" Abulle ta tambaya itama tana miƙewa "Eh wallahi, sai da safenku" cewar Sultana Mom sai da safe tayi musu itama sannan ta wuce ɗakinta Abulle da ta raka Sultana ta juyo kenan suka haɗu da Sadeeq a ƙofa, ƙoƙarin raɓewa tayi ta wuce ya damƙo hannunta Kallonta ya tsaya yi yana ƙarema beautiful round face ɗinta da kallo Hannu Abulle ta saka tana ƙoƙarin ƙwacewa dan tayi wucewarta Ƙara damƙeta Sadeeq yayi yace "ke bakida kunya ko, muna ta haɗuwa baki iya gaida mijinki ba ko" Harararsa Abulle tayi tace "ni banida wani miji, ka ƙyaleni" ta faɗa tana ƙoƙarin tumɓuke hannunsa daga jikinta Sadeeq yanda take magana cikin shagwaɓa sai yaji duk tsigar jikinsa ta fara tashi, kallon dark lips ɗinta yayi dake glowing sanadiyyar lip glows da ta shafa, ɗan ƙoƙarin kai nasa lips ɗin nata yayi Cikin azama Abulle ta gantsara masa cizo a tsintsiyar hannu, hakan ya sanyasa ya saketa babu shiri Da gudu ta matsa daga kusada shi tana faɗin "ni ba ƴar iska ba ce kamar matarka" ta faɗa tana hayewa sama da gudu Sadeeq sosai yaji cizon har kwanyarsa, ɗan shafa wajen yayi ya saki murmushi tareda cewa "she has grown to be cute" Abulle ko da ta haye ɗakinta kwanciya tayi sai nanata kalmar ɗan iska takeyi, da tunaninsa daren ranar tayi bacci A bangaren Sadeeq shima ko da ya koma sashensa sosai Abulle tayita faɗo masa a rai, lokaci lokaci idan shirmenta na baya ya faɗo masa sai ya saki murmushi, da ita yayi bacci a ransa dan har mafarkinta yayi daren ranar *2 days later* Abulle ce tsaye bakin mirror cikin peach material fitted gown anyi mata turban mai matuƙar kyau, fuskarta babu make up na hauka sai ɗan light one akayi mata sosai tayi kyau, bin jikinta tayi da kallo dan dukkan coca cola shape ɗinta ya bayyana, batada wata ƙiba amma sosai maƙerin budurci ya ƙerata da kyau, ɗan langaɓar da kai tayi tace "gaskiya ni bazan saka veil ba", high heels ɗinta ta saka, sannan ta sanya bracelet da agogonta ta feshe jikinta da perf, porch ta ɗauka cikin takun yanga ta sakko ƙasa, zaune ta tadda Mom da ƴan uwa anata hira masu zuwa dinner kuma nata shiri, wajen kowa na ganin Abulle ya fara yabata dan sosai tayi kyau matuƙa Mom ce ta dubeta ta galla mata harara tareda cewa "ina mayafinki" Turo baki Abulle tayi tace "Mom dan Allah bafa yawo zani ba" "Common je ki ɗauki mayafi in ba haka ba ki zauna gida" Mom ta ƙare tana harararta Cikin zumbure zumbure ta koma ɗakinta, ɗan siririn golden veil ta ɗauko wanda yayi matching da porch da takalmin haɗi da jewelleries ɗinta Mom murmushi tayi ko da ta ganta ta dawo tareda cewa "ko ke fa" Cikin iyayi ta fito harabar gidan inda motocin da zasu wajen dinner har sun kusa tashi, rasa motar shiga tayi ta tsaya tai tsuru, Fatima da suka jima basu magana sai dai ta shigo gaida Mom ta fice uffan bata shiga tsakaninsu ba ce ta ɗan yafito tareda cewa "ga mota chan taho muje" Abulle har zata ƙiya sai kuma ta ga kanta zata yiwa yanda ta ci burin dinner ɗin, dan haka tabi Fatima da ta nufi mota Kamar yanda tayi tsammani Sadeeq ne mazaunin driver, gidan baya ta shiga, kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kanta, shima bai tanka mata ba har suka ƙarasa cikin hotel ɗin Ƙofa ya buɗewa Fatima tareda cewa "in kin samu motar dawowa ki hau" Murmushi tayi masa sannan ta dubi Abulle tace "taho mu tafi" Sadeeq ne yayi saurin cewa "babu inda zata wannan da wannan yalolon mayafin gida zan maidata, kije kawai" Fatima ta so ta ɗan roƙesa amma ya ɗaga mata hannu Abulle kam sai ƙoƙarin buɗewa take idanunta ya cika da ƙwalla, tana ji tana gani Sadeeq ya figi motar Kuka sosai Abulle take harda shasheka, Sadeeq kam bai zame ko ina da ita sai a ƙofar sashensa, buɗe ƙofa yayi ya ɗaukota cak tana ta hawaye tana wutsil wutsil ya sauketa A parlor ya direta kan kujera, cikin hawaye tace "ni mai nayi maka, meyasa kake takuramin" Sadeeq hannunta ya kamo for the first time yace "Zainab" Ɗagowa tayi ta dubesa da idanta dake ɗigar hawaye tace "ni ka ƙyaleni" cikin turo baki Shima ɗan turo