AURE KO BOKO BOOK 1 AND 2 Complete Hausa Novel
AURE KO BOKO BOOK 1 AND 2 Complete Hausa Novel?
(Littafi Ga Matasa Maza da Mata)
SUMAYYAH ABDULKADIR
takorikabara@gmail.com
GABATARWA
Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai.
Duba da halin da matasa ke shiga a kasarmu Nijeriya a yau, daga mazan har matan, akan rashin aikin yi ga wadanda suka samu damar yin ilmin zamani mai zurfi da matsalolin da hakan yake haifarwa, sannan da halin wasu daga cikin manyan 'yan bokon wannan zamani na baiwa boko fifiko akan addini, yasa na yanke shawarar rubuta littafin AURE KO BOKO? Ba don komai ba sai domin ya zamo hannun ka mai sanda ga irin wadannan 'yan boko da matasa masu zurfin ilmi marasa aikin yi. Tasirin furucin iyaye akan 'ya'yan su mai kyau ko maras kyau, hakika shi bakin iyaye kaifin sa da tasirin sa yafi na reza. Sannan 'ya'ya amana ne a hannun mu, kasancewar Ubangiji yayi musu umarnin su yi wa iyaye biyayya sai da yayi tagociya ga cewa banda akan umarnin Ubangiji.
Ina fatan wannan dan littafi ya zamo mai amfani ga al'umma, matasa maza da mata, ya zamo sadaqatul jariya ga iyaye na ya yafe min kurakuran da ke cikinsa.
- Sumayyah Abdulkadir (Takori)
3rd June, 2021
GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a kowanne gidan radiyo ko kafafen yada labarai ba tare da izni na ba, ko copying dinsa a kafafen sada zumunta, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma daga Lauya na Barr. Sadiq Rufai Wali.
GODIYA
Ga dukkan members na Takori's online Forum, na gode da kaunar ku da goyon bayan ku.
FATAN ALKHAIRI
Ga duk makaranta littatafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda ban sani ba, ina godiya da yabo da fatan alkhairin da kuke yi mun, Allah ya barmu tare cikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi.
SHIMFIDA
BABI NA DAYA
A cikin babbar hedkwatar hukumar sadarwa ta kasa (Nigerian Communications Commission) da aka fi sani a takaice da (NCC) da ke kan titin Aguiyi Ironsi Street, Maitama, Abuja, motocin ma’aikatan su ke ta shigowa daya bayan daya harabar ma'aikatar suna fakawa a faffadar harabar ma'adanar motoci, wannan motar na wane waccan, duk da cewa ba ranar aiki ba ce, amma alamu sun nuna wani muhimmin taro ne za su yi na iya ma’aikatansu tare da (Board of Commissioners) din su a babban dakin taron su wanda ya fi kowanne girma cikin ma’aikatar. Duba da yadda suke ta shige da fice don ganin komai ya kammala ya yi yadda ake so kafin isowar Executive Chairman.
Kowannensu tsuke cikin suit mai kalar fari daga ciki, baki daga waje, wuyan ya sha tsuka da tie din bature, da takalma bakake sau ciki a kafafun su. Sai da duk suka gama hallara a dakin taron, suka nutsu wajen zaman su, kwamishinoni suka iso suka zazzauna, sannan suka ji daga wajen hall din dirin isowar jibgegiyar motar Executive Chairman wato PROF. ZUBAIR MOHD. NUMAN.
Farin dattijo mai kyakkyawar suffar fulanin usli da tsantsar ilmin boko. Inda ace ana kure boko to da mun ce Prof. Numan ya kure shi. Shi din fitacce ne, kuma sananne a kasarmu Najeriya akan harkar sadarwa, domin ya dade yana rike da manyan mukamai daban-daban a gwamanatin tarayyah tun kafin ya karbi ragamar (NCC), sannan tsohon malamin jami’ar Igbinedeon ne.
Prof. Zubair Muhammad bafullatanin garin Numan ne, don haka kallo daya za ka yi masa ka tabbatar an zuba kyau a zamanin kuruciya. An sha gwagwarmaya a ilmin boko da ma’aikatun gwamnati, sannan ana kan damawa da shi a shekarun girman sa, domin kuwa na hannun daman shugaban kasa ne, duk da ba ya siyasa, shi ne ya dora shi matsayin da yake kai a yanzu, wato Executive Chairman na Nigerian Communication Commission (NCC).
Prof. Zubair ya shigo hall din cikin kakkarfan takunsa, da ganin sa ka ga bakin bature, a gefensa hagu da dama wasu santala-santalan ‘yammata ne guda biyu; a ido daya ta girmi daya, sun yi shiga irin ta ‘yammatan zamani gogaggu, ‘ya’yan gata irin su, wato ‘ya’yan kusoshin gwamnatin Najeriya. Tafiyar su kadai abar kallo ce, yayin da suka maka bakin glass (prada) wanda ya cinye kusan rabin fuskar su. Mayafin jikinsu shi da babu duk daya. Har gara na babbar. Kallo daya za ka yi musu ka tabbatar ‘ya’yansa ne na cikinsa, sabida tsananin kamanninsu da mahaifin nasu, duk da cewa sun fi shi hasken fata kasancewar su mata.
Shigowar su hall din ke da wuya gabadaya ma’aikatan suka mike domin girmamawa ga shugabansu. Har sai da ya zauna a kujerar sa tare da ‘ya’yansa a dama da hagunsa a kujerar musamman da aka tanadar musu, sannan gabadaya ma’aikatan suka zauna a mazaunin su.
Bayan addu’ar bude taro daga limamin ma'aikatar mai gabatarwa ya yi bayanin makasudin taron, wato taron ba na komai ba ne, na taya murna ne ga ‘ya’yan shi Prof. Zubair ga kammala karatunsu daga jami'ar National Autonomous University, Mexico. Sannan Prof. Zubair ya mike ya yi jawabin godiya ga ma’aikatansa da kwamishinonin sa a kan hadin kan da suke ba shi wajen gudanar da ayyukan su na sadarwar Najeriya.
A karshen bayaninsa kuma ya ce, daga yau ya dora babbar ‘yar sa Engnr. Halimah Zubair Numan matsayin mataimakiyar sa wato (Executive Vice Chairman), ya kuma dora kanwar ta Hanan Zubair Numan a matsayin (Human Resource Manager), za su shiga ofis daga wannan satin mai kamawa.
Yana fatan za su ba su hadin kai wajen gudanar da ayyukan su tare da su, kamar yadda suka saba bashi. Su sani cewa ba ya hada komai da wadannan ‘ya’yan nasa guda biyu, dalilin sa ke nan na kawo su kusa da shi su yi aiki don ba zai iya barinsu su yi aiki a karkashin wani ba, balle a taka mishi su, shi ya sa ya kawo su karkashin sa.
Hanan sai gyada kai ta ke kamar jangwalagwada, tana taunar cingam kas-kas-kas, cikin jin dadin bayanan da mahaifinta ke yi. Ai gara duk su san matsayin su a gun Daddy tun yanzu, kada ma su kawo musu raini don sun gan su yara. Yayin da Haleemah ta sunkuyar da kai cike da jin kunyar wannan rashin kawaici na mahaifin ta. Me ya hada harkar ofis da kaunar da yake musu saboda Allah? (This is personal).
Daga nan shugaban bangaren daukar ma’aikata na baya (former Human Resource Manager) wanda yanzu ya koma karkashin Hanan ya mike cikin rashin jin dadi ya yi wa ‘ya’yan Prof. Zubair barka da zuwa ma'aikatar NCC, tare da alkawarta musu cewa, za su samu duk hadin kan da suke bukata tare da su. Ya yi bayanin ne cikin cijewa a madadin sauran ma’aikata, duk da kokarinsa na boye damuwar wannan ragin mukami da aka yi mishi da ‘yar cikin sa rana daya.
Daga nan aka fara ciye-ciye da shaye-shaye na alfarma, zukatan ma’aikata cike fal da magana wadda ba wanda ya isa ya furta. Don haka kowa ya hadiye abarsa. Taron da ya dauke su awanni biyu cif! Kafin a watse direba ya kwaso su Halima da Prof. Zubair zuwa gida.
Gidan Prof. Zubair na nan a unguwar Asokoro, wani tankareren gida mai ginin sama-da-kasa. Gabadaya ginin gidan an dauko samfur dinsa ne daga kasar Brunei. Sai dai abin da zai ba ka mamaki shi ne; daga shi sai ‘ya’yansa biyu suke rayuwa cikin wannan tafkeken tankareren gidan, sai tarin ma’aikata rututu maza da mata. Babu matar aure a cikin sa.
Asalin Prof. Zubair ya fito daga karamar hukumar Numan ta jihar Adamawa, ya auri matarsa uwar ‘ya’yansa Safeeyyah, aure na saurayi da budurwa wadda ita kuma Kanuri ce da ya auro daga Maiduguri, don haka Halima da kanwar ta Hanan kyawunsu na tudu biyu ne, wani irin sassanyan kyau da ya maida su tamkar ruwa biyu (fulani/kanuri). Ya basu wata irin kala mai kyau da daukar ido. Halima ce babba, sannan kanwarta Hanan, shekaru biyar kwarara Halima ta baiwa Hanan.
Hanan na da watanni tara mahaifiyarsu Safeyyah ta rasu a dalilin cutar (blood-cancer), wato kansar cikin jini. Daga dangin Halima har na Prof. Zubair sun yi kokarin karbar yaran su rike masa abin ya faskara, domin gabadaya soyayyar da yake yi wa mahaifiyar su ce ta dawo kan su. Ya dauki soyayya da kulawar duniya ya dora musu har fiye da kima, musamman Hanan wadda aka mayarwa sunan Safeeyyah.
Prof. Zubair shi ya ci gaba da rainon Hanan da madarar (NAN) har Allah ya raya ta, da taimakon dattijuwa (Nanny) da ya daukar musu daga Numan, amma fa aikin Asabe kawai in Zubair ba ya gida ne, da ya dawo zai janye ‘ya’yansa bangarensa ya ci gaba da kula da su da kansa baya taba gajiya da hidimar su. Sai da Halima ta yi shekaru goma sha biyu ne Babanta ya daina kwana kusa da ita, ya ware musu daki kusa da nashi.
Allah ya baiwa Halima wata irin kwakwalwa kamar kwamfutar na'ura mai kwakwalwa tun tana karama, wannan yana da alaka da tsadaddun makarantun da suke yi daga firamare har sakandire. Don haka ne ake ta yi mata promotion kan promotion ta gama sakandire a kananan shekaru tana da shekaru goma sha biyar.
Manyan darussan da Halima ta kware a kai sune lissafi da kimiyya, don haka tana gama sakandire Prof. Zubair ya kai ta kasar Mexico ta yi digiri na farko da na biyu cikin kankanin lokaci a fannin injiniyancin na’ura mai kwakwalwa (software engineering). Yayin da Hanan ta karanci digiri a kan (human resource management). A shekarar da Halima ta gama masters dinta, Hanan ma ta kammala digirinta.
Ko da suka dawo gida bayan kammala karatu Prof. Zubair ba tunanin da ya yi ban da ya zuba su a ma’aikatar sa karkashin kulawar sa, yadda babu wanda ya isa ya taka masa su. Ko su sha wahala yana raye.
Ba tare da la’akari da kankantar shekarunsu ba, ai dai suna da kwalayen da suka cancanta, domin Halima komai nata (first class) ne mai daraja ta farko, Hanan ce mai digiri mai daraja ta biyu. A hankali zai sa tsofaffin ma’aikata su wayar musu da kai a kan komai na NCC.
Haka nan yake zaune gwauro tun mutuwar Safiyyah bai kara aure ba, domin yana da labarin yadda matan uba ke wahalar da ‘ya’yan miji wadanda babu uwarsu a gidan, amma fa yana da dalilin da ke hana shi aure da ‘ya’yansa ba su taba sani ba, sabida yana matukar taka-tsan-tsan. Daga shi sai Ubangijin sa suka san yana dan taba neman mata.
Ba ‘ya’yansa kadai ba, babu wanda ya san da wannan bangaren nasa, sabida ba ya jan kowa a jiki, dangin sa gudun su yake sabida basu da shi, tsakanin sa da kowa harkar aiki ce kawai. Sannan bai amincewa su Halima yin kawaye ba bayan dawowar su karatu daga Mexico, kada a lalata masa su (wanzami baya son jarfa).
Kawar Halima ta jiki daya ce a duniya, wato Zarah Datti. Tare suka yi karatu a Autonomous, ita Zarah diya ce ga tsohon gwamnan Bauchi, har gobe suna tare da Halimah kusan kullum a waya.
Wadannan ‘ya’ya biyu na Prof. Zubair halayensu sun matukar bambanta. Duk da cewa kamar su daya a fuska da zubin halitta. Halima duk wani hali na mahaifiyarsu ta kwashe shi kaf, na gudun duniya da Yakanah. Yarinya ce mai hankali da sanin yakamata, sannan ba ta dauki duniya a bakin komai ba, mahaifinsu ya kware su ta fannin addini, domin bai ba su ilmin addini yadda ya kamata ba, ya fi bada karfi ga ba su tsadadden ilmin boko.
A tarayyarta da Zarah Datti, Halima ta koyi muhimman abubuwa na addini, wankan janaba, alwallah, hatta sallarta sai da ta gyara. Tana kuma ci gaba da neman sani a kan addini daga yanar gizo da kasasuwan wa’azin Malamai iri-iri data ke saya domin inganta addininta.
Yayin da Hanan duk wani halin mahaifinsu ta kwashe shi tsaf har da kari; fadin rai, son duniya da gudun talauci. Duk wata harka in dai da talaka za a yi ta, to Hanan ba ta cikinta. Shekarun Halima ashirin da hudu da haihuwa, yayin da Hanan ke da sha tara.
*****
Bayan sun dawo gida a ranar, da daddare suka hadu da mahaifinsu a babban falonsa, "Daddy", kamar yadda suke kiran Baban nasu Prof. Zubair, ya dubi kowacce yana murmushi da kofin tataccen inibi a hannunsa.
“Duk gajiyar taron ne Halima tun dawowar mu ban ji motsin ki ba?”
Halima ta yamutsa fuska, sannan ta jingina kai a kafadun sa. “Actually Daddy ina cikin wani tunani ne, sai na ga kamar matsayin da ka ba ni ya fi karfi na, Executive Vice Chairman ta NCC gabadaya fa! Ni ce mataimakiyar ka, kai kadai ne a sama na, ai ma’aikatan ba za su ga girmana yadda ka ke tsammani ba tunda sun san experience dina bai kai in karbi wannan babban matsayin ba”.
Prof. Zubair ya ajiye kofin hannunsa, ya maida hankalin sa ga Halima, ya ce, “Halima ki fahimci wani abu, Nigeria ta riga ta yi lalacewar da kowa nasa kadai yake ginawa, ba ki da matsalar komai zan daukar miki P.A (Personal Assistant), sannan tsohon mataimaki na ba korarshi na yi ba, na hada shi da wani mukamin ne daban da bai kai naki ba. Cikin ma’aikata kuwa duk wanda ba zai darajja ku ba ko ya girmama ku, wallahi korarsa zan yi, zan kara hada su in jaddada musu wannan”.
Halimah ta kama kai, “Daddy Please.... don’t, ka barsu haka, na tabbata za su bi umarnin ka kada ka yi musu tsauri da yawa a kan mu za su tsane mu. Na san yadda zan tafiyar da komai, amma kamar yadda ka ce din ne ina bukatar personal mataimaki kwakkwara, wanda ilminsa ya kai ya zama P.A dina”.
Ya ce, “Muna da applicants (masu neman aiki) da muka yi (shortlisting) din su ba da jimawa ba. Zan duba daya a ciki wanda na tabbatar bai taba aiki da kowa ba, kuma bai taba aiki da kowacce ma'aikata ba. Hikimar a nan shi ne, ina so ya zama abokin shawarar ki, kuma mataimaki wanda ba zai yarda da munafurcin ofis ba, don na ga duk sun shaqa da mukamin da na ba ku. To sai dai su mutu, amma kun shigo NCC ke nan in ga wanda ya isa ya taka min ku”.
Halima kasa cewa komai ta yi, sai Hanan ce ke dariya, ta ce,
“Shi ya sa nake son Daddyna, aikin ka yana kyau, Allah ya bar min kai Daddy”.
Ta fada tana mai kwanciya a gefen kafadarsa.
Prof. ya yi murmushi ya ce, “Anything for you my lovely daughters. Ni dai burina ku kula da kan ku, ku fita harkar maza, ba ku babu samari, don ba zan iya aura wa kowa ku ba, don ba na jin a wannan zamanin zan samu mijin da zai iya rike min ku yadda nake so ku samu a gidan aure.
Don haka da muguwar rawa gwamma kin tashi, don zan iya daure duk wanda ya bata muku rai, ko ya muzguna muku har sai igiya ta yi rara. Koda kuwa mijin auren ku ne. So, hakura da auren shi ya fi alkhairi. Ba abinda ba zan yi muku ba, ko me kuke so, ina kara jaddada muku da ku fita harkar maza duk mayaudara ne.
Sannan idan namiji ya wulakanta ku ni ba zan iya dauka ba, ba zan iya yafewa ba. In kuka maida hankali bisa ayyukanku, ba irin arzikin da ba za ku tara ba, ba abinda ba zan yi ba don ganin kun dore cikin kwanciyar hankali da jin dadi. Ina fatan kun fahimce ni?”
A sanyaye Halimah ta gyada kai, Hanan kuwa da karsashi ta amsa, “Mun fahimta Daddy, kuma insha Allahu za mu kiyaye. Allah na tuba ni Daddy ko a Mexico ban taba haduwa da namijin da ya yi min ba balle a Nigeria, ba'a haifi wanda zai ishe ni kallo ba, ka kwantar da hankalinka, ‘ya’yanka are safe at this side (‘ya’yanka a kebe suke a wannan bangaren)”.
Prof. ya ce, “Da kyau my daughter. Halimah kin yi shiru kina jin mu, tunanin me kike?”.
Murmushi Halima ta kakalo wanda iyakarsa fatar bakin ta, ta ce, “Daddy me zan ce to? Sai dai in ce Allah ya taimaka mana wajen sauke nauyin da a rataya a wuyan mu. I will work harder yadda ma’aikatan NCC duka za su amince da zabin ka, su ga cewa ko da gata da kananan shekaru to da cancanta cikin zabin da ka yi musu”.
Hanan ta yi dariya, “Wai ke Sis Leemah, me ye damuwarki da ma’aikata ne? Cewa nake duka karkashin Daddy suke? Ko basu amince da zabin Daddy din ba sai me? Sun isa su cire ki ne?”
Daddy ya ce, “Is okey Hanan, kin santa akwai concern, ni kuma na san za ta iya shi yasa na bata, and that is good nuna damuwa ga damuwar wasu, balle ma duka ba su da matsala. Your P.A will assist you also, sannan tsohon mataimaki na zai nuna miki yadda komai yake, ba za ki samu matsala ba insha Allah, as sharp as this brain of yours”.
Halima ta yi murmushi, “Allah ya taimaka mana Daddy, mun gode, Allah ya ba mu ikon faranta maka yadda ka ke faranta mana”.
Su duka biyun ya dora hannu a kafadunsu dama da hagu yana fadin,
“These are my daughters”.
Ko da Halima ta koma dakinta a wannan daren kasa barci ta yi. Tunani kala-kala ya yi wa zuciyarta kawanya. Shekarunta ashirin da hudu, amma Babanta ya fito fili ya ce, bai so ta yi aure a bisa wasu hujjojin sa wadanda addini ba zai taba karba ba. Ga shi ita tana son yin auren, don duk wadanda suka yi karatu tare har babbar kawarta Zarah sun yi aure sun barta, sai ta tsufa ta tsofe a gida? Ko sai ta kai shekarun da maza za su daina sha’awarta? Daddy dai so yake su rayu ba aure, kamar yadda yake rayuwar sa!
To kuma what about the call of nature? Na kowanne lafiyayyen dan adam?
A yanzu haka ma ba wani saurayi ko manemi tare da ita, duk sun gudu sun kama gaban su. Ba irin maneman da ba ta yi ba a Mexico, don Ubangiji ya kyautata halittar ta, amma barazanar Daddy na kullum cewa, muddin suka saurari saurayi zai dakatar da karatunsu, ya sa duk ta kore su. To sai yaushe Daddy yake nufi zai musu aure? Ko ko irin rayuwarsa yake so su ma su yi har tsufan su? Da yawon daren da yake zuwa basu san inda yake zuwa ba?
Tunani ne da ba ta da amsoshinsa, kuma ba za ta iya yi wa kowa maganar ba, ta bar wa Allah komai. Shine masanin gaibu. Ya yi mata zabin abin da ya fi zama alkhairi ga rayuwar ta.
****
BABI NA BIYU
La’asar sakaliya, a wani madaidaicin gida ckin wata unguwa mai tsohon tarihi a jihar Kano, wadda aka fi sani da 'Yakasai'.
Gidan wadatacce ne sosai, mai dakuna biyar ciki da falo. Madafi da bandaki biyu. A tsakiyar gidan bishiyar umbrella ce mai yawan ganyayyaki da nunannun ‘ya’ya yalaye sharr, amma ga dukkan alamu masu gidan ba sa tsinkar su. Watakila don ba su da yara ne. Ko basu iya cin 'ya'yan umbrella ba.
Inna Hajara ce zaune ta shimfida tabarma a karkashin bishiyar tana tankaden garin masara. A gefe ta kunna rediyonta tana sauraron shirye-shiryen gidan radiyon Freedom. Sallamar babban dan nata ta sa ta mika hannu ta rage sautin rediyon. Ya shigo cikin takunsa na nutsuwada haiba, ya ja kujera ‘yar tsugunne ya zauna yana fuskantar mahaifiyar sa.
Dogo ne sosai, baki mai dogon hanci. Kalarsa ta fi kama da ta mazan kasar Addis-Ababa, musamman lallausar sumar kansa da ta nuna shi ruwa biyu ne. Innar sa Hajara basudaniya ce ta usul, daga garin Jazeera, Sudan, mahaifinsa ne Bahaushe, wanda karatu ya kai shi Sudan ya auro Haajara, shekararsu goma tare Allah ya yi masa rasuwa, tun daga lokacin kuma ba ta koma kasarsu ba, sannan bata kara aure ba, ta maida hankali ga tarbiyyar ‘ya’yanta uku da uban su ya mutu ya bar mata.
A lokacin da maigidanta ke raye, sun yi rayuwa ta sukuni da yalwa, domin shi din Dr. ne a jami’ar Bayero, suna zaune a unguwar Janbulo tun kafin a yi gidaje da yawa a cikin ta. Bayan rasuwarsa rayuwa ta yi tsananin da dole ta sayar da gidan ta sayi karami a cikin gari wanda suke ciki a halin yanzu don ta tallafi rayuwa da karatun ‘ya’yanta. Ta kuma kama sana’ar gidan gona har yau, inda ake kiwon kaji da raguna har da shanu, inda ake fidda madarar shanu a sayar da kwai da kaji, in shekara ta zagayo lokacin babbar sallah ta sayar da ragunan da ta kiwata ta zuba wasu.
Da wannan sana’a Inna Hajara ke tallafe da marayunta. Suka kuma zame mata abin alfahari domin sun bada himma a karatu na addini da na zamani. Babbar ‘yarta Rabi’a ita ta gaji mahaifinta. A kasar sudan ta yi karatun shari’ar addinin musulunci a yanzu haka babbar lecturer ce a (Aminu Kano School of Legal and Islamic Studies), shi da ya biyo bayanta a wannan shekarar ya gama masters dinsa daga jami’ar Ahmadu Bello, inda ya karanci injiniyan sadarwa (Telecommunication Engineering) da kwalayen digiri da masta masu daraja ta farko.
Kanwarshi mai binshi Sa’adatu tana jami’ar Bayero tana karantar harshen Larabci (B.A Arabic) duk a kokari da jajircewar uwa irin Inna Hajara wadda ba ta hada komai da ilmin ‘ya’yanta ba, domin kuwa a cewarta babansu ya sha yi mata wasiyya a kan hakan.
Ba su cikin arziki, basu cikin daula, amma suna cikin rufin asirin Ubangiji wanda shi ya fi komai kwanciyar hankali. Sun fi karfin abinda zasu ci, da sutturar da zasu daura. Yayarsa Dr. Rabi’ah na nata kokarin wajen ganin ba su rasa komai ba tunda shi har yanzu bai fara aiki ba. Yana dai aikin koyarwa a wata makaranta mai zaman kanta wai ita ‘yan Dutse a Kano, bai jima da farawa ba.
Inna Hajara ta dube shi kamanninsa kullum da mahaifinsa marigayi Dr. Ismael Yakasai har razana ta yake. Wani lokacin ko kallonta ya yi sai gabanta ya fadi don hatta kwayar idanunsu iri daya ne. Gashin kansa da launin fatarsa shi ne irin nata na Sudanese. Saurayi ne ajin farko, wanda ya dama ya kutsa cikin ilmummuka daban-daban.
Babban sirrin kyawunsa shi ne dogon karan-hancinsa wanda har wani lankwashewa ya yi a karshe, ko maza ‘yan uwansa ba za su bar fatan ina ma a ce su ne shi be, balle kuma mata.
Shi kam zai ce ya sha wuya a hannun mata lokacin karatu a jami’a, musamman ‘ya’yan masu da shi, wadanda suke ganin kudin iyayensu zai iya jawo ra’ayinsa gare su. A hankali suka fahimci nagarta da kamewa, sannan uwa-uba rikon addini irin nasa daban ne dana sauran maza. Ba kowa Allah ke yiwa irin baiwarwakin da yayi masa ba. A daddafe ya kammala karatu ya huta, ya zauna a gida yana ta neman aiki lungu da sako. Shekarunsa talatin da daya cif, in har lissafin da yake yi daidai ne. Duk inda ya ji wani online vacant dake bukatar profession din sa sai ya shige cike ya aika.
Inna Hajara ta dube shi da murmushi, “Yau ina ka shiga ne? tun dazu ban ji dawowarka ba, bana jin ko abinci ka ci”.
Ya ce, “Inna, abincin nan yau ba zai shiga cikina ba, zuwa na yi in gaya miki gobe zan yi sammako zuwa Abuja ma’aikatar da suka yi mana aptitude watannin baya, sun kira ni da gaggawa. Sai a sanya mu cikin addu’a”.
Inna Haajara ta washe baki cikin murna, ta ce, “Addu’a ai duk bayan sallar farilla kuna cikinta, Allah ya shige gaba Ya bada sa’a, Ya kuma karawa rayuwa albarka”.
A daren ranar ya kulle kayansa kala biyu da duk abin da zai bukata, da ma jiya makarantar da yake koyarwa wato ‘YAN DUTSE suka biya shi albashin wata. Don haka ba shi da matsalar kudin mota har wajen kwana zai iya kamawa.
Ya kira Yayarsa Dr. Rabi’a ya gaya mata batun tafiyarsa Abuja, ta yi masa addu’a sosai, ko ita tana so kanin nata ya samu kwakkwaran aiki ya yi settling down ba aikin private school ba wanda babu fansho ba garatuti. Ga karatun shi mai matukar kyau ga kyawun sakamako, don dai yanayin kasar tamu ne sai alhamdulillahi.
Washegari tun asubahi ya bi motar farko zuwa birnin tarayyah.
****
Su biyar ne a kan luntsuma-luntsuman kujerun da aka tanada don baki maziyarta masu son ganin shugabar bangaren daukar ma’aikata. Tun safe suke kan layi har yanzu da azahar ta gabato, ya ga cewa komai runtsi dole ya je ya yi sallah, aiki dai na duniya ba na lahira ba. Don haka ya mike tare da gaya wa abokan zamansa zai je ya yi sallah ya dawo.
Kallon mahaukaci suka hau yi masa, bai kula ba ya yi wucewarsa. Su kam ai ko za su kwana wurin nan ba su matsawa ko nan da can.
Minti biyar bayan fitarsa sakatariya ta fito da takardu a hannunta ta kira sunan sa, duk cikin wadanda ke zaune babu mai wannan sunan. Don haka ta tsallake shi ta kira na gaba. Ya rungumi file din da credentials dinsa ke ciki tamkar ya rungume zuciyar sa, ya shigo ofishin da sallama.
Bayan ya idar da sallah ya dawo, nan suke gaya masa an kira shi ba ya nan. Ya mike zuwa ga tebirin sakatariyar, calmly ya ce,
“Excuse me Ma’am, I went to pray for some minutes”.
Wani kallon banza ta yi masa da ma gata kirista ce. Nan ta ke gaya masa, gara ma ya kama gabansa don layi ya riga ya wuce shi.
Kyale ta ya yi ya koma wajen zamansa ya zauna yana kallo daya bayan daya suka shiga suka fito, amma matar nan ta hana shi shiga. Wayar da ke kan tebirin ta ce ta yi kara ta daga da sauri, yana tsaye a kanta rungume da hannayensa a kirjinsa. Daga ido ta yi ta dube shi, sannan ta ce,
“Ok Ma!” Tare da kife wayar,
“Allah ya so ka, ta ce ka shiga”.
Murmushi ya yi wa kansa, ya dauki jakar goyonsa ya saba a baya, wadda ke dauke da dukkan takardunsa. Ya sanya kai a katafaren ofishin.
Yana shirin ganin dattijo ko magidanci, sai ya ga wata kyakkyawar budurwa son kowa na juyi a kan kujera, kwata-kwata shekarunta ba su fice na Sa’adatu kanwarsa ba.
Mamaki ne ko al’ajabi ya hana shi yin abin da ya kamata, wato gaisuwa, sai ya tsaya kikam yana kallon ta. Kyawunta kam zai iya cewa bai taba ganin mace mai irinsa ba. Ba wannan ne abin da ya tafi da hankalinsa ba, kankantar shekarunta ne da wannan mukamin.
Hanan ta kufula da kallon da ya tsaya yana yi mata, babu gaisuwa babu nuna girmamawa sai kallo. Ga ta da son girma kamar gyambo. Ta ga kuma kamar kallon raini yake yi mata. A fusace ta ce,
“Please get out, idan ka zo ne don ka kare min kallo”.
Ya sauke idanunsa kasa, “I’m sorry Ma”. Sannan ya samu kujerar da ta dace da shi ya zauna. Amma sai Hanan ta maida kai ga files din da ke gabanta, ta ce,
“In ka gama zama ka san inda dare ya yi maka. Ba zan duba takardunka ba, domin ba zan dauki mayun kallon mata ba”.
Ya yi ‘yan mintuna a zaune ya kasa cewa komai. Zai so ya gaigaya mata magana cewa, ba ta isa ya tsaya kallonta ba, bata da abinda zai kalla; rather mamakin mahaukacin da ya ba ta ofishin yake.
Cikin bacin rai ya mike ya juya ya fita, yana fadi cikin ransa; ashe NCC ta mahaukata ce, in ba haka ba ya za a yi a dauki babban mukami irin wannan a bawa wannan shashashar yarinyar da ba ta ko kai shekaru ashirin ba?
Shi ma in dai irinta ne za su shugabance shi suna ba shi order ya fasa aikin, ba ya so.
Ta bi shi da kallo baki bude don ta dauka zai yi apologizing.
Tafiya yake yana zancen zuci ba tare da lura da cewa a kan titin motocin ma’aikatar yake tafiya ba. Daidai lokacin da wata sullubebiyar mota ta taho kan titin da gudu, direban motar yana ta yi masa horn amma bai ji ba tsabar bacin ran da wannan yarinyar ta kunsa masa. Yana tuno wahalar da ya sha na zuwa Abuja da albashinsa da ya karar wajen kudin mota, da kama daki da yayi a hotel, ga layin da ya hau tun karfe bakwai na safe, har zuwa yanzu bai sanya komai a cikinsa ba.
Sannan yarinya kanwar bayansa ta zo ta yi masa wannan wulakancin? Tun fil’azal kowa da ya sanshi a duniya ya san abu daya da ba ya dauka a rayuwarsa shi ne raini, musamman daga wanda ya girma.
Duk kokarin da Halima ta yi na sarrafa sitiyarin motarta sai da ta dauke shi ta yi cilli da shi a gefe. Ta take totur din motar tana kiran sunan Allah. Securities da tsilli-tsillin mutanen da ke wajen suka yo kansa don ba shi taimako. Halima ta bude kofar motar ta fito sanye cikin doguwar riga fitted gown ta wani sassalkan yadi ruwan madara, ta yane kanta da wani karamin mayafi baki, idanunta rufe cikin prada dinta kamar kullum.
Sabanin Hanan, Halima ba ta so a tuka ta a mota, ko a hada ta da mai tsaron lafiya a matsayinta na EVC/CEO, tafi so tayi driving kanta in dai ofis za ta je, sauran wurare ne ta ke shiga karkashin kulawar masu tsaron lafiya for security reason.
Suna kokarin sanya shi a wata mota ta ma’aikatar NCC don kai shi asibiti sakamakon jinin da yake zubarwa, Halima ta ce,
“Ku sanya shi a motata, mutum biyu ku shigo mu je tare”.
Jikinta sai rawa yake don ba ta taba kade ko zakara ba balle dan mutum. Wani asibiti mai zaman kansa suka nufa kusa da ma’aikatar inda aka karbe shi da gaggawa sabida matsayin Halima.
Duk wani taimako da ya kamata sun ba shi, sun masa dinki a goshinsa da gyara gocewar kashi, sauran kananan ciwuwwukan duk sun manne su da plasta. Likita ya ce, za su rike shi tsawon kwana biyu don tabbatar da cewa babu internal injury. Halima ta kama daki V.I.P aka shigar da shi can bayan likitoci sun gama duba shi sun ba shi kwanciya ta kwanaki biyu.
Gida ta koma don ya samu barci sakamakon allurar barcin da aka yi masa. Aikin da ta je domin ta yi mai muhimmanci dole ta fasa shi. Wanka ta yi tare da sallar la’asar, sai a lokacin ta samu nutsuwa. Ta kira mai girkin abincinsu Helen ta ce ta shirya mata lunch a basket ta sanya mata a mota za ta fita nan da twenty minutes (mintina ashirin).
Tana shiga mota domin ta tuka, sai jakarsa da ke gefe wadda wani security ya sako a motarta ta dauki hankalinta. Ta san babu kyau yi wa mutum bincike, amma haka kawai ta ji tana son ta duba ba don tsoro ba sai don tsaro, ta san wane mutum ta ke dawainiya da shi.
