Auren Shehu Book 2 Complete Hausa Novel
Auren Shehu 2
Afuwan akan rashin cika alkwari, aiki ya min yawa, a yi min hakuri.
Nan Kawu Iliya ya bar Usman da Bello ba tare da yayi kokarin rarrashin su ba, yana cike da tsabagen takaicin dauke kafa da Usman yayi daga Rugar Shehu. Sun kai kusan minti talatin gaban kabarin Mahaifiyar su, Usman gani yake tamkar ita din ce zaune kusa da shi. Sai da sauran matasan Ruga su ka zo su ka ja shi suna mai bashi baki sannan ya hakura ya ta so su ka nufi cikin Rugar Shehu.
Tuni labarin dawowar Usman ya zaga lungu da sako na Rugar Shehu, har ya ga kai kunnan Baffa Mudi, hankalin sa tashe ya zo ganin shin da gaske Usman din ne dan kuwa bai taba tsammanin zai sake taka kafar sa a Rugar Shehu ba bayan kurciyar da ya masa, babban tashin hankalin sa be wuce kar Usman ya ce zai kwaci sarautar Rugar Shehu ba dan shi kan sa ya san jama'ar Rugar sun gaji da mulki irin na sa.
A dandalin shadi ya tarar da jama'a sun taru makil maza da mata, Yara da manya, mata da maza, masu kida na yi, haka masu tafi, tsuffin cikin su kuwa kuka biyu su ke, kukan dawowar Usman da kuma kukan rashin Iyar sa. Cike da tsana da faduwar gaba Baffa ya tsaya gefe ya na duban duk abubuwan da ke wakana, ganin yanda Usman ya ƙara girma ya zama cikakken matashi ma'abocin karfi da kwarjini, ga matasa zagaye da shi, sai koda shi su ke, su na masa kirari da fulatanci, fadi su ke
"Dan Shehu jikan Shehu, karen bana mai maganin zoman ba na, Shehu ya tafi, Shehu ya dawo!"
Ya sanya Baffa Mudi barin wajen a fusace, cikin ran sa ya na saka yanda zai dauki mataki akan dawowar Usman. Shi kuwa Usman gangan jikin sa ne kawai a wajan, zuciyar wacce ke cike da bakin cikin rashin Iyarsa tuni ta yi nisa wajan saka yanda za ta hukunta wacce ta ke da alhakin rashin ganawar sa da iyar sa na har abada, Amma ya kudiri niyar fara raba Rugar Shehu da ummul abasin dalilin da Iyar sa ta tilas ta masa barin Rugar a karan farko, wato Baffa Mudi.
Duk yanda ya so ya kadaice shi kadai yayi makokin Iyar sa abin gagarar, mutane ke ta kai kawo cikin sashen su domin masa maraba da kuma ta'aziya. Haka kuma kishiyoyin Iyasar sa Yagwalgwal da Duduwa su ka sako shi gaba da mitar barin Rugar Shehu da ya yi. Ba shi ya sami kan shi ba sai bayan ishi'i, ya na shirin shiga bukkan sa sai ga yan uwar Mahaifiyar sa sun zo. Yayar ta wacce ake kira da Huwaila, sai kuma kanwar ta mai suna Iyalle, da kuma matar shi Kawu Iliya Hansai.
Sune su ka sa Usman gaba da fadan barin gida da yayi shekara da shekaru babu ko waige, har Iyar sa ta fadi ta mutu. Usman ya kasa musu bayanin umarnin Iyar ta sa ne ya sanya shi barin Rugar dan kuwa har lokacin be yi niyar tonawa Baffa Mudi asiri ba. Jin su na rokan sa da ya kaunaci Allah ya karbi mulkin Rugar Shehu, a cewar Huwaila wasiyar da Iyar sa ta bar ma sa kenan, ya sa shi tambayar ko da wani abun da be sani ba ne?
Nan su ka bude ciki su ka bayyana masa mulkin zalinci da Baffa Mudi ya ke aikata mu su, tare da sana'ar da babban dan sa Tanko ya shiga na garkuwa da mutanen birni ana biyan shi kudi kafin ya sake su, Kuma duka ya na yi ne da sanin Baffa Mudi. Matukar ba so ya ke a maishe da duk matasan garin yan garkuwa da mutane ba, har gwamnati ta gane ta turo a ayi kan mai uwa da wabi toh lalle yayi wani abu.
Cikin bakin ciki da jimami su ka tafi su ka bar Usman, ba su dade da fita ba sai ga dattawan Rugar Sheshu su ma sun iso gare shi da irin bukatar da dangin Mahaifiyar shi su ka zo da shi, cewar su dan babu yanda za su yi ne da tuni sun bawa Muhammadu Bello sarautar Rugar Shehu, ya duba girman Allah ya fanshe su daga wannan ukuba da su ke ciki, Allah ne ya dube su ya dawo da shi.
Cike da girmamawa Usman ya sallame su tare da mu su alkawarin zai kwana da maganar cikin ran sa, in Sha Allah zai samar mu su mafita.
Sai da kafa ta dauke sannan Usman ya sami damar shiga dakin Mahaifiyar sa cikin faduwar gaba, gani ya ke kamar zai gan ta kwance bisa gadon karar ta. Har lokacin dakin cike ya ke da kayan ta kamar ta na raye. Duk yanda ya so daurewa kasawa yayi, Yana mai rungumar zanin Iyar ta sa hawaye ke fita daga idanun sa, haka ya zauna bakin gadon ta ya ci kukan sa ya koshi, be fita ba sai da ya daukarwa kan sa alkwari biyu, na farko shi ne tabbatar da cigaba da yancin Rugar Shehu ta hanyar karbar ta daga hannun Baffa Mudi kamar yanda Mahaifiyar sa ta bar masa wasiyya, na biyu kuma shi ne Zainab, ya yi alkawarin sai ta yi da na sanin zama silar rashin sake ganawa da mahaifiyar sa har abada, zai iya yafe komai amma ban da wannan.
Washegari tun kafin Usman ya je in da Baffa Mudi ya kafa fadansa dattawan Ruga su ka tada bukatar Baffa Mudi ya bawa mai mulki mulkin sa, dama ya kan yi ikirarin rashin Magajin Shehu ya sanya shi zama kan mulkin, toh Allah ya dawo da magajin Shehu.
Nan fa Baffa Mudi yayi kyememe ya ce be san zance ba, mulki ya rigada ya koma gidan sa, saboda haka be da wani magaji da ya wuce Tanko, in Sha Allah kuwa ko bayan ya mutu Tanko ne mai gadon Rugar Shehu. Nan fa aka hau kace na ce, masu goyan bayan Baffa Mudi na yi, haka kuma masu rantsewa sai ya sauka ba su fasa ba, ana cikin wannan yanayi ne Usman ya karaso.
Ganin sa gaban Baffa Mudi yayi mummunar faduwar, ga shi dai Usman din da ya sani ne, haka kuma tufar jikin sa ba ta sauya ba, rigar saki nan dai da kowa ke sakawa ne jikin sa, Amma wani irin cika ido da kwarjinin da Allah ya wa Usman sai ya zamewa Baffa Mudi tamkar Dodo, dan kuwa yanda ya ke shakkar Usman be ji shakkar Maihaifin Usman marigayiya Shehu ba. Usman be fasa gaishe shi cike da ladabi ba a matsayin sa na kanin mahaifin sa ba. Ba komai ne ya dagawa Baffa Mudi hankali ba sai jin furucin Usman na
"Baffa abubuwa da dama sun faru, wanda mun sani, ka sani, ka kuma san mun sani, wanda tonasu na nufin zubewar darajar ka a Rugar Shehu na har abada, haka ba ya cikin abin da na tanadar ma ka....."
"Zancen banza zancen hofi!"
Baffa Mudi ya katse Usman cike da burin kunya, be gushe ba ya cigaba da fadin
" Kai Usman ni za ka zo ka nunawa bude idanu? Wai kai na birni idon ka ya bude ko? Nan ba kafa ka sa ka tsallake Rugar Shehun ba? Sai da ka ji labarin mun fara samin cigaba, shugaban kasa ya ce zai tallafawa fulani ta hanyar gina mana Ruga mai inganci, da asibitoci, da makarantu da kayan more rayuwa shi ne za ka wanko kafa ka dawo ko? Toh ko uban ka Tanko be isa ba....."
"Baffa Mudi!!!!"
Usman ya daka masa tsawar da sai da ya sha ruwan jikin sa, a fusace Usman ya ce
"Kada ka yarda ka bari na take dan guntun girman da na ke ba ka! Mulki! Taimakon shugaban kasa da koma menene baya gaba na, cigabar Rugar Shehu shi ne gaba na..."
Ya tashi tsaye ya na mai duban dattawa da Kuma yan gari da ganin Usman ya sa su karasawa fadar Shehu. Cikin bada umarni Usman ya ce
"Ni Usman magajin Shehu ina mai sanar mu ku cewa ba na zo ne dan karbi sarautar Rugar Shehu ba, na zo ne ganin Iya ta, wacce Allah yayi ba za mu gana ba, duk da haka ba zan iya kau da kai daga gare ku ba bayan shekaru da dama, haka kuma ba zan ce kada ku bi Baffa Mudi ba, Amma ku sani ba a sarki biyu, dan haka idan har kuna so na kasance Shugaba gare ku sai mun canza sheka, ina mai umartar duk wanda ya ga zai iya zama karkashin jagoranci na da ya hade na shi ya nashi, kwanku da kwarkwatar ku, lokacin da Rugar Shehu za ta bar falgore yayi, za mu tasarwa barin falgore rana ita yau"
"Saboda da kai ne wa? Ka juyawa Rugar ta ka baya shekara da shekaru rana a tsaka ka zo ka na wani kurari? Sai mu ga wanda zai bika ai!"
Cewar wani dattijo wanda ke zaune kusa da shi ya kara da
"rabu da shi ya maishe da mutane sakarkaru, mutumin da be damu da uwar sa ba ina zai damu da mu?"
Wani ya ara ya yafa.
"Mu na biye da kai Shehu Usman, kafar ka kafar mu har illa mashaAllah!"
Cewar matasa da wasu daga cikin dattawan wanda su ka yi na'am da batun Usman. Da wanan rudani fadar Rugar Shehu ta watse, in da na jikin Baffa Mudi ke goyan bayan Shehu Mudi, duk da dai hankalin fiye da rabin jama'ar Rugar ya fi karkata ga bin Shehu Usman.
****
Maiduguri kuwa shirye shiryen auran Halitta da Sudais ne ya kankama duk da daurin aure kawai za a yi su tare. A nan cikin wannan hidimar Hajja Kilish ta nemi bukatar a bawa maneman Zinaru da Kori damar fitowa, idan sun shirya a hada auren gaba daya. Hakan kuwa ake yi Allah ya sa aka dace wanda ke neman Zinaru a shirye ya ke, na Kori ne dai ya turo iyayen sa amma tare da bukatar a dan ba shi lokaci be gama shirin sa ba.
Ganin kiri kiri za a aurar da yan uwan na ta biyu ga mazaje na gani na fada ne ya hana Zainab sukuni. Haka ta saka su Anty Sauda gaba da kuka, ta dena cin abinci ta dena walwala cewar ta da ta zauna da auren Usman gwara ta rasa ran ta. Ammy kuwa ta ce ba ita kadai ta haifa ba, idan mutuwar ta ce alkhairi gare su toh Allah ya sa a tafi a sa'a.
Duniya ta yi mata zafi, cikin kwana uku kacal ta rame ta fara lalacewa. Ganin haka Anty Sauda ta yanke hukuncin daukar mataki, gidan Malam ta je, ta saka Ammy gaba tare da Zainab, ta ce lalle ta kira gidan Kano ta ce Usman ya zo Maiduguri ta na san ganin sa.
Ammy na girgiza kai ta ce
"Ah ah ba zan kira shi ba fa, toh na kira shi ma akan me? Na fa fada mu ku wallahi babu yawu na cikin lamarin auren Yakura, gwara ma ta hakura ta zauna da mijin ta...."
"Na gaji da yin wannan maganar da ke Aleesha! Taurin kai gare ki kamar mutanan farko! Toh tantabara! Tunda masoyin ki ya daura ke kuma ba ki rabawa ko? Toh bari ki ga mu yi mai gaba daya, ni nan zan kira shi kuma sakin yarinyar nan ne sai yayi!"
Ammy na mai zuba mata idanu Anty Sauda ta kira numbar wayar da Malam ya aje bangaran masu gadi, wayar na kara ba a dauka ba, ta na shirin katsewa aka daga tare da yin sallama.
"Sunana Hajiya Sauda daga gidan Malam nan Maiduguri, ina son magana da Usman Maigadin"
Cewar Hajiya Sauda cikin dakiya. Shiru ne ya biyo baya daga bisani ta aje wayar ta na mai fadin
"Toh madallah, ke Yakura ai sai ki kwanatar da hankalin ki, Almajiri dai ya hade kayan sa yayi gaba, abin da abokin aikin sa ya sheda min kenan!"
"Yanzu haka ya tafi be sake ni ba? Toh wallahi ko da wasa kar a kara danganta ni da shi! Kada a sake cewa ina da aure...."
"Idan kuma ba haka ba fa?"
Cewar Ammy cikin tsawa, ta na mai nuna ta da yatsa ta ce
"Sai me za ki yi? As far as I'm concern Yakura ke matar aure ce ko kin ki ko kin so!"
Kuka Yakura ta saka wanda hakan ya sanya Anty Sauda fadin
"Sai ki kashe ta ki huta, ko kuwa ki janyo ta gudu ta bi duniya ayi biyu babu. Ke dena kuka na ce dai kun kusa komawa makaranta?"
Cikin muryar kuka ta ce
"Registration ma mu ke, na fadawa Ammy ko kudin registration din ma ba ta ba ni ba"
"Kudin registration dai? Ai kuwa a dangin uwar ki ba matsiyaci! Ki zo gida na ki karba gobe zan baki kudin registration da ma na kashewa"
"Waya ta ma ta lalace Anty Sauda"
Cewar Zainab cike da shagwaba.
"Toh kar ki damu sai a siyi wata ai, ki duba duk wacce ki ke so I got your back. Haka kuma ki hade na ki ya na ki ki koma makaranta, idan ma kin so kar ki halarci daurin auren gidan nan babu lalle ba tilas!"
Jin abin nema ya samu Zainab ta share hawayen ta tare da yiwa Anty Sauda godiya dan kuwa sai a sannan ta dan ji sanyi cikin ran ta, ta fice ta bar Anty Sauda da Ammy su na musayar magana kan ta, har sai da ran Anty Sauda ya baci sosai, cikin fushi su ka yi sallama ta tafi.
***
Washagari da sassafe Zainab ta nufi gidan Anty Sauda, Nan ta yi karin kumallo. Anty Sauda ta ba ta kudi masu yawan gaske domin registration da na kashewa har da na siyan wayar sanan ta kai ta super market ta mata siyayya sosai irin wanda Dady ya ke mata duk sanda za ta koma makaranta. Hatta tiket din jirgi Anty Sauda ce ta siya, Ammy ta sa mata idanu kawai. Wayewar gari Anty Sauda ta zo ta tisa ta gaba, Hajja Kilishi na fadin ba za ta jira a yi auren yan uwan ta ba? Anty Sauda ta ce
"idan lokaci yayi ta dawo, ai ba wani abu ba ne"
Ta yiwa kowa sallama amma ban da Halitta wacce dama idan ba dole ba magana ba ta hada su. Anty Sauda ce ta kai ta Airport, sai da ta tabbatar jirgin su ya tashi sannan ta juya gida.
Haka ma da jirgin su ya sauka birnin Yola Anty Sauda ta kira ta shedawa, Sai Anty Sauda ce ta sheda ma Ammy diyar ta ta sauka lafiya, ta kuma koma makaranta. Ammy da har ranta ba ta jin dadin halin da Zainab ke ciki ba addua ta yi, Allah ya shirya mata ita, ya sa ta gama makarantar nan lafiya ko Allah ya sa ta dawo gida gaba daya sai a san wani matsayi auren ta ya ke, idan kuma kafin nan Usman ya dawo a tura shi can makarantar ya je ya same ta.
***
A Rugar Shehu kuwa jama'ar Rugar na kan shiri na barin dajin falgore. Duk yanda Baffa Mudi ya buga surkullen shi jama'a ba su fasa shiri ba dan kuwa shiri su ke haikan, tare da taimakon Usman wanda cikin kankanin lokaci ya sami soyayyar jama'ar Rugar yara da manya. Iya kwanakin da ya rage mu su a kulli yaumin ya kan ziyarci kabarin Iyar sa, ya ke shafe awanni ya na hawaye ya na mata addua.
Ana sauran kwana daya su tafi aka kwana ana ruwan sama mai karfi a Rugar Shehu wanda ya hana kowa runtsawa, saboda tsoran rushewar gidagen su. Kusan awanni biyar aka dauka kafin ruwan ya tsaya, ruwa na tsayawa kenan ihu da kururruwar Bello ya karaɗe Rugar Shehu.
Usman da sauri ya isa gare shi, ga mamakin sa sai ganin Bello yayi ya na birgima kasa yayinda wani irin bakin abu ke fita daga bakin sa.
"Innalillahi wainnailaihi rajiun!"
Cewar Usman yayinda ya tallabo Bello, be tsaya bata lokaci ba ya shiga karanto masa ayoyin rukiyya da ya koya wajan Malam dan ya tabbatar halin da Bello ya ke ciki ba zai wuce ko dai aikin sihiri ba ko kuma jinni. Sai da su ka kai kusan minti talatin cikin wannan hali, makota duk sun shigo suna tsaye bakin rumfar cike da al'ajabi, cikin su har da kawo Iliya. Bello ya saki nannauyar ajiyar zuciya sai kuma shiru jikin sa yayi sanyi tamkar matacce.
Ganin haka Usman ya rikici yayinda ya shiga jijjiga Bello ya na mai kiran sunan sa da karfi, jin haka Kawo Iliya ya shigo dakin da sauri ya na kokarin duba Bello ta hanyar saka kan sa bisa kirjin Bello. Cikin kaduwa Usman ya furta
"Shikenan Muhammadu Bello ma ya bi Iya! Muhammadu Bello ya tafi ya bar ni ni kadai Kawu Iliya...."
"Babu in da Muhammadu Bello ya tafi, a raye ya ke dan kuwa har yanzu zuciyar shi na harbawa"
Cewar Kawu Iliya ya na gyara kwanciyar Bello, be gushe ba ya kara da
"Kome aka yi Muhammadu ya shiga yanayi ko dai na sammu ko kuma makarin sammu da aka taba yi kan sa, zai fi kyau ka zauna nan tare da shi ka na masa tofi, in Sha Allah zai farfado cikin koshin lafiya"
Usman na mai kokarin saka zuciyar shi da ta amince akan bayanin da Kawu Iliya ya masa su ka yi sallama, Nan ya zauna tare da Bello ya na masa addua kamar yanda Kawu Iliya ya umarce shi, haka har ladanin Rugar Shehu ya kira sallar asuba Usman ya fita Sallah.
Bayan an idar da Sallah Usman ya dawo ya ji abin al'ajabin da ya zaci har ya koma ga mahallicin sa ba zai kara ji ba, wato muryar Bello da ta daki kunan shi ya na mai fadin
"Shehu......Shehu.....ka na jin murya ta kokwa dai a zuci na ke ma ka magana kamar yanda na saba?"
"Lailahailallah Muhamadur rasulillahi sallahu alaihi wasallam!"
Cewar Usman yayinda ya zube kasa ya na mai sujjada ga Allah. Ko da ya dago rungume Muhammadu Bello yayi, ya na hawayen murna ya ce
"Muhammadu Bello muryar ka na ji! Muhammadu Allah ya dawo ma ka da muryar ka! Ashe zan kara jin muryar ka? Ina ma Iya ta na raye Muhammad! Yau ga burin ta ya cika amma babu damar sanar mata"
Kamar yanda Usman ke hawayen murna haka shi ma Bello ya ke, fadi ya ke
"Zan sanarwa Iya, gari na haske zan je na sanar mata, zan yiwa Iya addua a zahiri ba a zuci ba, Zan yiwa Iya sallama, Allah ya sa za ta ji ni Shehu"
"Za ta ji ka Muhammadu Bello! Za ta ji ka da yardar Allah"
Cewar Usman cike da so da kaunar dan uwan na sa. Gari na wayewa labarin dawowar muryar Muhammadu Bello ya zagaye Rugar Shehu, labarin ne ya sanya Baffa Mudi ziyartar makabarta Rugar Shehu cike da tashin hankali domin neman amsar tambayar da ta addabi kwakkwalwar sa,
'shin ya aka yi maganar Muhammadu Bello ta dawo alhalin yanda ya birne layar da ya masa asiri da shi tare da gawar ladan matukar ba tono gawar aka yi ba Muhammadu Bello ba zai sake magana a doran kasa ba'
Ile kuwa nan ya sami amsar tambayar, ashe daminace ta yi gyara a tsohuwar makabarta da ta dade da cika, ruwan da aka yi daren jiya ne yayi ambaliya makabarta har ya bude wasu daga cikin makwancin mamata, in ban da farin yadi babu abin da ke yawo.
"Lalle damina baki mugunta, na tabbata ruwan nan shi ya tono asirin da na rufe shekara da shekaru, matukar ban nemo layar nan na sa an sake rufe wani mamaci da shi ba toh fa asiri zai tonu!"
Cewar Baffa Mudi yayinda ya cire rawani ya aje gefe, sai gashi tsome tsome da shi cikin ruwa da cabi ya na neman laya. Yana cikin wannan yanayi ne Usman da Bello su ka karaso. Cikin kwalla kira Bello ya ce
"Kawu Mudi! Halan wannan ka ke nema?"
Ya daga masa layar da tun sassafe da su ka ziyarci kabarin Iyar su Bello ya tsinta, ruwan da aka yi ne ya korota makabartar su Iya. Ganin abin da ke hannun Bello da kuma yanda yanayin Usman ya canza gaba daya, dan yanda ya ke kallan sa tamkar aka ba shi wuka zai iya birma masa ya sa Baffa Mudi karasowa gaban su jiki sanyaye, gwiwowin su biyu ya durkusa gaban su tare da furta
"Na zalince ku, na ci amanar mahaifin ku, dan Allah ku yafe min kada ku tona min asiri! Duk abin da ku ke so ni me yi ne! Kai in har Shehuntakar Rugar nan ce ma ni na hakura na bar mu ku, Ni dai rufin asiri, kun ga dai ko ba komai ni kani ne gun Mahaifin ku, haka kuma ga iyali ga tsufa..."
"Ka san da haka ka aikta abubuwan da ka aikata?"
Cewar Usman cikin tsawa, be gushe ba ya kara da
"Ka cuce mu, ka cuci yar ka ta cikin ka ka cuci iyayen mu, Amma duka kan ka kafi cuta har ka na da bakin cewa a rufa ma ka asiri?"
"Dan Allah ba dan hali na ba! Ku tuna fa Allah na san rufin asiri! Ku rufa min asiri"
Cewar Baffa Mudi cikin rawar murya. Usman na duban sa ya ce
"In dai rufin asiri ne, za mu iya rufa ma ka, Amma da sharadi daya!"
"Koma menene sharadin na yarda! Zan bi!'
"Sharadin shi ne za mu bar wannan dajin, ba kuma zan hana masoyan ka zama da kai ba, Amma ko da wasa kada ka tako kafa ka zo in da mu ke! In ko ka kuskure ka biyo mu Baffa Mudi ko Kuma ka yi yunkurin lalata min tafiyar nan ta hanyar tsubbun da ka saba na lahira sai ya fi ka jin dadi!"
Baffa Mudi na mai jinjina kai ya ke fadi
"Na yarda Shehu adali, na yarda! Ka cika mai yafiya, in Sha Allah zan kiyaye sharadin ka"
Da haka ya tashi ya koma Rugar shehu cike da borin kunya. Usman kuwa wuta su ka sa suka kone layar da ke dauke da sunan Muhammadu Bello. Ranar wuni aka yi ana gayara makabarta, washagari da sassafe bayan Usman da Bello sun je sunyiwa Iyar su Sallama tare da addua, su ka tabbatar sun killace kabarin ta yanda ruwa ba zai taba tona shi ba, sannan su ka hada na su ya na su, kwansu da kwarkwatar su ka tasarwar barin dajin falgore. Baffa Mudi na ji ya na gani Usman ya kada duka Shanun da ya ke mallakin gidan Shehu be bar masa ko daya ba. Shanu ne masu yawa kwarai da gaske dan kuwa idan aka ce za a tsaya lissafa adadin su ace sharata ta ake. Haka kusan duka jama'ar Rugar Usman su ka bi, illa kalilan ne su ka tsaya tare da Baffa Mudi.
In da Rugar Shehu ke sauya sheka, gidan Malam kuwa auran su Halitta aka daura. Ba wani taro aka yi ba, auren kawai aka dora. Zainab ba ta halacci daurin auren ba bare ta kira amare ta mu su Allah ya sanya alkhairi. Babban bakin cikin ta shi ne tafiya Saudia da Sudais ya ke so yayi da Halitta a sakamakon aikin da ya samu a can. Zinaru kuwa a ranar aka mika ta dakin mijin ta.
Zainab sam ba ta canza zani ba, yanda ta ke rayuwa a da haka ta dora bayan ta koma makaranta, haka kuma ta sake bude saban account na Instagram bayan ta siyi dalleliyar wayar ta mai dauke da tambarin tufa ta cigaba da sharholiyar ta kamar yanda ta saba.
Satin su Usman da tawagar sa biyu suna yawo daga wannan dajin zuwa wannan dajin, su kutsa nan, su kutsa can, in da ya kamata a yada zango a yada cikin kokarin kare hakkin nomama ta hanyar kada shanun sa daga barin shiga gonaki, a haka har su ka iskewa wani daji arewa masogabashin kudu, dajin ya kasance mararraba tsakanin kudu da arewa.
Kasancewar dajin ya yalwatu da 'ya'yan itatuwa, ga ruwa da yanayi mai kyau, haka kuma aikwai wadataccan fili tuni su ka yada zangon su na zama dirshen, kwanan su uku suna gine ginan bukka, haka kuma masu ilimin surkulle su ma su ka dukafa wajan kafe dajin, suna shiga lungu da sako sai da su ka kafe dajin kaf ya zame mu su tamakar gida hatta macijan dajin sai da su ka san da kafuwar Rugar Shehu.
Cikin watanni biyu Usman ya kafa daular sa, Shehuntakar sa ta ginu sosai musammam da Allah ya hore masa ilimin da ya koya daga wajan Malam. Ganin yanda ya habaka gashi babu mata ne ya sanya magidan ta da yawa yiwa Usman tayin matar aure daga cikin yan matan Rugar Shehu, musammam yanda kowacce da ta ke ji da kan ta ke da burin kasancewar mata wajen Shehu. Amma Usman kullun cikin ba su uzurin cewa zai karba, Amma akwai wata ajiya da ya ke da shi birnin Kano, matukar ba ajiyar nan ya dauko ba toh be shirya aure ba.
Bayan wata biyu da sati daya da kafuwar daular Rugar Shehu, Usman ya shirya tsaf da shirin zuwa dauko ajiyar sa, in da ya wakilta Muhammadu Bello ya kula da Rugar su kafin ya dawo.
Komawar shi Kano ya so ba shi wuya kasancewar ba da mota su ka shiga dajin su ba, tafiyar kasa ce su ka yi mikakkiya. Da kyar da taimakon Allah ya sami motar da ta kai shi Mambila, daga nan ya sami motar Taraba, a can ne ya sami na Kano direct.
Ganin Usman da kuma yanda ya canza ya kara kwarjini kamar wanda ya sha maganin kwarjini ba karamin mamaki su Isa su ka yi ba, musammam Jauro da ya kama kan sa dan shi kan sa ya san akwai bambamci tsakanin Usman din da da na yanzu, har da yanda Ammy ta karbe shi hannu bibbiyu. Ta dawo Kano ita da Falmat bayan sun fita takaba. Bakin ta ya ke jin labarin auran Halitta wacce a yanzu haka ta na can Saudiya tare da mijin ta. Yayi murna kwarai tare da mata addua. Amma ko da Ammy ta kawo maganar Zainab, ta na mai tambayar sa dalilin da ya sa ya tafi babu sallama sai cewa yayi
"A yi hakuri abin ne ya zo min a gaggawa, shi ya sa ma na dawo na gyara, ta na nan ne?
Ya tambaya ko Zainab ta na nan ne ba dan ya na so ya ji amsar da Ammy za ta ba shi ba, abu daya da ya sani shi ne ya zo tafiya da ita, ko ta nan ko bata nan kwana daya kacal ya ba ta za ta dawo ta same shi har in da ya ke.
Ammy ce ta masa bayanin Zainab din ta na makaranta, jami'ar da ta ke yi a Yola, Amma kada ya damu ai ta ma kusa fara jarabawa, kuma da ta dawo be fi watanni biyu zuwa uku za su kara su gama makarantar gaba daya ma
'ai kuwa na ta makarantar ya kare daga gobe!'
Cewar Usman cikin ran sa, zahiri kuma cewa yayi
"babu komai ai kamar yau ne, Allah ya ba da sa'a"
BQ din nan dai da Malam ya basu nan aka sauke shi. Allah ya amsa adduar shi har lokacin akwai wasu daga cikin kayan Zainab, dan haka a daren ranar ya yanki daya daga cikin bakaken rugunan ta da ta bari a dakin, ya hada da wani ganyen turare da ya taho da shi daga Rugar Shehu. Sai da ya kulle dakin sannan ya hada garwashi ya ruru sosai yayi jajur, sannan ya dauki kyallen da ya yanka, ya hada da ganyen turare ya dora kan garwashin, yana murmushin mugunta ya ke duban yanda tufar ke konewa hayaki na ta shi, ya ce
"Kamar yanda tufar ki ke konewa haka zuciyar ki za ta na mi ki kuna matukar ba ki baro duk abin da ki ke kin zo gare ni ba Zainab, kamar yanda hayakin nan daya ke bin daya haka za ki bini duk in da na sa kafa....matata Abu"
***
Duk yanda Zainab ta so ta yi karatu daren ranar kasawa ta yi, ga shi ta na da jarabawar safiya. Washagari tun da asuba ta hado kayan ta, ba tare da ta nemi shawarar kowa ba ta na kallo kowa na shirin fita jarabawa amma ta tsallake ta dauki hanyar Kano a motar haya abin da ba ta taba shiga ba tun da ta fara karatu a Yola. Sai yamma likis ta isa Kano, wanda tun isowar ta jikin Usman ya bashi dan haka shi ma din ya fita kofar gida da shirin sa ba tare da ya bari su Jauro sun san da fitar shi ba. Be yi cakakken minti talatin da tsayuwa kofar gidan ba sai ga dan sahu ya zo ya tsaya gaban gidan Malam. Zainab ta fito sanye da bakar abaya, hannun ta rike da dan akwatin ta da ta debo kadan daga cikin kayan ta. Ta na sallamar dan sahu ta karasa gaban Usman ta tsaya, wanda tun saukowar ta ya tsura mata Ido cike da tsana. Wani farin mayafi da ya sha ado da kaloli irin na fulbe ya mika mata, Zainab ta sa hannu ta karba.
"Ki yafa shi yanzu"
Cewar Usman. Zainab ta amsa da toh sannan ta ware mayafin ta yafa.
"Sunan ki Abu...."
Cikin gasgatawa ta furta
"Sunana Abu..."
Usman ya kara da
"Ni mijin ki ne Shehu"
"Kai miji na ne, Shehu"
"Mu na hanyar komawa gida Rugar Shehu"
"Mu na hanyar komawa gida Rugar Shehu"
Zainab ta sake maimaitawa.
"Duk wanda ya mi ki magana a hanya kada ki tanka masa, matukar ba ni Shehu mijin ki ba ne ya baki umarni kin ji ko?"
Zainab ta na mai girgiza kai cike da ladabi ta furta
"Toh miji na Shehu..."
Kallan ta yayi sama da kasa ya gamsu da yanda mayafin da ta yafa ya dan ragewa rigar da ke sanye jikin ta kyau, cikin ran sa ya na mai neman yafiyar Ammy da Malam, ya ce da ita
"Biyo ni mu tafi!"
Babu musu Zainab ta bi bayan shi hanun ta rike da akwatin ta, ko waige ba ta yi ba bare ta tuna da gidan su ne nan ta bari.
*khadija sidi*Auren Shehu 2
2
Zainab na biye da Usman duk in da ya sa kafa nan ta ke dire na ta. Dan sahu ya tara ba su zame ko ina ba sai tashar Kano Line amma su ka yi rashin sa'a motar Taraba ba ta tashi sai sassafe. Direba ya dubi Zainab da gaba daya alamun gajiya ya bayyana a fuskar, a zahirin gaskiya idan aka dauke mayafin fulbe da ke yafe jikin ta, sam yanayin ta da zubin ta be nuna wani alaka tsakanin ta da Usman ba, Dan kuwa kana ganin Usman ka ga bafulatanin usul wanda babu wata alamun wayewa a tare da shi. Cikin dabarar Jin ko wacece Zainab ga Usman Driver ya kada baki ya ce
"Halan mikakkiyar tafiya ka yi tare da uwargiyar ta ka?"
"Eh mikakkiyar tafiya mu ka yi, haka kuma ita za mu tasarwa, shin ko akwai irin gidan kwana da ake biya nan kusa? Sai mu kwana washagari mu dau hanya"
Usman ya bashi amsa ba tare da ya fadi abin da Driver ke da muradin ji ba. Ganin yanda Driver ke kallan Zainab ba kakkautawa ya sanya Usman fadin
"Ni ta ita na ke ji ma, a gajiye ta ke...."
Driver na mai sosa kyeya ya ce
"Toh ka ga yanda za a yi, gida na nan kusa ne, ina da daki mai dauke da gado da katifa cikin zaure, haka kuma akwai bandaki ciki, ban fiye san saukar bakin da ban sani ba ciki, Amma ganin halin gajiyar da wannan baiwar Allah ke ciki, mu je sai na ba ku shi a kan naira dubu biyar..."
"Dubu biyar be yi yawa ba?"
Cewar Usman yayinda ya kai hannu aljihun shi domin jiyo lafiyar tattalin arzikin da ke ciki. Jin haka Driver ya ce
" Kai fullo ba dai san sisi ba, toh ai babu damuwa, kawo uku toh, ai matafiyi abin a tausaya masa ne"
"Toh babu laifi, gashi nan kirga ka gani"
Ya mika masa kudin da ya fidda daga aljihun sa. Driver ya dirga dubu uku cus sun cika. Sannan ya ce
"Toh Madallah sai ku shigo mota mu tafi nan tsallake ne ba nisa, ka ga da sassafe kafin shida sai mu fito mu yi lodi mu dau hanya"
"Abu shiga gidan baya mu tafi"
Cewar Usman cikin dakiya. Jin Zainab ta furta
"Toh Shehu mijin na"
Ya sanya Driver sake waigawa ya kalli Zainab kafin ya shiga motar ya tada cike da mamaki, ya tabbata dai wannan gabjejen bafulatanin Ruga majin wannan kyakkyawar yarinya ce, Driver ya dau hanya ya na al'ajabin yanda Usman ya tsinci dami a akala.
Kamar yanda Driver ya fada gidan na sa be da nisa da tashar. Dakin da yayi alkawarin bawa su Usman ya sauke su, babu laifi dakin be fiya dauda sosai ba, gadon gyare ya ke tsaf haka kuma kasan dakin shimfide ya ke da leda. Haka kuma akwai wutar lantarki. Daudar dai daya ne na rashin shara da dakin be samu ba. Shi ma din kafin su shiga Driver ya turo yaro daga cikin gidan sa aka share, tare da cire zanin gadon da ke shimfide bisa gadon, ya shimfida wankakken sai kamshin sabulun wanki ya ke, Sannan ya sa aka kunna mu su maganin sauro na igiyar leko, ya kuma debo ruwa ya zuba a robobin cikin bandaki. Yaron na shirin fita Usman ya tambaya ko akwai in da ake siyar da abinci nan kusa? Yaro ya ce babu sai dai akwai wajen me shayi ya na Kuma dafa indome. Usman na mai godiya ya sallami yaron da sauri saboda yanda wayar Zainab ta ishe su da kara. Ya na duban Zainab wacce ga wayar a hannun ta amma ta kasa dagawa saboda be ba ta izini ba.
"Waye ke kiran ki?"
Ko da ta duba wayar 'Ammy na' ta ga an rubuta, budar bakin ta sai cewa ta yi
"Wani suna ne wai Ammy na, haka dazu ma wasu su ka ta kira ban san su ba"
Zainab ta bashi amsa a sanyaye.
"Ki tura mu su sako na lafiyar ki lau, kada a sake kiran ki"
"Toh Miji na Shehu"
Cewar Zainab yayinda ta aikata umarnin sa. Yanayin gajiya da ta ke ciki da kuma yanda surkullen da ya mata ya kamata sam be saka tausayin ta ya tsirga zuciyar Usman ba, sai ma tsananin kiyayyar ta da ya ke ji cikin ran sa, da kuma bakin cikin da ke ziyartar zuciyar sa a duk sanda ya tuna ita ce sanadiyar rashin ganawar karshe tsakanin sa da Iyar sa.
"Ki kashe wayar kada ki sake kunna ta, zan fita na siyo abinci"
Cewar Usman cikin kokarin ficewa daga dakin, har ya kai kofa ya sake juyowa ya kara da
"Ki jawo kofa ki sa sakata idan na fita, kada ki budewa kowa idan ba ni ba ne, Ki yi wanka da sallah idan har ki na yi......."
Ya na jiyo amsar ta na
"Toh Miji na Shehu"
Ya fice zuciyar shi na tafasa na ba gaira ba dalili, shi kan shi ya san iya yan watannin nan gaba daya baya cikin hayyacin sa, babu abin da ke masa ciwo sai rashin Iya, yanayin da Bello ya shiga a sanadiyar Zainab da kuma dukan kawo wuka da aka yiwa Bello, duka a sanadiyar auren Zainab.
Bayan tafiyar Usman Zainab ta sa sakata kamar yanda Usman ya umarce ta, cire kayan ta tayi, tare da daura dan karamin towel din da ta saka cikin akwaitin ta. Cike da kyamkayami ta shiga bandakin, ba ta yarda ta tsugunna ba gudun daukar cutar bayan gida. Har ta gama wanka ta dauro alwala Usaman be dawo ba. Wata rigar baccin ta saka iya gwiwa mai dan karamin hannu sannan ta sanya hijabi har kasa ta shiga gabatar da sallah.
Idawar ta ke da wuya ta cire hijabi kan ta daure da kallabi ta ji ana buga kofa, ta karasa gaban kofar tare da fadin
"Waye?"
"Shehu"
Ya bata amsa a taikaice. Cikin rawar jiki ta bude kofar tare da fadin
"Sannu da zuwa"
Hanun sa rike da bakaken ledoji guda biyu, da kofi wanda ke fitar da turirin zafin bakin shayin da ya ke ciki ya wuce ba tare da ya tanka mata ba. Sai da ya aje ledojin da kofin shayin sannan ya daga ido ya kalle ta, tuni yayi saurin kawar da kai, cikin mummunar faduwar gaba, kan sa ya sara ganin yar rigar da ke jikin ta, da kuma yanda ya bayyana surar jikin ta duk da dai rigar ba matsattsiya ba ce, Zainab din ce MashaAllah. Cikin tsawa da fada ya ce
"Me ki ke jira a nan Abu? Ki rufowa mutane kofa ki zo ki saka hijabin ki! Kada ki sake yawo haka matukar ina wajen!"
A gigice Zainab ta rufe kofar tare da sa sakata, ta karasa da sauri hannu na rawa ta dau hijabin ta ta saka, can gefe ta sami waje ta zauna har lokacin gaban ta be bar faduwa.
Jin ta shiru ya dago kai ya dube ta, ganin yanda ta zauna ta yi shiru kamar ba tsigalalliyar Zainab din da ya sani ba, da Kuma kwallar da ta ciko idanun ta be sa yayi dana sanin ihun da ya mata ba, sai ma danasanin ganin surar ta da yayi da har lokacin ya ke masa yawo a idaniyar sa. Murya ya gyara ya na mai neman nutsuwar karfi da yaji, ya mata nuni da yatsa tare da fadin
"Ki zo nan ki ci abinci ga shayi nan shi za ki fara sha kin ji ko?"
Ya na maganar ne cikin dakiya. A hankali ta taso ta zauna in da ya umarce ta, shi ne ya bude mata ledar indomie din, yanda ya ga ta na ci hannu baka hannu kwarya ya tabbatar masa da cewa da yunwa ta wuni. Na shi ledar ya ja dan kuwa ji ya ke ya na bukatar kaɗaicewa a wannan lokaci, a hankali ya ja jikin sa ya fita ya bar mata dakin. Bakin kofar dakin ya zauna duk yanda ya so ya ci abinci ya kasa, tunani kala kala ke yawo cikin kwakwalwarsa, sam be da niya kuma ba zai yi danasanin tafiya da Zainab ba! Hakan shi ya fi cancan ta mutane irin ta!'
Furucin da zuciyar sa ke jaddada masa kenan har ya dan sami karfin gwiwar cin indomie din. Haka ya zauna a soro, 'ya'yan Driver na kai kawo haka na makota, har kafa ta dauke aka ma rufe gidan gaba daya. Nan soro cikin sauro ya kwana, da asubar fari ya buga mata kofa, ya ce ta tashi ta yi sallah ta yi wanka za su wuce.
Sai da aka idar da sallah sannan Zainab ta yi wanka. Ta na jiyo shi shi ma yayi na sa wankar tare da goge baki da dakakken gawayin da ya kullu tun daga Rugar Shehu. Cikin bandakin ya shirya tsaf ya fito cikin kayan saki riga da wando, haka kuma be fasa nada rawanin sa da bakin yadi ba. Ya na mai duban shigar da ta yi na bakar duguwar riga ya ce
"Ki cire kayan nan ki sanya hijabi"
Ga mamakin sa sai ga Zainab na kokarin zare ruga gaban sa, cikin tsawa ya ce
"Wai ke wata irin mara kunyar Bingel ce Abu???"
A dibirbice dan kuwa tsawar Usman rikita ta ya ke ta ce
"Ya zan yi miji na? Kai ka ce na cire rigar..."
"Mace da kunya aka santa duk da na dade da sanin ke ba ki da ita ko na miskala zarratun! Idan kin ga dama ki yi tsirara kafin ki saka hijabin!"
Ya na gama fadin haka ya bude kofa ya fice. Zainab ta yi kasake ta na kallan sa cikin tunanin laifin me ta yi har ran Mijin ta Shehu ya baci haka. Jin ya na buga mata kofa ta yi saurin saka hijabin haka ba tare da ta cire rigar ba, ta hade komai na ta cikin karamin akwatin ta ta fito.
A mota ta tarar da su, Driver ma ya fito ita kawai ake jira. Dan haka ta na shiga kai tsaye tasha su ka wuce. Nan tasha ya siya mata shayi da bredi ta ci kayan ta ba musu. Haka kuma ya siya mata silifas na roba ya ce ta cire mai tsinin da ke kafar ta, ya dau mai tsinin ya bawa wata yarinya mai tallar masara cikin tasha. Karfe shida daidai mota ta cika, su ka dauki hanyar Taraba.
Tafiya ce mikakkiya su ka sha, gashi sam hanyar ba kyau, ga checking point da yawa duk in da su ka tsaya kuwa sai sojojin nan sun tanka Zainab duk da can gidan baya su ke zaune tare da Usman. Yawanci su kance kamar sun san fuskar Zainab.
Ba su suka isa Taraba ba sai shida na yamma. Dake dama Driver da su ka kwana gidan sa ne ya ja su, Wajan kwana be basu wuya ba. Kamar yanda ya bata umarni ba ta cire hijabin ta ba, har sai da ya ce mata za ta iya cirewa ta yi wanka idan ta na so idan ya fita. Ya na ficewa ta cire hijabin ta sha iska.
Washagari da sassafe su ka sami motar Mambila. Shi ma din sai yamma likis su ka tasarwa shiga garin. Dake Mambila bisa dutse ne ko Dirobobi sai kwararru ne su ke iya hawa dutse, Zainab ba bata san sanda ta rugume Usman kam ba, ta na mai dora fuskar ta kan fadarsa sai da ya ji tsigar cikin sa ya tashi, haka kuma duk yanda ya so ya zare ta daga jikin sa ta ki, har sauran yan cikin motar suna mu su dariya. Haka babu yanda zai yi ya barta kwance jikin sa yayinda zuciyar sa ke bugawa tamkar za ta fado.
