Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

AUREN WUCIN GADI Complete Hausa Novel

[5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI Complete Hausa Novel FREE PAGE Na Zahra Ali Abdullahi Chapter 1 Bismillahir rahmanir rahim. __ƴan matan biyu tafe suke suna hira daka gansu kasan sun fitone daga gidan masu matsakaicin karfi duba da yanda kayan jikin su duka yasha jiki. Fadila ta kalli Aisha tace"kawata nifa gaskiya nagaji da wannan rayuwa tamu kiduba dan Allah kigani an haifimu cikin talauci mun girma cikinta sannan aca wani takalan ya auremu kinga ko ba canji a rayuwar tamu kenan a haka zamu kare rayuwar mu daga mu har yaƴan da zamu haifa nan gaba. Ɗan murmushi wacce aka kira da Aisha tayi tana dafa kawartata tace"fadila a rayuwa duk wanda kika gani cikin kowani irin hali to haka Allah yaso ya gansa ciki,da talaka da mai kuɗi duka matsayin su ɗaya awajen Allah. Bawai dan Allah baya sonmu bane yayimu a matalauta sannan su mawadatan bawai Allah yafi sonsu akanmu bane yawadace su,yabasu ne don ya jarraba imanin su shin zasuyi taimako da wannan dukiya nasu da sadaka ko ko. Misali yanzu aca yau wani hamshakin mai kuɗin dare ɗaya wani iftila'i ya faɗawa dukiyarsa aka wayi gari bashi da komai wallahi idan basa'a yaci ba sai ya kusa haukacewa,idan kobe haukace ba to wallahi halin da ze tsinci kansa ciki sai yafi wanda mu matalautan muke ciki muni. Haka shima talakan wani idan yau cikin dare yasami kuɗi misali millon biyar tsaban farin cikin wani har mutuwa zeyi saboda yasami abunda betaɓa gani ko amafarki ba. Ɗan dukan wasa fadila takai mata tana cewa"wallahi kefa muguwace kawata. "To yanzu in banda abunki fadila tunda duniya ta xauna kin taɓa gani ko jin inda akace talakawa sun fito zanga zanga saboda su basu dashi kuma masu kuɗi sun riƙe abunsu basa basu?"a'a cewa fadila tana girjiza kanta"yo to mai nawani abun damuwa dan mu talakawa ne. Naga ko annabawan Allah akwai talakawa,kede fadila ki godewa Allah dan duk halin da ake ciki na babu ba taɓa fashin ɗaura tukunya a gidan ku ba,amma mufa wallahi wataran sai ayi kwana biyu ba ɗaura tukunya a gidan namu ba. Cike da tausawa fadila take kallon Aisha dan duk halin da suke ciki na babu da take rainawa su Aisha sun fisu rashi amma koda wasa baxaka taɓa jin Aisha na ƙorafi ba. "Nikan kawata ya kukai da wannan masu ɗin kinnan?dan Aisha ta ƙore a dinki amma matsalar bata da keken dinki kuma bata da hanyan samu. Nisawa Aisha tayi tace"wallahi kawata sau ɗaya naje na yini ina ɗinki tun karfe takwas ɗin safe naje bani nabaro shagon ba sai karfe shidan yamma amma wannan mutumin saboda rashin imani ya ɗauki ɗari biyar kawai yabani ko kuɗin abinci babu,wallahi sai da na haɗa masa riguna set baƙwai a hakan ma banda dogayen riga dana ɗinkawa wasu ɗinki express ina gani aka bashi dubu goma a riga uku. "Kan bala fadila tace a masifance yanzu dama haka hafiz yayi miki rashin mutunci shine yake wani tambayata ya bakije ba,tab amma meyasa ke baki faɗamun haka yayi miki ba. Dan ko ɗari ze baki akan kowace riga dakika haɗa yafi karfin yabaki ɗari biyar tunda ba koyo kike ba,sai kumfar baki fadila take kaman taga hafiz ɗin riƙo hannun Aisha tayi tace zo muje muji dalilin da yasa yaƙi baki hakkin ki. "Haba fadila mai kuma zamuje muyi ai wannan zubar da ƙimane sannan ze zamana mun buɗe ƙofa dan a wulakanta mu yanzu da bansake zuwan ba bashi kenan ba,shima kansa yasan abunda yayi be kyauta ba kinga bashi da zarran aikowa yace naje. Hakade sukai ta hiran suna tafiya har sukazo inda zasu rabu kowacce takama hanyan gidan su.   Alhaji badamasi dake zaune saman ɗaya daga cikin kugerun da sukaima falon ƙawanya ya kalli ɗansa Ahmad dake duƙe gaban sa cike da ɓacin rai yake magana"yanzu Ahmad saboda ban isa dakai ba,shine har ni zan yanke hukunci akanka amma kake neman zubamun ƙasa a ido? "Ba haka bane ba,ai naje rannan,katseshi Alhaji yayi da cewa"to yanzu ma nace kaje haka gobe har sai kun fahunci juna da ita yarinya ƴar babba gida ga ilimi ga wayewa. "Nide daddy gaskiya daso samune da anbar wannan magana dan ni kwata kwata wannan yarinyar batayi zubin irin mace da nake ra'ayin ba,wallahi. "Shut up my friend yadaka masa ina magana kana magana sau nawa nabaka daman kafito da wacce kake so kakasa saboda haka wannan itace wacce tadace da rayuwar ka itace kuma zaɓin da nama dan haka kaje ku daidai ko kaje ko karkaje wannan ruwan kane yarage naka nagama magana itace matarka baka da wata mata bayan ita,umurni nake baka bawai shawaranka nake nema ba.. Ɗagowa yayi ya kalli hajiya mardiyya mahaifiyar Ahmad din da tunda suke magana bata samusu baki ba. Yace"wallahi matukar yaron nan yaƙi zuwa su daidai ta da yarinyar nan to yanemi wani uban ba niba.....   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Na zahra Ali Abdullahi Bismillahir rahmanir rahim Chapter 2 __fuuu Alhaji badamasi yabar musu falon cike da ɓacin rai,sauke numfashi sukai kusan a tare shafa kansa hajia mardiya tasoyi shiko yayi luf ya ɗaura kansa saman cinyarta kaman wani karamin yaro,shagwaɓe fuska yayi yace. "Mama wai meyasa Alhajin nan naki bayason farin cikina ne sam?"kul kakuma cewa haka Ahmad yaza'ayi mutum ya haifi ɗan sa amma yace bayason farin cikin sa. Kawai de ina ganin yanason zumunci tsakanin sa da abokin nasa ya ɗaure ne wajen kulla auratayya tsakanin ku"hmmm yace kawai yana sake nitsuwa jikin mamar tashi dan yasan ita kanta hakuri kawai take da halin mijin nata kasancewar ta mace mai hakuri amma ba dan tanajin daɗin zama dashi bane ba. Aisha ina shiga cikin gidan mu naci karo da kayan wanki dila guda wai na wankau cike da taƙaicin wacce takawo wankin nayi sallama ciki ciki amsamun anna tayi ƴan ƙannena suka tahu da gudu suka rungumeni suna mun oyoyo. Shafa kansu nashigayi nace"ya bakuyi shirin zuwa islamiyar ba?kallo na sukai kaman zasuyi kuka murmushi nasakar musu dan nasan matsalan nasu yunwa sukeji kuma sunyi ƙokarima dan tun kunun kokon hansin damuka tattaɓa da safe ba abunda sukaci ko kuma ince ba abunda mukaci. Anna ce ta katseni da cewa"Aisha matso mana kon tsaya da bakin ƙofa matsowa nayi ina kallon tulin kayan wanki dake ajiye gabanta nace"waƴan nan kayan fa?nunomun matashiyar yarinya dake tsaye tayi tace"hajia mariya ce ta aiko da kayanta takuma ce tana bukata gobe. Juyowa nayi na kalli yarinyar dake tsaye sai yatsine take ita ala dole ƙyanƙyami mai da kallona nayi ina bin madaidaicin gidan namu da kallo nide banga wani abun ƙazanta ba,dan gidan namu a share yake tass na maida dubana gareta nace"ƴan mata ɗauki kayan kimai dasu inda suka fito ki faɗa mata mai wanki tadena dan bazamu rinƙa ɓata lokacin mu da karfin ga waƴanda basusan darajan mutane ba. Ina kaiwa nan najuya na shiga ɗan madaidaicin kitchen ɗinmu dan jiƙa mana garin kwaki da nasayo mana a shagon mati,bansan yanda sukai ba kwai nafito na tadda hajia mariya tana zazzaga masifa wa anna ta cikin waya,wai har cewa take ita ba faƙiriya bace wallahi tafi karfin mumata wulakanci. Murmushi nayi mai faɗi nace"hajia duk faƙirancinmu ai bamuje gidanki maula ba,ki adana fushinki zai miki amfani wani lokaci ba bayinkin bane mu balle mumiki aiki bazaki biyamu hakkinmu ba. Sannan kitsaya kina wasu maganganu ai ko a addinance amfiso mutum idan yamaka aiki tunkafin gumin sa yabushe kaɗauki hakkinsa kabasa. "Nikike faɗama magana Aisha dama ashe fitsararriyace ke bansani ina taimakonku nayi danake aiko muku da wankin ai biya nake ba kyauta kuke mun ba. "Idan wannan shine biya riƙe abunki bama buƙata mu da Allah muka dogara ba dawani ba"au dan banzan dubunku biyar dake hannuna kike neman rainani kinsan koni wacece?cike da ƙosawa da yawan maganan ga yunwa na damuna har wani dishi dishi nake kallon kunsan idan mutum yajin ƴar gusau a wuya yake dan haka kana taɓashi kaɗan ze soma zazzagama maka masifa to nima hakance ta faru dani dan haka a ƙufule nace da ita"kewaye kewaye?be shafeni ba koma keɗin wacece kawai abunda nasani wankine anna bazata sake miki ba. Sannan kina kiran banzan dubu biyar ai saboda sanin mahimmancin sa yasa kika riƙe mai yasa baki bada kin huta ba,sai wani kurin kike kina kiran kewacece mtsss naja gajren tsaki. Iya hasala hajia mariya ta hasala dan haka cikin ɗaga murya tafara zazzaga masifa kaman ta ari baki ji take kaman ta jawoni ta cikin wayan takifkifamun mari,sai da tayi mai isanta nide bansake anƙata ba. Sai hakuri da Anna ke bata nikan tasa ƴan ƙannena nayi gaba muka soma shan garin kwakinmu hankali kwance,can aka kashe kiran yarinyar da naji hajia mariya takira da Basma ta bude pouse ɗin dake hannun ta taciro ƴan dubu dubu guda biyar ta miƙama Anna tana wani yatsene fuska kaman taga kashi"gatsiyar ku nan daidai zata juya tace da Anna. Saurin amsa nayi nace" godiya muke ɗiyar ƙaruna umma tagaida ashsha,juyawa tayi tasoma tafiya harta kusa kaiwa ƙofa sannan hankalina ya kai wajen kayan wankin