Babu komai cikin jakar sai takardun shaidar karatu (qualifications) tun daga firame har jami’a. sai kuma CV wanda ke dauke da dukkan bayanan da suka jibanci ilminsa da shi kansa. Kwarai hazakarsa ta yi matukar impressing dinta. Sannan kamannin sa, kwarjinin sa da haibar sa sun tsaya mata a rai.
A hankali ta maida takardun cikin jakar, sannu a hankali ta ja motar ta fita daga harabar gidansu zuwa asibitin Nizamiye.
Yana zaune a gefen gadon kafafunsa a kasa, baki, dogo, siriri wanda kai tsaye za ka kira shi da handsome, gantleman. Ga Halima ba wannan ne a ranta ba; kimarsa ta karu a idanunta ne bayan takardunsa da ta gani. Ta kuma tabbata neman aiki ya kawo shi NCC don tana sane da zuwan applicants din da aka yi shortlisting dinsu, wadanda aka yi wa aptitude test tun kafin kama aikinsu ita da Hanan. Wanda muhimmin abin da ya sa Daddy bankado takardunsu don ya nema mata P.A ne a cikinsu.
Da sallama ta shiga, ya dago manyan idanunsa ya dube ta. Ba su da maraba ita da yarinyar dazu, abin da ya sa ya gane ba ita ba ce shi ne, wannan ba ta kai ta haske ba, sannan ta fi ta kaurin jiki, kuma tana da tauwadar Allah a gefen dogon hancinta. Sai ya kasa amsa sallamarta.
Ta ja farar kujerar da ke gabansa ta zauna.
“I’m sorry, ni ce na buge ka dazun accidently kana tafiya bisa titi, na yi horn, na yi horn ba ka matsa ba. Ina kokarin kauce maka wata motar ta fuskanto ni dole motata ta shafe ka ka yi hakuri please, tsautsayi ne”.
Ta fada cikin tattausar muryarta wadda ta kara tabbatar masa ba yarinyar dazu ba ce. Wannan ta san mutuncin mutane kuma tana da hankali. Amma duk yadda aka yi suna da kakkarfar alaka.
“I’m Halimah Numan”.
Ta fada in subdued (cikin yin kasa da murya).
“I’m Hashim Yakasai”. Ya bata amsa a takaice.
“Na gode Mr. Hashim, takardunka suna wajena, in ka amince zan yi amfani da su, daga nan zuwa jibi da za a sallame ka”.
“Babu komai”. Ya fada yana kara mamakin ma’aikatar da ya kawo kansa, ma'aikatar da tayi ficce da kaurin suna a Najeriya, highly compepetitive, ashe NCC din duka ma’aikatar kananan yara ce?
“Ga abinci Mr. Hashim, let me serve you”. Ta fada tana mai janyo kwandon da ta shigo da shi. Ta zuba lafiyayyen abincin da farfesun kayan ciki a dan karamin bowl ta mika masa. Karba ya yi don cikinsa rabonsa da abinci tun daren jiya. Ba bata lokaci ya soma ci yayin da Halima ta maida hankali ga danna wayar hannunta.
Da ya gama cin abincin ne ta soma yi masa tambayoyi, daga wane gari yake? Me ya zo yi NCC har ta buge shi? Me ya kautar da hankalinsa haka?
A takaice ya ce, ya zo intabiyu ne, unfortunately bai samu ya yi ba. Hawan shi kan titi kuwa ya yi nisa a tunani ne, daga Kano yake.
Daidai lokacin aka kira sallar magriba, don haka Halima ta yi masa sallama da alkawarin gobe kafin ta shiga wajen aikinta za ta zo ta ga lafiyarsa.
Halima ta koma gida ta tarar Daddy da Hanan sun dawo. Sallah ta yi, sannan ta fadi abin da mai girkinsu za ta kawo mata. Sai da ta gama cin abinci sannan ta sanya takalminta na zaman gida ta nufi falon Daddy.
Prof. Zubair ya kura mata ido. Tana karasowa zuwa kujerar da yake zaune, ta zauna gefensa tare da dafa kafarsa ta dama.
“Daddy sannu da gida”.
“Yau ina ki ka je Halima throughout ban ganki a ofis ba?”
“Tsautsayi ne ya same ni Daddy, wani bawan Allah na buge da mota, yanzu haka na kai shi asibiti yana karbar treatment, ina wajensa tun dazu”.
Hanan ta ce, “To tunda kin kai shi asibiti kin biya kudin magani zaman me za ki je ki yi a wajensa?”
Harararta Halima ta yi, “Ki daina sa min baki in ina magana tunda ba da ke nake magana ba”.
Hanan ta zumburo baki, ta kauda kai.
Halima ta dubi Daddy tana murmushi, “Daddy I have found my P.A (na samu P.A dina)”.
Prof. Zubair ya kalle ta yana dan cakuda fuska, “Bayan ma’aikatan da Hanan ta dauka yau? Na zata a cikinsu za a zabi daya?”
Girgiza kai Halima ta yi, “No Daddy, na zabi Mr. Hashim, bari in kawo maka takardunsa ka gani. Shi ma ya yi aptitude tuntuni”.
Ta mike zuwa dakinta ta dauko takardun daga inda ta adana su. Ta kawo wa mahaifinta.
“Hashim Isma’eel Yakasai”. Prof. Zubair ya fada a fili, “Takardunsa are excellent. Tunda kuma ya yi miki shi ke nan, gobe Hanan sai ku ba shi offer”.
Hanan ta sake zumburo baki.
Halima ta yi wa mahaifin nasu godiya, ta ce za ta je ta kwanta don gobe sammako za ta yi tunda yau ba ta je ofis ba.
Washegari ma haka Halima ta karbi breakfast ta tafi da shi asibiti.
Yana kwance idanunsa a lumshe. Tsammani za ka yi barci yake yi, nan kuwa zugin dinkin da ke goshinsa ne ya dame shi. Halima ta yi sallama ta shigo biye da ita nurse ce dauke da kwandon abinci. Ya bude idanunsa da ke lumshe sun canza launi sabida rashin barcin da bai samu ba jiya. Ya amsa sallamarta, Nurse din ta ba shi magani ta fita bayan ta zuba masa abincin da Halima ta kawo.
“Ya ya jikin Mr. Hashim?”
“Alhamdu lillah Ma’am”.
Daga haka duk suka ja baki suka yi shiru. Daga bisani Halima ta duba agogon (swatch) da ke daure a damtsen hannunta. Ta dube shi fuskarta na nuna kulawa.
“Lokacin shiga ofis dina ya yi, idan na tashi zan biyo ta nan in kara ganin jikin naka. Ga karin kumallon ka, let me serve you…” Ta fada tana janyo kwandon gabanta, ta zuba mishi chips da egg da plaintain a plate ta hada mishi shayi mai kauri ta ba shi, sannan ta yi masa sallama ta juya cikin takunta na nutsuwa ta fita.
Shi kuma ya bi ta da kallo, kafin ya sauke idanunsa a kan farantin hannunsa, cikin ransa yana jinjina wannan kirki irin nata, duk da cewa daga ganinta ka ga ‘yar wani kusa a kasarmu ta Najeriya.
****
BABI NA UKU
Engnr. Halima Zubair Numan, ta shiga ofishinta a kan lokaci yau. Ta daidaita bisa teburinta yayin da sakatariyarta Rose ta shigo mata da files din da za ta duba. Da adadin mutanen da za ta gani a yau. Amma ko me take yi tunanin patient dinta na Nizamiye Hospital yana manne cikin ranta.
Waya ta dauka ta buga ofishin Hanan suka yi magana, sannan ta kira sakataren Hanan ya karbi umarnin da ta ba shi. Kafin lokacin tashinta ya yi offer din Mr. Hashim ta shigo hannunta, don haka tana tashi asibitin Nizamiye ta nufa tana murza sitiyarin motarta cikin gwaninta.
Ta same shi yana sallar la’asar, za ka iya gane daga wanka ya fito, domin sumar kansa a jike ta ke, sai dai kayan jikinsa su ya mayar, wadanda har da digon jini a jikinsu. Halima ta ji ba dadi, me ya sa ba ta yi tunanin sayo masa ko da jallabiyya ba ne? Ko ta karbo masa kayan Daddy?
Da ya idar da sallah ne suka hada ido a lokaci guda, Halima ta yi masa murmushi. Sannan ta ja kujera ta zauna, shi ma ya koma gefen gadon ya zauna. Magana ta ke a waya inda ya fahimci tana kwatanta wa wani dakin da suke ne. Ba jimawa sai ga wata budurwa kabila ta shigo dauke kwandon abinci. Tana gaishe su ba ta tsaya ba ta fita.
“Ka yi hakuri Mr. Hashim, I was too occupied at office ban samu kawo abincin rananka a kan lokaci ba. Ga wannan please ka duba”. Ta mika masa takardar da ke kalmashe cikin ambulan sannan ta maida hankali ga zuba masa abinci.
Hashim Yakasai ya dauka mafarki yake yi, ko ko cikin zautuwa yake ganin abin da yake gani rubuce a kan takardar. Doguwar takardar daukar aiki ce (offer letter) da NCC dauke da matsayin Technical Assistant ga mataimakiyar shugaba. Sai ka’idojin daukar aiki. Ya tambayi kansa, “Ba dai wannan yarinyar da ke gabansa ce mataimakiyar shugaban NCC ba? He can’t believe it”. Ya kasa gaskata idanunsa.
“Ina fatan Mr. Hashim zai yi farin cikin yin aiki tare da ni, matsayin personal assistant dina?” Ta fada tana mika masa plate din abinci.
Hashim ya kasa magana don har yanzu bai fita daga shock din da yake ciki ba. Amma a karshe sai ya ga bai kamata ya yi mamaki ba, don da ganin Halima ka ga mai dimbin ilmi a kananan shekaru, sannan bai san matsayin ubanta ba. Don haka daukansa aiki da ta yi a dare daya bai kamata ya mamakantar da shi har haka ba.
Ya karbi plate din da ta ke mika masa, sannan bakinsa ya motsa wajen yin godiya. Godiyar da bai san iyakar wadda zai yi ba. Halima ba ta bi ta kan godiyarsa ba ta mike tana rataya jakarta.
“Zan wuce gida Mr. Hashim, sai gobe kuma, direba zai zo ya tafi da kai ka dauko kayanka daga inda ka sauka. Muna da estate na ma’aikatan mu, za a ware maka gida a yau in ya dauko ka zai wuce da kai can. Sannan akwai motar office da za ka rika amfani da ita, gobe zai damka maka mukullin in ya kai ka”.
Tana fadin haka ta juya a kan duga-duganta tana fadin,
“Na barka lafiya Mr. Hashim”.
Hashim saukowa ya yi daga gadon ya yi sujudush-shukr, ya dauko wayarsa da ya jona a caji ya kira Inna Hajara da yayarsa Dr. Rabi’a duk ya gaya musu wannan nasibi da ya same shi rana daya. Kusan sun fi shi farin ciki, Inna nata zabgawa Halima addu’a.
Wannan shi ne mafari, tushen duka kaddarorin Halima da Hashim. Wanda yake a rubuce tamkar zanen dutse a allon kaddarar su. Kaddarorin da da a ce sun san za su faru, da tun daga asibiti kowanne ya kama gabansa. To amma ita kaddara rubutacciya ce da ba abin da ya isa ya kankare ta.
****
Hashim Yakasai, zaune a kan kafafunsa ya sunkuyar da kai yana sauraron Prof. Zubair, a lokacin da Halima ta gabatar da shi gare shi. Prof. Zubair ya dube shi ya dinga zubo masa tambayoyi kamar ma’aikacin BBC. Hatta tushen uwarsa da ubansa sai da ya tambaya, da sana’ar mahaifinsa kafin ya rasu, tunda Hashim yake bai taba haduwa da murdadden dan boko irin Prof. Zubair ba. Daga karshe Prof. ya ce,
“Ka yi hakuri tambayoyina sun yi yawa, wasu kuma za ka ga ba su da alaka da aikinka. And you may find my questions too strict (za ka iya jin tambayoyina sun yi tsauri), hakan ya faru ne saboda da gudan jinina za ka yi aiki, yaran da bana hada su da komai, don haka duk wanda zai yi alaka da su dole in sanshi ciki-da-bai. Sannan in ja masa kunne… my two daughters are precious than diamond!. Ko da wasa kada ka yi abin da zai bata wa Halimatu rai, ka yi duk abin da ta umarce ka ba tare da musu ba. Ka yi mata biyayya kamar yadda za ka yi mini muddin kana so aikinka ya dore.
Idan ta kawo min complain ko guda daya a kanka, ka sani ka bar NCC kenan. Ina karbar excuse a kan komai amma ban da akan my daughters. Sannan duk abin da ka gaya min ba wai na hau kai na zauna ba ne, a’ah, ina da mutane a Kano da zan sa su binciko min komai a kanka. Idan na samu karya ko daya cikin abin da ka fada a kanka ko iyayenka da muhallin ku, ka bar NCC. Ina fatan Mr. Hashim ya fahimce ni?”
Hashim kansa na duke, yana mamakin wanna dattijo ya amsa da cewa,
“Na fahimta ranka ya dade, kuma insha Allahu zan kiyaye”.
Halima ta lumshe idonta cikin takaicin Daddyn nata, ba ta san yaushe zai daina wannan halin nasa na rashin kawaici a kansu ba.
Hanan kuwa ba abin da ta ke so a duniya irin ya dinga wannan gargadin a kansu, wannan ne ke ba ta damar taka su yadda ta ke so, yake kuma kara mata fadin rai da ji da kai.
Daga wannan ranar Engnr. Hashim Yakasai ya kama aiki a NCC karkashin ofishin Executive Vice Chairman wato Engnr. Halimah Numan. Ofishinsa na manne da nata kamar ciki da falo ne, sannan a tadda ofishin sakatariya inda ake karbar baki. Cikin dan lokaci suka gane cewa, kowannensu mai kwazo ne har fiye da dan uwasa. Tun Hashim na mamaki idan Halima tana initiating abubuwa tana fadin yadda za su tsara su cikin ilmi da sanin makamar aiki, da yadda shi kansa mahaifinta ta ke cin sa gyara a wasu abubuwan, Hashim har ya zo ya daina mamaki. Ya yarda yarinyar gifted ce. Babanta ya san haka, shi ya sa ya ba ta matsayin da ya san za ta iya rikewa.
Shi yake handling duka al’amuranta, kama daga shirya mata appointments, seminers, workshop na ma’aikata da kula da bayanan sirrinta.
Cikin wata guda kacal wani irin sabo da aminci mai karfi ya shiga tsakaninsu, wanda kowa da ke aiki karkashin Halima ya san Mr. Hashim yana da wani special reception fiye da na kowa a gare ta.
Hanan ba zuwa ofishin Halima ta ke ba, sai da babban dalili. Duk wata magana da ta shafi aiki a ofis ta waya suke yinta ko Hanan din ta aiko sakatariyarta. Sai a gida suke haduwa. Ta san Halima ta dau P.A, amma ba su taba katarin haduwa ba, don Mr. Hashim ba ya zuwa gidan Prof, sabgar aiki ce kadai ke hada su, in sun tashi kowa ya nufi gida shi ke nan, inda wani abun kuma sai dai su tattauna shi ta waya.
Yau litinin Mr. Hashim ya tashi da zazzabin cizon sauro (malaria) duk karfin halinsa ya kasa fita aiki, ya kira sakatariyar Halima ya fada mata. Ko da Halima ta iso ofis ta ga kujerarsa wayam, kasancewar sai an wuce ta ofishinsa za a isa nata ofishin. Ta tambayi Rose ko ina yake? Nan ta ke gaya mata wayar da suka yi na rashin lafiyarsa ba zai iya driving zuwa ofis ba.
Halima na aiki, amma sai ta samu kanta da shiga damuwa. Damuwar da ta rasa dalilinta. Amma da ta yi tsam da ranta, sai ta fahimci rashin lafiyar Hashim ne ya tsaya mata a zuciya, ya hana ta walwala. Ta san duk ciwon da zai kwantar da hashim ya kasa fitowa aiki, to ya isa a kira shi ciwo. Domin kuwa Mr. Hashim jarumi ne ba a fannin aiki kadai ba, har ma a koshin lafiya. He is always healthy and energetic.
Don haka da ta tashi aiki sai ta samu kanta da karya kan motarta Toyota Avensis ta nufi unguwar Colorado Close inda estate din ma’aikatan NCC yake.
Gidaje ne (flat) duk iri daya. Akwai parking space wanda akalla zai ci motoci biyu a gaban kowanne gida. Da shuke-shuken korran furanni. Dakunan barci biyu da falo, sai wadataccen kitchen da toilet manne da kowanne bedroom. Akwai faffadan terrace a gaban gidan wadda ke dauke da kujerun shan iska.
A hankali Halima ta yi parking motarta kusa da ta Hashim ta dauko jakarta ta fito. Sau biyu ta danna kararrawa kafin Hashim ya iya fitowa ya bude, wanda ke dukunkune cikin blanket, idanunsa sun kada sabida zafin zazzabi. Yana sanye da sweater mai kauri (V-neck) ruwan toka da bakin trouser. Yana bude kofar idanun ta suka sauka cikin nasa. Hashim da Halimah, a tare suka ji wani abu mai mai karfi ya fizgi zukatansu a lokaci guda. Ba karamin kyau ya yi mata ba duk da kadawar da idanunsa suka yi, sai hakan ya ba su wani launi mai sanyaya gabban diya mace. Ji ta yi wata irin kunya ta lullube ta. Me ya kawo ta? Har gadon barcinsa?
Duk irin hudubobin da Daddy ke yi musu kullum na su nisanci maza! Idan Daddy ya san ta biyo Hashim gida wane hukunci zai yanke mata??
Hashim ya kauce daga hanya yana kokarin saisaita kansa a gaban uwar gijiyar tasa, kada ta fahimci effect din da ta yi masa a yau, wanda ya fito kai tsaye daga kwayar idanunta zuwa cikin nasa, ya haifar da wani intimacy na zuciya da zuciya. A dakushe muryar sa ke fita, inda ya ce keenly.
“Welcome Halimahhh!".
Rana ta farko da ya taba kiran sunanta na ainahi, ba tare da tunanin ko hakan zai zama laifi ba. He used to call her; Ma'am. Cikin jin kunya irin wanda bai taba gani a tare da ita ba ta sunkuyar da kai tana wasa da mukullin motar hannunta.
“Ai ba sai na shigo ba ma, I just came to check on you, ya ya jikin naka?"
“Tunda har kin zo, to ki karasa ladanki ki shigo daga ciki ki sha ruwa, na san daga ofis ki ke, ki dan huta kadan sai ki tafi Ma'am”.
Ba ta san me ya sa ta kasa yi masa musu ba. Gabadaya yau ya canza mata kamar yadda ita ma ta canza masa. Wata sabuwar fuska ce da ita mai dauke da kunya, wani muhimmin bangare na diya mace da bai taba gani a tare da ita ba. Kullum ayyuka ta ke kamar namiji, order kawai ta ke bayarwa (with guts and professionalism). Amma yau sai ta fito a asalin kamanni da dabi’un diya mace. Ta zauna a doguwar kujerar leda (leather chairs) farare da ke falon tana karewa falon kallo. Hashim ya tsara shi da kyau. Babu tarkace sosai, daga kayan kallo sai mackbook da yake amfani da ita bisa wani dan tebiri. Sai ash tray da ‘yan kananun tobbacco a ciki. Mamaki ya kamata, da ma Mr. Hashim yana taba smoking?
Kasa yin shiru ta yi a lokacin da ya iso dauke da kofunan glass guda biyu, lemu mai sanyi na chivita da gorar ruwan aquafina, ya zo har gabanta ya ja tebur ya dora. Cike da dan murmushi mai nuna girmamawa ya ce,
“Ranki ya dade, ruwa ko lemu zan zuba ma bakuwata?”
Gani ya yi tana girgiza kai, ta tsare shi da ido, sannan ta ce authoritatively,
“Mr. Hashim why are you smoking?”
Ya yi saurin kai dubansa ga dan ash-tray din, shaf! Ya manta bai kawar da shi ba, other side dinsa ne da ko Innarsa ba ta sani ba, kuma bai taba son wani nasa ya sani ba. Ya sa hannu ya dan shafo kansa daga keyarsa zuwa goshinsa cikin rashin sanin abin cewa. A hankali ya dubi tsakiyar kwayar idanunta da ke kafe akan sa ya ce,
“Yes Ma! But not always, only when I’m bored”.
Halima ta kura masa ido, yana ji kamar furious (fusatattun) idanunta na yi masa bulala, ta ce,
“Da hankalinka da tunaninka da ilminka ka ke siyan abin da zai cuce ka Mr. Hashim? Idan ba ka damu da rayuwar ka da lafiyar ka ba I know your family cares, other people around you also cares… ya kamata ka yi kiwon lafiyarka ko don saboda su. I’m highly disappointed da zuwana gidanka, because I hate it”.
Ta dauki jakarta za ta fita, taku biyu ta yi ya sha gabanta.
“Please Halima excuse me, na yi miki alkawarin zan bari a hankali, it is not easy in bari a lokaci guda. I’m always bored with work in na dawo gida sabida banda iyali da za su debe min kewa.
A ofis aiki, a gida aiki, so ina dan zuka kadan, in sami sanyi a zuciyata”.
“Wane irin sanyi ne a smoke (hayaki)?”
Halima ta tambaya tana kokarin danne bacin ranta.
“Ka yi karatun Alqur’ani mana maganin kore kowacce damuwa ne, ko ka yi auren, ai kana da halin yin sa i'm sure”.
Ta sa kai za ta wuce, bai san sanda ya riko hannunta ba. Cikin mantawa da cewa Ogiyarsa ce,
“It’s a promise zan bari Halimah, please bear with me. Na yi maki alkawari daga ranar da na yi aure I will quit smoking”.
Halima ba ta da abin cewa, sabida yadda ya bi ya narke mata tamkar mijin da ke gaban matarsa. A hankali ta zame hannunta daga nashi, shi kuma ya kasa dauke ido a kanta. Jakarta ta bude ta fiddo magungunan malaria da paracetamol da ta sayo masa a hanya, ta dora a kan hannun kujera. Kanta a kasa ta ce,
“Make sure ka sha magani yanzu”.
Ta sa kai ta fice daga falon zuciyar ta na racing a cikin kirjin ta akan dalilin da ba ta sani ba. Watakila hakan na da nasaba da hannunta da Hashim ya rike, wani abu da babu namijin da ya taba kwatantawa a gare ta. Ta jima cikin mota kanta kwance a kan sitiyari kafin ta tada motar a kasalance ta bar estate din zuciyarta na ci gaba da tsere a sararin kirjinta.
****
BABI NA HUDU
Engnr. Halima Zubair zaune a kujerarta mai juyawa dama zuwa hagu. Washegarin zuwanta gidan Hashim. Takarda ce a hannunta wadda ta fito daga ofishin Chairman. Hashim na daga gefenta a tsaye yana jira ta gama nazarin takardar ta ba shi amsa don ya san yadda zai tsara musu komai. Takarda ce ta gayyatar taron ma’aikatan sadarwa na duniya wanda za a yi a kasar Holland birnin Malta. Inda ofishin Chairman ya turata ta wakilci Nigerian Communications Commission a matsayin ta na mataimakiyar shugaba. Mutum uku daga ofishinta za su tafi karkashin rakiyarta; P.A dinta, Hashim Yakasai, Adama Joseph, (akawun ofishi) sai daya daga cikin lauyoyinsu Attorney Alkasim Bello. Da tana da halin zamewa wannan tafiya da ta yi, sabida a rayuwarta Halima ba ta son hawa jirgin sama ko kadan.
A daddafe ta gama karatu, kuma tun dawowarta daga Mexico ba ta kara hawa jirgi ta fita kasar waje ba.
To amma Daddy yana da uzuri zai je Porthearcourt wata seminar din shi da Hanan, sannan wannan taron yana da matukar muhimanci ga ma'aikatar su domin dukkan ma’aikatan hukumomin sadarwa na duniya sun tura deligates din su. Kamar yadda ita da tawagarta su ne deligates din Nigerian Communications Commission.
Ba tare da nuna damuwa a kan fuskarta ba, Halimah ta ce, ya rubuta takardar approval zuwa ofishin Chairman. Wato ta amince za ta yi tafiyar ke nan.
Tun jiya da ta dawo gidan Hashim ta ke jin kanta wani irin sukuku! Komai na duniya ya daina yi mata dadi, zuciyarta ke mata wassafe-wassafe da kissime-kissime iri-iri duk a kan Engnr. Hashim. Jikin ta da zuciyarta yana kokarin gaya mata; ita HALEEMAH ta rasa wani bangare mafi muhimmanci a rayuwar diya mace. Ga dai kudi; ga mukami; ga mulki; ga tarin ilmi; ga motoci kirar jiya-jiya, amma babu life-supporter and partner. Hashim da yake namiji ya kasa jure nashi loneliness din har sai da ya hada da quenching dinsa da smoking.
To ita kwaya za ta sha ko cocaine za ta shaka ya gusar mata da nata kadaicin? Za ta iya rantsuwa jiya har mafarki ta yi da Hashim cikin wata irin rayuwa da ba ta ko son tunawa sabida nauyinta.
Don haka ne yau tunda ta zo ofis ta kasa hada ido da Hashim Yakasai, order kawai ta ke ba shi, kanta na kasa. Suna cikin magana Hanan ta bude kofar ofishin ta shigo babu ko daukar excuse.
“Sis Leemah, ashe Holland za ki tafi shi ne ni za'a kada ni wata Porthearcourt?”
Idanunta suka kai kan Hashim, dake tsaye a gefen daman Halimah, sai ta ga kamar ta san shi, somewhere else, nan da nan kwakwalwarta ta tariyo mata inda ta sanshi...…
“This irresponsible man…...!”
Ta fada da karfi,99 tana nuna shi da dan alin ta.
“How dare you enter here?”
Halima ta dago kai ta balla mata harara.
“He’s my P.A”.
“Kina nufin wai shi ne P.A din da ki ka dauka?”
Halima ta gyada mata kai.
Hanan ta hau masifa tana fadin da ta san shi ne da ba ta bada offer ba, ya yi mata rashin kunya randa ya zo.
Halima ta harare ta, ta ce, “Yanzun ma ai sai ki kore shi in kin isa, please me ki ke so? Kin zo kina sa min ciwon kai”.
Hanan ta yi kwafa ta juya ta fice tana fadace-fadacenta wanda ba ta rabo da shi. Allah da ya halicce ta ya halicce ta ne da mita da rashin mantuwa. Sannan gata da wuyar afuwa. Halima ta juya side din da yake ba tare da ta dube shi ba, ta ce,
“I’m sorry, kanwa ta tana da hayaniya, sannan ga rigima”.
Dan murmushi ya yi.
“Kada ki damu, na dade da gane hakan, ni na yi mata laifi ai, na tsaya ina ta kallon ta the very first time i saw her (as a baby Human Resource Manager), ina ta mamaki ne sabida kankantar ta, to the extent that I’m lost a cikin kallon ta, shi ne abin da ya ba ta haushi”.
Nan ya labarta mata yadda suka yi da Hanan a ranar da ya zo.
Halimah ta yi ta dariyar da ba ta shirya ba. Son girma irin na Hanan na bata mamaki.
“Ashe Hanan ce ta sa aka yi kwallo da kai a kan kwalta?”
Dan murmushi ya yi, domin ya shagala da kallon dariyar ta, wani abu mai kyau da bai taba gani daga gare ta ba; kamar furen fulawa ta koma don kyau. Shi kadai ya san a halin da ya kwana jiya a kan Halimah, zazzabi ya warke, sai zazzabin tunanin Halima da wani irin daddadan feeling akan ta da ya maye gurbin sa.
Kamar Halima ta san hakan, tun daga ranar ta ke dojewa haduwar su. Ta fi yin magana da shi ta waya ba ta kiransa face to face domin a duk sanda ta ganshi kwana ta ke mafarkinsa cikin wata irin rayuwa da ba za ta iya kwatantawa ba. Don gujewa sharrin shaidan, sai ta takaita haduwar su.
Cikin sati daya shirye-shiryen tafiyar su Holland ya kammala, visar su ta zo hannun su.
Prof. ya tara su su ukun ana i-gobe za su tafi, ya jaddada musu su kula masa da Halimah, kada su barta ta yi komai da zai wahalar da ita. Adama Joseph ta tabbatar ta ci abinci sau uku a rana, kuma a kan lokaci.
Alkasim Bello ya dinga rubuta mata rahoton komai, shi kuma P.A ya san aikinsa dama, hatta jakar hannun ta yana so ta kasance karkashin kulawarsa.
Halima ba za ta gaji da jin kunya ba a duk lokacin da Daddy ya yi wa ma’aikatan NCC wannan keke-da-keke a kanta ko a kan Hanan. Su kam har sun saba, ba ya zame musu sabon abu.
Tun a airport za ka fahimci irin girman da ma’aikatan ke baiwa Halimah. Trolley dinta na hannun Hashim tare da tasa, yayin da handbag dinta ke hannun Adama Joseph. Hatta wayar hannunta sai an bugo Adama ke daukowa ta mika mata.
A cikin jirgin Ethiopian air ita da Hashim suna a first class seats yayin da Alkasim da Adama ke can economy class.
Prof. ya sanya P.A a first class kusa da ita ne saboda kada ta nemi wani taimako babu ko dayansu a kusa da ita. Dadin dadawa komai nata har ipad dinta yana hannun Hashim din.
Kujerarta na kusa da tasa, tana daga jikin taga. Lokacin da jirgi ya karci kasa zai daga cikin ta ya yi hautsinawar da yake yi in ta shiga jirgi. Ba shiri ta kama hannun Hashim da dukkan karfin ta ta kankame sosai tana salati, ba tare da ta san abin da ta yi ba.
Har sai da jirgi ya daidaita a sararin samaniyar subhana, sannan ta iya dawowa hayyacinta, ta kuma lura da abin da ta yi. Kunya ta kam ta. Shi kam Hashim kallonta kawai yake yi, ya kasa dauke ido a kanta. Cikin jin kunyar abin da ta aikata ta sakar masa hannu tare da gyara zama cikin kujerarta, a hankali ta ce da shi,
“Sorry, bana son karar tashin jirgi, ina shiga ne kadai idan ya zame min dole”.
Hashim wanda ke kokarin sanya ear-piece a kunnensa ya ce, “I can relate’. Da haka ya kunna karatun Alkur’ani ya sa a kunnensa. Tun daga ranar da Halima ta yi masa fada a kan sauraron Alkur’ani maimakon smoking ya ke kokarin kamantawa, ya mayar da shi abin jinsa. Ba surar da yake jin dadin sauraro irin Suratul Yusufa.
Halima ta ga sai lumshe ido yake yi, ta kasa yin shiru ta ce.
“Are you listenig a music?”
Bai ji ta ba, sai da ta bubbuga hannun kujerarsa.
“Na ce is it a music you are listening?”
A hankali ya bude kwayar idanunsa wadda dogayen gassun idonsa suka lullube. Halima ji ta yi wani abu ya tsirga a zuciyar ta da ilahirin gangar jikin ta. Yaa Allah! He is so handsome fiye da duk sanin da ta yi masa a baya, ko kuma watakila don ba ta taba zama so close da shi irin haka ba ne? Lokaci guda duk wani tunani nata ya soma fita daga saiti, gangar jikinta ta shiga karbar wasu irin sakonni da ba ta taba ji a rayuwarta ba.
Hashim ya sa hannu ya cire ear-piece daya daga kunnensa na dama ya sanya a kunnenta daya. Bai sani ba gabadaya ba ta cikin nutsuwa, the call of nature (sha’awa) irin wanda Ubangiji ya halitta a tare da kowace baligar diya mace mai shekaru da koshin lafiya kamar nata; na babu abin da ya yi saurawa mace a rayuwa sai wannan, shi ne ya ziyarce ta a wannan lokacin. Rufe idanunta ta yi a lokacin da ya makala mata ear-piece din a kunnenta na dama, suka ci gaba da sauraron karatun tare. Nutsuwa na saukar musu. Karatun da ya nutsar da zuciyar Halima, ya kawo saiti cikin rudanin gangar jikinta, daga sabon unexpressable feelings din da ya ziyarce ta akan Hashim.
Tsoron Allah ya cika mata zuciya, ta amince shaidan ya ziyarce ta a 'yan dakikan da suka gabata, dole ta kara taka-tsan-tsan a cikin mu’amalarta da Hashim. Ta gama lura zuciyarta na matukar sonsa, so mai tsanani, wanda ke sabbaba mata sha’awarsa, wanda ta san hakan haramun ne a cikin musulunci.
Daga ita har Hashim lumshe idanu kawai suka yi, suna sauraron suratu Yusufa, abincin da aka ajiye musu ba su ko kalle shi ba. Kamshin turarensa na shiga hancin ta a hankali. Zukata kadai ke aiki, aikin da baki ba zai iya furtawa ba.
Duba da matsayin da kowanne yake da shi ga dan uwansa (hierarchy of social class). A zuciyar sa Hashim ya san ko feelings zai kashe shi, ko so zai yi karshen numfashin sa, Halimah Numan, haka zai ganta ya bar ta. Ta fi karfinsa ta kowane bangare, bai san me ya sa zuciyarsa ta yi masa wannan lahanin ba a kan Halimah, zuciyar sa ba ta yi masa adalci ba ko kankani in dai Halimah ta zaba.
Yayin da Halimah ke kissima wace irin sa’a za ta yi idan Hashim ya zamo mahadin rayuwarta? Wace hanya za ta bi Hashim ya so ta irin son da zuciyarta ke masa? Ba ta daga ido ta hango wani hierarchy ba irin wanda shi yake hangowa. Ko gargadin Daddy a gare su. Abin da zuciyarta ke gaya mata kawai, “This is her Mr. Right, her soul-mate", wanda Ubangiji ya assasa kaunarsa a ruhinta, don sanin cewa shi ne daidai da rayuwarta.
Har aka soma shelar daura belt jirgi zai sauka a garin Malta Hashim da Halima suna cikin halin da suke ciki, idanuwa a lumshe, da warin ear-piece a kunnen kowannen su. Har sai da wata ma’aikaciyar jirgi ta zo kansu ta yi musu magana. Ita kam Halima ba ta ma ji ta ba, sai jin hannayen Hashim ta yi zagaye da ita yana fastening mata belt din. Wannan ya ba ta damar shakar masculine turarensa da kyau (Eternity Moment). Ta kara lumshe ido ta kankame jikinta wuri guda lokacin da jirgin ya karci kasa, ya soma zura gudu a kan kwalta da irin karar da ba ta so. Ba ta san lokacin da ta kara kankame hannuwan Hashim ba, har sai da ya gama gudunsa ya tsaya waje daya sannan ta sake shi tana sauke ajiyar zuciya.
