Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Allah Ne Shaida Book 2 Complete Hausa Novel

Allah Ne Shaida Book 2 Complete Hausa Novel ALHAMDULILLAHI NOW I WILL BE CONTINUE IN MY NOVEL ALLAH NE SHEDA 2, Special tnx to my fans Allah yabar xumunci daso da kauna. GOLEN’S WRITERS ASSOCIATION Dedicated to my sweet and dearling husby Bamalli ustax. WRITING BY XEE’ABU SAFANA MRS’SALIHU BAMALLI USTAX.   UMMA ta cigaba dajan hannun taslima ita kuwa kuka kawai take rusawa dakyal sukabar kauyen roni, suka hau motar jigawa, Around 9pm suka shiga tasha babu kowa sai masu gadi wata rumfa dake chan gefe umma tajata suka tafi randar ruwan data gani a gefe ta bude tare da debo musu sukai alwala sallar magruba da isha sukayi suka cigaba da zama a gurin kowane da abunda yaje sakawa a zuciyarsa a haka sukaga safe, umma tace’ yanxu yah zamuyi gashi bamuda kowa ina zamuje sanin datayi umma batajin duk abunda zata fada hakan yasa tajawo hannun umma suka nufi inda taji wani kwandasta nata fadin Abuja! Abuja!! Yana ganinsu yace” hajiya Abuja zakuje? Eh chanxamu Toku shiga yanxu motar zata tashi kushiga muje, Babu bata lokaci motar ta cika suka wuce” sai a yanxu take ganin kamar tayi kuskuren cewa suje Abuja, to wama sukeda shi a abujan? Doguwar tafiya sukai sannan suka isa garin Abuja inda kowa yasauka dole suma suka sauka, umma ce tace”taslima ga gurin siyarda abinci chan bari nasiyo mana, a’a umma muje tare to tace” tareda kama hannun taslimar da zummar su tsallaka titi. Horn ake danna musu da karfi wanda ya gigita taslima ta fara kokaarin jawo hannun ummar ita kuwa umman inah! Batajin komai, ita kuwa datake jin horn din gashi bata gani basuyi aune ba motar tayi gaba dasu, Da sauri matashiyar yarinyar ta fito wacce bazata wuce 16 years ba a rude ta nema taimakon mutane aka saka mata su a mota medical hospital ta nufa dasu aka karbesu emergency aka shiga dasu, Duk wani abu daya kamata ayi tabiya akayi kiran mamanta taga yana shigowa wayanta da sauri ta daga tareda fadi”momma na akwai problem na kade wasu matane ina hanyar dawowa gida yanxu haka ina medical hospital. Ayyah! Gani nan zuwa kijira ni”to saikin zo, A lokacin da momma tazo yayi dai’dai da fitowar doctor dan haka office suka bias bayan ya zauna yake musu bayani, Karku damu jikin nasu da sauki ita yarinyar ne sai zuwa gobe zata farfado, but dattijuwar kuma kanta ne yadan bugu but munmata dinki itama at any time zata iya farkawa, kuje gida kawai hajiya zansaka nurses su kulada su, A’a doctor its not better’ momma kije gida ke nizan zauna nakwana dasu insha Allah tunda dama gobe weekend ne kinga bazanje school bad an haka kije, momma. Ba musu tace” to dan haka ta wuce, bayanta koma gidane tasaka driver yakawo musu abinci da ruwan zafi, Idonta biyu ko kadan babu alamar bacci a idonta umma ce ta fara farkawa da salati dasauri ta matso kusada umman tana mata sannu! Cikin mamaki umma take kallonta domin jintana jin abunda take cewa ita kuwa sannu tacigaba dayiwa ummar tare da cewa”niceh na kade kuda mota sunana yusra dan ALLAH ku gafarce ni tsautsayi ne. Ita kuwa umma farin cikin take da hamdalah domin jinta yadawo tanajin komai, dagama yusra kai tayi, Tea ta hadawa umma mai kauri ta tayarda da