AMANI Book 4 Complete Hausa Novel
AMANI
4
Littafin
SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)
takorikabara@gmail.com
MUKHTAR
H
ar ya isa sassan Ummami yana tunanin abubuwan da suka faru tsakanin sa da Amani yan mintunan da suka shige. Mukhtar yace a ran sa kenan gatan iyaye ma wani abu ne mai girma ga dan adam! Da Maimartaba bai bijiro da zancen bashi Sa-daka ba, da bai san ranar da Amani zata yi nadamar halayen ta har da abubuwan data yi masa irin haka ba, don shi har yanzu jikin sa bai karbi ikirarin Amani tana son shi yanzu ba, ya dai ji ta, and he was puzzled, ya dai fi yarda da cewa gudun kishiya ne ya ruda ta.
Bai dawo gidan ba ma don baya son ta sake saka shi gaba da kukan ta da fitinar ta, sai lokacin da ya kintata cewa ta yi barci, don baya son ta kuma saka shi a kwana kada tayi saurin samun lagon sa, da raunin zuciya ya wuni yau, sabida kasalar da nadamar Amani da kukan ta suka saukar masa.
Sai da ya dauke takun sawun sa kamar mara gaskiya da ya shigo falon da ya raba nashi da nata. Kuma yana shigewa dakin sa ya rufe a hankali har da key, ba tare da Amani ta san dawowar sa ba sam.
So yake ta koyi son nasa da gasken gaske, har ta zo tana kewar ganin sa, mai yuwuwa in ta daina ganin sa ta yi kewar sa, don ya ga canji mai yawa ranar da ya dawo daga Burkina Fasso.
Amani kamar tayi hauka, ganin har washegari Mukhy bai neme ta ba, ga dakin sa ya rufe da key, ta kasa gane a gidan ya kwana ko aah? Jikin ta ya bata kawai watakila an kawo sadakokin, a can wajen su Mukhtar ya kwana, to a ina aka sauke su bata da masaniya?
Kafin garin Allah ya waye in ka ga yar Daddy bazaka gane ta ba, ta zama kamar kudin guzurin da kullum ake yafita yake karewa.
Haka Mukhy ya dinga yi mata wannan batan dabon har kwana uku, ko sassan Ummami bata iya zuwa yanzu don ta san sai ta tambayeta me ke damun ta. don Amani bata saba da shiga damuwa ba a rayuwar ta, shi yasa yanzu data sameta ta kasa controlling din ta, gashi in zaa kashe ta idan an tambaye ta meye damuwar ta ta san ba abinda zata ce yana damun nata din sai kewar Mukhy. Tunda ta ajiye damuwar sadakokin sa aside, ta bar musu shi, amma hakika rashin ganin sa (for good three days) dinnan yana azabtar da ita yadda bata zato a zuci da ruhi. Da tunanin ta na yana can tare da sadakoki yana shan shagalin sa, shiyasa ta daina ganin sa a sassan ta kwata-kwata.
Baba Sahura kuwa in ta zo bata ko bari su yi doguwar magana zata ce ta kyaleta ta, ta tafi gunUmmami don Allah, bata son dogon surutu irin na Baba Sahura. Hatta Sugra da Tahirah sun san uwardakin su ta shiga yanayi, ta ce kada ta kara ganin kowaccen su a gaban ta in ba ita ta neme ta ba. Baba Sahura sai dai ta yi dariya, ta ce,
ai wato shi Allah haka yake alamarin sa, duniya rawar yammata wai na gaba ya koma baya.
Amani ta zama daga kwanciya sai kwanciya bata umh bata umh umh, domin ta gama gayawa ran ta an kawo sadakokin nan, an basu wani gidan, Mukhy yana can tare da su.
