Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

AKWAI LOKACI COMPLETE HAUSA NOVEL

[30/04, 5:37 PM] UMMU AFAN : Bissimillahir Rahmanir Rahim Ya Allah kamar yadda nafara wannan novel lafiya kasa nagama lafiya Wannan novel hakkin ummu afan ne mallakarta ne kuma banyarda wata ta juyashi zuwa nata book dinba Dedicated this page to GORGEOUS WRITERS FORUM   GORGEOUS WRITERS FORUM G.W.F HOME OF GORGEOUS, INTELLIGENT AND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST   AKWAI LOKACI COMPLETE HAUSA NOVEL     PAGE 1 to 5 Alhaji abubakar dankoli shahararan Dan kasuwa ne Wanda yashahara gida da wajen kasan nan Allahji abubakar d'an asalin garin Kaduna ne dake zaune a anguwar tudun wada Ficeccene a duniya duk inda kuke tunani sunan shi yaje Alhaji abubakar shikadai ne agurin mahaifiyarshi kuma amma agurin mahaifinsa su goma sha hudune Mahaifiyarshi amina itace amarya agurin mahaifinsa kuma ita kadai Allah yaba d'a namiji wannan dalili yasa kishiyoyinta suke mugun matsa mata Bama iya kishiyoyi ba harda 'yan uwan alhaji abubakar duk ba mai sonta kasancewar Allah yawa Dan uwansu arziki Kofaduwa yayi yamutu suna da kaso mai tsoka acikin dukiyar tunda bashida da namiji Sai kuma gashi kwatsam ya auro matarshi ta hudu kuma karamar yarinya tahaihu da namiji Shikuma alhaji shuaib dankoli yayi murnar samun magaji da yayi Ranar suna yaci sunan Abubakar Tunda aka haifi abubakar mahaifiyarsa batada ishashan lafiya Uwargidanta hajiya suwaiba da maibinta suka je gurin wani hatsabibin boka shine yabasu magani sukasa mata a abinci ranar sunan abubakar Haka tayi ta fama da ciwo Abubakar na da shekara daya aduniya Allah yayi wa mahaifiyarsa amina rasuwa Rikonshi yakoma hanun uwargida hajiya suwaiba Hajiya suwaiba yaranta biyar mata Babbar yarta rukaiya sai kannata hudu Rukayya tadau komai na bakin halin mahaifiyarta Dan haka kawai itama tadauki tsanar duniyar nan ta daura akan abubakar Gashi duk yadda zasuyi abubakar yabar duniya sunyi amma Allah yace basu isaba Cikin tsanani da kunci abubakar ya rayu agidan mahaifinsa 'Yan uwan Alhaji shuaib ma sunfi nuna mishi tsana karara   Bayan shekaru 30 abubakar anzama saurayi kuma mai jini ajika Mai Neman nakamshi duk da yawan dukiyar mahaifinsa hakan baisa ya nade hannu ba Yayi karatu sosai inda yakai matsayin babban a karatunsa Bayanwata biyar da kammala karatun professor abubakar ne Mahaifinsa ya mishi maganar aure yace ba yanzu ba sai yasamu matar da ta dace dashi Hajiya suwaiba uwargidan allahji shuaib tasameshi da zancen Yakama ta ya matsawa abubakar akan yayi aure Dan duk abokanshi yanzu suna da matayensu Alhaji shuaib yace mata tunda yace abashi lokaci abashi mana suwaiba Ran hajiya suwaiba yabaci tace wallahi alhaji kana bata yaron nan dayawa yanzu auren ne sai yagada ma zaiyi Tashi yayi yabata guri Dan baicika San surutuba Hajiya suwaiba taje tasamu kishiyarta maibinta tafada mata yadda sukayi da allahji akan abubakar Hajiya larai tace aikema dai wasa kika tsaya Mai zai hana muje musami baffa kisan shima mafa ba kaunar yaron nan abubakar yake Sai muji shawarar dazai yanke Hajiya suwaiba ta amince da shawarar hajiya larai Sukayi gidan baffa sunci sa akuwa suka sameshi agida Nan yazauna bayan sungaisa sukace fada mishi abinda ketafedasu Yace aikin banza shi shaaibun ne yake daure masa gindin Dan na lura da hakan amma badamuwa zanyi maganinsu Zan hada shida hafsat kunga kenan kawar dashi aduniya bazai mana wuya ba Cikin jindadi sukace hakan ma yayi baffa Dan wallahi muddin yaron nan yana gidan nan fa bawani morar dukiyar Dan uwanku zakuyi Dan komai nashi abubakar yakesawa akai yanzu kamai na kadarorin alhaji abubakar ne jagoransu Baffa yace nima abin yana damuna Komai yazo karshe ita wannan yarin hafsa zata gama mana dashi Nan dai su hajiya suwaiba murna yakamasu Sukayi sallama sukatafi gida Bayan kwana biyu baffa yasamu kaninshi alhaji shuaib da maganar hada yaransu auren zumunci Alhaji shuaib yace abashi lokaci yayi magana da abubakar tukun Baffa yace lalle ma shuaibu Ashe maganar da mutane suke fada akanka dagaske ne nawan wai yaronka yafi karfinka Alhaji shuaib yace yaya kenan Wannan kuma wani maganane na mutane Wanda idan mutum yanajin irin wannan jita jitar bazaiyi abinkashi ba Baffa yace kwarai kuwa shuaibu dole kanunamin ban isa da kai ba balle danka Duk abunda kefaruwa akunnen abubakar Yashiga cikin falon yadurkusa harkasa yace wa babanshi abbu na amince a aura min wace baffan yakeso abbu dalilina bazanso kasaba wa 'yan uwan kaba Allah yasa haka shine mafi alkari Alhaji shuaib yace Allah yamaka all albarka abubakar Allah yarabaka da sharrin duniya da na lahira Allah kuma yakareka daga sharrin mutum da aljan Abubakar yace ameen abbu Baffa yace kagani ba Dan naka ma yafika hangen nesa idan bamu hadasu zumunci tun yanzu sai bayan ranmu zasuyi Alhaji shuaib yace tunda ya amince ai shikenan acikin yaran nawa Wacece za ahadsun Baffa ya wage baki yace hafsatu mana Alhaji shuaib yace Allah yasanya alkari Sukace amin Baffa yace saika shirya kaje kufahimci juna ko abubakar Abubakar yace insha Allah baffa zanyi kokari naga nasamu lokaci naje Baffa yace yauwa hakan ma yayi kyau Yace nizanwuce Abbu yace tun yanzu yaya Baffa yace tunda nayi abinda yakawoni zama ai banawa bane Abbu yace hakane kagaida gida yace gida zaiji Bayan tafiyar baffa abbu yakalli abubakar yace nidai hankali na baikwanta da wannan auren ba abubakar Abubakar yayi murmushi yace karka damu abbu kasa albarka kawai aciki Hajiya suwaiba da kishiyarta hajiya larai sunji dadin wannan Abu koba komai idan abubakar yamutu suna da kaso maitsoka cikin dukiyar alhaji shuaib   Hafsa yarinyace ga baffa kuma itace babbar yarshi Hafsat kyakkyawace ajin farko Dan danginsu sungaji kyau ne Dan shima Abubakar ba bayaba gurin kyau Hafsat tana da zafi Dan ita bata son raini ko kannata ba kasafai tafiye sake musu fuska ba Dan karsu rainata Ko a school ba mai taka ta barshi sai dai kuma tana da wani hali Wanda ko agidansu ba asanta nadashi wato tausayi da son 'yan uwanta Kwatata bata nunawa dan tasan halin iyayen nata Lokacin da zancen hadasu aure da Abubakar yazo kunnen ta hafsat tayi murna sosai amma sai ta bar abinda acinkinta Ba Wanda ya fahimceta ****** Bayan auren abubakar da hafsat tun abubakar baya kulata irin kyautatawar da take mishi yasa yafara sakin jikinsa da ita Soyayya sosai suke inda kasan auren soyayya sukayi Bayan shekara daya da aurensu Ranar asabar hafsat tana zaune kusa da abubakar tasa mishi ido kawai tana kallonshi yace yadai madam Tace wallahi dama sonake kabarni naje gida na wuni yau kaga nafi wata banjeba Abubakar yace shikenan bukatar tace shikenan Da kanshi yashirya hafsa ma ta shirya suka shiga mota yajasu sai gidansu su hafsat Suna zuwa yasauketa yabata kudi masu yawa yace tashiga shi sai yazo daukarta zaishiga Tace Allah yadawo da kai lafiya Yace ameen matar kirki tayi murmushi tashiga gidansu Kannanta na murna ga adda hafsat ga adda hafsat tayi murna ita ma da ganinsu Taci sa akuwa YAU suna da babbar bakuwa wato rukayya babbar yarinyar hajiya suwaiba Wato yayar abubakar kenan Nan akagaisa Rukayya tace anya hafsat kina amfani da maganin da akebaki kizubawa abubakar a abinci Maman hafsat dinta ce nima dai abin yadameni wallahi ace duk wata sai munkashe makudan kudi akan sa munkarbo maganin amma sai muji sajinkanya kuwa kina yin yadda akesaki kuwa Hafsat ta zumburo baki tace inayi mana kawai dai shifa yana da addua sosai ajinkinshi Dan infada muku gaskiya ma baicika bacci ba saboda makiyansa   Rukayya tace a lalle wato mune ma makiyansa ko Ashe bakida kunya hafsat Hafsat tace kai nifa barin fito muku a mutum ina son mijina Kuma koda banasonshi bazan taba kashe mutum ba balle ma Dan uwana kuma mijina Salati sukasa tare da tafa hanu suna salati cikin tsananin kaduwa da maganar hafsat dasukayi Hafsat batayi aune aune ba taji saukar bugu kota inta Bakowa bane yake dukanta illa mahaifinta baffa yace ai wanna yarinya da haihuwarki gwamma barinki Ashe bakya son cigaban mu kinje soyayya ya rufe miki ido ko Maman ta tace to wallahi ko kiyi abinda mukace ko na tsine miki Cikin tsananin tashin hankali hafsat tace mama babu biyayya ga aikata sabo Barin taba aikata abinda kukeso ba sai dai kuhada dani da shi kukashe gaba daya Nan ma baffa da maman ta suka rufu mata da duka dakyar rukayya takarbeta aikuwa tana samun anbarta tadauki Jakarta da gudu tabar gidan takal manta a hanu Tayi bakin titi ta tari keke nafef Sai gidanta tana shiga tayi dakinta tayi kuka mai isarta kafin Ta bakanta hakuri takudiri aniyar koza a kasheta bazata barisuyi galaba akan abubakar ba Takira abubakar tafada mishi ya wuco gida kawai tadawo Yana zuwa yasameta ba kaman yadda suka rabu ba Yace meyasameki madam tace bani da lafiya ne shiyasa ma baffa yace na dawo gida Yace ashsha maza tashi muje asibiti Tace a a basainaje asibiti ma jikinda sauki yace shidai baiyarda ba Bata son mishi gardama sosai Cikin ikon Allah kuwa kitoci sukayi mata tambayoyi Tayi ta bada na karya Daga karshe dai suka mata pregnancy test aikuwa aka sameta da ciki na sati hudu Itakam ma bata sani ba Dan bata laulayi komai Cikin farinciki abubakar yayi wa Allah godiya Bayan sundawo gida ne abubakar yatafi hargidansu yafada wa abbu mahaifinsa cewan hafsat na da ciki Abbu ma yayi murna sosai daga karshe yayi fatan alkairi Labarin cikin hafsat yabaza ko ina duk dangi asan da cikin dake jikin hafsat Hajiya suwaiba da kishiyar ce cikin tashin hankali suke tattaunawa Hajiya suwaiba tace amma larai kinsan baffa ya mugun raina mana wayo Hajiya larai tace nima nayi tunanin haka kinga gashi yarinyar zata haihu idan ta haihu musamman akasamu namji fa shikenan kashin mu ya bushe Shikuwa baffa jika za ahaifar mai kinga koba komai za anfana tanan Nan dai suma suka hau kulla kullansu Bayan wata tara hafsat tahaifi danta kyakkyawa namiji fari Sol dashi kaman atsaga jini yafito Yaro sonkowa kin Wanda yarasa Ranar suna yaro yaci sunan ABDUL HAKEEM ana kiransa da HAKEEM Hakeem yataso cikin soyayyar iyayensa ga wayo ga farinjini Tako inta Hakeem ya hadu     Mujezuwa taku ummu afan ce Sai mun hadu a next page Comments & share [30/04, 5:40 PM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN   DEDICATED THIS PAGE TO UMMY KHALEEL   GORGEOUS WRITERS FORUM G.W.F HOME OF GORGEOUS ,INTELLIGETAND EXPERT WRITERS WE ARE THE BEST AMONG THE REST   AKWAI LOKACI   PAGE 6 to 10   Please masu karatu karku rikice shuaib shine baban alhaji abubakar   ****** BAYAN SHEKARA ASHIRIN Hakeem yaro Dan kwalisa Wanda yagaji kyau tako ta ina kama daga kan uwa uba dangi da dai sauransu Duk wani kulla kulla yafaru acikin shekaru ashirin nan amma Allah bai ba wa makiyan alhaji abubakar nasaran cin galaba akanshi Tare da gudumawar uwargida ran gida hajiya hafsat Kwatata taki bada hanyar da za a cutar mata da miji ko danta Dan yanzu mahaifinta wato baffa ya saduda tunda yaga samu tunda an Haifa mishi jika namiji Hajiya suwaiba tare da hajiya larai sune basu yarda ba su sai sunga bayan alhaji abubakar da iyalanshi Yayar alhaji abubakar wato hajiya rukayya itama fa tana nan akan bakanta Naganin kanin nata yabar duniya da iyalansa amma hakan ya gagara .   Hajiya hafsat zaune makeken falonta tana duba wani littafin ahalarine Sai taji sallamar dan nata Hakeem Tadaga kai ta kalleshi tace Dan albarka yace na am abin alfaharina ki tashi lafiya , Hajiya hafsat tace lafiya qalau Dan albarka daman kainake jira kamin dauri akan inda nake jiya Hakeem yayi murmushi yace da fatan dai d'alibartawa zata kawo hadda Idan bata kawo hadda ba yau ba dori Mummyn shi tayi murmushi tace tunda kaga yau baka kirani ba kaima nakejira aikasan nawuce gun Hakeem yayi murmushi yace a a fa mummy bagirin girin ba tayi mai fa Mummy tace mai sosai makuwa Yace muje zuwa inajinki d'alibata Nan mummy hafsat tafara karatun da ya Dora mata najiya tiryan tirya. Tana gamawa yace allahuakbar yaufa gaskiya daliba tayi kokari Nan yaci gaba da Dora mata Duk abinda suke daddynshi abubakar yana kallonsu cike da sha awa Dan Allah ya daura mishi son iyalanshi da Akullum ya kallesu yana godewa wa Allah daya bashi family kaman Wanda yake dashi a yanzu Yana alfahari da hafsat Saukowa yayi falon tare da sallama Hakeem yaje ya Rungume dad din nasa Dan kullum haka suke gaisuwa kaman wasu larabawa Baban yace Allah yamaka albarka Hakeem Mummy tace ameen daddyn Hakeem Nikam ina da tambaya daddyn Hakeem yace inajinki mummyn Hakeem inajinki yi tambayarki Tace kullum saika tasawa Hakeem albarka Dan wani lokacin sainaji jikina yana sanyi saikace mai bankwana Alhaji abubakar tayi murmushi manya yace hafsat kenan a duk lokacin da kalli Hakeem inajinsane harcikin raina kullum son d'ana karuwa yake acikin zuciya Sai nakeganin ba Kalmar da dace dashi sai aduk lokacin da na kalleshi nasamishi albarka Daddy yace tukun nama badai kishi kike bako Mummy hafsat tayi murmushi tace kishim ma ai sainayi daddyn Hakeem kafin na haifi Hakeem duk ni kama irin wannan abubawar amma tunda aka haifeshi karage Komai naka Hakeem Hakeem yayi dariya yace wato ma d'aliba kishi kike dani ko zamuzo karatu zan fanshe ai Daddyn Hakeem yayi dariya yace gaskiya kam yakamata kadau mataki Mummy hafsat tace inkuwa hakane Nima saina dau maki Nima Baku abinci d'an kadan Kasan danka da ci kaman gara Gashi bayacin abincin kowa sai na mummyn shi Haka dai sukayi ta hira cikin nishadi Hakeem tun yana shekara shabiyar yagama secondary school Kuma ashekarar mahaifi sa yakaishi Saudi Arabian karatu , Duk shekara Hakeem yake da wowa gida Hutu. Wannan shekarar ma yadawo ne har yanasa ran komawa nan da sati daya Islamic law ne acan saudiya Karatu yake sosai bakama kafar yaro wancen da wowar dayayi ne yayi service dinshi a Kano Kafin yakoma Dan hado degree dinsa nabiyu wato masters Yanzu yake da shekara ashirin aduniya cas   Hajiya rukayya yayar alhaji abubakar suna zauna da mahaifiyarta Tazo gida tace nikam hajiya maizai hana muhada su Hakeem da laila aure Kinga dai laila kam kanwar lasa bace zata iya komai akasata Hajiya suwaiba tace amma kinsan baza a wa Hakeem aure yanzu bako Duka duka fa shekararsa ashirin Kuma kakansa ya yarda ko babanshi ya yarda kinsanshifa da taurin rai Dakyar ya yarda aka aura wa abubakar hafsat amma Kinga yadda tazama bata jin maganar kowa Hajiya rukayya tadubi uwartata tace hajiya tunda kekika rike abubakar , Ki aika akira miki shi kinsan shi da biyayya har kuka kisamishi akan lalle kina son a hada auren laila da Hakeem inyatashi komawa karatu yatafi da matarshi , Kinga idan kika gama kama kafar abubakar na Abba ba maiwuya bane saboda Abba yana son abubakar Kuma yana jin maganar shi , Hajiya suwaiba tace naji dadin wannan shawarar taki rukayya Allah yamiki albarka 'ya mai kishin uwarta , Nan hajiya rukayya tace wa uwarta zata wuce gida dan taje tasamu laila tafara gaya mata abinda suke shirin yi . Alhaji abubakar yana office dinsa na kasuwancinsa dan tunda yayi karatun shima har zama professor Sai yazabi da yayi kasuwanci Kuma alhamdullila komai yasamu asanshi gida da wajen kasan nan Yana zaune bayan sun gama meeting yaga kiran matar baban nashi wato hajiya suwaiba Ta shaida mishi tana son ganinshi Cikin girmamawa yace insha Allah yanzu zaizo Wacece Laila Laila 'ya ce agurin hajiya rukayya yayar alhaji abubakar Laila ta taso cikin gata ga tabara bairin wacce batayinsa Laila duk wani halin rashin mutumci takwashe tsaf na uwarta da kakanta hajiya suwaiba Shekara daya ne a tsakaninsu da Hakeem amma saboda son zuciya irin nasu hajiya suwaiba da 'yarta suke kokarin hadasu aure. Lokacin da hajiya rukayya tasamu 'yartata da zancen auren Hakeem bakaramin murna tayi saboda Hakeem tun bai kai koina ba billionaire ne Dan komai na mahaifinsa nasane kowa yashaida hakan so ake kawai Yagama makaranta adanqa mushi komai a hanunshi shiyasa takesonshi Dan kudin shi Kuma laila tana ganin akan kudi zata iya komai ciki kuwa harda kissa Dan haka taba uwarta rukayya goyan baya Dari bisa Dari   Hajiya rukayya tasan dama bazata samu matsala da 'yartata ba sanin halinta datayi"   **** Hajiya suwaiba ta zauna da alhaji abubakar tace tana son taroki wani alfarma agunshi Allah yasa zai iya mata alhaji abubakar yayi murmushi yace haba hajiya kema uwatace Ba alfarma a tsakanin mu Sai umarni , Umarni kawai Zaki bani na aiwatar Cike da jin dadi hajiya suwaiba tawage baki tace Allah yamaka albarka abubakar Yace ameen hajiya Tace daman 'yar uwarkace tace maizai hana kuhada yaranku aure wato Hakeem da laila kaga za adada karfafa zumunci atsakanin mu ko yajagani Cikin tsananin mamaki Alhaji abubakar ya kalli hajiya jin abinda tace Yace hajiya aure fa kikace duka duka Hakeem din gudawa nawa yake yanzu fa yake ashirin hajiya gwamma ita lailar ta kai amma shifa namiji ne hajiya ai dasauranshi Hajiya suwaiba tace inbanda abunka baka so muga 'ya'yan jikokinmune ai gwamma tun kan kasa ya rufe mana ido muga munbar baya ana zumunci a tsakani Tace amma daman shawarane ba umarni dan nasan ban isa nabaka umarni ba tunda bani na haifeka ba saita fasheda kuka Cikin tashin hankali Alhaji abubakar yace kiyi hakuri kidaina kuka na amince da bukatarki Allah yasa haka ne mafi alkairi agaremu baki daya Tace Allah yamaka albarka abubakar wallahi yadda kake min biyayya ko 'ya'yan Dana Haifa basa min haka Allah yajikan Amina mahaifiyarka ya haskaka kabarinta Abubakar yace ameen Nizan wuce hajiya tace to yaushe zaka samu baban naka da maganar yace badamuwa gobe zandawo Ya wuce cike da jin tausayin dan nashi a wannan shekarun zai hada damuwar mata akansa ""   Bayan yakoma gida ya huta Ya ce hajiya ina Hakeem tace aitunda kuka dawo daga isha banganshiba baishigo ba alhaji yace OK namanta Yana ganawa da wasu committee na gidan marayu Nisuka zo gani nace yaji abinda suke bukata Sai yafada min Mummy hafsat tace Allah sarki gaskiya daddyn Hakeem kana kokari Allah yakara budi Kafin daddy yace wani Abu Hakeem yayi sallama yashigo bayan ya zauna yafada mishi yadda sukayi da committee din marayun Sai dadddy yace dama inason zamuyi wata magana mudiga uku Duk suka bada Hankalinsu ga abinda daddy zaice Nan yafede musu biri har wutsiya aikuwa Hakeem cikin tashin Hankali yace aure kuma daddy at this age of mine No impossible Daddy Mummy hafsat tace kwantar da Hankalinka babu Wanda ya isa maka aure a wannan shekarun Wallahi basu isaba su samu a damuwa ba Indai ni hafsat inaraye inkuna nasamu goyon bayan mahaifinka Ta nuna daddyn da han nunta """     Muje zuwa fans' Naji dadin comments dinku a first page dina ina alfahari da Ku masoya akwai lokaci   Please your comments is needed naji comments dinku [30/04, 5:42 PM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN I DEDICATE THIS PAGE TO AKWAI LOKACI FANS' MUCH LOVE TO YOUR COMMENTS   GORGEOUS WRITERS FORUM G.W.F   HOME OF GORGEOUS, INTELLIGENT AND EXPERTS WRITERS WE ARE THE BEST AMONG REST.   AKWAI LOKACI   PAGE 11 to 15   Alhaji abubakar yanisa yace abin duk baikaiga haka ba hafsat Nasanki da biyayya da jin magana ina son kubani goyon bayan akan wannan abun da hajiya takeso Zata ga kaman dan ba ita ta haifeni bane yasa na kibin umarninta Hajiya hafsat tace amma alhaji HAKEEM guda nawa yake da za ace wai za amishi aure yanzu Gaskiya dai nasan wannan auren Bana Allah da annabi bane auren manufa ne kawai dan sucinmma wani burinsu na daban Alhaji abubakar yace ina son kidinga kyakkyawar zato akan mutum kuma kisa wa abin albarka a matsayinki na uwa Kuma ai Hakeem namiji ne ko awani lokaci zai iya kara aure a lokacin dayake bukatar hakan Wannan kawai kutai maka kubani goyan baya nasamu ladar zumunci Hajiya hafsat tace amma dai kasan yaya rukayya ba sonka take bako Tayi hakane dan kawai tasamu hanya ta cucemu Daddy yace a musu kyakkyawar zato Shidai Hakeem tunda yasaukar da kansa kasa baisake dagowa ba Dan yadda yakejin zuciyarsa kaman zata bugs Hajiya hafsat tace kuma ma arasa yarinyar da za ahadashi da ita Sai wannan Mara kunyar yarinyar da ita kanta yaya rukayyar ma bata barta ba Alhaji abubakar yace shina mijine ai zai gayrata Yadda yakeso ta zama Hakeem dai yace Sai dasafenku Daddyn yace harzaka bacci son Hakeem yace a daddy Ya kalli mummynshi yace mummy Sai da safe Tace Allah yatashemu dan albarka Daddy yace bakace min komai ba zakatafi bacci Hakeem yace duk abinda kayi dai dai ne kawai daddy bazaka taba umartata akan Abu nakasa yima ba koda kuwa ni banasonshi Ya wuce yatafi zuwa dakinsa Alhaji abubakar yace masha Allah Allah yayi gaskiya kabi iyayenka kaima za a bika Kinga abinda nayi wa mahaifina nima nawa d'an yadawomun dashi , Hajiya hafsat tace hakane daddyn Hakeem gaskiya Allah yabamu d'a nagari fatanmu kawai shine Allah yarabashi da sharrin makiya . amma wallahi wannan aure na Hakeem bai kwanta minba kokadan Haka dai sukayi ta tattaunawa tsakaninsu .   HAKEEM bayan yakoma dakinshi yashiga duniyar tunani yace tabas gaskiyar mummyn shine auren manufa zasuyi , Dan yadade da gane 'yan uwan mahaifinsa basa kaunarshi koka dan , Inba haka zasuce wai za a hadashi aure da yarinyar da bata da mutunci batada tarbiya , Nifa idan asona nane sai nan da shekara goma sha nayi aure , Dan sai tsaya na zaba matar da ta dace da rayuwata , amma idan tasake tashiga rayuwa ta a yanzu zan nuna mata waye ABBULHAKEEM zata San koni waye duk wani shige da ficen dangin mahafin nasa yasani sarai Dan haka yadauki aniyar yiwa mahaifinsa biyayya Sai zai nuna musu shidin namijine wato dangin mahaifinsa kenan Haka dai Hakeem yayi ta sake da warwara Washagari da safe bayan Hakeem yagama break fast ne yadauki phone dinshi yakira Ahmad Abokinsa yace kana inane ahamad yace ganin agida Hakeem yace OK ganin nan shigowa gidan """"' Ahmad abokin Hakeem kud da kud dan tare sukayu primary da secondary school Kuma tare sukatafi makaranta a Saudi Arabian tare suke dawowa Hutu , Hakeem da Ahmad basa boye wa juna sirrinsu kokadan Komai nasu tare sukeyi dalilin hakan yasa iyayensu sanin juna har ake zumunci sosai "" HAKEEM yayi parking a harabar gidansu Ahmad Kai tsaye ya wuce part din Ahmad yana shiga yafada kan kujerar falon Ahmad din Ahmad yace ya man yanaga duk kayi wani iri meyake faruwa ne Hakeem yaja dogon numfashi yace kaidai bari man wallahi so ake a hada min zafi agida Ahmad yace zafi kuma kaman yaya Ahmad yakwashe komai yafada wa Ahmad Ahmad yayi dariya sosai yace to ai kai Allah ya kashe yabaka tunkana very young dinka zaka angonce ni wallahi banga abinda damuwa Ba Tunda Ahmad yafara magana Hakeem yake kallonshi dan yabashi haushi sosai Yace wato dariya ma nabaka ko Ahmad yace dariya kabani mana kaida za ama auren gata Ahmad yace amma fa ina tausayawa yarinyar saboda by the time din kake cikin samartakarka by then itakuma bayadda takaraji fa dan tazama baba Hakeem yace kai man har ka mata lissafi kasan ko yar ten years za abani Ahmad yace ai nasan baza a tabaka yarinyar da bata wuce goma Ba Kaga kuwa may be 16 to 17 years haka Kagakuwa ai kafin nan da wani lokaci tazama mama Hakeem yace duk ma baka zogunba Todai yarinyar shekara daya nabata a duniya Ahmad yace cab wallahi hartabani tausayayi dan nasan bayadda za ayi kazauna da ita kadai a lokacin da samartaka yazo maka Hakeem yace kaji dan rainin hankali yanzun wanene idan ba saurayin Ba Ahmad yayi dariya yace sau dai baka kai rayi dinba Hakeem yadauki trowing pillow ya jefeshi dashi Yace kaiko nazo nafada maka damuwa ta memakon kakwantar min da hankali sai kuma bige da da yimin shiririta ko Ahmad yace to naji abikona yanzu dai kasan muhimmancin bin umarnin iyayeko dan haka kawai kabi maganar daddy insha Allah komai zaizo dasauki Ya da amaryar zamuwuce ne Hakeem ya yatsina fuska yace Allah yasauwake natafi da ita akanme Ahmad yace ya hakuri maida wukar Yanzu dai katashi mushiga cikin gida kugaisa dasu mummy Sai muwuce sallar azahar ko dan naga time yayi .   