baki yayi cikin kwaikwayonta yace "ni bazan ƙyaleki ba" Hakan da yayi ya sanyata ta ɗanyi murmushi Cikin zolaya yace "mai kuka tana dariya ai mata ɗan kwaɗon daddawa" Abulle dariya ta fashe da ita sosai, can kuma ta haɗe rai tareda galla masa harara "Fushi kikeyi?" Ya faɗa tana ɗaga gira guda Ɗan turo baki tayi tace "ni ka maidani wajen dinner" "Ki shirya na kaiki mu siyo furgun" ya faɗa yana dariya ƙasa ƙasa Ɗan turo baki tayi tace "ni pringles nake cewa" Murmushi Sadeeq yayi sannan ya shiga ɗakin Fatima, hijab ya ɗauko mata, da kansa sanan yace "shall we" Ɗan turo baki Abulle tayi sannan tace " ni dai dinner nakeson tafiya" Sadeeq kallonta yayi cikin narkar da murya yace " ni banason kije wajen can maza suna kallemin ke" Harararsa Abulle tayi sannan tace " bayan ni da ka gama wulaƙantawa a baya" ta ƙare idonta na kawo ruwa Hannu ya sanya ya rungumeta jikinsa yace "shhhh ko a baya ba dan ban sonki bane, gudun rashin kunyarki nakeyi" ya faɗa yana goge mata ƙwallar da ke zubo mata Sun jima yana lallaɓata kafin nan ta saki ranta, hannunta ya riƙe suka nufi wajen da yayi packing "Laaaa mai nake gani, iskancin naka ya cigaba Sadeeq yanzu dan matarka ta fita party sai ka kawo karuwarka" cewar Maman Sultana da fitowarta kenan Abulle cikin ɓacin rai tace "ni ba karuwa bace malama" Maman Sultana da sai lokacin ta kula da Abulle ce yarinyar tace "Aljana ni ai bansan ke ce ba" chan ƙasan murya, sannan ta wuce sumsum dan a yanzu bata cika magana cikin gidan ba bare takalar faɗa tun ranar da ta takali Mom Abulle tayi mata hauka da tijara ta wanketa da ruwan wanki sanan ta dinga tsala mata tsinken kwakwa dama dai bata manta da fuskar Abulle da ta karya mata hannu ba duk da kuwa ta washe, shine dalilin da yasa ta shafawa gidan lafiya Siyayya sosai Sadeeq ya shiga yi ma ƴar yarinyar da shekarunta basu wuce sha shida ba, sosai ya narkar da dukiya a ranar kamar baisan zafinta ba, bayan sun gama ya wuce da ita valentino ya siyo mata ice cream Shaƙuwa mai ƙarfi ce ta ƙullu tsakaninsu a wannan dare, bai maidata gida ba sai da yayi nasarar goge baƙin fentin da tayi masa a zuciyarta.... [8/14, 11:53 AM] Mss Flower: *44* *years later* Rayuwa haka take ta gudu, tun bayan alƙawarin da Abulle tayi na fita harkar Sadeeq hakan ce ta kasance domin duk kafar da zata sadasu kaucewa take, harta zaman parlor daina yinsa tayi a lokutan da ta gane yana zama, babu abinda take sai karatunta na boko da na islama da ta sa gaba Ta ziyarci ƙauyensu sau biyar a cikin shekaru biyu da rabi inda Mom ta kaita, sosai kuwa Isuwulle da Hansatu sukayi murnar ganinta da canzawarta domin ta goge ta waye ta kumayi hankali sosai sai dai ƴan halayyarta na rashin kunya ba duka ta yasar ba A ɓangaren Sadeeq hankalinsa a kwance yake domin iya kula da tattali gamida biyayya yana samu daga wajen Fatima, abinda dai ke ɗan damunsa shine rashin haihuwarta amma bai nuna mata ba ya fawwalawa Allah yana masu addu'a da fatan alheri, zancen Abulle kam tsaf ya mance da ita gabaɗaya domin harkokin gabansa kawai yakeyi Yau ta kama ranar dasu Abulle zasuyi last exam ɗinsu ta junior waec, a gurguje ta sakko domin ta makara Wajen Mom ta ƙarasa ta karɓi kuɗin mota da na makaranta cikin sauri Mom ta dubeta tace "ai na ɗauka kin haƙura da exams ɗin ne na yau" Turo baki Abulle tayi cikin shagwaɓa tace "Mom kina jina shiru baki tasheni ba" Mom dubanta tayi ta harareta tace "wanne tashin kuma Zainab na nawa" Abulle karɓar kuɗin tayi tace "ni dai sai na dawo" Ta nufo ƙofa shikuma ya kawo suka bugi juna, cikin sauri Sadeeq ya janye ya bi kyakyawar black beauty ɗin da kallo yana ƙoƙarin tuna inda ya santa Abulle duba ɗaya tayi masa ta ɗauke kanta ta raɓe ta gefensa tayi wucewarta Sadeeq bin bayanta yayi da kallo yana duban yanda surarta ta ƙayatu, ga kuma uniform ɗin jikinta da alama an matse mata su, wandon ma anyi pencil da shi, guntuwar hijab ɗin jikinta iya kacinta kafaɗa Mom ganin hankalinsa ya ɗauku da kallon Abulle tace "Sadeeq