ita tana bata ciki kulawa tsaf! Umma ta shanye tea din dan haka filet yusra ta dauka tareda zuba mata ferfesun kaza da dankali shima taci sosai sannan ta bata ruwa tasha, a haka suka kwana taslima kuwa sai safe ta farka, yusra c eta kira doctor bayan ya dubata yace” bawata matsala kuma babu abunda yasamu yaran dasuke a cikinta, Lalube ta farayi tana kiran ummah! Da mamaki suke kallonta doctor yace” bata gani neh? Eh umma tace”cikin kuka, Da makantar aka haifeta ya tambaya? A’a yau kwana biyu kenan da makancewar jefarta akayi a ido, Yusra ta kalli doctor tace” doctor what is the solution now? Daga kafada yayi yace”what do you went? I went help her, Ok go ahead ya fadi, Kamar nawa kake ganin zasu isa ayi mata aiki? Ehto tunda da wuri kike so ayimata zaki iya biyan dubu dari ukku da hamsin, Ok so nake daga yau zuwa gobe kumata domin nanda ranar Monday nizan bar kasar nan abbana yana son inkuma Egypt da karatu kuma maybe this Monday zantafi dan haka inason ayi komai kafin intafi, Ok,ya fadi tashi tayi tareda fadin zanje gida indawo zan dawo maka da kudinka kallon umma tayi tareda cewa” nixanje zandawo anjima za’a kawo muku breakfast yanxu Allah yakara sauki,”amin” Bata wani jimaba ta dawo da kayan abinci bayan taje ta biya kudin aikin doctor yace”anjima da yamma zasuyi mata, Da yamma aka shiga akayiwa taslima aikin ido doctor yace’ after 3days za’a cire mata, sosai umma kewa yusra godiya tace’ bakomai. Ranar Monday tunda safe yusra tazo asibitin tayiwa su umma sallama ta wuce’ airport. Ta bawa doctor kudi kimanin dubu dari takwas tace’ ya basu, Umma yasamu yabamawa tace” bawan Allah nayarda dakai kaje kasamar mana gida na daidai kudinmu nida yata muxauna bamuda kowa a Abuja, wallahi kataimake mu, nasan gidaje suna tsada a Abuja amma karufa mana asiri kamar yadda Allah yarufa maka, kallonta doctor yayi, sannan yace"to shikenan. A ranar da aka cirewa taslima aikin idonta Umma tayi farin ciki sosai Wanda baya misaltuwa, Doctor yasama Umma yai Mata bayanin ansamu gida amma Karami ne daki biyune ciki sai toilet da kitchen sai wani karamin shago a kofar gidan, yace idan anyi discharging dinsu zai kaisu. Sosai Umma tayi farin ciki tare da godewa ubangiji, ta kuma godewa doctor sosai. 1week sukai a asibitin doctor ne ya daukesu yakaisu gidansu, Alhamdulillah domin yanxu taslima tana gani sai dai an yankar mata glass medical Wanda zata ringa sakawa idan zata shiga Rana, A motarsa ya daukesu yakai su anguwar akwai mutane kowa harkar gaban sa yakeyi gwanin sha'awa parking yayi ya fito, sannan ya bude musu, key yasaka ya bude gidan karamin shagone a kofar gidan Wanda akwai kofa ta cikin gidan. Dan karamin soro ke akwai tun daga zaure har tsakar gidan shafe yakeda siminti, tsakar gidan ma Karami ne, sai dakuna guda2 kowane yana dauke da kofa sai window, cikin dakunan kuwa duka tayils ne, bayin su a tsakar gidan yake shima shafe yakeda siminti gashida kyaure kuma a rufe yake, Kitchen dinsu ma ansaka tayils a kasa sannan akwai kanta shima yana dauke da kyaure, gaskiya gidan ya burgesu godiya sukama doctor sosai domin sunsan gidan yafi karfin kudinsu, yadai siyar musu ne kawai. A haka yai musu sallama ya tafi, zama taslima tayi a kasa taji sanyin tayils