Alhaji abubakar yasamu mahaifinsa alhaji shuaib akan maganar dasukayi da hajiya suwaiba aikuwa alhaji shuaib yace baisan San zance Ba Yace waini abubakar sai yaushe za abarka kayi abun kankane Kai an baka mata batareda son rankaba ka karba sakamokon biyayyar da kayi Allah yasa kadace da mata tagari Sai kuma yanzu andawo kan danka Wanda shi ko auren ma bai isaba ance za abashi mata Hajiya suwaiba tafito daga dakinta tana cewa haba alhaji ai nagani yaran nan fa duk jikokinkane daga ita lailar har Abdulhakeem din Idan akayi wannan aure sai munfi kowa farinciki Kaga ai tuwona maina kenan Alhaji shuaib yace yanzu Nagano kekika kitsa komai suwaiba Hajiya suwaiba tace a nice alhaji ganinayi da abubakar da rukayya ai duk 'ya'yanane To ina laifi dan nace suhada yaransu aure tunda sauran numfashin mu muga hakan Alhaji shuaib zaiyi magana abubakar yace dan Allah Abba maganar yawuce kawai ka amince kawai da bukatarta Alhaji shuaib yanisa yace yanzu Abdulhakeem din ya amince Abubakar yace namishi magana tunjiya kuma ya amince Alhaji shuaib yace banyardaba katuromin shi idan bayason auren ba maiyi mashi dole .. Bayan kwana biyu Hakeem yayi shiri tsaf ya wuce gidan kaman nasa alhaji shuaib Yana shiga falon gidan yasamu kakan nasa yana zaune yana kallon sunna TV Sai yace a a tsoho mairan karfe an kura wa TV ido kaman kanagani da gaske Alhaji shuaib yace aikuwa dai idona yafinaka naka karfi dan tar nakeganin ka Hakeem yayi dariya yace fadi gaskiya dai kakus Alhaji shuaib yace yanzu dai Ba wannan Maganar da kuka yi da mahaifin ka nakeson naji ka amince ne ko baka aminceba idan baka amintaba Ba zanbada goyon baya amaka doleba amma idan ka amince shikenan Allah yasa albarka Hakeem yayi shiru dan dai kawai yariga yayi wa mahaifinsa alkawarin amincewa ne Nan yace na amince kakus Alhaji shuaib yace Allah yasaka albarka Sannan kuma ina maka albishir da cewan duk lokacin da zuciyarka yabaka kanason auren zabinka kana da dama yin hakan Dan wannan aure ne kawai na hadi nasu na daban Harcikin ran Hakeem yaji dadin maganar tsohon yayi wata dariya Allah yakara maka Nisan kwana kakus dina na kaina kaga irin wacce zanzabo a matsayin mata Kakan yace Ameen dan albarka Allah yasa muna raye muga wannan rana Hajiya suwaiba tashiigo taji duk abinda suke fada Cike da isa tace wa alhaji shuaib aidai kabari ayi wannan din kafin afara zancen wata Hakeem ganin shigowar hajiya suwaiba yasa yadaure fuska yakoma Hakeem dinsa Danshi Sam jinin bai hadu da matar kakan nashi Ba Ganin haka yasa yace sai anjima kakus zan dawo muyi hira na musamman Batareda yakalli inda hajiya suwaiba take ba Yace ina wuni hajiya Baijira amsawarta Ba yayi hanyar waje Tabishi da harara tace inan daku ai Zamu hadu a karo na biyu ne Laila da mahaifiyarta sunan suna ta murnar samun nasara Dan ansa sati nan sati daya saboda komawar Hakeem school Mummyn Hakeem kam batayi wani gayya Ba dan ita wannan auren ba aure bane agurinta Duk lokacin da yakawo matar da zai aura alokacin ne zata yi nata bikin Zata nunawa dunniya sai a lokacin dan yayi aure Next page Your comments is needed fan's Much love to your comments [30/04, 5:46 PM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN   I DEDICATE THIS PAGE TO MY LOVELY MOM MUCH LOVE TO YOU MOM NO ONE LIKE YOU IN THIS WORLD❤❤❤   GORGEOUS WRITERS FORUM G.W.F HOME OF GORGEOUS, INTELLIGENT AND EXPERTS WRITERS WE ARE THE BEST AMONG THE REST   AKWAI LOKACI   PAGE 16 to 20   Hajiya suwaiba da hajiya rukayya kadai suke kidansu kuma suke rawar su Abin yana basu haushi ganin Ba Wanda yake shiri akan bikin Sai dai dayake suna ganin dazarar anyi auren shikenan Zuriar alhaji abubakar sundawo hanunsu dan sai yadda suka juyasu amarya laila ta gayya ci kawayenta sosai dan halartar bikinta Maman amarya hajiya rukayya ce tazaunar da ita tace wai ke yau saura kwana biyu biki amma baki tambayi shi Hakeem din kudin dazakiyi hidima dasu Ba Laila tace hmm mama kenan to ina managanshi ballantana har na tambayeshi kudi Hajiya rukayya tace lalle ma yaron nan ya raina wa mutane hankali amma zai shigo hanunmu ne ai Yanzu abinda nakeso dake kitashi kidauki kawarki daya tarakaki zuwa gidan su Hakeem din Kikarbo kudin dazakiyi Hidima dasu Laila tace wannan ma shawara ne mamana yanzu kuwa zan tafi Haka laila tadauki biky daya daga cikin kawarta taraka zuwa gidan su Hakeem Laila shiga tayi cikin wasu Riga da wondo parkistan Wanda siririn gyalenta tayafashi akan gashin dokinta dayazubo mata har gadon bayanta Ga farce da akasa musu duk ita da kawar tata kana ganinsu kasan dai Ba tarbiyya Laila tana parking cikin gidan su Hakeem tashiga direct zuwa falon gidan Tana shiga ta tarar da hajiya hafsat mom din Hakeem zaune kan two sitter tana kallon tasharta na MBC 4 Mummy hafsat kawai ganin mutane tayi tsakiyar falo batare da sunyi sallama ba Tadaga kai takallesu suka hada ido da laila Laila cikin rashin gaskiya tace mummy ina wuni wallahi banganki bane nazo gurin Abdul Hakeem ne Mummy hafsat tamusu wani kallon takaici tace Ku wasu irin marasa tarbiyar yarane dazaku shigo gida Ba sallama ko haka aka koya muku agidajenku Cikin in ina laila tace sorry mom please ina Hakeem yake muna sauri lokaci na kurewa Cikin tsanin mamaki mummy hafsat take kallonsu laila da suke tsaye kikam kaman andasasu suna karkada jiki Mummy hafsat tace nikuke wa rashin kunya laila ankuwa fada miki halina To kikoma kitambayi uwarki wacece ni idan ita ta turoki kimin rashin ni ina dai dai da lokacinku Kuma kije kifada wa uwarki dan tana yar mijina hakan bazai bata dama hakan bazai bata damar saku kuzo harcikin gida kuna min dibar albarka Ba Ita tasan wacece ni niba kanwar lasa bace aikuwa daga Laila har biky kawarta sun tsorata da yanayin mummy hafsat Mummy hafsat tace kubace min daga gida yanzun nan insake ganin kafarki agidan nan kiga abinda zaifaru Da gudu suka fice agidan kuwa harsuna tun tube Suna zuwa parking space Zasu shiga mota sai ga motar abdulhakeem aikuwa Laila washe baki tayi tace biky Gashi nan fa biky tace waw wannan Zazzafar motar shice Laila tace kadan ma kika gani indai Hakeem ne kinga zomuje musameshi karyashiga Hakeem kuwa shida Ahmad ne Ahmad yace wa Hakeem ya kaman kunyi baki Hakeem yace maikagani Ahmad yanuna mashi su wurinsu laila Hakeem yakai idonshi gurin aikuwa yana ganin sun nufosu yadaure fuska Ahmad yace kai harda bakin ma zaka nunawa halinka ko Hakeem dai baice komai Laila suka karaso gurin su Hakeem din Sai Ahmad yadan durkusa yace anty ina wuni Cikin tashin hankali Laila tace wace ce antyn taka Ahmad yakalleta cikin rashin mahimta danshi yadauka yayar Hakeem ce dangin su Danshi baitaba sanin laila Ba tunda Hakeem bazuwa yakeba Abin yaba wa Hakeem dariya amma yaci fuska sosai dan kar laila taga hakorinsa da sunan dariya Yarufe motarshi ya kalli Ahmad yace mujeko Laila ta tari gabanshi tace haba Abdul kasanfa gurinka nazo ko Hakeem yakalleta ya watsamata wani mummunar kallo yace gurina kikazo namiki me Abin yaba Laila haushi dan ya tsinkata agaban babbar kawarta Ta daure tace naga har yanzu baka zo gida munyi maganaba kuma baka kuma tambayeni abinda nake bukata na game da harkar bikinba shine mama tace nazo nakarbi kudin dazan yi hidima dasu Sai a lokacin Hakeem yayi wani killer smile yace lalle kuwa bazakiyiba Kikoma gurin wacce ta hada abin sai tabaki Nikam kwandala ta bazaiyi ciwo akanki Ba Nan ya wuce ta Ahmad yabi bayansa suka shiga cikin gida aikuwa da gudu Laila tafada mota Dan tunda take Ba a taba wulakantata irin wannan Ba Kawarta biky tayi ta rarrashinta kasa driving tayi biky ce tayi Hakeem da Ahmad suna shiga falon mummy Suka ganta zaune kan kujera Hakeem yasaki murmushi yace mummy na yadai naga kaman antaba minke Ahmad yanemi guri yazauna yace mummy an wuni lafiya Cikin fara a mummy hafsat tace lafiya qalau Ahmad ya su hajiyartaka Ahmad yace lafiya qalau tace zata zo anjima Mummy hafsat tace aikuwa kaman tasan inason ganinta Allah yakawo ta lafiya Hakeem yace mummy shine wato kinga Ahmad ina miki magana kina wani basarwa ko Mummy tayi murmushi tace ai matarka ce taba tamin rai shiyasa Hakeem yadaure fuska yace daliba zakifara ko Mummy tayi murmushi takalli Ahmad tace Ahmad katayini da abokinka dan Allah matarshi tazo ta bata min rai dan Allah basai na huce akanshi Ba Ahmad yayi dariya yace kinyi dai dai mummy Tace a to kaima kafada dai Hakeem ya harari Ahmad ya kalli mummy yace daliba bazaki daina kiran wannan Mara kunyar yarinyar da mata ta bako Mummy hafsat tace toya zamuyi komunki ko munso sai anyi Nan tabasu labarin yadda sukayi da su Laila dasuka shigo Hakeem yatashi ya suri key din motarshi yayi hanyar fita Mummy hafsat tace dagata dan albarka ina zaka yace mummy kibarni naje naci ubanta har tana da gost da zata zo gidan nan tasaki magana haka Mummy hafsat tace kalesu nima din ai sunsan wacece ni zata je tafada wa uwarta Zasu sake sabon shiri mu basusan shirinmu yafi nasu dan muda Allah muka dogara Hakeem yace wai mummy maiyasa daddy yakasa gane mutanen basa kaunarshi Ba sonshi suke ba fa Mummy hafsat tace nima abun yana damuna wallahi hakurin mahaifinka yayi yawa wallahi amma bakomai duk mai hakuri wataran yana tareda riba Mummy tace kutashi kushiga kuci abinci Suka tashi zuwa part din HAKEEM Suna shiga dariyar dayake cin Ahmad yafito dashi Yayi sosai Hakeem yace wai kai kuma wakake wa dariya Ahmad yace wallhi matarka da nacewa anty Hakeem yace karkasake cewa matana kace kawai matar kaddara Ahmad yace narki gaskiya man na tausaya ma wannan yarinyar wallahi kokadan wallahi bakuyi marching ba kokadan Da zanbata shawara data nemi mijinta a wani wajen tabarka Hakeem yayi dariya yace akai man shine wannan dariya haka amma nima naso nayi dariyar Dan bakaramin dariya abin yabani ba Kawai dai banson rainine yasa na make kawai Ahmad yace oh baruwana fa randa zaka angonce ina ina Dan haka nayishiru Allah yabada zaman lafiya Tsaki Hakeem yayi yace katashi muje muci lunch idan kuma baka gama surutun ba to Nan dai sukayi hira amma Rabin hirar tsokanane Ahmad yakewa Hakeem *** Bayan komawar su Laila gida tana kuka tana bawa mamanta labarin abinda mummyn Hakeem da Hakeem din suka mata Ran hajiya rukayya yabaci Tadauki waya takira uwarta hajiya suwaiba ta fada mata komai abinda Laila tafada mata Nan itama hajiya suwaiba ranta yabaci tace bakomai ai sunkusa shigowa hanunmu Tayi hidimarta da kudinta kawai zata fanshe ai Hajiya ruakayy tace amma hajiya kinsan wallahi bakudi a hanu na sosai Hajiya suwaiba tace kwantar da hankalinkki Kituro min ita jikallen sai nabata wasu kudi Nan hajiya rukayya tayi godiya ga mahaifiyarta kafin takashe wayar takalli 'yartata dake kukan wulakancin da akamata Tace kidaina kuka kitashi kitafi gidan hajiyata zata baki kudi konawane sai kufara hidimarku na kawaye Nan Laila ta washe baki tace kai Allah yabarmin kakallena yanzu ita zata bani kudin Hajiya rukayya tace kwarai kuwa aiba abida bazatayi miki ba kece fa jikarta tafarko Nan dai Laila suka tashi suka tafi karbo kudin """"   Ranar daurin aure dasafe hajiya suwaiba takira alhaji abubakar tace mishi yau daurin aure amma haryanzu basuga kayan lefe ba Alhaji abubakar yace ai mun sha afa ne hajiya kaman nawane za a hada lefen dashi anzo inda takeso tace million biyu sun isa Alhaji abubakar yayi signing a cheque yabata tace yauwa Allah yayi albarka Alhaji abubakar yace Ameen hajiya Nan yatashi yashige wajen mahaiginsa alhaji shuaib Yanashiga yasameshi yagama shirin daurin auren ne ma Yace a a abubakar kaine tafe kohar kafito gurin daurin auren ne Alhaji abubakar yayi murmurshi yace ai hajiya ce takirani akan maganar kayan lefen Daba akawo ba Alhaji shuaib yayi dariya yace wargi ma guri yakesamu Tamin magana nace tawa angon magana shine taki kai dayake sunga kana da hakuri shine suka bita kanka ko Alhaji abubakar murmushi kawai yayi baice komai ba Alhaji shuaib yace yadda yaron nan yake yana burgeni suna mugun shakkarsa Dan ina mata maganar ta tambayi Abdul Hakeem dakanta bakaga yadda ta yiba Alhaji abubakar yace ai yaron nan nima yana bani mamaki wlh gashi karamin yaro amma koyanzu nasake mishi komai zai riqe sosai Alhaji shuaib yace ai Allah ne yama sakayyar biyayyarka gareni da wannan d'anaka ABDULHAKEEM Zakayi alfahari da haihuwar Abdul Hakeem saboda kaima nayi alfahari da haihuwarka Allah yajikan mahaifiyarka amina Alhaji abubakar yace ameen Abba Nan sukayita hirarsu har lokacin daurin aure yayi suka fita zuwa gurin daurin auren   Hajiya suwaiba ta kira yarta hajiya rukayya tafada mata yadda sukayi da alhaji abubakar Wani irin ihu hajiya rukayya tayi tacikin waya tace million biyu fa kika ce hajiya Hajiya suwaiba tace to meza afasa Hajiya rukayya tace aikin ki nakyau hajiya ta Kinga munfara bambara tun yanzu ko Hajiya suwaiba ta ce kidai bari yarinya dai Allah yakashe yabata     **** Bayan andaura auren Abdul Hakeem da Laila usman   Daddyn Hakeem ya dawo gida bayan yazauna Mummy hafsat takawo mishi abinshi yaci sannan yabata labarin yadda sukayi akan kudin lefe Mummy hafsat tayi murmushi tace a lalle sun wankeka Yanzu zasuga kaman shirinsu yafara aiki kenan Murmushi Daddyn Hakeem yayi yace Hafsat mata agurin abubakar maman Abdul Hakeem Rigimar ki yana bandariya kefa baki yarda dawannan auren bako Mummy hafsat tayi murmushi tace ai Dana baiyi aureba Dan banmasan anyiba wallahi kawai dai za aiya kiran aurn da kaddara Daddyn Hakeem yayi murmushi yace zanso kimishi fatan dacewa kamar yadda nadace dake Dan ko zabin kaina nayi ba lalle nayi dacen danayi akankiba hafsat Next page Your comments is needed fan's [30/04, 5:48 PM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN DEDICATED THIS PAGE TO LOVELY SON AFAN ❤❤❤❤❤❤❤ GORGEOUS WRITERS FORUM G.W.F HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERTS WRITERS WE ARE THE AMONG THE REST   A KAWAI LOKACI   PAGE 21 to 25   Ankai amarya Dan kararen part dinta dake gidan su Hakeem . Mummy hafsat kam a ranar ma gidansu taje wa wuni Saboda batason damuwa """"' HAKEEM suna zaune shida Ahmad Ahmad yace kai kasan karfe nawa yanzu katashi muje narakaka dakin amarya fa . Cikin halin ko inkula Hakeem yace lalle kuwa su amarya manya bari ma kagani Ya kashe phone din shi ya gyara kwanciyarsa akan bed din Ahmad . Ahmad yace banganeba mekake nufi badai anan zaka kwana ba Hakeem yayi banza dashi yayi baccinsa Ahmad yace OK halin ya motsa ko ai wannan amarya taja wa kanta data waye. Hakeem da bata kanta wahala ba wajen auranka ba Nan shima yakwanta abinshi Dan yasan duk yadda zaikai ga magiya Hakeem bazai tashi ba .   Amarya Laila tana ta zuba ido taga ango yashigo shiru kakeji malam yaci shirwa kawayenta ma sun gaji suntafine Idonta biyu har wajen karfe uku ba ango Tadauki waya takira Maman ta Maman tace yadai laila naga kiranki yanzu Kingane dai yadda akace kiyi anfani da maganin ko karfa kiyi wani abin da zaisa yaki kusantarki kinsan maganin na yau ne kawai Duk hanyar da zakibi yakusance ki Kiyi shi karmuyi asara makudan kudaden da muka narkar wajen karboshi Laila tace yanzu dai dakin tsaya na fada miki abinda zanfada miki Hajiya rukayya tace inajinki meyafaru Laila tace haryanzu fa bai shigo gidan ba ma Cikin tashin hankali hajiya rukayya tace munshiga uku Yanzu soyake muyi asarar makudan kudaden nan Ki kirashi a waya mana Laila tace ina naga numbarsa Hajiya rukayya tace shikenan munyi asarar kudinmu Dan malam yace maganin kwana daya yakeyi idan yakusanceki zai zaima rakumi da akala bazaiji maganar kowa ba sai abinda kikace mishi Kuma zai tsani iyayensa To gashi Hakan su bai comma ruwaba Har kuka sai da hajiya rukayya tayi Dan maganin nan naira million daya haka suka caske wa malam Gashi yanzu wannan Dan ban zan yaron yaja musu asara Daga laila har uwarta basuyi bacci ba ********* Washagari da misalin karfe goma Hakeem yafito daga wanka daga bathroom din Ahmad Yashirya cikin wasu kananun kaya sun balain mishi kyau ya fesa turare Kafin nan yakalli Ahmad da yariga yashirya Dan yariga Hakeem tashi tunda suka dawo daga sallar asuba shi Hakeem sai yanzu yatashi Hakeem ya kalleshi yace yace muje mukarya zanje naga dalibata fa Ahmad yace to ango muje dining din ko Suka wuce zuwa dining area na Ahmad Sukayi break fast Kafin suka dauki hanyar zuwa gidan su Hakeem Suna hanya kafin sukai gidan su Hakeem sai daddyn Ahmad yakirashi akan yazo zai aikeshi Ahmad yace man sauke ni kawai nakoma gida idan na dawo daga aikan dad zan shigo mugaisa da amarya Hakeem bai kalleshi yajuya da motar yamaida Ahmad gida kafin shikuma yakoma gida yanazuwa yayi parking a gurin parking dinsu """" Laila tana jin shigowar mota tabude labulen window din ta ai kuwa taga shine Harfitowarsa tagani Yamata kyau kuwa Dan Hakeem mai kyau ne bakarya Da badan son kudin dayamusu yawaba ai Hakeem miji ne na nuna wa sa a Hakeem ya kulle motarsa yayi part din mummy Yanashiga yaga bata falo ya haura bedroom dinta aikuwa tana can tana ninkin kayan ta tana jerawa a sif Yashigo yace assalamualaikum mummy na Cikin murmushi mummy tace Dan mummy yakake Dafatan dai katashi lafiya ko Hakeem yace lafiya qalau daliba kawo kiga ni koma kawai kizauna muyi hira Mummy hafsat ta nemi gefen bed din ta tazauna Tsaf Hakeem yagyara wa mummy kayan ta yasake gyara mata bedroom din kafin yace mummy kinci abinci kuwa Mummy tayi dariya tace kaima dai tsokanata kake yaushe zankai har wannan time ban ci abinciba "''' Hakeem yayi dariya yace acici nasan ai dama agurinki na dauko ci Mummy tayi dariya tace a a nikarka min sharri Mummy tace ba wannan ba ma Dama inason magana dakai Hakeem yadawo da hankalinsa kanta Tace Dan albarka jiya ba agida ka kwanaba hakane Hakeem yace hakane mummy a gidansu Ahmad na kwana Mummy tace ai baka kyauta ba Tunda anriga andaura dole zamu rungumi kaddara Yanzu dai Laila tariga zama matarka Dan haka ina umartarka da karka wulankanta aure Aure ba abin wasabane duk kuma wani sharrinsu zai koma kansune da izinin Allah bazasu taba tasiri akanmu ba Hakeem yace ai mummy ki kwatar da Hankalinki adduoi na tsarin jiki ba Wanda bamayi agidan nan dai Dan haka ba abinda zasu iya mana Mummy tace Allah yasa Dan albarka acigaba da kula da addua Dan ina tsoron sharrin mutane """""" Bayan sun gama magana yace Mum zanje wajen Daddy a office Dan kinsan jibi mukeson dagawa fa Hutu yakare zamuje mutattauna Mummy tace kadage dai sai katafi ajibinko To da amaryar zakatafi Hakeem yace Allah yasauwake tayi zamanta ba inda zantafi da ita Mummy tace bazan maka doleba amma ka tabbatar komai kabari a kafin tafi Hakeem yace insha Allah mummy Yace barinje gurin daddyn Mummy hafsat tace a a kafara shiga kaduba yar mutane tukun ko Koba komai fa yar uwarkace Yace to mummy sai na dawo Tana jin dadin inda Dan nata baya mata musu Hakeem yashiga part din shi Direct bedroom din shi yawuce Yaje yadauko wani file kafin yasake fitowa Laila kuwa basan shigowarshi ba fitanshi tagani aikuwa kafin yakarasa fita tasha gabanshi Yace lafiya kuwa zaki sha gabana haka Laila cikin yanga tace Haba Abdul ya kake min wasu Abu kaman ba mijina kuma Dan uwana ba Dan Allah kadawo muzauna kona minti biyar ne . Hakeem ya watsa mata wani kallo Wanda dakanta tabashi hanya yawuce abinshi zuwa office din dad dinsa Hankalin Laila yatashi tace anya kuwa wannan Mutum """ ******** Da daddare bayan daddy da Hakeem sundawo sunci abinci can wajen karfe goma Mummy tace Dan albarka tashi katafi kabar Laila ita kadai Badan yasoba yamusu sai safe ya wuce part dinsa , Yana shiga falon Laila ta na kashe wayarta dasukaga gama da gawarta Ko kallo bata isheshiba ya wuce abinsa zuwa bedroom dinsa Yanashiga wanka yafada Yana fitowa sukayi ido hudu da Laila cikin wasu arnar kayan bacci wato sleeping dress kenan Kallo daya yamata yakau da kanshi Danshi idan ya raina kasuwa ko sauto baya mata Ya goge jikinsa yashafa mayukansa masu kamshi kafin yasaka night Wear din shi Ya kwanta tare da kashe wutar dakin """"" ai kuwa Laila tafashe da kuka Tun abin na bashi haushi har yagaji yace dalla malama kitashi kifita min adaki Cikin kuka tace Haba Abdul yanzu wannan shine zumuncin da iyayenmu suka hada muyi kenan Hakeem yayi wani uban tsaki kafin yajuya ya kwanta abinshi Can tace ai idan kai baka bukatata ni ina bukatarka Bai kamata kahanani hakkina da Allah yarataya a wuyarka ba """"' Tabbas yasan hakane kuma mummynshi ma ta mashi tuni akan haka Koba komai gwamma yafita a hakkinta Yajuya yace mata damuwarki kenan yasa aka miki aure ko Kafin tayi magana ya bajadda ita akan bed din Yacire sleeping dress din nata yayi wurgi da shi bako romance Sai dai adduar da akeyi lokacin da miji zai sadu da iyalinsa ai kuwa dai Laila tafada musu Tagane shayi ruwane Yanagama abin da zaiyi ya tureta ya kwanta abinshi Ita kuwa Laila tana cikin farin ciki Dan ita yadda taji din ne kuma bazata iya hakuriba """"" Kullum zata kawo kan nata indai zai biya mata bukatarta kafin ta shekashi lahira taci dukiya Nan itama ta kwanta bacci ya dauketa cike da farincikin kasancewarsu da Hakeem a Daren nan . Washagari Hakeem kota kanta baiyiba yana gama shirinsa cikin wata yadi mai tsadar gaske iri daya ma sukayi da Ahmad Yadin ash colour ne sai yasa bakin takalmi da hula Wanda akekira da senator Duk Wanda yakalli Hakeem sai yasake kallonsa Dan ya hadu iya haduwa Yana fitowa Laila ta tareshi tace abdul ga break fast dinka fa mai aiki tagama , Wani matsiyacin kallo yamata yace kinga nayi miki kama da mai cin abincin masu aiki """ Ban guri nawuce ni Tabishi da kallo tace aikuwa sai dai idan bazaka ci abinci agidan nan ba Dan ko kwai ban iya soyawa tayi dadi batare da ya kone ba """   Hakeem suna break fast daddy yace mishi Shi Ahmad din yashirya kuwa Dan naga kaman kai ka matsa kutafi Hakeem yayi dariya yace bahaka bane dad kasan fa I want to be come professor like you kaga yakamata indage ko dad Daddyn Hakeem yace hakane but please son take care of your self sosai kaji ko banda harka da mutanen banza """   Mummy tayi murmushi tace kai daddyn Hakeem duk komawarshi school saikayi mishi wannan nasihar yanzu fa babban mutum ne tunda ya ajiye iyali Daddy yayi murmushi yace wai haka son Shidai Hakeem baice komaiba Daddy yace nifa wallhi ina mantawa yarinyar nan tana cikin gidan nan Ya bara kace tazo akarya da itaba . Hakeem yace daddy ai tana da mai aikinta har tagama komai sunci abincinsu Daddy yace duk da hakadai ai itama yar gida ce Mummy tace kasan alamarin yara sai a hankali Kawai kabarsu nan dai mummy ta canja magana Tace jirgin safe zakubi ko Abdul Hakeem yace da asuba makuwa mummy tace aikuwa kaman nasani nagama hada ma komai Mummy Allah yasa kinmin wanna cake din naki medadi Tace ai duk abinda kasan ina maka ba abin da na rage Cikin jin dadi Hakeem yace that's my mom Allah yabar minku iyayena Daddy da mummy sukace ameen Allah yamaka albarka   Yauma da daddare sai da Laila takai kanta gurin Hakeem Tun karfe uku yatashi yagama shirinsa tsaf bai Dade da gamawa ba Ahmad ya kira yace man kataho tafa nigani a air port ma Hakeem yace OK gani nan Yadauki cheque ya rubuta dubu Dari biyar yasama Laila akan bed Da kuma short note Yafita daddy da mummy shi kawai suke jira suka rakashi   Next page Your comment is needed fan's [30/04, 5:49 PM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHI RAHMANIR RAHIM HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN   DEDICATE THIS PAGE TO MY ONE AND ONLY HUSBAND ABU AFAN (DOCTOR SULEIMAN)❤   GORGEOUS WRITERS FORUM G.W.F HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPAERT WRITER'S WE ARE THE BEST AMONG THE REST   AKWAI LOKACI   PAGE 26 to 30   Laila ta tayi taga ba Hakeem Sai ta tashi tashiga tayi wanka tana fitowa idonta yakai kan takardar da ya ajiye mata Tadauka ta duba taga cheque ne na kudi """"" Nan da tawashe baki tace kai tun yanzu bata gama rufe baki ba taga wani guntun takarda . Tadauka taduba Cewa yayi Nina wuce ga kudi nan Idan kina bukatar wani Abu zaki iya samun mummy Laila na gama karantawa ta wurgi da takardar tace kutuman uba Ashe tafiya yayi yabarni anan , Nida nake ta burin tafiya Saudi Ashe ma badani zaitafiba """ Tadauki wayarta takira hajiya rukayya Tanadawa Laila tafashe da kuka Hajiya rukayya tace Lafiya kike kuka Laila cikin kukan Laila tace mama kinsan Abdul Hakeem yakoma Saudi yau """ Maman tace yakoma fa kika ce Lalle ma yaron nan wato badake zai wuce ba kenan """" Laila tace ai niban Masan yatafi ba rubuta min yayi amma yabarmin dubu dari biyar yace kuma idan ina bukatar wani Abu na sami mummynshi , Hajiya rukayya tace aikuwa sun ja wa Kansu Nan da jibi kice kina bukatar kudi Kinga sai musamu mufara shiri kafin yadawo , Laila tace to mama wallahi amma naji haushin rashin tafiya dani din nan dayayi , Hajiya rukayya tace kwantar da hankalinki zai dawo ne ai zai shigo hanunmu daga shi har iyayensa . Yanzu zanzo gidan naki nakarbi kudin na ajiye su a wajena ai gwamma ma da yatafi abinsa kinga matara kafin yashigo hanu mu kawar dashi banza"''''' ****** Bayan kwana biyu Laila taje gidansu daga nan itada mahaifiyarta suka wuce gidan hajiya suwaiba wato kakan Laila kenan , Suna isa hajiya suwaiba takira hajiya larai kishiyar suka shige can dakin hajiya suwaiba Laila ta kwantar da kanta akan cinyar kakarta Nan hajiya rukayya tafada musu komai abin da Hakeem ya ma Laila Hajiya suwaiba tashafa kan rukayya tace hakuri kinji jikalle zai shigo hanun mu ne kinji ko , Dazaran yashigo hanun mu sai yadda kikayi dashi kinji ko Cikin jin dadi Laila tace Allah yasa haka kakalle na Dakuwa kinga gata Dan sai na canja maki gida kekadai basai da wannan tsohon ba Hajiya rukayya tace a lalle ma uban nawa ko Hajiya larai tace Dana dashi aka ware Hajiya suwaiba tace a dinta ji anwarekun Nan dai suka ta kulla tsiya Sai can wajen karfe goma na dare kafin Laila ta tashi tayi hanyar gida Dan dama ita tasaba da driving din dare , tana shiga maigadi yabude mata gate din yana gaisheta ko ta amsa mai . Tana parking sai daddyn Hakeem yafito yace Laila daga ina a wannan Daren haka Laila tace daddy daga gidansu alhaji nake a can na wuni . Daddy yagane wani alhaji take nufi wato alhajinsa, Yace kin tabbata tace a daddy kakira ma katambaya Yace a a shikenan karkisake kai dare a waje haka kinji ko tace naji Daddy Yace maza wuce dakin kin dare yayi Namishi saida safe Tana shiga falonta tayi wurgi da gyalenta tace nifa bana son sa ido haka kawai mutum yafita amma ana gadinsa   ***** Bayan wata biyu Laila ce kwace cikin lallausar kujerun falon Hakeem tana kallo Sai tafara jin tashin zuciya Ta tashi tayi hanyar bathroom tafara amai sosai take amai kaman zata fitar da kayan cikin ta Kanwarta suby wacce taci sunan hajiya suwaiba ce tazo Tana ta sallama amma shiru Dan tunda Hakeem ya tafi suby tadawo gidan gurin yarta , Itama dai duk halin nasu dayane da yaruwarta Taje siyo wa Laila balangune a bakin titi Taduba bedroom din Laila bata ganta ba tace anty Laila da karfi Can ta duba bathroom din falon Hakeem aikuwa nan taganta tayi sharaf , aikuwa suby ta rude ganin yar uwar tata a kasa jiki ba karfi tadauki waya takira uwarsu hajiya rukayya tafada mata tace gatanan zuwa Can dai taga karfa Laila ta mutu Dan haka sai ta Tashi tayi hanyar part din mom din Hakeem Mummy hafsat tana kitchen Dan daura abincin rana sai taga suby kaman anjifota Tace lafiya kuwa suwaiba zakishigo ba sallama Suwaiba tace kiyi hakuri mummy anty laila ce balafiya , Mummy hafsat tace meyasameta tace wallahi bansaniba nima naje aika kafin nadawo nasameta a haka Mummyn Hakeem tace wace muje naganta Wannan shine farkon shigowar mummy hafsat part din Dan nata Kusan atare suka iso da Maman su Lalai hajiya rukayya Mummy hafsat tace a a yaya ashekema kinzo Hajiya rukayya tace a gani nan ai Mummy hafsat tace bara na dauko mota akaita asibiti ko Hajiya rukayya tace duk yadda kikayi Mummy hafsat tace afito da ita mutafi ko Hajiya rukayya ta kalli mummy hafsat wato ita bazata kamata afita da ita ba sai dai tabasu command Hajiya rukayya da suby suka kama Laila zuwa mota Mummy hafsat ita taja motar zuwa hospital Bayan gwaje gwajen da aka wa Laila likita yagano tana da cikin wata biyu aikuwa hajiya rukayya da suby dama ita kanta Lailar murna suka hauyi sosai ko kunyar mummy hafsat basaji Itadai mummy hafsat tunda doctor yace Laila cikine da ita Bata ce komai ba tausayi kawai danta yabata hada zuria da irin hajiya suwaiba Nan dai tana ta tunanin zuci Hajiya rukayya tace hafsat bakice komai ba zamuyi jika mummy hafsat tayi murmushi kawai tace Allah yaraba lafiya Yanzu dai bari na sami doctor nabiya komai sai muzo muwuce gida Hajiya rukayya tace ai inaganin zan wuce da ita gida kawai idan tasamu lafiya sai ta koma dakinta Mummy hafsat tace badamuwa hakan ma yayi zama Ku iya bari saita haihu sata dawo Hajiya rukayya maganar mummy hafsat yamata zafi sosai wato subasa ma bukatar zaman Lailar agidan kenan Hajiya rukayya tace tokuma idan mijinta yadawo fa Mummy hafsat tayi dariya tace ai daga har ta haihu son bazai sami damar zuwa ba Hajiya rukayya tace duk karatun ne zaisa yaki dawowa gida ai yanzu idan kika kirashi kikafada mishi zai iya samin lokaci yazo yaga matarahi kafin yakoma ko Mummy hafsat tace sai dai nabaku numbar nashi ita lailar saita kira tafada mishi Cike da jin haushi hajiya rukayya tace ai ashikenan takira tafada mishi da kanta Mummy hafsat tace dayafi dai bara na biya kudin nazo mutafi ko Hajiya rukayya tace a a kibarshi kawai driver na zaizo yanzu yamaida mu gida Mummy hafsat tace to Allah yabata lafiya ni na wuce Laila tayi saurin cewa mummy baki bani numbar abdulhakeem dinba Mummy tace OK kawa wayar taki na samiki Laila Tamika wa mummy hafsat wayar Nan tasamata numbar HAKEEM Laila tace thanks mom Mummy Hakeem tawuce abinta aikuwa tana fita hajiya rukayya tace zanyi maganinkine Muza ayi wa