Ko da suka fito daga jirgi jakar hannunta ta karba daga hannun Adama, suna tafe zuwa inda motoci suke tana kokarin roaming layin ta don kiran Daddy don gaya masa sun sauka lafiya, yayin da Hashim ke fidda musu jakunkunan su. Suka samu motar da za ta dauke su zuwa masauki tana jiransu, nan aka kwashe su zuwa Star Hotel Malta.
Dakin da aka bai wa Halima duk ya fi nasu girma da kayatuwa. Tana shiga ta fada wanka, kafin ta fito abinci na jiranta. A saukake ta yi kwalliya cikin doguwar riga dark blue mai adon duwarwatsu masu haske, ta zauna don ta ci abinci, amma kawai sai ta samu kanta da kasa kai ko loma daya a bakinta, ba tare da ta san halin da Hashim ke ciki ba.
Mikewa ta yi don fita zuwa dakinsa ba tare da tunanin komai ba. Dacewa ko rashin dacewar hakan, kawai ita so ta ke ta ganshi in ba haka ba, ba za ta samu nutsuwar yin komai ba.
Tana kokarin fita yana kokarin shigowa, sai suka yi karo garam! Da goshinsu. Hashim ya dan ja da baya yana sosa goshi yana fadin,
“Sorry Ma!”.
Shi ma a can ya kasa cin abincinsa, idanunsa kawai so suke su ganta. Wata irin rashin nutsuwa ce ta same shi da bai san dalilinta ba. Yayi ta safa da marwa adakin sa. Sai da ya yi tsam da ransa ya gane Halimah yake son gani.
Tare suka juya cikin dakin, Halimah ta kasa gaya masa ta taso ne don ta je ta dubo shi. In da hali ta kira shi su ci abinci tare. Sai ta bige da yi masa tayin cin abinci. A kasan ledar cin abinci suka zauna suka fara cin abincin, lokaci-lokaci suna satar kallon juna.
Bayan sun gama Halimah ta yi waya aka zo aka fidda kayan. Smoking yake so ya yi, ya san bai isa ba a gaban Halimah. Dole ya hakura, ya zuba mata ido. Daga shi har Halimah kusan tunani iri daya suke yi. Ina ma su ma’aurata ne…! Suka zo Malta yawon amarci? Yanayin garin Malta ya fi daidai da yanayin da masoya sabon aure za su kasance a karkashin inuwar aure. Domin kawar da wannan tunanin da gujewa hudubar shaidan sai Hashim ya tambayi Halima yana son sanin labarin rayuwar ta.
Murmushi ta yi, kanta a kasa. “Sai idan ka yi min alkawarin kai ma za ka ba ni naka’.
Hashim ya amince, sai suka koma bisa kujerun da ke fuskantar juna suka zauna. Hashim ya tattara nutsuwar sa da hankalin sa akan Halimah. Halima ta dau remote ta rage sautin talabijin da ke burari, ta dubi Hashim a raunane, ta ce,
“We are raised up without a mother, ta rasu tun Hanan na watanni tara. Babanmu shi ya raine mu da kan sa. Mahaifin mu ya fito daga Numan ta jihar Adamawa, Mamanmu daga Maiduguri cikin kabilar kanuri. Duk wata kulawa da uwa ke wa ‘ya’ya mu mahaifinmu ne ya yi mana, shi ya sa muka taso da wata irin shakuwa tsakaninmu da shi.
Tun bayan rasuwar mahaifiyarmu bai kara aure ba, bansan dalilin sa ba, amma an ce saboda ba ya so matarsa ta cutar da mu. Daddy is an examplary DAD da na san kafin a samu uba kamarshi sai an tona. Domin kuwa shi ya raini Hanan da madarar jarirai, aikin Nanny gare mu bai taka kara ba balle ya karya.
Na yi dukkan karatuna na firamare da sakandire a garin Abuja, daga nan Daddy ya kai ni kasar Mexico na karanci software engineering a digiri na farko da na biyu daga Autonomous University Mexico.
Na san za ka yi mamakin ganina a kan kujerar COE a kananun shekaruna, wannan ra’ayin Daddy ne. da farko na yi tunanin ba zan iya ba domin kujera ce da ta dace da namiji, kuma mai yawan shekaru da tarin experiences, amma da tsohon COE ya nuna min komai, da yadda ake tafiyar da dukkan ayyukan NCC alhamdulillah I find it possible".
Ta karashe zancenta da murmushi, sannan ta kara da cewa, '‘Sai kuma Allah ya hada ni da wani irin genius personal assistant, wanda ya kara maida impossible din possible. Tell me everything about you kaima”.
Hashim ya cure yatsunsa cikin junan su, ya dora habarsa a kai yana kallonta with strong affection kai tsaye cikin tsakiyar idon ta. A hankali ya ce,
“Working as an Executive Vice Chairman of NCC is not easy, the lady on the throne is indeed extraodinary, gifted, talented and magnificient. Sunana Engr. Hashim Isma’eel Yakasai. Mahaifina Ba-Kano ne, mahaifiyata Ba-Sudaniya ce. Ni ne Da na biyu a wajen iyayena, ina da yaya mace Rabi’a da kanwa Sa’adatu, mahaifinmu ya rasu tun muna kanana, we’re raised by our able mother also. Yadda Daddy dinku yake sonku, yake kula da komai naku haka ita ma ta ke son mu. Take kula damu da hidimomin mu. Na yi karatun firamare da sakandire a makarantun gwamnati, daga nan na wuce A.B.U Zaria na karanci Telecommunications Engineering. Na kwashe shekaru uku ina neman aiki online (ta yanar gizo).
A cikin irin neman aikin da nake yi ta yanar gizo din ne na ci karo da neman ma’aikatan da NCC ke yi masu irin fannin dana karanta, na yi applying. Ba jimawa suka kira ni aptitude test, an dade da yin hakan domin har na fidda rai sai kwatsam ku ka kira ni Ma’am!"
Ya karasa fada yana murmushi.
Ita ma murmushin ta yi, ta mike ta isa ga firji ta dauko musu lemon shany gwangwani biyu, ta kawo masa guda ta rike guda. Suka ci gaba da wata irin sassanyar hira ta fahitar juna, kowanne na kokarin boye feeling din sa a kan dan uwansa, sanin cewa hakan ba mai yiwuwa ba ne ta kowanne bangare.
Har sai da lokacin sallah ya yi Hashim ya mike. Lokacin da zai fita idanunsu suka yi wani irin maiko kamar hawaye ne kwance a cikinsu. Ba sa son rabuwa, amma ya zama dole. Da baya da baya Hashim ya iya ficewa daga dakin fuskarsa dauke da wani irin murmushi da bai san yana yi ba.
Filon kujera ta dauka ta rungume bayan fitar sa, tana tunanin abin da ke shirin faruwa da ita, wanda ko ta wanne bangare ba ta hango masa nasara daga mahaifin ta ba. Ba ta hango yiwuwar sa nan kusa ba… ba ta hango dorewar sa ba.
‘AURE’ shi ta ke so ta yi, duk abinda take bukata a rayuwa ta same shi, kuma ba da kowa ba sai da P.A dinta Engnr. Hashim Yakasai. Wannan karon za ta fito fili ta yi jayayya da Daddy in dai ba zai barta ta raya sunnar Manzo (S.A.W) ba. Ba shi da hujjar hana su yin aure har ga Allah. Gara ta yi aure tun kafin shaidan ya ribace ta ta yi abin da ba shi ke nan ba.
To amma in ta san zuciyar ta, ta san feelings din ta a kanshi ne, shi Hashim ta san nasa din? Idan ba shi da feeling irin wanda ta ke da shi a kansa fa? Idan bai da ra’ayin auren mace irin ta fa? To amma ita me ye makusanta?
Ta sani Ubangiji ya kyautata halittarta, sannan ba alfahari ba halayenta masu kyau ne. Babban abin da ta hango zai zame mata matsala da samun Hashim bayan ra’ayin Daddy mara tushe a addini da al'ada, shi ne hierarchy of social status da yake a tsakaninsu.
Amma ita ba ta hango hakan zai zamo mata shinge daga samun abin da rai da zuciyarta ke so ba. Za ta iya barin komai da ta mallaka da kujerar aikinta in har za ta samu alfarmar auren Hashim. Bai shigo rayuwarta da sauki ba, da wani irin karfi ya shigo ya kutsa cikin zuciyarta… a lokacin da ba ta taba zata ba.
Ringing din wayarta ne ya farfado da ita daga zuzzurfan tunanin da ta fada. Ba tare da ta duba sunan mai kiran ba ta daga a kasalance da hannun damanta.
Kafin ta ce komai husky muryar Hashim ta ji a kunnuwan ta.
“I just called to say goodnight (na kira ne kawai don in ce, mu kwana lafiya)”.
Halimah ta zuki numfashi ta fesar, ya yi fami a kan gyambon da ke neman fashewa. Ba ta gama fita daga wannan shaukin ba Hashim ya kashe ta da mafi girmansa.
“I’m sorry to say..... I love you Halimahhhh”.
Halimah dimaucewa ta yi a duniyar da ta fi ta gajimare shawagi da dan Adam. Kafin ta ce komai, Hashim ya kashe wayarsa ya bar ta cikin tarin mamaki.
Barcin Halimah na yau, wani irin birkitacce ne. Ragagge.
Washegari suka durfafi abin da ya kawo su, kamar ba abinda ya faru tsakanin su jiya, ba su samu kansu ba sai yamma liss. Don haka suna sauka daga mota su duka hudun kowa ya bi elavator zuwa dakinsa.
Ba su iya tsinana komai ba bayan dawowar su daga wajen taron sai barcin gajiya. Da suka farka ma basu hadu ba, sai wasu irin zafafan text da suka yi ta aika wa junansu cikin daren. Shikenan, daga wannan ranar, daga wannan lokacin, daga wadannan awannin, rayuwar Halima Numan, bata kara komawa yadda take ba. Kakkarfar soyayya mai ban mamaki da tarihi a birnin Malta ta samu muhalli, ta kafa kanta. Soyayyar da ta jirkita rayuwar Halima upside-down. Ta kuma sa ni believing cewa har gobe, komai lalacewar zamani akwai sauran mata masu soyayya ta gaskiya, ta saboda Allah. Ban sani ba ko rayuwar Halima zata kara komawa yadda take a baya???
*****
BABI NA BIYAR
Zaman kwanaki uku domin halartar seminar din Communication Engineers na duniya, sai ya zamo kwanakin kulla wata irin kakkarfar soyayya mai ma’ana tsakanin Hashim da uwar dakinsa Halimah. A kan karan-kansa ya zauna ya yi tunani ya san ba shi da arzikin da zai auri Halimah, amma soyayyarta da Allah ya dora masa ta cika idanunsa, ta yadda har ta ture kambun arzikin Halimah daga idanun sa. Yake kallon ta daidai da sauran mata sabida ita bata dauki kanta a bakin komai ba. Ita kadai yake kallo ba arzikinta ba! Ba ya kuma hangen komai nata sai ita kanta.
Abubuwa da yawa kan sa a so mutum, muhimmi shi ne halayensa. Halayenta na kwarai da ya dade yana fahimta, juriyarta da jarumtakarta su ne manyan abubuwan da suka ja hankalinsa gare ta. Kullum tunaninsa ya ya zai yi ya mallake ta? Ta wace hanya? Da wane kwabon? Amma ya san with ALLAH everything is possible!
A bangaren Halimah, tana sane da gargadi, ko ta ce ra’ayin Prof. a gare su ba wai ta manta ba ne, sai dai soyayyar da ta shiga zuciyarta ba lokaci daya ta shige ta ba. Ta shige ta ne a hankali like a biological virus a lokacin da ta gama fahimtar ko wane ne Hashim?
Mutum ne da kafin ka samu kamarsa cikin maza dubu sai an tona. Jajirtacce ne a kan dukkan abin da ya sa gaba, yana da wata irin gaskiya da amana, with extraordinary talent da ba ta taba gani a tare da kowa ba. Kamalarsa da kamewarsa da rikon addinin sa suka jagoranci zuciyarta zuwa gare shi.
Ta dade tana nazarin sa, tana nakaltar halayen sa, dabi’unsa da yadda yake gudanar da ayyukansa. Idan ya shirya mata al’amuran ofis dinta ko wanda ya shekara goma a NCC sai ya sara masa.
Ta yarda success dinta na tafiya tare da taimakonsa ne. Ra’ayi da akidarsu daya. Idan aka zo maganar suffa ta halitta, Hashim shi ne crush dinta, irin mazan da kowace mace da ta san kanta ta ke yi wa kanta burin samu.
Ta nakalci cewa, yana da tsantseni sosai a kan addini, komai zai yi sai ya hada da kalmar insha Allah sannan kalmar subhanallah ita ce wow! Dinsa. Ga kula da lokacin sallah komai runtsi duk muhimmancin aikin da yake yi, koda kuwa aikin Prof. ne ya sanya shi, da zarar lokacin sallah ya yi zai ajiye shi ya je ya yi sallah.
Zamanta da shi yana kara tunasar da ita lokutan sallah, wanda a can baya ba ta fiya kiyayewa ba. Ga kula da mahaifiya, kusan kullum sai ta ji shi yana waya da Innarsa, duk safiya da ya shiga ofis ita yake fara kira kafin ya gabatar da komai. Abubuwan da ke burge ta a Hashim yawa gare su. Za ta iya kiransa role-model dinta.
A wannan lokacin da soyayyar ta yi kamari a zukatansu, sun amince wa juna cikin dan lokaci za su iya aure. Ba zasu bar abin ya dau lokaci ba. Ba sa hango duk wani bambanci da ke tsakanin su. A ganin Halimah, Hashim na da komai tunda yana da zuzzurfan ilmi, da aikin da zai iya ciyar da ita. Ta gama shirya tunkarar Daddy kan cewa ita fa aure ta ke so… auren kuma za ta yi don raya sunnar Ma'aiki, da wanda zuciya da ruhin ta ke so, suka kuma aminta da shi wato P. A dinta Engnr. Hashim. Ta shirya aure… a dan tsukin nan, ba ta jin akwai abin da zai dakatar da ita daga kan wannan kyakkyawan kudurin, sai dai idan ba ta numfashi.
Sai da suka kara kwana biyu a kasar Holland, don su kara samun lokacin fahimtar juna, sun san in sun koma gida Abuja aiki ne jingim yake jiran su bazasu samu lokacin juna ba. A washegari suka shirya tsaf suka bar abokan tafiyar su a hotel suka shiga cikin birnin Malta a taxi don bude ido.
Garin Malta zagaye yake da (deep blue waters of the Mediterranean Sea). Can suka fara zuwa wato Maltese Islands (Malta Gozo, and Comino). Suka zauna akan rairayin gaban ruwa suna cigaba da tsara rayuwar su daki-daki, cikin matsanancin nishadi, daga yawon amarci da zasu je kasar Cape-Town (South Africa), don Halima tace kasashen Africa ne suke burgeta, har gidan da zasu zauna da irin tsarin da kowannen su yake so, da yadda zasu raini 'ya'yan su in Allah ya basu. Sai suka gane cewa a mafi yawan al'amuran rayuwa ra'ayin su daya, sha'awar su daya, tunanin su daya, haka simplicity din su ya zo daya. Dukkan su ba masu sha'awar rayuwa mai tsada bane.
Har yamma suna gabar ruwan Malta, daga nan suka je Valetta (Capital of Malta). A can suka zauna a restaurant suka yi odar abinci (african cuisine), a baki Hashim ke baiwa Halima tana jin kunya tana dariya, da suka gama sai da ya jira ta ta sha PEPSI sabida shi baya shan softdrinks. Suka yi hotuna a Valetta, Maltese Islands da wayoyin hannun su.
Sun gama shirya komai ita da Hashim kafin su baro kasar Holland, cewa da sun koma zata gabatar da zancensu ga Daddy, shi ma kuma ya ce zai gaya wa Innar sa. Iya abin da ya tara daga fara aikinsa a NCC zuwa yanzu ya san ya ishe shi sayen flat house komai kankantar sa a garin Abuja. Sabida NCC suna biyan ma'aikatan su fairly.
Daga shi har Halimah ba masu high taste ba ne. Sun fi son moderate life irin ta ‘yan bokon da suka san ciwon kansu, don haka Halimah ta ce da shi, kada ya taba takura wa kansa a kanta, ita Hashim ta ke so, shi kuma za ta aura. Bayan wannan ba ta bukatar komai.
Yayin da ta fadi hakan, Hashim kallonta ya yi affectionately, ya ce,
“Ni kuma zan yi iya yi na in zamo miki miji abin alfahari… mijin da bazaki taba dana-sanin aure ba. Halimah zan yi amfani da karfina da lafiyata in suturta ki, in ciyar da ke da halaaal, in kare alfarmar ki da martabar ki. In daga darajarki a idanun sauran mata ‘yan uwan ki.
Zan zamo miki bango abin jingina, kafadar da za ki kwantar da kai ki yi kuka, ko dariya. Allah shi ne shaida, ina tsananin sonki Halimahhh”.
Duk wata soyayya sun gama kullo ta daga Malta sun yo gammon ta sun taho Abuja da ita. Dauke da alkawurra masu karfi a tsakanin su. Ko da suka dawo, Halima ta dauki hutun sati guda, don ta samu ta warware gajiyar tafiya, inda ta damka komai a hannun Hashim her Technical Asistant sannan P.A dinta, da sakatariyarta, Rose.
Hashim ya je gida Kano washegarin dawowarsu ya kwana daya, ya gaya wa Inna da Yaya Rabi’a cewa ya samu mata a can Abuja. Daga Inna har Rabi’a ba su ji dadi ba, don ba irin auren da suke so ya yi ba kenan, so su ke ya zo ya nemi yarinya a Kano daidai karfinsa. A hakan ma don ma ba su ji wace ce ya kinkimo ba.
Ita Dr. Rabi’a ma har ta yi masa kamun wata dalibarta a Legal da ta yaba da hankalinta. Ba za ta fice sa’ar Sa’adatu ba. Amma sun kwana da sanin halin Hashim in ya sa kai a abu sai ya ga abin da ya ture wa buzu nadi, kuma dai yana da foresight (tsinkaye) ba zai dauko matar da za ta cutar da shi ba, ko wadda ba za ta girmama su ba. Don haka suka ba shi kyawawan addu’o’i daga bakunansu.
Inna ta ce, in sun tsaida lokacin zuwa gaisuwa ya yi magana ta yi wa Yayanta da ke Sudan waya, da ‘yan uwan mahaifinsa.
A washegari Hashim ya dawo Abuja, ya rungumi ofishin Halimah. Don ta samu ta huta sosai. Prof. yana yabawa da yadda yake gudanar da komai, ya gayawa Halimah nan da dan lokaci,.. her P.A deserves promotion. (Mataimakin ta ya cancanci karin girma). Wannan abu da Daddy ya fada ba karamin faranta ran Halimah ya yi ba, har ta ke hango alamun nasara cikin rigimar da ta ke shirin gabatarwa.
A daren yau misalin karfe tara na dare ta zuge labulayen dakin ta don ta samu ta shaki fresh air. Wani abu ne guda daya ya dauki hankalin ta, a cikin wata bakuwar mota ta hangi Hanan tare da wani kyakkyawan saurayi, abinda idanunta suka gane mata ba karamin kidimata ya yi ba.
Hanan ta bude kofa kafarta daya na waje, yayin da jikinta ke cikin motar suna sumbatar juna ita da saurayin. Sun jima a haka kafin Hanan din ta fito tana daga masa hannu, yana daga mata ya ja motar ya bar gidan.
Da sauri ta saki labulen gabanta na wani irin bugu na tashin hankali. Hanan ta murda kofar dakin ta shigo tana cilla jakarta tana cafewa, da gani cikin nishadi ta ke. Amma kallon fuskar Halimah kawai ta yi ta shiga taitayinta. Halimah ta hadiyi miyau da kyar, ta ce.
“Hanan, waye ya sauke ki a mota yanzun nan?”
Hanan ta yi shiru, Halimah ba ta jira amsarta ba, ta kwashe ta da mari, tace,
“Me na ga kuna yi cikin mota haka?”
Da farko Hanan ta nuna firgici, don ba ta taba zaton Halimah ta gansu ba. Sai kuma ta fuske ta dubi cikin idon Halima tana hawaye ta ce.
“Saurayi na ne… an ce ba za mu yi aure ba… bautar ofis kawai za mu yi muna tarawa Daddy kudi… bayan ni kuma mutum ce ba mutum-mutumi ba. In ba mu yi romancing a mota don rage wa kanmu zafi ba so ake mu je mu kama daki a hotel ko me? Mts!”
Ta yi tsaki tare da ficewa daga dakin, ta banko wa Halimah kofarta.
Da kyar Halimah ta lalubi gefen gado ta zauna. Ga wadda ta fi ta iya protest, sai dai nata akwai tarin kuruciya a ciki da karancin ilmin addini. Amma sai ta ga cewa tunda har Hanan ta bude baki ta fadi haka, ya tabbata aure ta ke so itama, ba ta da yadda za ta yi. Sai ta ga cewa kamar wata sassaukar hanya ce Allah ya kawo mata wajen gabatar da bukatarta ga Daddy, idan har Hanan za ta ba ta hadin kai su duka su taru su ce aure suke so.
Fita ta yi zuwa dakin Hanan, don sauri har tana tuntube. Ta same ta tana canza kayan jikinta, ga yatsun Halima sun kwanta lambam a farar fuskarta, ta tausasa murya ta ce,
“Ki yi hakuri Hanan!”
Jin da sulhu ta zo ba da wa’azi ba, ya sa Hanan ta dakata da abin da ta ke yi, ta dan ba ta hankalinta. Halimah ta yi mata murmushi ta ce, “Wajen ki na zo, magana za mu yi ta fahimta”.
Hanan ta koma bakin gado ta zauna, Halimah ta zauna a kusa da ita, ta dubi Hanan ta ce, “Na samu miji, aure zan yi Hanan”.
Hanan ta bude baki tana kallonta, da kyar ta iya cewa, “With Daddy’s consent (da amincewar Daddy)?”
Halima ta ce, “Har yanzu ban samu guts din gaya masa ba, amma tabbas aure zan yi”.
Hanan ta motsa baki a hankali kamar mai ciwon hakori ta ce,
“Ni sau nawa ina samun mijin yana korar su? Amma wallahi wannan karon ba zan iya rabuwa da Saleem ba”.
Halimah ta sanya hannunta cikin na Hanan ta ratsa yatsun su (fingers cross) Sannan ta ce,
“Then we have to unite and protest!”
Hanan ta dan fiddo ido cikin tsoro ta ce, “Ina tsoron Daddy, kin san dai tunda muka taso maganarsa daya ce ba zai aurar da mu ba, saboda baza'a iya rike masa mu ba, amma zai yi mana komai a rayuwa…”.
“Kina tsoron Daddy, amma ba kya tsoron Mahaliccinki? Wannan abin da ki ke aikatawa is an act of fornication (nau’in zina ne) wanda ba komai ya janyo miki ba sai rashin aure. Hanan, mu karfafi kanmu mu fuskanci Daddy, ni na gaya miki a karshe zai hakura ko da da farko ya nuna rashin amincewar sa, kada ki manta shi ya haife mu, ba shi da abin da ya wuce mu.
Duk hukuncin da zai mana a kan hakan ba zai yanke mu daga jikinsa ba. Iyaka ya yi fushi na dan lokaci ya huce. Idan ba za ki ba ni goyon baya ba mu kwaci ‘yancin mu da addini ya ba mu ba, ni zan yi aure na in tafi in barki a gidan nan ke kadai. Ya rage naki”.
Tana gama fadin haka ta mike za ta bar dakin. Har ta kai bakin kofa hanan ta kira sunanta. Dakatawa ta yi ba tare da ta juyo ba.
Hanan ta tako a hankali ta zagayo gabanta, idanunta fal hawaye ta ce,
“Ba zan iya zama a gidan nan babu ke ba. I’m with you sis Leemah”.
Sai hawaye ya gangaro daga idonta.
Halimah ta kai hannu tana share mata.
“In dai Saleem da gaske yake ki gaya masa ya fito. A goben nan za mu tunkari Daddy a yi ta ta kare. Amma sai kin cire tsoron Daddy a ranki Hanan za mu yi nasara”.
Hanan ta gyada kai, ta ce, “Insha Allah”.
*****
BABI NA SHIDDA
Prof. Zubair Muhammad Numan, yana zaune a balcony din shan iskarsa kan wasu kujeru sakar kaba, yana sauraron radiyon da ke gefenshi, inda ake labaran VOA na harshen hausa, misalin karfe goma na safe, kasancewar ranar asabar ce babu aiki. Halima da Hanan suka shigo a tare, kowacce sanye da bakar jallabiya kamar wasu takarun Makkah, kai a kasa salalaf-salalaf suka shigo inda yake, kowacce ta je gefen kafarsa daya ta zauna.
Ya rage sautin radiyon ya ba su hankalin sa.
“What happened my daughters?” Saboda bai saba su zo su zauna a kasa don yana kan kujera ba, sai dai su zauna a hagu da daman sa.
Halimah ta ambaci sunan Allah Al-Hakeem gwanin hikima, don ya bata hikimar zance, Zarah ta taba koya mata wasu ayoyi daga Suratul-Daha in kana so a fahimce ka, tace a hankali;
"Rabbi sharahli sadry, wayassirly amri, wahlul uqdatan min lisany, yafqahu qauly...... sannan ta kwarara zuciyarta, ta soma magana cikin sanyin murya.
“I’m sorry Dad, I’m very sorry Daddy, idan abinda zan fada bai maka dadi ba. Na zo yau in gaya maka cewa, na tsayar da miji. Suna so a ba su lokaci su zo tambaya”.
Tana rufe baki, Hanan ta dora nata.
“Daddy, ni ma na samu miji, dan gidan Minister Usman ne, sun ce suna so su zo tambaya in an ba su appointment”.
Kowacce ta sunkuyar da kai kasa, gabanta na dukan tara-tara ba uku-uku ba. Don ba karamin practice da rehearsal suka sha a daki ba kafin su shirya wadannan gajerun kalaman.
Prof. ya yi musu kallon tsaf, sannan yayi dan murmushi, ya ce,
“Wato kun je mazan banza sun hure muku kunne ku yi min rashin biyayya ko? Sau nawa zan gaya muku ba zan iya aurar da ku ba? Yanzu har kun yi girman da za ku dubi tsabar idona ku ce min aure ku ke so Halima da Hanan? Me ku ke so? Me za ku samo a gidan auren wanda babu shi a gidanku? Ku tashi ku ba ni waje tun ban sa kafar wando daya da ku ba”.
Halima ta hadiyi miyau da kyar tace "Dad! Na gaya maka aure nake so, shekaruna 24, sai na tsufa na rasa mashinshini saboda biyayyar ka? Kace karatu, mun yi kowanne irin karatu, kace aiki, gashi muna ta yi maka, mun tara maka kudi wadanda zasu isheka har karshen rayuwar ka, a yanzu hakkin mu na 'yan adam muke bukata, 'yancin da Allah ya baiwa kowa na raya sunnar Manzo, ko don mu bamu da UWA? Bamu da wani majibinci da zamu kaiwa bukatar mu bayan kai?" Ta fashe da kuka.
Hanan ma ta zaburo "Daddy na yi hakurin Allah na yi na manzo, ka yi min aure ina son Salim bazan iya hakura da shi ba".
Don bakin ciki ya rasa me zai ce musu, anya 'ya'yan sa da ya sani ne wadannan? Hanan da Halimah masu kunya da kawaici? Wace irin fitsara suka koyo haka? Aure wane iri? Ba dai a gidan sa ba! Shi da girman sa bai damu kan sa da wani aure ba sai su? Da me ya rage su?
Sai kawai ya tashi ya bar su a wurin, don ya tabbata in ya cigaba da kallon su a gaban sa zai iya illata su. Auren banza auren wofi me zasu je su samo a gidan auren wanda baya basu? Su yara ne basu san wani me auren ya kunsa ba (a tunanin sa fa).
Tun daga ranar Hanan da Halima suka hada baki suka daina cin abinci, suka daina zuwa ofis, ko falo sun daina fitowa, kullum suna kwance a gadon dakunansu kamar ruwa. Shi ma Daddyn ya yi fushi mai tsanani ba ya neman su. Damuwarsa daya ce, ofis da suka daina zuwa. Ba ya son ya bai wa bare ko ‘ya’yan talakawa wadannan guraben aikin a NCC, ya fi so daga shi sai ‘ya’yan cikinsa su ci gaba da cin gajiyar NCC su kadai, ga ‘ya’yan sun yi masa murabus za su bula masa kasa a ido.
Kwarai yake cikin damuwa, musamman da kukunsu Helen ta same shi har falonsa ta gaya masa yau kwana uku tana kai abincin Halimah da Hanan dining amma yadda ta kai haka ta ke daukowa, ba sa tabawa. Ba ta san me suke ci ba, tana tsoron kada ulcer ta kama su. A kwance suke wuni, a kwance suke kwana, in ta musu magana ba sa amsa mata.
Hankalin Prof. ya fara tashi, zai iya jure komai, amma ban da zamansu cikin yunwa. Shi kuma har gobe bai shirya rabuwa da ‘ya'yan nan nasa ba. Ya damka su ga wani banzan namiji da bai san darajar su ba. Me zai gaya musu su gane bayan wanda ya yi shekara da shekau yana gaya musu, amma rana daya suka sa kafa suka yi fatali da shi?
Haka ya danne bacin ransa yau da ya dawo ya shiga dakin nasu. Halin da ya riske su a ciki ya yi matukar daga masa hankali.
Kwanaki uku kacal bai gansu ba, amma har kasusuwan wuya sun yi. Sannan kwanaki uku kenan da fatar jikinsu ba ta ga ruwa ba balle sabulu. Idanunsu sun yi zuru-zuru sun zurma ciki da yunwar da suka sanya kansu. Ruwan lipton kawai suke sha, wanda suke jonawa a kettle a dakunansu. Shi kuma lipton ma’abota shanshi sun sani ba ya maganin yunwa, sai ma ya rarake ciki.
Ya ce, “Is that serious to this extent? Ku same ni a falo mu yanke magana ta karshe”.
Suna tangadi da dafa bango kamar wadanda suka sha kayan maye suka bi bayan Daddy falon sa kamar yadda ya bukata.
Sai da suka zauna a gefen kafafunsa sannan ya fara da tambayar Hanan wane ne mijin da ta samo, kuma a ina suka hadu? Kada ta boye masa komai, ta gaya masa gaskiya.
Hanan ba ta boye ba, ta gaya masa haduwarta da Saleem a wajen dinner din kawarta, da inda yake aiki, wato shell company da kuma ko wane ne mahaifinsa. Ta kare zancenta da cewa, kuma shi da gaske aurenta zai yi, idan har Daddyn ya ba shi dama.
Ko babu komai Prof. Zubair ya dan ji sanyi a kan zabin nata, jin cewa ba karamin gida ta samo mijin ba. Domin Minister Usman sananne ne a Nigeria. Halimah ma ya yi mata tambaya irin yadda ya yi wa Hanan.
Halimah ta sunkuyar da kanta, kirjinta na bugawa. She is not sure… ko Daddy zai yi farin ciki da zabinta. Ga alama ya karbi na Hanan. A hankali cikin sanyin muryarta ta ce,
“Daddy, Hashim ne!”.
Kwata-kwata hankalinsa bai kawo masa wanda ta ke nufi ba. Ya ce, “Wane ne ubansa?”
Wannan tambaya ta yi wa Halimah rashin dadi. A raunane ta ce, “Mahaifinsa ya rasu”.
Ya yi dan jim, sannan ya ce, "Waye mahaifin nasa nake tambayarki?”
Halimah ta karfafi zuciyarta ta fito fili ta gaya wa mahaifinta ko wane Hashim ta ke nufi, ba wani ba ne sai Personal Assistant din ta Engnr. Hashim Yakasai.
Wani ashar Prof. ya saki, ya kara da cewa, “Ban san ba ki da hankali ba sai yau, domin a da kallon wadda ta fi kowa hankali da tsinkaye nake miki".
Halimah ta soma kuka tana rokon mahaifinta, ta kama kafarsa ya fizge ya tashi ya barta a wurin tana gursheken kuka.
Hanan ce ta kamata zuwa daki, kafin azahar sai ga Halima tana suma idanunta na kakkafewa. Hanan ta firgita, a guje ta fita falo tana kuka tana rokon Daddy ya zo ya ga Halimah. Da farko ya ki ko kallon inda ta ke, sai ga kukunsu a guje tana gaya musu Halimah rai ya yi halinsa… she is no more… tana cilla hannuwa tana kiran Jesus ya taimake ta.
Zuciyar UBA… Jin cewa Halimah ta mutu bai sa shi yin nadamar hukuncin da ya yi mata ba, don da ya hada jini da talaka mai ci a karkashinsa gara komai zai faru da ita ya faru. Zuciyar sa ta yi laushi ne da ya tuno ko wace ce Halimah a gare shi. Ta rayu cikin biyayyarsa da kaunarsa a kulliyar rayuwarta. Ta fi Hanan yi masa biyayya… hatta aikin nan ba so ta ke yi ba, tana yi ne don amfaninsa. Albashinta bata taba komi a banki take barin sa....tace shi take taramawa. A hankali ya mike ya bi bayan Hanan wadda ta rufa a guje (helter-skelter) zuwa dakin Halimah.
Tsintsiyar hannunta ya kama ya saurara, sai ya fahimci da sauran numfashinta, watakila dai doguwar suma ta yi, da kansa ya dauke ta zuwa mota, ya yi asibitin da suke zuwa da ita.
Suna zuwalikitoci suka karbi Halimah, aka rufu a kan ta. Kwana uku ana abu daya, Halima ko ta farfado sai ta kara sumewa, Hashim bai san abindaake yi ba don a zaton sa har lokacin Halima na hutu ne.