na ratsa ta tace" ummah! Mene ne abunyi? Bangane abunyi be kamar ya? Jakarta ta jawo Wanda take tara albashin ta a ciki ta zazzage duk yan dubu"dubu ne Masu yawan gaskiya domin bata taba kashe albashin ta, Kirgawa tai kudin sun haura dubu dari hudu, dan haka ta dubi Umma tace" Umma Ina kudin kike Tarawa, irin Wanda antyna take bani Ina Kawo mini? Gasu nan ta mika Mata wata Leda, Umma tace" Ina tarasu ne idan kintashi aure inmiki kayan aure, Dubawa tayi taga suna da yawa tace, Umma naga mun wuto wata kasuwa zanje inyo mana siyayya da kudin gurin ki, su kuma na wajena a ajiyesu bari inyi sauri zangane gurin bazan dade ba insha Allah. Kallonta Umma tayi tareda fadin to saikin dawo, haka taja kafa da katon cikinta ta fita, ai kuwa tana fita taga wasu yara su ukku a kofar gidan maza biyu sai mace daya, gaisheta sukai ta amsa tare da tambayar su Dan Allah daga nan zuwa kasuwa babu nisa KO? Eh macen tai saurin cewa tareda fadin" muje inraka ki, OK nagode muje. A kafa suka taka tafiya ta 10munites ta kaisu kasuwar inda babu abunda babu, a nanfa taslima ta fara siyan abubuwa komai saita ringaji da sauki ma, dariya yarinyar tayi tace" ai nan kasuwar komai sauki garesa shi yasa wasu kece Mata kasuwar yan'san banza. Murmushi kawai taslima tayi" tukunyar girki ta sai musu guda ukku 3 sai murhu biyu, yarinyar tace' kinga risho nan mai biyu second new ne ki siya, ba musu tasiya, sai kasko na suya da ludayi nashan kunu Dana girki da spoons, filat'filat kwanoni duk dai wani abun amfani na talaka, tabarma tasai musu guda ukku manya 2 karama 1, Yarinyar tajata sukaje gurin siyar da kayan kallo t.v tasiyo mai kyau da d.v.d duk second new itafa saukin kayan yafara bata tsoro kodai kayan sata ne, kettle na dafa ruwan zafi tasiya, sannan sai labulaye gaskiya ta kashe kudi sosai, sai katifu marassa yadi yan yanke manya ta yanko musu kudin data rage basu wuce dubu hamsin ba, buhun shinka tasiya sai taliya da masara, tayo cefanen abinci dai, yarinyar kuwa Mai shegen surutu ta nufi gurin gwanjo,,,,,,,lollz! Dagawa ta dunga yi tana zabar t.shirt da rigada siket da dogayen riguna, tana wllh idan kika haihu wannan zasuyi miki kyau ki siya, kamota tayi tace' kinga zo muje inada kayan sawa ai. Mota suka samu ta loda musu kayan har kofar gida yarinyar da kannenta suka dunga shiga da kayan cikin gida ko ummah tayi mamakin yawan kayan. Bayan sungama ne taslima ta basu Dari biyar tace ita macen ta dauki Dari ukku sukuma tabasu dari'dari, Godiya sukai sannan ta umarce su suje gida yamma tayi. Ita dakanta ta shirya komai na gidan ta saka musu labulaye da katifu sannan tajera kayan kallo tasaka komai a inda yadace sannan ta nufi bayi ta dauro alwala tazo ta gabatar da sallah, Zama tayi akan daddumar tana lazimi har akai isha'i tayi tacigaba da zama tana kai kukanta ga Allah, tana kallon Umma har lokacin da bacci yasace umman! Allah sarki rayuwa dukkan su babu wanda ya nemi abinci a haka suka kwana, Yarinyar nan makotan su ne sunanta saudat kannenta kuma murtala da Abdullahi mahaifiyar su tana da mutunci sosai duk sadda tagama abinci tana zubowa a kawo ma ummah kuma takan shigo su gaisa su kumayi fira. ALLAH NE SHEDA 2 mrs"sweet dearling busby Salihu Bamalli on top