da tabar mana nace"amm Basma kike kowa?kinbar kayan fa?kobakiji yanda mukayi da hajiyar taki bane ai daga yanzu mundena wanki basai anjima ko gobe ba. "Sai ki biyoni dashi tafaɗa a gadarance,ƴar dariya nayi rin mai ƙulawar nan gawanda a kaima nace"ayyar ƴar gidan ƙaruna saide ba nice nashigo da su ba,dan haka sai ki zo kiɗauki tsiyarki kice da ita matsiyatan da tace sunce bazasu sake aikin wahala ba. "Haba Aisha nifa banason irin wannan hali naki na kafewa akan abu guda da rashin hakuri haba Aisha sai kuma ta sassauta murya tace bana son haka a irin haka na rasa mahaifinku nazo ina rayuwa kaman wacce tayi lefin kissa nake ɓoye kaina daku baki ɗaya duk saboda ku.... Kuka sosai Anna take wanda yasa muma muka tasa namu nakuma yi danasanin biyewa zuciyata danayi dan gani nake kaman nice nasa Anna kuka jiki a sanyaye nace"dan Allah Anna kiyi hakuri idan har amsan wanki shine zai faranta miki rai bara nace su maido,nafaɗa ina ƙoƙarin miƙewa tsaye sauri riƙo hannun tayi tace. "bawai ina kukane saboda abunda kika faɗawa hajiya mariya ba,a'a kawai inayine saboda tunawa da nayi da mahaifinku a rayuwa Aisha kizama mai hakuri dakuma kawar da kai akan komai banason rashin hakuri Aisha abunda hakuri be baki ba rashin sa baxe baki ba,takare magananta tana mai rungumo dukkan mu jikin ta inasonku ƴayana sanyin idanuna"muma munasonki Anna uwa ɗaya tamkar ta dubu a garemu. ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Na Zahra Ali Abdullahi Bismillahir rahmanir rahim. Chapter 3 __"Anna bani kuɗin naje nayo mana cafene muma yau ɗaya muci mai daɗi,yanda nakare maganan da ɗan ihun murna yasa suma ƙannena tayani ihun murnan jin nace zamuci mai daɗi wato khadiza da mubaraq ita de Anna sake baki tayi tana kallon irin taɓarar da nake kaman wata yarinya karama. Muna cikin yin ihu wani yaro yashigo gidan namu da sallama amsa masa mukai kasancewar zaune muke a tsakar gida"wai ana sallama da Aisha zuciyana ne yafara dukan uku²da jin abunda yaron. Cikin rawar baki nace"kai kaje kace banan bane gidan,har yaron ya juya zeyi ficewarsa yasa Anna cewa"kai jekace gata nan zuwa,yaron yafita rau rau nayi da ido kaman zanyi kuka kauda kai Anna tayi daga kallona tace"zama tashi kije kiga ko waye?amma de kinsan ba kyau wulakanta mutum dan ɗan adam darajane dashi"amma Anna aini ba wanda mukai dashi ze...katsane ni tayi da cewa haba Aisha yanzu sai wanda kika kasani ko yasanki shine kawai zai iya turowa amiki sallama yau naga ikon Allah kinga maza tashi kije kigani sai kizo kuwuce islamiya kinga lokacin tafiyanku yayi. Badan naso ba,haka namiki na saka hijabina nariko hannun mubaraq muka doshi kofa,tunkan na karaso ya tsareni da mayun idanun sa yana mai sakin murmushi,haɗa giran sama da ƙasa nayi danma karya kawomun wargi. Ahmad Wanka yayi yafito ɗaure da towel a ƙugunsa yana goge jikinsa da ɗan karami wayansa dake burari yakai hannusan ya ɗauka ganin mai kiran nasa yasashi sakin guntun murmushi yana kai wayan kunnen sa"kaifa ɗan iskane wallahi in kasan bazaka tafi ba ai saika sanar dani dawuri dan bazaka ɓatamun lokaci ba ehem. Suƙe fuska yayi cikin hocky voice ɗinsa yace"to ai sai mutum yakama gabansa idan na son gulma ba ai nima nasan hanya mtsss yakare magana yana jan guntun tsuka"dariya akai daga ɗaya ɓangaren ana cewa"eh son gulmar dama shiya tsaidamu oya kai maxa kafito gamu a falo muna tare da mama"khalid ya ambaci sunan cikin sanyi'na'am yason ranka malam kayi mamakine to karkayi kasan lamarin tuzurun abokina dole nabashi mahimmanci idan ma wankan naka beyi ba sai nasa kacanzo dan karmuje babin daddy taga tsofanka tace bata sonka,dole yayi ɗan dariya dan yasan halin khalid"meyasa baza shigo nan ɗin ba dot?"ina tare da mamata tana bani abinci ya amsa masa agajarce. Shaf shaf yashirya yana fitowa daga ɗakinsa khalid nasa kai tsaye khalid yayi yana karewa ɗakin kallo yanda ya hargitsa komai"mutumina gaskiya kana bukatar aure da wuri kodan kasami mai gyarama daki dan Allah kalli yanda ɗakinka yake ka kuma kalli kanka ta madubi idan kafita wajene kawai kake guy amma gaskiya wannan ɗakinaka um um. "Kai ɗan sa idone khalid ina ruwanka da makwancina in banda rainin wayo,kasan Allah har yanzu har yanzu banga macen da tayi daidai da rayuwata ba,kaga kowannan ɗin zan jenine saboda banaso mama tasami matsala da Alhajinta idan ba haka ba wallahi ba inda zani. Raƙe haɓa khalid yayi yana kare masa kallo danson tabbatar masa kai ya jinjina masa,hmm"kai ko wacce irin mace kakeson ka aure?nagade ƴan mata zuƙa zuƙa kaman su sukai kansu kawo maka tallan kansu sannan ga waƴanda ake kawo makasu daga waje ma bambanta kade tsaya ruwan idon kazaɓo mana wata bagidajiya. Murmushin gefen baki yayi sannan yafara takawa a hankali yace"inason takasance bazata ji shakku ko tsoron wani ba matukar akan gaskiyarta ne,sannan takasance mai hakuri dakuma ɓoye sirrin gidan su wacce abun duniya be tsone mata ido ba,mara ƙiwa wacce ko karfe ɗayan darene idan nace coffe zata tashi ta dafomun kafin natashi daga bacci an haɗamun break fast ɗina sannan ta haɗamun ruwan wanka na. Tafi kawai khalid yasoma yimasa dan yaga yanda abokin nasa yazage yana ta karonta masa halin macen da yake so kaman a littafi"karon farko a rayuwata naji kayi maganan halin mace saide baka faɗamun yanda tsarin ta ze kasance ba,saboda tsaro ba tsoro ba kaga sai na riƙe matukar gana mai irin hali dakuma yanayinda ka zaiyano sai... Duka Ahmad yakai masa yayi saurin gaucewa yana masa dariya.   Wannan littafin mai suna a sama na kuɗine dazaran mun gama free page zamu sanar daku yanda zamu biya kuɗinku #300 kacal zaki biya ƴar uwa dan kikaranta. ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Na Zahra Ali Abdullahi Bismillahir rahmanir rahim.   Chapter 4 A tare suka shigo falo mama na zaune tana kallon labarai a tashar aljazeera yayinda auta marwan ke zaune daga gefe yana duba littafinsa. Murmushi mama ta sakarmusu da kiran"masha Allah fatan nasara"amin khalid ya amsa shiko oga Ahmad sharewa yayi dayin gaba. Assalamu alaikum yafaɗa sanda na iso bakin kofan sanin mahimmancin sallama yasa na amsa da "Wa'alaikum salam. Shirune ya ɗan ɗaukemu ganin bashi ba da abun faɗi yasani katse shirun da cewa malam hafiz ina da abunyi zan iya komawa? "Am am wato malama Aisha am naga baki koma ba shisa nabiyo bayanki nagani de ko lafiya?kallon sa nayi a mamakance araina nace kaji rainin wayyo wato shi abunda yamun be ɗauka abinkin komai ba kenan. Amma a zahiri murmushi nayi nace"in badan abunka ba malam hafiz ai dama ni nakai kaina shagon naka neman alfarma kuma baka koreni ba kamun alfarma harma nasamu nayi aiki da kai kakuma biya ai sai godiya. Saurin katseni yayi da cewa"dan Allah Aisha kiyi hakuri nasan ban kyauta miki ba,a lokacin amma dan Allah kibani wata daman wallahi zan biyaki hakkinki kaman yanda kika buƙata tashin biya kokuma adadin ɗinki da kikayi a rana adadin biyanki duk yanda kikace haka za'ayi ina bukatar ki a shagon mu. "Nagode malam hafiz saide kasani ba abunda ze sake kaini shagon naka kaman yanda kaimun kora da hali to nima yanzu dan biyan bukatan kanka da kanka bani zuwa,dan nasan da biyu kabiyo sawuna ba haka kawai kazo ba, idan waƴanda nama dinki susukace ni suke bukata namusu ɗiki sai kakoma kasan yanda zakayi dasu da mutuncina da darajata banza ƙaskantar dakai gawani bawa yanemi takani ba,Allah kaɗai shine wanda ya cancanci haka kuma yasan dani baze taɓar dani ba. Sautari mutane sukan so wulakanta mutane ƴan uwansu batare dasanin ƙimansu da darajar suba,kuma basusan baiwa da Allah yama bayinsa ba,da zamu zauna mu mutane mu nitsu da wallahi zamu karu da baiwarda Allah yayima wasu daga cikin bayin sa,wulakanci bashi kyau ka wulakanta dan uwanka amma bakasan abunda shi wanda ka wulakanta ze zama nan gababa na barka lafiya nakuma gode da ziyara da haka nayi wuce wata gida nabarshi tsaye kaman wani dogari. "Wai nikan Ahmad bazamu danyi mata shoppin ba haka zamu hannu rabbana?