lafiya dai kayi sororo a nan ƙofa" Sai a lokacin ya dawo hayyacinsa, ɗan sosa ƙeya yayi ransa fal tunanin inda Mom ta samo budurwa dan sam hankalinsa bai taɓa hasaso masa Abulle bace Mom ce tace "yau kuma matar taka da ka watsar itace kake ta kame kame kanta?" Cikin borin kunya yace "matata kuma, wace matar?" Cikin mamaki Mom watsa masa harara tayi tace "au ka saki ita Zainab ɗin ne bansani ba, shugaban marasa adalcin duniya" Sosai Sadeeq ya shiga ruɗu dan shi har ga Allah sam ya manta da wanzuwarta a doron ƙasa, daa yakan ɗan tunata har yayi mamakin yanda ta ɓuya shiru amma yanzu kam ya ma mance da ita dan ko batunta baiji wajen Mom Haka dai yayi ƴan kame kamensa, sannan ya tashi ya nufi asibiti Misalin takwas na dare Sadeeq ya shigo parlor, zaune ya tadda Mom tana kallon sunnah tv, waige waige ya fara ko zai ga Abulle amma shiru haka ya haƙura ya bar abin a ransa, suna tsaka da hira Sultana ta faɗo sashen da sallama Bayan sun gaisa ta dubi Mom tace "Mom ina Zainab ne rabona da ita yau kwana uku kenan" Mom ɗan taɓe baki tayi tace "tana chan sama, yau ta gama exams sai hutu" Murmushi Sultana tayi tace "Masha Allah, saura sakamako da boarding, bari na kirata" "Ta dai dage boarding wai chan Amira zata tafi, ki kira wayata ba sai kin wahala ba tana hannunta" cewar Mom Sultana wayar Mom ta kira aikuwa Abulle ta ɗaga da "hello Anty wayar bata wajenta bari na kai mata", bata saurari Sultana ba ta datse kiran Babu jimawa ta fara sakkowa cikin pyjamas ɗinta baby pink wanda sukayi matuƙar yi mata kyau, sai hular kanta itama baby pink irin buzu buzu ɗin nan, tana ganin Sultana ta taho da gudu, faɗawa tayi jikinta tana faɗin "oyoyo anty amarya" Dariya Sultana tayi tace "ai Anty Zainab naji ki shiru ne kin yada zancen bikin nace bari nazo naji ba'asi ko laifi nayi" Dariya itama Abulle tayi tace "wallahi ni yanda nake ɗaukin auren nan har ƙila na fiki, kuma ki daina cemin Anty ni banaso" ta ƙare tana turo baki Sosai Sadeeq ya shagala da kallonta, dan sai tazama irin classy ladies ɗin nan yanda take magana da komai nata da skin kala nata is very attractive Abulle ji tayi ana kallonta, ɗago idonta tayi suka sauka cikin na Sadeeq. ...... [8/14, 11:53 AM] Mss Flower: *46* Alhamdulillah anyi biki lafiya, an kai amarya Sultana gidanta dake garin katsina, ƴan biki duk sun watse gida ya rage iya mutanen cikinsa na baya Abulle da Sadeeq friendship ne sosai ya ƙulla tsakaninsu dan duk faɗan da sukeyi a baya sun daina sai ma mutunta juna da sukeyi Yau ta kama ranar da Mom ta bawa Abulle kan taje ƙauye hutun sati guda, sosai Abulle ke murna dan tunda ta baro ƙauyen in taje ziyara bai fi tayi awanni ba su dawo. Mom Sadeeq ta sanya ya kai Abulle Misalin goma na safe suka fito, Abulle rungume Mom tayi harda ƴar ƙwallarta, haka suka fito Tafiya sukeyi suna ɗan taɓa hira suna dariya, Sadeeq ne ya dubeta yace "yaushe zaki dawo gidanki ne" Da mamaki ta kallesa tace "wani gidan" "Gidan mijinki" ya faɗa a taƙaice Taɓe baki tayi tace "nayi yarinya sai nagama university" Cikin sauri ya dubeta yace "kiyi addua Allah ya sanya na bari ki gama secondary ma" Dariya Abulle tayi ƙasa ƙasa sanan tace "Mom dai bazata taɓa cewa nakoma ba" "Ko bata ce ba ni mai ɗaukoki ne nadawo dake, ko nayi abinda zai sa dole ta bani ke" ya faɗa "Mai kenan" Abulle ta tambaya cikin rashin fahimta "Zaki bayani ne" ya faɗa yana ɗan murmushi Hira suka sha sosai duk akan dawowarta har suka ƙarasa gida. Suna parking Abulle ta fice a guje tana "Mama Hansatu nazo" Hansatu dake bisa tabarma tana cin ɗumame tayi maza ta miƙe jin muryar gudan jininta, Da gudu Abulle ta faɗa jikinta tana faɗin "Mama Hansatu nayi kewarki" Hansatu rungume ɗiyarta tayi itama tana jin ƙaunarta, chan ta raba tace "ina Hajiya ne, bata shigo ba" "Ba tare muke ba, ni da Ya Sadeeq ne, amma naji yace ma ba zama zaiyi ba ana nemansa asibiti" cewar Abulle Hansatu cikin fara'a tace "toh shigo dashi mana mu gaisa" Gyaɗa kai Abulle tayi tana miƙewa gamida tambayar "ina Baba" "Ke dai jeki shigo da baƙo kafin nan" Hansatu ta faɗa tana ɗauraye hannunta tareda zura hijabi Tare suka shigo cikin fara'a suna ɗan hira fuskokinsu ɗauke da murmushi yana riƙe da traveling bag ɗinta Hansatu wani daɗi ne ya kamata ganin yanda Abullen ta ta waye ga kuma haɗaɗɗen miji suna kuma zaman lafiya da alama, cikin fara'a ta tarbi Sadeeq Sadeeq cikin kunya ya gaidata har ƙasa, sosai yaji nauyinta shekaru da dama sun bashi auren ƴar su amma bai taɓa zuwa ko gaidasu ba Hansatu ce ta dubi Abulle tace "je ki duba randa ɗazu nayi kunun aya ki kawo masa" Abulle miƙewa tayi ta ɗauko ɗaurin kunun aya guda uku ta ɗoro bisa plate ta kawo masa duk da bata tunanin zai sha Sadeeq ɗauka yayi ya zuƙe ɗaya sannan ya ƙara, bai wani jima ba ya miƙe ya dubi Hansatu tareda cewa "Mama ni zan wuce" Hansatu tace "toh Allah ya maidaka lafiya, sai anjima zaka zo ɗaukar matar taka ne?" "A'a nan zan barta zuwa wani makon" ya faɗa yana saka hannu aljihu, sabbin kuɗi ƴan ɗari biyar biyar ya ajiye na dubu ashirin sanan ya fice Abulle rakiya tayi masa har bakin mota Sadeeq ɗan dubanta yayi ya ɗan langaɓar da kai tareda cewa "ni ya zanyi yanzu" Cikin rashin fahimta tace "da me fa?" "Da kewarki" ya faɗa yana ɗan ɓata fuska Dariya Abulle tayi tace "daa yaushe muka saba ɗin" Ɗan langaɓar da kai Sadeeq yayi yace "ki bari muyi ko sau ɗaya" cikin shagwaɓa "Me zamuyi ne ɗan autan Mom" ta faɗa cikin tsokana Nuni yayi da lips ɗinta sannan yayi pointing nasa ya kashe mata ido Dariya Abulle ta saki tana rufe fuska sannan ta ruga cikin gida Da murmushi ya bi bayanta da kallo, sannan ya tada mota ya bar wajen Misalin huɗu Abulle ta dubi Hansatu tace " bari na zagaya gidansu Bintalo, Allah yasa tana nan batayi aure ba" "Aikuwa tayi aure amma sai mijin ya rasu, yanzu tana gida" cewar Hansatu "Ayyah, Allah ya bata wanda ya fisa, bari naje" cewar Abulle Tafe take cikin doguwar rigar atamfa sai mayafi ɗan daidai na ƴammata, duk inda ta wuce sai ta saki murmushi in ta tuna gwagwarmayar da akayi a wajen Wajen dandalin samari ta zo wuce da keta hirarrakinsu irinta majalisa, suna ganinta suka fara nunata irin dai yanda samari keyi in sunga budurwa Wani daga cikin samarin mai suna ɗan talle ne ya biyota, yana gyara tazuge da karkata hula wai a dole shi ga saurayi yanata wani ƙwaƙwambarewa tareda cewa "baby wallahi tunda na ganki naji yes kece the one, ki duba ni dake ai kinsan munyi to match" Abulle da surutunsa ya isheta sai ta dakata, juyowa tayi ta zuba mai manyan idanuwanta "Kaiiiiiii!!!" Ya faɗa yana zaro ido, a guje ya sheƙa yana faɗin "wallahi Abulle ce", ai nan da nan samarin suka fara rantar na kare Dariya Abulle tayi da taga kowa nata zuba gudu, ta taƙarƙare tace "kai ku dawo" Ai suna jinta suka ƙara taƙarƙarewa bakin fama harda masu hantsilawa Dariya sosai ta sha harda ciwon ciki, sannan ta gangara gidansu Bintalo Da gudu Bintalo ta rungume Abulle cikin farinciki, ƙarasawa ciki sukayi cikin farinciki da ganin juna Hira suka sha sosai gamida tuna rayuwarsu ta baya, dariya Abulle tayi tace "ni ko Yagwalgwal na nan" Karaf Bintalo tace "tsohuwa ƴar yi ba, tana nan wallahi kullum na leƙa gidan sai ta ɗebe mana albarka, dariya ma take ban Qur'ani" "Aikuwa zani mu gana da Mai gari nawa, ja'iri" cewar Abulle tana dariya Ɗan murmushi Bintalo tayi tana " ai tun barinki dai garin nan in munyi kayan mata kwantai yake, ƴan jar uba sun gaji da siyan kashin shanu da karara" Dariya Abulle ta kwashe dashi tace "ƙawata kan na koma ai zamu ɗan tuna baya" ....... [8/14, 11:53 AM] Mss Flower: *49* *3 years later* Abubuwa da dama sun faru a shekarun kamar samun ƙaruwa da Sadeeq da Fatima sukayi ta ɗiya mace, gama makarantar Abulle, zuwan mahaifiyar Sultana wajen Mom ta nemi gafararta bisa abubuwan da tayi mata tun wata jinya da tayi kamar baza tayi rai ba, shiryawar Abulle da Fatima dalilin yarinyar Fatima mai suna Khadija dan Allah ya jarabci Abulle da ƙaunar yarinyar kusan kullum tana wajenta wanan