Haka tafiyar awanni ta zame masa tamkar gwale gwale. Suna Isa Mammbila ya banbare ta daga jikin sa ya fito daga motar ya bar Zainab ciki ta na mai raba idanu ta fito daga motar. Baki bude ta ke duban in da take, wato Allah mai hilitta yayi hilitta a kasar Mambila, ba ga kasar ba ba ga halittun da ke kasar ba.
Gari ne mai kyawun gaske da yalwataccen ni'ima, haka ma matan kasar don idan kaga wata ta keto daga gefan duwatsu gashi har mazauni ka ce gamo ka yi tsabagen kyau. Ganin dawowar Shehu da dama sun ga tafiyar shi ba karamin dadi su ka ji ba, sun karbe su hannu bibbiyu in da ya gabatar mu su dayl Zainab matsayin matar shi.
Daki na musammam aka ba su, haka kuma an ba su abinci mai kyau, ga fura da nono ga kayan marmari na daga 'ya'yan itace. Yanda su ke yarawa da Usman da kuma yanda ya ke musu fara'a ya sanya Zainab zuba masa idanu, ta na mamakin dama ashe Shehu mijin ta ya na dariya?
Usman ya so wucewa a ranar amma jama'ar Mambila su ka hana shi, su ka ce ya bari gari ya waye ido na ganin Ido duk da dai ba su san ainihin dajin da Rugar Shehu ta ke ba. Haka bai sa ran sa ba ya hakura su ka kwana, cikin dare matan da su ka zo su ka buga masa kofa tare da tambayar ko ya na bukatar yar tayin hirar dare Allah yayi yawa da su. Shi kuma be fasa ba su amsa da matar shi ba ta saba kwana ita kadai ba, Kar ya fito kiri kiri ya ce ba ya so wata ta kullace shi ta aikata masa wata kullalliyar. Sai ya tabbatar kafa ta dauke sannan ya fito waje ya bar Zainab ciki ta na baccin ta hankali kwance. Kofar dakin da aka bashi ya samu ya kishingida, Zainab ya ke gani cikin kayan bacci duk sanda ya runtse idanun sa, haka kuma sassanyar kamshin turaren ta da ya mamaye rigar sa sanda ta rungume shi a cikin mota. A fusace ya mike tsaye, tafiya ya ke tamkar zai tashi sama tsabagen bacin rai. Wani dan dutse mai rubar ruwa ya nufa, ya na mai cire rawanin kan sa ya tsaya karkashin sa ruwa na kwaranya bisa kansa ya na sauka gangar jikin sa. Sai da ya dau kusan minti talatin a wannan halin, zuciyar sa ta dan yi sanyi sannan ya fito ya zauna gefan dutsen. Wani irin iska ke kadawa ya na shiga jikin sa, idanun sa runtse kansa bisa dutse Allah ya kadai ya san awannin da ya bata nan zaune ya na ambaton sunan Allah. Sai da ya bushe tsaf zuciyar sa ta dan yi sanyi sannan ya tashi ya koma masaukin sa.
Da sassafe bayan sun yi sallama, an kuma hada mu su goma ta arziki na guziri su ka tasarwa Rugar Shehu haikan. Dake tafiya da mata sai a hankali duk yanda Usman ya so su yi sauri su isa Rugar Shehu ko ya rage tarayya da Zainab, abin ya gagara. Tun suna shiga dajin suna ganin yan tsirran mutane da yawancin su fulani ne masu kiwo ko mafarauta, har su ka dena ganin kowa sai bishiyu da halittun dajin da ba a rasa ba. Duk sanda lokacin sallah yayi Usman kan ce su tsaya su yi sallah, haka kuma be bar Zainab da yunwa ba duk da dukkan alamu ya nuna ta jigata kwarai da tafiyar kasa da suke duk da silifas ne kafar ta tun da su ka baro Kano.
Ko da su ka tsaya sallar la'asar nan Zainab ta kakare, tsabagen tafiya kafarta har ta fara kumburi. Amma Usman be tausaya mata ba bare ya ce su yada dogon zango, sai dai ta sami saukin daukar akwaiti, dan da tafiyar ta yi tafiya shi ya dauki akwatin.
Yana yin duhu da gari ya fara be sa Usman ya fasa tafiya ba, da taimakon tocila su ka cigaba da kutsawa cikin daji, Allah kadai ya san adadin macijai da Usman ya kashe, tun Zainab na saka masa ihu tare da dane jikin sa, har gajiya ya sa tsoran ta ya gushe, tafiya ta ke tamkar za ta fadi, ganin haka Usman ya ɗauke ta cak ya saba a kafada, ba ta jima ba baccin wahala ya dauke ta, a haka har su ka isa Rugar Shehu wajan karfe shabiyu na dare.
Rugar duhu dulum yawanci jama'ar rugar sun kashe fitilar su ta aci balbal sun kwanta. Sai matasa yan kalilan ciki har da Muhammadu Bello ne zaune suna hira, ganin mutum dauke da wani abu bisa kafada ga kaya nan hannun sa ya ruko ya na tafiya niki niki ya tasarwa Rugar Shehu ya sa su Muhamadu Bello zabura, su na mai daukar gororun su suka nufo Usman, cikin harshen fulatanci su ke fadin
"Kai hattara Nan! Waye Nan!"
"Usman! Shehun ku Usman!"
Usman ya ba su amsa ya na mai tadda su. Ganin da gaske Usman ne, dauke da mace su ka sauke gogorun su cike da mamaki, Amma aka rasa wanda zai iya budar baki ya tambayi baasi. Bello ya karbi akwatin hannun Usman har rumfar Shehu su ka raka shi, sannan su ka juya da tambaya fal bakin su.
Bello ne kadai ya tsaya taimakawa Usman ta hanyar bude ma sa kofar kara, ya daga assabari yanda Usman zai iya wucewa ba tare da ya buge Zainab ba. Bello na biye da shi su ka shiga dakin yayinda ya aje akwatin Zainab gefe. Bisa gadon kara Usman ya kwantar da Zainab tare da gyara mata kwanciya.
"Shehu ka dawo mana da sabon abu a wannan ranar"
Cewar Bello ya na duban Zainab da har lokacin bacci ta ke. Shiru ne ya biyo baya yayinda Usman ya zauna gefan gado yana duba kafar Zainab da ta kumbura. Ganin Usman be da niyar tanka masa ya saka Bello sake fadin
"Wacece wannan matar? Daga ina ka dauko ta? Shin ba ka gudun ace Shehu ya zama dan garkuwa da mutane kamar Tanko dan Baffa....."
"Bello!"
Usman ya dakatar da shi cikin tsawa hakan ya sa shi kame bakin sa. Ya juya zai fita ya ji Usman ya ce
"Ina so ka duba cikin garke, ka tatsar min nonan saniya mai dauke da juna biyu ka kawo min yanzun nan!"
Kallan sa Bello ya tsaya yi cikin faduwar gaba, kenan da abin da Shehu yayi ya dauko baiwar Allah nan ba wai cikin hankalin ta ta biyo shi ba.....
"Ka na nan tsaye ne?"
Cewar Usman wanda ya lura da halin rudanin da Bello ya shiga. Cikin azama Bello ya fice, Jim kadan Bello ya dawo dauke da kwaryar nonon da ya tatso, ya tadda Usman na shirin kunnan wani ice da su ke amfani da shi wajan koran soro.
Ya mikawa Usman kwaryar, bayan Usman ya karba yayi Bisimillah sannan ya fara karanto wasu adduo'i a zuci bakin sa na motsi, ya na gamawa ya tofa cikin kwaryar nonon yayinda ya fara kokarin tada Zainab. Cikin magagin bacci ta ke jin maganar Usman ya na fadin
"Tashi ki Sha Abu"
Hakan cikin mamagi Zainab ta kurbi nonon, ba ta jima da sha ba bacci mai nauyi ya sake dauke ta. Usman na duban Bello da ya tsura masa idanu cike da al'ajabi ya ce
"Ka jira ni daga waje"
Bello ya sa kai ya fice. Bayan fitar shi Usman ya cire hijabin da ke jikin Zainab saboda zufa da ke tsattsafowa daga jikin ta sanadiyar nonan da ta sha, ya rage daga ita sai doguwar riga ruwan hoda mara hannu, kan ta rufe da dankwali. Sai da ya karanta ayatul qursiya da falaqi da nasi ya tofe ta tsaf ya fito ya tadda Bello tsaye ya na ciran sa.
"Mata ta ce Muhamadu Bello"
Cewar Usman ya na mai kokarin cire rawanin sa. Mamaki ne ya bayyana fuskar Bello, kana ya ce
"Dama da gaske ka na da aure? Kar dai ita ce matar da ake neman sakin ta daga waje na?"
"Ita ce sanadin kashin da aka baka sanda Iya ta aiko ka kira na, haka kuma sanadiyar ta Iya ta kwanta dama ba tare da mun gana ba"
Usman ya bashi Amsa. Shiru ne ya biyo baya kafin daga bisani Bello ya furta
"Ya aka yi ta zama matar ka? Dama ka yi aure ban sani ba?"
"Zan maka bayani daga baya, yanzu na gaji matuka"
"Shin ya aka yi ta yarda ta biyo ka? Nonon da ka bata yanzu kar dai......?
Bello ya kasa karasa maganar cikin shakkar tambayar da zai yi. Usman na mai girgiza kai ya ce
"Kiranye?"
Bello ya girgiza kai. Usman na mai murmushin mugunta ya cigaba da fadin
"Tabbas shi na mata, shi ne hanya mafi sauki da zan iya taho da ita, ka ga wannan yarinyar da ke kwance bisa gado na? Hatsabibiya ce, fitinanniya ce dan haka kada ka taba tausaya mata! Idan har ka ga na mata wani abu na alkhairi toh ka tabbata darajar mahaifin ta za ta ci, na kuma ba ta makarin kiranyen da na mata ba don komai ba da dai ina bukatar ta cikin hayyacin ta, ina so na gan ta cikin kunci kamar yanda zuciya ta take cikin kunci!"
Jikin Bello ne yayi sanyi kwarai, tun da ya zo duniya be taba ganin Usman cikin halin bacin rai da neman daukar fansa kamar yanda ya ke a yau ba, shi da ya sha duka ma be kullece ta kamar yanda Usman ya kulla ce ta ba, lalle Zainab abar a tausaya mata ce tunda ta iya tado fushin mai hakuri, tabbas ta kai bango.
"Ka na nufin babu soyayyar ta cikin ran ka?"
Cewar Bello cikin adduar Allah ya saukaka. Usman na mai girgiza kai ya furta
"Daukar fansa shi ya kawo Abu Rugar Shehu, Abu ce mace ta karshe da zan iya so a duniya!"
Ya na gama fadin haka ya wuce ya bar Bello cikin tunani da sakar zuci.
*Khadija Sidi*
Auren Shehu 2
3
Allah yayi dare gari ya waye, carar zakara tare da kukan shanu, gami da guje guje da ihu da yara ke yi ne ya sanya Zainab sanya hannayen ta bisa kunnuwan ta, tare da runtse idanu, ga wani zugin azama da take ji a kafafun ta, haka kuma kan ta ya mata nauyi. Tun tana jin komai tamkar cikin mafarki, har ya fi karfin kunnuwan ta ya kai ga sanya ta bude idanu a hankali. Maimakon ta ga silin da fanka sai ganin karare ta yi jere reras, idanun ta ta rufe a karo na biyu ta na mai fatan farkawa daga mafarkin da ta ke. Ko da ta sake budewa ta ga dai har lokacin rufin kara idanun ta ke gane mata ta shi zaune a firgice ta na mai bin bukkar da idanu, bukka ce maidaidaciya wacce aka gina da jar kasa mai dauke da yayin ciyawa da rufin kara. A kideme ta kai kallan ta ga in da ta ke kwance, sai a sannan ta lura da gadon kara mai dauke da matacciyar katifar da ta ke zaune kai. A hankali ta ke karewa bukkar kallo tundaga ledar da ke shimfide kasan bukkar, har zuwa koren akwaitin karfe da ke aje gefe kusa da katan kwaryar da aka rufe da wani fefe, sai butoci guda biyu, na roba da na karfe.
"Mafarki na ke!"
Cewar Zainab ta na mai duban kayan da ke jikin ta, sam ta kasa tuna sanda ta sanya shi, abun da za ta tuna kadai shi ne sanda ta ke karatu cikin dare ba kayan ba ne jikin ta. Ta na jinjina kai ta kara fadin
"Da na gama karatu bacci ya sace ni, shi ne na ke mafarki! Da kabari kato ake yin shi da sai na ce mutuwa na yi, bari dai na koma bacci ko Allah zai sa na farka!"
Ta na maganar ne yayinda ta koma ta kwanta tare da rufe idanun ta. Jim kadan taurin gadon karen ya dame ta, haka ma hayaniyar yara da ta ke jiyowa daga waje ya sa duk yanda taso ta koma bacci ko Allah ya sa ta tashi ya gagara. Tsaki ta ja ta na mai tashi da sauri da niyar ta fita ta tsawatarwa ma su hayaniyar, ko da ta taka kafarta wani raradi ne ya ziyarci kwakwalwar ta har sai da ta koma ta zauna da sauri tana fadin
"Wayyoo Dady!"
Sai a sannan ta lura da yanayin kumburi da kafafun ta su ka yi. Hakan ne ya karasa ta tsorata da halin da ta tsinci kan ta ciki. A haka ta yi karfin hali ta tashi ta na mai takawa da kyar wanda duk sanda ta taka sai ta cije lebe har ta kai ga assabarin da aka saka bakin kofar daki, hannun ta biyu ta saka ta daga shi nan ta yi tozali da abin da tun da ta zo duniya ba ta taba gani ba, kanta ya zuye ya na mai sarawa ganin bukkai ba adadi, gabas da yamma kudu da arewa, Rugace ta gargajiya tsantsa in da jama'ar wajan mata da yara ke kai kawo cikin kwanciyar hankali.
Matan sanye da rigar saki irin na fulani mai hade da zani, in da wasu su ka sanya fari, wasun su shudi ne jikin su, duk da akwai dankwali kan su, sun saki jiki rabashe rabashe su na hidimar su, daga mai share na su bangaran bukkar, sai mai kwasar manshanu daga cikin kwaryar nonon da ta tatso tare da taimakon yara mata guda hudu wanda ba su fi shekara goma sha uku ba, can gefe kuwa mata ne guda shida wanda dudu ba za su haura shekara ishirin ba amma gaba daya cikin su ya sake saboda wahala, musammam kirgin su wanda ya ya kwanta sharkaf kamar tsumma, sun zage dantse wajan dakan geron fura. Kusa da su mata biyu ne zaune daga gani ka san kishiyoyi ne, suna cin abinci hannu baka hannu kwarya, daya daga cikin su dauke da yaro akan cinya ta tana ba shi nonan da tsabagen yanda ya kwanta kai ka ce tsumma ne. Daga can gefe kuwa tsoffine guda biyu zaune suna koyawa yara mata guda biyu da ke zaune gaban su sakar riga, wanda za su kimanin shekara goma. Sai kuma yara maza da ke wasan langa sun yi kacaca tsabagen wasan bazan da su ke yi cikin kasa. Sai kuma
Yaran ne su ka fara ganin Zainab wacce ta saki baki da hanci ta na kallan sarautar Allah. Shirun da yaran su ka yi ya ja hankalin iyayen su ka ankare da Zainab. Kamar yanda ta bude baki ta na kallan su haka su ma su ka bude baki su na kallan ta cike da mamaki. Sun ji labarin Shehu ya dawo da Kado Rugar Shehu, wanda har aka mu su kashedin kada wanda ya yarda yayi wani yare cikin Rugar face fulatanci, musammam ga Kado, Amma sam ba su taba tunanin irin wannan kadon Shehun su ya kawo Ruga ba.
Kallon Zainab su ke tun daga dankwalin da ke kan ta, zuwa doguwar riga mara hannu da ke sanye jikin ta, surar Zainab, da kuma yanayin fatar ta da ya fita daban, duk da yawancin su farare ne, ita baka ce amma yanda fatar Zainab ya ke subul subul ya na sheki kadai abin kallo ne.
Tuni su ka fara kuskus a junan su, in da yara su sa tafi suna fadin
"Kado! Kado! Kado"
Hakan ne ya sanya Zainab sakin assabarin da sauri cikin faduwar gaba, ta na dingishi jikin ta har rawa ya ke ta komo cikin bukkar. Cikin yanayin tashin hankali ta ke kara duban bukkar, gani ta ke kamar za ta ga wata alama da zai bayyana mata halin dimuwar da ta tsinci kan ta ciki.
Ganin jikin wani abu kamar akwaitin ta leko ta karkashin gado ya sanya Zainab ta karasa gaban gadon da dingishi, dan gaba daya ji tayi zafin kafar ya dena damun ta. Cikin zafin nama ta janyo akwatin, ganin nata ne da gaske ta ji wani dan sanyi cikin ranta yayinda ta bude da sauri ta na mai mamakin yanda aka yi akwaitin ya je in da ta ganshi ta zuge zip din akwatin, haka kuma kayan ta da ke ciki ya bata mamaki dan kuwa ba za ta iya tuna sanda ta jera kayan cikin akwatin ba.
Ciki ta yi kacibus da wayar ta, da murnar ta ta dauko wayar, hannu na rawa ta kunna ganin a kashe ta ke. Allah Allah ta ke ya gama kunnuwa ta samu ta kira waya ko Allah ya sa ta sami mafita, amma ko da wayar ta kunnu ta shiga cikin wajan kira sai taga anbuga mata waya a adadi, kuma duka miskul ne, kiran Ammy ya fi sau goma, haka ma na Falmat da sauran yan ajin su. Sakon waya kuwa su ma ga su nan birjik.
Jin wayar na kugin neman chaji ne ya sa Zainab dena duba kira da sakonnin da aka tura mata, ta shiga kokarin kiran Ammy kafin wayar ta mutu, Nan ma wani tashin hankali ne ya ziyarci idanun ta, domin kuwa wayar nunawa ta yi ba za ta iya kiran kowa ba sanadiyar rashin sabis, haka kuma wajan da ke nuna alamar sabis a wayar ma ya dauke gaba daya, a sannan Zainab ta dada jaddada kalmar 'babu sarki sai Allah'
Zufa na ketowa daga goshin ta rufe akwatin, hannun ta ruke da wayar ta tashi tsaye ta na dingisawa ta sanya silfas din da ke aje kusa da akwatin na ta, ta ja akwatin yayinda ta bude assabari ta fito waje, cak ta tsaya ganin yanda yaran nan da iyayan su duka su ka baro abin da su ke, su ka yi da'ira bakin kofar bukkar Shehu kamar masu jiran tsammani.
Babban abin da ya kara tsorata Zainab shi ne yanda su ka karu dan kuwa har na gona sai da yaran nan su ka je su ka kira su zo su ka ga Kado a dakin Shehu. Zainab na mai ja da baya cikin dakiya da rashin nuna tsoro ta ce
"Ban san ko su waye ba! Ban san wata duniya na ke ba! Ban kuma damu da na sani ba! Roko na daya dan Allah....ku nuna min hanyar da zan koma tawa duniyar! Kada ku cutar da ni....."
Inda Iyayen yara su ka zubawa Zainab Idanu ba tare da sun tanka mata ba, yaran kuwa matsawa su ka yi kusa da ita suna kokarin taba akwatin ta, Zainab ta matsar da shi cike da kyamkayamin yara, ba ta ankara ba daya daga cikin yaran ya kai hannun sa kan wayar da ta har ya na taba hannun ta, cikin tsawa Zainab ta furta
"Stay away from me stupid boy kawai mara kunya da tarbiya! Sai na ci uban ka wallahi!!!!"
Yaro yayi baya da sauri haka ma sauran yan uwan sa, wanda daga baya su ka sanya dariya su na mai tafa hannu sanadiyar karar rashin chajin da wayar Zainab ta yi ta na mai kawo wuta. Zainab na girgiza kai ta ce
"Innalillahi wainnailaihi rajiun!"
Ta na ja akwaitin ta ta nufo iyayen yaran in da su kuma suka fara ja da baya, yara kuma ba su fasa shafa akwatin Zainab ba, inda ta ke kokarin hana su ta hanyar jijjiga akwaitin, ce mu su ta ke
"Dan Allah ku taimaka, ku min magana ko na sami sauki"
Ga mamakin ta sai ji tayi sun fara mata magana amma da fulatanci, a fusace Zainab ta ce
"Dallah ku yi min hausa ba na jin yaren da ku ke min! Sokwaye kawai!"
Maimakon ta ji hausan da ta ke bukatar ji, sai ma dada yara mata su ke cikin yaran fillo. Hakan ya sa Zainab fusata, ta na jan akwaitin yayinda ta ke dingisawa ta bi hanyar da ta ji ta kwanta mata ta na tafe yara na biye da ita suna tafa hannun ganin yanda Zainab ke jan akwaitin ta mai taya ne ya fi burgesu, tafi su ke suna fadin
"Kado! Kado! Kado! Kado"
Haka kuma masu kiriniyar cikin su ba su fasa kokarin taba akwati da wayar Zainab ba, haka su ka mayar da ita tamkar zararriya yayinda hawayen bakin ciki ya cika fal idanun ta. Fadi ta ke
"Madness! Mad people everywhere! Wallahi zan ci uban ku! Shegu 'ya'yan asara!"
Usman kuwa tun sassafe ya tafi fadar shi da ke can gefan bukkokin Rugar Shehu. Zaune ya ke da dattawan gari da kuma matasa, kasancewar shi ne ranar zaman fada na farko tun tafiyar Usman ya sanya babu wanda ya je kiwo ko gona, kowa ya hallacci zaman. Maganar Zainab kowa ke son ji daga bakin Zainab, Amma shakkar Usman ya sa su kasa bude baki su tambaye shi.
Zaune su ke kan tabarma karkashin katuwar bishiyar mangaro da ta yi mu su lema, Usman sanye cikin farin yadi da farin rawani wanda shi ya banbantashi da sauran jama'a da ke sanye da kayan saki, a matsayin shi na Shehu.
Ana tattaunawa ne akan sabbin tsari da dokokin da Usman ya kawo wanda za su shafe wanda su ke yi a da, sun hada da wajabta sanya mayafi ga duk wata mace baliga, dena shiga sassan da ba na iyalin ka ba kai tsaye ba tare da neman iso ba, dena koyar da karatun surkulle in da za a musanya shi da karatun qur'ani zalla.
Tun daga nesa ya hango ta tafe, yara da iyayen su biye da ita, haka shi ma Muhammadu Bello wanda ke zaune gefan Usman ta hannun dama ya hango ta, tun daren jiya ya ke fargaban tashin Zainab, ilekuwa sai ga abin da ya ke tsoro na faruwa. Usman na mai aje takardar da ke hannun shi ya tsaya cak yana tsimayin karasowar ta, haka ma sauran yan fada wanda su ka lura da inda hankalin Shehun na su ya tafi, su ma su ka zubawa sarautar Allah idanu yayinda Zainab ke dada matsowa gare su.
Tun da ta hango mutane zaune zuciyar ta ke Allah Allah ta karasa gaban su kila ta samu masu hankali ciki, idan har ta damu da zugin azabar da kafarta ta ke mata, ba ta nuna ba, sai dai dinkishin da take yi ne zai tabbatar da azabar da ta ke ciki. Ganin wani zaune tsakiyar mutanen, da kuma yanda shigar sa ta banbanta da na su ya tabbatar ma Zainab da shi ne shugaban Rugar, cikin fatan neman doki ta karasa. Zuciyar ta daya ta fara kokarin kutsawa ta cikin tarin mazan domin karasawa ga Shehu ta na fadin
"Ku matsa dallah! Malam matsa dallah!"
Duk da ba dukanninsu ne su ka fahimci abinda ta ke fada ba, ganin yanda ta tasar mu su da sauri su ka dara mata hanya, suna mai binta da kallo cike da mamaki har ta kai ga gaban Usman, idanun ta kan yaran da tun da su ka iso gaban Usman kowa ya nutsu kamar ba su ba ne su ke mata tafin atile ba, Zainab ta ce
"Kai ne shugaban wannan shedanun yaran da mahaukatan Iyayen su....."
Juyowa da ta yi ta kalli Usman wanda lafazan Zainab ba karamin tunzurashi yayi ba, ya tashi tsaye haka ma sauran yan fada su ka yi yunkurin tashi amma ya musu alama da hannu da su zauna. Zainab na girgiza kai ta ke nuna shi da dan yatsa, tsayin shi, fadin shi, da idanun shi ne ya kara tabbatar mata da Usman din ne, Abu na farko da ya tsirga zuciyar ta shi ne zaton ta ya tabbata, Usman ya cika dan garkuwa da mutane, gashi ya dauko ta duk da ta kasa tuna yanda aka yi . Cikin faduwar gaba ta saki akwatin hannun ta yayinda ta zube kasa, ta zauna dirshen ta na duban kasa tamkar mai nazari.
Yanda Zainab ta firgita da ganin shi, da kuma yanayin da ganin na shi ya sanya Zainab ciki ba karamin faranta ran Usman yayi ba dan a tunanin shi ta karaya ne. Jin Zainab ta furta
"Ya aka yi ka kawo ni nan? Menene dalilin ka na kawo ni nan?"
Usman ya tsaya ya na duban ta kamar yanda sauran jama'ar su ka zuba mata Ido. Ganin be da niyar amsa mata ta tashi a fusace dan masifa ma mancewa ta yi da kafar ta, sai da ta taka kafar ta cije lebe cike da azaba, ta na dingisawa ta karasa gaban Usman hannu a kugu take magana cike da tsiwa
"Dan ka na dan garkuwa da mutane ba wai zanji tsoran ka ba ne! Tun ranar farko da na dora idanu kan ka na san kai wanene! Dady ka yaudara har ka masa rufa ido ya kasa gane kalar ka! Haka Anty Sauda da Ammy su ka ki yarda da ni akan a min katangar karfe tsakanina da mugu irin ka! Nawa ka ke bukata? Nawa ka ke bukata ka mayar da ni gidan mu?? matsiyaci kawai!"
Ganin yanda Zainab ke yiwa Shehun su magana cikin tsawa da tsiwa ne ya sa matasa tashi tsaye cikin fushi suna mai yiwa Zainab ihu, da harshen fulatanci su ke fadin
"Karyar ki ta sha karya kado! Ki tuba ko kuwa muna tasar miki da bugu"
Ganin haka Zainab ta yi baya a tsorace kamar mai shirin ranta a na kare. Usman ya daka mu su tsawa cikin harshen fulatanci, ya ce
"Kada ku kuskura! Mata ta ce! Ni kadai na ke da ikon hukunta ta!"
Gaba daya su ka runsunar da kai sannan su ka koma wajan zaman su suka zauna, hakan ne ya bawa Zainab damar cigaba da tsiwa duk da cikin ranta ta gama tsorata da Usman, tsoran ne ba ta san nuna masa gudun kar hakan ya bashi damar cutar da ita, cikin karfin hali ta furta
"Ihun ku na banza ne dan ba ku bani tsora! Ku tambayi dan uwan ku ku ji yanda ya sha dakyar hannun sojoji!"
Usman ya kai kallan sa ga Muhammadu Bello, wanda ya kawar da kai gefe yayainda ya tuna kashin da ya sha a barikin soja. Cikin danne zuciya Usman ya mayar da kallan sa ga Zainab, wacce ba ta gushe ba ta cigaba da fadin
"Wallahi tun kafin na sabar maka ina mai baka umarnin ka yi duk yanda ka yi na wayi gari a nan ka mayar da ni makaranta! ba na san iskanci ban da lokacin batawa jarabawa na ke Idan ba haka ba sai na lahira ya fi ka jin dadi, kai ba kai ba har wa'annan yen koran na ka"
Ta karasa maganar ta na mai nuna jama'ar wajan da dan yatsa.
Cike da isa Usman ya koma wajan zaman shi ya zauna kamar ba da shi Zainab ta ke magana ba. Daya daga cikin dattijawan ne ya kada baki cikin harshen fulatanci ya ce
"Shehu ka gafarce ni, wannan mata taka sam ba ta da tarbiya, ba ka tunanin zaman ta a wannan Ruga za ta iya lalala ta mana tarbiyar yaran mu da matan mu?"
Sauran dattawa su ka goyi bayan shi ta hanyar jinjina kai. Wani ya kara da
"Shehu duk matan da ke Rugar nan, ga 'ya'yan mu amma ka rasa wacce za ka aura sai Kado? Wacce ba ta san darajar Shehu ba bare na al'ada ba? Ji fa yanda ta tsaya kerere gaban mu muna dattawa, ba kunya bare tarbiya"
Shehu na murmushi ya mayar musu da amsa cikin hausa ya ce
"Ba a san rai na aka daura min ita ba, sadakar ta mahaifin ta ya bani! Tabbas ba ta kai darajar matan Rugar Shehu ba, dan haka kada ku damu tamkar baiwa ta ke a Rugar nan"
Yanda Zainab ta kai hannu baki ta na kallan shi tamkar wacce ta ke shirin burma masa wuka, ya sa Usman canza harshe, dama yayi hausan ne saboda ta san abin da ya ke fada, ya na murmushi yayinda mazan wajan daga samari har dattawa ke kallan Zainab cike da mamaki, matan wajan kuwa dariya su ka sa bayan Usman ya dada maimaita musu cewa sadakar Zainab aka bashi, haka kuma ba takai matan rugar su daraja ba. Cikin ihu kamar mai shirun rufe shi da duka ta ke fadin
"Ka yi hausa mana! Idan ba munafunci ba ka yi yaran da na ke ji! Ni ba sadaka ba ce! Ba zan taba zama matar ka ba! Ni ba baiwar ku bace! Bloody fool! Ka mayar da ni na ce!"
Hankali kwance Usman ya ce
"Ni na kawo ki nan? Ko kin ga sanda na dauko ki? Ki tuna yanda aka yi ki ka zo sai ki koma da kan ki, matukar ba haka ba ki shirya zama karkashi na a matsayayin miji ke kuma baiwa ta......."
"Ba za ka taba zama miji gare ni ba! Uban kuturu yayi kadan! Ni ce baiwar ta ka? Ka san dawa ka ke kuwa? Da na zauna karkashin ka gwara na kwanta kabari!"
Ta katse shi a fusace, ta na mai daukar akwaitin ta ta furta
"Fine zan nemi hanya ta da kai na, Amma dukkan ku ku kuka da kan ku! Sai kun dandana gudar ku!"
Ta fara jan akwaitin ta, wayar ta dake ta kukan neman chaji ta duba ko alamar sabis ya dawo, fadi ta ke
"Wawaye jahilai kawai! no wonder aka ce a guji iskancin bakauye! Kun ci sa'a network di na ya dauke da ban ma tsaya musayar magana da almajirai irin ku ba, ka yi da diyar halak"
Ko da ta karasa wajan yara da iyayen su mata, sai su ka ki dara mata hanya, a fusace ta ce
"Dallah ku matsa min na wuce! Duk karnin manshanu ku ke da warin rana! Ga warin talauci! Kai wannan masifa har ina! Kazamai kawai!"
Ganin da gaske ba su da niyar matsawa ya sanya ta juya ta kalli Usman
"ka fada mu su su bani hanya ko na ci kaniyar su wallahi!"
Usman ya kawar da kai gefe ba tare da ya tanka ba, Bello ne ya taso ya ce da mata da yaran su bata hanya ta wuce cikin harshen fulatanci sannan su ka buda mata hanya, sai a sannan Zainab ta gan shi da kyau, ta gane shi ne kanin Usman da aka kamo. Ta na duban Bello ta ce
"Halan ba ka bashi labarin kashin da ka sha ba ne shi ya sa be daddara ba! Toh tun wuri ka masa bayani idan ma giyar wake ya sha gwara ya wattsake! Sakakkaru kawai!"
Tana gama maganar ta ja akwaitin ta. Bata kula da kugin yunwa da cikin ta ya ke mata ba, bare ta tuna da sallar asubahi da ke kan ya, ta na takawa da kyar ta doshi wata yar siririyar hanya da take tunanin shi zai fitar da ita hanyar da zai sada ta ga titin barin Rugar Shehu, nan kuwa bata san dokar daji ta kara nufa ba. da sauri Bello ya dawo wajan Usman ya ce
"Ta tafi fa Shehu, hanyar da ta dosa hanya ce da zai kara batar da ita cikin dokar daji, ka ga yanda ta ke tafiya da kyar, gashi akwai hatsari sosai cikin dajin kasan bata daya daga cikin mu, halittun dajin ba su san da zaman ta ba kada ta je ta hakala, ba za ka dakatar da ita ba?"
Usman na duban mata da yara ya ce kowa ya koma harkokin sa, haka kuma ya gyara zama in da ya ba da umarnin su cigaba da tattauna abin da su ke tattaunawa kafin zuwan Zainab. Ganin haka Bello ya san Usman be da niyar amsa masa, dan haka shi ma ya koma wajan zaman sa, zuciyar na da tunanin dangantakar da ke tsakanin Zainab da Shehun su, da kuma halin da Zainab za ta iya shiga cikin dokar daji.
*Khadija Sidi*
Auren Shehu 2
4
In da Ammy da Anty Sauda ke cikin fargaban halin da Zainab ta ke ciki, Zainab kuwa kasa daurewa ta yi, cikin akwatin ta ta sami dankwalin wata atamfar ta dinkin doguwar riga, hannun ta dauke da buta ta sa kai ta fito daga bukka.
Hankalin ta yayi gaba bare ta lura da jama'ar da ke kallan ta, ta na dingisawa kai tsaye bandakin da aka nuna mata ta sake komawa. Ta na shiga ta sami busasshen waje nan ta baje dankwalin ta saboda gudun cutar bandaki, sannan ta tsugunna ta gandara kashin ta sai da ta kasayar da komai sannan ta dawo hayyacin ta. Cike da kyamkayamin kan ta ta matsa daga gefe ta yi tsarki, Nan ta bar mu su kashin ta fito ta na yarfe hannu ta shige daki cikin akwatin ta ta dauko sabulun wankan ta da Allah ya sa ta hado da shi, ta sake fitowa tsakar gidan tana waige waige ko Allah ya sa ta ga boki.
Allah ya taimake ta ta hangi bokitin karfe, cikin dauriya ta karasa wajan bokiti, ganin babu komai ciki ta zara ta na waigawa lungu da sakon nema ma'ajiyar ruwa. Ta karaci waige waigen ta ko rijiya ba ta hanga ba bare famfo, haka kuma tambayar jama'ar gidan da suka mayar da ita tamkar talabijin bata lokaci ne. Idanun ta ne su ka sauka kan randuna manya guda uku, duka rufe da murfin langa, kawannan su da moda bisa kai. Kai tsaye ta nufi randar, ta fara duba na farko ta ga ba ruwa, na biyun kuma ruwan ya kai rabi, sai na ukun ne cike da ruwa. Wani dan yaro ta kalla ta ce
"Kai zo ka zuba min ruwa...."
Yaro ya tsaya ya na kallan ta ba tare da ya motsa ba, Zainab ta ja tsaki yayinda ta aje bokitin, hannun ta na dama ta sa ta bude randar, da modar da ta gani bisa randar ta debo ruwa ta na mai murzar sabulu ta wanke hannun ta, sannan ta goga sabulun cikin bokitin ta na cudawa da hannun ta. Kan ka ce me tuni yara sun matso suna mamakin kumfar da sabalun Zainab ke bayarwa, dan kuwa ba kowa ba ne ke samun damar wanka da omo bare kuma uwa uba sabulu.
Sai da ta wanke bokitin tas, ta dauraye da ruwan randar nan da dama rabi ne ciki, har ta karar da ruwan, sannan kuma ta bude randar da ke cike da ruwa, Amma babu damar dauka, hannun ta ruke da sabulun ta, ta jefa modar cikin bokiti ta fara ja, ta yi ta na hutawa haka kuma ruwa be fasa zubewa ba, haka ta shige bukka ta na jiyo maganganun mata gidan da ta tabbatar da ita su ke akan ruwan da ta kwasa.
Cikin bukka ta aje bokitin gefe guda, tana mai tura kwararen abincin da aka aje mata karkashin gadon kara, ta sa hannu ta tattare yar ledar da ke shimfide, da ke dama ba wata ledar arziki ba ce, bukkar ya zama sai kasa ne kamar yanda tsakar gida da bandaki. Assabarin daki ta saka ta na fadin
"Duk wanda ya shigo kan sa yayiwa in ba dai wannan tsinannan ba ne"
Ta na mai juyawa kofa baya ta cire kayan ta, ya rage daga ita sai dan fantari. Nan tsakar bukkar ta dau moda ta shiga kwararawa jikin ta ruwa, duk sanda ruwan ya sauka jikin ta sai ta kusan shidewa tsabagen sanyi, Amma haka ta zake dantse ta cigaba watsa ruwa ta na kwashewa Usman albarka.
Can tsakar gida kuwa kanwar mahaifyar Usman wato Iyalle ce ta shiga bandaki, Nan ta tarar da kashin Zainab malale bisa dankwali. Ta juyo ta na salati da sallallami ta ke shedawa jama'ar gidan ta'asar da Kado ta mu su na bahaya a bandaki. Hansai matar Kawu Iliya wacce dama ta fi kowa zafi cikin gidan ce ta fusata cikin harshen fulatanci ta ce
"Kan uban can! Kashi ta mana a bayi? Ita sarauniya ba za ta iya yankar daji ba? Nan fa kuna kallo ta kwashe ruwan shan gidan nan kaf ta shige daka da shi! Zan yi magana aka hana ni! Wallahi ba za sabu ba!"
Fuuuu ta wuce bukkar Usman, su Iyalle na tsayar da ita amma ta mu su banza, ta na isa bakin bukkar ta sa hannu ta daga assabari ta cusa kai, Nan ta yi arba da Zainab daga ita sai fantari ta juya baya ta na saba jikin ta sabulu. Hansai ta saki assabari ta na salati har da kuka fadi ta ke
"Innalillahi ni Hansai an cuce ni! Wayyo na shiga uku na lalace wannan Kadon be da mutunci! Wayyo na yi gamo Allah ya isa ban yafe ba! Wayyoo...."
Da gudun ta ta bar bakin kofar bukkar in da ta tsugunna musu a tsakar gida ta na rafka ihu kamar wacce aka aikowa sakon mutuwa, jama'a na tambayar ta lafiya amma ta kasa magana sai nuni ta ke ga bukkar Shehu, Iyalle ta yi kokarin zuwa ta duba abin da ya birkita Hansai haka amma Hansai ta ruke kafar ta, fadi ta ke
"kada wanda ya je kusa da bukkan can! Ku kira Shehu! Fitina ta sauka Rugar Shehu! Masifa ta saukar mana!"
Zainab kuwa tun da ta ji alamar an daga assabari gaban ta ya fadi, jin salatin mace ya tabbatar mata ba Usman ba ne ya leko, cikin azama ta dauraye jikin ta tas ruwa na malalewa tsakar dakin. Bisa gadon kara ta haye, tana daga durkushe ta fitar da dan towel din ta ta tsane jikin ta sannan ta daura, ko da ta duba ta ga tana da fantari har hudu cikin akwatin ta, wulgi ta yi da wanda ta cire. Kaya set biyar ne kacal cikin jakar, atamfa dinkin doguwar riga guda uku, duk da akan kallabin daya daga ciki ta yi kashi, sai kuma dogwayen ruguna, wanda ta bar makaranta sanye jikin ta da shi, da kuma wata koriya mara hannu, sai panties guda hudu, da bra guda hudu, sai kuma bumshort din ta guda biyu da yan rugunan su suma guda biyu. Koriyar doguwar rigar ta fitar, cikin azama ta ke shiryawa saboda hayaniyar da take jiyowa daga waje duk da dai ba ta san takamammen abun da ake cewa ba.
*****
Usman na zaune fadar Shehu, tattaunawa su ke akan maganar cigaba da Shehu ya kawo mu su, wato na azancin Shugaban kasa Muhammdu Buhari akan 'Ruga settlement policy'. Cewar shi zai so ace Rugar Shehu na daya daga cikin Rugar da za ta amfana da wannan tsari da shugaban kasa ke kokarin kafawa cikin kasar Nigeria. Kawu Iliya ne ya nisa, kana ya ce
"Allah ya gafarta Shehu, ban tari numfashin ka ba, na san ka yi zaman birne, Kuma ka san halayyar Kado, Kado ba mutunci sai shegen san zuciya! shin ka na tunanin wannan ba wani salo na zalunta da toye hakkin mu fillo na ne? Ace za a killace bafulatani da shanun sa waje guda? Ba kiwo ba yawo? Ni fa na fi zatan hadi ne! Hadin baki ne da manoma domin a tauye hakkin mu!"
"Fakat! Fakat!"
Cewar sauran jama'a cikin nuna amincewa da da maganar Kawu Iliya. Wani ya kada baki ya ce
"Wai tunda mu ke kun tabajin wani shugaba a kasa nan ya taba waiwayar mu? In ba da tsiya ba ko laifi, sai dai fa ace mun haura gonaki a taro mu! Ko kuwa a kira mu yan ta'adda ma su kidinafan"
Shehu na mai jinjina kai ya ke jin jawabin su. Wani matashi ne ya ce
"Ni kuwa sai na ga kamar cigaban ne da gaske, matukar za a kawo mana asibiti, da makaranta da wutan lantarki...."
"Asibiti? Makaranta?wutan lantarki?"
Wani Dattijo ya katse shi a fusace, kana ya kara da
"Su kawo mana makaranta irin ta su ta boko su lalata tarbiyar 'ya'yan mu musammam mata ko? Ko kuwa asibiti za su kawo mana daga nan su cusa mana hana haihuwa? Su hana matan mu haihuwa dama sun ce mun fiya haihuwa, to dan Allah idan ka dauke saduwa da matan mu wani abu ne ke kawo mana jin dadi ko nishadi duk duniya? Ina su ke so mu sa kan mu ne saboda Allah? Matan mu idan sun kai ma su tallan nono su hure mu su kunne wasu har cikin shege su ke kawo mana, yawanci 'ya'yan shegun su ne ke girma su ke koma mu su kidinafas!"
"Gaske Malam Madu, maganar ka gaskiya ta ke!"
Shehu na duban su ya furta
"Na ji koken ku duka, na kuma fahimta, Amma zan so mu dubi wannan lamarin ta bangaran amfani da masalaha......"
Tahowar yaro da gudun famfalaki ne ya katse Usman, yaro na haki yayinda ya karasa gaban Usman ya zube har kasa tare da fadin
"Allah shi taimaki Shehu, gida dai kam babu lafiya, Hansai ta na can Kado ta sa ta kuka har da firgici, Allah kadai ya san abin da ta mata...."
Usman yayi zumbur ya tashi rai bace cikin ran sa ya na ayyana hukuncin da zai aikata matukar Zainab ta cutar da al'umar Rugar sa, Musammam ma ahalin gidan Shehu.
"Ka ga sharrin Kado ai, ga shegentakar nan ai, ita dai tilo tun da ta wayi gari cikin Rugar nan ba ta bari an huta ba! Kado ba mutunci! "
Cewar Kawu Iliya. Bello ne ya tashi tare da fadin
"Bari na je gidan na ga abin da ke faruwa"
"Ni zan je da kai na, ku yi hakuri yanzu za a kare zaman yau, sai kuma Allah ya kai mu gobe, bissalam"
Ya na fadin haka ya zura takalmin sa, yanda ya ke tafe cikin sauri kadai ya isa ya nuna yanayin bacin ran da ya ke ciki.
Auren Sheshu 2
4
Tafiya ta ke ta na dingisawa, tsoron duhun daji be hana ta kutsawa cikin dajin ba dan kuwa a zaton ta za ta iske titi nan kusa. Yanayin duhun bishiyoyi da kuma kukan tsuntsaye da birrai ne ya hana ta zama duk yanda ta so ta zauna ko tafin kafar ta zai sarara daga zugin da su ke mata. Ta na tafe tana kwashewa Usman da jama'ar Rugar Shehu albarka, hannu daya na jan akwatin ta da ke makalewa cikin itace lokaci lokaci, dayan kuma ruke da wayar ta, har lokacin ba ta fasa neman sabis ba ta na ta gwada numbobin waya ko zai shiga. Ganin hasken rana kusa ya sanya ta kara himma a zaton ta titi za ta bullu, ko da ta karasa sai ganin ta ta yi cikin wani fili mai bishiyu yan tsirara wanda hakan ne ya bawa rana damar haskaka filin. Wayar ta ta yi kukan karshe sai dib ta dauke gaba daya chaji ya kare.