ɗan tsuka yayi yana kauda kansa gefe yace"haka naga daman zuwa ko kana da jaa akaine?murmushi yayi yana cewa"wane ni ni na isa jada ango to be,mtsss tsuka yayi mai faɗi yace"kanka akeji mutum sai shegen surutu wallahi idan bakai ma mutane shiru ba yanzun nan sai mukuma,daga haka shiru yaɗauke su Ahmad na driven shikuma khalid yakai hannun sa gefen set kugera abunda ya taɓone yaja hankalin sa saurin ciro abun yayi abun hannune mata irin ta duwatsu ɗagawa yayi yana karewa abun kallo. Shide a iya sanin sa yasan Ahmad baya hulɗa da mata to mai yakawo wannan abun nan?"wannan abun ɗan wai gowa kaɗan ahmad yayi ganin abun ke hannun khalid yasa shi ɗan cizan lips ɗin kaman yanzu yake ganin ta yafurta sai na koya miki hankali"ita wa?"wata fitsararriyace kullum da ita nake kwana nake tashi amma haryau komai kama da ita bansake gani ba ba ita. Fadila dake kwance gefen wani Alhaji saman makeken gadon yana shafa mata sassan jikinta yace"baby kinsan harkar nan bani gishiri inbaki manda ne kuma kinsan na kwaɗaito da wannan ƙawartaki. "Hmmm Alhajina kenan Ai inde Aisha ce gaskiya jawota wannan harka ba abune mai sauki ba,dan wallahi ko shekara zasuyi basuci abinci ba,banajin zata yarda amma kabar komai a hannuna. Dayake ansan da zuwan su tarɓa ta musamman suka samu daga gimbiya sai wani ƙwarƙwasa take kawai dan ta burge masoyin nata,amma shi ko kallo bata ishe shi ba. A sittin room a kai musu masauki ƴar aikin gidan takawo musu ɗan abun taɓawa ta jera musu,har tamiƙe zata tafi basma ta ƙwaɗa mata tsawa,wanda yasa hanta cikin mai aikin kaɗawa"uban wa zeyi saven ɗinmu koso keki ninayi biyanki aike ba kyauta kike mana aikin ba idan kinga bazaki iya ba ƙofa abude take ire irenki yauwane dasu. jiki na ɓarin matan takoma ta raƙuɓe daga gefe ta tsaya,kallonta Ahmad yayi da kaman bazeyi magana ba sai kuma yace. "Kin tsaida ita mezata miki bara kiji a tsarina ba ƴan aiki kinfi kowa sanin gidan mu tunda kina zuwa dan Allah jibeki yanzu bakiji kunya ba wajen yiwa wanda a haife tama haifeki irin wannan tsawa kawai dan tana aiki aƙarƙashinku idan zaki gyara ki gyara idan baki gyara ba yarage naki daga haka yamike fuuu yafita baki sake tabi bayansa da kallo har taɓacewa ganinta dama tun kafin tazo sai da Mamatar wato hajia mariya taja kunnen ta kan halinta nayiwa ƴan aiki tsawa da sanin waye ahmad.. "Abokina harla fito kenan cewar khalid dake zaune cikin motar dama sanin hali yasa bebishi sun shiga ba,taɓe baki yayi yana maida zaman glass din idon sa yace"to ma mai ze tsaidani bayan ita ɗin bawata halittace ta daban ba,wani irin tuƙuƙin bakin ciki yasake turniƙe basma data biyo shi a baya dan ta bashi hakuri. Masu karatu karku manta wannan littafi na kuɗine kibiya 300 kacal dan samun labarin har kashe.   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Na Zahra Ali Abdullahi Bismillahir rahmanir rahim.   Chapter 5 Ba tare da tanuna ɓacin ranta ko da a fuska ne ba,ta ƙaraso inda suke tsaye cike da duniyanci tana wani shaƙe murya tace"barka da yamma abokin mu. "Yauwa barka de amaryar mu yakike? Ya gida? Yakuma su mama? Fatan kowa lafiya duka tambayan yayi sune a tare"kowa lafiya ta amsa masa da murmushi saman fuskarta. "Am my dan Allah kai hakuri kazo mukoma ciki muyi magana tawani marairaice kaman zatayi kuka yanda tayi dole tabaka tausayi amma gogan ko a kwalarsa sai ma kokarin bude motar da yakeyi sauri dakatar dashi khalid yayi"dot mushiga mu gaisa da hajia mana in kungama da gimbiyar taka kaga ba daɗi muzo kuma bamu gaisa ba. Wata uwar harara ya kamawa khalid shiko khalid dauke kansa yayi kaman bashine yayi maganan ba,kwafa yayi sannan yarufe mufin motar da karfi tabbacin ransa aɓace yake gaba kawai yayi batare da kalli kowan su ba. Zaune suka tadda hajia mariya tana waya da kawarta hajiya bilkisu tana cewa"hajiya balki wai kaman ni ƴar mitsisiyar yarinya dako ƴunwan cikin su be mutu ba take gayan magana ɗan shiru tayi da alaman sauraron wanda suke maganan tare takeyi sai kuma tace so nake kawai kiyi duk yanda zakiyi tazo tafaramun aiki a gidan nan wallahi sai nayi ƙasa ƙasa da ita mara kunyar ƴa sai nasa su Abdul sun yayyagamun wannan bakin nata na rashin kunya wallahi. Sallamarsu Ahmad shiya katsemata magana tashiga washe baki"a'a my son angirma ya mamar taka?lafiya yace kawai fuska ba walwala dan yaji maganarta ta ƙarshe a zuciyarsa cewa kawai yake to wace zata saka Abdul ɗin yayyagawa lalle wannan mata batada imani. Zungurin sa khalid yayi jin hajia na magana amma hankalinsa baya gunta"zamu tafi yace yana mai miƙewa tsaye"harzaku tafi fatan de kunɗan taɓa wani abun"a'a badamuwa idan munsake zuwa ma taɓa sauri muke dan munada mettin da wasu baƙi ne. Yakare magana yana mai kallon agogon dake hannun sa"Allah yatsare ka gaida mun da hajia ko amsata beyi ba yayi waje,bin bayansa hajia mariya tayi tana mai fashewa da dariya tace ɗan iska zaka shigo hannu ne ai idan ka tsallake wannan tarkon akwai wasu tarkunan da naɗana maka masu yawa sai inga ta yanda zaka tsalleke duka. Anna yana yau kaman jikin naki yayi nauyi?nayi maganan fuskata nanuna tsanyar tausawa mahaifiyarta mu gashi bamu da halin kaita asibiti bare kuma takaimu ga iya saya mata magani idan an rubututa Allah de yakawo mana mafita. Ganin kaman nashiga damuwa Anna tace"ke zo ki zauna kusa dani tana mai nunan gefenta ba musu nazo na zauna riƙo hannu na tayi tace kinga kar ganin halinda muke ciki yasa ki zubarda mutuncinki saboda abun duniya. Aduk lokacin da kika tsinci kanki awani halin to kisaka Allah ranki shi zekawo mana mafita sannan a rayuwa kirinƙa kallon na ƙasa dake karki kalli wanda yafiki kiyi duba da yatsun hannunki zakiga ba kansu ɗaya ba, Allah shiyasan hikimar sa nayin hakan,tashi maza ki kawomun ruwan bunun nan naɗan sha sai kuma ki leƙa gidan hajia bilkisu ta'aiko ayi kiranki ɗazu. "Dot gaskiya abunda kayi kwata kwata baka kyauta ba wallahi?"da nayi fa?shima ya maida masa da tambayan hararar sa khalid yayi yana maida hankalin sa ga tuƙin da yake dan shi ya amshi tuƙin yanzu,murmushin gefen baki yayi yana mai cewa"inde akan wancan yarinyar kake fushi kamanta kawai inaga tafiyanmu ahakan zefi dan bata da hankali. Hmm"kai kuma sai kabiye mata haba dot wai sai yaushe zaka fara sakewa da ƴan matane,mata fa duniyace dan Allah ka gwada son wata koda da wasane zaka yarda da abunda nake nace ma"yen yen yen bakada bakada magana sai ta mata mata so so nifa wannan duka abun baya genda na amma da zaran nasami wacce tazo daidai da ra'ayina ko auren wucin gadi nayi da ita"wucin gadi kuma?yayi tambayan yana mai zaro masada idanun sa. "Aisha sai da na waigo naga ashe fadila ce amsawa nayi fuska sake"kwana biyu ƙawata kinyi wuyan gani?tace dani tana ƴar dariya nima dariyar nayi nace"wallahi Anna ce bata ɗanji daɗin jikinta ba shisa kika jini shiru. "Allah yabata lafiya"amin fadila nagode nace data" kai gaskiya talauci beyi ba wallahi a rayuwa yanzu kiduba in banda talauci ai ba abunda zesa mubarta a gida da ciwo,dan wallahi ko mahaucine yaga Anna yasan bata da lafiya dauriya kawai take kai ina. Shisafa nake yawan cemiki natsani talauci duk da acikin ta aka haifemu mukakai har wannan muzalin amma wallahi bazan auri talaka in kare rayuwata a talauci ba,ɗan murmushi nayi ina kallonta dan kullum lamarin fadila kara bani mamaki yake. Dan Allah yanzu ke kanki Aisha a ranki idan kika zauna bakya tsanan talauci ko kiji wani irin ƙunci a ranki idan akawayi gari ba abunda zaku dafa a gidan ku?murmushi mai ɗaci nayi sannan cikin sanyi murya mai cike da rauni nace"zancen gaskiya fadila bana jin haushi ko ƙuncin kasancewar mu a matalauta abu ɗayane idan aka wayi gari nake jin wani iri idan bamu dashi abinci. Murmushi fadila tayi to amma fa bawai hakan zesani jin ƙunci ne araina ba a'a kawai inajin ba daɗine idan naga yunwa ta hanawa ƴan ƙannena walwala da sukuni sannan ga Anna itama ba lafiya bane ya isheta tunani na ako da yaushe ya za'ayi nasamu aiki da zamu dogara dashi fadila duk da Allah yayimu mata muna da karfin zuciya dakuma ta jiki ta yanda zamu iya yin amfani dashi dan ganin mun taimakawa iyayenmu. "Taya Aisha bayan muna mata kinsande bazamu iyayin dako ba,a'a kosokike muje bakin titi muna suyan awara da doya takare maganan tana huci wani lokacin wallahi har mamaki fadila ke bani idan tana irin wannan maganan. "Yi hakuri kawata maida wukar nace da ita"Allah Aisha keɗince wani lokacin da kayan ban haushi ta faɗa tana ƙaremun kallo kaman maison gano wani abu a gareni. "Fadila nakira sunanta sannan nace suyan awara dake cewa itama sana'ace na rufin asiri ni kinganni nan wallahi ko aikatau nasamu zanyi matukar zan samu abunda zamu rufawa kanmu asiri burina a duniya be wuce naga Anna cikin ƙoshin lafiya ba sannan ƴan kannena suyi karatu kaman kowa bani da burin saina ganni cikin wata daula Allah dayayimu a hakan shi yasan hikimarsa Allah de makawo mana mafita kede kawai fadila abunda zance dake kirage buri ki sanyaya zuciyarki hakan da hakan zefi. Mtsss"wallahi duk kin ɓatamun rai harma kinsa na mance abunda nazo miki dashi"share kawata idan kin sauka kika tuna saiki faɗamun,nace da ita kinga tunɗazu muna ta tsaye anan kizo kirakani gidan hajiya bilkisu to tace jerawa mukai da ita gwanin sha'awa muna hira har mukaje gida sallama mukai a baki falon gida. Mai aikinta tafito tana ganin mu tawashe baki dayake tasanni ina zuwa yima hajia wanki tace"a'a Aisha kece yau agidan namu"wallahi nice tani gaisawa mukai sannan tace kushigo itade fadila tatafi duniyar kallon gidan saida na dan zungureta sannan ta sauke numfashi tana cewa"Aisha kalli gida dan Allah kaman baza mutu ba. Daidai muna zama daga kasat carpet hajia bilkisu ta fito daga wani coridor cikin da shiga ta alfarma,fuskarta sake ta ƙaraso ta zauna saman ɗaya daga cikin kugerun falon gaidata mukai ta amsa mana fuska sake tana kallon fadila tace"wannan?"