Xee"Abu"Safana A bangaren tauhid kuwa bayan sungama wayada tauhida bacci ya kwashe sa washe gari around9 abbansa yakira sa yake fada masa yazo gida, Lapiya ya tambaya abban yace" tauhid kasan ita rayuwa duk sonda kakewa mutum Allah yafika son bawan sa kuma dukkan mu bazamu dawwama a duniyar nan ba, sannan kasan na daga cikar ka musulmi kai imani da kaddara mai kyau KO sabanin haka, kuma komeh yadame ka cigaba da addu'a domin hadith ne ingantacce daga manzon Allah (s.a.w) yana fada mana addu'a'u huwal ibadah! Tauhid Ina mai baka hakuri Allah yayiwa tauhida rasuwa a Daren jiya.......! Tsaye ya tashi cikin tsawa domin yama mance da mahaifin sa yake magana yace" whatttt! Nasan kaji meh nace" Dan haka ka shirya kataho Nigeria, Baisan sadda yasaki wayar yana dogon salati ba, jiyayi komai nasa ya tsaya masa da karfi yasaki kuka kamar wani karamin yaro sojojin dake gadin bakin kofar suka shigo domin suga mene ne? Ganin ogan nasu yana kuka yasaka suka fara kallon juna cikeda mamaki da tsoro, bindiga ya dauka tareda sakin wani irin harbi asama Dan haka da sauri suka fita, shi kansa baisan halinda yake ciki ba, office din ogan shi ya nufa ya fada masa matarsa ta rasu yanaso yaje gida yanzu, Kai tsaye ogan ya nuna rashin amincewar sa zai cigaba da magana tauhid yadaga masa hannu tareda ficewa baiko rufe kofar ba, jiri yaji yana kwasar sa dakyal yaje cikin gidansa yana kokarin shiga falo ya fadi! Dasauri sojijin dake gadinsa suka sungume sa sai asibiti domin ceto rayuwar sa yashiga matsa nan cin hali harta kaiga ansaka masa oxygen sai da yayi kusan 2weeks a haka kafin yafara samun sauki watansa guda a hospital kafin ayi discharging nashi yana dawowa da kwana 2 ya shirya kayansa tsaf! Ya nufi office din ogansu gabaki daya ya bashi takarda yace" na'aje aikin soja har abada sir, Yana fadin haka yakama gabansa sai airport dukda kiran da ogan yadinga masa amma inah zuviyar maza tayi zafi dan haka sai Nigeria saida yazo gida kuma damuwar tasake tasowa sabuwa da taimakon iyayen sa suka dunga rarrashin sa, but badai kagan sa yanxu yana fara'a ba kullum fuska a murtuke babu annuri ga rashin kuzari gashi baya zuwa ko'ina kullum yana gida, akullum tunanin tauhidar sa yakeyi yana kuma binta da addu'o'i. Abba ne yasame sa yace" tauhid organ ku yakira ni yana bani hakuri in rarrasheka ka koma aiki domin kai mutum ne mai amfani a garesu. Abba kace masa yayi hakuri bazan koma ba, ni nakeda amfani a gurin su amma ni yanxu rayuwata batamin wani amfani...... Tauhid Karna sakejin wannan kalmar a bakinka kaifa musulmi ne bai kamata ba ya kamata ka kiyaye harshen ka, kuma kasani zaman ka gida bashida amfani saima damuwa dazai kara dora maka Dan haka mungama magana dashi zaka koma aiki amma anan Nigeria sun kuma amince harsun gama komai zaka koma abuja da aiki insha Allahu kuma akwai yaron abokina yana nan zan hadaku mutum ne mai barkwan ci da iya zamada mutane sunan sa cpt.Adam Dan haka Kai hakuri end of this month zaka tafi abuja kacigaba da aiki. A sanyaye yace"to Abba, Yawwa Allah yai maka albarka"amin" Bada son ransa ba ya tattara yakoma abuja anguwar dayake ta burgesa domin shi mutum ne mai son jama'a anguwar kuwa akwai mutane kuma akwai tsari da ban sha'awa ga