Da safe Baba Sahura ta shigo dakin ta don taga lafiyar ta yau da safe, ta same ta ta hada kai da guiwa tana kuka tamkar marainiya, haushi mai tsanani ya kama Baba Sahura, sai ta kada kai ta ce, lallai, aure mai ladabtar da mace, Uwa duk kin yi sanyi kamar ba Tafisun Alhaji ba, kin koma talalabuwa, yo idan ma Sadakan ne aka kawo ai ba ta haka zaki gabza da su ba, tsaf kina nan kina wannan doloncin zasu janye shi, ke kina nan kina cika bokiti da hawaye, ai ta shi tsaye zaki yi ki zama kamar Ummami wajen karawa da kishiyoyi komin yawan su, in ya so mai karfi da iya kissa da iya gado da iya kula da miji ta kwata.
Ba miji irin Maina ake sakarwa kwarkwarori a koma gefe ana kuka ba, ni wallahi duk kin zama sullutuwa, wannan karfin ikon naki da izzar taki duk sun bar ki, a irin wannan lokacin kuma suna da amfani, ni nafi son Tafisu ta baya ba ta yanzu ba da namiji ke neman kassarawa.
Sai ta ji tamkar Baba Sahura ta yi mata allurar sanya kuzari, da gaske kishi da soyayyar Mukhtar ke neman kashe ta a tsaye in tayi wasa, ya gama narka Tafisu ya gama kashe lagon ta da soyayyar sa, shi bai san ma tana yi ba, yana can yana murzar kuruciyara sa da kyawawan yammatan abzinawa har biyu. Shin da soyyar sa da ke cin ran ta, da kishin Mukhy da ke azabtar da ita zata ji ko da bakakaen maganganun Baba Sahura na yau daban na gobe daban? A wani bangaren, ga kuma kwadayin son ganin fusatattar kyakyawar fuskar sa da ke addabar ta a yanzu.
Don haka yau Tafisu ta kwarara zuciyar ta, ta kuduri aniyar ko zata kwana a zaune zata hana idon ta barci zata yi hakan, don ta bincika ta ga inda Mukhtar ke kwana. Aka ce sa kai ya fi bauta ciwo.
Kuma shima wani ikon Allah yau ya kasa yin daren da yake yi a gun Ummami don kan sa ciwo yake yi kadan-kadan, kuma shi kan sa ya gaji da boyon da yake yi mata don yana takura kan sa a daki ne, domin ya gane wahalar da yake baiwa zuciyar sa ba kadan bane, ko ya ki ko ya so, yayi kewar kyawawan idanun Tafisu, masu kama da kwan zabo, koko dan itacen nan na almond.
Murmushin ta da bata fiya yi ba sai wuri ya kure, da takun tafiyar nan nata mai kama dana macen Dawisu don rangaji da iya takun tafiya mai daukar hankalin namiji.
Mukhy ya sa hannu ya rike kan sa da ke sarawa tamkar zai rabe gida biyu. Ya ce.
Wash!
Ummami ta juyo tana tambayar shi lafiya kake rike kai? In barci kake ji ka tafi ka kwanta mana? Nima yanzu gun Mai zan wuce, kwana biyun nan na rasa gane kan ka, duk ka bi ka hanani sakat da binbini, duk inda nayi sai ka bi ni cikin gidan nan Maina kamar yaron goye? Ni ina matar ka ne ma kwana biyun? Itama na daina ganin gilmawar ta a sassa na sai kai uban yan binbini, bita zai-zai.
Mukhy yayi murmushi bai ce komai ba yana kara dafe kan sa da ya kara sarawa.
Na rasa dalilin da yasa kake yin dare yanzu a waje na ko wajen Mai, kai da aka ajiyewa amarya ko sati bata rufa ba, amma sam baka dokin ta, anya Maina? Lafiya?.
Murmushi ya sake yi kadan, ya ce Ummami ai kanwa ta ce wane irin doki kuma? Ni kanwa nake yi da ita, ba amarya ba.
Tun daga nan Ummami ta ke fahimtar wani abu is fishy a tsakanin su a kwana biyun. Ta fahimci tun ranar da aka yi zancen sadakoki ne Amani tayi mata batan dabo. Don itama Tafisun kwana biyu da ya tsiri shigowar ya jima mata a sassa har wani lokacin yayi barci ya farka, ita kuma ta daina shigowa kwata-kwata.
