Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Auren Shehu Book 1 Complete Hausa Novel

FIKRA WRITER'S ASSOCIATION Auren Shehu Complete Hausa Novel ✍ Khadija Sidi Kwance ya ke a rigingine kan ciyayi irin wannan ciyayin da ake kira "carpet grass" Hannayen sa biyu tallabe da ƙoƙon kansa, cikin nazari yake duban taurarin da ke jere reras suna sheƙi bisa sararin samaniya. Babban lambu ne mai ɗauke da ɓangare biyu, ɓangaren bishiyoyin 'ya'yan itatuwa, bishiyar mangoro, gwaiba, yazawa (cashew) da dai sauran su, sai kuma ɓangaren da ke ɗauke da kujerun hutawa. In ka ɗauke kukan tsuntsaya babu sautin da ake ji kasancewar dare ya fara tsalawa, kusan ƙarfe biyu ne. Sanye yake cikin rigar saƙa irin na fulani, kan sa ɗauke da rawanin da ya zaga har kewayen fuskar sa hakan ya sa fiye da rabin fuskar shi ɓuya. Kasancewar shi na daya daga cikin masu gadin daddare na gidan, kusan kullum ya kan kai biyu a nan cikin lambun, yayi kwanciyar sa ya na mai nazari, hakan ba ƙaramin nishaɗi ya ke saka shi ba. Gefan sa ƙatuwar sanda ce wacce ake kira da gora, ta korar shanun sa ce duk da kuwa rabon shi da rugar su wacce ake kira "Rugar Shehu" ya kusa shekara. Jin dirar mutum tare da haushin karnukan gidan lokaci ɗaya ya sanya shi yin zumbur ya tashi zauna ya na mai duban in da ya ke kyautata zaton mutum ne ya diro cikin gida. Jin shiru babu wani motsi sai na haushin karnuka ya sanya ya tashi tare da jan sandar gorar shi kai tsaye bakin bishiyar da ke kusa da katangar lambun ya nufa, idan ya ke kyautata zaton koma menene ya diro nan ne hanyar shi. Tun dirowar ta take ƙoƙarin janye niƙabin ta da ya maƙale jikin reshen bishiyar da ya mata tsani. Ƙoƙari ta ke iya ƙarfinta don ta ga ta ciro amma ina, gashi ta san mutukar ba ta samu ta shige ciki ba lalle masu gadi za su kama ta yau, don kuwa haushin karnukan yau ya fi na kullum. Jin ta ku a bayan ta ya sanya ta juyawa da sauri, ganin ya ɗaga sanda ya na shirin runtsuma ma ta aka, ta runtse idanu ta na mai faɗin "Wayyo ni Dady!!!!!" Cak ya tsaya, hannun shi na rawa tsabar firgici na ganin kyawun halittar Allah, tabbas kyau dai babu irin wanda bai gani ba a Rugar su, amma sam bai taɓa ganin wacce ta firgita shi ba kamar wannan halittar da ke gaban sa. Fuskar ta ya bi da kallo, wanda rashin niƙab ya ba shi wannan damar, domin kuwa jikin ta rufe ya ke da hijabi tun daga sama har ƙasa. Kamar yanda ya ke nazartar taurari haka ya tsinci kan sa cikin nishaɗi yayin da ya shiga nazari akan fuskar ta. Baka ce, irin wannan bakin mai shek'i kamar jikin tarwaɗa. Tsayuwar hancin ta da ya zo dab da ƙaramin bakin ta ba ƙaramin ƙarawa doguwar fuskar ta kyau yayi ba...... Jin shiru ba ta ji saukar gora kan ta ba ya sanya ya ta buɗe manyan idanun ta, hakan ba ƙaramin sake rikita shi ta yi ba ganin fararen idanun ta bisa kan shi har sai da ya ɗan ja da baya ya na mai tasbihi ga ubangijin sa, domin ya tabbatar wannan halittar da ke gaban shi ba mutum ba ce. Ta na mai duban shi cike da tsoro musammam ganin mutum mai faɗi da tsayin da tun da ta zo duniya ba ta taɓa ganin irin shi ba, daɗin daɗawa gashi yanayin shigar shiri irin na waɗannan mutanen da suka saka Nijeriya a gaba ko kuma Fulani masu garkuwa da mutane, wannan tunanin tare da jin taku da haushin karnukan da ya ƙaru, wanda hakan ya tabbatar ma ta masu gadin sun kusa shigowa lambun ya sa ta sakin niƙab din ta na mai ɗage hijabin ta yanda za ta sami damar sauri, ta yi amfani da damar gushewar tunanin mutumin da yayi kasake ya na duban ta, ta bi hanyar da zai sada ta da kitchen da sauri, hannu na rawa ta ke ƙoƙarin fidda ɗan mukulli da ta ɓoye cikin dan wando da ke sanye jikin ta. Har tuntuɓe ta ke garin waige domin tabbatarwa ba ya biye da ita. Allah ya taimake ta ƙofar ya buɗu, kasancewar ta sababbiya a harkar, cikin sanɗa da lalube ta ke tafiya domin wutan lantarkin kitchen din a kashe ya ke, sai dai hasken farin wata da yake ratsowa ta taga. Ba ta tsorata ba sai da ta jiyo muryar masu gadi daga cikin garden, ta na mai roƙon Allah ya sa ba asirin ta ba ne ke shirin tonuwa ba, ta bi ta falo ta shige ɗakin ta cikin rawar jiki. Dan tun da take fitar dare ba ta taɓa shiga tsaka mai wuya kamar na yau ba. Hijabin jikin ta ta cire, ta na mai ajiyar zuciya ta zube bisa gadon ta. Hasken da ya gauraye ɗakin sanadiyyar wutan lantarkin da aka kunna ya sanya ta yi zumbur ta tashi zaune a tsoro ce. Ganin wacce ke jingine jikin bango ya sanya ta fiddo ido tare da faɗin "Wai ke Halitta ba za ki fita harka ta ba? Wannan masifar har ina haka?" A hankali Halitta ke ƙare ma ta kallo, tun daga dan ƙaramin matsattsan wandan da ke jikin ta (bumshort) zuwa matsatsiyar jar riga wacce ta tsaya ma ta iya cibiya, ga kan nan ya sha kitson attachment da aka yi da gashin doki mai tsada da ake kira (Brazilian hair). Ta na mai girgiza kai ta furta "Yakura......." "please Halitta, ba yanzu ba, na gaji da yawa!!" Ta katse ta tana ɗaga mata hannu. Ganin an murɗa ƙofar ɗakin ya sanya ta saurin janyo bargo domin ɓoye shigar da ke jikin ta. Mahaifiyar su wacce su ke kira Ammy ce ta shigo, ta na hamma tsabagen baccin da ke idanun ta, ta ke duban su cike da damuwa ta ce " dama na san dole kuma kun tashi, hayaniyar su Audu da haushin karnuku ne ya tada ku ko?" "eh wallahi Ammy....." Su ka faɗa a tare wanda hakan ya sanya Halitta sakin baki cike da mamaki ta ke kallan yayar ta ta, ita kuwa ko aji kin ta ta ce "na kasa gane menene matsalar su da za su na sakar mana karnuka su na mana hayaniya, ya kamata a hana su shiga garden ma kawai...." "ke da ki ke ɗaki ya aka yi kika san garden su ke?" Halitta ta na sane ta jefa mata wannan tambayar, domin kuwa duk wani rashin ji da 'yar uwar ta ta ke yi babu wanda ba ta sani ba. Jin haka ta san in da ta dosa dan haka sai ta yi burus tare da faɗin "Ammy dan Allah daga ina hayaniyar nan ke tashi?" "eh toh ni ma na fi tunanin garden din ne, ai Malam shi ma ya fita ya mu su magana...." Ras! gaban ta ya faɗi "Allah ka rufa min asiri ba dan hali na ba ba dan aiki na ba" Adduar da ta shiga jerowa cikin ran ta kenan. Ita kuwa Halitta dariyar mugunta ta saki, sannan ta furta "Allah ya sa Dady ya gano dalilin wannan hayaniyar ta su ya mana magani, ni dai sai da safen ku" Ta na murmushin mugunta ta dubi yayar ta wacce ke watsa ma ta harara, ta ƙara da "a juri kai zuga gabas wata rana ya zo da ruwa, ko ya ki ka ce Yakura" "uhum" Cewar ta dan tsoro ta kasa magana, gani ta ke burin Halitta ta biye ma ta su yi hayaniya dan ta sami damar tona mata asiri. Halitta na fita Ammy ta bi bayan ta na faɗin "bari na bi bayan ki Halitta, babu mamaki Falmata na nan ɗakin ta tsoro ya hana ta motsawa" Suna fita ta fidda wayar ta da ya dame ta ta da ƙugi, ganin wanda ke kiran ta ta ja tsaki, ɗagawa ta yi tare da karawa bisa kunnan ta, cikin nuna fushi ta ke magana "Bobo wai menene? Na faɗa ma ka zuwa na club in dai na dawo hutu gidan nan abu ne mai hatsari, ka bari mu koma school ka ce ah ah, ga shi kai ba za ka iya bari mu dawo da asuba ba sobada jarabar bacci irin na ka, ai gashi yau saura kiris Dady ya kama ni!" Shiru ta yi na wani ɗan lokaci ta na sauraran shi, kafin daga bisani ta kashe wayar ba tare da ta sake tankawa ba. Nan ta kwanta ta na jiran tsammani, jin shiru babu wanda ya dawo ta san asirin ta bai tonu ba tukunna, dan haka ta tashi, kai tsaye toilet ta nufa ta yi wanka tare da ɗauro alwala domin rama salloli uku da ke kan ta, la'asar, magariba da isha'i. *** Allah yayi dare gari ya waye. Babban ɗaki ne irin na ƴaƴan manya, komai na ɗakin an yi masa ado da kala biyu, wato shuɗi da fari. Ba wani tarkace ba ne a ɗakin, face ƙatan gado na alfarma tare da setin madubi da dirowa. Kamar kullum yau ma sai da rana ta take, bayan ladanin masallacin da ke cikin gidan su ya ƙira sallar azahar sannan ta iya motsawa, wayar ta ta jawo, ta shiga Instagram in da ta saka hotan da ta yi daren jiya a club. Nan da nan hotan ya sami karbuwa in da samari da wasu yan mata su ka shiga danna mata "like" tare da "comments" kamar yanda aka saba. Sai da ta gamsu sannan ta aje wayar ta tashi da kyar ta yi wanka tare da ɗauro alwala. Maimakon da ta fito ta yi azama wajen rama sallolin da ake bin ta, wato Asuba da Azahar, sai ma tsayawa ta yi gaban madubi ɗaure da tawul da ya tsaya iya gwiwa, cikin jin daɗi da alfaharin baiwar dirin da Allah ya mata, da ke masha Allah ita kan ta ta san Allah ya mata mata dire. Hakan ya s koda yaushe ta na kan social media cikin saka hotunan ta wanda ta yi da matsattsun kaya, dan kuwa ta na cikin ɗaya daga cikin sannanun matan nan da ake kira "Slay Queen" a Instagram. Sai da ta ɓata lokaci wajen shafe shafe da kwalliya, ta fito fes cikin ɗinkin atamfa riga da siket, sannan ta ɗauko hijabi wanda ya ke kai mata har ƙasa ta sanya. Murmushi ta ke ganin yanda ta fito saliha sak, ita da kan ta ta shiga yiwa kan ta kirari "woo ni Zeee the slay mama, the club mama, kuma salihar Daddyn ta" Nan ta gama juye juye gaban madubi, sannan ta shimfiɗi sallalaya aka shiga jera sallar asuba da azahar. *** Malam Abubakar Birma sananne kuma hamshaƙin Malami ne wanda ya yi suna a Nijeriya, musamman Kano da Maiduguri. Babarbare ne ɗan asalin garin Maiduguri. Matan shi biyu, Hajja Kulu ita ce matar shi ta farko, wacce ta ke ƙabilar Barebari, ta na zaune ne gidan Malam da ke birnin Maiduguri. Yaran ta da shida, maza huɗu da mata biyu. Sai kuma Hajja Aleesha, wacce ta ke ƙabilar Shuwa Arab. Ita ce ke zaune Kano, ƴaƴa uku gare ta, kuma duka mata, sun haɗa da ɗiyar ta ta farko Zainab mai kimanin shekara ishirin da biyu, wacce ake kira Yakura, sai mai bi mata, Halitta mai shekara ishirin, sai auta Falmata, wacce ta ke da shekaru goma sha takwas a duniya. Cikin ƴa'yan Malam, Allah ya jarrabe shi da fitinanniyar ɗiya, wacce babu wanda zai ga ɗabi'un ta ya danganta ta da Malam. Ba kowa ba ce fyace ɗiyar Hajja Aleesha ta farko, wato Zainab. Club ne daga na cikin gida Nigeria kudu da Arewa har zuwa ƙasashen ƙetare babu wanda ba ta zaga ba, sai dai wanda ba ta sami dama ba, haka kuwa buɗe ido babu wanda Zainab ba ta yi ba kasancewar ta na yawan harka da gurɓattun yaran masu kuɗi, yawanci ta haɗu da su ne ta cuɗanyar makarantun boko da su ka yi tare. Social media kuwa ta yi ƙauran suna, mabiyan ta bila adadin haka, haka kuma masoyan ta da masu hure mata kunne domin kuwa abu biyu ne ya haɗar mata, ga kyau ga naira, babu shakka Allah ya bata duniya. Duk wannan hali da Zainab ke ciki Malam bai sani ba, shi a na shi ganin cikin ƴaƴan shi babu mai kamala da nutsuwa da ya kai ta, domin kuwa kullum a haka ta ke zuwa ma sa a nutse. Ga shi shi ba ma'abocin social media bane bare ya san wainar da ta ke toyawa, haka zalika shi ba mazauni ba, yau ya na Maiduguri, gobe ya na Misira, gata ya na saudiya. Sanda ya ke gari kuma ita kuma Zainab ta na makaranta, nan American University of Nigeria da ke yola, dama nan ta fi sheƙa ayar ta, dan idan ka ga irin rayuwar da ta ke yi ba za ka taɓa cewa ɗiyar Malam ba ce, ɗiyar Malam taƙi halin Malam. *** Jin a ranar Malam zai tafi Maiduguri ya sanya Zainab kafewa a lalle ita za ta kai ma sa kayan shayin da ya nema a kai ma sa falon shi na baki, saboda ta na so ta ga Malam akan buƙatar ta na sake wayar ta ƙirar Samsung da ko wata huɗu ba ta yi da siya ba, a cewar ta cemeran ba ta da kyau sam, ta na buƙutar latest IPhone da gaggawa. Da shigar nan na ta cikin hijab har ƙasa, ta tura ƙofar falon a hankali, zuciyar ta ɗaya da sallamar ta da Shigan ta falon lokaci guda ta yi, cak ta tsaya yayinda idanun ta su sauka kan fuskar nan da ke ɓuye cikin rawani, kamar yanda ta yi arba da shi jiya da daddare. Tuni gaban ta ya fara faɗuwa, babu shiri ta juya da niyar komawa, muryar Malam ne ya dakatar da ita, ya na mai faɗin "Yakura shigo mana, wannan da ki ke gani ɗalibai na ne, da kuma driver da masu gadi, kasancewar kullum kuna killece cikin gida shiyasa ba za ki gane su ba, muna tattaunawa ne akan zargin wasu ɓata garin da su ke yunƙurin hauro mana gida cikin dare......." Duk da mazan da ke zaune falon sun kai su goma, babu wanda ta ke iya gani sai wannan mai rawani, hankalin ta bai ƙara ta shi ba sai da ta ji kalaman da Malam ya furta, ba ta san sanda ta kara kai kallon ta ga mutumin ba, shi ma ɗin kallan ta ya ke ya na mai gasgata abun da zuciyar shi ke raya masa "wannan ita ce ɓingel din da na yi gamo jiya, ashe ba aljanah ba ce, to menene dangantakar ta da Malam? " Abin da ya yake rayawa cikin ransa kenan, kamar kuwa Malam ya sani, sai ji yayi ya furta "ɗiya ta ce, wannan ita ce Zainab, ɗiyar mai ɗaki na ta biyu, mahaddaciya kuma kamila a cikin ƴaƴana" Jin haka ya daɗa kallon ta, a hankali ya maimaita sunan "Zainab.." To idan dai lafazin Malam haka ne, to babu shakka ba ita ya gani ba. Hukuncin da ya yanke kenan yayinda ya sake ƙura mata ido domin neman bambamcin tsakanin wannan kamilar ɗiyar Malam da kuma waccar da ya gani a daren jiya. Aje tiren abincin ta yi gaban Malam, kai a sunkuye ta gaishe shi, ya na amsawa ta tashi da sauri ta fice daga falon dan kuwa ita kan ta tana jin idanun wannan bawan Allah a kan ta. Sai da ta kusa isa kitchen sannan ta dan tsaya ta nutsu gudun kar su Ammy da Halitta su gane halin da ta ke ciki. Katon kitchen ne wanda mutum goma za su iya aiki ciki ba tare da an takura ba. Ya tsaru sosai dan kuwa cike ya ke bam da duk wani kayan amfanin kitchen. hatta fridge biyu ne cikin kitchen din, na kayan miya da nama daban, sai kuma na ruwa da lemoku da kuma kayan marmari. Ta tarar da Halitta na jera lemo da ruwa cikin fridge, gefe kuma Ammy ce ta ke yiwa Iya mai aikin su bayanin abincin da ta ke so a dafa da rana. "Ammy anya kuwa cikin masu aikin gidan nan ko daliban Dady babu yan Boko Haram ko masu garkuwa da mutane?" Cewar ta yayinda ta dauki daya daga cikin ruwan da Halitta ke jerawa a fridge. "Auzubillallah!" Ammy da Iya su ka furta tare, ita kuwa Halitta tsayawa ta yi ta na duban yar uwar tata, da ko a jikin ta, kofi ta ja ta zuba ruwa ta jika makoshin ta. Sannan ta kara da "Ya ki ke kallo na haka kamar wata gaula? Wallahi I'm very serious about this one" Tsakanin ta da Allah ta ke bayani yayinda ta mayar da hankalin ta ga Ammy, ta ce "Ammy kin dai san yan boko haram din nan dai malamai su ke hari, ki tuna fa shugaban su Yusuf wanda aka kashe lokacin shugaban kasa yar aduwa an ce ya taba neman ilimi gun shiek Jafa'ar Allah ya ji kan rai, kin ga dole Dady yayi takatsantsan dan wallahi ina kyautata zatan wanda na gani gun Dady dan boko haram ne.....!" "Kul kar na sake ji!" Ammy ta katse ta, cikin tsawatarwa ta juya harshe zuwa yaren ta na shuwa, fadi ta ke "Idan ki ka kuskura Malam ya ji wannan maganar wallahi sai ran ki ya baci, ke fa dadi na da ke danyan kai! Kina maganar Boko haram gaban iya kalan ta fita ta yada cewa Malam na aje yan boko haram gidan sa ko? Oh ni wannan rashin hankalin na ki Yakura ina za ki da shi?" "Toh bare ma ni gidan nan kaf ban ga wanda ke kama da Boko haram ba......laaaa ko dai Usman ta ke magana ne?" Cewar Hallita, yanda ta ambato sunan Usman ɗin cike da farin ciki, in da idanun ta har wani sheki su ke ya sanya Ammy da Zainab kura mata idanu. Ita ma din sai a sannan. Ta ankare ta yi saurin faɗin "Daya daga cikin almajiran Dady ne fa, ina ranar da mu ka je taron makarantar su Falmat? Ranar mu ka tarar da shi bakin gate ya na jiran Dady ,a gaban mu ya gabatar da kan shi wajan Dady, ya ce sunan shi Usman, ya na so ya zama daya daga cikin almajiran Dady in da hali, Amma sai dai be da kudin sadaka sai da a bashi aikin yi, Ammy I'm sure Dady ya fada mi ki sai dai kin manta tunda daliban na sa da yawa, ku tambayi Falmat ma ku ji zancen fa ba na yau ba ne an kwana biyu" "Ahaaa kin ji ai Ammy, kawai out of blue mutum ya zo Dady ya karbe shi! Gashi nan dai magana za ta fito, Dan Boko haram......" Ammy na mai kallan Zainab ta ce da Iya "Iya dan je ki zan neme ki zuwa anjima kadan, bari dai na gama da yaran nan" "Toh Hajiya" Iya ta fita ba a san ran ta ba, dan kuwa ta na dan tsintar zancen da ake duk da Ammy ta sauya harshe. Iya na fita Ammy ta mayar da hankalin ta ga yan matan na ta biyu, ta na mai nuna Zainab da dan yatsa ta ce "Kin ga Yakura? Idan kalmar Boko haram din nan ba ta fita bakin ki ba Allah sai na sabar mi ki! Malam ne zai aje dan boko Haram gidan sa?" "Bare ma ba dan Boko Haram ba ne, mutum ne kamili mai ilimi da zurfin tunani....." Cewar Hallita ta na mai hango Usman cikin ranta. "Halitta?????" Ammy da Zainab su ka kira sunan ta a tare. Nan ta yi wuki wuki da idanu, gudun kar mahaifiyar ta da yar uwar ta su gano tuni ta kamu da san almajiri kuma daya daga cikin masu gadin gidan ne ya sanya ta tashi da sauri ta na mai aje ruwan da ya rage cikin fridge. Sai da ta rufe fridge din sannan ta juyo ga Ammy da Zainab wanda su ka tsura mata idanu su na jiran jin ba'asi. "Ammy na gama bari na je na gyara daki na" Ta fada in da ta yi hanyar fita. Kan ta kai koma Ammy ta katse ta, in da ta ce " Halitta ya aka yi ki ka san mutumin da Yakura ke magana akai kamili ne? Mai ilimi da zurfin tunani....?" Gaban ta na faduwa ta juyo su ka hada idanu, ta yi saurin mayar da kallan ta ga Zainab wacce ta daga mata gira cikin alamar tambaya. "Dady na ji ya na fada Ammy, Kuma duk wanda Dady ya amince ya rabe shi ko shakka babu mutumin kirki ne" Ta na gama fadin haka ta fice. Zainab kuwa dan tsalle ta yi tana dariyar mugunta har da tafa hannu ta ce "Ammyyyy you see your child abi? Allah ya sa ba siriki za ki yi da Mai gadi ba" Duka Ammy ta kai mata ta na fadin "Bakin ki baya fadan alkhairi Yakura! Allah ya rufa mana asiri da wannan mugun fata, bakin ki ya sari danyan kashi" "Toh ni kam sai dai na taimaka da amen, kin dai san halin diyar ki sarai ba hankali gare ta ba, bari na dena kiran sa Boko haram kar dai brother in-law ne, Ni kam na yi gaba" Ta fice ta na jiyo Ammy na fad'in "Yar butan uwa, za ki dawo ki same ni ne, oh ni Aleesha Allah ka raba ni da mugun ji da mugun gani!" Ta na maganar ne tana girgiza kai. *** Halitta dakin ta ta shige, har lokacin gaban ta bai dena faduwa ba, in da ta haye bisa kan gadon ta tana mai rufe idanu. Tun da ta ke babu mahalukin da ya taba shiga ran ta tamkar wannan bawan Allah da yar uwarta ke ikirarin dan Boka haram ne. Ba za ta taba mance ran da ta fara tuzali da shi ba. Watanni bakwai da su ka wuce, sun dawo daga taron makarantar su Falmat su ka tadda shi bakin gate. Ka na ganin shi ka ga buzu ko bafulatani saboda yanda yayi nadin rawani da kuma yar riga yar shawara da ke jikin sa. Kasancewar shi bafulatani sam be yi karamin jiki irin na zubin fulani ba, dogo ne mai alamun karfi da faffadar kafada. Kafin Mai gadi ya bude gate Malam da ke zaune a gidan gaba tare da direba ya sa aka sauke masa gilashin motar in da yayi masa Sallama. Ganin Malam ya taso da sauri, har kasa ya durkusa zai gaishe shi, Amma ya ce ah ah ya tashi su gaisa, Malam ya bashi hannu su ka gaisa. Nan ya gabatar da kan sa a matsayin Usman, bafulatani dan cirani, ya zo ne gidan Malam domin neman ilimi kasancewar Malam na daya daga cikin Malaman da ya ke sauraran tafsirin su gidan rediyo, be da arzikin biyan Malam sadaka, Amma zai yi masa aiki har lokacin da zai gama samin ilimin a sallame shi. Daga gidan baya Halitta da Falmat ke hango shi, ita kan ta Falmat ta yaba da kamalan sa, bare Halitta da ta saki baki da hanci ta na kallan sa. Bayan Malam ya gama nazari kan sa na wasu mintina ya ce da shi ya bari ya dawo gobe da safe. Da haka su ka yi sallama ya tafi, inda su kuma su ka shige ciki. Bayan sun sauka daga motar ne Hallita ta dubi Malam ta ce "Dady dan Allah ka duba lamarin bawan Allan can, kamar dai ya na da kamala, idan da yiyuwar taimaka masa a taimaka masa" Malam na murmushin jin dadin yanda diyar ta shi ke da tausayi ya ce "Toh in Sha Allah diyar albarka, dadi na da ke tausayi da jin kai, na mi ki alkawarin matukar na yi bincike na ga be da aibu zan dauke shi matsayin dalibi na, kin san rayuwar ce yanzu ba kamar da ba, mutane sun zama abin tsoro" "Wallahi da gaskiyar ka Dady, muna zaman zaman mu kilu ta ja bau, ka yi binciken dai, rabi da wannan sarkin tausayin" Falmat ta fada yayinda ta ja hannun yayar ta su ka yi hanyar ciki. "Dady a duba dan Allah" Cewar Hallita ta na mai sake waigowa. Kai Malam ya jinjina mata alamar ya ji ta. Haka Halitta ta yi ta bibiyan lamarin har Allah ya taimaka bayan Malam yayi bincike, a iya binciken da aka yi ya gano Usman bafulatanin wata riga da ake kira rugar Shehu ne, Baban shi ne shugaban rugar, haka kuma Usman shi ne babban dan sa. Kasancewar bai ga wata bayyananniyar matsala daga gare shi ba ya sanya Malam karbar shi a matsayin daya daga cikin almajiran sa da ke daukar karatu a gida. Malam ya ce zai iya bashi ilimi ba tare da ya biya sadaka ba, Amma shi ya dage lalle a bashi aiki cikin gidan, idan har ya sami ilimi a arha ba lalle ya ga darajar sa yanda ya kamata ba. A wannan dalilin ne Malam ya bar shi ya na taya Mai gadin gidan gadi cikin dare. Ajiyar zuciya ta saki ta na mai juyi bisa gado, ita kan ta tasan lamarin da zuciyar ta ke bijiro mata akan Mai gadin nan lamari ne mai girma a gaban iyayen ta. Ba ta ji shigowar ta ba, sai jin zaman ta tayi bisa gado. A hankali ta furta "Halitta shin ba za ki dena sa kan ki cikin tunani ba? Sai kin sakawa kan ki cuta akan abin da ba zai taba yiyuwa ba!" A hankali ta bude idanun ta tana mai duban kanwar tata Falmat. Falmat ta na da jiki sosai da kuwa gidan kaf babu wanda ya kai ta kiba. Kiban ta be sa ta yi muni ba dan kuwa irin matan nan ne Duma duma masu kyau na kayatarwa. Kamar Zainab ita ma Falmat baka ce, ta na da hanci har baka da manyan idanu. Duniyar nan kaf babu wanda ya san cikin ta kamar wannan kanwar ta ta, ita kan ta takan yi mamakin yanda ta ke bude mata cikin ta. Falmat sanye cikin kamfala mai ratsin shudi da ja, dinkin goguwar riga har kasa, kannan ya sha tauri da kallabi kai ka ce gidan biki za ta je. "Falmat ya zan yi da jarabawar ubangiji? Kin san dazu na yi barin baki gaban Ammy da Yakura kuwa?" Halitta ta fada cike da damuwa. Falmat na mai dafe kirji ta ce "Kai Halitta! Wasa ki ke yi wayan ki ya fi gaban haka!" Kai ta girgiza sannan ta ce "Idan dai a kan abin da rai ke so, I'm full of disappointment Falmat, wallahilazim! Amma dai na gyara maganar, Allah ya sa dai kar su gane halin da na ke ciki" Shiru ne ya biyu baya, kamin daga bisani Falmat ta ce "Halitta?" Halitta ta amsa mata da "Uhm" "Ina mai baki shawara da ki sassauta wannan lamarin, kin san ba abu ba ne mai yiyuwa ko da kowa wannan mutum ya kai matsayin haka, bare kuma bakauye, dadin dadawa Mai gadi a gidan mu....." "Bakauye Mai gadi ba mutum ba ne? Ba Allah ne ya halicce shi kamayar yanda ya Halicce mu ni da ke da su Dady ba??" Halitta ta katse, ba ta gushe ba ta kara da " Saboda Allah ya dan san mana kankani daga ni'iman shi sai mu zamo ma su butulci ta hanyar kaskantar da bayin shi? Bari na fada mi ki magana daya Falmat! Ina san shi! Ina san Usman tsakani da Allah!" Jikin Falmat sanyaye ta ce "Allah ya ba ki hakuri, Allah ya kawo sauki cikin lamarin ki, dama na zo fada mi ki Dady ya tafi, kin ce ya na tafiya na fada mi ki" Zumbur Halitta ta yi ta mi ke, da sauri ta nufi bandaki, ta na fadin "Toh ina zuwa na wanke fuska ta, Allah ya taimake yau dai na kara ganin Usman Falmat" Shiru Falmat ta mata ta na kallan ikon Allah. Bayan ta fito daga bandaki ga mamakin Falmat sai ga Halitta an tsaya gaban madubi ana goge fuska tare da shafa hoda. Dake Halitta irin matan nan ne jajur sam ba ta damu da shafa powder ba tsabagen farin ta, ita da Zainab kamar su daya, kalar fata ne ya bambamta su, in da Zainab ke baka, Halitta Fara ce sol, dan fari har wani jaja ta kan yi musammam idan ta sha wuya ko ta shiga rana. "Wannan shafa powder na menene? Ina za ki wai?" Ta na shafa man lebe ta ke duban Falmat ta cikin madubi, ta ce "Ina dai za mu je, ai har da ke za mu fita yanda Ammy ba za ta zargi komai ba" "Ina za mu toh" Falmat ta tambaya cikin rashin fahimtar in da Halitta ta dosa. Sai da ta shirya tsaf cikin bakar doguwar riga, tare da nada bakin mayafi, kallo daya za ka mata ka san ko shakka babu Halitta jinin larabawa ce, dan kuwa ta fito a shuwar ta sak. Zuwa ta yi ta na mai ruko hannun Falmat ta ce "I want to see him, please, na san dai ba zai yiyu cikin gidan nan ba, Amma duk yanda za mu yi na gan shi ko sau daya ne Falmat, ba sai mun yi magana ba, kawai na gan shi ya ganni Falmat....." 'wannan bawan Allah ko dai asiri ya yiwa Halitta' Cewar Falmat cikin zuciyar ta, dan kuwa lamarin na Halitta ya fara bata tsoro, lalle lokacin da za ta shaidawa Ammy halin da take ciki yayi! AUREN SHEHU Biyu *** Kamar ta san abin da ta ke ayyanawa cikin ran ta, ta na mai duban idanun ta ta ce "Falmat na yarda da ke, Amma ki sani matukar na ji wannan maganar ta zaga wajan Ammy ke zan tuhama.." Cike da nuna rashin gaskiya Falmat ta shiga girgiza kai tare da fadin "Kin san dai ni mai rufa mi ki asiri ce Halitta, amma wannan abun da ki ke shirin yi ba daidai ba ne, ki tuna fa Dady ya ce ko saurayi bai yarda mu kula a waje ba ko mu kawo masa gida ba tare da yana da masaniya akai ba, Amma yanzu kin shirya dan baya nan ki ce mu yi karya ki ga namiji Halitta?" Hannun Falmat ta saki, ta na mai dafe kai ta furta "Ya Ilahi! Ya iIlahi! Ya Allah ga Falmat! Dalla wa ya ce ma ki zance zan yi da shi? Kawai fa yi za mu yi kamar za mu fita ne idan Allah ya sa yana waje sai na ɗan gan shi..." Cike da mamaki gami da tausayin halin da yar uwar ta ke ciki Falmat ta zura mata idanu. Ganin haka Halitta ta kara da "Haba mana yar ƙanwa ta, in ba ki taimaka min ba wazai taimake ni? Kin san dai Yakura is a snob, ji da kanta ba zai bari ma ta saurare ni ba balle ma taimaka min sai dai ma ta tona min asiri idan dai wannan ce, please Falmat! Zan baki wannan abayar tawa da ki ke so" Jin batun abaya sai ga Falmat ta mike tsaye, ta ce "Da ga yau shikenan gaskiya ba zan kara yin karya dan kawai ki ga Usman Mai gadi ba Halitta..." "Usman! Sunan shi Usman ba Usman Mai gadi ba" Halitta ta gyara mata cikin jaddadawa. Fita Falmat ta yi tana mitar kar Halitta ta takura mata wallahi sai ta fasa raka ta. Haka ta lallaba ta, bayan ta ɗauko mayafin ta, su ka yiwa Ammy karyar za su je gidan wata kawar Falmat, dan kuwa cikin su Falmat ce kadai mai kawa a cikin unguwar. Sai da Ammy ta yi mitar dama jira su ke Malam ya tafi su sami kafar yawo, tare da kashedin kar su dade sannan su ka kama hanya. Tun da su ka kama hanyar fita gaban Halitta ke faduwa, fatan ta Allah ya cika mata buri ya sa Usman na nan farfajiyar gidan. Ai kuwa su ka ci sa'a can kusa da gate ta hango shi tare da abokin gadin shi. Zaune su ke bisa teburi ga ledar dafaffiyar gyada gaban su, suna afawa a baki su na hirar duniya. Tun da ya hangi fitowar su idanun sa ke kan su, kokari ya ke ko zai iya gano wacce ta diro daren jiya cikin su. Sam Halitta ba ta lura da yanda ya saka mu su Ido ba domin kuwa ta yi kasa da na ta idanun tun fitowar su, Falmat ce dai ta ke kokarin kare masa kallo tun daga nesa ta na mai mamakin yanda yayarta ta fada ma san dankauye irin shi. Ganin yanda ya tsura musu ido Falmat ta ja tsaki "Mtsw ashe ma mayen kallo ne! Ji fa yanda ya tsura ma mutane idanu sai ka ce mujiya! Wallahi ya ci sa'ar ki da sai na tsawatar masa!" "Kai Falmat ke da wani ido ki ka san ya na kallan ki? Bare kuma ai ban da burin da ya wuce ya lura da ni nima..........." "Hajiyoyi za a fita ne?" Cewar abokin gadin Usman yayin da ya tashi ya nufi gate din gidan domin bude musu kofa. "Eh sannun ku da aiki" Falmat ta furta ta na mai kai kallon ta ga Usman wanda fuskar sa ke ɗauke da fara'a, haka ma Halitta wacce tunda ta sauke idanun ta bisa fuskarsa mai kwarjini da dumbun annuri gaban ta ya shiga faduwa. "Toh Allah ya dawo da ku lafiya" Ya fada sa'ad da ya bude kofar ya na jira su fita ya kulle. Ganin yanda Halitta ta yi kasake ta na duban shi ya sanya shi fadada fara'ar shi, cike da girmamawa ya sunkuyar da kai alamar gaisuwa, ba Halitta ba hatta Falmat sai da hakan ya burge ta, ganin Halitta na shirin ba da su ya sanya ta jan hannun ta su ka yi waje ta na fadin "Amen Isa, godiya mu ke" Isa na mayar da kofar gate ya koma wajan zaman shi ya zauna, tare da fadin "Ina ruwan Falmat, 'ya'yan Malam ne ai, kila ba za ka san su sosai ba saboda ba sa fita, in za su fita kuma fuskarsu kullum a rufe, na yi mamaki ma yau ka ga ba su rufe ba" Kai Usman ya gyada masa da ke mutum ne da be fiya magana ba, tunanin Falmat ya ke dan ko shakka babu ita ma ta yi kama da wacce ta diro daren jiya, sai dai kuma yanayin kibar Falmat ce ke karyata ita ce din. Duk da waccar hijabi ne jikin ta har kasa, Amma ba ya Jin ta kai Falmat kiba. Nisawa yayi kafin ya furta "Isa ina da wata tambaya domin Allah" "Ina jin ka" Cewar Isa ya yayinda ya bare gyada ya afa a baki. "Shin Malam ya na da 'ya'ya mata da yawa ne,?" "'ya'yan sa uku ne, wannan biyun da ka gani, sai guda, ita ba ta fiye zama a gida ba, jami'ar kwana ta ke ai" Isa ya amsa masa zuciya daya ba tare da ya kawo wani abu cikin ran sa ba. Shiru ne ya biyo baya, Isa bai fasa cin gyadar sa ba, shi kuwa Usman zaton shi ne ya tabbata, Zainab ita ce diyar Malam da ya gani jiya ta hauro kan katanga. 'ita ko wannan Bingel me zai sa ta haura katangar gidan su tsakar dare haka?' Tambayar da yayiwa kan sa kenan, ji yayi duk duniya be da muradin da ya wuce ya san musabbabin wannan lamari na diyar Malam. Halitta kuwa tun bayan fitar su take washe baki kamar wacce aka ma bushara da gidan aljanna. Ba ta bari sun dade gidan da su ka je ba ta ringa azalzalal Falmat su tafi gida, dan kawai su dawo ta kara ganin shi. Su ka yi rashin sa'a kafin su dawo Usman ya tashi sai Isa kawai su ka tadda. Haka ba yanda ta so ba su ka wuce ciki. Dakin ta tayi kwance, bayan ta sallami Falmat da abayar da ta yi mata alkawari. Da kwanciyar ta ishe ta ne ta leka account din ta na Instagram, nan ta ci karo da hotunan Zainab na club, tun tana dauke kai har ta kai hotan da tayi tsakiyar maza ta na busa hayakin shisha, ka na gani ka san sababbiya ce a harkar. kasa zama ta yi, zuciya na zafi ta tashi ta nufi dakin ta. Kai tsaye ta bude kofar dakin ta shiga batare da ta buga mata ba. Bisa gadon ta tarar da ita ta yi kwanciyar rub da ciki, sanye cikin wando "bump short", da yar riga wacce ko cibiya bai rufe mata ba. Ba komai ya dauki hankalin Halitta ba face wata yar zanen fulawa da ta gani kugun Zainab, dab da mazaunan ta, ta na mai tafa hannu ta furta "Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun Mai Zan gani jikin ki Yakura kamar Tattoo?" Jin maganar kamar daga sama ya sanya ta sakin wayar hannun ta ta tashi zaune da sauri ta na duban Halitta. "Haba Halitta! Ya za ki shigo min daki haka ba sallama! In aka yi magana you claimed Ustaziya ke diyar Dady! Yes Tattoo ne jiki na so what?" "Tattoo fa Yakura? Ki na diyar musulmai ki yi tattoo? Ba ki ji tsoran tsinuwar Allah? Yanzu dan Allah idan Dady ya gani ya ki ke tunani zai ji....?" "It's not meant for Daddy's view shi ya sa na yi shi kusa da ass dina ok?" Cewar Zainab ta na mai sake nunawa Halitta inda zanen tattoo din ya ke. Halitta kamar za ta yi kuka dan takaici. Zainab kuwa ko a jikin ta, sai ma ta kara mata da yi da "Toh dan ma na yi tattoo na kafirta ne? Tsinuwar Allah kuma ai tsakani na da Allah na ne, bare ke da ki ke claiming ki na tsoran tsinuwar Allah na ga ai kina make up once in a while, kuma in za a zana mi ki gira sai an aske...." "Auzubillallah! Allah ya tsare ni da aske gira, ban taba ba, kuma ba zan taba ba in Sha Allah" Halitta ta katse ta. Komawa ta yi, ta yi irin wannan kwanciyar ta rigingine, ta na duban Halitta ta ce "An yi rashin sa'a ban sami wanda su ka iya permanent one ba ne, wannan iyakan sa shekara daya, Amma ya na gogewa zan fita US a yi min permanent, after all jiki na ne ba naki ba, oya me ma ya kawo ki daki na?" Shanye bakin cikin da ya taso mata cikin ranta ta yi, wayyar ta ta daga mata, nan hotan nan ya bayyana a idanun Zainab, Halitta ta ce "Wannan wani irin shiga ne Yakura? Yanzu har kya iya zama cikin maza da wannan shigar ta ki? Har ki dauka ki sa a social media? Kuma ki na busa hayaki Yakura! You smoke? You are smoking in the picture! Me mutane za su yi tunani akan Dady muddun su ka san ke diyar shi ce?" Zainab na kallan ta irin kallan nan na hadarin kaji ta ce "Wai ke Haliita ba za ki fita harka ta ba? It's my life, my personal life! Ko kin ga na sa sunan Dady jikin sunana? Ina ruwan Dady da rayuwa ta a waje? Cikin gida na ke diyar sa, ina shiga irin wanda ya ke so a cikin gida in da ya ke gani na, ina masa ladabi da biyayya and he is satisfied! a school da social media I'm the person I chose to be, I don't use his name! mahaifina kenan bare ke da kike kanwa ta! Dan Allah ki fita harka ta Halitta!!" Ta dan tsagaita ta na mai jan wayar ta, Instagram ta shiga ta dubo sunan Halitta, ta ce "Alright ga shi nan na yi unfollowing din ki, I expect you to do the same in dai ke ba mayya ba ce! Wannan masifar har ina!" Ran Halitta idan yayi dubu ya baci, cikin zafin rai take kallan Zainab, ta ce "Ki tuba Yakura! Ko dan darajar mahaifin mu ki tuba, kuma ki sani idan babu mutuwa akwai tsufa, ke mace ce, Rayuwar diya mace kalilan ce, Me za ki ce da 'ya'ya duk randa su ka wayi gari aka yi musu nuni da wannan hoto aka ce ke mahaifiyar su ce? Da wani ido za ki kalle su?......" "Get out of my room! Ba na bukatar wa'azin ki, ki bari sai Dady ya hau mambari ki ja masa baki! Nonsense!" Ta katse ta cike da masifa. Jiki sanyaye Halitta ta juya, ko da ta kai kofa sai ta sake juyowa ta da dubi Zainab da ke kallan ta kamar zakanya, ta ce "Ba zan fasa mi ki wa'azi ba Yakura, ba zan fasa mi ki addua ba, Allah ya shirye ki" "Mtswww" Amsar Zainab kenan, yayin da ta tashi ta rufe kofarta da key bayan fitar Halitta. Idan ran ta yayi dubu ya baci dan kuwa a rayuwar ta ta tsani sa ido, gani ta ke duk duniya babu wanda ya sa mata ido kamar Halitta, shi ya sa ma sam ba sa shiri. AUREN SHEHU 3 Ta na zama bisa gado ta ɗau wayarta ta kira abokin zuwa club din ta da ta ke kira Bobo, bugu daya ya daga tare da faɗin "Zeee oh Zeee the slay mama the club mama, diyar Malam ta ki halin Malam! Ai ni na san baki fushi Zeeena....." "Eh en fa Bobo!" Ta katse shi, ba ta gushe ba ta kara da " Kar ka wani dame ni da dadin baki! Da ka san masifar da ka kusa jawo min jiya da ka ji tsoran ɗaga waya ta!" "Toh yanzu dai Allah ya baki hakuri, ko da ya ke tun da ki ka kira ni ma na san kin huce, wetin dey sup? Malam don commot?" Cewar Bobo cikin muryar zolaya. "Ehen na, him don go Maid, toh ya za a yi? Any happening tonight? Amma dan Allah kar ka kai ni club din talakawa, ka san I can't stand them!" Ta fada ta na mai yamutsa fuska. Dariyar kyeta ya saki, fadi ya ke "Heheheheh Zeeena na daɗe ban ga wanda ya ke kyamkyamin talauci kamar ki ba, babe don't worry I got you, ki shirya 12 daidai ta yi mi ki gaban gate din ku, na san dai yau ba batun haurawa tunda Malam baya nan" "Ba ka da matsala, su Isa ne ai wa'inan, in su ka sa shayi gaba har na wuce ma ba lalle su sani ba, sai ka zo" Ta na maganar ne yayinda Usman ya fado mata rai, ta na mai adduar Allah ya mata katangar karfe da shi, su ka yi sallama da Bobo ta aje wayar. *** Kamar yanda ta saba duk sanda ta san ta kulla harkallar ta, ana isha'i ta fara kukan ciwon kai, daga Ammy har Falmat babu wanda ya kawo wani abu cikin ran su, sai ma tararraya ta da su ka din ga yi, musammam ma Ammy. Halitta kuwa ko kallan in da take ba ta yi, dan cike fal ta ke da Zainab. Ammy ce ta bata magani ta sha, ta ce lalle ta je ta kwanta, amma Zainab ta ce ah ah, gwara ta zauna jikin su za ta fi jin dadi. Sai da ta bari goma da rabi yayi sannan ta ce ciwan ya ci karfin ta, bari ta kwanta dan Allah kada wanda ya shigo ya tada ita, dan idan aka tada ita ba lallai ta iya komawa bacci ba, gashi kuma dama ciwon kai ta ke. Ana bin ta da sannu haka ta mu su sallama, ta koma daki ta yi kwanciyar ta har da kashe wuta. Da ya ke uwa uwa ce wajen sha daya Ammy ta kasa hakuri, sai ga ta a dakin, ganin wutan a kashe ya sanya ta yin sanda zuwa ga gadon Zainab, wacce jin shigowar uwar ta saki jiki ta yi lum kamar mai bacci. Hannun ta dora bisa goshin Zainab ta na mai hamadala, fadi ta ke "Alhamdulillah ta sami bacci" Ta na mai jawo bargo ta dada rufe ta. Sai da ta karanta mata adduar bacci ta shefa jikin ta sannan ta juya ta fita. Ta na fita Zainab ta yi zumbur ta mike, dan kuwa ta san babu mahalukin da zai sake shigo mata daki tunda har Ammy ta ga ta yi bacci, bari ma kuwa idan akwai wacce za ta iya shigo mata munafunci Halitta ce, ita kuma sun yi fada toh ta tabbatar hakan ta ya cimma ruwa. Wankan ta tayi ta fito tsaf cikin wondan ta pencil Jean blue tare da yar karamar riga ja, ta faka gashin nan tsakiyar ka kai ka ce ba diyar musulmai ba ce. Ba ta damu da yin make up, dan irin su Zainab ake yiwa kirari da "black beauty better than gold always shining". Tsadaddiyar powder mai sanya fuska sheki ta shafa, turaruka kuwa 212 sexy, escada magnetism, tare da Indian night Jasmine sai da su ka koka. Gaban madubi ta tsaya ta na mai karkada kugu ta ke yiwa kan ta kirari "Zeee oh Zeee the slay mama, the club mama, kuma salihar Dadyn ta" Sai da ta yi mai isar ta, ganin sha biyu ta kusa ta sanya hijabi har kasa, bayan ta gama gyara gado, ta saita fululluka kai kace mutum ne kwance ta sa bargo ta rufa mu su, takalmin ta mai tsinin gaske a hannun ta na mai sanda ta fito. Ganin wutan falon a kashe ta san kowa ya kwanta, sadaf sadaf ta zaga ta baya ta fice. Isa kuwa da Jauro masu gadin gidan nan gaban gate su ke kwance bacci ya sace su dan yau ko karnukan gidan ba su sake ba. Kallo ɗaya Zainab ta mu su ta ja tsaki tare da fadin " Ji be su kwance kamar mushe! Idan ma sace gidan za a yi wato a yi tunda Dady bayanan, Allah ya kai mu gobe za ku yiwa Ammy bayani!" Ba ta kara tsorata ba sai da ta ga gate din bude, wato ko sakata ma ba su sa ba! Har ta juya a fusace za ta tada su, sai ta tuna tana tayar da su shikenan asirin ta ya tonu, ta na mai adduar Allah ya kare su Ammy ta sa kafa ta fita, hakan yayi daidai da dalle ta da tocilit da aka yi, yanda hasken ya dalle idanun ta ya sanya runtse idanun ta na mai fadin "Oh my God" Tsaye ya ke ya na duban ta, suna hira da su Isa bacci ya kwashe su, dan haka ya dan fita waje mike kafa. Kusan mitunan shi ishirin waje gaban gate, dake unguwar ba mai hayaniya bace sosai kafar mutane ya dan dauke, jin wani ni'imataccen kamshi ya sanya shi dan waige waige tare da tunanin ko dai aljana mai turare ce ta bakunce yau, wanda fitowar ta ya gasgata masa da haka, dan kuwa dai da ya haske ta ganin ta ya ke tamkar aljanar ce tsaye gaban shi. Ganin ba a da niyar daina haska ta ya sanya ta kare fuskar ta da tafin hannun ta, cike da nuna bacin rai ta ce "Dalla Bobo dena haska ni kafin ka sa a kama mu! Kai fa iskancin ka yawa gare shi!" Jin haka ya sanya shi kashe tocilan ba tare da ya iya furta komai ba, dan kuwa harshen sa ya sarke kamar wanda aka daure harshen cikin bakin sa. Bude idanun ta tayi tare da fadin "Bobo....." Ganin wanda ke tsaye gaban ta sai da ta dan ja da baya, shi din nan dai Usman, sanye da rigar saka da rawani irin na buzaye, hannun sa na dama rike da sandar gora, dayan hannun kuma tocilan ne. Ta na shirin juyawa ta koma sai ga motar Bobo, ai kuwa kafin Usman ya ankare da gudun ta ta nufi motar, ganin haka Bobo ya tsaya ta shige ta na fadin "Kai let's get the hell out of here, ina tsoran Allah ina tsoran wannan dan boko haram din can!" AUREN SHEHU 4.   