makarantu boko da islamiya ga yawan massalatai, sannan daga nan gefe duk gidajen sojoji ne Wanda suke zagaye da babban get a takaice dai barrack ce sabuwa domin dayar wacce keda Dan nisa kadan gidajen sun cika shine aka musu wa'yannan kuma duk musulmai ne a cikin su, gidan sa jere da gidan cpt.adam a ranar dayaxo tun a ranar yagama fahimtar cpt.adam mutum ne mai barkwan ci da surutu, sai dare cpt.adam yashiga gida. Tunda safe yaji Ana masa nocking a tunanin sa sojojin dake gadinsa ne wani dan yaro yagani wanda bazai wuce 9years ba ya gaishesa ya amsa, sannan yabashi bascket dinda ke dauke da breakfast yace'inji dadyn sa , dagani ya fahimci yaron adam ne Dan yaga Kama, godiya ya masa ya tafi yaron, Satinsa daya da zuwa kullum cpt.adam suke Kawo masa breakfast sai kuma na dare domin na Rana yanaci a office,, cpt.adam ya matsa masa suje gidansa hardai rannan ya amince sukaje, a falo suka tarar da yar karamar yarinyar sa ta goye tanata kuka daukarta yayi tareda Fara kwalawa matar kira yana fada" fitowa tayi sanye da hijab tace" wallahi Ina sallah ne yi hakuri, ta fada tareda karbar yar' Sai a lokacin ta lurada tauhid fara'a tasaki tana abban yasir wannan shine mejor" tauhid din? Eh shine Ayyah sannu zama tayi tareda gaishesa bayan sungama ta nufi kitchen ruwa ta Kawo masa da drinks with fruits, suna nan yaran cpt.adam suka dawo yasir da deen ita kuwa kitchen ta nufa haka suka sha fira bayanta kammala musu abinci, cpt.adam yafito ya taka masa harya shige gida yana kara fadawa cpt.adam yayi dacen mata gaskiya. A haka sukaci gaba da rayuwa duk sadda yasama time yakanje gida yadubo su yadawo. ∆¶Π¶∆¶Π¶∆¶Π¶∆¶Π Taslima kuwa ciki fa sai kara tsufa yakeyi mama(wato makociyar su mahaifiyar su saudat) tacewa"Umma yakamata ta Fara wata sana'a domin zaman a haka bazai yiwwu ba, Dan haka Umma ta Fara dama koko da kosai da safe na siyarwa, Alhamdulillahi ana ciniki sosai taslima ke dama koko Umma ta soya kosai a cikin soron su suke siyarwa. Sosai suka saki jiki suka cigaba da rayuwar su anan duk dare bayan magrub su saudat suna dauko littatafan suna islamiya suzo taslima ta biya musu, idan na boko ne kuma tana musu assignment da lesson. Tunda watan haihuwar taslima yakama ita batama san haihuwar ce ba dama tauhida ce take kirga watannin cikin, ciwo ya isheta tafi sati a haka amma daurewa kawai takeyi, bata so Umma tagane hardai yau da abun yaci tura ta dunga nukurkuso Umma ta nemi taimakon maman saudat suka samu mota aka nufi asibiti da taslima lokacin harta fita hayya cinta, doctor ya fito da sauri ya nufosu yana fadin" Munada bukatar Ku kawo kudi nanda awa daya zamuyi mata aiki yaran bazata iya haihuwar suba gashi daya harya koma Mata saitin zuciya Dan haka ku hanzarta Ku kawo dubu Dari da saba'in yanzu, Dasauri ummah tadawo gida ta bude jakar taslima ta deba kudinta koma takai sai kuka take domin bataso tarasa tilon yarta. Aiki aka shiga yimata da sauri umma kuwa alwala tayo ta tada sallar nafila tacigaba da jero addu'o'i. Wajen 2hrs doctor yafito yana share gumi yace" congratulations anyi nasarar Ciro Mata yaranta biyu namiji da mace" kuma duk suna lapiya itada yaran, nurses suna gyara su idan sungama zasu kawo maku yaran ita kuma tana dakin Hutu! Tun