Baba Sahura dai ta tabbatar mata Amani lafiya take, shakiyancin ta ne ya motsa ko kofar falo ta daina fitowa. Ta kori su Sugra ma.
Ya shiga gidan sa ko in ce bangaren sa cikin jin ciwon kan na karuwa masa, shi kan sa ya san akwai matsala a tare da shi yau, don duk dauriyar sa ta kare, da gaske daurewa kawai yake amma tunanin Amani da yake kwana da shi yak e tashi da shi da son kasancewa da ita ko sau daya ne a rayuwar su, ya fara haifar masa da rashin sukuni a cikin jikin sa, zai ratsa ta falon karshe wanda a nan dakunan barcin su suke, ya ga Amani zaune firgai-firgai tana dakon jiran shigowar sa, ta ki shiga dakin ta balle ta kwanta, ta yi rantuwa yau sai ta ga gadon barcin Mukhy da sadakokin sa.
Sai ya sa kai zai wuce ta ba tare da ya ce mata komai ba, but hes touched da ganin yadda ta rame ta yi zuru-zuru kamar ba yar gayun nan Amani Faskari ba, hakan ya taba zuciyar sa sosai, kuma hakan yasa nan take ya tuna Alhaji, da yadda yake lelen abar sa, sai ya ji kamar baya kyautawa abinda yake mata, kamar yana cin amanar Alhaji Usman, duk da haka har yau Amani bata yi hankalin da yake so ba, shi kuma in har ba ya tabbatar da canzawar ta da halayen ta da baya so, ko da ba duka ba, tunda ance hali zanen dutse ne, amma a kalla ta cire wanda Allah baya so (girman kai), izza da fariya da tunanin ta na ta fi kowa, yana so ya tabbatar da cewa tana mishi so na hakika na fisabilillah irin wanda zata sake da shi a shimfida da zuciyar ta da gangar jikin ta bakidaya, ba don shaawar gangar jikin ta na yar adam ba, sai don so da kauna na domin Allah, sannan ne zai iya sakin jiki da Amani su fara rayuwar da yake musu tanadi shi da ita.
Makeken Gadon sa ya haye ya kudundune yana amsar zafin da jikin sa ya dauka, jikin sa har yana rawar dari, domin tuni zazzabi ya kawo masa hari, ya ja bargo ya kudunduna har kan sa. Amani duk da bai kula ta ba, ya wuce ta ne a zaune sai bata yi kasa a gwiwa ba wajen biyo shi dakin, ta yi saa bai saka key din ba yau, don bai san inda kansa yake bama, amma kuma bata ga wata sadaka a dakin ba sai shikadai.
Amani har da sauke wata lafiyayyar ajiyar zuciya, rigimar da ta shigo da ita ta nema ta rasa, ko don irin kwanciyar da taga Mukhy yayi da kudunduna cikin duvet kullihin sa ko AC bai kunna ba. Sai jikin ta yayi dan sanyi, kuzarin balain data shigo da shi yayi kasa sosai, ko daga irin kwanciyar da Mukhy yayi yau zaka fahimci bashi da lafiya.
Farar rigar barci ce a jikin ta iya guiwar ta mai santsi, amma ta daura zanin atamfa a kai, gashin kan ta ma duk ya susuce babu taza, babu kitso, tafi dacewa da a kira ta da birkitacciya Amani yanzu ba yar gaye Amani Faskari ba, sabida yadda ta koma sam ba nutsuwa da walwala da farin ciki a tare da ita, duk a dalilin rashin samun kan Mukhtar Issouffou Massaoudou.
A lokacin da zuciyar ta ta afu a kan sa, da son ganin su a wani matsayi na cikakkun mata da miji cikin kauna da soyayya kamar kowadanne maaurata, ba wannan matsayin da suke kai a yanzu ba, kamar dai Mai Diffa da Ummami, kai bazaka ce sun tsufa ba, kullum cikin kaunar juna da tattalin juna suke, da ka zauna da dayan su sai ka ji ya ambaci dayan a cikin zancen sa na koyaushe, ta hanyar bada misali da kyautatawar da dayan su ke yi masa.