ƙawatace na amsa mata"yayi kyau ya Anna da karfin jiki?"Alhamdulillahi nakuma amsamata. Gyara zama hajia bilkisu tayi sannan tace badan komai na aika akiramun ke ba,dama kawata hajia mariya dam gabana yabada sauti tun kafin tafaɗi abunda take shirin faɗi Aisha ki nitsu dan ganin kaman yanayina yacanza tace dani. Dama mai aikinta tayi tafiya to tana neman wanda zeriƙa mata kafin tadawo shine nace ko zakije tunda ba abunda kikeyi a gida"sai na faɗawa Anna duk abunda tace zan faɗa miki. Na amsa mata dan gaskiya hankalina be kwanta ba da wannan aiki gani nake kaman matar tashirya cimun mutuncine tunda nace bazamu sake yimata wanki ba haka kawai naji zuciyata ta amince mun da hakan. "Haba Aisha mena saikin faɗawa Anna kinde san bazata hana ba"duk da haka tanada hakkin sani ko hanani na amsa ina miƙewa nafita gani haka itama fadila mikewa tarufamun baya daidai bakin get naji na mangari mutum baya nayi zan faɗi yayi saurin riƙoni"yi a hankali bakiji ciwo bako?ware manyan idanuna dasuke a lumshe nayi saman fuskarsa cikin rawar murya data jiki nace kaine ina nunashi da ɗan yatsa. Saurin sakemun hannuna yayi yaga goge hannun sa da handkerchief ya ɗago da daidai zeyi....   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Chapter 7 Nakai kusan minti talatin ina cikin wannan yanayi natsoro dan ni kaina nakasa tantance shin ganin mutumin nan shi yasani tsoro ko ya?wata zuciyar tace shiɗinne bakiga yanda ya gargadeki da ido ba wannan ko kinyi abun azo a gani balalle ya ɗaukeki aikin ba,kawai ki tattara tsumman rayuwarki ki arce ba tare da kowa yasani ba. Wannan shawara da zuciyata tabani yashigeni dan haka buɗe idanuna nayi dana lumshesu tuntuni nafara wulga ido naga kowa tsabgar gabansa yake wasuma sungama yanka har sun zo sun fara ɗinki kaman daga sama tsinkawo wata murya cikin kamala anmun sallama daga gefe na. Amsa masa nayi fuska ba walwala yace"ƙanwata idan bazaki damu ba zan iya cewa wani abun?lumshe idona nayi sannan nasake bude su murmushi yayi mai sauti sai kuma ya ɗan kaɗa kansa yace naga tunɗazu kina zaune baki tashi kin ɗauki abunda kike bukata ba?shiru namasa ok na fahinta saurin kallon sa nayi jin yace ya fahinta a raina nace kode shima ya fahinci tsoron da nake ciki kaman kuwa yasan abunda dake cewa yace tsoro ko?wannan karon ɗaga masa kaina nayi alamar eh ƴar dariya yayi yace matsoraci baya zama goni kicire tsoro aranki ki hangowa kanki nasara karki hango daɗiwa kowace nasara tana tare da ƙalubale dan haka ki yaƙi tsoranki ki hango nasara dake gabanki maza ɗauki hoton da aka kabaki kije kizaɓi kayan da zakiyi amfani da shi,karon farko a rayuwata da wani yakarkamun gwiwa batare da sanin niɗin wacece ba"nagode nace dashi cikin sanyin murya wanda yake nuni da rauni na a baiyane. Wani irin gwarin gwiwa naji da maganan da wannan dan uwa da nasamu ko sunan sa bansani ba take naji wani karfi ya shigeni kallo ɗaya nawa hoton na ajiye saman keken na nufi wajen tulin kayan na almakashi da tape na ɗauka sannan nanufi wajen kayan nayanka daidai abunda nake da bukata na yanka duk da kalan yadin irin mai tsilɓen nan ce mafi akasarin kiristoci sunfi amfani dashi sukan ɗinka dogin riguna amarya da kawayenta ranan aure mun dinka irinsu da yawa da wacce nakoyi ɗinki a wajenta wata ibo ce wacce muke kiranta da maman joy.   Cike da ƙorewa nayanka doguwar riga wato fitet gawn mai zizza namikawa yamun cikin ƙanƙanin lokaci nashiga sarrafa keken cike da ƙorewa ta da kuma son na burge kowa. Dajin kare kukanka Cikin wata ƴar bukka wani mutum ne zaune cikin kamilallaliyar fuska saide da kagansa kasan yana cikin matsanancin wahala duba da yanayin sa,wasu kattine majiya karfi suka shigo ƴar bukkar da yake tare da wasu manyan alhazawa biyu kugera aka kawo musu suka zauna suna fuskantar sa ɗaya yaɗago yana kallon masu tsaron sa yace"wai mai yasa kuke dauresane? kuringa sassauta masa"oga ai idan ba dauresan mukai ba zai iya guduwa ne. Murmushin taƙaici yayi ya kalle su yace"wallahi dan banason saka ahalina cikin matsalane badan haka ba wannan igiyan be isa hanani fita daga nan ba wallahi. Dariya duka suka kwashe dashi sai da sukai mai isarsu sannan Alhaji sunusi ya gimtse fuska kira sunan sa da ishaq" da kunyan duniya kwara ta lahira awajena da nabarka kafita ka tonamun asiri kwara na kasheka amma haryanzu de wata daman zan sake baka a karo na ba adadi ina waƴan nan ƙundaddakin suke? Kauda kansa yayi gefe yana tuna abotarsu tun suna ƴan samari suka taso amma dare daya saboda abun duniya sunusi abokin sa aminansa da yafi yarda dashi duk duniya sama da kowa idan kacire mahaifinsa yau shine yake neman ganin bayansa akan dukiya. Shirun da yayi besake koda kallon inda yake ɗin ba hakan yasake ƙular da shi dan haka cike da mugunta yabuɗe tafin hannun sa ɗaya ya shaƙi iska yafara wasu surutai kai nan da nan wanda akakira da ishaq yayi sama yariƙe wuyansa da hannu yayinda idanunsa kaɗa suka fiffito kaman zasu faɗo sai kakarin yake Alhaji sunusi yada ya tabbata amininnasa ya galabata sannan yasauke hannun yana saukewa kuwa ishaq yafaɗo ƙasa sau tari yake a wahalce zuciyan shikuma sai kiran sunan Allah yake da kakkausan murya alhaji sunusi yace"zankuma tambayanka ina waƴannan ƙundaddaki suke?amma ina ishaq be masan yanayi ba sabodq suman da yayi cike da takaici suka fito daga bukkar yana mai cewa masu tsaron nasa"a daren yau kuɗauke shi kukoma can gidan gonata da zama dan zaifi nan zan kuma irinƙa samun ku ta waya"angama ranka yadaɗe suka amsa masa suna take masa baya. Ahmad Ƙurawa allon systerm dake gabansa ido yayi yana ƙare mata kallo yanda take ɗinkinta batare da tana kallon hoton ba,tsaɓanin sauran da sauke ɗan kallon hoton lokaci zuwa lokaci“ƴan yarinyar nan zatayi abun kirki kuwa?ya tambayi kansa"me kawani sa systerm a gaba kana kallon ta idan so kake ka kalleta kawai umurni zaka bada tataho da keken nan kaga sai kaji daɗin kare mata kallo. Mtsss tsuka yayi cike da jin haushin kansa shi yamarasa mai yaɗauki hankalinsa wajen kallon nata. Munada aiki mai tarin yawa a gabanmu amma katsaya kana ɓata lokaci wajen kallon duniya khalid yasake faɗa. Shide Ahmad banza yamasa yana ɗaga wani wayan bayan sun gama magana yadubi khalid yace"saif ne yana magana akan kayan da aka tura masa yakuma ce yaturo samfarin wanda zasake ɗinka masa. Wajen nasu babba company yana da fannoni daban daban akwai magina sunada kwararrun masu zane wato architect akwai masu walda ƙofofi da tagogi sai masu ɗinki suna kuma da motocin sufiri masu tafiya garuwa suna kuma yin kasuwancinsu ta online suna aika kayayyakin su garuruwa da dama harma da ƙetare irin su chadi cameroon ghana niger cotouno sudan dade sauransu. "Ok kasaka hannun kawai ake jira yanzu zasuyi lodi dan komai ya kammala. Ataikaice de saida kusan kowa yagama yarage dagani sai wata yarinya wacce zatakai sa'ata muka rage kallona tayi a raunane tace"kema baki gamaba"eh na amsa mata dan zuwa yanzu ga ƴunwa gakuma gajiya duka sun addabeni sai kusan karfe biyar da rabin yamma muka gama kusan atare gugan kayan nayi na linke nasaka a ledar da nagani kowa nasawa na ɗan juya nakalli yarinyar nace yar uwa fatan nasara murmushi ta sakarmun nima namai damata muka fito a tare kusan a tare muka fito da Ahmad dake ta zabga sauri khalid na biye dashi a baya danshi yarasa gane saurin me abokin nasa yakeyi haka garin dauka jakata data zame daga kafaɗata kawai sai naji na bugu da abu ɗago kanda zanyi mukai ido hudu dashi bansan sanda nafurta"fatan nasara oga Ahmad ba.   Ƴan uwa karku shagala ku manta wannan littafi na kuɗine ki biya 300 dan samun complet dinsa.   