AMRAH MACIJIYA Complete Hausa Novel
By Rabeauty
Page 2
Labarin mutuwar malam Abu ya riski kowa dake kauyen, hankalinsu ya matukar tashi dasu kaji cewa macijine ya kashe shi.
A fadar mai gari kuwa kowa ya taru ana jiran iliya mai macixai yaxo, yana isowa a kace ya bude macixai nai a duba bakin su aiko aka duba amman sarar batayi kama da bakin macixanba, haka aka taro akayiwa malam abu wanka da sallah aka kaishi makwancinsa.
Washe gari amrah tana daki tana bacci gwaggo ta shigo ta tayarda ita tana cewa”yar jikalle tashi Dan Allah na aikeki gidansu harira ki karbomin daudawa gurin innah”toh gwaggo ta tashi ta fito bayi ta shiga ta wanke fuskarta ta fito ta dauki mayafinta Green tasaka ta nufi gidansu harira, tana xuwa ta tararda harira na wanke_wanke gaisawa sukayi sannan ta nufi inda innah suka gaisa sannan tagaya mata abunda gwaggo ta aiko ta karba, bata tayi sannan ta fito xata wuce harira tace “amrah bayan la’asar xanxo mutafi rafi, toh kawai tace tafice daga gidan, a hanyarta ta komawa gida taga wasu samari su biyu suna mgn kuma akan mutuwar malam Abu ne, dan tsayawa tayi Dan taji me suke fada, dayanne yace” hmmmmm ni wlh wannan abun yafara bani tsoro ace anrasa gane wane macijine ke wannan kisan har yau”dayanne yadafa kafadarsa yana cewa “nima dai abun yafara bani tsoro, amma ai gobe ne maigari yace maccido maciji xaixo da kuma magani, kowa dake kauyen nan xa’a bashi yasha, duk Wanda a maciji toh yanashan wannan maganin xai fara rikidewa, kuma na rantse muddin wannan macijin ya kasance acikinmu toh wlh saina kashe shi har lahira wlh, gaban amrah ne yafadi saikuma naga tana wani shu’umin murmushi Wanda daka gani kasan bana alkhairi bane, gida ta karasa tana xuwa tabawa gwaggo daudawarta ta shige daki, da kallo gwaggo tabita sbd taga yanxu duk ta canxa kamar ba amrah taba, ynx mugun halin shiga daki tabijiro dashi, girgixa kai kawai gwaggo tayi ta tashi tashiga bayi, tana fitowa ta dauro alwallah ta nufo dakin, ta tayarda sallah, tashi amrah tayi itama tayi alwallah tayi sallah, bayan sun idar amrah ta juyo ta fuskanci gwaggo tace “waini gwaggo meyasa me gari xaice sai wani maccido maciji yaxo yabawa kowa magani, meyasa su baxasu yi bincikeba tukunnah ai…… Wani kallo da gwaggo tayi matane yasata kasa karasa xancen, waike amrah yaushe xaki fara tausayin mu ke kwata kwata bakida tausayi damuwar mutane bata damekiba, waini kam wace irin xuciyace dake, nidai nasan cewa baban ki da mamanki ba haka sukeba kuma nima dai ba halina kika biyoba, dan Allah amrah ki gyara kinji kuma gobe maccido xaixo da karfe biyar dan haka tun karfe 4:30 xamuje fadar mai gari kinajina, kai kawai ta daga.
Bayan sallar la’asar harira tayi sallama tashigo, gaida gwaggo tayi sannan suka fice xuwa rafi, suna tafe suna yar firarsu, can dai harira ta kasa hkr tace “waini amrah na tambayeki? Eh kawai tace, harira tace” wai meyasa naga tafiyarki ba irin tamu bace kina tafiya kina wani lankwasa kamar macijiya, dariya amrah tayi sannan tace “toh ai macijiyar ce” dariya harira tayi tace da baki fadaba wlh, shiru amrah tayi bata kara cewa uffanbah, suna isa bakin rafin suka xauna kafafunsu sukasa a cikin ruwan, wasu samarine su uku sukaxo wucewa dayanne ya hangesu yayi saurin tabo su yana cewa kai kunga wasu yam mata, dayan ne ya juyo yace kai ashe yau xansha dadina da yammatan nan, karasawa suka yi gurin su, da isarsu suka fara yimusu iskanci.
Harira ce tace da ganinku ba’a yankin nan kukeba Dan haka Dan Allah ku koma yankin ku, dariya suka sheke da ita dayan yasa hannu ya fixgo harira ya mannata da jikinsa ya shiga shinshinar wuyanta dayan kuma amrah ya cafko yana kokarin yaye mayafinda ta rufe fuskar ta dashi, amman yakasa wani wawan Mari yabata wadda saida gefen bakinta yafashe, harira kuma har sun kaita kasa suna kokarin daga mata riga, jin suka yi ance “ku kyaleta da wata irin murya” Wanda yamare tane ya juyo yace ke yimana shiru, kuma damun gama da ita kanki xamu dawo Dan haka kishirya, ya juya ga harira wadda tariga data sadakat sbd harya cire wando, hucin maciji suka ji a bayan su, ai da sauri suka saki harira suka juyo, wani irin raxanannen ihu suka saka a tare, sbd toxalinda sukayi da wata shirgegiyar macijiya green , harira mah tsoro ne yakamata nan tashiga neman amrah amma bata gantaba, jin sukayi macijiyar tace “saida nayi muku kashedi amma kukaki ji Dan haka dolene na kashe ku, kafin suyi wani yunkuri gaba daya tabi ta saresu nan take suka xube matattu a gurin, gurin harira tayo, harira koh harta juya xata fece taji tace” tsaya “ai da sauri ta tsaya, karasuwa tayi gurin ta, sannan ta girgije takoma mutum, ai harira na ganin AMRAH nan take ta sumee a gurin.