Cike da taikaici Zainab ta karasa inuwar wata yar bishiya yayinda ta yi cilli da akwatin na ta gefe guda ta zube a kasa ta na kuka mai fitar da sauti, ji ta ke ina ma bacci ta ke Allah ya taimake ta wani ya tashe ta da kuwa duk abin da wanan nan zai ce ya na so daga gare ta sai ta masa. Sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi shiru sai ajiyar zuciya cikin ranta ta na mai tunanin mafita
Sam ba ta lura da lallausan abin da ta kafar ta ke take kai ba, bare ta ankare da katoton koran macijiya wanda ake kira kasa da ke kwance karkashin in da ta aje kafar ta ta ba ta na bacci. Sai da kasar ta dan motsa kadan sannan ta ankare, tsabagen firgice kasa ihu ta yi, haka kuma ta kasa tashi ta ruga dan karshen tsami kafar ta tayi dan zaman nan da ta yi bayan ta gama fama kafar. Dan rarrafawa ta yi ta na mai cije lebe yayinda duwatsu da itacen wajen ke sukar gwiwowin ta ta cikin duguwar riga, sai da ta tabbatar ta yi nesa da macijiyar sannan ta yi zaman ta dirshen a kasa tamkar zararriya. Hanyen ta biyu ta saka ta rufe fuskar ta tana fadin
"Innalillahi wainnailaihi rajiun! Allah ka fitar da ni daga wannan kangin rayuwa, Allah ka kawo mafita, Allah ka kawo min doki....."
Kamar daga sama ta ji muryar shi ya ce
"Bar kuka Abu, Allah ya amsa gani ya kawo ni!"
A firgice ta dago kan ta, ganin wanda ke tsugunne gaban ta, idanun sa har sheki suke, duk da rabin fuskarsa rufe ya ke be sa ta kasa ganin murmushin mugun ta da fuskar sa ke dauke da shi. Wani irin tsanar sa ce ta mamaye zuciyar sa, kai tsaye ta furta
"Na tsane ka!"
"Alhamdulillah! Dama na fi so ki tsaneni, me zan mi ki ki kara tsana ta? Dan Allah ki ta tsana ta har illa mashaAllah! Ni Usman na mi ki alkawari zan mi ki rainon wannan tsana da ki ka mi ni!"
Cikin rashin fahimtar in da ya dosa ta ce
" Me ya sa? Me ya sa ka biyo ni? Kudi ka ke so? Idan shi ka ke so wallahi Ammy za ta ba ka ko nawa ne......"
Ya na mai dariyar mugunta ya sami waje ya zauna hakan ya sa Zainab kara jan na ta jiki domin yin nesa da shi. Sai da yayi dariya mai isar sa ya ce
"Kudi? Da shi ki ke takama ko? Shi ya sa ki ke tunanin kowa shi ne burin sa? Ki na tunanin dukiya ya sa na dauko ki? Wallahil azim in da za a hade dukiyar ku kaf ba zai yi kwatar dukiya ta ba, Ni bakauye ne amma ba matsiyaci ba, Dan haka dukiya ba ta daga cikin dalilin zuwan ki Rugar Shehu....!!!"
Baki bude Zainab ta ke kallan sa, ta na mai hadiyan yawun azaba domin kuwa makogaron ta ya bushe, ta kada baki ta ce
"Menene dalilin ka? Ya aka yi na zo nan? Ka mayar da ni makaranta yanzun nan!"
"Shhhhh!"
Usman ya katse ta ya na mai dora yatsa bisa labban sa ya ce
"Kul kar da ki tada macijiya, a matsayi na na Shehun rugar ga ba zan iya hana ko wani halitta abincin sa ba, ko da kuwa abincin halittar nan mata ta ce!"
Wani irin zufa ne ya ketowa Zainab yayinda da ta kai kallan ta ga inda kasar ke kwance ta na bacci, sannan ta mayar da kallan ta ga Usman ta sake furta
"Na tsane ka wallahi! Ka mayar da ni gida na ce! Damn you!"
Yana murmushin mugunta ya ce
"Umarni ki ke ba ni halan? Har yanzu ba ki gane cewa a dajin da Rugar Shehu take ki ke ba, Ni Usman ni ne Shehu, ba bil'adama kadai ba, hatta dabbobin dajin nan ni an Shehun su, Ni an shugaban su! Ina mi ki bayanin nan ba dan komai ba sai dan kar ki halaka....."
"Mtswww!"
Zainab ta ja masa dogon tsaki wanda ya tunzura Usman, ya tashi tsaye cike da motsawar zuciya ya ce
"Idan har ban cire mi ki wannan rashin kunya ta ki ba Abu cikin kwanaki kalilan wallahi ban isa Usman ba! Sai kin roki sassauci Abu, da bakin ki za ki roke ni sassauci...."
"Tir! Allah ya sauwake! Ba zan taba rokan ka ba ko da kuwa zan rasa rai na!
"Idan kin shirya rasa ran na ki ki zauna anan duk sanda maciyar can ta tashi ta yi kalaci da ke, idan kuwa kina son ran ki tashi ki bi mijin ki dakin auren ki"
Banza ta yi masa, ta na gani ya juya ya tafi zuciyar ta na dukan uku uku tsabagen tsoro, Amma kafiya ya sa ta dauke kai. Usman kuwa be yi zaton zai yi takun da yayi ba tare da ta biyo shi ba. Jin ba ta biyo shi ba har ya fara nisa ya sa ya juyo, ya gan ta zaune in da ya bar ta ko motsawa ba ta yi ba. Ya na mai girgiza kai ya dawo gare ta. Dan akwaitin ta ya fara dauka, ganin ya nufo ta ta kafe shi da manyan idanun ta da ta san ya na firgita duk wanda ta yiwa irin kallan, ba ta ankara ba sai ji ta yi ya furta
"Idanun ki ba za su taba firgita ni ba, idan kuma mutuwar ki ke son yi ba zan bari ki yi ba tare da na cimma buri na kan ki ba, ba ki isa ba"
Sungumarta yayi ya aza bisa kafada. Ihu ta ke ta na kai masa duka da wayar hannun ta, da dayan hannun har ma da kafafun ta. Idan Usman ya na jin zafin dukan sam be nuna ba, tun ta na ihu har ta koma sirfa masa zagi, ko a jikin sa haka ya shiga Rugar Shehu, duk in da su ka gifta jama'a na gida da na waje kowa fitowa yake domin ya ka ga Shehu dauke da Kado, wannan lamari ba karamin mamaki ya ba su ba.
Ba shi ya sauke Zainab ba sai a tsakar bukkar sa, ta na mai mayar da ajiyar zuciya ta ke fadin
"Mugu azzalumi! Allah ya isa jiki na da ka hada da na ka!"
Rai bace ya ke duban yanda ta ke kabe jikin ta kamar wacce najasa ta taba ta, ta kara fadin
"Allah ya isa ka hada kazamin jikin ka....."
A fusace ya kai hannayen sa ya biyu bisa kafadar ta ya fizgo ta tsaye ya na mai hankado ta jikin sa ta fada kirgin sa, ya sa hannu ya rungume ta gam yanda ko kwakkwarar motsi ba za ta iya ba, haka kuma ihun da take son yi ya tsaya iya makogoro sanadiyar wani yanayi da ta tsinci kan ta, tun tana kokarin kwatar kan ta, har ta gaji, kan ta bisa kirjin sa ga mamakin ta duk da dai ba ta ji kamshin turaren da ta saba ji daga jikin abokan ta irin su Mike ko Bobo duk sanda su ka rungumi juna ba, Sam ba ta ji warin datti ko na hammata da take kyautata zaton za ta ji daga jikin Usman ba. Jin hanyen sa na shafa gadon bayan ta sai da ta ji yar tun daka yatsun kafar ta har zuwa gashin kan ta, ba ta san sanda ta runtse idanun ta ba yayin da bugun zuciyar ta ya karu, bakin sa dab da kunnen ta na dama ta na jiyo numfashin sa, ya furta
"Ni mijin ki ne! Jikin ki nawa ne ina da ikon hada shi da nawa duk sanda na ga dama, ku ma na san zaki sakar min jikin na ki, ji yanda ki ka saki jiki kina mayar da numfashi, ko da yake ba abin mamaki ba ne, tamakar karya ki ke kin saba sakarwa ko wani kare da biri jikin ki......"
Kamar wacce aka watswa ruwan zafi haka Zainab ta farfado daga shaukin da ta shiga na kankanin lokaci sanadiyar rungumar da Usman ya mata, kukan kura ta yi ta na mai ture Usman hakan ya sa shi sakin ta ya na murmushin mugunta, dama abin da ya ke so kenan ya gasa mata bacin rai, ran ta ya soyu shi ne farin cikin sa. Cike da bacin rai yayinda idanun ta ke fitar da kwallar bakin ciki ta ke fadin
"Ni Zee? Ni ka yiwa wannan cin fuska ka na almajiri mai gadin gidan mu? Allah ya isa! Abin da ka ke min Allah ya ma ka! Mugu azzalumi! Allah ya isa! Kai ne kare! Azzalumin! You will pay for this wallahi you will pay for this!"
Usman na murmushin jindadi da gamsuwar halin da ya sa Zainab ya sa kai ya fita ya bar Zainab zube ta na kuka. Kukan na ta biyu ne, na tsanar Usman da kuma haushin kan ta da har ta bari kaskantacce kamar Usman ya rungume ta, sannan ya kara mata da zagi tare da bakar magana, har ya kira ta karya!
Ta na cikin wannan tunanin ta ji alamar an bude assabarin daki an shigo, ba tare da ta daga kai ta ga wanda ya shigo ba ta ce
"Na tsane ka! Kada ka sake kai hannun ka jiki na domin kai ba ma ka kai darajar kare da birin ba! Wallahi da na hada jiki da kai gwara na hada da dabba...."
Jin shiru ba a tanka mata ba ya sa ta daga Ido ta ga wanda ya shigo, Nan ta yi Ido biyu da kyakkywar budurwa fara sol, wacce dudu ba ta wuce shekara goma sha biyar ba, hannun ta dauke da kwaryar nono, kamar yanda Zainab ta bude baki ta na duban ta, haka ita ma ta ke kallan Zainab cike da mamaki musammam da Zainab ta tashi tsaye da kyar, yarinyar ta ga tsayi da dirin Zainab, cikin ran ta fadi ta ce 'Babu shakka dole Shehu yayi duk abin da aka ce yayi akan Kadon Nan, ciki kuwa har da daukan ta da yayi a bainar jama'a'
Ta ji labarin kyaun fata da ido da Allah ya yiwa Zainab, amma ba ta taba tunanin Zainab din haka ta ke ba. Kumatunta yayi jajur sanadiyar kalaman da Zainab ke fadi tsabagen nauyin maganar, Abu daya ya mata dadi shi ne , wato kenan akwai kiyayya ta gaske tsakanin masoyin na ta da Kadon sa, ko ba komai wannan zai kara ba ta damar zama matar shi.....
"Wacece ke? Ki taimake ni na tsira daga hannun wannan azzalumin almajirin...!"
Maganar Zainab ya dawo da ita hayyacin ta, Har ta budi baki za ta bata amsa da ta san wanda ta ke magana akai kuwa? Sai ta tuna gargadin Shehu na kada su sake su nunawa matar shi suna jin hausa bare su mata magana da shi. Dan haka kawai sai ta aje kwaryar hannun ta ta juya ta fita ta na ji Zainab na ce mata dan Allah ta tsaya.
Jim kadan ta kara dawowa tare da wata kwaryar mai dauke da kwan zabi, Nan ma Zainab ta sake kokarin yi mata magana, yarinya ta nuna kamar ba ta gane abin da Zainab ke fadi ba, ta aje kwarya ta fita. Haka ta na kai kawo sai da ta aje kwarya har biyar, na naman zabi, sai ruwa, sai kuma 'yayan itatuwa.
Jin shiru ba ta sake shigowa ba ya sa Zainab tashi cikin dingishi, dan kuwa kamar yanda marar ta ta cika da fitsari haka hanjin ta ya cika da tutu, gashi gaba daya jikin ta ciwo ya ke mata ba ta daburin da ya wuce ta sami ruwan dumi ta yi wanka. Ta na tafiya da kyar ta fito waje yayinda ta ke ware idanu cikin fatan Allah ya sa Usman ba ya nan dan kuwa sam ba ta kaunar sake ganin shi. Ganin fitowar ta mata da yara kowa ya bar abin da ya ke ya na kallan ta. Cikin dauriya Zainab ta ce da su
"Ina ne toilet please?"
Kallan ta su ka tsaya suna yi babu mahalukin da ya san abin da ta ke nufi da "toilet" ganin haka Zainab ta kara da
"Mtswww na manta da jahilai na ke magana! Toh ina ne bandaki!"
Babu wanda ya tanka mata, hakan ya sa Zainab komawa bukkar Shehu, ta dauko butar da ta gani aje ciki ta ci sa'a akwai ruwa, da ta fito ta tarar suna nan dai tsaye kamar masu jiran tsammani, Zainab na mai musu alama da butar ta kara fadin
"Bandaki....wanka...ina zan yi?"
Duka su ka sa mata dariya, iya kulewa Zainab ta yi, ta na shirin juyawa ta koma daki sai ga Bello ya shigo da sallamar sa, ganin shi Zainab na mai yi masa alamar wanka da hannun ta ce
"Wanka, ina zan yi?"
Bello ya mata nuni da wani fili da ke zagaye da kara can gefe, ganin yanda Zainab ta zare idanu ta na kallan wajan shi kan shi Bello sai da dariya ta kusa subuce masa, ga tausayin ta da ya ke ji.
Ta na mai dawo da hankalin ta ga Bello ta sake fadin
"Oh my God! Yanzu fisabilillahi wancan zagayen shi ne toilet din ku? Ni Zee ni ce zan yi wanka cikin zagayen kara?"
Shi ma Bello tsayawa yayi ya na kallan ta kamar sauran yan gidan. Hakan ya sa Zainab juyawa ta nufi bandakin ta na fadin
"Na manta duka sokwaye ne a dajin nan! Ace rasa mai jin hausa sai wannan azzalumin! Kai wannan masifa da me ta yi takama! Bari dai na je na gani ko zan iya wanka, Duk Daddy da Ammy su su ka ja min wannan masifa! You will not get away with this! Wallahi you will not bari na tafi gida!"
Cikin tashin hankali da tsoran dattin da kazantar da za ta je ta tadda ciki ta yi adduar shiga bandaki ta kusa kai. Wayam ta gani, kasa ne shimfide a filin Allah, sai dan zarni da ke tashi sanadiyar rana da ya daki kasar, sam babu ko da masai ta tsugunno bare na tangaran da Zainab ta saba hawa, gashi a zahirin gaske a matse ta ke. Har za ta koma ta sake tambayar su ko dai sun yi kuskure ne ba su gane abin da ta ke nufi ba, idanun ta ya sauka kan wani dan roba mai dauke da sosan waya na wanka, ta tabbatar bandakin ne, kila sun bambamta shi da na ba haya ne.
Cike da kyamkayami ta sami gefe ta yi fitsarin cikin dabara ba tare da ta tsugunna ba, hakan ya ba ta damar ruke tutun da matse ta, Da niyar neman wajan yin tutun da wanka bayan ta idar da sallah. Da ta gama ta dauraye kafafun ta da ruwa sannan ta fito daga bandakin tana kakkabe kakkabe yayinda ta ke jin wani iri a jikin ta tsabagen kyamkayami da tashin hankali.
Har ta yi alwala ba su dena kallan ta ba, ta na idarwa ta yi sauri ta shiga ciki hannun ta dauke da butar ta ke fadin
"Mayu kurwa ta kul sai dai ku ci kan ku!"
Dankwalin ta ta shimfida kan ledar dakin, ba tare da ta tambayi ina ne gabas ba dan ta san ma babu mai amsa mata matukar ba Usman ba ta tayar da Sallah daga zaune, ta rama Asuba sannan ta gabatar da azahar. Ta idar ta na tunanin wanda za ta tambaya ina ne bayan gidan da za ta kasayar da tutun da ke cikin ta, ji ta ke tamkar zawo ne ke shirin kama ta, gashi Rugar kaf babu wanda ke amsa mata in ban da Usman.
*****
Can birnin Kano kuwa tun washagarin tafiyar su Usman labari ya iski Ammy bayan ta bayar da abinci a kai masa. Ta yi mamakin dalilin tafiyar na sa ba sallama, amma ba ta kawo komai cikin ran ta ba. Hankalin ta be fara tashi ba har bayan da ta kira Zainab ba ta dauka ba, sai ma sakon txt da ta tura mata, ta yi tunanin rashin da'ar Zainab ne ya tashi kila Falmat ta sanar mata da zuwa Usman. Kiran ta da aka yi daga makaranta aka tabbatar mata da rashin ganin Zainab a dakin jarabawa ne ya tada hankalin Ammy, musammam da ta lissafa tafiyar Usman da kuma ranar karshe da aka ce an ga Zainab a makaranta, sai ga Ammy ta na kuka wiwi, haka ma Falmat wacce ita ce ta kira Anty Sauda ta fada mata halin da ake ciki. Sai da ta tabbatar mijin ta ya raba hotunan Zainab bariki bariki, check point na kowani hanya, haka kuma aka fara kokarin bincike ta hanyar kididdigar wayar salulun Zainab, sannan ta hawo jirgi ta tawo garin Kano.
Fada sosai ta rufe Ammy da shi fadi ta ke
"Kukan me ki ke Aleesha? Ba abinda ki ke so ba kenan? Kun cuci yarinya kun lalata mata rayuwa! Ga irin ta nan ai! Gashi na dai za ki yi biyu babu cifar gafiyar baidu! Shi mijin na ki dama babu shi, diyar ta ki ma Allah kadai ya san halin da ta ke ciki a raye ko a mace!"
"Innalillahi wainnailaihi rajiun! Dan Allah Hajja Sauda ki dena fadin haka, ke ma kin san uwa ba za ta cutar da diyar ta da gangan ba! Oh ni Aleesha Yakura ko a ina ki ke? Ya Allah ka kare min Yakura! Kai amma yaran nan be yi halacci ba! Be Kuma yiwa Malam adalci ba! Be min adalci ba!"
Cewar Ammy cikin kuka. Anty Sauda wacce ta dau zafi matuka ta kara da cewa
"Ku Kuma fa? Kun mata adalci ne? Gashi kun jawo ya dakile mata karatun ta dan wallahi ko yanzu aka ga Yakura kun gama cutar da ita, she missed two exams, talk more of halin da ta ke ciki, kai Aleesha ba ku yiwa yarinyar nan adalci ba!"
"Innalillahi wainnailaihi rajiun!"
Cewar Ammy yayin da maganar Anty Sauda ke dada rura zuciyar ta. Wayar Anty Sauda ne yayi kara, ta yi saurin dagawa ta kara a kunnan ta ganin mijin ta ne mai kiran wayar. Nan ya sheda mata cewar sojojin da ke check point sun tabbatar da wucewar Yakura ranar da ta baro Yola zuwa Kano, haka kuma ta sake biyo hanyar a washagarin ranar a karo na biyu, Amma kada su damu in Sha Allah su na kan yin bincike.
Bayan ta aje wayar ne Anty Sauda ke fada ma Ammy halin da ake ciki. Ammy na mai daga hannu sama ta ce
"Ya Allah ba dan halin mu, Allah ka bayyana mana Yakura! Ba a ce an gan ta tare da Usman din ba?"
"Cikin motar haya wai zai san ko tare da wani ta ke tafe? Dama dai kuna da hotan almajirin ne da da sauki...."
Anty Sauda ta amsa mata ta na mai tabe baki cikin jimami.
"Yanayin shigar shi fa? Ai shigar sa daban ta ke da na mutane? Kai ta ya ma aka yi Yakura ta yarda ta bishi? Anya kuwa ba asiri ya mata ba kuwa?"
Cewar Ammy ta na sharar hawaye.
Anty Sauda ta amsa da
"Amen Ashe dai kuna kaunar ta kuka cuce ta"
Auren Shehu 2
5
Ko da ya isa gidan Hansai ba ta dena kuka ba, Iyalle ce ta masa bayanin rashin darajar da Zainab ta aikata musu, da kuma kwashe ruwan shan gidan da ta yi ta ja zuwa bukkar Shehun, Allah kadai ya san abin da ta yiwa Hansai sa'ad da ta leka dakin dan kuwa har lokacin Hansai ba ta dawo hayyacin ta ba. A fusace ya wuce bukkar ba tare da ya tambayi Hansai baasi ba, ya na sa kai cikin bukkar kafar sa ta sauka kan sauran ruwan wankan Zainab mai jirwaye da be gama shanyewa ba, haka kuma idanun sa ya sauka kan dan fantarin ta da ta wulgar gefe.
"Me ya faru a dakin nan?"
Cewar Usman a fusace.
"Au dama wannan bukkar daki ne? Caf ai ina na gane? Bayan hada jiki da irin ka ai sai an yi saukar dauda, wanka na yi......"
Wani irin mugun kallo da ya jefe ta da shi ne ya sanya ta dada gyara zama tana mayar masa da martani da irin kallan da yake mata. Tsiwar da ta ke masa be sa ya kasa ganin kyawun ta ba, duguwar rigar jikin ta ya mata kyau sosai musammam yanda ya bi jikin ta ya zauna daram. Haka kuma da niya ta yiwa bakin ta ado da jan janbaki duk dan ta boyewa Shehu halin kunci da ya saka ta ciki, dan ta lura ya gan ta cikin bakin ciki shi ne babban burin sa.
"Wanka ki ka yi cikin dakin nan? Yanzu fisabilillahi dakin nan ya miki kama da wurin kwana?"
Ta na mai daga gira ta ce
"Wallahi kuwa wanka na yi, ka fa san tsatona, ko bandakin masu gadin gidan mu ya fi bukkar nan daraja, bare na Zee, ka manta daga in da ka sato ni ne?"
Ya na jinjina kai ya kara da
"Da ruwan shan gidan nan gaba daya ki ka kashe ki ka yi wanka?"
Ta jinjina masa kai alamar
"Eh wallahi"
Usman yayi shiru kamar mai nazari, sannan ya furta
"Abin da aka yi bayan gida...."
"Kashi? Eh shi ma ni na yi wallahi!"
Yanda ta yi saurin katse shi duk bacin ran sa sai da dariya ta kusa kwace masa, wato lalle ya gane so ta ke ta tunzura shi ya yanke hukunci a kan ta, lalle 'yaro yaro ne' cewar Usman cikin ran sa, ya na mai murmushi ya furta
"In dai kashi ne ai mu muna maraba da shi, gwamnati ba ta ba mu takin zamani, dama da kashin mu ke taki, daga na dabbobin har na mu na mutane, Nan gaba in za ki yi sai ki min magana ni zan raka ki har daji yankin shukar mijin ki, kin ga sai ki saki jikin ki ki kasayar da hujja, yanda shuka za ta fito mu sami amfanin gona, yanzun ma ba ta baci ba na sa yara su kai daji....."
Yanda Zainab ta yi da fuska kamar mai shirin yin amai ne ya kara kawata nishadin Usman, be dena murmushi ba ya kara da
"Hansai kuma fa? Me ki ka mata?"
Zuciyar ta na tashi tsabagen tashin hankalin da furucin da Usaman ya saka ta, Ganin yanda idanun sa ke rawa jikin ta ya bata murmushi ya ke, cikin rashin fahimtar dalilin annushuwan sa duk wannan aika aikan da ta masa ta ce
"Ka tambaye ta mana! God you sting!"
"Abu duk lalacewar ki sai na tankwasa ki, idan ba haka ba ban Isa Shehu Usman ba, kin ci darajar amanar da mahaifin ki ya bani da kuwa sai kin kwashe kashin ki da hannun ki, haka kuma zan tambayi Hansai, matukar wani abu ki ka mata mai muni wallahi sai na aika kwatankwacin shi kan ki sai dai ita din ce ta ce ta yafe...."
"Allah ya sa kar ta yafe! Na tsane ka! Na tsane ku! Wallahi da ni ke da kai na da tuni na kashe kai na da wannan rayuwar azaba da ka saka ni....."
Shiru ya mata ya juya zai fita, har ya daga assabarin ya sauke, kana ya juyo ya na murmushin mugunta yayinda ya ke duban Zainab da idanun ta su ka cika da kwalla, ya ce
"Alhamdulillah, Alhamdulillah wannan shi ne kwatankwacin bakin cikin da na ke so na dasa zuciyar ki, ki sani wannan sumin tabi kenan domin kuwa nan gaba ba ni kadai za ki tsana ba Abu, na mi ki alkwarin kamar yanda ki ka tsani rayuwar wannan Ruga har kina tunanin kashe kan ki, sai kin tsani kan ki fiye da yanda ki ka tsane ni, wannan shi ne buri na, dan haka duk wannan abubuwan da ki ke aikatawa sun yi kadan su sa na karaya, ki sake sabon shiri..."
"Allah ya sa! Allah ya sa! Macuci! Allah ya isa"
Cewar Zainab cikin gunjin kuka. Yana dariyar jin dadi ya fita ya bar ta tana kukan takaici. Zuciyar sa fara sakamakon halin da ya bar Zainab ciki ya koma wajan Hansai. Wanda sai a sannan ta masa bayanin ganin Zainab da ta yi ba kaya ta na wanka tsakar daki, fadi ta ke
"Wallahi Kado batta mutunci, haka tibi tibi na gan ta..."
Cikin rarrashi Usaman ya mu su jawabi da
"Ku yi hakurin zama da Abu matukar kuna so na zauna da ku, idan kuma hakan zai zama da takura ku yi hakuri ku bari na hada nawa ya nawa na dau iyali na mu koma can birni....."
"Ah ah za mu zauna da ita Shehu, me yayi zafi da mu ka samu ma Allah ya dawo da kai, ai hakuri ya zama dole!"
Iyalle ce ta yi saurin katse shi. Cikin goyan baya sauran ma su ka yi alkawarin hakurin zama da Zainab, ita kuwa yar budurwa wacce ake kira Raqeeba zuciyar ta ce ta dada cushewa, lalle auren Shehu matukar yana tare da Kadon nan tasa ba karamin abu ba ne, ta yanke hukuncin lallba gyatumar ta Hansai cikin azanci ta bijirowa Usman da maganar auren.
Kamar yanda ya shedawa Zainab, yara ya sa suka kwashe kashin su ka kai daji, wanda da su ka dawo ko wanke hannu ba su yi ba su ka cigaba da hidimar gaban su.
Bayan da ta ci kukan ta ta koshi ne yunwa ya sako ta gaba, gashi bayan abin da Usman ya sheda mata ko ruwan Rugar Shehu ba ta sha'awan sha. Duk yanda ta so ta roki afuwan Usman da ya mata rangwame ya mayar da ita gida taurin kai ya hana ta. Sai da la'asar ta yi sannan ta sauko daga kan gadon karar, ta ci sa'a kasa ta shanye ruwan wankan ta, sai dan ragowa da ba a rasa ba. Daga can gefe in da dama be jike ba ta shimfida ledar dakin ta yi sallah.
Rabon da ta yi sallah mai cike da nutsuwa kamar ta ranar tun tana jami'a sai yanzu da Usaman ya kawo ta Rugar Shehu. Gun Allah ta kai karar shi, ta na mai rokan Allah ya fitar da ita daga hannun shi ya kuma mata sakayya da gaggawa. Kukan yunwan da cikin ta ya ke mata ya sa ta tuna da ajiyar kwararen da ta tura karkashin gadon, ta na adduar Allah ya sa ta sami abin da za ta iya ci ba tare da ta tuna kalaman Usman ba ta janyo su waje. Ganin dafaffen kwai ta yi hamdala, dan kuwa shi ta ci sai da cikin ta ya dan tasa sannan ta yi hamdala ta na mai duban ruwan shan da aka aje mata. Ko dan daukan fansa dole ta rayu, dan Usman dai sai ta ga bayan sa matukar ta na numfashi, kudirin da ta ke yi a ranta kenan yayinda ta daga kwaryar ruwan ta kai daidai saitin bakin ta ta na mai zubawa ba tare da ta yarda kwaryar ta sauka bakin ta ba. Sai da ta kusa kwarewa ta aje, azahiri ta na furta
"Idan har ban ga bayan wannan almajirin ba ban isa Zeee ba!"
******
Yanda Zainab ta ga rana haka ta ga dare, itacen korar sauro da Usman ya kunna mata a bukkar be sa Zainab ta iya bacci ba saboda zugin da kafarta ta ke mata duk da kumburin ya ragu, da kuma taurin gadon karar Usman da yake ikirarin ta godewa da ta samu ya iya bar mata.
Duk yanda ta so musgunawa Usman ko ya ji haushi ya mayar da ita abu ya ci tira, haka kuma ba ta fasa yi masu kashi ko wanka in da ta so ba, Usman na dauke kai ya sa yara su gyara. A haka har Zainab ta yi kwana uku Rugar Shehu, gaba daya ta fita hayyacin ta, kafa kam Alhamdulillah ta warke sosai ta bar zuciyar Zainab da jinya, tun tana kuka har hawayen ya sauke sai dai na zuci.
Da Safe bayan ya tashi daga zaman fada, ya zauna wajan bitar karatu da ya saba yi tare da yara maza. Zaune su ke tsakar gida, sun saka Usman tsakiya kowannan su dauke da alqur'ani ko kuma allo sanadiyar rashin wadatuwar alqur'ani cikin Rugar. Kai kawo da Zainab ke yi a tsakar gidan na ba gyara ba dalili ya sa Usman kasa nutsuwa. Sanye ta ke cikin daya daga cikin doguwar rigunan da ta zo da shi, ramar da ta yi be saka kirji ko hips din ta raguwa ba, illa dai kashin wuya da tsayin wuya da ta kara, ba sururu Zainab kadai ba hatta tafiyar ta ma abin sha'awa ne ga duk mai kallo, duk sanda ta gifta sai ya bita da idanu hatta daliban na sa sai da suka fahimci hankalin Shehu yau dai ba ya gare su.
Sallamar Bello da kuma ganin wanda su ke biye da shi ne ya sanya Usman hade rai kamar hadari yaAuren Shehu 2
6
Haɗe ran da yayi bai sa sun fasa ƙarasawa har in da su ke ba, su uku ne namiji ɗaya da mata biyu da za a iya cewa miji, mata da ƴarsu ne don ƴar ba za ta wuce shekaru goma ba.
"Me ya kawo ku nan Tanko"
usman ya faɗi cikin tsawa, ya kara da
"Bello me kake nufi kenan? So kake ka nuna ka isa a Rugar nan ko me ye dalilin ka na shigowa da wainnan iblisan?"
Ya cigaba da faɗi yana mai kallon Bello wanda ya sha jinin jikin sa jin lafazan Usman. Gyara tsayawa zainab ta yi cikin nishadi wanda ya kira jinin sa ya mata aikin da ta dade tana yi baya kama shi, amma kuma kallo ɗaya ta yi ma wanda ya kira da Tanko ta hango kamanni na jini tsakanin su sai dai shi din baki ne, sabanin Usman da ya ke farar fata. Duk da ba jin yaren ta ke yi ba za ta tsaya ta kalli dramar da za a yi.
Haka ma sauran jama'ar gidan su ka fito suna mai kallan Tanko cike da mamaki da al'ajabi, dan kuwa babu wanda be san mugun halin Tanko ba. Daliban Shehu kuwa musammam kanana cikin su har rawar jiki su ke ganin yanda Usman ke bambami.
"ka dubi girman Allah Shehu, ka dubi nasaba da martaban ka, ka dubi darajan yarinyar nan Cangwai da ta fito daga tsatsonka ka yafe mana"
Macen ta faɗi tana mai share hawaye.
"Baffa Allah ya masa cikawa bayan kun baro sa, ba mu da kowa shi ya sanya muka ce mu zo cikin ƴan uwa mu zauna, wallahi duk wani mugun abu na bar shi a dajin falgore, Tanko mai kyawun hali ne nan, ka yafe mana"
Tanko ya caɓe cikin fullanci yana mai rusunawa kamar zai yi sujada. Cikin lafiya da nuna rashin tausayi Usman ya furta
"Rugar nan tsarkakakke ne babu ɗigon mugun aiki a cikinta, saboda haka baku da matsuguni ku fice kafin na saukar da fushi na akanku"
yayi maganar ya na mai nuna masu hanyar ficewa daga ɓangaren nasu. Daga Tanko har matar shi zubewa su ka yi gwiwowi biyu, hawaye na zuba daga idanun sa ya ce
"Ka taimaka Shehu, ba mu da matsuguni Shehu, duniya ta juya mana baya, idan ma ba za ka karbe ni ba ka duba Rahila da Cangwai, Raliya diya mace ce, ko ba komai Cangwai diyar ka ce...."
"Cangwai ba diya ta bace!"
Usman ya katse shi cikin tsawa yayinda ya kai kallan sa ga yarinyar da Tanko ya kira Cangwai, be gushe ba ya kara da
"Na sani! Ka sani! Na san ka sani! ku kama hanyar ku tunkafin rai na ya fi haka baci"
Maimakon su juya Tanko ya shiga waige waige yana mai rokon mutanen da ke wajen da su sanya baki Shehu ya yafe musu a nan ne ya hango zainab da ke tsaye. Ba shigar da tayi na doguwar riga kaɗai ya ɗauke hankalinsa ba har da bambamta da tayi da sauran matan rugar, in bai yi ƙarya ba irin matan birni da su kan sace don neman kudin fansa ne.
'toh me ta ke yi a rugar shehu' ya tambayi kansa. Gaba ɗaya ta manta abin da ya ke yi ya saki baki yana kallon zainab tare da zantawa da zuciyar sa. Yanda ya saki baki ya na kallan ta ne ya sa Usman ya kai kallo gare ta, ganin Tanko ya sa shaf ya manta da ita. Wani irin bakin kishi da tun da ya zo duniya be taba jin irin shi ba ya taso masa har kahon zuciyar ta, musammam da ya lura Zainab din ma Tankon ta ke kallo
"Me kike yi a wajen nan? maza shige ciki!"
Shehu ya daka mata tsawa da firgici ya hana mata musawa cikin sauri ta shige bukkan, sai da ta shige sannan ta ji haushin kanta na yin biyayya da ya daka mata tsawar. Daga bakin assabari ta laɓe tana kallon yanda mutane ke roƙon usman yana botsarewa.
"Kai an yi azzalumi! komai aka yi wani zalincin ya ke aikatawa! Wannan masifa har ina! Ina ma ina jin abin da su ke fada! Ya Allah idan har wannan bawa zai iya aikata sharri da zalinci ga jinin sa, Allah kai kadai ka san irin zalincin da zai iya aikatawa kai na, ya ke kuma kan aikatawa, ya Allah ka mana maganin shi.
"Zan iya karbar Rahila da kuma diyar tsohuwar mata Cangwai saboda raunin su na 'ya'ya mata! Wajan ka dai babu shi Rugar Shehu, idan har hakan ya maka toh, idan be ma ka ba su ma din kana iya tafiya da su!"
Cewar Usman wanda kallan da ya ga Tanko ya na yiwa Zainab ne dalilin shi na biyu na rashin yarda ya zauna a Rugar Shehu. Rahila matar Tanko ta na ji tana gani Tanko ya mata sallama tare da mata alkawarin zai dawowa da ya sami matsugunni. Kukan Rahila da Cangwai be sa Usman ya tausaya ma su ba, sai ma sallamar yara da yayi daga karatu, shi da Bello su ka tasa Tanko gaba, sai da su ka tabbatar yayi nisa da Rugar Shehu, sannan Usman ya ce da shi be hana shi zaman dajin ba matukar ya kiyaye kusantar Rugar Shehu.
Tuni labarin zuwan Tanko ya kadaye Rugar, ranar da jimamin abin da ya faru aka wuni, ita kan ta Zainab sai da zuciyar ta ta dan yi rawa sanadiyar ganin rikidewar Usman cikin kankanin lokaci duk da sam ba ta fahimci ainihin abin da ya gudana a tsakar gidan ba.
Usman kuwa tun bayan da ya tasa kyeyar Tanko, haka kuma ya tabbatar ya ja kunnan Bello be iya komawa sashan shi ba gudun kar ya kara saka Zainab a idanun sa, wani irin bacin rai ke addabar zuciyar duk sanda ya tuna yanda Tanko ya shagala ya na kalle Zainab, wacce ta tsaya kerere da ita ko mayafi babu.
Sai bayan da ya idar sallar ishai sannan ya koma gida ya tarar Zainab na zauna sai surutai ta ke. Fadi ta ke
"Babu ruwa, babu wuta, babu bandaki, babu siturar arziki! Babu waya! Babu club! Babu mai jin hausa! babu Jin dadi! Babu babu babu, babu civilization! bambamcin wannan daji da kabari shi ne can lahira ne! wannna wani irin rayuwa ce!...Ammy in ma ke ce ki ka kullace ni dan Allah ki yafe min, Dady.... Dady ka mutu ka bar ni da masifa Dady! Auren Shehu masifa ne Dady!"
"Akwai maza amma ko?"
Da sauri ta kai kallan ta ga Usman sam ba ta san da shigowar sa ba, tsaye ya ke jikin bango hannu sa harde a kirjin sa, yayinda hasken acibalbal ya haske fuskar sa, idanun sa har kyalli su ke tsabagen bacin ran da ya ke tattare da shi.
"Na'am?"
Ta mayar masa cikin rashin fahimta. Maimakon ya bata amsa, sai ya wuce ciki ya dauko wasu acibalbal har biyu, ya kunna haske sosai ya gauraya dakin, sannan ya dawo ya tsaya gaban ta, idanun sa cikin na ta ya furta
"Maza da ki ka fi so a rayuwar ki, akwai su ko? Na ga yanda ki ka kasa boye maitar ki sanadiyar ganin Tanko...."
"Tanko? Wanene Tanko?"
Zainab ta tambaya dan kuwa gaba daya kan ta ya juye ta kasa gane in da Usman ya dosa. Zainab na murmushi bayan ta gano bakin zaren ta ce
"Ya ba zan nuna maita ta ba bayan na ga namiji iya namiji? Ai wannan dajin kaf babu namiji da ya amsa sunan sa namiji kamar wannan....ya ma ka kira sunan sa?"
"Zainab!!!!"
Ya daka mata tsawa ya na mai kiran sunan ta na ainihi a karo na farko cike da gargadi, duk da hantar cikin Zainab ya kada ba ta fasa fadin
"Ga shi baki, ga faffadar ka fada....."
"Zainab!!!!!"
Ya kara daka mata tsawa tare da daga hannu kamar me shirin marin ta, har ta kai ga runtse idanu. Jin ba ta ji saukar marin ba ta bude idanun ta a hankali ta kai kallan ta gare shi. Idanun sa sun yi jajur sai huci ya ke
"Me ya sa ka fasa? Ka mare ni mana! Ka dake ni! Idan har ba ka daga hannu ka dake ni ba Usman ba ka isa namiji ba!"
Murmushin mugun ta ya sakar mata kana ya na mai ja da baya ya furta
"Idan har duka shi ne zai gwada mi ki isa ta namiji, Ni kuwa zan dake Abu, Amma duka mai dadi Abu ba irin wanda ki ke tunani ba, Irin wanda za ki dena maitar duk wani damiji face ni Usman..."
Ya na gama fadin haka ya fice da sauri dan kuwa yanda ya ke ji zai iya aikata abin da zai zo yayi dana sani.
*Khadija Sidi*
Auren Shehu 2
7
Ta na mai nana ta maganar Usman cikin ran ta yanda ta ga rana haka ta ga dare, dan raban da ta sami ishesahen bacci tun ranar da aka wayi gari a Rugar Shehu.
Kamar yadda kowa ya kwanta da sanyi jikin zuwan su cangwai rugar da tsoron abin da Tanko zai iya aikatawa saboda korar da aka masa haka aka tashi washe gari, hakan bai hana mata dakan hura da zuwa tatsar nono asubahin fari ba. Bukkar da ke kusa da ta Atuwayye , matar taubashin Shehu ya sauke Rahila da Cangwai saboda aminta da yayi da ita sannan zaman da su ka yi a ƙasar Benue da mijinta lokacin da su ke ganiyar kaɗe shanu ya sanya ta ɗan fi sauran wayewa.
Duk wannan kai komon da ake yi da Rahila ake yi, sakin jiki tayi tana aiki tana lura da rugar sosai, cangwai kuwa tuni ta shige cikin yan mata sa'annin suna ta hidimar gaban su.
Ko da aka kammala girki, Raqiba aka kwalawa kira don ta kai ma Zainab nata.
"Iyalle barshi zan kai"
Rahila ta yi saurin faɗi don dama neman hanyar shiga sashin Shehu take.
"Ayi haka, tun safe kike aiki fa, Allah ya miki albarka" faɗin Iyalle ta na mamakin sauyin halin da ta gani a tattare da Rahila.
"Ba komi Inna, ai mu masu laifi ne, duk abin da zamu yi don mu rage nauyin zunubinmu za mu yi"
"Aikuwa dai Shehu na son debbo ma, ga ta Kaɗo maras daraja" .
Hansai ta caɓe tana mai taɓe baki
"Kinga ki iya bakin ki, ba da ni za a yi shari'a ba, in bai so ta ba wa zai so, da gani ai ka san yar birni ce"
Cewar Iyalle tana mai tashi daga wajen. Kalaman nan ne su ka ƙara sanya Rahila son zuwa ko don ta gane ma idon ta matar da kyau, gashi dai zuwan su jiya ta shaidi cewa yana kishin ta.
Da tunanin nan ne ta nufi hanyar sashin Shehu, da sallama ta shiga bukkar ba tare da ta jira an amsa ba duk da cewa zainab ba amsa sallamar su take ba.
Zaune ta iske ta ta baje kayan ta a saman gado tana ɗaga su, neman mai gwara gwaran da za ta sanya take yi kasancewar duk sun yi datti.
Buga wayar ta take a tafin hannun ta kamar hakan zan sanya ma batirin charji har ya kawo
"A ce mutum ya zama kurma a ƙungurmin dajin nan ta ina zai fara ga waya a kashe ba charji"
Tace tana mai jan tsaki daidai lokacin da Rahila ke kai bakin ƙofa za ta fice daga ɗakin. Jin haka ta juyo tana mai kallon hannun zainab, ko da ta shigo bata maida hankali ga hannun ta ba illa suturar da ta gani zube a gado musamman gajeren wandon zainab.
"Laaaaaaa!!! Wallahi irin abin da mai gidana ke magana da mutane in sun yi kinnafin, salla ko me ma sunan"
Tace tana ɓingere baki, duniya in akwai abin da ke birge ta yana bayan waya, don ta so Tanko ya bata ɗaya wata rana da ya shigo da su ya ce mata ai kudi ne maƙudai in ya siyar da su
"in sun yi mene? Ya aka yi ke kika iya hausa"
Zainab tace cikin firgici da farin ciki. Firgicin ambaton kidnapping da kuma farin cikin wacce ta ke jin hausa, hakan ya sa Rahila ankarewa da subul da bakan da ta yi, ta yi saurin gyara maganar ta hanyar fadin
"A'a wai in sun dawo daga wajen Sana'a na ke nufi..."
"Laaaa hausa ki ke min? Ki na jin hausa? Kin iya hausa?"
"Ai kusan rabin matan rugar nan in ba ma fiye da rabi ba suna jin hausa, Ce mi ki su ka yi ba da ji?"
Cewar Rahila ta na mai duban Zainab wacce alamar mamaki ya bayya na a fuskar ta, kafin bacin rai ya maye gurbin mamakin, murya kasa kasa ta ce
"Babu mahalukin da ya taba min, ko na mu su magana ba su nunawa sun gane bare su amsa, sai tsinannan dariya kamar mahaukata!"
"Hmmmm kadan daga cikin aikin Usman kenan!"
Cewar Rahila ta na mai jinjina kai na.