Jin kalmar "Boko Haram" jiki na rawa Bobo ya figi motar ya na mai tayar da kura, fadi ya ke "How? Ya aka yi ki ka san dan Boko Haram ne?" Karar yanda Bobo ya figi motar ne ya sanya su Isa da Jauro fitowa a guje suna fadin "Su waye nan! A tare! A tare!" Ina sai sahun tayar motor Bobo su ka gani, idan shi kan shi Usman da ke tsaye kamar mutum mutumi Jauro ya ce "Yo kai ɗan cirani kana nan tsaye ashe, me ke faruwa ne?" Isa ya kara da "Wacce mota ce ta tashi a guje yanzu? Su waye?" Maimakon ya ba su amsa, sai ya juya abin sa yayi ciki, suna tafe bayan sa, su ka koma ciki, daki yayi wucewar sa ba tare da ya tanka mu su ba. Isa da Jauro su ka tsaya jugum jugum suna duban juna, Jauro ne ya gyara tsayuwa ya ce "Ina Isa? Ni fa Allah na gani ban yarda da wancan dan ciranin ba! Ga fa karar tashin motar da mu ka ji! Mu ka tashi mu ka ga gidan nan bude, shi kuma mu ka taras waje tsaye kamar gunki, Anya kuwa Isa?" Isa wanda kamar Jauro ya shiga ransa, ya dan yi ta maza ya dake, ya na mai yamutsa fuska ya ce "Anya kuwa me?" "Anya kuwa lafiyayyan mutum ne?" Jauro ya fada cike da damuwa. "Ka gan shi da wata rashin lafiya ne?" Cewar Isa cikin dakiya dan ya san in da Jauro ya dosa. Jauro na mai girgiza kai ya sake cewa "Ka san abin da na ke nufi Isa, dan kuwa na san kai ma zuciyar ka ta yi rawa akan lamarin Usman....." "Na raba ka Jauro, na raba ka! Kar ka manta Malam ya karantar da mu akan zato, ya ce zato zunubi ne ko da kowa ya kasance gaskiya, Ni ka ga tafiya ta kunto karnukan nan, da bacci be dauke mu ba ai duk da ba haka ba!" Isa ya tafi ya na mita, Amma cikin ransa tunanin da Jauro ya ke shi ma din shi ya addabi zuciyar sa. Usman kuwa can lambu ya shige in da ya saba raba dare, wata yar doguwar kujera ta hutawa ya samu yayi kwance idanun sa na kallan sararin samaniya. Kamanin Zainab ke masa gizo, haka kuma kan sa ya dada kullewa akan lamarin ta, "Shin ita wannan diyar Malam din ina za ta je da tsohon daren nan? Shin mahaifiyarta ta san da fitar ta? Shi wannan da ya ɗauke ta a bakar mota mai bakin gilashi wanene shi?' Tambayoyin da ya ke yi cikin ran sa ke, wanda ya kagu ya samu amsar su. Ita kuwa Zainab tun da su ka tafi Bobo ke tambayar ta ya aka yi ta san mutumin nan dan boko haram ne? Wanene shi? Sai da ta nutsu sannan ta iya amsa masa da "Daya daga cikin daliban Dady ne, kuma ya na mana gadi, haka kawai jinina be hadu da shi ba wallahi, ka ga jiya ma shi ya kama ni, gashi yau ma an kuma! Allah dai ya tushe bakin sa...." "Wa ya ce mi ki dan boko haram ne?" Bobo ya sake tambaya cike da damuwa. "Haaaaa'a! Are you even listening?" Zainab ta fada cike da tsiwa, ba ta gushe ba ta kara da "Dallah waye zai yarda dan boko haram ya zauna gidan su? Na ce da kai dalibin Dady ne!" "Toh Zeeee ke ce na ji kin kira shi da boko haram....." "Saboda ya na min kama da su ba! Ba wai ina nufin shi din ba ne, ko da ya ke it's possible shi din ne tunda ba wai kwakkwarar bincike aka yi ba...." Ta fada ta na kallan Bobo wanda ya fara hada zufa. Dariya ne ya kwace mata, ta ce "Sai shegen tsora, dallah wasa na ke ma" Bobo na mai goge zufa da hankaci ya ce "Ai dai mutanan ne abun tsoro, Allah ya mana tsari da su, mugu be da kama Zee" Cikin faduwar gaba yayin da kamannin Usman su ka bayyana a zuciyar ta, ya fito mata sak a kamannin mugu, ta na mai saurin kawar da tunanin ta ce "Amen, Allah ya min tsari da shi!" "Wa fa?" "Dan Boko haram mana, Maigadin gidan mu!" Ta fada kai tsaye. "Ki ka ce ba dan boko haram ba ne?" Bobo ya sake tambaya cike da damuwa. "Aaaarrrrghhhh Bobo don't spoil my mood!" Ta fada cikin tsawa. Hannun ya daka tare da fadin "Allah ya baki hakuri Zeee Mama!" "Ba Allah ya ba ni hakuri ba, you better take me to a nice club!" "I got you, kafin nan bari na baki sauti mai dadi" Cewar Bobo yayinda kunna waka ya na mai kure karar. Ranar club yayi ma Zainab dadi, ta hadu da sabon saurayi wanda tare su ka cashe a daren ranar har ta shagala da lokaci, dan kuwa dai ba ita ta ankara ba sai da shida ta wuce. A kidime ta azalzali Bobo wanda ta janyo shi tsakiyar kedaru su na cashewa. Sabon saurayin da ya Kira kan sa Mike ne ya nuna dacewar ya aje ta gida, hakan ba karamin dadi yayiwa Bobo ba, amma Zainab ta hana, ta dai ce ya bari sa yi magana daga baya. Haka su ka yi sallama Bobo na mitar ta katse masa shagali su ka dauki hanyar gida. Dab da za su shiga unguwar ya kalle ta ya ce "Babe kin katse min runs wallahi" "Mtswww" Ta ja tsaki ba tare da tanka ma sa ba, gaba daya hankalin ta ba ya tare da ita, shikenan yau kam asirinta ya tono, tun da take zuwa club ba ta taba kaiwa haka a waje ba, har a idar da sallar asuba ba ta koma gida ba? shin me za ta ce da Ammy idan har ta shiga dakin ta tashin ta sallar asuba ta ga ba ta dakin? Ya ma za ta yi ta shiga gida gari waye haka babu daman ta haura? Kuma ta san su Isa da Jauro ba lalle sun bude gidan ba in ba dai dan boko haram din nan ya kwana nan in da ta barshi tsaye ba ne, wanda ko jikin ta kunne ne ta san ba abu ba ne mai yiyuwa ba, kila ma ya riga ya fadawa Ammy fitar ta..... Tsigar jikin ta ne ya tashi yayinda gaban ta yayi mummunar faduwa, a zahiri kuma fadi ta ke "Ya Ilahi....." "Kai Zeeena ashe kin iya ambaton Allah!" Cewar Bobo cike da zolaye. Harara ta watsa masa, tare da fadin "Dadi na da kai Bobo rashin sanin ciwon kai! Ba ka ga halin da na ke ciki ba ne wai?" Dariya ya ke yayin da ya sami waje ya faka, suna hango gidan Malam ya ce "Come na, stop panicking! Kwantar da hankalin ki babe, calm down, ki fita ki je gate din gidan ku, idan bude ya ke ki shigewar ki kai tsaye, ba kya bin masu gadin ku bashin bayani, idan rufe ya ke ki buga mu su su bude mi ki, gidan uban ki ne, idan Momcy ta gan ki tell her kin fita exercises ne, shikenan!" "Yen yen yen yen! Ni na rasa yanda aka yi na ke mu'amala da kai Bobo! Duk randa na fita da kai sai ka jawo min matsala!" Ta na gama fadin haka ta fice a fusace tare da buga masa murfin mota. Zuciyar ta na bugu ko wani taku ta yi, wayar Halitta ta shiga kira, ta yi ringing ta gama ba ta daga ba, hannu na rawa ta kira Falmat, ita ma din ba ta daga ba, isar ta gate din ta dan tura ta ji a rufe, sai da ta dan yi jim sannan ta yi karfin halin bugawa. Har ta fitar da rai da bude gate din, ta na shirin juyawa sai ta ga an bude hujun da aka yi jikin gate din domin ganin na waje. Idanun ta ta tsinta cikin na sa, tuni ta tsinci kanta cikin mummunar faduwar gaba, yayin da bugun zuciyar ta ya karu, sai da yayi sakanni ya na kallan ta, ta na mai cuna kumatu cike da tsiwa ta ke mayar masa da martanin kallan, dan kuwa tsoro baya hana Zainab rashin kunya.. "Malam dalla ka bude min gate! Ka zuba min na mujiya ba ka taba ganina ba ne?" Ga mamakin ta sai kuwa ya bude, shigar nan dai da ta gan shi da ita jiya da daddare, shi ne jikin sa, Goran nan dai be aje ba, ta na rike hannun sa na hagu, hannun sa na dama kuma ruke da rediyo ya na jin labarai. Ko kallan sa ba ta kara yarda ta yi ba, bare su hada idanu kai tsaye ta wuce ciki kamar dai yanda Bobo ya ce ta yi, addua ta ke Allah ya rufa mata asiri kar ta hadu da Isa ko Jauro, sa'ar da ta yi da an idar da sallar asubahi su ke komawa su yi baccin su tun zuwa Usman gidan, shi kadai su ke bari da gadin safe, karnuka kuwa ana kiran sallar farko ake daure su, saboda kar su dami masu sallah masallacin gidan da haushi, duk da dai ta waje masallacin ya ke. Sai da ta kurewa ganin sa, zuciyar sa cike da tunani kalala wanda duk yanda ya so ya cire daga zuciyar sa ya gagara, ya mayar da gate ya rufe. "Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun! Babu shakka Allah ya jarabci Malam da diya kamar yanda ya ke jarafta salihan bayin sa cikin ikon sa! Ya Allah ka kare Malam daga sharrin wannan Bingel!" Cewar shi a zahiri, yayinda ya koma mazaunin shi bisa benci, ya kishingida ya na mai cigaba da sauraron labaran shi a tashar BBC hausa. Cikin sanda takalman ta a hannu ta ke tafiya, ta kitchen ta bi ta shiga falon, dab da zata karasa dakin ta muryar Halitta ya daki kunnan ta "Yakura daga ina ki ke?" Jiki na rawa ta saki takalman su ka zubi kasa, Kallan Halitta ta ke ta na mai waige waige ta ga ko ita kaidai ce. Ita kadai din ce sanye cikin hijab har kasa, hannun ta ruke ta carbi dan Halitta ba ta komawa bacci bayan sallar asuba, zama ta ke ta yi zikiri da adduo'i har gari ya waye rana ta fito, sannan ta shiga kitchen ta taya iya abin karin kumallo. Ta fito za ta kitchen din kenan su ka yi kacibus da Zainab ta na sanda za ta shige dakin ta. AUREN SHEHU 5.   Wani irin sassanyar ajiyar zuciya ta saki, ta na mai duban Halitta murya kasa kasa ta ce "daga ina na ke kuwa? Dage exercise mana!" "Exercise din tun karfe 4:45 na dare Yakura? Ki ji tsoran Allah! Ammy ta turo ni tashin ki sallah Yakura, na san ba gidan nan ki ka kwana ba, daga ina ki ke?" Halitta ta kara tambaya ta na mai tsare ta da idanu. "Daga yawon ta zubar na ke ko da yanda za ki iya ne? Ki na da abin yi ne? Kuma Allah ya mana katangar karfe da saidawa!" Kafin Halitta ta bata amsa ta yi saurin kwasar takalman ta, ta yi wuf ta shige dakin ta. Jim ta yi ta na maimaita kalaman Zainab cikin ran ta "Daga yawon ta zubar na ke......" Ta kara maimaita. "Shin anya kuwa shirun nan da na ke akan abin da Yakura ta ke yi Allah ba zai tambaye ni ba? Ko dai Ammy zan fadawa? Ko da ya ke in har na fadawa Ammy kamar na fadawa Dady ne, Allah kadai ya san halin da Dady zai shiga muddin ya sani, Allah ka ga zuciya ta, Allah ka mana magani" Kitchen ta wuce, ganin Iya har lokacin ba ta fito ba sai ta wuce dakin Iya domin ta ga ko lafiya. Zainab kuwa ta na shiga bandaki ta shige ta yi wanka, fitowar ta daga wanka ta tarar Ammy tsaye tsakar dakin, abin ku da mara gaskiya sai da zuciyar ta ta dan yi rawa. Ta na kame kame ta ce "Ammy, aw ashe ke ce" "Ni ce jiki yayi sauki kenan, ai na turo Halitta ta tashe ki sallah da asuba...." "Eh mun hadu ai" Ta yi saurin katse ta. Kallon ta Ammy ta ke kamar mai nazari, kafin daga bisani ta ce "Me ki ke cewa ne? Kamar yaya kun hadu?" Zainab na mai sosa kyeya ta ce "Ah ah ina nufin na gan ta, da ta zo tashi na, eh ta tashe ni din" "Oh toh, Ni ce min ta yi ba ta gan ki ba, ta na tunanin kin tashi tuni har kin shiga toilet" "Eh ai ina toilet din na jiyo shigowar ta, haka na ke nufi Ammy" Kai Ammy ta gyada, sa'annan ta kara da "Ya ciwon kai?" "Ciwon kai? Aw Alhamdulillah na sami sauki, Ina kwana Ammy?" Cewar Zainab yayin da ta zauna bakin gado, Allah Allah ta ke Ammy ta fita ko ta samu gaban ta ya bar faduwa. "Lafiya lau Alhamdulillah, ashe ba mu gaisa ba, Allah ya kara sauki, sai ki yi maza ki fito mu karya ko? "Wallahi Ammy ba zan iya cin abinci yanzu ba, wani irin bacci na ke ji, rabona da bacci tun jiya da safe, kin san bacci ba a cin bashin sa " Ta na mai duban ta cikin nazari ta ce "Wannan baccin na ki kuwa anya Yakura? Me ya hana ki bacci? Nan fa na shigo na tarar ki na ta bacci?" "Ah ah, wai ina nufin ban yi ishasshe ba, ina yi ina tashi saboda ciwan kai" "Toh Allah ya sauke, ki daure dai ki ci wani abu kafin ki kwanta" Zainab ta amsa mata da toh, dan dai kuwa ba ta da buri da ya wuce Ammy ta fita ta samu ta ji hakarkarin ta bisa katifa. Illai kuwa ta na fita ko mai ba ta iya shafawa, ta dauko wata yar riga iya gwiwa ta sanya, ba batun sallar asubahi ta bi lafiyan gado abin ta. Nan da nan bacci ya dauke ta. *** Haka rayuwa ta cigaba da gudana. Zainab ta kasa hakura da club ta bari sai ta koma makaranta kamar yanda ta saba, saboda sabon saurayin ta Mike, shi ne ke zuwa daukar ta ya dawo da ita. Ba komai ne ya bata lasisin wannan shagalin na ta ba face shawarar Mike da ta bi na siye daya daga cikin masu gadin gidan. Cikin masu gadin uku ta san Isa da tsattsauran ra'ayi ko da wasa ba zai amince da ita ba, Usman kuwa shi tsoran sa ma ta ke ji, dan haka sai ta kama Jauro ta rike gam. A kulli yaumin ta kan tabbatar ta masa alkhari na safe daban na yamma da daban, ta haka ta samo hanyar shawo kan sa. Ta masa karyar cewa akwai kungiyar bitan karatu da su ka hada ne ita da yan makarantar su da ke zaune Kano, kafin su koma makaranta, Amma da daddare ake yi, ta na tsoran kar ta fadawa su Ammy ne su hana ta gabadaya, shi ya sa ta yanke hukuncin ta na bi ta bayan kasa, har su koma makaranta. Duk da Jauro ya san maganar Zainab yashesshen zance ne, da ke ido a kabo ne da ta bashi sai ya sa hannu ya karfe, idan dare yayi sai ya tabbatar Usman da Isa ba sa kusa sai ya bude mata kofa, haka idan ta dawo shi ne ke bude mata. Duk wannan hidimar da ya ke yi akan idanun Usman, tun ya na ɗauke kai har ya gaji wata ranar Juma'a da yamma, ana saura sati daya Malam ya dawo Usman ya sami Jauro kishingide karkashin bishiya ya na shan rake, dan kuwa tunda Zainab ta fara bashi kudi kullum cikin kudi ya ke. Sallama ya masa tare da zama kusa da shi. Tayin rake Jauro ya masa bayan ya amsa sallamar. Usman na mai godiya, cikin maganar sa mai cike da nutsuwa, yanayin yanda ya ke fito da kalmomin hausa daga bakin sa ne ki kara jaddada kasancewar sa na kabilar fulani, ya ce "Alhamdulillah, na gode Jauro ka sha raken ka, dama akwai yar magana da na ke so mu yi da kai" "Toh Madallah dan cirani, da me ka zo" Cewar Jauro bai fasa shan raken sa ba. Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani Usman ya ce "Ka yi hakuri zan ma ka shisshigi, wala'alla za ka fahimce ni" Jauro na mai fuzar da totuwar rake daga bakin sa ya ce "Uhum, ina sauraron ka. "Zancen fitar dare da Bingel din nan ke yi, diyar wajan Malam" Cikin halin ko in kula Jauro ya ce "Uhum? Menene na ka a ciki?" "Akwai, Malam ya ba mu gadin gidan sa bisa amana, ni da na ke gani ina dauke kai ba tare da fadawa mahaifan ta ba, ina da alhaki, bare kai kuma da ka ke ba da gudunmawa Jauro!" Jauro na mai tashi zaune ya ce "oho! Ashe dai ka na gani, kuma ka san ka na da alhaki! Tun da ka ke gani ba ka san ka na da alhaki ba sai yanzu da ka ga ina dan samu ko fillo? Ni za ka yiwa halin na ku na fulanin daji ko? Dan bakin ciki!" Usman na mai dafe kai ya ce "Ya ilahi! Ba ka fahimce ni ba Jauro! Ba dan komai ya sa ban iya fuskantar Malam akan wannan batun ba sai dai dan kunya da nauyin sa da na ke ji! Da wani ido ko baki zan iya kallan Malam na ce masa diyar sa na haura katanga? Ko kuma duk dare ana zuwa ana daukar ta? A dawo da ita da safe?" "Dan sa ido! Da Idon da bakin da ka zo ka tinkare ni yanzu mana! Yarinya na fita bitar digiri(Degree) din da ta ke yi a jami'a, ko da yake kai fa ko zo na kashe ka da turanci ba ka sani ba bare ka san kalmar Degree! Kai Allah dai ya raba mu da jahilci!" Duk zuciya irin na Usman sai ya tsinci kan sa ya na mai murmusawa, ka na ya ce "Ban da cin fuska mana Malam Jauro, na zaci za mu iya samin fahimtar juna shi ya sa ma na tunkare ka da maganar, amma tun da abin haka ne, Allah ya ba ka hakuri!" "Ni kuma na taimaka da Aameen! Eh amen, kuma Allah ya raba mu da munafukai da yan bakin ciki" Usman na murmushi ya amsa da amen, tashi yayi tare da yiwa Jauro sallama duk da dai be ji dadin yanda Jauro ya kasa fahimtar ta shi, sam be ruke shi a rai ba, shi dai fatan sa Allah ya bashi ikon kawo karshen wannan masifar da ke faruwa gidan Malam, duk da kamar yanda Jauro ya fada be san "digiri" ba, Amma koma menene wannan digirin in dai haka ake yin sa toh lalle ba alkhairi ba ne. *** In da Usman ke kokarin neman mafita akan iftilakin da ke faruwa gidan Malam, ita kuma Halita soyayyar Usman ce ta sami wajan zama cikin zuciyar ta. Zaune su ke a falo, sun gama cin abinci kenan su ka zauna zaman hira. Falmat sanye da atamfa koriya dinkin doguwar riga, Halita kuwa kananan kaya ne cikin ta, riga da sikit jajaye, kanta daure da jan mayafi. "Ni kuwa Halitta ina mamakin yanda ki ke kaunar Usman din nan, dan kuwa dai sai dai na kira shi kauna dan ya fi karfin so" Cewar Falmat yayinda yanayin fuskar ta ke gasgata lafazan ta. Sanyayyar ajiyar zuciya Halitta ta saki kafin ta ce "Daga Allah ne Falmat, Ni dai kawai ki taya ni addua" "Toh zan taya ki, Amma duk randa Ammy ta san Usman ki ke so Halitta, I mean not just Usman o, but Maigadin gidan nan wallahi akwai kura...." "Shhhhh" Halitta ta katse ta, ta na mai kasa da murya ta ce "Ke fa matsala ta da ke Falmat handsfree! Ki rufa min asiri kar Yakura ta ji....." "Ji kuma na nawa?" Da sauri su ka juya su na kallon ta, ba wanda ya san da shigowar ta bare ya san adadin mintunan da ta yi tsaye ta na sauraran su. Sanye ta ke cikin bakin material, doguwar riga ta yi daurin nan da ake Kira tura ka tsiya. Idanun ta kan Halitta wacce har ga Allah ba ta so maganar ya je kunnan ta ba ta ce "Yanzu ke Halitta ki rasa wanda za ki so sai wannan Maigadin? Yo to menene abin so a wannan kazamin bafulatanin hammata fal gashi?" In da Halitta ta fusata, ita kuwa Falmat mamakin yanda aka yi Zainab ta ga hammatar, ba ta san sanda dariya ta kwace mata ba, wanda hakan ba karamin tunzura Halitta yayi ba. Yakura ba ta gushe ba ta kara "Ke anya kuwa bakin wannan ya san brush? As in kafin na so mutum I first imagine things people do when they're in love, as in can you imagine yourself with him? Like imagine kissing wannan dagageggen bakin na shi?" "Wayyo Allah Ammy!" Falmat ce ta saka ihu ta na mai dariyar mugunta, ita kuwa Halitta iya kulewa ta kule. A fusace ta ce "Malama ina ruwan ki? Kin manta ba kiss ba! Abin da ya fi kiss! Idan ma auren shi na ce zan yi ina ruwan ki!" Ta na mai daga hannu sama yayinda ta zagaya ta shigo falon sosai, kujerar da ke kusa da Falmat ta zauna, sannan ta ce "Babu fa, babu ruwa na ko kadan, aw kin san abin da ya fi kiss ashe, yo ai na zaci uztazanci ya hana ki sani, Sha it's your life, Bari na ja baki na!" "Alhamdulillah tunda kin san haka, da fatan za ki yi aiki da shi...." "Ke fa ba kunya gare ki ba Halitta!" Zainab ta katse ta cikin tsawa, ta kara da "Kar ki ga kin yi tsayin kafa wallahi ina iya doke ki, mara kunya fitsararriya" "Toh sarkin tsiwa! Tun daga daki na ke jiyo hayanoyar ku! Anya kuwa Yakura? Ke da waye kuma?" Ammy ce wacce ihun Falmat ya sanya ta fito da sauri ta ke tambaya. "Babu komai Ammy" Halitta ta fada gudun kar Yakura ta mata tunan asiri, ilekuwa sai cewa ta yi "Da komai fa Ammy, ai dai gaban ki yarinyar nan ta gama azazzabi da rawan jiki wajan jaddada bayani akan wannan dan bokon haram din, toh dai ruwa ba ya tsami banza, ga shi nan na ji tana managanar son shi ya kamata..." Ta karasa maganar ta na yar dariya tare da girgiza kai. Daga Falmat har Halitta mutuwar zaune su ka yi, sun san Zainab da barin zance amma ba su taba zatan za ta tonawa Halitta asiri hakan nan kara zube ba. Ammy na dariyar yake ta ce "Ke kuwa Yakura ba dai zolaya ba, ina Halitta ina kula wani da namiji? Har kuma ki ce Maigadi? No wonder na jiyo ku tun daga daki, ah ah ni ma ban goyi bayan wannan wasan ba!" "Atoh Ammy ke dai kya fada" Cewar Falmat ta na mai fatan rufe asirin Halitta. Zainab kuwa ba ta damu da irin sakon da Halitta ke aika mata ta ido ba, sake cewa ta yi "Wallahi Ammy ba wasa na ke ba, Halitta soyayya ta ke da Maigadin gidan nan" "Lailaha ilallahu Muhammad a rasulillahi!" Cewar Ammy ta na mai tafa hannu cikin tashin hankali ta ke duban Halitta wacce ita ma din kallo daya za ka mata ka tabbatar da damuwan da ta shiga. "Halitta me na ke ji haka? Wannan wani irin mummunar labari na ke ji Halitta? Duka tarbiya, kulawa da soyayyar da mu ke baki abin da za ki saka mana da shi kenan Halitta?" Tuni hawaye ya shiga fita daga idanun Halitta, ta na girgiza kai ta ke fadin "Ah ah Ammy, wallahi ba haka ba ne Ammy...." Cikin bambami Ammy ta ce "Ba haka ba ne uban ki ne? Yi min shiru! Wallahi kin ba ni kunya kin yi asara Halitta! Yanzu idan Malam ya ji wannan tozarcin da cin amana ya ki ke tunanin zai ji. Dama aka ce tsintacciyar mage ba ta mage! Hakan nan mutum daga sama ya zo gidan ka ka karbe shi har da bashi wajan kwana, gashi nan zai masa sakayya ta hanyar hure ma diyar sa kunne ai! Toh kuwa zaman shi a gidan nan ya zo karshe" Jin Ammy na batun zai bar gidan wani dadi ne ya mamaye Zainab, dan kuwa burin ta ke nan. "Atoh ai tun da na fara ganin sa na san ba za a wanye lafiya ba, na yi magana a ce na fiya kyaman yan kauye, ga dai irin ta nan!" Cewar Zainab ta na mai daga kafada tare da saukewa. Falmat ce ta saka baki ta ce "Ammy ba ki fahimta ba, wallahi ba haka ba ne, shi wannan bawan Allah sam be ma san da Halitta ba, bare ma ya hure mata kunne, ba soyayya su ke ba, kawai dai Halitta na yawan maganar sa ne ya sa ke tsokanar ta da shi, Amma babu komai tsakanin su Ammy!" "Ki ji wani yashesahen zance idan babu rami me ya kawo rami?" Ammy ta tambaya a fusace, in da Zainab ta taya ta da atoh. Halitta kuwa ta ma kasa magana sai hawayen takaici da ge gangarowa daga idanun ta. "Allah Ammy gaskiya na ke fada mi ki, in kuma ya kama a kira shi ne ki tambaye shi ki kira shi Ammy" Shiru ne ya biyo baya na dan sakanni, Zainab sai adduar Allah ya sa kar Ammy ta yarda da zancen Falmat ta ke cikin zuciyar ta. Jin abin da Ammy ke fadi ne ya sanya ran Zainab yin baki. Tana mai ajiyar zuci ta ke fadin "Toh ni fa in ce, jinina ba za ta taba san Maigadi mara asali ba, haba har na dan ji sanyi cikin rai na, toh wallahi kar na sake jin maganar nan ko da wasa!" Ta na mai duban Halitta ta kara da "Ke kuma Halitta na kara jin maganar Maigadin nan bakin ki sai na sabar mi ki" Kai Halitta ta gyada kafin ta tashi ta fice da ga falon, dan kuwa gani ta ke muddin ta cigaba da zama zafin rai zai sa ta iya tonawa Zainab asiri akan yawan daren da ta ke, ita kuwa ba ta so ta biye mata garin ramuwar gayya su jawa mahaifiyar su matsalar hawan jini. Ta na jiyo Zainab na cigaba da sukar zaman Usaman a gidan. Ita kuwa Falmat mamakin yanda Zainab ta hakikance ta na bata Usman da karya da gaskiya wajan Ammy, har ta kai ga ta na tunanin shin me ya taba hada su ta ke masa wannan tsana haka? Duk yanda ta so a kori Usman a gidan, ranar haƙon ta ya kasa cimma ruwa, duk da dai ta ci nasarar tusawa Ammy kiyayyar sa cikin zuciyar ta, ko ba komai yau da gobe in dai Ammy ta tsane shi tabbas sai zaman gidan ya gagare shi. Ta sha alwashin sai ta san yanda za ta yi ta sa Malam ya kori Usman daga gidan. **** Ana sauran kwana biyu Malam ya dawo Kano, haka kuma wata daya ya rage a fara azumin watan ramadan, bayan sun idar da sallar isha'i gidan Malam da ke Maiduguri, Malam ya karbi bakwancin aminin shi, Shiek Ahmad Suraj. Kamar yanda Malam ya ke babban Malami haka ma Shiek Ahmad ya ke sananne a cikin garin Maiduguri, ba dan malamtakan sa kadai ba, har dama tarin dukiya da Allah ya ba shi. Duk da dai shi asalin sa dan Chad ne. Ba karamin farin ciki masa tarba na ban girma kamar yanda ya saba masa duk sanda ya zo. Babban Falon Malam su ke zaune, falo ne ya kayatu kwaran gaske. Bayan sun gaisa tare da hirar bayan saduwa, Shiek Ahmad ya ce "Ya Shiek dan wajan ka Sudais fa ya hada karatu, mu na sa ran dawowar shi gida Nigeria farkon shauwal da an kammala azumi" Malam na mai washe baki ya furta "Toh Alhamdulillah, ka ce Sudais ya zama cikakken likita, kuma mahaddaci wannan labari abin alfahari ne, Allah ya masa albarka, ya albarkaci ilimin da aka samu, ya sa a yi aiki da shi, ya kawo abokiyar rayuwa ta gari" "Allahumma amen, abokiyar zaman kuwa Ya Shiek gidan ka na ke so a samu, dan kuwa sami 'ya'ya masu tarbiya irin 'ya'yan ka mata sai an duba akaramallah" Cewar Shiek Ahmad wanda ke maganar har cikin ran sa da zuciya daya. Hakan ya sanya farin ciki bayyana a fuskar Malam, idanun sa har sheki su ke, ya na mai ruko hannun Shiek Ahmad ya ce "Jazakallahu khair, jazakallahu khair, jazakallahu bi jannah da wannan sheda ta ka Shiek, Ni kuwa na maka alkawarin bawa Sudais diya ta mafi soyuwa a rai na, cikin su tafi kuwa nutsuwa, ga ladabi da biyayya, ga rukon addini, ga kunya, ga...ga...ga....sai Zainab! Ta na aji uku a matakin karatun jami'a, in da take karantar Microbiology anan American university of nigeria da ke Yola" Cikin gamsuwa da jin dadi Shiek Ahmad ya ce "Madallah da wannan diya da ta sami shaida mafi daraja daga wajan mahaifin ta, muna so" Malam na mai murmushi ya ce "An ba ku" Hannun Malam Shiek ya rike cikin musabaha ya ce "Mun karba, mun gode, Allah ya saka da alkhairi, in Sha Allah da yaron nan ya dawo sai a turo a sa ranar daurin auren ko?" "Su waye za su saka rana da ya wuce mu? Ai kawai tsaya ka gani ya Shiek" Malam ya dauko calendar ya na dubawa, ranar Juma'a ya zagaye wanda ya kama shabiyu ga watan juli Malam ya ce "Ga rana nan duba ka ga, idan har ya maka, sai mu yi fatan Allah ya kai mu da rai da lafiya" Shiek Ahmad na duba calendar da Malam ya nuna masa ya ce "Hamdan ya yi Ya Shiek, Allah ya nuna mana da rai da lafiya" Malam ya amsa da Allahumma amen. AUREN SHEHU Biyu *** Kamar ta san abin da ta ke ayyanawa cikin ran ta, ta na mai duban idanun ta ta ce "Falmat na yarda da ke, Amma ki sani matukar na ji wannan maganar ta zaga wajan Ammy ke zan tuhama.." Cike da nuna rashin gaskiya Falmat ta shiga girgiza kai tare da fadin "Kin san dai ni mai rufa mi ki asiri ce Halitta, amma wannan abun da ki ke shirin yi ba daidai ba ne, ki tuna fa Dady ya ce ko saurayi bai yarda mu kula a waje ba ko mu kawo masa gida ba tare da yana da masaniya akai ba, Amma yanzu kin shirya dan baya nan ki ce mu yi karya ki ga namiji Halitta?" Hannun Falmat ta saki, ta na mai dafe kai ta furta "Ya Ilahi! Ya iIlahi! Ya Allah ga Falmat! Dalla wa ya ce ma ki zance zan yi da shi? Kawai fa yi za mu yi kamar za mu fita ne idan Allah ya sa yana waje sai na ɗan gan shi..." Cike da mamaki gami da tausayin halin da yar uwar ta ke ciki Falmat ta zura mata idanu. Ganin haka Halitta ta kara da "Haba mana yar ƙanwa ta, in ba ki taimaka min ba wazai taimake ni? Kin san dai Yakura is a snob, ji da kanta ba zai bari ma ta saurare ni ba balle ma taimaka min sai dai ma ta tona min asiri idan dai wannan ce, please Falmat! Zan baki wannan abayar tawa da ki ke so" Jin batun abaya sai ga Falmat ta mike tsaye, ta ce "Da ga yau shikenan gaskiya ba zan kara yin karya dan kawai ki ga Usman Mai gadi ba Halitta..." "Usman! Sunan shi Usman ba Usman Mai gadi ba" Halitta ta gyara mata cikin jaddadawa. Fita Falmat ta yi tana mitar kar Halitta ta takura mata wallahi sai ta fasa raka ta. Haka ta lallaba ta, bayan ta ɗauko mayafin ta, su ka yiwa Ammy karyar za su je gidan wata kawar Falmat, dan kuwa cikin su Falmat ce kadai mai kawa a cikin unguwar. Sai da Ammy ta yi mitar dama jira su ke Malam ya tafi su sami kafar yawo, tare da kashedin kar su dade sannan su ka kama hanya. Tun da su ka kama hanyar fita gaban Halitta ke faduwa, fatan ta Allah ya cika mata buri ya sa Usman na nan farfajiyar gidan. Ai kuwa su ka ci sa'a can kusa da gate ta hango shi tare da abokin gadin shi. Zaune su ke bisa teburi ga ledar dafaffiyar gyada gaban su, suna afawa a baki su na hirar duniya. Tun da ya hangi fitowar su idanun sa ke kan su, kokari ya ke ko zai iya gano wacce ta diro daren jiya cikin su. Sam Halitta ba ta lura da yanda ya saka mu su Ido ba domin kuwa ta yi kasa da na ta idanun tun fitowar su, Falmat ce dai ta ke kokarin kare masa kallo tun daga nesa ta na mai mamakin yanda yayarta ta fada ma san dankauye irin shi. Ganin yanda ya tsura musu ido Falmat ta ja tsaki "Mtsw ashe ma mayen kallo ne! Ji fa yanda ya tsura ma mutane idanu sai ka ce mujiya! Wallahi ya ci sa'ar ki da sai na tsawatar masa!" "Kai Falmat ke da wani ido ki ka san ya na kallan ki? Bare kuma ai ban da burin da ya wuce ya lura da ni nima..........." "Hajiyoyi za a fita ne?" Cewar abokin gadin Usman yayin da ya tashi ya nufi gate din gidan domin bude musu kofa. "Eh sannun ku da aiki" Falmat ta furta ta na mai kai kallon ta ga Usman wanda fuskar sa ke ɗauke da fara'a, haka ma Halitta wacce tunda ta sauke idanun ta bisa fuskarsa mai kwarjini da dumbun annuri gaban ta ya shiga faduwa. "Toh Allah ya dawo da ku lafiya" Ya fada sa'ad da ya bude kofar ya na jira su fita ya kulle. Ganin yanda Halitta ta yi kasake ta na duban shi ya sanya shi fadada fara'ar shi, cike da girmamawa ya sunkuyar da kai alamar gaisuwa, ba Halitta ba hatta Falmat sai da hakan ya burge ta, ganin Halitta na shirin ba da su ya sanya ta jan hannun ta su ka yi waje ta na fadin "Amen Isa, godiya mu ke" Isa na mayar da kofar gate ya koma wajan zaman shi ya zauna, tare da fadin "Ina ruwan Falmat, 'ya'yan Malam ne ai, kila ba za ka san su sosai ba saboda ba sa fita, in za su fita kuma fuskarsu kullum a rufe, na yi mamaki ma yau ka ga ba su rufe ba" Kai Usman ya gyada masa da ke mutum ne da be fiya magana ba, tunanin Falmat ya ke dan ko shakka babu ita ma ta yi kama da wacce ta diro daren jiya, sai dai kuma yanayin kibar Falmat ce ke karyata ita ce din. Duk da waccar hijabi ne jikin ta har kasa, Amma ba ya Jin ta kai Falmat kiba. Nisawa yayi kafin ya furta "Isa ina da wata tambaya domin Allah" "Ina jin ka" Cewar Isa ya yayinda ya bare gyada ya afa a baki. "Shin Malam ya na da 'ya'ya mata da yawa ne,?" "'ya'yan sa uku ne, wannan biyun da ka gani, sai guda, ita ba ta fiye zama a gida ba, jami'ar kwana ta ke ai" Isa ya amsa masa zuciya daya ba tare da ya kawo wani abu cikin ran sa ba. Shiru ne ya biyo baya, Isa bai fasa cin gyadar sa ba, shi kuwa Usman zaton shi ne ya tabbata, Zainab ita ce diyar Malam da ya gani jiya ta hauro kan katanga. 'ita ko wannan Bingel me zai sa ta haura katangar gidan su tsakar dare haka?' Tambayar da yayiwa kan sa kenan, ji yayi duk duniya be da muradin da ya wuce ya san musabbabin wannan lamari na diyar Malam. Halitta kuwa tun bayan fitar su take washe baki kamar wacce aka ma bushara da gidan aljanna. Ba ta bari sun dade gidan da su ka je ba ta ringa azalzalal Falmat su tafi gida, dan kawai su dawo ta kara ganin shi. Su ka yi rashin sa'a kafin su dawo Usman ya tashi sai Isa kawai su ka tadda. Haka ba yanda ta so ba su ka wuce ciki. Dakin ta tayi kwance, bayan ta sallami Falmat da abayar da ta yi mata alkawari. Da kwanciyar ta ishe ta ne ta leka account din ta na Instagram, nan ta ci karo da hotunan Zainab na club, tun tana dauke kai har ta kai hotan da tayi tsakiyar maza ta na busa hayakin shisha, ka na gani ka san sababbiya ce a harkar. kasa zama ta yi, zuciya na zafi ta tashi ta nufi dakin ta. Kai tsaye ta bude kofar dakin ta shiga batare da ta buga mata ba. Bisa gadon ta tarar da ita ta yi kwanciyar rub da ciki, sanye cikin wando "bump short", da yar riga wacce ko cibiya bai rufe mata ba. Ba komai ya dauki hankalin Halitta ba face wata yar zanen fulawa da ta gani kugun Zainab, dab da mazaunan ta, ta na mai tafa hannu ta furta "Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun Mai Zan gani jikin ki Yakura kamar Tattoo?" Jin maganar kamar daga sama ya sanya ta sakin wayar hannun ta ta tashi zaune da sauri ta na duban Halitta. "Haba Halitta! Ya za ki shigo min daki haka ba sallama! In aka yi magana you claimed Ustaziya ke diyar Dady! Yes Tattoo ne jiki na so what?" "Tattoo fa Yakura? Ki na diyar musulmai ki yi tattoo? Ba ki ji tsoran tsinuwar Allah? Yanzu dan Allah idan Dady ya gani ya ki ke tunani zai ji....?" "It's not meant for Daddy's view shi ya sa na yi shi kusa da ass dina ok?" Cewar Zainab ta na mai sake nunawa Halitta inda zanen tattoo din ya ke. Halitta kamar za ta yi kuka dan takaici. Zainab kuwa ko a jikin ta, sai ma ta kara mata da yi da "Toh dan ma na yi tattoo na kafirta ne? Tsinuwar Allah kuma ai tsakani na da Allah na ne, bare ke da ki ke claiming ki na tsoran tsinuwar Allah na ga ai kina make up once in a while, kuma in za a zana mi ki gira sai an aske...." "Auzubillallah! Allah ya tsare ni da aske gira, ban taba ba, kuma ba zan taba ba in Sha Allah" Halitta ta katse ta. Komawa ta yi, ta yi irin wannan kwanciyar ta rigingine, ta na duban Halitta ta ce "An yi rashin sa'a ban sami wanda su ka iya permanent one ba ne, wannan iyakan sa shekara daya, Amma ya na gogewa zan fita US a yi min permanent, after all jiki na ne ba naki ba, oya me ma ya kawo ki daki na?" Shanye bakin cikin da ya taso mata cikin ranta ta yi, wayyar ta ta daga mata, nan hotan nan ya bayyana a idanun Zainab, Halitta ta ce "Wannan wani irin shiga ne Yakura? Yanzu har kya iya zama cikin maza da wannan shigar ta ki? Har ki dauka ki sa a social media? Kuma ki na busa hayaki Yakura! You smoke? You are smoking in the picture! Me mutane za su yi tunani akan Dady muddun su ka san ke diyar shi ce?" Zainab na kallan ta irin kallan nan na hadarin kaji ta ce "Wai ke Haliita ba za ki fita harka ta ba? It's my life, my personal life! Ko kin ga na sa sunan Dady jikin sunana? Ina ruwan Dady da rayuwa ta a waje? Cikin gida na ke diyar sa, ina shiga irin wanda ya ke so a cikin gida in da ya ke gani na, ina masa ladabi da biyayya and he is satisfied! a school da social media I'm the person I chose to be, I don't use his name! mahaifina kenan bare ke da kike kanwa ta! Dan Allah ki fita harka ta Halitta!!" Ta dan tsagaita ta na mai jan wayar ta, Instagram ta shiga ta dubo sunan Halitta, ta ce "Alright ga shi nan na yi unfollowing din ki, I expect you to do the same in dai ke ba mayya ba ce! Wannan masifar har ina!" Ran Halitta idan yayi dubu ya baci, cikin zafin rai take kallan Zainab, ta ce "Ki tuba Yakura! Ko dan darajar mahaifin mu ki tuba, kuma ki sani idan babu mutuwa akwai tsufa, ke mace ce, Rayuwar diya mace kalilan ce, Me za ki ce da 'ya'ya duk randa su ka wayi gari aka yi musu nuni da wannan hoto aka ce ke mahaifiyar su ce? Da wani ido za ki kalle su?......" "Get out of my room! Ba na bukatar wa'azin ki, ki bari sai Dady ya hau mambari ki ja masa baki! Nonsense!" Ta katse ta cike da masifa. Jiki sanyaye Halitta ta juya, ko da ta kai kofa sai ta sake juyowa ta da dubi Zainab da ke kallan ta kamar zakanya, ta ce "Ba zan fasa mi ki wa'azi ba Yakura, ba zan fasa mi ki addua ba, Allah ya shirye ki" "Mtswww" Amsar Zainab kenan, yayin da ta tashi ta rufe kofarta da key bayan fitar Halitta. Idan ran ta yayi dubu ya baci dan kuwa a rayuwar ta ta tsani sa ido, gani ta ke duk duniya babu wanda ya sa mata ido kamar Halitta, shi ya sa ma sam ba sa shiri. *Khadija Sidi* AUREN SHEHU 3 Ta na zama bisa gado ta ɗau wayarta ta kira abokin zuwa club din ta da ta ke kira Bobo, bugu daya ya daga tare da faɗin "Zeee oh Zeee the slay mama the club mama, diyar Malam ta ki halin Malam! Ai ni na san baki fushi Zeeena....." "Eh en fa Bobo!" Ta katse shi, ba ta gushe ba ta kara da " Kar ka wani dame ni da dadin baki! Da ka san masifar da ka kusa jawo min jiya da ka ji tsoran ɗaga waya ta!" "Toh yanzu dai Allah ya baki hakuri, ko da ya ke tun da ki ka kira ni ma na san kin huce, wetin dey sup? Malam don commot?" Cewar Bobo cikin muryar zolaya. "Ehen na, him don go Maid, toh ya za a yi? Any happening tonight? Amma dan Allah kar ka kai ni club din talakawa, ka san I can't stand them!" Ta fada ta na mai yamutsa fuska. Dariyar kyeta ya saki, fadi ya ke "Heheheheh Zeeena na daɗe ban ga wanda ya ke kyamkyamin talauci kamar ki ba, babe don't worry I got you, ki shirya 12 daidai ta yi mi ki gaban gate din ku, na san dai yau ba batun haurawa tunda Malam baya nan" "Ba ka da matsala, su Isa ne ai wa'inan, in su ka sa shayi gaba har na wuce ma ba lalle su sani ba, sai ka zo" Ta na maganar ne yayinda Usman ya fado mata rai, ta na mai adduar Allah ya mata katangar karfe da shi, su ka yi sallama da Bobo ta aje wayar. *** Kamar yanda ta saba duk sanda ta san ta kulla harkallar ta, ana isha'i ta fara kukan ciwon kai, daga Ammy har Falmat babu wanda ya kawo wani abu cikin ran su, sai ma tararraya ta da su ka din ga yi, musammam ma Ammy. Halitta kuwa ko kallan in da take ba ta yi, dan cike fal ta ke da Zainab. Ammy ce ta bata magani ta sha, ta ce lalle ta je ta kwanta, amma Zainab ta ce ah ah, gwara ta zauna jikin su za ta fi jin dadi. Sai da ta bari goma da rabi yayi sannan ta ce ciwan ya ci karfin ta, bari ta kwanta dan Allah kada wanda ya shigo ya tada ita, dan idan aka tada ita ba lallai ta iya komawa bacci ba, gashi kuma dama ciwon kai ta ke. Ana bin ta da sannu haka ta mu su sallama, ta koma daki ta yi kwanciyar ta har da kashe wuta. Da ya ke uwa uwa ce wajen sha daya Ammy ta kasa hakuri, sai ga ta a dakin, ganin wutan a kashe ya sanya ta yin sanda zuwa ga gadon Zainab, wacce jin shigowar uwar ta saki jiki ta yi lum kamar mai bacci. Hannun ta dora bisa goshin Zainab ta na mai hamadala, fadi ta ke "Alhamdulillah ta sami bacci" Ta na mai jawo bargo ta dada rufe ta. Sai da ta karanta mata adduar bacci ta shefa jikin ta sannan ta juya ta fita. Ta na fita Zainab ta yi zumbur ta mike, dan kuwa ta san babu mahalukin da zai sake shigo mata daki tunda har Ammy ta ga ta yi bacci, bari ma kuwa idan akwai wacce za ta iya shigo mata munafunci Halitta ce, ita kuma sun yi fada toh ta tabbatar hakan ta ya cimma ruwa. Wankan ta tayi ta fito tsaf cikin wondan ta pencil Jean blue tare da yar karamar riga ja, ta faka gashin nan tsakiyar ka kai ka ce ba diyar musulmai ba ce. Ba ta damu da yin make up, dan irin su Zainab ake yiwa kirari da "black beauty better than gold always shining". Tsadaddiyar powder mai sanya fuska sheki ta shafa, turaruka kuwa 212 sexy, escada magnetism, tare da Indian night Jasmine sai da su ka koka. Gaban madubi ta tsaya ta na mai karkada kugu ta ke yiwa kan ta kirari "Zeee oh Zeee the slay mama, the club mama, kuma salihar Dadyn ta" Sai da ta yi mai isar ta, ganin sha biyu ta kusa ta sanya hijabi har kasa, bayan ta gama gyara gado, ta saita fululluka kai kace mutum ne kwance ta sa bargo ta rufa mu su, takalmin ta mai tsinin gaske a hannun ta na mai sanda ta fito. Ganin wutan falon a kashe ta san kowa ya kwanta, sadaf sadaf ta zaga ta baya ta fice. Isa kuwa da Jauro masu gadin gidan nan gaban gate su ke kwance bacci ya sace su dan yau ko karnukan gidan ba su sake ba. Kallo ɗaya Zainab ta mu su ta ja tsaki tare da fadin " Ji be su kwance kamar mushe! Idan ma sace gidan za a yi wato a yi tunda Dady bayanan, Allah ya kai mu gobe za ku yiwa Ammy bayani!" Ba ta kara tsorata ba sai da ta ga gate din bude, wato ko sakata ma ba su sa ba! Har ta juya a fusace za ta tada su, sai ta tuna tana tayar da su shikenan asirin ta ya tonu, ta na mai adduar Allah ya kare su Ammy ta sa kafa ta fita, hakan yayi daidai da dalle ta da tocilit da aka yi, yanda hasken ya dalle idanun ta ya sanya runtse idanun ta na mai fadin "Oh my God" Tsaye ya ke ya na duban ta, suna hira da su Isa bacci ya kwashe su, dan haka ya dan fita waje mike kafa. Kusan mitunan shi ishirin waje gaban gate, dake unguwar ba mai hayaniya bace sosai kafar mutane ya dan dauke, jin wani ni'imataccen kamshi ya sanya shi dan waige waige tare da tunanin ko dai aljana mai turare ce ta bakunce yau, wanda fitowar ta ya gasgata masa da haka, dan kuwa dai da ya haske ta ganin ta ya ke tamkar aljanar ce tsaye gaban shi. Ganin ba a da niyar daina haska ta ya sanya ta kare fuskar ta da tafin hannun ta, cike da nuna bacin rai ta ce "Dalla Bobo dena haska ni kafin ka sa a kama mu! Kai fa iskancin ka yawa gare shi!" Jin haka ya sanya shi kashe tocilan ba tare da ya iya furta komai ba, dan kuwa harshen sa ya sarke kamar wanda aka daure harshen cikin bakin sa. Bude idanun ta tayi tare da fadin "Bobo....." Ganin wanda ke tsaye gaban ta sai da ta dan ja da baya, shi din nan dai Usman, sanye da rigar saka da rawani irin na buzaye, hannun sa na dama rike da sandar gora, dayan hannun kuma tocilan ne. Ta na shirin juyawa ta koma sai ga motar Bobo, ai kuwa kafin Usman ya ankare da gudun ta ta nufi motar, ganin haka Bobo ya tsaya ta shige ta na fadin "Kai let's get the hell out of here, ina tsoran Allah ina tsoran wannan dan boko haram din can!" *Khadija Sidi*AUREN SHEHU 4.   