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Chapter 6 "Aisha lafiya muke irin wannan gudu kaman waƴan da akace munyima sarki sata?"hmm fadila bazaki gane bane?"to ki fahintar dani mana ta yanda zangane kuma wannan da kike gudun sa wayeshi? "Ɗan Hajia bilkisu ne na amsa mata ina samun gefen wani bishi nakai zaune ina haki,itama zaman tayi tana maida numfashi tasake cewa "wai kan wani dalili kikasa mukayi wannan uban gudun?dariya nayi mata kawai dan son kawar da zargi nace"ke marina ya taɓayi kuma kinsan banason abunda ze taɓamun lafiyata. Dogon tsaki naji tayi tace"amma de anyi matsoraciya wallahi kikasa mukaci uban gudu haka nadauka ma wani abunne da nasan hakane wallahi dan banci wannan uban gudun ba,takare magana cike da jin haushina nide hakuri kawai narinka bata har nasamu ta hakura. "Mummy gaskiya kiyi wani abu dan kar narasa guy ɗinnan wallahi inason shi takare maganan tana marairaice fuska murmurshi Hajia mariya tayi tace"kede kibar komai a hannuna ai bakida wani miji sama da Ahmad ko uwar da takawoshi duniya bata isa ta hana wannan auren ba,kede abunda nakeso dake duk wani abunda kikasan ze burgeshi kiyi sannan kiriƙa kai masa ziyara office ɗinsa tanan ne zaki saka ido a kansa inma so kike kikoma da aiki can inda yake kinga sai inma mahaifinki magana kinga hakan ma wata damance ta yanda zaku kasance kullum tare koya kikace?tsalle tayi tadire cike da murna ta rungumi mummyn nata tace"wayyo mummy wallahi wannan shawara tayi dan kinga tanan ne zan samu daman nuna masa soyayyata. "Dot kasan fa gobene zamu fara ɗaukan sabbin ma'aikata ko?numfasawa yayi dayin ɗan tsaki"ai basai nazo ba kaima zaka iyayi"saifa kazo dan tantance masu ɗinki kasan wancan karon da kabarmun aiki yamun yawa daga baya ansamu matsala dan haka gobe karfe 8:00am yazamana kana office dan wannan karon akwai tsala tsalan ƴan mata ko zamu sami wata mai sa'a tayi mana wuf dakai,yafada cike da zolaya banza Ahmad yayi dashi dan shi yanzu hanyan da zebi ya gujewa aurensa da basma yake nema kwata kwata yarinyar bata daga cikin tsarin matan da yakeso. "Wash Anna mungaji wallahi"salamu alaikum anna barka da gida. Wa'alaikum salam fadila sannunki kinji ƴar albarka kwalo fadila tama Aisha"au anna dan banyi sallama shine kika sanya mata albarkar ita ɗaya"eh hakane kinko canka daidai. Aisha Allah yashiryeki inba lalaci ba nan da gidan hajia bilkisu shine zakice kingaji?kafin Aisha tayi magana fadila ta amshe da Anna ba dole mugaji ba kinga yanda tasa muka dinga gudu kaman marasa gaskiya"kai Aisha kina girma amma kina daɗa maida kanki kaman wata karamar yarinya"gwarade ki faɗa mata Anna dan bakiga gudun famfalakin da makasha ba. "Ba dole muyi gudu ba kinfi kowa sanin koda can yanda banason taɓamun lafiyar jiki shisa koda yaushe nake kiyaye latti zuwa makaranta,riƙe haɓa Anna tayi tace"oh niƴasu Allah de yashiryeki Aisha ta wannan tsoro naki dan kika bari akasan logonki wallahi haka kawai zaki bewa wasu hanyan tsorataki. Suna cikin hira Maman Abba tayi salam tashigo amsa mata sukai Aisha da fadila na rige rigen amsan ƴar karamar ƴarta mai suna yusra,dariya maman abba tayi tana samun gefen tabarma ta zauna suna gaisawa da Anna nan suma su Aisha suka gaisheta daga nan maman abba ta kalli Aisha tace"nikan Aisha kwanaki kinfara tafiya shagon hafiz dinki yakuka kare haryanzun kina tafiya ko ya?"tab hmmm maman abba ai sau ɗaya taje dan iska tantiri mai riƙe hakkin mutame katse fadila nayi nace"haba fadila dena irin wannan zagin ai sai kasa mudauki zunubi madadin kawai kibada amsa kai tsaye. Na ɗan juyo na kalli maman abba nace"wallahi sau daya kawai naje amma bansake zuwa ba,dan jiyama yazo yana bani hakuri akan nakoma shagonsa nace bazan sake zuwa ba,kumama kinga yanzu haka ma daga gidan hajia bilkisu nake wai kawarta hajia mariya taso naje gidanta narikewa mai aikinta aiki har tadawo daga tafi. "To Aisha wani hanzari ba gudu ba amma kafin kije can ɗin mai zai hana ki gwada zuwa can ma'aikatan su Baban abba kinsan suna da fanni daban daban to gobe suna son ɗaukar sabbin ma'aikata fanni ɗinki ko zaki gwada sa'anki dan wallahi idan kisamu nan kin haye suna bada albashi mai tsoka ta yanda zaki samu daman kula da anna harma da makarantar su khadija koya kika gani? Kan nayi magana anna tace Allah yazaɓa mana abunda yafi zamowa alheri"amin muka amsa baki ɗaya,nan muka barsu nan tsakar gida muka ƙule ɗaki da fadila muna shiga taciro wata dan ƙareriyar waya tare da kuɗi masu yawa ta nunamun. Zaro ido nayi nakarɓi wayan ina kallo baki sake kan nace"fadila ina kika samu wannan waya bade sata kika fara ba?dariya tayi tana dafani tace"ko daya kawata wallahi wata babbar harkace shisa nakeso kizo mu jone amma naga ki haryanzu kaman kanki a tukunya yake duba kigani jiya wani Alhaji da muka haɗu dashi yabani harma da kuɗi dubu ashirin yace nasaka kati kinma gansu nan. Jiki a sanyaye nace"fadila gaskiya bazan ɓoyemiki ba dan bani da ƙawa sama dake tun muna yara haka muka taso duk inda akaga ɗayanmu to ɗaya nakusa amma wannan hanya dakika ɗauka bamai ɓollewa bace ba. Fadila kalli irin rayuwar da kuke wallahi kinfini gata tunda ke kota halin ƙaƙa mahaifinku zai nemo baze bari ku kwana da yunwa ba"amma mufa?sai anna ta fita zata samo mana aikatau wanki ba wanda bamayi duk de dan murufawa kanmu asiri fadila kar abun duniya da tsanar da kikewa talauci yajefa rayuwa cikin ha ula'i. "Au Aisha yanzu baƙi ciki zakimun dan kinga naci gaba ashe kima kina daga cikon waƴanda zasu nuna basason ganin cigabana to ai shikenan da naɗauka zakifi kowa farin ciki da cigabana"ayya fadila dan Allah kiyi hakuri wallahi banyi dan inuna baƙin ciki kan cigabanki ba wallahi zanfi kowa farin ciki kawai de gani nake kaman dan nuna adawarki da talauci my fadee ta kauce hanya dan tafaso gari nakare maganan cikin tsigar zolaya dacewa yauwa tashi muyi photo muma kaman sauran mutane kinsan andade da barinmu abaya dole tasaki ranta mukai photona masu yawa amma har kasan raina bana farin ciki da wannan sauyi na fadila lokaci ɗaya dan gani nake kaman bata hanyan mai kyau tasamu ba. Washe gari Tun karfe 7:30 nafita daga gida bayan munci ɗumamen tuwo nama anna sallama fatan samun nasara tamun ta miƙamun naira ɗari tace nahau napep karna makara. Doguwar riga ta shadda light blue nasaka ire iren kayanda hajia ikilima kan bani tuɓensu hijabi ma da takalmina da jakana duka fari nasa banwani wahala samun wajen ba,dayake wajen sanannen wajene mutane da nagani tabbas yasaka zuciyata karaya saboda yawanmu har wata zuciya tana cemun nakoma gida kawai bazan samu ba. Karfe 8:00 daidai aka bude mana wani ƙaton hall kekunan ɗinki a ciki sukai ɗari biyar ga fankoki ko ta ina kaɗawa suke shiga mukai kowa yasami waje ya zauna nayi mamakin ganin duk yawanmu da nake gani amma wajen ya dauke mu harma kekunan dayawa yarage. Zamanmu befi miti biyar ba sai gawani ƙamshi mai daɗi daya doke mana hanci tun kafin maishi ya ƙaraso wani haɗaɗɗen matashine yana tafiya irin na zaratan maza sallama yayi mana muka amsa kai ɗaya sannan yafara jawabi kaman haka. Sunana Ahmad kuma nine mai wannan wajen matsayinku na matasa ƴan uwana inason kawannen ku yamai da hankalin sa da nutsuwar kan abunda zeyi yanzu za raba muku hotunan ɗinki kowannen ku saiya zaɓi kayan da ze dace da ɗikin fatan nasara yamana harzai juya yasake juyowa ya kalleni akai dace nima shinake kallo karaf mukai ido hudu dashi take natuna rashin m danayi masa kwanaki daga taimako mukut na hadiye ƴawu. Warning yamun da ido take tsoro ya dabai bayeni duk kan ilahirin jikina ba inda baya rawa can yana fita wasu yanmata suka fara bara hoton ɗinkuna da zamuyi kowa ana bashi idan an baka sai a ɗauki sunanka dakuma numbar keken ka miƙomun nawa akai ina kallon ɗinki take wani irin zufa yakaryomu tun daga tsakar kaina harzuwa yatsan kafata hanyan guduwa kawai nake nema dan nasan da gayya aka bani wannan ɗinkin mai shegen wahala. Masu karatu Karfa kumanta wannan littafin nakuɗine idan kina kibiya ɗari 300 dan karanta labarin har karshe. ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Chapter 8 Wannan littafi na kuɗine ga masu bukata su tuntuɓeni ta wannan Number kai tsaye 07038486776 Wucemu yayi batare da ya kalli kowa cikin mu ba,sauke nannausan ajiyar zuciya nayi har yarintar da muke tare sai data tuntsure da dariya tana cewa"amma wallahi muguwar matsoraciyace ke murmushi nayi nace"kede bari ai tsoroma rahamace"tab bade irin taki dakike kasa ɓoyeta ba kinga duk sanda mutane suka fahinci tsoranki afili tofa kinzama abun wasan su dan haka lalle lalle ki koyawa kanki jarumta koda kinji tsoro ya shigeki to kiyi ƙoƙarin ɓoye tsoronki daga karshe sunana laila kefa?"nikuma Aisha naji daɗin haduwata dake kuma insha Allah daga yanzuma zan koyawa kaina jarumta dariya mukai sannan muka tsaida abun hawa kan sai gobe. Ina cikin napep Allah Allah nake nakai gida na ɗan huta araina kuma ina ta addu'an Allah yasade yau muna da ɗan abunda zamuci a gida dan yunwa nakeji kaman ƴaƴan hanjina zasu zagwanye. Alhaji sunusi dake zaune cikin wani katsaitaccan falo tare da wasu manyan Alhazawa ya kalle su ɗaya bayan ɗaya yatsaida kallon sa kan ɗaya daga cikin su yace"Alhaji mahdi kasan wannan tafiya dole ayita tunda yanzu anfito da wata fasahar kaman yanda kuke gani yanzu a cikin allon majigin nan nan duka suka maida hankalinsu kan allon daya hasko musu. Kunde gani a zahiri magunguna ne masu lasisi amma a baɗininta kuma hudar ibilisce kowane capsule kana buɗewa kayane a ciki kuma zamu rinƙa turawa dukkan nin inda mukeso acikin africa dama kasashen ƙatare amma kafin nan kasan muna bukatar bullet? Dukkan su kallon rashin fahinta suka masa sai Alhaji lawali ne yayi karfin halin tambayan sa"oga wani irin bullet kuma mukeda bukata? Dariya yayi irin ta bosawa sannan ya gimtse fuska yace"makami wannan tafiya dole sai da mata yara ƴan shilla zamu ɗauke su aiki suna mana tallan magunguna mukuma ta ƙasan ƙasa zamuna wannan bussiness ɗin idan anyi order sai mu basu sukai tasha subawa driver sukai kai kuma Alhaji badamasi sai ka ƙara bincike dakuma