Yadda son Mukhy da kishin sa suka taru suka sukurkuta Amani sai ta koma kamar ba yar gayun nan kuma yar kwalisa (wanke hannu kafin ka taba) da ya sani a gidan Hon. Usman mai suna Amani Usman Faskari ba.
Amma yanzu kam fama yake da kan sa da ya tambaye ta dalilin wannan ramar haka, da dalilin susucewar ta, to ko magana baya son yi, ya rasa dalilin wannan masassara data same shi yanzun nan, jikin ta duk yayi sanyi da yanayin da ta gan shi a ciki na rawar dari don bata taba ganin sa cikin irin sa ba, sai ta zauna a gefen gadon jikin ta ya dau rawa itama, murya a sanyaye kuma tana yar rawa ta ce.
Ya Mukhy are you alright? Why are you shivering?!
Ya ce umh cikin karfin hali, sai ta zauna a daidai kan sa ta ce. Na ji dadi yau ka dawo da wuri, amma kamar baka da lafiya sai itama ta soma karkarwa, ta tambaye shi da me zan iya taimaka maka? Akwai magani a dakin? Ya sake cewa umh da murya irin ta mai jin zazzabi, Amani ta gama firgita, ta yi kwanciyar yan bori a kusa da Mukhy don ta gane ba kalau yake ba, ko ta hanyar saukar numfashin sa da ke sauka a kai-akai cikin hucin zafi, don haka ta ji ta kasa korafin ina yake kwana da ta so yi, ko tambayar sa an kawo masa kwarkwarorin ne ta daina ganin sa yana kwana a nan?
Maimakon hakan, sai ta samu kan ta da cigaba da nacin tambayar sa Yaya Mukhy, don Allah da me zan iya taimaka maka? Kwarai a wannan yanayin yana bukatar taimakon nata, amma kuma…
Im not well! Ya bata amsa da kyar, ta kara matsowa daidai kan sa, bakin ta tasa daidai kunnen sa ta ce me yake damun ka Ya Mukhy? A gajarce yace sanyi. Amani sanyi nake ji, wani irin sanyi har cikin bargo na, duk da na rufa, amma kamar ina ciki kankara still, ko dai mutuwa zan yi? Amani ta kara gigicewa ta mike a sukwane to bari in kashe maka A/Cn, ta mike da niyyar tafiya kashe AC sai taji Mukhtar ya riko ta da hannnun hagun sa da ya dauki dumi da karkarwa, ta juyo ta dube shi idanun ta sungama kwalalowa, cikin karkarwar jiki ta tsaya, domin gabadaya ta rude ta rasa abin yi, sai ta ji muryar Mukhtar a hankali yana fadin.
“Amani sammin dumin jikin ki, it wil be absolutely okay for me.
Ta so ta gane me yake nufi wato dumin jikin ta yake so, shi kadai zai taimaka masa ya samu rangwamen sanyin da yake ji, amma da ko kusa bata kawo hakan a ran ta ba kuma a rude take, sai bata gane me yake nufi din da dumin jikin ta ba, don haka ta tsaya tana dawurwura, sai ji ta yi Mukhy ya ja ta a hankali ya kwantar, ba tayi musu ba ta bi umarnin sa, sannan ya daga bigilar rigar jikin nata ya cire ta ta sama, ya warware zanin jikin ta da kyar cikin rawar hannu ya jefar da shi a kasa, da wata irin azama Mukhtar ya manna Amani a jikin sa, wuyansa da sajen fuskar sa cikin nata wuyan. Ya kuma kudundune su cikin bargon tare. Wato su sha zafin zazzabin tare. In ma mutuwa zai yi, yana fatan ya mutu manne ciki jikin ta.. Ko hakan ya sa su tashi tare ranar lahira a matsayin mata da miji, tunda a duniya Allah bai yi zasu rayu tare ba.
Kusan zafin jikin Mukhy jikin Amani ya dinga komawa, irin yadda ya mannata a jikin sa ya sa komai nasa ya fara sauyawa, hatta saukar numfashin sa ya sauya, Amani ta samu kan ta da kara rungume Mukhtar, suna raba zazzabin nasa tare. Duk da cewa kuwa ba karamar wahala take sha ba, ga zafi kamar ya kashe ta.