ne musababbin shirin nasu Yau ta kama ranar da Mom ta shirya ƴar ƙwarya ƙwaryar walima domin Abulle da Sadeeq, dan yau za'a kaita gidanta, gidane Sadeeq ya danƙara musu mai ɗan karan kyau two section ɗaya nata ɗaya na Fatima Abulle ce tsugunne gaban Mom tana ta sharcar ƙwalla tana faɗin "ni dai Mom na fasa zuwa bazani ba" Sultana ce wadda take goye da ɗanta na biyu ta riƙeta tana faɗin "kiyi haƙuri Anty ki dai je" Haka Abulle aka kaita gidanta wanda Mom ta ƙayata mata section ɗinta da kaya tsadaddu masu kyan gaske, kuka ta fashe dashi da taga Sultana tana haramar tafiya Sultana zama tayi ta mata nasiha sosai mai ratsa jiki haɗe da tausarta sanan ta bar gidan Abulle dafe cikinta tayi dake kukan yunwa, miƙewa tayi tana faɗin "ni bari naji na sama ma kaina abinda zanci, dan bansan ranar dawowarsa ba". Kitchen ta nufa sanan ta koma store cikin sa'a taga kwalin indomie, guda biyu ta ɗauko ta koma kitchen Dafawa tayi abunta sanan ta koma parlor ta baje ta fara kwasar abincinta Misalin tara da rabi Abulle ta faɗa wanka, fitowarta keda wuya ta tadda Sadeeq zaune bisa gado yana danne danne a waya, a guje ta juya tana faɗin "haba sharukhan ba sai kace min kana ciki ba" Sadeeq dariya ma ta bashi dan tun da yake bai taɓa jin amarya ta shige wanka ba amma gata itakam ba abinda ya mata zafi, chan yace "ina na san wanka kikeyi toh" "Ni dai miƙomin hijab tukunna" ta faɗa tana miƙo hannu waje Hijab Sadeeq ya miƙa mata yana faɗin "zaki bayani" Bayan Abulle ta shirya ne Sadeeq yace "je kiyi alwala muyi sallah kici abinci nasan kina jin yunwa" Dariya Abulle ta ƙyalƙyale da ita sanan tace "ai tuni na dafa indomie, jiranka zanyi da ka dawo" Shima Sadeeq dariya ya kwashe da ita yana faɗin "girman kujerarki amarya kuma uwargida" Murmushi tayi tareda nufar toilet, alwala ta ɗauro, sallah suka gabatar raka'a biyu sanan ya kama kanta ya dinga kwararomata adduo'i Sadeeq na cika Abulle ta janyo leda, bai ko ce taci ba ta fara tura kaza tareda ɓarke kwalin hollandia, Sadeeq cikeda ƙaunarta da burgewa yake kallonta har ta gama ta ture Abulle zama tayi kan gado tana faɗin "gaskiya na ƙoshi dayawa, ji yanda cikina yayi tulluwa kamar ƴar yaye" Sadeeq shima hawowa yayi tareda cewa "tunda kin ƙoshi sai ki biyani kayana" ya faɗa yana riƙe hannunta tareda murzawa Abulle dariya tayi tace "ba abinda zan biya wallahi ai harda ciyarwa ka yadda ka ɗauka" Janyota yayi jikinsa yana ɗan shinshinarta, duk da sun saɓa ɗan wasanan sai yau jikinta yayi laƙwas, bakinsa ya kai kan bakinta ya fara sucking a hankali, hannunsa ya kai kan. .... ya fara wasa dasu, a hankali ya rabata da kayan jikinta Sosai ya shiga romancing ɗinta duk ya burkice, daganan ya koma abin nan, kuka sosai Abulle ta shiga rairawa, sun jima suna abu ɗaya kafin su rabu, ƙanƙameta yayi jikinsa yana saka mata albarka, wanka ya cicciɓeta ya tayata sanan ya dawo ya shiryata cikin free riga da wando na bacci cotton, blanket ya rufa musu ya kuma ƙanƙameta kamar za'a ƙwace masa ita, haka dai bacci yayi gaba da su Washegari Abulle ko da ta tashi bata jin daɗin jikinta, bayan tayi sallah taci ragowar kaza da hollandia lokacin Sadeeq bai dawo ba Sadeeq na shigowa ya ganta kan kujera, ƙarasawa yayi jikinta ya rungumeta cikeda tsantsar ƙaunarta, yayinda itakuma ta hau zuba masa shagwaɓa Wunin ranar haka Abulle da Sadeeq sukayi ta tana shagwaɓa yana rarrashi cikin tsantsa da madarar ƙauna *5 years later* Abulle ce zaune tareda ƴan yara guda biyu wanda kallo guda zaka musu kasan ƴan biyu ne, homework take koya musu inda sai faman faɗa takeyiwa ƴar macen da ta zumɓuro baki tana harare harare, hannu Abulle ta saka ta sakar mata ranƙwashi tana faɗin "wallahi in baki maida hankali kan karatu ba sai nayi ƙasa ƙasa dake a gidan nan" Kuka yarinyar ta fashe dashi tana faɗin "baza'a maida ɗin ba, kuma sai na faɗawa Daddy kin dakeni bana sonki nafison Mamy" Fatima da ta shigo tareda Khadija ga kuma wani cikin da yayi nata tulele ta janyo yarinyar jikinta tana