wulakanci duk abin mutaum dai Ciki dai sai an haife shi tsaf Ta kalli Laila tace kekuma harda wani godiya Dan anbaki numbar mijinki Suby tayi dariya tace kai mama kaman Bakisan halin anty Laila ba Tasan metakeyi fa Laila tayi dariya tace Haba mama anfada miki Dan Allah nayi godiyar caf Nan dai sukayi gidan hajiya suwaiba suka shaida mata abin farin aikuwa harda gud'a hajiya suwaiba tayi Dan murna tace kaman muzuba ruwa a kasa musha Dan dadi Hajiya rukayya tace kinga yanzu saimuyi addua ta haifi namiji Dan mukasa mutsare gidan aikuwa hajiya suwaiba tace ai namijin ne ma zata Haifa kuzuba ido kugani ai tunada wuri zamuje gurin malamin nan yabamu taimako Haka dai sukulla wannan su kulla wancan ***** Mummy hafsat bayan daddy ya dawo gida ta shaida mishi abin dake faruwa Daddyn Hakeem yace kai amma naji dadi Allah yaraba lafiya Kice son dina yagirma fa Harda da d'a Mummy dai bata ce komai ba Yace ai sai a tura musu kudin dazai ishesu kula da ita abin da kecikinta Mummy hafsat tayi murmushi tace hakane Nan daddy yakira yayarshi wato hajiya rukayya maman laila Tana ganin kiran daddyn Hakeem tasan sunwarke Dan tasan zai jikasu da kudi Nan da nan tadaga wayar daddyn Hakeem yafara gaisheta kafin yace yaji abin farinciki Allah yaraba lafiya Sannan kuma inason kuturo da account number dazanturo muku da abinda zatayi anfani dashi aikuwa farinciki Yakama hajiya rukayya tace yanzu kuwa zanturo angode fa Allah yakara arziki Tunda yake bai taba jinta tamishi godiya ba sai yau yace bakomai Mudai fatanmu dai Allah yarabasu lafiya Ameen hajiya rukayya tace takashe wayar nan da nan taba wa suby wayar tace ta tura wa daddyn Hakeem account number din Laila aikuwa suby bata Dade da turawaba sukaji alert din dubu Dari takwas cas aikuwa murna awajen su kaman me Hajiya rukayya tace wanna ma ai kadanne ne Dan nasan nan da wani lokaci zai kara mana Nan dai Laila ta dauki wayarta takira Hakeem sai da yayi ta ringing kafin yadauki Tare da sallama cikin kwarewa da harshen larabci Dan bazaka kadauka bahaushebane Can yace dawa nake magana please Cikin sauri Laila tace Laila ce Hakeem yace inajinki ya akayi Nan tafada mishi what's kina da ciki Laila tace a mummynka cema takaini asibiti Hakeem yaja numfashi yace Allah yasauke ki lafiya daga haka baikara cewa komai ba yakashe wayarsa Laila tabi wayar da kallo ta kalli mahaifiyarta tace mama kodai shima baya farinciki da cikin ne Suby tace kai bahaka bane kinsan halin ya Abdul yanzu hakama murna ne yasa yakashe wayar Hajiya rukayya tace komai dai menene shine dai uban d'a Da su so da karsu so duk uwa ubansu daya can ta matse musu ***** Hakeem bayan ya kashe wayar ya kalli Ahmad dake fire musu doya Dan basa cin abincin waje Yace man kasan meye kuwa Ahmad yace saika fada Hakeem yace wai Laila cikine da ita har na wata biyu Cike da farinciki Ahmad ya ajiye wukar yadaga hanu sama Yace Allah mungode maka Wai mune zamu baba Hakeem ya watsa mishi harara Yace dadina da kai Ahmad yarinta wallahi Ahmad yace nayarda yarinta nedan gaskiya kam yanzu fa ka girmeni tunda gashi kana shirin ajiye baby Hakeem yace please man muyi maganar arziki mana Nifa harga Allah banso samun da daga jikin lailaba amma tunda Allah yabani Allah ya albarkaci abinda za a Haifa Ahmad yace adduar kenan kawai Allah yashige mana gaba Nan Hakeem yace ameen   ******* Bayan wata bakwai Abubuwa da dama sunfaru Su hajiya dai an tatsi Daddy Dan abin kadan zasuce a turo kudi ** Yau laraba Laila ta tashi da nakuda Sukayi da ita hospital Nan da nan aka shiga da ita labour room Mummy hafsat itama ana fada mata tazo asibitin daddy ne yasauketa kafin yawuce office bayan kaman awa hudu da shigarta Ta haifo yarinyarta maikama da ita sak Aka gyarasu itada babyn kafin akazo sanardasu mummy ana ce ta haihu sukayi cikin dakin dasauri banda mummy hafsat Tace wa likitar me akasamu likita taçe mace Mummy Hafsat tace Allah yaraya Takira daddy tafada mishi Yace gashinan zuwa Su hajiya kuwa ganin Allah baicika musu burinsuba yasa sukacika tam kaman zasu fashe amma ganin yadda daddy yake farinciki da samunjika yasa suka kwantar da hankalinsu kadan Nan daddy yakira Hakeem yafada mishi Hakeem yace Allah yaraya Daddy yace Ameen Ameen Yakamata kasamu lokaci kazo kaga yarinyar da ita Lailar ko Hakeem yace ai daddy bayanzu Dan karatu yafara zafi sosai sai dai mumsami time zanshigo Daddy yace Allah yamuku albarka inashi Ahmad din Hakeem yace yashiga wanka Nan sukayi sallama da daddy Ranar suna yarinya taci sunan maman daddy wato amina Mahaifiyar daddyn Hakeem kenan marigayiya Alhaji shuaib yasaka sunan da kanshi ba ma daddynba Haka Laila tacigaba da rainon yarta Amina   *********"******** Tofa Yanzu akafara kubiyo ummu afan Your comment is needed fans   [30/04, 5:51 PM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM   HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN DEDICATE THIS PAGE TO MY ONE AND ONLY HUSBAND ABU AFAN (DOCTOR SULAIMAN)❤   GORGEOUS WRITERS FORUM G.W.F HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERT WE ARE THE BEST AMONG THE REST   AkWAI LOKACI   PAGE 31 to 35   Laila kwance take tana danna wayarta Yayinda hajiya rukayya takeba wa Amina cerelack Hajiya rukayya tace kinga wasa wasa fa watan meenat shadaya amma amma haryanzu mahaifinta baizoba Suby tace wai Ku meye kuka damu sai yadawo ne bakusan idan yadawo Baku basamun abinda kuke samu yanzu ba """"" Laila tace nimadai haka nagani Nifa wallahi tunda acikamin jaka da abinda nakeso yashekara goma ma baizoba ba abinda yadameni Hajiya rukayya tace duk kurinta ne yake damunku inba yarinta ba ai wallahi idan yashigo hanu zamufi yadda muke yanzu Dan sai abinda tace zaibata komai ta tambaya zaiyi jiki na bari amma hakan bazaiyu ba sai Yaci abinci da maganin har na wajen wata daya inji malam To ta yaya hakan zaifaru idan bata jawo shi jikinta ba Laila tace kuma fa hakane mama yanzu manene shawararki mama Hajiya rukayya tace yauwa anzo gun danakeson azo Kinga yanzu abinda zakiyi ke Laila kisamu Daddyn Hakeem kice kizakibi mijinki can saudin Nasan shi da hangen nesa bazaiso shiga hakkin waniba Idan kikaje can duk wani Abu na biyayyya ki kirkiro kiringa mishi inda zamusamu yasaki jiki dake sosai inda har zaki bashi abinci kuma yaci Laila tace to mama yanzu dai zanshirya na tafi gidan mummy hafsat Zanfada wa daddy komai Hajiya rukayya tace yauwa yar gari tashi maza kishirya kiyi kama hanya Suby tace anty Laila zanrakaki Lailatace shirya muje Hajiya rukayya tace kuje kawai kubar min yarinyar Laila tace dama bazamu jeda itaba   **** Laila sukayi sallama a falon mummyn hafsat tana zaune tace a a Laila kune atafe Laila tace a mummy Allah yasa daddy na nan Munzo gurinshi ne Mummy hafsat idan da sabo tasaba da zuwa Neman daddy agunsu Laila Mummy tace yanan yanzu zaishigo ya fita sallah ne Nan su Laila suka zauna zaman jiran daddy aikuwa daddy shigowa suka gaisa Yace Lafiya kuwa Laila kokuna bukatar wani abunne Laila tafada mashi damuwarta nason bin mijinta Daddy yace wannan ba wani abinda damuwa bane Kishirya kawai kije kiyi passport agama komai kafin jibi sai kitafi Laila tace To daddy Allah yakara girma yace Ameen Ina amaryar tawa Suby tace tana wajen hajiya Yace to ace angonta na gaisheta Nan suka wa mummy sallama suka fita Daddy ya kalli mummy yace Lafiya kuwa mummyn Hakeem Mummy tace wallahi alhaji mutanen kotata ban yarda dasuba Mezaisa tabishi har can yabari mana ai komai daran dadewa zadawo yanzu haka uwartace ta kitsa mata komai Daddy yayi murmushi yace insha Allah ba abinda zaisamu Hakeem Kokin manta Dan naki Ma abocin riko da addini ne Dakuma yawaita adduoin tsarin jiki Mummy tayi murmushi tace hakane daddyn Hakeem Gaskiya Hakeem kam akwai addua Sai dai muce Allah yadada tsare mana shi Daddy yace Ameen Washagari daddy yagama wa Laila komai nashirin tafiya Wanda jibi jirginsu zaitashi Zuwa Saudi Hajiya rukayya da hajiya suwaiba ne suka sata gaba kan yadda zata yi anfani da magun gunan dasuka karbo daga gurin malam Komai Laila ta haddace Dan hartafara hango kanta cikin daula   Washagari jirginsu Laila yadaga zuwa Saudi Inda tabar meenat 'yarta agurin mahaifiyarta hajiya rukayya Daddy yadauki waya yakira Abdul Hakeem cikin ladabi Abdul yagaida mahaifin nasa Daddy yace kashirya kaje airport kadauki matarka Tana hanya Cikin mamaki Abdul Hakeem yace Laila kuma daddy Meyasa zata biyoni har nan Gaskiya takoma gida kawai Daddy Daddy yace Haba Dan albarka aure fa ba abin wasa bane Na kusan shekara bakanan Ta nemi data zo tagan ka ai baza a hanata bako Hakeem yace amma daddy Daddy yace karkace komai ka je airport kadauketa kawai kaji ko Yace naji daddy Allah yakara Lafiya daddy yace Ameen Allah yamuku albarka Hakeem yace ameen daddy Suna gama waya da daddy yace ya Allah Ahmad yace Lafiya kuwa Man naganka haka Hakeem yasauke ajiyar zuciya yafada wa Ahmad komai Ahmad yayi murmushi yace kace nakoma dayan part tunda amarya zata zo Hakeem dai baice komai ba Yazauna akan kujera Karfe hudu dai dai yaje yadauko Laila Tana ta rawar kai shikuwa Hakeem tunda tagaisheshi ya amsa bakaracewa komai Wannan shine mafarin zaman Laila a saudiya Dan bata koma ba ******* Bayan shekara goma shabiyar PROFESSOR ABDUL HAKEEM ABUBAKAR Dan shekara talatindashida aduniya Cikakken saurayine Wanda ya amsa sunan THE YOUNG PROFESSOR ko ina haka akeranshi gida da wajen kasan nan Yayi suna sosai aduniya saboda kudi da kuma ilimin da Allah yabashi Har yanzu yanazama a sauddiya ne a inda yake koyarwa a jamiar Saudi Arabian Dashi da babban abokinshi professor Ahmad Wanda a yanzu suke shirye shirye komawa kasarsu Nigeria Laila anzama manyan mata koda wasa bazaka kaga Hakeem kace shine mijinta ba Ba alamun dacewa a tsakaninsu HAKEEM bashida rowa koka kadan kudi masu sunan kudi yana cika Laila dasu Dan yanzu taza business wuman sosai suke kasuwanci da kanwarta Suby Idan ta saro kaya a Saudi sai ta tura wa Suby Nigeria Su duk aganin su Hakeem magani ne yake aiki akansa Wanda abin bahaka bane dai niyya kawai yayi yake mata abinda yake mata Amina kuwa agurin hajiya rukayya take sun shaku sosai Dan yarinya dai tayi mugun gado Shiyasa basa shiri da kakarta mummyn Hakeem Dan tana mata wa azin tabi a hankali kartayi mugun gado Yanzu haka ma basa Kaduna suna can kano nan hajiya rukayya takoma Dan mijinta yayi ritaya sai ya koma garinshi kano Shiyasa hajiya rukayya tadauki jikarta meenat suka koma can Yanzu meenat ta Dade a kano Tana zuwa Hutu Saudi gurin iyayenta Wannan kenan KANO Malam sualaiman yana zaune a wata unguwar talakwa ne dake nan kano Yana da mata daya da rana biyu Yaya shamsu shine babba zaikai shekara 36 aduniya alokacin da umma ta haifi yaya shamsu sai da yashekara ashirin cas Kafin tasamu cikin asmaullahil husna Wato asmau kenan Inda akecemata husnah Husnah ta taso cikin gata da tattalin uwa Dana uba da kuma Dan uwa rabinjiki wato yaya shamsu Tunda aka haifi husnah shamsu ne me dawainiya da ita kasancewar yadade baisamu kani ko kanwa ba A yanzu haka husna tasamu scholarship a wani makarantar masu kudi a inda take s s two a halin yanzu Husna tana da hankali da nutsuwa ga kuma uwa uba kyau da needed da Allah ya horemata Husna yar kimanin shekara shabiyar aduniya Sun hadu da Amina Abdul Hakeem abubakar A school lokacin da husna ta samu scholarship tashigo itama Amina alokacin tashigo makarantar Amina taso husna Dan Abu guda biyu ne na farko iliminta farinjininta da kuma kyau Dakyar husnah ta amince wa Amina suka zama kawaye sosai duk inda kaji ance husnah to za ace amina Muje zuwa anfra fa Fan's kubiyo ummu AFAN Kawai Your comments is needed [30/04, 5:53 PM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN GORGEOUS WRITERS FORUM G.WF. HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERT WRITERS WE ARE THE BEST AMONG THE REST DEDICATED THIS PAGE TO MY ENTIRE FAMILIES   AKWAI LOKACI   PAGE 36 to 40   HUSNA nata saurine saboda tayi latti yau Monday yau ne za a Nada zabin prefect a school dinsu Ummu tace husnah naga kina ta sauri yau Lafiya kuwa Husnah tayi murmushi har dimple dinta suka lotsa tace wallahi ummu yau za a nad'a sabbin prefect a school ne shiyasa mukeson muje muga wadda za a ba Yaya shamsu yace kokuma kije a nad'a kuba Husnah tace aini bandani yaya Dan an min Interview ma naki bada amsa a hall din Duk Dan kar abani damuwar nan Yaya shamsu yace ai duk yadda kikayi sunsani tunda sunsan dalibarsu Kokinyi shiru sunsan bawai baki sani bane Tunda dama sunsan bakyaso Bakince min saki dole akayi kiyi interview din ba Husnah tace wallahi wani malaminmu ne copper yace lalle sai nayi interview Kuma duk abinda suka tambayeni Nace I don't no Komai I don't no kawai Yaya shamsu yayi dariya yace kedai jekidawo kiban labarin wadda akazaba Husnah tace to shikenan yaya Tajuya ta kalli ummanta tace ummu sai na dawo Ummu tace Allah yadawo dake Lafiya tace ameen umma na Har takai bakin kofa yaya shamsu yace husnah kiyi hakuri kinji bakudi ajikina yanzu nakeson zuwa nayi buga buga naga abinda za a samo acigidan amma namiki alkawari idan nafita nasamu wani abin zana biyo har school dinku Inbaki Abu mai dadi Husnah tayi murmushi tace karka damu yaya na wallahi bani da damuwar komai Dan bancika son cin komai a school ba ma ai kana kokari yayana Allah yakawo maka aiki maitsoka nasan zamu huta sosai Yace ameen yar kanwata jeki karkiyi latti Tafita abinta tana murmushi Umma ta sauke ajiyar zuciya tace wa yaya shamsu Kasan wani Abu kuwa shamsu deen yaya shamsu yace a a umma saikin fada Tace wato akullum na kalleku kaida kanwar ka ina wa Allah godiya daya mallakamin 'ya'ya nagari Dan ba abinda zance wa Allah sai godiya kawai amma duk inda ake neman 'ya'ya nagari nasamu Abba dayake shirin fitowa daga dakinsa yace munsamu dai zakice zainaba Tunda Allah yasa shamsu yakawo kwari fa shiyake dawainiyya damu agidan Shine komai na kanwarsa shine namu aiba abinda zamuce sai muce shima Allah yabashi mai mishi Umma tace Ameen malam Malam sulaima yace babban damuwata shine inga kasamu aiki kayi aure Dan shine cikar mutuncin mutum Umma tace hakane ai baki yayi tunda yana da wacce yakeso khadija yarinyar kirki taki kowa saishi take jira Ko a yanzu aka tura za ayi komai tunda iyayen ma sun komai Malam sule yaja numfashi yace hakane kam to Allah yabamu yadda zamuyi Ya kalli shamsu da tunda suka fara zancen auranshi yashiga duniyar tunani Dan yana matukar son budurwarshi khadijat wacce akekira da kubra kitama tana son yaya shamsu sosai Dan Shekarar ta daya kenan dagama secondary school Manema sunzo Neman aurenta taki ita sai shamsu Haka iyayen suka hakura suke zaman jiran shamsu yakawo sadaki a daura aure   Malam sule yakalli shamsu yace karka damu akwai Allah Shamsu yace barinje Abba sai na dawo ya ma umma ma sallama ya wuce zuwa Neman abinda zasuci YAYA SHAMSU daga secondary bai kara gaba ba saboda rashin kudi daya musu katutu shida mahaifansa Dan haka kawai ya hakura yake Dan buga bugansa dahaka kuma har Allah yasa aka haifi kanwarsa husna saiya yaci burin Husna zatayi karatu tunda shi Allah baisa zaiyi mezurfiba Sai kuma gashi Allah yafara cikawa shamsu burinsa inda husnah taci scholarship ** Husnah tana isa school tasamu anfara assembly Ta tsaya daga bayan 'yan mate dinsu suna sauraron jawabi daga bakin principal dinsu   Can sai vice principal yace yace zamufara kiran new prefect dinmu daya bayan daya Principal tace a fara da head girl ko Sai copper bash yace am sorry ma Gwamma afara da sauran kafin head girl Zaifi Jan ra ayin su Principal tace OK afara kira kawai Nan akafara kiransu ana samusu hula da kuma belt Dansu prefect din hula suke sawa green gabadayansu na head girl ce kawai ya banbanta Dan nata read cap take sawa Can taji ance social prefect AMINA HAKEEM ABUBBAKAR   Nan aka dau tafi raf raf raf ana murna Can sai vice principal yayi gyaran murya yace yanzu zamu Kira me gayya me aiki wato our head girl Nan aka kira sunan ASMAU SULAIMAN SHAMSU cikin gigicewa Husnah tadago kanta aikuwa tana dogowa sukayi ido hudu da Copper bashir Ya kashe mata ido daya Cikin tashin hankali Husnah ta daga kafa dakyar tana zuwa ta hau kan stage Principal ta rungume Husnah tare da Da samata hulan head girl dinta read cap Ta daura mata belt dinta read shima aikuwa daga students har malaman dake wajen aka dautafi Dan sunburge kowa ga read cap din yawa Husnah kyau sosai kaman Dan ita akayi hulan Nan dai aka rantsar dasu Husnah a matsayin new prefect *** Copper Bash ya tsare Husnah alokacin dazata wuce gida itada meenat Copper bash yace asmau Ya naga kina ta shan kamshi ne Yau Meenat tafashe da dariya Tace uncle ai Husnah fa batasan za abata prefect ba ballantana Head girl Copper bash yayi murmushi yace ai kuwa ta yaudari kanta To inba a bata ba waza aba wa Meenat tace aifa dai kam Husnah dai tana jin su batace komaiba Nan driver din meenat yazo daukarta Husnah kuma dama da kafa take zuwa take komawa Meenat tace Dan Allah Husnah kizo musaukeki a gidan kinga sai naga gidanku ko Husnah tayi murmushi dimple dinta suka lotsa Copper bash ya tsaya kawai yana kallon Husnah komai nata cikin aji takeyinsa da nutsuwa shiyasa takeda farinjini a school din Husnah tace wallahi meenat idan ya shamsu ya ganni a mota zai min fada sosai . Meenat tace kedai kawai bakyason kibimu sai kiyi tayiwa yaya shamsu sharri Copper bash yace kinga kuyi sauri kutafi gida kar anemeku kuntsaya surutu Meenat tace to shikenan sai mun hadu goben idan munzo ko Husnah tace to meenat Allah yakaimu kigaida gidan Nan sukayi sallama Copper bash yace wa Husnah muje nakaiki gida da kaina Tunda kinki kawarki takaiki Husnah tace Dan Allah uncle kayi hakuri wallahi yayana yaganni da kai zaimin fada Copper bash yace mezaisa yamiki fada baki kai a rakakin bane ko yaya Husnah tayi shiru tace kayi hakuri Dan Allah Yace wato har yanzu Husnah kinkasa yarda da sonda nake miki ko Kibani dama nasan gidanku da iyayenki wallahi dagaske nake auranki zanyi Asmau Husnah tace Dan Allah malam kayi hakuri kar yaya yasan da wannan maganar Dan ya hanani kula koda kawace ballantana Maganar soyayya tun yanzu Da kyar yabani dama kawance da Àmina Hakeem ma   Copper bash yace OK na fahinceki Ba wai nidinne bakyaso ba umarnin yayanki kikebi ko Husnah ta rufe ido tana murmushi tayi hanyar fita daga gate din school din Copper bash yayi murmushi tunda ya gano yafara shiga zuciyar Husnah Zaisan hanyar da zaibi Dan yasan iyayenta da yayanta shamsu   Bashir Dan wani hamshakin maikudi ne sosai acikin garin kano Bautar kasa wato NYSC yakaishi school dinsu Husnah Tunda yadora idonshi kan Husna yaji yakamu da son ta amma takibashi daman hakan   Next page [05/05, 11:05 AM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION F.C.T.W.A   HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITERS OF THE NATION   DEDICATE THIS PAGE TO UMMY KINA KOKARI WAJEN GANIN NOVELS DINA SUNA KARBUWA A KOWANI GROUP ALLAH YABAR KAUNA   AKWAI LOKACI   PAGE 41 to 45   ABDUL HAKEEM THE YOUNG PROFESSOR kwannansu biyu da dawowa daga saudiya dashi da madam laila HAKEEM yana shirin zuwa sashen iyayensa ne don yagaishesu Yafito daga wanka ne yashirya cikin wani farisol din jallabiya ya faffesa turarruka masu kamshi Dan akwaishi da son kamshi sosai Har yagama shiransa zaifita Laila bata tashiba Ya kalleta kawai ya girgiza kai yayi gaba abinsa zuwa part din su mummynshi Yanashiga yasamesu akan dining da mummy da daddy Daddy yace Dan halal kaki anbato yanzu nace baka shigo break fast ba mummyn ka tace ai tasan kana hanya HAKEEM yayi murmushi cike da kaunar iyayensa Yace ai mummy tafadi gaskiya Dan bazan taba karyawa a wani waje ba matukar muna tare da mummy Mummy tace yauwa son fada mishi dai Nan mummy tayi serving din HAKEEM abinci yafara ci Bayan sungama break fast ne mummy zata kwashe kwanukan Hakeem yace haba daliba yazakimin haka kuma Kezaki kwashe kayan zuwa kitchen nikuma meye anfani na Mummy hafsat tace nabari tashi ka kawashe Daddy dai dariya yake musu yakoma kujerar falo yazauna Hakeem bayan yagama kwashe kwanukan zuwa kitchen saiya dawo falo Dan hira da iyayen nasa Daddy yace wai acikin makarantu biyu dasuke bukatarka wanne kazaba kayi lecturing din agun HAKEEM yayi murmushi yace ai daddy daga ni har Ahmad munzabi muje BUK kano Daddy yace Allah yasa haka shine alkairi Mummy hafsat tace amin Daddy yace kace kuna tare da amaryata kenan Mummy hafsat tayi murmushi tace MEENAT ko rigima Yakama ta ma suturota tazo tagaida iyayenta ai Daddy yace karkice komai tunda basuyi hakan ba shi saiyaje yaganta Kafin Hakeem yayi magana wayar daddy yadau kara Daddy yadaga sai sukaga daddy yace subuhanallla a wani asubiti Mummy da Hakeem suka maida kallonsu kan daddy Bayan daddy yakashe wayar ne suka tambayeshi abinda kefaruwa Yace Abba na aka kai hospital HAkeem yace subuhanalla muje kawai daddy Mummy hafsat tace nima bazaku barniba muje tare Suka he asibitin Hakeem ne me driving dinsu Suna isa suka sami alhaji shuaib bayadda yakara ji Dan yanajin jiki sosai Alhaji shuaib yarike hanun Dan nashi wato daddy Yace Allah yamaka albarka abubakar da kai da zuriarka Ba abin da zance dakai sai Allah yàmaka sakayya da gidan aljanna duk inda akeneman yaro nagari ka kai abubakar Ya kamo hanun Hakeem yace jikallena ga mahaifinka nan nabar maka amanarshi duniya da lahira Kabishi kamar yadda yabini Ya kalli mummy hafsat yace kema Hafsatu Allah shizai biyaki akan yadda kika nuna kaunarki ga abubakar Duk yadda aka kai cutar dashi kinki bada damar hakan Allah yamiki albarka Tunda alhaji shuaib yafara magana suke kuka musamman daddyn Hakeem Da mummy ABDUL HAKEEM ne kawai ya daure amma shima idonshi yayi ja sosai Can dai likitoci sukace sufita zasu samishi Oxygen Dan numfashinsa yafara kasa Alhaji abubakar ne kawai akabari a dakin Can wajen La asar 'yan kano suka iso asibitin Kuma harda meenat Hajiya rukayya itama a rikice tazo jincewa jikin mahaifin nasu ya tashi amma anhanata shiga taganshi Hakan kuma ya bata mata rai sosai Amina kuwa tana ganin daddynta Hakeem tare da mummynshi takarasa wajensu cike da murnar ganin uban nata Bayan tagaida Hakeem ne take tambayarsa dad ina mummyna yace tana gida yanzu zata zo itama Amina ta kalli mummy hafsat tace wato ma bazaki kimin magana ba ko Mummy hafsat tace kaga jaira kinga babanki bakima San ina wajenba zaki ce ban miki maganaba Sannu uwata mummy hafsat takarasa maganar tana tsokanarta Amina tace ai wallahi duk abin kidai saina auri mijinki sai naga yadda zakiyi Mummy hafsat tayi murmushi tace kishigo mana kigani da tabarya zan koraki ai nan mummy Hafsat tana jikinta ajiki sukata Dan hirarsu amma cikin jimamin rashin lafiyar alhaji shuaib Ahmad yakaraso hospital din shima cikin jimami Hakeem na ganin Ahmad yace Man ka karaso kenan Ahmad yace ai kana kirana nace wa mummy zanzo hospital namata bayani Itama zasu zo tanason gama abincine sai ta taho dashi Hakeem yace Allah yakawota Lafiya Ahmad yace barinje na gaida su mummy suka karasa harwajensu mummy Yagaishesu yamusu ya maijiki Amina tace daddy Ahmad ina wuni yace Lafiya qalau daughter ya mummyn ki Tace banganta ba mu yanzu mukazo daga kano Kafin Ahmad yayi magana daddyn Hakeem yafito daga dakin yana goge hawaye Hakeem da Ahmad suka karasa dasauri Hakeem yace daddy yajikin alhajin Daddy abubakar yace Hakeem Allah ya yi wa mahaifina rusuwa Alhaji yatafi yabarni Hakeem Yanzu bani dakowa dama bansan mahaifiyata ba shikadaine min aduniya Shima yatafi Duk matan dake gun sukasa kuka ****** Bayan arbain din alhaji shuaib ABDUL HAKEEM da aminin sa suka fara lecturing B U K Dan karakaran gidaje makaranta tabasu a matsayinsu na professional akan aikin su Yanzu Haka suna shirye shiryen auran Ahmad kuma a kano zaitare da matarsa Itakuma Laila tayi tayi yabarta tadawo kano yaki Sai dai yazo masu Hutu yakoma Yanzu haka bikin Ahmad saura sati biyu cas a daura auren Ahmad   ***** Yaya shamsu zaune akan kujera yar tsugune umma kuma na hada zobo Dan duku gidan suna azumin Monday da alhamis Itakuma Husnah tana kan hada musu abincin buda baki a kitchen Kanin kubra budurwar yaya shamsu ne yayi sallma yashigo ya tire Ya gaisheda umma kafin ya ajiye abincin yace yaya shamsu gashi anty kubra Kafin shamsu yayi magana umma Tadauko naira hamsin tace zoka karba ko kace mata angode Allah yasaka da alkairi Yaron yaki karbar kudin umma yaya shamsu yace haba kanina karba mana ai ba roka kayiba Yakarba yayi godiya zaifita kenan Husnah ta tace sani kace wa anty kubra gobe zanzo kitso Sani kanin kubra yace to zanfada mata Umma tace kajita kaman wani kitson takeso Yanzu zatace maka zata kitso taje tadawo da kalba Husnah tayi murmushi tace umma wallahi banason kitso nafison dai amin kalban kawai Tagama kwashe komai ta ajiye musu akan taburma Jelouf din taliya ta musu Wanda ya shamsu yakawo dazu yace a dafa yasan tana son taliya sosai Umma tace wallahi yarinyar nan kubra akwai kokari Bata gajiya da aiko maka da abinci duk Monday da alhamis Husnah tace gaskiya kam wallahi anty kubra Nada kirki Yaya shamsu Allah yabaka kudi wannan sallar dai kasamu kamata kayan sallah Umma tace amin gaskiya kam ta cancan hakan Shamsu yaja numfashi yace kuma wallahi umma kubra bata jin dadin gidansu Indai ba abbanta yana gidaba Kishiyar mamanta tana matsa mata sosai Yanzu fa wai akwai Wanda yamata magana yanson kubra shine tadage sai kubra ta amince da auran wani baniba Dan taki amincewa shine take bata wahala Kuma abbanta yace bazai mata auren doleba Sai Wanda takeso zaibata Shine tayi bakin jini agidan Umma tace Allah sarki marainiyar Allah Allah yabaka abinda zaka auro yarinyar nan karabata da gidan nan Shamsu yace amin umma Husnah ma tace amin Yaya shamsu yace barinje sallar magriba indawo muyi buda baki   Shamsu yana fita Husnah tace wallahi ummu yaya shamsu yana bani tausayi Dan wallahi shima yana son kubra sosai Umma tace bakomai AKWA LOKACI watarana sai labari Husnah tace Allah yanuna mana lokacin amin ummu tace Suma tashi sukayi Dan gabatar da sallah   ** Bayan kwana biyu wani abokin shamsu yabashi Shawarar mezaihana yakai takardunsa Neman aiki B U K koda masinja aka bashi zai rage zafi ai Shamsu yace gaskiya naji dadin shawarar nan daka bani kabiru Allah yabar zumunci Kabiru yace bakomai ai zaman taren kenan Kaga ni a secondary school nake masinja amma alhamdulilla ina samu Ya shamsu yace hakane yanzu zanyi wanka nakai kuwa Bayan ya shamsu yashirya zuwa kai application dinsa Saiya wa umma sallama Yakama hanya   Bayan yakai akace za anemeshi idan yasamu idan kuma baisamuba zaiji shiru Yabasu number dinsa Yatafi gida yana ta aduar samun nasara Idan Allah yasa yasamu aikin nan zaiyi kokarin raba kubra da gidansu tazo suyita maneji yasan kubra zatayi hakuri da abinda zaibata umma kuma bata da matsala zasu zauna Lafiya ***** Professor Abdul Hakeem zaune a