"Usman kuma, akan wani dalili"
zainab tace cikin ɓacin rai
"Zalunci! Ai babu azzalumi sama da Usman, Kinga da mahaifin Usman da na Tanko miji na uwa daya uba daya su ke, Amma Usman ya tunkude siriki na daga sarautar Rugar Shehu, haka kuma ya haye kujerat tare da haɗe dukiya gaba ɗaya, ya kada shanu kaf be bar mana ko daya ba ya tai dajin ga, ya bar mu ba cin yau bare na gobe, bakin cikin haka ya kar siriki na har lahira, dole ta sa mu ka bi sahun Rugar Shehu, gaban ki dai aka yi komai jiya....."
Ta kare maganar ta matsar kwalla. Cike da tausayawa Zainab ta furta
"Lalle ya cika azzalumi na gaske, tun da har ya iyayiwa jinin sa haka, ban yi mamakin abin da ya aikata gare ni ba......"
Nan ta kwashe komai ta fadawa Rahila, ta kare da
"Ni ban san yanda aka yi ba, zan dai tuna sanda na gama karatun jarabawar da zan zana, kawai sai wayar gari na yi na ganni kurgurmin daji hannun wannan azzalumin!"
"Surkulle kenan! Ai kiranye ya mi ki!"
Cewar Rahila ta na mai hango tarin dukiyar da Tanko zai samu ta sanadiyar Zainab, Dan kuwa kifi ne daga sama gashesahe, za su yi amfani da Zainab ta hanyoyi har biyu, na farko su kwaci Rugar Shehu ta hanyar hada baki da ita, Dan kuwa tun jiya ta gano Shehu na so da kishin Zainab, Zainab din ce dai ta kasa fahimta, haka kuma bayan sun kawar da Shehu su karbi kudi makudai na fansar Zainab, dan kuwa dai ba ta ga dalilin da zai sa Tanko ya ga Zainab ya mayar da ita salin alin hakan nan ba.
"ikon Allah, yanzu dai tun da na same ki baki munafunce ni ba kamar saura"
Maganar da ya dawo da Raliya daga wasikar jakin da ta fara. Jin Zainab na fadin
"ki min hanyar barin wajen nan ni kuma na miki alkawarin dukiya mai yawa sannan zan sa a kama azzalumin nan"
ya sanya Raliha murmusawa, kana ta bata amsa da
"In dai daga bangare na ne kar ki ji komai"
"Ni damuwata ma yanzu kaya na da duk suka yi datti, kazamai ne kaf dajin nan!"
Zainab tace ta na mai daga bumshort din ta biyu da su ka rage ma su tsafta.
"Laaaa wannan kamfai ne ko fatari?"
Yanda Rahila ta yi tambayar ne ya sanya Zainab dariya tare da fadin
"Bumshort sunan sa"
"Toh toh shi ma din a kasan tufa ake sawa ko? Kamar dai kamfe ko?"
"Ah ah, hakan nan din shi ake sawa, kuma kyau ya ke sosai, musammam in aka saka da yar riga kamar wannan..."
Ta yi maganar ta na mai daga shudiyar rigar ta, idanun Raliha har rawa ya ke tuni ta fara sakar zuci. Jin Zainab ta furta
"Ina ma birni na ke da na sa kin ga rayuwa, wannan dajin ma ina mutum zai saka...."
"Za ki iya mana!"
Rahila ta katse ta cikin farin ciki.
"Zan iya me?"
Zainab ta tambaya da zuciya daya.
"Sakawa, wannan hanya ce mafi sauki na tunzuru Usman, dan kuwa na lura ya na matukar kishin ki...."
"Mtswww kishin wa? Allah ya sauwake!"
Ta katse ta a fusace. Rahila na mai girgiza kai ta ce
"Na ce dai yanzun nan ki ka gama fadin na taimake ki ki bar dajin nan?"
Zainab ta girgiza kai alamar "eh"
"Toh ki saurara da kyau ki ji, mutum kamar Shehu sai fa kin masa bita da kulle dukan kabarin kishiya! Ni ba zance mi ki ga hanya daya da zan iya taimaka mi ki da shi ba matukar ba surkulle za mu yi ba, Usman kuwa babu surkullen da zai ci shi, ko siriki na ya buga ya bar shi...."
"Wani sirikin na ki? Ba kin ce ya rasu ba?"
Zainab ta tambaya cikin rashin fahimta, hakan ya sanya Rahila saurin gyara maganar na ta
"Ina nufin kafin ya rasu, eh kafin ya rasu din, toh dai abin da na ke nufi za mu ta gwadawa ne ko Allah ya sa a dace, yanzu dai ki fara da wannan shawarar da zan baki, ki saka wannan ki tai har fadar Shehu, na san matukar manya su ka gan ki da wannan shiga dole Usman ya ji kunya da kishi, kin ga a dole ya mayar da ke gun iyayen ki"
Zainab na mai tunanin ya aka yi wannan azancin be zo mata tun da ba ta amsa ma Rahila da toh.
"Anjima zan zo in je in wanke miki"
Rahila tace kafin ta fice tana barin zainab da auno kalar azabar da za ta sa a ma Shehu in ta isa gida. Ita kuwa Rahila tunanin yanda za ta isarwa mijin ta da wannan kyakkyawan labarin, dan ta san halin Usman duk hakurin shi matukar aka kai shi bango ya kan yanke hukunci mai tsauri, ko shakka babu idan har hakin ta ya cimma ruwa ya kori Zainab, mijin ta ya sami nama har gida, tsaf kame ta zai yi yayi gaba ko ba komai sa dan farfado.
Bayan fitowar Rahila Hansai ke tambayar ta dalilin dadewar ta a bukkar, tare da mata kashedi ta ce dai baki ta saki baki ta na ma Kado zance da Hausa ba, in haka ne ta kuka da kan ta. Cikin nuna kyamkayami ta ce
"Tir Allah wadar na ka ya lalace! Ina ni ina Kado maras daraja kamar wannan dai?"
Hansai na jinjina kai ta ce
"Gwara dai, babu ruwan ki da ita"
Zainab kuwa Raliya na fita ta aikata shawarar da aka bata. Shudin rigar ta damammiya ta saka, tare da bumshort din ta shi ma shudi, komai ya fitu zanzan duk da ramar da ta yi. Dan mitsitsin mayafi daya daga cikin doguwar rigar ta ta daura, dan shi kadai ya rage mata sauran duk tayi tutu akai.
Cikin annushuwan abin da ta ke shirin yi ta sa kai ta fito, wato ba Hansai da sauran jama'ar gidan ba, hatta Rahila da ta bata shawarar sai da ta bude baki cikin al'ajabi.
*Khadija Sidi*
Auren Shehu 2
8
Yanda kowa ya ke kallan ta ya sanya Zainab shakkar irin shigan da ta yi a kara na farko. Matan sun yi tsit in da masa yara ke kokarin rufe idanun yaran su gudun kar su ga tsairaici.
'Mata da yara kenan su ka shiga dimuwa saboda shigar da ta yi ina ga maza matasa da dattija da ke zaune fadar Shehu? Lalle babu maras daraja kamar wanga Kado'
Cewar Rahila cikin ran ta tana mai adduar Allah ya sa Zainab ta tabbata ballagaza ta taka har fada. Ganin Zainab ta dauki kafa tinkis tinkis ta na shirin fita Iyalle da ta kasa jurewa ta sha gaban ta cikin tsawa ta furta
"Waiyazubillah! Ina za ki fita haka tsurara? Wannan wani irin rashin daraja ne!"
Tafa hannu Zainab ta ke jin hausa radau bakin Iyalle wacce dimuwar ganin Zainab ya sa ta manta ta yiwa Zainab hausa.
"Ikon Allah da kin iya hausa shi ne da ki ka min kunne uwar shegu?"
Sai a sannan daga Iyallen har sauran matan gidan su ka ankare da subul da bakan da Iyalle ta yi. Cikin wayencewa ta na mai sosa kyeya ta karya harshe ta koma fulatanci. Hakan ne ya batawa Zainab rai ba tare da ta yi la'akari da shekarun Iyalle ba ta furta
"Dakin uwar ki zani! Na san kin ji wannan ma!"
Kuka Iyalle ta sa, ta na mai tafa hannu in da sauran matan gidan su ka shiga bata baki, Rahila ce mai ruko Hansai wacce ta ke kokarin damko Zainab da niyar bata kashi.
Cikin wannan hali ta sa kai ta fice daga gidan. Kamar yanda shigar Zainab ya girgiza ahalin gidan Shehu, haka ma sauran jama'ar Rugur, musammam maza domin kuwa shiga irin ta Zainab ko da wasa ba su taba ganin irin ta ba, dan a wajen su ba ta da maraba da tsirara. Babban abin da ya ke jan hankalin jama'ar rugur kuwa jikin Zainab ne, dan kuwa Rugar Shehu kaf babu mai irin shi, yawanci yara mata da sun fara dirgen dangin, mama ya dan tasa a kirjin su ake mu su aure, haka kuma maman ba ya zuwa koina daga sun haihuwa daya sun shayar sai ya zube sharkaf, dan haka akasalin Rugar daga wanda na su ya dan fara tasawa haka kuma duka an mu su baiko, sai na matan aure da ya zama silifas.
Wasu matasa da su ka kasa hakuri bin ta su ka ke yi a baya, Zainab kuwa ba ta fasa nufar Fadar Shehu ba. Bello wanda ya baro fadar kenan da niyar kai sako gidan Shehu ne ya fara ganin ta, ganin haka yayi ba shiri ya juya da saurin sa domin yiwa Usman gargadin masifar da ta dumfaro shi.
Cikin tashin hankali Usman ya bar fadar, abin ku da dogo nan da nan ya cimma Zainab tun kafin ta karasa fadar.
Ganin yanda ya tunkaro ta kamar zakin da ya shekara dari be ci abinci ba ya sanya matasa juyawa da sauri, ita kan ta sai da gaban ta ya fadi, Amma hakan be sa ta fasa tunkarar sa ba. Wani irin damka ya kai wa hannun ta har sai da ta saki kara, be kula ba haka kuma be iya duban ta ba gudun abin da zai iya aikatawa nan bainar jama'a matukar be danne zuciyar shi ba, ya soma jan ta kamar leda ba tare da ya ce mata uffan ba.
Duk yanda ta so ta cije ta ki bin sa abin ya gagara, ta na ji ta na gani haka su ka wuce sashin Shehu da sauran bukkoki, Zainab na waige waige cikin neman doki amma ganin yanda kowa ke dauke kai sanadiyar fushin Shehu ya sa Zainab saduda ta mai jiran tsammani. Ganin ya kutsa da ita dokar daji ya sa Zainab farin ciki, hakin ta ya cimma ruwa Usman yayi fushi gashi zai fitar da ita hanya.....wata boyayyar bukkar da ta hanga ne ya sanya murnar ta komawa ciki, musammam da ta ga sun nufi bukkar bilhakki. Cikin kokarin kwatar kan ta Zainab ta ke fadin
"Dallah malam ka sake ni! Ka sake ni! Ina ka ke ja na!"
Idan Usman ya tankawa Zainab toh dutse ma ya tanka. Bukka ce kwallin kwal sai garken Shanu wanda tsayawa fadar adadin su ma bata lokaci ne. Daga dayan gefen kuma yar karamar gona ce, sai kuma bishiyon kayan marmari da su ka hada da mangoro, leman tsaki, ayaba, fasadabur da dai sauran su.
Maimakom kufar karar da ta saba gani, kofa garwa ce jikin bukkar wanda duka daya Usman ya mata da kafadar sa ta bude, ya na mai jan Zainab su ka shige bukar sannan ya sake ta ta fadi kasa. Juyawa yayi ya jawo kofar ya rufe ta hanyar sanya mukulli da kwado ya datse.
Cikin faduwar gaba Zainab ta ke duban kofar, kafin daga bisani ta bi bukkar da kallo, bukkar na da girma sosai dan ta ma fi bukkar Shehu girma kadan, Amma idan aka dauke tabarmar kaba da ke shimfide tsakar dakin babu komai ciki. Da sauri Zainab ta tashi ta na mai fadin
"Da ka kawo ni nan uban me za ka...."
Yanda Usman ya juyo ya sanya ta zuke zancen ta, idanun ta cikin na sa da su ka yi jajur tamkar garwashi Zainab ta ja da baya a hankali ta na mai fadin
"Usman......"
Hannu biyu ya sa ya cire rawanin kan sa a saukake, karo na farko da ya bayyana mata fuskar shi hakan me ya sanya Zainab ruke numfashin ta. Ta sha ji ana cewa kyawu kamar mutum shi yayi kan sa, kokuwa ace kyawu kamar aljan ba ta taba gasgata akwai irin wannan kyawun ba sai a yau. Lokaci guda Usman ya rikide mata ya koma mata tamkar balarabe.
Ta san Usman fari ne, haka kuma ko ina ta ga manyan idanun Usman da kuma bakin gashin gira da na idanun sa za ta gane Usman din ne, haka kuma tun asali ba ta rena tsayin hancin sa ba, bakin lallausar gashi da ya taho tun daga kan sa, ya bi layin saje haka kuma ya sauka ta bakin sa ya na mai zagaye bakin ne ya kara kawata fuskar shi, ta zaci duk duniya babu gemu da shaje da zai kai na Sudais mijin Halitta kyau ba, ashe ba a banza Usman ya ke boye fuskar shi ba.
Ganin Usman ya sa hannu ya cire rigar jikin sa, yayinda faffadar kirjin sa wanda ke rufe ruf ruf da lallausar gashi ya bayyana, ga kuma kaunji nan duka hannayen sa ya sanya Zainab ja da baya. Yanayin bacin ran da ya ke ciki, wanda ya hadu da kyawun sa ya mayar da shi tamkar hatsabibi mai hatsabibin kyau.
"Usman.....me ka ke yi?"
Cewar Zainab cikin rawar murya ta na mai fitar da idanu.
"Hakkin ki zan baki Abu! Na ga kin fara fita hayyacin ki har ki na fitowa tsirara nema na...."
Cewar Usman yayinda ya nufota ya na kokarin kwance tazuge. Ganin haka haka Zainab ta fara ja da baya tana fadin
"Kar ka zo kusa da ni! Wallahi kar ka zo kusa da ni! Da na hada jiki da kai gwara na hada da kare! Kar ka zo...!"
Ina tuni ya kai ta makura, ta yi saurin gocewa ta na kokarin arta a na kare Usman ya cafko ta, sai gasu duka a kasa, ta na ihu, yayinda ta ke kokarin kai masa duka da yakoshi, Usman fe fasa hada jikin su ba yayinda ya sa hannun sa daya ya ruke duka hannayen na ta biyu cikin nuna mata karfi.
Duk yanda ta so kwatar kan ta abin ya gagara, tun tana zagi da tsinuwa, ganin da gaske Usman ya ke hakkin na sa ya ke kokarin karba har ya kai ga raba ta da tufar jikin ta, Zainab ta shiga hada sa da Allah, fadi ta ke
"Dan Allah Usman kar ka min haka! Dan Allah Usman.....dan Allah....."
Sam baya hayyacin sa bare ya san abin da Zainab ke fadi har sai da ya karbi hakkin na sa, Zainab ta tabbata matar shi ta sunna. Cike da mamakin kasancewar ta budurwa ya ke duk lalacewar ta da nuna tsairaici, ba kamar tsohuwar matar shi Cangwai ba. Yanzu shi ne namiji na farko da ya fara sanin Zainab a matsayin ta na diya mace! Abin da ya ke nanatawa cikin ran sa kenan yayinda ya ke jin zuciyar sa cikin wani irin yanayi da tun da ya zo duniya be taba jin irin shi ba.
A hankali ya kai kallan sa gare ta a karo na farko tun bayan da ya iya sakin ta, in banda ajiyar zuciya babu abin da ta ke, hawayen ke fita daga lumsasshen idanun. Takan yi wasa da komai amma ban da budurcin ta, ta yi tattalin sa duk da takan ji kunyar kasancewar ta budurwa duk sanda abokan huldar ta su ka sako ta gaba da tsokana, cewar su har yanzu ba ta da yancin kan ta, haka kuma an so kakarin raba ta da shi ba sau daya ba sau biyu ba amma Allah na bata nasarar tsallakewa sai yau, babban takaicin ta shi ne a rasa wanda zai aikata mata hakan sai Usman...
"Dan Allah dan annabi ka raba ni da rai na kamar yanda ka raba ni da martaba na, dan Allah ka kashe ni, idan ba ka kashe ni ba ni zan kashe kai na....."
Khadija Sidi
Auren Shehu 2
9
Ya na mai duban ta ya ce
"Ba zan kashe ki ba Abu, ba kuma za ki kashe kan ki ba har sai kin haifa min yaro ko yarinya, bayan nan sai ki yi duk abin da ki ka so da rayuwar ki"
"Allah ya isa! Da hankali na ba zan haihu da bagidaje kamar ka ba! Da na san rana irin ta yau za ta zo, ranar da kazami irin ka zai min fyade da ban adana kai na ba!"
Cewar Zainab cikin tsananin tsanar Usman. Ba ta gushe ba ta kara da
"Ka cuce ni! Ka lalata min rayuwa! Na tsane ka! Na tsane ka!"
Cikin nuna halin ko in kula Usman ya tashi ya shirya tsaf duk da har cikin zuciyar sa ya ke jin zafin kukan Zainab. Ya na gama shiryawa ya sa mukulli ya bude daki ya fita, har zai fita sai kuma ya tsaya ya na kallan ta ta wutsiyar ido ya ce
"Na gane darajar ki be kai ki zauna cikin ahali na ba, dan haka daga yau wajan zaman ki kenan....."
"Allah ya isa! Mugu azzalumi! Har wani ahali gare ka? Yanda ka min Allah ya ma ka!"
Cewar Zainab a fusace, ji ta ke kamar ta sheke Usman har sai ta ga ya dena numfashi. Ta na juyo sa ya sa kwado daga waje ya kullo daki. Duk yanda ta so ta sami makami a dakin rasawa ta yi, tabarmar ce dai nan tilo ciki. Ta na mai hade kai da gwiwa ta fashe da kuka tamkar ran ta zai fita.
Usman kuwa da fitar shi kogin da ya bi ta yankin gidan gonar ya nufa, da ke dama an killace wajan ne musammam saboda Shehu, Dake ruwan kogin ba tsayayye ba ne, mai tafiya ne, ciki yayi wankan shi har da na tsarki sannan ya koma cikin Rugar Shehu. Tun shigar sa Rahila ke zuba ido ko za ta ga Zainab dan kuwa matukar Usman ya mayar da ita ba tare da Tanko ya damke ta ba ba karamar asara za su yi ba. Sauran jama'ar gidan kuwa farin cikin ganin Usman shi kadai ya dawo su ka yi, a tunanin ya sallami Zainab sun huta.
Bukkar sa ya shiga ya hade kayan Zainab tsaf cikin akwaiti, sanan ya kira Iyalle ya ce da ita idan ta na da sabbin kayan saki na siyarwa ta ba shi zai siya. Cike da mamakin wacce za a siya Iyalle ta dauko kayan saki har biyu ta bashi, Nan ta ba shi labarin zagin da Zainab ta yi ma ta. Ya na mai bata hakuri tare da mata alkawarin hakan ba zai kara faruwa ba dan kuwa yayiwa tufkar hanci, can gidan gonar sa Zainab za ta zauna ita kadai. Iyalle ta amsa da
"toh hakan ma yayi"
Duk da har cikin ran ta ba haka ta so ba. Shi ya dauki akwatin Zainab da kan sa ba tare da ya bari an daukar masa ba, ya koma gidan gona. In da ya bar ta nan ya tadda ita zaune ba ta motsa ba, ganin shi da akwaiti ta ga kuma kayan saki hannun shi, ta zuba masa jajayen manyan idanun ta ba tare da ta tanka masa ba. Shi ma din tun da su ka hada idanu ya ya dauke kai tare da aje akwatin gefe guda, ya daura kayan bisa sannan ya fice.
Jim kadan ya dawo, ya na duban ta ya ce
"Tashi ki yi wanka"
Zainab ta masa banza. Hakan ya shi kara fadin
"Wankan tsarki na ke nufi, lokacin sallah na gabatowa....."
Zainab ta ki kula sa sai ido kawai. Da ya ga haka sai yayi ficewar sa. Nan cikin gidan gonar ya ta kai kawo, ya rasa abin da ke masa dadi dan ko fada ya kasa komawa tunanin Zainab da halin da ta ke ciki ne ya addabi rayuwar sa, fata ya ke Allah ya sa be ji mata rauni ba dan be taba kallan Zainab a matsayin budurwa ba, ba dan komai ba sai dan dabiun ta da kuma yanda ta kaya tsakanin sa da tsohuwar matar shi Cangwai.
Da ya kasa hakuri sai ya komawa Iyalle, kunya da nauyin ta da ya ke ji ya aje gefe ya tambaye ta ya su kewa macen da ta kai budurcin ta dakin miji. Jin haka Iyalle ta san ta faru ta kare an yiwa mai dami daya sata, Kado dai zama ma yanzu ta fara kenan. Nan ta sheda masa cewar lalle ya kamata ta kama ruwa da ruwan dumi koda kuwa ba za ta yi wanka da shi ba, haka kuma za a bata abinci mai kyau da nama tare da kunu ta sha da zafin shi wannan tukwici ne na musammam.
Itace ya sa a aika masa gidan gona, ya na mai adduar Allah ya sa su wanye lafiya da Abu. Sai da ya tabbatar ya barwa Iyalle dukkanin abin da za a bukata domin a yiwa Zainab girkin tukwici sannan ya sake komawa gidan. Da kan sa ya hada murhu ya dora ruwan zafin, ya sami bokiti da kuma wani garwa mai fadi ya aje kewaye wanda be da maraba da na gidan Shehu, dan shi ma din babu masai. Sai da ya jira ruwan yayi zafi, ya zuba cikin bokitin da garwan ya sirka yanda Zainab za ta ji dadin sannan ya koma bukkar ya tadda ta zaune in da ya bar ta. Ganin ya nufota be sa ta motsawa ba, sai da ta ga ya sunkume ta ta rufe shi da zagi da tsinuwa ta na mai kai masa duka. Sam be kula ba haka ya kai ta har kewaye, da kayan jikin ta da komai ya aje ta cikin garwan ruwan na mai fantsalo masa gaba daya ya jika gaban rigar sa.
"Ba dan ina gudun kar na kai ki kogi wani ya gane min ke ba wallahi da can zan kai ki na ga karshen taurin kunne!"
Cewar Usaman ya na mai kara mayar da Zainab cikin garwar wacce har lokacin yunkurin tashi ta ke, hannyen sa biyu ya sa a kafadar ta yayinda ya ke dada zaunar da ita cikin ruwan.
"Allah ya isa! Mugu azzalumi! Ba zan yi wankar ba jikin ka ko nawa!"
"Jiki na! Ke makalla ki na ce haka Allah ya tsara shi ya sa ma duk lalacewar ki ba ki ba da budurcin ki ga wani ba...."
Tas ta dauke shi da mari, maimakon ta tunzura shi sai ma ya sakar mata murmushi, yayinda ya saki kafadar ta ya ce
"Ko Iya ta bata taba kai hannu fuskata ba Abu, Amma na mi ki uziri domin yau kin bani abin da ban taba tsammani zan samu daga gare ki ba duk da ta karfi na karba amma hakan ma na gode Allah ya yi albarka...."
"Allah ya isa!"
Zainab ta katse shi cikin kuka da ihu. Hakan ya sa Usman ficewa ya na mata dariyar mugunta. Bayan fitar Usman Zainab ta dan sami nutsuwa har ta fara jin dadin ruwan. Da burin kwatarwa kan ta yanci ta hakura ta cire kayan ta yi wanka ta na kuka, sosai ta wanke jikin ta ta na mai fatan wanke daudar hada jikin ta da na Usman.
Zanin da ya aje mata ta daga waje ta janyo ta daura bayan ta gama dauraye jikin ta ta yi wankan tsarki. Ko da ta fito ba ta gan shi ba sai ta yi maza ta shige ciki. Kayan ta mai dauda ta saka ta na mai watsi da kayan sakin da Usman ya aje mata. Wajan karfe uku aka aiko yara da kwararen abinci. Zainab na kalla ga bakin yunwa ta na ji amma bakin ciki ya sa ta kasa bude kwararen bare ma ta san abinda de ciki. Haka ta wuni ita kadai, tun tana firgita duk sanda shanu su ka yi kuka, har ta saba da jin koken su.
Da la'asar sakaliya ya dawo ya tadda ta zaune baci ba sha, ya na mai duban kwararen da daga gani ko bude su ba a yi ba ya furta
"Halan azumi ki ke?"
Ta masa banza. Ya na mai gyara tsayuwa ya kara da
"Toh ai ko azumin ne ai na karya shi dazu Abu, ki saki ran ki ki ci abinci"
"Ba zan ci abincin ba! Ina ruwan ka da cin abinci na?"
"Ni kuwa na ke da ruwa! Idan har ba ki ci kin koshi ba ina za ki sami damar bani hakki na?"
Usman ya bata amsa ya na mata murmushin mugunta. Hakan ba karamin tunzurata yayi ba, a fusace ta ce
"Ka sake ka kara zuwa kusa da ni sai na lahanta ka Usman!"
"Zuwa kusa da ke yanzu na fara, hakki na sai kin bani! Kuma ni ba na son raguwar mace! Na fi son mace mai kuzari, Dole ki ci abinci ko kuwa na dura ma ki ta karfi da yaji!"
"Hakan nan dai! Abin da ka iya kenan! Sai ka yi mu gani ai"
"Na baki minti talatin kacal matukar na dawo ba ki ci abinci ba ki kuka da kan ki"
Cewar Usman yayinda ya fice ya bar Zainab ta na bambami. Ko da ya koma bayan minti talatin din da ya ce, ba ta ci abincin ba. Kamar yanda ya ce zai mata dure, haka ya cafko ta cikin kokuwa ya matse kafafun ta cikin na sa, yayinda ya daure hannayen ta biyu ta bayan ta da wani dan kyelle, kunun da Iyalle ta aiko mata da shi ya shiga dura mata ta karfi da yaji Zainab ta datse bakin ta ki budewa bare ma ya samu ya shiga bakin ta.
Ganin haka Usman ya sa hannu ya ruke hancin ta yanda ba za ta iya nufashi ba matukar ba baki ta bude ba, da wuya ta yi wuya sai gashi ta bude bakin, yayi saurin dura mata, cikin kokarin numfashi kunun ya shige makoshin ta har ta kusa kwarewa amma Usman be sarara mata ba, haka sai da ta kusa shan rabin kunun sannan Allah ya bata iko ta sanya duka karfin ta ta kwabar da kwaryar da kirjin ta, nan bisa tabarma kunun ya malale.
Bin kunun yayi da kallo kafin ya dawo da kallan sa bisa fuskar ta wanda yayi shabe shabe da hawaye, ya bi bakin ta da yayi dumu dumu da kunun da ta tuzur ya ganganra har wuyar ta. Ba ta ankara ba sai gashi ya fara lashe kunun tun daga bakin ta yana kokarin sauka har wuya. Zainab ta saka ihu fadi ta ke
"Allah ya isa! Allah ya isa ban yafe ba! Allah ya isa wallahi sai Allah ya saka min! Maye! Maye kawai!"
Sai da ya lashe kunun nan tsaf sannan ya sake ta ba tare da ya kunce mata hannu ba, cikin akwaitin ta ya bude ya dauko doguwar rigar ta da bumshort, ganin ya sunkuya ya na goge kunun da ya zube bisa tabarmar cikin haki Zainab ta furta
"Wai kai wani irin azzalumi ne! Tufa ta ka mayar tsumma! Wallahi sai na saka an daure ka! Bari na samu na fita daga dajin nan! Ka kuka da kan ka Usman!"
Sai da ya gama gyara wajan tsaf, Zainab ta na ji ta na gani ya watsa kayan waje sannan ya kunce ta. A hankali ya furta
"Tun da wannan rayuwar ki ka zaba, Ni ma ita na fi so Abu, ki cigaba da taurin kunne ni ma kuma ba zan fasa aikata san rai na akan ki ba, ki sani daga ni sai ke a nan, ihun ki banza gwara ma kin sadudu...."
"Akwai Allah! Allah ne zai min maganin ka!"
Cewar Zainab cikin mayar da martani. Usman na murmushi ya furta
"Ashe kin san akwai Allah Abu?"
Shiru ta masa yayinda ta ke duban sa cike da tsana, cikin ran ta kuwa alwashin ramuwar gayya ta dauka kan Usman ko da kuwa za ta rasa ran ta ta sanadiyar haka.
Rahila kuwa ba ta yi kasa a gwiwa ba ta saci hanyar zuwa neman mijin ta Tanko, har ta fara fitar da rai sai gashi zaune in da Usman ya masa mararraba da Rugar Shehu. Sam be yi mamakin ganin ta ba dama tun kafin su iso sun shiryawa Usman, sun san zai iya hana Tanko zaman Rugar, dan haka su ka yi Rahila ta mu su leken asiri, haka kuma da ta sami wani hanyar tunkube Usman ta fito ta nemi Tanko.
Cikin rawar jiki ta kwashe komai ta fada ma Tanko. Cike da jin dadi Tanko ya ce
"Biri yayi kama da mutum! Ni na ga soyayyar kwadon nan cikin idanun Usman, ko shakka babu Usman ya kasance mai rauni a kan ta. Haka kuma daga gani diyar masu daula da daukaka ce, lalle kuwa za mu jefi tsuntsu biyu da dutse daya Rahila, kin yi aiki mai kyau ina alfahari da ke"
Jin yabo daga bakin mijin ta dadi ya cika Rahila, ba su sallama ba sai da ta masa alkawarin cika masa burin sa.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Usman da Zainab suna zaman doya da manja har tsahon kwana uku, haka kuma be mayar da ita cikin ahalin sa ba ba sai ma kwaso na sa kayan yayi, nan su ka zauna da ga shi sai ita a gidan gona. A iya kwanakin da su ka yi tare, Zainab ta gano wasu dabiu na Usman da ya sanya sam ba ta taba jin wari ko makamanci shi ba a tattare da Usman. Na farko dai Usman mai yawan aswaki ne, yayi koyi da wannan hadisin da Manzo (SAW) ya ce ba dan kar na takurawa al'umata ba da na ce su dinga aswaki duk sanda za su yi alwala, haka Usman ya ke shi ya sa ko da yaushe bakin sa ya ke wasai haka kuma ya ke da fararen hakora. Bayan wannan duk da ba a raba hammatar Usman da gashi, sam ba ta taba ji ya na bugawa ba, ta sha ganin yana shafa farin abu kamar gari a hammatar shi duk sanda yar tsokanar ta tashi ya zabi ya sanya kaya gaban ta, sai daga baya ta gano ashe alimun ya ke shafawa, har ita ma ta fara fakar idanun shi ta na dan shafawa. Batun kamanin Usman kuwa bugun zuciyar ta na karuwa duk sanda ta ga Usman ba rawani, har ta kai ta na gujewa kallan sa musammam idan be da riga jikin sa.
Ran da ta cika kwana hudu ne ta tashi da zazzabi, hankalin Usman ba karamin tashi yayi ba musammam yanda ya ga ta na rawar dari. Duk taurin kan Zainab sai da ta yi laushi, cutar ta mata mugun cafka dan har da rashin cin abinci da ta ke yi. Hatta wanka shi yayi mata a ranar, rigar nan ta saki ya sanya mata tare da rufa mata zani, kafin ya shiga daji neman magani.
Cikin kankanin lokaci ya samo maganin da su ka saba sha duk sanda su ke mashasshara, Iyalle ya bawa ta dafa masa shi tare da jan kanwa, aka hada da abinci aka kai gidan gona in da Usman ke ta kai kawo dan zama ma kasawa yayi.
Kamar yanda ta saba masa gardama, yau din ma da kyar ya samu ta ci abincin da aka aiko musu, shinkafa ne da mai da yaji. Sai da ya ga ta danci sannan ya fara kokarin bata magani, nan ma sai yayi da gaske ta sha, aje kwaryar maganin yayi yayinda da ya jawo ta kirjin sa ya rungume. Yanda ya ji ta yi lamo ba tare da ta yi yunkurin kwatar kan ta ba Usman ya tabbatar Zainab na jin jiki. Cikin rada ya furta
"Ya zan yi da ke Abu? Duk yanda ki ka bata min! Duk yanda na so na gana mi ki azaba Abu na kasa, Abu kin cutar da ni amma gashi kin shiga rai na, ya zan yi da ke Abu?"
"Ka rabu da ni na mutu ko kuwa ka mayar da ni in da ka dauko ni"
Cewar Zainab daga can kasan makogaro. Usman ya dada rungume ta kamar wanda zai mayar da ita jikin sa ya furta
"Ba zan iya ko wani daya daga cikin su ba Abu, ba zan iya rabuwa da ke ba..."
Jin haka Zainab ta fara kokarin cire jikin ta daga na shi, hakan ya sa shi kara ruko ta sosai. Ya na shafa bayan ta ya ce
"Shhhhh! Ni da ke ba mu taba samun kusanci mai cike da nutsuwa irin na wannan yanayin ba, ki kwanta kawai Abu, ki yi shiru abin ki idan kin sami sauki za mu tattauna, Allah ya baki lafiya"
Karo na farko da Zainab ta bi umarnin sa cikin kwanciyar hankali, ta na mai runtse idanu ta yi kwanciyar ta jikin sa har bacci ya sace ta.
*Khadija Sidi*
Auren Shehu 2
10
A hankali ya kwantar da ita tare da mata matashi da daya daga cikin kullin rawanin sa, ya mata addua ya tofe ta. Cikin sanda kar ya tashe ta ya wuce fada da niyar sauraran korafe korafen jama'ar Rugan Shehu kafin Zainab ta tashi.
Be yi cikakken minti ishirin da tafiya ba kukun daya daga cikin shanun gonar ya dami Zainab har ta kai ga farkawa. Duk wanda ya saurari yanda saniyar ke kuka dole ya gane ta na cikin azaba. Tun Zainab na iya jurewa a tunanin ta Usman na tare da shanu, har ta kasa ta fito, Nan ta ci karo da abin da ba ta taba gani ba tun da ta zo duniya, ba ga bil adama ba bare dabba. Saniya ce ke kai kawo, ta baro cikin yan uwan ta shanu zuwa farfajiyar bukka, duk sanda ta taka daya biyu sai ta tsaya ta na mai fitar da sauti yayinda wani farin abu ke kokarin fita daga jikin ta.
Ganin haka Zainab ta ja da baya a tsorace har ta na shirin rugawa duk da dai sam ba ta jin dadin jikin ta, kiran sunan Usman ta ke bilhakki yayinda ta duba lungu da sako na gidan gonar babu Usman babu alamar sa.
Jiki na rawa ta kara dawowa ga saniyar, sai sannan ta gane wannan farin abun mai yauki yauki ba komai ba ne fyace dan saniya ne ke kokarin fiitowa, Saniyar nan dai nakuda ta ke. Hankali Zainab ba karamin tashi yayi ba musammam yanda ta ga wajan na kara budawa duk sanda Saniyar ta dan tsaya tare da durkusar da kafafun ta na baya, haka kuma ta dan tasa sai ta cigaba da takawa, da ke dabba dabba ce ciwan da take be hana ta cin ciyawa ba duk sanda ta gifta ta gaban sa.
Kamar yanda Saniyar ke kuka haka Zainab ke taya ta, haka kuma ita ma ba ta fasa safa da marwa ba ta na mai bin sahun Saniyar. Usman tafe tun kafin ya iso gidan gonar ya ke jiyo kukan Saniyar, tsoran kar ta cutar da Zainab ya sa shi karasawa da gudu.
Sa kafar sa gidan yayi daidai da lokacin da saniyar ta durkusar da kafafun ta na baya, kamar mai Shirin zama kasa ta sullubo yar saniyar ta akan idanun Zainab. Idanun Usman kan Zainab, tashin hankalin da ta ke ciki be boye kyawun halittar ta ba, dan kuwa Usamn zai iya rantsewa tun da ya zo duniya be taba ganin bafulanar da kayan saki ya mata kyau ba kamar yanda yayiwa Zainab, rigar ya saukar mata har ciki, abun ku da mai hips sai zanin ya zauna mata a kugu ya mata cif cif.
"Abu..."
Usman ya kira sunan ta cikin wani irin yanayi, hakan ya sa Zainab juyowa da sauri dan sam ba ta lura da shigowar sa ba saboda idanun ta na kan saniyar nan da ke kokarin lashe abin da ta haifa. Ganin sa da gudu ta nufe shi, cikin kuka ta shige jikin sa hakan ya sanya Usman runtse idanun sa, kan ta bisa kirjin sa yayinda ta ruke sa gam ta ke fadin
"Haihuwa ta yi, a gaba na ta haihu! Wallahi ta haihu!"
Usman na mai shafa bayan ta cikin rarrashi yayi karfin halin furta
"Yi shiru bar kuka Abu, kin ga baki da lafiya, ai ta riga ta haihu ni ma kin ga wata rana haka za ki haifo min diya mai kama da ke....."
Cikin sauri ta zare jikin ta daga nashi, cike da tsiwa ta furta
"Allah ya sauwake na haihu da kai gwara...."
Cike da danasanin furucin sa da ya ja masa rage jin dadi ya furta
"Don Allah kar ki karasa! Kin ga dai muna da mai jego be kamata mu na hayaniya gaban yar jinjira ba! Bari na taimaka mu su"
"Mtswww"
Amsar da Zainab ta bashi kenan yayinda ya wuce ta ya na mata dariyar kyeta. Sai da ya cire rigar sakin sa da rawani ya rage daga shi sai dogon wando sannan ya shiga taimakawa saniya. Bini bini sai ya kama Zainab wacce ke zaune bisa kujerar tsakar gida daga gefe ta na satar kallan sa, daga sun hada ido ta yi saurin kau da kai gefe.
Cikin ranta mamakin kyau da kyan sura irin na Usman ta ke, lalle Usman ya isa wannan kalmar ta "Man" dan kuwa da a ce wayayye ne da Zainab ta yi alfahari da shi, duk abin da ta ke mafarki na kyawun da namiji Usman na da shi, gaba daya sai ya dishashe mata duk wani kyan Sudais da ta ke gani, sai dai Usman kauyenci ya masa kan ta.
"Ina ma a dauki wayewar Sudais a bawa Usman"
Cewar Zainab cikin ran ta, gaba daya ta shagala cikin tunani sai tsuntar idanun ta tayi cikin na Usman, hakan ya sa ta kawar da kai cike da jin kunya. Usman na murmushin jin dadin yanda matar ta sa ke satar kallan sa ya ce
"Babu komai Abu ki kalle ni da kyau, ai ni mijin ki ne lillahi warasulihi! Jira na ke ki shirya na fara biyan bashin sadakin da na mora!"
Cike da jin kunyar ya kamata a karo na farko Zainab ta nemi amsar da za ta bashi ta rasa, ta tsinci kan ta tana mai tambayar
"Mace ce ko namji?"
Cikin rashin fahimtar abin da ta ke tambaya ya ce
"Me fa?"
"Abin da ta haifa, mace ce ko namji"
"Oh mace ce"
Ya bata amsa a taikaice yayinda ya ke duban yar jinjirar saniyar, har lokacin saniyar na lasar abar ta.
"Wani suna za a sa mata?
Zainab ta kara tambaya zuciyar ta daya. Usman na mai darawa ya bata amsa da
"Har wani suna na musammam ake sakawa dabba? Kai wani abun sai yan birni, toh wani suna ki ke so a saka mata?"
"Halitta!"
Cewar Zainab kai tsaye. Yanda ta fada da iya gaskiyar ta da kuma yanda ta yi mirsisi da fuska ne ya sanya Usman fashewa da dariya mai karfi har yana jefa kai baya. Yanda ya ke dariyar ya sa Zainab saka dariya. Sai ga su duka biyun suna dariya har Usman ya kare ta sa dariyar Zainab ba ta dena ba tsabagen na ta na muguntar ta ga yar saniyar ta mata kama da kanwar ta ta Halitta.
Tsayawa Usman yayi ya na kallan ta cike da sha'awar yanda fara'a ke yiwa Zainab kyau, tun da ya ke be taba ganin ta cikin annushuwa haka ba. Ko da ta ankare da kallan da ya ke mata nan ta ke ta tsuke fuska, Usman na murmushi ya ce
"Fara'a na mi ki kyau Abu, MashaAllah ki na da kyau"
Shiru ne ya biyo baya na dan wani lokaci, kafin daga bisani yayi gyara muryar ya ce
"Allah sarki Halitta, mace ce ta gari mai tsoran Allah....."
Wani irin bakin kishi ya taso ya tukare kirjin Zainab musammam da ta ji Usman ya kara da
"Darajar ta ya wuce a saka ma saniya sunan ta, ki bari idan ki ka haifar min diya a saka mata Halitta...."
"Aikin banza aikin wofi! Toh da ka san ita ka ke so ai da ka fadawa Daddy da be yi kuskuran aura maka macen da ba ta gari ba! Ka ga ita ba ma sai ka sato ba! Amma ka yi kum aka daura min auren masifa! Ka rabo ni da uwa ta, da yan uwa na! Da wayewa! Da makaranta ka kawo ni duhun daji bayan ka san natsane ka! Ran da na fara ganin ka na tsane ka! Har wata mace ta gari! Me ya sa ba ka aure ta ba! Allah ya isa wallahi!"
Ta wuce jiki da suri gudun kar hawayen da ke idanun ta su kunyata ta su zubo gaban Usman. Cike da mamakin me ya fada har ya tunzura ta haka ya bi ta da kallo dan sam be kawo a ran sa kishi ba ne. Zainab kuwa zubewa ta yi bisa tabarma ta sha kukan ta, wato ko a kauyen ma sai Halitta ta daga mata hankali, ta na can Saudia tare da na ta mijin amma ga Usman nan sai yaban ta ya ke.
Usman kuwa nan ya yi zaman sa sai da ya killace saniyar sa tsaf, har ya samu karamar ta fara shan nono, sannan ya nufi bukkar dauke da damammiyar furar da aka aiko masa da shi bayan Zainab ta shige ciki.
Ko da ya shiga ya aje kwaryar yayi gefe ba tare da ya tanka mata ba, yana kokarin saka riga ya ga ta ja kwaryar da kan ta, ta bude ta fara shan furar. Cike da mamaki ya ce
"Yau kuma yunwa ake ji Abu?"
"Na ga alamar so ka ke ka kashe ni, gwara na ci na koshi ko na sami damar yakar ka"
Cewar Zainab yayinda ta ke hadiyar furar da ko sukar babu, ta karfi da yaji ta ke sha. Be bata amsa ba sai da ya sanya rigar sa tsaf, ya zo ya zauna kusa da ita, hakan ya sanya Zainab matsawa da sauri gudun kar su hada jiki. Sai a sannan ya lura da idanun ta da yayi jajur, da alama kuka ta sha. Be tambaye ta dalili ba, Hannu ya kai goshin ta domin ya ji ko zabin da jikin ta ya kara raguwa dan dazu da ta rungume shi be ji zafin sosai ba. Da sauri ta buge hannun ta na mai kokarin kwada masa lodayi, ya janye hannun tare da fadin
"Na zaci mutuwar ki ke so ki yi ai? Me m ki ka ce? "
Ya fada cikin kokarin tuno kalaman Zainab, ya kara da
"Yauwa ka kashe ni ko na kashe kai na...."
Zainab ta masa banza ta cigaba da shan furar ta, har ya fitar da ran za ta kara tankawa sai ji yayi ta ce
"Wannan wani irin rayuwa ne a ce babu asibiti? Yanzu wannan dabba ce ta haihu fa, ina ga mutum?"
"Mu na da unguwar zoma"
Ya bata amsa a taikaice. Cikin rashin gamsuwa Zainab ta furta
"Idan kuma haihuwar ta zo da tangarda fa? Unguwar zoma ta iya tiyata ne? Sauran rashin lafiyar ina ake duba mutum bare a san cutar da ke damun shi a bashi magani?"
Shiru Usman ya mata yayinda ya ke tuno haihuwar Cangwai da ya zo da tangarda har ta kai ga rasa ran ta, haka ma na wasu dirgaggu da ba zai iya mantawa ba. Daga bisani ya furta
"Abu?"
"Uhum"
Ta bashi amsa baki cike da fura.
"Ya jikin ki?"