faɗin "yi shiru Nanata, bari Daddy ya dawo mu faɗa masa" Fatima duban Abulle tayi tace "Mommy a dinga yi wa yarinyar nan haƙuri" Abulle hararar Nana tayi tace "wallahi Yaya sam ita batajin magana kuma kayi mata gyara sai ta hau yi maka rashin kunya" Sadeeq da shigowarsa kenan yace "ni dai a daina dukarmin mamana in tayi rashin ji ma ai ba karambani tayi ba" Da gudu ƴan yaran guda biyu mata sai namiji guda suka nufi Sadeeq suna "oyoyoo Daddy", ɗaukarsu ɗaya bayan ɗaya ya farayi suna dariya Nana ce da ya sauketa tace "Daddy ni gobe ka kaini wajen Kaka Hansatu" ta faɗa tana hararar Abulle ta ƙasan ido Sadeeq haɗe rai yayi yace "bazan kai ki ɗin ba, in kinason zuwa kije ki bama Mommynki haƙuri sanan ki daina harararta" Turo baki yarinyar tayi tace "chabb" Sadeeq yace "toh sai ki zauna a gida" Ɗan bubbuga ƙafa tayi sanan ta ƙarasa gaban Abulle ta turo baki tace "i'm sorry" Girgiza kai Abulle tayi tace "Allah ya shiryeki" ..... [8/14, 11:53 AM] Mss Flower: *48* "Assalamu Alaikum munzo sana'a ba sata ba" Abulle ta faɗa cikin ɗaga murya sanan ta kutsa kai cikin gidan Matan gidan da Yagwalgwal nan da nan suka juyo a firgice suka zubawa ƙofa idanu Abulle murmushi ta saki gamida ƴar shewa tace "jama'ar gidan nan ga nifa nazo, kwarankwatsa baya tsohuwar ƴar bala'in nan" ta faɗa tana nuna Yagwalgwal da keta zuba mata harara "Kinyi da uwarki Hansatu, ni wallahi banga wace masifar ce ta dawo dake garin nan ba, da kika tafi rayuwa tai mana saƙat, ƙauye ya ɗau shiru, farinciki da zaman lafiya" ta faɗa tana ƙarewa da tsaki "Tau, gani nan nadawo tada muku hankali kuwa" ta faɗa tana kai kanta kan uwargida da amarya tace "ku kuma ku taimaka min na haɗa maganin mata ku saya, nasan kun kwan biyu ana jinku lami gara na gyareku kan nakoma" "Alhamdulillah ashe dai zaki tafi, tau barka dan ni babban baƙincikina zamanki ƙauyen nan ɗiyar aljanu kawai" cewar Yagwalgwal Abulle ce ta ɗan shaƙi ƙamshi tareda cewa "uwargida ƙamshin kaji nakeji fa, ɗauko min" Amarya ce tayi maza tai caraf tace "Mai gari zaiyi baƙi yasa a soye zabbi huɗu, ke kam kiyi haƙuri na baƙi ne" "Tau, sa ci kashin shanu tunda baku bani", ta faɗa tana jan tsuka tareda cewa "ke Bintalo tashi muje, gidan nan kwarankwatsa yau basa rintsa ba tunda ni suka wulaƙanta" A guje uwargida ta riƙota tace "dan Allah kiyi haƙuri, wallahi akwai zabbi bara na kawo miki ki ɗiba" Zama Abulle tayi bisa kujera ƴar tsugunno tace "tau yi maza dan ƴan cikina har sun fara bada ƙuuu" Yagwalgwal ta dubeta tace "ɗiyar mayu kawai" "Na kula Yagwalgwal kinyi kewar cinnaku, to billahillazi kika kuma tankawa sai na aza miki dumar aljanu bisa baki kuma baki iya cireta har gaban abada" Yagwalgwal zaro ido tayi zatayi magana sai kuma ta gimtse ta koma harare harare Uwargida ce ta ajiye mata kwanon zabbin sanan ta koma jikin bango inda amarya ke jingine ta tsaya suka fara aika mata harara ta ƙasan ido Abulle bata wani ci dayawa ba dan cinya biyu ta ci sai kuma Bintalo data ɗebi yanka huɗu ta riƙe a hannu, Abulle duban uwargida tayi tace "toh na ƙoshi hakanan, kin kuma ceceku bilahillazi" Yagwalgwal ce ta dubi Abulle tace "Ab uhm uhm" ta faɗa tana riƙe bakinta da sauri dan da alama mantuwa tayi zatayi magana Abulle harararta tayi tace "Allah ya taimakeki" Yagwalgwal hannu ta watsa mata tayi mata daƙuwa tana ɓallamata harara Abulle ce ta dubi matan tace "ni fa da zan daka kayan mata amma ya gani" Cikin sauri da haɗa baki suka ce "ai ki barshi ki huta kawai" Dariya Abulle tayi tace "toh shikenan na fasa, ni bara na wuce, saduwar alkhairi " ta faɗa tana miƙewa Haka suka kamo hanyar dawowa gida, sunata tsayawa hanya suna neman magana har suka kai gida ********* Yau ta kama ranar da Abulle zata koma gida, sosai take jin zatayi kewar iyayenta da aminiyarta wadda suke yawon tsokana. Misalin sha ɗaya Sadeeq ya iso garinsu, kaya sosai niƙi niƙi kama daga shinkafa, macaroni, taliya, mai, maggi da sauransu ya kawo musu, murna sosai suka shiga yi tareda masa godiya, cikin