baza basiran ka dan ganin ka inganta magungunan wajenka tare da sarrafa su yanda yadace. Sannan mukuma namu zakana durawa a mazubin capsule sai ayi pakin ɗinsu cikin ƙwalba mai tsabta amma kuma dole sai ansamo ma aikata masu amana dakuma sirrin. "Wannan ba damuwa bace ba cewar Alhaji badamasi mahaifi ga Ahmad sannan shiɗin masanine ta hanyan kiwon lafiya Allah yabashi ilimin sarrafa magungunan gargajiya tun tuni yanzu kuma da komai yakoma zamanance suna sarrafa magungunasu tare da gwaje gwaje wajen inganta magungunan wajen nasa yayi fice sosai saboda ingancin magungunan sa shine yanzu waƴan nan manyan suke son suyi amfani dashi wajen cimma nasu manufan. Basma ta kalli mummynta dake riƙe da waya a hannu yanzu suka gama magana da kawarta hajia balkisu take sanar mata yanda sukai da Aishan jiya. "Mummy nifa na rasa gane me yarinyar nan take takama dashi wai me tatakane da har zakice kinaso tazo tamiki aiki zataƙi itada naji hajia balkisu nacewa saboda talauci watarana sai suyi kwana biyu batare da sun hura wuta a gidan nasu ba. Eh haka nan nima naji hajia balkisu nacewa saide kawai abunda nake tunani suɗin ba irin sauran talakawan nan bane masu yawon maula ba dan ni kaina sama da shekara goma kenan da sanin mahaifiyar Aishan tunma aisha na ƙarama amma tun can ita ɗin mai neman na kantane bata yarda wani yabata ba,cewar hajia mariya. Amma kibarni da su nasan yanda zanje gidan na kalallamesu da baki"mummy basma takirata tana zaro ido"gyaɗa mata kai tayi tace ai tsugunnawa wada ba gajiyawa bace asiyasance zan jawota zuwa masarautarmu sannan nayi wasan kurah da rayuwarta ita ɗin banza itaɗin wofi mai akai Nafi balle wata Aisha can takare maganan suna sakin shewa tare da tafawa kaman wasu ƙawaye. A gajiye na sauka a napep ɗin bakin layin mu na ratayo jakata ina tafiya cikin nutsuwata da ta gama zamemun jiki wasu na ganin kaman yanga nake amma ni nasan ba yanga bace ba haka Allah yayini. Ina ɗiyar talaka mara galihu ina ni ina wata yanga kullum muna fafutukar neman abunda zamu ci,tunda na doso lungunmu naji gabana na tsananta buguwa ganin lungun namu cike da mutane yanda nakejin gabana na harbawa har yana ɗagamun riga take wani tsoro ya shigeni Allah yasa ba Anna bace wani abun yasameta. Shine kawai abunda yake tafiya araina ratsa mutanen da suke tsastsaye nayi zuwa cikin gida ganin kowa kallona yake dana wuce ba mai iya yimun magana zuciya tagama saddakar mun cewa la shakka Anna ce. Sai de me ina dosan cikin gida kalma da natsinkayo ya nasani faɗawa a matukar fusace Anna nagani duƙe tana sharan hawaye raina idan yayi dubu to duka ya ɓaci bansan sanda nayi kan mai maganan ba. "Ilu nakira sunan sa kai tsaye cikin ƙaraji"ilu kuma?ya maimaita dan bantaɓa kiran sa da sunan kai tsaye ba sai yau kuma anzo limit dinda bazan iya hakura ba,dan mutum duk girman sa idan yace ze taɓamun Anna ta to wallahi sai inda karfina yakare. Koba sunan kaba ne hakan?na tambayeshi kai tsaye na ɗaura da cewa karuwanci yawon dandi dakake ta hargowa kana ɗaga murya da tara ƴan kallo kana wani faɗin hakan ai shima iyawane idan wani ya isa yayi idan besha ɗankaren duka ba. Ko cema akai haurawa katanga gidan matan aurene,yayi matukar harzuƙa kaman ze kaimun duka haka ya hayayyaƙomun yafara zagezagen borin kunya. Dan halin sa kenan kowa a nan anguwar yasani ganin zagin nasa bana karewa bane nace"to dan Allah idan kagama kafita mana daga gida dan wallahi ko maza sun kare ba abinda Anna zatayi da ƙazami irin ka idan tallata kanka kazo to albarka bazamu taya ba shashasha wanda besan mutuncin kansa ba. Haka ake zuwa gidan mutane kai tsaye dan kawai muna haya a gidan ka,nagade kowa anan anguwar yasani idan ba munafinci ba aiko waƴanda suke kiran kansu maza wallahi sai mun biya kuɗi suke bada nasu daga baya kawai dan an shirya cimana mutunci shine shine...."ya isa Aisha cewa Anna tana dakatar dani tuni ƴan kallon suka suka watse dan ɗaga murya nake ina magana kowama yaji kai kuma nafada ina nuna malam ilu da ɗan yatsa nace kasaurari kira daga mai anguwa saboda karya doka dakayi kashiga mana gida sannan katasa mata da ƴaƴanta da maganan banza.....salati kawai malam ilu yasa tun karfinsa.   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Chapter 9 Bayan ficewar malam ilu da muƙarraban sa ƴan kallo ɗago Anna nayi daga ɗuƙen da take muka shiga ɗaki da ita maman manu da muke gida ɗaya da ita tashigo har ɗaki ta zauna ta kalli Anna da har lokacin takasa koda ƙwaƙƙwaran motsi sai ajiyar zuciya da take saukewa dama muddin kaga Anna a irin wannan yanayin to lalle ranta yakai ƙololuwar ɓaci dan haka cikin sanyin murya maman manu ta buɗe baki tace"maman Aisha dan girman Allah kiyi hakuri da abunda malam ilu yazo yayi miki karkisaka abun arai ballema yazo ya dameki ya hanaki sukuni a ranki. Sai kuma taɗanyi shiru ɗan muskutawa nayi nace"amma maman manu tsakani da Allah yanzu duk zaman da mukeyi da mutane a nan anguwar amma arasa wanda ze dakatar da irin cin mutunci da wannan mutumin yakewa Anna magana ashe duk taron yuyuyu taron kuɗaji marasa amfani muke zaune dasu bamu sani?wannan yanuna koda cutar damu za ayi a unguwar nan ba wanda zaiyi magana wallahi maman manu da zaran nasami albashin wannan watan wallahi ɗaukar uwata zanyi mubar nan unguwar da ba wajen zama bane ba. "Haba ƴar nan katseta nayi raina a mugun ɓace nace"kinga maman manu tashi kawai ki fitar mana a ɗaki dan dukkan ku halinku ɗaya banga wani abun kizo kina mana karamar murya bayan kowa ya watse ba,ai wannan duka gulmace kiji mai zamuce kisami na barbaɗamu. "Yi hakuri maman manu rabu da Aisha ai kinsan sha'anin yaro ba kowani ɗan halak ne zaiga ana wulakanta masa iyaye yayi shiru ba cewar Anna da har lokacin bata kalli inda maman manun ke zaune ba tayi maganan. Washe baki maman manu tashiga yi tagyara zama tana cewa wallahi maman aisha ai wannan maƙwabciyartamu mai ɗan wake ita ke kai gulma wajen malam ilu dake shikuma ba hankaline da shi ba shikuma yazo yana ta tada jijiyoyon wuya kawai dan baku biya da kuɗin wannan wata ba,rainane yasake ɓaci jin wai mai ɗanwake ce ta haɗa wannan tarzomar yasani cewa ai wallahi sai namata rashin mutunci. Saurin dakatar dani maman manu tayi tace"haba keko aisha daga ganin ɗan fawa sai miya tayi zaƙi haba de ai basai kinje ba kinama zaune zata ciyota ta zo tasame ku nan zaune. Daga haba ba wanda yasake yin magana haka ta karashe zaman ta harta tashi tatafi ƙofarta mude bataji ta bankin mu ba kamqn yanda Anna tajamur burki nima shirun nayi. Saboda ɓacin randa nake ciki wallahi sai na nemi ƴunwar dakuma gajiyar da na ƙwaso duka narasa. Dadare muna zaune ina sake kwantarwa da anna hankali sai ga fadila kaman anjehota ta faɗo mana ɗaki tana ta huci ko sallama babu tashiga cewa yanzu dama wannan mara mutunci mutum haka yazo yamiki anna wallahi sai yasan yataɓoki hukumace zata rabamu da shi wallahi. Murmushi mai ciwo anna tayi tace"yo mai natada jijiyoyin wuya ai idan mukace zamu rama abunda yamana mun zama ɗaya kenan barin shi da Allah kawai zamuyi shine ze bimana hakkin mu dan Allah ba azzalumin bawa bane saide bawa ya zalumci kansa,Allah yana gani tunda nazo nagarin nan bantaɓa yi da kowa ba,to mai zetada mun da hankali dan ɗan kwaya irin malwm ilu yamun tijara kawai de naji ba dadine gani yanda yan anguwa suka zama ƴan kallo akarasa wanda zece da ilu abunda yayi ba daidai bane ba. Amma duk da haka nagode Allah haihuwa tamun rana tunda yanta tazo ta tsayamun haka yarba gidan cike da kunya harda su masu kallon. Daga haka taɗauko wata hiran nan muka shigayi sai can fadila takalli ni tace"nikan yau tunda garin Allah ya waye nake ta zaune ina jiran dawowarki naji ya rananki ta farko ta kasance duk da nasan keɗin kwararriyace inde ta fanin ɗinkine banida haufin ko matar shugaban ƙasa zaki iyama dinki amma kuma kedin matsoraciyace lamba ɗaya masamman ma wajen da ba idon sani. Dariya nayi nace bawanda yasanni sama dake da anna na nashiga faɗamusu yanda na tsorata kafin wani saurayi ya fahinci halin da nake ciki yabani kwarin gwiwa dariya sosai fadila tamun anna kan cewa tayi Allah yakyauta yarabaki da wannan tsoro naki,sai karfe taran dare fadila tamana sallama rakota mukai nida khadija nan take sanar dani ai takusan samun aiki a masana'antar sarrafa magunguna na al hakk natayata murna dakuma yi mata addu'ar samun nasara tunda tace gobe zataje dan ayi musu gwaji. Washe gari bayan munyi sallan asubahi nayi karatun al qur'ani mai girma kaman de yanda nasaba nade sallayar nayi na maida qur'anin na ajiye sannan naje na gaida anna datake zaune take lazumin ta sai kuma nafita naɗaura mana ɗumamen abincin jiya dadare saboda ɓacin rai bawanda ya iyaci tsakanin ni da anna harma kwara mubaraq ya ɗanci nasauke na daura mana ruwan wanka sai ga maman manu tazo tana wani washe baki ita ala dole fara'a"a'a aisha kece da sassafen nan"eh nice na amsa mata