Jin kalmar "Boko Haram" jiki na rawa Bobo ya figi motar ya na mai tayar da kura, fadi ya ke "How? Ya aka yi ki ka san dan Boko Haram ne?" Karar yanda Bobo ya figi motar ne ya sanya su Isa da Jauro fitowa a guje suna fadin "Su waye nan! A tare! A tare!" Ina sai sahun tayar motor Bobo su ka gani, idan shi kan shi Usman da ke tsaye kamar mutum mutumi Jauro ya ce "Yo kai ɗan cirani kana nan tsaye ashe, me ke faruwa ne?" Isa ya kara da "Wacce mota ce ta tashi a guje yanzu? Su waye?" Maimakon ya ba su amsa, sai ya juya abin sa yayi ciki, suna tafe bayan sa, su ka koma ciki, daki yayi wucewar sa ba tare da ya tanka mu su ba. Isa da Jauro su ka tsaya jugum jugum suna duban juna, Jauro ne ya gyara tsayuwa ya ce "Ina Isa? Ni fa Allah na gani ban yarda da wancan dan ciranin ba! Ga fa karar tashin motar da mu ka ji! Mu ka tashi mu ka ga gidan nan bude, shi kuma mu ka taras waje tsaye kamar gunki, Anya kuwa Isa?" Isa wanda kamar Jauro ya shiga ransa, ya dan yi ta maza ya dake, ya na mai yamutsa fuska ya ce "Anya kuwa me?" "Anya kuwa lafiyayyan mutum ne?" Jauro ya fada cike da damuwa. "Ka gan shi da wata rashin lafiya ne?" Cewar Isa cikin dakiya dan ya san in da Jauro ya dosa. Jauro na mai girgiza kai ya sake cewa "Ka san abin da na ke nufi Isa, dan kuwa na san kai ma zuciyar ka ta yi rawa akan lamarin Usman....." "Na raba ka Jauro, na raba ka! Kar ka manta Malam ya karantar da mu akan zato, ya ce zato zunubi ne ko da kowa ya kasance gaskiya, Ni ka ga tafiya ta kunto karnukan nan, da bacci be dauke mu ba ai duk da ba haka ba!" Isa ya tafi ya na mita, Amma cikin ransa tunanin da Jauro ya ke shi ma din shi ya addabi zuciyar sa. Usman kuwa can lambu ya shige in da ya saba raba dare, wata yar doguwar kujera ta hutawa ya samu yayi kwance idanun sa na kallan sararin samaniya. Kamanin Zainab ke masa gizo, haka kuma kan sa ya dada kullewa akan lamarin ta, "Shin ita wannan diyar Malam din ina za ta je da tsohon daren nan? Shin mahaifiyarta ta san da fitar ta? Shi wannan da ya ɗauke ta a bakar mota mai bakin gilashi wanene shi?' Tambayoyin da ya ke yi cikin ran sa ke, wanda ya kagu ya samu amsar su. Ita kuwa Zainab tun da su ka tafi Bobo ke tambayar ta ya aka yi ta san mutumin nan dan boko haram ne? Wanene shi? Sai da ta nutsu sannan ta iya amsa masa da "Daya daga cikin daliban Dady ne, kuma ya na mana gadi, haka kawai jinina be hadu da shi ba wallahi, ka ga jiya ma shi ya kama ni, gashi yau ma an kuma! Allah dai ya tushe bakin sa...." "Wa ya ce mi ki dan boko haram ne?" Bobo ya sake tambaya cike da damuwa. "Haaaaa'a! Are you even listening?" Zainab ta fada cike da tsiwa, ba ta gushe ba ta kara da "Dallah waye zai yarda dan boko haram ya zauna gidan su? Na ce da kai dalibin Dady ne!" "Toh Zeeee ke ce na ji kin kira shi da boko haram....." "Saboda ya na min kama da su ba! Ba wai ina nufin shi din ba ne, ko da ya ke it's possible shi din ne tunda ba wai kwakkwarar bincike aka yi ba...." Ta fada ta na kallan Bobo wanda ya fara hada zufa. Dariya ne ya kwace mata, ta ce "Sai shegen tsora, dallah wasa na ke ma" Bobo na mai goge zufa da hankaci ya ce "Ai dai mutanan ne abun tsoro, Allah ya mana tsari da su, mugu be da kama Zee" Cikin faduwar gaba yayin da kamannin Usman su ka bayyana a zuciyar ta, ya fito mata sak a kamannin mugu, ta na mai saurin kawar da tunanin ta ce "Amen, Allah ya min tsari da shi!" "Wa fa?" "Dan Boko haram mana, Maigadin gidan mu!" Ta fada kai tsaye. "Ki ka ce ba dan boko haram ba ne?" Bobo ya sake tambaya cike da damuwa. "Aaaarrrrghhhh Bobo don't spoil my mood!" Ta fada cikin tsawa. Hannun ya daka tare da fadin "Allah ya baki hakuri Zeee Mama!" "Ba Allah ya ba ni hakuri ba, you better take me to a nice club!" "I got you, kafin nan bari na baki sauti mai dadi" Cewar Bobo yayinda kunna waka ya na mai kure karar. Ranar club yayi ma Zainab dadi, ta hadu da sabon saurayi wanda tare su ka cashe a daren ranar har ta shagala da lokaci, dan kuwa dai ba ita ta ankara ba sai da shida ta wuce. A kidime ta azalzali Bobo wanda ta janyo shi tsakiyar kedaru su na cashewa. Sabon saurayin da ya Kira kan sa Mike ne ya nuna dacewar ya aje ta gida, hakan ba karamin dadi yayiwa Bobo ba, amma Zainab ta hana, ta dai ce ya bari sa yi magana daga baya. Haka su ka yi sallama Bobo na mitar ta katse masa shagali su ka dauki hanyar gida. Dab da za su shiga unguwar ya kalle ta ya ce "Babe kin katse min runs wallahi" "Mtswww" Ta ja tsaki ba tare da tanka ma sa ba, gaba daya hankalin ta ba ya tare da ita, shikenan yau kam asirinta ya tono, tun da take zuwa club ba ta taba kaiwa haka a waje ba, har a idar da sallar asuba ba ta koma gida ba? shin me za ta ce da Ammy idan har ta shiga dakin ta tashin ta sallar asuba ta ga ba ta dakin? Ya ma za ta yi ta shiga gida gari waye haka babu daman ta haura? Kuma ta san su Isa da Jauro ba lalle sun bude gidan ba in ba dai dan boko haram din nan ya kwana nan in da ta barshi tsaye ba ne, wanda ko jikin ta kunne ne ta san ba abu ba ne mai yiyuwa ba, kila ma ya riga ya fadawa Ammy fitar ta..... Tsigar jikin ta ne ya tashi yayinda gaban ta yayi mummunar faduwa, a zahiri kuma fadi ta ke "Ya Ilahi....." "Kai Zeeena ashe kin iya ambaton Allah!" Cewar Bobo cike da zolaye. Harara ta watsa masa, tare da fadin "Dadi na da kai Bobo rashin sanin ciwon kai! Ba ka ga halin da na ke ciki ba ne wai?" Dariya ya ke yayin da ya sami waje ya faka, suna hango gidan Malam ya ce "Come na, stop panicking! Kwantar da hankalin ki babe, calm down, ki fita ki je gate din gidan ku, idan bude ya ke ki shigewar ki kai tsaye, ba kya bin masu gadin ku bashin bayani, idan rufe ya ke ki buga mu su su bude mi ki, gidan uban ki ne, idan Momcy ta gan ki tell her kin fita exercises ne, shikenan!" "Yen yen yen yen! Ni na rasa yanda aka yi na ke mu'amala da kai Bobo! Duk randa na fita da kai sai ka jawo min matsala!" Ta na gama fadin haka ta fice a fusace tare da buga masa murfin mota. Zuciyar ta na bugu ko wani taku ta yi, wayar Halitta ta shiga kira, ta yi ringing ta gama ba ta daga ba, hannu na rawa ta kira Falmat, ita ma din ba ta daga ba, isar ta gate din ta dan tura ta ji a rufe, sai da ta dan yi jim sannan ta yi karfin halin bugawa. Har ta fitar da rai da bude gate din, ta na shirin juyawa sai ta ga an bude hujun da aka yi jikin gate din domin ganin na waje. Idanun ta ta tsinta cikin na sa, tuni ta tsinci kanta cikin mummunar faduwar gaba, yayin da bugun zuciyar ta ya karu, sai da yayi sakanni ya na kallan ta, ta na mai cuna kumatu cike da tsiwa ta ke mayar masa da martanin kallan, dan kuwa tsoro baya hana Zainab rashin kunya.. "Malam dalla ka bude min gate! Ka zuba min na mujiya ba ka taba ganina ba ne?" Ga mamakin ta sai kuwa ya bude, shigar nan dai da ta gan shi da ita jiya da daddare, shi ne jikin sa, Goran nan dai be aje ba, ta na rike hannun sa na hagu, hannun sa na dama kuma ruke da rediyo ya na jin labarai. Ko kallan sa ba ta kara yarda ta yi ba, bare su hada idanu kai tsaye ta wuce ciki kamar dai yanda Bobo ya ce ta yi, addua ta ke Allah ya rufa mata asiri kar ta hadu da Isa ko Jauro, sa'ar da ta yi da an idar da sallar asubahi su ke komawa su yi baccin su tun zuwa Usman gidan, shi kadai su ke bari da gadin safe, karnuka kuwa ana kiran sallar farko ake daure su, saboda kar su dami masu sallah masallacin gidan da haushi, duk da dai ta waje masallacin ya ke. Sai da ta kurewa ganin sa, zuciyar sa cike da tunani kalala wanda duk yanda ya so ya cire daga zuciyar sa ya gagara, ya mayar da gate ya rufe. "Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun! Babu shakka Allah ya jarabci Malam da diya kamar yanda ya ke jarafta salihan bayin sa cikin ikon sa! Ya Allah ka kare Malam daga sharrin wannan Bingel!" Cewar shi a zahiri, yayinda ya koma mazaunin shi bisa benci, ya kishingida ya na mai cigaba da sauraron labaran shi a tashar BBC hausa. Cikin sanda takalman ta a hannu ta ke tafiya, ta kitchen ta bi ta shiga falon, dab da zata karasa dakin ta muryar Halitta ya daki kunnan ta "Yakura daga ina ki ke?" Jiki na rawa ta saki takalman su ka zubi kasa, Kallan Halitta ta ke ta na mai waige waige ta ga ko ita kaidai ce. Ita kadai din ce sanye cikin hijab har kasa, hannun ta ruke ta carbi dan Halitta ba ta komawa bacci bayan sallar asuba, zama ta ke ta yi zikiri da adduo'i har gari ya waye rana ta fito, sannan ta shiga kitchen ta taya iya abin karin kumallo. Ta fito za ta kitchen din kenan su ka yi kacibus da Zainab ta na sanda za ta shige dakin ta. *khadija sidi* AUREN SHEHU 5.   Wani irin sassanyar ajiyar zuciya ta saki, ta na mai duban Halitta murya kasa kasa ta ce "daga ina na ke kuwa? Dage exercise mana!" "Exercise din tun karfe 4:45 na dare Yakura? Ki ji tsoran Allah! Ammy ta turo ni tashin ki sallah Yakura, na san ba gidan nan ki ka kwana ba, daga ina ki ke?" Halitta ta kara tambaya ta na mai tsare ta da idanu. "Daga yawon ta zubar na ke ko da yanda za ki iya ne? Ki na da abin yi ne? Kuma Allah ya mana katangar karfe da saidawa!" Kafin Halitta ta bata amsa ta yi saurin kwasar takalman ta, ta yi wuf ta shige dakin ta. Jim ta yi ta na maimaita kalaman Zainab cikin ran ta "Daga yawon ta zubar na ke......" Ta kara maimaita. "Shin anya kuwa shirun nan da na ke akan abin da Yakura ta ke yi Allah ba zai tambaye ni ba? Ko dai Ammy zan fadawa? Ko da ya ke in har na fadawa Ammy kamar na fadawa Dady ne, Allah kadai ya san halin da Dady zai shiga muddin ya sani, Allah ka ga zuciya ta, Allah ka mana magani" Kitchen ta wuce, ganin Iya har lokacin ba ta fito ba sai ta wuce dakin Iya domin ta ga ko lafiya. Zainab kuwa ta na shiga bandaki ta shige ta yi wanka, fitowar ta daga wanka ta tarar Ammy tsaye tsakar dakin, abin ku da mara gaskiya sai da zuciyar ta ta dan yi rawa. Ta na kame kame ta ce "Ammy, aw ashe ke ce" "Ni ce jiki yayi sauki kenan, ai na turo Halitta ta tashe ki sallah da asuba...." "Eh mun hadu ai" Ta yi saurin katse ta. Kallon ta Ammy ta ke kamar mai nazari, kafin daga bisani ta ce "Me ki ke cewa ne? Kamar yaya kun hadu?" Zainab na mai sosa kyeya ta ce "Ah ah ina nufin na gan ta, da ta zo tashi na, eh ta tashe ni din" "Oh toh, Ni ce min ta yi ba ta gan ki ba, ta na tunanin kin tashi tuni har kin shiga toilet" "Eh ai ina toilet din na jiyo shigowar ta, haka na ke nufi Ammy" Kai Ammy ta gyada, sa'annan ta kara da "Ya ciwon kai?" "Ciwon kai? Aw Alhamdulillah na sami sauki, Ina kwana Ammy?" Cewar Zainab yayin da ta zauna bakin gado, Allah Allah ta ke Ammy ta fita ko ta samu gaban ta ya bar faduwa. "Lafiya lau Alhamdulillah, ashe ba mu gaisa ba, Allah ya kara sauki, sai ki yi maza ki fito mu karya ko? "Wallahi Ammy ba zan iya cin abinci yanzu ba, wani irin bacci na ke ji, rabona da bacci tun jiya da safe, kin san bacci ba a cin bashin sa " Ta na mai duban ta cikin nazari ta ce "Wannan baccin na ki kuwa anya Yakura? Me ya hana ki bacci? Nan fa na shigo na tarar ki na ta bacci?" "Ah ah, wai ina nufin ban yi ishasshe ba, ina yi ina tashi saboda ciwan kai" "Toh Allah ya sauke, ki daure dai ki ci wani abu kafin ki kwanta" Zainab ta amsa mata da toh, dan dai kuwa ba ta da buri da ya wuce Ammy ta fita ta samu ta ji hakarkarin ta bisa katifa. Illai kuwa ta na fita ko mai ba ta iya shafawa, ta dauko wata yar riga iya gwiwa ta sanya, ba batun sallar asubahi ta bi lafiyan gado abin ta. Nan da nan bacci ya dauke ta. *** Haka rayuwa ta cigaba da gudana. Zainab ta kasa hakura da club ta bari sai ta koma makaranta kamar yanda ta saba, saboda sabon saurayin ta Mike, shi ne ke zuwa daukar ta ya dawo da ita. Ba komai ne ya bata lasisin wannan shagalin na ta ba face shawarar Mike da ta bi na siye daya daga cikin masu gadin gidan. Cikin masu gadin uku ta san Isa da tsattsauran ra'ayi ko da wasa ba zai amince da ita ba, Usman kuwa shi tsoran sa ma ta ke ji, dan haka sai ta kama Jauro ta rike gam. A kulli yaumin ta kan tabbatar ta masa alkhari na safe daban na yamma da daban, ta haka ta samo hanyar shawo kan sa. Ta masa karyar cewa akwai kungiyar bitan karatu da su ka hada ne ita da yan makarantar su da ke zaune Kano, kafin su koma makaranta, Amma da daddare ake yi, ta na tsoran kar ta fadawa su Ammy ne su hana ta gabadaya, shi ya sa ta yanke hukuncin ta na bi ta bayan kasa, har su koma makaranta. Duk da Jauro ya san maganar Zainab yashesshen zance ne, da ke ido a kabo ne da ta bashi sai ya sa hannu ya karfe, idan dare yayi sai ya tabbatar Usman da Isa ba sa kusa sai ya bude mata kofa, haka idan ta dawo shi ne ke bude mata. Duk wannan hidimar da ya ke yi akan idanun Usman, tun ya na ɗauke kai har ya gaji wata ranar Juma'a da yamma, ana saura sati daya Malam ya dawo Usman ya sami Jauro kishingide karkashin bishiya ya na shan rake, dan kuwa tunda Zainab ta fara bashi kudi kullum cikin kudi ya ke. Sallama ya masa tare da zama kusa da shi. Tayin rake Jauro ya masa bayan ya amsa sallamar. Usman na mai godiya, cikin maganar sa mai cike da nutsuwa, yanayin yanda ya ke fito da kalmomin hausa daga bakin sa ne ki kara jaddada kasancewar sa na kabilar fulani, ya ce "Alhamdulillah, na gode Jauro ka sha raken ka, dama akwai yar magana da na ke so mu yi da kai" "Toh Madallah dan cirani, da me ka zo" Cewar Jauro bai fasa shan raken sa ba. Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani Usman ya ce "Ka yi hakuri zan ma ka shisshigi, wala'alla za ka fahimce ni" Jauro na mai fuzar da totuwar rake daga bakin sa ya ce "Uhum, ina sauraron ka. "Zancen fitar dare da Bingel din nan ke yi, diyar wajan Malam" Cikin halin ko in kula Jauro ya ce "Uhum? Menene na ka a ciki?" "Akwai, Malam ya ba mu gadin gidan sa bisa amana, ni da na ke gani ina dauke kai ba tare da fadawa mahaifan ta ba, ina da alhaki, bare kai kuma da ka ke ba da gudunmawa Jauro!" Jauro na mai tashi zaune ya ce "oho! Ashe dai ka na gani, kuma ka san ka na da alhaki! Tun da ka ke gani ba ka san ka na da alhaki ba sai yanzu da ka ga ina dan samu ko fillo? Ni za ka yiwa halin na ku na fulanin daji ko? Dan bakin ciki!" Usman na mai dafe kai ya ce "Ya ilahi! Ba ka fahimce ni ba Jauro! Ba dan komai ya sa ban iya fuskantar Malam akan wannan batun ba sai dai dan kunya da nauyin sa da na ke ji! Da wani ido ko baki zan iya kallan Malam na ce masa diyar sa na haura katanga? Ko kuma duk dare ana zuwa ana daukar ta? A dawo da ita da safe?" "Dan sa ido! Da Idon da bakin da ka zo ka tinkare ni yanzu mana! Yarinya na fita bitar digiri(Degree) din da ta ke yi a jami'a, ko da yake kai fa ko zo na kashe ka da turanci ba ka sani ba bare ka san kalmar Degree! Kai Allah dai ya raba mu da jahilci!" Duk zuciya irin na Usman sai ya tsinci kan sa ya na mai murmusawa, ka na ya ce "Ban da cin fuska mana Malam Jauro, na zaci za mu iya samin fahimtar juna shi ya sa ma na tunkare ka da maganar, amma tun da abin haka ne, Allah ya ba ka hakuri!" "Ni kuma na taimaka da Aameen! Eh amen, kuma Allah ya raba mu da munafukai da yan bakin ciki" Usman na murmushi ya amsa da amen, tashi yayi tare da yiwa Jauro sallama duk da dai be ji dadin yanda Jauro ya kasa fahimtar ta shi, sam be ruke shi a rai ba, shi dai fatan sa Allah ya bashi ikon kawo karshen wannan masifar da ke faruwa gidan Malam, duk da kamar yanda Jauro ya fada be san "digiri" ba, Amma koma menene wannan digirin in dai haka ake yin sa toh lalle ba alkhairi ba ne. *** In da Usman ke kokarin neman mafita akan iftilakin da ke faruwa gidan Malam, ita kuma Halita soyayyar Usman ce ta sami wajan zama cikin zuciyar ta. Zaune su ke a falo, sun gama cin abinci kenan su ka zauna zaman hira. Falmat sanye da atamfa koriya dinkin doguwar riga, Halita kuwa kananan kaya ne cikin ta, riga da sikit jajaye, kanta daure da jan mayafi. "Ni kuwa Halitta ina mamakin yanda ki ke kaunar Usman din nan, dan kuwa dai sai dai na kira shi kauna dan ya fi karfin so" Cewar Falmat yayinda yanayin fuskar ta ke gasgata lafazan ta. Sanyayyar ajiyar zuciya Halitta ta saki kafin ta ce "Daga Allah ne Falmat, Ni dai kawai ki taya ni addua" "Toh zan taya ki, Amma duk randa Ammy ta san Usman ki ke so Halitta, I mean not just Usman o, but Maigadin gidan nan wallahi akwai kura...." "Shhhhh" Halitta ta katse ta, ta na mai kasa da murya ta ce "Ke fa matsala ta da ke Falmat handsfree! Ki rufa min asiri kar Yakura ta ji....." "Ji kuma na nawa?" Da sauri su ka juya su na kallon ta, ba wanda ya san da shigowar ta bare ya san adadin mintunan da ta yi tsaye ta na sauraran su. Sanye ta ke cikin bakin material, doguwar riga ta yi daurin nan da ake Kira tura ka tsiya. Idanun ta kan Halitta wacce har ga Allah ba ta so maganar ya je kunnan ta ba ta ce "Yanzu ke Halitta ki rasa wanda za ki so sai wannan Maigadin? Yo to menene abin so a wannan kazamin bafulatanin hammata fal gashi?" In da Halitta ta fusata, ita kuwa Falmat mamakin yanda aka yi Zainab ta ga hammatar, ba ta san sanda dariya ta kwace mata ba, wanda hakan ba karamin tunzura Halitta yayi ba. Yakura ba ta gushe ba ta kara "Ke anya kuwa bakin wannan ya san brush? As in kafin na so mutum I first imagine things people do when they're in love, as in can you imagine yourself with him? Like imagine kissing wannan dagageggen bakin na shi?" "Wayyo Allah Ammy!" Falmat ce ta saka ihu ta na mai dariyar mugunta, ita kuwa Halitta iya kulewa ta kule. A fusace ta ce "Malama ina ruwan ki? Kin manta ba kiss ba! Abin da ya fi kiss! Idan ma auren shi na ce zan yi ina ruwan ki!" Ta na mai daga hannu sama yayinda ta zagaya ta shigo falon sosai, kujerar da ke kusa da Falmat ta zauna, sannan ta ce "Babu fa, babu ruwa na ko kadan, aw kin san abin da ya fi kiss ashe, yo ai na zaci uztazanci ya hana ki sani, Sha it's your life, Bari na ja baki na!" "Alhamdulillah tunda kin san haka, da fatan za ki yi aiki da shi...." "Ke fa ba kunya gare ki ba Halitta!" Zainab ta katse ta cikin tsawa, ta kara da "Kar ki ga kin yi tsayin kafa wallahi ina iya doke ki, mara kunya fitsararriya" "Toh sarkin tsiwa! Tun daga daki na ke jiyo hayanoyar ku! Anya kuwa Yakura? Ke da waye kuma?" Ammy ce wacce ihun Falmat ya sanya ta fito da sauri ta ke tambaya. "Babu komai Ammy" Halitta ta fada gudun kar Yakura ta mata tunan asiri, ilekuwa sai cewa ta yi "Da komai fa Ammy, ai dai gaban ki yarinyar nan ta gama azazzabi da rawan jiki wajan jaddada bayani akan wannan dan bokon haram din, toh dai ruwa ba ya tsami banza, ga shi nan na ji tana managanar son shi ya kamata..." Ta karasa maganar ta na yar dariya tare da girgiza kai. Daga Falmat har Halitta mutuwar zaune su ka yi, sun san Zainab da barin zance amma ba su taba zatan za ta tonawa Halitta asiri hakan nan kara zube ba. Ammy na dariyar yake ta ce "Ke kuwa Yakura ba dai zolaya ba, ina Halitta ina kula wani da namiji? Har kuma ki ce Maigadi? No wonder na jiyo ku tun daga daki, ah ah ni ma ban goyi bayan wannan wasan ba!" "Atoh Ammy ke dai kya fada" Cewar Falmat ta na mai fatan rufe asirin Halitta. Zainab kuwa ba ta damu da irin sakon da Halitta ke aika mata ta ido ba, sake cewa ta yi "Wallahi Ammy ba wasa na ke ba, Halitta soyayya ta ke da Maigadin gidan nan" "Lailaha ilallahu Muhammad a rasulillahi!" Cewar Ammy ta na mai tafa hannu cikin tashin hankali ta ke duban Halitta wacce ita ma din kallo daya za ka mata ka tabbatar da damuwan da ta shiga. "Halitta me na ke ji haka? Wannan wani irin mummunar labari na ke ji Halitta? Duka tarbiya, kulawa da soyayyar da mu ke baki abin da za ki saka mana da shi kenan Halitta?" Tuni hawaye ya shiga fita daga idanun Halitta, ta na girgiza kai ta ke fadin "Ah ah Ammy, wallahi ba haka ba ne Ammy...." Cikin bambami Ammy ta ce "Ba haka ba ne uban ki ne? Yi min shiru! Wallahi kin ba ni kunya kin yi asara Halitta! Yanzu idan Malam ya ji wannan tozarcin da cin amana ya ki ke tunanin zai ji. Dama aka ce tsintacciyar mage ba ta mage! Hakan nan mutum daga sama ya zo gidan ka ka karbe shi har da bashi wajan kwana, gashi nan zai masa sakayya ta hanyar hure ma diyar sa kunne ai! Toh kuwa zaman shi a gidan nan ya zo karshe" Jin Ammy na batun zai bar gidan wani dadi ne ya mamaye Zainab, dan kuwa burin ta ke nan. "Atoh ai tun da na fara ganin sa na san ba za a wanye lafiya ba, na yi magana a ce na fiya kyaman yan kauye, ga dai irin ta nan!" Cewar Zainab ta na mai daga kafada tare da saukewa. Falmat ce ta saka baki ta ce "Ammy ba ki fahimta ba, wallahi ba haka ba ne, shi wannan bawan Allah sam be ma san da Halitta ba, bare ma ya hure mata kunne, ba soyayya su ke ba, kawai dai Halitta na yawan maganar sa ne ya sa ke tsokanar ta da shi, Amma babu komai tsakanin su Ammy!" "Ki ji wani yashesahen zance idan babu rami me ya kawo rami?" Ammy ta tambaya a fusace, in da Zainab ta taya ta da atoh. Halitta kuwa ta ma kasa magana sai hawayen takaici da ge gangarowa daga idanun ta. "Allah Ammy gaskiya na ke fada mi ki, in kuma ya kama a kira shi ne ki tambaye shi ki kira shi Ammy" Shiru ne ya biyo baya na dan sakanni, Zainab sai adduar Allah ya sa kar Ammy ta yarda da zancen Falmat ta ke cikin zuciyar ta. Jin abin da Ammy ke fadi ne ya sanya ran Zainab yin baki. Tana mai ajiyar zuci ta ke fadin "Toh ni fa in ce, jinina ba za ta taba san Maigadi mara asali ba, haba har na dan ji sanyi cikin rai na, toh wallahi kar na sake jin maganar nan ko da wasa!" Ta na mai duban Halitta ta kara da "Ke kuma Halitta na kara jin maganar Maigadin nan bakin ki sai na sabar mi ki" Kai Halitta ta gyada kafin ta tashi ta fice da ga falon, dan kuwa gani ta ke muddin ta cigaba da zama zafin rai zai sa ta iya tonawa Zainab asiri akan yawan daren da ta ke, ita kuwa ba ta so ta biye mata garin ramuwar gayya su jawa mahaifiyar su matsalar hawan jini. Ta na jiyo Zainab na cigaba da sukar zaman Usaman a gidan. Ita kuwa Falmat mamakin yanda Zainab ta hakikance ta na bata Usman da karya da gaskiya wajan Ammy, har ta kai ga ta na tunanin shin me ya taba hada su ta ke masa wannan tsana haka? Duk yanda ta so a kori Usman a gidan, ranar haƙon ta ya kasa cimma ruwa, duk da dai ta ci nasarar tusawa Ammy kiyayyar sa cikin zuciyar ta, ko ba komai yau da gobe in dai Ammy ta tsane shi tabbas sai zaman gidan ya gagare shi. Ta sha alwashin sai ta san yanda za ta yi ta sa Malam ya kori Usman daga gidan. **** Ana sauran kwana biyu Malam ya dawo Kano, haka kuma wata daya ya rage a fara azumin watan ramadan, bayan sun idar da sallar isha'i gidan Malam da ke Maiduguri, Malam ya karbi bakwancin aminin shi, Shiek Ahmad Suraj. Kamar yanda Malam ya ke babban Malami haka ma Shiek Ahmad ya ke sananne a cikin garin Maiduguri, ba dan malamtakan sa kadai ba, har dama tarin dukiya da Allah ya ba shi. Duk da dai shi asalin sa dan Chad ne. Ba karamin farin ciki masa tarba na ban girma kamar yanda ya saba masa duk sanda ya zo. Babban Falon Malam su ke zaune, falo ne ya kayatu kwaran gaske. Bayan sun gaisa tare da hirar bayan saduwa, Shiek Ahmad ya ce "Ya Shiek dan wajan ka Sudais fa ya hada karatu, mu na sa ran dawowar shi gida Nigeria farkon shauwal da an kammala azumi" Malam na mai washe baki ya furta "Toh Alhamdulillah, ka ce Sudais ya zama cikakken likita, kuma mahaddaci wannan labari abin alfahari ne, Allah ya masa albarka, ya albarkaci ilimin da aka samu, ya sa a yi aiki da shi, ya kawo abokiyar rayuwa ta gari" "Allahumma amen, abokiyar zaman kuwa Ya Shiek gidan ka na ke so a samu, dan kuwa sami 'ya'ya masu tarbiya irin 'ya'yan ka mata sai an duba akaramallah" Cewar Shiek Ahmad wanda ke maganar har cikin ran sa da zuciya daya. Hakan ya sanya farin ciki bayyana a fuskar Malam, idanun sa har sheki su ke, ya na mai ruko hannun Shiek Ahmad ya ce "Jazakallahu khair, jazakallahu khair, jazakallahu bi jannah da wannan sheda ta ka Shiek, Ni kuwa na maka alkawarin bawa Sudais diya ta mafi soyuwa a rai na, cikin su tafi kuwa nutsuwa, ga ladabi da biyayya, ga rukon addini, ga kunya, ga...ga...ga....sai Zainab! Ta na aji uku a matakin karatun jami'a, in da take karantar Microbiology anan American university of nigeria da ke Yola" Cikin gamsuwa da jin dadi Shiek Ahmad ya ce "Madallah da wannan diya da ta sami shaida mafi daraja daga wajan mahaifin ta, muna so" Malam na mai murmushi ya ce "An ba ku" Hannun Malam Shiek ya rike cikin musabaha ya ce "Mun karba, mun gode, Allah ya saka da alkhairi, in Sha Allah da yaron nan ya dawo sai a turo a sa ranar daurin auren ko?" "Su waye za su saka rana da ya wuce mu? Ai kawai tsaya ka gani ya Shiek" Malam ya dauko calendar ya na dubawa, ranar Juma'a ya zagaye wanda ya kama shabiyu ga watan juli Malam ya ce "Ga rana nan duba ka ga, idan har ya maka, sai mu yi fatan Allah ya kai mu da rai da lafiya" Shiek Ahmad na duba calendar da Malam ya nuna masa ya ce "Hamdan ya yi Ya Shiek, Allah ya nuna mana da rai da lafiya" Malam ya amsa da Allahumma amen. *khadija sidi* AUREN SHEHU Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun, mu na mika ta'aziyar mu ga Sis Aysha, Allah ya mata rahama, Allah ya gafarta mana, Allah ya sa ta huta, ya albarkaci bayan ta. Allahumma amen 7. Majalisar tasu wacce ta ke kusa da gidan Malam ya isa, Ya tarar ta cika yanda ya so, Dan haka zuciyar sa wasai ya ce "Na zo da labari da ɗumi ɗumi, wannan jaridar sabuwa ce kal!" Cikin kaguwa su ji labarin daga me cewa "Siyar mana" Sai wanda ya ce "Ba mu mu sha" Sai da ya sami waje ya zauna, cikin nuna gwaninta ya ce "Yau da ido na na ga mace ta hauro daga gidan Malam........." "Ahab! Toh wannan sabon abu ne? Har wani labari da dumi dumi? Toh ai idan wanan ne na sha gani malam!" Daya daga cikin samarin ya katse shi. Uku da ga cikin su da sam ba su taba ji bare su gani ba kuwa baki su ka ruke, cike da mamaki guda ya ce "Kai Uzairu ka ji tsoran Allah! Da kai ma Khalifa! Gidan Malam fa ka ce! Wannan ya tashi daga karya sai dai a kira shi kazafi!" "Mtsw kai ne a gun ka sabo, kai Uzairu fada mana sabon abu ba wannan ba Alhaji" Cewar daya daga cikin samarin da shi dama ya taba gani shi ma. Shi kuwa Uzairu da ya kawo gulma gwiwar sa ce ta yi sanyi, dan kuwa sun sace masa gwiwa, cikin so ya burge ya ce "Ba nan kawai abin ya tsaya ba, wani namiji ne ya ruko kugun ta, gaban ido na su ke ta badala, tun suna daga waje har su ka shige mota, Allah ya kadai ya san me su ke aikatawa ciki dan kuwa gilashin baki ne wuluk...." "Kai auzubillallah ko ma wacece wannan ba ta da ala'aka da Malam! Ba jinin Malam ba ce!" "Eh toh ko ma wacece dai daga gidan Malam ta ke, dan kuwa a kulli yaumin in za ka gan ta fuskata rufe ta ke da wannan abun da su ke rufe fuska da shi tsabagen munafunci! Kai ni har da asuba na sha gani ana dawowa da ita!" Cewar Uzairu ba tare da ya kula da tashin hankali da sauran samari da su ke masoya Malam su ka shiga ba. Daya daga cikin su wanda har lokacin ya kasa yarda da abin da ya ke ji ne ya ce "Kai Uzairu, tsakani da Allah ban ji dadin wannan magana ta ka ba, Bai kamata ba, shin yanzu ina amfanin wannan kazafi haka?" "Oh toh kazafi ne ma?" Uzairu ya tambaya cikin nuna bacin rai. "Eh kazafi mana, yanzu idan mun je za mu ga abin da ka fada zahiri?" Uzairu na susa kyeya ya ce "Ai sun bar wajan......" "Ai dama ba nan za su zauna ba, amma da za ku zauna waccar rumfar ta kusa da gidan Malam har dare ya raba ko ma asubar fari kila ku ga an zo an sauke ta" Cewar Khalifa wanda ya ke maganar ko shakka babu. Daya daga cikin su wanda dama dan adawar Malam ne sakamakon rashin jituwa da ke tsakanin mahaifin shi da Malam ya ce "Allah dai ya biya, ka ce yau za mu yi kwanan waje, dan kuwa sai mun ga abin da ya turewa buzu nadi!" "Ni ma dai Habibu, za mu kasa mu tsare sai mun ga mai kan uwar daka!" Cewar Uzairu da dama haka ya ke so, ya sami wanda zai taya shi dan kuwa dai muddin bai gano wacece ba hankalin sa ba zai kwanta ba. Su kuwa samari biyu wanda su ke ganin hakan bai dace ba saboda darajar da Malam ke da shi, tashi su ka yi su ka bar wajen, sauran na bin su da habaici kila Malam ya mu su alkawarin kujerar makka ne. Su Zainab kuwa kasancewar lokacin da su ka saba shiga club bai yi ba, yawo Mike ya wuce da ita, sai da su ka gama zagayen su sannan su ka zauna wani dan garden da ake sayar da kayan kwalama. Mike ya siya mu su abin jika makoshi da gashesshen kifi. Da kyar ya samu ta ci ta dan koshi, sannan ya sake tambayar ta abin da ke faru. Nan ta labarta ma sa komai. Ran Mike yayi matukar baci, ba tare da yayi la'akari da iyayen Zainab ake magana akai ba ya furta "Why? Me ya sa ka? Wannan ai son kai ne! Shekarun ki ya wuce 18, kin wuce a mi ki dole! Ba wanda ya ke da wannan damar! Kar da ki yarda a yi mi ki auren dole kin ji ko? In sun takura mi ki you should take them to the court! Ni zan tsaya mi ki" Fuska cike da hawaye ta ke duban shi, ta na mai girgiza kai ta ce "No Mike you don't understand, they're my parent, ba zan iya ba, Daddy Malami ne, sananne kuma, imagine yanda zai ji idan na kai shi court......" "Just listen to yourself! You should think about yourself, your happiness first kafin na kowa! Shi yayi tunanin wani hali za ki shiga in ya mi ki auren dole?" Mike ne katse ta, ya na mai ruko hannun ta ya ce "Zeee look at me!" Ta dago manyan idanun ta ta na duban sa, cikin murya mai ratsa zuciya ya ce "You're beautiful, God you're very very beautiful! ga ki yarinya! You have a long way to go in life, in ki ka bari aka mi ki aure I'm sorry to say it might be the end of everything, your freedom, your happiness and even your beauty musammam ki fara having children....." Zainab na girgiza kai ta ce "Ah ah, ba na so Mike, ba na so" "Then tell your Dad, ba ni ba, in kin je gida look him in the eyes and tell him, ki fada masa ba ki yi shirin aure yanzu ba, ki fada masa ba za ki auri dan abokin sa ba, ya bar ki ki yi rayuwar ki! Ya dena wani yaudaran ki da ke ce favorite child din shi, he should know by now kin girma, kuma kin san yancin ki!" Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani Zainab ta nisa, ta na mai goge hawaye ta ce "Zan yi kokari na ganar da shi Mike, I promise you auren nan ba za a yi shi ba" Cikin jin dadi ya ce "Yauwa ko ke fa! Oya share hawayen ki, mu tafi ma mu ji dadin mu a club da fatan dai you're wearing something sexy under this your agbada hijab" Ya karasa maganar ne ya na mai bin jikin ta da kallo. Ba tare da ta nuna damuwa da irin kallan da ya bi ta da shi ba, Jin batun club ya sa ta duba lokaci, in da agogon ta ya nuna karfe shabiyu da minti 40. Tashi ta yi da sauri ta ce "No ba zan iya dadewa a waje ba, kasan Daddy ya na nan Mike" "Ohoooo! Ke da Dadyn nan na ki! Kin fiya tsoro wallahi! Idan ya na nan sai menene! Haba mana" "Ba za ka gane ba" "Try me, ganar da ni mana" "Mu shiga mota, mu na tafiya ina ma ka bayani" Haka ba yanda ya so shi ma ya taso su ka shige mota in da su ka dau hanyar gida. Ammy kuwa har ta kwanta amma ta nemi bacci ta rasa, Zainab da damuwar da ta ke ciki ne ya sa ta kasa bacci. Da abin ya ishe ta ne ta tashi ta nufi dakin Zainab. Ko da ta shiga ta ga ba ta nan sai ta yi tunanin ko bandaki ta shiga, Nan ma ta buga kofar tare da kiran sunan ta. Shirun da ta ji ya sanya ta bude kofar yayin da gaban ta ya shiga faduwa ganin bandakin ma wayam Zainab ba ta ciki. Dakin Halitta ta nufa jikin ta na rawa ta na mai fatan ko dai Zainab din kasa bacci ta yi, ta koma dakin Halitta ko Falmat duk dai ta san abu ne mawuyaci. Ta tarar idanun Halitta biyu, kallo ma ta ke a kan laptop. Cikin rawar murya ta ce "Halitta ina Yakura?" Gaban ta yayi mummunar faduwa jin tambayar Mahaifiyar su, a zahiri kuma cewa ta yi "Ta na dakin ta mana" "Ah ah ba ta ciki, daga nan na ke, ba ta shigo nan ba?" Halitta na girgiza kai a sanyaye ta ce "Ba ta shigo ba, kila ko ta na dakin Falmat....." Da sauri Ammy ta juya ta fice, dakin Falmat ta nufa, ita ma Halitta tasowa ta yi ta bi bayan ta, ta na mai kokarin kiran Zainab amma wayar ta ki shiga. Sun tarar Falmat ta yi dai dai ta na baccin ta har da munshari, ganin babu Zainab babu alamar ta hankalin Ammy ya fara tashi matuka. Cikin zafin nama ta fara tashin Falmat, da kyar ta samu ta bude idanun ta, cikin magagin bacci ta ke kallan Ammy. "Ke tashi da Allah! Ina Yakura?" Jin tambayar da aka mata take ta wastsake ta ce "Yakura kuma Ammy? Ba ta dakin ta?" "Mtsw da ta na can da zan zo ina tambayar ki ne? Ba ta shigo nan ba?" "Rabona da ita tun sanda na shiga dakin ta kiran ta mu ci abinci, kun duba kitchen? Kila yunwa ya tada da ita ta je kitchen neman. ...." Ammy ba ta bari ta karasa ba ta juya ta fita da sauri, kitchen din ta nufa, Halitta da Falmat biye da ita, hatta store da dakin baki sai da su ka duba, babu Zainab babu alamar ta. Falo su ka dawo, Ammy wacce ta fara fita hayyacin ta tsabagen firgici sai ga ta tana duban bayan kujera, idanu cike da kwalla, murya na rawa ta ce "Oh ni Aleesha na shiga uku ina Yakura ta shiga da tsohon daren nan? Malam! Kila ta na bangaran Malam! In kuwa ba ta nan gwara na tashe shi na sanar ma sa tun wuri Yakura ta bata! Toh ko sace ta aka yi! Na shiga uku wayyo Allah na!" Ganin yanda ta zabura za ta wuce bangaran Malam Halitta ta yi saurin dakatar da ita ta hanyar fadin "Ammy dan Allah ki tsaya ki kwantar da hankalin ki, kar ki tashi Daddy Yakura ba ta bangaran shi, ba sace ta aka yi ba, da kafar ta ta fita......" "Ki na nufin guduwa ta yi saboda za a mata auren nan? Wayyo Yakura da ba ki yanke wannan danyan hukuncin ba! Mun sanya diyar mu cikin wani hali, ya Allah ka kare mana ita! Halitta kin san za ta gudu ya aka yi ki ka bari ba ki fada min ba" Ammy ce ke simbatu ta rasa abin da ke mata dadi sai kai kawo ta ke. Falmat kuwa kallan su ta ke a tsorace dan kuwa har lokacin ta kasa fahimtar abin da ke faruwa. Ammy na mai goge hawayen da ya fara fita daga idanun ta, ta ce "Kai bari na shedawa Malam Yakura ta gudu, Yakura ta sa kafa ta gudu da tsohon daren nan tsagen ba ta son auren da ya kulla" "Ammy na ce kar ki fadawa Daddy, Yakura ba guduwa ta yi ba! Za ta dawo! Ki kwantar da hankalin ki dama ta saba fita!" Daga Ammy har Falmat Halitta su ke duba cike da mamaki, wacce kallan da su ke mata ya sanya ta farga da subul da bakan sa ta yi "Me ki ke nufi ta saba fita?" Ammy ta tambaya cikin tuhuma "Babu komai Ammy, kawai ina nufin ko ina ta je ma za ta dawo...." "Halitta!" Ammy ta daka mata tsawa wanda ita kan ta Halitta sai da ta ji har zuciyar ta. Ammy ba ta gushe ba ta kara da "Ba kya magana hakan nan kara zube, me ki ke nufi da sama ta saba fita?" Baki na rawa ta ce "Dama..... dama...dama wani sa'in ta na fita cikin dare, sai ta dawo da asuba, duk sanda mu ke ji kamar ana haurowa ta garden, ita ce......" Tas Ammy ta dauke Halitta da wani gigitaccan marin da sai da ta ga wuta a idanun ta, ta na mai huci ta ke fadin "Kun haince ni! Kun zalin ce ni! Kun cuce ni! Gani shashashar uwa, ina can ina bacci ku kuma ku nan kuna cutar da mu? Da ku ke hada baki ta na fita gidan uwarwa ta ke zuwa??" Tunda Ammy ta fara magana Halitta wacce hannun ke rike da kuncin ta take girgiza mata kai, dan kuka ta ma kasa magana. "Ba da ke na ke magana ba? Gidan uwar wa ta ke zuwa!" "Ammy dan Allah ki yi magana a hankali kar da Daddy ya jiyo mu" Cewar Falmat wacce ita ma din kukan ta ke. "Idan ya ji sai me? Sai na fada masa diyar ta shi da ya fi yiwa kyakkyawan zato ce ke hada baki da kanwar ta, ta na haura katanga! Wannan masifa har ina ni Aleesha!" "Dan Allah Ammy ki yi hakuri, wallahi tallahi ba hada baki mu ka yi ba, sam ban da masaniya da ya wuce fitar da ta ke, shi ma din gudin halin da za ku shiga ya sa na kasa fada mu ku, Amma ina kokari na wajan yi mata nasiha da kuma addua..." Halitta ce ke magana cikin kuka. Hannu biyu Ammy ta dora aka, ba su kara firgita ta ba sai da su ka ga hawayen na kwaranya daga idanun Ammy. A tare su ka furta "Dan Allah Ammy ki yi hakuri" Tuni ta canza harshe to koma yare, ta na mai fadin "Menene amfanin rufewar da ki ka yi? Yanzun kin min adalci kenan Halitta? Ki na gani yar uwar ki na cutar mu da mu Amma ki kasa fada min, nasihar ta ki da adduar ta ki amfanin me ta yi mana? Yakura ta cuce ni, ta cuci kan ta, ta cuci Malam! Ina waya ta? Ba ni waya ta!" Wayar ta ta shiga nema, ganin wayar ba ta kusa ta dubi Halitta wacce ke rike da na ta wayar, ta ce "Kira min ita, kira ta ta faɗa min gidan uwar wa ta ke!" Hannu na rawa Halitta ta kara kiran wayar Zainab, ta ci sa'a ya shiga amma kuma har ta gama kara ta katse ba ta daga ba. Haka ta yi ta kiran ta amma ba a dagawa, ganin haka Ammy ta koma kan kujera ta na tunanin mafita, shin Malam za ta tasa ta fada masa halin da su ke ciki ko kuwa dai ta jira Zainab yanda za ta hukunta ta ba tare da Malam ya san halin da su ke ciki ba? Su Uzairu kuwa a na su bangaran zama su ka yi a mararrabar gidan Malam su na jiran dawowar Zainab da Mike, saura da su ka gaji da jira cewa su ka da Allah in dan sun karaso su ma a yi mu su waya. Ganin shiru har karfe daya babu alamar motar Mike Khalifa ya ce "Baba kamar fa wannan mutanan ba za su dawo ba, Ni ma gwara na tafi na......" Motar da ta dan haske su kadan kafin a rage hasken motar ta gifta gaban su ya sanya Khalifa shanye sauran maganar da ya ke. Daga shi har Uzairu bin motar su ka yi da kallo, illa kuwa mota ta ja ta tsaya dan gaba kadan da gate din gidan Malam, ta daidai garden da ta saba haurawa. "Alquran wannan motar ce, wabillahilazi!" Cewar Uzairu ya na mai nuna motar da dan yatsa. "In dai kuwa su ne maza kirawa so Munir da Habibu, su zo maza yau za su sha mamaki!" Khalifa ne ke maganar in da shi ma ya ke kokarin kiran na shi mutanen dan kuwa yau sun sha alwashin gano ko ma wacece wannan yarinyar mai haura katangar gidan Malam. Sam Mike bai lura da su Uzairu ba, bare ma ya san da zaman su. Bayan ya faka ya riko hannun Zainab, cikin bata kwarin gwiwa ya ce "Na san za ki iya kwatarwa kan ki hakki Zee, please do it for us" Karar wayar ta da ta fada hannun kujera ta ji, da kyar ta iya daukowa, da ta duba ta ga wacce ke kiran ta ya sa ta jan tsaki "Mtsw wannan wawuyar yarinyar ba za ta sakar min mara ba ko!" "Wacece?" "Sister na ce, I'm sure ta shiga daki na ta ga ba na nan ne ya sa ta ke kira na, rabu da ita ba zan dauka ba, bari na yi sauri na haura sai na ce mata daga garden na ke" Ta bashi amsa yayin da wayar ta katse, hakan ya bata damar ganin miss calls din Halitta har goma sha uku. "Kai wannan ba dai mayya ba, bari na tafi kar ta jaza min masifa" Ta na maganar ne yayin da ta fito da sauri ta mayar da murfin mota ta rufe, sannan ta zaga wajan Mike da niyar masa sallama, hakan yayi daidai da hango samari hudu da ko shakka babu gun su su ka nufo. Da ke garin da dan duhu daga Zainab har Mike ba su iya tantace wasu irin mutane ba ne. Hantar Mike tuni ta kala, cike da tsoro ya ke duban Zainab da ga cikin mota ya ce "Su waye wannan?" "I don't know, ban sani ba, I don't think it's safe, bari na koma mota mu bar wajan kawai" Cewar Zainab dan kuwa ta tsorata ainun, ta na kokarin bude motar Mike ta koma ciki, ga mamakin ta sai gani yayi ya tada motar shi, ya ce "No Zee, kar ki shigar min mota, babu mamaki set up ne daga Baban ki, dan a kama ni, gani Christian, I can't go with you, I can't risk it!" Yanda ya figi motar da yanda samarin su ka bi motar a guje kamar za su iya kama motar ya sanya Zainab kaduwa, ta yi shahada ta sheda babu sarki sai Allah, dan kuwa ko da Mike ya tsarewa samarin nan kan ta su ka dawo, ganin haka ita ma sai ta gwada yin abin da Mike yayi, ta juya za ta arta a na kare, ba ta kai ga wuce gate din gidan su ba su ka cimma ta, in da su ka zagaye ta, yanda su ke mayar da numfashi, Daya bayan daya ta ke bin su ka bin su kallo, dan tsoro ta kasa furta komai. "Ke wacece? Ki bude fuskar ki Malama! Duk abin da ki ke mana a unguwa muna sane da ke! Kuma yau din nan sai mun tona mi ki asiri!" Cewar Uzairu wanda ya fi kowa za kewa. Ganin an bude gate din gidan Malam tuni hankalin su ya koma can, musammam Zainab wacce jikin ta har rawa ya ke. Haushin karnuka ke tashi daga cikin gidan dan kuwa karar tashin motar Mike da Kuma guje gujen v ne su ka fito a tare hannun su ruke torchlights. *Khadija Sidi* AUREN SHEHU 6. Ranar da Malam ya koma gida ya sanarwa Hajja Aleesha maganar auren Zainab da Sudais. Zaune su ke a daki, Ammy ta na yi Malam wanda ke sanye cikin jallabiya ya gyara zama, sannan ya ce "Hakkun, ya na ga kin yi jim maganar ta yi mi ki bazata ko? Ki yi hakuri abin ne ya zo ba shiri, kwana uku da su ka wuce Shiekh Ahmad ya zo mun da kyakkyawan labari na gama makarantar Sudais, ya kuma nemi a ba shi auren ɗaya daga cikin 'ya'ya na mata, Ni kuma na masa alkawarin zan ba shi diya ta mafi soyuwa cikin rai na, na tabbata idan na zo mata da maganar za ta karba hannun bibbiyu dan kuwa Yakura ba ta taba yi min musu ba" Shiru ne ya biyo baya na dan sakanni, kafin daga bisani Ammy ta nisa ta ce "Allah ya tabbatar da alkhairi Malam, ya nuna mana, Amma zan so ka dena wannan furucin na cewa Yakura ce mafi soyuwa cikin ranka, sauran 'ya'yan su ka ji ba za su ji dadi ba, na tabbatar ba ma 'ya'ya na kadai ba, hatta 'ya'ya Hajja kulu babu wanda za ka zartar da hukunci ya ma ka musu da yardar Allah" Murmushi Malam yake yayinda ya jawo hannun ta, ya motso da ita kusa da shi, ya ce "Dadi na da ke adalci Hajja ta, in Sha Allah zan kula da furuci na, Amma kin san cikin 'ya'ya da iyali dole akwai wanda zai fi shiga ranka, ina alfahari da Yakura ba dan komai ba sai dan halin ta na gari, ga nutsuwa, ga hankali dadin dadawa ga kamun kai, ace yarinya ta gama secondary, ta shiga jami'a ko saurayi ba ta da shi? Ta taba kawo mi ki maganar wani ko kuwa kin ji ta na maganar wani da yan uwan ta?" Kai Ammy ta girgiza alamar 'ah ah' "Kin gani shi ne ai, kunya irin na Yakura ai ba zai iya bari ta tsaya da wani da namiji ba, Allah ya mata albarka, Allah ya sa yan uwan ta su yi koyi da ita" Ammy ta amsa da 'amen' Nan su ka cigaba da hirar yanda za a tsara daurin auren ba tare da bidi'a ba, in da Malam ke da shirin shedawa amaryar abinda ake ciki a washagari. ***** Washegari bayan sallar la'asar Malam ya nemi ganin su Zainab. A falon shi su ka tarar da shi zaune tare da Ammy. Dukkannin su cikin fargaban dalilin kiran su ke, musammam Halitta wacce ta ke zargin ko dai Zainab ta sake zagayawa ta tuna mata asiri gurin Malam. Zainab kuwa fargaban kar dai Usman ya tona mata asiri. Falmat kuwa tunanin duniyar na ta rasa laifin da za a iya cewa ta yi, Amma hakan be sanya hankalin ta kwanciya ba. Kamar yanda Malam ya saba duk sanda ya zauna tare da iyalin sa, nasiha ya mu su akan tsoran Allah da yanayin rayuwa, ya kare da kalamin da ya sanya dodon kunan Zainab toshewa "Alhamdulillah na zabawa Yakura mijin aure, Sudais babban dan aboki na Shiekh Ahmad, mun sanya ranar daurin aure, shabiyu ga watan Juli....." Cikin faduwar gaba ba ta san sanda ta dago ta kalli Malam ba, har su ka hada ido, in da ta yi saurin yin kasa da na ta idanun yayinda zuciyar ta ke tafasa kamar ruwan zafi. Halitta da Falmat da su kan su maganar ta zo mu su a bazata idanun su akan Zainab ya ke, in da wani sanyi ya sauka zuciyar Halitta, dan ta tabbata Allah ne ya karbi adduar ta ya kawo hanyar shiriyar yar uwar ta. Malam be gushe ba ya kara da "Ba komai ya sa na yanke hukunci haka kai tsaye ba, sai dai dan mun san mun Isa da ku, ba ni da haufi a kan ku, Yakura ba ki taba min mu su ba, na san ki da ladabi da biyayya, ina fatan za ki yi na'am da wannan hadi na alkhairi da mu ka kulla, za ki cigaba da zama abin alfahari a gare mu" Murya can kasa ta na kokarin makale kwallan da ke shirin fara zarya daga idanun ta ta ce "In Sha Allahu Dady, zan kasance mai biyayya a gare ku a ko da yaushe" Cikin jindadi duk da ya lura da sauyin yanayin da Zainab ta samu sanadiyar jin furucin auren ta, Malam ya ce "Allah ya mi ki albarka, yanda ki ka mana Allah ya baki ma su yi mana" "Amen" Ta amsa can kasan makogoro. Malam ya kara da "Ku ma Allah ya mu ku albarka, Allah ya ba ni ikon zaba mu ku mazaje na gari kamar yanda na zaba ma yar uwar ku, bisa sunnah, ku tafi na sallame ku" Falmat da Halitta su ka amsa da "Ameeen ameen" Jiki sanyaye su ka tashi su ka tafi. Zainab kuwa su na shiga bangaran su da gudu ta wuce dakin ta yayinda kuka mai karfi ya kwace mata. A falo Halitta da Falmat su ka zauna jigum, kowa ya na sakar zuciya. "Ki na ga...." "Ni a gani na...." Falmat da Halitta su ka fara magana a tare, gannin haka sai duka su ka sake yin shiru, Halitta ce ta sake fadin "Ni a gani na wannan aure na Zainab alkhairi ne Falmat, ko ba komai Allah zai kare Daddy daga halin Yakura!" "Halin Yakura? Me ki ke nufi? Shin Yakura na da wani hali mara kyau da ban sani ba? Har ki ke tunanin zai iya cutar da Daddy?" Shiru Halitta ta yi cikin wasiwasi da auna fadawa Falmat ko kuwa rashin fada mata a mizani, dan kuwa ko Instagram Falmat ba ta yi bare a ce ta san account din Zainab, ita dai a bar ta da WhatsApp din ta da Facebook. "Ke na ke sauraro Halitta, kin yi shiru?" Kai Halitta ta girgiza sannan ta ce "Kar ki damu ba wani hali ba ne, kawai kin san yanayin Yakura da rawan kan ta ne sai a hankali" Ajiyar zuciya ta saki sannan ta ce "Kai har kin sa hankali na ya tashi, ki na gani hukuncin da Dady ya yanke be yi tsauri ba? Ina ma laifi ya tambaye ta ko ta na da manemi, idan ta ce babu ne sai ya bawa dan abokin na sa dama ya dan zo su gana su kuma fahimci juna, idan mai yiyuwa ne sai a kai ga maganar auren, ba hakan nan tashi guda kamar yankar wuka ba, sai ka ce a zamanin da!" Ta kare maganar cikin nuna rashin jin dadi. "Etoh kin yi gaskiya, Amma dai a musulunce iyaye ke da alhakin zabarwa 'ya'ya mata mazaje a auren su na fari, kuma dai kin san Dady ba zai cutar da mu ba" "Eh ba zai cutar da mu ba, but at least ya kamata ya duba lamarin nan, wallahi na ji tausayin Yakura, haba mana, yanzu idan ke ce aka yiwa haka Allah kadai ya san halin da za ki shiga" "Zan damu na sani, Amma zan yi tawassali na auri duk wanda Dady ya zaba min, na mi ki wannan alkawarin Falmat" Ta fada cikin jaddawa "Toh kuwa ni dai ba zan iya ba wallahi, haba mana ai an sami cigaba, Sudais din da ko ganin shi ba mu taba yi ba, kawai a ce wani za a aura mata shi, gaskiya ba a kyautawa Yakura ba!" Cewar falmata ta na mai kara nuna bacin ran ta, ita kuwa Halitta ta shi ta yi, kana ta ce "Hajiya Falmat ai sai ki je ki fadawa Dady kin ji uwar Yakura? Ni dai na yi gaba, ko a tafin kafa ta" "Wallahi ba dan kar na mi ki fata ba da na ce Allah ya sa Dady ya canza da ke Halitta yanda ki ke son Usman din nan na ki sai mu ga yanda za ki yi!" Cikin nuna ko in kula ta ce "Ai Allah na duba izuwa zuciyoyin mu ne, Allah ya sani ba dan komai na goyi bayan wannan aure na Yakura ba, sai dai dan ina gani shi ne mafi alkhairi ga rayuwar mu duka, Allah dai ya sa mu dace" Ta na gama magana ta wuce ciki inda Falmat ta bi ta da kallo cike da mamakin lafuzzan ta, da kuma halin ko in kula da ta ke nunawa akan tashin hankalin da yar uwar su ke ciki. Zainab kuwa kuka ta ci ta koshi, tuni manyan idanun ta su ka kumbura su ka yi rubu rubu. Cikin wannan hali Ammy ta zo ta same ta, ganin yanda ta fita daga hayyacin ta ya sa Ammy salati ta na mai tafa hannu ta ce "Yanzu duk yabon nan na ki da Malam ya ke akan ladabi da biyayya ashe ke kina nan kina kuka kamar wacce aka turowa da sakon mutuwa? Menene dalilin wannan kuka haka Yakura?" Cikin shassheka Zainab ta ce "Ammy ya ma Dady zai min haka dan Allah, ya Dady zai saka min ranar aure da wanda tun da na zo duniya ban taba ganin shi ba Ammy, ban san halin shi ba, be san hali na ba, be san ya na ke ba, ban san ya yake ba, tashi guda ku hada mu rayuwar aure Ammy....." Ta karasa cikin kuka. Jiki sanyaye Ammy ta zauna kusa da ita, har ga Allah ta ji sanyi a cikin ran ta jin Zainab ba ta furta ta na da wanda su ke soyayya ba, kenan hashashen Malam akan Zainab gaskiya ne, ba ta da wani saurayi, dan kuwa shi ne babban fargaban Ammy, dan ta san rabuwa da masoyi abu ne mai wuya matuka. Ta na mai kamo hannun ta tace "Ki yi hakuri Yakura, ki sani da nufin alkhairi Malam ya ke so ya kulla wannan dangantakar, ki tuna ba ke kadai ba ce diyar shi, ba kuma mu kadai ba ne iyalan sa, Amma ya tsallake kowa ya zabe ki, ba dan komai sai dan ganin kin fi kowa cancan ta, kuma ya isa da ke....." Nan ta cigaba da bata baki, amma ta inda ya ke shiganta nan take ya ke fita, sai da ta bari Ammy ta gama jawaban ta kaf sanan ta ce "Ammy duka na ji, na yarda kuma na gode, Amma Allah na gani ba na san auren nan, dan Allah ki saka baki Dady ya fasa" A fusace Ammy ta tashi, cikin nuna fushi ta ke nuna ta da dan yatsa, ta ce "Ba zan saka baki ba Yakura, idan kin isa yar halak, Ni Aleesha ni na haife ki toh kuwa kar na kara ji kin yi musu akan maganar auren nan ba!" Ta juya ta fice a fusace, hakan ba karamin tunzura zuciyar Zainab yayi ba, Nan ta fara wani saban kukan. Kuka ta yi mai isar ta, har magrib ta yi. Da kyar ta iya tashi ta yi sallah. Ta na idarwa ta fara neman number sabon saurayin ta Mike, amma ba ya shiga, sai ta tura masa sako kamar haka "Hello Mike, I need you, I need to talk to you it's an emergency, call me ASAP" Ta na tura masa ta aje wayar gefe in da ta kara haurawa gado ta kwanta, tsabagen ta yi kukan mai isar ta sam sai ta nemi kukan ta rasa, sai ajiyar zuci. Sau biyu Falmat da Yakura su na lekowa dan su kira ta su ci abinci, Amma ta ki kula su bare ma ta tashi ta fito su ci abinci, har Ammy ta yi fushi ta ce kada wanda ya sake kiran ta, su bar ta ai yunwa ba kanin uban kowa ba ne. Wajan karfe goman dare har fitar da ran Mike zai kira ta, sai ga Kiran shi. Hannun ta na rawa ta daga, Amma ta kasa magana sai kuka, yayi juyin duniyar nan ta masa bayanin abun da ke faruwa amma ina sai kuka kawai. Har ya gaji ya aje wayar. Bayan minti arbain ya sake kiran ta, ta na dagawa ya ce "Ina waje, come out" Murya dashe tsabagen kuka ta furta "Mike....I can't, Dady ya na nan" "I don't care, just come out, bazan iya jure kukan ki ba Zeee, kin daga min hankali, I need to see you right now!" Shiru ta yi ta na tunanin yanda za a yi fita, daga bisani ta nisa ta ce "Ka koma gefen gidan mu, ta side din da bishiyoyi su ka yi yawa, zan hauro yanzu" "Alright babe, ina jiran ki" Cewar Mike yayinda ya aje wayar yana mai kokarin yin ribus ya koma in da ta kwatanta masa. A gurguje ta shiga bandaki ta wanke fuska, kayan jikin ta ta sauya, ta sanya shudin riga mai haske tare da shudin wando wanda ya kamata sosai ya bi jikin ta. Hijabi ta jawo yanda ta saba ta sanya har kasa, har ta kai kofa ta dawo ta dauki nikabin ta ta saka, wayar ta kawai ta dauka, takalmi a hannu ta zaga ta bayan dakin su, ta na jiyo muryar su Falmat a parlour ko tsoran kar su kamata ba ta ji ba tsabagen yau zuciyar a dake ta ke, kai tsaye garden ta wuce. Da ya ke yau Malam ya na nan, Usman na can wajan shi suna daukar karatu bare ma su hadu yanda aka saba, dan haka ta sami damar taka wani rashe na bishiya da ya mata tsani zuwa katanga, da ke sababbiya ce tuni ta haura, da taimakon Mike, hannun sa bisa kugun ta ya dire ta kasa. Ya na dire ta ya rungume cikin rarrashi ya ke fadin "Oh my baby, me ya faru?" Cikin tashi hankali ta ke waige waige gudun idanun jama'a duk da dai wajan akwai duhu amma dare be yi sosai ba, mutane na dan wucewa ta ce "Mike let's just get out of here" Hanun ta cikin na shi da sauri ya bude mata gaban mota, sai da ta zauna ya rufe motar sannan ya zaga da sauri shi ma ya shiga motar, hannun ta ya kara rukewa yayinda ya tashi motar. Duk wannab abun da su ke yi akan idan wani dan saurayi matashi da ya zo wucewa ta layin. Cike da mamaki ya ke jinjina kai, wato dai rade radin da ake a unguwa na ana daukar wata a cikin bakar mota daga gidan Malam gaskiya ne, yau ya ga zahiri dan kuwa akan idan shi Miki ya riko kugun Zainab ya dire ta kasa, kuma ya rungume ta. Jiki na rawa yayi gaba zuwa majalisa domin ya kunsawa abokan sa abin da ya gani. *khadija SidiAUREN SHEHU 8. Da sauri su Jauro ka karasa wajen, su na haske Zainab su ke tambayar ko lafiya? Menene ke faruwa? "Wannan yarinyar mu ka kama wani mai bakar mota ya sauke ta, dadin dadawa kuma mun ga sanda ta diro daga kan katangar gidan Malam! Ba tun yau ta saba yi ba, yau duban ta ya cika! Wallahi sai ta cire wannan nikabin na munafunci mun ga kowacece!" Cewar Uzairu yayinda ya ke bin Zainab da kallan banza. Jauro wanda kallo daya ya mata ya san uwargijiyar ta shi ce, tuni ya hakikan ce ya ce "Wannan maganar banza ne! Ina ruwan ku da matar mutane? Dan sharri har za ku ce daga gidan Malam ta diro? Ke malama kama hanya ki tafi!" Jin haka Zainab ta dan motsa da niyar wucewa, su ka yi saurin dada tare hanyar. "Idan har ta bar wajan nan toh ban isa dan halas ba! Idan ma za ta tafi sai ta fada mana ita wacece kuma daga ina take! A wannan marra ta masifar duniya ba za mu ga haka mu bari ba!" Cewar Khalifa, shi kuma Uzairu cewa yayi "Me ku ke jira? Ku fizge tsinannayir abar mana ko ta fi karfin ku ne?" Jin haka Zainab ta sa hannun ta ruke nikaf din da ya jike jagab da hawaye, Ganin haka Jauro ya yi saurin shiga tsakani ya na fadin "Kul! Kar wani dan iska ya kai hannun jikin ta!" "Toh ka san wacece kenan, idan ka san wacece ka fada mana mu dena bata lokacin mu!" Daya daga cikin jama'ar da su Uzairu su ka tara ma Zainab ne ke maganar cike da rashin kunya "Zan ci uban ka ka min rashin kunya anan! Sakarai mara tarbiya!" "Mara tarbiya ga ta nan bayan ka Malam, kuma wallahi ba wani wane wane! Sai ta bude fuskar ta mun gani!" Tuni hayaniya ta kara kaurewa a wajan, in da kowa ke fadin albarkacin bakin sa, Jauro kuwa be fasa kare Zainab ba, ya tsaya tsayin daka babu mai ganin fuskar ta, shi kan sa Isa mamakin yanda Jauro ya hakikance ya ke. Jin an furta "Me ka faruwa a nan? Hayaniyar me ku ke haka? Dare mahutar bawa amma ba za ku bari mu huta ba?" Kowa yayi tsit saboda kwarjini da Malam ya ke da shi a idanun jama'a. Zainab kuwa ganin shi tsaye tare da Usman ji ta yi dama kasa ta bude ta shige tsabagen tsoro da firgici. Hayaniyar su da haushin karnuka ya sanya Malam fitowa, Usman kuwa da kyar ya samu ya dan ja hankalin karnukan ciki kafin shi ma ya biyo bayan Malam. "Kai Jauro wacece wannan matar da ke tsaye bayan ka?" Malam ya kara tambaya, in da hankalin Jauro ya tashi dan be so Malam ya fito ba, ya so a yi ta ta kare ba tare da Malam ya sani ba. Kafin Jauro ya iya tunanin amsar da zai bawa Malam, sai ji su ka yi an furta "Mata ta ce....." Hankalin kowa ya koma kan Usman, yayinda cecekuce ya dada kaurewa, da daga mai cewa "Kar ka rena mana hankali!" Sai me cewa "Karya ne wallahi! Akan wani dalili za a sauke matar ka daga wannan bakin daren? Kuma a kan idanun mu ta diro daga katanga! Ba kuma tun yau ta fara ba!" "Malam mu fatan mu kawai a tuntubi wacece, kuma ta bude fuskar ta mu ga wacece kar mu na zaune a cutar da mu" Jin wannan batu kan Malam ba karamin kullewa yayi ba, ya furta "Daga wani katanga kenan? Kai Usman ta Yaya ta zama matar ka? Dama ka na da aure? Me zai sa matar ka fitowa da tsakar dare haka?" Malam ya tambaya yayinda gaban sa ya shiga faduwa ya na mai haske Zainab ta hasken tocilit. Tuni ta dada sunkuyar da kan ta, cike da dana sanin fitar ta a daren ranar. Usman ne ya shiga tsakani, ya na mai kare Zainab daga haske ta da Malam ya ke, ya ce "Na yi kuskure, duka wannan laifi na ne Malam, kamar yanda na fada wannan mata matata ce, Sam ba ma zaman lafiya, wannan dalili ya sanya ban sheda ma ka ina tare da ita ba, dan kuwa na san tabbas idan ka sani ba lalle ka bari mu zauna a gidan ka ba Malam....." Ya dan nisa, ganin irin kallan da Malam ya ke ma sa ne ya sanya shi tsugannawa, dan shi kan sa be taba tsammanin ya iya shirya karya haka ba, ganin hakan shi ne sutura ga Malam da iyalan sa, Usman be gushe ba, ya cigaba da fadin "Na sama mata haya can kasan unguwa, ta yi gta yi na kawo ta gidan nan, kuma fitinar ta ya sanya na kasa. Hakan ya ke sanya ta haura katanga duk sanda ta so gani na, Ni kuma na nuna mata rashin yiyuwar haka sai dai kawai na gan ta cikin gidan ba dan komai ba sai dan kawai ta tayar min da hankali ta tafi. Kasancewar amana aka ba ni ita babu damar na sake ta, duk da ta nemi hakan daga gare ni, haushin hakan ya sanya ta shan alwashin bata ni a idanun ka Malam, ban taba tunanin za ta aikata wannan tozarcin a gare ni ba, haka kuma wanda ya sauke ta a mota ban da masiya akan shi, ka yafe min....." Jin kalaman Usman idan ran Malam yayi dubu ya baci, dan takaici kasa magana yayi, shi kuwa Jauro kallan Usman ya ke cike da mamakin yanda ya iya sharara karya har haka dan kare Zainab. Isa kuwa mamakin rashin adalci irin na Usman ya ke, gani ya ke duk lalacewar da matar shi ta ke shi ya jawo, da kakkausar murya ya ce "Lalle ka cika azzalumi! Mahainci! Kai Usman ka bani kunya, ka ci amanar aure, domin kuwa wannan halin da matar ka ke ciki kai ne ummul abaisi, da ka killece ta in da kake da duk haka be faru ba, maza irin ku azzulumai ke jawo mana zagi kwarai da gaske" "Mu dai ko ma wacece ta bude mu ga fuskar ta!" Cewar wasu daga cikin samarin wanda su har lokacin ba su gamsu da jawabin Usman ba. Cikin nuna bacin rai Usman ya ce "Mata ta ce, akwai hakkin kare darajar ta, dan haka ba za ta cire nikabin fuskar ta ba, babu mai bude min fuskar ta...." "Ashe? Shin ka san darajar matar ta ka ka sake ta sakaka har ta fada ga mummunar halaka haka? Na ji takaicin kasancewar ka dalibi a gare ni, na yi danasanin karbar wanda be san darajar mata ba a matsayin dalibi, Allah ya wadar da azzaluman maza irin ka!" Cewar Malam wanda ya ke maganar a fusace tsabagen yanda zuciyar shi ki radadin danasanin karbar Usman, kallan jama'ar wajen yayi, kana ya ce "Ina mai neman afuwan hakkin ku da aka shiga ta sanadiyar wannan dalibi nawa, ban da masaniya akan wannan zalunci da ya ke aikatawa wannan baiwar Allah, bare na san da haurawa gida na da take, so dayawa mu kan yi zaton ko dai barayi me ke son hauro min, dan haka ne ma masu gadin gidan su ke har su uku ga su nan, Ashe matar dayan su ce mai aikata barnar, ku yafe mana, zancen sai kun ga fuskar ta be taso ba, shi addinin musulunci ya na san rufin asiri, ya zabi ya rufa asirin iyalin sa, dan haka ku rabu da su kada ku tsanan ta bincike! Ina fatan kowa zai koma gidan sa, Allah ya tashe mu lafiya" Daga mai cewa "Amen Malam" Sai masu "Amen Allah ya kyauta" "Amen amman dai ba haka mu ka so ba" Haka su ka ja jiki, kowa yayi na sa wajan, su Uzairu da har lokacin gani su ke rufa rufa kawai aka mu su, suna tafe cewa su ke "Yau an rufa, Amma a juri zuwa rafi dai, mu na nan mu na sa ido wallahi" Zainab ta yi tsuru tsuru da idanu, so ta ke ta shige gida amma ta na tsoran yanda za ta samu ta shige ba tare da Usman ba, gashi dai ya kira ta matar shi. "Kai kuma Usman daga yau na sallame ka daga aji na, haka kuma kar na kara ganin ka saka kafa a gida na!" Cewar Malam ya na mai nuna Usman da yatsa, shi kuwa Usman da maganar ta masa bazata kasa cewa komai yayi, dan kuwa dai sam be yi zatan Malam zai yanke hukuncin akan sa haka ba. Ita kuwa Zainab farin ciki ne ya mamaye zuciyar ta jin Malam ya ce "Me ka ke jira nan tsugunne? Ka dauki matar ka ku tafi kar na sake ganin ka gida na!" Shikenan za ta samu ta gudu ba tare da Malam ya san ita kowacece ba, Usman ne ya sa murnar ta ta koma ciki, Wanda batun ya tafi da Zainab ba karamin kaduwa zuciyar shi ta yi ba, A tsorace ya ke kallan Zainab, Fadi ya ke "Kamin afuwa Malam mu dan kwana, sai mu tafi ido na ganin ido, ina tsoran dare da masifun da ke cikin sa, ba mu san me zai mu tarar a hanya ba!" Kara tunzura Malam yayi, cikin nuna bacin rai ya ce "Ka na tsoran dare ka bar iyalin ka ta ke yawan dare?" "Malam ba wai ina goyan bayan sa ba ne, amma ni ma ina ga zai fi ya bari sai goben, ko dan jama'ar da su ka tara mana kofar gidan nan, babu mamaki akwai wanda su ke nan labe su na jira su taho su ci mutuncin wannan baiwar Allah, ba shi ake ji ba, matar ta sa ake ji" Isa ne ya saka baki, wanda tausayin matar da Usman ya kira tashi ya mamaye zuciyar sa. Shiru ne ya biyu baya, kafin daga bisani Malam ya juya, ya na fadin "Ka ci darajar iyalin ka, amma gari na wayewa ka tattara na ka ya na ka ka bar min gida!" Ya na tafiya Jauro da Isa biye da shi su ka shige aka bar sa daga shi sai Zainab nan waje, babu wanda ya motsa cikin su bare su tankawa junan su, Isa ne ya kara lekowa tare da fadin "Malam za ka tsaya nan kuna kallan juna ne mu rufe gida? Allah ya wadar na ka ya lalace! Ilimi dai be yi amfani ba!" Jin haka sim sim Zainab ta wuce gaba, Usman na biye da ita su ka shiga farfajiyar gidan Malam. Har lokacin Malam be shige cikin gidan ba, mitar tashin hankali da tozarcin da Usman ya ma sa ya ke, Ashe duk wannan lokacin da ake hauro ma sa gida matar Usman ce amma ya na ji yayi shiru. Karnukan gidan ba su fasa haushi sama sama ba, Amma ganin shigowar Zainab be sa sun harzuka kamar yanda su ka saba ba duk sanda su ka ga baki ba, sai ma zuwa da su ka yi su ka tsaya in da Zainab da Usman ke tsaye. Yanda hasken fitulun gidan ya haske su sosai ya bawa Malam damar kallan ta da kyau, sai a sannan ya lura da yanayin ta, hakan ya sa shi kaguwa ya ga fuskar ta a karo na farko, "Usman wannan matar ta ka ya sunan ta? Yar wani gari ce? An ya kuwa ban taba ganin ta ba?" Dam gaban Zainab ya fadi, shi kuwa Usman ganin an shigo gida dama ya rufa asiri ne ba dan komai ba sai dan darajar Malam, shiru yayi kawai ya na duban Malam. Ganin haka Malam ya dube ta ya ce "Ke bude fuskar ki!" Zainab na mai girgiza kai ta ke duban Usman cikin neman dauki, shi kuwa Usman ya kawar da kai gefe guda. "Ba da ke na ke magana! Ki daga wannan nikabin na ce!" Cewar Malam karo na biyu cikin tsawa domin kuwa hakan nan ya ji gaban sa na faduwa. Zainab ba ta san sanda ta ruko hannun Usman ba, cikin rada ta dada matsawa kusa da shi, karo na farko da ta yi magana kenan tun sanda Mike ya gudu ya bar ta, cewa ta yi "Dan Allah ka rufa min asiri, dan Allah, dan Allah......." "Usman ina so na ga fuskar matar ka! Ka bude min fuskar ta na gani yanzun nan!" Cewar Malam wanda ganin yanayin da Zainab ta shiga ya kara kyautata zatan shi akan ta na rashin gaskiya, ganin Usman be da niyar motsawa bare ya aikata umarnin Malam ya sanya Malam karasawa gaban su, tare da fadin "Ko dai ku bude fuskar nan, ko kuma na mika ku ga hukuma a daren nan!" Jin haka Usman ya tsinci kan sa ya na fadin "Diyar ka ce Malam, daya daga cikin 'ya'yan ka........!" Kamar takobi haka maganar ta soki zuciyar Malam, hannu ya sa ya yaye nikabin yayinda fuskar diyar sa, diyar ta sa ma wacce ya ke mata mafi kyakkyawan zato ya bayyana gare shi. Kuka ta ke sosai ta na fadin " Dan Allah dady ka yafe min, dan Allah dadi ka yafe min......sharrin shedan ne" Malam yayi baya tsabagen firgici sai gashi zai fadi, Jauro da Isa ne su ka yi saurin taro shi, yayinda hawaye bibbiyu ke fita daga idanun sa. *Khadija Sidi**Auren Shehu 9   "Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun! Allahumma ajirni fi masibati haza wakallifna minha!" Lafazin da Malam ke ta nanatawa kenan ya na mai kawar da kai daga kallan Zainab. Sai da su ka tabbatar ya tsaya sosai da kafafun sa sannan su ka sake shi, kamar wanda be da lada a jiki haka ya juya ya nufi cikin gida, shi kan shi tafiyar kawai ya ke ba tare da ya san ya na yi ba, haka kuma be fasa furta "Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun" dan kuwa tun da ya zo duniya be taba tsammanin zai ga rana irin ta yau ba. Ganin Malam ya shige ciki Jauro ya sami damar kallan Usman ya ce "Toh munafuki ka tona ka ji dadi ko? Dan bakin ciki ai sai ka zuba ruwa a kasa ka sha! Ga dai halin da ka sa bawan Allah!" Shiru Usman ya ma sa gaba daya hankalin sa kan Yakura ya ke, musammam da ya ga ta daura hannayen ta biyu a ka ta na rusa kuka mai ratsa zuciya. Kirjin sa cike da tausayin ta ya matsa kusa da ita da niyar mata magana, kan ya kai ga bude baki ya furta komai ta daka masa tsawa cike da tsana ta ce "Dallah kar ka matso kusa da ni munafukin banza munafukin hofi, na tsane ka, na tsane ka tun randa na fara dora idanu akan wannan muguwar fuskar ta ka, Allah ya isa tsakani na kai!" Ta wuce ciki fuuuu, in da Jaura ke kara goyan bayan abun da ta fada ta hanyar yiwa Usman shagude. Isa wanda gaba daya ya rasa ta cewa ne ya matso kusa da shi, ya dan taba kafadar Usman, sannan ya wuce dakin su na Maigadi, zuciyar sa cike da al'ajabi. Yanda ya shigo falon afujajan, fuska fal hawaye ga salati ya na futa daga bakin sa ne ya ruda su Ammy da Halitta wanda har lokacin ba su san wainar da ake toyawa a waje ba, su dai suna nan cikin tashin hankalin rashin samin Zainab a dakin ta. "Malam lafiya? Me ke faruwa? An yi Rashi ne?" Zama yayi dirshen a kan carpet, kai ya ke jinjinawa yayinda ya fashe da kuka mai karfin, ya na kuka ya ke fadin "Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun" Daga Ammyn har su Halitta su ma din kukan su ka sa, Dan kuwa ganin kukan Malam ba karamin tashin hankali ba ne. Ammy na kuka ta ke fadin "Malam me ya faru Yakura ta mutu ne?" Duban ta ya ke da idanun sa da su ka yi jajur, tsabagen bacin rai jikin san har rawa ya ke, murya na kakkarwa ya ce "Da wannan mummunar ranar gwara ranar mutuwar Zainab! Har ki na tambaya ko ta mutu? Wato kin ma san da fitar ta? Ki na nan shashashar uwa diyar ki na haura katanga ta fita yawan banza ki na tambaya ta ko mutuwa ta yi?" Ammy na mai girgiza kai ta ke fadin "Ban da masaniya idan ba dazu da na duba bata nan ba, wallahilazim kamar yanda ba ka sani ba....." "Ina amanar da na baki? Yau na yi dana sanin yawan nisa da ku da na ke yi! Yau na yi danasanin tura Yakura jami'a can uwa duniya! Yau na yi dana sanin rashin aurar da su da wuri da ban yi ba! Kun cuce ni! Yanzu ace cikin ku duka babu wanda ya san wannan halin da Zainab ke aikatawa ba? Har Mai gadi da yan unguwa su sani amma ku da kuke tare da ita ba ku sani ba?" "Wallahi ban sani Malam, wallahi ban sani ba in ba dai yau da Halitta ta sheda min ba........!" Cewar Ammy wacce kafin ta kai aya Malam ya katse ta cikin tsawa ya ce "Halitta ta sheda mi ki? Halitta kin sani ki ka boye min saboda tare kuke lalacewar ku ko? Tare ku ke cin mutunci na?" "Wallahi Dady ba tare mu ke ba, ban taba aikata makamancin haka ba, tsoran halinda za ka shiga ya sa ban fada mu ku ba......" Halitta ta bashi amsa cikin kuka. Murya kasa kasa ya ce "Halin da zan shiga? Kin gwammaci yar uwar ki ta cigaba da aikata barna ta na sabawa Allah ta na bata min suna a gari akan halin da zan shiga? Maigadi da yan unguwa su na gani har ana taruwa kofar gida na domin a sheda fuskar fitinanniya cikin 'ya'ya na! Zainab da na ke ikirarin ta fi kowa cikin 'ya'yq na sai ga ta tsakar dare tsakiyar maza sun dage sai sun ga kowacece ake kawo ta a mota, ta na haurawa tsabagen lalacewa da wulakanci?????" "Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun!" Wannan karan Ammy ce ke salati, hakan yayi daidai da shigowar Zainab wacce dama ta dade ta na shawarar shigowa falon ko kuwa ta yi zaman ta waje. Ganin ta Ammy ta yi wuf ta damko ta tana mai rufe ta da duka, fadi ta ke "Gwara na kashe ki Yakura! Gwara na kashe ki kafin ki kashe mu, haihuwa ba ta yi rana ba! Kashe ki zan yi na huta" Ihu da kukan Zainab be saka an ceto ta daga hannun Ammy ba, Malam na mai kawar da kai ya ce "Dukan ta da ki ke ba zai amfana mana komai ba, Zainab ta wulkanta ni, Ashe zan haifi diya irin ki Zainab? Ashe duk Kamala da na ke ganin ki da ita duk na munafunci ne? Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun yau na yi danasanin haihuwar diya mace irin ki Zainab, kin zalince ni, kin haince ni kin ci amana ta Zainab......." Kaucewa ta yi daga rukon Ammy, da sauri ta karasa gaban Malam, hannayen ta biyu ta sa ta ruko kafafun sa fadi ta ke "Dan Allah Dady ka yafe min, Dady ka yafe ni, Dady ka yafe min na tuba, duk hukuncin da ka yanke kai na zan bi, zan auri wannan dan abokin na ka da ka ke so na aura, amma dan Allah Dady kar ka min baki....." Jin haka sai ga Malam ya murmusa, ya na mai share hawaye ya ce " Ana idar da sallar asuba ku zo ku same ni a nan falon da na ke ba da karatu!" Ya tashi cikin hanzari har ya na hambare Zainab ba tare da ya kula ba ya fice ya bar Zainab hannun Ammy, dan kuwa ba ta fasa jibgar ta ba har sai da Halitta da Falmat su ka tausaya mata su ka shiga tsakani. Ammy na haki tsabagen yanda ta daki Zainab ta ce "Da sani na zaune ki tun ran da na haife ki da baki ja min wannan masifar ba!". ****** Kamar yanda Malam be runtsa ba, haka iyalan sa su ka yi kwanan zaune. Ko da aka kira sallar asuba Malam be fasa fita ya ja salla a masallaci ba. Bayan an idar ne ya nemi ganin masu gadin sa duka ukun. Zaune su ke falan da su ke daukar karatu, Malam zaune bisa doguwar kujerar sa, su Usman zaune gaban sa suna ta raba idanu cikin jiran tsammani. Jim kadan Ammy ta yi sallama, sanye ta ke cikin hijabi tun daga sama har kasa, kallo daya za ka mata ka tabbatar da matsanincin damuwar da ta ke ciki. Biye da ita Halitta da Falmat ne, suma din hijabin ne jikin su. Halin da ake ciki be hana Halitta satar kallan Usman ta wutsiyar ido ba, ta na mai adduar Allah ya sassauta mata son da ta ke yiwa wannan bawan Allah dan kuwa ko an kai dubu shi kawai ta ke iya hangowa duk inda ya ke muddin ta sa kafa a wajan. Ganin Malam ba shi kadai ba ne ba ya sanya su ka sami waje can gefan Malam domin samin tazara sosai tsakanin su da su Usman. Malam na shirin tamabayar ina Zainab sai ga ta nan kamar an cefo ta. Har lokacin hijabin da ta fita da shi ne a jikin ta, ta na shiga ta tsinci idanun ta cikin na Usman, hakan ya sa ta mummunar faduwar gaba tare da fargabar dalilin da ya sa Malam tara su tare da ma'aikatan sa maza, ta yi saurin dauke kan ta, kusa da su Falmat ta samu ta dan rakade. Malam kuwa ganin Zainab jiyayi wani ciwon bakin ciki ya tasar ma kahon zuciyar sa, idan akwai abin da ya tsani gani ya bi bayan Zainab. Gaba daya ta bata kan ta a idanun sa dan ji yake kamar ya sallama ta ya huta. Zaman ta ke da wuya Malam na mai kawar da tunanin da ya ke cikin zuciyar sa ya furta "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sa na tara ku nan tare da iyali na, Amma kafin na aiwatar da komai, ina so na san shin bayan diya ta da take haurawa ta na fita yawan dare, ku na ji kuna gani amma ku ka ki fada min, wata amana ta ku ka ku ke ci?" Ya na maganar ne idanun sa kan su Usman, in da duka su ka sunkuyar da kai, musammam Jauro wanda in ban da zufa babu abin da ke keto masa. Shiru ne ya biyo baya kafin daga bisani Isa ya nisa ya ce "Allah shi gafarta Malam, na rantse ma ka da Allah ban taba cin amanar ka ba, wallahi tallahi ban da masaniya akan wannan lamari da ya faru a daren yau, Ni ma lamarin sabo ne a gare ni" Ya kare maganar na sa cike da ladabi ya na mai tausayawa Malam dan kuwa damuwa tuni ta bayyana a tare da shi, lokaci guda tsuafar shi ta bayyana karara. Jauro na mai sakar zuciya ya sa hannu ya goge zufar da ke keto masa, jin Malam ya ce "Malam Jauro! Shin ka na da masaniya a kai?" "Ah ah Malam, lillahi wa rasulillahi ban da sani akan wannan lamari!" Ya ba da amsa cikin sauri ba tare da ya damu da kallan da Usman ya ke masa cike da mamaki ba. Shi kuwa Malam Usman ya ke kallo ya na mai nazari akan shi, bayan wasu yan dakikai Malam ya furta "Sai kai Usman, tun yaushe ka san da wannan barnar?" Idanun Zainab da Halitta kan Usman yayinda ko waccar su bugun zuciyar ta ya karu, in da na Halitta ke bugawa cike da tausayi, so da kaunar Usman, haka na Zainab ki bugawa cike da gaba, tsana da kiyayyar da take masa, gani ta ke duk duniyar nan ba ta da makiyi da ya wuce Usman. Cike da ladabi Usman ya ce "Ka yafe min Malam, ba a yi cikakken wata da sani na ba" "Wani dalili ya hana ka sheda min" Shiru ne ya biyu baya, dan kuwa Usman ya kasa budar baki ya bawa Malam amsa, sai ma sunkuyar da kan sa kasa da yayi. Malam ya ce "Ka yarda ka ci amana ta?" Usman yayi shiru ya na mai dada sin da kai. Malam na mai kara jaddada tambayar sa ya ce "Ka yarda ka ci amanar gadin da na ba ka? Ka yarda ka cutar da ni?" Usman na mai girgiza kai ya ce "Na yarda Malam" "Ka amince da duk hukuncin da zan yanke akan ka, ko da kuwa na korar ka daga gida na ne? ko kuma hana ka cigaba da aikin gadi a gida na daidai ne? Ka yarda adalci ne?" Wannan magana ta Malam ba karamin dadi ta yiwa Jauro ba, dama tunda Usman yayi azarzabin rufawa Malam asiri gaba daya bakin ciki da kishin Usman zai zama numba daya gun Malam ya kama shi, Amma ko da ya ga reshe ya juye da mujiya tuni zuciyar shi ta yi kal, shi dai fatan sa kar Usman ya shedawa Malam har da hadin bakin shi Zainab ke samin damar fita, gwara Malam ya kore shi kowa ya huta. Halitta kuwa idanun ta ne ya ciko da kwalla, musammam da ta ji ya amsa da "Na yarda Malam!" Tuni ta fara kukan zuci, Dan ta san halin Malam ya iya yanke hukunci cikin fushi, sam ba ta so ya kori Usman ko da kuwa zai dawo yayi dana sani. Shiru ne ya biyu baya, kafin daga bisani Malam ya nisa tare da fadin "Menene dalilin ka na rufa min asiri bayan ka bari ana barna a bayan ido na?" Shiru Usman ya kasa amsawa, Malam be gushe ba, ya kara fadin "Shin wani abu na ma ka da na cancanci wannan abu biyu daga gare ka? Cin amana da kuma rufin asiri? Ka ci amana ta, daga baya ka zo da rufin asiri? Ka na da wata manufa ne na yin haka?" Usman na mai girgiza kai ya ce "Ina neman yafiyar ka Malam, dan Allah ka min yafe min, ban da wata manufa da ya wuce kare mutuncin ka da gujewar tashin hankalin ka, na yi kuskure, ka yafe min" "Kai wanene?" Malam ya kara masa tambaya mai rikitarwa. Cikin nuna rashin fahimta ya ce "Ni Usman ne, ban taba tunanin cin amanar ka, ko kuwa zaluntar wani daga cikin iyalin ka ba" Malam na mai duban shi cikin nazari ya ce "Iya binciken da na yi akan ka kai bafulatani ne dan cirani, ka fito daga wata ruga da ake kira Rugar Shehu, bayan abin da ka min a yau ya sanya ina tsoran zamantakewa ta da kai, dan kuwa idan har za ka iya ganin diya ta cikin halaka haka ka kawar da kai, to ko shakka babu za ka iya halaka ni kai na! Wannan ya sa na ke son jin cikakken tarihin rayuwar ka, wanene kai, da wata manufa ka zo gida na?" Maganar Malam ta sanya zuciyar Usman rauni, cikin kokarin kare kan sa ya furta "Allah ya sani ban zo da cuta ba tun ranar da na sa kafa ta gidan nan, haka ma yanzu da na ke zaune gaban ka. Kamar yanda ka sani tun a baya, Sunana Usman, Usman Tanko, na zo ne daga rugar Shehu, in da maihaifina shi ke da sauratar Shehuntakar rugur, Ya gada ne tun kaka da kakan ni. Ba mu da takamamman wajan zama, dan haka yawo mu ke daji daji, mukan yada zango a duk dajin da Allah ya nufa, muddin akwai ruwan da shanun mu za su sha, haka ciyawa da da harawar da za su ci. Babban abin da Rugar Shehu ta yi suna akai kuwa shine surkulle dan haka ba ma zama a daji sai an yi surkulle an kafe dukkannin dajin kaf ciki da waje ya zama mallakin mu.............."     *Khadija Sidi*AUREN SHEHU 10. Khadija Sidi   Cikin daji mai suna santali wanda ya ke arewa moso gabashin mararrabar Nigeria da Nijar ne Rugar Shehu su ka yada zango. Babu laifi akwai ruwa da 'yayan itatuwa wadatacce hakan ya sanya su jimawa a dajin. Rugar Shehu ba su da wani yare face fulatanci, kaɗan daga cikin jama'ar rugar wanda su ke fita suna cudanya da hausawa ne ke jin hausa. Babu laifi mahaifina ya yi aure aure da yawa, duk a dalilin neman magaji kasancewar duka matan sa 'ya'ya mata su ke haifa masa wanda da sun kai shekara goma sha uku zuwa sha biyar ake mu su aure. Sai da ya haifi 'ya'ya Ashirin duka mata, har ya fitar da rai dan kuwa shekaru sun ja ya bawa arbain baya, sannan Allah ya amsa masa ya azurta matar sa ta hudu wacce dama ita ta fi kuwa karancin shekaru da haihuwar da namiji. Murna gun mahaifina ba a magana dan har kyautar shanu biyu mace da namiji yayiwa unguwar zoma da ta karbi haihuwar. In da mahaifina ke murna samun magaji, Dan uwan shi wanda ya ke cikin ummansa, shi maihaifina ya sha nono ya bar ma, babban abin bakin ciki ya zame masa dan kuwa ya ci burin kujerar da mahaifina ke kai, rashin magajin mahaifina shi ne babban takobin da ya rike. Kamar yanda Baffa Mudi ke bakin cikin jaririn da aka haifa, haka ma sauran matan gidan su ka nuna bakin ciki karara, dan sam babu wacce ke hubbasa wajan taimakawa mai jego, haka ta yi jegon ta sai dai 'ya'yan ta mata ko kuwa dai mokota su agaza mata, idan kuwa an ga sauran matan kusa to lalle mahaifina ke kusa, ana yi ne dan ganin idanun sa. Haka a daddafe sati ya zagayo, ranar suna aka sanya min suna Usman, mahaifina ke kira na "Magaji" wannan kalma ta zamo tamkar wuka a kirjin Kawu Mudi. Baffa Mudi ne dan uwa daya tilo da su ke ciki daya da Mahaifina, su biyu kacal Mahaifin su ya haifa a duniya. Matar Baffa Mudi daya, haihuwar matar shi goma sai dai biyar daga ciki sun rasu, biyar kadai ke a raya, duka mata ne. Bayan an haife ni da sati biyu matar Baffa Mudi ma ta haifi dan ta namiji, yaro ya ci sunan Mahaifina amma ana kiransa da Tanko. Gata da soyayya karara da mahaifina ke nuna min ba karamin bakin jini ya jawowa Iya ta da ni kai na ba. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, ana jifa da surkulle domin halaka mu, Allah kuma na kare mu. Tun kafin na cika shekara biyu a duniya na yaye kai na na ki nono, Wanda hakan ya nunawa Iya ta alamun cikin da ta ke dauke da shi. Murna gun mahaifina ba a cewa komai, shi dai fatan sa Allah ya maimaita a haifa ma sa da namiji. Cikin da Iya ta ke dauke da shi ya sanya Mahaifina dakatar da canza shekar da ake da niyar yi duk da kuwa ruwa da kayan itatuwa sun ja baya. Wannan ya bawa Baffa Mudi damar yiwa mahaifina zagwan kasa ta hanyar hore mu su kunne akan wannan hukuncin da mahaifina ya dauka saboda a cewar shi hakan na nuna rashin adalcin Shehun rugar. Da ya ke jama'ar rugar Shehu amintattu ne, kalilan ne su ka dauki zugan Baffa Mudi dan haka hakan sa bai cimma ruwa ba, Nan dajin Santali Iya ta ta sake haifo dan ta namiji, da mako ya zagayo aka sanya masa Muhammadu Bello. Sai da Bello ya dan yi kwari sannan aka tasanma barin dajin Santali, nan mu ka niki gari, mu ka hada kwan mu da kwarkwatar mu, mu ka shigo Nigeria, mu na tafe muna tare da shanun mu su na kiwo, duk in da dare ya mana mu yada zango. Duk yanda mu ka so kiyaye shanun mu kar su shiga gona, yau da gobe sai sun shiga, dan haka ko da yaushe cikin fada mu ke da manoma, wani sa'in har a kai da bata kashi. A haka Allah ya isar da mu wani yanki da ke cikin kungurmin dajin falgore. Bayan dube dube da Maihaifina yayi na surkulle ya ce a kafa bukkar rugar Shehu a nan dajin. Cikin sati daya aka kafe dajin nan kaf ya zama babu mahalukin da ya isa ya dumfari rugar Shehu da kowani barna ko mugun nufi. Toh rayuwar ruga dai haka mu ke yin ta, babu wutan lantarki, babu asibiti, babu makaranta babu ko wani irin taimako daga gwamnati dan kuwa idan ba dai wani tarzoma ta hado mu da manoma ba gwamnati ba ta waiwayan mu bare ta ba mu agaji, dan haka ban san wani abu wai shi boko ba. Ina da shekara hudu a duniya matar Baffa Mudi ta kara haihuwa, ta haifi diya mace wacce aka sa mata suna Ummakaltime, ana kiran ta Cangwai. Kasancewar mahaifina shi ne Shehun rugar dama shi ke koyar da yara da samarin ruga karatu wanda ya hada da kur'ani, littafan addini, sai kuma rubutu da karatun ajami. Soyayyar da ke tsakanin mu, da Kuma ganin ni ne magajin shi wanda ya ke sa ran zan zama shehu ya sanya shi ya fara ba ni ilimin surkulle tun ina dan shekara takwas a duniya, duk yanda ya so ya jawo Bello jiki a koyar da mu tare hakan ya gagara saboda lalurar bebantaka da ta sami Bello sanda ya na da shekaru biyar a duniya. Ba na manta ranar ta kasance wata juma'a ne aka tashi da rashin ladanin Rugar Shehu, bayan an masa sutura, aka kai shi kushewa aka rufe mu ka dawo gida mu tadda Bello na ta kurari da kuka, juyin duniyar nan an yi ya fadi abin da ke damun shi, amma ya gagara sai dai gwalangwalanto, wanda hakan shi ne karshen maganar sa kenan duniya. Sanda na cika shekara goma na fara kora shanu nawa na kai na, Mahaifina ya ba ni mace da namiji wanda su ke aure, cikin shekaru kalilan su ka hayayyafa sosai Allah ya albarkaci kiwo na sai gani da shanu har guda koma, sanda na cika shekara shabiyar a duniya shanu na tuni sun kai ishirin. Ba yaban kai ba, tarbiya da kuma yanayin karatu da na ke samu daga wajan Mahaifina ya sa na fita daban daga sauran matasan rugar mu, idan ka dauke Baffa Mudi da iyalan sa babu wanda ba ya girmama ni a rugar Shehu. Sam ba ma ga miciji da Tanko dan Baffa Mudi, dan kuwa yayi kauran suna wajan fiti na da neman fadan manoma, hakan nan babu gyara babu dalili ya ke kora shanu cikin gona su yi barna su bata amfanin gona ba dan komai ba sai dan neman fitina. Da ta fara fitinar mutane ne Mahaifina ya Umarci Baffa Mudi da yayi wa Tanko magana, ko dai ya canza hali, ko kuwa ya bar masa rugar baki daya. Maganar da ta kara kawo rashin jituwa tsakani na da Tanko kenan, har ta kai ba ya amsa sallama idan na masa. Idan kuwa batun amana ne sau dayawa jama'ar rugar Shehu na bani amanar Shanun su duk sanda su ke da uzuri, cewar su duk rugar Shehu ni kadai zan kora shanun jama'a na kiyaye mu su kamar yanda zan kora nawa, kafin ka ce menene tuni na kasance kamar mataimaki gurin Mahaifina wanda shekaru sun ja sosai, hidimomi da dama ba ya iya yi, duk yanda Baffa ya so ya ja ragamar shehuntakar kuma Mahaifina ya ki sakar masa, sai dai ya sanya na wakilce shi, cewar sa tunda ina da nutsuwa zaifi na fara gwada mulki tun ya na raye. Ba zan manta da wata ranar labara ba, lokacin ina da shekara goma sha bakwai, na dawo daga kiwo Mahaifina ke fada min shawarar da su ka yanke na daura min taubashiyata, daya daga cikin 'ya'yan Baffa Mudi, wato Cangwai. Cangwai dai yarinya ce mai hankali da nutsuwa, wajan kyawu ma babu laifi, idan aka dauke kiyayyar da mahaifin ta ya ke min sam bata da laifi, dan haka na yi na'am tare da godiya da wannan hadin. Iya ta kuwa nunawa ta yi sam ba ta yarda da wannan hadin ba, a cewar ta ba hadin alkhairi ba ne, yanda Baffa Mudi ba ya kaunar mu me zai sa ya so ya kulla wannan kulli haka? Sai da rai ya baci sosai tsakanin ta da Mahaifina, ni na zaunar da ita, na nusar da ita ce komai nufi ne na Allah, muddin ba ma nufin kowa da sharri to kuwa Allah ba zai bari a jefo mu da sharri ba, ta kwantar da hankalin ta, khairan in Sha Allah. Da haka da haka aka daura min Cangwai. Daya daga cikin bukkokin da ke wajen gidan Shehu mu ka tare cikin yarda Allah. Bayan sati daya da auren mu Cangwai ta fara laulayi, Iya ta ce ta fara lura da cikin da ta ke dauke da shi, za ta yi surutun yayi wuri na ce da ita babu komai ni da iyali na mun yi tarayya tun a daran fari, dan haka ba wani abu ba ne dan ta na dauke da juna biyu. Abu dai kamar wasa cikin kankanin lokaci cikin Cangwai ya bayyana sosai, Ni kai na na kanyi mamakin shin watanni nawa da auren mu da har abu zai fito sarari haka kamar kwarya? Gashi mu ba asibiti ba bare bokan ture ya duba ya fada min adadin watannin cikin. Dangantakar mu ya sanya ban yi kokarin neman warware wannan sarkakkiyar ba, na rufa asiri mu ka zauna haka, ko da wasa ban taba nuna mata wani damuwa ko bambamci ba, ina kula da ita kwatankwacin yanda na ke ganin Mahaifina ke kula da Iya ta, sai ita ce ma da na ga kamar ta na cikin damuwa, duk sanda na so na ji dalilin ta kan ce min babu komai. Iyar ta kullum ta na hanyar gidan mu, haka ma Baffa Mudi, ni kuwa sam ban taba kawo wani abu cikin rai na ba. Cikin wannan halin mu ka kai wata shida tare da Cangwai. Wata ranar lahadi da daddare na dawo daga hirar dare na tarar Cangwai ba ta bukkar mu, na yi tsammanin ta zagaya bayan gida, ni kuwa dama na debo gajiya sai na yi kwance bisa gadon karar mu bacci na diba na sama sama Ban yi cikakken minti goma da kwanciyar ba kamar daga sama na ke jiyo muryar su, a bakin kofar bukkar na ji mahaifiyar Cangwai na tambayar yaushe zan dawo. Cangwai ta ba ta amsar da sai can cikin dare ai wajan hira na je, Bukkar su ka shigo, Cangwai na niyar kunna futular acibalbal Iyatar ta ce ta bari saboda ba ta san jama'ar gidan su san da zuwan ta. Ina shirin mu su gyaran murya dan su san da ni kenan na ji Iyar Cangwai ta ce "Ba dai ki tona mana asiri ba ko?" Mutuwar zaune na yi jin amsa Cangwai na cewa "Ah ah Iya, Amma wallahi a tsorace na ke, gani na ke kamar fa ya san ba cikin shi ba ne, dama Baba ya sani ya bari sai da na zo gidan na sami cikin halak, ai ya fi......" Wani irin zufa na ji ya na keto min, Ashe dai duk yanda na so kar na zargi baiwar Allah nan ashe hainta ta su ka yi. Babban abin taikaici shi ne amsar da iyar ta ta bata, cewar ta "Ke yiwa mutane shiru! Wa ya ce mi ki Baban na ki ya na so ki haifa masa jika da wannan la'anan nan yaron? Ko kin manta dalilin da ya sa ki ka tare da sangami har ya mi ki ciki?" "Sangami" na maimaita cikin rai na, Sangami na daya daga cikin fitattun matasan da ke wata ruga kusa da rugar Shehu, mahaifin sa yayi suna kwarai wajan tarin shanu, haka kuma abokin fitinar Tanko ne. Iyar Cangwai ba ta gushe ba ta kara da "Kar ki manta yarjejeniyar da aka yi tsakanin Mahaifin Sangami da na ki, na farko dai ki samu ki haife dan nan, wannan wawan mijin na ki da Shehu su gama azazzabin samin magaji, sai a sheka su barzau, kin ga kenan burin Mahaifinki na zama Shehu ya tabbata, ke kuwa mu aurar da ke ga Sangami, tare da bawa baban shi rabin shanun rugar Shehu kamar yanda aka yi alkawarin matukar ya taimaka aka dauke Shehu da magajin su daga doran kasa, shi wancan beben dan na sa da mu ka lakasa tun shekarun baya be Isa ya aiwatar da komai ba, ina Bebe zai iya shehuntakar ruga? Ina ya ga bakin magana?....." "Usman mutumin kirki ne Iya, ba ki ga yanda ke mutunta ni ba, ya na kula da ni....." Cewar Cangwai cikin nuna damuwa, cikin hantara Iyar ta ta ce "Ke rufawa mutane baki! Ko dai kin fara son shi ne?" "Ah ah" "Toh idan kin fara sai ki zaba ko shi ko uban ki! Dama abin da ya kawo ni kenan! Na ja kunnan ki! Sakarya kawai na ji kin tona mana asiri uban ki ne a rana ai" "Zan kiyaye!" Da wannan Iyar Cangwai ta tafi, Cangwai ta fita ta dan taka mata. Jiki sanyaye na tashi zaune, dan tashin hankali na ma rasa abin yi bare na motsa. Zuciyar ta daya ta dawo, ashanar da na mata tsaraba da shi sanda na fita kiwo ta kesta haske ya gwauraya daki hakan ya bata damar ganina zaune na doka tagumi fuska fal zufa kamar wanda ke zaune gaban wuta. A razane ta ke dubana yayinda jikin ta ya dau kyarma, saura kirin ta wulgar da acibalbal din da ke rike a hannun ta Allah ya sa na tashi da sauri na riko shi. Gefe in da mu ka saba ajiyar shi na aje. Ina mai bata baya dan sam ba na kaunar ganin ta, na ce "Me ku ka yi ku ka nakasa kanina Bello?" Murya na rawa da alama ta fara kuka ta amsa min da cewa "Dan Allah kar ka tona min asiri, ka rufawa Mahaifina asiri na maka alkawarin kare lafiyar ka da mahifin ka...." "Ba wannan na tambaye ki ba!" Na katse ta cikin tsawa, juyowa na yi na karasa gaban ta, hannaye na biyu bisa kafadar ta ina mai jijjiga ta ba tare da na yi la'akari da tsohon cikin da ta ke dauke da shi ba na ce "Me ku ka yiwa kanina ya dena magana? Ko ki fada min ko na halaka ki da cikin shegen da ki ke dauke da shi nan take kafin na je na riske azzalumin uban na ki" Yanda ta ga na rikide cikin kankanin lokaci ya sanya ta kara tsorata da lafazan da ke futowa daga baki na, tana kuka ta ke fadin "Lokacin da abin ya faru ina da karancin shekaru, Amma dai na san surkullen da aka yi masa da tare da gawa aka hada aka birne, yanda gawar ba za ta kara magana a duniya ba, haka shi ma Bello ba zai sake magana a duniya......." Tas na dauke ta da mari kafin ta kai da karasa maganar ta, ta yi baya sauran kiris ta fada na riko ta da sauri cikin danasanin marin ta da na yi, dan kuwa tun da na zo duniya ban taba dukan wata diya mace ba, face Cangwai. "Dan Allah ka yafe min, kada ka halaka ni, zan hade kaya na, na bar rugar Shehu ba zan sake dawowa ba har abada" Takaici ya sa na kasa magana, kallan ta na ke cike da tsana karara cikin idona. Mun kai kusan minti biyar cikin wannan halin kafin na sake ta, rai na na kuna fice da bar mata Bukkar gaba daya gudun halin zuciya. Bukkar Mahaifina na nufa, ganin babu alamar haske ya sanya na sake shawara, na juya na fice ba tare da na dubi bukkar Iya ta ba, dan kuwa ba na jin zan iya tunkarar ta da wannan maganar ta tashin hankali cikin dare haka. Can turkar shanu na na je, Nan na kwana amma ban runtsa ba, yanda na ga rana haka na ga dare, sai da asuba ta yi sannan bacci ya fara dauka ta, ban kai ga runtsawa ba korarin Bello da ya zo ya na tashi na ne ya katse min baccin. Yanda ya ke maganar ya na mai nuni izuwa gida ya sanya ni kara tsanar Baffa Mudi, kiri kiri ya nakasa yaro karamin dan kawai san mulki da san zuciya, ban san sanda na fara zubar da hawaye ba, shi kuwa Bello da yayi tunanin sakon da ya isar min ne ya sa ni hawaye tuni ya fara kokarin lallashina, ya na mai dafa kafada ta, kafin daga bisani ya fara jan hannu na. Sai a sannan na fahimta lalle akai wani abun tashin hankali da ke faruwa a gida, da sauri na tashi, ko silifa ban saka ba. Bello na janye da hannu na mu ka isa gida. Mutane ne fal bakin kofar gidan wasu na alwala wasu kuma tabarma su ke shimfidawa, ganin Baffa zaune dirshen a kasa ga Tanko gefe ya na matsar kwalla, jama'a na ta min sannu da sai hakuri ya sanya na karasa cikin gidan da sauri. Cikin gidan ma tashin hankali na tarar, kuka da kurarin mata ne ke tashi, haka ina tsallake mata na isa ga bukkar Iya ta, Nan na iyi idu biyu da gawar Cangwai kwance, gefe kuwa Iya ta ce riƙe da jinjirar da ta haifa, cikin dare rai yayi halin sa bayan ta haifi diyar ta mace. Kalaman Cangwai ke dawo min sanda ta ke rokan karda na halaka ta, za ta hade kayan ta tabar Rugar Shehu ba za ta sake dawowa ba, ɗana sanin barin ta ita kadai da tsohon ciki ya mamaye ni, haka tsananin tsanan Baffa Mudi da shi kan sa mulkin da ya ke kwadayi har ya kai ga saka diyar shi cikin halak. Bayan an shirya Cangwai ana shirin a fito da ita, sai ga Baffa Mudi ya shigo, ya nemi a bar masa gawar zai gana da ita kafin a fito da ita. Tun da ya kebe da gawar hankali na ya kasa kwanciya. Ya dan jima ciki kafin ya fito ya ce za a iya fito da ita. Hankali na ya kasa kwanciya dan haka, kafin a kai da fito da ita na ce da su su dakata, Iyar Cangwai ta ce ban isa ba, tun dazu me ya hana na zo na mu yi sallamar karshe sai yanzu? Iya ta da sauran kishiyoyin ta ne su ka sa baki, haka ba a san ran Iyar Cangwai ba na shiga dakin. Ranar na yi abin da ban taba tsammanin zan iya ba, Yanda gaba na ke faduwa da hawayen da ke kwaranya daga idanuna be sa na fasa kunce suturar da aka yiwa Cangwai ba, hannun ta na hagu na yi arba da wani abu dunkule an daure shi da bakin kyalle, na yi sauri na sunce, daga waje ina jiyo Iyar ta na kuka da kururuwan na ki fitowa a tafi a rufe Cangwai. Cikin azama na tura abun cikin wandan saki na, hakan yayi daidai da shigowar Iya ta, ganin na bude Cangwai ta hau ni da fada, tare da taimakon ta mu ka yi sauri mu ka rufe ta, cikin kankanin lokaci aka sallace ta, mu ka je aka rufe ta. Cikin dare na sami Iya ta zaune dakin ta rike da jinjirar da Cangwai ta bari, ganina ta yi yunkurin bani yarinyar, Amma na ki karba. Hakan ba karamin tunzura Iya ta yayi ba, a zatan ta zafin mutuwar Cangwai ya sa na tsani jinjirar da ta bari. Nan kuwa kwashe komai na sheda mata, har da abinda aka kunsa hannun gawar Cangwai. Mamaki da takaici ne ya rufe iya ta, kuka ta ke cike da takaicin zaluncin da aka yiwa Bello. Tare mu ka kunce abin da na ciro daga hannun gawar Cangwai, laya ce mai dauke da sunana da sunan baro baro da rubutun ajimi, an rubuta "Kamar yanda gawar nan ta bar duniya, haka za ka bace a doran kasa Usman , kamar yanda wanan gawar ta ba za ta taba shakar iskar duniya ba, haka kai ma na za ka taba zama Shehun Rugar Shehu ba Usman" Ko da na gama karantawa Iya ta ba karamin tashin hankali da rudani ta shiga ba, da kyar na samu na kwantar mata da hankali, na kuma umarce ta da kar ta shedawa Mahaifina halin da ake ciki, ta bari mu sami mafita a tsakanin mu, dan kuwa halin da Baffa Mudi ya nuna zai aikata komai dan ya cima burin shi na san rai da san duniya. A wannan daren Iya ta ta yanke hukuncin da ya sa yayi sanadin bari na gida har na ke zaune tare da ku a yau, Iya ta ta umarce ni da na sakarwa Baffa Mudi Shehuntakar Rugar Shehu, ta Umarce ni da tunda a nashi tunanin ya birne gawar diyar sa da surkullen watsa ni uwa duniya, matukar ya ga ban tafi ba zai fahimci asirin sa ya tonu, ya kuma cigaba da kulla zalunci har ya kai ga cin nasara, da na bi uwa duniya ba a cikin hayyaci ba, gwara na tafi da niyar neman ilimi, dan haka ta na so na hada kaya na, na shiga arewacin Nigeria, duk gidan da na ga Malami na tabbatar na nemi ilimi daga gare shi, haka kuma duk sanda na canza sheka na sami hanyar sanar da ita ko da kuwa hakan ya na nufin ziyartar ta ta shigar batda kama, ita kuma muddin ta san in da na ke za ta turo min Bello duk sanda bukatar haka ya taso. Ina ji ina gani haka ta hade kaya na, ba tare da na yiwa Mahaifina sallama ba na baro Rugar Shehu na shiga uwa duniya..." Usman ya nisa, ya na mai duba Malam ya kara da "Hakan ba karamin ciwo ya yiwa Mahaifina ba, a tunanin shi mutuwar Cangwai ya sa na bi uwa duniya, tun ya na cigiya har ya sadakar ya fawwalawa Allah. Shekara goma sha biyu kenan da barin Rugar Shehu, kamar yanda Iya ta ta umarce ni, na kan ziyarce ta duk sanda na sami dama cikin bat da kama, haka kuma duk in da na ke tana da masaniya akai, ina barin mata bayanin wajan a rubuce, ta kan aiko Bello duk sanda bukatar haka ta taso. Allah yayiwa Mahaifina rasuwa bayan shekara uku da barin Rugar, yanzu haka Baffa Mudi ne Shehun Rugar" Usman ya kare maganar cikin kewar Iyar sa da bakin cikin mahaifin sa ba tare da sun samu sun gana ba. Gaba daya falon babu wanda be tausayawa Usman ba, Musammam Halitta wacce har hawaye ta zubar saboda hakan. Cikin jimami Malam ya nisa ya ce "Da farko dai ina ma ka ta'aziyar rashin mahaifin ka, da kuma matar ka. Ba kai kadai ka ci amana ta ba, hatta yar ciki na ta ci amana ta, idan kuwa haka ne na yafe ma ka duniya da lahira......" Karar wayar Malam ne ya katse maganar da ya ke, ko da Malam ya duba ya ga makocin sa kuma daya daga cikin amintattun abokan sa ne Alhaji Sidi, ya daga wayar, bayan sun gaisa ya ce da shi ya jira ana zuwa. Bayan da ya aje wayar ya umarci Jauro ya je ya budewa Alhaji Sidi gate, ya shigo da shi ciki. Cikin himma Jauro ya fita, in da Malam ya dakata da jawabin shi har lokacin da Jauro ya shigo biye da shi Alhaji Sidi tafe. Alhaji Sidi na mai bawa Malam hannu yayinda ya zauna kusa da Malam ya ke tambayar abin da ke faruwa cikin al'ajabi, Da safiyar nan ya ji dan sa ya shigo da wani labari hakan nan babu dadin ji, wai an kama wata yarinya ta na haurowa daga gidan Malam, shin menene gaskiyar maganar? Murmushin yake ne ya maye fuskar Malam, hannun sa cikin na Alhaji Sidi ya ce "Zan ma ka bayani Alhaji Sidi, Amma kafin nan na ji dadin zuwan ka har rai na, domin kuwa ina da bukatar shedu, zuwan ka ya cika min shedun na ke bukata" "Shedu? Na me kuma Malam?" Alhaji Sidi ya tamabaya cike da mamaki. "Kar ka damu Alhaji, a sannu za ka fahimci komai, ina kai Usman matso nan kusa da ni" Cikin shakku Usman ya taso ya zauna gaban Malam in da ya nuna masa. Malam na mai dafa kafadar sa ya ce "Usman a daren jiya ka yi min abinda babu wani mahaluki da ya taba yi min cikin duniyar nan, ka rufa min asirin da diyar cikina ta so tona min a duniya, ba zan yi butulci akan jarabawar Allah ba, Allah ya jarabci annabin sa, annabi Nuhu AS ta hanyar dan sa, sa bare ni da ba ko wan kowa ba, Amma akwai alfarma daya da na ke so ka min...." Ya karasa maganar ya na mai duban Usman. Cikin girmamawa da kaskantar da kai Usman ya ce "Malam duk abinda ka ke so ni mai yi maka ne, wanda ya ba ka ilimi nan duniya ai ya ma ka komai" Cikin jin dadin amasar da Usman ya ba shi Malam ya ce "Ina so ka taimaka ka auri diya ta Zainab..." A firgice Usman ya dago ya kalli Malam, haka ma Halitta da su Ammy, gaba daya falon babu wanda be girgiza da maganar Malam ba, Zainab kuwa ji ta yi gaba daya dodon kunnan ta ya toshe tsabagen yanda maganar ta doki kunnan ta. Cikin in'ina Usman ya furta "Ma...l..am" Alhaji Sidi kuwa mamaki ne ya sanya shi furta "Me ke faruwa haka? Wata Zainab ka ke nufi ne haka?" "Diya ta ta ciki na, ka ga wannan bawan Allah da ke zaune gaba na? Shi ne kadai zai iya rayuwar aure da waccar yarinyar asiri na ya rufu, dan kuwa ya rufa min asiri a yau fiye da tunanin ka! Wannan dalilin ya sa na yanke hukuncin daura ma sa ita ta zame masa halak malak ko mutuwa na yi na san na fita hakkin ta" Jin haka tuni Zainab ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, fadi ta ke "Dan Allah Dady ka yafe min kar ka yanke wannan danyan hukuncin a kai na, dan Allah Ammy ki sa baki, dan Allah Halitta ku taimaka min, Alhaji ku sa baki" Hawaye ke zuba daga idanun Halitta daya na bin daya, kiri kiri ta na ganin mahaifin ta na shirin mata yankar kauna tsakanin ta da masoyi abin kaunar ta. Cike da kishi Jauro ke duban Usman, da ya san Malam zai yanke hukuncin haka da shi ma ya ce Zainab matar shi ce, yanzu gashi Usman da ya zo ya tarar da su cikin gidan ya sami garabasa kara zube. "Malam dan Allah kada ka yanke hukunci cikin gaggawa haka, Yakura jinin ka ce, kada ka bata rayuwar Yakura" Ammy ce ke magana cikin magiya. Idan Malam ya ji Ammy toh sam be nuna alamun da shi ta ke ba. Ya na duban Usman ya ce "Kai na ke tsimayi Usman, shin ka karba? Za ka iya auren diya ta?" A hankali ya daga idanu ya kai kallan sa ga Zainab wacce ta ke kuka mai fitar da sauti, har ga Allah be taba jin wani abu na so game da ita ba, bare yayi tunanin aure zai shiga tsakanin su. Yanda ta ke kallan sa ne ya sa shi saurin kau da kai gefe "Usman?" Malam ya kira sunan sa da kakkausar murya. "Na'am Malam, na yarda na amince, sai dai matsalar abu biyu ne" "Ina sauraran ka Usman" "Banda kudin sadaki, haka kuma banda muhallin da zan iya aje mata Malam" Jin haka Malam ya dara tare da fadin "In dai wannan ne matsalar ka toh Alhamdulillah, na tabbatar ka haddace Riyaadul Saliheen?" Cike da girmamawa ya gyada kai alamar eh. "Toh Alhamdulillah, na yanke maka wannan littafin a matsayin sadakin Zainab, ina so ka koyar da ita wannan littafai, batun muhalli kuma ga BQ nan babu kowa da ciki, zan sa a gyara maka ku zauna, Allah bashi idan ka yi na ka sai ku tashi ku koma can ko?" Baki bude Ammy ta ke duban Malam har ya kare jawabin sa, ba ta taba tunanin Malam zai iya kaiwa matuka wajan wulakanta ta da yaran ta ba sa sai a yanzu. "Innalillahi wainnailaihi rajiun yau! Innalillahi wainnailaihi rajiun! Innalillahi wainnailaihi rajiun!" Salatin da Zainab ke yi kenan cikin kuka, dan kuwa ji ta ke kamar rayuwar ta ce ta zo karshe. Halitta ma kukan ta ke haka ma Falmat wacce tausayin yar uwar ta ya maye zuciyar ta. Alhaji Sidi na mai gyaran murya ya ce "Malam ran ka a bace ya ke, ka tuna yanke hukunci cikin fushi....." Hannu Malam ya daga masa, ganin haka Alhaji Sidi yayi shiru. Kana Malam ya ce "Malam Usman dama kai namiji ne, kai kan ka mai karɓa ma kanka aure ne a kaidar shari'a ka isa ka karbarwa kan ka aure, ga shedu uku nan, Jauro, Isa da kuma abokina Alhaji Sidi, dan haka idan ka shirya sai a hanzar ta a daura auren ko?" Kai Usman ya gyada abun ya zo masa kamar almara. Haka kuwa Zainab ta na ji ta na gani Malam ya daura mata aure da Usman, akan sa dakin koyar da ita littafin Riyaadul saliheen. Ana shafa fatiha Zainab ta zube mu su nan sumammiya.Auren Shehu 11   Ganin Zainab a sume da kururuwan kukan su Ammy sam be sa Malam ya motsa ba. Alhaji Sidi ne ma ya kawo doki ya na mai umartar Usman yayi maza ya dauko ruwa daga cikin fridge din Parlour. Ammy da Falmat ne ke jijjiga kafadun ta, Halitta kuwa kasa motsawa ta yi, hukuncin da Malam ya yanke ba Zainab yayiwa ba, gani ta ke tamkar ita Malam yayiwa gwale gwale, ta na ji ta na gani wanda ta ke so, ta ke kauna ya zamanto miji ga yayar ta uwa daya uba daya. Yayyafin ruwan sanyin da ya sauka fuskar ta ya sanya ta farfadowa, a hankali ta bude idanun ta. "Alhamdulillah, Malam ta farfado ka yiwa Allah ka warware auren nan, Alhaji Sidi ka sa ba ki!" Ammy ke magana cikin magajiya ta na mai rungumo Zainab wacce ta ke ji kan ta na sarawa tsabagen ciwon da ya ke ma ta. Maganar da Ammy ta ke yi ne ya sa ta farga ta tuna da halin da ta ke ciki, kuka ta saki mai tsuma zuciya ta na fadin "Dan Allah Dady na tuba, ba zan kara ba, Dan Allah Dady kar ka daura min wannan nauyin a kai na Dady!" Idan dutse na motsi toh Malam ya motsa, ko nunawa ya san da shi ta ke bare ya amsa mata be yi ba. Usman wanda kamar yanda Zainab ke kukan bakin ciki shi ma har ga Allah wannan auren da aka daura ma sa be so ba, shi ya fara zamewa ya fice daga parlour, Jauro da Isa su ka bi bayan shi. Ammy kuwa Alhaji Sidi ne ya ce su dan ba shi wuri su zanta da Malam in Sha Allah za a sami mafita. Zainab kwance jikin Ammy kamar mai jinya haka su ka fice ya rage daga Malam sai Alhaji Sidi. Alhaji na duban Malam ya ce "Malam kai fa mai sani ne, ka sani cewa yanke hukunci cikin fushi da gaggawa na tare da dimbin danasani, shin me wannan yarinyar ta aikata da har za ka yanke wannan hukuncin mai nauyi akan ta Malam?" Ga mamakin Alhaji Sidi sai ga Malam ya na zubda hawaye. "Ya hayyu ya qayyum! Munin abun ya kai haka?" Cewar Alhaji Sidi cikin alajabi. Kai Malam ya girgiza, kana ya ce "Alhaji Sidi ka na daya daga cikin amintattuna na, abokin arziki da amana, Alhaji Sidi ba zan boye ma ka komai ba. Na kasance mai rauni aka 'ya'ya, musammam ma Zainab. Allah ya jarabce ni da diya, sai dai na ce Alhamdulillah. Amma Zainab ba ta min adalci ba, ina nan idanuna kan 'ya'yan wasu, Wai ni Malami mai wa'azi ashe tawa diyar wacce na fi yarda da ita ta nan ta na barna a bayan ido na, Innalillahi wainnailaihi rajiun.....!" Nan Malam ya kwashe komai ya fadawa Alhaji Sidi, ya kare maganar da "Yaron da zai kare mutunci na haka, wanda zai rufa min asiri haka me zai hana na bashi ita? Yanda ya ke da kyawawan halayya ina kyautata zaton idan har Zainab ta zauna karkashin sa, ta nemi wannan gatan ta take da shi ta rasa za ta nutsu Alhaji Sidi, haka kuma Na yi imanin Usman zai ruke ta da amana" Cikin jimami Alhaji Sidi ke jinjina kai, kana ya nisa tare da fadin "Innalillahi wainnailaihi rajiun! Zainab ba ta kyauta ba, duk da dai har da sakacin ka Malam, ai ba a shedar dan yau Malam, ka yarda da Zainab da yawa, haka kuma Hajiya ta yi sakaci duk dai rabin rayuwar yarinyar nan ba a gida ta ke yi ba, Amma da ana bibiyan ta duk sanda ta dawo da duk wannan masifar ba ta afku ba Malam, yardar ta yi yawa, sakacin yayi yawa!" "Ka duba yanda na tsani kare Alhaji Sidi, har karnuka na debo na sa a gidan nan tun sanda mu ka fara zargin ana hauro mana gida, ashe dai tawa karyar ta gida ce......" "Waiyazubillah!" Alhaji Sidi ya katse Malam cikin hanzari, be gushe ba ya kara da "Ka kausasa harshe da yawa Malam, Amma wani hanzari ba gudu ba, yarinyar nan haura katanga ta ke, ta na fita yawan dare, shin ka tambaye ta ina ta ke zuwa? Shin iya ka yawan abun ya tsaya? Ta na nan matsayin ta na budurwa ko kuwa dai istibiraqi ya hau kan ta?" "Diya ta ba mazinaciya ba ce! Na yi imani diya ta ba za ta aikata zina ba kamar yanda ni ma ban taba aikata zina ba " Malam ya bashi amsa kai tsaye. Kai Alhaji Sidi ya dafe, cikin nuna bacin rai ya ce "Ga ba irin ta ba! Ka na shedar gaibu kai tsaye! Ka taba tunanin Zainab za ta iya tsayuwa da wani da namiji? Bare kuma har ta na yawan dare? Amma yanzu ina gari ya waye? Haba Malam ya ka na Malami kana da sani ka ke ta ke sanin haka?" Shiru ne ya biyu baya na dan wani lokaci, sannan Alhaji Sidi ya ce "Na sani Malam, it's not easy, shi ya sa na ce ma ka kada ka yanke hukunci cikin fushi, Dan kuwa matukar yarinyar nan akwai istibiraqi kan ta auren nan sai an warware shi....." "Idan kuma babu wallahilazim sai ta zauna da mijin ta matukar ba shi da bakin sa ya sake ta ba" Ajiyar zuciya Alhaji Sidi ya saki, kana ya ce "Idan har auren be sabawa addinin musulunci ba, be saba shari'a ba ai aure kam ka daura shi Malam" Kai Malam ya jinjina cikin gamsuwa, Amma har ga Allah ba ya fatan wargatsewar auren Zainab da Usman, har lokacin be yi dana sani ba, ba kuma zai yi dana sani ba, da wannan kudirin su ka yi sallama da Alhaji Sidi. Maimakon ya kira Zainab kamar yanda yayiwa Alhaji Sidi alkawari, sai ya kiran kiran su Jauro yayi ya ba su umarnin su taya Usman a kwashe kayan BQ gaba daya a gyarawa Zainab da Usman dan kuwa a ranar za ta tare dakin mijin ta. Ganin yanda su Isa su ke kai kawo hauka ne kawai Zainab ba ta yi ba. Hatta wayar ta da ta addabe ta da kara ganin Mike ne ke damun ta ba ta san sanda ta doka shi kasa ba, screen ya fashe. Halitta kuwa tun da su ka baro wajan Malam ta shige dakin ta ta kulle, kuka ta yi sosai kamar ran ta zai fita, duk da ba ta taba tunanin samin Usman a matsayin miji ba, Amma kasancewar shi mijin yar uwar ta abu ne mai ciwo a gare ta. Sam Ammy ba ta damu da halin da Halitta ta ke ciki ba, a tunanin ta halin abin da ya faru da Zainab ne ya sanya ta halin da ta ke ciki. Yan uwan Malam na jiki da kuma na ta yan uwan da su ke ta kira ta saka mu su kuka, cewar ta su kawo mu su doki Malam ya bayar da auren Yakura ga Maigadi, auren ma na sadaka ba tare da sadaki ba. Haka su ka ringa kiran Malam ya na gani ya ki dauka, karshe ma kashe wayan yayi gaba daya. Haka kuma ya ki sauraran ta bare su yi magana, tun ta na kuka har ta koma fada fada, ta na cewa Malam ya tsane ta ya tsani yayan ta shi ya sa ya mata wannan wulakancin. Kafin azahar ta yi su Usman su ka gama gyaran BQ tas, dama kanana dakuna ne guda biyu, sai dan karamin kitchen da bandaki. Tun da su ka fara aiki Jauro ke jifan Usman da Habaici, bini bini ka ji ya ce "Dan cirani an zama dan masu gida, an bar daji an zo birne ana mana surkulle" Ko kuma ya ce "Kai da na sani ni ma na yi kanzagi wajan neman suna da fa Malam ya dauran mata...." Usaman na jin shi amma ya masa banza dan kuwa idan akwai abun da ya dami kwakwalwar sa ya bi bayan auren Zainab da aka daura masa, har ga Allah be da niyar kara aure saboda yanda auren shi da Cangwai ya kaya, bare kuma Malam ya aura masa mace wayayyiya, yar birni kuma yar boko kamar Zainab, shin ya rayuwar shi da Zainab zai kasance? Da wani idanu zai dubi Malam ya roke shi da ya sauwake masa wannan nauyi da ya dora masa? Da wannan tunanin a ran sa ya wuni, dan kuwa ranar sam be sami kwanciyar hankali ba bare har ya samu ya kai lomar abinci bakin salati. Bayan la'asar Malam ya nemi ganin Usman a falon sa, Nan ma Jauro ya fara "Dan masu gida sirikin Malam, an baka mata an baka wajen zama, maza je ka kila abin hawa kuma za a baka, kai ya kamata ka mu sirrin wannan surkullen na ka!" Usman be kula shi ba ya wuce falon Malam. Sanye ya ke cikin rigar sakin shi fara, da bakin wando, fuskarsa rufe da farin rawani. Ganin takalma a waje ya sanya shi sallama tare da tsayawa daga waje. Malam ne ya amsa masa sallam sannan ya ba shi izinin shigowa. Ganin ta zaune tare da Halitta sai da gaban shi fadi, badan komai ba sai dan yanda dukan su biyun su ka zuba masa idanun su da ya yi jajur kai ka ce mutuwa aka mu su, in da Halitta ke kallan sa cike da kewa, so da kauna, Zainab kuwa tsantsan tsana ne cikin na ta idanun, dan kuwa nan duniya idan akwai wanda ta tsana ya bi bayan Usman, wanda a yanzu haka shi ne mijin ta. Da sauri ya kawar da kai gefe ya sami waje can baya ya na shirin zama Malam ya ce ya motso kusa da shi ya zauna. Cike da jin nauyi ya matsa gaban Malam wanda ke zaune kan doguwar kujera. Malam na daga zaune ya ke kare mu su kallo, Halitta sanye cikin bakar abaya, kan ta nade da mayafin, Abin ku da farar mace har wani jaja fuskarta ta yi tsabagen kukan da ta sha. Shi kan shi Malam yayi mamakin damuwar da Halitta ta shiga sanadiyar hukuncin da ya yanke na auran yayar ta. Zainab kuwa Hijabin jikin ta har jirwaye yayi tsabagen hawaye da majinar da ya sha. Daci rai da bakin ciki ya sanya shi saurin dauke kai daga kallan Zainab yayinda ya furta "Na yanke hukunci cikin gaggawa ba tare da na tambayi abu mai muhimmanci na game da shiri'ar musulunci ba sai da Alhaji Sidi ya nusar dani, ka sani Usman ko kadan ban yi danasanin daura ma ka diya ta da na yi...." Jin haka wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar Zainab, a tunanin ta Allah ya amsa adduar ta, Malam zai saka Usman ya sauwake mata igiya ukun da Malam daure ta da shi. Malam be gushe ba ya cigaba da fadin " akwai tambaya mai muhimmanci da ya kamata na yi mata kafin na daura ma ka ita, kuma zan yi mata shi gaban ka tun da tsakanin mu da kai babu boye boye, amsar da za ta bani shi zai bani haske akan tarewar ka da ita ko kishiyar haka..." Usman na mai dukar da kai cikin fatan Allah ya warware masa wannan nauyi da aka daura masa ya furta "Na'am" Zainab ba ta ankara ba sai ji ta yi Malam ya kira sunan ta da kakkausar murya ya na mai fadin "Zainab ki duba girman Allah, tsakanin ki da Allah ki kin taba aikata zina? Yaushe ne ranar karshe da ki ka aikata?" "Innalillahi wainnailaihi rajiun!" Cewar Zainab hannun ta biyu ta sa ta toshe bakin ta tsananin kukan da ya ci karfin ta. Ita kan ta Halitta tambayar ta mata tsauri da bazata, shi kuwa Usman kan sa sunkuye ya na jiran amsar da zai iya zama mafita a rayuwar sa. "Ke dallah rufa mana baki! Ki amsa min tambaya yanzu yanzu shasha kawai! Ba kya yawo ne? Idan ke kamila ce kamar yanda na yi tunani a da me zai sa na mi ki wannan tambayar? Ko za ki ce min ba ki taba kusantar zina ba idan har ma ba ki aikatawa ba!" Malam ya fada a fusace, hakan ya sanya Zainab saurin fadin "Wallahi dadi na rantse da Allah ban taba aikata zina ba Daddy, Daddy wallahi iyakaci na club, shi ma na maka alkawari ba zan kara zuwa ba Daddy...." "Diya ta ni Birma a club!" Malam ya katse ta cike da takaici. Zainab ta kara da "Daddy idan har ka aurar da ni ga Sudais zan kasance mace ta gari a gare shi, Daddy ban taba zina ba Daddy, Daddy dan Allah ka sa ya sake ni, Daddy na tuba....." Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar Malam, dan kuwa shi kan shi ya san da Zainab mazinaciya ce tabbas zai iya hadiyar zuciya ya mutu. Ya na mai godiya ga Allah da iya club din ya tsaya, ya ce "Bakin alkalami ya bushe, Usman shi ne mijin ki, auren shi ya tabbata akan ki...." Kukan Zainab be sa Malam ya tausaya mata ba, idanun sa kan Usman ya ce "Usman ga ta nan halak din ka ce, ci, sha da suturar ta ya rataya hannun ka, dan Allah ka kasance mai adalci, Zainab amana ce gun ka, na ba ka ita amana ko bayan rai na, kamin alkawarin duk runtsi duk wuya ba za ka sake ta ba, dan Allah Usman....." "Malam ba sai ka roke ni ba, Na daukar maka alkawari, Zan ruke ta amana, Na dau maka alkawari matukar ba a shiga hakkin Allah ba, ba zan taba sakin ta ba" Jin alkawarin da Usman ya daukarwa Malam kamar wuka ya ke daba mata a kahon zuciyar, wasu zafafa hawaye ne ke zuba daga idaniyar ta tamkar wuta. Malam na duban Halitta wacce ita ma din hawaye ne ke kwaranya daga idanun ta jin alkawarin da Malam ya sa Usman ya dauka, Malam ya ce "Halitta na yanke hukuncin ba da auren ki ga Sudais amadadin yar uwar ki, in Sha Allah kamar yanda mu ka tsara shabiyu ga wata juli zai kasance ranar daurin auren ki" Da dashasshiyar muryar ta Halitta ta amsawa Malam da "Toh Daddy, na yi biyayya" "Allah ya mi ki albarka" Halitta ta amsa da amin, kafin ya mayar da kallan sa ga Zainab wacce jin za a daurawa Halitta Sudais ba karamin bakin ciki ne ya kara taruwa cikin zuciyar ta ba. Gani ta ke Malam ya tsane ta cikin 'ya'yan sa ya aurar da ita ga Mai gadi, gashi zai aurar da Halitta ga dan abokin sa. Ba ta kara sarewa da Malam na sai da ta ji ya ce "Usman sai matar ka ta hado na ta ya nata ku tare can BQ da na tanadar mu ku ko? Da ga yau kada ta sake kwanan min cikin gida, ki kwana dakin mijin ki, na sallame ki har abada" Daga Usman har Zainab Malam su ke kallo, ganin babu alamar sassauci a fuskar sa ya sanya Usman kallan Zainab, kamar yanda yayi imani zai mutu haka ya tabbatar da tashin hankalin da ke tattare da Zainab.       *Khadija Sidi*Auren Shehu   12     Umarnin da Malam ya bawa Zainab na ta koma BQ ba karamin tashin hankali ya haddasa tsakanin Malam da Ammy ba, abin da bai taba shiga tsakanin Ammy da mijin ta ba ranar kuwa sun yi abin sam ba dadin gani bare ji. Shi kan shi Malam mamakin dama akwai ranar da Ammy za ta dubi tsabar idanunsa ta gasa masa maganganu haka ya ke. Ya na daga kwance ya ke kallonta, tun shigowar ta falon ta tsaya kan sa hannu rike da kugu in da ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba, sai da ta dan tsagaita Malam ya furta "Alesha kin gama?" "Ban gama ba Malam, idan ka ga na gama to ka raba wannan bakin aure mai cike da cuta da ka kulla tsakanin diyarka ta cikinka da Mai gadi wanda be da asali Malam! Ai ko addini cewa yayi mu zaba ma 'ya'yan mu mazaje na gari, haka kuma mu yi bincike akan mutum kafin mu ba su auren 'ya'yan mu, ban ga dalilin da zai sa ka lalatawa yarinya rayuwa ka aura mata maigadi wanda ba mu san komai game da shi ba! Ni jinin shuwa sulallan gwal ka biya sadaki na, Amma ka dauki diya ta, jini na ka bayar da ita sadaka!" Ammy ta bashi amsa cikin tsiwa. Shiru Malam ya mata tamkar ba da shi ta ke magana ba. A hasale Ammy ta furta "Malam ka na ji na fa!" Dagowa yayi yana duban ta, ainihin so da kauna na hakika ya ke yiwa baiwar Allah nan, dan kuwa yanda ya ke san ta be so uwargidan sa Hajja Kulu ba, badan komai ba sai dan Ammy ita ce zabin ran sa, uwargidan sa kuwa zabin iyaye ce. "Alesha duk yanda ki ke tunanin kaunar ki ga Zainab ya kai, ba ki fi ni san ta ba, Ni ne mahaifin Zainab dan haka ba zan cutar da Zainab ba, aure kuma na daura, babu abin da zai kashe auren nan sai Allah....." "Karatun ta Malam? ka na nufin ka salwartar da karatun ta kenan? Yakura ta yi nisa a jami'a, wata daya ya rage su koma makaranta, aji uku Yakura ta ke, semester daya ya rage ta shiga aji hudu, yar jami'a ka daurawa ma Maigadi dan ruga Malam!" Ammy ta katse shi ta na maganar ne kamar mai shirin fashewa da kuka. Cikin halin ko in kula Malam ya ba ta amsa da "Wannan tsakanin ta da mijin ta ne, karatun na ta, idan ya ga zai iya barin ta ta karasa fabini'ima, idan ba zai bari ta karasa ba ma wannan zabin sa ne..." "Toh kuwa sai ka zaba! Aure na da kai ko kuwa auren Zainab da Maigadi! Wannan zalinci ba zan iya jurar ganin shi ba!" Gaban Malam ne yayi mummunar faduwa, da sauri ya tashi tsaye ya na mai duban Ammy ya ke fadin "Alesha? Ni ki ke fadawa haka? Auren mu ko auren Zainab?" "Kwarai Malam, ba zan iya zama gidan nan diya ta ta ciki na ta na auren Maigadi ta na kwana a BQ ba, ba zan iya zuba ido ina kallo ana tauye hakkin diya ta ba, ka zaba Malam" Ta bashi amsa cikin dakiya, dan kuwa ta san yanda Malam ke kaunar ta ba zai taba zaban wani bayan ta ba duk da tsanar subda ta ke zargin ya yi. Ga mamakin ta sai ji ta yi Malam ya ce "Na zabi auran Zainab da Usman, sai yaya? Me zai biyo baya?" Zuciya tsinke dan kuwa sam ba ta yi zato ba Ammy ta ce "Ka zabi ka sake ni kenan? Saki nawa ka min?" Kai Malam ya girgiza yayinda ya koma ya zauna, fuskar sa dauke da murmushi ya kai hannun sa ga qur'anin da ke aje can gefe bisa dan teburi. Ya na kokarin budewa Ammy ta sake fadin "Saki nawa ka min" Ya na murmushi kaici ya ke girgiza kai, kana ya ce "Alesha ashe dai har yanzu ba ki dena tunani irin na yara ba, saki? Ni Birma na saki mata ta? Ban taba sakin iyali na ba, ba zan fara akan ki ba Alesha, kin ce na zaba ko auren Zainab da Usman, ko aure na da ke, na zabi auren diya ta, ban yarda na mayar da diyata bazawara ba, haka kuma ban sake ki ba, ba zan kuma sake ki ba...!" "Ni kuma ba zan zauna da azzalumin miji irin ka ba! Kai ne kullum cikin wa'azi Allah ya ce annabi ya ce! Amma ka kasa kare hakkin iyalin ka sai ma cutar da mu da ka ke kokarin yi! Allah ya saka mana! Ko ka sake ni ko ba ka sake ni ba zama na da kai ya kare!" Baki bude Malam ke duban ta ya kasa magana tsabagen mamakin maganganun da Ammy ke fada masa. A fusace ta juya fuuuu ta fice ta na mai buga masa kofa ta wuce bangaran su. Ganin yanda ta shigo a fusace ya sa Falmat bin bayan ta tana tambayar Ammy lafiya? Me ya faru? Ba ta bata amsa ba, sai ma hade kayan ta da ta shiga yi. Cikin kankanin lokaci ta hade kayan ta tsaf cikin yar akwati. Ganin haka Falmat ta kira Halitta da Zainab wanda duk abin nan da ake ko waccar su na dakin ta tana fama da kan ta. A falo su ka tadda Ammy ta na jan akwatin ta niki niki za ta fita. Iya na tambayar lafiya Hajiya za ki yi bulaguro ne? da sauri Halitta ta karasa gaban ta, ta na mai taro akwatin ta ke fadin "Innalillahi Ammy me zan gani? Ina za ki je haka da yamma likis Ammy?" "Gidan uban ku zan bari, aure na da shi ya kare, ya zabi auren Zainab akan aure na da shi!" "Ammy ki rufa min asiri idan ki ka tafi ina zan sa kai na?" Cewar Zainab ta na mai riko hannun Ammy. "Uban ki ya dafa ki ya cinye!" Ammy ta bata amsa a hasale. Cike da tashin hankali Falmat ta ke kuka, Zainab kuwa dama ta nemi kuka ta rasa sai dai na zuci, wani tsanar Usman ta kara ji, ta kuma kullaci Malam da har ya zabi rabuwa da mahaifiyar ta akan auren ta da Usman, wato ya tabbata Malam ya tsane ta ya kuma tsani mahaifiyar ta. Halitta na mai girgiza kai cikin rashin gasgata maganar Ammy ta ce "Ammy ba haka ba ne, Daddy ba zai taba zabar rashin zama da ke ba Ammy, wannan masifa har ina, Innalillahi wainnailaihi rajiun! Ammy da kuruciya ba ki taba yin yaji ba, dan Allah kar ki yi da tsufan ku, Dan Allah Ammy....." "Ke rufa min baki! Kuruciya ko tsufa namiji namiji ne! Uban ku ma namiji ne! Ba uba na ba ne, ba gidan uba na ba ne, wallahi ba zan zauna bakin ciki ya kashe ni ba, matsa min daga hanya!" Ta na mai hambare Halitta ta tare da buge hannun Zainab ta ja akwatin ta ta yi waje. Iya kuwa wacce duk abin da ya faru ba ta gidan cike da al'ajabi ta ke bawa Ammy hakuri, Ganin dai Ammy ta ki ji Iya ta ce da Falmat ta yi maza ta shedawa Malam halin da ake ciki. Falmat ta fita da sauri ta nufi bangaran Malam, ta tarar da shi zaune in da Ammy ta barshi ya na karatun al'qur'ani, ganin Falmat da kuma abin da take fada masa hankali tashe be sa ya motsa ba, bare ya nuna mata wani damuwa. Kallan ta yayi cikin nazari kafin daga bisani ya bata amsa da "Ammyn ku ta zabi ta tafi, ku bar ta ta tafi za ta dawo ne da kafafun ta, ku kasance masu hakuri Falmat" "Daddy ba za ka tsayar da ita ba? Ba za ka hana ta tafiya ba Daddy?" Kai ya gyada mata, sannan ya kara da "Ki yi hakuri Falmat, babu yanda zan iya da hukuncin ubangiji dan kuwa auren Yakura ba mai rabuwa ba ne har illa mashaAllah" Shiru ne ya biyu baya, jiki sanyaye Falmat ta juya ta fita. Malam ya bi bayan ta da kallo na wasu dan mintina kafin ya mayar da hankalin sa ga karatun da yake. Duk kokarin su na dakatar da Ammy a iska ya tashi, karshe ma cewa ta yi duk wanda ya biyo ta wajan gate sai ta tsine masa, su na ji suna gani ta ja akwatin ta ta fice, ko da ta zo giftawa ta bangaran Malam can kasan zuciyar ta ta so Malam ya fito yayi kokarin hana ta tafiya kamar yanda 'ya'yan ta su ka yi. Haka ta na share kwalla ta damkawa Jauro akwatin wanda ganin fitowar ta ya taso da sauri. Shi ya sanya mata cikin mota, ya na mata fatan Allah ya kiyaye hanya. Ta na mai watsawa Usman harara ta shige mota. Shi kuwa gate ya bude, haka kuma be fasa mata a sauka lafiya ba yayinda mota ta fice daga cikin gidan. ***** Kamar gidan makoki haka gidan Malam ya kasance. Duk yanda Iya ta yi kokarin sanin halin da ake ciki daga wajan su Falmat abin ya gagara. Sai da ta sami Jauro ya kwashe komai da karya da gaskiya ya fada mata. Ita kan ta sai da ta kullaci Malam da Usman. Tsoran fushin Malam ya sa Zainab ta hade kayan ta tsaf kamar yanda ya umarce ta. Iya ta sa ta kai mata su BQ ta aje, Amma ta yi kwanciyar ta daki duk da dai ta na jiran tsammanin shigowar Malam matukar ya san ba ta bi umarnin shi na komawa BQ din ba. Malam shiru be shigo ba, haka kuma ba ta ji muryar shi sanda aka yi sallar Magariba da isha'i a masallaci ba kamar yanda su ka saba ji idan ya na jan sallah ba. Fushin da ta ke da shi be sa ta kasa shiga damuwa ba, Amma tashi ta je bangaran sa ta duba ko lafiya ne ba za ta iya ba gudun abin da hakan zai jawo mata. Da wannan tunanin ta fito falo ta tarar da Halitta sanye da hijabi da alama shirin fita ta ke. "Ina za ki je?" Zainab ta tambaya a dake, maganar da ta fara shiga tsakanin ta da Halitta kenan tun faruwar masifar da Zainab ta jawo mu su. "Daddy zan kai wa abinci" Ta bata amsa a takaice kafin ta shige kitchen, jin batun abinci ya tunawa Zainab raban ta da abinci tun jiya da rana, dan haka ita ma kitchen din ta nufa. Iya ta hade abincin Malam bisa wani dan kwando, Halitta ta dauka, ta na jiyo Zainab na tambayar Iya ko da kaza ta na so ta yi mata farfes Halitta ta fice, cikin ran ta tana fadin 'dole ki ci ferfesu hankalin ki kwance ya ke Yakura bayan kin dagula na kowa kin hana mu farin ciki' A bakin kofar da zai sada ta da bangaran Malam ta hangi Usman tsaye, tuni gaban ta ya shiga faduwa hannun ta na rawa tsabagen yanda zuciyar ta ke harbawa, ta na shirin juyawa ta koma ya gan ta, cikin hanzari ya nufo ta da sauri ya na mai fadin "Alhamdulillah, kada ki juya ina bukatar taimakon ki" Yanda zuciyar ta ke bugawa kamar mai shirin fitowa ya sanya ta runtse idanun ta, ta na mai saurin bude idanun ta juyo ta na kallan shi yayinda ya karaso kusa da ita. Tsayin Usman ya sanya sai ta dan daga kai kadan take iya duban fuskarsa, dan kuwa in dai tsayi ne da fadi ka sami Usman an shafa fatiha. "Yi hakuri na tsayar da ke, Malam be fito sallar Magarib ba haka ma Isha'i, a zato na wani uzuri ne ya hana shi, sai yanzu da lokacin karatu yayi Jauro ke sheda mana duk sanda ya shigo ya karaci sallamar shi Malam be amsa ba, kin ga abun da damuwa, yanzu ma na yi sallama na ji shiru" Tun da ya fara magana ta saki baki da hanci ta na kallan sa, yanda muryar sa ta ke da girma be hana sa magana mai cike da kwanciyar hankali ba, Iyakar gaskiyar shi ya ke mata bayani duk da dai hausar ta shi ba ta fita sosai. "Ko yaya ki gani? Ki taimaka ki duba mana domin Allah" Halitta na mai gyara murya ta ce "Toh toh, bari na shiga" Ta yi saurin wuce shi ta na mai tasbihi ga Allah akan wannan masifa da ke dankare cikin zuciyar ta, wato masifar son Usman da ya ke miji ga yar uwar ta. Ba ta sami nutsuwa ba sai da ta shiga falon Malam ta na mai doka sallama, shirun da ta ji ne ya sanya ta karasawa har tsakar falon, ganin Malam ba ya ciki ya sa ta aje kwandon abinci, ta nufi dakin sa ta fara sallama, Nan ma shiru, a tsorace ta fara bugawa da karfi ta na sallama, jin shiru ta bude kofar dakin da sauri ta shiga, nan ma Malam ba ya ciki. Ta na shirin juyawa ta fita ta jiyo kamar gurnanin numfashi na fita daga bandaki, a guje ta karasa ta bude bandakin, idanun ta yayi tozali da tashin hankali, Malam kwance a kasan bandaki hannun sa bisa kirjin sa, yanda ya ke gurnanin wajan fitar da numfashi ya sanya Halitta fasa ihu ta na fadin "Daddy! Na shiga uku! Daddy Innalillahi wainnailaihi rajiun!!" Jan shi ta fara yi tana kokarin tada shi, sai da ta sa iya karfin ta, Amma ta kasa sannan ta tuna da Usman da ke tsaye ya na jiran ta. A guje ta fita ta na fadin "Usman Daddy na! Usman zo ka taimaki Daddy na!" Tun kafin ta karaso ya juyo ihun ta, da sauri ya kutsa kai ciki kafin ta kai ga fitowa in da ya ke, tambayar ta ya ke "Me ya faru? Me ya sami Mallam?" Nuni ta ke masa da hannu izuwa dakin Malam, ta kasa magana tsabagen kuka da ya ci karfin ta. Cikin zafin nama Usman ya karasa dakin Malam, in da ya tarar da Malam kwance cikin halin da Halitta ta barshi. "Allahumma ajirni fi masibati haza wakallifna minha! Innalillahi wainnailaihi rajiun" Cewar Usman yayinda yake duba tufafin jikin Malam domin ya tabbatar da duka tsaraicin sa rufe ya ke. Ganin Malam na sanye da dogon wando kasan farar jallabiyar da ke jikin sa ya sanya Usman daukan Malam cak da ke Usman ba aboci karfi ne, cikin sassarfa ya yi waje da Malam Halitta na biye da shi. Kafin su kai ga farfajiyar gidan in da daliban Malam ke jira Usman ya dakatar da Halitta cikin bada umarni ya ce "Ka da ki biyo mu, ki koma wajan yan uwan ki ku shedawa duk wanda ya kamata su sani, na mi ki alkawarin kula da shi, za mu tafi asibiti yanzu, wani asibiti ya ke zuwa?." Halitta na shirin ma sa musu, Amma yanda ya juyo ya kalli idanun ta cike da tabbacin alkawarin da ya dauka mata ya sanya ta gyada kai tare da fadin "Premier, a court road ya ke, Dan Allah kada ya rasa ran shi...." "In Sha Allah......" Cewar Usman yayinda ya juya da sauri, Halitta na kallan sa har ya kure ganin ta. Yanda ya fito dauke da Malam ya sanya hankali kowa tashi. Tuni daliban Malam su ka to kan sa, kowa na tamabayar lafiya, me ya sami Malam, me ya faru. Auren Shehu 13 Da taimakon direban da ya kai Ammy Wanda dawowar sa kenan aka sa Malam cikin mota. "Ba mu san me ya same shi ba, mun tarar da shi kwance a bandaki cikin wanan hali da ku ka gan shi yanzu, diyar sa ta fadi sunan asibitin da za a kai shi, wani turanci ne wallahi ya kwanta min" Cewar Usman wanda shi ke zaune bayan mota, kan Malam kwance bisa kafarsa, ya na maganar ne cikin kokarin tuna asibitin da Halitta ta fada masa. "Toh ai zaifi wata daga cikin iyalan na shi su fito a tafi asibitin da su, Hajiya ba ta nan ne?" Daya daga cikin daliban Malam ne ya tambaya cike da damuwa. "Eh haka zai fi, Hajiya ba ta nan, bari a kira daya daga cikin 'ya'yan na sa" Usman ya fada ya na mai duban Jauro da Isa da niyar daya daga cikin su ya taimaka ya kira su Halitta. Ganin haka Jaura ya kada baki ya ce "Dan cirani wannan kuma ai aikin ne kai da ka ke sirikin gidan, mu masu gadi ina mu ina shiga gida haka? Maza shiga ka kirawo matar ka a tafi" Wani mugun kallo da Usman ya harbi Jauro da shi ya sanya shi saurin wucewa ciki ya na fadin "Toh ni jan idan ka me zai min, dan ka zama surikin Malam ba zai ba ka lasisin aikan mutane kamar yaran ka ba, ka dai ci darajar masu daraja!" Maganganun da Jauro ya ke ne ya dan ja hankalin wasu daka cikin daliban Malam har suna musayar kallan juna, dama suna da labarin abin da ya faru daren jiya. Idan Usman ya damu da lafazan jauro sam be nuna ba, kallan Malam ya ke ya na fadin "Sannu Malam, Allah ya ba ka lafiya, Allah ya ma ka afuwa" Jim kadan Jauro ya dawo Halitta biye da shi, hijabin da ta saka tare da nikabin da ta saka be boye hawayen da ke zuba daga idanun ta ba dan kuwa har ya dan jika nikabin. "Matar ta ka ta ki fitowa sai kanwar ka" Cewar Jauro ya na mai nuna halin ko in kula da kallan da Isa ya bi shi da shi. Cikin azama Halitta ta shiga gaban mota ta na mai rufo kofa, direba wanda dama shi ma tuni ya zauna a nashi guri ya sakawa mota key, Isa da sauran dalibai suna mai yiwa Malam addua aka rufowa Usman kofa. Tuni Jauro ya bude gate, direba na mai tashin mota cikin gaggawa su ka dauki hanyar asibiti. Tun da su ka dauki hanyar asibiti Halitta ke gwada numbar Ammy duk sanda ta kira amsa daya nakurar ke bata, na 'numbar da ta kira a kashe ta ke, ta sake gwadawa anjima' Har su ka kusa isa asibiti ba ta sami numbar Ammy ba, sai na kanwar Ammy wacce ita ma din Kano ta ke aure. Bayan Halitta ta sheda mata abin da ke faruwa na game da rashin lafiyar Malam ta tambaya ko Ammy ta je gidan ta? Cike da mamaki da damuwa ta ce ba ta je ba, a tambayi direban da ya tafi ina ya kai ta, sai a sannan wannan azancin ya zo wa Halitta. Bayan ta aje wayar ta ke tambayar direba ina ya aje Ammy? Direba ya ce shi dai tasha ya aje ta. Isar su asibiti likitan da ke duti ya mu su karbar gaggawa ta hanyar sawa Malam robar shakar numfashi ta hanci da baki, sannan aka kwantar da Malam kan gadon da ke offishin sa. Halitta kadai ya amincewa zaman Office din sa'ilin da ya gama duba Malam ya ke tambayar ta ko ya shiga matsanincin damu ne? Allah ya takaita da ya fadi wani bangare na jikin sa be dena aiki ba, Halitta ta amsa da "uhum" kawai ba tare da ta iya ba shi cikakken amsa ba. Sai da aka samu jikin Malam ya dan lafa sannan aka mayar da shi dakin kwantar da masu jinya, Amma har lokacin robar bada taimakon numfashi ne a bakin sa. Usman na mai duban Halitta ya furta "Shin kin sanarwa Hajiya kuwa?" Kai ta girgiza masa, murya dashe tsabagen kukan da ta sha ta amsa da "Wayar ta ba ya shiga, kuma ban san in da ta je ba bare na kira su" Shiru ne ya biyo baya na wani dan lokaci, daga bisani ya nisa tare da fadin "Dare na yi, ina ga zai fi a mayar da ke gida ko? In ya so kya dawo da safe kila kafin nan an sami Hajiya...." "Ni ah ah nan zan kwana gun Dady" Halitta ta katse shi cikin nuna kafiya. Usman na kallan ta cike da tausayi ya sake fadin "Ki yi hakuri ki tafi, jinyar namiji sai namiji, ba za ki iya....." "Ba namiji ba ne, Dady na ne fa!" Ta fada ta na mai fashewa da kuka. Shiru ya mata na wani dan lokaci, har ta yi kukan ta ta gama. Sai ji ta yi ya na kiran direba, cike da umarni ya ce da direba "Maza ka mayar da ita gida...." "Ni ba zan je ba ai na fada..." "Shhhhh za ki je yanzu ma kuwa..." Yanda yayi maganar ne cikin ba da umarni ya sa da ga Halitta har Direba tsayawa su na duban shi, ganin haka ya dan sassauta murya tare da fadin "Malam ba zai ji dadi ba idan har ki ka zauna a nan, kuma kin ga ai farin ciki da samun lafiyar shi ki ke fata ko?" Kai ta gyada masa kamar karamar yarinyar. Cikin rarrashi ya furta "Yauwa diyar halak, Allah ya mi ki albarka. Yanzu sai ki tashi ku tafi ko?" Ga mamakin Direba sai ga Halitta ta tashi, bayan ta sake duban Malam, ta kalli Usman ta ce "Ka kulan min da shi, Zan dawo da safe" "In Sha Allah" Ya amsa mata a takaice. Hakan nan ba a san ran ta ba su ka bar asibitin. A hanya ta yanke hukuncin kiran yayar babbar Malam Hajja Dudu wacce dama ta san da auren Zainab da Maigadi da Malam ya daura. Nan ta fada mata halin da ake ciki na rashin lafiyar Malam, tare da tafiyar Ammy. Ta na mai salati da sallalmi ta yiwa Halitta alkawarin baro Maiduguri da asubar fari. Da misalin karfe goma Halitta ta isa gida, ta tarar da Falmat zaune cikin zulumi, ganin ta taso da sauri ta na tambayar jikin Malam. Halitta ta amsa mata da sauki, ko ta sami Ammy a waya? Falmat ta ce ba ta same ta ba, Amma bari ta sake tambayar Zainab. Ta wuce dakin Zainab ganin ta yi dai dai ta na baccin ta cikin kwanciyar hankali da ke dama akwai bashin bacci kan ta ya sanya Falmat dawowa falo, Amma ta kasa fadawa Halitta Zainab din bacci ta ke, ta yi karya Zainab din ma ta ce ba ta same ta ba. Iya ce ta shigo jin sun dawo, ita ma tun tafiyar su Halitta asibiti ta ke zaman jiran su. Bayan ta tambayi jikin Malam, tare da ko an sami Ammy ne ta yiwa Halitta tayin abinci, Halitta ta ce mata ta koshi sam bakin ta ba dandano. Da haka ta shige dakin ta, alwala ta yi ta yi sallar ishai tare da yiwa Malam addua, Allah ya kawo sauki cikin lamarin sa. Washagari da sassafe Halitta da Falmat su ka nufi asibiti, Zainab kyememe ta ki bin su cewar ta ba ta so ta je ta ga wannan dan Boko haram din da Malam ya ce ya daura mata aure da shi. Sai da su ka isa sannan Usman ya tafi ya bar Malam tare da su Halitta da direba. Jikin Malam kam a iya cewa da sauki na bahaushe amma har lokacin ya na jin jiki, haka kuma be fara magana ba bare ma ya ci abincin da Halitta ta girka masa. Kamar wasa Halitta ta gwada wayar Ammy sai gashi ta shiga, ta na kuka ta ke fadin "Ammy kin tafi kin bar mu ga Dady nan kwance a asibiti rai a hannun mai duka...." Salati Ammy ta ke yi daga dayan bangaran, cike da damuwa ta ke tambayar me ya faru? Me ya sami Malam? Nan Halitta ta kwashe komai ta fada mata, ta kare da "Dan Allah Ammy ki tausaya mana ki dawo.." Ammy wacce jikin ta ya gama sanyi ta yiwa Halitta alkawarin dawowa da sun isa Yobe, dan kuwa ta na hanyar Maiduguri amma sun kusa isa Yobe. Da wannan su ka yi sallama. Halitta ba ta jima da aje wayar Ammy ba sai ga Hajja Dudu, tare Uwargidan Malam Hajja Kilishi, sai kuma babban dan Malam wanda ake kira Gana. Tun asubar fari su ka dau hanyar Kano. Ganin halin da Malam ya ke ciki tuni Hajja Kilishi ta fashe da kuka ta na mai tambayar musabbabin halin da Malam ke ciki. Daga Halitta har Falmat ba su so zuwan Hajja Kilishi ba, dan kuwa sun san ran Ammy ba karamin baci zai yi ba muddin ta zo ta tarar da ita. Haka su ka wuni a asibiti, an samu Malam ya fara magana sama sama haka kuma ya dan ci abinci. Da yamma Usman ya dawo, ganin dakin Malam cike, ciki har da Zainab wacce tun ta hango sa ta ke watsa masa harara ya sa yayi jim kamar zai koma. Halitta ce ta masa iso ta hanyar fadin "Usman shigo mana, ya za ka koma" Cike da yar kunya ya shigo, ya tsugunna har kasa ya gaishe da Hajja Kilishi da Hajja Dudu. Su ka amsa ba yabo ba fallasa, Gana ya bashi hannun su ka gaisa. Hajja Dudu ce ta tambayi Halitta ko wanene Usman. Kafin Halitta ta ba da amsa Zainab ta yi carab ta ce "Maigadin mu ne" Gudun kar Halitta ta fadi dangantakar auratayya da Malam ya kulla tsakanin su, Nan kuwa ba ta san labari ya riga ya iske mu su. Maganar da Hajja Kilishi ta yi ne ya tabbatar mu su da hakan na cewa "Ko shi ne sirikin namu mijin Zainab?" Ras! Gaban Zainab ya fada, ta na mai dauke kai ta hadiyi yawun bakin ciki. "Eh shi ne" Cewar Halitta wacce amsar da ta bawa Hajja Kilishi ya mata nauyi matuka a baki, ta na mai danne kishin da ya taso mata ta kara da "Shi ne ma ya kwana da Dady jiya" Dukan su kallan Usman su ke, kan sa ke sunkuye. Jin amsar da Halitta ta ba su ya sanya ya dan dago kai ya na mai duban Zainab ta wutsiyar idanu. Ganin haka ya sanya Zainab watsa masa harara cike da tarin tsana. "Allah sarki, sannu Allah ya ma ka albarka, ba a banza Malam ya ba ka auren diyar sa ba, ka cika dan halas, yanda ka rufa mana asiri Allah ya rufa na ka duniya da lahira" Cewar Hajja Dudu wacce tun shigowar Usman ta yaba da hankali sa. Zainab kuwa ji ta ke kamar ta tashi ta fita a guje tsabagen tsanar Usman da ta yi. Jin Usman ya mu su sallama ya ce zai koma tunda Gana ya na nan ne ya sa Zainab dan samin sauki cikin ran ta. Bayan tafiyar shi su ka shiga tattauna auren Zainab, in da Gana ke nuna rashin dacewar auren a nashi ganin auren zai iya zama wani barna maimakon gyara a rayuwar Zainab, in aka yi la'akari da yanayin wayewar Zainab da kuma ilimin ta. Ya ce zai yiwa Malam magana a san yanda za a yi a warware wannan aure tun kafin ya haddasa wata matsalar gaba. Maganar ba karamin dadi ta yiwa Zainab ba, duk da dai Hajja Dudu da Hajja Kilishi sun nuna rashin goyan baya akan hakan. Sai dab da magrib Ammy ta iso dauke da akwatin ta, dan ko gida ba ta je ba bare ta ji labarin zuwan su Hajja Kilishi wanda ganin ta ba karamin bakan ta mata rai yayi ba. Ta tarar Malam ya na bacci amma ganin Hajja Kilishi tuni ta fara kalallame shi, daga ya dan motsa sai ta zabura ta matsa kusa da shi cikin nuna kulawa. Ita kuwa Hajja Kilishi ta na daga gefe ta zuba mata Ido kawai. Cikin ran ta mamakin yajin da Ammy ta yi ta ke ji. Ko da Malam ya bude ido ya ga Ammy sam be nuna wani farin cikin ganin ta ba, sai ma idan ya na da bukatar wani abu ya ce da Hajja Dudu ko Hajja Kilishi ta masa. Hakan ba karamin musgunawa Ammy yayi ba. Haka kuma duk yanda Ammy ta so kwanan asibitin Hajja Dudu ta yi kyememe ta hana, cewar ta gwara Gana ya zauna da Malam ai jinyar namiji sai namiji. Bayan kwana uku Hajja Dudu ta koma Maiduguri, Ammy na ji ta na gani Hajja Kilishi ta tare mata a gida, cewar ta babu in da za ta je sai Malam ya sami sauki sosai. Duk yanda ta so ta tunzura ta ta koma ta ki, haka ta hakura. Wasa wasa sai da Malam yayi sati biyu a asibiti, kafin a sallame shi sai da likita ya jaddada hutu da kwanciyar hankalin da Malam ya ke bukata wanda hakan ne ya sanya Gana yanke hukuncin wucewa da Malam Maiduguri bayan ya ji cikakken bayanin abun da ya faru daga bakin Jauro, wanda be boye masa komai ba. Sai ga Gana mai kudirin samar ma Zainab yanci na mai gargadin ta matukar ta kashe mu su uba ita da uwar ta wallahi ba su yafe mata ba. Sai da su ka dawo gida Gana ya hade kayan Malam kaf, ga mamakin Ammy Malam be yi musu ba, shi ne ma ya ke fadawa Gana kalar kayan da zai zaba masa, in da ya ke cewa ya fi san farare saboda tafsirin azumi ya gabato, sati biyu ya rage a fara. Bayan Malam ya sallami su Halitta, tare da mu su alkawarin zai dawo bayan sati biyu kafin azumi ya kamkama, ya na mai duban Zainab ya furta "Yakura kin dai san ke matar aure ce, cikin sati biyun nan da na ke kwance asibiti ban sani ba ko kin cigaba da halin ki na haura katanga ki fita yawan lalace, toh ki budi kunnuwan ki ji ni da kyau, wallahilazim matukar ki ka kara aikata haka ba za ki gama da duniya lafiya ba, Allah ya isa ban yafe mi ki ba...." Dagowa ta yi a gigice ta na duban Malam, hakan ya sa Malam jinjina kai, ya kara da "Ware ido ki kalle ni da kyau, ba dan da karar kwana ba da tuni bakin cikin ki ya kashe ni Yakura, toh amma Alhamdulillah Allah shi ne zai jibanci lamura na, ba za ki tuzarta ni ba! Ba ki isa ba!" Jiki sanyaye Zainab ta furta "Ba zan kara ba Dady" "Idan ma kin kara kan ki za ki yiwa, kin dai san ke matar aure ce. Bayan haka daga yau idan ki ka sake kwana a dakin da ba namijin ki ba ba tare da kwakkwarar hujja ko dalili ba Yakura shi ma ban yafe mi ki ba" Jin haka ta saki kukan da ta ruke shi can kasan magoro, fadi ta ke "Dan Allah Dady ka kawo min dauki ka sauwake min wannan nauyi da ka daura min, wallahi ba zan iya kwana daki daya da shi ba Dady, dan Allah Dady" Cikin halin ko in kula Malam ya furta "Ki ka iya kwana gidan rawa bare dakin auren ki? Kai Gana kana ina? Maza zo mu tafi ko Allah zai sa na dena ganin wannan yarinyar!" Zainab na gani Malam ya shige mota ya barta da nauyi mafi tsanani a rayuwar ta. Haka kuma Ammy wacce duk yanda ta so ta sauke girman kai ta bawa Malam hakuri ta kasa tsabagen kishin zaman Hajja Kilishi, gashi ta na ji ta na gan ta ci nasararr tafiya da shi. _ *A gafarce ni, in Sha Allah zan sake posting kafin Sunday.* _ *Khadija Sidi* Auren Shehu 14   Tun da Malam ya sa kafa ya tafi gaba daya ya dauki hidimar Ammy da 'yayan ta ya watsar. Washagarin ranar da ya isa Maiduguri ya kira Shiek, in da ya sheda masa sauyin da yayi na auren Halitta da Sudais a maimakon Zainab da su ka yi alkawari akai. Kamar yanda yayi na'am a wancan karan, haka wannan karan ma ya amsa cikin godiya ba tare da neman ba'asi ba, haka kuma ba a sauya watan auren da su ka sa ba. Kamar yanda Malam yayi burus da su, haka ita ma Ammy ta yi da shi. Kwanci tashi asarar mai rai, haka Malam yayi sati biyu a Maiduguri, idan aka ga kiran sa to ya kira ne ya duba lafiyar su, haka kuma ya fadawa Ammy ya tura mata kudi, da kuma kudin na menene. Ammy na gani Zainab ta ki bin maganar sa na ta koma BQ amma sam ba ta damu da hakan ba bare ta tsawatar mata, sai ma tambayar ta lokacin komawar ta makaranta da ta yi, jin be fi wata daya ya rage ba Ammy ta yi hamadala, ita a na ta ganin komawar Zainab makaranta shi ne mafi a'ala a rayuwar ta, kila kafin ta dawo Malam ya sauka ya raba auren Zainab da Usman. Ana sauran kwana biyu a tashi da azumin ramadana, da daddare Ammy ta idar da sallar isha'i a dakin ta, zaune ta ke kan dadduma ta doka uban tagumi dan kuwa gidan ya mata kunci, abin duniya ya ishe ta ji ta ke kamar ta hada nata ya nata ta sake barin gidan. Sallamar Halitta ya sanya ta dago a hankali tare da amsa mata. Ta na mai kallan Halitta wacce ta tsaya bakin kofa hannun ta dauke da waya, cikin yaran shuwa ta ce "Halitta ya dai? Lafiya ko?" "Lafiya lau Ammy, zan iya shigowa?" Ta mayar mata da harshen hausa. Kai Ammy ta gyada mata, cike da nutsuwa Halitta ta shigo cikin daki, ta sami waje kusa da Ammy ta zauna. Sanye ta ke cikin shudiyar atamfa dinkin doguwar riga, kan ta tufke da dankwali. Ta na mai duban Ammy cike da tausayi ta furta "Ammy dama akwai wani abun da na ke so na nuna mi ki, da kamar ba zan nuna mi ki ba, ganin yanda dangantakar ki da Dady ya zamu wani abu na daban ya sanya ni yanke hukuncin fada miki" Ammy na mai tattaro dukannin nutsuwar ta, ta dubi Halitta cike da fargaba dan kuwa a cikin dan kwanakin nan ta ga abubuwa kala kala har ta gode. "Ke kuwa Halitta wannan abu menene shi haka?" Maimakon ta bata amsa, sai ta shiga danna wayar hannun ta, Instagram ta shiga har ta kai ga shafin Zainab, ta shiga hutunan ta, musammam wanda ta yi ba da jimawa ba a club, ta na mai nuna fuskar wayar ga Ammy ta ce "Ammy kin gane wacece wannan?" Wayar Ammy ta karba daga hannun Halitta, tare da fadin "Waiyazubillah wannan rashin tarbiya har ina? Ke kuwa Halitta ina zan san wannan lalatacciyar yarinya haka? Ji tufar da ke jikin ta? Wannan ai arniya ce! Kai wannan a arnan ma ba dai tambatsastsiya ba!" Halitta na duban Ammy cike da tausayi ta ce "Ammy duba fa da kyau ki ga, ba ki gane ta ba....." Ta na mai jefa mata waya ta ce "Ke ni ban san shashanci ina na san wannan arniyar bare na gane ta! Toh idan ma kin san ta babu ke babu ita! Wannan lalalcewa har ina? Ji fa hayaki ta ke busawa....!" "Ammy Yakura ce fa....." Cike da mamaki Ammy ta ce "Ki na nufin kawar Yakura ce? Ta taba kawo ta gidan nan? Ina Yakura irin kawayen da ta ke mu'amala da su kenan?" Halitta na mai girgiza kai yayinda ta ke dada nunawa Ammy hotan Yakura da ke kan fuskar wayar ta, ta ce "Ba ki gane ta ba ne, ba kawar Yakura ba ce, Yakuran ce da kan ta Ammy duba ki gani....." "Zancen banza zancen hofi!" Cewar Ammy yayinda ta fuzgi wayar hannun Halitta ta na mai kurawa hotan idanu a karo na farko. Kallan kurilla da ta yiwa hotan ya sanya ta furta "Innalillahi wainnailaihi rajiun" Hawaye ne bibbiyu ke fita daga idanun ta, fadi ta ke "Halitta wannan diyar da na haifa ce haka? Wannan Yakura ce Halitta? Wannan me kama da Yakura ce....." "Wallahi Ammy ita ce, idan kin yi gaba ma za ki ga sauran hotunan ta da videos din da ta ke sakawa" Cewar Halitta wacce ita ma din kukan ta ke ganin yanayin da Ammy ta shiga. Ammy kuwa yanda Halitta ta ce ta yi hakan ta yi, ta ringa bi ta na ganin munanan hotuna da videos din da Zainab ta yi, har ta kai ta kasa jurewa ta na mai wulgi da wayar ta tashi a fusace ta fita ta na kwallawa Zainab kira. A falo su ka tadda ta ta fito a tsorace, haka ma Falmat wacce ihun kiran da Ammy ke yi ya firgita ta. "Ammy gani lafiya....." "Tas" Ammy ta dauke kumatun ta da mari har sai da ta ga walkiya a idun ta. Kafin ta kai ga farfalowa ta kara daga hannun ta wanke kumatun ta da mari har sai da ta zube kasa tsabagen zafi, kuka ta ke mai kara kamar wacce ran ta zai fita, musammam ganin yanda Ammy ta rufe ta da duka kamar wacce Allah ya aiko. Cewa ta ke "Na shiga uku! Ammy za ta kashe ni! Halitta ku taimaka min, Falmat ku ceci ni kashe ni Ammy za ta yi!" Duk yanda Falmat ta so karbar Zainab daga hannun Ammy sai da abin ya gagara, dan kuwa garin haka ita ma sai da ta sami raban ta. Ganin Halitta ta tsaya gefe ta na kuka ba ta da niyar agazawa Falmat ta ce "Halitta dan Allah ki taimaka ko Iya ne ki kira mana!" Gudun kar ta kira Iya asiri ya dada tonuwa duk da ta na da yakinin Iyan ba ta nan, dan yanda Zainab ke ihu ya ci ace ta ji, Halitta ta taimaka, ita da Falmat ne su ka shiga tsakanin Zainab da Ammy, Ammy na haki ta ke furta "Ku barni na kashe yar banza na huta, wallahi da haihuwar ki gwara barin ki Yakura! Innalillahi wainnailaihi rajiun! Da na sani na take kanki na mukurkushe ki sanda ki ka zo duniya da ba ki ja min wannan bakin ciki haka ba! Macuciya azzaluma! Allah ya........." "Innalillahi Ammy ki duba girman Allah kar ki mata baki haka!" Halitta ta yi saurin katse Ammy, yayinda Falmat ta ja Zainab kusa da kujera, kuka ta ke sosai dan kuwa ta daku kwarai. "Wani baki kuma ya rage? Ai Yakura ko ban mata baki ba ai duniya ta mata, ace diya ta ta ciki na ce haka? Allah sarki Malam! Allah sarki Malam, ciki mai haife haife ya haifo mana masifa! Sai yanzu na fahimci hukuncin da ya yanke kan wannan lalatacciyar