office dinsa yana duba wasu takardu sai wata mata tashigo tagisheshi Tace wai itace sabuwar sakatariyarsa Abdul Hakeem yace OK zaki iya tafiya sai na nemeki Tafita Tana fita Hakeem yakira management din makarantar Suna ganin wayar office dinsa Aka je dasauri Dan yanakirane Manager nashiga yagaishe da professor Hakeem Hakeem yace ina buka tar a canza min secretary ma ana bayason mace Namiji yakeso akawo mishi Manager yace angama sir Hakeem yabashi izinin tafiya Sukaje suka zauna meeting Nan akayi shawarar daukar SHAMSUNDEEN SULAIMAN a matsayin secretary na THE YOUNG PROFESSOR ABDUL HAKEEM   Yaya shamsu yana kofar gidansu kubra yaje zance Sai yaga kira da bakuwar number Yayi picking call din aikuwa kubra taga yana ta fara a yana godiya Bayan ya kashe wayar ne Ya kalli kubra yace kiyimana murna munsami aiki kinga kenan burinmu yakusa cikako Cikin tsananin farinciki kubra tace alhamdulillahi Gobe zafara azumina kenan Da mamaki shamsu ya kalli kubra yace azumin mekuma zakiyi Kubra tayi murmushi tace aina wa Allah alkawarin cewa duk randa kasamu aiki sainayi azumi uku cas Shamsu yace aikuwa bazakiyi kekadaiba tare zamuyi Nan dai yamata sallama ya wuce gida Dan yasanar wa umma ** Umma tayi farinciki sosai haka ma mahaifinsa Husnah kuwa tsalle taringa yi tana murnar ankusa kawo musu anty kubra gidansu Mahaifinsa yace gobe zaka fara zuwa kenan Yaya shamsu yace a daga gobe sukace wai karfe takwas zandinga zuwa Sainaje ma zasubani dokokinsu Nan iyayen sukayi ta albarka Washagari yaya shamsu yashirya zuwa wajen aiki Bayan yayi sallama da su umma Ya wuce gidansu kubra itama tamishi adawo Lafiya   Yana isa aka gama komai aka turashi office din PROFESSOR HAKEEM yana zuwa yayi nocking akace yashiga Professor Hakeem yanakan kujerar shi yana fama da wasu takardu Shamsu yashiga yagaisheshi professor Hakeem ya amsa batare da kalleshiba Yace ta akayi malam Shamsu yace daman nine sabon secretary din da aka turo office dinka Professor Hakeem yace OK dafatan zamuyi da gaskiya malam Shamsu insha Allah sir Sai alokacin professor Hakeem yadago kai ya kalli ya shamsu Yace ko zan iya sanin sunan malamin Yaya shamsu yayi murmushi yace Shamsuddeen Hakeem yace malam shamsu Allah yatayaka riko za iya tafiya Shamsu yayi godiya yace nagode sir Ya wuce abinshi professor Hakeem yacigaba da aikinsa Can wajen shabiyu da rabi professor Ahmad yashigo office din Hakeem yace ya man muje muyi lunch kasanfa bana jure yunwa Hakeem yayi murmushi yace wai damma ka kusa shiga daga ciki Aisha Nada aiki wallahi sai dai ta ringa samaka wani flask   Ahmad yayi dariya yace ai dani dakai duk jirgi daya yakwàso mu Nan dai Hakeem ya tattara suka fito tare Hakeem yakalli shamsu dake kan kurarshi yace Abokina zamufita ga key din office din take care Shamsu OK adawo Lafiya   Suna zaune a gurin cin abinci Ahmad yace waini wannan Dan gayun ne sakatarenka Hakeem yace kaima kaji mamaki ko Da naso namishi tambayoyi sai naga rashin dacewar hakan gwamma nagama fahimtarshi kafin Naji tarihinsa Ahmad yace hakan ma yayi amma mutum very responsible person kaman wannan ace yana sakatare Shamsu yashiga office din maigidan nashi yaga kudi a kasa Ya dauka ya ajeye mishi a saman tebur   Bayan su Hakeem sundawo yashiga office din sa Sai ya kalli inda ya zubar da kudi yaga babusu Dan dama da gangan yayi hakan Dan ya gwada shamsu ne kawai Yazauna akan kujerarshi aikuwa idonshi yakai kan kudinshi da shamsu ya ajiye mashi su Professor Hakeem yayi murmushi akaro na farko Yaya shamsu yashiga ranshi Karfe hudu dai dai Hakeem yatashi a office dayafito yaga kujerar da shamsu yake yaga yana waya ne amma yanaganin fitowar Hakeem yawa kubra sallama Hakeem yayi murmushi yace hala kaida uwargida kuke wayar kuma ka kashe Yaya shamsu baice komai ba sai murmushi kawai Hakeem yace natashi kaima zaka iya tafiya Shamsu yace aisunce wai sai time din tashi yayi zantashi Hakeem yace no zan musu magana kaje kawai abinka Hakeem har yayi gaba ya dawo yace sunbaka kudi kuwa Ya shamsu yace wani kudi kuma nida nafara aiki yau sir yakarasa yana murmushi Hakeem yayi murmushi yace yakamata subaka kudin daukar aiki amma zanbaka aro idan anbaka sai ka dawo mundasu ko Ya shamsu yayi dariya kabarshi kawai sir kar azo basu baniba Hakeem yayi murmushi yace idan basu baka na barma Kuma banason musu yashiga tsakaninmu malam shamsu ka karba kawai karmuyi haka dakai Shamsu yakarba yace nagode yallabai Yace karka damu Sai gobe kayi kokari ka koma gida Shamsu yasake baki kawai yana kallon Hakeem Yaduba damin kudin da Hakeem yabashi Nan dai yayi wa Allah godiya cike da farinciki shamsu ya kulle kofar office din su Yayi gida Yana zuwa Husnah ta tareshi da murna oyoyo yaya na sannu da dawowa Shamsu yayi dariya yace yauwa yar kanwata ina umma Ummu ta fito daga daki tana daura dankwali tace a a dawuri haka Yaya shamsu yace wallahi Allah ne ya hadani da shugaba nagari yace karfe hudu ma ina iya tafiya Umma ta ce alhamdulilla ai haka akeso Yaya shamsu yace umma ina Abba tace yanzu zaishigo sunje gaisuwar Mara Lafiya shida malam tanko Kafin tarufe baki ma sai ga Abba yayi sallama yace a a Dan albarka har andawo Nan suka zauna kan ta Burma yafito da kudin ya ajiye gaban mahaifinsa Nan yamusu bayanin komai Abba yayi gyaran murya yace to yanzu idan akazo ba a baka kudin daukan aikin bafa Ya shamsu yace nima haka nagani dai Na nuna yabar kudinsa kawai yace aishi yabani Umma tace to kaidai duk inda kake ka tabbatar karike gaskiya kazauna da kowa zuciyarka daya Ya shamsu yace insha Allah Zankiyaye Nan dai Abba da umma sukace baza a taba kudinba harsai anbaka angani koba hakaba yaya shamsu yace hakan ma yayi gaskiya Husnah tace Abba kawai da yaya shamsu yayi anfani da kudin gurin kai sadakin anty kubra Koba a bashi tunda yana aiki saiya biyashi a hankali Abba yayi murmushi yace uwatakenan ke yarinyace har yanzu bakisan duniyaba Indai aure ne ai zaiyi insha Allah Suka ce Allah yasa Bayan kwana biyu ranar alhamis ya shamsu yaje wurin aiki aka kirashi akabashi kudin daukar aiki naira dubu goma shabiyar Da yadaqo gida yace wa ma haifinsa ambashi yanuna musu Abba yace alhamdulilla kaga gobe saika mayar mashi da kudinsa Allah yayi albarka ya shamsu yace ameen Abba Abba yace yakabar kudin kuma anan Ya shamsu yace Abba kayi abinda yadace kawai Abba yace wa umma tadebi kudin ta ajiye agunta   Washagari ya shamsu yasami professor Hakeem a office yamishi bayani yamayar mashi da kudinsa Hakeem shi har ya manta ma yaba wa ya shamsu kudi Ba karamin burgeshi ya shamsu yayi ba Yace Gashi kasiya wa yara sweet Ya shamsu yayi dariya yace ai banida aure Hakeem yakalleshi yace Malam shamsu idan bazaka damu zanso jin labarinka   Next page Your comments is needed Fan's [05/05, 11:08 AM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION F.C.T.W.A   HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITERS OF THE NATION   DEDICATE THIS PAGE TO UMMU HANIF   AKWAI LOKACI   PAGE 46 to 50   PROFESSOR HAKEEM yace ina sauraronka malam shamsu Ya shamsu yayi murmushi nan yabashi kadan daga cikin tarin rayauwarsu Hakeem yace kace kai din dai har yanzu dai gaurone murkusheshen gaurone Ya shamsu yayi murmushi yace a nakusa fita a layin gaurayen tunda nasamu abinyi Hakeem yace hakane Ya kalli kudin da ya shamsu ya ajiye mashi akan tebur Yadauko wani rafar ya hada mashi dasu yace Kadauki wannan kudin kaje kamuku cefane Sannan kuma ka Isar min da gaisuwata wajen Abba da umma Da kuma yar kanwarmu Ya shamsu yace amma ai kudin sunyu yawa yallabai Hakeem yayi murmushi yace karkadamu Malam shamsu kana da sha awar cigaba da karatu ne Shamsu yayi murmushi yace Zanyi kokari bayan aure na ga nasamu ko degree na samu insha Allah Hakeem yace Allah ya nuna mana ya shamsu yace nagode Allah yasaka da alkairi Hakeem yace godiyan yana yawa kuma.banason godiya malam shamsu Ya shamsu yayi murmushi yace ai ka canci hakan ne yallabai Nan dai suka Dan taba hira har lokacin tashin Hakeem yayi suka tafi shida Ahmad Ya shamsu kuwa yana fita yaje kasuwa yamusu cefane sosai har kaji da lemuka masu sanyi Yana isa kofar gidansu mai adai daita sahu ya tsaya yabiyashi yafito da ka yansa Yashiga cikin gidan da sallaman shi alokacin Husnah tana alolar La asar Tana ganinshi ta karasa wanke kafarta ta zo takarbeshi tana mishi sannu da zuwa Yace alolar mekikeyi tace LA asar ya shamsu yace haba Husnah yazaki bari lokacin sallah ya wuce kina da lafiyanki Kafin tayi magana umma daga kitchen tace ai yau Husnah bataji dadiba ne Tun da tadawo daga makaranta take kwance kanta naciwo Ya shamsu yace ashsha barin je nasiyo miki magani Yanzu zandawo Husnah ta rike rigar ya shamsu tace wallahi naji sauki yaya Dama abin da ya haddasa min ciwon kan ma Wani taro akayi a school dinmu kuma nice presenter Hayaniya ce yasani ciwon kan amma Dana dawo gida umma tabani magani nasha na kwanta yadaina Ya shamsu yace kinta tabbata Husnah tadaga kai alamun ta tabbatar Abba ne yayi sallama yashigo Da Leda a hannunsa Husnah ta ajiye Wanda ya shamsu yakawo akan taburma tayi saurin karbar na Abba alkamace Abba ya auno Dan Abba akwai son tuwon alkama dashida ya shamsu Bayan sun zauna ne ya shamsu yace Husnah dauko kayan can kiraba mana Husnah ta tashi ta dauko Plate guda uku da tasawa Abba kajin da kuma Irish potato wato dankalin turawa Ta ajiye mashi maltina Dan tasan zaifi sonshi Kafin tasawa umma itama maltina tamata Sai ta hada musu itada ya shamsu ta dauki lacasera Ta dauka wa ya shamsu fanta dantasan abinda kowa yakeso Umma ta ce yau fa shagwaban yatashi Abba yace a din tayi baruwanki ai sunfi kusa yakarasa maganar yana dariya Husnah tace yauwa Abba fada mata dai Ya shamsu yayi murmushi Dan yanason yadda suke rayuwarsu cikin son juna acikin gidansu Suna gamawa Husnah ta tashi tadauko Dan karamin kula tasaka naman da komai yadda sukasha sai wannan lemu sunkai uku Tasaka a Leda tace ya shamsu wannan na anty kubra ne idan kaje kace mata inji sweet kanwarta Umma tace kai wannan soyayya da Husnah takewa kubra Inba auren nan akayi ba hankalin Husnah bazai kwanta ba ba Abba yace ai soyayyar Dan uwantane yashafi khadijan Husnah tace gaskiya Abba kana da ganewa wallahi yadda anty kubra takeson ya shamsu yasa na ke ganin girmanta Shidai shamsu inbanda murmushi ba abinda yakeyi Nan yawa mahaifinsa da ummansa bayanin yadda sukayi da maigidansa Abba yace Allah yasa hakan shine mafi alkairi Kaga girman alkawariko To haka akeson mutum aduk inda yake ya rike gaskiya Ya shamsu yace hanekam Nan yabawa mahaifin nasa kudin gabadaya yace ya ajiye agunsa Ya tashi yashiga wanka Wanda Husnah ce takai mai yana fitowa yayi alwala zuwa sallar magriba Bayan ya dawo daga isha ne yadauki kayan da Husnah tabashi yakaiwa kubra Ya fesa turarensa mai Dan arha duk da talaucin su ya shamsu baya rabuwa da turare danshi mutum ne mai tsafta sosai Dan gado sukayi a wajen iyayensu Saikuma Husnah tace matsa kaban guri akan tsafta kokadan Husnah bata son datti Yana isa gidansu kubra ta fito da hijabinta dogo Duk yadda takai taboye abinda aka mata agida kubra takasa sai da yagane Yace Lafiya naga fuskarki haka kubra Kubra tayi yake tace bakomai wallahi abune yafada min a idona amma nacire Kafin ya shamsu yayi magana wata kanwarta wadda suke uba daya tazo tace wai kizo inji mama kicigaba mata da abinda tasaki Kubra tace kice inzuwa yarinyar tajuya takoma zuwa cikin gidan Tausayin kubra Yakama shamsu sosai yace kiyi hakuri kinji watarana sai labari nasan duk akaina kikaganin wulakanci Dan kin ki bada hadin kai amma namiki alkaqarin komai yazo karshe insha Allah Yace karbi wannan inji kanwarki tace nakawo miki Kubra tace Allah sarki Husnah Dan Allah kace mata nagode sosai Yaciro dubu uku a aljihunsa yace karbi wannan kirike a hanunki Kubra ta kalleshi ta kalli kudin tace haba sahibina ya daga samun aiki zaka fara barna da kudi kawai kabarshi Yace ai duk abinda zansamu kina da kaso aciki kikarba kawai kubra idan baki karba ba zaki bata min rai Cikin sanyin jiki kubra ta karbi kudin Tace nagode Allah yakara budi yace amin Maza koma gida kikarasa abinda aka saki karkiyi laifi ko Tace to sai anjima ko kuma saigobe ba inji ya shamsu   Washa gari dasafe ya shamsu yagama shirin zuwa aiki bayan sun karya Yafito yace wa Husnah muje ko Husnah tace to yaya suka wa umma sallama Suna futa kuwa suka yi sa ar keke napep yaya shamsu yatare musu sukashiga Suna tafiya suna hira yace inga jakanki tabashi bata kawo komai a ranta ba Ya shamsu kuwa yafaketa yasaka mata 1000 a ciki dubu daya kenan Suna zuwa dai dai gate din su Husnah ya shamsu yace wa driver tsaya ta sauka nikuma kayi dani BUK Husnah tasauka tana daga wa ya shamsu hanu Yayi dai dai dannowar motar copper bash Yaji lokacin datace ya shamsu kanan ya shamsu ne acikin keke napep din nan Inkuwa shine zanbisa namishi bayanin komai aikuwa copper bash yayi ta bin yaya shamsu abaya har yasauka a gate din BUK Bayan ya shamsu yabiya kudin yayi gaba abinsa Copper bash yayi parking yafito Yabi bayan ya shamsu Har yaje yayi signing yazo kafin yaje can kujerashi kofar PROFESSOR HAKEEM yazauna Copper bash yamishi sallama ya shamsu ya amsa yace kozan iya taimakonka Copper bash yace a daman taimakon nazo nema amma a gurinka ya shamsu Yadda copper bash yakirashi ya shamsu yasan duk yadda akayi yasanshi ne Ya shamsu yanuna mishi kujera Nan copperbash yafada wa yaya shamsu irin son da yake wa kanwar shi amma taki bashi dama hakan Ya shamsu yace bazata ta taba amince maka har sai nabata izini Umarni nabata nima kuma bazan taba amincewaba har sai nayi bincike akanka kafin nan kuma na tabbatar tana sonka na uku kuma zakamin alkawarin barin ta tayi karatu bayan kinyi aure amma wannan zaizone bayan nayi bincike nagar tarka Copper bash yace wallahi ya shamsu indai akan asali ne bana shakku aje ayi bincike fata na kawai idan kabincika bani da matsala ka amince min nakawo sadakina gidanku shikadai ne zaisa hankalina yakwanta Ya shamsu yayi murmushi yace karka damu Allah yashige mana gaba Nan yawa ya shamsu sallama yatafi   ******* HUSNAH zaune kan kujerar class dinsu teacher din dazata shiga musu ta haihu shiyasa suka samu Free time Meenat tace gaskiya Husnah baki da kirki yanzu kakan dad dina da mummy na ya mutu amma kikasa Neman gidan mu kije kiwa kakata ta aziyya Husnah tace afuwan aminyi insha Allah ranar asabar zanzo gidanku nawa kakanmu ta aziyya Meenat tace kai amma danaji wallahi har na matsu asabar tayi Hajiya ta taganki labarinki kawai takeji agurina Husnah tace aikuwa zanzo nagaisheta Tace amin Allah yasa daddy ma yazo sai kigaisheshi Kinsan tun yadawo kano aiki duk Saturday yake zuwa yaganni Husnah tace to Allah yakaimu ranar Suna haka wata junior tashigo tace anty husnah wai kizo inji uncle bash Husnah tace OK kice ganinan zuwa Meenat ta kebe baki tace wai meke tsakaninku da copper bash ne Husnah tace sirrine amma zakiji nan gaba tashi muje kirakani kawai Meenat ta tashi jiki a sanyaye tabi Husnah zuwa office din uncle bash Suna shiga suka gaishe da bash ya amsa idonsa akan Husnah Takaici Yakama meenat Dan ita ba namijin datakeso irin copper bash Tayi shishigin amma bata samu karbuwa ba Ya kalleta yace zaki iya jiranta a kofa magana zamuyi Meenat cike da bakin ciki ta fito Copper bash ya kalli Husnah yace munhadu da ya shamsu Cikin sauri husnah ta dago kanta da sauri tace meyace maka shikenan nasan yaya zaiyi fishi dani Copper bash yace karkidamu ba abinda zai miki shima naga alama yana da fahimta Nan yafada mata yadda sukayi da ya shamsu Cike da jin dadi Husnah ta tashi tayi hangar waje Yana kiranta amma taki juyowa saboda kunya Tana shiga sukacikaro da meenat Kuka shabe shabe a fuskar meenat Husnah cikin tashin hankali tace lafiya kuwa meenat cikin rashin sanin mezatace tafara in inna Tace wallahi bansan menayi wa copper bash ba ya tsani yaganni aguri sai yakoreni Husnah tace kiyi hakuri zanmishi magana kuma I sha Allah zaiyi dai dai Meenat ta share hawayenta tace Husnah na tambayeki meketsakaninku da shi baki fada min ba Husnah tayi murmushi tabata labarin komai Meenat tace yanzu kinaso kice min kun Dade kuna soyayya da shi Husnah tayi murmushi tace a Amma ni banbashi daman zuwa gidan mu ba Shine yanzu yake cemin ya wa yayana magana Meenat tarike kai alamun jiri nason yarda ita Husnah ta taimaka mata tazauna tace Amina Hakeem anya lafiyarki kalau kuwa Gaskiya kitashi mu dispensary Abaki magani Meenat tace gida ma zantafi tai maka min da phone dina acikin bag Husnah tabude jakar meenat taga wasu hadaddun wayoyi masu tsadar gaske kuda biyu aciki Ta kwaso duka tace gasu meenat ta karbi daya takira driver din ta Taba wa Husnah wayar ta mayar mata dashi jaka   ****** Bayan kwana hudu ankai sadakin yaya shamsu gidansu kubra Sannan kuma Abba yasai block da yashi ma aikata sukafara aikin gyaran inda ya shamsu zai zauna acikin gidan ne amma ciki da fall da bayan gida acikinshi Har Dan karamin kitchen dinta basai ta fito tsakar gida ba Komai nasu aciki yake Umma da Husnah sukaje kasuwa suka nemo akwatunansu masu kyau guda uku Aciki akafara zuba kayan lefe Wanda yanzu kusan duk asabar sai sunfita kasuwa Dai dai gwargwado dai aka hada lefen ya shamsu Aka kai gidansu kubra Nan da sati biyu za adaura auren   Dubu ashirin ya shamsu yaba wa kubra tayi hidiman biki dashi   ***** Hakeem zaune kan kujerar yana hada wani muhimman file Sai Ahmad yashigo yace wai baka gama ba har yanzu kasan time kuwa Hakeem yace nagani ai nan da Kaduna dai insha Allah komai dare Ahmad yace Allah yasa nidai kai nake jira kawai nagama shirina Hakeem yayi dariya yace bantaba ganin ango merawankai irinka ba Ahmad Ahmad yayi dariya yace ai gwamma ni kai inkatashi karawa ai bansan dokin dazakayi ba Hakeem yayi murmushi dayake kara fito da zallan kyanshi Yace tabbas kuwa lokaci yakusa zuwa inji ajikina nakusa samun choice dina sai dai bansan a inabane Ahmad yace kai amma fa akwai rigima Dan madam Laila zatayi rikici bakadanba Hakeem yayi murmushi yace zatawa kanta danzan iya komai akan matata da zan aura Dan itace zabina Kaga kuwa ta taka a sannu Ahmad yace wallahi man I like your style gaskiya zanso Gina gidana kaman yadda kake handling naka Hakeem yayi murmushi yace banbaka shawarar hakanba Dan na tabbatar Aisha ba halinsu daya da Laila ba Kagakuwa ba za amusu hukunci iri dayaba ko Ahamad yace gaskiya Dan hankalin Aishat nagani yasa har nayi shaawar aurenta   Ya shamsu yashigo ya musu sallama suka amsa suka mika mishi hanu suka gaisa Ya shamsu yace wa Hakeem gani yallabai Hakeem yace dama zanfada maka ne zamu tafi Kaduna Sai nan da sati daya zamu dawo Hakeem yadauko invitation card na auren Ahmad Yabawa ya shamsu yace muna gayya tarka daurin aure Ya shamsu yayi murmushi yace masha Allah Allah yabasu zaman Lafiya Sai dai ranar yazo dai dai danawa auren Hakeem yakalleshi yace har ansa rana baka fada minba malam shamsu Dama bakayi niyyar gayya tarmu bakenan kokana ganin inka fada ma bazamu bane Ya shamsu yayi murmushi kawai yace aikuna kokari ma da aiki Kuma har ga Allah bani tunanin inna Baku invitation zakuzoba Saboda matsayinmu badayaba Hakeem da Ahmad suka kalli juna Ahmad yace haba malam shamsu karkace haka saikasa muga kaman mu ba mutane bane Ya shamsu yace to afuwan Nayi kuskure Hakeem yace to yanzu dai bazamu samu zuwaba amma muna maka fatan alkairi Tace ban account number din ka inbada nawa gudumawar asiyawa amarya kaji Ya shamsu yace wannan yana daga cikin dalilin dayasa naji fada muku zamanin yanzu kowa yana fama da kanshi Dan Allah kabarshi karka damu kanka Hakeem yace karka damu ni nayi niyya kuma kasan bakyau maida hanun kyauta baya Ya shamsu yace hakane yakaranto wa Hakeem number account din Shima Ahmad yanaji kuma ya kwashe number.   Hakeem yace zakaji alert Allah yabada zaman Lafiya Ya shamsu yace ameen nagode Sukayi sallama har wajen mota   ***** Da daddare suna zaune tsakar gida ya shamsu yace Abba da ina son ba wa manemin auran Husnah dama yaturo iyayensa Kaga tana gama makaranta sai aiyi aurenko Baban yace ai nalura yaron nan bashir kaman da gaske yakeyi Umma ta ce sau biyu yana kawo mahaifiyarsa muna gaisawa Shamsu yace alhamdulillahi gaskiya konina yaba da bashir Kara shigowar sako yaji a wayarsa yaduba yaga alert ne na dubu Dari biyardaga professor Ahmad Kafin yayi magana wani alert din yasake fadowa daga boss dinshi a office Wato professor Hakeem Shima dai dubu Dari biyar dinne yaturo Sun hada mishi 1 million NIRA cas su biyu suka bashi Nan shamsu yakalli mahifinsa yafada musu Abba yace kai amma wannan uban gida naka Allah yasaka mishi da alkairi Umma tace ameen wallahi ko a mafarki bamutaba tunanin samun dubu Dari nan kusaba Ballantana har million daya Allah yasaka musu da alkairi Kai kuma saika kazauna dasu da zuciya daya Nan dai ya shamsu yakira Hakeem a waya yace ga Abba na zai muku godiya Hakeem yace haba shamsu yanzu saboda kyautar da baitaka kara ya karya ba zaka wahalar da Abba wajen gode mana To gaskiya indai Dan inbari Abba yagode min ne zankashe wayata Insha Allah idan nadawo zanzo nagaisheshi da ka ina amma banda godiya tsakanin malam shamsu Ka gaida umma da kanwarmu Sai da safe Dif Hakeem yakashe wayarsa Dama wayar ya shamsu a handsfree take duk su Abba sunji komai Abba yace gaskiya duk inda akeneman shugaba nagari wannan yaro ya kai Allah yarabashi da sharrin duniya Lafiya Ameen Ameen gaskiya dai bantabajin mekudi hakaba da Jan talakawa ajikinsa kamar wannan uban gidan naka Nan dai suka ta tatattaunawa akan yadda za ayi da kudin Abba da umma dai suka barmai zabi Ya shamsu yace shikenan Allah yakaimu gobe aga yadda za ayi Itakuwa Husnah Allah Allah take safiya tayi taje school taba wa aminiyarta labari Za a ba copper bash daman turowa gidansu   Washagari Husnah da meenat suna zaune a inda suka saba zama Husnah tabata labarin za a ba copper bash daman turowa gidansu aikuwa gaban Meenat yatsinke ras Wani tashin hankali ya ziyarceta Tarasa meyake mata dadi aikuwa har aka tashi daga school meenat batadawo dai dai ba Tana kallo copper bash ya budewa Husnah gaban motarshi zai kaita gida Dan tunda aka sanshi yaroki alfarmar zai dinga dawo da Husnah gida idan antashi Da kyar aka yarda mashi Dan saida yahada da mom dinshi Husnah tana daga wa meenat hanu Ina AMIN ABDUL HAKEEM kam batasan tanayiba Ta Lula dunitar tunani   ** MEENAT tana zuwa gida tafada cinyar hajiya rukayya kakanta Tafashe da kuka maitsanani Hankalin hajiya rukayya yatashi Dan ta dauki soyayyar duniya ta daura akan 'yar jikan nata bakaramin so takewa Amina ba Nan dai dakyar tasamu meenat tayi magana Tace hajiya nashiga uku nakusan mutuwa Wallahi idan ban auri copper bash hajiya zaku iya rasani dan mutuwa zanyi Nan hajiya rukayya tace kwantar da hankalinki kimin bayanin komai Nan meenat ta kwashe komai tafada mata Ba abinda yafi burge Hajiya rukayya a labarin sai jin cewan Bash Dan hamshakin mai kudine a kano Tace kwantar da hankalinki kaman yazama naki ma anfama Aure shida Husnah kuma yazama tarihi Zanje Kaduna aiko Zan baki mamaki bash da bakinshi zaice yanasonki Next page Your comments is needed fans Kamar yadda nayi typing metsayi haka nakeson Comments dinki da tsayi Wallahi comments mai tsayi yana burgeni Sosai Ina yinku masoya AKWAI LOKACI   [05/05, 11:08 AM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION F.C.T.W.A   HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITERS OF THE NATION   DEDICATE THIS PAGE TO adda khadija and shamsu ina yinki over sister Dik ina ganin comment din ki akan novel di na Wato AKWAI LOKACI Daya bayan daya zakuji sunanku masoya AKWAI LOKACI FANS GROUP keep comments kawai   AKWAI LOKACI   PAGE 51 to 60     Ya shamsu ya yagyara wa iyayensa gida dai dai gwargwado Har anyi fenti sabo gida sai kamshin sabon fenti yakeyi da sabon siminti Ya zuba wa umma sabbin kujeru dai dai karfinshi Sannan shima ya zuba a dakinsu shida kubra Yasai TV guda biyu dayasa wa iyayensa daya kuma yasa a sashinsa Sannan kuma yama umman shi dinkuna kala biyar na fitan biki sai yama abbanshi ma kala biyar shima masu kyau shadda da kuma yadi Umma har da hijab uku da ta kallamansu Uku Sai Husnah kuma yamata kusan kala bakwai dai dai karfinsa Ya hada mata da mayafai guda biyar da takalman ta hudu Sai kayan kwalliya da dai sauransu Yafi kashe wa Husnah kudi acewanshi ita tafi bukatar hakan Yama kubra ma kayan fitan biki yace kartayi amfani Dana lefenta Sannan kuma yasa wa abbanshi kaya a shago Dan dama Abba yana shawa ar sana ar awu na hatsi   ***** Yauce ranar daurin auren shamsu da amaryarsa khadija Komai yatafi yadda akeso ankai amarya dakinta dake cikin gidan su shamsu   **** an daura auren Ahmad da amaryarsa Aisha Suna shirin zuwa dinner ne Wanda PROFESSOR HAKEEM ya hada wa babban abokinsa Hakeem da Ahmad sunyi shiga iri daya wani hadadden suit suka saka ango yasaka baki nacikin ja Sai Hakeem kuma yasaka brown colour na cikin sa fari Duk Wanda ya kalli PROF HAKEEM sai yasake kallonshi 'Yam mata sai rawankai suke musam man kawayen amarya Laila ma taci ado cikin wani tsadadden less Wanda tayi order daga malesia Tayi kyau kan nan yasha gashin doki Fuska kuma yaci bleaching kana ganinta dai kasan anci duniya Ango yashiga mota zuwa gurin dinner Hakeem yabude mishi bayan mota Laila kuma ta babbar kawar amarya kuma ta bude wa amarya dayan gefen tashiga Hakeem ne zaija motar ahmad yace Man please kamin wata alfarma mana Hakeem yace ina sauraronka malam ango Ahmad yace kasan idan muisa wajen babbar kawar Aisha ce zata bude mata kofa tunda kai kadaine a gaban motar ta shiga muje kawai Hakeem yayi shiru alamun ya amince kenan Shine rahma kawar amarya tashige gaban mota tana gaida Hakeem ya amsa a dakile kaman bayaso   Suna isa kuwa bayan Hakeem yayi parking aikuwa har 'yan gulma sunje sun sanar da Laila cewan ga Mijinta ya dauko budurwa a gaban mota ai kuwa tafito kaman wata mahaukaciya dai dai lokacin da rahma kawar amarya take fitowa daga motar Hakeem aikuwa rahma batayi tsammani ba sai taji mari kau sannan kuma akasa kafa aka kwasheta aikuwa yazo da tsautsayi rahma tabuga kai sosai take kuwa ta suma aikuwa cikin tsannanin bacinrai Hakeem yadauki hanu ya zabga wa Laila mari yasake kwasheta da mari Nan fa mutane aka taru ganin wannan Abu da Laila ta aikata Nan da nan 'yan uwan rahma dama suma suna gun sukace basu yarda bayan ansa mata ruwa ta farka Hakeem yace kinayin abin kika dama ina kyaleki idan zanyi aure kin isa kiha nanine To barin fada miki daga yau kikasake min dabban ci irin haka wallahi zanyi maganin ki ban wawaiya kawai Wasu da basusan suwayeba Wata 'yar dattijuwa ta matso tace haba 'yar nan Kinsan fa yaran yanzu ba a hanasu auren abinda sukeso koda kuwa iyayensu ne Ballantana keda gani dai baki haifeshi saidai kizama yarshi aisai hakuri Tajuya kan Hakeem tace haba d'ana da hankalinka