Ba karamar jinya Halima tayi ba, kafin ta soma shaida wadanda ke kanta, gabadaya ta fita hayyacin ta, kwana bakwai cur tana kwance gadon asibiti sai ruwa da ake kara mata akai-akai da allurai. Daddy ba karamin tsorata yayi ba, ya yarda da gaske take soyayyar, Hanan ce mai jinya, duk sanda Halima ta farka sunan Hashim take ambato tana rokon Hanan ta kira mata shi su yi sallama mutuwa zata yi. Bazata iya cigaba da rayuwa ba shi ba. Hanan sai kuka. Don ita bata son zancen Hashim dinnan itama, ta kuma yarda da gaske Halima take zata iya rasa arayuwar ta a kan sa.
Don haka ta dau wayar Halima ta kira Hashim da sunan da Halima tayi saving din lambarsa "Cheriè". Hashim na dagawa yace "Sweatheart, kina so ki kashe ni ne? Ba kira ba messege? Ni in na kira bata shiga, saura kadan ki ganni a kofar dakin ki, hutun nan ya isa ki dawo haka! I can't afford missing you....i love you....". Hanan tayi maza ta cire wayar daga kunnen ta, he's so caring dole ya tafi da rayuwar diya mace. Sai ta ji bazata iya karya zuciyar sa ba, don ko ya zo Daddy ba bari zai yi ya shigo ba, ya kafa ya tsare da kujera a gaban gadon Halima kullum. Shima bai zuwa ofis, komai akan sakatare da Hashim yake.
Jinyar Halima ta ki ci ta ki cinyewa. Daddy bai da niyyar janye ra'ayin sa itama bata da niyyar janye nata. A binciken likitoci kuma sun ga cewa jinin Halimah ya yi mugun hawa, zuciyarta kuma ta tabu. Suka yi wa Daddy nasiha a kan ya yi hakuri ya yi mata abin da ta ke so don tserar da lafiyarta. Yaran yanzu ne ka haife su, amma sai dai ka bi su ba dai su bi ka ba. Daddy don bakin ciki kasa kallon Halimah ya yi lokacin da ta sake farfadowa, wannan karon ta dan jima bata kara suma ba, don haka aka kai ta aminity room.
Daddy ya tura kofa ya shiga dakin da Halima ke kwance. Tsayawa ya yi a kanta yana kallon irin zabgewar data yi, gabadaya ta lalace ta fice hayyacinta. Babban takaicin sa wai akan Da namiji. Da namijin ma wanda bai isa ya mallake ta ba, mai ci a karkashin ta, yayi kwafa ya dube ta cikin ido ya ce.
“To Halimah, zan miki abin da ki ke so, wato auren dan talakawa, dan aikinki, boyi-boyin ki. Amma bisa sharudda uku kwarara in kin amince”.
Halimah ta daga kumburarrun idanunta tana sauraron Daddynta.
A yadda yanayin fuskar Daddy ya nuna ba ta hango tausayinta ba, ba ta hango jin kai da rahmar nan da kullum ke cikin idanunsa in zai dube su ba. Sai dai duk da haka zuciyarta na karfafarta da cewa, ta amince da ko me zai ce in dai zai yarda ta auri Hashim. A yanzun yana cikin fushi ne, da ya huce zai koma Daddy dinta da ta sani a baya.
Kuma ba ta jin za ta kasa daukar komai in dai za ta tsira da Hashim.
Prof. Zubair ya ce, “Na amince ki auri zabin ki, a bisa sharudda guda uku; na farko daga ke har shi kun bar aiki da NCC, ku je can ku nemi aikin da za ku yi ko ma a ina ne ba ruwa na.
Na biyu ba yaji, ba saki babu kawo kara.
Na uku kin daina amfana da dukiyata da komai ya fito daga aljihuna. Zan yi miki kayan aure kamar yadda kowanne uba ke yi wa ‘yar da ya haifa. Bayan wannan kin gama rabar arziki na Halimah, ki je can ki yi mummunar rayuwar da ki ka zaba wa kanki”.
Halimah na kuka ta ke neman sassauci daga wadannan tsauraran sharudda na Prof. amma bai saurare ta ba, cewa ya yi tana bata masa lokaci, ta ba shi amsa kawai, yes or no, don yana da abin yi a gabansa.
Halimah cikin shesshekar kuka, ta ce, “Daddy aure fa na zabi in yi, sunnar ma’aiki, ba yawon dandi za ni ba, don Allah Daddy ka sassauta min…...”.
Juyawa ya yi ya ba ta baya jin kukanta na neman karya masa zuciya, ya san dalilin sa na kafa wadannan sharuddan, dole ta hakura da yaron don ba shi da arzikin da zai iya rike ta, ita kuma ba za ta iya rayuwar wahala ba, shi ya sa ya yanke wadannan sharuddan. Amma ga dimbin mamakinsa sai ya ji Halimah ta ce cikin shesshekar kuka,
“Na amince Daddy, innallaha yarzuqu man ya sha’u bigairi hisab”.
Prof. ya juyo ya yi mata kallon sannu tantabara sarkin soyayyah, sannan ya yi murmushi mischievous smile (murmushin keta), ya ce,
“Na ba shi dama ya aiko magabatansa”.
Zai fita daga dakin Halimah ta toshe kukan bakinta, ta ce, “Daddy, ba ka sanya mana albarka ba!.
Ya sa kai zai fita, jin abin da ta fada sai ya dakata, ya juyo sosai.
“Albarkata ku ke nema ku ka kasa yi min biyayya? Ku je mazanku su sa muku albarka”.
Ya fice daga dakin kamar ya kifa don sauri da bacin rai.
Halimah ta sa kanta a tsakankanin cinyoyinta ta fashe da kuka. Ya’ilahi! Wane irin hukunci ta yanke wa rayuwarta haka? Shin tsakanin ita da Daddy wane ne mai gaskiya a addini da al’ada? Shin Hashim zai yi mata halacci irin wanda ta yi masa? How sure is she danginsa za su zamo mata makwafin Daddy? Arziki wannan na Allah ne, don haka ba ta nadamar wannan sharadin na daddy, ta fi damuwa da wanda ya ce, babu yaji, babu kawo kara. Ta sani a karkashin kowace soyayya akwai yau da gobe, akwai sabawa irin ta harshe da hakori, to ranar da Hashim ya bata mata ko ya bakanta mata wajen wa za ta kai kukanta? Ita da bata da Uwa bata da dangi? Anya ba ta yi kuskure ba?
Da wadannan tunane-tunanen Halima ta kwana ta wuni. Kafin a sallame ta daga gadon asibiti.
Ta kira lambar Hashim, yana dagawa bata tsaya sauraron komai ba ta ce, “Daddy accepted the proposal, kana iya turowa daga yanzu zuwa kowanne lokaci”.
Ba ta saurari cewarsa ba ta kashe wayarta. Domin ji ta yi duk ta daina dokin abun, soyayyar ta ragu, ba ta ma marmarin ganin Hashim din, something like hatred (wani abu kamar tsana) take ji a ranta, tunda shi ne ya shiga tsakaninta da Daddynta mai sonta.
Tana kallon kiransa na ta shigowa ta ki dagawa, ya koma turo text su ma ta ki karantawa. Sai da ta dauki wayar domin ta kashe ne ta ga text dinsa na karshe.
Sweatheart
This is the beginning of our blessings insha Allah… na san yakin da ki ka yi kafin ki samo min wannan damar mai girma ne. Ni kuma na yi miki alkawarin I will never ever let you down… I will not disappoint you!!!
Much love, Hashim.
A hankali ta runtse idonta rike da wayar a hannunta, zuciyarta ta dan samu sassauci. Ba ta da haufi daman a kansa, sannan ta sani he is a man of his word. Ga iya kalamai masu wanke zuciya. Tana son komai nasa, tana sonsa tana mugun kaunarsa. Amma yau yadda ranta ke jagule din nan Engnr. Hashim Yakasai, bai da kalaman da za su yi tasirin wanke zuciyarta.
*****
BABI NA SHIDDA
Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba. An zo an yi tambayar su duka biyun a rana daya. Daddy ya ce ba ya so a bata masa lokaci, in sun shirya sati mai zuwa su kawo sadaki, sannan shi ba zai yi wa ‘ya’yansa biki ba domin ba farin ciki yake da auren ba, aure kawai za a daura da safe, da daddare kowanne ango ya zo ya dauki matarsa. In za su yi bikin can a gidansu su suka sani, amma shi ba a gabansa ba, zai yiwa kamfanin shirya gidaje magana ya je ya yi musu jere, ba ya bukatar wasu taron mata.
Ba abin da ke dugunzuma zuciyar Prof. irin rabuwa da zai yi da ‘ya’yan nan nasa dare daya, it’s not easy for him, yana dai daurewa ne.
Sati na zagayowa aka kawo sadaki, sadakin Hanan ya fi na halima nesa ba kusa ba. Wannan ya kara dugunzuma ran Prof. amma bai ce komai ba.
Ranar asabar ‘yan kalilan mutanen da Prof. ya gayyato wadanda duk ‘yan uwansa ne kawai daga Numan babu abokansa kusoshin gwamnati ko guda daya, ta fannin angwayen ma ba a ba su isasshen lokacin da za su yi gayyata yadda ya kamata ba, don haka su ma ba su yi gayyata sosai ba.
Karfe goma sha daya na safe aka daura auren ENGNR. HASHIM ISMA’EEL YAKASAI da ENGNR. HALIMAH ZUBAIR MUHAMMAD NUMAN, HANAN da angonta SALEEM USMAN. Dan reception din nan da ake yi bayan daurin aure Prof. ya ce ba za a yi ba, kowa ya kama gabansa, da daddare su zo su dauki amaren su.
Sai lokacin da ya shiga dakinsa ya kulle ya samu kansa da zama yana hawaye. Hawayen sa ba na komai ba ne na bakin cikin ‘ya’yansa sun zabi aure a kan zama da shi, duk kokarinsa na inganta rayuwarsu. Duk kokarinsa na ganin cewa ba su nemi komai sun rasa ba. Duk kokarinsa na ganin cewa sun yi zarra a ilmi da career mafi tsada. Duk rainon da ya yi musu ba tare da taimakon kowa ba, ya kasa yi musu uzuri, yana ganin sun zabi soyayyah ne a kansa, da yake shi ma ba wai ya yi zurfi ba ne a karatun addini yana ganin tunda ya rayu shekaru ashirin da uku ba tare da mace ba, su me zai hana su iyawa?
Yau ne Hanan da Halimah suka yi kukan rashin mahaifiya, zahiri wanda ya rasa UWA a ganinsu shi ne maraya ba wanda ya rasa uba ba.
Ko ‘yar nasihar nan da ake yi wa amare su ba su samu ba. Ko dan lallen amarci ba su samu ba balle uwa-uba gyaran da ake yi wa mata a yayin aurensu. Sun yi kuka sosai suna rungume da juna, angwayen sun iso kusan a lokaci daya, inda Daddy ya sa aka yi musu jagora zuwa falonsa, ya kuma je da kansa ya taho da Hanan da Halimah.
Sai da suka zauna daga gefen mazan nasu, sannan daddy ya fiddo fararen ambulan guda uku, ya mika wa Hashim, Haleemah da Hanan, sannan ya dora bayani.
“Takardar sallama (dissmissal) daga ma’aikatar NCC. Ba lallai ne sun yi muku bayanin yadda muka yi da su ba, amma na amince da aurenku ne based on sharudda guda uku, kuma suka amince.
Babu career dinku na NCC.
Babu yaji, babu kawo kara.
Babu kwabona da zai kara ciwon kai wajen hidimarsu.
Sai ku je ku nemi arzikin ku da gumin ku, domin wannan gumi na ne. ranar da ku ka gaji da daukan nauyin rayuwar su sai ku dawo min da su, ni bazan taba gajiya dasu ba”.
Ya mike ya bi wani corridor a falon zuwa dakinsa yana share hawayen idonsa.
Halimah ta fashe da kuka, amma Hanan idanunta mirsisi. Ita ba ta ga abin damuwa ba a nan. Account dinta shake yake da kudi, har doller account gare su. Tana da kwalin digirin jami’ar National Autonomous University of Mexico, wanda duk inda ta nemi aiki da shi a Abuja da gudu za a ba ta. Ga mijinta mai babban aiki, dan minister. Sister Halimah ita ce cikin matsala tunda Hashim bai ajiye ba, bai kuma ba wani ajiya ba. Ita ko ba sa aiki daga ita har mijinta ba za su tagayyara ba, maganin Halimah kenan tantabara uwar soyayya.
To amma me? Da Hanan ta shiga daki don dauko ATM Cards dinsu da files din credentials dinsu suka ce dauke mu inda ki ka ajiye mu. Tana tsaye baki a bude, alert ya shigo wayarta, inda ta ga an zuke duk wasu kudi da ke cikin asusunta. Infact ta san ba aikin kowa ba ne, face Daddy.
Ashe dai da gasken yake ba za su kara rabar arzikinsa ba?
Hankali tashe ta koma falo tana gaya wa Halimah, a lokacin ne hawaye ya balle daga idanun Hanan.
Hashim ya sanya tafin hannunsa cikin na Halimah ya mikar da ita, tare da sakalo ta a jikinsa, a haka suka fita a falon yana jin wata sabuwar soyayyarta na kara mamaye shi. Abin da Prof. ya yi wa ‘ya’yansa akan sa maimakon ya bata ran Hashim, sai ya dasa wata katuwar bishiya mai korran yabanya ta soyayyar Halimah koriya sharr a zuciyarsa..... Ta sadaukar da komai saboda shi… soyayyar mahaifinta, kujerarta ta aiki… dukiyarta… qualifications dinta…...
Sai ya ji filin zuciyarsa ya yi wa soyayyar Halimah kadan, ya aro wani katoton filin ya kara shimfida mata. Zai tsaya mata a rayuwa irin tsayawar da babu wani namiji da ya taba yi wa matarsa… zai ba ta soyayya da kauna irin wanda ko a fim da litattafan hikaya na soyayya babu kamarsu… zai himmatu wajen neman arziki ta kowacce hanyar halali don ganin Halimah ba ta sha wahalar da babanta ke burin ta sha ba, zai zame mata namiji dan goyo har sai ta rasa katoton zanin da za ta goya shi… zai zame mata uwa, uba, miji, aboki, dan uwa wanda a kowane lokaci kirjinsa zai zame mata wajen yin kuka don ta ji sanyi, ko dariya don ta yi nishadi. Yana rokon Allah ya cika masa wadannan burika nashi don jin dadin masoyiyar da bai taba gani ko jin labarin irinta ba.
*****
Wani taimako da Allah ya yi wa Hashim shi ne, ya sayi mota Henessy bayan dawowarsu daga Holland da kudin sallamar da aka yi musu a ofis, kamar ya san hakan zai faru. A cikinta ya tuko su zuwa apartment din da ya kama musu a Maitama, sabida yadda auren ya zo afujajan bai kai ga sayen gida ba kamar yadda ya yi niyya, don haka yanzu suna tafe a kan titi yake tunanin ya fasa sayen gida a Abuja tunda zamanshi a garin ya kare, babu aiki. Gara ya koma mahaifarsa da matarsa ya saya a can, tunda na can Kano ma zai fi arha har zai samu rarar kudi ya yi musu wasu muhimman bukatun kafin su ga abin da Allah zai yi.
Tun jiya ya kwashe komai nasa daga estate ya maida gidan da ya kama a Maitama a bisa tunanin da ya yi na bai kamata ya aure ta a gidan ubanta ba. Sai ga shi kuma tunaninsa ya yi masa rana.
Tukin motar kawai yake yi zuciyarsa a cunkushe. Ya rasa da kalmar da zai rarrashi Halimah, wadda ke ta kuka tun fitowarsu. Ta rasa me Daddy yake nufi da ita. Wannan wace irin mugunta ce bayan ya kore su aiki ya kwace asusun bankunansu, hatta takardun karatun su ma ba za su tsira da su ba? Idan wani ne ya ce mata Daddy zai yi wa wani haka ba za ta taba yarda ba balle su ‘ya’yan cikinsa, abin sonsa.
Shin me ye laifinsu don sun yi aure raya sunar ma’aiki? So yake su dauwama a gida tare da shi har su tsufa su rasa mai aurensu? Hujjarsa daya ce, Hashim bai fito daga irin gidan da yake so ba, kuma a karkashinsu yake, to ita Hanan in haka ne me ya hana ya kaunaci nata auren?
Da ta hada komai waje daya, sai ta ga cewa, auren ne kawai ba ya so su yi ba tare da wata hujja kwakkwara ba. Sai bokon sa da yayi masa katutu.
Tana wadannan tunane-tunanen suka isa gidan Hashim, flat house ne karami mai karamin get, da space na adana mota guda daya. Gaba daya girman gidan bai fi girman bangaren maigadin gidan Prof. ba, amma Halimah ji ta yi wata irin nutsuwa ta shige ta, wani irin contentment ya lullube zuciyarta, irin wanda ni’imar aure ke haifarwa ga mace, a lokacin da ta mallaki gidanta ita kadai.
Da kansa ya je ya rufe get din ya dawo ya rungumi Halimah zuwa ciki. Sai da ya kai ta har gefen kyakkyawan gadonta, ya yi kokarin bude mayafin kanta, amma ta ki saki. Duk da cewa zuwa yanzu ta hakura ta daina kukan.
Ya koma ya shigo da akwatunan kayanta, ya rufe ko’ina ya shiga nashi dakin don ya watsa ruwa, bayan ya gaya wa Halimah in tana bukatar toilet ga shi nan a cikin dakinta.
Bayan ya rufe komai ya dawo gaban Halimah ya zo ya durkusa ya dora hannayensa biyu a kan gwiwoyinta. Cikin muryar nan tasa mai kidimata, ta gigitata.... a yau ya qawatata ya sirantata ya kyautata ta fiye da kullum. Ya yi kasa da ita in a very low tone. Ya ce,
“Among all the beautiful names of the world, that husbands calls their wives, I chose to call you; Ma’am, because you earn my respect, I respect you Halimah and will forever remember this respect… I promise you a respect till my last breadth… now, I want to see your beautiful face. Yanzu ina son ganin kyakkyawar fuskar ki.....) Ko da kuwa a jike ta ke da hawaye…
Hawayen da na san ni ne silar fitarsu kuma da yardar Allah zan zama silar komawarsu murmushi…"
Ya fada yana bude mayafin fuskarta, wannan karon ba ta hana shi ba, sabida yadda kalamansa suka sanyaya mata zuciya.
(A cikin duka sunaye masu dadi na duniya, da maza ke kiran matansu da su na zabi in kira ki Ma’am”. Sabida kin samu girmamawata, ina girmamaki Halimah. Kuma har abada zan dinga tuna wannan girman… na yi miki alkawarin girmamawa har zuwa karshen numfashina)”.
Ta bar shi ya bude fuskar, amma duk kokarinta ta kasa yin murmushi. Ta dago hannayen Hashim daga durkuson da ya yi a gabanta, wata soyayyarsa na kara mamayarta. Ko da irin wadannan kalaman na bakinsa sun ishe ta rayuwar farin ciki.
“Ka daina durkusa min, you are my husband, and there is no NCC now, not even the throne, we are now equal, sai ma kai da Allah ya bai wa fifikon daraja mai girma a kaina, darajar mijin aure (ka daina durkusa min kai mijina ne, kuma babu NCC yanzu ka sani, balle kujerar ofishin. Don haka daidai muke ni da kai (ba oga ba subordinate).
Karo na farko da ya rungume Halimah cikin jikinsa, da ata irin azama, ya sumbaci goshinta, karan hancinta sannan bakinta. Bai zurfafa sumbar ba sabida yadda jikin Halimah ya soma kyarma. Bai san kyarmar ta mece ce ba, he just kissed her lightly idan hakan ne ya ba ta tsoro, shi da ma bai shirya hakan tsakanin su yanzu ba. Daga haduwar su har zuwa aurensu abu ne da ya faru cikin dan kankanin lokaci kamar kiftawar ido cikin kudura da iradar Ubangiji, shi da Halima suna bukatar karin fahimtar juna, shakuwa da sakin jiki da juna kafin mu’amalar aure ta gifta a tsakaninsu.
Duk da ya dauke bakinsa daga fuskarta jikinta bai bar kyarmar da yake yi ba. Ya rike ta sosai cikin jikinsa, ya ce, “Why are you shivering?”
Daga Halimah babu amsa, sai runtse idanunta da ta yi. Ita kadai ta san me ta ke ji a zuciya da gangar jikinta. Amma ba za ta iya fada masa cewa ya ci gaba da kissing dinta ba. Kada ya yi mata daukan abin da ba haka yake ba. Ta dade da fahimtar nature dinta, ta dade tana kula da kanta don ganin ba ta yi zina ba, ko wani abu mai kama da ita. Tun daga lokacin da ta fahimci ita din na da halittar nymphomaniac, ba don ba ta da damar yin zinar a Mexico ba ko an tsoratar da ita a kan illarta a addini ko ala’ada, sai don ta dade da burin son yin aure, duk kuwa da ta san shi ne abu na karshe da mahaifinsu ba ya so su yi.
Now that Hashim is passionately kissing her as her choosen husband, gaba daya sha’awar duniya ce ta sauko ta rufto mata. Suddenly he stopped, asking her why she's shivering, wanda hakan ya sanya ta cikin mawuyacin hali. That’s why she is shivering. Amma ta san dole ta rike kanta don tsira da mutunci da martabarta a idon mijinta kada ya dauka ko dama ta saba ne.
Hashim ya umarce ta da su yi alwallah su yi sallar nafila don nuna godiya ga Ubangiji, wanda ya maida impossiple-possible ba tare da tsimi ko dabararsu ba. Ita dai binsa ta ke da yadda ya ce, amma idanunta kusan a runtse suke. A haka aka yi sallar, ya yi addu’o’in da manzon rahma ya umarta. Sannan ya daga ta zuwa gadonta, ita dai ji ta ke kamar ta rike shi lokacin da ya rufa mata bargo mai santsi (quilt) ya sake russunawa ya sumbaci kuncinta da idanunta. Ya mika hannu ya yi mata light-off, da muryar nan tasa mai shiga har cikin jinin jikinta ya ce,
“Sleep well Ma’am, goodnight’.
Ya sake sumbato bakinta a hankali. Sannan ya bar dakin zuwa nasa tare da rufo mata kofa. So yake ta samu hutu da nutsuwar fuskantar sabuwar rayuwarta. Tabbatar da auratayyarsu a yau is not a good decision (ba hukunci ne mai kyau ba). Amma ga Halimah abin ba haka yake ba, ko kadan bai yi mata gwaninta ba.
*****
BABI NA BAKWAI
Da asubahi Halimah ta ji husky muryar Hashim na rera karatun Alkur’ani cikin suratul Baqara. Wani abu da ba ta taba ji ana yi a gidansu ba. Sosai karatun ya yi mata dadi, ta nutsu daga kwance tana sauraro. Kai ka ce Balaraben Madina ke rera karatun sabida yadda yake baiwa kowanne harafi hakkinsa da izhari, idghami da iklabi. A can Mexico Zarah na koya mata karatu, amma ko kusa karatun nata bai yi iri daya da na Hashim ba wanda ke yi da cikakken tajweedi.
Har lumshe ido ta yi tana sauraronsa. Ta mance da lokacin sallah, sai da ya dasa aya, ta kuma ji shi yana murda kofar dakinta. Ita da fushinsa ta kwana, ya lasa mata zuma kuma ya janye kayar sa, don haka ta yi maza ta shige cikin quilt ta kudundune ita a dole barci ta ke.
Hashim ya ga lokacin da ta yi wuf! Ta shige bargon. Murmushi ya yi ya karaso gaban gadon, wasu tausasan kayan barci ne a jikinsa da ya sayo a Malta samfurin (Ralph Lauren). Yana zuwa ya janye bargon gabadaya tana rikewa yana ja har ya yi nasarar dauke shi tsaf! Gabadayanta ya dauke ta tana wutsil-wutsil da kyawawan kafafunta ita ya sauke ta ba ta so, bai dire ta a ko’ina ba sai a toilet.
Ya ce, “Now, make your ablution (yi alwalarki) lokacin sallah na fita”.
Ta wani zumburo baki tare da juya masa baya, “Ka fita na ji”.
Kin fita ya yi, ya ce, “Are you pouting at me? (ni ki ke zumburo wa baki)”.
Tana so ta yi fitsari kuma ya ki fita. Ya dauko sabon brush ya matsa mata maclean din Sensodyne a jiki.
“Brush your teethes”.
“Na ji, ka fita dai”.
“Mene ne in na ga fitsarinki?”
Halimah ta sa hannu tana tura shi waje yana dariya har ya fice, ta rufe kofar tare da murza mata key.
Cikin nutsuwa ta yi brush din, ta kama ruwa da alwala. Ta fito don ta tada sallah, sai ta samu Hashim kwance tsakiyar gadonta. Dauke kai ta yi kamar ba ta ganshi ba, amma wani irin sanyi ta ji a zuciyarta. The pleasant feeling din da mace ke ji in ta ga mijinta kwance a gadonta. Ta nufi wajen da suka yi sallah jiya, ta yafa mayafi ta tada sallah.
Hashim na observing sallahr Halimah sosai, a take ya gano gyararraki masu yawa a cikinta, kuma tana idarwa ya gaya mata (in a very polite way) ta yadda ba ta ji ta tozarta ba. Kuma nan da nan ta dauke gyaran cikin kanta.
Lokacin har alfijir ya keto, ya tashi ya fita ya barta tana shirin wanka. Kafin ta fito ta ji gida ya dume da kamshin suyar kwai da dankali. Ta fito daure da towel santala-santalan kafafunta na digar ruwa, ta bude jakar kayanta na gida ta zari marasa nauyi ta saka. Ta koma gaban madubi ta shafa mai, hoda, lip-gloss, ta yi dauri sassauka da dankwalin material din wanda kalarsa ja ne da ratsin baki. Kin san irin wannan colour a jikin farar mace, nan da nan ta dauki walkiya ga natural fatar jikinta mai wani irin glowing na ‘ya’yan hutu.
Hashim da ya shigo ya kusa sakin tray din hannunsa wanda ya jero musu abin karin kumallo sabida kyan da Halima ta yi. Ya ajiye tray din a gefe ya karasa ga Halimah, hannayensa biyu ya sa ya zagaye ta cikinsu daga waist dinta. Kallon da ya ke mata duk sai ya sa ta jin kunya, ta boye kanta a kafadunsa. Ya rankwafa kasancewar ya kere ta a tsawo ya hada bakinsu wuri guda ya soma wani irin kissing dinta with extreme passion, very deep kisses wanda ya zauta Halimah ya fitar da ita a hayyacinta nan da nan, ba ta san lokacin da ta riko Hashim a cikin jikinta ba, kyakkyawan riko mai tsanani kamar za ta balla shi.
Sun dauki lokaci a haka. Hashim na shawagi da ita a duniyar sumba har sai da Halimah ta kasa daurewa ta kankame shi sosai. Is a great new experience wanda bata san da me zata kwatanta shi ba.
Ya zame da kyar daga tsatstsauran rikon da ta yi masa, ya ja hannunta zuwa inda ya ajiye musu karin kumallo. Kunya kamar ta kashe Halimah in ta tuno abin da ta yi. Wanda ta tabbata Hashim ya gane basarwa yayi. So Hashim is not that Ustaz she is looking him as! Murmushi ta yi mai fidda sauti a lokacin da Hashim ya dauko dankali a fork ya nufo bakinta.
“Oya take your breakfast first, sai ki ji dadin sumbatar miji yadda ki ke so".
Zaro ido Halimah ta yi har sai da ta ba shi dariya. Ture hannunsa ta yi, ta ce, ba za ta ci ba.
Ya ce, “Saboda sumba ki ke so ba shi ba ko?”
Ta narke fuska kamar za ta yi kuka, ta ce, “Haaasheeem…!”
Murmushi ya yi, ya ce, “More kisses are coming, only if you take your breakfast…”.
Tashi ta yi a fusace za ta shige toilet ya yi maza ya riko hannunta.
“Sorry Ma’am, na ga you like it ne”.
Ta soma kokawar kwace hannunta, ba ta san lokacin da ya mike ba sai ganinta ta yi dauke a hannunsa, yana juyi da ita a tsakiyar dakin. Kafin ya dire ta tsakiyar gadonta ya rungume ta tsam ya soma yi mata abin da ya fahimci ta fi so. Na yanzu yana wane na dazu. Sai kawai Halimah ta fara hawaye, bi ya yi da harshensa yana side hawayen bai bar ko daya ya diga a kasa ba. Hawayen da ta ke yi ba na komai ba ne na farin ciki ne da Allah ya mallaka mata Hashim. Ta san ta gama yin sa’a in dai a fannin soyayya ne sai ko a sauran fannonin da dan Adam ba ya rasa ajizanci. Ita kuma in dai da irin wannan soyayyar ko Hashim yankar naman jikinta zai dinga yi ta alkawarta wa kanta ci gaba da zama da shi har zuwa karshen numfashinta.
*****
Wannan abinci dai, sai da ya sandare sannan aka ci shi. Da rana ma shi ya dafa musu jallof din sphaghetti da kifin gwangwani suka ci. Ba zai manta ba, ya iya girkin ceton kai ne a zamansa na dalibtaka a ABU Zaria. Wunin ranar zungur bai je ko’ina ba sai masallaci, yana like da Halimah tana zuba masa shawagaba son ranta kan jiya ya barta ta kwana ita kadai. Sallah in zai yi sai ya ce su yi jam’i tare, kasancewar babu masallaci a kusa da su.
Da daddare ya ce ta shirya su fita eatry su samu abin da za su ci. Ko da suka dawo gida, Halimah ta tsaya tana kare wa gidanta kallo, tana kiyasta ‘yan kayan dakin da Daddy ya yi mata, duk da kayan masu quality ne odar waje, amma a matsayin Daddy da arzikin da Allah ya yi masa ‘yar aikinsa zai yi wa wannan kayan a matsayin sadaka ba ‘yar cikinsa ba. Ba ta damu ba ko kadan don da ma ita ba ta son tarkace, she lives a moderate and simple life, ko a gidansu dakin Hanan ya fi nata kyale-kyale.
A lokacin ne Hanan ta fado mata a rai ta karbi wayar Hashim ta saka lambarta a ciki ta kira ta.
“Wato kin samu miji kin manta da ni ko?”
Hanan ta yi wata irin dariya ta ce, “Sis, ashe haka auren yake? Gaskiya Daddy ya kware mu da yawa, da na san haka auren yake ai da tun gama sakandire na yi PROTEST na yi aure”.
Halimah ta ce, “Sannu maras kunya, ni kawarki ce da ki ke min wannan maganar?”
Hanan ta ce, “Fisabilillahi wa zan yi wa in ba ke ba? We have missed a lot. Yanzu haka ni da Saleem muna kan hanyarmu ta komawa PortHearcourt, can inda yake aiki. Hope we will keep in touch”.
Halima ta yi musu fatan sauka lafiya, ta bai wa Hashim wayarsa.
Ya yi dan murmushi jin abin da Hanan ke cewa, a zuciyarsa kuma ya ji yana tausaya musu. Ba su da kowa da za su kira nasu sai junansu, sai mahaifin da ya juya musu baya.
Halimah ta yi shirin kwanciya kenan cikin wata sassaukar rigar barci, Hashim ya shigo hannunsa da glass cup mai cike da tatacciyar madarar shanu mai sanyi (fresh milk), ya mika wa Halimah, ta karba tana masa godiya don dazu ne ta gaya masa sai ta sha fresh milk ta ke iya barci, don haka a hanyarsu ta dawowa ya tsaya ya saya mata katon din madarar oldenburger suka dawo da ita. Ya sanya su a firjinta na kitchen.
Ta shanye tare da mika masa kofin, ya karba ya aje gefe, sannan ya matsa gareta yace, “I want be your masseur (ina so in zama professional mai yi miki tausa)”.
Murmushi Halimah ta yi, ta mika masa santala-santalan kafafunta. A hankali ya soma yi mata wata irin tausa da ba ta taba ji a rayuwarta ba. Kafin ya saki kafar ya kanainaye ta, tausar da ta rikide ta koma wani babban al’amari wanda ya rikita duniyar Halimah.
Hashim bai yi niyyar tabbatar da aurensa a daren yau ba, amma halin da Halimah ta samu kanta ya tabbatar in ya kyale ta, za ta cutu, cutuwa ba ‘yar kadan ba, don haka da amincewarta komai ya faru, domin lokacin da ta mika wuya ba ta sani ba.
Amma lokacin da Halimah ta bi sahun sauran mata Hashim ya sha duka, cizo, har da yakushi. Ta gane ashe shayi, ruwa ne, hangen kitse ta ke wa rogo. Ta jinjinawa kowace mace da ke gidan aure ta kuma gode wa Allah da ta killace kanta wa mijin aurenta kadai, yau da ba ta san da wane bayani za ta wanke kanta a idon Hashim ba.
Wanda farin cikin hakan ya gaza boyuwa daga emotions dinsa. Irin tight rungumar da ya yi mata, da irin deep kisses din da yake blowing mata lungu-lungu, sako-sako, kusfa-kusfa ya nuna how surprise and excited he was... da samunta da cikakkiyar daraja da martabarta, a matsayinta na wadda ta yi karatu mai zurfi a Turai. Take kuma yin rayuwa ta walwala da ‘yanci ta ‘ya’yan da ake yi wa kallon rashin cikakkiyar tarbiyya.
A tsayin daren bakidayansa daga Hashim har Halimah babu wanda ya runtsa. Sun kira daren night of majesty a rayuwar aurensu. Hashim bai karanci aikin likita ba, amma taimakon da ya bai wa Halimah ko likita sai haka.
Kuka kam da shagwaba ya sha su, sai dai ya yi murmushi ya shafa kai ya bada hakuri. Ma’am ta tashi daga Ma’am ta koma sweetheart a cikin bakinsa ba tare da ya san lokacin da yake fada ba.
*****
Kwana uku ana shan amarci mai suna amarci. A duka kwanakin nan Hashim ke girka musu dan abin da za su ci. Har kwana biyar ya ga Ma’am ba ta da niyyar shiga kitchen, sai dai ta nade hannu ya gama ta side tana santi, tare da mamakin yadda aka yi ya iya girki haka.
Ya je ya yo musu cefane mai dumbin yawa ya cika musu fridge da freezer, ga nama da kifi nau’i-nau’I babu wanda bai sayo ba. Sai girkin Ma’am yake jira ya dandana.
Amma har kwana bakwai Halimah ko ruwan shayi ba ta taba dafa musu ba. Yau dai ya nade hannu a kirji ya ce, “Sweetheart, yau fa girkinki za mu ci, na gaji da cin girkin kato. I want to taste my wife's cook”.