"Da sauki, wannan maganin da bani ya taimaka min"
Usman na gyada kai ya ce
"Kenan muna da magani mai kyau ko? Muna shiga dawa mu samo Allah ya mu ilimin, sarrafa su kamar yanda yan birni su ke sarrafa shi ne ba mu iya ba, shi ya sa na ke mana kwadayin sayasar tallfin ruga da shugaban kasa ke san kawowa"
"Ruga settlement policy?"
Zainab ta tambaya. Ya girgiza kai tare da fadin
"Haka na ji ana ce masa a turance, Allah ya sa dai ba zagin mu ku ke ba"
Zainab na mai murmusawa yayinda ta rufe kwaryar furar ta na kokarin aje ludayi Usman ya karbe, ya ja kwaryar gaban sa, maimakon ya dau nasa ludayin, sai ya ki da na ta ludayin ya fara sha yana mai sai ta daidai in da Zainab ta sanya na ta bakin, ita kanta Zainab ta lura da hakan dan kuwa ta ji wani irin yar har tafin kafar ta. Shiru ne ya biyu baya kafin daga bisani Usman ya ce
"Abu ina neman alfarma, me zai hana ki na dan koyar da yaran Rugar nan boko...."
"Gidan fa? Na ce da kai ka mayar da ni gida!"
Zainab ta katse shi cikin bamnami. Kai ya girgiza mata alamar "ah ah" ba tare da ya tanka ba. Tashi ta yi za ta fita har ta kai kofa sai ta sake dawowa ta ce da shi
"Dajin nan ba su iya hausa ba kuma ba sa ji, ni kuma ba na jin fulatanci, ban iya ba, ta yaya ka ke so na koyar da su?"
Jin haka Usman har da kwarewa, ta na kallan sa ya karaci tarin sa babu ko sannu, bayan da ya gama ya dago ya na duban it bakin sa kunshe da dariyar mugunta ya ce
"Kar ki damu ai da na ce mu su da ga yau kun iya hausa kawai za ki ji sun yi"
Yanda ta yi da fuska ta na kallan sa ya sa shi kasa daurewa sai gashi na ya na dariya sosai, hakan ne ya kara tunzura ta ta furta
"Na dade ban ga azzalumi irin ka ba Usman!"
Ta fice cike da fushi, Usman kuwa be dena kyakyacewa ba.
Sai da Zainab ta kwana uku ta na jinya sama sama sannan ta sami sauki. Wata ranar lahadi da safe, Usman na shirin tafiya fadar Shehu Zainab ta ce da shi ta amince za ta koyar da yaran Rugar sa. Jim yayi ya na mamakin amincewar ta dan kuwa sam be yi zato ba. Cike da mamakin yanda Zainab ta ke canza masa ya ce da ita ta bari idan ya dawo za su yi maganar.
Ko da ya dawo ya kara tambayar ta, ta jaddada masa eh da gaske ta ke Usman yayi murna kwarai. Sai dai duk yanda ya ke jin dadin zaman gidan gonar daga shi sai Zainab dole ya mayar da ita cikin alhalin sa. Cikin lallami ya sheda mata, nan ma mamaki ta ba sa dan kuwa nuna masa ta yi ta na maraba da hakan dama ta gaji da zaman kadaici duk sanda ya fita hakan nan ta ke zama daga ita sai shanu da tsintsaye.
Usman be mayar da Zainab ba sai da ya tabbatar ya gina mata bandakin kara na ta ita kadai, duk da dai shi ma din ba masai gare shi ba sai dai duk sanda tutu ya matso ta shi da kan sa ya ke raka ta daji. Ba Usman ba hatta su Iyalle sun yi mamakin sauyin da su ka gani tattare da Zainab, haka kuma Usman ya ba da umarnin a ringa yiwa Zainab hausa hakan ya ba ta damar koyawa yara har da yan mata karatu, matasa maza ne dai Usman ya hana saboda kishin kar su na kalle masa Zainab. Duk sanda wani daga cikin yan rugar ta yiwa Zainab hausa sai ran ta ya sosa, wato da gaske dai sun iya hausan, kawai mugunta ya sa da ba sa kula ta. Ta sha alwashin sakawa Usman da daidai yanda ya mata ta hanyar da be taba tsammani ba.
Inda kowa ke nan nan da Zainab, Raqeeba da Rahila kuwa bakin ciki ne ya maye zuciyar su, musammam Rahila wacce ta riga ta yiwa mijin ta Tanko alkawarin kawo karshen Usman ta hanyar Zainab, da kuma samin damar cafkar ita kan ta Zainab hankali kwance, gashi duk yanda ta so ta dan kyebe da Zainab ko ta dan zuge ta abin ya gagara.
Babban tashin hankalin ta shi ne yanda Usman ke nan nan da Zainab, babu wanda be lura da yanda ya canza ba, walwalar shi ta karu, haka ma yawan zaman shi cikin gidan. So tari sai ya faki lokacin da Zainab za ta koyawa yara karatu sai ya kirkiri wani aikin da zai iya zama tsakar gidan yanda shi ma zai samu ya dan tsinci darasin, ya na so ya ce ta na koyar da shi amma ya na tsoran harshen Zainab.
Haka rayuwa ta cigaba har tsayin sati biyu, Rugar Shehu kaf maganar Zainab ne a bakin su domin kuwa jan su jikin ta ta ke sosai, haka ya sa Usman fara sakin jiki da ita, duk dai har lokacin ta ki yarda ya fara biyan bashin sadakin ta, duk sanda ya zo da batun ta tashi su yi karatu ya fara sauke nauyi sai ta ce bacci ta ke ji.
Misalin shadaya da rabi na dare Usman na zaune bakin kofar bukkar sa, tunanin duniya da yanda zai yi da Zainab ne ya addabi zuciyar sa, haka kawai ya ji zuciyar sa na kwadaita masa san ganin ta. Tun yana iya jurewa ya kasawa yayi, cikin himma ya tashi ya shige bukkar.
Bisa gadon kara ya tadda ta kwance ta yi daidai ta na bacci, da ke garin akwai hasken wata be damu da ya kunna fitilar acibalbal ba. Sanye ta ke cikin kayan saki, ta dunkule jikin ta kamar mai jin sanyi hakan ya Usman dauko daya daga cikin haramin sa mai kauri ya rufe ta da shi, tare da mata addua ya tofa hannun sa sannan ya bi jikin ta ya shafe, ga mamakin sa sai ji yayi ta furta
"Usman"
"Abu"
Ya amsa ya na mai kokarin kallan fuskar ta dan a tunanin sa tashi ta yi. Ganin idanun ta rufe ya san bacci ta ke yi, cikin mafarki ta ke kiran sunan sa. Ya na mai shafa fuskar ta ya yunkura zai tashi Zainab ta ruko hannun sa, cikin magagin bacci ta ce
"Kar ka tafi, ka kwanta mu yi bacci"
Toh dama abin nema ne ya samu, ba musu Usman ya shimfide kusa da Zainab, yayinda ta yi saurin dora kan ta jikin sa ta na mai sakin ajiyar zuciya. Dama mafarki ta ke da Usman tun kafin ya shigo dan haka ba ta yi yunkurun hana shi aika mata sakonnin da ya fara da hannun sa ba, sai ma taya shi da ta yi ta hanyar masa sabon abun da sai da ya je birni ya taba gani turawa na yi a talabijin, wato "kiss" a baki, a hankali shi ma ya shiga mayar mata da martani. Can dai abu ya wuce gona da iri Zainab ta bude idanu, ta ga a zahiri Usman din ne ba wai mafarki ta ke ba, ta fara kokarin ture shi Usman na mai girgiza mata kai ya ce
"Kar ki hana mu abin da Allah ya halatta mana Abu, ni halak din ki ne ba a mafarki ba kadai, har a zahiri, ki bari na ba ki hakkin ki.."
Ta bude baki ta niyar magana yayi saurin katse ta ta hanyar rufe bakin ta da nashi. Ganin Zainab ta saki jiki har da ba da na ta gudunmawar na ja mu su assabari na yi gaba abu na, dan da alama yau soyayya za a sha.
Da sanyin asuba Usman ya sa Iyalle dora ruwan zafi. Cikin al'ajabin rashin kunyar da su ke gani kala kala Kado ta sanya Usman ya zama mara kunyar kamar ba bafulatanin usul ba ta dafa masa ruwan zafi, ita ta kaiwa Zainab har saban bandakin kara da Usman ya sa aka yi mata.
Tunda ta bude ido abubuwan da su ka faru tsakanin ta da Usman ya fara dawo mata cikin ran ta, ta tsani kan ta, duk yanda zuciyar ta ta kauracewa gangan jikin ta, sai da gangan jikin ta ya fi karfin zuciyar ta har ta kai ga sakarwa Usman jikin ta dan abin kunya. Allah ya so ta dama ba ya dawowa daga masallaci har sai gari ya waye sosai, kuma ko ya dawo din ma ba ya shiga bukkar ta, dan haka ta na idar da sallah ta yi kokarin komawa bacci, amma fargabar halin da tsinci kan ta ciki ya sa ta kasa komawa bacci.
Gari ya waye tangararan Zainab ba ta ko rintsa ba, ta na shirin tashi ta fara shiri kafin yan karatu su fara zuwa kamar daga sama ta juyo muryar Usman a tsakar gida ya na amsa gaisuwa, kafin ta ankara sai gashi ya shigo bukkar. Gaban ta yayi mummunar faduwa yayinda bugun zuciyar ta ya karu sa'ad da su ka hada idanu, ta yi saurin kawar da kanta, yin hakan ne ya sanya Usman tunanin kunyar sa ta ke ji, kenan Zainab ta na san sa tunda har ta kai ba iya hada idanu da shi. Ciki da jin dadi ya janyo ta jikin sa, hannun sa hagu sa zagaye da kugun ta ya furta
"Ina kwana Gimbiya Abu? Kunya ta ake ji haka?"
Cikin kokarin boye tasirin da ya ke da shi akan ta, ta furta
"Dallah Malam ka sake ni! Me zai sa na ji kunyar ka!"
Dariya Usman ya sa dan kuwa yau Abu ta na masa tsiwa amma ta kasa daga idanu ta kalle shi, hannu ya sa ya dago habar ta yanda zai iya sanya idanun sa cikin na ta, kamar mai rada ya ce
"Ki kalle ni toh, ki kalli idanu na ki min magana Abu...."
Maimakon ta kalle shi, ta tsinci kan ta tana mai lumshe idanun ta, hakan ya bawa Usman bin kyakkywar fuskar ta da kallo, yayinda ya tsaya daidai lips din ta. Murya kasa kasa ya furta
"A daren jiya kin koyar da ni wani abu da ban taba tunanin zan yiwa wata ba Abu, ina alfahari kan ki na koya, ina alfahari ke na fara yiwa...."
Ya na gama fadin haka ya fara kissing din ta, yanda ya ke saban shiga kuma bagidaje be kasa ruda Zainab ba, dan kuwa ta sha kissing samarin ta wayayyu, Amma babu wanda ya tafi da ita har ta kai ga mance in da ta ke face Usman.
Saukar assabari da alamar mutum ne ya daga yayi saurin saki ne ya dawo da su hayyacin su, yayinda Zainab ta yi saurin matsawa daga jikin sa. Usman kuwa juyawa yayi ya fice da sauri kamar yana tsoran abin d zaman sa dakin zai iya haifarwa.
Hannayen ta biyu rufe da fuskar ta ta zauna bakin gado ta na fadin
"Innalillahi wainnailaihi rajiun! Me ke damu na ni Zainab! What I'm doing to myself! This is not what I've been planning!"
Sallamar da ta ji an yi ya sanya ta daga kai ta kalli wacce ta shigo dauke da kwaryar nono. Yanda ta yi sin da kai ta gaishe da Zainab ba tare da ta bari sun hada ido ba cikin ta ya bata itace ta shigo dazu ta gan ta tare da Usman. Bayan ta aje kwaryar ta na shirin juyawa Zainab ta ce
"Rahila ki shedawa mijin ki Tanko na shirya! Na shirya damka masa Usman da Rugar nan mukar zai fitar da ni daga wannan kangin rayuwar!"
Cike da mamaki Rahila ta juyo ta na kallan ta ta na mai fadin
"Da gaske ki ke? Dama ba ki hakura ba? Yanda ki ka saki jiki da jama'ar Rugar nan har ki na koyarwa, na ji labarin Usman ya kauda budurcin ki...."
Zainab ta dago a razane ta na duban Rahila, wacce ganin haka ta girgiza kai cikin jaddawa ta ce
"Kwarai kuwa nan ya zo ya na fadawa kowa cikin fariya. Kuma yanda Raqeeba ta dawo jiki na rawa bayan ta ga Shehu ya na....."
Nauyin maganar ya sa Rahila karasawa yayinda ta ke tuno fuskar Raqeeba sanda ta nufo ta jiki na rawa idanu na fito da kwalla ta ke fadin
"Rahila Kado ta maishe da Shehu dan iska! Wallahi ganin su na yi bakin shi cikin na ta kamar za su cinye juna...."
"Duka shiri na Rahila!"
Maganar Zainab ne ya dawo da Rahila daga kogin tunanin da ta ke shirin fadawa. Zainab ba ta gushe ba ta kara da
"Duka na yi ne domin Usman ya saki jiki da ni, Amma zancen budurci kwata yayi! Fyade ya min kuma ba zan taba yafe mi shi ba shi ya sa na yanke hukunci bullo masa ta wannan sigar, Rahila ki taimaka ki fadawa Tanko ni Zainab zan bashi gudunmawa dari bisa bisa dari domin kawo karshen wannan azzalumin!"
Dan farin ciki jikin Rahila har rawa ya ke yayinda ta yiwa Zainab sallama ta fita, dan kuwa Allah Allah ta ke ta kaiwa Tanko sakon Zainab, ashe dai yau Tanko zai yi alfahari da ita, haka kuma takusa zama matar Shehu, mijin ta Tanko zai haye kujerar Usman.
Zainab kuwa tun fitar Rahila ba ta motsa ba, babban fargaban ta shi ne yanda Usman ya fara tasiri akan ta, dan bayan fitar shi ta gane ba wai kawai gangan jikin ta kadai Usaman ya mallaka ba, ya na neman ya mallaki zuciyar ta wanda hakan ta ke gani ba za ta iya bari ya faru ba, nan kuwa ba ta san bakin alkalami ya riga ya bushe, tsanar da ta ke ikirarin ta yiwa Usman ne ya sa ta kasa fahimtar hakan.
AUREN SHEHU 2
11
Rahila ba ta iya jiran dare yayi ba ta yi amfani da damar annushuwar da Usman ya ke ciki ta tambaye shi ko ya na da labarin in da Tanko ya ke ba tare da ta nuna dama ta san in da ya ke ba bare ma a gano ta saba satar hanya.
Tausayin Rahila ne ya kama Usman musammam yanzu da ya san darajar soyayya, Dan haka ya ce da Muhammad Bello ya raka Rahila ta ga mijin ta, idan ma ta na so ta koma wajen shi ne gaba daya ta na iya komawa babu laifi in ya so duk sanda ta ke da bukatar shigowa Rugar Shehu neman abinci ko wata bukatar mai muhummanci kofa a bude ta ke gare ta. Ta na murna ta yi bankwana da jama'ar rugar, in da ta yiwa Zainab alkawari cewar tafiyar ta ba ya na nufin lalacewar maganar su bane, shi ne ma dalilin da ya sa za ta wajan Tanko, duk yanda su ka yi da Tanko za ta dawo ta fada mata, haka kuma za ta na kawo mata ziyara a kan kari.
Cike da farin ciki ta riski mijin ta Tanko wanda sam be nuna farin cikin sa na ganin Rahila dauke da kaya niki niki ba, a tunanin sa Usman ya karota ne, sai da ta masa bayani tare da albishir da ta zo masa da shi sannan ya dan saki ran sa.
Bayan Bello ya masa sallama ya juya ne Tanko ya kada baki ya ce
"Ban so dawowar ki waje na ba, kamata yayi ki zauna can in da za ki fi ganin duk abin da ya ke faruwa, yanzu da ki ka kwaso kafa ki ka dawo uwar me za ki min a nan?"
Cikin sosuwar rai Rahila ta furta
"Kai kuwa Tanko ai zato na farin ciki za ka yi da zuwa na, na ga kowani namiji burin shi ya kasance tare da iyali saboda jiki da jini...."
"Toh yar jaraba! Jaraba ce dai ta dawo da ke! Ke jikin ki ma duk ya sake amma ba za ki hakura ba?"
Jiki sanyeye Rahila ta furta
"Haba kai kuwa, ai sai ana son ka ake mararin ka.."
"Toh uwar jaraba wuce mu je na mi ki abin da ki ke so, Amma dai zaman ki a nan ba zai yiyu ba! Dole ki koma Rugar Shehu!"
Rahila ba ta yi zuciya ba ta bi bayan Tanko, sai da ya ba ta hakkin ta sannan ya shiga zayyana mata yanda za a yi su cafke daga Usman har Zainab, in da ya ce ta shedawa Zainab yanda ta yi yayi daidai, ta kara dagewa wajan samin yardar Usman, hakan ne kadai zai sa su iya cin nasara. Su ka yi sallama Tanko na farin cikin burin su ya kusa cika, dadin dadawa kuma ya kusa samun Zainab, wacce tun da ya gan ta be da mafarki sai na ta, duniyar nan kab be da buri da ya wuce samin Zainab ko da kuwa na wuni daya ne.
Babu wanda be yi mamakin dawowar Rahila ba, cike da bakin cikin Tanko ya hana ta zama da shi, ta mu su karyar ga mata yan uwan ta me zai sa ta je can gefe ta ware kan ta, zaman cikin Rugar Shehu shi ya fi mata alkhairi. Sai da ta faki idanun matan Rugar sannan ta iske Zainab a daki, ta kwashe yanda ta yi da Tanko na game da Usman ta sheda ma ta, tare da sakon Tanko gare ta, kana ta kara da
"Kin ga kenan yanda ki ka yi ba karamin dabara ba ne, yanzu ki dada jan shi jiki, ki sa ya yarda da ke sosai ya saki jiki da ke, kya iya nuna masa ma kin kamu da son shi....."
"Mtswww Allah ya sauwake na kamu da san wannan bagidaje!"
Zainab ta katse ta a fusace. Jin haka Rahila ta dada godewa Allah, kenan hasashen ta ba daidai ba ne, Zainab dai ba ta fadama san Usman ba, gudun kar daga baya ta ba su matsala.
****
Can birnin Kano kuwa anyi cigiya da shelar neman Zainab, haka kuma an bi sahunta har Mambila amma an kasa gano takamamman in da ta ke, musammam yanda Jama'ar garin su ka yi kyameme su ka nuna ba su taba ganin Usman ba bare Zainab, hatta dajin Rugar Shehu sun shiga, amma gajen hakuri ya sa su ka juyo saboda yanda dajin ke da ban so tsoro, gani su ke bil'adama ba zai iya rayuwa ciki ba.
Kudin da Ammy ta kashe na sadaka da sauka ba adadi, tun tana sa rai ta na yarda da maganar yaran General da Anty Sauda, har ta fara karaya, ta yanke hukunci ziyartar kasa mai girma dakin Allah ta yi addua, idan har. Zainab na raye Allah ya bayyana ta, idan kuma ta mutu Allah ya nuna mata kabarin ta ko ta sami kwanciyar hankali.
Da wannan niyya, da kuma burin ganin Halitta Ammy da Falmat su ka tashi zuwa kasa mai tsarki.
***
Cikin kankanin lokaci jama'ar Rugar Shehu su ka kamu da kaunar Kado kamar yanda su ke kiran zainab, daga manyan su har zuwa yara. Ya kasance ko magana ta yi ya zaunu ba a mata musu, haka ma ta shige cikin zuciyar Usman ta zauna daram, Dan kuwa shawarar Rahila ta dauka, jan shi ta ke a jiki ta na masa soyayya irin ta yan birni musammam Zainab ta gama gogewa a wannan fanni.
Wani sabon al'amari shi ne yanda Usman ya tashi tsaye kan Muhammad Bello, duk wata hidima da ilimin tafiya da Rugar Shehu kokari ya ke ya koyawa Bello, haka kuma ya sanya ranar auren Bello da Raqeeba wata daya kacal, Allah ya so dama Bello ya jima ya na muradin Raqeeba duk da ya fahimci ba shi ne gaban ta ba, shi din ne ya ke san maso wani sai kuma faduwa to zo daidai da zama.
In da Bello da jama'ar Rugar Shehu aka shiga shirye shiryen biki, Amarya Raqeeba a nata bangaran bakin ciki ne ya mamaye zuciyar ta, ta na ji ta na ana gani za a daura mata Bello bayan Usman ta ke so, Kuma mahaifiyar ta ta san da haka amma ta ce ko da wasa kar da ta sake wani mahaluki ya ji zancen nan in ba haka ba sai ta tsine mata.
Rahila ce ta fara gano halin da Raqeeba ta ke ciki ana gobe Bikin Sharon da aka shirya musammam dan auren Bello, in da sati daya ya rage auren na Bello. Rahila ta yi ta bugun cikin ta har yarinyar ta hakura ta sheda mata soyayyar da ta ke yiwa Usman, da kuma maganar mahaifiyar ta na kar ta bari kowa ya sani.
Hakan yayiwa Rahila dadi, dan kuwa kwana biyu ko maganar Usman Zainab ba ta yi mata, ta na ganin hashashen ta dai zai kasance gaskiya, Zainab ta fara san Usman, dan haka ta yi amfani da damar ta shiryawa Raqeeba duk yanda za ta yi, sai da ta tabbatar Usman ba ya nan sannan ta tura ta dakin.
Zainab kwance bisa gadon kara, tunanin Ammy da su Falmat ta ke, ta na mamaki ace har ta yi wata hudu wani uwa duniya amma a kasa samin wanda zai biyo sahun ta? Wani zuciyar kuma ta raya mata kila an bi ba su same ta ba ne. Kamar daga sama ta juyo sallamar Raqeeba, Zainab ta tashi zaune tare da amsa sallamar, da fara'ar ta ta bata izinin shigowa, Raqeeba ta shigo kan ta a kasa ta zube gaban Zainab.
Cike da fara'a Zainab ta furta
"Ha'a Amarya ta shi zauna gado mana, kya zauna a kasa?"
Maimakon ta tashi sai ta fashe da kuka har da shassheka. Hankalin Zainab ya tashi, cikin sauri ta sauko kasa gurin Raqeeba yayinda ta shiga rarrashin ta tare da tambayar ba'asi. Da kyar ta iya lallaba Raqeeba ta yi shiru, cikin lallami da lumana Zainab ta ce da Raqeeba
"Me ya faru? Me ya sa ki kuka haka? Auren ne ba ki so?"
Raqeeba ta gyada mata kai alamar
"Eh"
"Auren dole za su mi ki?"
Ta gyada mata kai. Shiru ne ya biyo baya kafin daga bisani ta furta
"Kin fadawa Usman ba kya so?"
Ta girgiza mata kai alamar
"Ah ah"
"Me ya sa ba ki fada masa ba? Kin fadawa Hansai?"
Nan ma sai ta sa mata kuka, da kyar ta samu ta yi shiru har ta sheda mata abin da maifiyar ta ta ke so. Cikin jimami Zainab ta furta
"Shi wanda ki ka ce ki na so, wanene shi?"
Budar bakin Raqeeba sai cewa ta yi
"Shehu...."
Dam! Maganar ya doki kunnan Zainab yayinda gaban ta ya yi mummunar faduwa, kishi ne ya taso ya tsaya mata kahon zuci, ba ta san sanda ta furta
"Shehu? Usman miji na ki ke so?"
Raqeeba ta gyada kai, ta lura sarai da halin da Zainab ta shiga kamar yanda Raheela ta ce mata zai faru, haka kuma ta ce kada ta sake ta nuna ta san abin da ta ke, dan haka Raheela ta yi burus ta kara da
"Idan babu shi ba zan iya rayuwa ba, ya san ina san shi ba tun yau ba, Amma ya ce na auri Bello, mun san ba kya san shi, kamar yanda mu ma ya sha fada mana ba ya kaunar ki......"
Kamar takobi haka maganar ta soki zuciyar Zainab, musammam da ta ji Raqeeba ta kara da
"Sadakar ki aka ba shi, tsoran hukuma da kuma yanda ya ke jin dadin kwanciya da ke ya sa be mayar da ke gida ba, Amma ya ce da zarar kin gundire shi ko kuwa ki ka haife cikin da ki ke dauke da shi zai......!"
"Shut up!"
Zainab ta dakawa Raqeeba tsawar da sai da jikin Raqeeba ya dau rawa tsabagen firgita. Ita kan ta Zainab din jikin ta rawa ya ke saboda bacin rai, ta na mai nuna mata hanya ta ce
"Tashi ki fita"
Maimakon Raqeeba ta fita, sai ta yi kamar yanda Rahila ta ce ta yi duk da ta tsora ta ainun, ta na mai ruqo kafar Zainab ta furta
"Dan Allah ki taimaka min kada ki bari Shehu ya san na mi ki wannan maganar, matukar ya san na fada mi ki ya na sawa a daure ni, koma a kar ni har lahira shiya sa ma mahaifiya ta ta haneni ga fadawa kowa, ki min rai ki taimake ni"
Ganin yanda ta marairaice sai tausayin ta da tausayin kan ta ya kamata, lalle Raqeeba abar tausayi ce tunda har ta fada soyayyar azzalumi kamar Usman. Cikin sanyin murya ta furta
"Na ji, ki sakar min kafa ki kuma fitar min daga daki, in dai Usman ne na kusa barin rayuwar shi har abada!"
Jin haka Raqeeba ta tashi da sauri ta fice gudun kar Zainab ta gane shara ta take.
Nan bakin gado Zainab ta zube, so ta ke ta yi kuka amma ta nemi hawayen ta rasa.
".....mun san ba kya san shi, kamar yanda mu ma ya sha fada mana ba ya kaunar ki......"
Maganganun Raqeeba da ke yawo cikin ran Zainab kenan. Ko da ta tuna
"Sadakar ki aka ba shi, tsoran hukuma da kuma yanda ya ke jin dadin kwanciya da ke ya sa be mayar da ke gida ba, Amma ya ce da zarar kin gundire ko kuwa ki ka haife cikin da ki ke dauke da shi zai......!"
Ta yi saurin shafa cikin ta, nan ta ke wani tunani ya bugi kan ta, tun da tazo Rugar Shehu ba ta taba yin al'ada ba, duk da dai nata mai wuyar sha'ani ne ba kowani wata ta ke yi ba, Wani lokacin kuma ta kan yi sau biyu a wata. Haka kuma tun da ta fara sakarwa Usman jikin ta kusan kullum sai ya kusance ta, Tuni ta fashe da kuka ta na fadin
"Allah ya isa! Allah ya isa ba zan taba yafe ma ka ba Usman duniya da lahira! Allah ya isa!"
Babban tashin hankalin ta shi ne gaba daya ta manta zuciya ba ta da kashi, kamar yanda ta ke kokarin sace zuciyar Usman, tuni na ta zuciyar ta yi rauni, ba ta iya yin cikakken minti goma ba tare da ta yi tunanin Usman ba, haka har Allah Allah ta ke dare yayi su kebe, dama ga ta Allah yayi ta mace mai yawan bukatar mijin ta.
Sai da ta yi mai isar ta, sannan ta share hawaye bayan ta gama yanke hukunci ta kwallawa Rahila Kira, wacce dama ta yi lamo ta na tsammanin kiran. Da saurin ta ta shigo, ganin yanda idanun Zainab ya kumbura su ka yi suntun ta fara tambayar ko lafiya. Murya shake Zainab ta furta
"Ki ce da mijin ki Tanko na shirya tsaf, ya gaggauta kawo mafita idan ba haka ba zan yi gaban kai na!"
Cike da munafunci Rahila ta shiga doka salati ta na tambayar Zainab shin ko menene ya faru. Zainab ta ce ita yar sako ce ta tafi ta kai sakon ta. Rahila ta amsa da toh ta fice jiki na rawa kamar wacce za ta yi tsuntsu dan sauri.
Nan cikin gonar Bello ta wuce Usman da Bello, yanda ba ta lura da su ba haka su ma ba su ga giftawar ta ba. Musammam Bello wanda maganar Usman ta sa kan shi yayi tsawa. Cikin jinjinawa ya ke maimaita
"Za ka bar min sarautar Rugar Shehu?"
Usman na mai murmushi ya gyada masa kai, in da Bello ke masa kallan zararre. Zaune su ke karkashin bishiya da ta mu su lema, dukkanin su sanye cikin fararen ruguna yar shara. Bello na kallan fuskar Usman wanda tun da ya gane yanda Zainab ta ke satar kallan sa duk sanda be daura rawani ba ya dena saka rawanin gaba daya sai dai hula, Bello ya furta
"Akan wani dalili zan gaje ka bayan kana raye?"
"Murabus na ke so na yi"
Usman ya ba shi amsa a takaice, ya kara da
"Shi ya sa na ke ta sa ka a hanya, ban dawo Rugar Shehu dan na zauna ba, na dawo ne sanadiyar kiran Iya, Iya kuma ta kwanta dama mun kuma baro kabarin ta can falgore, bakin cikin haka ya sanya ni dauko Abu daga birni, na kawo ta daji dan kuwa a nawa wautar hakan ne zai sa na rama babban asarar da ta ja min, da zalincin da ta ma ka, Amma na huce yanzu Bello, ba zan iya jure ganin Abu cikin wahala haka ba, ba ta saba da rayuwa irin ta mu ba...."
"Toh ka sake ta mana..."
Bello ya katse shi da iya gaskiyar sa. Murmusawa Usman yayi, kana ya ce
"Ai ko da da Allah be jarrabe ni da soyayyar Abu ba ba zan iya sakin ta ba saboda alkawari mai girma da na daukarwa mahaifin ta, bare yanzu da son ta ya bi jiki na jini da tsokana, ina san mata ta Muhamadu, ina san ta lillahi warasulihi, ba zan iya rayuwa babu Abu ba"
Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani Bello ya nisa ya ce
"Shin ita maidakin ta ka ka ji ta bakin ta? Idan ita kuma ba ta da wannan ra'ayin fa? Shi fa kado ba shi da tabbas..."
"Ko ban yarda da komai ba, na sheda Abu ta na kauna ta, Abu na ta na so na, daren yau zan sheda mata soyayyar da na ke mata, Zan nemi yafiyar ta akan dauko ta da na yi daga birni duk da dai ni banyi dana sanin hakan ba, Rugar Shehu shi ne tsatson soyayyar mu"
"Yanzu Shehu akan mace za ka bar sarauta? Ka bar shanu? Ka bar yan uwa ka tai birni?"
"In ka dauke yan uwa duka sauran abubuwan da ka lissafa na dade da barin su, sai dai wannan karan zan yi amfani da dama ta na gina gidan gona cikin birni, yanda za mu bunkasa tattalin arzikin Rugar Shehu a can birni, in Sha Allah ko ban iya yin yanda Shugaban kasa ke da hashashen kawo cigaba birni ba, zan kwantata, haka kuma zan sayar da wasu daga cikin shanu wanda su ke mallaki na domin ginawa Abu gida irin na yan birni"
Ya kare maganar ya na murmushi yayinda ya ke ayyana irin gidan da zai gina mata cikin ran sa. Jikin Bello sanyaye ya ke duban sa, ya sha ji ana cewa asiri ba ya kama Usman, Amma ko shakka babu wanda Zainab ta yiwa Usman bakara min asiri ba ne. Cewar Bello cikin ran sa.
Aure shehu 2
12.
Muhammad Bello be bari sun yi sallama da Usman ba sai da ya tabbatar ya ma sa alkawarin zai kara tunani akan lamaran.
Rahila kuwa ko da ta shedawa Tanko sakon Zainab, Tanko ya dara ya na mai jinjinawa matar shi akan makircin da ta iya kulkawa, haka kuma ya na mamakin rashin dabara irin na Zainab, Dan kuwa ko shi da ba ya cikin Rugar Shehu ya sheda da irin soyayyar da Shehu ya ke yiwa Zainab. Tanko ya ce dama shi ma a shirye ya ke, abu daya sa ya ke so Zainab za ta ma sa, shi ne ta tabbatar ta ja Usman bakin ruwan da ke makota da gidan gona lokacin da ake tsaka da bikin sharo, shi kuma ya mata alkawarin matukar ta masa wannan to zai mata hanyar da za ta koma gida a ranar.
Rahila ta ba ta yi kasa a gwiwa ba ta koma Rugar Shehu in da ta bar Tanko ya na shirin yanda goben za ta kasance ta hanyar aika sako ga yaran sa wanda dama suna nan cikin Taraba suna jira.
Jin sakon Tanko Zainab ta fara shirya kayan ta a boye. Sai da ta hade kayan ta tsaf cikin akwati sannan ta haye gadon karfe yayinda kirjin ta ke bugun uku uku, gaba daya hankalin ta ya kasa kwanciya. Sai bayan Ishai'i Usman ya nufi gida, bayan ya gama hidimar sa kaf, ya tsaya kogi yayi wankan sa na musammam dan kuwa so ya ke ya raya daren ranar suna soyayya da Zainab, sannan ya sheda mata burin sa na mayar da ita birni su karasa rayuwar su a can.
Ko da ya ga fitilar bukkar a kashe be damu da ya kunna ta ba, kai tsaye ya nufi gadon su ya na mai lalube har hannun sa ya sauka jikin Zainab wacce ta dan firgita ta na kokarin tashi yayi saurin janyo ta jikin sa tare da fadin
"Shhhh Abu....Ni ne"
Ya kara rungume ta sosai kamar mai kokarin mayar da ita cikin jikin sa, hakan ya sanya Zainab narkewa ba ta san sanda hawaye ya fara fita daga idanun ta ba, sai saukar su da Usman ya ji a kirjin sa, ya furta
"Subhabanallahi me ya faru? Ba ki da lafiya ne? Bari na dauko haske Abu"
Ya yi yunkurin tashi, amma Zainab ta kamkame shi ta hana shi tashi
"Menene Abu?"
"Babu komai"
Ta bashi amsa cikin rawar murya. Shiru ne ya biyu baya, inda Usman ya ke tuntuni, ya san ko Zainab ba ta fada ma sa ba tunanin gida da su Ammy ne ya sanya ta kuka, dan haka ya furta
"Kin ga Abu, na san dalilin kukan ki, kada ki damu dama akwai maganar da na ke so mu yi......"
"Ba yanzu ba dan Allah, please..."
Zainab ta katse shi, babu abin da ta ke so a lokacin fyace tarayyar ta da Usman, dan kowa komai da ta ke masa na bankwana ne. Yanda ta ke dada kamkame shi ne ya sanya Usman ya fahimci abin da ta ke bukata, tuni ya aje maganar da ya ke so su yi, shi ma ya bi yarema a sha kida. Yanda Zainab ta saki jiki ta nuna masa salo iri iri ne ya kara jaddawa Usman irin san da ta ke masa, nan kuwa be san duka na bankwana ba ne.
Sanda su ka sami nutsuwa Usman ya kara kokarin zayyanawa Zainab abin da ke ran sa, Amma be an kara ba sai ji yayi ta kara nauyi a jikin sa, Ashe bacci yayi awan gaba da ita. Dan haka a dole ya hakura, ya na mai sumbatar da a goshi ya furta
"Ina kaunar ki Abu, so na tsakani da Allah, da fatan za ki yafe min ki karbi soyayya ta"
******
Washagari sassafe aka tashi da girkin bikin sharo, masu daka fura na yi, masu tuka tuwo ma haka, haka ma masu tatsa da dafa nono ba a bar su baya ba. Zainab kuwa tun da garin Allah ya waye ba ta saka Usman a idon ta ba, haka shi ma Usman wanda tun fitar shi sallar asuba be sami damar dawowa ba bare ya samu yayi magana da Zainab. Cikin dabara ta ja Rahila gefe, ta fada mata cewa da zarar an fara sharo ta saci jiki ta dawo gida ta tafi mata da dan akwatin ta can inda su ka yi za su hadu da Tanko, ta duba girman Allah kada ta bari a ganna ta, Rahila ta amsa da an gama.
Sai wajan sha biyu sai gashi ya shigo gidan, ya tadda Zainab sai kai kawo ta ke cikin bukka domin kuwa lokacin da su ka yi da Tanko sai gabatowa ya ke, dan kuwa ana idar da sallar azahar za a fara bikin.
Jawo ta yayi bangaran jikin sa na dama, tare da sumbatar ta a goshi, sam be lura da yanda Zainab ta kasa daga ido ta kalle shi ba, ya na mai damka mata ledar da ya ke dauke da shi ya ce
"Ga kayan fitar Sharon ki, na so ace kin taba gani da ba zan yarda ki je wajan ba dan kar a kalle min ke, toh amma dan Allah idan kin je kada ki jima...."
Jin haka Zainab ta yi saurin fadin
"Toh idan na bar wajan ina zani? Sai na dawo gida na zauna ni kadai kamar mayya bayan an ce kowa can zai tafi..."
Usman na dariyar tsiwa irin na Zainab ya furta
"Ba fa kowa ba, ko kowa zai tafi ai ban da Iyalle.."
Zainab na mai buga kafa cikin shagwaba ta furta
"Ni dai ban yarda ba, Ni dai sai dai za ka biyo ni mu je yawo, dama ka ce akwai maganar da za mu yi, ka ga sai mu cikin annushuwa daga ni sai kai"
Kalmar daga " ni sai kai ne" ya sa Usman cin dadi har cikin ran sa, Wai yau shi ne Zainab ke san kebewa da shi, da ga ita sai shi yanda babu wanda zai dame su.
"Kamar dai yanda ya kasance a gidan gona?"
Ya tambaya ya na mai kokarin kallan idanun Zainab. Yanda kwayar idanun sa ke rawa ya sanya tsigad jikin Zainab tashi, ta yi saurin kawar da kai gefe, ta furta
"Ko ma ka kai ni wajan ruwan nan, ban taba ganin shi ba sai dai na ji labari"
"An gama gimbiya Abu, in Sha Allah za mu je, sai kuma tafiyar ta mu za mu yi ta da dabara, idan an fara da minti talatin haka sai na miki alama ni zan fara yin gaba, sai ki bi sahu na, ai dai za ki gane hanya ko? Ba nisa zan mi ki sosai ba"
Zainab ta gyada masa kai alamar "eh". Sallamar da aka yi ana neman Usman ne ya sa ta sake ta ya fita. Nan ya barta jiki na rawa, in da ta sami gefan gado ta zauna. Sai da ta yi kusan minti goma zaune sannan ta iya bude ledar da ya ba ta. Atamfa ce koriya da ja, dinkin riga da zani, rigar an dinka ta doguwa sosai dan za ta kaiwa Zainab har gwiwa, ga fadi ko ado babu jiki, sai kuma mayafi shi kuma shudi da ruwan dorawa. da ka gani ka ga kalar fulanin kauye, sai kuma sifas shi ma din ruwan dorawa ne. Ko da ta gama dagawa sai ta ja tsaki, a zahiri ta ce
"Yau dai Allah zai raba ni da wannan gidadanci! Dan ji wani jahilin kaya da ya kawo min! Macuci azzalumi!"
Da kamar ba za ta saka kayan ba, Amma da ta tuna da hudubar Rahila haka ta rufe idanu ta sanya kaya, tun da ta zo duniya ba ta taba muni irin na ranar ba, ita kan ta sai da ta tsargu da kan ta.
Amma ko da lokacin tafiya yayi ta fito waje, hankalin kowa kan ta ya koma, in da ake ta yaba kyan ta da koma kyan kayan jikin ta. Ita kan ta Rahila kasa shiru ta yi ta furta
"Kai wannan ko ke ce amaryar sai haka! Gaskiya kin fito ziza da ke, ko da shi ke ai matar Shehu guda!"
Wani malulun bakin ciki ne ya tsaya makoshin Zainab, Amma daga baya da ta lura da irin shigar da sauran jama'ar su ka yi, daga matan har mazan wani irin farin takalmin roba su ka sanya sau ciki, inda yawanci matan atamfa ne jikin su irin wannan ma su kalar rambatsau din nan, yan matan cikin su sun ci gilashin roba kala kala, haka ma samarin wajan wanda ba za su ba da gudunmawa wajan Shadin ba dauke da rediyo a kafada, sai bada iska su ke a dole gayu su ka sha.
Tun Zainab na daurewa har ta fara dariya musammam da su ka isa filin Sharon, ta ga shigar da Bello yayi, kan sa har da gashi da wata irin hula na angwanci. Amarya Raqeeba kuwa can ta hango cikin kawayen ta, tabbas babu wani bambamcin shigar ta da na Zainab idan aka dauke gilashin robar da ta sanya da kuma farin takalmin robar da ke kafar ta. Kallo daya Zainab ta mata ta dauke kai dan kuwa ji ta ke ta yi mugun tsanar Raqeeba.
Daira aka yi yayinda aka bar fili a tsakiya, samari masu jini a jika su ka tsaya daga su sai gajeran wando hannun su dauke da sandar gora su na mai yiwa kan su kirara, ganin haka Bello ma ya kwabe rigar jikin sa, ya ja gora shi ma ya fada fili, tuni waje ya dau sowa da tafi. Hakan yayi daidai da isowar Usman cikin shigar sa na fararin yadi yar shara, yau din ma hula ne kan sa ba rawani ba, kallo daya za ka masa ka tabbatar da jin dadin da ke tattare da shi.
Dage gefe ya tsaya yanda zai na hango Zainab. Ita ma din kallan sa ta ke ta ya kiyas ta lokacin da ya kamata su bar wajan. Usman be jima da isowa ba aka fara bikin sharo, wani matashin saurayi ya na mai kuwa ya furta
"In dai ka kai namiji wanda zai daga hannun sa haka a bashi itace! In Allah ya so ya yarda zai yi farin jinin yan mata a dandali kayyasa!"
Ya na gama fadin haka daya daga cikin samarin ya daka wani katan sanda ya zuba masa a gadan baya, in da shi kuma ya cije cike da jarumta ya na mai taka rawa. Ganin haka Zainab ta ja tsaki cikin ran ta, ta na mai fadin 'jahili dai jahili ne!'
Haka su ka ta bugun junan su wani har jini na fita, tuni abin ya hau kan Zainab ta na tunanin yanda za ta ja Usman su yi gaba ta ga ya janye cikin sa da kan sa ya tafi, can gefe ta hangi Rahila ta dan mata alama da idanu sannan ta bi bayan Usman.
Karkashin wata bishiya ta tarar da shi ya na tsimayin ta, in da su ka nufi hanyar kogin Usman na jan ta da hira, Zainab na kokarin amsa ma sa duk da sam hankalin ta ba ya gare shi, lissafin ko Rahila ta dauko mata kayan ta? Za su tarar da Tanko wajan?
Tun da su ka isa bakin ruwan Zainab ke dan waige waige har Usman ya gane ya tambaye ta tana tsammanin wata ne?
Ta girgiza kai alamar ah ah ba tare da ta iya tanka masa ba. Daga bakin ruwan su ka zauna. Yanayin yanda ruwan ke zuba daga dutse ya na mai gangarowa kasa, da kuwa kukan tsuntsaye da ke tashi wajan ba karamin karawa wajan annushuwa yayi ba. Usman na mai janyo Zainab kusa da shi ta hanyar sanya hannun sa ta cikin ta ya zagayo ta kugun ta ya furta
"Abu mata ta ta kai na, kin yi kyau kwarai"
Zainab ta murmusa kawai yayinda bugun zuciyar ta ke karuwa musammam da ta ji Usman ya kara da
"Ki yafe min Abu, na yi kuskure, idona ya rufe akan ramuwar gayya, ba komai ya sa na dauko ki daga birni na kawo ki nan kauye ba fyace sanadiyar rashin ganawa da mahaifiya ta da ki ka yi har ta rasu, ta hanyar kame Muhammad Bello da ki ka sa aka yi . ...."
"Usman......"
Zainab ta furta cikin rawan murya. Usman na mai daura yatsa bisa leban ta ya furta
"Shhhhhhh, ban gama ba ai. Akan wannan dokin fushin na rabo ki da komai na kawo ki dajin nan, ki yafe min Abu, Allah ya jarabce ni da soyayyar ki, Kuma ina da yakinin ki na so na...."