zaka mari yayarka a cikin mutane akan mace Wasu abin dariya yabasu wasu kunya wasu kuma haushi Musammam meenat cikin gatsali tafito daga cikin taron Tacewa matar nan dalla malama kirufemana baki Wayafada miki kanintane dazakisa mutane agaba da surutu to banana ne itakuma mamana ne Dan haka kikama gabanki bamason muna furci Wato cikin tsananin bacin rai Hakeem yadanko Amina yayi mota da ita ya wurga ta ta tashi motar sai gida aikuwa Laila tace shikenan zaikashe min 'yartawa Dan zata kwacewa uwarta 'yanci Tana ihu tana kokarin shiga mota sai saiga motan police nan sunzo tafiya da ita 'yan uwan rahma kawar amaryace suka dauko 'yansanda aikuwa suka tafi da Laila Hankalin Ahmad yatashi yace wa Aisha amarya tayi hakuri bari yakira akawo mishi mota subi bayan Hakeem Dan komai zaiya faruwa   Hakeem na isa gidansu yayi sashen sa Meenat ya dauki belt dukanta yasoma Kuka sosai meenat take tana bashi hakuri Wayyo Allah daddy kayi hakuri wallahi bazan sakeba yace Ashe baki da mutunci kikalli kaman wannan matar kimata rashin kunya ko Abinda uwarki da kakanki suka koya miki ko To ba agidana ba Dan ubanki Mummy hafsat ce yashigo da kyar ta karbi meenat agurin uban Hakeem ya kalli mummy yace mummy Dan Allah bana son yarinyar nan ta koma gurinsu Kwatata sunbata wa yarinya tarbiyya Mummy hafsat tace wai meyafarune nan Hakeem yafada wa mummy hafsat komai harda dabbancin da uwarta tayi a wajen dinner Mummy hafsat tayi salati tace yanzu wadan nan mutane bazasu canja haliba gashi harsuna Neman bata mana jika Kaman daga sama kuwa suka ance sannu masu tarbiyya Dana nasan ba Wanda yake haddasa fituna saike hafsat To wallahi anzo gurin da banzan bariba dan me zaudauki hanu yata dukan matarshi acikin bainar jama a Mummyn Hakeem tace aini abinda Hakeem yayi amin dai dai duk abinda Laila takeyi tasamu daurin gidinkine yaya rukayya Hajiya rukayya tace wato kekikabashi daman yadauki karuwa a mota ko Mummyn Hakeem tace ya isa haka yaya rukayya wallahi zanyadda da komai amma banda mummunan kazafi akan Abdul Hakeem To wai ma da kuke wannan haukan wayace muku Hakeem bazai kara aure ba ai Karin aure akan Hakeem wajibine Dan wallahi koshi baiyi niyya ba nizansashi aure dolene aikuwa hajiya rukayya tafashe da kuka tace yanzu hafsat nizaki cewa mahaukata ina matsayin yar mijinki kidubi tsaban idona kice muna hauka Mummy hafsat tace duk abinda yafaru kokuka janyo Kuma wannan yarinya da kuka sangarta bazata koma wajenkuba Zanriketa har Allah yasa tagane gaskiya tadawo hanya bakaman Ku da kuka bata ba   Hajiya rukayya tace wannan kuma baki isaba hafsat kinyi kadan kirabani da jikata Mummy hafsat tace zancen kikeso Tana amina fuuuuuu suka bar falon   Hakeem kuwa barin falon yayi zuwa dakinsa Sukabar hajiya rukayya kaman tafashe dan bakin ciki Wayar hajiya rukayya tayi kara taduba taga Suby ce kanwar Laila tace kekuma ya akayi Suby cikin tashin hankali tace mama gamunan a police station ankulle anty Laila Hajiya rukayya tace wani station din kuke Nan tafada mata tafita zuwa police station din Hakeem yana shiga bedroom dinshi wanka yashiga Kafin yafito yadan kwanta yana tunanin bakin hali irin na Laila da 'yan uwanta ** alhaji abubakar yana office din shi azaune saboda yayi baki daga India Sai yaji kiran yayarshi hajiya rukayya Yadauka tare da sallama Hajiya rukayya tafashe da kuka tace duk inda kake kazo gida ba Lafiya Matarka da 'danka zasukashemin 'yata da jikata alhaji abuabakar yace subahanalla ganin zuwa yaya kidaina kukan Dan Allah Ya kashe wayar yadau hanyar gida Yana zuwa yasamu yayansa hajiya rukayya a kofar gidanshi Yafito amota da sauri yace mekefaruwa ne haka Nan dai ta kwashe karya da gaskiya tafada mashi yace yanzu kishiga mota muji police station din ayi belinta Inyaso sai mudawo gida a yi magana Hajiya rukayya tashiga mota suka nufi can police station din Suna isa tun kamin ayi parking suka ga Ahmad da Laila Ahmad yaga motar daddyn Hakeem sai yakaraso gurin motar yagai da daddy Daddy yace sunbaka belin kenan Ahmad yace a amma dakyar suka bayar sai da nasa hanun zata je har gida tabawa yarinyar data sumar hakuri Daddy yace Allah yarufa asiri kaima kayi kokari Ahmad Allah yabaku masu yimuku Ahmad yace ameen daddy barin karasa gidan Daddy yace wa Laila tashiga bayan motar sutafi tabude bayan tashiga Ta madubi hajiya rukayya tace Dan Allah kalli yadda suka mayar min yarinya saikace wacce bata da gata Alhaji abubakar dai baice komai har suka isa gida Duk yatarasu a falo Hakeem na zaune daddy yace banji daddyn abinda yafaruba naji komai amma ina insan kai Hakeem wace mata kadauko agaban mota nan Hakeem yawa mahaifinsa bayanin Hajiya rukayya tace karya kakeyi kana nufin Laila Karya zata maka Mummyn Hakeem tace to ita Lailar uwarshice dabazata mishi karya ba Daddyn Hakeem ya ce ban baki iznin maganaba hafsatu kiyi shiru Mummy hafsat tayi kwafa Nan dai daddy yayi musu nasiha meshiga jiki Hajiya rukayya tace sai maganar yarinya sunce wai bazan koma da Amina ba Daddy ya kalli Hakeem yace yazakayi haka bayan kuma yarinya dasu tasaba Hakeem yace daddy idan har yarinyar nan zata koma to ta gaggauta fito da miji tana gama secondary school kawai aiyi aure Dan wannan da irin tarbiyyar dasuka bata nan gaba zata iya fin karfin mutane Mummy hafsat tace wannan shawarar taka tayi dai dai Dan bazanso jikata ta acikin wannan rayuwar da ba asan nagaba ba Hajiya rukayya tace kaga abubakar kashiga tskanina da matarka Daddy Hakeem yace wa mummy hafsat Dan Allah karkisake cewa komai sai na baki dama Nan alhaji abubakar yace zata koma amma gaskiya nima anan naba da goyan bayan tafitar da miji kafin nan da tagama secondary school Hajiya rukayya tace wannan ba abin muwabane Abamu nan wani lokaci saurayinta zaizo dakanshi yagaisheku aitana dashi Alhaji abubakar yace to alhamdullila Dan Allah komai ya wuce Ke Laila ba wa mijinki hakuri aikuwa hajiya rukayya tace ya za ace tabashi hakuri bayan shiyakamata yabata hakuri daya dauki hanu ya tsinka mata mari acikin mutane Ganin abinda hajiya rukayya takeyi yasa Hakeem barin falon yayi sashinsa Yana fita suka hadu da Ahmad Hakeem yace ango Ahmad yace komaidai yakoma dai dai ko Hakeem yace barin shiga nashirya nazo muwuce Muje musallami friends dinmu na nesa Ahmad yace karka damu nagama komai Hakeem yace yanzu har ka rakasu airport Ahmad yace kwarai Hakeem yace amayar fa Ahmad yayi murmushi yace ai andade da tafiya da amarya Dan dazu nakirata harsun huta ma Yan uwanta ma sun kamo hanyar dawowa Hakeem yace to ai sai musamu mushirya muwuce muma ko karnayi laifi dayawa agurin Madam Aisha Ahmad yayi murmushi yace a haba aitasan komai Idan taga bamuzo ba tasan abinda yatsare mu Hakeem yace yau zaka shiga dakin amaryar ka Barima kagani Hakeem yashige sashinsa Yafada bathroom yayi wanka Yana gama shiri cikin shadda marun colour ya balain masa kyau kamar danshi akayi shaddar Yana fesa turare Laila tashigo Tace daddyn meenat naga kaman tafiya zakayi baka sallamemuba Hakeem ya watsa mata wani kallo Yace mekuke bukata tace kayan abinci da na amfanin gida yace kizauna kirubuta duk abinda bukata zansa driver yakawo muku Daga yau nabar baki daman da kikesamu harkike ganin kaman kinfi karfina sai yadda kikayi dani ko cikin tashin Hankali Laila tace Dan Allah karkamin wannan horon kasan nasaba sayan abinda nake bukata da kaina Hakeem yayi murmushi mugunta yace nawa nakebaki dama Laila tace dubu Dari uku duk wata Hakeem yace hakane ko ta ce a hakane Yace kedawa nabari agidan nan tace nikadai Yace good yanzu duk wata zanturo miki dubu hamsin Kekadai dai nasan zasu isheki Yana gama fadan haka yayi waje da brief case dinshi   Haukane Kane kawai Laila batayi ba Amma hankalinsa yatashi sosai nan tadauki gyalanta tayi gurin mahaifiyarta hajiya rukayya **** Bayan wata shida professor Hakeem zaune kan kujerar office din shi Yadauki wayarshi yakira yaya shamsu Ya shamsu yashigo yace Barka dai yallabai sannu da aiki Hakeem yayi murmushi yace yauwa malam shamsu Yace ga wannan ya shamsu yakarba yace ina zankai yallabai Hakeem yayi murmushi yace nakane malam shamsu zaka kaiya dubawa kagani Ya shamsu yabude Aikuwa ya shamsu ya dago ido yakalli PROF Hakeem Yace admission fa nake gani yallabai Hakeem yace yes nasan kana da burin karatu a rayuwarka Iyakacin zamana da kai na lura kai mutum ne mai son karatu So yanzu ga dama nan malam shamsu zaka iya farawa nagama komai har registration da komai sai dai ka kai credentials dinka asa maka a file Kuma daga Level two zakafara nariga nayi komai A department of business administration Ya shamsu baisan lokacin da tashiba yace yallabai gaskiya ba abinda zance da sai dai Allah yabaka abinda kake nema duniya da lahira Allah ya jikan mahaifanka ya ramaka zuria Hakeem yace ameen malam shamsu na gode kwarai da adduarka a gareni Sai dai ni har yanzu baka taba tambayata wani Abu da yashafi rayuwata ba malam shamsu koba bukatar sanin daga ina nafito ne Ya shamsu yayi murmushi yace zanso sanin tarihinka dakuma tarihin nagartarka a rayuwar alumma Nan professor Hakeem yayi murmushi Yabashi labarin rayuwarshi kaf bai boye mai komai ba Ya shamsu yaja numfashi yace yanzu tun kana 20years kayi aure kenan Hakeem yace kwaraikuwa ina da 17 year old girl yanzu haka Da mamaki ya shamsu ya kalleshi yace masha Allah Gaskiya kai kam duk abinda ake nema a rayuwa Allah yabaka Hakeem yace zakasan daughter nawa ma ai duk sati tana zuwa ranar alhamis Ya shamsu ko wacce kake cewa amina Hakeem yace yes ita nake nufi Ya shamsu yayi shiru yace am sorry sir wallahi duk azatona madam dinkace Hakeem yayi murmushi yace 'yata ne nacikina Ya shamsu yace masha Allah wallahi gaskiya labarinka ya burgeni Bude kofar office akayi Prof Ahmad ne yashigo yace Kace kuna tare da malam shamsu ne Hakeem yace ai tundazu muke hira anan Ahmad yabawa ya shamsu hanu sukayi gaisa Ahmad yace wa Hakeem madam fa tagama abincin rana yakamata muje muyi lunch Hakeem yace gaskiya dai nima yaka mata nasan abinyi Kaga madam Aisha sai tadinga hutawa ko Ahmad yace Aisha ce zagaji wai caf yanzu kasan Allah da zankoma inje cin abinci nikadai sai tambayi ina kake baka biyoni ba Duk randa kake azumi haka nake fama da ita   Hakeem yace Allah sarki madam tana tausaya wa marayan Allah Ahmad yayi murmushi yace maraya a kano ba Ahmad ya kalli ya shamsu yace malam shamsu gaskiya yau Na kamaka sai munje kaci abincin amarya Hakeem yace aifa dai kam tunda shi yana mana rowan abincin amaryarsa da kuma ladan da zamu samu wajen gaida su umma da Abba Ya shamsu yayi murmushi yace bahaka bane banyi tunanin inna gayyaceku zakujeba shiyasa Hakeem yayi murmushi yace saboda gamu aljanu bama cikin jinsin mutane ko Ahmad yayi dariya yace zamu baka mamaki sai dai kaganmu agidanka Ya shamsu yace ina zuba ido ,nan dai kyar ya shamsu ya yarda suka je dashi cin lunch   Suna kan dining din Ahmad suna cin abinci itakuma Aisha tana kan two sitter Tace wa Ahmad honey yaushe zaka kaini yawo kasan fa bansan kowaba a kano kuma inason inga gari Ahmad yace zan hadaki da kawance da madam din malam shamsu kinga saikije mata itama tazo miki amma sai malam shamsu ya amince Ya shamsu yayi dariya yace ina zata iya erea mu ai sai mu Hakeem yace kaidai kawai malam shamsu kace bazaka bar madam dinka suyi zumunciba Ya shamsu yayi murmushi yace shikenan Allah yashige mana gaba Sukace amin Dazasu tafi ne Aisha tace wa ya shamsu Dan Allah agaisar mata da kawarta kafin suhadu Ya shamsu yace zataji insha Allah **** Bayan wata biyu da fara zuwa makarantar shi Ankawo sadakin Husnah Harda kayan lefe akwati gomashabiyu cas Sadaki kuma naira dubu Dari biyu Yanzu haka ana jiran suyi waec da neco ne kawai asha biki Shakuwa ce maitsanani da kaunar juna tsakanin copper bash da Husnah *** Meenat zaune kan carpet dinsu hajiya rukayya tadawo daga tafiyan datayine wajen boka Dan karbowa meenat maganin MALLAKA da zata mallake copper bash yazama nata Hajiya rukayya tace a abinci zaki zuba mishi idan yaci zai kamu da soyayyarki Wanda ko uwarsa bazai mata Sannan kuma zaiji ya tsani Husnah aduniya Cikin farincki amina tace kai Allah yabar minke kakus dina Laila dake gefe tana kallonsu Dan itama jiya tazo Laila tace hajiya Nifa ba abinda kika karbo min Akan daddyn meenat Hajiya rukayya tace ai wannan yaro fa asiri bazai kamashi ba sai dai kawai musa a kawar mana dashi Har lahira kinga masamu dukiya muyi yadda mukeso da shi   Meenat caf daddyn nawa za a kashe wallahi bazaiyi yiwuba Haka kawai ita mummyn bata San yadda zata karbi kudi a ahanunshi ba sai ankasheshi Hajiya rukayya tace to ai murasa yadda zamuyi da wannan uban naki ne jikalle Meenat tace natabbata baza arasa wani hanyar ba kudaiyi tunanin   Husnah zaune a dakin amarya kubra tana asigment dinta Kubra tace kedai Husnah kinji dadi wallahi wannan irin gashi aikoda shi zaki yaki mijinki balantana ga uwa uba kyau da diri duk Allah yabaki Husnah tadago manyan idonta ta kalli kubra tayi murmushi Tace anty kubra kenan sai kace ke Kubra tayi murmushi tace zakicimin fuska ko ai idan dai kina guri muai saidai muyi shiru Husnah tace banda zuga fa matar yaya Husnah ta fashe da dariya ita kadai Sai kubra tace meyabaki dariya Husnah tace kawai danku nakeson gani keda yaya wannan irin kyau da kyau ai sai dai kuhaifo mana aljani Dan kyau fa Kafin Husnah takarasa maganarta kubra ta dauki pilon kujerarta zata kwadawa Husnah Husnah ta tashi ta gudu dai dai shigowar ya shamsu Yace lafiya kekuma Husnah tace Lafiya qlw ya shamsu anty kubra ce ta biyoni Umma dake kan sallaya a faranda tace o keda kubra dai zanga ranar rabuwanku akwai drama Ya shamsu yayi murmushi yace sai tabita ai Umma tayi murmushi tace andawo Dan albarka ya makarantar Ya shamsu yace alhamdulillah umma bara nayi wanka sai nazo muyi hira umma tace To banana Ya shamsu yashiga dakinsa yasami kubra zaune ta tashi tana mishi sannu da da wowa Yayi murmushi Dan kullum son matanshi karuwa yakeyi saboda yadda take matukar mutunta 'yan uwanshi hakan nasa yana Dada jinta cikin ranshi Murmushi yasakar mata yace kamu hanunta yace meya hadaki da kanwartaki Kubra ta yi murmushi tace tsokanata tayi shiyasa tagudu Wai karmu haifi aljanu Dan kyau fa Ya shamsu yayi dariya yace ai haka tace Shiyasa na tambayeta tamin shiru   Washagari da safe bayan anfito break sai copper bash yakira Husnah office din sa Dan ta serving din abinci Dan baya break shima sai goma Shiyasa daga gida akekawo mishi Ba kullum yake kiran Husnah ba Dan idan yakirata bata zuwa Dan kare mutuncin kanta Ba kullum ana ganinta a office din shi ba Suna zaune itada meenat wayarta yayi kara ta dauka tace aslammu ailaikum Yace wa alaikumussalam my love Husnah tayi murmushi tace inajinka ranka yadade Yace alfarma nake nema kizo Dan Allah ki serving dina break fast Husnah takalli meenat tace kice to Dan Allah Husnah tace shikenan ganin nan zuwa Husnah takashe wayar ta kalli meenat tace meyasa kikasa na amsa mishi Meenat tace tace haba kekuwa Dan ya roki alfarmar yau dai ai sai kiyi mishi Husnah tace bazaki gane bane amma tashi muje kiraka ni dama abinda meenat kesonji Suna isa office din copper bash Yace wa amina taje cikin motarahi zataga basket din abinci ta dauko mishi Aikuwa amina cike da farinciki ta wuce class dinsu ta dauko maganin ta da zata sawa bash Sai da ta bude flask din ta zuzzuba dama soyayyan doya da kwai ne Sai ruwan tea Aikuwa ta zuba ta dauka takai mai Husnah tayi serving dinshi Yayi dai dai lokacin komarwar su class Husnah tace zata wuce class yace ita bazataciba Tace ai yau alhamis suna tana azumi Yace yayi kyau kikula min da kanki kinji ko Tayi murmushi dimple dinta suka lutsa yace I like your smile Husnah tace thanks Ta wuce zuwa class Wanda tuni meenat tarigata Yagama break dinshi tsaf   Washagari jumma a Dama bashir yasaba zuwa duk Jumma a Husnah zaune tagama shirinta tsaf bashir kawai take jira Kubra tace gaskiya dai tunda yasaba kiranki kuma yasaba zuwa yakamata kikarashi kiji kolafiya Husnah ta yarda da shawarar anty kubra Takira bashir yakai sau goma amma yaki dauka sai a kiran karshe Yadauka yace dalla malama me na damuna haka Kebari nafada miki karkisake kirana daga yau banza Mara mutunci Na tsaneki Husnah bana son jin sunanki kifita a rayuwata Sadakina da kayan aurena duk za azo karba kafin yafadi wata magana Husnah ta yanke jiki ta fadi Ya yi dai dai da shigowar kubra Aikuwa kubra tayi ihu umma da abba da ya shamsu suka zo   Next page Your comments is needed fans Ina dadin comment din Ku fan's   Ina alfahari da Ku [05/05, 11:08 AM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION F.C.T.W.A   HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITERS OF THE NATION   DEDICATE THIS PAGE TO MOM IMAN &HANIFA MUCH LOVE TO YOUR COMMENTS SIS KEEP IT UP Ina alfahari daku masoya novel din AKWAI LOKACI daya bayan daya zakuji sunanku ina bin comments dinku sosai Allah yabar zumunci     AKWAI LOKACI     PAGE 61 to 65     HUSNAH kan cinyar umma ansamata ruwa ta farfado Ya shamsu yace Husnah kiyi magana meya haddasa miki wannan suman Husnah ba baki sai kuka Abba yace ke kubra kukinsan abinda yafaru Kubra tace gaskiya dai ba abinda yafaru sai takira bashir Bansan meyace mata ba kuma nasan tabbas abinda yasameta yana da alaka da bashir   Kafin suyi wata magana wasu mata sukayi sallama suka shigo Umma ta sannunku da zuwa suka yauwa Umma ta ce sannunku da zuwa sukace yauwa Allah yasa nan ne gidan su Husnah ba bata mukayi ba Ya shamsu ya kallesu yace nan Suka shiga yiwa gidan kallon wulankanci suna kebe baki Dayar tace ni wallahi dama banga gamin kifi da kaska ba da za ace wai bashir yarsa gidan dazai nemi matar aure sai gidan matsiyata Wato kubran ya shamsu wani takaici ya debeta ta tashi Ta cakumo wuyar wacce tayi maganar Ta wanke ta da mari zata kara mata ne ya shamsu yariketa Kubra tace Dan Allah ya shamsu kabari Nakara mata Inbanda cin mutunci kishigo har gidan mu kuce zakuci mana zarafi To wallahi ubanku yayi kadan Ita wacce aka Mara tace kika mareni to wallahi sai kinyi da nasanin marina Kuma abinda yakawo muda ma munzo abamu kayan auren mu da sadakinmu Mai auren yace bayayi mudama bason gidan matsyata irinku mukeba Cikin tace kune kuwa babban matsiyata wadda basusan darajan nagaba dasuba Abba yace wa kubra shiga daki Kubra tabi maganar Abba tayi dakin Abba yace wa ya shamsu fito musu da kayansu Ya shamsu yafito da kayan daya bayan daya Umma ta ce kuna iya kwashewa kufita mana daga gida ko Ita wacce aka Mara tace aiko bakuce mufita zamu fita ehe Ya shamsu yace ke idan kina rashin kunyarki ya tsaya iya kan dai dai ke banda iyayena Kwarjinin ya shamsu ya musu suka kasa mishi rashin kunyar Nan da nan suka fara jidan kayansu suna fita dashi Ya shamsu yashiga daki yadauko musu sadakinsu yakai musu har gurin mota Yace gashi sai Ku hada basai wani yasake zuwa mana gida Suka karba shiru Dan sunkasa magana ma   Ya shamsu yashiga gida yaga yadda Husnah take kuka yace kiyi shiru kidaina kuka kinji yar kanwata Allah zai miki canji da mafi alkairi Umma tace gaskiya yaron nan yabani mamaki yanzu memuka mishi da zai mana wannan cin mutunci Abba yace ai sai agode wa Allah ba akaiga aurenba Da anyi auren ne ya wulakanta mana yarinya ai bazamu ji dadi ba Ya shamsu yayi ajiyan zuciya yace shiyasa ba kuwani maikudi ake yarda da soyayyrashi akan talaka ba Yayi amfani da talaucin mu ne yasa har ya iya yin abin da yayi Amma bakomai watarana sai labari Shiyasa ni kwatata yanzu bazan sake wa Husnah auren mai kudi Ba Gwamma ta auri dai dai ita sayi arzikin tare zaifi ganin mutuncinta Umma ta ce wallahi na goyi bayanka Dari bisa Dari Abba yace muna namune kuma Allah na nasa Allah yazaba mana abinda yafi alkairi Sukace amin Nan akayi ta rarrashin Husnah da kyar tasamu tayi shiru *** Satin Husnah biyu bata je makarantaba school ba saboda rashin Lafiya datayi amma yanzu jikin alhamdullila Dan tana ma shirin zuwa school gobe insha Allah Washagari Monday da safe Husnah tashirya cikin sabon uniform dinta Wanda ya shamsu yadinka mata Tayi kyau sosai tasaka read cap dinta da belt dinta na head girl Bayan ta fito tayi wa umma sallama umma tace Allah miki lbarka kinje Dan kicire komai aranki Tace umma namiki alkawari cire damuwa daga raina Tawuce bangaren ya shamsu Ta Dan bubbuga kofar ya shamsu tace ya shamsu nagama mutafi yace OK daman kenake jira Suka fito tare da kubra tana rataye da jakar mijinta Ta kalli Husnah tace kai tawan wallahi kinyi kyau sosai Husnah tayi murmushi tace anty kubra kenan ya Shamsu Mutafi kasan anty idan tafara sai tasa muyi latti Kubra tayi murmushi tace to Dan Allah kisayo Wannan kunun ayar da kike kawo min Husnah tace karki damu Zantaho miki dashi Kubra yauwa kanwata Nan dai ya shamsu da Husnah suka fita yatare musu keke napep   Yabata dari biyar tace kai yaya shamsu yamin yawa ai Ya shamsu yace ai nasan bakya azumi Dan haka kiyi amfani dashi kiyi break karkizauna da yunwa Husnah tace wallahi umma ce ta hanani yin azumin wai saina warke Ya shamsu yace ai gaskiyar tane Gwamma yar kanwata tayi katuwa Husnah tayi murmushi tace nagode yaya Ta shige cikin school dinsu Tana shiga an buga assembly nan ada sauran prefect din suka tayata Shirya yara Assembly Nan dai Husnah ta hau kan stage tafara control din data sabayi Bayan angama assembly principal ta aika akira mata head girl dinta Husnah Tace mata nakiraki ne nabaki hakuri akan kinyi rashin Lafiya har natsawon sati biyu school bataje tadubokiba Husnah tayi murmushi tace mummy ai an wakilta prefect sunje sun dubani Mummy principal tayi murmushi tace ai duk da haka yakamata a hada da malamai amma dai muna Neman afuwa Husnah tace wallahi mummy bakomai aikema bakya gari da kinje Nan mummy principal tace bata wani envelope tace ga wannan kikai gida Husnah tace to mummy Nan principal tabata daman ta koma class Husnah nazuwa class taga meenat sai alokacin take zuwa Husnah tayi murmushi tace ai wallahi aminyi bakida kirki Banda Lafiya kokije kidubani ko Amina ta kalleta sama da kasa tace Allah yabaki Lafiya Abin yaba wa Husnah mamaki Har zatayi magana sai Ku ma tafasa Dagana kuma malamin su na Math's yashigo Ana cikin musu teaching wata daliba tayi excuse sir copper bash yana kiran anty amina Hakeem Sir yace amina Hakeem Meenat tace yes sir Yace oya tashi kije Kafin amina ta fita sai da tajiyo taga ko Husnah tana kallonta Itakuwa Husnah batasan tanayi ba Dan ita kosunan bashir bata son ji tatsaneshi sosai   Har aka fita break amina batadawo ba   ****** Yauce su Husnah suke graduating a school dinsu Aka kawata hall dinzasu yi taron aciki Principal bata ba da damar graduating students Susa kayan gidaba wato personal wear's kenan Shiyasa duk inda kaga SS 3 zaka gansu sunsha guga sunsha kyau Dan ba hana suyi make up ba Duk prefect kowacce da hulanta akanta sunjeru a kujera na musamman sai kuma sauran graduated students dinsuma suna nan akujera ta musamaman Husnah ma duk 'yan gidansu sunzo mata Abba ne kawai baisamu zuwaba amma ya shamsu da anty kubra da umma duk sunzo Amina Hakeem dakyar tasamu daddynta Hakeem yace zaizo Ahmad da amaryarsa sai Hakeem sukazo sai mamanta da kuma hajiya rukayya duk sunzo Hakeem tunda yazauna yake ta fama da wayarsa Dagowar da Ahmad zaiyi yaga ai anzauna kusadashi aikuwa dai ya shamsu ne da anty kubra umma kuma tanacan bangaren dattijai mata Ahmad yace kaga ikon Allah malam shamsu kai ne anan kokuma wa Ya shamsu yajuyo jin ankira sunanshi aikuwa yaga su Ahmad da Hakeem Hakeem ma jin an ambaci sunan malam shamsu Yasa yadago mai suka yi murmushi gadayansu Nan ya shamsu yabasu hanu suka gaisa Yace wasuka zowa Ahmad yace daughter dinmu ai nan take karatu Kaifa yace nikuma kanwata ce anan Kubra tace ina wuninku Hakeem da Ahmad suka amsa Ahmad yakalli inda madam dinshi Aisha take yatashi yaje yarada mata magana akunne aikuwa Aisha ta task da sauri Tana zuwa ta kama hanun kubra tace alhamdullilahi yau dai nima na hadu da kawata Kubra ma dayame wayayyiyace tace nima naji dadin haduwata dake Nan Aisha taja hanun kubra suka koma gurin su daban Nan kuma ya shamsu da Hakeem da Ahmad suka can gaba wajen special guest Nan akafara taron da addua Can principal tafara jawabinta kamaryadda aka saba Daga can kuma ta ce itada kanta zatakira best student of the year Wanda duk shekara akeba principal dama tazaba da kanta ta kuma bata kyauta duk karshen shekara haka akeyi Wani daga cikin teachers dinsu ya tashi yakarbi Mike din hanun principal da list din hanunta Yafara kiran suna kaman haka Best student of the year Kowa ya kasa kunne ASMAU SULEIMAN SHAMSU aikuwa duk student aka dauki tafi raf raf raf Dan daga malamai har student sunsan Husnah ta cancanta sosai Cikin nutsuwa Husnah ta tashi ta isa gurin principal Nan principal tace wazata kira ya tayata karba Husnah tace wa principal ya shamsu za akiramin ya shamsu suna zaune duk hankalinsu yakoma kan head girl Shi ya shamsu baifada musu wacece kanwar tashiba Sai jisukayi ankira ya shamsu yatashi cike da alfahari da 'yar kanwarshi bata bashi kunya kokadan Ahmad da Hakeem suka hada ido Ahmad kaddai itace kanwar tashi Hakeem yayi murmushi yace ga zahiri amma fa yarinyar taburgeni matuka Yayi maganar yana kallonsu Husnah Cike da mamaki Ahmad yakalli abokin nashi am I dreaming ? Man what are you saying Hakeem bai kalleshiba murmushi kawai yayi ya dauke idonshi daga gurin su Husnah ya mayar da kanshi kan wayarshi Murmushi Ahmad yayi dai dai lokacin ya shamsu yadawo yazauna Ahmad yace kanwarkace ya shamsu yayi murmushi yace yar karamar kanwata kenan Yace masha Allah Allah ya albarkaci rayuwarta Ya shamsu da Hakeem suka ce ameen Daga nan kuma sai akafara ba wa prefect satificate dinsu ya rage sauran na social prefect da Head girl Aka kira social prefect AMINA HAKEEM ABUBAKAR Nan akabata sertificate dinta da kuma gift dinta maman Laila ita tayata karba Hakeem kallo daya yamusu yacigaba da abinda yakeyi Can akakira me gayya mai aiki wato head girl Husnah taje ta karba itada yaya shamsu principal Tamika kyautar aka musu hoto Duk wani kyauta da akerabawa Husnah ita takarbi na farko abin yaburge kowa ana karshen Husna ta tashi zata karba sai kawai tafashe da kuka Dan tasan koba komai yayanta zaiyi alfahari da ita Principal ta rungumeta tana share mata hawayen Tace asmau Allah ya albarkaci rayuwarki Ya shamsu yaji dadin adduar principal Yace Ameen hajiya mungode Allah yabar zumunci Nan fa students sukayi tazuwa suna daukar hoto da Husnah suna mata fatan alkairi Masu bata gift nabata kai gaskiya Husnah tayi farin jini sosai har malamai suna tururruwar hoto da ita Meenat zaune abin duniya yadameta tana matukar jin bakin ciki abin da kefaruwa da Husnah Laila tace wai ita wannan yarinyar fa saikace aljana komai ta handame ita kadai Meenat tace kyaleta dama yunwa ne yakawota school din Dan dama 'yar matsiyata ce