Rabeauty
*please vote, comment, and share *
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: AMRAH MACIJIYA Complete Hausa Novel
By Rabeauty
(4)
Harira na kaiwa bakin suro ta hadu da gwaggo xata shigo, yadda gwaggo taga harira a rikice neh yasa itama hankalinta tashi, tace menene harira koh wani abun neh ya samu amrah, harira ta bude baki xata gayawa gwaggo gsky cewar amrah macijiya ce, sukayi ido hudu da amrah tana mata wani irin kallo, ai da sauri tafita daga gidan har tana yin tuntube, juyowa gwaggo tayi dan tayiwa amrah mgn, amman me wayam tagani bbu ita a gurin, tsoro neh ya kamata tace “toh yarinya sai kace aljana hmmmmm gaskiya da sake, koh dai abun da ake fadi a kauyen nan gaskiya neh?
Toh idan kuma gaskiya amrah macijiya ce fah innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, tunowa tayi da maganar mai gari” asabe mutanen kauyen nan sun fara xargin jikanyar ki ba mutum bace, duba da yadda take tafiya duk mai hankali yagani yasan cewa tafiyar macixai ce, kuma kaf kauyen nan bbu Wanda yataba ganin fuskar ta daga harira sai innah mahaifiyar harira sai ke, dan haka inason kisaka idanu akanta muma xamu saka idanu, kuma muddin xargin mu ya tabbata toh fa xamu kashe ta, dan bbu makawa ita ke kashe mana mutane ”
Duk sanda ta tuna da wannan maganar sai hankalinta ya tashi.
Toh idan kuma ta tabbata ita macijiya ce kenan kashe ta xasuyi, inaaa baxan taba bari hakan ta faruba.
♀️♀️♀️♀️♀️
KANO STATE.
Wani makeken gida nagani Wanda duk layin bbu Wanda yayi kyansa, ciki na shiga wasu mata na gani a harabar gidan, wata yanmata ce a tsaye baxasu wuce shekara 25 bah,sanye take da riga da wando wa’enda suka bala’eeeen fito da surarta, fara ce amman bacanbah, sai wata mata wacce xata kai shekaru 48,kamarsu daya da yarinyar saidai tafita hasken fata, sai wani saurayi matashi Wanda baxai wuce shekaru 27 bah a duniya, irin black beauty’s din nan neh.
Gate aka bude wata hadaddiyar motace tashigo kirar benz Black color, parking space ta nufa da sauri driver ya fito yaxagayo ya bude kofar Baya.
Saida akadauki 5 minutes sannan ya xuro kafarsa ta dama, saidai ya kara wasu 5 minutes sannan ya xuro ta hagu, fitowa yayi yana karewa gidan kallo, subhanallah wannan balarabe koh shuwa’arab domin bbu inda yayi kamada hausawa kai wannan mah koh cikin larabawan da wuya a samu mai kyau irinsa, fari ne kal dugu mai faffadan kirji, jikinsa a murde yake gwanin ban sha’awa, matashine dan kimanin shekaru 33.
Kara suwa yayi gurin su “hajiya barka da yamma” kawai yace yayi shigewarsa ciki, dawani irin kallon tsana tabishi, inda xa’a bata wuka ace taka she duk Wanda ta so tohfa shine Wanda xata fara kashewa.
Driver neh ya kwaso masa luggage dinsa yanufu hanyar shiga falon, tsawa hajiya ta daka mishi tace dallah ajiye anan, da sauri ya aje ya juya, kallon NAJEEB tayi tace”daukar masa luggage dinsa kakai part dinsa kace masa idan yayi wanka yaxo yaci abinci”rai bace yaja luggage din yanufi part din yayan nashi,
Ke kuma suhaima wuce mutafi, wucewa tayi tana turo baki, falon suka shiga, woowhaduwa, wannan falon ai da kadan nasu vansh yafishi kyau, dramarda akeyi a bollywood, vansh da ridima
A bangarensa kuwa NAJEEB yana kai masa luggage dinsa ya juya yayi ficewarsa, koh gaisheshi beyiba.
Hajiya koh tana nan hakince akan makeken dining gefenta koh suhaima ce tana latsa wayarta, NAJEEB neh yaxo ya xauna kusa da hajiya, ba’a dadeba saiga wannan balaraben yafito cikin shigar kananan kaya fuska a daure hanyar waje ya nufa, da sauri hajiya Sarah tace “JALALUDDEEN baka ci abincifa” koh juyowa beyiba yasa kai ya fice, hajiya Sarah ji tayi kamar ta kurma ihu sbd takaici, NAJEEB neh yace mommy nace kibari nida kaina xan iya kashe shi ba dole sai anbi ta hanyar sa masa guba a abinci bah kawai kibari nasa su bardee sutare shi a hanya su aika manashi barxahu,
Da sauri suhaima tace “please aunty Sarah don’t kill my JALAL, kinsan yadda nake sanshi ke shedace kuma kinsan akan shi na kwaso kayana na dawo nan gidan, ke dallah rufemun baki Wanda koh kallo baki isheshi bah kinkasa jawo hankalinsa gareki, balantana muyi using dake gurin cikar burinmu mtswwww taja wani dugun tsaki hadi da tashi dg kan dining ta nufi room dinta,
Suhaima mah tashi tayi ta nufi room dinta akabar NAJEEB anan