a takaice. Zata kuma yin magana nace kinga sauri nake dan zuwa human right kai karan malam ilu da mai ɗanwake dan bima Anna hakkinta na kalaman batanci dasukai gareta dan shiga tsakanin mu dasu da dukma wani mai hali irin tasu kinga maman manu bar wajen kirki ɓatan lokaci. Yanda nayi magana cikin haɗe fuska nima kaina nayi mamakin irin jarumta da nanu,barin wajen tayi tanufi kofarta cikin sauri nikuma abincin na dauka nashiga dashi ɗaki mukaci nace maza khadija tashi kiyi wanka kafin nan nayi shara bayan duka mun shirya sai muna anna sai anjima sai anjima dan sai naraka su khadija makaranta kafin na wuce sai ga sallaman mamman saje wani dattijo makwabcin mu sai kuma ɗaiɗai kun ƴan anguwa da mai danwake. Har kasa na zauna nagaida mamma saje dan saida nakira sunan sa ma nagaida shi saboda sukara sanin ma haushi suke bamu"Aisha humaira ina ita nafisan take?"tana ɗaki baba nace dashi tare damiƙewa na dauko tabarma na shimfiɗa masu sannan nashiga daɗi nasanar da Anna zuwa su a tare muka fito ta zauna daga baƙin kofar daki da carbin ta a hannu ta gaida mamman saje cike da girmamawa dan dattijon ƙwarai ne mutumne wanda koda wasa bayason ganin anayin ba daidai ba acikin anguwa yanzun nan zai tsawatar da babba ko yaro. Nisawa yayi yace"nafisa wajenki mukazo bada hakuri akan abunda yafaru jiya,wallahi jiyan bana nan hakan yafaru sai can dare dana dawo mai ɗakina take sanar dani abunda yafaru,sa'ilin dare yayi shisa ban zo ajiyan ba,wallahi raina yaɓaci sosai da abunda malam ilu yayi ina kallon sa babban mutum ashe shiɗin bashi da cikekken hankali dan Allah kidubi girman Allah da manzon sa kiyi hakuri idan kinji ance da mutum yayi hakuri tabbas an cutar dashine,a kuma janye maganan human right da zakukai ƙara insha Allah hakan baze sake faruwa ba. Sai da yakai aya sannan Anna ta ɗago tana kallon sa tace"hakika baba saje ba'aɓa muzantani kaman yanda ilu yamun jiya ba,nasan bakomai yakawo haka ba saboda kawai yana ganin bani dashi shiyasa yamun haka da ace ina da kuɗi koda a titi nake kasa haja wallahi be isa yamun koda kwata kwatancin abunda yamun ba amma bakomai gidane dama wannan wata damuke ciki kuɗinmu ze kare insha Allah karshen watan zamu barmasa gidan sa basai yazo yacimun mutunci a gaban mutane ba. Baba saje juyawa ga malam ilu yayi daya sinne kai kasa alamun rashin gaskiya ya bayyana ƙarara a tare dashi yace"ashe kai ilu mutumin banzane dama kai bansani ba?ashe kuɗin suma basu cinye ba kazo kamushi tijara haka wai ma akan wani dalili kaxo kasamu mata da yaranta karamata mutane kayi ta aibatata mai tama?ku kuma yanuna su malam kalla maƙwabcinmu sai baban manu sai malam ashiru yace anyi dattawan banza wallahi tirr da hali irin naku ace kuna anguwa kuna ganin irin wannan abun nafaruwa bazaku tsawatawa mai yi ba saide ku zuba ido kuna kallo kuna dariya. Mainene aibun matar nan?dan tana zaune cikin mu tunda tazo garin nan yau kimanin shekara takwas ba wanda yataɓa ganin tayi abunda bashine ba tana zaune kalau da kowa tatsaya tsayin daka dan ganin ta tarbiyatar da ƴaƴanta tabasu ilimi,shin kanta farau hijira daga garin da kake zuwa wani gari ko kanta karau nagade dukkan mu nan zuwa mukai ba ƴan nan bane. Hakade baba saje yayi ta musu faɗa karshe kuma yaɗaura da musu nasiha jikin su yayi sanyi sosai na suka shiga bawa Anna hakuri bama kaman malam ilu da mai ɗanwake dan cemata nayi wallahi ko kallon banza sukama Anna sai nakai mutum human right dariya baba saje yayi yace"yauwa Aishatul humaira faɗamusu suji tunda basu da hankali haka akeson ɗan halak yazama mai kishin iyayen sa. Alhaji sunusi ne zaune da mukarraban sa yadubi Alh shehu tace"kai Alhaji shehu ya ake cikine?dariya ya kwashe dashi sannan yace"an sami tawa ƴar talakawa mai masifar son kuɗi inaga wannan za ayi tafiyan da ita nan duka suka saka dariya sannan Alh sunusi ya ɗaura da cewa"ko saurayi ko magidanci matukar aka sami mai irin wannan hali to azo dashi dan za ayi tafiyar tare dasu. Ahmad ya ɗaga rigar da Aisha ta dinka yafi aƙirga yana girgiza kai yana ƙara jinjina ma kwarewarta khalid cike da tsokala yace"wai nikan kode rigar nan ajiye zamuyi ne kawai kadinga kallo?"mtsss yayi tsuka yace"nifa ɗinki bewani yimun kyau ba"kai kasani cewar khalid yana fita daga office dan kiran sunayen waƴanda suka samu aiki,yana doso hall din duka suka zuba masa ido kowa na addu'an Allah yasa yasamu aikin ina Aisha ishaq sunar farko daya yakira amsawa nayi tare da sujjada shukura dan godewa Allah dayasa nasami wannan aiki badan wayona ko ƙware wata ba hakan da nayi ya burge kowa hatta shikansa uban gayya da yake kallon komai ta cctv nasan cewa samun aikin nan da nayi rufin asirin mune nida anna dakuma ƴan ƙannena. Saida yakira sunayen mu duka wayanda suka ɗauka aiki saura yabasu hakuri dakuma bawa ko wanne cikin su 5k sannan ya juyo kanmu yace musame shi a office din oga Ahmad tunda muka doso wajen sai naji zuciyata takasa nutsuwa nice farkon shiga sallama ɗauke a bakina nashiga office din wanda sanyi ac dakuma wani irin daddaɗan kamshi suka daki hanci na take yasaukar mu da wata iriyar kasala. "Aisha ishaq³na amsa cikin sanyi murya tare da fargaban abunda zai biyo baya ɗaga rigar da na ɗinka jiya yayi sama yana kare masa kallo sai can yace ba lefi kinɗanyi abun azo a gani amma duk da hakan sai kin sake ɗinka biyu irin sa nagani kafin na ɗauke ki aiki gudun samun matsala daga baya take ƙirjina yabada sautin dam ganin ina farin cikin samun aiki ashe abun ba haka bane ba jikinane yafara rawa tsaban kiɗima har bansan sanda hawaye ya ɗan zubo daga idona ba.   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Chapter 10 Saurin maida hawayena nayi dana tuna maganan Anna inda take cewa dani karki bari mutum yasan dalilin kukanki idan yasani gobe shi zesaki kuka, "Ok tom kawai nace dashi ba tare dana ko kalli inda yake ba nayi hanyan waje a raina ko cewa nake kajimun da ɗan rainin hankali,ai ko makaho ne ya laluɓa yasan kayan nan ta ɗinku amma jishi har dawani cewa kin ɗanyi ƙoƙari yana yauƙi kamar ta mace abunda bata sani ba duka maganar tata afili tashi kuma yajita cizan lips dinsa na ƙasa yayi aransa yana cewa zannuna miki rashin hankali na kuwa. Fadila zaune take a office din Alhaji sunusi bisa jagorancin Alh shehu kallon ta kawai Alh sunusi keyi yana kara nazartarta yace"fadila ko? Sauri ɗaga masa kanta tayi dan ita duk a tsarge take ganin irin kallon da yake binta dashi",zaki iya aiki damu? Zan iya da yardan Allah ta amsa mishi baki na ɓari gyaɗa mata kansa yayi yana juyi a saman kugeran sa sai can yace menene dalilin ki nason aiki damu? Fadila ba tare data tsaya janbaki ba tace"saboda nagaji da rayuwar talauci kullum mu kenan bawani canji daga miyar kuka sai wake da shinkafa wannan ɗinma sai wata ran wata ran,dan haka sonake abani aiki yallaɓa komai wahala zanyi shi matakur zan sami farare bugun habuja inci shawarma anci pizza in ɗaura kaza a duk sanda naso in riƙe babbar waya nasanya kayan da nakeso na gammu cikin daula wannan shine babban burina. Ƙyalkyalewa da dariya sukai baki ɗayansu jin abunda tace"yarinya inde wannan ce damuwar ki, To kaddara damuwarki tazo karshe zamu baki aiki sannan zaki shiga ƙungiya wajibi ne akan duk wani member dake cikinta halartan meetin a duk inda zamuyi kuma koda wani lokacine bamason kawo mana yashashen uzuri sannan buɗe sirrin mu gawani wanda ba cikin mu yake ba kaman wasa kike da rayuwarki,ki tashi ku tafi kabata duk abunda take da buƙata kafin zuwa ranan meetin. "Da to Alh shehu ya amsa duk girman Alh shehu saboda girmamawa kaman zeyi sujjada wa Alh sunusi saboda biyayya,godiya tayi masa sannan suka fita, A hanyar su ta tafiya gida Alh shehu ya tsaya a wani haɗaɗɗen wajen suya yasiyo mata kaji danƙwala danƙwala har ƙunshi biyu sannan pizza da shawarma da lemunkan gora masu ɗan karen sanyi fadila tunda taga yashigo da ledar kajin nan take yawunta ya tsinke Allah Allah kawai take aranta yace ta ɗauka tasoma ci. "Aisha nikan ɗinkin wannan kaya kaman baya baki wahala? Cewan shamsu dake zaune shima saman kugeran keken sa daura da ni",hmm shamsu kenan bawai dan baya bani wahala bane ba kawai de dan bayan da zanyi tunda mai abun yace su yakeso yaga ina ɗin kawa. Sai yamma lis muka tashi nan na fahinci karfe biyar ake tashi a ma'aikatar dan da muka fita naga dandazon mutane kowa na kama gaban sa,sai na tsinci kaina da matukar farin ciki dakuma son aikina koba komai nasan rufin asiri gareni da Anna ta da ƙannena. "Fadila ina kika sami kudi harkika iya sayo danƙwa danƙwal kaji haka? kinsan fa banson ɗauko magana muna zaune ƙalau bamu rasa ci ko sha ba,amma saboda dan banzan baƙin halinki na kyamatar talauci zaki kai kanki ga halaka. Kuka tafashe dashi tana cewa"ai dama nasan komai nayi ba daidai bane a gunki,yanzu mama fisabilillahi dan na kawo wannan abun yanzu har abun magana ne wallahi da Aisha ce takai