Scholarship taci tashigo Hajiya rukayya dole ai yanzu naji batu Motar school ce ta kaiwa Husnah gift dinta har gidan   **** PROFESSOR HAKEEM yana zaune cikin falonshi kusan sati kenan da graduation dinsu Husnah amma kullum da ita yake kwana da itayake tashi aranshi Kuma tunda yake a rayuwarshi bai taba saka 'ya mace a rayuwarahi ba Kuma a yadda ya fuskanci zuciyarshi takamau son 'yar baby nan Shida kanshi yake wa kanshi dariya Ya duba agogo yaga sai yanzu 8:30 nadare tayi Yaje ya hada Kofi Yanasha kadan yana tunanin Husnah Abinda baisaniba shine Ahmad yadade a bakin kofa yana kallon abokin nashi daya fada shauki Ahmad yayi gyaran murya hade da sallama Hakeem yajiyo suka hada ido da Ahmad Ahmad yace abokina wai meyake faruwa ne Kwana biyu naganka kaman akwai wani Abu Hakeem yayi murmushi tareda kurbar copee yace shine kabar matarka kazo gulma ko   Ahmad shima dariyar tare da dauko lemu maisanyi a fridge Yadawo yazauna Ahmad yace inkarashida gulma kaikaso amma dai ni bazan bar nan ba sai kafada min Hakeem yatashi yakoma bayan kujera yace Ahmad am in love Ahmad yayi dariya yace daman nasani Duk wannan boye boyen naka duk kallonka nakeyi amma gaskiya idan har kasamu yarinyar nan kayi sa a wallahi Hakeem yace wace yarinya kenan tunda nidai ban fada wacce nakeso da bakinaba Ahmad yayi dariya yace karka rainawa wa kanka hankali mana Kawanwar shamsu koba hakabane Hakeem yayi murmushi yace amma ya akayi kagane hakan dawuri Ahmad yace shekaru talatin muna tare fa dan uwa taya za ayi barangane matsalarka ba Hakeem yayi murmushi yace hakane amma bazan fada ba sai na musu Jarabawa daya kaga daga tabbatar gidan danaje Neman iri Next page Your comments is needed fans❤❤❤❤❤ Anfara wasa fa fans❤❤❤❤ Sainaji ku [05/05, 11:08 AM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION F.C.T.W.A   HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITERS OF THE NATION   DEDICATE THIS PAGE TO sis JIDDER (BAEWAR ALLAH) WANNAN PAGE IN NAKI SABODA KAUNA DA KIKE NUNA WA WANNAN NOVEL NAWA NA AKWAI LOKACI Allah yabar zumunci keep it up ❤❤   Masu comment ina sane da Ku kafin na kamla littafin nan duk sai kunji sunanku daya bayan daya so kucigaba da bin ummu afan takuce ❤     AKWAI LOKACI     PAGE 66 to 70     PROF HAKEEM zaune kan resting chair dinsa a bakin sweeming fool yana shan iska dan yanzu yafito daga cikin ruwan Wayarshi ta daukara yana dubawa yaga dalibata wato mummynshi kenan dan sunan dayasa mata kenan Bayan sungaisa Hakeem yace mummyna albishirinki mummy hafsat tace goro Yace naga matar aure a kano fa Cikin tsananin farin ciki mummy hafsat tace alhamdulilla naji dadin wannan albishir Yaushe zakazo katura mahaifinka gidansu yarinyar Hakeem yayi murmushi yace daliba kenan ai ban ma taba fada wa yarinyar ba nikadai nake kida kuma nake rawa na Mummy tace shirme ni harkasani ina murna to idan bazaka iya fada mata nika nuna min gidansu yarin sai naje Ayau saina zo kano wallahi akanka my son Hakeem yayi murmushi yace nasani mummy na Nasan zakifi kowa farinciki shiyasa nafada miki tunkafin na fada wa yarinyar Sai mummy Kinsan masu soyayyar Allah kadan suke aduniyar nan Kuma dadin da dawa ma yarinyar danagani din ba masu karfi bane Kinga idan naje kaitsaye Kuma akayi rashin sa a saikiga sun soni don kudina badan Allah Mummy taja numfashi tace hakane son sai dai zuciyata tana bani bazataba son abinda baidace dakaiba Hakeem yayi murmushi yace Kinsan menakesonyi mummy tace a a son sai kafada Yace zan jarabasu nagani zanje amatsayin talaka banida komai Ingani zasu karbeni kokuwa Mummy tace hakan ma tayi son dina Kuma ina maka fatan alkairi Insha Allah zasuci duk wani jarabawar da zakayi musu Wasunan surukartawa Hakeem yayi murmushi mummy ta sosa mishi inda yake mai kaikayi Yace ai harma tazama surukarki Mummy tace aiba surukaba ma 'yata zama son Hakeem yayi murmushi yace asmau amma anakiranta da HUSNA kai masha Allah ashema babban suna ne da ita Insha Allah asmau zata Mata agareka tun kafin naganta naji inasonta Hakeem yace shiyasa nakeson Ku iyayena kuna matukar daraja abinda nakeso Allah yabani matar da zata bauta muku da zuciya daya badan kudinku ba ko kudin danku Mummy hafsat tace aikasamu son zantayaka da addua   **** Washagari Hakeem Bayan sungama komai ya shamsu yazo musu sallama zai wuce gida dan karfe hudu yake tashi a lectures Ahmad yace wa ya shamsu yaufa kafanmu kafarka zamuje mugaida Abba da umma Dan idan muka biye maka bazaka gayyace zuwa samun ladan nan ba Ya shamsu yayi dariya yace shikenan idan kun shirya muna iya tafiya Hakeem yace na dauka zaka kawo wani excuse ne ince ai ba umma kai kadaibane muma namune Ahmad da ya shamsu sukayi dariya a motar Hakeem akatafi ya shamsu agaba Ahmad yabaya Ya shamsu yana nuna wa PROF HAKEEM hanya   ****** HUSNAH ce zaune tsakar gida tagama aikin gidan kenan tas ko ina yadau kamshi Ita kuma anty kubra tana kitchen tana hada abincin dare Wanda sudama kafin biyar sungama komai sun zuba a kula Kuma aikin sukayi Husnah da kubra yau idan kece da aikin gida to dayar kuma saitayi abinci Yau Husnah ce da aikin gida Tagama komai da wuri tana wa anty kubra dariya tana kitchen dan yau ya shamsu yace ayi tuwon semovita miyar kubewa danya Har kudin danyar kifi yabayar   Anty kubra tace zanrama ai Allah yasa ran girkinki Abba yace sakwara yakeso Husnah tayi murmushi tace kai ai danagane kuskurena kuwa Umma datake jinsu tace tun tuni kinjuye ruwa Yakama kishiga kiyi kisamu kifito kije min aika ko Husnah tace to umma Umma ta kalli kubra tace sannu kinji kubra Allah dai yamaku albarka yabaku masu yimuku kuma Kubra acikin zuciyarta ta amsa da amin dan tana jin kunyar umma idan tace Allah yabasu masuyi musu   Husnah tafito daga wanka tayi dakinsu tashafa mai tadauko powder tashafa sai kwalli sai tasa lips glow alebenta Tabude akwatin kayan ta tafara zaban wadda zata saka aikuwa idon ta yakai kan wani material pink da kuma ratsin baki ajiki Wanda ya shamsu yamata a bikin shi Tunda tasa a biki batasake sawaba Sai tadauko shi tasaka dinki duguwa Riga ce Daga sama ya dameta sosai dan Husnah fa akwai kayan aiki Shiyasa umma bata cika barinta fita da gyaleba saidai hijabi dan Allah yamata kira Husnah takalli kanta a madubi itakanta tasan tayi kyau sosai Sai kuma tasan dakyar umma zata bari tasaka gyalen material din Itakuma yau mayafi takeson yafawa tace barin gwada dai tagyara gashinta tadaure da ribbon fari Kafin tayafa gyalenta dan bata saka dankwaliba Kota saka dankwalima abanza Dan bayazama akanta sabonda tsantsin gashinta Tadauko turarenta tafesa kafin tadauki Jakarta na suwaga pink da takalminshi duk pink tasaka Kai masha Allah da wannan kyakkyawar hallita Tafito tace umma nafito Umma ta kalli 'yartata tace au da wannan gyalen zakifita Husnah tace Allah sarki umma na gyalen kayan nefa Kuma kinga kayan ai yana da fadi sosai Kafin umma tayi magana anty kubra taleko tace umma dan Allah kibarta wallahi tayi kyau kuma kinga ai kayan yana da fadi Umma ta ce wato bakinku daya ko to shikenan kije Allah yakiyaye hanya Husnah tace to umma baki min bayaninba umma tace kinci gidanku yau kika saba karbomin zuman ne Husnah tayi murmushi dimple dinta tsuka lotsa sosai Tace to ummana afuwan nadauka bakaman na kullum bane Tayi waje sukace mata adawo Lafiya   adai dai kofar gidansu ya shamsu yanuna wa Hakeem yayi parking Suka fito atare Ahmad yace kashiga saikamana iso Ya shamsu yace to shikenan yaya cikin gidan alokacin umma ce kadai a tsakar gida kubra ta fito mata da taburma Dan anna suke hirar Daren su gadaya Ya shamsu yayi sallama umma tace a a ubana har andawo yace a umma yagidan nan dai yagaida umma kafin yace umma daman su ogana na office ne sukazo gaisheku Umma ta ce shine kabarsu a waje kuma sushigo ciki dan Allah haba waje Ya shamsu yaje ya musu iso zuwa cikin gidan Umma ta ce kashiga dasu daki Ahmad yace a umma mu kusa da ummanmu zamu zauna basai munshiga dakiba Umma taji dadin har ranta tace to shikenan 'ya'yan ummu kuzauna nan suka kwashi gaisuwa agurin umma ta amsa cike da farin ciki Nan kuma ta musu godiyar hidimar dasukeyi da su Hakeem yace haba umma ai mu da shamsu Yanzu munzama 'yankuma bagodiya tsakaninmu ai yiwa Kaine Umma ta ce hakane kam Allah yake mutum da mutum Kodai Allah yasaka muku da aljanna Umma ta ce wa shamsu ubana aisai kayi maza kaje nan shagon mati ka karbo musu lemu mai sanyi da ruwa Hakeem yace haba dai umma mufa ba bakibane Komai ummanmu tabamu cizamuyi Ba umma ba harta ya shamsu yaji dadin wannan kara da Hakeem da Ahmed suke musu Sallmar HUSNAH ce yasa Hakeem daga ido yakalli hanyar waje aikuwa suka hada ido cikin ido Husnah tayi saurin dauke idonta dan dama akasi aka samu ta kalleshi HAKEEM yasamu Kansa cikin wani yanayi Wanda yakasa fassarashi ba Ashe ganin da yayi mata a school ma tafi haka Husnah ta durkusa har kasa tagaishe da su Hakeem Ahmad ne karfin amsawa shikam ogan ba baki Yakasa komai ne Ba Wanda ya kula da canzawarshi sai Ahmad Ahmad murmushi yayi shikadai Kubra tafito tagaishesu Ahmad yace ai kawarki basan zamuzo ba dakinganta Kubra tace dan allah yakawo mata Aisha Dan zaman da sukayi a gurin graduate dinsu Husnah sun saba sosai Ahmad yace ya mata alkawari ran sabar zai kawo Aisha tamata wuni daga nan tagaida umma Umma ta ce Allah yakawo ta Lafiya umma na maraba da ita Husnah da kubra suka kawo musu abinci a kula da biyu suka ajiye Husnah tadauko plate guda biyu da serving spoon duk ta ajiye musu Sai ta dauki jug ta kawo musu ruwa maisanyi na randar umma ta kawo musu da cups biyu Umma ta ce maza hada musu zobo Husnah Husnah tace to umma ai na dafa tunda dazu hadawa kawai zanyi saidai ba kankara Ya shamsu yace hada barin karbo kankara Ya shamsu yafita jimawa kadan sai ga shida kankara yakawo yaba wa husnah Hadaddan zobo ta hada Wanda yasha kayam kamshi da cocumba Tasa musu a jug shima takai musu kafin ta wuce dakin anty kubra umma tace bara nashiga kuci abincin Ku Ya shamsu yace bissimillarku kuci abinci Hakeem yayi murmushi yace aiko baka fada ba Ahmad yayi murmushi dan yasan dalilinsa na fadar hakan Hakeem yayi serving kanshi Tuwo daya yasaka sai sai yasa miyar baiga ruwan wanke hanuba sai Yace yaya shamsu ruwan wanke hanu dan bana cin tuwo da cokali Ya shamsu yayi dariya yace amma yallabai kaso barkwanci ninekuma yayan Hakeem yayi murmushi baice komai ba Ya shamsu yakira Husnah takawo ruwan wanke hanun Takawo ta ajiye gaban ya shamsu shikuma ya mikawa Hakeem gabansa Hakeem sosai yaci tuwon dai Bayan ya cinye Leda daya sai ya kara Ahmad nema yarage kadan Ya shamsu yace haba yallabai dan Allah kacinye wallahi umma zataji dadi Hakeem yace rabudashi ya shamsu tsoron madam Aisha yakeyi kartatsareshi sai ya cinye abinta yakasa Bayan yacinye na gidan umma Duk suka kwashe da dariya Hakeem yatsiyayi zobon da Husnah ta hada musu yasha Aikuwa yaji kunnenshi kaman zai yanke dan dadi Kodan ya hadu da soyayyane oho Kafin yayi magana Abba yashigo dattijon arziki Duk suka mike tsaye sai da Abba yazauna suka zauna suka kwashi gaisuwa Ya shamsu yagabatar dasu Abba yace a manya baki ne damu agidan Ashe Nan shima yashiga musu godiyar hidimansu akansu   Sun dan taba hira kafin Abba yashiga daki yabarsu nan da ya shamsu Hakeem yace Gaskiya ya shamsu wannan zobon asamin awani Abu natafi dashi zansha zuwa dare Ahmad yace narigaka azuci karigani a baki dan kasan duk inda nasha abinda yamin dadi sai narage wa madam Hakeem yayi murmushi yace kai man kafadi gaskiya Ya shamsu dai dariya yakira Husnah yace tasamo jugs guda biyu ta zubo zobo tace to Hakeem tabita da kallo komai na yarinyar yamishi Dari bisa Dari Tana da duk wasu qualities din dayake bukata ga mace Husnah ta zuba takawo ta ajiye Ta yigaba abinta Sai da akakira magrib suka yi sallama da su umma da Abba da anty kubra Husnah tana kan sallaya idan tayi magrib bata ta shi sai tayi isha Hakeem yaso yasake ganin Husnah Amma taki fitowa Ahmad ya ajiye bandir din kudi 'yan dubu dubu yace a ba wa kanwarsu tasai kayan kwalliya Ya shamsu yace dan Allah karmuyi haka kudauki kudinku Ahmad yace ai nariga na ajiye kuma ma aibakai muka ba ba kanwarmu muka ma kyauta Da kyar ya shamsu yabar kudin nan Suna cikin mota Hakeem ya karya kwana zuwa baibi hanyar gida ba Ahmad yace man yana zaka kaimu kuma Hakeem yayi murmushi yace sa ido kawai kayi kallo man Ahmad yace OK baringa ikon Allah to Hakeem yayi parking adai dai gurin wani malamin almajirai suka sauka Malam na ganin HAKEEM yataso yazo sannu da Zuwa professor Hakeem yayi murmushi suka gaisa da malam Garba Malam Garba yace mukarasa daga taburma nan suka karasa Hakeem yace malam bawani Abu yakawoni ba illa Neman wata alfarma Malam Garba yace alfarma kuma alhaji da kanka Hakeem yace a malam Aure nake nema malam Amma kasan rayuwa ta baci yanzu sai aureka badan anasonkaba sai dai don abinda kakedashi Malam yace hakane Hakeem yaja dogon numfashi Ya kalli Ahmed da ya kagu yaji dalilin abokin nashi nazuwa nan Hakeem yace malam zanje Neman aure da sunan talaka talakan ma futuk Mara iyaye Koda anzo Neman tarihina guringa za azo dan Kai zanfada a matsayin malamin danayi karatu agurin shi Kai kuma inason kanuna tun ina karami aka kawo maka ni Wannan kadai nakeson kamin malam Malam Garba yayi murmushi yace gaskiya alhaji kana da tunani mai kyau Allah ya tabbatar da alkairi Hakeem da Ahmad suka ce amin malam Nan suka wa malam sallama Hakeem yadauko bandir din kudi yaba malam yace gashi a rabawa yara sadaka Ya ba malam wani kuma yace Gashi wannan nashine Malam Garba yayi ta musu addua Acikin mota Ahmad yace amma meyasa makayi wannan tunanin haka Hakeem Ahmad yace kana nufin bazasu ganeka ba wai kome Hakeem yayi murmushi yace duk zan shirya wa hakan Ahmad yace Allah yasa amma dai yakamata duk wani abinda zakayi wallahi kayi sauri kafin wani yariga ka Hakeem yayi murmushi yace inaji ajikina wannan yarinyar rabonace Ahmad yace to tunda kana da tabbacin haka Meye na gwada ta kuma Hakeem yace inason nasan mena aura ne kuma rayuwata zanbata kaga kuwa ina bukatar bincike sosai Ahmad yace sai prof komai naka daban ne wallahi gaskiya bazan boye maka ba I like your life style Bros Keep it up Hakeem yayi dariya yace baka jiya abokina Ahmad yace ai bazangaji Komai naka is so special **** Bayan sati uku Hakeem yayi order na fuska daga India Yau yakesaran za akawo mishi Hakeem ya zaune wani abokin Wayar shi tadau kara yana sai yaga number din Wanda yaba sautun siyo mishi fuska Yadaga wayar yace badai har kun isoba Doctor isah yace gani ma acikin school dinku Hakeem yace what's a surprise Ganin zuwa Hakeem yafita yaje yashigo da doctor isah Nan Bayan sungaisa doctor isah Yafito mishi da sakonsa Hakeem yakarba yace masha Allah kuma gaskiya kayi yadda nace Doctor isha yace to ai kasan aikan manya irinku ba kasafai akacika muku shirme ba Hakeem yace zakafara kaima ko Doctor isha yayi murmushi yace ansamu ragi sosai yallbai dan Rabin yakai dubu Dari da hamsin Hakeem yace OK zaka iya barinshi a wajenka yazama naka doctor Doctor yace a yi haka yallabai Hakeem yace karka damu ai kamin komai   *** Da daddare Hakeem ya fesa wanka yadauki jallabiyya yasaka yadauko fuskarsa yasaka kafin yadauki carbi yarike a hanu Yadauko wayar Nokia da yasa akasayo mishi second hand wacce duk tasha dauri da roba Ya kalli kanshi a madubi shida kanshi yaba kanshi dariya Yadauki kudi yan hamsin da kuma 'yan goma yasaka a aljihunshi Ya kulle gidanshi yafita zuwa gidan Ahmad yayi sallama Maigadin yace sannu malam daga ina haka kuma gurin wakazo Yace inason kamin sallama da maigidan ne Bayan Ahmad yafito ne yaga mutum ustaz har da gemunshi Yace assalmu alaikum Hakeem ya amsa mishi cikin canjawar murya Hakeem dai yakasa danne dariyar shi yacire fuskan Ahmad wazaigani Hakeem ne Cike da mamaki Ahmad yace amma ka shammaceni A ina kasamu masks nasan dakyar akesamu a Nigeria Hakeem yace daga India aka kawo min Kaga kai ma danake tunanin zaka ganeni baka ganeniba Bana tunanin shamsu da mutan gidansu zasu ganeni Dan haka ni wuce daga yau zafara basu exam's din su Hakeem ya mayar da fuskarshi yagyara da kyau yadda baza a ganeba Yayi bakin titi yatari kekenapep zuwa anguwar su Husnah Next page Tofa fans za afara wasa fa Your comments is needed Ina alfahari da masoya novel na AKWAI LOKACI   [05/05, 11:08 AM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Story & written By The special writer UMMU AFAN   FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION (F.C.T.W.A)   HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATION   I DEDICATE THIS PAGE TO YOU sister surayya auwal ina matukar jin dadin comments din ki amma Dan Allah sister kikara yawan comments din ki ina alfahari da Ku da da comments din ku❤❤❤❤❤     AKWAI LOKACI     PAGE 86 to 90     HUSNAH zaune tana gyaran farcenta Umma tace auta nikam ya kukayi da Alhaji ne naga jiya yazo Husnah ta bata fuska tace wallahi Umma guduwa nayi dakin anty kubra na buya Dan wallahi Umma nibana sonshi Umma tayi salati tasanar da ubangiji Tace aidaman zaran hijabin dakikayi kaman kinje Bazuwa kikayi ba To ma wai meyasa bakya sonshi meyamiki husnah karki zamo me saka alkairi da sharri mana Tunda Allah baiyi aurenki da shi abdullahinba sai ki ba Wannan dama kodan halinsa na kirki badan abin hanun shiba   Anty kubra tace wallahi Umma kullum sai namata wannan nasihar amma kamar anshuka dusa   Husnah tace wallahi ni kwatata bana jin zan iya son wani bayan ustaz ne Kuma bana son na aureshi nakasa yimashi biyayya Umma na Dan Allah kufahimceni Umma tace ai shi so ahankali yake shiga Kyawawan halaiyar wannan yaro kadai zaisa kifara sonshi azuciyarki Dan yana da duk wani nagarta atare dashi   Kafin Husnah ta yi magana ya shamsu yayi sallama yashigo yazauna Yana gaida umma kubra ta tashi tace sannu dazuwa tayi hanyar fridge tadauko mishi ruwa maisanyi Takawo mishi Ya dauka yasha kafin yakalli umma yace mekuke ta tattaunawa ne ummana Umma tayi murmushi tace wallahi wannan shasharce muke taba baki saikace wata uwarmu Sai waina mu takeyi Ya shamsu ya kalli Husnah yace wai meyake damun kine husnah Ustaz yariga yatafi bazai dawoba Wallahi husnah da ace zaidawo lokacin da akeshirin daurin auranki da Abdul Hakeem za afasa a daura dashi Sai dai kash ba a mutuwa adawo Sai dai ina miki albishir dacewan Allah yamiki sakayya da mafificin alkairi Mun dade muna Neman hanyar da zamu sakawa wadan nan mutane Sai gashi Allah yakawo tunda yasawa yallbai kaunar ki aransa Maizai hana kitayamu maida alkairi da alkairi husnah Abdul Hakeem yamana komai a rayuwa kuma duk abubawan da yayi mana na tabbatar Dan Allah yayisu Kaman yadda kema zamu bashi dan Allah badan abin hanun shiba   Husnah tace shikenan yayana Namaka alkwarin bazan baka kunya ba Na amince da shi Amma wallahi danku Dan wallahi yaya bana sonshi   Ya shamsu yayi murmushi yace Abu mafi mahim manci dai shine ki amince   Husnah ta turo bakin shagwabar tace wato bakadamu dani bako yaya na   Ya shamsu yayi dariya yace caf waya fada miki yar kanwata Yace ai nafi jidake Dan idan kikayi aure ma fa tare zamu tafi Husnah tayi murmushi tace ai wallahi yaya da dagaske kake da naji dadi sosai Amma nasan kana fada be kawai Amma nifa kullum sai nazo gidan nan   Umma tace kwarai kuwa daga ke har yayan naki zan ga me hankali acikin Ku Anty kubra tace gaskiya kam umma Nima naga alama tana dariya Ya shamsu yace dawa kikeyi yadauki pillow na gefensa ya wurga mata ta tashi Tagudu yabita shima Umma tayi murmushi Dan yadda Dan ta guda yake zaune lafiya da matarshi bata taba ganin wani abun ki agurin kubra   Husnah tace umma Dan Allah yau kimana danbun tsaki da kanki Kinga yau nice da girki Umma tayi murmushi tace naki wayon sai girkin 'yata azo zanyi aikuwa husnah tayi murmushi duk kugama badaini ba wato sai ran girkin anty kubra zakiyi ko Shikenan nasan mezanyi muku a gidan kuma dole kuci Umma tayi dariya tace kinga kuwa kyayi aiki har dare kenan   Husnah tayi murmushi ta tashi tace Abba yakusan da wowa Barin yi kitchen Tana shiga kitchen din tafara tunanin abinda zata daura Taduba store dinsu taga suna da doya Tadauki guda biyu tafere shi tas ta wanke Ta rarraba shi kanana Tazuba tunkuya takawo gishiri tasa dai dai misali   Kafin tadebo albasa attaruhu da tattasai dakuma tomatoes amma kwaya hudu tasa tomatoes din bata bukatar tumatir dayawa Nan ta wanke komai tas Tafara greating dinsu a greater ba a blender ba Dan bata bukatar suyi laushi Nan tasoya su da mangyada saidataga tayi soyu sannan tadauko yankakkakun kayan namanta kanana dake cikin fridge tafashashshe Tazuba tadauko gyararran kifinta Wanda tariga tacire kayar tas shima tazuba tacigaba da juyawa Kafin tadauko maggi tazuba dai su curry da thyme da dai sauransu Tahada tacigaba da soyawa haba ai nan da nan gida ya hau kamshin girkin husnah Sai da ta tabbatar ya soyu kafin tarage gas din kadan Tadebo kwai (eggs) guda biyar Tafasa su a kwano daban tasaka magi guda daya takada Kafin tadauko tana zubawa kadan kadan tana gaurawa har tagama tacigaba da juyawa Gaskiya ko itada datayi miyar yakayatar da ita balantana Wanda saidai yagani kawai saici Nan ta sauke tasama Abba a kulansa kafin tasa ma umma ma anata kulan Ta ajiye a gefe Tadauko nasu ya shamsu da anty kubra tasamusu dama tumsafe tayi kunun ayarta Wanda yasha madara tasaka a fridge yayi balin sanyi kuwa Ta dauka nasu yaya shamsu tayi da shi part dinsu Taje tana ta sallama taji shiru Can saiga anty kubra tafito da gudu daga bedroom dinsu kanta ba Dan kwali ga gashinta duk an hargitsa Ga rigarta zif din agaba yake kana ganin kasan akwai magana Dan anfara Jan zif din amma baikai kasaba   Kubra bata San ma da mutum a falonba ganin husnah kawai tayi tasake baki tana kallonta Kubra ganin kallon yayi tace ke malama lafiya kuwa Husnah tayi murmushi tace a a bakomai gani nayi kinfi to kamar wacce tayi dambe da zaki Takarasa maganar tana dariya Kubra tasan metake nufi Itama tayi murmushi tace kema kwana nawane zakije fada da zakin aikuwa husnah tabarai ta turo bakin tace zakifara ko anty kubra Ta ajiye musu abincin tace gashi idan kungama soyayyar kwaci aikuwa tana fadar haka tagudu Kubra tayi murmushi kawai kafin ta koma ciki   Husnah wanka tafada tana fitowa tayi sallar La asar dinta kafin taje gaban dressing mirro dinta tafara shafa mai abinta tanagama shafa maidin tadauko body spray tafesa kafin dauko wani doguwar rigar English wear tasaka Ta dauki gashinta daure da ribom baki kasancewar kayanta marun colour ne Yana da bakin dankwali tadaura tayi daurin tauban Tasaka jambaki shima marun colour gaskiya ba karya duk Wanda ya kalli husnah sai yaso yasake kallo Kayan dama dayane daga cikin kayan da mummy hafsat takawo mata ne Ta fito tasami Abba da umma sungama cin abincinsu Abba yayi murmushi yace autar Abba gaskiya abincin yayi dadi wallahi Waya koya miki ne autar ummanta Umma tayi murmushi aini wani girkin ma fa kirkiran abinta takeyi kuma saikaga yayi dadi Husnah tayi murmushi tace aini a school dinmu Abba food &nutrition naza ba akan agriculture Abba yace kai amma auta ta kinyi dabara Umma ce takatse musu zancen nasu Tace anya kuwa kinci abinci Dan nasan halinki sarai idan ba aganki ba saiki kai har goma na dare bakici komai ba   Abba yace wai har yanzu rashin cin abincinta yanan Umma tace sai abin da yakaru Idan tagadama wataran dakanta zata dafa indomie Ya shamsu ne yashigo falon yagaida iyayen nasa Ganin fitowar ya shamsu yasa husnah zuwa gurin kubra Wayar ya Shamsu yayi kara yana yaga yallabai kamar yadda ya saving wayar Yadauka bayan sungaisa prof yakecewa gani acikin gidanku Ya shamsu yace haba yallabai kaman wani bako kashigo mana Hakeem yayi murmushi yace ai gurin matata nazo katurota Dan Allah yakashe wayar yana dariya Ya shamsu yafada wasu Abba Hakeem ne yazo Abba yace ya zai tsaya a waje kuma kaje kashiga da shi falonku tunda yau surkunta yakeji damu Umma tayi murmushi tace ina ruwan Abdul Hakeem yaron kirki wallahi Ya shamsu yaje suka shigo tare da Hakeem harkasa Prof yatsuguna yagaida su umma Kafin ya shamsu yace mune daga ciki tana can ma Suna sallama dai dai lokacin husnah take gwadawa kubra rawan ittiki aikuwa Hakeem idonsa kyam akanta ya shamsu yace to dancer of the year Anty kubra tayi dariya tace sannu dazuwa tana wa Hakeem cike da kulawa ya amsa tareda tambayarta gida Nan ta tashi tayi falon su umma Husnah zata bita ya shamsu ke dawo nan baki iya gaisuwa bako Cike da jinkuyar Prof tun ranar daya ganta half nacked bata kaunar su hada ido Tadawo tazauna gefen ya shamsu kai a kasa Ya shamsu yace to yallabai saika fito professor Hakeem yace Weldon ya shamsu Ya shamsu yayi murmushi yafita Hakeem yamaida kallonshi kan husnah wacce take ta wasada da yatsunta daya sha Jan lalle Batayi tsam Mani ba kawai taganshi agabanta Zama yayi kasan shima yana fuskantarta kasa dagowa tayi saboda kunyarshi gashi itadai bawani sonshi take ba Yace tunda nibaza a gaisheniba nibarin gaisheda my wife Dafatan kin wuni lafiya kasa amsawa tayi Yace koki amsa gaisuwata konasa hanu na dago da fuskarki   aikuwa bashiri tadago tace cikin shagwabbiyar murya tace kayi hakuri karka tabani ina wuni Professor Hakeem yayi matukar kaduwa jin wanann murya na husnah Gawani masifaffan kyau tamishi Kayan data sa ajikinta kaman Dan ita akayisu Prof jiyayi kaman ya rungumeta a kirjinsa kozai zamu saukin sha'awar data taso mishi lokaci daya Husnah ganin hanun Prof kawai tayi yadanki hanunta Cikin tashin hankali husnah tabi hanunshi da kallo Yace baby kinsan damuwata wallahi kece ina matukar son kasacewa dake amatsayin mata amma haryanzu bansan matsayina ba agurinki Husnah tace zanfada maka amman saika sake min hanu Hakeem yayi murmushi yace shike nan inajinki Husnah tafara magana tace na'amince zan aurekà amma bana jin zaka sàmi soyayyata Dan nariga nagama soyayya a rayuwatà Dan ni kwata kwatà soyayya bai karbeniba Kar sàinafara sonka kaima narasàka Takarasa maganar da kuka mecin rai Hakeem jiyayi kukan har cikin ranshi yadauko hand kacif a aljihunsa fari Sol yasha kamshi yamika mata aikuwa ganin hankacif din nan saiyada ta girgiza Ta karba dasauri tace Dan Allah yaya a ina kasamu wannan hand kacif din Hakeem yace nawane kokina sone cikin sauri tadaga kai tace Dan Allah kabarmin wallahi irin Wanda ya muallim yake amfani dashine Koranar da zamu rabuma shine a hanunshi Takarasa maganar hawaye mai tsanani Hakeem yace banason kukan nan kigoge fuska kimin magana Wanda yamutu ai yamutu Husnah tayi murmushin data kumatunta lotsawa sosai Tace aikuwa sai dai kayi hakuri Dan har abada bazan daina tunaninshi ba saboda yatafi da zuciyata gabadaya Hakeem yaji matukar jintausayinta kaman yarungumeta ya rarrasheta Husnah tacigaba da bashi labarin soyayyarta Akan bashir da abinda yayi mata bayan tadauki zuciyarta tabashi lokaci kawai akejira ayi biki amma