"Dan Allah Usman ka dena fadin haka"
Cewar Zainab ta na mai zare hannun Usman daga jikin ta yayinda ta mi ke tsaye, shi ma din tashi yayi yayi saurin shan gaban ta ya na fadin
"Ki yi hakuri ki saurare ni Zainab, na san na yi kuskure, Kuma na san ni ba sa'an auran ki ba ne, Amma tunda kiga ga haka ya faru da mu toh kaddarar mu kenan, Zainab na dade ina istigifari akan abun da na mi ki, haka kuma na yi nadama, Kuma shirye na ke na gyara komai, za mu koma birni, in akwai makarantar da zan shiga na dan sami wayewar kai Zainab zan shiga saboda ke, duk abin da ki ke so Zainab zan yi....dan Allah Kar da ki juya min baya...."
"Toh tantabarar sarkin soyayya!"
Muryar Tanko da dariyar yaran sa ne ya daki kunnan Usman da Zainab. Sam ba su lura da zuwan su ba, su goma ne idan aka hada da Rahila wacce ke dauke da akwatin Zainab. Daga Tanko har yaran sa dauke su ke da bindiga irin dogwayen nan da ake kira AK 47, kasancewar sun rufe fuskokin su be hana Usman gane Tanko ba. Can kasan makogaranta Zainab ta furta
"Ya Allahu me na yi ni Zainab!"
"Me ya kawo ka cikin Ruga ta? Ban ma ka tazara da Rugar Shehu ba?"
Cewar Usman a fusace ya na mai tsayawa gaban Zainab yanda zai kare ta daga ganin Tanko da yaran sa domin kuwa ya lura da yanda jikin Zainab ya dau kakkaura. Dariyar mugunta Tanko ya saki ya na mai jefa kai baya, sai da yayi mai isar ta ya ce
"Matar Shehu ga mu mun iso kamar yanda ki ka umarce mu, ga kuma jakar ki nan Rahila ta dauko mi ki, kamar yanda ki ka sa ta"
Kamar wanda aka kwarawa ruwan sanyi haka Usman ya yi mutuwar tsaye na wani dan sakanni, sai a sannan ya lura da Rahila, haka kuma ya kai kallan sa ga akwatin da Rahila ke dauke da shi, ko shakka babu akwaitin Zainab din ne. kwakwalwar sa ta tsaya har sai da ya din yi jim kafin ya juya a hankali ya dubi Zainab wacce tuni idanun ta ya cika da hawaye, ta kasa magana sai kai ta ke girgiza masa.
"Fito mana! Ko ba ki gama ban kwana da Shehun ba ne, Malam dan matsa mata hanya mana!"
Ga mamakin kowa sai kuwa Usman ya matsa, amma Zainab ta kasa motsawa bare ta karasa wajan su Tanko, kallan Usman ta ke yayinda idanun shi ke aika mata sako kala kala. Ganin haka Tanko ya furta
"Usman ka sani cewa yau zan raba ka da abubuwa uku kamar yanda ka so ka raba mahaifina da ..... Na farko zan raba ka da sarautar Rugar Shehu kamar yanda ka yiwa mahaifina, haka kuma na raba ka da farin cikin ka ta hanyar raba ka da matar ka, kamar yanda ka raba mahaifina da farin cikin sa, na uku kuma zan kashe ka, duk da dai shi mahaifin nawa ya na nan raye"
Jin haka hankalin Zainab ya tashi, murya na rawa ta ce
"Ba mu yi haka da kai ba! Ke Rahila ba mu yi haka da ke ba! Ba ku ce za ku kashe shi ba! Ba za ku kashe shi ba! Gida kuka ce za ku mayar da ni ba ki ce za ku kashe shi ba!"
Usman kuwa cewa yayi
"Zainab me ya sa? Duk zaman nan da mu ka yi da ke, duk kwanciyar hankalin da mu ka samu.... Zainab... Zainab me ya sa...? Dama kin yi ne dan ki cutar da ni?"
"Ta yi ne domin haka na ce ta yi! Kai a tunanin ka yarinya kamar wannan za ta taba san gidahumi irin ka? Ai ka godewa Allah ma ka sami raban ka!"
Cewar Tanko, be gushe ba ya mayar da kallan sa ga Zainab ya na mata irin kallan nan na kurulli ya furta
"Ke kuma zan mayar da ke gida amma sai na karfi kudi makudai daga wajen iyayen ki sannan na more jikin ki san rai na....."
Be san sanda Usman ya matsa gaban sa ba sai saukar mari ya ji kawai, ya ja da baya ya na mai dura zagi. In da yaran sa su ka yo kan Usman a fusace su na Shirin bugun sa, Tanko na mai huci ya furta
"Ah ah kada ma ku soma, Ni nan ni zan jibgi dan bantan uba! Ku daure min shi!"
Nan su ka fara yunkurin daure Usman in da shi kuma ya ke kokarin bubbuge su musammam da ya ga Tanko ya kai hannun sa jikin Zainab wacce ke kuka da ihu ya ja ta gefe, fadi ta ke
"Dan Allah ku rabu da shi, duk abin da ku ke so za a baku, kada ku kashe shi"
Sai da su ka sa igiya suka daure Usman tun daga kafadar sa har zuwa kafafun sa, sai gashi kwance tamkar gawa. Tanko na mai duban Zainab ya furta
"Abu uku na ke so, kuma duka sai na dauka, sarautar Rugar Shehu! Jikin ki! Sai kuma raba mijin ki da ran san sa!"
Ba Zainab ba, ita kan ta Rahila sai da gaban ta ya fadi jin har da jikin Zainab cikin lissafi. Zainab kuwa yawu da kaki ta tofa fuskar Tanko, tare da fadin
"Sai dai gawa ta kaskantacce mara mutunci! Za ka sake shi ko sai na bata ma ka rai!"
Tanko ya tunzura saboda sam ba ya iya jure tsiwa, bare kuma ga yawu Zainab ta tofa masa. A fusace ya dauke ta da marin da sai da Usman ya motsa ya na kokarin kuncewa, Zainab kuwa sai ta ga wuta a idanun ta ba, ba ta gama warewa daga zafin marin ba Tanko ya soma jibgar Usman da bakin bindigar sa har ya kai ga fasa ma sa kai. Kuka sosai Zainab ta ke yayinda ta ke kokarin shigar masa, Tanko ya hankada ta gefe, ya durkusa gaban shi ya furta
"Ka san dalilin da ya sa na ce a daure min kai haka dan uwa na? Saboda ba zan kashe ka da bindiga ba gudun kar yan sharo su ji karar ta, haka kuma ba zan kashe ka da wuka ba, mutuwar za ta ma ka sauki da yawa, yanda ka ke haka haka zan jefa ka cikin kogi, ka sha ruwa ka koshi har ka sheka barzawu, ni kuwa ina can ina morewa da matar ka, sai na tabbatar dukkanin tudun jikin ta ya saki sannan na mayar da ita ga iyayan ta, Rugar Shehu kuwa ka tabbatar ta zama tawa yanda na yi ma ka, haka zan wa Bello! Bissalam"
Ya tashi tsaye yayinda ya bawa yaran sa Umarnin su dau Usman su jefa shi ruwa. Akan idan ta su ka dau Usman gadan gadan, idanun sa wanda su ke rabi a rufe a kan ta, ta fara ihu kamar wacce ke shirin zarewa fadi ta ke
"Dan Allah ku yi hakuri kar ku kashe shi! Dan Allah Rahila ki sa baki kar su saka Usman cikin ruwan nan!"
Karar saukar Usman cikin ruwa da yanda ruwan ya tashi daboda yanda su ka jefa shi da karfi ne ya sanya Zainab saka ihu mai tsananin kara kafin ta zube kasa sumammiya.
Auren shehu 2.
Tanko na dariyar mugunta ya dauki Zainab ya ɗaura a kafada, ko kallon in da Rahila ta ke be yi ba bare ya lura da yanayin da ta shiga na sanadiyar zantukan da ya ke fada game da Zainab. Da sauri ta sha gaban sa, cikin bambami ta furta
"Me ka ke nufi Tanko? Ina fatan kalaman da ka ke akan tarewa da wannan kaɗon ba gaskiya ba ne, In kuwa da gaske ka ke wallahi ba ka isa ba! Ba ka isa ka tara da wata mace wacce ta ke ba halas din ka ba gaban idona na"
"In kuma na yi fa? Me za ka yi? Ku ji mu da shashasha! Jiki duk ya bushe ya jeme ki na tunanin zan ga jiki kamar na kado na bari? Sakarya kawai!"
Cike da bacin rai Tanko ya maida mata da martani yana mai cigaba da tafiya, ganin da gaske tafiya yayi da Zainab nan take wani turirin kishi ya yi gaba da ita, gaba ɗaya ta daina ganin gabanta, juyawa ta yi a guje, tana tafe kamar kububuwa, daga Tanko har yaran sa ba su lura da juyawar Rahila ba, halin su ya raja'a kan nasaban da su ka ci kan Shehu, ga kuma Kado an samu, idan Tanko be yi san zuciya ba kila su ma su sami raban su daga jikin ta.
Inda ake sharo Rahila ta koma a guje, ihu take ba ta ko iya tantance mai take fadi. Ganin yanda ta iso filin da ake sharo ɗin ne ya dawo da hankalin mutane gareta
"Me ya faru? Me aka yi?"
ƴan matasan da ke wajen su fadi a tare suna masu ɗaga sanduna da addunansu. Haka Kuma Muhammad Bello ya shiga raba idanu, nan ya ankare da rashin Usman da Zainab a filin.
"Tannn... ko! Kaaaaɗo!! Sheehu ruwa!!!"
Rahila ta ce muryarta na haɗewa. Nan wajen ta faɗi tana mai kuka cike da ƙunan zuciya, tana jin labarin kishi amma Sam ba ta san haka ya ke da raɗaɗi ba, ta san ko kusa ba za ta haɗa kanta da abu ba, ta san matukar Tanko ya lashi zumar kaɗo tabbas ba za ta sake ji ta kansa ba. Kuka ta ke yi mata na rarrashinta duk a tunaninsu su zainab ta ke tausayi.
Su Bello kuwa tare da sauran ƴan matasa har ma da wasu daga cikin manyan da su ke da saurin ƙarfin su, Rarraba kansu su ka yi cikin daji Allah suna neman zainab, wainda su ka iya ruwa a cikin su kuwa su ka far ma ruwan da Rahila ta ce an jefa shehu.
Wajen zaman Tanko aka fara zuwa nan su ka iske babu kowa a wajen, har tawagar su Bello za su juya su ka hangi wata sabuwar bukka can nesa ta gabas daga inda su ke, ba su yi ƙasa a guiwa ba su ka isa, mazan da su ka gani a tsaitsaiye riƙe da bindigogi ya sanya su yin turus, sai da su ka ƙaraso ne su ka ga ashe ba ma bukka ɗaya bane sun kai biyar.
Ɗaga bindigogin su ka yi suna mai sai ta su, dakatawa su ka yi da fari, amma tunawa da su ka yi Shehu ya sa an haɗa maganin bindiga sun sha kwanaki ya sanya su dosar bukkar ba tare da ko wace shakka ba.
Karar fitar harshashi ne ya sanya Zainab farfadowa daga suman da ta yi. Ta mai raba idanu cikin kokarin gano in da ta ke, idanun ta ya sauka kan Tanko, wanda ke tsaye kan ta ya na shirin afka mata kenan ya ji alamun isowar su Bello.
Cike da bakin cikin an katse masa abin da ya ci buri ya ja tsaki, ya dau bindigar sa a fusace ya na duban Zainab ya ce
"Ki gyara sosai kafin na dawo! Yau sai na more abin da na ke mafarki! Na tabbatar mi ki sai kin kasa takawa! Bari na gama da wancan karamin kwaron!"
Ficewar sa da manganganun sa ne ya sanya Zainab dawowa cikin hayyacin ta.
"Usman! Na shiga uku ni Zainab sun kashe min Usman!"
Cewar Zainab yayinda ta tashi tsaye cikin neman mafita, kuka ta ke wiwi daya na bin daya. Gani take duk abin da Tanko zai mata ba zai kankare rabin zunubi da ta aikata ba na cin amanar shehu. Karar harsashe da ke ta shi be sa ta tsora ta ba, sai ma kokarin tusa kai waje da ta yi, a tunanin ta in ma mutuwan ne gwara harsashi ya kashe ta da ta mutu hannun Tanko.
Duk yanda Tanko da yaran sa su ka so cin galaba kan su Muhammad Bello kasancewar su na da bindiga hakan gagara yayi saboda maganin bindigar da ke aiki jikin su, dama ma su iya magana sun ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi, tuni su ka sami nasarar kwace bindigun yayin da su ka kwantar da su da dukar kawo wuka. Inda su Bello ke kururruwar daukar fansa, su Tanko ihun neman doki su ke, su na fadin
"Mun tuba ku yafe mu! Mun tuba!"
"Kar ku raga mu su! Kar ku tausaya mu su! Sun jefa min Usman a ruwa! Sun kashe min Usman!"
Cewar Zainab cike da tsana yayinda su Muhammad Bello su ka dada tsage dantse wajan jibgar su Tanko da gora, gaba daya su ka mu su jini da majina amma hakan be sa Zainab ta tausaya mu su ba, sai ma dada cewa ta ke a kara mu su. Ana cikin wannan halin ne daya daga cikin wanda su wanda su ka je kaiwa Usman ne ya cimma su ya na mai ihu
"An dauko Shehu! Muhammad Bello an dauko Shehu!"
Ya na fadin haka ya juya a guje. Zainab ce ta fara yin gaba cikin gudu gudu sauri sauri, yayin da Muhammad Bello ya ba da umarnin daure su Tanko a taho da su, shi ma ya bi bayan su Zainab.
Nan bakin ruwa su ka tadda an fito da Usman, ana kokarin fitar da ruwan da sha. Ganin Bello da Zainab tuni aka dara mu su hanya wasu da ga cikin jama'ar na fadin
"Allahu akbar ruwan Rugar Shehu ba ya ci Shehu ba! Shehu ikon Allah! Allahu akbar!"
A tsorace Zainab ke kallan Usman da ke kwance tamkar matacce yayinda Muhammad ya cigaba da matso cikin sa, sai da yayi hakan kusan sau uku sannan ruwa ya fito daga bakin Usman cikin karfi, hakan ya sa Usman tari ya na mai bude murfin idan sa cikin magagi, jama'a aka sa kabbara, haka kuma mu su ihu da sowa na yi. Cikin kankanin lokaci ya sake mayar da murfin idanun ya rufe. Cike da tashin hankali Zainab ke fadin
"Kar ku bari ya rufe idanun shi! Kar ku bari ya mutu ya bar ni! Na shiga uku na lalace!"
"Ba zai mutu ba, ki kwantar da hankalin ki"
Cewar Muhammad Bello yayin da ya cincibi Usman ya aza a kafada. Babu wanda be tausayawa Zainab ba ganin yanda ta ke cikin tashin hankali. Ta na biye da Muhammad Bello har su ka koma bukkar Shehu. Da kyar su Iyalle su ka ja ta gefe lokacin da mai magani ya ke duba Shehu. Allah ya so babu karaya, in aka dauke raunin da Tanko ya masa akai, sai kuma ciwon jiki sanadiyar dauri da dukan da aka masa.
Sai da ya tabbatar Usman ya farfado ya bashi magani sannan ya kara bari ya koma baccin azabar da ke daukar sa. Su Tanko kuwa cikin garkon Shanu Bello ya sa aka daure su, ba dan halin da Usman ke ciki ba da tuni ya gama da su.
Murna da farin cikin biki ya koma bakin ciki, Rugar Shehu ya koma tamkar ana makoki. Washagari da sassafe Rahila ta saci hanya ta gudu, babu wanda ya damu da tafiyar na ta saboda Zainab kadai ta san wainar da su ka toya.
Kwana uku Usman yayi sai dai a kwantar a tayar, duk wani abin da ya shafi karfi su Bello ke masa amma fa a kan idan Zainab, ta kasa ta tsare ita take jinyar sa dan kuwa gani ta ke idan har ta matsa Tanko zai iya shigowa ya karasawa mata shi. Haka shi ma Usman din tsakanin sa da Zainab sai ido. Kuka kuwa ta yi har ta gaji, tun su Iyalle su na ba ta baki, har su ka gaji su ka sa mata idanu.
Da yammaci Zainab zaune bakin bukka ta yi uban tagumi gaba daya duniyar ta mata zafi. Kamar daga sama ta ji muryar Usman ya na kwallawa Bello kira, fadi ya ke
"Muhamadu! Muhammadu! Muhammadu!"
A zabure Zainab ta tashi ta shige dakin. Ta tarar ya na yunkurin tashi tsaye ya hada zufa sosai. Zainab ta karasa gare shi da sauri da niyar taimaka ma sa. Yanda yayi saurin janye hannun shi sa'ad da ta kai hannun ta jikin sa, da kuma irin kallon da ya bi ta da shi ya sa Zainab ja da baya jiki sanyaye, yayinda Muhamadu Bello ya shigo cikin sassarfa. Ganin Usman na kokarin tsayawa ya karasa gare shi da sauri, ya taimaka masa ya tsaya ya na fadin
"Hankali Shehu, ya aka yi ki ka bari ya tashi Uwargida?"
"Ina Tanko? Ina Tanko na ce??"
Usman ya fada a fusace ya na mai raba idanu.
"Ya na can cikin shanu tare da yaran nan, dama jira mu ke ka sami sauki sai a san yanda za a yi da su"
Cewar Bello cikin shakkar yanayin bacin rai da ya lura Usman ke ciki.
"Ba na son ganin Tanko, wallahilazim ina iya kashe shi har lahira...."
Cewar Usman ya na mai danna kwayar idanun sa cikin na Zainab, wacce ta ke duban shi cikin yanayi mai wuyar fasaltuwa. Usman be gushe ba ya kara da
"Idan akwai abin da na koya cikin rayuwa ta da wannan baiwar Allah (ya nuna ta dan yatsa) shi ne rashin faidar ramuwar gayya, domin kuwa yakan jefa dan Adam ga halaka, ku kai Tanko da duk wanda ya rabe shi ga hukuma dama sun jima suna neman shi"
"Toh Shehu"
Cewar Bello. Usman be gushe ba ya kara da
"Sannan kuma ranar Juma'a na mako mai zuwa, ka shirya zan sake aika ka Mambila ka saka ta tashar da zai kai ta Taraba ina ga daga nan za ta iya kai kan ta gida...."
Ji ta yi tamkar an kwara mata ruwan kankara. Shi kan shi Bello dagowa yayi firgice ya na duban Zainab da Usman. Cikin in ina ta furta
"Wa...wa... ce... ce za a kai tasha?"
"Shehu ina ga zai fi....."
Hannun da Usman ya daga masa tare da fadin
"na sallame ka"
Ya sanya Bello kokarin ficewa da sauri, ga mamakin sa sai ji yayi Usman ya furta
"Ku yi kokarin kiyaye lafiya ta ta hanyar hana jama'a shigowa in da na ke, ina nufin idan ba kai ba ko Iyalle ban yarda wani ya shigo min ba"
Idanun Bello kan Zainab wacce idanun ta ke shekin kwalla, ya furta
"Toh Shehu"
Amma ya kasa cewa Zainab ta fita, dan haka sai yayi saurin juyawa ya fita. Usman ya koma yana kokarin zama, ganin yanda ya ke cikin ciwo sai da ta yi da gaske wajan dauke kan ta gudun kar ya kyamace ta kamar yanda yayi mintinan baya.
"Wacece za a kai Mambila?"
Maimakon ya bata amsa, sai yayi kwanciyar sa kamar be ma san ta na dakin ba. Ran ta yayi rauni, ta kara furta
"Kai waye! How dare you! Wa ya ba ka damar ka dauko ni ka mayar da ni sanda ka ga dama! Zaman Rugar nan yanzu na fara kai ka yi ka kadan! Ka ci moriyar gangan ko? Toh zama daram!"
Usman ya mata banza, ya na mai juya mata baya. Ganin haka ta yi saurin fita daga dakin. Su Iyalle na mata barka Shehu ya fara warwarewa ko tan ka su ba ta yi ba ta tsallake su da saurin ta ta shige dakin Iyalle. Nan ta fashe da kuka mai karfin gaske har da shesaheka, su Iyalle da su ka biyo bayan ta ne ma su rarrashi, fadi su ke
"Yo toh yar nan ai murna za ki yi ba kuka ba, tunda Allah ya sa an tsira da rai ga shi har ya farfado...."
Hansai kuwa fadi ta ke
"Ina ga kuka ai na murnar ne, ai mun tarba arziki kwarai kuwa"
Zainab kuwa ita kadai ta san radadin da ran ta ya ke yi, yau an wayi gari Usman da kan shi ya ce zai mayar da ita gida, maimakon ta yi farin ciki, kishiyar haka ta yi, dan Allah ya dasa mata son Usman, sai da Allah ya jarabce ta da kaunar sa shi ne ya ke ikirarin zai mayar da ita gida, kamar yanda ta ce babu in da za ta je, babu in da za ta je.
Su Iyalle ba su kara karaya ba sai da su ka dare yayi, Bello ya fito da akwaitin Zainab ya mayar da shi wata bukka daban wacce babu wanda ke kwana ciki, da kan shi ya gyara yayiwa Zainab shimfida. Ko da Iyalle ta tambaye shi dalili, ya ce umarnin Shehu ya ke bi. Jin haka su ma su ka fara shan jinin jikin su, lalle wannan lamari mai wuyar ganewa ne.
Sai da Zainab ta yi da gaske sannan ta iya runtsawa. Har cikin ran ta so ta ke ta sami Usman ta bashi hakuri, ta fada masa ta yi kuskure ta kuma bayyana masa sirrin ran ta, dan kuwa ba ta iya ji za ta iya rayuwa babu Usman ba, bayan ganin yanda ya kusa rasa ran sa a sanadiyar ta, lalle za ta iya rasa ran ta idan ya rabu da ita. Amma wani bangare na zuciyar ta ne ya hana ta tashi ta same shi. Haka tai ta juyi dab da asuba bacci ya sace ta. Sai tashi ta yi ta ga an tafi da su Tanko, haka kuma Usman ya ba da umarnin kada wanda ya shigo masa daki idan ba Iyalle ba, idan kuwa aike za a masa, za a iya aiko matar da Bello zai aura, wato Raaqeeba.
Ganin yanda Raqeeba ke kai kawo cikin dakin Usman fashewa ne kadai zuciyar Zainab be yi ba tsabagen kishi. Sai a sannan ta gane tsabagen kishi ya rufe mata idanu ne ta aikata abin da ta aikata. Tun tana iya jurewa har ta kasa ta je ta sami Iyalle ta ce da ita
"Iyalle ina ga zai fi in ki na da sako gun Shehu ki ba ni, ki dena aika Raqeeba ai tunda ni ce matar shi ko?"
Daga jin maganar Iyalle ta gane kishi ne na mata karara, dan haka sai ta murmusa cike da siyasa ta ce
"Wai da nauyin aiken na ki na ji, Amma ai an gama kai komai, zuwa gaba idan da aike na ba kira ki"
"Toh Iyalle, na gode"
Cewar Zainab amma har ga Allah ba haka ran ta ya so ba. Haka ta wuni ta ja jiran tsammanin kiran Iyalle, ba ta san an yiwa Iyalle gargadin kada ta sake ta bari Zainab ta kusance shi ba, dan haka ne ma Iyalle ta gwammace da ta aiki Zainab din ko kuma Raqeeba da Zainab ta nuna kishi akai, gwara ita din ta yi kai kawo zai fi mata sauki.
Balain so ta ke ta gan sa, ta ji ya jikin sa amma jin kai ya sa ta kasa shiga hakan nan, ta gwammaci ta jira a sami dalilin shigar na ta, Amma abin ya gagara har ta na shirin fita daga hayyacin ta. Haka ta hakura ta na mai neman sauki daga Allah dan kuwa shi ya jarabce ta, jarabawar ma kuwa babba.
Sai washagari su Bello su ka dawo. Ranar har tsakar gida Usman ya fito amma ko inda Zainab ta ke be tambaya ba, bare ya yi yunkurin shiga wajan ta. Ta na daga cikin daki ta ke jiyo hirar shi da mutan gidan da harshen fulatanci, wanda har ta fara tsintsinta kadan kadan. Jin har ya karaci hirar shi ya koma be neme ta ba, ita ma ta sha alwashin ko da kuwa zuciyar ta za ta fashe ba za ta neme shi ba. Cikin kankanin lokaci sai ta kara zama bare a Rugar Shehu, kullum ta na cikin bukka idan ba dai uzuri ne ya fito da ita ba, haka kuma ta lura ko giftawa ta yi gaban Usman matukar ya na fara'a sai fuskar sa ya hade ya murtuke tamkar hadari, ya guje ta ya juya mata baya farat daya, yayinda ta ke bukatar shi, ta ke kaunar sa tamkar ran ta. Idan akwai ranar da ta ke tsoro ya bi bayan juma'ar da Usman ya ce za a tafi da ita, duk ran da rana ya fadi garin Allah ya waye sai ta yi kuka, ranar alhamis kuwa ko kafa ba ta iya sakawa tsakar gidan ba, bukkar ta ta wuni cikin bakin ciki da adduar Allah ya sa Usman ya canza ra'ayi.
Ranar Juma'a da asubar fari sai ga Iyalle dauke da irin kayan da Usman ya bata ranar shadi. Ta tarar Zainab zaune kan tabarma in da ta idar da sallah ta na jan jarbi, Iyalle ta zauna kusa da ita tare da fadin
"Ayya Abu, ashe hukuncin da Shehu ya yanke kenan? Mun yi bakin ciki kwarai ke abin alfahari ce a Rugar nan, ba mu ji dadin sakin ki da yayi ba....."
A kidime cike mummunar faduwar gaba Zainab ta yi saurin fadin
"Saki! Cewa yayi ya sake ni? Wa ya ce ma ki ya sake ni?"
Ganin yanda ta kidime Iyalle wacce dama da biyu ta yi maganar ta maganar ta furta
"Ashha babu wanda ya fada min, ganin ya bani kaya ya ce na kawo mi ki, tare da sheda min Bello zai mayar da ke birni ki koma can uwa uba Kano na yi zaton ko hakan aka yi, dan kuwa aure ke kina can shi ya na nan kusan sai a ce ya mutu, ki yi hakuri da azanci na"
Ta karasa maganar ta mai fatan Zainab za ta bijire ta ki yarda da maganar Usman. Aikuwa nan Zainab ta ce sam ba ta san zancen ba ta juya ta mayar masa da kayan sa, babu in da za ta je.
Bayan fitar Iyalle Zainab ta koma ta yi kwanciyar ta. Jim kadan ta ji muryasa a kan ta ya na fadin
"Za ki tashi ki sanya ko na sanya mi ki ta karfi?"
Tsaye ya ke hannun sa dauke da kayan da Iyalle ta mayar masa, yanda ta gan shi tsaye babu wani alamar ciwo a tattare da shi ta ji dadi har ran ta. Ta na daga kwance ta furta
"Sai ka sanya min din na gani ai...."
Ba ta kai gama rufe bakin ta ba ya durkusa ya wufto ta ya na kokarin raba ta da kayan jikin ta, ihu ta fara sosai cikin kokuwar kwatar kan ta, Amma ko a jikin sa har sai da ya raba ta da rigar ta. Ga shi ko rigar mama babu jikin ta, be san sanda ya bi kirjin ta da kallo ba, sanyin da ya ziyarci fatar har ya kai ga sanya ta dan rawar dari da kuma yanda ya zuba mata idanu ya saka ta yi saurin shigewa jikin sa, Usman ya runtse idanu lalle zuciya ba ta da kashi, ganin Zainab da kuma yanda ta kamkame ya sa gaba daya gwiwarsa ta yi sanyi. Cikin zafin nama ya zare ta daga jikin sa, yayinda ya ke kokawar danna rigar kan ta, Zainab ta dada bijirewa ta hanyar yin rawa da kanta, ta na samin damar kwatar kanta ta yi saurin sake shigewa jikin sa, ta rungume shi kam kamar me shirin shigewa jikin sa, cikin kuka ta ke fadin
"Dan Allah kar ka bari a tafi da ni, ba zan iya komawa gida ba"
Usman ya runtse idanun sa cikin karfin hali, shi kan shi ya na jin zafin tafiyar ta, Amma bayan abin da ya faru ta tabbatar ma sa ba ta da makiyi da ya wuce shi, ta kuma tabbatar masa yanayin tsanar da ta masa da kuma tsanar zama da shi a Rugar Shehu....
"Ka riga ka gama bata min rayuwa shi ne za ka yada ni, wallahi ba ka isa ba....."
Maganar da ya dawo da shi cikin hayyacin sa kenan, yayi saurin banbare ta daga jikin ta, ya tashi tsaye, a dake ya furta
"Ki shirya nan da awa daya Bello zai tafi da ke....."
"Na san ka so ni Usman, ka fada min kuma na gani a idanun ka, me zai sa ka guje ni? Na san na ma ka laifi......"
Hannu ya daga mata tare da fadin
"Ba na son ki! Dama na dauko ki ne ina cikin magagin bakin cikin rashin mahaifiya ta, wacce a sanadin ki ban gana da ita ba, yanzu kuma na huce ba kuma na bukatar ki!"
Wani irin zafafan hawaye ne su ka gangaro daga idanun ta. Zanin jikin ta ta kunce domin janyo shi samai yanda za ta rufe kirjin ta, ta tashi ta yi ta sha gaban sa ta na mai kokarin sanya idanun ta cikin na sa, murya kasa kasa ta furta
"Ba gaskiya ba ne, ka ce min ka yi nadama, ranan a bakin ruwa, ka ce min ka na so na......"
Ya na mai girgiza kai yayinda maganganun sa da Tanko ke kara saka zuciyar sa radadi su na mai masa ya yawo a kunne
"Zainab me ya sa? Duk zaman nan da mu ka yi da ke, duk kwanciyar hankalin da mu ka samu.... Zainab... Zainab me ya sa...? Dama kin yi ne dan ki cutar da ni?"
"Ta yi ne domin haka na ce ta yi! Kai a tunanin ka yarinya kamar wannan za ta taba san gidahumi irin ka? Ai ka godewa Allah ma ka sami raban ka!"
"Ki manta da abin da na fada mi ki rannan na fada ne bisa kuskure.......ba na san ki....."
Maganar ya soke ta tamkar takobi. Cikin dauriya ta furta
"Ka na so na Usman, fushi ka ke da ni kawai in ka huce komai zai wuce.."
Kai ya girgiza mata, kana ya ce
"Ba zan iya zama da ke ba......"
"Ko da kuwa ina dauke da juna biyu?"
Kallan ta ya ke cike da bakin cikin karyar da ta ke sharara ma sa, har ta kai za a iya karya ciki, maganar Tanko ya kara ratsa zuciyar sa na
"Ta yi ne domin haka na ce ta yi! Kai a tunanin ka yarinya kamar wannan za ta taba san gidahumi irin ka? Ai ka godewa Allah ma ka sami raban ka!"
Ya sake juyawa zai fice Zainab ta dakatar da shi ta hanyar fadin
"Ka sake ni toh! Idan har za ka mayar da ni gida ka sauwake min wannan auren na masifa!"
Ga mamakin ta sai ga shi ya juyo, hannu ya sanya cikin aljihu ya fitar da takarda, ya na mai ruko hannun ta ya sanya takardar tafin hannun ta. Ba tare da ya bari sun hada idanu ba ya juya zai fita, har ya kai kofa Zainab ta furta
"Ka yi min yanda ka yi sanda za ka dauko ni, dan Allah ka gusar da hankali na Usman....."
A sanyaye ya juyo ya na duban ta, sai a sannan ta lura da yanda idanun sa su ka yi jajur. Cike da nadama ya furta
"Ina fatan za ki yafe min...."
Ya fice da sauri in da ya bar Zainab durkushe hannun ta rike da takardar da ya bata ta na kuka mai tsuma zuciya.
AUREN SHEHU 2
Bayan ta yi mai isar ta, ta tashi ta fara hade na ta ya na ta, tsoron abin da ke cikin takardar da Usman ya bata ya sa ta kasa budewa bare ta karanta, dan kuwa idan ta ga saki uku za ta iya zarewa. Kayan da Usman ya kawo mata ta sanya, kafarta sanye da silifas ruwan dorawa. Kallo daya za a mata a danganta ta da fulanin daji.
Idan aka dauke Raqeeba babu wanda jikin sa be yi sanyi ba ganin Zainab ta fito dauke da akwatin ta, tsakar gidan Shehu cike da jama'a manya da yara sun zo mata sallama, su Iyalle kuwa cikin su har da ma su kuka. Zainab ta karaci waige waigen ta ko za ta ga Shehu, hakan ya sa Bello fadin
"Tun dazu ya fice.....ya ce ba sai mun tsimaye shi ba"
Kai Zainab ta gyada kawai ba tare da ta iya furta komai ba. Ta na kuka su Iyalle na kuka tare da neman yafiyar juna, har su ka mata rakiya daidai mararraba da Usman ya taba aje Tanko sannan su ka juya cike da alhini.
Tafiya ce mikakkiya Muhamadu Bello da Zainab su ka yi, duk sanda ya nemi su zauna ko dan Zainab ta samu ta huta, sai ta ki, gaba daya a tafiyar ta ke sauke fushin ta, ganin haka duk sanda lokacin sallah yayi Muhamad Bello ya ke bata lokaci ko ya samu ta huta.
Ta ki ci, ta ki sha sai kuka. Sai yamma likis su ka Isa Mambila, dake sun saba sosai da Bello sun sami tarba na karamci, in da aka ware ma Zainab daki na musammam dake wasu daga cikin su ba su mance Zainab ba. Ita kuwa sam ba ta iya tuna komai bare ma ta gane su. Da adduar Allah ya sa Usman ya biyo sahun su ya ce ta dawo ya fasa mayar da ita ta kwana cikin ran ta. Ba ta yanke zato ba sai da washagari da sassafe Bello ya sanya ta cikin motan Taraba. Makudan kudin da Usman ya ce a bata, kulle cikin bakar leda Bello ya aje a kan kafarta bayan yayi yayi ta karba, ta ki.
Har zai juya ganin halin da Zainab ta ke ciki ya sa ya kasa tafiya ya bar ta kamar yanda Usman ya ce, tare su ka karasa Taraba. Wajan kwana ne ya gagara sai da Allah ya taimaka wani driver ya kai su wani dan karamin hotel wanda za a kira shi da ba yabo ba fallasa, Bello ya kama mata daki guda, tare da siya mata abinci. Ya sheda mata shi ya na daga can waje kila ya kwana wajan masu gadi dan kuwa shi be saba da rayuwa mai tsada haka ba.
Abincin na su babu laifi, Amma kasancewar ta na cikin bakin ciki da kewar Usman da kyar ta dan caccaka sannan ta yi sallah ta na mai rokan Allah mafita. Kasancewar Zainab ta kwana biyu ba ta kwana kan katifa ba, sai ta ji gadon ya mata wani irin, ta gwammaci ta yi kwanciyar ta bisa dadduma duk da ta san baccin ba zuwa zai yi ba.
Da sassafe wajan karfe Shida ya sanya ta motar Kano, Zainab na masa magiyar kar ya barta shi kuma Bello ya na bata hakuri, har ta kusa tara masa jama'a ciki har da masu cewa
"Toh ana tafiya dole ne? Tun da ta ce ba ta yi a rabu da ita mana"
Wani kuma fadi ya ke
"Kai kuwa ka juya da ita mana"
Cike da rarrashi Bello ya furta
"Ki yi hakuri uwar gida, ban san takamamman dalilin da ya sa Shehu hakuri da ke ba, bayan jaddada soyayyar ki da yayi a gare ni, Shehu na kaunar ki matuka kusan sai na ce ke ce diya mace dal tilo da zan iya bugar kirji na ce Shehu ya so, so daya tal! Shehu ya zabi barin mu, barin Rugar Shehu da komai na shi domin ya dawo birni ya rayu da ke. Dan haka ni sai dai na ce ki yi hakuri, wannan al'amari na ku da daure kai ya ke, Allah ya saka hakan ya fi zama alkhairi, Allah ya sada mu da alkhairin sa, bissalam"
Ya juya ya na mai matse kwalla, in da ya bar Zainab cike da da na sani iri iri, musammam na kasa rokan Usman da ta yi, da ta sani da ta nemi yafiyar shi, da ta san zai ce su dawo birni da ba ta ji zugar Rahila ba, da kuma ba ta bari zugar Raqeeba ya rude ta ba, duk da a lokacin neman hanyar tafiya ta ke Ido rufe, yanzu gashi Allah ya yassare mata lokacin da sam ba ta bukatar komawar ta gidan. Gaba daya rayuwar ta ta sauya cikin watanni kalilan, shin ina ta dosa? Daga ina za ta fara? Tunanin da ta yi ta yi kenan a hanya.
Ba kamar da ba duk check point in aka tsaya sojoji sai sun tanka ta, wannan karan babu wanda ya lura da ita saboda shigar fulanin da Usman ya sanya ta tayi, da kuma wannan shekin da fatar ta take gaba daya ya tafi. Sanda su ka isa Kano Magarib ta yi, dan sahu ta tara ya kai ta gida. Amma ko da ta doshi kofar gate din gidan Malam, gaban ta na faduwa ta shiga bugawa, wani saban maigadi ne ya bude. Ganin mace tsaye bakin kofa ta yi dagaje dagaje da ita cikin kayan fulani ya dube ta ya ce
"Lafiya? Ku barar ku ba dare ba rana?"
Cike da bacin rai Zainab ta furta
"Na ma ka kama da yar bara? Kai wanene ma?"
"Kut! Kanin uban ki ne ni! Ja'ira! Sai ki ta zama a nan tunda ke abin na ki ma har da rashin kunya!"
Baki Zainab ta bude, duk tsiwar ta yau sai gashi ta rasa ta cewa, wai ita ake kira almajira a gidan uban ta. Katan dutse ta dauka ta shiga buga kofar da iya karfin ta. Isowar mota tare da fitowar Jauro da saban maigadi wanda bugun da Zainab ta ke yiwa gate din ya sanya su fitowa a fusace lokaci guda ne. Motar ce ta dalle Zainab wacce Jauro ya hau da fada da shi kan shi be gane ta ba, fadi ya ke
"Wallahi sai mu yi kasa kasa da ke a wajen nan! Kofar gidan uban ki ne za ki kama da bugu ko akwai wanda ki ke bi bashi? Kai muntari ko wani ya siyi nono gun ta ne be biya ta ba?"
Cike da takaici Zainab ta furta
"Kai din gidan uban ka ne ai! Ba nono ba Shanu ya sa siya! Wallahi duka sai kun ci uban ka ni Zainab sai na yi maganin ku!"
Jin Murya irin ta Zainab Jaura ya bude idanu ya na duban ta, gaba daya ya ma manta da motar da ta tsaya ta na shirin a bude kofa su shiga. Muntari da har lokacin be gano komai ba cewa yayi
"Wallahi ban taba siyan nono gun ta ba, kai ni yau ma na fara ganin ta...."
"Hayaniyar me ku ke mana ne da ba za ku zo ku bude mana kofa ba?"
Cewar Falmat wacce ta gaji da sakarcin su Jauro, ta sauke gilashi cikin neman ba'asi. Gefan ta Halitta ce zaune, da ke sa'ad da su ka je umara ta makale lalle sai da Sudais ya bari ta biyo su Nigeria, za ta yi wata guda ya zo ya dauke ta.
Tsayawa Zainab ta yi ta na duban motar cikin wani irin yanayi mai wuyar fasaltuwa, dukan su biyun ba su lura da ita ba, musammam Falmat wacce ta ke bambamin sun ki su bude mu su gate su shigar da mota.
Cikin inina ya na mai nuna Zainab da yatsa Jauro ya furta
"Ran-ran-ki ya da-de ina ga fa kamar dai Hajiya Yakura ce......"
Sai a sannan su ka lura da Zainab, Halitta ce ta fara fitowa da sauri inda Falmat ma ta bi bayan ta, gaban ta su ka karasa idanun su kan Zainab yayinda ita ma din su ta ke kallo, shigar su, yanayin su da kamai na su yayi daban, musammam Halitta wacce ta yi jajur kamar balarabiya cikin bakar abaya. Sai Zainab ta ke jin kan na ta tamkar almajira kamar yanda saban mai gadi ya yi zato, hawayen da su ka dade ba su zuba daga idanun ta ne su ka fara shirin zubowa, ta yi saurin kawar da kai gefe.
"Yakura.........."
Cewar Halitta yayinda ta rungumo ta da sauri, kamshin turaren ta ya maye warin ranar da Zainab ta kwaso, ta ma rasa yanda za ta yi, murnar ganin Yakura ko kuwa kuka za ta yi, Falmat kuwa rugawa ta yi ciki ta ihu fadi ta ke
"Yakura! Yakura ce! Wallahi Yakura ce! Ammy Allah ya karbi adduar mu!
Halitta ta janye Zainab ciki dan kuwa yan unguwa har sun fara tsayawa ganin ba'asi. Ammy ba ta gasgata maganar Falmat ba sai da ta ga Halitta ta shigo hannun ta rike da na Zainab, nan ta zube ta yi sujjada na godiya ga Allah sannan ta tashi ta rugume Zainab, dukan su hudu kuka su ke, aka rasa wanda zai rarrashi wani, musammam Zainab wacce ita na ta kukan biyu ne, har da na rashin Usman.
Sai da su ka dan nusta ne Falmat ta fita shigo da mota, Halitta zaune kusa da Zainab har lokacin ta kasa sakin ta, Ammy ce ki ta kiran yan uwa da abokan arziki ta na sheda mu su Allah ya dawo da Zainab, Yakura ta dawo. Anty Sauda kuwa cewa ta yi da Yakura ta huta Ammy ta fara tambayar ta in da za a samo tsinannen almajirin nan da kuma in da ya kai ta, idan Allah ya wayi gari ita za ta zo.
Duk yanda su ka so Zainab ta fada mu su daga in da ta ke, ko kuma yanda aka yi aka tafi da ita, da kuma wanda ya tafi da ita sai Zainab ta sa mu su kuka. Hakan ba karamin dada tayarwa Ammy da hankali yayi ba, dan haka ta ce kada wanda ya kara tambayar ta komai, a bari ta huta tukunna ko zuwa gobe ne.
Ruwan wanka aka hada mata, bayan Falmat da kan ta ta gyara mata daki. Sai ta ke ganin komai daban musammam da ta shiga bandaki, wai itace cikin tangaran maimakon zagayen kara da Usman ya sa aka mata, cikin kokarin tsayar da hawayen ta yi wanka ta fito. Cikin kayan ta da ta bari a gida ta sami wata doguwar riga mara hannu ta sanya. Gaba daya jin ta ke tamakar bakuwa, komai na gida ya zame mata tamkar sabon abu, gadon katako maimaikon gadon karar da ta saba, carpet maimakon tabarma ko ledar da ta saba, tiles maimakon kasa da tsakuwar da ta saba takawa.
Ta idar da sallah kenan sai ga Halitta dauke da farantin abinci, ta aje gaban ta tare da fadin
"Yakura ki daure ki ci abinci"
Zainab ta yi mata shiru kawai ta na duban ta. Ganin ba ta da niyar bude kolar ne Halitta ta bude ta fara zuba mata, shinkafa ce jellof ya sha bushesshen kifi, yanayin turirin da ke fitar da kamshin kifin ne ya daki hancin yakura, tun ta na iya jurewa har ta kai ga toshe hanci da hannu, cikin ta ne ki hautsinawa sanadiyar rashin abincin da ba ta ci ba tun safe, ba ta ankara ba sai ji ta yi amai ya taso mata, ta tashi a guje ta shiga bandaki. Nan ta yi ta amai kamar wacce za ta amayar da hanjin cikin ta. Hankali tashe Halitta ta kira Ammy.
Cike da tsoran abin da zuciyar ta ke ayya na mata Ammy ta furta
"Yakura ayya kuwa? Tun da na gan ki na san ba ki da cikakkiyar lafiya, tin kafin dare yayi mu tafi asibi..."
"Ammy gajiya ce kawai da yunwa, tun safe ban ci abinci ba hanji na ya kulle, da na sha ruwan zafi I will be fine"
"Duk da haka gobe sai mun je asibiti Yakura....."
"Allah ya kai mu"
Cewar Zainab cikin kaguwar su tafi ko ta samu ta huta. Ammy ba ta barta ba sai da ta tabbatar ta sha ruwan bakin shayi kamar yanda ta bukata, bayan shi ba ta iya cin komai ba, dole haka su ka bar ta ta kwanta.