Halimah ta sunkuyar da kanta feeling embarrased, ta ina za ta fara fada wa Hashim ko indomie ba ta iya dafawa ba? Hatta ruwan zafi cook ce ta ke dafa musu, ita ba za ta iya tuna shekara nawa ta yi rabonta da kicin din gidansu ba. Ba ta taba kawo wa ranta wata rana irin wannan na zuwa ba, da za ta yi aure har ta yi girki tunda abu ne da suka riga suka cire rai da shi.
Mu karasa a littafi na biyu, tare suke.
-Takori
AURE KO BOKO?
(Littafi Ga Matasa Maza da Mata)
2
SUMAYYAH ABDULKADIR
takorikabara@gmail.com
GABATARWA
Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai.
Duba da halin da matasa ke shiga a kasarmu Nijeriya a yau, daga mazan har matan, akan rashin aikin yi ga wadanda suka samu damar yin ilmin zamani mai zurfi da matsalolin da hakan yake haifarwa, sannan da halin wasu daga cikin manyan 'yan bokon wannan zamani na baiwa boko fifiko akan addini, yasa na yanke shawarar rubuta littafin AURE KO BOKO? Ba don komai ba sai domin ya zamo hannun ka mai sanda ga irin wadannan 'yan boko da matasa masu zurfin ilmi marasa aikin yi. Tasirin furucin iyaye akan 'ya'yan su mai kyau ko maras kyau, hakika shi bakin iyaye kaifin sa da tasirin sa yafi na reza. Sannan 'ya'ya amana ne a hannun mu, kasancewar Ubangiji yayi musu umarnin su yi wa iyaye biyayya sai da yayi tagociya ga cewa banda akan umarnin Ubangiji.
Ina fatan wannan dan littafi ya zamo mai amfani ga al'umma, matasa maza da mata, ya zamo sadaqatul jariya ga iyaye na ya yafe min kurakuran da ke cikinsa.
- Sumayyah Abdulkadir (Takori)
3rd June, 2021
GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a kowanne gidan radiyo ko kafafen yada labarai ba tare da izni na ba, ko copying dinsa a kafafen sada zumunta, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma daga Lauya na Barr. Sadiq Rufai Wali.
GODIYA
Ga dukkan members na Takori's online Forum, na gode da kaunar ku da goyon bayan ku.
FATAN ALKHAIRI
Ga duk makaranta littatafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda ban sani ba, ina godiya da yabo da fatan alkhairin da kuke yi mun, Allah ya barmu tare cikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi.
AURE KO BOKO?
Amma tsakaninta da Hashim soyayya ce da amana babu boye-boye ko ha’inci, don haka ta rausayar da kai tana mai kautar da idanunta daga kallon sexy eyes din shi, ta ce,
“Wallahi Cherie ban iya ba, ban san yadda ake yi ba”.
Ko daman ya tsammaci hakan, yana so ya tabbatar ne. Ganin irin tsananin damuwar da fuskarta ta nuna sai ya sunkuya ya sumbaci wuyanta ya sakalo ta cikin jikinsa.
“Halimah, kada ki damu, in dai kina da niyya za ki zama expert a girki watarana, just say kina son koya, kuma kina da passion a kai”.
Da sauri ta ce, “Wallahi ina so na koya ko don kada ka yi min kishiya”.
Dariya ta ba shi sosai, ya ce, “Don’t ever think of this between us. Idona ba zai iya kllon wata diya mace ba bayan Ma’am dina, my Boss, my Oga on top, my uwargida, my amarya, my Sweetheart, mother of my children, apple of my eyes… Halimatus-Sa’adiyyah Hashim Yakasai…”
Dole ya sanya ta murmshi daga damuwar da ta shiga. Hakan yake so da ma shi ya sa ya kawo rahar. Ya kwantar da ita a kirjinsa kanta na bisa kafadunsa. Gashin kanta yake shafawa a hankali zuwa gadon bayan ta, yana rada mata wasu kalamai wadanda suka zamanto sirri ne a tsakanin su. Birona ba zai iya rubuta su ba.
Tun daga wannan rana Hashim ya zage yana koya wa Halima girki iyakar wadanda ya iya, ya kuma sayo mata littattafan koyon girki na Hadiza Umar Dogon Daji da na Chef Azizah Idris Gombe. Wadanda ke koyar da girki a saukake na gargajiya da na zamani, My Essential Kitchen (Aziza), from my kitchen (Hadiza Dogon Daji).
Ga kuma online class da ta yi joining na Mami Gabdo (manti’s kitchen). Kasancewar ba ta komai sai ta maida hankali, kuma da yake ta sa damuwar abin a ranta cikin sati uku abubuwa da yawa suka zauna mata. Ta fara girka musu saukakan abubuwa.
Hashim bai tsaya a nan ba ya shiga cikin ibadar Halimah, sallah, wanka, tsarki, alwala da sauransu duk sai da ya tsaya ya yi correcting dinta. Sannan ya fara yi mata dorin karatun Alkur’ani mai girma duk bayan sallar asuba kafin su koma barci, da ya lura bai fi hizfi biyu ta iya ba, shi ma a wajen Zarah ta koya.
Tana missing Zarah, amma tunda ta yi aure a Misissipi ba ta kara samun contact da ita ba.
Rayuwar Halimah ta samu kyakkyawan cigaba cikin watanni uku. Addini ya kara ratsa ta, ta daukar wa kanta duk wasu responsibilities na macen aure. Sosai ta ke kula da mijinta wanda ke yin komai iya karfinsa don inganta rayuwarta da kasancewarta cikin walwala da kwanciyar hankali. Ya gama karantar Halimah tsaf! ‘yar love ce, ita dai a yi love, idan hakan ta samu babu irin biyayyar da ita kuma ba za ta yi mishi ba. Sai ta samu Hashim ya zarta tunaninta ya dame ta ya shanye a fannin nuna soyayya da iya making love din, babu gazawa he is always available at her service a duk lokacin da ta ke bukatarsa.
Wannan satin ya ce ta shirya za su je Kano wajen su Inna, don ya ki kai ta ne har sai hankalinta ya kwanta. Kullum ya gaisa da Inna ko Yaya Rabi’a sai ya ba ta wayar sun gaisa, har sun dan saba suna hira sama-sama.
Jikin Inna da Rabi’a ya yi sanyi da suka ji sacrifice din da Halimah ta yi a kan soyayyarsa, da kuma ko wace ce Haliman da ko wane ne ubanta gare shi. Da yadda ta dauke shi aiki cikin mutunci da karramawa.
Sun yarda in ban da soyayyah ta hakika, shi din da bai isa ya samu Halimah ba. Duk da haka sun so a ce ya dauko musu daidai su, don samun nutsuwa da kwanciyar hankalinsu, amm tunda komai ya riga ya faru, ba su da ja da yin Allah.
Sosai Halimah ta ke shiri don tafiya Kano, ta ware wasu manyan atamfofinta da ba ta dinka ba da niyyar kai wa Inna Hajara da Dr. Rabi’a, sannan ta ware kayan kwalliyarta masu tsada don kai wa Sa’adatu.
Ana i-gobe za su tafi, Hashim ya shigo dakinta ya same ta tana hada kaya. Tunda ta ke a rayuwarta ba ta taba zuwa Kano ba, daga Adamawa sai Maiduguri wajen dangin iyayenta, su din ma ba sosai ba, kasancewar Daddy ba wani damuwa ya yi da su ba, saboda talakawa ne, shi kuma ba ya son su zame masa liability sai tasa ta taso shi yake nemansu in za su yi masa amfani. Saboda haka ne babu wata shakuwa tsakaninsu da danginsa na uwa ko uba.
Zama ya yi gefenta bisa carpet, ya dauko wayarsa ya yi danne-danne ya mika mata, ya ce ta sa mishi account number dinta, amma kada ta tambaye shi komai.
Ta yi hakan cikin dari-dari ta mika masa.
Ya karba ya yi ‘yan danne-danne sai ga alert ta samu, kudi ne masu dama, ya ce, “Ki yi hakuri auren mu ya zo at a smart pace (afujajan) ban samu damar yi miki lefe ba. Mun yi shawara da Yaya Rabi’a ta ce kawai in ba ki kudin, kin fi ta sanin abin da ki ke so”.
“Haba Cherie? Ni wallahi na yafe, duba tulin suturar da nake da ita wadda za su yi min shekaru biyar nan gaba, ba su mutu ba ban daina saka su ba sabida kaya ne masu nagarta. Don Allah ka maida kudin nan ka ji da hidimar yau da gobe, kada ka manta daga ni har kai unemployed ne (marasa aikin yi) yanzu. Bar ganin ka tara ‘yan kudade gaba ta fi baya yawa”.
Ya ji dadin maganganunta sosai, ya kuma kara yaba hankalinta.
“Na sani sweetheart, amma wannan hakkinki ne na al’ada, insha Allahu Allah zai rufa mana asiri. Ina ginin gida a Kano, za a gama zuwa next year mu koma mu daina zaman gidan haya, don haka nauyin zai ragu. Alhamdu lillahi kun biya ni sosai a NCC na samu na tara na gina gidan kaina, ga mota na mallaka alhamdu lillah. Things will be alright da yardar Ubangiji. So ki karba kawai”.
“Na gode, Allah ya kara budi na alkhairi”.
Ya janyo ta jikinsa yana fadin, “Tun safe ki ke hada kaya, kwana uku fa kawai za mu yi”.
Ta girgiza kai, ta ce, “Ka bar ni in yi sati tare da Inna. In ba haka ba ba za mu saba ba”.
“Abin da Kanon gaba daya za mu koma sweetheart?”
“Duk da haka. Ban taba zuwa ba tun aurenmu sai yanzu. Ka yi hakuri ka bar ni mu yi sati”.
“Your wish is my command Ma’am, I have missed calling you Ma’am… from the time I know how sweet you are sweetheart ya mamaye bakina”.
Ya fada yana kokarin hade bakinsu wuri guda, ita kuma tana sinne kai a jikinshi. Har gobe in ya kusance ta ba ta fasa jin kunyarshi kamar a lokacin ta fara zama matarshi. Tana son Hashim, yadda harshenta ba zai iya bayyanawa ba.
****
BABI NA TAKWAS
Tunda suka kamo hanyar Kano suke hira abinsu kasa-kasa, hirar da daga jinta za ka san masoya ne na hakika, kuma sabon aure. A lokacin ne ta kara sanin abubuwa da yawa da suka shafe shi da ba ta sani ba a baya. Ita ma ya kara sanin nata, a kan asalin mahaifiyarta. Ya yi mata alkawari watarana zai kai ta har Maiduguri ta ziyarci dangin mahaifiyarta.
Sun shigo Kano yamma lis, ta shiyyar Na’ibawa suka shigo, kafin a hankali su gangaro cikin gari. Ya dauke kan motar suka shiga unguwar Yakasai.
Kowa ya san Inna Hajara, ya san ma’abociyar tsafta ce. Gidanta ko ruwanka ne ya zube za ka iya tsugunnawa ka kurbe abinka. Kullum a share tas-tas a kintse, don ma dai ganyen bishiyar umbrella kan bata gidan wasu lokuta, amma a take ta ke kwashewa, da yake bishiyar ba ta zubda ganyen da yawa.
To yau ma hakan ta gama sharar yamma ta yi wanka ta zauna tana sauraron Aminci radio, Sa’adatu ta zo hutu daga makarantar kwana da ta ke yi a GGC Kano, ta aike ta ta debo mata kwai a kangon da suke gidan gonarsu, wanda like yake da katangar gidan.
Sallamar Hashim da santaleliyar matarsa ya dauki hankalinta. Ta mika hannu ta rage sautin radiyon tare da amsa sallamarsu tana murmushi. Halima sai sunkuyar da kai ta ke, ta mika mata hannu tana fadim, ta zo gabanta ta zauna. Yara suka soma shigo da jakar kayansu da tsarabar doya da potatoes da Hashim ya yi wa Inna a kan hanya.
“Masha Allah, masha Allah”. Kawai Inna ke fadi, domin ta ga Haliman ba yadda ta tsammace ta ba. An ce mataimakiyar shugaban ma’aikata sukutum, ta dauka za ta ga uwar mata irin matan Abuja da ke like wa kananan yara, sai ta ga yarinyar da a fuska ba ta fi Sa’adatu mai shekaru ashirin ba, wannan ya kara sanyaya zuciyarta da auren hankalinta ya kara kwanciya da auren.
Har kasa Halimah ta durkusa tana gayar da Inna, ita kuma sai saka musu albarka ta ke. Ta mike zuwa firjinta da ke kicin ta debo musu kunun aya mai sanyi da gardi. Tana fadin, “Kin sha hanya Halimatu, maraba da Sa’adiyyah”.
A lokacin Sa’adatu ta shigo, niki-niki da crets din kwai. Saura kadan ta saki kwan a kasa don murna. Cewa ta ke,
“Welcome Aunty Halimah”.
Ta zo gaban Halima ta kama hannunta, sai kallonta ta ke tana mamakin kyawun halittarta. Ba ta san sanda ta ce,
“Brother you are among the luckiest”.
Murmushi ya yi idanunsa na satar kallon Halimar ya ce, “Koh?”
Inna ta ce, “Tashi sarkin magana ki kai musu abinci su samu su huta gajiya, ina ce dai kin gyara dakin nasa da na ce ki gyara suna hanya?”
Sa’adatu ta ce, “Ai tun safe na kalkale shi Inna, na sa turare na san brother da son turaren wuta”.
Inna ta ce, “To dauki jakar kayansu ki shigar musu da ita. Halimatu tashi ku je ki huta, ina fatan kinyi sallar la’asar?”
Halimah cikin jin dadin tarbar da ta samu daga family din Hashim, ta ce, “Mun tsaya a hanya mun yi Inna”.
“To madallah, Allah ya huta gajiya”.
Halima ta bi bayan Sa’adatu wadda ta dauki trolley dinsu da handbag dinta zuwa dakin Hashim da ke gidan.
Babu komai a dakin, daga shimfidadden carpet mai taushi blue, sai dirkekiyar sabuwar katifa da aka jefa a kasa, aka kalailaye ta da kyakkyawan bedsheet, sai sababbin filulluka guda biyu. Halima ba ta fahimci Hashim ma a dakin zai kwana ba sai can bayan isha da ya shigo daga masallaci ya zare rigarsa ya bar farar singlet da dogon wandon jeans din da ke jikinsa ya fada gefenta a kan katifar yana fadin,
“Na gaji, yau sai kin kwana kina min tausa tunda ba ki karbe ni tuki ba har muka zo Kano”.
Halimah ta zaro ido, “Don Allah ka tashi ka fita, kada Inna ko Sa’adatu su shigo, ka yi wa Allah ka fita ko ni in fita”.
Wani kallon so ya jefe ta da shi, sannan ya yi dariya.
“Ai nan dakina ne tun na samartaka, kuma kina ji ita Innar da kanta ta ce a nan za ki sauka. Gara ma ki saki jikinki yarinya ba alfahari ba, Innata is very simple and easy going. Sannan tana da wayewar kai daidai misali…”
Halima ba sauraronsa ta ke ba, mikewa ta yi jikinta har rawa yake ta yayibi mayafinta ta fice dakin Inna.
Inna da Sa’adatu na kallon talabijin, Halima ta fado dakin duk suka dube ta, sai duk kunya ta kamata, ta ce, “Inna… am… na ce ko ina ne dakin Sa’adatu? Ina so zan kwanta”.
Inna Haajar ta dube ta with concern cikin yaba nutsuwarta a ranta ta ce,
“Dakin mijinki za ki zauna, daga yau har ku koma. Sai in ba ya nan ne za ki kwana tare da Sa’adatu. Ki saki jikinki da mu mun zama uwa daya uba daya. Ni uwarki ce ba suruka ba”.
Hawaye ne ya cicciko idanun Halimah, ta ji dadin kalaman Inna Haajara, something she missed from a mother, wato kulawa. Za ta iya cewa ta ji kaunar dattijuwar har cikin ranta. Ta yi musu sallama cikin jin kunya ta juya ta koma.
Hashim na waya lokacin da ta shiga, da turanci yake magana ba ta san ko shi da waye ba, ta zauna gefen katifar tana zumburo baki, ya rufe wayar da murmushi ya ce, “Kin dawo? Da fatan kin samu su Inna lafiya?”
Filo ta dauka ta hau buga masa shi kuma ya rike yana mata dariyar keta. Ya ce, “Ita Inna ai so ta ke a yi maza a dire mata jika tunda haka ne kuwa dole ta dawo da ke ki kwana bisa hakarkarin mijinki”.
Washegari Inna ta hada musu breakfast mai kyau, kunun gyada fari tas ya ji madarar ruwa ta peak da wani lafiyayyen kosai mai dadi wanda aka fasa kwai a cikinsa. Sa’adatu ce ta kawo musu, suna ci tana ta santi. What a simple life! Wato a rayuwa ko kwalin PhD gare ka ba za ka daina daukar ilmi ba. Yau ta shigo wata rayuwa da ba ta san da ita ba. Amma sai ta samu ta fi tata dadi da armashi. Tabbas dumbin arziki ba shi ne jin dadin rayuwa ba.
A ganin Halimah ka samu mijin da ke sonka, uwa mai sonka a gefe da rufin asirin Allah ba tare da ka ci hakkin kowa ba shi ne jin dadin rayuwa. Tana missing Daddy, amma ta fi maraba da sabuwar rayuwar da ta tsinci kanta.
Washegari Inna sai fitowa ta yi ta ga Halimah na yi mata wanke-wanke. Ta share tsakar gidan tsaf! Inna ta runtse idonta tana fadin,
“Me ya sa Halimah? Don me za ki wahalar da kanki daga zuwanki jiya-jiya? In kin bari ai Sa’adatu na gida za ta yi in gari ya gama haske. Don Allah kada ki kara tunda kanwarku tana nan”.
Maganganun Inna ne suka taso Hashim daga barcin da ya koma bayan ya dawo masallaci. Ya shafa gefensa babu Halimah. Mikewa ya yi ya zura jallabiyyarsa kan wandon jikinsa wanda bai karasa idon sawunsa ba ya fita.
Nan ya same su ita da Inna, Innar na ta yi mata fadan wanke-wanke da shara. Murmushi ya yi ya koma daki, Halimah ta kara shigewa sukuf! Cikin ransa ta yi wa kowacce mace fintinkau a zuciyarsa.
Kullum kafin a dora abincin rana sai Inna ta tambayi Halima abin da ta ke so shi za a girka, haka duk dare. Halimah ta fi ambatar abincin gargajiya wanda ba ta saba da shi ba. Ga Inna gwanar girkin gargajiya, Halimah kan zauna gefe ita da Sa’adatu suna taya ta ayyuka tana nuna musu yadda za su yi, tana kuma yi wa Halima bayanin komai don ta iya a karan-kanta. Da ma kuma kwakwalwar Halima ba irin ta kowa ba ce tsaf! Ta ke dauke komai, har ana i-gobe za su koma Abuja Inna ta sakar musu girki ita da Sa’adatu, suka yi sinasir da miyar ganye. Kuma sinasir din ya yi kyau sosai. Dare ya yi su shige daki mijinta ya shayar da ita soyayya mai zakin da ta fi ruwan zuma, wanda bukatar Halimah a rayuwa ke nan. Ba ta fito fili ta fada ba, amma Hashim a matsayinsa na mai ilmi ya gama gane she’s a nymphomaniac. Yana rokon Allah ya tsawaita ransa, ya ci gaba da ba shi lafiyar da zai ci gaba da iya wa Halimah da dukkan bukatun rayuwarta.
Sun je gidan Dr. Rabi’a sun wuni, sai dai ko kadan Halimah ba ta ji dadin tarbar da ta samu daga Rabi’a ba, kamar ba ta farin ciki da ita matsayin matar kaninta, kuma ba ta san me ya sa ba. Ita kuwa Rabi’a a bangarenta gani ta ke Halimah ta fi karfinsu, za ta mallake musu dan uwa ko da wannan fitinannen kyawun nata. Bayan wannan ba ta da wani dalili na not welcoming Haleemah.
Da za su tafi Halimah ta kawo tsarabar swiss-lace mai kalar ruwan zuma ta ba ta. Dr. Rabi’a ba ta taba haihuwa ba.
Kafin su bar Kano sai da aka aza harsashin ginin Hashim a matsakaicin filin da ya saya a unguwar Janbulo, karamin gida ya sa aka zana masa wanda ba zai ci kudi ba. Amma ya samu tsari mai kyau. Only three bedrooms da falo mai yalwa, kitchen wadatacce da toilets guda biyu, get din gidan karami ne, parking space mai cin mota daya.
Sun je shi da Halimah sun ga yadda ake aikin. Sosai Halimah ta yaba kai ka ce wani hadadden gida ake mata a G.R.A, Allah Ubangiji da ya halicce ta sai ya sako ta cikin masu wadatar zuci, masu yakanah, masu godiya ga duk ni’imar da ya yi musu komai kankantarta.
Kwanakinsu bakwai cif! Suka kamo hanyar Abuja, bayan motarsu dankare da tsarabobin da Inna Haajara ta hada musu. Halimah ta yi kewar dattijuwar har ta ke rokon Hashim ya dauko musu ita ta kwana biyu tare da su a Abuja. Hashim ya ce, Inna ba za ta yarda ba.
Bayan dawowarsu daga Kano, Hashim ya soma buga-bugar neman aiki a ma’aikatu ko Allah zai sa ya dace, Halimah da babu takardu a hannu sai zaman gida, da girka wa maigida abinci. Haka bai hakura da cike vacancies ta online ba. Wasu za su kira shi aptitude daga nan ba ya kara ji daga gare su.
Dan kudin hannunsa gabadaya gini ya lamushe, inda Allah ya taimake su ma kudin hayar na shekara suka biya, kuma sun shake store da freezer da abinci, abin da suke saya ba shi da yawa. Haka zai fita tun safe goye da jakar takardunsa sai magriba zai dawo a yunwace babu ko sisi.
Halimah ta koyi wani abu wai shi tattali na kayan abinci da kayan sanyawa, wanda a rayuwarta ba ta taba zaton watarana irin wannan za ta zo mata ba. Da za ta yi wa kaya sanyawa har uku kafin ta wanke su.
Inda Allah ya kara taimakonta cikin kayan da Daddy ya yi mata har da karamin injin wanki, da shi suke wanki, ta zauna ta goge musu kayan da kanta da iron, wanda shi kansa amfani da iron din Hashim ne ya koya mata.
Sabida zurfin ciki irin na Halimah, suna yawan waya da Hanan amma ko da subutar baki ba ta taba gaya wa Hanan suna cikin wani hali ba, balle ta nemi taimako daga gare ta. Abin da ta sa wa ranta shi ne, Allah na tare da su, kuma bai manta da su ba.
Shekara ta zagayo Halimah ko batan wata ba ta taba yi ba, babu aiki ga Hashim babu alamarsa. Allah kadai ya san da yadda suka cimma shekarar nan a cikin garin Abuja. Kudin haya ya kare aka ba su notice, dole suka tattaro komai nasu da ke cikin gidan cikin akori-kura, kudin akori-kurar ma Landlord (mai gidan da suke haya) shi ya biya musu (full tank) sabida sun yi zaman mutunci tare da shi.
Gidan nasu an gama ginin, an yi plasta, amma ba a samu zarafin yi masa fenti ba. A haka suka shiga abinsu, Sa’adatu da Dr. Rabia suka zo suka taimaka musu suka jera kayan Halimah, sabida kayan masu quality ne ba abin da suka yi. Dr. Rabi’a ta tambaye shi ya ba a yi fenti ba? Shiru ya yi yana sosa kai, ta san halin Hashim sarai, ba ya bayyana babunsa sai samunsa. Idan ya samu kowa da ke jikinsa sai ya shaida ta hanyar kasonsa da zai ware masa.
Dan aikin da ya yi a Abuja na shekara guda ba karamar hidima ya yi musu ba, don haka washegari sai ga masu yin fenti ta turo su yi duk gidan, ba tare da ta yi shawara da Hashim ba.
Kwarai ya ji dadin wannan karamci na ‘yar uwarsa. Har gida ya je ya yi mata godiya. Halimah gwanar iya tsari, sosai ta tsara gidanta, ya yi kyau sosai kamar gidan wani ma’aikacin banki.
*****
A yayin da rayuwa ta juya wa dan Adam, abin da ake so shi ne, ya karfafa imaninsa, ya sa a ransa Allah na sane da shi. Yana jarraba imaninsa ne. To hakan ce ta faru da Halima, ranar da ta budi ido a gidan mijinta ko kwayar shinkafar da za su dafa ba su da ita. Ba irin buga-bugar neman aikin da Hashim ba ya yi har kuwa da koyarwa a sakandire, amma condition na kasarmu da komai sai kana da kafa ya hana Hashim samun aiki. Har tsohuwar makarantar da ya yi koyarwa wato ‘Yan Dutse ya je ya roki su maida shi, inda suka sanar da shi ai tuni suka maye gurbinsa da wani. For now ba sa bukatar sabbin malamai.
Don haka wuni guda sur! Yau Hashim ya kasa fita ko’ina, babbar damuwarsa ita ce ya bar Halimah da yunwa. Wasu hawaye masu zafi ke taruwar masa a ido yana maida su. Ba ya nadamar auran Halimah, kuma har abada ba zai yi ba. Ya yi alkawarin rike Halimah da kula da ita, amma in bai da abin yi da me zai kula da itan? Da me zai ciyar da ita? Ba ya son ya gaya wa Inna halin da suke ciki, don kuwa yanzu za ta maida ciyarwarsu a kanta, dan jarin kiwon kaji da ragunanta ya kare a kansa. A wannan matakin na rayuwa kam, in bai ciyar da Inna ba, ai ba zai bari ta ciyar mishi da mata da shi kanshi ba.
Wani tunani ne ya zo masa, zumbur ya mike ya dau mukullin motarsa ya fita. Halimah na kallon talabijin shirin Arewa24 cikinta yana ta damka, yunwa kamar ta mutu, rabonta da abinci tun daren jiya da suka ci gurasar teburin mai tsire. Tana ta cijewa tana daurewa, tare da kurbar ruwan bunun da ke cikin kofi a gefenta, wanda ko sukari babu a cikinsa.
Ta gabanta ya zo ya wuce da sauri, tana tambayarsa inda za shi, yana tafiya yana ce mata, “I’m coming…”
Wajen sayar da motocin hannu ya nufa, aka yi cinikin henessy dinsa, kashi uku cikin goman kudin da ya siye ta. Ya bada takardu aka dunkulo kudinsa aka ba shi.
Bai zame ko’ina ba sai super market ya dankaro wa Halimah shopping ya sayo kayan abinci, aka cika masa dan sahu taf! Ya nufo gida. Halimah sai gani ta yi ana ta sauke mata kaya, mamaki ya hana ta cewa komai, har yaran suka gama Hashim ya sallame su.
Zama ya yi rigijib a kan kujera cike da gajiya. Halimah ta zauna kusa da shi a sanyaye.
“Cherie, ina ka samo kudi haka? I hope it’s by halal means?”
Rungumota ya yi barin jikinsa na dama, “Ki min zaton alkhairi Sweetheart, ba zan taba ciyar da ke da haraam ba”.
Tana wasa da botirin rigarshi ta yi murmushi, ta ce, “I trust my husband, but I need an explanation”.
Ya ce, “Sai kin ci abinci ga kaji nan a ciki ki gyara ki yi mana farfesu. Tashi mu je in taimaka miki”.
Tare suka yi girkinsu mai rai da motsi, wanda suka dade ba su ci irinshi ba, suka ci cikin marmari. Sai lokacin kwanciya barcinsu yake sanar da ita motarsu ya siyar, ba zai iya jure ganinta tana jin yunwa ba, in Allah bai kama shi da laifin hakan ba, shi ba zai taba yafe wa kansa ba.
Ko kadan Halimah ba ta ji dadi ba, domin ta saba da motar, amma ta yarda ba su da wani option na samun kudi masu kauri ban da hakan.
Ta ce, “Sauran kudin me za ka yi da su?”
Ya jingina a jikinta, ya ce, “Karamin provision shop zan bude a dan shagon jikin gidan nan”.
Halimah ta amince da shawararsa, ta kuma ce ya debi kayan abincin ya kai wa Inna ko don ta sa musu albarka.
Cikin sati daya provision shop ya budu, Hashim na zama a ciki daga karfe tara na safe zuwa azahar, ya shigo ya ci abinci ya koma, la’asar ya shigo ya yi sallah ya kuma zuwa magriba ya rufe shagon sai kuma gobe. Dr. Rabi’a ma na kokarin nema masa lecturing a Legal, amma abu ya faskara sabida ba sa karantar da field dinsa.
****
BABI NA TARA
Halimah na suyar manja da za su ci wake da shinkafa da shi, ta ji kauri wanda ba ta san daga ina yake fitowa ba. Ta dudduba dakunansu ta tabbatar ba daga nan ba ne, sai kawai ta koma kicin ta ci gaba da aikinta.
Hashim ya tafi kasuwa zai saro kayayyakin da suka kare a shago. Bude wannan shago ba karamin taimako ya yi musu ba, ba sa samun wata riba ta a zo a gani, amma suna daukar komai su yi amfani da shi kenan ribar a cikinsu suke cinye ta.
Ba su da matsalar abinci, omon wanki, sabulun wanka ko sauran kananun abubuwan amfanin yau da kullum. Sannan suna diba su kai wa Inna na neman albarka. Ita kuma lokaci-lokaci tana aiko musu da cret din kwai da kajin gidan gona biyu ko uku.
Ta gama suyar manjanta wanda ya ji albasa, sai tashin kamshi yake yi, ta ji hayaniya daga waje ana fadin, “A kawo taimako… gobara! Gobara a shagon Hashim!!!”
Saboda kidimewa ba ta san sanda ta saki soyayyen manjan hannunta ba ya kware a kan kafafunta.
Wani ihu hade da salati Halimah ta saki, duk da azabar da ta ke ji, amma hankalinta na kan gobarar da ake fadi a shagon Hashim. Kafin ka ce me ye wannan fatar farar kyakkyawar kafarta ta tashi ta kukkumbura. Amma a haka ta yo waje da gudu ko mayafi ba ta tsaya dauka ba, domin ta manta da shi.
Wuta ce ganga-ganga mutane nata watsa mata ruwan omo, amma sabida kayan da ke ciki masu cin wuta ne sai kara habaka ta ke yi, Halima ta koma gefe tana hawaye tana kallon yadda gabadaya abin da suka dogara da shi yake konewa kurmus! Shago kam ya kone, ba abin da ya yi saura sai gawayi.
Sai da ya gama konewa aka samu wutar ta tsaya, already ba abin da aka iya cirewa sai gawayi. Har ta soma lasar wani bangare na bangon gidan ya yi bakikirin. Babu wanda ya lura da Halimah ta durkushe ta ci kukanta ta koshi, sai da mutane suka watse ana ta cigiyar Hashim, sannan ta lallaba ta koma gida.
Sai yamma lis Hashim ya dawo cikin adaidaita sahun da aka dankaro wa kayan provision. Tun daga nesa ya hango bangon gidansa ya yi bakikkirin.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Kawai yake ambata, har mai adaidaita ya juyo yana tambayarsa, “Malam lafiya?”
Motar na tafiya haka Hashim ya dirgo ya yanka a guje, ba abin da yake masa amsa-kuwwa a kunne irin HALIMAH!!!
Ga babban kwanciyar hankalinsa da ita ya fara tozali yana shiga harabar gidan, tana zaune a kan kujerar roba da suke zama da yamma su sha iska ta kada kanwa tana ta kwara wa kafarta bayan tuni ta riga ta tashi. Da sauri ya duka ya rungume ta yana fadin,
“Halima, are you alright?”
Har wani irin girgiza ta yake yi. Da ganinta ta ci kuka ta koshi.
“Tell me Halimah, are you okey?”
Ta sanya fuskarsa cikin tafukanta ta ce, “I’m okey Hashim. But shagon mu ya kone kurmus, shi ne garin kidima na kone kafafuna da manja”.
Ya kai idonsa ga kafafun nata, tsigar jikinsa ta yi wani irin tashi. Ga shi ba shi da motar da zai saka ta a ciki ya kai ta asibiti, kada kuma ya goya ta a bayansa a ce ya haukace. Amma tabbas ba shi da maraba da zautaccen a wannan lokacin. Ba shago ne damuwarsa ba, lafiyar Halimah ce.
“Bari in samo adaidaita sai mu tafi asibiti kin ji? Sorry sweetheart”.
Ko ta kan zancen shago bai bi ba, ya juya ya fita jikinsa na kyarma, mutanen unguwa nata yi masa jaje, amma ko amsawa ba ya iya yi, ya tare dan sahu ya shige ba bayani, da kyar ya ce da shi matarsa za su kai asibiti.
Har cikin get suka shiga da adaidaitan, ya dauko mata hijabin sallarta. Bai ji kunyar mutumin ba ya sunkuce ta ya sa ta a motar tana fadin, ya kyale ta za ta iya takawa, amma ina!
Asibitin malam Aminu Kano suka je, bangaren accident & emergency, da kyar suka samu aka karbe su. Aka yi mata treatment sosai tana ta kuka da hawayenta don azaba. Daga asibiti gidan Inna ya wuce da ita, don ya san wannan jinyar ta fi karfinsa.
Inna ta yi salati ta sanar da Ubangiji da ta ji abin da ya faru, ta yi addu’ar Allah ya mayar da alkhairi. Ta shiga kula da Halimah bilhakki. Rabi’a ta zo ta yi masa jaje, ta kuma duba Halima, duk da dai ba wai tana sonta ba ne har yanzu. Ta ba ta hakkinta ne da ya rataya a kanta.
Watan Halimah biyu a gidan Inna tana jinya kafin ta samu lafiyar kafarta, amma tabo ya kwanta lambam. Suka koma Janbulo inda aka koma ‘yar gidan jiya.
Sai kuma laulayin ciki ya sako Halima a gaba. Ba ta iya cin komai sai yalo data. Duk ta rame ta yankwane, a karshe likita ya rike ta a asibiti ake ta sa mata ruwa.
Kwanansu hudu aka sallame su. Hashim ya ga cewa, ba zai iya da Halimah ba don ko kudin yalo datan watarana rasawa yake yi, don haka ya kara maida ita gidan Inna.
Inna da yake babba ce ta san abin da za ta iya ci, kuma shi ta ke mata, kunun tsamiya, tuwon laushi miyar kalkashi da miyar zogale, sosai Halimah ke bude ciki ta ci, tuni ta kara murmurewa.