yafasa Kuma yakoma suna soyayya da babbar kawarta Sannan takarabashi labarin masoyin asali ya muallim Hakeem yace nikuma na godewa Allah nakuma godewa saurayinki dayace yafasa Dan da befasaba danayi asarar zukekiyar yarinya kamarki Kinga kuwa nidan gatan Allah Akaro nabiyu yasake kama hanun Husnah yace please baby kiyarda dani Yakura mata ido tace naji amince amma kasake min hanu Dan Allah bakyau fa Hakeem yace nasani baby shiyasa nakeson abanike a matsayin mata saboda banason nacigaba da sabawa Allah taba jikinki batareda aure ba Because I can't control my self in front of baby Husnah ta tabbatar dagaske yakeyi Tayi murmushi bara maka ruwa da lemu Yaji dadi har ranshi data nuna kulawar ta agareshi Murmushi kawai yayi tare da 'daga mata gira ta tashi zata je sai kuma taga idonshi akanta Ta juyo a shagwabe please yaya kajuya kadaina kallona inbasokake nafadiba Maganar yaba Hakeem dariya yace jeki na rufe idon Da gudu kuwa tafita yabi bayanta da kallo Sai yatuna da ranar dayazo amatsayin ustaz Zataje dauko masa kudi wai sai yarufe idonsa Murmushi kawai yayi shikadai Tare da zaro wayarsa daga aljihunsa Sallama tayi da tire a hanunta dauke da abinci ta ajiye gabansa Hakeem yaganta cikin wata jibgegen hijabi abin yaso bashi dariya ma Kar dai ace tagane abinda yake kallo Sai yayi murmushi kawai Husnah tace ga abinci yaya Hakeem yace nakoshi Husnah takalleshi tace saboda me Hakeem yace saikin fada dalilin ki nasaka min hijabi daga shiganki dauko min ruwa Husnah tayi murmushi kawai Tace sanyi nakeji tafada tareda boye kanta cikin hibinta Hakeem yace baby husnah tadago batareda ta amsa ba Yace cire hijabin nan kizo ki serving dina Husnah ta marairai ce kaman zatayi kuka tace Dan Allah kayi hakuri yaya wallahi kunyarka nakeji Prof ya tsareta da maya tattun idonshi masu kwarjini Yace OK kinfison acire miki da kauna ko Husnah tayi saurin girgiza kai Yace OK do as I said cikin sanyin jiki husnah tacire hijabin ta ajiye kan kujera tasauko kasa ta Samishi abinci Prof ya gyara zama yafara cin abincin tareda tsareta da ido Duk kallonshi yasa ta takura Yace batayi tsanmani ba taka spoon din a hanyar bakinta Tadago ido takalleshi ya daga mata gira Tace azumi nake yi Yau Wednesday dama ana azumin nafila Husnah tace wallahi Nina koshi cikina ma kaman zafashe Yace tunda yayi niyar bata tabude baki kawai yasamata Bata da zabi haka tabude Dan karamin bakinta yasaka mata Yanayin yadda take cin abincin nata ma kawai abin kallone Yatsaya kawai yana kallon ikon Allah Yace bude bakin nagani Tayi saurin cewa na am da karfi Tace inazuwa umma nakirana ta tashi tagudu abinta Hakeem murmushi yayi kawai yagama cin abincinsa yafita yashamsu yace har zaka gudu Hakeem yace a nayi bakine Shine zanje nagansu Ya shamsu yarakashi har gurin mota Prof yakira megadi yabashi manyan lodoji yashiga dasu gida Ya shamsu yace yallabai Dan Allah karage kashe mata kudi haka sunyi yawa karka manta fa yarinyace Husnah har yanzu bata gama sanin kantaba   Prof yayi murmushi yace karkadamu itama ai hakkinace so konawa zankashe mata basuyi yawaba Karka damu ya shamsu Nagode da kulawarka Yashige mota yayi gaba Yabar ya shamsu da tunanin irin karamcin na PROFESSOR HAKEEM   **** Meenat sun wuce honey moon itada agonta bashir a inda zasu zaga kasashe sama da biyar Shiyasa ma suke saran sai nan da 5 months zasu dawo Nigeria   Dadddyn Hakeem da shi dawasu amin tattun abokansa sukaje nemawa ABDUL HAKEEM ABUBAKAR SHUAIB Auran ASMAU SULAIMAN SHAMSU Sun bada sadakin husnah da zinare Wanda akalla zai kai million daya da rabi Abba da ya shamsu suka suka kikarba Daddyn Hakeem yanuna rashin jindadin shi Sai su Abba suka karba tare da wa abin albarka Nan daddyn Hakeem yace yana Neman alfarmar asaka auran nan da two Weeks Next page Your comments is needed Fan's   Ina alfahari daku masoyana ❤❤❤❤❤❤ [05/05, 11:08 AM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Story & written By The special writer UMMU AFAN   FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION (F.C.T.W.A)   HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATION   I DEDICATE THIS PAGE TO YOU SIS NERFEESERT A MUSA INA MATUKAR JIN DADIN YADDA KIKE COMMENTS DINKI DAFATAN ZAKI CI GABA DA SUBURBUDO COMMENTS KEEP IT UP     AKWAI LOKACI     PAGE 91 to 95     PROF zaune cikin falonshi na gidansu yanawa da Ahmad madam Laila tazo tazauna kusa da shi fuska a kode Tace ina da magana fa baban meenat Hakeem yakalleta da nutsuwa yace ina sauraronki maman meenat Laila tadago kanta ta kalleshi Dan taga kaman yau akwai abin arziki Sai tadauko ko kwalliyar da tayi ne ta burgeshi aikuwa sai tasake wani shagwabe fuska wai ita zatayi shagwaba Abin yaso ba Prof dariya amma sai ya make Tace daman inason wasu kudine Dan Allah Hakeem yayi murmushi tare da kurban copee dinshi Yace kaman nawa kike bukata uwargida rangida idan bake bagida aikuwa kanta yasake fashewa Tayi dariya tace kuma daga ni bawata nice amarya nice uwargida Saboda dariya Hakeem har kwarewa yayi Ya ajiye coffee din yana murmushi Wanda yake karawa kyakkyawar fuskarshi kyau Yace Allah ko tace sosai Yace nawa kike bukata kenan Tace million biyu Hakeem ya kalleta yace sun isheki Laila tankalleshi da mamaki Sai dai kuma tabasar tace a idan zansamu kari ma aizankarba Yace OK yatashi yaje dakinsa yadauko cheque yarubuta naira million biyar Yabata aikuwa madam laila data karba taga abinda keciki Kusan suman zaune tayi agun Sosai takasa control din kanta A take ta dau waya takira hajiya rukayya tafada mata kudin da hakeem yabata Tsaban batan basira irin nasu daga uwa har 'yar suka hau murna Ta ma mance agaban Prof take da mamaki Hakeem yake kallonta Kuma godiya haka ta tashi zata fita Hakeem yace baki jiba zokizauna Baki tambayeni kudin menene ba Laila tace aina sani tunda Nina tambayeka kuma ka nunka min fin abinda na tambayeka Hakeem yace OK wannan kudi kiyi amfani dasu ne naki Dan nan da two weeks za a daura min aure Kinga saiki sai abinda kike bukata ko wani wawan ihu tafashe dashi Tacire Dan kwali ta yar tace cikin tsananin tashin hankali tace wallahi Abdul baka isa ka cimin mutunci ba kayi kadan Kuma wallahi banga 'yar iskar data isa nayi kishi da ita Wani wawan kallo Hakeem wa watsa mata Yadawo PROFESSOR ABDUL HAKEEM dinsa data sani yace karkisake kiran matata da 'yar iska if not zan baki mamaki aikuwa Laila ta tafa hanu tace auwa harma tazama matar taka to wallahi Baku isaba Kodayake kaima ba yinkanka bane duk abinda kakeyi saka akeyi aikuwa tawuce fuuuuuuuuuuu tayi hanyar part din mummy hafsat Hakeem daya kai cup din coffee baki ganin tafita ya ajiye coffee din Yace tashin hankali badai matar nan gurin mummy na zata ba aikuwa yatashi yazare belt din jikinsa yayi part din mummy hafsat Mummy tana zaune tana waya da hajiyar Ahmad suna shirya yadda zasu tsara komai kafin bikin ganin Laila tashigo a fusace yasa mummy hafsat tace zankiraki hajiya   Laila ta tsaya agaban mummy hafsat tana girgiza jiki Mummy hafsat tace ke lafiyar ki kuwa zakizo kitsaya kina girgiza Laila tace burin ki yacika sai dai ina son kisani wallahi ba aisa akawo min wata 'yar iska gidaba Nidaman nadade dasanin bakya kaunata kuma wallahi ba yadda kika iya dani Mummy sake baki kawai tayi tana kallonta Zata sake wata maganar taji belt ta kota ina ajikinta Hakeem ne sosai yake sauke mata belt din nan ajiki Mummy hafsat tashiga tsakani tace barta haka son Yace mummy kibarni na babballata hartana da gost dazata sameki tana miki rashin kunya Who is she by the way To bari kiji bazan dauki raini ba ballanta na ki ma mummy na wacce bani da kaman su aduniya Kekinsan zamana dake ma ai darajarsu kike ci Dan ubanki To kije nasakeki kuma yanzu zaki bar gidan nan nonsense '""   Ya kalli mummyn shi yace mummy Dan Allah kiyafemin wallahi nayi da nasanin hada zuria da hajiya rukayya Bantaba tunanin zan ajiye matar da zata iya miki abinda Laila tamiki yanzu ba Mummy tace kayya son kayi sauri da baka saketa ba aiko wace mata da irin nata kishin idan mijinta yazo mata da zancen Karin aure amma ni baka min komai ba hasali ma kanuna min kai d'ane Allah yamaka albarka Tajuya ta kalli Laila dake kurma ihu tana kuka kaman ranta zai fita Mummy tace kekuma tunda rayuwa da kika zaba wa kanki kenan aishikenan Mummy ta wuce abinta Hakeem shima komawa sashinsa yayi nan da Laila ta dauko waya tafashe da kuka hajiya rukayya ta rude tace ke lafiya kike kuka waya mutu Laila tafada mata abinda kefaruwa aikuwa itama hajiya rukayyar kusan haukar tayi Tace ba inda zakije ganin nan zuwa kadunan shidin banza share hawayanki Kekadaice a gidan mijinki Kwantar da hankalinki ganin ta howa   Alhaji abubakar daddyn Hakeem yana hanyar dawowa daga office Hajiya rukayya takira wayarshi tana kuka Daddyn Hakeem yayi tafada mishi abinda abinda kefaruwa Daddyn Hakeem yace Abu baiyi kyau ba ammanshima yanzu zaikoma gidan Tace itama gatanan a hanyar zuwa yace Allah yakawoki lafiya Ya kashe wayar yacigaba da tukinsa Hajiya rukayya nazuwa sai da tabi tacan gidansu ta taho da uwarta itama wato hajiya suwaiba sukazo tare Laila na zaune tana jiran hajiya rukayya suby kanwarta tuntuni tazo suke zaman jimami tare Karasowar kowa da kowa aka hadu a falon daddyn Hakeem Tunda daga kan hajiya suwaiba mummy hafsat hajiya rukayya Laila suby da kuma uban gayya ABDUL HAKEEM suna zaune gaba dayansu Daddyn Hakeem yafara gaida hajiya suwaiba tunda itace uwa agaresu bakidaya Kafin yagaida yayarsa hajiya rukayya Daga nan kuma yabukaci yasan abinda kefaruwa Hajiya rukayya tafara magana cike da zafin zuciya Tace bantaba tunanin abinda wannan yaro zaimana bakenan ya suna zamansu lafiya da matarsa Za azuga shi yayi aure wannan ma ai Neman tashin hankali ne Kuma abin batsaya nan ba sai su hadu shida uwarshi sun mata duka Sannan kuma tabashi umarnin ya saketa saboda bakin hali da akasha a nono Ran Hakeem tafarfasa yake saboda bakaken maganganun da akejifar uwarsa dasu Hajiya suwaiba tayi salati tasanar da ubangiji tace yanzu duk wannan abubuwan dake faruwa shine ba asanar daniba Ta kalli Hakeem tace yanzu kai Ashe har yanzu baka daukemu da mutunciba Kokana ganin Dan bani na haifi ubanka ba To bari kaji idan bani da iko da kai inadashi da ubanka kuma ai ubanka yana da iko dakai ko To wannan aure bazakayi shiba Kuma maganar saki babushi dole yarinya ta zauna gidan ka Daddyn Hakeem da tun da hajiya suwaiba tafara magana baice komaiba Yayi gyaran murya yace to hajiya naji duk hukuncin dakika yanke Maganar Saki tabbas zai maida matarsa kobakomai saboda darajar 'yar da ke tsakaninsu Maganar fasa aure kuma babushi Ba fashi Idan bazaki matanba alokacin dakika zo da bukatar hada su aure sai da Abba na Allah yajikan rai yafada cewan duk lokacin dayazo da bukatar kara aure bawanda ya isa ya hanashi Sannan kuma koda SON bashida sha awar kara wallahi sai namishi da kaina Saboda kugirbi abinda kuka shuka Hajiya rukayya da Hajiya suwaiba suka kalli juna Daddyn Hakeem yaciga dacewa Narayu cikin maraici tunda natashi bansan dadin uwaba sai na uba ga kuma gallazar matar uba wato ke Hajiya suwaiba narayu a hanunki cikin kunci da gallazawa Kuma.abinda bakisaniba shine kice silar mutuwar mahaifiyata amina bayan ta haifeni kukamata jifa da ciwo da haka har Allah yadau abinsa Kinsan a ina naji kamaku nayi kuna zancen keda Hajiya larai kishiyar ki Nayi kuka kaman raina zaifita Dana ji wannan magana daga bakinki Kunsani maraicin dole kuma kuka kasa rikeni tsakaninku da Allah Ba irin abinda bakuyiba ganin namutu amma Allah yace saina rayu a duniya Alokacin da Allah yabani haihuwar ABDUL HAKEEM nadade ina mishi adduar Allah yarabashi da sharrinku Dan nasan yanzu hankalinku zai komo kan 'Dana Kullum cikin mishi addua a ruwa nake inabashi yasha Wanda nasan ko mahaifiyarshi batasan niyya na ba   Saikuma kwatsam kukazo da gudirin aurawa Hakeem Laila alokacin shekarunsa basu wuce ashirinba kuka dage sai anyi na amince ne saboda wani dalili Dan koda din ma abbana bai aminceba inzaku iya tunawa Saboda haka babu Wanda ya isa ya hanshi aure Idan kunga 'yarku bazata zauna da kishiya you are free to live with her Hajiya rukayya da jike sharkaf da zufa Zatayi magana daddyn Hakeem yadaga mata hanu ba abinda zakice yaya rukayya Hajiya suwaiba ta sauka har kasa tace Dan Allah abubakar kayafe min wallahi duk sharrin shaidan ne hakan bazai kara faruwaba Daddyn Hakeem yace haba Hajiya ai duk da abinda kika min bazaisa nadaina ganin ki a matsayin uwaba Dan haka kitashi daga tsuguna min Hajiya suwaiba tace nagode Allah yamaka albarka kaida zuriarka Hajiya rukayya ma tana kuka taba wa daddyn Hakeem hakuri daddy dayake shiba meruko bane ya yafemata Hakeem ya kalli mahaifin nasa yaga daddy na goge kwalla Bakomai yasa daddy kukaba sai rashin imani irin nasu Idan ya tuna sune sillar rabashida mahaifiyarshi da ko kamannin ta baisaniba saiyaji wani kunci Daddy kasa jurewa yayi yatashi yashige bedroom dinsa Abdul Hakeem yabi bayansa mummy hafsat ma tashi tayi tabisu Hajiya rukayya tabuga tsaki aikin banza wallahi wannan kukan danayi bazai tagi banzaba Hajiya suwaiba tace towayafada miki dama tubar gaskiyace ai kawai ganinayi asirinmu yatonu shiyasa na bullo musu tanan Laila cikin kuka tace yanzu dai kuna gani Hakeem zaikawo wata dasunan mata Suby kanwar Laila ta ce ai wallahi duk wacce tayi gigin shigowa gidan ki anty Laila wallahi taja wakanta balain duniya Dan wallahi sai mun nakasa rayuwarta Hajiya rukayya tace ai zama bai kamamuba Ke Hajiya bari musa driver yamaidake gida Gobe zamuyi nijar saboda ke Laila yau kije kibashi hakuri Kinuna kinyi ladamar abinda kika aikata har dai yasamu yabarki gobe mutafi Laila tace shikenan hajiyarmu Allah yabar mana.ke kina kokari ganin farin cikinmu Nan sukatashi kowa yakama gabansa Laila ta koma part dinsu tazauna tana tunanin abubuwan da suka faru Wanda sana diyarshi allura ta tono garma   **** Laila sundawo daga nijar yanzu tana zaune ne zaman jiran amarya Dan tafara aiwatar da niyarta Hakeem kuwa sake tsarin gidannasu yabayar akeyi badare ba rana aiki ake zabgawa Zama yayi yaga gaskiya a yanzu yakamata dadinsa yadaina fita office Shiyakamata yayi komai su su huta Kuma bashida da sha'awar raba gida da mahaifansa Yayi shawarar dawowa A B U Zaria sunfi kusa da nan Zaisamu daman da dazaije ya kula da harkokin kasuwancin daddynsa Ahmad ma yace shima kawai kadunan zaidawo yacigaba da rike company daddynsa Shiya sama yasa ma aikata gyaran gidanshi na Kaduna Sunyi parking gabadaya zuwa Kaduna Aisha matar Ahmad ta tare a sabon gidanta dake Kaduna   Hakeem ankam mala komai ainda aka fitar wa da kowa dinshi Part din Hakeem yana tsakiyarsu A babban folon PROF zai iya shiga part din kowacce falon nashi guda biyu akwai a sama Wanda idan ka haura sama falon PROF shima daga gefe kuma wasu maka makan bedroom dinshi guda biyune Kai gaskiya dai naira tayi kuka a gidan Prof Gabakidayansu yasakewa was furniture's har daiyayensa Komai yazuba wa Husnah Wanda uba yake wa 'yarsa Prof ya dau nauyin komai Bakin ciki kamar zai kashe Laila amma ba yadda ta iya dole tanuna bakomai saboda tasamu ta cimma burin ta akan amaryarsa   Mummy hafsat gobe zasu daga zuwa Dubai itada mummyn Ahmad Hado kayan lefe ******* Biki ya rage saura kwana hudu Hakeem ne cikin motarshi yana zaune agefen mai zaman banza Yayinda Ahmad kuma yake driving zasu kano gidan su husnah Ahmad yace kai prof gaskiya kacanja wallahi gaskiya Allah yawa husnah albarka data saita mana kai Dafa magana wahala yakebaka amman yanzu sai a zauna dakai asha hira musam man ma na husnah Hakeem yayi murmushi yace kaikuma dadina dakai sa ido wallahi Ahmad yace aidole ne asamaka ido yadda yarinya karama tacanja ka Hakeem dai murmushi yayi yace bazaka kanebane abokina bakasan yadda nakejin babyn a raina bane ko   Ana kiran la asar suna shiga gidansu husnah ya shamsu yataresuda murna yace kaga manyan kannena Ahmad yayi murmushi yace fada dakyau ya shamsu girma fa Allah yabaka Hakeem yace kana mamakine yaya shamsu Ya shamsu yayi dariya yace waneni da mamaki Dan na zama yayan manyan maza Daga shiya shamsun dayayi maganar harsu Ahmad da Hakeem sai da sukadara Ya shamsu yace bissimilla mushiga daga ciki Hakeem yace mudai fara gabatar da sallah tukun Nan suka wuce masallacin unguwar   Husnah zaune itada anty kubra Anty kubra tace Dan Allah husnah kisanar da kawayenki Maganar bikinki Husnah ta yatsina fuska tace nifa bazanyi taroba ma Nibana mason hayaniya wallahi Kuma da kika damu bagakiba dake da anty Aisha kusai kuzama kawayena Kubra tarike baki tace lalle husnah wuyanki ya isa yanka Nice ma zan zama kawarki ko Husnah tace to Baku kuka dage saina aureshi ba Anty kubra tayi murmushi tace aini dadina da gobe saurin zuwa Kaman yaune zakizo kinacemin anty kubra Wallahi inason mijina Husnah tayi murmushi tace humm anty kenan nifa nafada miki auren biyayya kawai zanyi amma ba wai danso ba ai nagama soyayya Anty kubra tace shikenan tunda haka kikace akwai ranar maida martani Anty jumai wacce aka dauko tunda Sudan saboda gyaran amarya tunda akasa bikin washagari ummu tayi Sudan dama can ita mutuniyar cance Anty jumai tadubi husnah tace tashi muje kishiga wankar tunda Hadin yayi awa biyu da shafawa Husnah tace anty wai Dan Allah yaushe za adaina min wannan shafe shafen nan da shaye shayen nan Anty jumai tayi dariya tace sai randa kikabar gidan Kuma kuji dakyau dawasu zaki taki tafi aikuwa Husnah ta turo baki ta tashi taje ta shiga wanka Tana kansaka kaya taji muryar su yayanta da PROF suna gaisawa da umma a falo Tayi niyar kwalliya tafasa Dan mutumin nan yabata tsoro ranar Riga da skirt tasaka nawani tsadaddan net tayi kyau bakadanba Powda kawai tashafa sai man baki Tana kan maida kayanta cikin durowa anty kubra tashigo tace amarya ango nakira yana falonmu husnah ta turo baki tace anty kinfara ko Zanrama wallahi nasan abinda zanmiki kema Kubra tace ya hakuri 'yar kanwata nadaina Dan nasan ki sarai wallahi Husnah tayi murmushi tace a to dole abani hakuri dai Tadauki mayafin kayan tayafa Kubra tace kai husnah kedai komai baki baiwane Wallahi kinwani canja ne fa gabadaya Kinciko tako ta ina Jin abinda anty kubra tace yasa husnah tunani tabbas ko itakanta tasan komai nata yacanja Kuma acikin sati biyun nan da akafara mata gyaran jiki ne To gaskiya bazata tasa gyaleba Ta ajiye gyalen tadauki jibgegen jijabinta Anty kubra tace haba Dan Allah mijinkine fa yazo zakije masa da wannan katon hijabin ai gwamma dai kidau ki mayafin dakikayi niyar sawa Kinga zaisake shiga hanu kafin nan da kwana hudun nan Husnah tace aikuwa kinja ma wallahi rayuwar hijabin zanyi agidansa Ta wuce anty kubra tayi falon Tashiga da sallama ya amsa mata tamkar wani balarabe Kamshin sa yacika falon Husnah tanemi kasa tazauna PROF yakureta da kallo wani kyau yaga tamishi Kaman yau yafara ganinta Husnah tagaisheshi bai amsa ba jin bai amsa ba yasa tadago suka hada ido yakafeta da idonshi Kasan yasauko yazauna yana fuskantarta yace haka ake tarbar miji baby Tayi shiru batace komaiba yace babay magana nake fa Husnah cikin shagwabarta Wanda ita bada niyya tayi shiba tace menama kuma Yace nafarko nace kidaina samin hijabi idan zakizo gurina bakida mayafaine Tace tokai meyasa bakason insa hijabin Hakeem very good question Nafarko inason hijabi amma a muhallin daya dace asaka kaman kiganni da wani ko abokaina da kuma sauransu amma banda dagani saike kisaka Bakisan nazo naganki Dan nasamu nutsuwabane ? Husnah tayi shiru tana wasada da zobenta Murmushi Prof yayi Yakama hanunta tana kokarin janye hanunta prof yacire zoben hanunta Kafin yasaketa aikuwa Husnah ta kalleshi a tsorace tace Dan Allah kayi hakuri kabani zobenan Yace meyasa zan baki tace nima bani akayi Yace wakenan tayi rau da ido kaman zatayi kuka Tace masoyina ya muallim Yace zan baki amman saikinbi maganana kicire wannan jijabin Dan ba anan yakamata kisaba Husnah tace Dan Allah yaya kayi hakuri kabarni da hijabina nariga nasaba Hakeem yace OK yasaka zoben a aljihunsa Yace nawa kike bukata game da events din ki Husnah takalleshi tace nima bana bukatar komai Ya kalleta da mamaki yace saboda me tace bakomai wallahi ni duk wani Abu dayashafi bidia bana kaunarsa Dan Allah yaya daman inason na roki alfarmar events din dakukasa akatin nan wallahi banaso Dan Allah kabarshi kawai   Hakeem yace duk abindakikace haka za ayi amma bashi ne Duk randa kika haifamin baby zan baki mamaki duk abinda ba ayi a bikin nan ba saina yishi Husnah tayi shiru can tace tokabani zoben yashare zancen Yafito da kudi dubu Dari shida ya aje mata yace gasu nasan zaki bukaci kudi banason kitambayi ya shamsu ko Abba Duk abinda kike bukata let me know OK Ya cigaba da kallonta kawai kaman yasami TV Husnah tace maganar zoben Yace sakinyi abinda nace miki Husnah tace nayarda amma saidai nakoma na dauko mayafina Baice komaiba sai binta dayayi da kallo Shigowar husnah Hakeem kusan suman zaune yayi Dan baitaba tunanin abinda idonshi zaiganiba kenan Da sauri yace baby go and wear your hijab please Husnah takoma da sauri Tana shiga dakinta fashe da dariya Dan bakaramin dariya yabata ba Hakeem dafe kai yayi take hankalinsa ya tashi Nan yafara tambayar kansa Meyasa sai akan yarinyar nan yake jin feelings haka Maiyasa komai nata is so special to me Da kyar yaja kafarsa yafita zuwa gurinsu Ahmad da ya shamsu Ahmad yace muwuce ko PROF yace Hakeem yace muje muma su umma sallama ******* Laila takira meenat tafada mata duk abinda kefaruwa aikuwa meenat kaman tayi tsuntsuwa tazo Nigeria Tace kiyi abinki mummy babu matar data isa kiyi kishi da ita wallahi Idan mukazo koni ko 'yar iskar da tayi kasadar auran daddyna Suna gama waya da Mummynta Laila Tadubi Bashir tace kaji kuwa mekefaruwa agidanmu Bash yace saikin fada Takwashe komai tafada mishi Tsaki bash yayi yatashi Yabar gun   Next page Your comments is needed fan's Love u all [05/05, 8:53 PM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Story & written By The special writer UMMU AFAN   FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION (F.C.T.W.A)   HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATION   I DEDICATE THIS PAGE TO YOU Hauwa'u idris ( maman daddy ) Allah yabar zumunci inajin dadin comment din ki Allah yabar kauna keep it up     AKWAI lokaci   PAGE 101to105     PROF yashigo direct dakin amaryar ya wuce sai yaji kofa gam Kuma gashi bashida spire key Duk guda hudun suna hade da juna Ya koma dakinsa yayi wanka Ya koma kan bed dinsa yadauki waya Yasoma dialing din number husnah yayita ringing Husnah bata daga wayar ba Prof yayi mirmushi Wanda shikadai yasan abinda yasashi murmushi Ya rufe ido Dan bacci amma bacci yace baisan zancenba Yadauki wayarshi kawai yakira Ahmad Saida yakira Ahmad sau biyu kafin ya dauka Ahmad yace kai ango yadai kira da wannan lokacin Hakeem yace kai dai bari wallahi man Wallahi yarinyar nan ta kulle min kofa aikafin yakai karshe Ahmed yafashe da dariya sosai yayi dariyarshi Kafin yace amma wallahi husnah ta burgeni Sosai Hakeem yace Dan iska dariya zaka min ko Ahmad yace aikaine abokina duk kabi ka tsorata masu yarinya aidole ta kulle kofarta Dan batasan mezaifaruba idan akabarku Ku biyu Hakeem yayi murmushi yace duk tagama buyanta badai ta shigo hanu ba Zanbata mamaki zata shigo hanu ai Ahmad yace wallahi dai kabi yarinyar mutane a hankali Bafa babbar mace bace Dan nasan kasaba da manyan mata Yayi dariya yakashe wayar shi Hakeem cikin murmushi yabi wayar da kallo Yace zanrama ne Kafin yakoma amma bacci fa yaki Sam Daya rufe ido zaiga husnah alokacin da yake kissing dinta Sai yayi murmushi ya rungume pillow kawai bacci yayi awun gaba dashi Laila duk abinda kefaruwa tana lebe tana gani aikuwa ganin Hakeem ya burda kofa yaji akulle duk ta gani Har wayan dasukayi da Ahmad taji aikuwa cikin farinciki ta koma part dinta ta sanar da su hajiyarta da kanwarta suby Dan basu komaba ita suby auran nata ya mutu shiyasa zata zauna gurin Laila aikuwa cikin farinciki hajiya rukayya tace aikin banza Ashe ma duk abinda suke yarinya bata so Suby tace a a karku manta dama boka yace zai sa gaba a tsakaninsu Watakila aikin ne boka ne yafara aikitakanta Inbahakaba wazaiki yaya Hakeem a matsayin miji Hajiyarsu tace tabbas maganarki hakatake Kunga ganiba gwamma da muka sake mishi kudi gashi anfara aganin cigaba Laila dai da farin ciki ta kwanta abinta zuciyarta fati kal   Karfe hudu dai dai na asuba Husnah tafarka cikin nannauyar baccin da ya dauketa Tashi tayi tashiga bathroom alwala tayi kafin tayi nafilfilunta kamar yarda tasaba ana kiran sallar asuba tayi sallarta tayi adduointa da karatun alkur'ani Kafin tacire kayan jikinta Dan jiya bata samu daman cire kayan ba saboda gajiya Tashiga wanka kafin tafito Spray kawai da shuwa tashafa sleeping dress tasaka duguwar riga abinta tafada gado abinta Sosai taji dadin baccinta Hakeem bayan yadawo daga sallar asuba yasake tana dakin husnah shiru bata budeba Direct dakinshi ya wuce dakinsa Shima baccin yakoma Karfe bakwai da rabi dai dai mai aikin mummy ta buga kofa Suby kanwar Laila ita tabude kofar Taga me aikin mummyn Hakeem ce Tace sannu suby ta yatsina baki yadai ina zaki da basket din abinci haka Tace hajiya ce ta aikeni nakawo ma amarya abin karyawa Suby ta kebe baki tace to aikuma basu tashiba amma kawo saina na mika mata Tabata abincin Suby ta karba tashige dashi part dinsu gurin su Laila da hajiya rukayya Laila cikin murna tace yauwa suby dauko maganin a side drawer kikawo Aikuwa haka suka barbade komai da maganin nan Farfesuf na kayan ciki sai kunun gyada da kosai Kai kuma farfesun ganda Wanda yasha kayan hadi sosai Haka suka bikomai suka badeshi tas Hajiyq rukayya tace maza ke suby tashi kikaimata Laila tace abarta ta kai Dan tanason ganin amaryar Hajiya rukayya tace a a idan kika kai dakanki za azargi wani Abu Zakiganta ai mudai burinmu kawai tabar gidan Suby tace wallahi nimafa basanin amaryar nayi bama dan haushi Husnah cikin bacci taji ana buga mata kofa ta tashi tayi hanyar falonta Tayi kofa tabude sukayi ido hudu da suby Suby sai tadauka kaman gezo idonta suke mata wannan irin zukekiyar yarinyar kuma daga ina Husnah ta ce sannu suby tace ina antyntaki Husnah ta yatsina fuska tace antyna kuma Suby tace ina nufin amaya Husnah tayi murmushi tace OK ai tashiga wanka Tana ganin suby tasauke ajiyar zuciya Husnah ta kibata hanya kuma Suby tace ga shi inji hajiyar yaya Hakeem akawo mata Husnah tace OK angode barin kaimata Suby ta mika mata basket din husnah tarufe kofarta Murmushi husnah tayi ta ajiye basket din ta ajiye kan dining kafin ta koma kan bed koma bacci Sai karfe goma dai dai ta tashi Ta gyara bedroom dinta da falonta ta badeshi da kamshi Ko ina yadau kamshi kafin tashiga bathroom tayi wanka tafito ta shirya cikin wani tsadaddar super Holland dark blue sai adon pink ajikinsa