Sai tsakar dare suka samu zazzabin ya soma sauka, ta gane hakan ne da yadda ya soma yanka gumi yana jika ta, amma hakan bai sa Amani ta tashi ba, duk kuwa da cewa ba barcin take yi ba ita har tsayin lokacin. A yau ji take wata irin nutsuwa na shigar ta, kasancewar ta cikin wannan intimacy din na body contact tsakanin ta da mijin ta Mukhtar Diffa, soyayyyar Mukhtar da wata gigitacciyar kaunar sa na kara ratsa ta, yanayin jikin ta ya soma sauyawa itama ta kara kankame shi, shi kam zuwa lokacin ya samu barci mai nauyi, sai ta kara manna shi a cikin jikin ta, tana fatan su dawwama a haka. Tana fatan kada gari ya waye.
A haka suka kwana, da asubah Mukhy ne ya fara tashi da kyar ya raba jikin sa da na Amani saboda yadda ta bi ta makale shi cikin jikin ta, wadda ya gama jikawa da gumin jikin sa jagab, ji tayi kamar ta rike shi ta hana shi tashin, don ta fi so su dawwama a haka. Mukhy ya je yayi wanka da ruwan sanyi kana ya dauro alwallah ya fito, yana mamakin abinda ya same shi jiya kamar farfadiya kamar bugun aljannu, ita sai a lokacin ma ta samu barcin ya zo mata.
Mukhtar ya soma kokarin tuno abinda ya faru da shi a daren jiya da mamakin ganin Amani kwance a kan gadon sa, don ya manta ma yadda aka yi ta shigo tsabar yadda zazzabin ya buge shi jiya. Amani ta ji alamar tsayuwar Mukhy a kan ta don haka ta bude ido tana kallon Mukhtar a hankali da idanun ta da ke cike da barci, shima yana kallon ta da kyawawan idanun sa yana kara son komai nata, mace kamar ita tayi wa kanta halitta komai nata mai ban shaawa ne da daga hankalin da namiji. A hankali ta lumshe idanun ta cikin nasa, tana jin karin son sa a ran ta, sai hawayen suka dirgo marasa dalili bare madafa.
Mukhtar ya dauke kai kamar bai ga hawayen ba, ya kada kai ya wuce ga sallayar da yake sallah a kai, ya ce mata.
Tafisu ki tashi ki sallah haka!.
Daga kwancen da take ta ce ciki raunin murya Ya Mukhy ka yafe min? Na yarda banida kirki, na yarda bani da hali, na yarda ban fi kowa ba, na yarda wanda yafi kowa shine wanda yafi kowa tsoron Allah, na tuba na bi Allah na bi ka! Kada ka sake tafiya ka bar ni, I promised to become a changed person. Muryar Mukhtar wannan karon cikin jin dadi da tausayi. Ya ce cikin kwantar da idanun sa a kan ta.
Kiyi sallah Amani, sai ki zo mu yi magana ta fahimta, bana so wannan ramar da kike faman yi, kin ji?
Gayun ma duk kin daina, haba Tafisu ni ina son gayun ki fa!”
Dadi ne ya kama ta, tana son tashi amma ta kasa janye bargon daga jikin ta, sabida rigar ta da Mukhy ya cire cikin zazzabin da ya makanta shi jiya. Daga ita sai bra da panty din ta.
Cigaba da kwanciyar tayi har sai da ya tada sallah, sanan ta yi maza ta dauki rigar barcin ta ta maida amma bata daura zanin atamfar ba, ta wuce nata dakin don ta shirya sosai.
Sosai ta zauna ta cancada kwalliya, gayu iya gayu, cikin wani (swiss lace orange colour) da aka yi wa dinki riga sa da siket matsatstsu, ta fesa turaren ta na dindin watau Elizabeth Arden.