Sa’adatu ta samu miji wani malaminsu na sakandire, amma sai daga auren suke sabida ba su shirya ba. A karshe Inna ta sa ragunanta da ta ke kiwo manya-manya a kasuwa ta sayar, Dr. Rabi’a ta kawo nata gudunmawar, Hashim babu ko sisi, aka tsaida lokacin auren watanni uku masu zuwa.
Ta dade rabon da ta yi magana da Hanan, ko ta kira layin ba ya shiga. Ko dai Hanan ta daina amfani da layin, ko kuma ba ta kasar Nigeria. Ta taba gaya mata sun dawo Kano, amma ba ta gaya mata wani address ba. Ta so ta gaya mata maganar samun cikinta da konewarta. Sosai ta ke kewar Hanan duk da cewa in suna tare din fada suke yi irin na sako da sako.
Daddy fa?
Ta yi ajiyar zuciya tana lalubar zuciyarta, did she really missed him? A take amsa ta zo mata, “No, she didn’t. He is, but a cruel father (shi ba komai ba ne sai mugun uba a gare su), wanda ya zama silar duk wannan wahalalliyar rayuwar da suke ciki.
Ta kai hannu ta shafe hawayen idanunta. A fili ta ke addu’a ba ta san cewa a filin ta ke yi ba.
“Ya Allah ka ga zuciyata, Ka ga niyyata ta alkhairi ce, ta raya sunnar manzonKa. Ban yi aure don in zamo mara biyayya ga mahaifina ba, sai don kare kaina daga dattin ZINA. Allah ga HASHEEM! Ka dubi lamarinsa Ka tausaya masa. Ka sa sai dai ya zamo mai bayarwa ba mai karba ba. Allah ka yalwata masa, Ka azurta shi ta inda bai tsammani ba…’
Ji ta yi Hasheem ya kwantar da kai a gadon bayanta, ya lumshe ido yana jin addu’o’inta. Tana rufe baki ya dora tasa.
“Allah ga Halimatu-Sa’adiyyah, Ka ba ta aljannah albarkacin aure. Idan har miji ke daga wa mace kafa ta shiga aljannah, na daga, na kara dagawa. Ina rokonKa Ka ba ta mafi darajar aljannah (Firdaus). Ka sa ta zamo uwargidana a gidan aljannah ba tare da hurul-eeni ba”.
Da sauri ta juya ta rungume shi. Ya yi azama wajen ba ta masauki a katafaren kirjinsa. Sosai yake sumbatarta kamar zai cinye ta. Ba ta yi nawa ba wajen maida martani. Wani yanayi suka tsinci kansu wanda ya zarta na amarcinsu. Har suka manta cewa a gidan inna suke.
*****
Duk wani tattali na duniya Hashim ya dauka ya dora a kan cikin Halimah. Ba shi da zabi a kan jinsin da za ta haifa, kowanne ne ya san zai so, matukar zai yi kama da Halimarsa.
Sabida halin babu, a asibitin Murtala Halima ke bin layin awo, in ka ganta ba za ka taba tsammanin Engnr. Halimah Zubair ce ba, wadda manyan kasashen duniya daidaya ne ba ta taka kafarta ba. Wadda ba ta taba sanin wani abu wai shi BABU a rayuwarta tun haihuwarta ba. Haliman da ke jan motoci irin su Toyota Avensis, Discussion Continues da Rolls-Royces a titunan Abuja. Haliman da kafin ka samu appointment din ganinta sai ka isa wane a manyan kusoshin Nigeria. Ta dauki rayuwarta bakidaya a matsayin bautar Allah, bautar aure bautar Allah ne. Allah shi ne mai bayarwa kuma mai karba.
A wannan lokacin imaninta ya karu, ta kara dagewa da ibadah tana rokon Allah ya sauke ta lafiya, ta samu sanyin idaniya, wanda shi kadai za ta kalla a matsayin jininta a halin yanzu, don alkawarin da Hashim ya yi mata na kaita ga dangin mahaifiyarta har yau bai samu cika shi ba sabida yanayin da suke ciki.
Hashim ba shi da kowacce sana’a sai lesson da yake yi wa ‘ya’yan wani maikudi a nan unguwarsu ana biyanshi dubu goma a wata. Da wannan dubu goman da kuma taimakon Inna suke gangandawa suke cin abinci. Ya dade da daina smoking tun suna Abuja, sabida son da yake yi wa matarsa Halimah.
Cikin Halimah na da wata bakwai, ta fito toilet da daddare za ta kama ruwa ta ci uban tuntube da bokiti ta fada da baka a kan cikinta. Wata razananniyar kara ta saki, wadda ta taso Hashim a gigice, yana zuwa toilet din ya kunna fitila abin da ya gani ya razana shi, jini ne ke malala daga kasan kafafunta.
Ya rasa me zai yi? Ya rasa taimakon da zai ba ta. Ga shi cikin sulusin dare. Ya sunkutota ya fito da ita tsakiyar dakin ya shimfide. Tana ta murkususu shi kuma yana kiran sunanta yana rokonta ta yafe masa shi ya janyo mata duk wahalar da ta ke ciki.
Wani uban nishi da Halimah ta yi sai ga Da ya fado, ba jimawa mabiya ta biyo baya. Hannunsa na karkarwa ya dauki dan cikin kazantar haihuwa ya rungume a jikinsa. Sai dai tsawon lokaci bai ji ya yi kukan da ake cewa jarirai na yi in sun iso duniya ba. Bai ga yana wutsil-wutsil da kafafu da hannayensa ba.
Kada dai hakan na nufin… there baby is no more? Hashim ba ya son yarda da tunaninsa. Halimah don wahala bingirewa ta yi a wajen tana barcin wahala. Har aka yi kiran assalatu bai ga alamun babyn nan ya motsa ba. Gari ya soma haske dole ya ajiye jaririn a gefen Halimah ya fita ya buga wa makwabtansa kofa, ya ce su zo su taimaka masa, Halima ta haihu cikin dare.
Matar gidan suna mutunci da Halimah sosai, duk da ta girme ta nesa ba kusa ba. Ta dauko mayafi ta bi bayansa. Ta dauki jaririn nan ta bubbuga shi, amma babu motsi. Yaro babba da shi kamar ba bakwaini ba an gama yi masa cikakkiyar halittarsa.
“Ku yi hakuri Hashim, bai zo da rai ba, ko kuma bayan haihuwar ya koma”.
Hashim ya rike kansa yana fadin, “Ya Allah I seek your forgiveness, idan wani laifi na yi maka ka ke hukunta ni nau’i-nau’i”.
Hajiya Mukarrama ta ce, “Kul! Hashim, maza yi istigfari ga sabonka ka gaggauta cewa astagfirullah- alhamdu lillah…”
A hankali yake maimaitawa, kamar mara lafiyan da ya zo gargara ake lakanta masa kalmar shahada. Ya daga Halimah daga kasa jina-jina cikin kazantar haihuwa ya rungume ta a jikinsa. Ba ta san yana yi ba sai barci ta ke yi, wani wahalallen barci da ba ta taba yin irinsa a rayuwarta ba.
Hajiya mukarrama ta dauko kwalin indomie a kicin dinsu ta sanya jaririn a ciki ta rufe. Ta ce ya ba ta waje ta gyara Haliman, dole ta tashi daga barcin nata. Juyawar nan da za ta yi ta ji ta sakayau babu nauyin cikinta.
Ido ta bude a kan Hashim, shi kuma ya girgiza mata kai, sannan ya lumshe idonsa. Ta kai hannu ta shafo cikin ba ta san lokacin da ta mike zaune ba.
“Ina babyna Hashim?”
Ya kama ta ya rike yana magana cikin taushin murya.
“Allah da ya ba mu Ya fi mu sonsa, don haka kada ki yi bakin ciki don Ya karbi abinsa”.
Halima ji ta yi duniyar na juya mata, wani duhu ya mamayi idonta. Sai bude ido ta yi ta ganta a gadon asibiti, Hajiya Mukarrama a gabanta. Kanta bisa cinyar Hashim ko kunyar Hajiya Mukarrama bai ji ba.
Kwanan Halimah biyu a asibitin Murtala sannan aka sallame ta. Inna ta ce Yakasai za ta wuce da ita. Jego zata yi mata sosai domin kuwa ita da mai haihuwar wata tara ba su da maraba. Hashim bai ja ba, ko shi ya so hakan.
Sa’adatu ita ta dinga taimaka wa Inna wajen jegon Halimah, amma Dr. Rabi’a tunda ta zo sau daya ta jajanta ba ta kara zuwa ba. A ranta ta ce, Hashim ya je bariki ya auro mai farar kafa, ya kasa mallakar kwandalar kansa, dan da ya haifa ma a duniya kansa bai tsira ba.
(Hasbunallahu wani’imal wakeel. Wani babban kuskure da mata ke yi ke nan, kiran ‘yar uwarsu musulma da mai farar kafa in mijinta does not succeed in life. Sun manta an ce rabon bawa da arziki sai mutuwa. Sannan RAI DAI… ba ya rabuwa da rabo… sai dai idan ya kare. Sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba a je ba. Idan kuma Ubangiji ya riga ya rubuta wa bawa kaddarorinsa na rayuwa ciki har da arziki da talauci, babu dan Adam din da ya isa ya kankare. Allah ka hani harshenmu yi wa ‘yan uwanmu musulmi mugun alkaba’i, ameen).
Ranar da Halimah ta yi kwanaki talatin tana jego, wani mummunan tashin hankali wanda ya fi na rasa baby ya same su.
Ya tsayar da komai na rayuwarsu dungurugum!
Inna Haajara ce ta shiga bandaki da buta a hannunta za ta yi alwalar magriba, sai ta zame ta fadi, shiru-shiru Halimah da Sa’a ba su ganta ta fito ba, sai zuwa suka yi suka tadda ta ba rai a jikinta.
Halimah na ganin cewa, mutuwar Inna Haajara, ita aka yi wa mutuwa ba kowa ba, don ita ce ba ta da kowa da za ta kira uwarta bayan Innar.
Ta rike ta da amana da kyautatawa kamar uwar da ta haife ta. Ta zauna da ita da zuciya daya. Zuwa yanzu ta gama fahimtar Dr. Rabi’a ba ta sonta a kan dalilin da ba ta sani ba.
A wajen makokin Inna ta wulakantata a cikin mutane ya fi a kirga, sai dai ta shiga daki ta ci kukanta ta more. Har tana cewa tunda ta shigo gidan su masifa ke bibiyar Hashim. Sa’adatu ce ta samu Yayanta a boye wanda mutuwar mahaifiyarsa ya fyadar da shi a lokaci guda, don mutuwa ce kamar ta fuju’a, Inna lafiyarta kalau ko ciwon kai ba ta yi ba. Tana tsaka da hidimta wa rayuwarsu Allah ya amshi ranta.
Ta gaya masa duk abin da Dr. Rabi’a ke fada a kan Halima, kuma a gaban idon Haliman. Hatta gashin jikin Hashim gabadaya sai da ya mimmike, idanunsa suka kada suka yi jajir, bakinsa har rawa yake kamar yadda ilahirin jikinsa ke kyarma kamar ana kada masa gangi. Bai tsinci kansa a ko’ina ba, sai a gaban Yayarsa Rabi’a.
“Adda Rabi’a, ki sani daga yau babu ni babu ke. Ko a hanya muka gamu kada ki nuna kin taba sanina. Da ma Inna da Baba ne suka hada kuma babu su, me rabawa ta raba.
Wadda ki ke kira ‘yar barikin mai farar kafar ta fiye min ke sau shurin masaki. Sannan babu wanda ya isa ya taba mutuncin ta in kyale shi. Ko wane ne, idan na ce kowa… ina nufin ko KE!”
Rabi’a ta bude baki tana kallonsa.
“Hashim ni ka ke yi wa diban albarka a kan mace? Macen ma wadda ta zabi namiji a kan iyayenta? Tunda ka aure ta mun taba ganin wani nata? In ba daga barikin ta fito ba, daga ina ta ke?
Hannunsa ne ya fita daga jikinsa zai mari Rabi’a, ya tuna yawan shekarunta a kan nasa. Hankali tashe ya juya don barin wajen ya yi ido hudu da Halimah da ke rakube a bayan kofa. Yawan hawayen da ta ke bulbularwa su suka tabbatar masa ta gama jin maganganun Yayarsa Rabi’a. Hannunta kawai ya ja, suka bar dakin Inna zuwa nasu dakin.
“Hada kayanki tsaf mu koma gida”.
Ba ta iya ta ce komai ba ban da bin umarninsa. Ta gaban Adda Rabi’a da sauran ‘yan zaman makoki da ba su kai ga watsewa ba Hashim ya wuce rike da Halimah. Daya hannun nasa kuma jakar kayanta ne. Adda Rabi’a ta yi tsaki ta ce,
“Idan ka ga dama ku bar kasar kai da mai farar kafarka”.
A wannan daren, duk iya rarrashi irin na Hashim, duk kwarewarsa wajen sarrafa harshe, ya kasa rarrashin Halimah. Wadda ta hada kai da gwiwa tana rero kuka mai tsuma rai da keta zuciya. Tambayar kanta ta ke, to ko abin da ta yi don tserar da kanta daga zina wato AURE kuskure ne? Ko dai Daddy ne a kan daidai? Ya san haka auren yake shi ya sa ya ce ba za su yi ba, don ba zai iya jurar wani ya wulakanta masa su ba? Yau abin da ya fi wulakanci ta gani a gidan aure a bainar jama’a.
Shin mene ne laifi a cikin soyayyar da ta ke wa Hashim? Ta baro gatanta, pride dinta, duniyarta, kwalayen ilminta, reputation dinta, career dinta duk don ta rayu da Hashim, yau abokiyar haihuwarsa na neman kala mata witchraft (maita) tunda a fakaice so ta ke ta ce Inna ma ta rasu ne saboda ta rabe ta, kalmar farar kafa ta kasa bacewa daga zuciyarta. Yau ita ake yi wa gorin rashin yin arziki, bayan wanda ta tsallake saboda HASHIM!!!
****
BABI NA GOMA
Ba ta rarrasu ba sai da ta ga Hashim yana hawaye shi ma, abin da bai taba yi a gabanta ba. Ya tabbatar mata ba shi ba yaya Rabi’a, ya yanke duk wata ‘yan uwantaka da ke tsakaninsu. Ba ita ta ci wa mutunci ba shi ta ci wa. Tunda shi ne fakiri ba ita ba, shi ne mai farar kafar da ya raba ta da duniyarta, ya tsumbula ta a tasa duniyar ta talauci da wahala…”
Da sauri Halimah ta toshe masa baki, “In kana so in hakura sai ka janye kalaminka na cewa ka yanke zumunci da ‘yar uwarka. Kai fa ka ce min akwai wutar da Allah ya tanada saboda masu yanke zumunci. Ta kira ni duk abin da ta ga dama, BA ZAN DAINA SONKA BA!!!
Wata irin runguma Hashim ya yi mata, tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanya ta.
“Halimah you are indeed a virtous wife, who her price is far above rubies”. (Zaynab Alkali).
Soyayya nau’i-nau’i ya shiga nuna mata duk da ba ta responding amma ta yi accepting. Har sai da ya tabbatar ya mantar da ita Yaya Rabi’a and her hayaniya. Ya mantar da ita kalmar ‘Farar Kafa’ da ta ke ta yi mata yawo a kwanya. Bai bar komai cikin kwanyar tata ba, sai tunanin ci gaba da rayuwa da shi har zuwa karshen numfashinta.
*****
Lokacin da aka raba gadon Inna, wanda ba komai ba ne kajin gidan gona ne da wasu dabbobinta, kasancewarsa namiji ya samu rabin dabbobin yayin da Rabi’a da Sa’adatu suka samu kaso hamsin cikin dari su biyu.
Sa’adatu ta koma gidan Rabi’ah kafin lokacin bikinta ya cika, amma tana yawan kawowa Halima ziyara. Wani lokacin ma har ta kwana, duk da zagin da Dr. Rabi’a ke mata kan sai ta kwaso wa kanta wata masifar. Gidansu na gado ne, mallakinsu duka ukun don haka suka barshi ba tare da sun sayar ba.
Halima ta zauna ta yi tunani, ta ga cewa za ta iya zama a gidan Inna, ko don ta ci gaba da yin sana’ar Inna su kara samun rufin asiri. Don haka ta bai wa Hashim shawarar su koma Yakasai, gidansu su bayar da shi haya, tunda yana da kyau, kuma yana da yalwa. Sannan yana fitacciyar unguwa kamar Janbulo za su dinga karbar kudin haya mai kauri, su samu Hashim ya sake tada wata kakkarfar sana’ar.
Hashim mamakin Halimah ya hana shi cewa komai. Burin kowacce macen wannan zamani mai tashen kuruciya shi ne ta zauna a gida mai kyau, a fitacciyar unguwa, ta yi tafiya a mota dandasheshiya, yau ga tashi matar na fadin ta zabi ta bar gida mai kyau ta koma cikin gari don ci gabansa. Tabbas Halima halayen ‘yan aljannah gabadaya ta kwashe su. Ba zai gaji da cewa ya daga mata kafa ya kara dagawa, ta shige aljannah cikin aminci ba.
“Ki bar wannan maganar Halimah, yaya zan fidda ki daga gidanki in maida ke gidan gado don amfanin kaina? Ki bari don Allah bana so”.
Halimah ta ce, “Ba amfaninka ba ne kai kadai, amfaninmu ne mu duka. Ka ga har sai ka samu ka koma ka dora PhD dinka a nan B.U.K tunda aiki ya gagara, watarana kwalin zai yi mana amfani. Don Allah Cherie kada ka ce min a’ah, ina so in na koma Yakasai ni kuma in ci gaba da poultry din Inna”.
Kwana bakwai suna takun saka, ta dage a kan bakanta, shi ma ya dage ba zai yi mata haka ba, in ya yi hakan ya kware ta. Har sai da Halima ta fiddo masa bacin ranta karara sannan ya amince bisa sharadin idan sun tara kudin da zai ishe shi gama PhD za su tashi su koma gidansu.
Ai kuwa da kudi masu gwabi aka karbi hayar gidansu, kasancewar ana iya biyan kudin karatun in parts, babu jimawa ya nemi admission sabida kyawun takardunsa B.U.K suka dauke shi da sauri, inda zai yi digirinsa na uku a kan fanninsa na Telecommunication Engineering. Bai kuma fasa zuwa Janbulo yi wa yaran mai kudin nan lesson ba, sannan ga Halima a gida tana sayar da kwai cret-cret da kajin gidan gona wa tsofaffin customers din Inna, tana da yaro da yake kula da su ya kuma kwaso kwai kullum da safe. Gadon na Hashim ne shi kadai don Rab’a da Sa’adatu sun hada nasu wuri guda suna nasu kiwon a gidan Dr. Rabi’a, don haka a wannan shekarun asirinsu ya rufu. Hashim na ci gaba da karatunsa, ya sayi tsohuwar laptop don research work, kullum da dare Halima na taimaka masa da rubutu da karin idea, duk rabin research work din Halima ce ta yi masa.
Rana daya aka wayi gari da annobar mutuwar kajin gidan gona a Najeriya (chicken flu), kaji suka yi ta zazzabi suna mutuwa. Kafin dan lokaci na Hashim da Halimah ma babu su, domin gwamnati ta hana cinsu suna ji suna gani kajinsu suka yi ta faduwa suna mutuwa. A lokacin Halimah na dauke da ciki wata biyar. Sa’adatu kuwa ‘ya’yanta biyu.
Rushewar sana’ar poultry dinsu ba karamin shafar tattalin arzikinsu ya yi ba.
A baya Hashim bai san kudin cefane ba, awo kawai ya ke yi, duk wasu kananan bukatunsu Halimah cira kawai ta ke yi ta yi. Yanzu kuwa sai ya je ya yi buga-buga ya nemo, kudin haya shi ne kawai madogararsu, sai Ubangiji mahaliccinsu wanda ba ya barci.
Kafin watanni biyar kudin hayar da suka karba yake karewa a bukatun yau da kullum da na karatun Hashim, cikin mawuyacin hali suke kai wa karshen shekara har Allah ya taimake su Hashim ya kammala phD cikin shekaru uku cif! Babu jinkiri, sabida yadda suka taru suka maida hankali shi da Halimah suka kammala research work din cikin lokacin da jami’a ta bukata.
Halimah ta daga kwalin PhD din Hashim farin ciki fal ranta, ta ce,
“Ina ma ni ce?”
Duk sai ta bai wa Hashim tausayi, ya rungumo ta ya sumbaci goshinta, ya ce, “My achievement is yours sweetheart, kuma alkawari ne na dauka insha Allah watarana sai kin kammala PhD dinki”.
Halimah ta ce, “Kayya! Ta ina hakan zai yiwu alhalin ba ni da shaidar kammala ko sakandire a hannuna? Ga shekaruna sun tura zan fara hidimar iyali. Kamar yadda ka ce din ne your achievement is mine, to a barshi a hakan”.
Hashim tausayin Halima ya lullube shi. A take wani tunani ya zo masa, ya ce, “Halima ko in kai ki ki ga Daddy ne? Just greetings, mahaifi ne in ya bar ku bai kamata ku ku barshi ba, binsa za ku yi ta yi da neman gafara har sai ya huce”.
Halima ta girgiza kai da sauri, “Cewa zai yi wani abu na je nema a wajensa, ko wahala ce ta ishe ni na dawo masa. Ni kam alhamdulillahi I’m contented with my life as such. Damuwa ta daya ce rashin sanin halin da Hanan ke ciki. Haka kawai Hanan ba za ta manta da ni ba”.
Hashim ya ce “Kowacce fassara zai yi mana ki ba shi hakkinsa na haihuwa ki je. Allah shi ne shaida ba mu je don neman komai ba, sai don sauke hakkin da ya rataya a kanmu. Na hakkin haihuwa, wanda da shi zai yi hisabi ranar gobe kiyama. It’s almost four years rabon ki da mahaifin ki, ya kamata mu je din don wani lokacin na kan yi tunanin har da rashin albarkarsa cikin auren mu cikin abin da ke kara mana matsaloli a rayuwa”.
Halimah ta daga kai a hankali ta dube shi, ya gyada mata kai cikin karfafa zancensa, “Yes, rashin albarkar iyaye a cikin aure na hana ci gaban rayuwa. Kuma yana kwashe albarka, yana hana kwanciyar hankali, yana jawo rashin nasara a rayuwa…".
Hawaye ya fito daga idon Halima, ta ce, “Idan kuma ya ce mun zo neman aiki ne fa?”
“Whatever he will say”. In ji Hashim, “Ki tafi da kyakkyawar niyya, ki sa a ranki gafararsa kawai ki ka je nema”.
Halima ta kwantar da kai a kafadun Hashim ba ta ce komai ba, amma yanayinta ya nuna amincewa.
****
Allah kadai ya san irin fafutukar da Hashim ya yi tsawon sati guda kafin ya tara musu kudin motar zuwa Abuja. Lokacin da Halimah ta zo hada kaya kala biyu da za ta tafi da su, rasa wanne za ta dauka ta yi, duk sun mutu sun kode, amma dai wankakku ne, sun yi mugun jin jiki dai, don rabon da ta dinka suttura shekaru uku ke nan da suke cikin sukunin cinikin kaji da ta dinka wasu atamfofi (chiganvy) guda biyu da sallah, sauran kayanta tun na ‘yammatancinta ne.
Da a ce Halima ta san yadda ta koma a fuska, sai ta fi damuwa fiye da damuwar rashin kyakkyawar suttura.
Tun asubah suka bar gida zuwa tashar Na’ibawa, inda suka hau motar haya zuwa Abuja.
Wajejen azahar suka shiga Jabi Motor park, daga nan suka samu taxi suka nufi Asokoro.
Halima ta daga kai tana kallon garin da ta yi dabdalar kuruciyarta, komai ya sake mata cikin shekaru hudu. An samu ci gaba sosai a birnin tarayyar Nigeria. Kirjinta ban da balli-balli ba abinda yake yi. Lokacin da mai taxi ya yi parking kofar katafaren gidansu ji ta yi zuciyarta kamar za ta tsago allon kirjinta ta fito.
Mai taxi ya sauke su, Hashim ya kirgo kudinsa ya ba shi. Halima na barin kafadunsa na dama suke tafiya zuwa entrance na gidan. Hashim ya kwankwasa kofan, maigadin gidan wanda tsohon soja ne ya zo ya bude.
Kallon sama da kasa ya yi musu, ko kadan bai gane Halimah ba. Sakamakon shekaru biyar sun karu a kan ainahin ashirin da hudun ta, kodaddun sutturun jikinsu ya fara kallo, they look shabby, ba irin mutanen Prof. Bane, don haka a wulakance ya ce,
“Me ku ke nema a nan?”
Halimah ta yi murmushi, ta ce, “Seun, ba ka gane ni ba?”
Kokarin rufe kofarsa ya fara yi don ba shi da lokacin irin su.
Halima idonta cike taf da hawaye ta ce, “ABCDEFG…H for Halimah, H for Hanan…” Karatun da Seun, yake koya musu suna yara idan Daddy ya fita.
Seun ya zaro ido ya ce, “Halimah ke ne?”
Hawayen da suka cika idonta suka karasa gangarowa. Da sauri ya bude musu kofa yana fadin, “Oh my dear! My daughter Halima… where have you been?”
Ba ta ba shi amsa ba ta tambaye shi Daddy na nan?
Ya ce, “Ku shigo maza bai dade da shigowa ba, kuma yanzu zai fito ya tafi U.S”.
Kofofin shiga gidan duka a bude suke, don haka suka sa kai cikin dari-dari. Kai tsaye Halima falon da ta san Daddy ya fi zama ta kankame hannun Hashim suka shiga.
Ilai kuwa a nan suka same shi ya barbaza takardu a gabansa da farin gilashin kara karfin gani a idanunsa. Babu wani canji da Halima ta gani a tare da shi, yana nan a kyakkyawan bafillacensa, gani ma ta yi kamar an kara masa kuruciya, ko dayake an ce mai kudi ba ya tsufa.
Su biyu suka yi sallama, ba tare da sun jira ya amsa musu ba suka sanya kai, suka nemi can gefe suka zauna manne da juna.
Prof. ya cire gilashin idonsa don gani ya yi kamar yana ba shi false vision; ko ta zama tsohuwa ‘yar shekaru tamanin ba zai kasa gane ta ba. Tunda kuwa a kan hannunsa aka haife ta, ya kuma raini abarsa da kansa.
Kasa cewa komai ya yi sai kallonsu yake ita da Hashim din, Halimah ta rarrafo daga inda ta zauna ta zo ta zube a gabansa tana kuka.
“Daddy na zo neman afuwarka da albarkarka. Ka yafe mini, ka sa min albarka’.
Prof. ya yi wani murmushin keta. Ya dube ta a wulakance tare da cikin da ke manne da ita, ya ce, ‘Har kin dawo haka so soon? Ai kin zo da wuri, har wahalar ta ishe ki ne, ko kuwa talaucin ya ishe ki? Ko wanda ki ka zaba a kaina din ya sake ki kamar na ‘yar uwarki sabida rashin dangi?”
Makogaron Halimah ya bushe rayas! Yawun bakinta ya kafe. An saki Hanan? Wannan last sentence shi ya fi tsaya mata a rai ba surutun Daddy na wulakanci ba. A hankali ta girgiza kai, hawaye na sauka daga idanunta, ta ce,
“Babu ko daya Daddy, I’m here just to ask for forgiveness and your blessing”.
'‘Har abada ba za ki samu ba!” Daddy ya fada in exclamation. Ya dora da cewa, “Har sai ranar da wuya ta ishe ki kika dawo gidanku, dawowa ta gabadaya, bana hada jini da talaka, kuma ba zan taba ba insha Allahu… kai kuma… (ya nuna Hashim da dan’alinsa), ka yi ta zama unemployed kenan muddin ba ka dawo min da ‘yata ba, ka sake ta ko nawa ka ke so zan ba ka ka auri wata you can marry thausands of Halima not my daughter, zan kuma samar maka aiki mai babban matsayi a babban bankin Najeriya CBN. In kuma ka ki, to ku tattara ku tafi, kada ku sake tako min nan. Duk ranar da ku ka sake shigo min gida, kai ba da takardar saki ba, ita ba da nadamar yin aure ta bar ni ba, sai na sa karnuka sun yagalgala minku. Ku tashi ku ba ni wuri tun muna iya shaida juna ni da ku”.
Hashim ya tada Halimah wadda ke ta gunza kuka suka mike. Daddy ya kira waya, ga dukkan alamu da maigadinsa Seun yake magana.
“Idan ka bari suka sake shigo min gida, a bakin aikinka”.
Suna kokarin fita daga falon Halima na waiwayensa, Daddy ya ce,
“Kada Allah ya sa ki haifo abin da ke cikin ki lafiya”.
Wannan magana ta fi kowacce kona ran Hashim. Da sauri ya juya ya ce, “Allah na kowa ne”.
Ya so ya gaggaya masa raddi a kan maganganun da ya yi musu, ya tuna cewa; Baban Halimah ne, ba zai taba iya cin mutuncin wani da ya shafe ta ba balle iyayen da suka haife ta.
Da sauri ya ja Halimah suka tafi, a bakin get Seun ya faki ido ya jefar da wata farar takarda a gabansu. Halimah ta sunkuya ta dauka, lambar waya ce a jiki, a kasa ya rubuta ‘HANAN’.
Kallon godiya ta yi wa Seun, don ta san Daddy na kallonsu ta CCTV dinsa.
*****
BABI NA GOMA SHA DAYA
Tunda suka dawo daga Abuja wanda a tashar mota suka kwana ranar, ba ci ba sha don iyakacin kudin mota ne a aljihun Hashim. Halimah ta kwanta rashin lafiya. A karan-kanta ba ta san ciwon me ta ke ba, tana dai kwance ne kawai ba ta umh ba ta mh-umh. Amma ta san tana jin wani iri zafi a zuciyarta. Ya yi-yayi su je asibiti Halimah ta qi, don ya karbi albashin lesson din yara, ta ce, maimakon ya kashe kudin a asibiti ya je ya sayo mata ‘yan rigunan jarirai da su. Ta ba shi list din da aka ba ta na abubuwan bukatar haihuwa a Antinatal ta ce ya sayo ko rabinsu ne, diaper da shawul da rigar sanyi saiti guda biyu.
Ya ce, kudin duka dubu goma ne, kuma ba su da abinci a gidan. Halimah ta ce, bakin da Allah ya tsaga ba ya hana shi abin da zai ci.
Don haka ya tafi kasuwar Kofar Wambai da tambaya ya samu shagon kayan haihuwa masu arha ya sayo fiye da rabin list din.
Kamar yadda Halima ta ce, bakin da Allah ya tsaga ba ya hana shi abin da zai ci, hakan ce ta faru. A daren ranar sai ga Sa’adatu da mijinta Lawan sun kawo musu ziyara. Kallo daya Sa’adatu ta yi musu ta tabbatar yunwa suke ji, jikin Halimah har rawa yake yi, amma sabida karfin hali irin nata sai fara’a ta ke tana daga kwance.
Mijin Sa’adatu shi ma ba wani karfi gare shi ba, amma dai za a ce ya fi Hashim tunda ba su rasa abin da za su ci ba don yana hadawa da aikin kafinta, ko yanzu a bayan Vespa dinsa ya goyo ta.
Sa’adatu juyawa ta yi tana share hawaye, ta san duk rashin Inna ne, duk runtsi Inna ba za ta bar nata ya tozarta haka ba. Hashim ya dade da yanke alaka da Dr. Rabi’a da ma ita ce mai taimaka masa, amma tun rasuwar Inna da suka yi baram-baram a kan Halimah ba ta sake ba shi komai ba. Ta ce ya je ya karata da mai farar kafarsa tunda ya zabe ta a kanta. Shi ma kuma ko da wasa ko hanyar gidanta bai kara bi ba.
Sa’adatu ta dauko mayafin Halimah ta mikar da ita zaune ta yafa mata, ta ce lallai-lallai asibiti za ta kai ta da kanta tunda ba ta san muhimmancin lafiyarta ba, shi kuma Hashim din ya biye mata sabida ba ya son takura mata, duba da halin da zuciyarta ke ciki tun dawowarsu daga Abuja.
Asibitin Malam ta kai ta, ai kuwa nan da nan aka rike ta aka ba ta gado, don sun ce she is 60% dehydrated (ruwan jikinta ya kone kashi sittin cikin dari), sannan ulcer ta kama ta, ga rashin wadatar jini. Duk abin da aka caza Sa’adatu ta ce mijinta ya ranta mata za ta biya shi karshen wata in ta dauki dashinta.
A wannan ranar Hashim gefe ya koma yana kuka, yana jin kansa useless, yana jin kwalayen ilminsa useless, tunda duk a sanadin babunsa Halima ta shiga wannan hali, Haliman da ya daukar wa alkawarin mayarwa tauraruwa a cikin mata. Ya yi kudurin yi mata kyakkyawar sakayya a kan sacrifice (sadaukarwa)rta gare shi. Ga shi bai samu damar cika ko daya cikin alwashin da ya dauka ba. Bai taba tsammanin rayuwa za ta yi musu juyin waina kamar wannan ba.
A lokacin da Prof. ya sallame su ya yi zaton kwalayen ilminsa ba za su barshi ya tozarta ba.
Ga shi dukkan mafarkansa ba su taba zama reality ba.
Ga Haliman kwance rai kwakwai-mutu-kwakwai, ko nauyin asibitinta ya kasa dauka.
Tafiya ya kama yi a gefen titi, bai san inda yake jefa kafarsa ba. Ya san dai zuwa zai yi ya tashi ‘yan hayar gidansa ya sa gidan a kasuwa don ya kula da Halimah da abin da za ta haifa, ya ja jari da wani abun cikin kudin, ya sayi ragon suna ya ajiye don abu na karshe da ba zai taba yarda ya faru ba a rayuwarsa, shi ne Halimah ta haihu bai yanka wa dansa ragon suna ba.
Lokacin da ya ba wa maigidan notice din su tashi, cewa ya yi ai kudin shekara suka biya, kuma yanzu watanni biyar ke nan, sai dai in ya maido musu rabin kudinsu ko ya bari zuwa karshen shekara su tashi.
Hashim kamar ya yi hauka, ya ce su tashi ya sayar da gidan, zai cira a ciki ya ba su.