daga Umma har maman saudat hamdalah kawai sukewa ubangiji, ankawo masu yara manya kuma kyawa'wa kamar yaran larabawa, maman saudat tace" ikon Allah dukkan yaran babu mai kamada taslima to kodai sun biyo babansu ne, Umma kuwa murmushin yake tayi tareda mayarda kwallan dake son zubo mata, tafiya maman saudat tayida yaran gida a inda ta musu wanka, sadda tadawo har taslima ta farka tasamu ta gyara jikinta, Kullum maman saudat take musu hidima har saida taslima tai 1week suka sallame ta, ta koma gida sadda ta koma ta iske komai nata a dayan dakin maman saudat ta mayar Mata an gyara shi da dare kuma saudat kexuwa tayata kwana, Ummah dake hawaye ta. dubi taslima tace" ki fadamin gaskiyar yaran nan waye ubansu kinga a baya ganin kinada ciki yasana daga miki kafa, Saukowa tayi daga kan katifar ta duka tace" ummah na wallahi tallahi ban taba zina ba Umma wallahi cikin anty tauhida ne? Cikin rashin fahimta ummar ta dubeta Dan haka tai mata bayanin komai, tadata Umma tayi tareda fadin" na yarda dake taslima nasan ki share hawayen ki Allah yasan taimako kikai kuma zai baki ladar zai kuma Kawo miki mafita domin shine shedarki ALLAH NE SHEDA zamu kuma rike Mata yaranta muyi musu tarbiyya har iya karshen rayuwar mu yanxu inaso cikin kudin can asiyo raguna a yanka musu akuma rada musu suna Dan kar mutanen anguwa su fahimci wani abu sannan kisiyo musu kaya da sauran abubuwan amfani kinji, sannan kinga munata taba kudinnan Dan haka zamu siyo kayan provision muzuba a shagon gidan nan muna juya kudin haka Allah yake son ganin mu kuma mungode masa a kowane yanayi yabarmu Alhamdulillahi. Shawarar da Umma tabi duka aka dauka sun zuba provision dama duk kusada su babu shago sannan suna tayin kokon su da kosai, Taslima tanata kula da yaranta inda sukaci sunan iyayen su tauhid da tauhida amma tana kiransu uncle" macen kuma anty namijin shine yake kama da marigayiya tauhida macen kuma da babnta tauhid kasancewar duk zaman da taslima tayi basu taba haduwa da tauhid ba hakan yasata kasa gane dawa yarinyar yake Kama. Saudat kuwa tana matukar son yaran Dan haka a tare suke renon su idan ta dauke su sai taji suna kuka zata kaisu susha nono. Haka rayuwa taciga da tafiya cikin rufin asiri har Allah yasata yayesu lokacin babu inda basa zuwa ga wayau dashiga zuciyar jama'a haka tacigaba da renonsu. Harsuka Kai 3years maman saudat tai mata hanya aka dauketa islamiyar anguwar tana koyarwa safe da yamma dasafe karfe 9am xuwa 12am tanama matan aure 4pm to 6pm kuma yammata sosai tayi farin jini a dalibai suna son karatun ta domin suna ganewa a gida take barin anty da uncle gurin ummah suna tayata zaman shago abun ya cigaba domin har gida matan aure suke samunta tana basu shawarwari, Abdul kenan wani kyakyawan saurayi ne dake a anguwar mahaifin sa mai kudi ne sosai hakan yasa yake takama tunda yaga taslima yake sonta, Dan haka yau yashirya yazo har kofar gidan su, fitowa tayi ta nufo inda yake zaune saman motarsa, tai sallama ba tareda ya amsata ba yace" heyy! Wa'iyaxubillahi kai kuwa kamar ba musulmi ba Zan maka sallama ka mayar minda kalmar yahuwada KO bakasan darajar sallama bane a musulunci,,,, ,, Look ya fada tareda daga Mata hannu yace" is ok! Ba a wa'azin ki nazo