Yadda dinkin yazauna ajikinta shizaifi Baku sha'awa sosai das yamata dinkin ma kawai a in kallone Matsalarta daya bata son dankwali ta tace gashinta takama da ribbon pink Kafin ta murza daurin Dan kwalinta abin wuyanta ma pink ne Gaskiya husnah tayi kyau matuka Tadauki ta kalminta plate shoe tasaka Har ta zauna zatafara break fast saikuma taga rashin dacewar hakan Bata je tagaida mummy ba Gyalenta tadauka maishegen kyau tayafa Pink colour Tafita tayi hanyar kofarta tasaka key ta kulle Bayan ta fita Dama dole saitabi ta main falonsu gabadaya tana fitowa kuwa taga mutan gidan gaba dayansu a falo To itabasaninsu tayi ba Ganin harda manya yasa husnah ta durkusa tana gaida su hajiya rukayya da kuma Laila Laila ta watsa mata harara Wai ita hakimar bata fitowa ne saike Hajiya rukayya tace inazata fito ansamu duniya An auri mekudi an asirceshi Suby ta kalli husnah tace 'yar buzuwa kotafiya za ayi ne Husnah ta kalleta tace inje ina ai munsamu gida nida antyna Dan nadawo kenan gwamma muma muzauna muci arzikin Dan da alama bamu kadai bane 'yan cin arzikin Husnah tana gama yada musu magana tayi waje abinta Har suby zata bita hajiya rukayya tace a a kyaleta kar ajimu tun yanzu mana Laila race lalle ma Dan talaka be iya samun wuriba Wannan zakewa haka harda dauko 'yar riko To wallahi wannan yarinyar kamar aljana bazata tazauna min agida wallahi Kalli yadda take tafiya kamar wata 'yar sarki Hajiya rukayya tace aibakisan halin talakabakenan idan yasami guri Kuma ke Laila da kike cewa bazata zauna ba yayar tata ma ba zaman zatayi balle ita 'yar cin arziki Nan dai suka muna funcinsu Husnah tayi sallma a falon mumy shiru ba kowa Ta nemi guri tazauna a tafkeken falon su mummy Mummy ta sauko daga sama bata lura ba harzata shige kitchen Husnah tayi saurin sauka kasa tace mummy ina kwana Mummy hafsat tajuyo tayi tazali da surukar tata Tace a a husnah ai ban lura bama meyasa kika zauna nan baki haura saman ba saikace bakuwa Husnah tace bakomai mummy nan ma yayi Mummy hafsat tace a a nan gidanku ne ko ina zakishiga Kina da damar hakan kinjiko Ya bakunta husnah tayi murmushi kawai batace komai ba Mummy tace kinci abinci ko husnah tace yanzu zanje nayi Kafin mummy tayi magana Abdul Hakeem yayi sallama yashigo wata tsadaddiyar shadda milk colour sai wata hadaddiyar hula da ya murza akansa Wanda yasake fito da kyakkawar fuskarshi mai kewaye da kwantacen saje dayakarawa fuskar tashi kyau Gaskiya PROF Fa kyakkawar mutumne bankarya Yashigo idonsa yakai kan Husnah dake zaune kan kafet Wani farinciki yaji sosai Ya kalli mummy Yace mummy na antashi lafiya Mummy tace lafiya kalau son maza kuwuce dining kawai kuyi break idan kungama kukirani zanje nayi salar walha Hakeem yace angama dalibata Mummynsa tayi murmushi tace a a tun yaushe daliba ta canja malami ai Hakeem yace amma tunda yanzu nadawo gida Sai kisake sayan form agurina Husna da mummy sukayi murmushi Mummy tace kaga idan nabiye maka sai lokaci ya wuce banyi sallar ba Ta kalli husnah tace 'yata tashi kije dining kinji kikarya abinki kinji Ina zuwa yanzu Mummy tayi sama tabarsu anan Hakeem yakure wa husnah ido yace wana kama Husnah ta saukar dakai kasa Hakeem shima zamayayi shima tabayanta yakamota yasakalo Kansa tagefen wuyarta hanunshi yakai cikin rigarta ta yashafo cikinta Yace bakice abinciba baby jicikinki fa kaman zai hade da baya Itadai husnah wani iri takeji tabatan dayakeyi Yace tashi muje nabaki abinci banason musu Cikin shagwaba husnah tace ni anan zanci ba a dining ba Prof yace angama baby dakanshi yatashi yakawo musu komai plate daya yazuba musu Yace oya bude bakin bayan yadauko kofin kunun gyada tace dakaina zan sha kabari kawai Yace bason musu fa Badan tasoba tabude baki yabata Nan yabata farfesun ma kosai da duk wani abin dake gun saida yashiga cikin husnah tace mishi ta koshi yaki Yace daman ya shamsu yamishi bayanin bata cin abinci Cikin shagwaba husnah tace wallahi inaci kuma nakoshi sai da yaga tana shirin dawo Dana cikin nata yabarta haka kafin shima yafara cin abincin Bayan yagama ne yasa hanu zai dauke tiren abincin husnah targashi yace yadai yakureta da ido Tace kabarshi kawai zankai Bai hanataba husnah tadauka tayi hanyar datake tunanin nan ne kitchen din Tana zuwa ta ajiye a sink din wanke wanke ta wanke tas duk wani abin da za a wanke saida ta wanke Shikuma prof be biyo sa wuba saboda yana waya ne Mummy tasauko daga sama tagashi shikadai ne a falon Tace a a asmaun Hakeem yayi sallama dawani abokinshi yace tashiga kitchen Kai kwanuka Mummy taleka kitchen dintaga ko ina tsaf an goge Mummy tace kai haba husnah da kanki Aida kinbarima yanzu mai wankewar zatazo yau tayi ranar dawowa ma Husnah tace bakomai mummy Mummy tace maza jeki huta kafin nafito Husnah tayi murmushi tace a a mummy meza adaura Dan naga kaman abinci kikeson daurawa Mummy tace a haba dai daga zuwa harkifara shiga kitchen a a jeki huta Idan kunyi sati saikifara dafa abincinki Husnah tace mummy kigafarceni amma banzan taba zama inga kina shiga kitchen Yakamata kema kihuta Dan Allah Tunda na taso agidan mu Nina ke abinci umma ta na hutar da ita saboda haka Dan Allah mummy kibari na ringa miki abinci kihuta kema kisan kinada yarinya a yanzu Cike da mamakin kalaman husnah mummy tace lalle husnah kin haifu Allah ya wa iyayenki albarka dasuka miki tarbiya maikyau Nagode da kika daukeni matsayin uwa Allah yabaku zaman lafiya keda mijinki yazaunar daku lafiya kinjiko Husnah kai akasa tayi shiru Mummy tace na'amince zaki rinkawa mummy abinci amma fa mummy ma tayi alkawarin satayi sati kina cin abincin mummy kinjiko Saboda haka kibar mummy tacika alkawarin ta Husnah tayi murmushi kawai kafin tayi magana Hakeem yayi gyaran murya mummy da husnah suka kalleshi Mummy tace wato labe kake mana ko Hakeem yayi murmushi yakaraso cikin kitchen din Yakama hanun mummy yace haba mummy please kibar yarinki tasamu ladarki Allah ne ya amsa adduarki yakawo mana husnah cikin rayuwar mu Kinji mummyna Mummy hafsat tayi murmushi tace shikenan tunda kunmin yawa Allah yayi albarka amma bayanzu za adaura abinciba sai yamma idan anyi la'asar Yanzu muje kawai muyi hirar mu Mummy taja hanun husnah wacce tunda Hakeem yashigo takasa magana Ranar dai a sashin mummy husnah ta wuni sai da ka kira isha tabar dakin mummy ganin Hakeem da daddy sunfita sallah Mummy tace yau husnah Allah yatashemu ki huta gajiya ko Ita mummy a tunaninta husnah zata je tashirya ne kafin mijinta yasameta Husnah kuwa tashiga falon taga Laila da suby a zaune Ta wuce abinta batareda ta kalli kowa ba aikuwa suby tace ke zonan Kojuyowa husnah batayi bare ma tasan da ita sukeyi Ke 'yar talakwa bakiji menace bane husnah tayi banza dasu kafin suby ta karaso husnah tashige ta banko kofarta tasaka key Direct wanka tafara kafin tayi sallah tayi karatun ta data saba Suby tace anty anya kuwa ba wannan aljanar yarinyar bane kishiyarki kuwa aikuwa jitayi Laila ta zabga mata mari Suby tace mena miki anty Laila Cikin tashin hankali Laila tace damme zaki min wannan mugun fatan Taya za ayi yaje ya auro 'yar cikinsa Bama hakaba idan yakasance wannan yarinyar ce ai yayi abinkuya Nikuma nashiga uku taya zafara kishi da wannan yarinyar Suby tace aiko dai koki kokiso itace Dan agabanki tasa mukulli ta bude sashinta kuma dazu Dana kai mata abincin ma ita nagani kawai raina mana hankali take Laila ta daura hanu akai tace nashiga uku ni Laila wannan ai inaganin ko meenat ma ai tagir meta Lalle Hakeem yacuceni Yanzu sakayya da zaimin kenan ya auro 'yar cikina inyi kishi da aita ina Sam bazaiyuba wallahi Suby tace wallahi idan kika bari aljanar yarinyar tazauna agidan nan Zikidawo jaka wallahi Dan abinda kike samu bazaki samu ba Yarinya kaman ita tayi kanta Dan kyau tahada komai da d'anamiji yake bukata Laila tace ya isa haka suby zakisa zuciyata tafashe kibarni naji da Abu daya Dan Allah   Hakeem yashigo falon da sallama Laila ta taso sannu da zuwa baban meenat Hakeem yace yauwa yashige bedroom dinshi Dan karya taba kofar husnah yaji akulle agabasu su fahimci wani Abu Laila tabishi har yafito Daga wanka yana yashirya ya kwanta Laila taga bashida niyar kulata yasata ce baban meenat har yanzu fa bansan kanwartawaba Sai kanwarta muke ta gani tana shige da fice Hakeem yayi murmushi Dan ta tabo inda yake mishi kaikayi Yace kanwa kuma ai bata da kanwa itadai wacce kikagani din itace amaryata aikuwa Laila ta tashi tace amma wallahi kaji kunya Hakeem yanzu da girman ka da darajarka zaka auro 'yar cikinka wannan ma ai zubda mutuncin Kaine da zubar wa 'yarka da mutunci Prof baki kawai yasake kallon ta Yayi murmushi yace kinyi sake maman meenat da kika auri mijin asmau saboda yanzu nasan nima namijine kuma na auri dai dai Dani kije aduba miki nidake bamu taba dacewa ba kuma bazamu daceba Meenat da Allah yabani na karba kuma inason 'yata Idan tazo ruwantane taso matata ruwantane takita amma zanfada miki wannan Kalmar mummy da daddyne kawai bazan iya rabuwa dasu ba saboda husnah Amma bayansu zan sabama kowa akan matata so get out of my room Cikin tashin hankali Laila tafito Daga bedroom din Hakeem Kuka sosai taci suby nabata hankuri **** Bayan sati uku Hakeem ya Dade da komawa aikinsa gashi aikin yamishi yawa ga kullum tunanin husnah ne da sha'warta acikin ranshi Ba inda yake samun ganinta sai a part din umma Dan Anna take wuninta Tana fita sallar isha zata gudu Hakeem zaune kan kujerar office dinsa Ahmad kuma yana cike wani file's Ahmad yace yauwa kagani ko yana nuna wa Hakeem abinda yacike amma hankalinsa baya taredashi Ahmad yace wai meke faruwane Prof Hakeem yayi murmushi wallahi baby ce take bani ciwonkai Taki bari na rabeta Sam wallahi Bana ganinta idan ba a gurin mummy ba Ahmad yace zanbaka shawara idankabi yau din nan kadaina damuwa Hakeem yabada hankalinsa sosai Ahmad yace bakace agurin mummy take wuniba prof yace a Ahmad yace sallar ishar dazakaje yau kabari kawai kamuku jam'i Kana shiga kacewa mummya da daddy da ciwon kai kadawo Idan kaga zata tashi saikace jirani mutafi tare agaban mummy nasan bazatayi musu ba Hakeem yace kuma wallahi sai dai kuma yau laila ce da kwana Ahmad yace saikayi hakuri yau da gobe ai duk dayane yayi dariya Hakeem yace a a baduk dayabane wallahi kai bakasan halin danake cikibane shiyasa Ahmad yace kai haba mai mata biyu fa amma kana fadin haka ai saika kabani tsoro nakasa kara tabiyu Hakeem ya harareshi   Husnah falonta suna waya da ummanta da ya shamsu da anty kubra Bayan sunagama wayarne ta dauko mayafinta zata koma banngaren mummy Sai taji Laila tana waya amma bata San dawa take ba Laila tace dadin abinma fa yarinyar baso shi take kullum a dakinta take kwana amma wannan aikin bokane yace bazai taba bari harya kusanceta ba Yanzu fa kusan sati uku kenan amma suna wasan buya bata ma bari yaganta Shikuma na mamajo kina gani shi kisan yana cikin damuwa Can ta matse mishi kinga haka malam zaicire mishi sonta aranshi kwatata Dan nima yace karnabari ya kusanceni har sai yarinyar tabar gidan Kinga kuwa ai yana cikin matsala dannima bana zuwa bedroom dinsa harsai ranar da wannan aljanar yarinyar tabar gidan Nan dai sukayi sallama da kawartata Ta kalli suby tace insha Allah saura kiris yarinyar nan tabar gidan nan Daga nan kuma sai mufara shirin yadda zamuyi mukasheshi idanba haka ba wallahi wata zaisake hangowa Suby tace wallahi da dai yafikam Dan wallahi nima inason naga munfara fantamawa fa anty Laila tace kidai yishirunki kawai saura kiris Husnah toshe baki tayi sai kuma wani jiri data ji yana dibanta dakyar tasamu takai kanta kan kujerarta Tace innalillahi qainnairraihirraju'un nashiga uku meya musu suke son kasheshi Gaskiya bazantabari kuyi nasara da yardar Allah Kuma mijina zaisamu abinda yakeso insha Allah Allah yakaimu gobe nashiga ukuna ni husnah wani irin zunubi na daukarwa kaina Tabbas yaya Hakeem bai can canci wannan sakaiyar daga garaniba kayafemin Dan Allah duk da banasonka nayi alkawarin faranta maka kamar yadda kake faranta mana nida iyayena Duk wannan maganar da husnah take yi tanayinsane itakadai Hmmmmmmmm Next page Your comment is needed fan's. Love u all Duk wacce bantaba bata page ba Tayi comments mezafi next page natane [05/05, 8:53 PM] UMMU AFAN : BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Story & written By The special writer UMMU AFAN   FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION (F.C.T.W.A)   HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATION   I DEDICATE THIS PAGE TO YOU BINTA ADAM (MAMAN IMAM) COMMENTS DINKI YANA SANI SANI CEWA NIMA WATACE SO PLS KEEP IT UP INA ALFAHARI DAKE ❤     AKWAI LOKACI     PAGE 96 to 100     YAU take asabar daurin auren prof da husna Wanda za adaura karfe uku na rana saboda bakin da zasuzo daga kasashen waje saudiya da sauransu Duk Wanda baisamu yakaraso tun juma'a ba saboda wani uzirin Shine aka daga daurin auren   Kuma a yaune ake kai za akai lefe gidansu husna anasu aladarkenan Mummy hafsat ce zaune cikin kawayenta matan mayan mutane Da kuma 'yan uwa da abokan arziki Kowa taganta yasan tana cikin farin ciki Mara misaltuwa Ana ta kallon lefen Hakeem Wanda za akaima husnah anata yabawa Mummyn Ahmad tace kafin atafi kai lefen yakamata akira uwargida tazo taga kaya ko   Mummy hafsat tace to akirasu mana Dai dai lokacin Aisha matar Ahmad tashigo da daukar wayarta data saka caji Dan tunda aka fara hidam bikin nan agidan mummy take kwana Mummy hafsat tace yauwa 'yar albarka mazaje kicewa su Laila suzo zuga kaya Aisha tace to mummy tayi part din Hakeem tashiga part din Laila anan ta tarar da suby kanwar Laila da hajiya rukayya da hajiya suwaiba da ita Lailar kanta Sai kuma kawayenta Aisha ta gaishesu bawanda ya kalleta suby kanwar Laila ce tace dalla malama meyakawoki nan Aisha tace to bani nakar zomom ba nima rataya akabani Hajiya rukayya zatayi magana Laila tace yishiru kawai hajiya bake yakamata kimayar mataba Suby tace kema anty bake yakamata kibata amsa ba nice dai dai da zamaninta Aisha dadina da jaki duk yadda akayi da shi saiyaci kara To nima bazuwan kaina nayiba mummy ce tace kuje kukaga kaya Dan za a wuce da shi Tajuya tayi waje abinta aikuwa Laila ta mulmulo zagi tabita da shi Hajiya rukayya ta yi saurin rufe bakin Laila tace ai banso kukayi sainsa ba Kunga idan muka ki zuwa ganin kayan zasuyi tunanin har yanzu akwai Abu akasa Kunga kuwa ida suka gano mu ai akwai matsala Dan haka ke Laila kidaure mutashi muje kinuna bakomai azuciyarki Suby tace kuma fa hakane hajiya gaskiya kin iya taku mai kyau Hajiya rukayya tayi murmushi tace kutsaya sanya yara Nan sukayi part din mummy aikuwa ganin irin mutanen da suke cikin makeken falon daddy suncika shi dam Duk wani dakuna na gidan suna cike da 'yanwan da kawaye dakuma makota   Wani katon bakiciki ya lullubesu su hajiya rukayya amma Sai suka make Hajiyar Ahmad tace sannu Ku da shigowa hajiya rukayya tayi taken dole Idon Laila yakai kan wasu maka makan tsadaddun akwatuna tagani tsakiyar falon akalla zasu kai goma sha takwas Nan Mummy hafsat tace kumatso kuga kayan mana nan suka shiga kallon aljan nar duniya duk akayan bakaramin zani Karami aciki shine 25 thousand Banda sarkoki masu tsadar gaske ga takalma da jakankuna suma awani jibgegen katon jaka aka narko su Jakar kanshi abin kallone Mummy Ahmad tashiga musu bayani kayan tace wannan shabiyun dakuka gani gefe shine Wanda ango yayi wannan kuma Wanda hajiya tayi ne Hajiya rukayya da Laila suka hada ido Tsaban bakin ciki sunkasa magana ma Dan haushi duk yadda sukayi kar agane su sunkasa Mummy hafsat murmushi kawai takeyi tace wa hajiyar Ahmad Yakama ta kukai kayan nan lokaci karyawuce Hajiyar Ahmad da wasu daga cikin kan nan mummy hafsat saiwata kawar mummy Suka tafi kano kai kaya kuma suzasu dauko amarya   Laila kuka take sosai bayan sunkoma sashin su Hajiya rukayya tace lalle hafsat tacika Mara mutunci kuma zan nuna mata nice gaba da ita aduniyar ma Zata kwashi kashinta a hunu Suby cikin bakin ciki tace ai ba ita kadai bace munafukar Kinga dukiyar da ya kashe a lefen Hajiya rukayya tace nashi shabiyu na hajiyar itama ta wa maryar shida Kuma wallahi duk kayan ba na nan kasar Suby tace wai wannan amaryar ma 'yar gidan uban waye ita da har suke rawar jiki akanta Hajiya rukayya tace talakawa ne futuk Dan a yadda nasa aka min bincikema gidan dasuke ciki shiya saya musu Laila ta ce nashiga uku hajiya yaushe rabon Hakeem yabaki ko naira Dari ne amma shine har da siyawa sirakanshi gida gaskiya saina kashe yarinyar nan Hajiya rukayya tace kedai kidaure kawai musamu bukatar mu ta biya Tana cin abincin nan fa shikenan Taya zata ci abinci saikin nuna mata bakomai azuciyarki   Laila tace kodan burina yacika ma zanyi kokarin ganin komai ba komai bane Suby tace wai fa harda mother's nigh mummyn Hakeem tahada Hajiya rukayya tace munafuka ba kinsan dama tace Sai zaisake aure zatayi biki   ***** Umma da mutanenta suka hadu suna ta karbar bakin 'yan kawo lefe su hajiyar Ahmad kenan Sosai sunji dadin karbar da aka yi musu daki guda aka ware musu ga kayan ciye ciye nan burjik Sai Wanda suka zaba Husnah kuwa tana nan zaune kan gadonta cikin wata kwalliya ta musamman Wanda aka dauko mai make up Husnah tayi kyau shar da ita Cikin wata rantsatstsiyar less Golden colour ga sarkarta mai tsada shima Anty kubra ce zaune gefenta da Aisha matar Ahmad Dan itama tabiyo masu kawo kaya Aisha tace gaskiya Laila zatayi hauka idan taga husnah ce kishiyarta Kubra tace kaman yaya Aisha tace to ai banbanci tsakaninsu a bayyane take Wallahi kubra koni danake mace bana gajiya da kallon wannan tsadaddiyar amaryarmun anty kubra tayi dariya tace gaskiya dai kam Husnah mace ce wallahi Wani lokacin sainaji dama husnah bamai mata ta aura ba saboda gaskiya dayar zata iya cutuwa Aisha tayi murmushi tace hakane kam Sai kuma Allah yasa itadin dai rabom ce Husnah dai batace musu komaiba tana ta shashshekar kuka ne ma tunda dataga dai tabbas auran za amata Wayar husnah tadau kara ta tsinke bata daga ba Aisha tasa hanu tadauki kiran Tayi sallama Hakeem yace wacece Aisha tayi dariya tace ango kasha kamshi wato ma harkagane ba ita tadau wayarba To Aisha ce Hakeem yayi murmushi madam dakanta kenan yace ina babyn Aisha tace gaskiya baccima take saboda ciwon kai Yace what meyasa bata fada minma Ganin nan zuwa Aisha tace haba dai cikin matan zaka shigo yace mata ko iyaye da 'yanuwa Naki wasane Ku kulamin da ita kafin nazo Aisha tace Dan Allah kabari a daura saikazo kaga mutane sun ragu Hakeem yayi murmushi yace kanki akeji Ya kashe wayarshi PROF yakalli Ahmad dasuke cikin tarin abokansu larabawa da turawa dama dai 'yan kasar baki daya Yace zanje inazuwa yanzu Ahmad yace zakafara ko Gaskiya ba Inda zakaje Sai andaura auran nan my sallami kowa Hakeem yace kafahimceni wallahi ko na zauana bazaku gane kainaba Idanba naje nadubo babyna naba Ahmad yace aidai idan kayi hakuri gidanka za akaita yau ko Duk yadda Hakeem yakai ga son zuwa gurin babynsa Ahmad yahana Haka ya hakura kawai amma zuciyar nawurin amaryarsa   3 : pm dai dai aka daura auran PROFESSOR ABDUL HAKEEM ABUBAKAR SHUAIB DA AMARYSA ASMAU SULAIMAN SHAMSUDEEN Wanda yasamu hallartar duban jama'a suka shaida daurin auran Ana gama daurin aure ango yafara gaisawa da mutane Wanda suke mushi fatan alkairi Sosai yake tajida jama'a kansa yayi zafi sosai Su daddy ma sun wuce Kaduna shida abokansa da kuma daddyn Ahmad Da kyar Hakeem yasaci idon Ahmad yayi gidansu Husnah Yana zuwa gidan yakira wayar Aisha matar Ahmad Yace please Aisha yaza ayi naganta Aisha tace barin zo saikashiga ta falon kubra amma fa Sai dai kashiga ciki Dan bacci take Hakeem yace OK ganin nan zuwa Yafita yashiga har dakin husnah anty kubra ta mishi sannu dazuwa suka gaisa kafin tafita itama Ya kalli gefen da husna ke kwance Hakeem yace baby meyasa baki fada min kanki naciwo ba Tayi shiru yace OK bazakiyi maganaba dama zoben ki na kawo miki Yana fadar haka Husnah tamike tace ina yake Dan Allah Tashin datayi dasauri Hakeem yazuba wa kyakkyawa fuskarta ido Shifa gani yake kulum karawa yarinyar nan kyau akeyi Sosai tamishi kyau Yace kinaso tace a Dan kabani Hakeem yaci fuska yace zoki karba aikuwa husnah bata kawo comai a rantaba ta tashi taje gaban prof Dan dama ta kunce daurin da akayi mata gyalen ne kawai akan lallausar gashinkanta daya sha gyara Sai kamshi yake fitarwa Gata ita kanta wani kanshi take fitarwa na musamman Tana zuwa kusa da Hakeem tamika hanu yabata bakin lallen da aka zana mata da ja Wanda yasha stone mai kyalli Hanun nata yabida kallo Husnah batayi tsammaniba kawai tajita ajikin mutum ya rungumeta tsam ajikinshi kaman zaimaida ita ciki Tabude baki zatayi magana ya hada bakinsu guri daya Tayi ta kokarin ta kwace kanta kar ashigo asamesu haka amma takasa Dan Prof namjin gaske ne aikuwa bai kyaletaba Sai da yaji wayarsa tana kara yanasaketa Husnah tadurkushe agurin datake Hakeem Ahmad yagani yake kiransa Yadaga yace wai ya akayi kuma Man Ahmad yace wai Dan Allah ina kayi Hakeem yayi wani murmushi kaman Ahmad nakallonshi Yace ganinan ina tare da matata Ahmad kai amma wallahi baka da kyau yanzu Sai da kaje zaka samusu yarinya agabako Anya kuwa prof zakabari sukawo maka itakuwa Hakeem yafashe da dariya yace gaskiya dai daza a mun adalci da anbani matana munwuce Ahmad yace lalle angon karshen zamani To Dan Allah yafito su shek zasu koma kuma suna son kuyi sallama Hakeem yace OK gani nan zuwa amma fa kan katse min hanzari wallahi Ahmad yayi dariya yace to sabonshiga Suka kashe wayar gabadayansu Husnah kuwa tunda ta durkushe agaban prof takasa tashi Tayi tayi ta tashi Amman takasa saboda bakon alamarin da prof yazo mata da shi Jikinta bari yake sosai Dan wani tsoron prof nema yakamata Shima durkushewa yayi gabanta yakamo hanunta yazura mata zobenta Kafin kuma yadago habanta suka hada ido Husnah tasaukar da nata kasa Hakeem yace I love you baby Kikula min da kanji kinji ko Bata dai bashi amsa ba saboda kunyarsa datakeji Ya manna mata kiss a goshi Ya tashi zai bude kofar kenan husnah tayi cewa Dan tsaya Dan Allah batareda ta kalleshiba tayi maganar Cikin mamaki Prof yajuyo yazuba mata ido ta tashi tadauko hankacif tabashi batare da tayi magana ba Tanuna mishi madubinta Bai ce komaiba yakarasa gaban dressing mirror dinta aikuwa jambaki yagani duk lebensa da kumatunsa Murmushi yayi Wanda yakara wa husnah tsoron shi Ya goge kafin yajuyo yakamota yace meyasa bakya son nafita ahaka Kowa yasan daga wurin matata nafito kobahaka bane Kuma ma wannan dadewar danayi agunki kowa yasan hakan saiya faru Husnah tadago fuskarta ta kalleshi kaman zatayi kuka Tace yanzu harsu umma ma sun San hakan Hakeem yayi murmushi yace duk Wanda ke cikin gidan nan Sai yayi zaton haka Toke meye na damuwa mijinkine fa Husnah tace nashiga ukuna Dan Allah kafita karsu shigo Hakeem yace inzan kwana anan bamai shigowa kowa yasan ina ganawa da matata ne Husnah kuka ya gangaro mata Tace wayyo Allah na Hakeem yace matso kusa da ita shima zaman yayi bakin gadon hawayenta tas saida goge mata su da harshensa Yace bana son nasake ganin kuka a wannan kyakkyawar fuskar Ya tashi ya wuce yabarta da kunya Dan idan duk ansan meya mata ai tashiga uku da wani idon zan kallesu ni husnah   Ganin fitan Prof yasa su anty kubra suka shigo dakin Anty kubra ta kalli husnah data kasa hada ido dasu Kubra tace har yafita kenan tanafada tana dariya Husnah tasaukar da kai kaman munafuka Aisha tace kai anty kubra wannan sa ido haka Anty kubra tayi dariya kitashi yanzu za ashigo asake miki make up saboda yanzu za awuce dake aikuwa husnah ido yayi rau rau jin za a wuce da ita Anty jumai mai gyaran amarya tazo tadauki husnah suka wuce zuwa bedroom din umma anan za amata kwalliyar tafiya gidan angon Aisha ta kalli kubraa tayi dariya tace wallahi na tausaya wa Husnah Dan daga ganin yadda Prof yake bare bare akanta basauki Anty kubra tace ai wallahi naga alama Sai dai muce Allah raba lafiya Dan nan da wata Tara suna zamu je Kaduna Kuma gaskiya husnah tayi dacen miji Allah yacika wa yayanta burinshi Kullum acikin addua yake Allah yabawa husnah mijin da zai kaunaceta tsakaninshi da Allah Aisha tace aikuwa dai addu'arshi taci Dan professor Hakeem badaga nan ba wallahi   Bayan angama gyara amarya tafito tayi shar daita Anty jumai ta kamota zuwa falonsu anan umma takara mata fada sosai tareda mata gargadi takula da ibada addua Umma saidatayi kukan rabuwa da 'yatata guda daya Abinda yasake ba husnah kuka kenan ma Sosai sukayi kuka da kyar aka rabasu Ya shamsu shiya rakata har mota Kafin yamata rada a kunne Saiga husnah tana murmushi da haka su hajiyar Ahmad suka shiga mota tadaga zuwa Kaduna   ankai amarya bangaren mummy hafsat aka ajiyeta sai dare za amikata sashenta Karfe takwas na dare akafara mother's night sosai Mummy hafsat tayi barin kudi Dan bakaramin kudi daddyn Hakeem da Hakeem dinkansa suka kashe mata ba Anci ansha ansa albarka Washagri kuma walima aka yi namaza daban na mata daban Inda aka gayyato manyan malamai nakasa dama kasashen ketare Karfe Tara na dare aka mika husnah sashin uwargida Da kyar ta danne zuciyarta duk da bata ga fuskar amaryarba saboda tana cikin lullubi Mummy hafsat dakanta taraka husnah zuwa part din ta darakiyarsu anty kubra da Aisha matar Ahmad Sai datasa husnah tayi addua sannan kuma tashiga dakinta da kafar dama Har bedroom dinta akaita mummy tazaunar da ita bakin gado Kafin nan tace wasu anty kubra sutayata hira Mummy tamusu Sai dasafe tafita zuwa part din ta   ***** MEENAT zaune abi duniya yadameta Wai yau ake auran babana dawata 'yar iskar Gashi kwatata bata gane kan bash Abinda yakemata duk ya daina shi bazai yi hira da ita Sai takama tarasa meke shirin faruwa da itane   Mummy bash takasa gane kan yaronta tunda aka yi auran Dan ita dama ba ason ranta yafasa auran husnah ba Kawarta ce tabata shawarar tsayawa da addua Allah ya karkato mata da kan danta lafiya Sadaka gidan marayu gajiyayyu bainda bata kai sadaka Ga azumi datake Cikin ikon Allah kuwa addua tasoma karbuwa Dan jiya wuni bashir yayi waya da 'yan uwansa Meenat takalli bashir tace uncle yashe zamu zamu koma gidane tunda har gashi mun wuce lokacin damuka tsara Bash yace Sai lokacin danaga dama zata sake magana ya daga mata yace ya isa bana son surutu shasha kawai wuce kibani guri Da gudu meenat tayi bedroom tafara kuka tace nashiga ukuna kar dai bash yadaina sona   Abinda zai burgeku daya ne Ahmad da ya shamsu sune suka rako Hakeem dakin amarya Ya shamsu yayi addua kafin kuma yamike tsam ya kalli kubra madam muwuce ko Ta tashi Aisha ganin Ahmad yatashi suka fito atare Hakeem yarakosu har gate Husnah tana ganin fitansu ta tashi tasawa kofarta key a kofarta Tayi bedroom dinta ma tasa key   Next page Your comments is needed Fan's Much love to your comments

Post a Comment for "AKWAI LOKACI COMPLETE HAUSA NOVEL"