Dillalin gidaje na unguwar Janbulo ganin yadda Hashim ya ke a uzurce da son saida gidan da gaggawa lokacin da ya je ya same shi, sai ya yi wa gidan tayin wulakanci, kashi talatin cikin dari na kudinsa na zahiri. Without a second thought Hashim ya ce ya sayar da gidan da ya zubar da guminsa da lokacinsa ya mallaka a kudade naira miliyan biyu kacal.
Makotan Hashim sune shaidun sa, suka sa hannu shima yasa, cinikin gida ya tabbata, gidan Janbulo ya tashi daga mallakar Hashim.
Hannu da hannu suka ba shi kudinsa, don Hashim ko account ba shi da shi yanzu, banki sun rufe shi, jimawa da ya yi ba ya amfani da shi.
Ya zubo kudinsa a babbar leda ya yana tafiya da sassarfa a gefen titi cike da farin ciki yana kiyasi, kiyasin abubuwan da zai saya wa Halimah da babynsu; Katon ragon sunan da zai saya; dandasheshen leshin da zai saya mata ta daura ranar suna; da kiwonta da zai dawo mata da shi ta yi ta cin kwai da nama ta samu jini a jikinta ta maida wannan komadar. Da shagon kayan masurufin da zai sake bude…....... sai ji ya yi da mugun karfi an warce ledar hannunsa, daya ya cilla wa daya sun haye lifan sun bace a titin kamar kiftawar ido.
Saboda gigicewa Hashim takawa ya yi da gudu iya karfinsa a kan titi ko zai cimma wadan nan marasa imani, amma yana hawa tsakiyar kwalta ya ji an yi sama da shi an wulwula shi, sannan ya fado tim! Tsakiyar titi jina-jina.
Duk da muguwar buguwar da ya yi ta ko’ina, amma bai fita a hayyacinsa ba, fadi yake, “Matata tana asibiti, don Allah ku taimake ni ku kai ni Aminu Kano”.
Wanda ya buge shi din ya ce, “Kai ma ai asibitin ka ke bukata, na yi zaton ba ka da hankali da ka hawo tsakiyar motoci kana gudu, ashe da hankalinka, tunda har kana sane da matarka da ke asibiti”.
Suka kakkama shi suka sanya shi a motar mutumin suka nufi Aminu Kano da shi.
A A&E aka karbe shi inda suka yi masa treating ciwuwwukan da ya ji, suka yi masa dorin karaya a kafa, wanda ya kade shi duk shi ya biya komai. Har ya gaji da surutun Hashim a kan matarsa da ke asibiti rai a hannun Allah, ya taimaka masa ya kai shi wajenta.
Da zai tafi ne ya ji tausayin Hashim ya kama shi, da ma har yanzu akwai mazan da ke son matansu haka cikin al’ummar Hausawa? Ya ce da shi,
“Gaya min dakin da matar taka ta ke, in je in gaya musu, ni zan wuce gida, ka yi hakuri ba ni da laifi domin kuwa gabana ka sha ina kwarara gudu”.
Hashim ya gaya msa tana gynae emergency ya tambayi nurses din Halimah Zubair da aka kawo dazu, tunda suna da sunan kowace patient tare da su, tana tare da kanwarta Sa’adatu da mijinta Lawal
Ba jimawa sai ga mutumin tare da Lawal da Sa’adatu hankali tashe. Sa’adatu ta fashe da kuka ganin mummunan yanayin da yake ciki, har da karaya. Lawal yana ta tambayarsa garin ya ya? Ya kau da kai ya labarta musu komai har mutumin da ya kade shi yana jin su.
Sa’adatu ta ce, “Yaya me ya kai ka? Wa ya aike ka ka sayar da kadarar da ta rage maka? Ka ke samun sanyi daga karkashinta?”
“Kaddara Sa’adatu, kaddara!” Ya fada yana lumshe idonsa.
“Ya ya jikin Halimah? Ta ci abinci?”
Lawal ya gaya masa tun kawo ta barci ta ke yi, amma an sa mata ruwa da jini, kuma likitoci na ta kokari a kanta. Sun ce babyn ma ba ya motsi yadda ya kamata sabida ba ta cin abinci.
Hawaye suka zubo daga idon Hashim, ya ce,
“Sa’adatu ba ni da sa’a a rayuwa ta!”.
Ta kama hannunsa ta rike cikin nata, “Kada ka ce haka Yaya, ka ce, alhamdulillah cikin kowanne hali, domin kuwa ka fi dubu. Ni zan je gida yanzu in samo muku abin da za ku ci, na yi waya da Yaya Rabi’a ta ce tana zuwa yanzu”.
Bai ce komai ba, ya maida idanunsa ya runtse. Mutumin ya fice ba tare da sun lura da shi ba. Sa’adatu da Lawal ma suka fita, shi Lawal sallah zai yi ya dawo, ita kuma adaidaita ta hau zuwa unguwarsu Dorayi.
Ba ta fi awanni biyu ba ta dawo da filas din shayi da na abinci, ta yi musu tuwon dawa miyar busasshiyar kubewa, Lawal ya zuba masa, ita kuma ta dau na Halima ta tafi.
Kwanansu biyar ke nan suna jinyar Hashim da Halimah. Halimah ta fara jin karfin jikinta, da ta tambayi Hashim, Sa’adatu ta gaya mata komai.
Halimah ta wani irin lumshe idonta..… gidan da ya rage musu ma ya sayar, barayi sun kwace kudin, mota ta buge shi...… duk a dalilinta. Ko dai gaskiya Yaya Rabi’a ta fada, farar kafar ce da ita?
Yaya Rabi’a tun zuwanta na farko da Sa’adatu ta gaya mata duk abin da ya faru, takaici bai barta ta kara dawowa ba. Ko duba Halimah ba ta shiga ba, sai abinci ta ke aiko musu kullum sau uku a rana, don haka Sa’adatu ta huta komawa gida yin girki.
An riga sallamar Halimah bayan likitoci sun tabbatar da koshin lafiyarta da ta abin da ke cikinta. An dade da maida Hashim male ward bangaren wadanda aka yi wa aikin kashi. Ana i-gobe za a sallame shi mutumin da ya kade shi ya zo don su yi sallama ta karshe.
Bayan sun gaisa ya ce da shi, “Sunana Alhaji Aminu Kwangila, ni dan Kano ne gaba da baya, sana’ata ita ce kwangila. Na tausaya maka kan abin da ya same ka, Allah ya yi maka sakayyah ta alkhairi.
Ga wannan na ba ka kyauta fisabilillahi, amma ka tabbata ka je banki ka bude account ka zuba su a ciki. Yanzu Najeriya ba irin ta baya ba ce, ba tsaro ba gaskiya, babu tausayi a zukatan bata-gari. Kada ka kara yawo da kudi masu kauri a jikin ka’.
Ya ajiye masa cheque na kudi na gugar wuri har naira miliyan uku. Hashim ya kasa gasgata abin da yake gani, don haka he is speechless, wordless, motionless har sai da ya ji Alhaji Aminu yana yi masa sallama zai wuce, ya sauko daga gadon ya ba shi hannu idanunsa taf! Hawaye,
“Allah ya yi maka sakayya da mafificin alherinSa”.
“Ameen kanina, Allah ya ba ka lafiya”.
Daga haka ya fice, sallamarsu da Alhaji Aminu kenan.
Washegari aka sallame shi, bai zarce ko ina ba daga asibiti sai bankin Zenith, ya bude account ya karbi kudinsa ya alkinta su. Aka ba shi ATM card, ya ciri wasu masu dama ya nufo gida.
Halima zaune ita da zungureren cikinta, daga ita har jaririnta kugi cikinsu yake yi, rabonta da abinci tun kokon safe da makwabciyarsu ke sayarwa da ta sayi na naira talatin ta sha. Jiran dawowar Hashim ta ke yi don yau za a sallame shi, ba ta da kudin mota da ta je sun taho tare.
Kafafunta mike kan yagalgalalliyar kujerar falon ta tun ta aure. Ta tsufa, yadin ya faffarke ta burma ciki. Tunani ta ke kafin ta haihu za ta kwashe su ta sayar wa Lawan da yake kafinta ne inyaso ko riga ce ta saya wa babynta da kudin.
Hashim ya shigo da sallama, hannunsa rike da ledoji manya-manya, rabon da ta ji muryar Hashim da wannan karsashin ba za ta iya tunawa ba. A hankali ya zauna saboda kafarsa ba duka ta warke ba. Wani kasalallen murmushi ya kashe Halimah da shi.
“Sannu da gida Maman Innata”.
Murmushi ta yi masa, “Sannu da dawowa, ya ya jikin?”
“Alhamdu lillah, kafa ta yi kyau, sai dai a can ciki ina jin ciwo sosai”.
Ledar farko ya janyo ya bude ya fiddo kwalin danyar madarar oldenburger sai rabar sanyi ke fita a jikinta. Yawun Halimah ya yi bala’in tsinkewa.
“Yaushe rabon duniya da ayyaraye!?”
Halima ta ce a zuciyarta kafin ta gama hadiye miyau, Hashim ya fiddo wata zazzafar gasassar kaza gashin Yahuza Suya, an yayyanka ta an zuba mata vegetables yankakku a kanta.
Tura su ya yi duka gaban Halimah.
“Ci ki koshi Sweetheart”.
Abinki da mai tsohon ciki, tana aika madarar nan a cikinta dan cikinta wani irin juyi ya hau yi, tabbacin bai taba cin abu mai dadin wannan ba. Saboda dokantuwa da cin naman ba ta samu zarafin yi wa Hashim tambayoyi ba sai da ta ci ta koshi, a lokacin shi kuma Hashim ya tafi don ya yi wanka.
Da ta bude sauran ledodin hawayen dadi ne suka zubo mata, shawul din daukar jariri guda uku, kayan sanyi saiti uku, dirkekiyar diaper da kayan baby (overall) wajen kala ashirin. Ga wani tsadadden leshi ruwan zuma mai duwatsu da ratsin choculate colour, atamfa Holland, Super da shadda, mayafai da suka shiga da kayan da takalma da jaka (flat) samfurin vincci
Hashim ya fito ya taddata tana duba kayan, da suka hada ido tambayoyi da tuhuma ne fal idanunta. Murmushi ya yi ya wuce yana saka kaya. Sai da ya shirya ya yi fresh abinsa, sannan ya zauna ya fayyace mata komai.
Farin ciki ya nuna a kan fuskarta, amma sai ta ce, “This is too much Cherie. Ya ba ka ne don ka yi wani muhimmin abun da su. Bai kamata mu yi bushasha ba, kada ka manta ba mu da sauran kadara yanzu”.
“Na sani Sweetheart, amma ban ga amfanin arzikin da ba za ki ci shi ba. Bai fi 150k na kashe ba, na kuma ware na ragon suna. Sa’adatu zan saya mata firji ta fara sana’a, ke ma haka in kina so, sannan poultry dinki zan mayar miki. Duka-duka za a kashe atleast 500k, saura 2m+ mu yi shawarar geniune business din da za mu yi”.
Halimah ta yi dan tunani, ta ce, “Duniyar bakidaya yanzu ta information technology ce. Ina ganin ka kama babban shago a bakin titi a yi business center and internet café, a kuma dinga sayar da assessories na waya a shagon, a sayi injin photocopy da duk abin da ya shafi computer na tabbata zai samu karbuwa. Ga ka guru a kan computer”.
Murmushi ya yi ya kwanto da barin jikinta a jikin sa.
“My wife is forever clever. She always thinks rationally. Wannan shawara ce mai kyau, kuma da ita zan yi amfani insha Allah”.
*****
Kafin Halimah ta shiga EDD dinta duk abin da suka shawarta ya kammala. Tare suka zauna suka tsara komai suka lissafa. Kyakkyawan business center and internet café ya kammala a kan titin tsohuwar jami’ar Bayero.
Yanzu sun maida hankalinsu ne kan jiran haihuwar Halimah.
Sa’adatu ta yi matukar murna da katoton freezer dinta, iri daya da na Halimah, ga kajinta sun dawo. Rayuwa ta fara yi musu gardi.
Hashim kullum ya tafi shago hankalinsa yana kan Halimah, don haka ya saya musu sababbin kananan wayoyi shi da ita. Akai-akai yake kiranta yana jin halin da ta ke ciki, sannan karfe biyar ya rufe shago ya dawo gida.
Sai yanzu da ta yi waya, ya tuno da lambar wayar Hanan da Seun ya taba bata, ta yi mata kyakkyawan boyo a cikin filonta.
Yau da Hashim ya fita ne ta tuno da lambar. Ta taka tinkis-tinkis da zungureren cikinta ta dauko takardar. Bugun farko layin ya shiga, amma har ta tsinke ba a daga ba. Haka ta yi ta gwadawa har Allah ya taimake ta mai wayar ta daga.
“Hello”. Hanan ta fada da muryar gayunta da ba ta taba canzawa.
Halimah ta lumshe idonta, wani irin farin ciki ya ratsa ta. For the first time da ta ji muryar Hanan bayan rabuwarsu shekaru kusan biyar.
“Sunana Halimah Zubair Numan”.
Hanan a kwance ta ke, ba ta san lokacin da ta mike tsaye ba. Ta kankame wayar hannunta. Da karfi ta ce, “Sis LEEMAH! Ke ce?
Where have you been all these while sis Leemah?
Ki ka bar ‘yar uwarki cikin wahala da qaqa-ni-kayi da rayuwar kaico! Babu kowa a tare da ita”.
“Ke ce ki ka bar ni Hanan, bayan tafiyarki PortHercourt ba ki kara kirana ba. Ni in na kira ba ta shiga. Muka zo muka bar Abuja zuwa Kano, tun daga nan life was not as it was before, things have changed abruptly. So many bitter experiences… months back, I came to Abuja just to reconcile with Daddy…
A karshe ya kore ni Hanan, ya kuma bini da muguwar addu'a. Seun, ya ba ni lambarki. I’m about to become a mother now Hanan, how was life there with you? Domin na ji wani abu mara dadi a bakin Daddy… concerning you!”
Tunda ta fara bayani ko sau daya ba ta tsaya ta sha numfashi ba don tsoron kada Hanan ta sake kubuce mata. Hawaye sai ambaliya suke a fuskarta.
“Salim ya sake ni Sis”.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. In ji Halimah.
Hanan ta kankame wayar hannunta sosai don kada Halimah ta kara kubuce mata. A gurguje ta shiga ba ta labari.
“Bayan mun rabu, PortHearcourt muka koma, zamana da Salim zama ne na soyayya zallah. Yana sona, yana kula da ni shekara biyu babu haihuwa, sai bari (miscarriage) da nake ta yi. Daddy bai taba nemana ba ko sau daya, danginsa ko na Mama ban san inda zan gansu ba.
Aka zo aka yi ma Dad din Salim sarauta muka dawo Arewa, nan Maman Salim ta ce sai dai ya bar ni wajensu ya koma shi kadai in ya so ya dinga zuwa duk karshen wata.
A wannan zaman da na yi tare da su ne suka gane komai da ya shafe ni, ba ni da dangi, ubana ya sallama ni. As a royal family as they are… wannan abun kunya ne a gare su, su hada iri da ni, jikokinsu za su tashi babu dangin uwa, wanda su kuma hakan abin kunya ne a gidan sarautarsu. Suka yi wa Salim umarni ya sake ni, suka aura masa mai asali da gatan iyaye.
An raini family dinsu da bin umarnin na gaba, don haka Salim ya rufe ido ya ba ni takardar saki har guda biyu.
Ba irin neman da ban yi miki a Abuja ba, har gidan da ku ka zauna na bincika na je, na tadda wasu a gidan suka ce kun dade da tashi, basu san inda ku ka koma ba, za ki ce waya, bayan mun koma PortHearcourt na canza layi to get rid of my boy friends don kare darajar aurena, na manta cewa lambarki na ciki, kuma na yi destroying layin.
Dole kan ba yadda zan yi na dawo gida kamar yadda ya kore ki ni ma korata ya yi, amma ban yarda na tafi ba, a wajen ajiye motoci nake shimfida dankwalina na kwanta, har tsayin kwana uku, duk yana kallona ta CCTV.
A rana ta hudu ne ban sani ba ko tausayina ya ji, sakamakon ruwan sama mai thunder daya kare a kaina, ya sa Seun ya kirawo ni, ya tambaye ni me ya dawo da ni? Na gaya masa komai.
Ya ce, "Yanzu kin yarda wannan shi ne abin da nake gudar muku… wulakanci da tozarcin maza? A raina na ce, kai ka jawo aka wulakanta nin ai, tunda kai ka maida ni mara gata don kawai na zabi AURE...sunar Anabi SAW......to such an extent that kowa zai iya taka ni. Da ka kare min alfarmata ta uba babu wanda zai wulakanta ni’.
Ya ce bisa sharadi uku za ki zauna tare da ni, in kin amince to, in ba ki amince ba ki manta kin taba sanina a rayuwarki.
-Ba za ki kara yin aure ba.
-Ba za ki yi alaka da Haleemah ba.
-Za ki koma karatu ki karo masters dinki ki dawo ki koma aikinki a NCC.
Duk na amince, as I have no alternative. Na koma Mexico tsayin shekara guda na hado masters dina na dawo. Ya dora ni a kan kujerar ki”.
Hanan ta dan yi shiru, sannan ta ci gaba.
“Sai ga Salim ya dawo yana so ya maida ni dakina mu zauna a PortHearcourt ba da sanin iyayensa ba. Na gaya miki muna son juna ni da Salim, iyaye ne suka raba mu ta karfin gaske. Na duba na ga babu mafita, komen nawa ba zai yiwu ba ba tare da Daddy ya sani ba, kuma ba tare da ya sake kora ta ba. Ga shi ina son Salim, so mai tsanani ba dan kadan ba.
I’m sorry sis Leemah, because I know I disappoint you, and I’m going to break your heart, sai muka ga tunda aure ya gagara bari muci gaba da rayuwarmu out of wedlock. Kullum Daddy ya fita, ko ya yi tafiya to ni da Salim muna tare a hotels. Zancen nan da nake miki ciki ne a jikina na wata biyar, mun yi mun yi ya fita ya qi. Idan na haife cikin nan this will tarnish the image of their royal house, abin kunyar da ya fi musu rashin asali na da rashin mahaifana. Shi kuma Daddy zai yi rainon dan shege a gidansa, tunda ya ki karbar na sunnah…”.
Hanan ta karasa cikin matsanancin kuka.
Halimah ta ce, “Hasbunallahu wani’imal wakeel”.
Bayan wannan ta kasa cewa komai, sai sauraron kukan Hanan mai keta zuciya. Daga baya bayan ambaton sunayen Allah da ta ke ta yi ta samu kwarin gwiwar cewa Hanan.
“Kada ki kara kokarin zubar da cikin wata biyar, you wll lose your precious life for nothing (za ki yi asarar rayuwaki a banza). Idan sun ki karbar dan, ni ki ba ni zan hada da nawa in rike mana Hanan. Ki barsu su girbi abin da suka shuka. Lallai tsakanin iyaye da ‘ya’ya ma akwai hisabi. Wata shari’ar sai a lahira”.
Tun daga ranar kullum sai daya ta kira daya, ta ji halin da ‘yar uwarta ke ciki. Hatta motsin jariran da ke kwance karkashin mararsu sai sun gaya wa juna. Rannan Hanan ta ce ta tura mata account number dinta za ta turo mata kudi ta yi sayayyar haihuwa.
Halimah ta girgiza kai, “Na haramta wa kaina kudin jikin Daddy har abada! Daga ranar da yace "kada Allah yasa na haihu lafiya". Kada ki damu, ba abin da Cherie bai saya mana ba, imagine har dinkin fitar suna ya karbo duk da ya ce ba taro za mu yi ba”.
Hanan ta ce, “Amma ai gumina ne, tuda aiki nake suna biyana”.
Halimah ta ce, “Ki bar zancen nan don Allah. Ba zan karbi kudin NCC ba ko da zan yi yawo tsirara”.
A daren ranar nakuda ta kama Halimah, ta kwana cikin gumurzu, sai da gari ya waye suka wuce asibiti. Tana shiga labour room ta sunkuto kyakkyawar ‘yarta mai tsananin kama da ita. Just as Hashim dreamt of (kamar yadda Hashim yake mafarki).
Duk addu’o’in da suka kamata Hashim ya yi wa ‘yarsa. Ya daga rigarta wajen al'aurarta ya karanta mata (Wa Maryama ibnat Imranallaty ahsanat farjaha fanafakhna fihi min ruhi na wa sadaqat bi kalimati rabbiha wa kutubihi wa kanat minal qaaniteen). Da Halimah ta dawo hayyacinta ya dauko ‘yar ya dora mata a kan ruwan cikinta.
Tana murmushi ta yunkura ta rike babyn sosai a kirjinta. Sannan ta sa ta a gaba da kallo. Har cute face irin tata. Amma hatta yatsun hannunta da na kafa irin na Hashim ne. Ta sumbaci ‘yar, Hashim kuma ya sumbace su tare, ya saita wayarsa ya yi musu hoto su ukun.
“Don Allah ka tura wa Hanan”.
Halimah ta fada wa Hashim.
“Cherie you know she don’t like me (kin san ba ta shiri da ni) ta ya ya zan tura mata hoton ‘ya ta?)”
Halimah ta yi murmushi, “Hanan din da ka sani a baya ba ita ce yanzu ba, she is now a changed person. Har cewa ta ke na gaishe ka.
Ta karanto masa lambar Hanan ya yi saving ya tura mata hoton.
Sai ga wayar Hanan nan da nan ta wayar Hashim.
Hashim ya mika wa Halimah, muryarta a hankali ta ke fita, ta ce, “Hanan kin ga ‘yarki ko? Labour akwai wahala, Allah ya jikan Mamanmu, ya haskaka kabarinta”.
“Ban taba ganin abin da ya shiga raina, nake so irin jaririyar mu ba”.
Hanan ta fada da murmushi mai sauti.
“Dole Aunty ta zo ganin diyarta. In na zo Kano wace unguwa zan ce a kai ni?”
Halimah ta zaro ido, “kada ki yi abin da zai ja miki matsala da Daddy, besides bai kamata ki kamo hanya ba a cikin condition din da ki ke ba, Allah ya gani cikinki ba na halal ba ne, ba kuma murna nake da faruwar hakan ba, amma so nake ki haife shi lafiya. Domin ya zamo ayar Ubangiji ga Daddy, in an hana aure ba za a hana afkuwar zina ba, sai wadanda Ubangiji ya tsallakar. Hanan duk abin da za ki haifa Dana ne, ni za ki haifawa. Ki yi zamanki ba sai kin zo ba, addu’arki za ta riske mu har inda muke.
Hanan na dade da gane ba tarin arziki da dukiya shi ne jin dadi ga diya mace ba, a’a samun miji na gari mai sonta da tausaya mata, wanda zai tsare mata lalurorinta iya karfinsa, ya kuma ba ta soyayyah da kauna da gangar jiki da zuciyarsa. Shi ne babbar sa’ar da mace za ta yi a rayuwar duniya. Daga hakan ba abin da ya rage mata sai zaman neman cikawa da imani”.
Hanan ta share hawayen da maganganun Halimah suka sa ta, ta ce, “Sis Leemah, I’m regretting, na biyewa son zuciya cikin bacin ran Daddy na aikata kuskuren da har abada ba zai goge daga tarihin rayuwar zuri’armu ba. Sis Leemah, na yi duk iya kokarina in zauna under marital rope (karkashin igiyar aure) Daddy bai ba ni dama ba, ya ki amincewa, yau ni ce zan haife dan shege a gidanmu ina ji ina gani? Don Allah me zan yi Allah ya yafe mini?” Ta fashe da kuka.
“Istigfari Hanan. Ki lazimci istigfari tun daga yanzu. Yunkurin cire wannan cikin babban hatsari ne ga rayuwarki, kuma kisan kai ne, wanda girman laifinsa ya fi na abin da ki ka aikata. Don haka ki ci gaba da istigfari ki bar wa Allah ikonSa. Tunda dai Salim din ya amince cikinsa ne”.
Ta ci gaba da lallashin Hanan wadda haihuwar Halimah ta hanyar halali ta bi ta birkitata, nadamarta ta karu. Da tasani ta yarda da shawarar Salim sun koma secret marriage din da ya fi alfanu fiye da wannan son zuciya da suka aikata.
Da kyar Halima ta samu ta yi shiru. Ta kanga mata kukan baby a kunne. Dariya ta hau yi, ga hawaye shabe-shabe a kan fuskarta. Da haka suka yi sallama.
Kwanan Halimah biyu likita ya ki sallamarta, sabida a bincikensu kan baby sun ga akwai matsala. Kuma sun gaya wa Hashim cewa akwai matsalar, amma suna kan yin test za su gaya masa washegari. Wannan duk ya bi ya damu Hashim, tun lokacin yake wani irin sukuku. Sa’adatu ke ta jigilar abincinsu ita da mijinta Lawal. Dr. Rabi’a ta zo sau daya, ko daga yadda ta ga baby dinsu a shirye cikin tsadaddun kayan sanyi ta fahimci akwai sauyi a tare da su, sannan cike suke da walwala ba kamar da ba.
Hashim ya lura da wani abu, babynsu ba ta bude idanun ta. Sau daya ya ga kwayar idon ta. Lokacin da ta zo duniya kawai. Daga wannan lokacin, tunda ta rufe ido ba ta sake budewa ba, amma tana ta wutsil-wutsil din ta na alamun koshin lafiya, kuma ta kama nono tana sha sosai.
Sai da suka yi kwanaki hudu sannan likita ya kira su shi da Halimahn, tana rungume da babyn a jikin ta. Ita sam ba ta lura da abin da Hashim ya lura da shi ba. Ta dauka babyn mai yawan barci ce kawai. Sai da suka nutsu a gabansa sannan ya duba _file_ dinsu da ke gabansa, ya gyara zaman farin gilashin idonsa. Ya dube su cike da alhinin abinda zai fada, kafin yayi ta maza ya ce.
“I’m sorry Mr&Mrs, your baby was born BLIND!”.
Numfashin Halimah ya dauke na wucin gadi. La-shakka da tana da B.P babu abin da zai hana hauhawar shi a nan take. Da sauri ta dubi babyn wadda ke rungume a kirjin ta. Hashim ya lumshe idanun sa, babu abin da ya zo masa a rai a wannan lokacin sai maganar mahaifin Halima Prof. Zubair Muhammad Numan. A ranar da suka je Abuja neman gafarar sa.
“Allah ya sa kada ki haifi duk abin da yake cikin ki lafiya!”.
Yayi nisa a wannan tunanin ya tsinkayi muryar likita can saman kansa.
“Za mu iya yi mata surgery, a samu ko remnant vision dinta a ceta, ta yadda ko haske ne zai iya ratsa idanunta. Amma wannan total blindness ne, babu likitan duniya da zai ce maka idanun nan za su bude. Surgery din kuma abu ne da zai ci kudi, saboda haka a shawarce; hakura da karbar kaddarar shi ya fi.
Saboda ko an kashe kudin an yi, dan abin da za a ceto ba zai sa idanun su bude ba. Haske ne kawai zai dinga ratsa idanunta. Wannan shi ne abin da consultant dinmu na Ophthalmology ya tabbatar, Dr. Abubakar Turaki Abdullahi GAYA. Kuma duk fadin asibitin nan babu na biyun sa”.
Hashim ya zuki numfashi da kyar ya fesar. Muryarsa ta dashe amma a haka ya yi wa likitan godiya, ya kuma tabbatar masa sun karbi kaddarar Ubangiji. Za su raini ‘yarsu yadda Ubangiji yake son ganin ta.
Halimah da ke hawaye tana ta kallon yarinyar da wata irin kauna, ta ce,
“A’a Cherie, a yi mata surgery din, ko Allah zai sa a dace”.
Hashim ya kama ta ya mikar da ita, ya karbi babyn daga hannunta.
“Ko za a yi ba yanzu ba Sweetheart, ba zan iya bari a kwantar da kankanuwar halittar Ubangiji irin wannan a gadon tiyata ba. Ki bari sai Allah ya raya ta ta fara girma.
We will raise our daughter with so much affection… ba abinda nakasarta zai taba daga soyayyar da za mu yi mata".
A haka suka bar ofishin, Halimah na kuka wurjanjan. Ba kukan kasancewar ‘yar ta da Hashim makauniya ta ke ba, kukan tausaya mata ta ke, tana hango mata rayuwa cikin wannan situation din musamman wajen neman ilmi, rainon 'ya'ya da rayuwar aure.
“Allah ya raya min ke *SAFEEYAH* ya albarkaci rayuwarki, Ya daukaka ki daukaka ta buwayarsa, a nakashen da ki ke”.
Ta fada a hankali, a lokacin da suka shiga adaidaita sahu don komawa gida.
****
BABI NA GOMA SHA BIYU
Suka ja bakinsu suka yi shiru ba su gaya wa kowa ba. Hatta Sa’adatu wadda ke taimaka wa Halimah da komai, ita ke wanke baby safe da yamma. Makota na ta shigowa suna musu barka da abokan arzikin Inna.
Hashim ya bar wa ‘yarsa suna Safiyyah kamar yadda Halimah ta roki alfarma. Ana i-gobe suna Hanan ta kira ta a waya, “Sis, ga ni cikin Kano, wace unguwa ku ke?”
Cikin matsanancin mamaki Halimah ta ce, “Kina Kano fa ki ka ce Hanan? Bana ce ki yi zamanki kada ki zo ba? Kina son jawo wa kanki matsala da Daddy? And our unborn baby”.
“Na yi kokarin hakan amma na kasa. I want to see my little Princess. Tunda na riga na zo magana ta kare, ki gaya min unguwar da kike zan zo”.
“Yakasai”. In ji Halimah. “Idan kin shigo Yakasai ki kira Cherie zai zo ya shigo da ku har gidanmu. Ga shi a gida ya hana Safiyyah sakat, wai wasa yake yi mata”.
Hanan ta lumshe ido, “So is our little Princess our dear mother! Allah ya tsawaita rayuwarta ta ba mu kulawar uwa da ba mu samu ba”.
Halimah ta yi murmushi.
Tun daga soron kofar gida Hanan ta soma shiga tashin hankali, ba dai a wannan gidan ‘yar uwarta ke rayuwa ba?
Hanan ba ta gama tsinkewa ba, tsoron Ubangiji bai gama ratsa ta ba, sai da ta tsinci kanta a dakin Halima.
Babu komai sai ledar tsakar daki, wasu rubabbun kujeru, wani tsohon gado karyayye, da wata wardrove duk kofofinta sun fita. Babu madubi balle kayan kwalliya, sai dai kuma dakin a tsaftace yake a share tas, a goge. Ga turaren wuta mai dadin kamshi Halimah ta kunna don kashe karnin jego.
Da ta yi tozali da Halimah kuma, sai hawaye ya tsinke a idanunta.
She is as old as 40 year old lady, unattractive, sai dai babu kazanta a jikinta. Wannan Halimahr mai gayu da kwalisa, wadda a kullum ta ke sparkling kamar wata dan daren goma sha hudu, fatar jikinta ta ke glowing kamar ana yi mata wankan inji. Amma a hakan tana jin dadin rayuwarta da mijinta. Abin da ba ta sani ba shi ne, yadda ka dauki rayuwa a haka ta ke zuwa maka, in ka dauke ta da sauki komai na duniya ba zai dame ka ba, idan ka cika zuciyarka da wadatar zuci, ka gama hutawa a rayuwarka.
“LEEMAH!”
Hanan ta fada muryarta na karkarwa.
Halimah ta ajiye Safiyyah a kan ‘yar katifarta ta mike ta rungume kanwarta Hanan suka fashe da kuka mai ban tausayi.
“I missed you Leemah…”
“I missed you Hanan, na yi kewar rigimarki da fitinarki”.
Hanan ta ture ta ta dunkule hannu tana bugunta a kirji. “Ni kuma na yi kewar discipline da authoritativeness din Yayata”.
Daga haka suka koma dariya ga hawaye shabe-shabe a kan fuskokinsu. Gyaran muryar Hashim ne ya ankarar da su shigowarsa, ya shigo da leda a hannunsa ya ajiye wa Hanan Maltina da ruwan roba masu sanyi, sannan da snacks din Oasis Bakery cikin farar ledar shagon.
“Na gode Mr. Hashim”. Hanan ta fada tana murmushi, karon farko da suka taba yin maganar arziki ita da shi. “But ni da driver na ne, please ka diba ka kai masa”.
“Already an ba shi. Barka da zuwa, ya ya hanya?”
“Alhamsu lillah, it was a nice experience, sabida ban taba tafiyar mota mai nisa haka ba. Na so in biyo jirgi aka ce ba jirgi yau sai gobe, ni kuma a matse nake da in dauki Mamana”.
Hashim ya yi murmushi, ya dauko babyn daga katifarta ya ba ta.
“Wow! Masha Allah, wannan hancin da bakin duk irin nawa ne”.
Hashim ya ce, “Allah ya sa kada ta yo halin, nason girma da fadin rai”. Amma a zuciyarsa. Ya fice ya barsu.
Kaji uku Halimah ta sa aka kamo aka gyare mata, ta soya su ta yi miyar dage-dage da su mai rai da lafiya, sannan ta yi hadin salad da dafaffen kwai, ta dafa farar shinkafa da macaroni duk don kanwarta Hanan, wadda ta zo kwanciya ta rasa inda za ta kwanta a dakin Halimah, don ba za ta iya kwanciya a wannan shamulalliyar katifar tata ba. Balle ta hau wadannan burmammun kujerun nata. Don haka bayan ta ci abinci ta huta, ta ce da Halima da ke shimfida mata sabon wankakken zanin gadonta.
“Sis, ni fa guest house zan je na kwana, gobe da safe in zo, I can’t sleep here…” Ta fada tana nuna mataccen gadon Halimah.
Halimah ta ji ba dadi, amma ta san da gaske ta ke, ba za ta iya kwana a kai ba. Ta yi magana da direbanta ta waya sai ga jakunkuna bi-da-bi yana shigowa da su, sai da suka cike filin dakin Halimah, set ne kamar na lefe har dozen guda.
Ta jawo ta farko ta bude, suttura ce damkam tun daga kan laces, atamfa, voile, materials, shadda babu irin wadda babu, ta ce, “Ga shi nan ki yi fitar suna”.
Ta biyu mayafai ne da slepping dresses, ta uku inner wears, ta hudu kayan kwalliya da tsadaddun kayan shafa. Ta biyar duk takalma da jaka ne. ragowar kuwa kayan baby ne lodi-lodi da pampers katon uku da duk abin da jariri zai bukata daga shekarar farko zuwa shekaru biyar.