Tun da su ka fita take juyi kan gado, Baccin gaji ya ke diban ta amma hakan be sa ta dena ganin Usman da ke mata gizo cikin idanun ta ba. Filo ta ja ta rungume tamkar shi ne Usman cikin magagin bacci ta furta
"Ina san ka Usman, ba zan iya rayuwa da wanin ka ba, dan Allah ka rufa min asiri ka dauke ni daga nan......."
Inda Zainab ke cikin radadin san Usman, shi ma a nashi bangaran gaba daya ya rikicewa su Iyalle tun bayan da ya dawo ya tadda Bello ya cika umarnin shi ya tafi da Zainab.
Ko zaman cikin Rugar baya iya yi bare ya yarda ya shiga bukkar sa ko wanda Zainab ta koma bayan ya farfado da ga ciwo. Kamar yanda ya ke mata gizo shi ma din gizo ta ke masa. Fatan shi Allah ya sa ta isa gida lafiya gashi be da hanyar da zai gane hakan.
***
Anty Sauda tare da Ammy da Halitta ne su kai Zainab asibitin premier washagari da azahar bayan isowar ta, tare ta ke da sojoji wanda a fadar ta su ne za su rubuta statement din da Zainab za ta ba su bayan sun dawo daga asibiti, ta sha alwashin kama Usman da duk wani da ya ke da sa hannun dauke Zainab. Babu gwajin da ba a yiwa Zainab ba, ciki har da na HIV, hepatitis da na juna biyu.
Bayan an gama gwaje gwajen suna zaune jiran fitowar sakamako Zainab ta yi zaman ta can gefe a reception, ba ta iya zama cikin su Halitta bare ta saki jiki da su.
Anty Sauda wacce ke zaune tare da Halitta da Ammy, ta girgiza kai bayan ta karewa Zainab kallo ta ce
"Wallahi wannan tsinannan almajirin ya cuce mu! Dan Allah ki ga yanda yayi breaking Zainab completely? Ji yanda Zainab ta koma, ji irin shigar da Zainab ta ke yi ta fita?"
Duka ukun kallan ta su ke yi, ita kuwa sam hankalin ta ba ya wajan su, tunanin sakamon gwajin da aka mata ta ke na game da juna biyu, duk da dai ita kan ta ba ta san wani irin sakamako ta ke fata ba, burin ta dai Allah ya tabbatar mata da abin da ya fi alkhairi.
Sanye ta ke cikin hijabi ruwan toka wanda ya sauka har kasa, sam babu wani alamar rawan kai da jin kai da aka san Zainab da shi. Hannu ta sa ta goge hawayen da ke gangarowa daga idanun ta, hakan ya sa Ammy dauke kai cike da jin zafin halin da diyar ta take ciki, ta na mai zargin kan ta da Malam da laifin sanya ta cikin duk wata masifa da ya afka mata.
Halitta da Anty Sauda ne su ka koma wajan ta, inda Halitta ta rungume ta cikin rarrashi, Anty Sauda kuwa fadi ta ke
"Ki dena kuka Yakura, wallahi sai an kwatar mi ki hakkin ki, na mi ki alkawarin kamo duk wanda ke da sa hunnu cikin wannan lamarin ko da kuwa wannan tsinannen almajirin ne! Ai ga irin ta nan! Na dage sai ya sake ki uwar ku ta ki goya mana baya, yanzu wa gari ya waya?"
Likita ce ta fito ta bukaci ganin Zainab ita kadai domin bata sakamakon gwaje gwajen da aka mata, Anty Sauda ta ki yarda lelle sai dai a fadi sakamakon a gaban su, ai su ne su ka kawo ta, da abin na sirrin Zainab ne da ba za su kawo ta ba sai su ce ta yi tafiyar ta ita kadai.
Sai da Zainab ta ba da izini sannan likitar ta yarda su ma din su ka bi Zainab zuwa ofishin likitan, Halitta ce kadai ta zauna waje.
Zainab da Anty Sauda zaune kujerar da ke fuskantar teburin likita, in da Ammy ta sami kujera can gefe ta zauna. Da Ammy har Anty Sauda likita su zubawa ido cikin jaran tsammani. Cike da nutsuwa likita ta musu bayanin cewa duka kwaje kwajen Zainab negative results aka samu ma'ana ba ta dauke da wani cuta da ake tsoro, likita ta kare jawabin ta ta hanyar fadin
" Sai dai kuma sakamakon gwajin juna biyun da aka mata ne mabambamci, dan kuwa ya nuna ta na dauke da juna biyu...."
Wani irin shauki ne ya ziyarci zuciyar Zainab ta tsinci kan ta tana mai runtse idanu, yayinda ta ke jiyo maganganun Anty Sauda tamkar ruwan zafi, fadi ta ke
"Ko juna dari ne zubar da shi za a yi wallahi! A yi polishing tsinannen......"
Ammy kuwa kuka ta saka ta salati, cewa ta ke
"Innalillahi wainnailaihi rajiun! Innalillahi wainnailaihi rajiun!"
Anty Sauda ta kara da
"Sai yanzu ki ke da bakin salati? Ai dama aka ce wanda be ji bari ba ya ji hoho, mu ka yi mu ka yi ki dakile auren nan ki ka min kunne uwar shegu! Ai ga irin ta nan! Kai idan har ba a kama min yaran nan ba ban isa Sauda ba! Likita mu na so a cire cikin nan da gaggawa....!"
"Babu wanda zai cire min ciki!"
Cewar Zainab a fusace. Hakan ya sa su Anty Sauda sakin baki su na kallan ta. Ba ta gushe ba ta kara da
"Cikin shege ake zubarwa ba na halas ba, dana dan halas ne kada wanda ya kara aibata min ciki bare ya tsinantar min da shi! Idan har wahalar hanya be zubar min da ciki ba, ban ga dalilin da zai sa wani mahaluki ya taba min shi ba!"
Ta na gama fadin haka ta tashi fuuuu ta fice ta bar Anty Sauda da salati da sallallami ta na tafa hannu. Fadi ta ke
"La'ilahaillahu muhammada rasulillahi! Hajja Aleesha wannan yarinya ba cikin hayyacin ta take ba! An riga an juyar da kan ta sai mun dage da addua!"
Ammy kuwa rasa ta cewa ta yi, dama dai in tsiwa ne kadan daga aikin Zainab, mamaki daya shi ne ikirarin da ta ke akan cikin ta,
"Allah dai ya sa ba cikin hayyacin na ta take ba...."
Ammy ta fada a sanyaye.
"There is no two ways about it! Ki ma dena raba dayan biyu ba cikin hayyacin ta take ba, sai an yi rokan Allah!"
Cewar Anty Sauda. Da haka su ka yiwa Likita sallama su ka tafi. Cikin mota su ka tadda Zainab zaune ta hada girar sama da na kasa. Babu wanda ya tanka ta sai bayan da su ka isa gida sannan Anty Sauda ta saka ta a gaba da tambaya. Zaune su ke a falo, sun zagaye Zainab kamar suna gudun za a iya sake sace ta
"Za ki gane wanda ya dauke ki? Wannan tsinannan almajirin ne ko?"
Zainab ta mu su banza. Anty Sauda ta kara da
"Yakura mun san abin da ciwo, matukar ba ki budi baki kin yi magana ba ta yaya za mu iya kwato mi ki hakkin ki daga zalincin da aka aikata mi ki? Ki fada mana ya aka yi ya sace ki, Kuma ina ya kai ki, ya sunan garin...?"
Zainab ta ki amsa ta. Cikin nuna gajiyawa Anty Sauda ta furta
"Ina ga sai dai sojojin nan su tambaye ta kila su ta fada mu su, in ba haka ba Hajja Aleesha sai mun tsaya tsayin daka akan Yakura! Wannan almajirin ya asirce ta ya kuma breaking din ta...."
"Ba zan yi magana da kowa ba!"
Zainab ya katse ta a fusace. Ba ta gushe ba ta kara da
"Kada ki kara kiran miji na da tsinannen almajirin! Usman miji na ne! Eh shi ya dauke ni saboda shi aka daura min! Da zai kai ni ya gusar min da hankali, Amma da ya tashi sallama ta da hankali na ya sallame ni, na roke shi ya sake gusar min da hankali na ko zuciya ta za ta dena min radadin barin sa, ya ki! Yanzu ya sa na dawo gida amma zuciya ta na can tare da shi, Kuma ku bar tunanin addua, cikin hankali na na ke, kuma Anty Sauda zan so ki sarara min dan kuwa maganganun ki kan miji na suna neman yin tsauri dayawa!"
Shiru ne ya biyo baya tamkar wanda ruwa ya cinye, inda kunyar yanda Zainab ta watsawa Anty Sauda kasa a Ido ya rufe Ammy, Anty Sauda kuwa ji ta yi tamkar kasa ta tsage ta shiga. Tashi Zainab ta yi ta shige ciki, bayan tafiyar ta Ammy ta nisa ta ce
"Tabbas Yakura ba ta cikin hayyacin ta, ya asirce ta yayi..."
"Hmmmm kin ga Hajja Aleesha matukar ba Yakura ce da kan ta ta zo ta same ni ta ce min ba cikin hayyacin ta take ba na yi hakuri, wallahi na cire hannuna a kan maganar ta, ke hatta General ma zan fada masa babu ruwan sa....."
"A yi haka Hajja Sauda? Ai hannun ka ba ya rube ka yanke ba ko?"
Anty Sauda na girgiza kai ta furta
"Ah ah Hajja, a dai yi mata addua, matukar ba ta canza ba toh tabbas ki cire rai akan ta kema, ki sa a ran ki babu Yakura. shikenan ya tsafe ta har abada"
"Innalillahi wainnailaihi rajiun!"
Cewar Ammy ta na mai sharar kwalla. Nan Anty Sauda ta barta, cike da bacin rai ta shige ciki tare da kiran mijin ta ta sheda masa halin da ake ciki.
*****
Bangaran Rugar Shehu kuwa, Muhamadu Bello ya tadda Usman tamkar mai makoki, cikin kankanin lokaci ya canza gaba daya. Zaune su ke karkashin bishiya in da Bello ya zo ya tadda shi bayan dawowar sa.
"Idan har ka na kaunar ta haka da ba ka bari ta tafi ba Shehu, domin kuwa Uwargida na kaunar ka ita ma, wallahi halin da ta ke ciki ya sanya na kasa barin ta har sai da na kai ta har Taraba, na bar ta a cikin wani hali"
Maimakon ya bashi amsa daidai da maganar sa, sai cewa yayi
"Ina nan a kan baka na na barin Rugar Shehu sati mai zuwa in Sha Allah, zan shiga uwa duniya kamar yanda na taba shiga a baya, Amma wannan karan hanyar neman cigaban Rugar nan ce zai fitar da ni"
Ya dan dakata kamar mai nazari. Muhamadu Bello ya nisa, kana ya ce
"Duk da ba haka aka so ba, Amma ka riga ka yanke hukunci ba tun yau ba. Ka ga Kado ba su da amana akan dukiya ko neman ta, akwai wani bafulatani dan uwan mu, Ibrahim Yerima Balla, dama mun saba cinikanyar shanu da shi, mutumin birne ne kwarai amma sai amana, ya kuma san darajar dan Adam. Nan Yola ya fiya zama duk da ya ce min ya na da gidaje a Kano da birnin tarayya, me zai hana idan ka tashi tafiya na hada ku?"
Bayan Usman yayi dan tuntuntuni ya furta
"Ka na gani zai iya saka ni hanya Bello? Ni fa yanzu tsoran bil'adama na ke"
" Mutum abin tsoro ne, Amma kada ka damu na shedi Ibrahim, ba ya cutarwa"
"Toh Alhamdulillah, zan shedawa su Kawu Iliya, sati mai zuwa sai mu tasarwa Yola, zan fara tafiya da shanu dari biyu mu gani, idan da bukata wasu nan gaba sai na yo aike"
Da wannan shawarar Usman ya bar Bello ya tinkari su Kawu Iliya. Dan kuwa shi ma ba zai iya jure zaman Rugar Shehu ba bayan tafiyar Zainab, komai na Rugar tuna masa da ita ya ke, sai ya zama tamkar zuciyar ta na ma zuciyar shi fatalwa. Ji ya ke kamar ya bi ta Kanon ko ya sami sauki, Amma taurin kai ya hana, shi ya sa ya yanke hukunci shiga duniya ko ya sami sauki.
******
Babu irin adduar da Ammy ba ta sa an yiwa Zainab ba, islamiyoyi da makarantur allo ta saka aka kai sadaka in da aka sa yara sauka da zikiri. Amma Zainab ko gizau, ta tsaya tsayin daka babu mai zubar mata da ciki.
Bayan sati guda da dawowar Zainab, da la'asar Zainab zaune bakin gadon ta dake tashin ta daga bacci kenan, kamar yanda ta saba ta yi mafarki da Usman, takaicin farkawar da ta yi ne ya sanya ta zaman bakin gado tare da doka uban tagumi.
A hankali aka kwankwasa mata kofa, sanin ba za ta amsa ba ya sa suka bude kofar su ka shigo, Ammy ce a gaba, biye da ita Anty Sauda ce da Halitta. Halitta ta zauna kusa da ita, in da Ammy da Anty Sauda ke tsaye suna duban ta. Cike da damuwa Ammy ta furta
"Yakura wannan tunanin da bakin cikin da ki ke ciki zai iya lahanta ki da dan cikin na ki, me zai hana ki bi Antyn ki ku koma Maiduguri, can zai fi mi ki kwanciyar hankali kafin ki samu ki koma makaranta....."
"Babu in da zani, ba kuma zan sake komawa makarantar ba, Nan zan zauna abu na har sai na haihu, idan kuma zaman nawa na damun ki Ammy sai na sami ko da gidan haya ne....."
"Ah ah Yakura"
Ammy ta yi saurin katse ta. Ta kara da
"Nan din ai gidan uban ku ne, ku ne magada dan ko da aka raba gadon Malam gidan a naku ya fado ina kuma batun neman haya? Kuma ina ki ka taba Jin zaman diya a gida ya dami uwar ta, dama farin cikin ki shi ne fatan mu...."
"Usman shi ne farin ciki na Ammy, rashin shi shi ne sanadin bakin ciki na, idan har kuna so ku sake ganin walwala ta a duniya ku barmin ciki na na haife shi, ban da makiyin da ya wuce wanda zai yi yunkurin raba ni da ciki na, wannan cikin shi ne rayuwa ta....."
Dan takaici Anty Sauda kasa magana ta yi ta juya ta fice fuuu tamkar za ta tashi sama. Ammy na mai dafa kafadar Zainab ta furta
"Na mi ki alkawari Yakura babu wanda zai sake cewa ki zubda cikin nan, Allah ya raba lafiya"
Ta fice jiki a sanyaye. Ya rage da Halitta sai Zainab cikin dakin. Shiru su ka yi kowannan su na sakar zuci, daga bisani Halitta ta furta
"Yakura?"
Halitta ta kira sunan ta a hankali. Zainab ta daga ido ta kalle ta. Karo na farko da su ka zauna tare cikin aminci ba tare da Zainab na neman ta da bakar magana ba. Halitta ta murmusa ta ce
"Kada ki damu, ina goyan bayan ki dari bisa dari"
"Na gode Halitta, Su Ammy sun kasa ganewa, ina son miji na, ina son Usman fiye da tunanin ku, akan wani dalili zan zubda cikin Usman?"
Duban ta Halitta ta ke cike da mamakin yanda te ke ikirarin kaunar da ta ke yiwa Usman wanda ada bubu wanda ta tsana kamar shi, lalle shi ya sa ba a so a fiya zurfafa kiyayya ko soyayya ga mutum. Halitta ta ruko hannun ta, cikin rarrashi ta furta
"Amma me zai sa ki dawo gida? Idan har ki na kaunar Usman me ya sa ki ka yarda ki taho ke kadai? Menene dalilin shi na barin ki ki taho?"
"Abubuwa sun faru dayawa Halitta, kin fi kowa sannin yanda na tsani Usman ada, ina zaman zama na Daddy ya daura min auren dole da shi, bayan rasuwar Daddy ni kuma na yi kuskuran sawa a kamo shi domin ya sake ni, shi ne aka kamo kanin sa......"
Nan takwashe komai ta fada ma Halitta, ta kare da
"Bayan ya warke shi ne ya gaba daya ya guje ni, dan Allah ina laifi na Halitta? Wallahi ban san kashe shi za su yi ba, I just wanted to go home then not knowing that Usman is the only home I've, yanzu gashi ya ba ni takarda, Allah kadai ya san saki nawa ya min...."
Ta kare maganar cikin kuka.
"Ina takardar ta ke?"
Kai ta girgiza mata ta ce
"Ah ah wallahi ba zan ba ki ba, ba za a bude ba, ba na so ma na san yawan sakin da ya min, ban shirya ba Halitta, haka ko da wasa kada ki bari su Ammy su san babu igiyar auren Usman a kai na"
"Kai amma be kyauta ba, Usman be ruke amanar Daddy ba....."
"Ya yi iyakar kokarin sa Halitta, Ni na hada baki da ma su neman ran sa, kada ki ga laifin sa Halitta"
"Haka ke ma ba ki da laifi Zainab, kin yi komai dan neman mafita ne, kin yi ne domin ke samu ki tsira, kuma duk wanda yayi judging din ki base on that ba adali ba ne, you did what you thought was right for you"
Shiru su ka yi na wasu mintina kafin Halitta ta nisa, kana ta ce
"Nan da sati biyu zan koma Saudia Yakura, Amma kafin na tafi zan so a ce kin yarda an je makarantar ku a san ya makomar karatun ki ya ke, mate din ki fa sun yi graduating"
Murmushi Zainab ta yi, yayinda ta ja filo yanda za ta dan kishingida, sannan ta furta
"Shin ki na tunanin zan iya komawa makaranta a wannan hali da na ke ciki? Ku yi hakuri ba zan iya ba Halitta, waccar Yakurar da ku ka sani is gone...har abada.."
Tausayin Zainab ya dada rufe Yakura, gashi hawaye ya na son zubo mata, Amma sai kokarin ruke shi ta ke dan kar Zainab ta gani ta kara karaya. Tashi ta yi da sauri za ta fita, har ta kai kofa ta tsaya, ta dan juyo kadan yanda Zainab ba za ta lura da hawayen da ke zuba daga idanun ta ba ta ce
"Falmat ta ce wayar ki ba za ta gyaru ba, wacce iri ki ke so a siyo mi ki?"
"Waya? I don't need it for now, ku bar ta kawai....."
"Yakura! Wani irin rayuwa ce wannan? Hatta waya ma ba za ki ruke ba?"
Zainab na murmushi ta ba ta amsa da
"Sanda ina slaying kun ce na fiya fitina, yanzu kuma I'm managing myself kuna ta kokawa! Dan Adam kenan, ba na bukata dole ne?"
"Ah ah ba dole fa"
Cewar Halitta yayinda ta fice abin ta tana zubda hawaye.
AUREN SHEHU 2
Kamar yanda Ammy ta mata alkawari babu wanda ya kara tunkarar Zainab da maganar zubda ciki, hakan ya sa ta dan sami kwanciyar hankali, musamman da Anty Sauda ta hada na ta ya nata ta koma Maiduguri.
Cikin sati daya Usman ya hade kayan sa, bayan ya shawo kan su kawu Iliya da kyar sun yarda ya sake barin Rugar Shehu. Ana saura kwana uku ya tafi aka daura auren Muhamad Bello da Raqeba. Iyalle ce ta karbi rukon Cangwai duk da a zahirin gaskiya sun gano ba diyar Usman ba ce, rashin Rahila da Tanko ya sanya dole su hakura su zauna da ita.
Muhamad Bello ne da kan sa ya raka Usman har Yola gidan Alhaji Ibrahim Balla kamar yanda ya yi alkawari. Ya karbi bakwancin Usman hannu bibbiyu musammam da ya ga harkar cigaban da ya zo da shi. Cikin gidan gonar sa ya bawa Usman masauki na musammam, cewar shi zai iya zama kafin ya bude ido shi ma ya sami na shi.
Alhaji Ibrahim Balla magidanci ne mai kimanin shekaru hamsin da biyar a duniya, matar shi daya haka kuma dan sa daya tilo kamar tsoka daya a miya, amma hakan be sa ya sangantar da dan na shi ba wanda ake kira Umar. Ya tashi da tarbiya, dattako dadin dadawa kuma ga gata, ilimi wayews da ado tamkar dawisu. Umar saurayi ne mai shekara talatin da biyar a duniya, kasancewar ya karanta health economics a Fannin digiri ya koma yayi development studies a masters ya sa ya zama shi ne jagaba wajan habbaka sana'ar mahaifin na sa, wato sana'ar gidan gona.
Cikin kankanin lokaci Alhaji Ibrahim ya lura da halayyar Usman, da kuma amanar sa, hakan ya sa zuciyar sa kwadaita masa hada shi da dan sa Umar wanda kusan duk abin da ya shafi gidan gonar shi ke tafiyar da shi. Ga kuma ilimin Isalama da ya tabbata Usman na da shi wanda ya ke da yakinin lalle Umar zai amfana sosai, da wannan ya yi kokarin kulla abotan Usman da Umar, duk da kuwa ya san in dai aka zo fannin wayewa hali ya sha bambam.
In da Allah ya kawo abin da sauki, sai ya hada jinin Umar da Usman, yanda ado da wayewar Umar ke burge Usman, shi kuma Usman kamala da ilimin addinin Usman ke burge shi, musamman da ya ji ya na larabcewa da wasu daga cikin abokan sana'ar su da su ke Larabawa, sannan duk wani muhadara da majalisin malamai Usman na kokarin zuwa wani lokaci har gayyatan Umar din ya ke. Kullu yaumin Umar na kokarin jan Usman jiki kamar yanda mahaifin sa ya ba shi umarnin, duk dai Usman na dan janye jikin sa ba dan komai ba sai gudun kar ya kwafsawa Umar, duk wata harka da ya shafi shiga cikin mutane sai Usman ya nemi ya janye jiki, har sai Umar yayi da gaske kafin ya yarda ya bishi. Duk wanda kuwa ya kuskure ko kallan banza ne ya yiwa Usman lalle kuwa a ga fushin Umar.
***
Hutun Halitta wacce ita ce mai debewa Zainab kewa ya kare, Sudais ya ce lalle ta hado nata ya nata ta koma Saudi ba zai iya zuwa Nigeria ba kamar yanda ya mata alkawari ba saboda yanayin aiki da ya yi yawa.
Da yamma likis Halitta shirye tsaf, sanye cikin bakar doguwar riga, suna tafe suna hira Zainab ta raka ta har mota in da Ammy da Falmat ke zaune suna jiran ta su kai ta Airport. Har ta zauna ta dubi Zainab wacce ke tsaye ta na duban ta. Sanye da hijab ruwan dorawa da ya kai mata har kasa, gaba daya ta sauya ba walwala ba farin ciki, kullum cikin damuwa ta ke har ta kai ya fara nunawa a jikin ta.
"Dan Allah Yakura ki rage damuwa ko dan cikin da ki ke dauke da shi"
Cewar Halitta cike da damuwa. Ta kara da.
"Zan mi ki addua in Sha Allah......"
"Idan har irin adduar da kuka min ne har Allah ya sa na dawo gidan ba na so, da ba ku min ba da yanzu ina tare da miji na..."
Jin haka Ammy ta kauda kai gefe. Falmat cikin ran ta cewa ta yi 'aha dama zancen kenan Yakura ta zama sai ka ce mayya!"
"In Sha Allah zan mi ki adduar mafi alkhairi a rayuwar ki"
Cewar Halitta. Zainab ta kada baki ta ce
"Usman ne mafi alkhairi Halitta"
Halitta na mai murmushin yake ta furta
"In dai shi ne toh Allah zai warware komai Yakura, bi'izinllah"
"Allahumma amen, Allah ya tsare ya sauke ku lafiya"
"Ameen ameen, ma yi chatting, ko da yake ke fa ko wayar ma ba ki da shi bare na chat, ki taimake ni Yakura, kira daga Saudi tsadi, ki samu yar waya sai mu ke gaisuwa ta social network, ki taimaka"
Zainab na murmushi ta bata amsa da
"Yar ana ce zai yi tunani akai"
Da haka su ka yi sallama jikin kowa a sanyaye.
***
Watannin Usman uku suna kasuwanci tare da Umar Balla. Hidimar da ke gaban sa be sa ya manta Zainab daidai da sakan daya ba, da ita ya ke tashi da ita ya ke kwanciya cikin ran sa. Wani sa'in sai yayi da gaske ya ke iya jure rashin ta. Har Umar ya kai ga ganewa akwai damuwar da ke tattare da shi, amma ko da ya tambaye shi dalili ce masa yayi babu komai kawai yakan dan yi tuntuntuni ne akan Rugar Shehu da kuma yanda zai bunkasa Rugar a sami cigaba.
Tafe su ke cikin motar Umar, kan hanyar dawowar su daga Mambila in da su ka je su ka yi cinikin shanu. Umar wanda ya ke baki, be da tsayi sosai amma kuma ba a kira shi gajere ba, haka kuma kyawun sa na ba yabo ba fallasa, sanye ya ke da kanana kaya, bakin wando da jar riga mai gajeran hannu. Usman da ke gefan sa sanye da wannan shigar ta sa da ya saba, riga yar shara, da rawanin sa da ya koma yi tun bayan tafiyar Zainab. Hankalin Umar kan kwalta ya furta
"Ni kuwa da za ka bi shawara ta Usman da fili za ka siya babba ko da kuwa a wajan, ka gina gidaje ciki in ya so ka kwaso duka jama'ar Rugar ta ka, ku yi zaman ku ciki "
Cikin kaguwa Usman ya furta
"Shin ka na ganin haka me yiwuwa ne? Kai mutane na fa ba kamar na ku ba ne, zaman bukka ya fiye mu su zaman binni da wahalar ta, Ni dai da ka ganni nan ni ke da kwadayin birni..."
Dariya Umar yayi jin furucin Usman, dan kuwa ya san har ga Allah ya sosa masa in da ya ke masa kyakayi. Kana ya ce
"Ina ce so kake ka bunkasa Rugar ta ku? Ka na tunanin wannan tsarin da Shugaban kasa ya ke so ya aiwatar mai yiyuwa ne? Ko ba ga yanda kudanci da wasu bangare na arewacin kasar nan ke sukar tsarin ba? Ka ga wannan Ruga settlement din ba abu ne mai faruwa nan kusa ba, Amma kai a karan kanka za ka iya kwatantawa ta ka Rugar, tun da babu laifi Allah ya ba ku arziki na dabbobi kwarai da gaske, da kuma taimakon yan kasuwa na nan Nigeria da kuma na kasashen waje wanda za su sa hannun jari a tada hanyar arziki mai girma, ina mai tabbatar maka za ka shahara kwarai"
"Kai wannan maganar ta ka ya sa ni tunani Umari, wa ya ga jama'ar Rugar Shehu kusa da birne!"
Umar na dariya ya furta
"Kai ba ma kusa da birni ba, idan ma cikin birni ka ke so ka kawo su ai ba abu ba ne mai wuya, dama naira ce wuyar, kuma Allah ya hore, ana nan ana nan sai ka aure matar birni, dama ana ta min maganar ka, ana ta kawo sakon gaisuwa fa"
Gaban Usman ne ya fadi, yayinda da Zainab ta fado zuciyar sa. Cikin kokarin waskewa da maganar aure ya furta
"Wace matar birni ce za ta so bagidaje dan kauye Irina? Ai mata sun fi son wayayyan mutum"
Umar na duban sa ta wutsiyar ido ya ce
"Wai kullum aka yi magana sai ka ke kawo wayewa wayewa wayewa! Wai kai wata irin wayewa ka ke magana?"
Zuciyar Usman daya ya furta
"Wayewa ai shi ne boko, ka ga kai da ka ke dan boko Umari hatta shigar ka daban ta ke, yanayin ka daban kai komai na ka ya fita daban ba kamar ni dan daji dan Ruga ba, wanda ko aji ban taba shiga ba bare a kai ga jami'a, ko zo a kashe ka da turanci ba ban sani ba...."
"Da larabci fa?"
Umar ya katse shi ya na mai take mota ganin ya sami sararin hanya.
"Ah wannan Alhamdulillah ai har labari sai na baka da shi"
Kai Umari ya gyada, be gushe ba ya kara da
"Wannan larabcin da ka iya ya fi turancin da ka ke ihun ba ka iya ba, ilimin da ke da shi na addini ya fi wannan bokon da ka ke tunanin shi ne wayewa, da ilimin boko shi ne wayewa da tun lokacin manzo (SAW) za a fara boko, addinin islama shi ne wayewa, ba ka taba yin bokon ba ne, da ka yi da za ka gane cewa komai da ake koyarwa a bokon musammam na bangaran kimiyya akwai su cikin alqur'ani da hadisin Manzo (SAW)"
Usman na mai gyada kai ya furta
"Allahu akbar"
Umar ya kara da
"Wannan rudun da ka ke gani na duniya, ba wayewa ba ne, wannan ba komai ba ne illa zamananci, ka ga wannan shiga tawa da ka ke gani ya ke burge ka, nan da shekaru masu zuwa sai ka ga ana kiran sa da old fashion, ma'ana an bar yayin sa, zamanin sa ya wuce, Allah shi ne zamani Usmanu! Haka kuma mutane nawa ne ga su yan birnin kuma yan boko amma hakan be sa sun kasa shirme ko rashin azanci a rayuwar su ba? Soboda sun yiwa wayewa fahimta daban har ya kai su ga halaka. Haka kuma ita jami'a da ka ke gani, waje ne koyan rayuwa, waje ne in da mutane iri iri daga sassa daban daban ke taruwa domin koyan ilimin boko, toh amma daga karshe ba ilimin kadai ake koya ba, har da dabi'u na dan Adam, mai kyau da mara kyau sai dai wanda yayi dace, da kuwa ilimin addini shi ma ya na da gurbi irin yanda boko ya samu a zukatar bil adama da kuwa boko ya zama ba koman komai ba"
Umar ya fadi ya na mai kallan Usman. Ya kara da
"Ai kai ma wayayye na Usmanu, in kuma ka na so ne ka zama dan zamani zan maisheka dan zamani na koya maka shigar yar birni, Amma fa idan matan birni su ka sako ka gaba ba ruwa na"
Ya karasa maganar ya na dariya. Shi ma Usman din dariyar ya ke, nan kuwa be san Umar har zuciyar sa ya ke magana ba, dan kuwa daga lokacin ya sha alwashin wanke Usman tas ya mayar da shi dan zamani kuma dan birni.
*****
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, in da Zainab ke renon cikin Usman, tare da fama da son shi da tsananin kewar sa, har ta kai in ta yi sujjada ta kan roki Allah ya cire mata soyayyar Usman daga zuciyar ta, amma sai ya zama tamakar abin ma dada karuwa ya ke, dan haka sai ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido. Halitta ce ta dage sai da Zainab ta sami waya, amma iyakar ta WhatsApp, bayan shi ba ta wani social network. Zainab the slay Mama ta zama salihar Dady a zahiri da badini, haka kuma ta na kokarin yiwa Malam addua sosai,
Bangaran Usman kuwa yanda Umar ya dage akan mayar da shi dan zamani ya sanya shi mika wuya wajan daukan darasi, ta suturun Usman ya fara, sai da ya tabbatar Usman ya ba da dukkanin kayan sa na ruga sannan tasa shi gaba ya masa ordering shaddu getzner na gani na fada daga SAFFAD Fabrics and more na Hajiya Safiyyah Ummu abdoul, . Rabin shaddu farare ne guda ishirin, sai kuma shudi, ruwan kwai, da kalar toka guda goma. Haka kuma ga material na maza da su boyel. Kanana kaya da takalma ne ya sa ka abokin sa mai shigo da kaya da Uk ya kawo masa. Tun Usman na kokawa akan kudin da Umar ya ke sa shi kashewa, sai gashi shi ma ya zo ya na alfahari da su bayan isowar kayan ya ga kyan su.
Dinki irin na zamani wanda yawanci irin na Umar din ne ya sa aka yiwa Usman, kai hatta roll on sai da Umar ya koyawa Usman yanda ake amfani da shi. A hankali ya ke kokarin fito da Usman gari duk da ba karamin fama ya ke sha da shi ba wajan saka kananan kaya, sai Usman ya ce masa shi wallahi ya na jin kan sa tamkar tsirara musammam idan rigar mai karamin hannu ce. Ran da kayan sa na Uk su ka iso ranar Umar ya zo har gidan gona ta tasa Usman a gaba lalle ya saka daya daga cikin su ya fito ya same shi ya na jiran sa cikin mota.
Umar na zaune cikin mota har ya fara tunanin sake komawa ciki ya taso kyeyar abokin na sa, sai gashi ya fito cikin kananan kaya, shudin riga mai haske, da shudin wando mai duhu, shi kan sa Umar be san sanda ya saka ihu ba ganin yanda kayan ya karbi Usman kwarai, fadi ya ke
"Yo mutumina! Lalle yau za mu dau magana!"
Cike da kunya Usman ya karasa gaban sa, sai a sannan Umar ya lura da silifas ruwan dorawa da ke kafar Usman. Ya na dariya har da kwarewa ya furta
"Toh Malam Shehu! Wannan silifas da ka sha haka ina zuwa?"
Usman na mai kallan kafar sa, da iya gaskiyar sa ya furta
"Yo menene toh? Silifa din ma ba ni sawa?"
"Ka ga wannan magana ta ka sai ka canza Alhaji, kar a ga gaye iya gaye amma in ya bude baki sai aji maganar yar Rugar Shehu"
Usman ya kai masa duka, Umar ya kauce ya na dariya, ya kara da
"Haka kuma tsakanin ka da silifas dan Usumanu sai dai a bandaki, wallahi babu in da zan kara zuwa da kai da silafas kafar ka!"
"Sai na yi zamana! Kai ni fa da na san haka za ka uzzara min da ban ce ina san wayewar nan ba!"
Umar na dariya ya wuce ciki ya na mai furta
"Zamananci dai ko, na fada ma ilimin addanin musulunci shi ne wayewa, wannan da ka ke koya zamananci ne, gishirin zaman duniya"
Usman na duban shi har ya shige ciki, cikin ran sa ya na mamakin yanda ya saba da Umar sosai, dan tun da ya ke be taba yin aminci da abota da kowa ba kamar Umar, cikin kankanin lokaci su ka saba da juna sosai kullum su na tare, haka kuma Alhamdulillah harkar gidan gona ta karbe shi, haka kuma shawarar Umar da ya bi shi ma da alama za ta bulle masa. Ya siyar da shanu fiye da dari biyu da hamsin daga cikin shanun sa, da kudin su ka yi cinikin wani katan fili duk da dai yayi wajan gari kadan amma babu laifi wajan da kwanciyar hakanli da kuma tsaro kasancewar yayi kusa da daya daga cikin check point na sojoji, in da dama nan su ka yada zango kusan na dundundin.
Umar ya fito dauke da daya daga cikin sau cikin da aka turowa Usman. Da kyar Usman ya yarda ya saka. Haka su ka fita ya na masa mitar ya takura masa, shi fa takalmin nan ya matsa masa. Asibitin hakurin da ya ke zuwa ya kai Usman, ga mamakin sa sai gashi dentist din da su ka gani ta ce Usman ba ya bukatar wanke hakori, hakoran sa are so perfect, sai dai Umar ne ke bukata. Ko da Umar ya koka sai Usman ya murmusa kana ya ce
"Kai ne fa Umar ka fadakar da ni cewa addinin mu shi ne wayewa, Manzo (SAW) ya ce ba dan kar ya takurawa al'umar sa ba da ya ce su dinga asuwaki kafin kowacce alwala. Ka ga ban san brush da wannan abun da ku ke shafawa kai ba, Amma na san aswaki da Manzo ya koyarda da mu, shi ya sa baki na ke da tsafta da haske"
Umar na gyada kai ya furta
"Hakkun ka yi gaskiya, Amma kuma wannan karan za ka kara da zamani, idan mu ka gama da asibitin nan za mu biya shopping mall mu siyo su brush da abin goge bakin ka ga sai ka kara wasai ko?"
Darawa Usman yayi, kafin ya kara magana Umar ya kara da
"Ka bari fa Usmanu, yanda ka zama gaye din nan sai fa mun yi da gaske, dan wallahi ba ka bina bashin rantsuwa matan da za su fara binka sai Allah, musammam ga ka da dukiya, fata na dai kada ka yi zaben tumun dare, na kuma san kai mai sani ne, ka ji tsoran Allah ka kuma roki Allah ya kare ka daga kaidin shedanun mata, ya kuma ba ka mace ta gari....."
"Amen summa amen"
Cewar Usman, cikin ran sa kuwa Zainab ya ke hangowa. Tunanin ko ta cigaba da rayuwar ta yanda ta ke a da ya ratsa zuciyar sa, be san sanda ya furta
"Innalillahi wainnailaihi rajiun! Allahumma ajirni fi masibati haza wakallifni khairan minha!"
A tsorace Umar ke kallan sa ya na tambayar lafiya? Me ya faru. Shi kuwa Usman bakin kishi ne da ya taso ma sa ya turnuke kirjin sa ya sanya shi salati. Amsawa Umar yayi da babu komai, kawai ya tuna wani abu ne. Yayi saurin barin wajen gudun kar Umar ya gane halin da ya ke ciki, dan kuwa sirri irin na Usman ya sa har yanzu be taba bawa Umar labarin Zainab ba.
*****
Sanda cikin Zainab ya cika wata tara chif, ya rage saura sati biyu EDD din ta ya cika Halitta ta dawo Nigeria. Ganin yanda Zainab ta bude ta zama katuwa zama da kyar ta shi da kyar Halitta ta sako ta a gaba da tsokana, duk dai ita ma din dauke ta ke da na ta yaron cikin wata uku cif.
Wata ranar lahadi da yamma likis, Zainab da Halitta sun dawo daga strolling, Halitta ke raka ta kusan kullum safe da yamma. Su ka tadda Anty Sauda zaune gaban Ammy ta hada kai da gwiwa ta na ta sharbar kuka. Hankalin su ba karamin tashi yayi ba dan kuwa a tunanin su ko General ne ya mutu. Muryar Halitta na rawa ta furta
"Anty Sauda lafiya? Ammy lafiya? Wani abu ya sami Genaral ne?"
"Ba gwara wani abu ya same shi ba da cin fuskar da ya min! Ni General zai ci Amana?"
Jin haka Zainab ta samu waje ta zauna cike da mamaki, shin dama akwai ranar da Anty Sauda za ta kuka da General? Mutumin da ta ke ikirarin ta gama da shi ko tsinke ta aje be isa ya tsallake ba sai da izinin ta. Zainab ba ta yi mutuwar zaune ba sai da ta ji Anty Sauda ta furta
"Wai Genaral ya rasa wacce zai auro min sai yar aiki! Da ilimi na! Da wayewa ta! Da arziki na amma ya auri yar aiki na? Wata jaka yar kauyen kayayau! Har ya na ikirarin matukar ba zan iya zama ba toh kofa bude ta ke!"
Jikin Halitta yayi sanyi kwarai, haka ma Falmat wacce shigowar ta kenan ita ma ta tsinci maganar. Ammy kuwa ta dade da kasa magana tsabagen al'ajabi. Zainab ce kadai ta furta
"Tooooh yar kauye fa Anty Sauda? Ki na nufin yar kauye dai kamar miji na Shehu?"
Ta yi maganar da manufa biyu wanda in aka dauki Anty Sauda babu wanda be fahimci in da Zainab ta dosa ba, Anty Sauda ta furta
"Irin su fa tsinannun tsintattun mage! Kuma ita ma din bafulatana ce waya sani ma ko Rugar su daya shi ne ya min shune tsinannun! Sai na yi maganin su! Wallahi bokan ta ya mata karya yanda na sha wahalar mallakar Malam sai ba ta isa ta zo da ruguje min ba! Yarinya ce fa kankanuwa! Ga ta bagidajiya! Kin san mazan nan daga na barta ta na masa girki saboda business ya dan fara hawa kai na, shi ne ta yi amfani da damar ta ta masa barbade...."
"Assha kin ga inda kuskuren na ki ya ke Anty Sauda, wayewa da ganin ke kin isa ya sanya ki ka bari wacce ki ke tunanin bagidajiya ce kuma yar kauye ta aure mutum mai daraja kamar General! Kenan akwai lokacin da wayewar ba ta amfani...!"
"Yakura!!!"
Ammy ta dakawa Zainab tsawa, in da Anty Sauda ta saki baki ta na duban ta. Zainab ta dubi Ammy ta furta
"Ammy kar ki hana ni magana! Ranar wanka ba a boye cibi! Ina ga nan Anty Sauda ta zauna ta gama kare min tatas! Har fadi ta ke ilimi na da jami'a ta be amfana min komai ba na rasa wanda zan so sai dan kauye! Da ke da na shiga jami'ar ko wayewar ita ce mizanin auna darajar dan adam ko azanci na dan adam! Ita ya aka yi ga shekarun, ga wayewar, ga arzikin ga ilimin amma ta yi sakaci irin wannan? Da wayewa, ilimin boko ko shiga jami'a shi ne mizani azancin dan Adam da wayyayu dayawa ba su halaka ba! Da yan kauye dayawa ba su cigaba ba! Wannan abun da ya faru da ke kukan kurciya ne Anty Sauda!"
Kuka Anty Sauda ta saka, fadi ta ke
"Ni Yakura? Ni ki ke gasawa maganganu haka? Na dade da sanin ba ki da kunya amma ban taba tunanin za ki iya shafawa idanun ki toka ki gasa min cin kashi haka ba!"
"Yakura ki bata hakuri! Ba ki kyauta ba!"
Cewar Ammy cikin tsawatarwa. Sai da ta yunkurin tashi da kyar, ta dubi Anty Sauda ta ce
"Allah ya ba ki hakuri tunda Ammy ta ce na baki hakuri, Amma sam ban yi dana sanin maganar da fada mi ki ba, rayuwa dai is a circle, na dade da gane haka ina kuma fatan ke ma za ki gane"
Ta wuce ciki ba tare da ta damu da kukan da Anty Sauda ta ke yi ba, bare fadan da Ammy ta bita da shi. Nan ta ke Anty Sauda ta ja jakar ta tace ta fasa zama gidan Ammy. Sai da su ka yi da gaske sannan ta hakura, ta ce amma Ammy ta mata tsakani da mara kunyar diyar ta. Ita kan ta Ammy mamakin yanda rayuwa ta juya ta ke, Halitta da Zainab wanda da ba sa ga maciji ne yau su ka zama tamkar aminan juna, Anty Sauda da Zainab wanda su ka saba kullawa su kunce babu wanda ya sani ne yau kuma ba sa ga maciji. Lalle kam rayuwa na da ban mamaki.
Tun kafin EDD din Zainab ya cika, ana sauran sati guda Zainab ta tashi da nakuda, wuni daya ta yi cur ta na yi sannan Allah ya sauke ta lafiya ta haifo dan ta namiji mai kama da Shehu sak tamkar yayi kaki ya tofar. Ita kan ta Zainab da aka daga mata shi sai da gaban ta ya fadi kasancewar shi jinjiri be sa ta kasa ganin Usman a fuskar sa da komai na sa ba.
Ko da aka miko sa hannun ta, ta na hawaye ta masa huduba ta saka masa suna Usman. Yanda ta ke yi ya sanya nurse din tambayar ta ko dai uban dan ya rasu ne? Zainab na duban Usman junior ta furta
"Eh ya rasu tun kafin na san ina dauke da cikin dan sa, Amma gashi Allah ya kara dawo min dashi, sai dai wannan karan jini na ne, tsatso na"
Cike da tausayawa nurse ta furta
"Allah sarki, Allah ya ji kan sa ya kuma raya dan sa"
Zainab ta amsa da "amen"
Babu wanda be yi murna da haihuwar Zainab ba, hatta Anty Sauda sai da ta aje fushin ta gefe da ta ga dan da Zainab ta haifa. yaro sak uban sa, kai ka ce balarabiya ta haifo sa. Jin Zainab ta saka sunan Usman ba Malam da kowa yayi zato ba sai da aka yi dan kananan maganganu. Zainab kuwa ta ce da dai ita ta haifo kayan ta, kuma Usman ta ga daman saka masa, za kuma ta kira shi Shehu, ta ga wanda ya ke da ikon canzawa dan ta suna.