Ta yi alkawarin yau ko kofar gida bazata bar Maina ya fita ba, jinyar sa zata yi da tarairayar abun ta, in an neme shi zata ce ai bai da lafiya, sai ta tabbatar ta wanke duk wata tsatsar ta dake ran sa, in dai ta amsa suna Amina-Amani, Aminatu Mamar Manzo, ba wai sauran mata ta rako duniya ba kamar yadda ake goran ta mata ta koina.
Zata gwada nata diyaucin na ya mace da kissar da ake cewa da ita aka haife kowaccen mu. Amani ta yarda za ta bada hakuri yau, ta duk hanyar da zata iya da irin nata baiwar da Allah ya yiwa kowacce diya mace. Ta koma dakin nasa ta same shi ya idar da sallah ya koma ya kwanta don jikin sa ba karfi. Hidima sosai take ta yi da shi yana daga kwance yayi dai-dai wai bayan sa ke ciwo, hatta tea yau har kan gadon sa ta hada masa ta kuma bashi da cokali a baki, har sai da ya ture ya ce ya ishe shi.
Amani ta koma taga an shirya musu kalaci kala-kala ta zubowa Mukhy farfesun koda da hanta ta kawo masa, ya ce na koshi fa, bani dai magani in sha, sai kiyi min tausa a bayan nan, duk jikina ciwo yake, akwai first aid box a cikin drawers din can, duba ki dauko min paracetamol,
Ta yi yadda ya umarta, ta dauko maganin ta ballo biyu ta hado da gorar ruwan Faro mara sanyi ta kawo masa, a baki ta saka masa maganin, sannan ta kafa masa gorar ruwan a baki ya hadiye.
Shi da kan sa bai yi marmarin fita ba yau, ganin yadda ake ta gatan ta shi, tuni zazzabin ya sake shi sai bin Tafisu da kasaitaccen kallo yake daga kwance, ga kwalliya ta fece ta fita tsara yadda yake son ganin ta, an yi daurin nan a kan goshi, irin dai yadda take yi a Katsina a lokacin da take kan ganiyar ta ta TAFISU! Yana hangota daga nesa yana hadiyar miyau yana faduwar gaba, domin babu karya Tafisu ta iya daukar wanka.
Abin mamaki shi da baya kashe wayar sa sam, amma yau sai ya samu kan sa da kashewa. Duk wanda ya neme shi ta waya ya samu wayar Maina a kashe, yau har Ummami ya kasa fita gaishe ta sabida uwargida ta murda kambu.
Ya Mukhy ka tashi muje na hada maka ruwan wanka ya kalle ta kasa-kasa yace ai na yi da asubahi, ko ke zaki cuda ni yanzun? Amani ta kai tafukan ta ta rufe fuska cikin jin kunya tana yar dariya, kuma sai ka tube a gaba na in hau cuda maka baya? Ai bazan iya ba kai ma bazaka iya ba.
Mukhy ya ce wa ya gaya miki bazan iya ba? Sai kace nima irin ki ne dan kauyen Faskari? Yanzu dubi daurin da kika yi a kan goshi, yammatan yanzu basa yin irin sa, sai na acuci, wannan daurin naki fa tun na zamanin Maryam Babangida
Amani me zata yi ba dariya ba! Bata san sanda ta tuntsire da dariya ba tayi ta yi, ta ce Ya Mukhy! A ina ka san a cuci da daurin Maryam Babangida kai ba dan Najeriya ba?
Ya mika mata hannu ya ce zo in gaya miki ta rufe ido tana murmushi domin cinyar sa ya gyara mata yana nufin ta zo ta zauna kai. Amani ta rasa inda zata sa kan ta don kunya, sai ta bige da cewa.
Ya Mukhy yau bazaka je fada bane?
Wannan shine kora a fakaice. Kin taba sa ni zuwa fada? Inada fadar da ta wuce wannan? Mukhtar ya fada tare da mikewa ya nufe ta da azama don ya fahimci neman guduwa take yi don ta fara tsorata da idanun Mukhy yau, caraf! Ya ruko ta ta baya, ya kuma rungumota gabadaya, ya kwantar da kan sa a kafadun ta, ya kai hannu ya shafi kirjin ta da ke zagin sa tun dazu, ahe ko bra babu jikin su, yayi wata irin ajiyar zuciya yace.