Halimah ta manta da irin wannan rayuwar, don haka ban da na baby ba abin da ya burge ta a ciki.
Ta ce, “Hanan, why? Na gaya miki Cherie ya mana komai, kuma ba zan yi amfani da kudin jikin Daddy ba balle na ma’aikatar sa. Ko da zan yi yawo tsirara.... fatara za ta yi karshen numfashina”.
Hanan ta runtse ido, “Ki sassauta kalamanki, na san ya bata miki rai, kuma yana kan bata miki, but that will not change the fact that he is your father. Komai ki ka fada a kansa Mala’iku na rubutawa.
Sannan wannan kudin ba na aikin NCC ba ne, kada ki manta dan minista na aura, kuma nake tare da shi har gobe. Ba abin da bana samu a jikinsa, kuma ina da business bayan aikina. Ina shigo da electronincs daga kasar Japan. So ni ba da Daddy na dogara ba, ba da ma’aikatarsa ba”.
Dole ta kashe bakin Halimah, ta yi ta mata godiya. Tana jinta tana ta kiraye-kirayen waya tana bada order. Ba ta dai san me ta ke saya ba don a hankali ta ke magana. Wajejen karfe tara na dare bayan sun gama cin abinci ta bar kayanta a nan, handbag dinta kawai ta dauka suka wuce Tahir Guest palace.
Washegari ya kama sunan Baby Safiyyah, Hashim ya yanka katoton ragon da ya tanada aka yi radin suna a masallaci. Wajejen karfe goma na safe Halimah ta yi wanka ta dandasa kwalliya da leshin da Hashim ya dinka mata, ta gyare Safiyya cikin kayan da babanta ya saya mata. Hashim ma ya yi ado da farar shadda kaftan sai walainiya suke.
Hanan ta iso, ta fiddo wayarta ta yi ta yi musu hoto su da babynsu. Sannan ta ce da Hashim tana neman izni za a yi gyara a dakin Halima.
Ai kuwa Hashim ya kankance ido ya ce ba ya so, ta yi abin da ya kawo ta (zumunci) ta koma gida, wadancan lodin akwatunan ma da ta tsibe musu ta kwashe abunta. Shi bai gaza da iyalinsa ba, kuma ba zai taba gazawa ba. Ran Hanan ya yi mummunan baci, ta ce, “You cannot stop me daga yi wa ‘yar uwata alheri, just don kana aurenta ba za ka raba mu ba. Ai a al’adance idan mace ta haihu ‘yan uwanta su na sayen kayan jariri da atamfofi su kawo mata”.
Da ya ji ta fi shi gaskiya sai ya sa kai ya fita kawai. Yana fita ta sa kamfanin furnitures din da ta zo tare da su su fidda komai na dakin Halima su kafa sababbin furnitures din da ta saya mata, farare sol, gogaggu ‘yan kasar italiya. Ga wasu luntsuma-luntsuman kujeru masu tsadar gaske, sannan aka kafa labulaye launin kujerun aka yada center carpet a kasa. Nan da nan dakin Halima ya dau walainiya.
Sallamar Sa’adatu da Dr. Rabi’a Hanan ce ta amsa, suka shigo suna ta mamakin abin da suka gani. Halimah ta gaya musu Hanan kanwarta ce uwa daya uba daya. Nan Dr. Rabi’a ta fara zare ido cikin borin kunya, don ita har ranta ta bayar Halimah ba ta da kowa, a bariki Hashim ya auro ta a Abuja.
Allah ya so ta ta yo musu girki cooler-cooler nan ta gabatar da shi gare su tana ta borin kunya. Hanan da ba ta san komai ba sai yaba mata ta ke, don Halimah ta gaya mata yayar su Hashim ce.
Makota sun shisshigo haka abokan arzikin Inna da ‘yan uwan mijin Sa’adatu, kowa ya ci abinci mai kyau ya yi guzurinsa. Sai kallon Hanan ake ana karawa, domin ta zamo kamar wata Zarah a cikin matan da suka halarci sunan, sutturarta da apperance dinta.
Sai bayan isha kowa ya watse aka bar Halimah da Hanan. Hashim saboda Hanan yana café dinsa bai dawo da wuri ba. Don ya bar su su yi sallama sosai kasancewar gobe Hanan za ta koma gida.
Hanan da ke rike da baby tana kallonta ta lura da wani abu. Tunda ta zo ba ta ga kwayar idanunta ba. Ta dubi Halimah tana murmushi, ta ce, “Sleeping beauty, ita ba ta gajiya da barci, da safe barci da dare ma bacci?”
Halimah ta dubi kanwarta, ta ce, “Umh”. Kawai in ta girma kowa ya sani, ba sa son baki ya kama ‘yarsu.
Sai karfe goma suka yi sallama kamar ba za su rabu ba, domin gobe da asubah za su dauki hanya don ta samu ofis a kan lokaci.
*****
Suka ci gaba da rainon diyarsu Safiyya tare da ba ta kulawa ta musamman, bayan soyayyar iyaye ita wannan ‘yar suna jinta sosai a ransu, saboda rauninta.
Watannin Safiyyah hudu, duk wanda ke tare da su ya san cewa ba ta gani. Ga wani irin kyau da Allah ya ba ta. Tausayi da kyawunta shi ne ke sayo mata soyayya a zukatan al’ummah.
Hanan ta gaya mata cewa, tun bayan haihuwar Safiyyah Daddy ya sanya ta a ma’aikatan NCC da aka tura karo kwas a kan harkar Telecommunication kasar Manrovia, ba ta so tafiyar ba, amma Salim ya karfafe ta da cewa, ta je, wannan zai ba ta damar rainon cikinta cikin kwanciyar hankali har sai ta haihu. Don kuwa ya shirya karbar dansa, in ya so iyayensa su zabi abin da ya fi musu amfani tsakanin barinsa da matarsa ko su raini abin da ta haifa masa. Kwas din zai dauke su watanni shidda.
Bayan tafiyar Hanan suna waya akai-akai, kuma ta gaya mata ta shiga EDD dinta.
Yau Hanan ta kira ta ne da kyakkyawan albishir na ta sauka lafiya, ta haifi diya mace mai tsananin kama da mahaifinta. Nan da watanni biyu za ta kammala kwas dinta ta dawo gida ta fuskanci Daddy.
An ce dai ba'a murna da haihuwar dan gaba da fatiha, amma Halimah sosai ta ke murna. Jin ‘yar ta ke kamar Safiyyah a zuciyarta musamman da Hanan ta turo mata hotunanta. Kyau har zuba yake, da ma an ce shegun ‘ya’ya kyawu ne da su. Ta gaya mata Salim ya je Manrovia ya ga babynsa ya ba ta kudi masu yawa don ta shayar masa da baby.
Ba dai haka aka so ba wai kanin miji ya fi miji kyau. Halimah ta kara tunatar da ita yawaita istigfari, hailala da salatin Annabi, to calm Allah’s anger against them. Ita ma tana taya su da roka musu gafarar Ubangiji.
****
BAYAN WATANNI BIYU
Gidan Proffessor Numan.
Asokoro, Abuja, Nigeria.
Direban da ya dauko Hanan da ‘yarta daga filin jirgi ya yi horn a tankareren get din gidan Prof. Numan, Seun ya zo ya fara shaida motar sannan ya bude suka shiga. Duk da cewa gabanta mugun faduwa yake yi, amma tana ta jan addu’a wadda Halimah ta koya mata. Ta ce, ita za ta yi ta karantawa a lokacin da za ta fuskanci Daddy. Direban ya bi bayanta da jakunkunanta.
A kasaitaccen falonsa ta fara yin tozali da shi. Dauke ta ke da yarinyar a kafadunta wadda ta radawa suna Yusra. Barcinta ta ke hankali kwance, ta zuge sliding door din da ta raba falon farko da falon da Daddy ke ciki.
Zaune yake yana ta aiki kamar yadda ya saba; bisa computer ne, bisa takardu ne, bisa macbook ne duk dai babu wanda ba ya yi. Yana yi yana duba agogo don jiran isowar ‘yar sa Hanan.
Da sallama ta shigo, ya daga kai ya dube ta da murmushi.
“Welcome back daughter…....”
Ta karaso ta rungume shi da hannu daya yayin da dayan ke dauke da baby.
“I missed you Daddy…”
“Missed you too daughter, how is Manrovia…?”
Sauran maganar ta makale a makoshin sa, sakamakon kuka da yarinyar hannun Hanan ta canyara. Cikin mamaki da al’ajabi ya dubi Hanan sosai wadda ta zauna gefe ta fiddo nono ta sa wa ‘yar a baki.
A firgice Prof. ya mike tsaye, “Me zan gani haka? ‘Yar wa ki ka dauko? Na ce daga ina ki ka dauko ta?”
Hanan ta sunkuyar da kai ta soma hawaye, ba ta ce komai ba. Ya sake maimaita tambayar sa, wannan karon a matukar fusace, Hanan ta soma shivering (karkarwa) kamin ta tattaro courage ta ce, “I’m sorry Daddy, ‘ya ta ce, ni na haife ta!”
Wani gigitaccen mari ya dauke ta da shi, ya sake dauke daya kuncin nata da wanda ya fi na farko, sannan ya nuna ta da dan yatsa.
“Karya ki ke ki tozarta ni. Ashe karuwanci ki ka tafi ba inda na tura ki ba? Fitar min da ita daga gida kafin na kashe ta, hukunci ya hau kaina”.
Kuka sosai Hanan ta saki, “Daddy ni ce ‘yarka Hanan, ‘yar da ka raina ba tare da taimakon uwa ba. Ka tuna girman amanarmu da Allah ya dora maka. Wannan yarinya da ka yi aiki da fadar Allah da ManzonSa da ba ta zo a haka ba. Ni ban yi karuwanci ba, ban taba sanin Da namiji ba bayan tsohon mijina, Salim. Kuma shi ne uban ‘yar sa, ka yi min alfarma ka bar ni in shayar da ita. Ranar da na yaye ta zan ba shi ‘yarsa in ci gaba da zama karkashin biyayyar ka”.
Tun daga yatsar kafarsa har gashin kansa gumi yake. Ji ya yi jikinsa ya yi bala’in sanyi. Wani abu mai kama da nadama na son ziyartarsa. Zama ya yi a kujera ya dafe kansa da hannu bibbiyu. Yayin da Hanan ta sauko daga kujera ta zube gwiwoyinta a gabansa tana hawaye dauke da ‘yarta.
“Daddy, ka hana mu aure, ka hana mu zaman gidan miji saboda boko. Mu din kuma ba waliyyai ba ne ‘yan Adam ne ajizai, wadanda shaidan ya yi alkawarin ja ga halaka muddin ba mu bi fadar Allah ba. Ubangiji ya yi maka umarnin ka yi mana aure daga shekarun fara balaga, amma Daddy ka ki hakan. Na zo na yi aure ba bisa yarda da amincewarka ba, ka bar ni babu kulawa a gidan aure kamar ba ni da kowa. Dangin mijina suka kasa karbata sabida rashin gatan iyaye. Mijina ya sake ni a kan dole, ba don yana so ba sai don bin iyayensa.
Daddy ka san bond din da ke tsakanin mata da mijinta? Musamman wadanda suka rabu ba bisa wata kwakkwarar hujja ba? A lokacin ne Ubangiji ke sanya musu kaunar juna wadda in ba a yi sa’a ba, sai ta kai su ga tabewa da halaka, wanda wannan shi ne hakikanin abin da ya faru da ni.
Daddy mu marayu ne, amana a hannunka ka yi tunani da mahaifiyarmu na raye, za ta amince da rayuwar da ka sanya mu a ciki?
Kudi dai Daddy na duniya ban san wane iri ka ke so ka yi ba. Ilmin boko na duniya ban san wane iri ka ke so mu yi ba. Ba ka bai wa masu bukata aiki sai mu da ba ma bukata. Ba ka tunanin lahirar mu, kullum cikin rayuwar duniya da neman kudi kawai ka ke cusa ni. Ba ka la’akari da kasancewata diya mace mai rauni, wadda halittar ta ta karfinta da juriyarta ba kamar namiji ba ne. Na samu komai da dan Adam ke bukata a rayuwa ban da aure. Ka gaya min in ban yi zina ba me ya rage min a duniya?
Sis Leemah. Ka yanke ta daga jikinka kawai saboda ta zabi ta raya sunnar Annabi, ba don ta kasance mai tsoron Allah ba babu shakka abin da ya same ni shi zai same ta. Ta jure duk wasu azabobinka shekara da shekaru, amma wallahi ta fi ni kwanciyar hankali a halin yanzu, tunda tana cikin rahmar aure tare da mijinta da ke sonta saboda Allah, da tsarkakkiyar zuri’a wadanda a ko’ina za ta yi alfahari da tutiya da cewa, ta hanyar sunna ta same su…”
Ta kama kafafunsa jikinta na karkarwa.
“Ka bar min ‘yata ina sonta. Ita ce sanyin idaniya ta. Na yi maka alkawarin zan ci gaba da yi maka biyayya har PhD zan dora in dawo in ci gaba da aiki har iya inda ka ke so. Amma don Allah ka yi min alfarma ka bar min ‘yata in raine ta in ta kai munzali ita in yi mata aure ta haifa min tsarkakkiyar zuri’a. Ka yafe min, ka sa min albarka. Na tuba na bi Allah na bi ka… ba zan kara yin zina ba!”
Ta hade hannayenta biyu cikin roko, fuskarta sharkaf da hawaye.
Prof. Bai ce mata komai ba ya juya cikin wani hali zuwa dakin sa.
Daga ranar bata kara ganin shi ba, ya shige daki ya rufe kamar wanda ya shiga halwa, bata san me yake ci a dakin ba ofis ma baya zuwa. Tun tana zuba idon zai kwace mata 'ya har ta saki jikin ta ta cigaba da hidimar 'yar ta cikin gidan.
A kwana na biyar ne rannan ta shiga wanka ta bar Yusra kwance akan gado tana ta tsala kuka. Prof. Yayi shirin ofis zai wuce ta gaban dakin Hanan amma kukan Yusra yasa dole ya dakata, yana jin wani iri a zuciyar sa. Hakika a kwanakinnan biyar ba abinda yake a daki sai neman gafarar Allah, ya yarda duk abinda Hanan ta fada gaskiya ne, kuma rashin mai gaya masa gaskiya akan iyalinsa shine babban abinda yayi tasiri a kansa.
Abin da ba ta taba zato ba, abin da ba ta taba tsammana ba. Daddy ya shigo dakin ta. Hannu biyu ya sa ya dauki 'yar. Idanunsa cike taf da hawaye, kamar ta daya da Safeeyah. Ya rungume ta a jikinsa tsawon lokaci bai ce komai ba. Hanan dake tsaye bakin kofar toilet daure da tawul don farin ciki ko motsi ta kasa yi.
Sannan ya ajiyeta a kan kujera yana kallonta, ya juya ga Hanan dake tsaye yace.
“Ki ba ta nono ta sha, tun daga daki na nake jiyo kukan ta”.
Hanan gigicewa ta yi don murna, ta kasa ba wa ‘yar nono sai jijjiga ta ta ke tana fadin, “Daddy, ka yafe mana? Za ka dawo da Sis Leemah? Za ka bar ni in koma gidan mijina? Za ka bayyana kanka a matsayin ubana ga dangin mijina?”
Tambayoyin ta ke jejjerowa a jere, ko numfashi ba ta shaka. Prof. bai ce mata komai ba, ‘yar cikinsa da ya haifa ta shayar da shi ilmi, ilmin rayuwa wanda bai taba zama ya ankara da shi ba.
Da gaske akwai mutane irinsa da yawa a wannan zamanin, wadanda suka riki boko da career da muhimmanci fiye da bautar Ubangijinsu, fiye da feelings din ‘ya’yansu. Neman duniya ya danne na lahira, burinsu kawai ‘ya’yansu su fi na kowa. Ba ruwansu da halin da ‘ya’yan talakawa ke ciki. Duk wani vacancy mai maiko na ‘ya’yansu ne, dan talaka ya mutu don rashin aikin yi ba damuwarsu ba ne.
Ga result (sakamako) na fifita duniya kan umarnin Ubangiji yau ‘yarsa ta kawo masa har gida, wanda ba zai taba kankaruwa daga jikinsa ba, jikar sa… 'yar gaba da fatiha…. Wai don ma Allah ya takaita korar da ya yi mata lokacin da mijinta ya sake ta, bai sa ta shiga duniya ba.
Tunani na karshe da ya kutso cikin kwakwalwarsa shi ne, HALEEMAH… his innocent daughter Haleemah!!! How cruelly he treated her… how he abandoned her… how he scolded her… how he sent her away, da zaluncin da ya yi mata kawai don ta zabi AURE a kan BOKO! Yau ya tabbata sai Ubangiji Ya tsayar da shi hisabi tsakaninsa da Haleemah, idan har bata yafe masa ba!
*****
BABI NA GOMA SHA UKU
Karfe goma na safe Hashim ya iso café (business center) dinsa. Abin da ya ba shi mamaki dirkeken kwadon da ya rufe kofar shagon ya tarar a gefe a yanke. Kofar shagon kuma a sakaye, wato an sakaye ta.
Cikin wata irin mummunar faduwar gaba ya finciki kofar iya karfinsa ya shiga. Fetal! Sunan wani fili. Duka computers, printers, scanners, photocopying machines, lamination machine da duk wani abu mai daraja da ke cikin shagon babu shi. Kwashewa aka yi? Tashi sama suka yi? Allahu A’alam, amma da ya tuna da yankakken padlock da ya baro a kofa sai ya gane shigowa aka yi ta karfin tsiya aka yashe shi.
Daga tsayen da yake ya sulale a kan kafafunsa. Yanayin da yake ciki ya fi dacewa da a kira shi suman ido biyu. Ya fi karfin awanni biyu a haka, kafin nutsuwa ta zo masa sakamakon kalmar innalillahi wa’inna ilaihi raji’un da ta samu muhalli a kan harshensa.
Sai kawai ya mike ya sabi hanya, tafiya yake tun daga filin tsohuwar jami’ar Bayero ba tare da ya san inda yake jefa kafarsa ba. Ya wuce Kofar Famfo, ya wuce Kofar Duka-Wuya, ya wuce Kofar Gadon Kaya, ya wuce Hauren Shanu, ya wuce Kofar Na’isa, ya wuce Kofar Dan’agundi, ya wuce ta cikin Sabuwar Kofa ya bulla Yakasai. Tun karfe sha biyu na rana har karfe biyar na yamma kafin kafafunsa su kawo shi gida.
Halimah na yi wa Safiyyah wankan yamma yadda ta ke yi kafin babanta ya dawo, ya same ta tsaf tana kamshi. Tsuke cikin kyakkyawar suttura, sai ga shi ya fado gidan kafafunsa futu-futu kamar an kwato shi daga bakin kura.
“Baban Safiyyah, lafiya?”
Ta fada hankali tashe.
Ya ja kujera ‘yar tsugunne wadda sun gaje ta ne daga Inna ya zauna yana maida numfashi. Kawai Halimah sai gani ta yi hawaye sun zubo masa.
“Ba ni wayarki zan yi reporting wa police, wayata babu kudi”.
Halima ta kara shiga tashin hankali.
“Police Baban Maama? Fara gaya min mene ne don Allah?”
Ya mike tsaye, “Ki bari in je police station in dawo”.
Sai da ya je ya dawo ne yake gaya mata komai. Halima ta runtse idonta, ta ce,
“Ya Salamu sallim!”
‘Yan sanda sun yi iya kokarinsu, amma kullum abu daya suke gaya musu, “Ana kan bincike”.
Ba shagonsa kadai aka yashe ba, har na kusa da shi da na gabansu. Tun suna jelen ofishin ‘yan sanda har sun gaji sun bar wa Allah komai.
Kasar Najeriya da shuwagabanninta suka kara sire wa Hashim. A kullum sai ya zauna yana kiyasce-kiyascen abin da zai yi idan Allah ya ba shi shugabanci komai kankantarsa. Wani irin determination ya shige shi a kan leadership (kwadayin shugabanci) da kuma kwadayin siyasa (political inclination). Har zama yake ya yi ta rubutun abubuwan da zai yi idan da a ce shi ne ke da shugabancin Nigeria, da kuma matsalolin masu ilmi irinsa da matasa ke fuskanta.
Rannan Halimah ta dauki daya daga cikin rubuce-rubucensa tana karantawa. Taken rubutun shi ne babban abin da ya dau hankalinta; NIGERIA’S TRAUMA IS POLITICAL DICHOTOMY… there is always a dichotomy between what our politicians say and what they do… insecurity overwhelmed us… thugging, insurgency, robbery, kidnapping, unemployment are the major problems of our youths......
Haka ya yi ta jero matsalolin matasa wadanda suka addabi al’umma, wanda unemployment shi ne silar mayar da su heartless suke cutar al’umma. Abubuwan da zai yi wa matasa idan ya samu damar shugabanci komai kankantarsa.
Ya koma shiru-shiru ya rage walwala, kullum cewa yake,
“Halima ba ni da sa’a!”.
Ita kuma sai ta ce, “Bar fadin haka Baban Maama, haka rayuwa ta ke, WATARANA ZUMA, WATARANA MADACI, ko kai ne beran masallaci saboda talauci, haka nake sonka. BA ZAN DAINA SONKA BA!” (Sunan littafin Watarana Zuma....na canza shi zuwa AURE KO BOKO?)
Hatta wasan da yake yawan yi wa Maama (Safiyyah) ya rage shi, ya rage fita, daga sana’ar kajin Halima suke ci suke sha. Halimah ta fahimci he is a bit depressed don haka ta dage wajen counselling dinsa, yi masa nasiha a kan muhimmancin yarda da kaddara, kunna masa wa’azin malamai masu tuni da cikar imanin bawa bai yiwuwa har sai ya yarda da kaddara mai dadi ce ko mara dadi. Ta kara dagewa wajen kyautata masa tare da faranta masa a shimfida.
Hashim ya yarda da fadar Manzon Rahma cewa, rabin addinin mutum shi ne dace da samun mace ta gari. Halima ba ta gaza ba har sai da ta samu Hashim ya saki ransa, ya koma cikin nutsuwarsa, ya fara fita ‘yar buga-bugarsa yana samo musu dan abin da ba za a rasa ba. Wani abu sai kasata Najeriya. Mutum mai kwalin digiri na uku kenan, babu irin cike neman aikin da ba ya yi online amma in magana ta fara kankama a karshe wanda ke da kafa (wanda ya san wani) shi za a ba wa aikin ko da kuwa kasa yake da shi a qualification.
Tuni Hashim ya daina neman aiki, aikin gwamnati ya fita ransa, ko aikin koyarwa a makarantu ya daina nema. Zuciyarsa ta kekashe ba abin da yake so yake mafarki irin SIYASA.
A daidai wanan lokacin Maama (Safiyyah) ta cika shekara guda, sabanin wasu makafin da idanunsu ke a bude garau gani ne ba sa yi, Safiyyah idanunta a rufe suke ruf! Tun a wannan lokacin Safiyyah ta san muryar uwarta ta san ta ubanta. Ta san ta lalubi fuskokinsu ta gane su. Ta san in ta ji muryar babanta ya dawo ta fito da gudu ta yi masa oyoyo! Ko da kuwa za ta ci karo da wani abun ta fadi ta buge ko ta ji ciwo ba ta fasawa.
Wata irin soyayyah suke yi wa Maama, ko sauro ba sa bari ya cije ta. Kullum tas-tas da ita cikin wanka da kyakkyawar suttura. Yadda Halima ke kula da ita ba ta kula da kanta haka.
******
“Duk inda za ki nemo min lambar wayar uban yaron nan ki nemo min yanzu-yanzu”. Prof. ya fada yana duban Hanan da rinannun idanunsa.
Wayarta ta dauko daga jakarta ta budo lambar Baban Salim ta mika masa.
A take ya dau lambar a wayarsa ya kira, sakatare ne ya dauka ba bata lokaci ya fada masa ko shi waye, kuma so yake ya ganshi, in zai yiwu a gida don family matter ne.
Minista ya san ko waye Zubair Numan, amma bai taba sanin yana da alaka da matar dansa ba. Sabida ba shi ya karbawa Salim auren ba kaninsa ne, kuma ba mazauni bane sannan irin mutanen nan ne ba masu kwakkwafi ba. Nan ya bada appointment karfe takwas na daren ranar.
Karfe takwas din kuwa a harabar gidan Ministan ta yi musu, shi da Hanan tana dauke da babynta.
Fargabar duniya ta ishe ta, don Daddy bai gaya mata inda za su zo kenan ba, da ta fara kiran Salim ta gaya masa.
Minista ya sa aka yi musu jagora zuwa falon saukar bakinsa na musamman. Ya sa aka cike gabansu da abin tarbar baki, amma sai ya lura chairman a masifar fusace yake.
A hakan suka gaisa, Daddy ya ce ya yi masa alfarma uwargidansa ta kasance a wajen don abin da ya kawo shi ya shafe ta.
“No problem”. In ji Minista, nan ya kira Hajiya Mubina. Ba jimawa ta shigo tana taku daidaya. Ganin Hanan zaune rungume da jaririya ya ba ta mamaki.
Daddy ya nuna Hanan, ‘Kun gane wannan?”
Hajiya Mubina ce ta ce, “Kwarai na gane ta mana, ba Hanan ba ce?”
Prof. ya ce, “Da kyau, ‘ya ta kenan ta biyu cikin ‘ya’ya biyu kacal da Allah ya ba ni, wadda dan ku ya aura ya saki babu dalili. Now, kun ga wannan…”
Ya nuna ‘yar hannun Hanan, “Ke ba ni ita nan”.
Jiki na rawa Hanan ta ba shi ita, ya dauka ya kai wa Minista har wajen zamansa. Da sauri ya karbi ‘yar ganin yana neman kwala ta da kasa.
“Jikarku ce ta gaba da fatiha na kawo muku, kun raba su ta karfi ba su rabu ba, ga sakamakon abin da suka zaba nan. Na gama nawa kukan, saura ku. Hanan tashi mu tafi, Allah ya ba mu alkhairi’.
Hanan ta ki tashi kamar an kafe ta, ZUCIYAR UWA! Ko kusa ba ta jin za ta yarda ta bar falon nan ba tare da ‘yarta ba.
“Daddy, Yusra fa?” Ta fada muryarta na rawa.
“Yusran uwarki? Kanwar uwarki ce ko kanwar ubanki? Za ki tashi mu tafi ko sai na fasa miki baki da hanci?”
Ya juya ga Minista, “Kai dan siyasa ne, muddin ka dawo min da ‘yar gaba da fatiha gidana sai na tona wa media ta ji. Wallahi ba ku san ni ba, ba wai bana son ‘yata ba ne, bata min rai kawai ta yi”.
Ya fizgi hannun Hanan ya tankada keyarta.
Minista ya sassauta murya abin tausayi.
“Amma Prof. kamata ya yi ka zauna mu yi magana ta nutsuwa ko? I never know she is your daughter, ce min suka yi ba a san salinta ba, ba ta da iyaye balle dangi. Ko ba haka ki ka ce ba?” Ya jefa tambayar ga maidakinsa.
Ta sunkuyar da kai hawaye na bulbula. Yau ina za ta kai dan shege a cikin jikokinta?
“Ka yi hakuri Prof. ka zauna mu fahimci juna. Na hada ka da girman Allah”.
Jikin Prof. ya yi sanyi, ya saki Hanan ya samu kujera ya zauna.
“Ka bari in kira Salim, ya zo ya tabbatar min ‘yar nan tasa ce, duk da biri ya yi kama da mutum, kuma ido ba mudu ba amma ya san kima. Ga kamanni sun bayyana kansu”.
Ya dauko waya yana goge hawaye ya kira Salim. Cikin sa’a shigowarsa gidan kenan.
Yana shigowa falon ya ja turus! Ya tsaya yana rarraba idanu. Uwar da uban suka bi shi da kallon takaici. Sai ya tsugunna yana gaida Prof. ya ki amsawa.
Minista ya ce, “Salim, is this your daughter?”
Ya nuna yarinyar da ke rike a hannunsa.
Kansa a kasa, bai taba jin kunyar iyayensa a duniya irin yau ba, jinsa yake tamkar tsirara a gabansu. (Kunyar duniya ma ke nan kafin ta lahira. Allah ka yafe mana kura-kuranmu, ka sa muna daga cikin bayinKa muminai, Ka kare mu daga dattin zina).
Cikin tsawa mahaifinsa ya maimaita masa tambayar. Kansa a kasa ya ce, “Eh, ni na haife ta, kuskure ne mun tuba mun bi Allah mun tuba”.
Uban ya ce, “Amma ka san you have tarnished the image of this house ko?”
Hawaye suka zubo wa Salim, ya ce, “Wallahi Daddy sau daya ne, Allah ne ya yi nufin kasancewar hakan. Mun tuba muna rokon Allah gafara, muna rokonku ku gafarta mana ku ma. Shaidan ne… kuskure ne...…”.
Ya fashe da kuka.
Minista ya maida dubansa ga Prof. cikin lallashi ya ce, “A karkashin sulhun da nake nema, ina rokon ka maida masa auran matarsa, tunda akwai sauran zama a tsakaninsu, ko nawa ka yanke sadaki zan biya. Mu taru mu yi ta istigfari, kuskure ne duk mun yi, ga shi garin kokarin kare martabarmu mun jawo rugujewar martabar gabadaya. Maida aurensu shi ne maganin komai, kuma rufin asirin yarinyar. Da kwanciyar hankalinmu gabadaya. Ka yi hakuri Prof. ka amshi wanan sulhun”.
Shiru Prof. ya yi, Minista bai yi kasa a gwiwa ba ya ci gaba da rokonsa, har sai da Hajiya Mubina ta sa baki ita ma, sannan ya koro musu sharudda na rikon auren diyarsa; za su rike ta da kulawa, mutunci da kyautatawa.
Za a sake dauro auren a garin Numan cikin danginsa ba a Abuja ba, don su daina zaton ba ta da dangi. Sannan babu gori tsakaninta da kowa nasu kan wannan yarinyar data haifa, duk Minista da Hajiya Mubina suka ce sun amince.
Ya yanka sadaki yadda ya ga dama, duk dai sun amince. Sannan ne ya amince za a mayar da auren jibi a Numan bayan saukowa daga sallar juma’a.
Salim da iyayensa suka yo musu rakiya har jikin motarsu. Hanan ta ki yarda ta kalli inda Salim yake, shi kuma sai kokarin su hada ido yake amma ta ki, har suka shige mota direbansu ya ja suka tafi.
Suna shigowa gida Hanan ta shige daki rike da Yusra ta kira Halimah ta labarta mata duk abin da ya faru. Halimah ta ji dadi, ta kuma taya ‘yar uwarta murnar samun maslahar rayuwarta, sannan ta ce da Hanan cikin wata irin kakkausar murya.
“In ki ka gaya wa Daddy kin san inda nake, ko kin san wani abu da ya shafe ni; BA ZAN TABA YAFE MIKI BA! Kamar yadda ba zan taba yafe masa ba har duniya ta nade’.
safiyya ta wayi gari da bakon dauro (kyanda). Wannan ya tada hankalin Halimah da Hashim ba dan kadan ba. Wadanda ko kuda ba sa so ya sauka a kan miskiniyar ‘yarsu. Ga shi ko kudin motar da za a kai ta asibitin Malam babu, balle kudin ganin likita, don haka Halimah ta ce, bari ta kai ta asibitin Murtala, za ta taka a kafa daga Yakasai zuwa can ba tafiya ce mai nisa ba.
Ta roki Hashim ya zauna a gida don akwai wadanda suka yi da ita za su sayi kaji biyar manya, in ya so sai su yi amfani da kudin wajen sayen maganin da aka rubuta musu.
Ba don ya so ba ya amince, don ya yarda ta fi shi gaskiya. Yana da wata kyakkyawar dabi’a ta kai ‘yarsa ko matarsa asibiti da kansa, sabanin wasu mazan da sai dai su hada mace da kudin mota amma ba za su kai ta ko ‘ya;yansu asibiti ba su tsaya su yi musu komai da kansu ba.
Halimah ko wanka ba ta tsaya yi ba sabida rashin nutsuwa. ‘Yar lele ba lafiya, ‘ya daya tamkar dubu, wadda tun a wadannan shekarun nata ta san soyayyar da iyayenta ke mata. Tana kuma tausaya musu duk da karancin shekarunta.
Duk da cewa atamfar jikinta mai tsada ce, amma ta fara kodewa. Tun cikin kayan haihuwar Maama ne. mayafin jikinta a cukurkude yake babu guga don ba su da ayon. Fuskarta ko basilin ba ta gani ba balle a kai fa zancen hoda. Duk da har yanzu kyawunta bai gushe ba, amma skin elasticity dinta ya kau, shekaru masu yawa sun karu a kan nata na ainihi. Rayuwar cikin wahala da rufin asirin Allah ake yinta, ta taimakekeniya tsakanin juna, wadda soyayyar da ke cikinta ce jigon kasancewarta ‘live’ har a yau. In suka fara soyayya kamar sabon saurayi da budurwa. Ga tausayin juna da karfafawa juna. They are not only husband and wife; su abokan juna ne kuma sirrin juna.
Halimah ta yi lullubi rike da hannun ‘yarta suna tafiya a gefen titi don zuwa asibitin Murtala. Wata mota ta danna horn daga bayansu, “Kun san makaho da ji”. Tuni Safiyyah ta gigice ta kwace hannunta daga hannun uwar ta yi kan titi a guje ba tare da ta san ina ta nufa ba. Halimah ta saki jakar hannunta ta dora hannayenta biyu a ka ta saki wani gigitaccen ihu a lokacin da ta hango wata mota Peageout 504 ta taho da mugun gudu ta yi kan Safiyyah.
Mu karasa a littafi na 3.
Yana tafe insha Allahu bada jimawa ba.
Gundarin labarin AURE KO BOKO yana cikin littafi na 3. Alkawari ne na dauka zai tsuma zukatan ku insha Allahu.
Taku har abada,
Sumayyah Abdulkadir.
YIWA KAI HISABI 1&2 da AURE KO BOKO 1&2 tare suka fito.
Ga mai bukatar tsofaffin littafai na, hardcopy ko softcopy, wadanda babu a kasuwa, ya tuntubeni a 07030137870 whtsp only......
Post a Comment for "AURE KO BOKO BOOK 1 AND 2 Complete Hausa Novel"