yarinya!" Ta karasa maganar ta na mai nuna ta da dan yatsa. Jikin gurnanin kuka Zainab ta furta "Ammy me na mi ki haka da na cancanci wannan la'anta Ammy?" "Uban ki ki ka min! Har ki na da bakin magana? Kai wannan yarinyar kashe ni za ta yi ni Aleesha!" Cewar Ammy ta na mai daura hannu biyu bisa kan ta, ta kai ta kawo, ta kai ta kawo ta dubi Halitta ta ce "Dauko wayar nan Halitta, maza dauko ta!" Cikin rawar jiki Halitta ta je ta dauko wayar ta kawowa Ammy, karba ta yi ta na mai jefawa kan jinyar Zainab ta ce "Dauka ki goge duka hotunan ki da kazaman videos din ki dan uban ki!" Hannun na rawa Zainab ta dau wayar, ko da ta duba ta ga dalilin da ya sa Ammy ta nakada mata na jaka, a hankali ta dago ta dubi Halitta, ta na mai kallan ta irin wannan kallan kin ci amana ta. Ganin haka Ammy ta ce "Ki dena kallan ta! Dubin ki ya gama cika Zainab! Ke ma Halitta duk wannan masifun da laifin ki, ki sani duk yanda Yakura ta cutar da mu ki na da gudunmawa akai, dan kin sa kyamatacciyar rayuwar da ta ke yi amma ki ka ki sanar da mu!" Cikin sanyin jiki Halitta ta furta "Ammy....." "Shhhhh! Kar ki ce min komai! Da kin fada min da duk haka be faru ba! Oh ni Aleesha me na mu ku haka Halitta? Me na muku?" Cewar Ammy ta na mai ware hannu cikin alamar tambaya. Ta na duban Zainab ta daka mata tsawa "Na ce ki goge me ki ke jira dan uban ki!" Baki na rawa tsabagen tsoro dan ba su taba ganin Ammy cikin matsanancin bacin rai kamar haka ba, ta ce "Ammy ai sai ta account dina, Kuma waya ta ta fashe, sai dai Halitta ta taimaka ta fita daga na ta account din...." "Maza Halitta fita ta shiga nata, ta goge komai delete everything, son samu ma ta rufe page din gaba daya! Wannan idan Malam ya gani mun kade har ganyen mu!" Ammy ta katse ta, ta na maganar ne cike da gaggawa. Halitta wacce sam ba ta yi danasanin tonawa Zainab asiri da ta yi ba, sai ma na yin jinkirin da ta yi. Hannu ta sa ta karbi wayar ba tare da ta damu da mugun kallon da Zainab ke watsa mata ba ta fita daga na ta account din, sannan ta mayarwa Zainab da wayar ita ma ta shiga na ta. Nan ta ringa bin duka hotunan da videos din da ta saka ta na deleting, sai da ta koke tas, sannan Ammy ta sa ta yi unfollowing kowa da da take following, ta na mai duban Ammy da jajayan idanun ta ta furta "Ammy na yi abin da ki ka ce....." "Saura delete! Ki yi deleting account din gaba daya ya dena aiki!" Cikin rawar murya ta ce "Ammy ban iya ba...." "Za ki iya ne dan uban ki, dukan da na mi ki ne be ishe ki ba ina ga!" Jin haka hannu na rawa Zainab ta bi yanda za ta yi, sai gashi ta yi deleting account din gaba daya. Sannan ta wulgawa Halitta wayar ta. A fusace Ammy ta ce "Maza ki fasa mata wayar ki siya mata sabo gal, asararriya kawai! Ki sani a daren yau za ki hade na ki ya na ki ki tafi can inda Malam ya ce ki na kwana da mijin ki, har ki na shirin kashe min aure ashe na bar jaki ina can ina dukan tanki!" "Dan Allah Ammy ki yafe min, kar ki ce na kwana BQ, Allah Ammy ba zan iya ba, Ammy dan Allah" Cewar Zainab cikin sheshekar kuka. Cikin nuna halin ko in kula da kukan ta Ammy ta ce "Wallahi sai kin koma! Na baki nan da minti talatin kacal ki hada naki ya naki ko na dan dena ganin ki na sami sarari cikin zuciya ta, kuma kada wanda ya saka mata hannu cikin ku! Idan ya so idan gari ya waye na ga kin sake haurawa kin bar gidan gaba daya! Shi ne zan san kin isa tabarayyi!" Da wannan ta juya ta shige dakin ta tabar Zainab ta na mai watsawa Halitta a harara, ta kara da "Na tsane ki Halitta, tsakanina da ke Allah ya isa ban yafe ba" "Mtswww" Halitta ta ja tsaki, sannan ta kara da "Allah ya isan ki ba zai ci ni ba, sai dai ya ciki ke kan ki! Kin ga tafiya ta!" Ta juya ta wuce na ta dakin ta na juyo zagin da Zainab ta ke sirfa ma ta. Falmat kuwa wacce dama jikin ta ya gama mutuwa waje ta samu ta zauna in da ta ke kallan Zainab cike da mamaki. Kallan da ta ke mata ya sanya Zainab tashi a fusace ta shige daki ta na mai doka kofa. Yanda Ammy ta yi kwance ta na kuka, haka Zainab ta zauna na ta dakin ta ci kukan ta ta koshi. Minti talatin daidai sai ga Ammy ta zo ta na mata oya oya ta fito ta wuce dakin ta, haka da kuka da majina ta na cijewa Ammy ta ja ta, zanin gado da filo kawai ta iya dauka, ita ta kai ta har corridor din da shi ne zai fita da ita waje, tafiya kalilan ce tsakanin kofar corridor din da BQ. Hakan yayi daidai da gyaftawar Jauro, zai je ya kunto karnukan gidan. Ganin abin da ke faruwa jiki na bari ya wuce simi simi ba tare da Zainab ta lura da wucewar sa ba ya koma ba tare da ya je kunto karnukan ba Bakin corridor ta zauna ta gama shan kukan ta, ganin sauro na shirin cinye ta ya sa ta lallaba ta karasa BQ din a tsorace hannun ta dauke da tsanin gadon ta da filo. Ganin Usman ba ya kusa ta shige dakin da ta fara cinkaro da, cikin sauri ta sakata da jam lock da kulle dakin gam. Cike da kyamkyami ta ke duban dan karamin gadon da ke dakin. Farin zanin gado ne, tuni ta yaye shi ta yi wulgi da shi gefe, yayinda ta dan shifida rabin na ta, haka kuma ta rufa da sauran rabin, sai ajiyar zuciya ta ke yi tsabagen kukan da ta sha. Jauro kuwa ko da ya koma wajan da ya bar Usman da Isa zaune kan benci, ya na mai dukan kafadan Usman ya furta "Dan cirani ka tsinci dami a akala!" Dukan su duban shi su ke cikin rashin fahimta, Jauro ya gyara tsayuwa ya ce "Ai yau za ka sha gara dan cira ni, abin ba a cewa komai Allah ya kashe ya ba ka, dan kuwa ga amaryar ka can a tafe zuwa dakin ka, ka ga da ni ne sai na ga abin da ya turewa buzu nadi, cargwadi! Sunan wani abinci wai rahadada! Za ka huta fa dancirani! Matsalar dai kila ba kai za ka fara....." Ji ka ke "Tas" Usman ya sauke yatsun sa biyar bisa kuncin Jauro har sai da ya ji ya dena ji na wasu dan sakanni baya ga jinin da ya shiga gangarowa daga hancin sa tsabagen karfi da zafin hannu na Usman, ya na mai nuna Jauro da yatsa ya ce "Idan ka na cin kasa, ka kiyayi na shuri! Sakarai mara daraja!" Ya juya a fusace ya nufi ciki ya bar Jauro hannu bisa kunci in da ya ke fadin "Ya kurmartar da ni, Isa ka na kallo ya raftama min gatari a fuska! Aradu ya mayar da ni kurma Isa" Fuskar Isa cike da jin dadin marin da Jauro ya fusha, ya na darawa ya ce "Ba gatari ba ne, wallahi hannun sa ya sa ya kwashe ka da uwar mari" Jauro na susa kunci ya ce "Kai dan manzo wai hannun mutum ne haka? Kai wannan ba dai basamude ba!" "Ka ma godewa Allah ba sandar nan ta shi ya rafta ma ka ba, ina fada ma ka ba ka ji Jauro! Ka dena rai na mutumin nan ga shi ka fari gani" Zafin marin da ya sha, da kuma maganganun Isa ne ya tunzuro Jauro, nan ya fara kurari ya na masifa, fadi ya ke "An rai na shi din, shi dan uban wane! Da ya isa da ya tsaya mana sanda ya mare ni! Tsoro ya sa shi shigewa ciki da sauri! Da mana ya tsaya!" Isa na mai taba kafadar Jauro ya furta "Idan ka gama ihun da ka ke bayan hari don Allah ka sheda min, bari na tai ta kunto karnukan nan da munafunci ya hana ka yin aikin ka" Jauro ya rikice nan ya fara ruwan ashar, In da Isa ya maishe shi mahaukaci, Nan ya bar shi ya na hayaniyar shi shi kadai. Ko motsin Usman ba ta ji ba, bare ma ta ga giftawar shi, garden ya je yayi zaman sa bisa kujera ya na mai neman tsari daga tafasar da zuciyar sa ta ke yi, Dan kuwa be taba jin zafin magana kamar wanda Jauro ya fada masa a yau ba. Yanda ba ta sami cikakken bacci ba a daren ranar gudun kar Usman ya zo ya fada mata duk da dai ta san ta rufe kofar. Gashi taurin kai irin na Zainab ya hana ta sake komawa ta lallabi Ammy ko ta hakura ta barta cikin gida. Haka ita Ammy, wacce tashin hankalin ko a wani hali Zainab ke ciki ya hana ta bacci. Sai da aka kira sallar asuba sannan bacci mai nauyi ya sace Zainab, ba ita ta tashi ba sai wajan karfe goma sha biyu na rana. Bandakin cikin dakin ta shiga, duk da bandakin fes ya ke sai da hankalin Zainab ya tashi matuka, dan ko fitsari ma ta kasa tsugunnawa ta yi, dan haka ta lallaba ta koma dakin ta cikin sanda, nan kuwa ba ta san Ammy ta gan ta ba. Wankan ta fara sannan ta hada asuba da azahar ta yi, ta na shirin haye gadon ta ta mike sai ga Ammy ta shigo, ta na mai salati ta ce "Lahaila me zan gani Yakura? Me ki ke min a cikin gida?" Cikin marairaicewa Zainab ta tashi zaune. Idanu na kawo kwalla ta ke fadin "Ammy ki rufa min asiri wallahi kyamkyamin BQ din na ke, wallahi Ammy...." Cike da takaici Ammy ta ke duban ta, ka na ta ce "Ba ki ji kyamkyamin rayuwar ki ba sai na BQ? BQ yanzu yanzu za ki iya gyara shi? Karkari ya sha shara da guga? Ki tashi ki fitar min daga gida, bana san ganin ki Yakura! Idan har abin ya mi ki ciwo toh ki zage ki gyara BQ din, Amma kar na sake ganin ki kwance cikin dakin nan, wallahi sai na sabar mi ki!" Cikin fushi Zainab ta tashi ta fice fuuuu ta na mai doka kofa. Sai da Ammy ta kai zuciyar ta nesa dan ji ta yi kamar ta bi ta ta kara nakada mata na jaki ko ta huce. Tsakanin 'ya da mahaifa aka ce sai Allah. Ammy ce da kanta ta hade abincin na cin mutum biyu, cikin dan kwando ta jera kulolun ta ce da Iya ta kaiwa Zainab, Amma kada ta ce ita ta saka ta. Halin da Iya ta ga Zainab ya sa ta tausaya mata matuka, ta yi ta yi Zainab ta ce abinci ta ce ba ta ci, ta koshi. Iya ce ta sa hannu ta wanke mata bandaki har ma da shara da gugan daki, ta tsaftace mata ko ina tsaf sannan ta kyale ta. Bayan tafiyar Iya Zainab ta farma abincin, ta ci ta koshi sosai dan kuwa daurewa ta yi ta ki cin abicin gaban Iya dan ta fadawa Ammy ko ta tausaya mata. ***** Da nadamar yanda ta bijerewa Malam Ammy ta kwana ta tashi, tunanin ta be wuce na yanda za ta yi ta nemi afuwan Malam, daga baya ta yanke hukuncin kiran sa. Sai da ta shiga dakin ta, cikin faduwar gaban yanda zai amsa mata, da kuma abin da za ta ce masa, ta kira har sau uku ba ya shiga, sai ta yi tunanin ko in da ya ke ne ba network mai kyau. Ba ta dade da aje wayar ba sai ga kiran Hajja Dudu. Da kamar ba za ta daga ba dan kuwa ta kullaci Hajja Dudu, gani ta ke ita ta dauko Hajja Kilishi ta kawo ta Kano har ta tafi da Malam. Ta na kallo har wayar ta tsinke. Ganin ta sake kiran ta bayan tsinkewar wayar Ammy ta dauka, muryar Hajja Dudu taji cikin kuka ta ke fadin "Aleesha ki hado yara maza ku taho Maiduguri komin dare! Malam sun yi hatsari hanyar tahowar su Kano!" Cikin ihu Ammy ke fadin "Innalillahi wainnailaihi rajiun! Innalillahi wainnailaihi rajiun! Ya jikin na sa? Me ya same shi? Lafiya ya ke?" "Ku dai taho Aleesha, abin dai sai kun gani!" Ta na gama fadin haka Hajja Dudu ta kashe wayar ta, Ammy ta saka kuka mai tsuma zuciya, hijabi ta saka gaba a baya, ta na surutai kamar zaucacciya fadi ta ke "Ya Allah kar ka raba ni da miji na ba tare da na nemi gafarar shi ba, ya Allah kar ka dau ran miji na ba tare da na nemi tafiyar shi ba! Innalillahi wainnailaihi rajiun!"     *Khadija Sidi* Auren Shehu 15   Yanda Ammy ta fito afujajan da kuma sumbatun da ta ke ne ya sanya su Halitta rudewa, kamar yanda ta ke kuka, haka su ma din kukan su ke. Cikin kankanin lokaci su ka shirya, gaba daya sun manta da Zainab da ke can BQ, sai da su ka shiga mota, dukan su uku gidan baya su ka zauna, direba na shirin tayarwa sannan Halitta ta furta "Yakura, Ammy ba a fadawa Yakura ba" Ammy na share hawaye ta furta "Ai kuwa dai, kai na yayi zafi wallahi! Halitta je ki sanar mata" Halitta ba ta so Ammy ta aike ta wajan Zainab ba, haka babu yanda ta so ba ta fita ta same ta ta yi dai dai ta na bacci hankali kwance. Yanda Halitta ta tashe ta cikin gaggawa fada fada, da kuma sakon da ta fada mata na hatsarin Malam ya sanya ta tashi a gigice har ta na neman fadowa daga kan godo. Fadi ta ke "Innalillahi na shiga uku! Ina Dadyn ya ke? Yaushe za mu tafi Maidugurin?" "Idan har kin iya shiryawa da wuri za ki iya tafiya da mu, dan kuwa har mun shiga mota Allah ya sa aka tuna da ke..." Halitta ta bata amsa tare da juyawa ta fice, ta na jiyo kukan Zainab wacce ke fadin "Tsabagen wulakanci ni din ce za a mance fisabilillahi! Dady be da lafiya har ku shiga mota sannan za a tuna da ni? Wallahi kin yi da yar halak Halitta! Duk wannan munafuncin da ki ke kulla min za ki gani a kwaryar cin tuwan ki....." Sai da kusan minti goma sha biyar ya shude suna jiran Zainab, Ammy ta kule har ta ce da direba ya ja mota su tafi, sai ga ta nan har da yar jakar ta da ta tsaya shiryawa, idan aka dauke Zainab wacce ta shirya tsaf cikin bakar rigar abaya, daga Ammy har su Halitta hijabi ne jikin su. Kafar nan ya sha takalmi mai tsini kamar mai zuwa club. Taikaici ne ya sa Ammy kau da kai gefe yayinda ta karaso, boot ta bude ta aje jakar kayan ta, sannan ta dawo jikin mota daidai saitin Falmat, ta na mai nuna ta da dan yatsa ta ce "Malama kin san dai ba za ki sani zama tare da Direba ba ko? Gwara ma ki fito ki bani waje!" "Kun ji irin halin sakarcin na ta ko? Sai da na ce mu tafi mu barta ku ka ce ah ah! Dan uban ki idan ba za ki shiga mu tafi ba ki sha zaman ki! Kai Malam Habibu ja mota mu tafi!" Cewar Ammy a fusace ta na mai watsa ma Zainab harara. Ganin direba ya tada mota ya sa ta bude gidan gaba ta zauna ta na zumbure zumburen baki da guna guni babu wanda ya tanka mata. Su Jauro na mu su Allah ya tsare hanya, tare da fatan Allah sa Malam be ji rauni sosai ba su ka dauki hanyar Maiduguri. Gudu direba yayi sosai dan kuwa Ammy ji take kamar ta rufe idanun ta ta bude ta ganta a Maiduguri. Tafiyar awa biyar sai gashi sun yi ta a awa hudu, dan kuwa baikwai daidai a Maiduguri ta mu su. Sun tarar gidan Malam da ke New GRA babu kowa sai mai gadi, gun shi su ka sami labarin mutuwar Direban da ke jan motar Malam, cewar Maigadin take Direban ya rasu be ko shura ba, haka kuma ya sheda mu su cewa Malam ma ya na can kwance rai a hannun Allah a nan UMTH (University of Maiduguri Teaching Hospital). Asibitin Ammy ta ce a kai su ba tare da ta tsaya jin sauran bayanan tashin hankali da Maigadi ke fada mu su ba. Tun kafin su isa asibitin ta ke kiran number din Hajja Dudu amma ya ki shiga, da kyar bayan isar su asibitin sannan ta sami numbar Gana, shi ya sheda mu su suna Emergency and accident. Tun daga nesa su ka hangi Hajja Dudu, Hajja Kilishi, Madu dan Malam na biyu sai kuma 'yayan Hajja Kilishi mata guda biyu, Zinaru wacce ita ke bin Madu, sai kuma Kori wacce ita ce sa'ar Zainab. Kukan da su ka tarar Hajja Kilishi da sauran yaran na yi ba karamin daga mu su hankali ya yi ba, Gana da Madu ne kawai su ka iya daurewa duk da dai su ma din idanun su cike ya ke fal da kwalla, musammam Gana wanda gaba daya jinin Malam ya bata gaban farar rigar sa sanadiyar rungumosa da yayi sa'ad da aka dauko su daga wani dan karamin asibiti kusa da kauyen da su ka yi hatsarin. "Menene wannan jikin ka Gana? Ina Malam? Kar ka ce min jinin Malam ne haka jikin ka!" Cewar Ammy ta na mai ruko hannun Gana. Kai kawai ya girgiza mata dan kuwa tsoro da tashin hankali ya sa ya kasa magana, a kan idanun sa Direban Malam ya cika, haka kuma har lokacin salatin Malam ne ke masa yawo cikin kunne. Salati ya ke yi da karfi wanda duk wanda ya ji ya san Malam na cikin tsananin ciwo, Malam be dena salatin nan ba har sai da su ka iso Maiduguri, sai kuma tsit. Har Gana ya fasa kuka a tonanin shi Malam ma ya cika, shigar su asibitin aka sheda ma sa Malam na raye, sai dai yayi doguwar suma ne mai kama da mutuwa, wato ya shiga "Coma" "Gana ku fada min mana, ku amsa min dan Allah wani hali Malam ke ciki!" Ammy ta sake tambaya ta na mai fashewa da kukan da take ta kokarin dannewa. "Malam ya na ciki, kusan awa hudu kenan da aka shige da shi, Amma har yanzu dai shiru, hana rantsuwa dazu wani likita ya ce da mu suna iyakan kokarin su, Bayan wannan ba mu kara ji daga gare su ba Hajiya" Madu ne ya amsa mata ganin Gana be da niyar magana. Jin haka su Halitta su ma su ka kara saka na su kukan, waje ya kaure da koken iyalan Malam kai ka ce Malam ya cika, tun Madu na kokarin tsawatar mu su, har ya gaji ya sa mu su Ido, sai jama'ar wajan ne ke ba su baki. Su Ammy ba su jima sosai da zuwa ba Likita ya fito, ganin sa gaba daya su ka yo kan sa kowa da tambayar da ya ke masa, hakan ya sa ya nemi ganin Hajja Kilishi da Gana a Office, Ammy ta ce ba ta san zance ba kafar ta kafar Likita, ita ma din matar Malam ce. Su uku su ka dunguna zuwa Office din Likita. Bayan Likita ya yi kokarin kwantar mu su da hankali ne ya sheda mu su cewar sun yi iyakar kokarin su domin ganin Malam ya farfado daga doguwar suman da yayi Amma abin ya ci tira, dadin dadawa kuma ya sami "Spinal cord" injury, ya ji ciwo kashin bayan sa "Innalillahi wainnailaihi rajiun!" Cewar matan Malam suna mai fashewa da kuka. Cikin dakiya Gana ya furta "Haba mana dan Allah! Ku shiru ko ma ji bayani daga bakin sa, yau ko mutuwa Malam yayi kukan nan na ku ba zai amfana masa sa komai ba sai ma azabtar da shi da zai yi!" Jin haka duka su ka yi kokarin yin shiru, Gana na mai kallan Likita ya ce "Yaya kenan? Menene shawara ko fitar da shi za mu yi zuwa karsar waje?" Likita na duban Gana ya ce "Zan ba ka shawara tsakani da Allah, kada ku wahalar da Malam, ku bar shi nan gida Nigeria, a kuma masa addua, sauki na Allah ne, Allah ya yassare masa" Jin haka gwiwowin Gana sun yi sanyi kwarai, dan kuwa jiyayi tamkar likita na fadin Malam ba zai tashi ba. Da sanyin gwiwa su ka yi sallama da likita, in da ya ce a bar Malam ya kwana emergency ward suna monitoring din shi ko Allah ya sa a dace. Madu da Gana aka bari za su kwana wajan Malam. Duk yanda Ammy ta so ganin Malam ba a bari ta gan shi ba saboda gudun abin da ganin na shi zai haifar mata ta, haka duka su ka koma gidan Malam. Kamar yanda aka saba duk sanda su ka zo hutu Maiduguri, bangaran da aka ware na musammam domin saukar baki su Ammy su ka sauka. Manyan dakuna uku ne kowannan su da bandaki ciki, sai kuma madaidaicin Parlour mai dauke da kanan kujeru ruwan kasa. Halitta da Falmat dama tare su ke zama duk sanda su ka zo, Ammy da na ta dakin da ta saba sauka, sai kuma karamin ciki Zainab ke kwana ita kadai. Idan aka dauke Zainab babu wanda ya iya runtsawa daren ranar, Musammam su Hajja Kilish da su Zinaru, mutuwar Direban nan ya tsaya mu su rai dan sun saba sosai. Mutum ne mai kirki da haba haba da mutane. Daren ranar sarkin Musulmai ya sanar da ganin watan Ramadan, aka kwanta da niyar tashi sahur domin daukar azumi. Washagari da sassafe su ka koma asibiti, ba a mayar da Malam patient ward ba, Amma an bar su sun ga Malam. Ganin yanda aka daure kirjin Malam, ga robar samar da numfashi baki, hannun sa makale da robar ruwa, ga kuma na fitsari nan wanda yar robar ta fito ta cikin jallabiyar da su Gana su ka sanya masa daren jiya. Gashi fuskar Malam kumbure sosai goshin sa an daure da bandaje saboda tsayar da jinin da ke zuba da gan kan shi da ya fashe, babu wanda be zubda hawaye ba, lalle mutum ba a bakin komai ya ke ba. Matan sa duka biyun hannun shi su ka ruke, Ammy ke furta "Malam dan Allah ka warke ko na nemi yafiyar ka, na yi nadama, dan Allah ka yafe min" Zainab kuwa kallo daya ta yi masa ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, Wai Dadyn ta ne kwance haka kamar mutum mutumi! Yanda su ka mayar da dakin tamakar gidan makoki, ya sanya Gana tsawatar mu su, tare da fadin "Duk wanda ya san zai zo mana asibiti ya mana kuka dan Allah yayi zaman sa gida, ba ma bukatan zuwan sa!" Hakan ya sa duk wanda kuka ya zowa sai ya fita yayi kayan sa waje gudun fadan Gana. Yan uwa da abokan arziki, ciki har da daliban Malam, Wanda ke sauraran tafsirin sa duk sanda aka fara azumin Ramadan, sun yi cincirindon zuwa duba Malam, Amma babu damar ganin shi likitoci sun hana. Asibitin nan babu wanda be san da kwanciyar Malam Birma ba, haka lungu da sakon Maiduguri haka labari ya zaga ko ina. Sai da Malam ya kwana uku Emergency Ward aka mayar da shi Aminity 4. Jikin sa dai ba canji, ya na kwance sai an tayar sai an kwantar, su Gana kullum suna cikin wanke kayan jinyar sa, da yi masa wanka idan ya kama. Satin Malam uku a asibiti aka fara shirye shiryen fita da shi India. Ammy da 'ya'yan kuwa hado nasu ya na su su ka yi su ka tare a Maiduguri karo na farko da kan iyalan Malam ya hadu sosai, kowa ya dukufa wajan ibada da rokawa Malam sauki alfarmar wata Mai girma. Ranar da aka akai azumi ishirin da biyar, Ammy ce a wajan Malam, ita ta karbi Gana da Madu ta ce su dan je gida su huta. Zaune ta ke kan kujera, ta kurawa fuskar Malam Ido ta na mai kukan zuci. Sam ba ta lura da motsin da hannun Malam ke yi ba tsabagen nisan da zuciyar ta ta yi na tunani da begen Malam. Ganin murfin idon Malam ya motsa ya sanya ta kara matsawa kusa da shi da sauri yayinda bugun zuciyar ta ya karu. Kamar gizo haka ta kara ganin murfin idanun Malam sun motsa, haka ma yatsun hannun sa. Cikin ihu ta ke kwallawa su Zainab wanda ke zauna daga waje kira. Da gudun su su ka shigo ciki, Ammy na goge kwalla ta ke fadin "Ku duba ku ga yau Malam ya motsa, Alhamdulillah Malam ya motsa! Maza ki kira likita ku fada masa Malam ya motsa" Ganin hannun Malam na motsawa Halitta ta fita da sauri sauri gudu gudu kiran likita, Zainab da Zinaru kuwa hannun Malam su ka ruko, daga mai fadin "Alhamdulillah Daddy dama na san za ka tashi" Sai mai fadin "Malam ya tashi, Alhamdulillah Malam ya tashi" Likitoci uku ne da Nurses biyu su ka biyo Hilitta jin motsawar Malam, a zahirin gaskiya sun ma fitar da rai da tashin sa. Cike da mamaki iko na Allah su ka umarci su Ammy su ba su waje. Nan su ka bar su ciki suna duba Malam, su Ammy kuwa sai kiran yan uwa da abokan arziki su ke suna sheda mu su Malam ya motsa. Sai da su ka dau kusan awa daya sannan su ka sami damar ganin Malam, su Gana da Hajja Kilish tuni su ka karaso jin labarin farin ciki. Rashin baki be hana Malam aika ma iyalan sa da murmushi ba ganin yanda su ka zagaye shi. An cire masa rubar taimakon numfashi, sai na fitsari da na ruwa ne kadai ya rage jikin sa. Kowa burin sa ya ruke Malam, ko kuwa Malam ya kai kallan sa gare shi. Hajja Kilish kadai farfadowar Malam da kuma ganin sa ya dan kashe mata gwiwa musammam rashin maganar sa, duk da likitoci sun tabbatar mu su cewar a hankali Malam zai fara maganar. Sai da la'asar su ka yiwa Gana da Madu Sallama domin su koma gida a yi girkin bude baki. Ana gobe Sallah da sassafe Usman da Isa su ka dauki hanyar Maiduguri, Dan tun da Malam yayi hatsari ba zo sun duba shi ba. Shadaya da rabi su ka isa Maiduguri kai tsaye asibiti su ka wuce. Likitoci sun hana yan dubiya ganin Malam sai dai iyalan sa kadai, Amma Gana yayi magana su ka shiga. Duk da Malam ba ya iya magana, ganin su Usman sai gashi ya na fara'a sosai. Shi kuwa Usman ganin yanda Malam yayi fari sosai ya kara tsayi ya sanya shi zubda hawaye, cike da mamakin hawayen Usman Gana ya ce "Ai Malam Usman jikin Malam Alhamdulillah, yayi kyau fa sosai Malam ya sami sauki, ji fa yanda yayi fari sol da shi, kashin bayan sa ne ya sami matsala shi ya sanya ba ya iya zama ko tashi, ba ya iya motsa kafafun sa, Amma ka ga ai yana dan motsa hannun sa, da kuwa ko hannun ma ba ya motsawa wallahi!" "Allahu akbar, Allah ya bawa Malam lafiya" "Allahumma amen, in Sha Allah sauki ya fara samuwa, bayan sallah da sati daya ma za a fitar da shi India, mun sami wani asibiti na kwararrun likitoci a can" Madu ya amsa mu su, ya na duban Usman ya kara da "Na gane Malam Isa sosai, shi dai Malam Usman ne ban waya ba, ko shi ne sirikin namu ne? Mijin Yakura?" Dab! Gaban Usman ya fadi jin an ambato auren da ya ke kwana da shi ya ke tashi da shi a kulli yaumin. Gana na mai murmusawa " Ya ce eh fa shi ne, Malam Usman wannan shi ne Madu, shi ne ke bi na" Nan Usman da Madu su ka kara gaisawa, in da Madu ya masa nasiha akan hakuri, a cewar sa zama da mace irin Yakura sai hakuri, dan kuwa mace ce mai taurin kunne. Sai da Gana ya dan zungure shi sannan yayi shiru, Usman kuwa cikin ran sa fadi ya ke be da buri da ya wuce a sauwake masa wannan karfen kafan da aka daura masa, wato auren Zainab. Ana yin azahar su Usman su ka yiwa Gana da Madu sallama, ga mamakin su sai ga Malam ya na ta motsa hannu kamar ya na son yiwa Usman magana, hakan ya sa Gana fadin "Tun da Malam ya kwanta ban taba ganin yayiwa wani mahaluki yanda ya ke ma ka ba Usman, ka ga fa kamar so ya ke ya ma ka magana" Cike da tausayawa Usman ya matsa gare shi, yana mai duban Malam ya sanya hannun shi cikin na sa, ganin har lokacin Malam be dena motsa hannun ba Usman ya ce "Malam Gana shin ko za a sami takarda da biro? Ina ga kamar akwai abin da Malam ya ke son ya fada min" Gana be ki ta Usman ba ya nemi yar takarda da biro, ya bawa Usman. Hannu na rawa Usman ya sanya biro cikin yatsun Malam, sannan ya dura hannun Malam bisa takardar. Ga mamakin kowa sai ga Malam na kokarin rubutu, amma ina rubutun ba ya fita tamkar na yaro dan koyo. Sai da Usman ya taya shi ruke biro, da ikon Allah sai ga Malam yayi dan rubutu da ajami sanin Usman be iya boko ba. Kalma biyu ya rubuta "Zainab.... Amana..... " Ya na rubuta haka ya saki birun, Usman ya daga rubutun da ya fi kama da jagwalgwalon yara, da kyar ya iya karantwa, hanun sa cikin na Malam ya furta "Na ma ka alkawarin Malam, Ni da Zainab mutu ka raba" Cikin nuna jin dadi Malam ya murmusa. Jiki sanyaye Usman ya tura takardar da Malam yayi rubutu cikin aljihun sa, su ka yi sallama su ka tafi. Tafiyar su ba da dadewa ba Ammy da Falmat su ka ta zo. Ganin yanda Malam yayi fari sai murna ya kamata, fadi ta ke "Kai Alhamdulillah ji yanda jikin Malam yayi fari, yayi kyau wallahi" Madu ya ce "Wallahi fa Hajiya, Amma tunda ya kwanta ba mu taba ganin fara'arsa ba kamar na yau da wannan bawan Allah Usman ya zo" "Allah sarki ashe ya zo" Cewar Ammy cikin faduwar gaba, dan kuwa ji ta yi ba za ta iya jiran Malam ya warke ba, gwara ta nemi yafiyar sa ko ta sami sauki cikin ran ta. Kamar yanda ta kudiri niya, sai da ta nemi gafarar Malam kafin ta tafi, ta na magana ta na zubda hawaye hakan ya sa Malam girgiza mata kai, sai da ta ga ya na murmushi sannan ta gamsu. Duk sanda ta dan gifta ta wajan gadon sa sai ta ga ya ruko hannun ta, hakan ba karamin dadi ya ke mata ba, ta san ta isa matar so, tunda ciwo be hana Malam nuna mata so da kauna ba. Cikin so da kewar Malam ta yi masa sallama, har ta juya za ta tafi ya kara ruko hannun ta. Ammy na mai darawa ta furta "Ka yi hakuri Malam, da sassafe zan dawo na kawo maka tuwan sallah in Sha Allah" Malam na darawa yayinda kwalla ya dan gangaro daga idanun sa ya dan motsa kan sa. Ita ma Ammy kwallan ce ta fara cikowa idanun ta, ta yi saurin zame hannun ta ta fita, idanun Malam na kan ta har ta fice. Daren ranar da ke daren duba watan sallah ne gari sai hidima ake. Gana da Madu ma zaman hira su ka yi bayan sun sha ruwa, hiran Usman da auren shi da Zainab su ke. In da Madu ke nuna jin dadin shi akan hukuncin da Malam ya yanke na auren Zainab, cewar shi "Ka san Allah Gana da ka san yanda yarinyar nan Yakura ta lalace a Instagram da sai ka koka, ai na nuna maka wani hotan ta ka musa min ka ce ba ita ba ce, har da kwaba ta kar da na bari Malam ya ji, ai ga irin ta nan, yanzu da komai ya fito zahiri wa gari ya waya? Bari ma ka ga na nuna maka wasu da ga ciki" Ya shiga Instagram ya na neman shafin Zainab, Amma ga mamakin sa babu shi babu alamar shi. Cikin cije ya yatsa ya ce "Kash yar banza ashe ta yi deleting, Shi ya sa Hajiyar mu ta birgeni da ta hana su Zinaru kowani Social Media! Wallahi ba karamin jan hankali yara mata ya ke ba, musammam masu rawan kai irin Yakura!" Gana na mai mikewa bisa carpet din da su ka shimfida tsakiyar daki ya ce "Toh sai dai Allah ya dada kare mana su, ba dai an aurar da ita kowa ya huta ba, Madu bari na dan mike kadan, dan Allah ka sheda min idan an ga wata, Allah ya sa ba talatin za a yi ba, azumin asibiti babu dadi" Madu ya amsa da "toh" yayinda ya cigaba da danne dannen wayar sa. Cikin yardar Allah aka sanar da ganin wata, gobe sallah. Madu ne ya kira su Hajja Kilish ya fada mu su, tare da jaddada mu su lalle a kawo mu su karin kumallo da wuri. Ranar Sallah rana ce da iyalan Malam ba su taba manatawa da ita ba. Motsin Malam ne ya tada Gana da asubar fari, ganin halin da Malam ke ciki, jiki sankare idunun sa sun kafe ya sanya shi ihu ya na salati ya ke fadin "Madu Malam! Innalillahi wainnailaihi rajiun! Madu Malam, Madu kira likita!" Hakan ya sa Madu fita a guje. Hannun Malam Gana ya ruko, ya na hawaye ya ke fadin "Innalillahi wainnailaihi rajiun! Lailahailallah Muhamadur rasulillahi! Lailahailallah Muhamadur rasulillahi!" Malam na mai damke hannun Gana ya tsinci kan sa ya na mai amsawa da karfi ya furta "Lailahailallah Muhamadur rasulillahi sallahu......" Sai tsit, Gana ya na ji ya na gani an zare ran Malam, kullu nafsin zaikatul maut *Khadija Sidi*   *Khadija Sidi*Auren Shehu (15 continuation)   Kafin likita ya karaso har Gana ya sa tafin hannun sa bisa fuskar Malam, ya na mai karanto adduar neman rahama ya rufe idanun Malam, tare da jan zani ya rufe fuskar sa, sannan ya zauna a kasa dirshen ya na kuka kamar kankanin yaro. Ko da Madu da likita su ka shigo, Madu ya ga Malam rufe sai ya rufe Gana da fada, akan wani dalili Gana zai rufe Malam! Yaushe ya zama likita! Shikenan ya kashe mu su Malam! Gana ya cigaba da kukan sa ba tare da ya kula Madu ba, wanda sam ba cikin hayyacin sa ya ke ba. Likita be fasa yaye zanin da Gana ya rufawa Malam ba, ya sanya safar hannu na roba, ya dan kara duba gawar ya tabbatar ya cika da gaske, sannan ya zare robar ruwan da ke hannun Malam, ya fara kokarin zare na fitsari wanda ba a yi cikakeken awa daya da saka shi ba, Amma azarbar fitar rai ya sa shi cika har ya na komawa sama. Ganin likita ya kara mayar da zani ya rufe Malam nan Madu rungume gawar Malam, ya na fadin "Hasbinallahu wani'imal wakilu! Allah ya yafe maka kurakuran ka Malam! Allah ya ji kan ka! Allah ya sa annabi ya san da zuwan ka!" Cikan kankanin lokaci aka hade komai na Malam. Gana ne ya kira Hajja Kilish ya ce kada su kawo mu su abinci, ga su nan ma an sallami su, Malam ya sami sauki, gida za su taho. Ita dai ta amsa da toh, azahiri kuma jikin ta ne ya dau rawa yayinda bugun zuciyar ta ya karu, dan kuwa jikin ta ya bata akwai abin da ya faru, hakan nan ba za a sallame su ba, in ba dai saukin mutuwa ya samu ba. Aikuwa zatan ta ya tabbata sai ga su Gana da gawar Malam, sun shimfide mata tsakar falo. Hajja Kilish neman kuka ta yi ta rasa, ta na zaune daidai kan Malam ta ke tsawatar su Ammy da yara, wanda su ne su ka fi kowa ihu da kuka, fadi ta ke "Kul kada ku kara mana ihu a nan! Sakayyar da za ku masa kenan? Ku dena mana kuka na ce!! Yanzu Aleesha har da ke? Malam fa ya na jin ku!" Zinaru kuwa aljanu ta ringa tayarwa. Hajja Kilish tare da Gana da Madu ne su ka wanki gawar Malam, su ka masa sutura. Ko da aka dauki Malam za a fita da shi Hajja Kilish ta tashi da sauri za ta ruko makarar amma ina tuni ta yanki jiki ta fadi sumammiya, ba ita ta farfado ba sai bayan da aka sallaci Malam aka kuma kai shi gidan gaskiya. MashaAllahu Malam yayi mutane matuka. Su Usman da daliban Malam ba su sami janaiza ba, dan kuwa sai da aka yi awanni da birne Malam su ka iso. Sun zubda hawayen rashin Malam kwarai sanda aka kai su kabarin Malam su ka masa addua. Kamar yanda Malam ya ke yawan fada idan ya mutu kar a masa zaman makoki, su Gana sun yi kokarin hanawa amma ina hakan ya ki yiyuwa, kullum gidan cike ya ke fal da jama'a, yan unguwa, yan uwa da abokan arziki abin takaici shi ne yanda gidan mutuwar ya so ya zama gidan biki, iyalan Malam da su aka yiwa rashi ne kadai ke cikin bakin ciki da kuka, in da ake bikin sallah su kuma su ke fama da bakin ciki da alhinin rashin Malam. Ranar da Malam ya cika kwana uku su Usman su ka nemi yiwa su Ammy gaisuwa, duka iyalan Malam sun fito an gaisa, ban da Zainab wacce a cewar ta zafin mutuwar Malam daya ya ke da zafin ganin fuskar Usman. Ganin ba ta fito ba Usman be tambayi ina ta ke ba, yayiwa su Ammy gaisuwa su ka juyo Kano ya na mai tunanin yanda rayuwa za ta kasance akan alkawarin da ya daukarwa Malam. Ranar da Malam ya yi bakwai Ammy ta so komawa Kano, yan uwan Malam ne su ka ruke ta da ta zauna nan gidan Malam ta gama takaba tare da yar uwar ta Hajja Kilishi, tunda ko ta je Kano ma gun wa za ta koma? Duk yan uwa suna nan Maiduguri. Da wannan ta hakura ta zauna. Sai da Malam ya yi sati biyu da rasuwa, jama'a ka dan dauke kafa. Gidan ya fara shiru, gashi babu wanda ya ke cikin walwala musammam mutum hudu, kusan za a ce mutuwar Malam ta fi duka, wato Hajja Kilish, Madu da Gana, sai kuma Halitta. Gaba daya ta rame ta lalace, sai ta kara fari da manyan idanu. Zainab kuwa bayan mutuwar Malam, babban burin ta shi ne a gama alhinin mutuwa a zo a raba auren ta da Usman, dan kuwa ko sama da kasa za ta hade ba za ta yarda da auren ba, musammam yanzu da aka wayi gari babu Malam a doran kasa. Da la'asar sakaliya Madu da Gana su ka karbi bakwancin Shiek tare dan shi Sudais da kanan sa mata biyu, Zara da Ummi, kasancewar sanda aka yi rasuwar ba sa nan suna Saudiya. Bayan sun yiwa su Ghana gaisuwa ne Madu ya shigar da matan cikin gidan wajan su Hajja Kilishi, tare da sheda mu su cewar Shiek da Sudais na Falon waje, idan sun shirya za su shigo su yi mu su ta'aziya. Ya ko ci sa'a Hajji Kilishin zaune ta ke tare da Ammy. Kanan Sudais su ka mu gaisuwa, tare da neman su Zinaru wanda dama su su ka sani, duk da dai suna kwadayin ganin amaryar yayan su da aka ce diyar amaryar Malam ce da ke zaune birnin Dabo. Zinaru da Kori ne su ka fito jin zuwan su Zara. Suna cikin gaisawa ne Madu ya dawo biye da shi Sudais da Shiek ne. Bayan sun yiwa su Hajja Kilish gaisuwa, Shiek ke tambayar Ammy ina su Halitta su ke, da fatan ba su koma Kano ba ko. Ammy ta ce "Eh suna nan tare da ita, Kano ai ta yi mana nisa in ba dai Zainab wacce ke da miji a can ba, bari a kira su, Kori kira yan uwan ki" Kori ta tashi ta shiga kiran su. Tun tashin ta gaban Sudais ke faduwa, ya zubawa kofar da Kori ta fita idanu, da ke shi ne ke zaune kurar da ke kallan kofar, Shirin ganin matar da Shiek ya zaba masa ya ke cikin zulumi. Jim kadan Kori ta dawo biye da ita Falmat ce sanye da hijabi har kasa, kallo daya Sudais ya mata ya tabbatar ba ita ba ce amaryar ta sa tsabagen kuruciya da fuskar Falmat ta nuna karara duk da kiban da ta ke da shi. Cike da ladabi ta durkusa har kasa ta gaishe da Shiek da Sudais. Su ka amsa tare da mata gaisuwa. Ammy ta gabatar da Falmat a matsayin autar ta. Zainab wacce har cikin ran ta ba ta yi niyar ganin baki yau ba, da kyar ta tashi daga kan gado, bakar abaya ta ja ta dora bisa yar karamar rigar da ke jikin ta, ta ja mayafin abayar ta rufe kan ta. Za ta wuce ta hango Halitta cikin dakin su, bisa sallaya. Tun da ta ji sakon isowar Sudais ta ji wani bakin ciki ya kara ziyartar zuciyar ta, ta ma kasa tashi bare ta fito su gai sa. "Malama wanda aka bawa ke ya zo,, you better bring your ass to the parlour, aha bari na je na ga wani local champion Daddy ya bawa" Cewar Zainab cikin tsoka na, ta wuce ta na yiwa Halitta yar dariyar mugunta. Tun kafin ta karasa falon ta fara jin wani irin ni'mantaccan kamshi, zuciyar ta daya ta sanya kafar ta hakan yayi daidai da hada idanu da shi, gaban ta yayi mummunar faduwa har ta tsinci kanta ta na mai fadin "Hasbinallahu wani'imal wakilu!" Ta sha ganin maza wanda su ka amsa sunan su maza ma su kyau, Amma ba ta taba ganin wanda ya tafi da imanin ta kamar Sudais. Sudais wankar tarwada ne mai duguwar fuska da ke dauke saje da gemu baki wuluk har sheki ya ke, ba wani dogo ko siririn hanci gare shi ba, girma da tsayin hancin sa yayi dadai da fasalin fuskars sa, haka kuma idanun sa da ke manya dan ko ita Zainab ba za ta nuna masa kyawun idanu ba. Kasancewar zaune ya ke kan kujera be boye tsayi da fadin da ya ke da shi ba, sai ma kwarjini da ya mata. Idan ko gayu da wayewa ne kallo daya za a yiwa Sudais a san gidan shi aka zo, murmushin da ya sakar mata, gefan kumatun sa biyu su ka lutsa wato alamun dimpol ne ya dada rikita Zainab wacce ta tsinci kanta ta na mai shigowa Falon da sauri gudun kar sauran yan falon su lura da halin da ta tsinci kan ta ciki. Cikin ran ta fadi ta ke "Innalillahi kar dai wannan shi ne mijin da Dady ya so aura min? Ya ilahi Allah wallahi da ni ya fi dacewa! Wayyo ya hadu! He should be mine! Da ni ya dace!" Da kyar ta iya daurewa da gaishe da Shiek ya amsa tare da mata gaisuwa, sannan ta kashe da Sudais, wanda ya amsa ya na mai duban ta da kyau. Tun shigowar ta ya so kare mata kallo, Amma yanda ta ke kallan sa ya sa shi kasa tsayawa ya kalle ta da kyau har sai bayan da ta shigo ta zauna kusa da Falmat. Ko shakka babu ya amince da abu daya, Zainab ta amsa sunan kyakkyawar mace ta ajin karshe, kuma ga dukkannin alamu wayayyiya ce kuma yar gayu, sai kuma akwai abinda ya ke so da be gani a tattare da ita ba, shi kan sa ya kasa gane menene abun, haka kuma ya tsinci kan sa ya na mai fatan Allah ya sa ba ita ba ce matar da Shiek ya zaba masa ba. Gaisuwa ya mata, ta na cikin amsawa yaji sassanyar muryar Halitta ya ziyarci kunan sa ta sigar sallama wanda shigowar ta yayi daidai ta furucin Ammy na "Wannan ita ce Zainab, wanda mu ke kira Yakura ita ce babbar su" "Allah sarki ita ce Malam ya sheda min maganar auren ta ranar da na masa ganin karshe, Allahu akbar duniya kenan" In da Zainab ta ji kamar ta kurma ihu jin furucin Shiek akan auren ta, Sudais kuwa wani dadi ne ya ziyarci zuciyar sa yayinda ya zubawa Halitta idanu, sanye ta ke cikin hijabi fari kal har kasa, kan ta sunkuye har ta shigo falon ba ta kalli Sudais ba bare ta lura da kallon da ya ke mata "Alhamdulillah for you, Alhamdulillah, she so MashaAllah! Na gode Abba da wannan zabi na ka" Cewar Sudais cikin zuciyar sa, wanda ya fadada fara'ar sa dan kuwa ya kasa boye farin cikin sa na ganin Halitta, ta yi masa har cikin zuciyar sa.   *Khadija Sidi* Auren Shehu 16 Cike da ladabi ta gaishe da Shiek, Wanda ya amsa cikin ran sa ya na mai yabawa da nutsuwar Halitta. Ta'aziya ya mata, sannan ya kara da "Ga dukkan alamu wannan ce matar da Malam ya bawa Sudais" Halitta ta sunkuyar da kai yayinda bugun zuciyar ta ya karu, dan tun da ta dunfaro falon ta ji kamar ana mata kallan kurulla, haka kuma jikin ta ya bata wannan da Shiek ya ke magana ne duk da ita ba ta daga ido ta kalle shi ba. Zainab kuwa wani irin bakin kishi ne ya dasu cikin ran ta, ai dama ita Malam ya yi niyar ya bawa Sudais ba Halitta ba, dan haka sai in da karfin ta ya kare. "Halitta ba, eh ita ce, ya ko yi dace da diya mai mutunci, Halitta ta san darajar manya" Cewar Hajja Kilish iya gaskiyar ta, hakan ya sa Zainab watsa ma Halitta harara ta wutsiyar idanu. "Ai daga gani ma, Allah ya tabbatar mana da alkhairin sa, ya sa a yi damu, in Sha Allah lokacin da mu ka saka da Malam ba za mu saba ba" Duka su ka ce "Amen" ban da Zainab wacce ta ke ta sakar yanda za a yi Sudais ya zama mamallakin ta. "Halitta ban ji kun gaisa da angon na ki ba" Hajja Kilish ta fada ta na mai duban Sudais wanda ya saka ma Halitta idanu ba tare da ya ji kunyar kowa ba. Cike da kunya Halitta ta kai kallan ta gare shi, sai ga idanun ta cikin nasa, ta yi saurin yin kasa da na ta idanun sannan ta furta "Ina wuni?" Zainab ta kauda kai dan kishi ji take kamar ta tashi ta bar mu su wajan. Babu abinda ya dada kona mata rai fyace yanda Sudais ke washewa Halitta baki sa'ad da ya amsa gaisuwar ta, tare da mata ta'aziya, dan kuwa rabin fara'ar da ya ke yiyiwa Halitta be yi mata ba. Kasa daurewa ta yi, ita ta fara tashi ta mu su sallama ta shige ciki. Shigar ta ba da dadewa ba Shiek ya mu su sallama, har sun fita sai ga Zara ta dawo, gun Halitta ta je ta dan tsugunna cikin rada ta furta "Ya Sudais ya ce na karba masa number dinki" Ta mika mata wayar, da kamar ba za ta karba ba, ganin yanda Ammy ke kallan ta ya sa ta karba ta saka numbar. Cikin jin dadi Zara ta karba tare da fadin "Na gode Anty Halitta, Allah ya ba mu alkhairin sa" Ta tashi ta fita. Kamar yanda su Zara su ka tafi da Halitta a baki, haka ma su Falmat da Kori su ka ta yaban Sudais. Har daki Falmat ta bi Halitta. Da ke tun tafiyar Shiek da iyalan sa ta komawar ta daki ta kwanta. Falmat ta shiga da gudun ta, ta fada kanta "Alhamdulillah wani hani ga Allah baiwa, Allah ya hana ki Usman dan ya ba ki mafi alkhairin sa!" A hankali ta dago ta na kallan Falmat, sai a sannan ta lura da jajayen idanun Halitta da hakuma hawayen da ke kwance kunci ta. Cike da mamaki Falmat ta ce "Ya salam! Kukan na menene? Ina dai fatan na rashin Dady ne a wannan rana ta farin ciki" "Na komai ne Falmat, komai ya cushe min, komai babu dadi, rayuwa babu dadi, rayuwa ta chanza, rayuwa ta zo min ba yanda na ke tsammani ba! Falmat ba na san shi...." Halitta ta fada ta na mai zubda hawaye, baki Falmat ta bude ta na kallan ta. Ba ta gushe ba ta kara da "Kin fi kowa sanin burin rai na miji ne gurin yaya ta, ina ji ina gani aka sanya tazara a tsakanin mu. Na daukar wa Dady alkawarin auran zabin shi, kuma ba zan saba alkawarin ba ko da kuwa hakan na nufin rasa farin ciki na, gashi yau an wayi gari babu Dady Falmat......" Ta karasa ta na mai fashewa da kuka. Tausayin Halitta ne ya rufe Falmat. Rungume ta ta yi cikin rarrashi ta ke magana, ta na fadin "Ki yi hakuri Halitta, rashin abin da rai ke so ba karamin rashi ba ne, sai dai kuma wani sa'in hakan shi ya fi alkhairi a gare mu, daga ganin Sudais alkhairi ne Halitta, wallahi hankalin kowa ya kwanta da shi, darajar biyayya Allah ba zai bari ki tabe ba Halitta" "Allah ya sa Falmat, Allah ya sa" Cewar Halitta ta na mai kokarin tsayar da hawayen da ke zuba daga idanun ta. Haka Falmat ta cigaba da ba ta baki har sai da ta sami nutsuwa ta dena kuka. Da tunanin Sudais Zainab ta kwana cikin ran ta, washagari da safe ta kasa dakewa, sai ga ta dakin su Halitta ta ci sa'a Halitta ce kadai zaune bisa gado ta amsa wayar Sudais kenan, ta zauna tunani. Ganin Zainab da yanda ta zo mata mamaki ya rufe Halitta, musammam da ta ga ta zauna kusa da ita har da riko hannun ta, ta ce "Halitta, dama wani shawara na zo da shii" Kallan ta ta yi na wani dan sakanni, sannan ta ba ta amsa da "Toh Yakura, ina jin ki" "Dama batun Sudais ne, na san ba kya san shi, Kuma idan har ba kuskure na yi ba, na san kin jima da saka wannan almajirin da Dady ya aura min a ran ki....." Daf! gaban Halitta yayi mummunar faduwa, ta yi saurin zare hannun ta daga cikin na Zainab ta na fadin "Auzubillallah! Wannan wani irin magana ne Yakura!" Murmushi Zainab ta sakar mata, kana ta ce "No kwantar da hankalin ki, ba wani abu ba ne dan kin so shi, ni yanzu ma hakan rahama ya za me min, domin kuwa Allah ya sa min san Sudais, wallahilazim Sudais shi ne mijin da na ke burin samu a rayuwa ta, sam be dace da ke ba, Kuma duka kwamacalar nan Dady ya hada, Allah ya masa rasuwa, kin ga kenan hankali kwance za a iya warware komai. shi wancan almajirin sai ya sake ni, in ya so ya aure ki, ni kuma na auri Sudais....." "Allah ya sauwake mi ki Yakura, tur da tunani irin na ki!" Halitta ta katse ta cikin dakiya duk da har ga Allah zuciyar ta ta kwadaitu da zance Zainab. Ba ta damu da irin kallan da ta ke mata ba, ta kara da "Ina hankalin ki ya tafi ne? Wai yaushe za ki gyara hali ne? Toh ki saurara ki ji ni da kyau, zabin Dady shi ne zabi na, hawainiyar ki ta kiyayi rama na, Sudais miji na ne In Sha Allah, gwara ma ki ruke mijin ki ko Allah ya sa ki dace...." "Ke dallah malama rufa mana baki! Yen! Yen! Yen!" Zainab ta daka mata tsawa ta na mai kwatanta yanda Halitta ta yi maganar, ba ta gushe ba ta kara da "Har ke kin sa! Wani rama gare ki! Ki asuwa cikon benci da ke? Na tabbatar aka jera mu ni da ke ba Sudais ba ko wani da namiji a duniyar nan sai ya dauke ni sau dubu kafin ya dube ki! Ki na nan banza a banza kashi a leda! Nunan rana da ke har kin samu ina shawara da ke! Toh ki saurara ki ji Halitta idan har ban mallaki Sudais ba ban cika diya mace ba! " Ta tashi fuuu ta fice ta na mai buga kofa. Tagumi Halitta ta yi idanun ta na kallan kofa, tun da take a duniya ba ta taba ganin mutum irin Zainab ba, in dai san kai da san zuciya ne, a komai ita kan ta ta sani sam ba ta tunanin kowa a cikin lamarin ta fyace abin da zai dada mata. Dakin Ammy ta nufa, ta tarar da Ammy ta fito daga wanka kenan ta zauna za ta shafa mai. Babu gaisuwa babu komai kai tsaye ta ce "Ammy akwai maganar da na ke so mu yi" Fasa shafa man ta yi, ta na duban Zainab ta ce "Ina sauraran ki" Zainab ta matso gaban Ammy ta zauna, hannayen ta bisa cinyar Ammy, hawaye na zuba daga idanun ta ta ce "Ammy dan Allah ki yafe min, na yi kuskure, dan Allah ki yafe min, Ammy dan Allah...." "Na yafe mi ki Zainab, na yafe mi ki duniya da lahira, bayan rasuwar Malam Zainab idan ban yafe mi ki ba me ya rage min a rayuwa? Na yafe mi ki" Zainab na murmushin jin dadi ta furta "Ammy na gode, Ammy dan Allah ina neman alfarma" "Ina jin ki" Cewar Ammy yayinda ta fara shafa mai. "Akan auren da Dady ya daura min Ammy, Ammy dan Allah ki raba aure na da.... " "Ba zai yiyu ba! Auren ki Malam ya daura shi, ba zan taba kashe shi ba Yakura, idan har kin ga auren nan ya mutu toh Usman ne ya sake ki da kan shi...." "Ammy dan Allah...." "Yakura!" Ammy ta katse ta cikin nuna bacin rai, ta kara da "Kada ki tsaya jayayya da ni!" Jiki sanyaye Yakura ta amsa da "Toh Ammy, Allah ya huci zuciyar ki" Tashi ta yi ta fita ran ta na radidi ba ta taba zaton Ammy za ta juya mata baya haka ba. Ta kasa zaune ta kasa kwance daga karshe hukunci kai maganar dangin Ammy wanda ta tabbatar za su mara mata baya akan kashe auren na ta tayi, dan kuwa babu wanda ya goyi bayan auren, duka sun nuna bakin cikin su karara akan auren Zainab da Usman. Jin za ta tafi gidan Babbar yayar su Ammy, Anty Sauda. Ammy ba ta hana ta ba, ta dai ce mata kada ta yi dare. Ta ci sa'a ta tarar da kanwar Ammy wacce su ke kira Anty Hannah ma ta je gidan. Nan Zainab ta saka mu su kuka, ta hada karya da gaskiya duka ta fada mu su. Cike da takaici Anty Hannah ta ce "Toh shi Malam ma fisabilillahi ya ma zai dauki yar sa, jinin mu ya aurar da ita ga almajirin sa! Dan ruga! Ai ya san tsadar mu, kila ya manta wahalar da ya sha kafin ya auri Hajja Aleesha ne!" "Toh da ke Allah ba azzalumin bawan sa ba ne ai gashi ya dauke Malam a doran kasa, ke bar kuka wallahi babu wanda ya isa ya sa ki zama da almajiri! Dangin mu ko talaka ba su taba aure ba bare almajiri!" Anty Saude ta ara ta yafa. Cikin jin dadi Zainab ta shiga share hawayen ta, ta kara da "Ammy ta ce matukar ba shi ya sake ni da kan shi, ita ba za ta kashe auren ba, Kuma wallahi na san da kyar ya sake ni Anty...." "Ke rabu da wannan Ammyn ta ki, kila zafin mutuwar mijin na ta ne ya toshe mata kwakwalwa, in ba haka ba ya sha giyar wake ne da za a aura masa kyalleliyar diya, jinin shuwa da Kanuri kuma ya sake ki dan kan sa? Mu nan za mu sa a kawo mana shi tun daga Kano har barracks, dan uban shi sai ya sake ki!" Cewar Anty Saude da ke mijin ta soja ne mai babban matsayi "General". Anty Hannah da Zainab su ka sa sowa, su na mai fadin "Yayi matar General" Zainab ta kara da "Wallahi shi ya sa na ke kaunar ki Anty Sauda, Allah ya ja da tsayin rai!" Anty Sauda na mai darawa ta furta "Ku ji yarinya fa! Ai yiwa akai ne! Yanzu ki na diyar mu sai mu bar ki da auren almajiri? Allah ya mana sutura! Ai ke din matar manya ce, san kowa kin wanda ya rasa, babu talauci a jinin mu, Kuma in Sha Allah ba za mu gan shi ba, ina ki ka ce shi almajirin ya ke yanzu" "Amen Anty Saude, ai ya na nan gidan mu, shi dan masu gida ba! Wai fa BQ Dady ya ce na koma, wai nan ya ce Ina kwana da shi...." "Lailahailallah! BQ!" Su ka fada a tare, Anty Hannah ta kara da "Yanzu ita Hajja Aleesha sai ta mike kafa ta na bacci diyar ta na kwance da almajiri a BQ?" Zainab ta rangwabar da kai ta ce "Wallahi Anty, har ma ta sa na kwashe kaya na, ana gobe Dady zai yi accident ma fa can na kwana...." "Kin kwana da shi???" Anty Hannah ta tambaya cikin tsawa. "Ah ah kofa na rufe ina zan yarda na kwana da shi" "Atoh yanzu na ji batu, yar tselan uwa da kin yabawa aya zakin ta ki ka shiga hannun wannan gardin!" Cewar Anty Saude ta na mai hango Usman a idanun ta sanda ya zo ta'aziyar Malam. Sai da Anty Saude ta yiwa Zainab alkawarin za a yi duk yanda za a yi Usman ya sake ta, ko da kuwa hakan ya na nufin za a je har kanon a dauko Usman ne, sannan Zainab ta dawo gida zuciyar tas, dan ta san auren ta da Usman ya kare, sai kuma batun soyayyar da ta ke shirin kullawa tsakanin ta da Sudais.   *Khadija Sidi* Auren Shehu 17   Da ya ke mijin Anty Sauda a barracks ya ke General, cikin gida kuwa sai yanda ta yi da shi, tuni ya dorar da bukatar ta, in da yayi waya Bokabo barracks ya ba da umarnin dauko masa Usman a daren ranar, ya bayar da adireshin gidan Malam, tare da fasalta kamannin Usman kamar yanda Zainab da matar shi su ka fasalta ma sa shi, ya ce a kawo shi Giwa barracks da ke Maiduguri. Dan haka wajan goman dare sojojin da aka tura su ka nufi gidan Malam. Bakin gate su ka tadda shi tsaye da alama jira ya ke a zo a bude masa kofa, kamar yanda Zainab ta fasalta yanayin shigar shi, sanye ya ke da riga yar shara, wando wanda shi wanda shi ba gajere ba, shi kuma be kai masa har kasa ba ke kara nuna daudar da kafarsa ta yi, dan kuwa yayi futu futu da shi tsabagen tafiyar kasa da ya sha kafin ya isa gidan Malam. Haka kuma kan sa dauke da rawani da ya zaga har fuska. Yanda su ka delle shi da hasken mota ya sanya shi saurin kai hannun ga fuskar shi ya na mai kare idanun sa. Su uku ne cikin motar dukan su sanye cikin shiga irin ta sojoji. Biyu da cikin su ne su ka diro daga cikin mota, su ka nufo shi gadan gadan hannayen su dauke da bindiga, dan kuwa yanayin shigar sa, tsayin sa da komai na sa ya tabbatar mu su da shi din ne wanda su ka zo tafiya da. Sai da su ka karasawa dab da shi sannan ya ankara da yayayin shigar su, hakan nan gaban sa yayi mummunar faduwa musammam ganin bindiga tsirarara a hannun su, ya zabura zai gudu daya daga cikin sojojin ya sa kafa ya tade shi, sai gashi tim ya fadi kasa wanwar "Gidan uban wa za ka je!" Cewar Soja yayayinda ya dago shi, ya na mai tisa kyeyar sa ta hanyar hanakada shi da bakin bindiga, be gushe ba ya kara "Dan uban ka ko tarin ka na ji sai na ci uban ka wallahi! Dan haka salin a lin ka wuce mu tafi!" Be yi mu su musuba, haka su ka tasa shi gaba su ka sanya shi bayan mota, shigar shi ke da wuya su ka hade hannun sa biyu a baya su ka daure, sannan su ka fidda bakin kyella su ka rufe masa idanu kai ka ce sun dauko dan fashi da makami. Motar su ka tada, hakan yayi daidai da lokacin da Isa ya bude gidan Malam dan kuwa ya ji sanda ake bugawa bawali ya ke, kuma shi kadai ne kusa shi ya sa be bude da wuri ba. Ganin tashin motar sai yayi tunanin ko na ciki ne ke bugawa su ka gaji su ka tafi, dan haka yayi kokarin tsayar da su, Amma ganin yanda su ka figi motar ya sanya shi fadin "Toh ko lahira za ku ai sai haka! A sauka lafiya!" Ya mayar da kofa ya rufe. Suna isa Bokabo barracks aka shedawa General isowar su. Yanda Anty Sauda ta matsa a kawo Usman ya sa General ba da umarnin a kawo shi Giwa barracks a daren. Cikin wani motar sojoji aka saka shi, wajan shabiyun dare su dauki hanyar Maiduguri. Tsabagen gudun da su ka yi, karfe uku a Giwa barracks ta mu su, har aka shiga barikin be san in da ya ke ba, illa bayan da aka sauko da shi, sun dan yi tafiyar kasa mai tsayi, sannan su ka tsaya, ya ji kamar ana bude kofa, ya na ji su ka caje shi tas, su ka cire duk wani abu da ke jikin sa, ciki har da takardar da yar tawadar sa da ya ke rubutu duk sanda bukatar haka ya taso, daga bisani aka hankada shi cikin wani waje da shi kan sa be san yanda wajen ya ke ba, ya ji an mayar da kofa an rufe. Sai a sannan wani sabon tsoro ya rufe shi, ya fashe da kuka cikin ran sa ya na mai ambaton ubangiji da ya kare shi daga sharri wannan mutanan da su ka dauko shi ba gaira babu dalili. Jiki da jini be jima ba baccin azaba ya dauke shi nan zaune. Tun sassafe labarin dauko Usman ya sami Zainab, ba karamin nishadi da annashuwa ta tashi da shi ba, musammam idan ta tuna umarnin da ta bayar na a tabbatar Usman ya ji a jikin sa sannan a gaggauta tilas ta masa sakin ta, dan kowa ko zuwa in da ya ke ba za ta yi ba, ita dai kawai a karbo mata takardar saki. Babu wanda ya san wainar da ta ke tauyawa daga Anty Sauda sai Anty Hannah dan haka hankalin ta kwance ya ke. Saukar ruwan sanyin da ya ji ya sanya shi tashi a gigice, be gama warewa ba ya ji saukar mari bisa kuncin sa, wanda hankan ya sa shi komawa ya zauna ya na mai ware idanu. Wanda ya watsa masa ruwan ya fara bi da kallo, Soja ne, daga gani sojan ma karamin wanda ake kira kurtu, sanye cikin kaki, ya tsare shi da jajayen idanun shi. "Dan uban ka an ce ma ka nan gidan bacci ne?" A tsorace ya shiga girgiza masa kai alamar "ah ah" "Ba ka da baki ne? Open your mouth and talk to me friend!" Maimakon ya bashi amsa, sai ya cigaba da girgiza masa kai, hakan ne ya kara tunzura kurtun, ledar abinci da ke aje bayan sa ya janyo, ya bude kosai ne da biuredi, da ke rabon sa da abinci tun jiya da rana tuni zuciyar shi ta kwadaitu da kosai da buredin. Ganin yanda ya ke kallan abincin ya sanya kurtun murmushin mugunta, ya ce "Duk sanda ka budi baki ka yi magana a ba ka abinci! Giwa barracks ka ke dan uban ka, ma'ajiyar tsinannu irin ka! Wai dan ka mushe mu yar da kai ba wani abu ba ne!" Ya na gama fadin haka ya ja bakin kyallen zai rufe masa fuska. Kai ya ke girgiza masa, kokarin rokan sa ya bar shi yayi sallar asuba ya ke amma babu dama dan kuwa yana ji ya na gani ya kara sanya bakin kyallen ya rufe masa fuska sannan ya ja kofar ya rufe ba tare da ya ba shi abinci ba. Da yammacin ranar Zainab ta ci ado kai ka ce gidan biki za ta je jin Kori da Falmat na tsokanan Halitta akan za ta yi bako. Sanye ta ke cikin material baki mai duwatsu ruwan zuman, dinkin goguwar riga ne da ya amshi jikin ta sosai. Karamin mayafi ta saka dan ta burge Sudais ganin shi din ma da alama wayayye ne, haka kuma ta shafa tsadaddun turaren ta masu tafiya da hankalin jama'a. Ta na zaune falo Madu ya shigo shedawa Halitta isowar Sudais, in da ya ce ta same shi falon da Malam ke saukar baki kafin Allah ya masa cikawa. Jin haka Zainab ta faki idon Halitta ta fice, sai ga ta falon baki ta tadda Sudais zaune ya na jiran Halitta. Fuskar ta kunshe da fara'a ta masa sallama, ganin ita ce maimakon Halitta da ya ke tsammani be sa ya fasa mata fara'a ba, tare da amsa sallamar ta. Cike da kissa ta ce "Ka ba ni izini na shigo? I'm welcome?" Zuciyar shi daya ya murmusa, murmushin da ke kashe Zainab dan kuwa sai da bugun zuciyar ta ya karu. Jin ya furta "Why not? You're welcome babbar Yaya" Zainab ta dan tsuke fuska, 'wato har wani yaya ka ke ce min ko? Wai kai mijin kanwa ta! Ka yi ka gama ni ce matar ka! Da ni ka dace' Abin da ta ke fada cikin ran ta kenan yayinda da ta karasa shiga falon, tana taku dai dai, ta sami kujera dab da shi ta zauna, wanda hakan ya sanya shi daga Ido ya kalle ta, ita kuwa ta sakar masa murmushin da ta san ba karamin jan hankali da rikita maza ta ke da shi ba. Sai a sannan ya lura da irin adon da ta yi, sai dai kuma sama Sudais ba abocin son ado irin na Zainab ba ne, sam ba ta burge shi ba. Ga mamakin ta sai gani ta yi ya dauke kai, yayinda ya kunna wayar hannun sa ya shiga dube dube. Cikin kulewa ta ce "Ina wuni?" "Lafiya lau Alhamdulillah" Ya amsa ba tare da ta daga Ido ya kalle ta ba. Zainab na mai cije lebe, ta kara da "Ya ku ka je gida rannan?" "Lafiya lau" Ya ba ta amsa a taikaice, har lokacin hankalin sa kan wayar sa ta ke. Ran Zainab ya fara baci, ta saba maza ke bin ta kamar jela, Amma ga wannan ita da kan ta ta zo wajan shi, ya share ta kamar ma be san da zaman ta a wajen ba. Jikin ta be yi sanyi ba sai da ta ga yanda fuskar Sudais ta sauya cikin kankanin lokaci yayinda ya ji sallamar Halitta, da kuma yanda ya bi ta da kallo tamkar zai cinye ta. Ta ga dai hijabi ne jikin Halitta, har kasa ma kuwa, haka kuma fuskar ta sam ba kwalliya kai ka ce ita ce ma mai takaba ba su Ammy ba, Amma hakan be sa Sudais fasa kallan ta da tarerayan ta ba har ta zauna kujera can nesa da shi. Yanda ya ke kokarin yiwa Halitta hira bayan sun gaisa, ya tambaye ta ko ta na cin abinci da kyau kuwa, tare da rokonta da ta rage damuwa cike da kulawa ne ya sanya Zainab ta shi ta fita ba tare da ta yi masa sallama ba. Dakin ta ta koma dan bacin rai ji take kamar za ta yi hauka. Gaba daya fushin ta ya fi karkata kan Usman, gani ta ke duk auran sa ne ya ja mata, dan ba dan Malam ya daura mata aure da Usman ba, da Sudais ne mijin ta, babu yanda za a yi ya kalli Halitta, har ma ya kulata bayan ga mace kamar ta gaban shi, idan har ta na son jan hankalin Sudais dole sai Usman ya sauwake mata auren masifar da aka daura mata. Ta na kuka ta kira Anty Sauda, fadi ta ke "Anty Sauda na gaji da nauyin auren almajirin nan kai na! Dan Allah ku karba min takarda ta ko na huta!" Jiki sanyaye Anty Sauda ke rarrashin ta, cewar ta "Ki yi hakuri Yakura, tun da ya shigo hannu zai sake ki ne ai, ba dan taurin kai irin na shi ba ai da tuni an wuce wajan, kin san kuwa yanzu na ke shirin kiran ki, yaran General sun ce mutumin nan tun da aka kawo shi ya ki yayi magana, babu irin horan da ba a masa ba, Amma sam ya ki nunawa ya san abin da ake magana a kai, bare ma ya furta komai, ya zama beben karfi da ya ji, an ya kuwa ba a yi kuskure ba wajan dauko shi?" "Zai ci uban shi kuwa! Wallahi sai ya sake ni! Babu kuskuren da aka yi tsabagen taurin kai ne irin na almajiri!" Cewar Zainab a fusace. Daga dayan bangaran Anty Sauda girgiza kai ta yi ta ce "Ah ah dai Yakura, gwara dai mu je mu gan shi da idanun mu, dan kuwa hotan da General ya nuna min na ga kamar ya dan canza akan ran da na gan shi a fili, ke kuma ba wayar arziki ba bare na ce zan turo mi ki ki gani, ko Halitta zan turowa....." "Halitta fa!" Zainab ta katse ta da saura, ba ta gushe ba ta kara da "Ai Anty Sauda Halitta ba za ta rufa min asiri ba, na dade da ganewa ba ta kauna ta, gwara dai mu je din kawai, da ban yi niyar kara ganin wannan kazamin mutumin ba wallahi, amma ya zan yi!" "Da dai ya fi din, gwara dai mu je. Ni ina ganin Halitta mai hankali me ya faru haka?" Zainab na mai girgiza kai ta ce "Kishi, envy, bakin ciki! tun da take kishi ta ke dani, na fita komai shi ya sa" "Kai amma ko kuna ciki daya? ba ta kyauta ba, toh sai ki shirya zan zo na dauke ki karfe goma. Zan kira Hajja Aleesha na sheda mata za ki raka ni" Cewar Anty Sauda cikin ran ta tana mai Allah wadar da halin Halitta. Da haka su ka yi sallama. Zainab ba ta kara bari sun hadu da Halitta ba tsabagen kishi da bakin cikin yanda Sudais ya mata. Washagari da safe wajen goma Anty Sauda da Direban ta su ka zo daukan Zainab, duk yanda Falmat ta so bin su, kiri kiri Anty Sauda ta hana. Haka su ka tafi, Zainab da Anty Sauda zaune a gidan baya, direba da sojan da ke kula da Anty Sauda zaune gidan gaba, ba su zame koina ba sai Giwa barracks. Ganin wacce ke tafe ba su sami damuwa wajan shiga barikin ba, kai tsaye aka wuce da su in da Usman ke kulle. Ana bude kofar wani warin datti ne ya buge su har sai da Zainab ta ja baya ta na mai rufe hanci da gefen mayafin ta, haka ma Anty Sauda wacce ta furta "Huum! Hammatar mijin Yakura ke wari haka?" "Ayya mana Anty Sauda!" Cewar Zainab yayinda ta danna kanta cikin dan karamin dakin, ita dai burin ta Usman ya sake ta su bar wajan. Gaban ta ne yayi mummunar faduwar ganin wanda ke kwance hajaran majaran sai nishi ya ke da alama ya sha duka, idan aka dauke shekaru, tsayin sa, fadin sa, yanayin tufar sa da fuskar yayi kama da Usman sak, dan duk wanda aka fasaltawa Usman ya ga wannan zai ce Usman din ne, Amma ban da Zainab wacce ta san Usman sosai kamar yunwar cikin ta. Ta na mai duban shi ta ce "Na shiga uku! Wannan ba Usman ba ne Anty Sauda! Wannan ba Usman ba ne! Wallahi ba shi ba ne!" "Toh matsala! Ai nima na yi tunanin haka wallahi, kila tsabagen kama ne, bari na kira General din na sheda masa" Cewar Anty Sauda cikin damuwa. Nan da nan ta kira General ta sheda masa halin da ake ciki. Waje su ka fito Zainab sai safa da marwa ta ke dan ta kasa nutsuwa. Suna cikin wannan yanayin ne wasu sojoji su ka zo su ka shige in da bawan Allah nan ya ke kwance, bayan wani yan mintini daya daga cikim sojojin ya fito dauke da takarda ya mikawa Anty Sauda, ka na ya ce "We are very sorry Madam, an sami matsalar ne daga wanda su ka dauko shi, kamar yanda mu ka yiwa General bayani wannan ko magana be yi ba, sai yanzu da ku ka tabbatar mana ba shi ne wanda ake bukata ba, sannan mu ka gane da gaske ba ya maganar ba wai pretence ba ne, sanda mu ka caje shi mun ga takarda da tawada, hakan ke nuna mana hanyar maganar shi kenan, Ashe tun da alamar mu bashi ta kardar ya ke mana mu kuma ba mu gane na sai yanzu, gashi yayi rubutu jiki amma kuma rubutun da larabci yayi ban sani ba ko za ku iya karantawa" Ya karasa maganar ya na mai mikawa Anty Sauda takardar. Zainab ce ta yi saurin karba ganin abin da ke rubuce jiki ji ta yi kamar ta kurma ihu yayinda ta mikawa Anty Sauda takardar. "Muhamad Bello daga rugar Shehu, Dan Allah kar ku kashe ni, na zo kiran dan uwana ne jikin Iyar mu yayi tsanani, ku taimaka ku sake ni ban san me ku ke magana akai ba..." Anty Sauda ta karanta a fili. Ta kara da "Yakura wanene Muhammad Bello kuma? Ina ne Rugar Shehu" "Ni ina zan san wanene shi! Na dai san Rugar Shehu sunan rugar su Usman ne, ya ma za su aikata wannan kuskuren dan Allah!!!" *Khadija Sidi*Auren Shehu 18   Anty Sauda na Mai duban Zainab ta ce "Yakura ni fa ganin yanda wannan ke kwance rai a hannun Allah gwara a sake shi kafin ya mace mu su a nan" Cikin nuna rashin tausayin Muhamad Bello Zainab ta zunbura baki tare da fadin " A sake shi? Idan aka sake shi sai a je a dauko shi almajirin ko Anty Sauda? Wallahi ni auren nan gaba ɗaya na tsana har rai na!" "Ah ah ba sai an dauko shi ba, wannan horon da aka yiwa dan uwan sa ma ya isa ya sake ki muddin ya na da hankali" Cewar Anty Sauda, ba ta gushe ba ta kara da "Su dauke shi yanda ya ke su kai mayar da shi Kano..." "Anty Sauda......" Zainab ta katse ta cike da damuwa. Murmusawa Anty Sauda ta yi, ba ta gushe ba ta kara da "In dai almajirin nan ne wallahi sai ya sake ki, yanzu dai a mayar da wannan kada ashahadun mutuwar shi ya rataya kan mu!" Haka ba a son ran Zainab ba ta na ji ta na gani kafin su tafi, Anty Sauda ta ba da umarni a mayar da Bello Kano gidan Malam in da aka dauko shi. A ranar aka wuce da Bello Kano, hajaran majaran, gaban gidan Malam su ka ajiye shi a wulakance, su ka juya su ka yi tafiyar su. Hayaniyar mutane ne ya sanya su Jauro bude kofa, ganin mutane sun yi cincirindon ya sa Jauro kutsawa cikin su domin ganewa idunun sa abin da ke faruwa, masu salati na yi, ma su Allah wadar da kasar nan na yi. Kallo daya Jauro ya masa ya san ko shakka babu wannan bafulatani na da dangantaka Usman, dan haka da sauri ya koma ya yi kiran Usman, wanda jin abinda kr faruwa ya sanya shi fitowa kafa ko takalmi babu. "Innalillahi wainnailaihi rajiun! Bello? Bello!!!" Cewar Usman yayinda idanun sa su ka sauka kan Bello. Tuni idanun sa su ka kada su ka yi jajur tamkar garwashi, cikin kankanin lokaci gaba daya ya sauya kamanni. Tsugunnawa yayi gaban sa tare da daura hannu bisa kirjin Bello, jin ya na bugawa be tsaya bata lokaci ba ya dauke shi cak ya daura a bisa kafada, Haka kafa babu takalmi, Isa biye da shi su ka dauki hanyar da zai sada su da titi, Allah ya so kafin su karasa sai ga dan sahu, Isa ne ya tsayar mu su da shi, su ka shige, Usman na mai umartar dan sahu ya kai su asibiti mafi kusa. Sun je asibitoci ya kai biyar, Amma duka sun ki karbar su, cewar su halin da Bello ya ke ciki ya kamata su zo da police report. Da kyar su ka samu aka karbe su wani karamin private hospital da ke cikin Tarauni, me suna Iklima Clinic, su ma din sai da Isa ya koma ya hado gaba daya abin da ya mallaka na kudi tare da wanda Usman ke da shi, su ka ba su sannan su ka yarda aka ba su gado, likita ya shiga duba Muhamadu Bello. Bayan wasu mintina Likita ya fito, Nan ya ke yiwa su Usman bayanin yanayi yunwa da kishin ruwa da Bello ya ke ciki, bayan haka ga dukkan alamu an bashi kashi sosai, jikin sa zane ya ke da alamun shatin belt. Allah ya sa be sami karaya ba ko daya ba. "Yanzu likita ya za a yi? Dan Allah ka taimaka ka ceto ran dan uwana" Cewar Usman, cikin ran sa ya na mai cin alwashin ramuwar gayya ga duk wanda ya aikatawa Bello tsananin azaba haka, ko da kuwa wanene. "Ka da ka damu, in Sha Allah za mu yi iyakar kokarin mu" Cewar likita, wanda tun shigowar Usman Allah ya dora masa tausayin sa, musammam ganin yanda hankalin Usman ya tashi akan abin da ya sami Bello. In da Usman ke zirga zirgan nemawa Bello lafiya, Zainab kuma a na ta bangaran tunanin yanda za ta kawo karshen auren ta da Usman ta ke, dan kuwa yanda ta ga ana maganar auren Halitta Sudais ba karamin daga mata hankali ya ke ba. Gashi duk wani dabarar da za ta ja hankalin Sudais ta yi, Amma ina kamar ta shuka dusa dan kuwa dai haƙonta ya kasa cimma ruwa. Bayan sati ɗaya da sakin Muhammad Bello Anty Sauda ta zo gidan Malam. Ta yi rashin sa'a Ammy ba ta nan, Halitta da Falmat sun raka ta asibiti a gwada jinin ta, dan ta na yawan fama da ciwon kai. Zainab ce ta saka Anty Sauda gaba a kan auren ta da Usman. Cike da Mamaki Anty Sauda ta ce "Wai ke wannan saurin ina zai kai ki ne? Na ga ke kan ki makaranta za ki koma, ki fita harkar almajirin nan, ki hada na ki ya na ki ki koma makaranta, duk ran da ya gaji zai sake ki, Ni na san bayan abin da ya faru da dan uwan sa zai sake ki Yakura, dolen sa ma" Zainab na kallan Anty Sauda ta kada baki ta ce "Anty Sauda idan kuma na sami mijin aure fa? Shikenan ina ji ina gani sai na bari ya wuce ni?" "Ina ki ka taba jin mijin wata ya wuce ta?ai matar mutum kabarin sa, toh tunda abin haka ne bari Hajja Aleesha ta dawo sai ki fada mana dan gidan wanene, in ya so duk yanda za a yi almajiri ya sake ki sai a yi, wancan din ya fito a hada auren da na Halitta" Cewar Anty Sauda hankali kwance. Kamar daga sama ta ji Zainab ta ce "Ba fa kowa ba ne face Sudais, dama ni Dady ya ce zai daurawa tun farko, kuma dani ya fi dacewa......" "Zancen banza zancen hofi!" Ammy ce ta katse ta a fusace, dawowar su kenan biye da ita Falmat da Halitta ne. Idan aka dauke Halitta babu wanda be tsorata da furucin Zainab ba. Ammy ba ta gushe ba ta kara da "Wannan bakin hali na ki Yakura ba guna ki ka dauka ba, haka kuma ba halin Malam ba ne....!" "Akwai bakin Hali da ya wuce na shalelen ta ki Halitta? Ace ta rasa wanda za ta yiwa hassada da bakin ciki sai yar uwar ta wacce ta sha nono ta sakar mata? Yarinya bakin hali kamar cinnaka ai muna sane da duk wani tuggu da ta ke shiryawa Yakura a gidan nan!" Anty Sauda ce ta ara ta yafa ta na mai watsawa Halitta wacce ta bude baki ta na kallan ta harara. Jin haka Ammy ta sami waje ta zauna, murya kasa kasa ta ce "In akwai wacce ta ke cinnaka kaf gidan nan Yakura ce! Ita da kan ta take kullawa kan ta koma menene! Nan ai ita aka ce za a aurawa Sudais din ta nuna mana iyakar mu ta hanyar haurawa katanga, haka Halitta ta na ji ta na gani Malam ya musayan ta a madadin Yakura, ta masa biyayya, komai na tafiya dai dai sai ta zo mana da yashesahen zance? Wallahi ko ita ce sarkin shedanun duniya ta yi kadan!" Zainab na mai zunburo baki, cikin neman doki ta ke duban Anty Sauda, wacce gaba daya ita ma din jikin ta ne yayi sanyi. Kai ta girgiza ta ce "Ah ah Yakura, kin yi kuskure nan kam, Ni ma ba zan goyi bayan ki a nan ba, Kuma na ji wannan yaron na kaunar yar uwar ki..." "Ita fa ba ta son shi, wannan almajirin da Dady ya daura min ta ke so! Ku tambaye ta mana!" Shiru ne ya biyo baya yayinda Halitta ke duban Zainab cike da mamakin halin ta. "Karya ki ke mata!" Cewar Ammy bayan ta farfado daga rudanin da ta shiga, ba ta gushe ba ta kara da "Karya ki ke ma ta, ke ko ma da gaske ki ke wallahilazim ba za ki auri yaron nan ba, matukar ina raye Halitta za a daura masa, idan kin so ki kashe auren ki, ki zauna ba aure har a bada, kai Yakura haihuwar ki ko haihuwar asara......!" "Kayya!! Kayya!! Na fa ce ki dena yiwa yarinyar nan baki" Anty Sauda ta katse Ammy. Cike da jimami ta ce "Toh ba dole ki sami hawan jini ba yanda ki ke daga hankalin ki aka abu kankani haka, kin fa san yarinta ke damun Yakura, Yakura yarinya ce har yanzu ba ta san ciwan kan ta ba. Kuma yaran nan fa duka na ki ne, ina laifi idan kin nusar da ita kin gyara ma ta Aleesha?" " Yakura ba yarinya ba ce tunda har ta san bin maza da busa hayaki! Babu wani nusar da ita da zan yi akan wannan maganar, magana daya ce dal, aure ne dai sai an daura shi tsakanin Sudais da Halitta da yardar Allah, na kuma sake jin kin furta wani abu akan auren nan wanda ya ke kishiyar alkhairi da zaman lafiyar Halitta wallahi sai na tsine mi ki Yakura! Tashi ki ba mu waje shashasha wacce ba ta san ciwan kan ta ba!!" Zainab ta tashi fuuu, saura kiris ta buge Halitta Allah ya sa ta yi maza ta kauce mata daga hanya. Duk yanda Anty Sauda ta so Ammy ta huci zuciyar ta ta duba lamarin ki ta yi, ta ce babu wanda ya isa ya saba alkawarin da Malam ya dauka na auran Halitta da Sudais, aure ne an daura shi an gama da yardar Allah. *** Muhamadu Bello kuwa sai da yayi sati a asibiti sannan ya dawo hayyacin sa. Duk yanda ya so ya bawa Usman amsar tambayoyin da ya ke ta jera masa kasawa yayi domin kuwa rashin lafiyar Iyar su ne kadai gaban sa. "Iya.....Iya na kwance rai a hannun Allah, ita ta ce na yi maza na kira ka, ta ce lalle ka zo" Ganin abin da Bello ya rubuta masa da rubutun ajami jikin takarda ya sanya Usman gigicewa. "Me ya sami Iya? Tun yaushe ta aiko ka? Su waye su ka aikata ma ka wannan abun?" Usman ya jera masa tambayoyi ya na duban Bello da ke zaune bisa gadon asibiti. Takardar ya dauka ya kara rubuta "Kwana na nawa a kwance a nan?" "Sati guda...." "Innalillahi wainnailaihi rajiun! Mun bata lokaci da yawa Allah ya sa Iya na raye." "Ta na raye! Babu abin da zai sami Iya ta!" Cewar Usman a fusace bayan ya karanta amsar da Bello ya bashi. Idanun sa ne su ka fiffito gani Bello ya rubuta "Dama ka yi aure ne? Mutanen da su ka kama ni suna ta duka na wai sai na saki matar da aka daura min, sai da wasu su ka zo, ina jin su duk da ba na iya ko da kwakkwarar motsi ne, na ji sun ce ba ni ba ne, a nan na gane kai su ke nema....." Cikin zafin nama ya fizgi takardar, ya na mai kara dubawa da kyau yayinda idanun sa su ka yi jajur tsabagen bacin rai. A fusace ya mayar masa da takardar tare da fadin "Ka fada min komai da komai! Me ya faru? Yaya mutanen su ke? A ina su ke?" Ji yake ina ma Bello na da baki ya fada masa dan kuwa rubutun na Bello ya masa rashin sauri da yawa a yau. A haka Bello ya zayyana masa komai. Ran Usman yayi baki sosai, zuciyar shi ba karamin ɓaci ta yi ba akan abin da Zainab ta sa aka aikatawa dan uwan sa. Lalle za ta ji a jikin ta, sai ta gwammaci ba ta zo duniya ba.... tunanin da yake a ran sa kenan kafin Bello ya sake rubuta masa wata tambayar "Wacece ita?" "Sannin wacece ita be da muhummanci Bello! Ka huta idan ka sami sauki sosai zuwa gobe in Sha Allahu za mu tafi Rugar Shehu wajen Iya" Ya na gama fadin haka ya fice. Shi kan shi Muhamadu Bello ya tsorata da ganin yanayin Usman, rokan shi Allah ya kiyaye kar ya aikata wani abun da za su zo su yi dana sani a gaba. ***** Kamar yanda Usman ya fada, washaegari da sassafe aka sallami Bello. Bayan ya biya sauran kudin da ake bin su, ya dauki yan kayan sa tare da yiwa su Jauro sallama, ya sa Bello gaba su ka nufi Rugar Shehu duk da jikin Bello be yi kwari sosai ba. Da yake Bus su ka shiga, ana ta tsaye tsaye ba su suka shiga rugar Shehu ba sai yamma likis. Tun da su ka nufi Rugar gaban Usman ke faduwa. Kafin su kai ga shiga rugar su ka fara kacibus da matasa da magidan ta wanda yawancin su dawowar su daga kiwo kenan, suna kada shanu gida, sanye su ke cikim kayan saki, wasu daga cikin matasan kitso ne kan su, wasun su kuma hular kaba ce bisa kan su, magidan tan ne ke sanye da hular saki. Ganin Bello tare da wani mai kama da yayan sa ya sa kowa ya bar hidimar gaban sa, su ka tasan ma su. Ko da su ka karaso dab da su, su ka duba da kyau su ka ga Usman din ne ko shakka babu tuni matasa su ka dau sowa su na mai jefa gora sama suna cafewa suna mai zagaye Usman, cikin harshen fulatanci su ke fadin "Maraba da magajin Rugar Shehu na kwarai! Ashe Rugar Shehu na da raban arziki har gobe!" Magidantan kuwa duk da sun yi maraba ba da ganin Usman, ba su fasa tambayar "Kai kuwa Shehu Magaji ina ka je ka juyawa tsatsun ka baya haka? Ashe rai kan ga rai?" Shauki da jimami ya sa Usman kasa fadin komai, hawayen farin ciki ne ke fita daga idanun sa, Allah Allah ya ke su karasa cikin Rugar ya ga Iyar sa. "Iya ta? Mu karasa ciki na ga Iya ta sai na mu ku bayanin komai!" Tuni matasa su ka tsaya da sowa, yayinda kowa ya sha jinin jikin sa. "Iyar ka? Ashe ka na da Iya? Ka damu da ita? Ya ka zo mu je na kai ka gun iyar ta ka ta na nan kwance ta na jiran ka!" Cewar wani magidanci ya ke kani wajan mahaifiyar Usman. Ya na magana ne da harshen fulatanci "Kawu Iliya...." "Shiiiiiii! Kar ka damu, biyo ni kawai!" Cewar Kawu Iliya yayinda ya fizgi hannun Usman, Bello na biye da su, sauran jama'a babu wanda ya biyo su. Usman be tsorata ba sosai sai da ya ga sun gifta Rugar Shehu ba su shiga ba, Kawu Iliya ya wuce da su can jeji in da ake rufe matattu. Gaban wani saban kabari ya tsaya, idanun sa na fidda kwalla ya ce "Ga iyar ka nan kwance! Yau kwana bakwai kenan da ƙasa ya rufe ta, ta mutu da sunan ka bakin ta, ta kira ka Usman, ta kira ka, ba ka zo sanda ta ke bukatar ka ba, yanzu ga ta kwance sai ka mata addua" Ihu da kururuwa Bello ya saka yayinda ya zube kan kabarin Maihaifiyar su ya na mai rungumo kasar. Wani irin tsawa Usman ya daka masa wanda ya sa shi tashi a firgice tare da shiga hayyacin sa. Hakan ya bawa Usman damar tsugunnawa gaban kabarin Iyar su, ya na mai dafawa ya mata addua sannan ya debo kasar kabarin da hannun shi, a hankali ya ke sakin kasar yayinda iska ke kadawa har duka kasar ya bi iska ya rage sai kura hannun sa. "Wallahi! Wallahi!! Wallahi!! Billahil azi! Na rantse da Allah kamar yanda wannan kasar ta baje a iska, haka farin ciki zai baje a rayuwar ki Zainab......wannan shi ne sakayya mafi dacewa da ke!" Cewar Usman ya na mai fitar da kwalla, daya na bin daya. Alhamdulillah.

Post a Comment for "Auren Shehu Book 1 Complete Hausa Novel"