By Allah you will be the death of me AMANI!.
Ya juyo ta suka fuskanci juna kafin ya sumbaci kirjin cikin lumshe idanu, sannan ya zuge zip din rigar gabadaya. Amani ta runtse idon ta tana kiran sunan sa kafin ta soma tirjiya cikin jin tsoron yanayin da Mukhtar ya koma mata yanzu, tuni ya balle bra din cikin dan lokaci da wayo da dibara, yana mata hira mara kan gado a cikin kunnuwan ta, Amani ta soma kokarin janyewa don ta soma tsorata, ya ce.
Oh Amani, Oh! Tafisu, don Allah kada ki bar ni yau, in kika yi min haka, zaki kashe ni da rai na!
Mukhtar ya gama saddaqarwa yau in Amani ta zuqe masa a wannan halin, ko ta yi amfani da damar ta ce zata rama abinda yake yi mata itama a kwanakin nan, babu shakka gawar sa zaa dauka.
Tun tana neman zuqewa yana riko ta cikin lallashi da shafa gashin kan ta zuwa tsakiyar gadon bayan ta, don ita bata tsammaci wannan a yau ba, don ta san bai da cikakkiyar lafiya kuma, tsakanin ta da Allah jinyar sa ce tasa take yin duk abinda take yi, ba don ta ja hankalin sa ba.
Shi kuwa Mukhtar a yau kam duk wasu EXPERIMENTS DA YA DORA AMANI A KAN SU, YA YARDA AMANI BATA FADI KO DAYA BA!!!
Don haka ya yarda wannan safiyar ta zama first morning din su maimakon first night da ake cewa. Don ji yake kamar an kawo sabuwar lafiya an kara masa.
Kafin kace meye wannan har Amani ta soma yin laushi, sumbar da Mukhy ya soma mata ta soma shigar ta, ta ratsa har cikin kwanyar ta. Saura kadan Amani ta sume sailin da Mukhtar ya susuce a sumbatar kirjin ta, sai zuba sambatu yake cikin hargitsa gashin kan ta, cikin rokon ta shima ya tuba. Ya daina muzanta mata.
Can na jiyo Mukhy da wata yar murya tamkar ba tasa ba, yana fadi wa Amani cikin kunnen ta Ya bi Allah ya tuba, ya mayar da duka kalaman shashasha, ballagaza, rakiyar mata da yake kiran ta da su a baya, yayi rantsuwar cewa yau ya mayar dasu cikin cikin sa!.
Hawayen farin ciki suka zubowa Amani, ta dora hannayen ta a kan kafadun sa ta ce MUKHY, I LOVE YOU YA MUKHY! Ta soma mayar masa da martanin sumbar kaunar da yake mata, Mukhy ya karasa rikicewa Amani, don bai zaci wannnan alfarmar daga gare ta ba, ya ce.
Pls Tafisu hug me today, it is the beginning of our blessings, the truth which I. I must confess loudly.
“ TAFISU KIN FI SAURAN MATA A ZUCIYA TA!.
Sai hawayen farin ciki suka shiga tsere suna diga dis-dis, daga idanun Amina-Amani, zuwa kan kyakkyawar fuskar Mukhtar Issoufou Massaoudou, kawai sai Mukhy yasa halshesa yana dauke mata su, silla-silla, wannan ya kara rikita Amani, ta kara sakar masa jikin ta sosai, ya shiga yin yadda ya ga dama da komai nata, domin kalamai ne da bata taba zaton ji daga Mukhtar ba. Tunda shi kullum burin sa shine yayi kasa da ita, don ya rage mata jin izzar wannan perception din nata na tafi sauran mata!!!
Sune kuma kalaman da suka fidda duk wani tsoro da fargabar abun da ke ran ta, ta mika wuya ta bashi damar da ya dade yana nema, wato ya tara da ita a lokacin da take son sa, so na hakika. Ta mallaka masa zuciya da ruhin ta da gangar jikin duka a tare. Ta kuma karbi kowane tayin sa da hannu bibbiyu.
**** **** ****