Ranar suna aka sha shagali, Hajja Kilishi da na ta ayarin sun yiwa Ammy kara kwarai dan kuwa sai bayan suna da kwana biyu su ka tafi.
****
Bangaran Usman kuwa ya na can ya na hidamar kafa Rugar Shehu cikin saban gidan gonar da ya ke ginawa sam be san an masa takwara ba. Umar ya mayar da shi dan zamani, dake dama mutum ne mai ilimin addini gashi ya hada da zamananci nan da nan ya zama goge. Kullum cikin masa tayin aure ake, abokan sana'ar su ne, mata masu kawo kan su kai har ma daga bangaran Alhaji Ibrahim Balla, Amma kullum Usman cikin zillewa ya ke. Har Umar ya gaji ya fito ya tambayi Usman shin lafiyar sa kalau kuwa? Usman ya bashi amsa da kada ya damu, dake su na shirin zuwa Rugar Shehu domin taho da wasu daga cikin shanun Usman, ya ce ya bari idan su ka dawo zai masa bayanin komai. Da haka su ka dauki hanyar su na Rugar Shehu.
Amma ko da su ka isa Mambila, aka yiwa Umar bayanin tafiyar kasa da za su yi kafin su karasa Rugar Shehu nan yayi kememe ya ce ba shi iyawa. Usman dai ya je ya dawo shi zai yi tsimayin shi nan Mambila. Hakan ko aka yi, Usman shi kadai ya niki hanya har Rugar Shehu.
Ganin yanda Usman ya canza kasa gasgata zatan su na Shehun na su ne da gaske. Nan fa Usman ya zama abin kallo kamar yanda Zainab ta zama farkon zuwan ta Rugar Shehu, bambamcin dai shi wannan mamakin yanda Usman ya canza gaba daya ne ya rufe su. Kowa burin sa ya taba Usman. Shaddar da ke sanye jikin sa, hular kan sa kai hatta takalmin kafarsa abin kallo ne gare su. Cikin su har da masu fadin babu shakka cikin wannan injin kyera mutane da aka ce akwai a birni aka sanya Usman, ya zama dan birni tamkar kado.
Bayan komai ya lafa ya mu su bayanin abin da ya ke tafe da shi. Wato na mayar da Rugar Shehu cikin birni. Kamar yanda yayi hashashe, dayawa daga cikin su sun yiwa maganar mummunar fahimta, ciki har da Kawu Iliya. Amma ko da Usman ya tsaya ya mu su bayani mai gamsarwa sai su ka dan sauko, Amma duk da haka su ka ce bazai yiyu kowa yaye a bar daji ba. Duk sanda Usman ya gama shirin sa ya zo wasu daga cikin jama'ar Rugar su bishi, a fara ganin yanayin zaman da yanda zai kasance, idan har abu yayi kyau saura jama'a su bi bayan su, idan aka sami kishiyar haka kuma toh lalle wanda su ka bishi sai su dawo gida. Haka kuma shanu mallakan sa ne, ko da kuwa dubu zai kore zuwa birni ba zai talauta Rugar Shehu ba, dan haka babu mai tsayar da shi, adduar su dai kawai Allah ya idda nufi, ya kawo mu su alkhairi.
Kwanan Usman biyu kacal a Rugar Shehu, ana gobe zai koma Bello ya zo masa da sakon Raqeeba na ta na so ta gan shi. Usman ya ce toh bisimillah mana. Nan cikin bukkar shi ta zauna tare da mijin ta Bello. Usman na daga zaune can gefe yayinda zuciyar sa ta masa nauyi jin maganganun da ke fita daga bakin Raqeeba. Ta kwashe abin da ya faru tsakanin ta da Zainab, da kuma yanda ta tunzura ta har ta yarda ta hada baki da su Rahila ta fada mu su. Cike da nadama ta kare da
"Abu mai kaunar ka ce kwarai, sharrin shedan ya sa na aikata abin da na aikata amma sam babu laifin ta, laifin ta daya shi ne zafin kishi, dan sai a sannan ni kai na na gane Abu mai kaunar ka ce....."
Ganin Usman ya runtse idanu ya sanya Raqeeba kasa magana, cikin neman agaji ta ke kallan Bello wanda tun da ta gano ta kamu da san shi ta fada masa abin da ta aikata. Bello ya gyara muryar sannan ya furta
"Ta yi kuskure, tun da ta fada min na nuna mata bacin rai na....."
"Tun da ta fada ma ka? Ka na nufin ta ma fada ma ka amma ka kasa sheda min Muhamadu?"
Ya na kokarin kare kan sa ya furta
"Ah ah watan jiya ta sanar da ni, dama jira na ke...."
"Ya salam matar ka ta cutar da ni, ni Kuma na cutar da Abu! Har ka san wannan maganar amma ka kasa fada min? Watan jiya? Kasan kwana nawa na yi kullum da kewan Abu? Ka san dare nawa ya shude kullum da ita na ke mafarki? Kasan kwanaki nawa na yi kullum zuciya ta na kukan rashin ta? Haba Muhamadu Bello! Haba dan Allah!"
Cewar Usman yayinda ya tashi a firgice ya shiga hada kayan sa. Alama Bello ya yiwa Raqeeba da ta tashi ta tafi. Tsoran fushin Usman ya sanya ta kiran su Kawu Iliya. Su ka tadda Usman ya dau jaka har ya fito. Sun yi sunyi su bashi hakuri ya bari gari ya waye sai su tafi amma Usman yaki. Gani ya ke kowani sakan idan ya wuce ba tare da ya na hanyar Kano ba asara ne a gare shi. Dole suna ji suna gani su ka bar shi ya dau hanyar Mambila cikin daren.
Sai da gari ya waye tangararan rana ta hudo kai sannan ya isa Mambila. Nan ma abinci kawai ya ci sannan ya tasa Umar a gaba lalle su dau hanya Kano. Yanda dawo masa afujajan ya sanya Umar shiryawa su ka dau hanya ba tare da ya masa mu su ba. Tun da su ka dau hanya Usman ya je rama baccin da be yi daren jiya ba. Umar ya daga masa kasa har sai da su ka isa Jalingo, bayan sun yada zango hotel din da su ka saba sauka ya je har daki ya same shi.
Babban daki ne wanda ya kai matakin dakunan da alhazawa su ke kamawa. Bayan ya buga masa kofa ya bude masa, ya sake komawa ya yi zaman sa bakin gado, sanye da farar singileti da gajeran wando. Umar ya dube shi ya ce
"Na lura tun da ka dawo ba ka cikin hayyacin ka, me ke faruwa? Me za su yi Kano?"
"Abu zan dauko"
"Wacece Abu Kuma?"
Umar ya tambaya cikin nuna rashin fahimta. Nan Usman ya bashi wani bangare daga cikin rayuwar shi da Zainab ba tare da ya tona sirrin da ya shafi dakin auren sa ba. Kafadar shi Umar ya dafa sannan ya ce
"Sai yanzu na fahimci dalilin da ya sanya ka ki kula kowa. Lalle ni zan raka ka har Kano, Amma fa gaskiya ba za mu je haka yanda ka ke a burkice ba Malam! Sai ka nutsu ka kuma kwantar da hankalin ka!"
"Shin ka na ganin Zainab za ta yafe min?"
Umar na jinjina kai
"Matukar ta na san ka kamar yanda ka nuna min, za ta yafe ma ka Usman, dukkan ku kun yanke hukunci ne cikin rashin sani da gaggawa, duk ilimin ka, ita kuma duk wayewar ta be sa kun iya gujewa kaddarar ku ba, yanda za ka sani ajizanci ne na dan adam, shi dan adam ajizi ne Usman"
Kai Usman ya gyada kawai. Umar ya masa sallama, ya bar shi nan zaune ya na fargaban yanda zai tunkari Zainab bayan wata da watanni da tura ta gida.
Kamar yanda Umar ya ce, sai da ta tabbatar Usman ya nutsu sosai, sun kuma shirya zuwa gidan surukai da kyau sannan su ka dauki hanyar Kano, Usman ya so su bi jirgi, Amma Umar ya dage sai dai su tafi a mota. Daya daga cikin manyan motocin Alhaji Ibrahim Balla ya dauko dan har lokacin Usman be iya mota ba, bare ya mallaki ta kan sa, Umar kuwa ganin za su je gidan surukai da aka dade ba a hadu ba ya ga dacewar a je da babba harka yanda za su cika ido da kyau.
Da ya ke tun asuba su ka bar Yola, kuma Umar ya taka motar sosai, karfe hudu a Kano ta mu su. Kai tsaye Prince hotel su ka wuce in da su ka kama dakuna biyu. Dan zumudi jikin Usman har rawa ya ke. Umar na duban sa cikin zolaya ya ce
"Wallahi in ba ka dena wannan rawar jiki da zumudi ba babu in da za mu je yau sai gobe"
Fuska murtuke Usman ya furta
"Sai in ga me hana ni fita! Da ka san yanda na ke ji Umar da ka tausaya min"
Umar na murmushi ya ce
"Ni ma zolayar ka na ke, maza ka je ka shirya, ka tabbatar ka kure a daka yanda ko Abun ta ka baza ta gane ka ba, bare masu gadin nan da ka ba ni labarin su"
Cike da farin ciki Usman ya bi bayan wanda zai nuna masa dakin sa, ya na mai bawa Umar amsa da
"Yau kuwa zan ba ka mamaki Umari, dan ko kai kan ka ba za ka gane ni ba"
Haka su ka yi sallama su na wasa da dariya. Usman be bata lokaci ba nan da nan yayi wanka. Wata danyar farar getzner wacce aka mata aiki da shudin zare dinkin babbar riga ya sanya. Bayan ya feshe jikin sa da tuare mai tambarin 'Boadicea the Victorious', ya dau hularsa da aka saka da manyan zare kalar aikin babbar rigar sa sai dai kuma akwai wasu kalolin da su ka ratsa jiki, hular ta sha wanki da kari ya sanya. Daga agogon hannun sa har zuwa takalmin kafarsa kudi ne. Shi kan shi da ya kalli madubi, mudubi sai da ya kara dubawa. Lalle kam sutura ita ce mutum!
A restaurant ya sami Umar ya na cin abinci, ko daga shigan Usman ba sauran jama'ar da ke wajan ba, hatta Umar sakin baki yayi ya na duban sa har ya karasa teburin da ya ke.
"Butar shayi mutumin nan ka hadu! Wannan ado duk na zuwa biko ne?"
Cewar Umar cikin zolaya. Kujera ya ja ya zauna, kana ya ce
"Ka yiwa girman Allah ka min adalci ka bar wannan abincin mu tafi, wallahi da ka san halin da na ke ciki da ka tausaya min Umar"
Baki cike da shibkafa Umar ya ce
"Adalcin shi ne ka bari na cika timbi na Alhaji, da dai ace zuwan dadi ne da sai na sa ran za a ba mu na dare, Amma hakan nan siddin mu taso tun daga Yola har Kano ka hana cin abinci? Babu wannan maganar"
Cikin kosawa Usman ya furta
"Sai ka ta ci ai, idan ka gama ina jiran ka a mota"
Ya tashi ya fice in da matan da ke wajan su ka bishi da kallo. Shi kuwa gaba daya hankalin sa yayi gaba, in ba Zainab ya sa a Ido ba ba zai sami nutsuwa ba.
Sai da Umar ya take tumbin sa sannan ya fito su ka dauki hanya. Ko da su ka karasa gidan Malam su ka yi hon, Jauro ya ga motar da ke fake bakin kofa tuni ya bude mu su gate ba tare da ya damu da ya duba su waye cikin motar. Umar ne ya fara fitowa bayan sun yi fakin farfajiyar gidan, da sauri Jauro ya karasa gaban sa ya ba fadin
"Barka da zuwa Alhaji, sannu da zuwa Alhaji"
Ganin dogan mutum fari sol, ga kyau ga kwarjini ga kuma sutura, ya fito daga motar, Jauro be sanda ya zube kasa ba cikin fadanci, fadi ya ke
"Allah shi ja zamanin ka, barka da zuwa"
Shi kan sa abokin aikin Jauro bude baki yayi ya na kallan sa, dan kuwa tun bayan tafiyar musu ya can ji gurbin sa, be taba ganin Jauro ya rikice kamar yau ba. Shi kan sa Usman ya san tabbas Jauro be gane sa ba. Ya na shirin tambayar in da Zainab ta ke sai ga Anty Sauda ta fito. Ganin mota mai numfashi fake farfajiyar gidan da kuma mazan da su ke tafe cikin motar tuni ta karaso ta na tambayar
"Baki mu ka yi ne? Ko wajan Falmat ku ka zo ne?"
Har kasa su ka tsugunna su ka gaishe ta, Anty Sauda na fadin
"Ku tashi, ai ba sai kun tsugunna ba"
Umar ne ya ce da ita wajan Zainab su ka zo. Duk yanda ta so ta buye disappointment din jin Zainab aka zo nema sai da ya dan nuna a fuskar ta. Ta kan ta ta yi mu su jagora har cikin falon Dady, sai da ta tabbatar su zauna sannan ta wuce ciki ta shedawa Ammy halin da ake ciki, ta kare da
"Wallahi matasa ne daga kin gan su kin ga 'ya'yan manya, Amma na san rashin mutuncin Yakura yanzu sai ta watsa ma na kasa a Ido, na ga tun da ta haihu ta ke jin maganar ki da kyau, ko za ki lallba ta fita su gaisa?"
"Toh Yakura ce ai ba a mata abin arziki, bari na gwada sa'a ta, a ina ki ka ce ke?"
Cewar Ammy cikin fargaban abin da zai je ya dawo.
"Su na can falon Malam"
Ammy ta ce
"Toh bari na gwada"
AUREN SHEHU 2
Finale...
"Ammy I'm not expecting visitors, Dan Allah ki ce mu su ba zan gan su ba"
Cewar Zainab ta na kokarin gyara diaper din Shehu. Tun da Ammy ta fada mata ta yi baki, ta ce su shigo ciki mana, ta ce da ita ai maza ne, ta yi mirsisi ta ki tashi. Ammy na duban ta ta kara fadin
"Ki yiwa Allah da manzan shi ki tashi ki je ki ga su waye Yakura, barka fa su ka zo mi ki"
"Toh Ammy me zai sa baki maza su zo nema na saboda Allah da manzan sa, har ki na ce da ni Anty Sauda ta ce daga gani 'ya'yan manya ne, Ni ina ruwana da girman iyayen su! Ban san su ba, ban zuwa kuma"
Rai bace Ammy ta furta
"A matsayi na na mahaifiyar ki na baki umarnin ki tashi ki je ki ga ko suwaye! Ba kuma na san musu!"
Zainab na jin haka ta shuna baki. Ta mike Tsaye ta na gunguni. Doguwar rigar atamfa ce jikin ta, dake jikin jego ta kara cikowa ta koina ta murmure. Dankwalin atamfar ta daura irin wannan daurin da ake kira ture ka ga tsiya, ta ja mayafi ta yafa a kafada. Ganin ta na kokarin daukar Shehu Ammy ta furta
"Ki bar shi mana tun da bacci ya ke"
Ta na mai aza shi kafada ta ce
"Ah ah ai na zaci barka su ka zo yi, na je ma yan barka ba jinjiri?"
Ba ta tsaya ta saurari amsar Ammy ba ta yi waje fuu kamar wacce za ta tashi sama.
Usman kuwa tunda su ka zauna ya tsurawa kofa idanu duk da Umar ne zaune daidai kofar. Umar na kokarin masa hira amma ina hankalin sa ba ya jikin sa, yayi nisa baya jin kira.
Sallamar ta da shigan ta falon lokaci daya ne, idanun ta kan Umar ya fara sauka, in da shi kuma Usman ya shiga duban ta cikin rudani. Idan aka dauke yanayin tsiwar da ta shigo da shi, da Kuma tsayin ta komai na Zainab ya canza, dama tunda Zainab dirarriyar mace ce, Amma yanzu sai ta zama irin matan nan da aka fi sani da zaratan mata, kamar wacce makerin dare ya kyara. Baban abin da ya saka shi cikin rudani shi ne yanda ya ga alamun kumburi kafar ta, da kuma yanda alamun jego ya bayyana dukkanin gabobobin jikin ta, dadin dadawa ga jinjiri kwance kafadar ta.
Ba kunya ta gama karewa Umar kallo tas, ta tabbatar ko mai kama da shi ba ta sani ba, ta na kokarin kallan Usman ta karasa ciki, fadi ta ke
"Sannu da zuwa, gashi kuma ni ban san ku ba bare na san a dangin wa ku ka zo min........"
Cak ta tsaya ta na duban shi kamar yanda shi ma idanun sa ke cikin na ta. Idanun da har ta koma ga mahaliccin ta ba za ta taba mantawa ba. Baki ta bude da niyar magana, bayan sakanni ta sake rufewa, ji ta ke tamkar mafarki ta ke, sai kuwa ta lumshe idanun ta na dab wani dan sakanni, sannan ta sake budewa. Mai kama da Usman din nan dai be bace ba, sai ma tasowa da yayi ya nufo ta. Kallan sa ta ke tun daga sama har kasa, shigar da yayi ya sa ya kara kwarjini kai ka ce wani basarake ne ko kuma wayayyen dan kasuwa wanda ya ci ya tara. Ba ta dada gasgata abin da zuciyar ta ke fada mata ba, sai da ya tsaya gaban ta, ya kalle ta, sai ya kalli jinjirin da ke kafadar ta da lokacin be samu ya ga fuskar sa ba, cikin yanayi mai wuyar fasaltuwa ya furta
"Abu......"
Zainab ta runtse idanun ta dan tun daga kwakwalwar kan ta, har zuwa yatsun kafarta ta ji kiran.
"Abu......"
Ya sake kiranta ya na kokarin ruko ta, Zainab ta ja da baya da sauri ta na mai girgiza masa kai. Murya na rawa ya furta
"Na sani Abu, na san ban kyauta mi ki ba, ban mi ki adalci ba......."
Juyawa ta yi da sauri za ta fita, sai a sannan Usman ya ga fuskar takwarar shi, wanda ganin sa sai da ya zauna dirshen kasa.
Umar ne ya taso ya tsugunna gaban sa tare da taba kafadar sa. Usman ya dago da sauri ya dube shi, gaba daya ya manta da zaman shi a falon. A hankali ya furta
"Da na ne.....na zalinci Abu Umar"
"Ba da niya ka yi ba, za ta fahimce ka, za kuma ta yafe ma ka....."
Cewar Umar yana kokarin karfafa gwiwar Usman. Zainab kuwa da ta shiga ciki ta tarar da Ammy, Anty Sauda, da Hallitta zaune falo ko takan su ba ta bi ba, ta shige dakin ta yayinda hawaye ke gudana daga idanun ta. Kallan kallo su ka shiga yi, kowanne na tunanin ko lafiya? Kafin daga bisani Ammy da Halitta su ka bi bayan ta, Anty Sauda ta yi zaman ta cewar ta koma menene ita dai ta na daga nan.
Ammy da Halitta sun yi juyin duniyar nan akan Zainab ta fada mu su dalilin kukan ta, Amma ta ki, sai kai da gwiwa da ta hada ta na rera kuka mai sauti, in da Shehu da ke kwance kusa da ita ya ke taya ta da na shi kukan.
Ganin ba za su sami abin da su ke so kusa ba Halitta ba ta dau Shehu ta mikawa Ammy tare da fadin
"Ammy bari dai na bi sahun bakin da ku ka ce sun zo gun ta, babu mamaki sakon mutuwa su ka zo mata da shi"
"Eh gaskiya, maza bi bayan su, Allah ya sa dai ba su tafi ba"
Da saurin ta ta fita. Anty Sauda na tambayar ko lafiya? Ta ce mata ta na zuwa. Cikin falon Dady tadda su zaune in da Zainab ta bar su. Kallo daya ta yiwa Usman ta gane shi. Fuskar ta dauke da emotions iri daban daban ta furta
"Me ya sa Usman? Me ya sa sai yanzu ka zo? Me ya makarar da kai har haka? Kar ka fada min duk watannin nan ba ka farga da kuskuran da kuka tafka ba sai yanzu?"
Be taba tunanin wani daga cikin dangin Zainab za su iya ganin shi su kyale ba tare da sun masa wankin babban bargo ba, Amma duka tunanin na sa ya manta Malam na da diya kamar Halitta, wacce har abada ba za ta taba canzawa ba. Ya na mai duban ta cike da godiya ya ce
"Na yi kuskure mafi girma kanwa ta... Shin ko za ku iya yafe min?"
"Yafiyar mutum daya ce mafi muhummanci a gare ka, shin za ka zauna ne nan ka na dana sani, ko kuwa ka shirya gyara lamarin ka da iyalin ka?"
Cewar Halitta ta na mai duban Usman. Wanda ya tashi cikin azama ya na fadin
"A shirye na ke kanwata"
"Toh bisimillah"
Nan su ka bar Umar, Halitta na tafe Usman na biye da ita, a bakin kofar ya dakata Halitta ta shiga ta ce da Ammy ta dan shirya za ta shigo da bakon da ya zo.
Har ya shigo ya tsugunna gaban ta ba ta gane shi ba, be sa ta cikin rudani ba sai da ta ji ya bude baki ya ce
"Hajiya ban san da wani ido zan kalle ku ba, ban san da wani baki zan ba ku hakuri ba......"
"Waye wannan wai Halitta?"
Ammy ta katse shi cikin kin gasgata zuciyar ta. Ta na nuna shi da dan yatsa ta sake furta
"Kar dai wannan maci amanan maigadin nan da Malam ya dau diyar cikin sa ya basa amma karshe ya saka mana da sharri"
Jin haka Anty Sauda ta ware idonu zuciyar ta daya ta furta
"Haba ke kuwa Hajja Aleesha, duba ki gani fa da kyau! Ina ke ina hada wannan wayye kamulallen mutum mai daraja ta wannan tsinannen almajirin...."
"Haba Anty Sauda, kada ki manta wannan da ki ke magana akai shi ne mahaifin dan da Yakura ta haifa, in da kara ba kya zagi uban dan Yakura ba"
Jiki sanyaye Anty Sauda ta ke kara duban shi, wato lalle da gaske shi ne mijin Yakura? Toh dama karya ake da aka ce shi maigadin gidan Malam ne, ko dai dama bad da kama yayi tun asali dan masu hali ne ya zo mu su a almajiri. Shi dai Usman ya sunkuyar da kai, zai iya jure duk hukuncin da za su dauka matukar ba za su hana shi iyalin sa.
Anty Sauda na sosa kyeya ta ce
"Uhum toh gaskiya dai ina ga dama tun farko akwai kuskure, ai ni da na san wannan aka aurawa Yakura da sam ban tada hankali na ba. Hajja Aleesha ai ina ga zai fi a bari ya shiga ya sami Yakuran can su sasan ta..."
"Sasan ta me?"
Ammy ta katse ta a fusace. Ba ta gushe ba ta kara da
"Babu wani abin sasantawa! Da tana so su sasan ta da ba ta shigo ciki ta na mana kuka kamar wacce aka aikowa sakon mutuwa ba! Ke kin san wacece Yakura! Ka sace min diya! Ka kai ta dokar daji! Ka katse mata karatun ta! Sai da ka tabbatar ka bata mata rayuwa sannan ka sako ta mota tsabagen zalinci! Tun da ta dawo ba mu kara gane kan ta ba, ta zame mana tamkar bakuwa, a haka ta yi renon ciki, sai da ta haihu za ka wani kwaso jiki cikin manyan kaya ka zo gare mu? Ka ga mun ma ka kama da matsiya ta? Ko kana tunanin za ka yaudare mu da wayewa ne....?"
Hawaye ke fita daga idanun Usman, cike da nadama ya furta
"Wallahilazim ba haka ba ne Hajiya, ba wannan ba ne munufa ta, na yi kuskure kuma na yi nadama, ku yafe min. A shirye na ke na dau duk wani hukuncin da za ki yanke, Amma kar ku raba ni da Zainab, wallahi ba zan iya rayuwa babu ita ba"
"Toh tantabara! Ai watannin da ka korota ba rayuwa ka ke ba ko? Gawa ne kai duk wannan lokacin hala? Tashi ka fitar min daga gida! Tashi ka fita!"
Cewar Ammy cikin daurewar Fuska. Nan su Halitta ta su ka shiga ba ta baki. Amma Ammy ta juya mu su baya. Haka kuma duk magiyar duniyar nan yayiwa Ammy da ta bari ya gana da Zainab ba, ya kuma dauki Shehu, Amma ina Ammy ta riga ta hau sama. Haka ya karaci hawayen sa ya fito ya tadda Umar jikin mota ya na jiran sa. Yanayin da ya ga Usman ya sa ko tambayar halin da ake ciki be yi ba, kawai mota su ka shiga in da Umar ya tada ya juya kan motar. Bakin gate Jauro ya cigaba da mu su fadanci har sai da Umar ya fito da kudi ya danka masa. Ya na godiya ya daga mu su hannu har su ka fice. Bayan tafiyar su abokin Jauro ke tambayar na shi kason, Jauro ya hana, cewa ya ke
"Kai me ya hana ka zuwa ka karbi na ka? Ka na ganin mota mai numfashi, da kuma irin manyan da ke jan motar amma ka yi fuska! Toh wallahi raban da na ga mota irin wannan ta shigo gidan nan tun Malam na da rai!"
"Yanzu dai ba za ka bani ko sisi ba?"
"Ko asi ban ba ka"
Cewar Jauro yayinda ya wuce abin sa ya na lissafa adadin dadin da zai ci da kudin sa.
*****
Har su ka kai hotel din su babu wanda ya tanka. Bayan sun yi fakin ne za su rabu Umar ya dube shi ya ce
"Kar ka damu Usman, komai zai daidaitu"
Murmushi Usman ya masa, sannan ya wuce ciki ba tare da ya iya ce masa komai ba. Umar ne ya masa order abinci ya sa aka kai masa har daki. Ganin yunwa na neman halaka sa ya sa ya dan caccaki abincin, Amma sam ya kasa sukuni bere ya runtsa, sai juyi ya ke akan gado. Ko da ya duba agogo ya ga sha biyu sai ya ta shi wuf, jallabiya ya sanya saman singiletin jikin sa, dakin Umar ya nufa kai tsaye.
Zainab kuwa tun tafiyar Usman ta shiga wani hali, zuwan shi ya fama mata ciwan da ta ke tunanin da ya fara warkewa. Ammy ce ta yi ta bata baki, ta kuma mata alkawarin kar da ta damu in dai Usman ne ba zai kara saka kafa gidan ba, ta masa korar kare. Maimakon ta ji sanyi cikin ran ta kamar yanda Ammy ke zato, sai ma dada saka ta cikin hali mai wuya ta yi.
Kwance ta ke bisa gadon ta, ta tsurawa Shehu ido amma a zahiri tunanin Baban sa ne ya addabi zuciyar ta. Tambayoyi kala kala ke yawo cikin kan ta, Shin me ya same shi har ya canza haka? Ya aka yi ya iya shiga irin na wayayyu haka? Me ya kawo sa wajan ta? Shin ya zo ya tafi da ita ko kuwa dai ya ji labarin ta haihu shi ne ya zo ya raba ta dan ta?
Tsigar jikin ta ne ya tashi yayinda ta ji makogaran ta ya bushe. Ta tashi ta yi, ta na neman ruwan da ta saba ajewa a dakin ta rasa, dole sai fita ta yi ta nufi kitchen neman ruwan sha.
Tun fitowar ta daga dakin ya lura da ita, yanayin duhun falon be sa ya kasa gane Zainab ba. Ta gaban shi ta gifta amma sam ba ta lura da shi har ta isa kitchen din. Hakan ya bashi damar shigewa dakin da ta fito daga cikin.
Ganin an bar kofar kitchen din wangale ba sakata bare a sa mukulli ya sanya ta jan tsaki. Ta yi saurin karasawa ta ja kofar ta rufe. Sai sannan tsoro ya kamata, ta yi saurin daukar ruwan gora ta shige ciki kamar wacce za ta arta a na kare.
Jin tahowar ta yayi sauri aje Shehu, ya koma bayan kofa ya tsaya. Ko da ta karaso ta ga kofar da ta rufe da hannun ta shi ma wangale, da gudu ta karasa ciki wajan Shehu, daukar shi ta yi ta na mai duba lafiyar sa, ta ga dai lafiya lau ya ke, sannan hankalin ta ya dan kwanta, babu mamaki tsabagen tunanin da ta ke yi ne ya sa ta yi zaton da ta fita ta rufe kofar. Kara aje Shehu ta yi, hannun ta dauke da ruwan da ta dauko ta karasa kofar dakin ta ja ta rufe. Nan su ka hada idanu, ta bude baki za ta saka masa ihu yayi saurin janyo ta jikin sa tare da hade bakin shi da na ta ya fara kissing din ta. Tun ta na kokarin kwacewa har jikin ta yayi sanyi ta yi lamo ta na ganin ikon Allah, kafin daga bisani ita ma din ta fara mayar masa da martani.
Kukan Shehu ne ya dawo da su daga cikin hayyacin su, Usman yayi baya da sauri yayinda ita kuma ta karasa wajan sa, cikin ran ta tana godewa Allah da ya kwace ta daga hannun Usman. Usman jingine jikin bango, cike da so da kauna ya ke duban ta yayinda ta dauki dan sa cikin tattali da rarrashi. Ba ta damu da ya na wajan ba ta sanya masa abin da ya ke bukata a baki, Shehu yayi saurin cafkewa ya shiga zuka dama abin da ya ke jira kenan. Yanda ya ga ta dan runtse idanu alamar ta ji zafi ya sanya shi motsawa kusa da ita da sauri ya na fadin
"Sannu Abu, da zafi ko?"
Sai a sannan ta tuna ashe fa ba mijin ta ba ne, ta yi saurin jan mayafi ta rufe kirjin ta, Manyan idanun ta ta watsa masa cike da harara ta furta
"Malam me ya kawo ka gidan nan tsakar dare haka? Yaushe ka fara haura katanga? Me ya kawo ka daki na?"
Daf da ita ya zauna hakan ya sa ta dada muskutawa domin ba da tazara a tsakanin su. Hakan ya kara sa Usman dada matsawa kusa da ita, ita ma din ta kara matsawa, haka su ka ta yi har ya kure ta jikin bango.
"Wai menene! Zan ma ka ihu wallahi!"
"Toh in kin min ihu an zo an gan ni dakin mata ta sai menene?!"
"Wacece matar ta ka? Idan ma kana shirin dawowa da ni wallahi gwara ma ka fidda rai! Ka riga ka sake ni, I don't care daya ne ko uku, babu ni babu kai"
"Saki kuma? Ni Usmanu na sake ki? Toh abin na ki kuma ya koma sharri ne Abu?"
Takaici ne ya sa ta kasa magana. Ganin ba ta da niyar tanka masa ya sake furta
"Yanzu dai menene shedar sakin da na mi ki fisabilillahi?"
Tashi ta yi a fusace har nono na fita daga bakin Shehu, ya dan saka kuka amma ko ta kan sa ba ta bi ba sai da ta dauko takardar da ya bata, ta aje masa, ya fi takardar da idanu. Cike da tsiwa ta kara da
"idan ka gama dubawa za ka iya fitar min daga daki!"
Takarda ya dauka ya buda, ganin abun da ke ciki ya sa shi dariya, tabbas zatan shi ya tabbata. Ganin yanda ya ke dariya ya sanya ran Zainab kara baci. Musammam da ta ji ya furta
"Shin ko sau daya kin bude takardar nan kuwa Abu, ko kuwa dai tsabagen ba a iya karanta ajami ba ne?"
Ba ta so ya san ba ta taba budewa ba saboda kar ya gane tsabagen tsoran yawan sakin da ya mata ya sa. Dan haka ta ba shi amsa da
"Na karanta mana da ban karanta ba ta ina zan san sakin da ka min?"
Ta karasa maganar tana mai dora Shehu bisa kafadar ta, domin ta samu yayi gyatsa. Idanun shi na mata dariya ya bude ta takardar ya ce
"Toh kuwa Abu sai dai wata takarda ki ka karanta ba wannan ba, dubi wannan da kyau ki gani, ban sani ba ko kin san yanayin rubutun Malam, Allah ya jikan sa da rahama, wannan rubutun shi ne duk da dai jinya ta sa be fita sosai ba"
Hannu na rawa Zainab ta karbi ta kardar, ko shakka babu rubutun ya fi kama da na dan koyo, kalma biyu ne kacal jiki, sai da ta nutsu da kyau ta gane menene ciki
"Zainab...... Amana...."
Fuskar ta cike da hawaye ta dago ta na duban sa. Usman be gushe ba ya furta
"Wannan shi ne nasiha ta karshe da Malam ya bar min, Malam be manta lamarin ki ba duk da ya na gabar mutuwa, Ni kuma na masa alkawarin ni da ke mutu ka raba Zainab, ba zan taba sakin ki ba duk runtsi duk wuya. Na san ban rukewa Malam amana yanda ya kamata ba, Amma wallahilazim duk nema na, da kokarin ganin ni ma na zama wayeyye dan zamani ina yi ne ba dan kowa ba sai dan ke, a tunanina ba ki kauna ta, shi ne dalilin ki na hada baki da makiya na dan a kashe ni, kuma na san babban dalilin da ya sa ba ki kauna na ta saboda ni bakauye ne bagidaje....."
Ta yi saurin katse shi ta hanyar dora yatsun ta bisa leban sa. Hannu ya sa ya kama yatsun na ta, ya yi kissing. Sannan ya tashi tsaye ya karbi Shehu daga hannun ta, babu mu su ta sakar ma sa shi ya kwantar da shi gefe sannan ya dada jawo ta jikin sa, ya yayinda ya zauna bakin gado ya dora ta bisa cinyar sa. Ya na mai goge hawayen da ke gangarowa daga idanun ta ya ce
"Na sani Abu, na san ki na so na, Rakeeba ta fada min ki na so na, ki na Kauna ta tun sanda na ke bagidaje na, shi ya sa ma na kasa jira na gama wayewar gaba daya, na falfalo da gudu domin neman yafiyar ki, ashe ina can an haifa min Shehu ....tsaya sunan wa ma ya ci be?"
Cike da kunya Zainab ta cusa kanta cikin wuyar sa. Usman na mai runtse idanu ya furta
"Idan ki ka cigaba da kalallame ni haka Abu zan fa baki kanin shehu a daren yau...!"
Jin haka ta yi saurin zame jikin ta daga na shi, yanda ya sa dariya ya fitar da sauti ne ta gane zolayar ta ya ke, ita ma din dariyar ta saka. Har sai da dariyar ta koma ta farin cikin yau gasu dai tare cikin so da kauna. Su ka yi mai isar su sannan Zainab ta furta
"Usman"
"Ummm"
Usman ya amsa ya na mai dada hanyo ta jikin sa.
"Ba kai ba, jinjiri na sunan shi Shehu Usman...."
Dago ta yayi ya na kallan ta, kallo mai narka zuciyar wanda ake yiwa. Idanun sa na shekin kwalla ya furta
"Duk bakin cikin da na sa ki ciki, ki na tunanin na sake ki amma ki ka sanyawa dan mu sunana Abu?"
Zainab ta gyada kai alamar eh. Ga mamakin ta sai gashi ya tada ita tsaye. Kana shi kuma ya durkusa har kasa, hakan ya sa ta yi yunkurin tada shi, Amma ya ki, cewa yayi
"Dan Allah Zainab ki yafe min, Dan Allah ba dan hali na ba ki yafe min, matukar ba ki yafe min ba toh wallahi ko dada sace ki zan yi sai dai na yi, Amma ba zan iya rayuwa babu ke ba Zainab"
Dadi kamar zai kashe ta, ta ma rasa abin cewa kawai sai rungume shi ta yi, hakan yayi daidai da shigowar Anty Sauda, Halitta, Ammy. Usman yayi saurin sakin ta cike da kunya. Ammy kuwa juyawa ta yi da sauri ta na fadin
"Kai yaran zamani! Wallahi Halitta kin cuce ni!"
Anty Sauda ma sim sim ta bi bayan ta, ya rage sai Halittt wacce bakin ta ke kunshe da dariyar mugunta, hakan ne ya sa Zainab fahimtar abin da ke faruwa, cikin tuhuma ta ce
"Halitta ke ce ko?"
"Ah ah fa, na dan ji hayaniya a dakin nan, tsoro ya kama ni dan kuwa na san ke da baby Shehu kun yi kadan ku yi making all those noises, shi ne fa na taso su su zo su ga ko lafiya.."
Ta karasa maganar ta na mai kashe mata ido daya.
"Kai yarinyar nan ba ki da mutunci wallahi!"
Cewar Zainab ta na mai jifan Halitta da filo, Halitta ta yi saurin kaucewa. Ta na duban Usman wanda tun shigowar su kunya ya sa ya kasa sukuni, ta ce
"Malam Usman bayan abin da ya faru yau zai fi kyau ka wuce da matar ka gobe, dan ko ban ji akwai wanda zai so ya kara hana ka..."
"Halitta!"
Zainab ta daka mata tsawa, in da Halitta ta yi saurin ficewa ta na mai rufo musu kofa. Ta na fita Zainab ta ce oya Usman ya zo shi ma ya kama hanya. Ta yaya ma ya shigo gidan? Ya bata amsa da
"sabon maigadin ku za ku sake kawai, duba ta biyar na bashi ya bude min kofa, abokina Umar na can ta bayan gida ya na jira na, ba zan tafi ba sai kin min alkawarin za ki bi ni mu koma Yola"
"Yola kuma? Rugar Shehu fa?"
"Rugar Shehu na ke so na mayar cikin garin Yola, irin wannan tsarin da Shugaban kasa ya ke da burin yi, labari ne mai tsayi, ki min alkawarin za ki bini tukun"
"Zan bi ka duk in da sa kafa Usman"
Cikin jin dadi ya janyo ta jikin sa, ya sumbace ta a goshi. Sannan ya sumbaci Shehu a kumatu tare da masa addua. Sannan ya fita suna kewan juna.
***
Epilogue
Sassanyar iskar damina da ke kadawa bai hana ta tsayuwa baranda in da ta saba tsayuwa duk yamma bayan ta kammala duk wani hidimar gaban ta. Ba komai ke sata tsayuwa wajan ba illa ta karewa estate din da mijin ta ya gina da sunan Rugar Shehu kallo ba, ba ta taba manta shekaru goma da su ka wuce, daren da Usman ya lallabo dakin ta bayan Ammy ta hana shi ganin ta ba. Ta na murmushi yayinda ta dora hannun ta bisa katan cikin ta haihuwa ko yau ko gobe ta ke tuna yanda Ammy ta sauko daga dokin fushin da ta hau bayan ganin su da ta yi rungume da juna. Ko da Usman ya koma washagari kin yarda su gaisa ta yi, ta dai ce ba ta yarda Zainab ta bi shi ita kadai ba, sai dai ya jira su yi arba'in, sannan su Anty Sauda su bi shi su ga muhallin da zai aje mata diya, haka kuma su gana da wasu daga cikin dangin sa. Kafin wa'adin Ammy ya cika Usman ya sha zarya tsakanin Kano da Yola. Daya daga cikin ziyarar ta shi ne ya bata labarin estate din da ya ke ginawa tare da Taimakon Umar da mahaifin sa. Da kuma tarin hannun jarin da su ke bukata domin tada Rugar ta zama wajan neman kudi da juya shi. Anty Sauda kuwa lallabawa ta yi to koma gidan General da kafar ta bayan ta ga muhallin Usman da irin tarin dukiyar da ya mallaka duk raina shi da ta yi, ta yi tawassali ga Allah ta gane mutum ba abin rainawa ba ne. Shi kuwa Jauro tunda bayan da ya gane Usman shi ma ya saduda, kullum cikin bin Usman ya ke da bukatun sa kai har ya kai ya na bin shi har Yola, da ke Usman mutum ne be gaza taimaka masa ba, har aiki ya bashi cikin estate din Rugar Shehu.
Sanda Usman ke mata jawab akan yanda su ke tsara Rugar Shehu, gani ta ke tamkar abu mawuyaci, Amma da yardar Allah cikin shekara goma Usman ya taka matsayi mafi girma wajan samin cigaba. Duk da su Kawu Iliya sun ki yarda su koma saban estate din kamar Yanda Usman ya bukata, sun ba da matasa da dama wanda su ne ke kula shanu wajan kiwo, haka kuma cikin su akwai manoma wanda ke noma a filin da aka ware na musammam.
Fili aka ware sosai in da ake kada shanun su yi shawagi da kiwo, wanda bayan an kada su turken su nan ake diban taki domin noma da kuma siyarwa gomnati a matsayin takin zamani. Bayan haka akwai wajan kiwan tsuntsaye kamar kaji, zabi, agwagwi, da dai sauran su. Haka zalika sauran kananan dabbobi ma ba a bar su baya ba. Hakan ya sa Umar ya samarwa Usman investors aka gina asibitin dabbobi cikin estate din, su na raba ribar 50-50 bayan sun samarwa dinbun jama'a job opportunities wanda ya hada da masu aiki a factory din sarrafa madarar shanu zuwa yogurt da fresh milk. Rugar Shehu ya zama daya daga cikin factory ma su samar da yogurt mafi inganci. Zainab ke koyar da matan matasan da aka taho da su daga Rugar Shehu, don gaba daya an hana su tatsar nono bare ma su kai da fita tallar fura da nono. Haka kuma Shehu ya gina yar karamar primary cikin Rugar, ya dauko malamai gwanaye ya na biyan su domin koyar da yara, ingancin makarantar ya sanya hatta jama'ar waje su ka fara kawo yaran su suna sa su cikin makarantar, hakan ya sanya Usman da Umar tunanin bude bangaran secondary da zarar sun yaye daliban primary na farko. Usman ya zama abin alfahari har a wajan gwamnatin jihar Yola saboda gudunmawar da ya ke bayarwa kwarai ta bangare daban daban wanda ya hada da killace jama'ar sa, sun dena yawan kiwo bare su shiga gonar wani, bare a zo ana tashin hankali. Rugar sa ta samarwa matasa dayawa aiki. Asibitin dabbobi da ya bude ya zama daya daga cikin ingantaccun asibiti cikin garin yola. Haka kuma ya yiwa Yola attracting foreign investors dayawa, ba larabawan ba ba turawa ba, wanda a da Umar ke bin su da yin ko za su za sa hannun jarin su cikin Rugar Shehu, yanzu su ne ke kawo kan su da bukatar yin haka. Haka kuma bangaran Malamtaka ba bar Usman baya ba, ya zama hamshakin malami kuma fitacce wanda ke da dunbin masoya cikin garin Yola da sauran garurruwar arewa.
Tsayuwar daya daga cikin motocin Usman kirar Range Rover ne ya ja hankalin Zainab. Usman ya fito sanye da manyan kaya, shudin shadda dinkin jamfa, hular sa a hannun gashin kan sa ya kwanta lublub tamkar hula. Shehu ne ya diro daga dayan bangaran, ta na ji Baban sa na masa fadan be hana shi dirowa daga mota kamar dan biri ba! Yayinda ya ke kokarin taimakawa kanan Shehu, Hassan da Husain su ma su ka fito daga motar.
In da Shehu ke da shekara goma a duniya, wata uku ya rage Hassan da Hussain su cika shekara shida a duniya. Hannun Usman rike da na yan biyu in da Shehu ya ruga a guje ya na fadin sai na riga ku zuwa gurin Mama. Su ka nufo ciki. Zainab na murmushi ta juya zuwa falo domin tarar su. Ta shiga falon Shehu ya karaso da gudu ya rungume ta, hakan ya sa Usman da shigowar sa kenan daka masa tsayawa fadi ya ke
"Ka sake ka kayar min da mata sai na lallasa ka Shehu!"
Hakan ya sa Shehu matsawa gefe da sauri. Dariya Zainab ta sa, kana ta ce
"Ayya mana Malam ina laifin shi dan ya rungume Maman sa?"
"Ba haka ake yi ba ai, a hankali zai rungume Maman ta shi kamar haka"
Cewar Usman ya na mai rungumo Zainab, duka yaran su su ke kallo. Usman ya ce
"Maza ku ma ku matso ku mata yanda na mata amma fa a hankali kar a buge gimbiya ta ta ciki"
Kamar dama jira su ke, da saurin su suka taho in da dukkan su uku su ka rungume kafafun Zainab cike da so da kauna.
Alhamdulillah.
Post a Comment for "Auren Shehu Book 2 Complete Hausa Novel"