ƙanƙanin lokaci Hansatu ta tura Isuwulle siyo kayan miya, cefane yayi mai kyau ya taho da salak da nama, shinkafa da miya Hansatu ta dafa mai rai da lafiya, sosai suka ci sukayi nak, hira Sadeeq da Isuwulle suka shigayi kamar tun can sun saba. Misalin uku motarsu ta tashi Abulle harda ƙwallarta dan sosai takejin zatayi kewar mahaifanta da yanzu suke janta tareda nuna mata gata, Sadeeq a mota haka yayita rarrashinta da ƙyar ya samu tayi shiru. Suna isa gida bai gama gyara parking ba ta ɓalle murfin ƙofa tana kwaɗawa Mom kira, da gudu ta faɗa jikinta tana faɗin "nayi missing ɗinki Mom ɗita" Mom cikin ƙaunar yarinyar ta rungumeta tana faɗin "welcome daughter", haka Sadeeq ya taddasu suna rungume da juna, murmushi yayi sanan ya dubi Abulle yace "wato ke dole nema kike ki ƙwace min uwa ko" Gwalo Abulle tayi masa tace "eh ɗin " ta ƙare da dariya, suna tsaka da hira Fatima ta faɗo ɗakin, gaida Mom tayi sanan ta dubi Sadeeq tace "ashe kun dawo" Murmushi yayi mata sanan yace "eh zo ki zauna" yayi mata nuni da kusada shi, ƙarasawa wajen tayi tana cewa "Abulle sannu da zuwa, an sha hutu", Abulle banza tayi mata Hira suka ɗan fara taɓawa banda Abulle da dai Fatima da Sadeeq kawai take aika ma harara har suka idasa hirar Misalin takwas na dare tana zaune a kan carpet ta bararraje tana kallon arewa ita kaɗai, Sadeeq ya turo ɗakin Kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai ta turo baki, Sadeeq ganin ta ɗaure masa fuska ya sanya ya nufeta Zama yayi ƙasa shima ya ɗan riƙe hannunta yace "sarauniyata ya dai" Turo baki tayi tace "ai ba nice sarauniyarka ba, waccan kake so" ta ƙare hawaye na cika mata idanu Janyota yayi jikinsa yana faɗin "kece sarauniyata mana, kece dai naga kamar bakya sona" Murmushi Abulle tayi ta kwanta luff jikinsa tana faɗin "ina sonka mana mijina" Cikin jindaɗi ya bararraje bisa carpet tareda ƙanƙameta jikinsa yana shaƙar daddaɗan ƙamshin dake tashi a jikinta Mom da ta fito kallo idanunta ya sauka a kansu kunya ta isheta tana ta mamakin randa wannan shaƙuwar har haka ta ƙullu tsakaninsu, juyawa tayi tana faɗin "Allah nuna min ranar da zaki kammala secondary na maidaki wajensa dan da alama bazai bari kiyi university ɗin nan ba" ************ Shaƙuwa mai tsananin ƙarfi da soyayya ce ta shiga tsakaninsu inda ɗaya baya iya rintsawa sai yaga ɗan uwansa, haka suke laɓewa a farfajiyar gidan su ɗanyi wasanninsu na soyayya, tun Mom na magana har ta haƙura ta sanya musu ido tana jiran lokacin gama makarantar Abulle..... [8/14, 11:53 AM] Mss Flower: *47* *days later* Abulle ce da Bintalo tafe a hanya suna taɓa hira, duk wanda ya gamu dasu a hanya sai ya zube ya kwashi gaisuwa kasancewar zuwan Abulle ya karaɗe ƙauyen Jabiru ne tafe bisa kekensa hannunsa riƙe da leda, tsayawa yayi ganin Abulle, cikin girmamawa yace "Abulle ina kwana" Da fara'a Abulle ta amsa tace "Jabiru kwana dayawa, ya kasuwar" Murmushi yayi sanan ya hau sosa ƙeya tareda cewa "Alhamdulillah, kuma ko da aka cen kin fito gidan mai gari da naje gidanku sai aka cen kin tafi birni, an cen an ɗaura miki aure amma gaskiya ban yadda ba tunda maganar gaskiya ni wallahi sonki nake" Abulle dariya ta saki sanan ta hau dubansa, chan ta gimtse dariyarta tace "Jabiru bana san shiririta ka nemi daidai kai dan ko a ƙauye nake ba abinda zai sa na aureka" ta faɗa tana jefa masa harara "Abulle ni fa wallahi duk faɗin duniya babu wacca take burgeni sama da ke, dan Allah ki bani dama kinsan ance sai an gwada akan san na ƙwarai" ya faɗa yana gyara zaman hularsa tareda ranƙwafawa wai shi a dole ya ɗau wanka Tsaki Abulle tayi sannan tace "wallahi ka nemi takuramin sai na ɗaureka jikin waccan kukar, dama dai Bintalo kace da sai na sa baki ku sasanta amma nikam yanzu ai bilahillazi na wuce zaman nan" ta ƙare tana nuni da wata jibgegiyar bishiyar kuka Wani murmushi Jabiru ya saki sanan ya jawo glass daga aljihu irin shigen na Baba ari ɗin nan ya ƙwama ya harɗe hannaye bisa ƙirji sanan ya kuma duban Abulle