sauraro ba ai nasan ke malamar islamiya ce basai kinmin wa'azi zangane. Murmushi tayi tace" hadith ne ingantacce na manzon Allah (s.a.w) Wanda yake cewa "manta allamal ilman sum'atan wa'riya faqad halaqa،،، ; duk Wanda yake neman ilimi Dan aji kodan a gani hakika ya halaka. To Ina tabbatar maka bana cikin halakakkun da hadisin nan yake magana akansu, sai dai kasani har ilah yau a wani hadith din yana cewa" kully ilmi wabalu ala salimihy i'lla man alamila'bihi،،،؛ ; dukkan ilimi rashin kwanciyar hankali ce ga Wanda yayi shi, sai dai ka Wanda yai aiki dashi, Toni nayi aiki dashi kuma yazamar min kwanciyar hankali, Kaga inaso ka gaggauta fadamin dalilin daya kawoka gurina, Kallonta yayi tareda jan tsoki kafin yace" taimakon ki naxoyi. Kaga indai wannan ne yakawo ka kaje nagode bana bukatar taimako a gurin kowa sai gurin ubangiji Dan haka kaga tafiyata. Binta yayi da ido harta shige cikin gida, anty ce zaune suna cin tuwo da ummah ind a uncle yakoma gefe yanata fushi, dafasa taslima tayi tace my uncle meke faruwa waya tabamin kai? Kallon Umma yayi yana turo baki, Umma tace" a'a wai bazai ci tuwoba shi indomie zaici ni kuma nace tokarya ci din shine yaketa cika yana hawa kamar buredi, Dariya taslima tayi tace" uncle dina Dan gayune bayacin tuwo oyahh! Zomuje kaji wata magana, Kama hannun sa tayi suka zauna indasu Umma kecin tuwon ta saka hannu tareda Fara magana tace" Uncle kanajina karka zama haka kaji mah boy ubangiji subhanahu wata'ala yakan jarabce muda rayuwa iri'iri ta wani tafi ta wani a kowane hali ka tsinci kanka yanada kyau kacigaba da godewa ubangiji domain bawai baya sonka bane ta iya yuwwu wa arzikin da kake so ba alkairi bane a gareka sau tari mu yan Adam mukanso abu alhalin wannan abun ba alkairi bane shi yasa a KO Ina a kuma koda yaushe na daga cikin dabi'ar mutanen kirki kome yafaru ko kuma suka samu zakaji sunce Allah ya tabbar da alkairi to irin wa'yannan mutanen tabbas abun koyi ne a rayuwa kuma abun Alfahari domin sunada tawalu'u Dan haka anty da uncle yarana Ina yimuku nasiha a rayuwa duk yadda taxo muku Ku karbeta kuyi addu'a sai kuga komai yazo muku da sauki kunji kuma kudaina kallon Wanda yafiku a rayuwa kuringa kallon Wanda bai kaiku ba saikuga kun samu nutsuwa kun zauna lapiya Dan haka uncle bude bakin ka inbaka tuwo kaji kasan ummana ta iya miya hard a man shanu duk sadda Allah ya horemin Zan dafa muku indomie kunji amma basai kunmin maganar ba nida kaina zan dafa. Bude baki yayi yana fara'a ta fara bashi tuwon yanaci sosai Umma taji dadin kalaman taslima ga yaran nata. (Ya kamata mugane ke uwa kezaki sauna kina yiwa yaronki nasiha kamar babban mutum kina kwatan ta masa kina jawosa a jiki domin yaro yafi Babba daukar abu, to mu matsalar yaro tun kafin yazo duniya tun yana ciki zata Fara zaginsa، haka yana jariri ko bare kuma ya girma ai shikenan kuma,,,,, Allah yasa mu gyara) A haka tabashi tuwo harya koshi ta kaisu suka wanke baki suka wuce daki kayan bacci tadauko tasaka musu sannan tasaka su sukai addu'a ta dauka uncle tasaka shi a cikin katifarsa tareda zage masa net(gidan sauron Sa) sannan ta ja anty suka kwanta a tasu katifar ta tofesu da addu'a. Tauhid ya dubi cpt.Adam yace" Adam wai kayi hauka ne da kake