yace "zaki rashi fa wallahi" Abulle duban Bintalo tayi da taketa kallon Jabiru cikeda burgewa tace "lallai na jima ban karya ba a ƙauyen nan, diba min bishiyar can akwai kogon da zan saka a rufe min wanan mara kunyar" Bintalo nan da nan idonta ya ƙwal, chan ta ce "dan Allah Abulle ki ƙyaleshi, in yaso ni sai ki haɗani da shi" Jabiru ɗagowa yayi ya dubi Bintalo yace "kingane na jima inason Abulle ne, amma idan batayi sai ayi da ke, normal ne" ya faɗa yana zare glass ɗinsa Murmushi Bintalo ta saki tana ɗan rufe fuska alamun taji daɗin batun dan tuntuni Jabiru yana masifar burgeta tun ma kafin tayi auren farko Abulle dubansa tayi tace "ya fi maka", sanan ta maida kanta kan Bintalo da fariciki ya isheta tace "malama taho mu wuce, yazo anjima" Hanyar gidan Mai gari suka ɗauka suna tafe suna taɓa tsokana, sun kawo dab da ƙofa idon Abulle ya sauka kan Sule na ƙoƙarin shigewa ƙasan benci Dariya ta saki sanan ta yafito Bintalo tai mata nuni, dariya Bintalo ta saki tace "kinsan kuwa ya daɗe baiyi sadaka ba ga tsadar tsiya" Abulle gaba tayi Bintalo na biye da ita, gaban teburin ta tsaya ta dubi Bintalo tace "wai nikam ina Sule ne" Bintalo tace "to ni ina nasani, kawai tunda bai nan ki fidda masa zakka ma naji shekaru har uku baiyi ba ma" ta ƙare tana tsinko ayaba guda biyu tareda ɓarewa, ta dunƙule ɓawon ta cilla goshin Sule dake ƙasan benci Hawaye kawai Sule yake ya gaza furta komai a kamasa Abulle chan tace " barshi dai muci cinmu, da zan biya amma tunda bai nan mu kwashi na bati kawai" zama sukayi suka naga musamman ayaba da kankana dan har ɗanɗanawa suke wadda batai musu ba su tofar. Bayan sun gama suka miƙe kowa ciki ya kusa ƙirji suka nufi gidan Mai gari...... *50* Washegari ta kama saturday, gabaɗaya gidan shiryawa sukayi inda Fatima da Khadija zasu wajen mahaifiyar Fatiman, Abulle da Nana Aysha, da Salim kuma zasu ƙauyensu Abulle Sadeeq ne duka ya kwashesu a mota, inda ya fara sauke Fatima da Khadija a gida sanan ya wuce da Abulle ƙauyensu, a mota sai drama sukeyi da Nana Da gudu Nana ta fita bayan yayi parking ta ruga gidan tana faɗin "Kaka Hansatu gani nazo, ina kazata" Hansatu rungume Nana da ta faɗa jikinta tayi tana faɗin "ke ba ma ni kikayi kewa ba daga zuwa ki fara tambayar kaza" Turo baki Nana tayi tace "ni dai ina kazata" "Na cinyeta" cewar Isuwulle dake zaune bisa tabarma Ihu Nana ta kurma ta zube ƙasa ta fara harbe harbe tana faɗin "wallahi sai an biyani kazata" Abulle da takaici ya kamata tun shigowarta ko zama batayi ba ta janyo Nana ta fara ɗumarta, sai da Hansatu ta janyeta, kuka sosai Nana takeyi tana faɗin "Allah zai sakamin" Hansatu ce tace "ai haƙuri zakiyi, tunda kika daina rashin ji wane bazai daina ba" Sun jima a gidan suna hira sama da awa uku sanan Sadeeq yace zasu koma Nana rungume kazarta tayi tace "kazata ki haihu ƴa ƴa tara kafin nadawo kinji" Dariya duka suka saki sanan su Hansatu sukayi musu rakiya zuwa mota, haka suka ɗau hanya suna ɗaga musu hannu Sai bayan magariba suka ƙarasa cikin gida, lokacin har Fatima ta dawo ta kuma yi abinci, aiko Khadija tayi da warmers ɗin da tayi musu jallop ɗin taliya mai kifi, sai da sukayi sallah sanan suka ci abinci Bayan isha'i Abulle ta yima Salim da Nana wanka inda sukayita shan daru da Nana dan sunyi faɗa ya kai uku kafin aka gama wankan Bayan ta kwantar da yaran a ɗakinsu, misalin goma Sadeeq ya shigo ɗakinta, hannu ya buɗe inda ta taso ta rungumesa tana faɗin "ina ƙaunarka mijina", rungumeta yayi yana faɗin "nima ina ƙaunarki matata, ina yarana", langaɓar da kai tayi tace "suna bacci, wanan Nana taka ta fiya rigima" Dariya Sadeeq yayi yace "in batayi ba ai bake kika haifeta ba", dariya itama tayi ta ɗan bugi ƙirjinsa cikin wasan soyayya.... *ALHMADULILLAH!! DUKA DUKA ANAN MUKA KAWO ƘARSHEN WANAN LITTAFI, UBANGIJI ALLAH YA SA KUYI AMFANI DA DARUSSAN DAKE CIKINSA KUYI WATSI DA ABINDA YAKE MARA KYAU. MUNA MUKU SON SO FISABILILLAH❤️❤️❤️*

Post a Comment for "ABULLE ANNOBA COMPLETE HAUSA NOVEL"