zancen kara sure? No oga wallahi inason karawa ne nafara gajiya da halin yarinyar nan sadiya haba inta magana daya haba, murmushi tauhid yayi tareda dafasa yace" look adam indai matane wallahi babu wacce batada matsa kowacce tanada irin ta tah matsalar kowa hakuri yakeda tasa kamar yadda muma mazan haka muke Dan haka Ina baka shawara karkace zakayiwa sadiya kishiya domin Kai kana ganin akwai matsala bari kai aure to ba haka yakamata ba domin Kai baka gyara wannan matsalar ba kuma zaka kwaso wata matsalar ka Kawo wallahi matsaloli ne zaka karowa kanka infada maka gaskiya zasu hanaka zaman lapiya, ga raba kan yaranka Kai abubuwan da yawa fa. Oga ai inba haka naimata ba baxata dainaba hakan zaisa tasan nadamu harna dauka mataki, Bari kaji adam a rayuwa ba'ayiwa mace haka inkana so tasan kadauki mataki wanda bazai iya cutarda ita matuka ba, adam ka daina cin abincin ta, kodaina walwala a gida kanuna Mata koda yaushe cikin damuwa kake wallahi nina fada maka itada kanta saita ringa baka hakuri tana tambayarka meke damunka, Amma kace Kai kishiya zaka Mata to maimakon tayi nadama ta baka hakuri wani sabon bala'in zata tsiro maka dashi ko anyi auren zakaga inbanda tashin hankali babu abunda suke saka. Aini maganar gaskiya ma sadiya tanada saurin yin nadama kotayi laifin zata dunga bani hakuri inbanyi ba wallahi Sam! Batada walwala,gashi tanason dangina ko mamana dataji zancemln auren bataji dadiba domin yadda sadiya ke kulada su, To kagani KO Adam. Nidai sir alfarma ce nake nema muje gidan ka sanar da ita dan tana ganin mutuncin ka nifa wallah I bansan yazatayi reacting ba gashi inason sadiya. Zaro ido tauhid yayi yace' Kai tsaya kaji duk fa tsuntsun daya jawo ruwa wallahi shi ruwan yake duka OK wato muje mutuncin datake ganina ya dishe wallahi saidai kaje zanjira ka a waje inka gama kafito muje. Shiga yayi gidan cikin daure fuska babu kowa sai ita a falo yaran duk sun fita zama yayi tace masa sannu ya amsa. Ta tashi da niyyar dauko masa ruwa yace" barshi na koshi, Zama tayi fuskarta da damuwa tace" Dan Allah laifin danai maka nace" Kai hakuri insha Allahu bazan karaba, Kallonta yayi tareda cewa naji ba wannan ba inaso in fada miki zankara aure nan...... Da sauri tace"wallahi baka isaba bazan zauna bakin cikin ka ya kashe niba wai meh nai maka da kake wulaqanta ni haka adam! Nagaji nagaji...... Tsoki yaja yatashi zai wuce ta riko hannunsa ya fisge harta fadi jikake timm! Tasaki kuka amma ko kallonta baiyi ba ya nufi kofa zai fita dai' dai nan tauhid yashigo cikin bacin rai ya zabgawa Adam Mari tareda fadin" Are you out of your sense adam matarka ta fadi sannan kuma tasaki wannan kukan har bazaka duba halinda take ciki ba me yasa? Adam kuwa yakasa magana ita kuwa tashi tayi tana jan kafarta harta shige daki, tauhid ransa bace ya fita Adam dinya biyosa, Kallon sa yayi yace" me yasa mu maza wani lokacin bama yiwa matan mu adalci ko kadan yanxu idan uwarka ce babanka yai Mata haka zakaji dadi, to itama wannan uwar wani ce inajin haushin namijin dabai iya rarrashin mace ba a rayuwa Mata rauni ne dasu dukda wani lokacin harda laifinsu amma kaima yakamata kasan abunda yakamata haba,

Post a Comment for "Allah Ne Shaida Book 2 Complete Hausa Novel"