irin wannan gidansu saide Anna tashi mata albarka amma bata ta dinga tuhumarta ina tasamu ba,takare maganan tana mai kara sautin kukanta. "jikin mamace yayi sanyi ganin yanda ƴartata ke kuka cikin sigar rarrashi tace"ai duk uwa tagari dole ta tuhumi ƴaƴanta da kike wani cewa Aisha ai ita ba haka take ba tasan talaucinsu kuma bata adawa da shi kullum fafutuka take dayin aiki tuƙuru dan ganin sun samu abunda zasuci kefa? to yanzu yi shiru share hawayenki faɗamun inda kika sami kuɗin tukunna kinga sai hankalina ya kwanta,jan majina tayi tukunna tace"banace miki zanje Al hakk neman aiki ba"eh kin faɗa mama ta amsa tana gyara zamanta"yauwa to can naje kuma andace sun ɗaukemu aiki shine suka raba mana dubu goma² a cewar su muyi kuɗin mota,nikuma ganin nasamu kuɗin shine fa nace yau ɗaya muma muci daɗi amma shine kike ta......sai kuma tayi shiru. "Ayya fadila ɗiyar albarka dole na tuhumeki yanzu ba gashi nasan daga inda kika samu ba,nide fatana a koda yaushe be wuce ki zubar da wannan banza aƙida taki nakin talauci ba wallahi,nan ta sauko sukaji kaza ɗaya suna korawa da ruwan lemu mai sanyi saida suka cinye sannan mama tafito waje jinta take wasai aranta kuwa cewa tayi yaushe rabon da naci kaza a gidan nan in baci nayi karya ba sai ince tun tunna amarcina lol. Shaƙan ni'imtaccen iskan waje nayi ina sakin ajiyar zuciya haka kawai nake jina cikin nishaɗi,hanyan waje nayi laila na biye dani tana tamun hira wani abun na amsa mata da eh ko na amsa da a'a da haka dar muka fito bakin get wata mota baƙa harta gitta mu sai kuma tadawo da baya baya ta tsaya daidai setin mu saurin ɗauke kaina nayi daga kallon sa nafara yin gaba banyi aune ba sai ganin mutum nayi yasha gabana na tsaya dan dole yasani jaa nima natsaya batare da nako kalle shi ba,anufin idan ya gaji da tsayuwan yabani hanya nawuce. Ganin naɗauke kaina yasa shi cewa"Assalamu alaikum sanin muhimmacin amsa sallama yasani amsa masa da wa'alaikum salam na daura dacewa ko zaka bani hanya nawuce dan Allah,hmm yasauke ajiya yace"in banda kince Allah da ba abunda ze sani kauce miki a hanyan har sai na fadallasa miki sirrin zuciyata amma duk da naga kaman ba'amaraba da ni sunan usman sunusi kuma a gaskiya kinmun tunda naganki naji duk duniya ba wata ɗiya mace da tamun kamanki ina son ki,take naji zuciya ta wontsolo kaman zata faso ƙirjina ta faɗi jikina ne ya dauki wani irin ɗumi take naji gumi ya karyomun take ƴawun bakina yakafe nama kasa buɗe bakina sabida wani irin nauyi dayamun batare da na bashi amsa ko sake tsayuwa a gunba,naraɓa gefen sa zan wuce yayi saurin riƙo hannuna nayi saurin fizgan hannuna na yarfa masa mari cikin rawan baki data jiki nanushi da tsaya nace"karka sakeyin gigin kawo ƙazamin hannun ka da nufin riƙemun hannu... Dafe ƙuncin sa yayi cike da jin haushin kansa wai yau shine yarinya ƙarama zata mara a cikin bainar jama'a,suma su Ahmad da khalid sunga marin da namasa amma basu san meya haɗani da shi ba,nufata yayi cikin zafin nama yakai hannu zai fizgoni yaji an riƙe masa hannu saurin ɗago kansa yayi dan son ganin uban waye kuma yake kokarin tsadashi dan sai ya yayyaga wa wannan mara kunyar rigar mutumcinta a idon jama'a kaman yanda tamishi. "Cool down bro Ahmad yayi maganan cikin hucky voice ɗin sa,ɗago da jajayen idanun sa yayi dasuka gama jirkice saboda ɓacin rai yayi yazuba cikin na Ahmad,take yaji yamasa ƙwarjini yabude baki cikin ɓacin rai yana nunani yace"wai yaushe nayi lalacin da wannan kucakar yarinyar zata saka hannu ta mareni kawai dan tace nabata 50k mu haɗe a hotel nikuma nace 20k zan bata. Tunda nake a rayuwata ban taɓa sanin inda hotel yake ba amma kaji sharri muraran bansan sanda nadawo gaban sa natsaya ba,ina kuka irin mai cin ran nan fuskana duk yaɓaci da hawaye nace"kaji tsoron Allah yaushe nataɓa ganin ka in ba yanzun nan ba dahar zaka jefeni da sharri na juya ina kallon oga Ahmad nace wallahi Allah bansan shi ba shi ya tsaya yace yana sona ban kula dashi ba nafara tafiya shine yariƙe mun hannuna nikuma bisa kuskure namare shi danjin haushin riƙemun hannu da yayi amma wallahi oga ka yarda dani ni ba ƴar iska bace ba,da har zanyi kuɗi da wani....ɗagamun hannu oga Ahmad yayi hakan yasani shiru amma fa idona be fasa tsiyayar da kwallan bakin cikin da wannan sharrin da ɗan talikin nan yajefeni da shi ba. "Ki bashi hakuri na tsikayo muryarsa ba alaman wasa a cikin ta maida idona nayi ga wannan bawan Allah dana mara watsomun da wani mugun kallo dayasa hantar cikina kaɗawa murya na rawa nace"dan Allah kayi hakuri bisa kuskure hakan tafaru kuma bazan sake ba. Hayayya kowa kaina yayi kaman ze kaimun bugu oga Ahmad ya tare sa yana cewa"ai ta baka hakuri ko?"amma ai katseshi khalid yayi cikin hargowa kaman zasu haɗa ƙirji yace"inaga abun naka rashin kunyace dama ba komai ba bara nanuna maka muma mun iya irin wannan ɗanyen kan wazaka nunawa tsageranci ɗan akuya kawai rikosa Ahmad yayi yana cewa"haba mutumina ba fa girmaka bane hakan kana abu gaban ma'aikatanka,dan dole usman yashiga motarsa yabar wajen bayan yamun nuni da idon sa mukut na hadiye miyawo. Kallona khalid yayi bayan tafiyan usman yace"Aisha kidena saurin yanke hukunci irin haka nan gaba sa'an ki ɗaya nan ne da a wani wajen kika masa hakan ze iya yimiki komai yatafi yabarki kuma kece da kunya matsayinki na ɗiya mace dan daka ki kula kinji,share hawayena nayi nabuɗe baki daƙyar nace nagode murmushi yasakarmun yawuce yashiga mota juyawa nayi da nufin nama oga Ahmad godiya amma ina juyawa ya watsamun wani mugun kallo da yasani maida kaina ƙasa kwafa yayi batare dayace dani uffan ba shiga mota khalid yaja suka tafi. bayan barin su gurin kuma sai tsoro ya shigeni dakyar nasamu na daidaita kaina na tari napep na hau tunda muka fara tafiya na lura wannan motar biye damu da alama bina yake yaga anguwarmu ko gidan mu kenan kirjina na shiga dukan uku uku take nashiga danasanin marin da nasama...   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Chapter 11 A speed motar tazo kusa da napep ɗinda nake ciki sai kuma ta rage gudun ta jinayi kaman nasaki fitsari saboda tsaban rudewa danayi,sauke glass din motar naga anyi wani mutum yaleƙo da kansa yace"ƴan mata gyara mayafinki ko gyaɗa masa kaina kawai na iyayi kaman wata ƙadangaruwa bayan wucewar motan nasauke wata ƙatuwar ajiyar zuci da godiya ga Allah daya saka ba wannan masharrancin nan ne yabiyo bayana ba. A gajiye na isa gida sallama ɗauke a bakina na shinga tadda Anna nayi zaune a tsakar gida da alama girki ta gama take shara,rungume nayi cike da farin cikin samunta da nayi cikin ƙoshin lafiya"nayi kewarki Anna nafaɗi ina saka ƴar dariya"nima haka tace dani tana shafa kaina cike da kulawa maza jeki kiyi wanka kizo"da to na amsa ina tambayarta ina su khadija suke? "Kinga kabiru ne yazo ɗazu yafita dasu yawo,takare maganan tana kwashe sharan da tatara hmm kawai nace dan harga Allah banason fitan da kabiru yake dasu dan de kawai karnai maganane Anna taga kaman kyautatawan da yake manane banaso,niko ba haka bane gareni kawai ina jiyewa wulakancin mutanene tunda kowa kallon rashin uba dakuma dangi yake mana. Ahmad tunda yabar bakin ma'aikatar nasu yakwanta jikin kugeran motan yayi lamu khalid nata masa magana amma ina bajinsa yake ba,sabida zurfi dayayi a tunanin da yake dakuma jinjina karfin hali irin tawa wai yarinya kaman wannan mai karancin shakaru ta iya ɗaga hannu batare da shayi ko tsoron komai ba tamari saurayi irin wannan ɗan manya wayanda ƴan mata ke mutuwa a kansu mari lalle wannan idan mutum yasake mata fuska dayawa zatayi rashin kunya idan kaganta kamar wata mumina amma da alama shirin kunyace fal cikinta. Usman a fusace yashiga main falon saboda ɓacin rai dayake ciki bema kula da mummy ɗinsa dasuke zaune da sister dinsa ba,sai dq mummy mariya tace"my son lafiya na ganka haka waya taɓamun kai? "Mummy wai kamanni wata figigiyar yarinya ta mareni can you imagen?wai ni mummy miƙewa tsaye hajia mariya tayi ta kafeshi da ido cike da ɓacin rai tace"waye ubanta a ƙasar nan dazata ɗaga hannu ta mareka,watsa hannun sa yayi alama shima be sani ba cigaba tayi da cewa ko waye ubanta inaso ka tattaka shegiya inga uban daya tsaya mata duk wanda yama kan kara kai masa na rodi ban yarda koda wasa kabari wani yataka kaba muna muke da ƴaƴan banki a hanu,murmushi yayi yana cewa"that my mom shisa nake kara sonki wallahi,dariya sukai baki ɗaya banda basma dake faman taɓe baki tana daddana waya. Ita kuma wannan menene matsalarta mummy? Taɓa baki hajia mariya tayi tace"ai kasan tatsuniyar gizo baya wuce ƙoƙi wai Ahmad take kira a waya kuma yaƙi ɗagawa,girgiza kansa yayi ya tashi daga kugeran da yake zaune yazo ya zauna kusa da ita yariƙo hannun ta yace"haba sister karki bada mata mana ki zauna namiji na ɗaya nawasa da hankalin ki,bashine ze kira kiba ke kikira ma baze ɗaga ba ai wannan ci bayane cike da masifa ta miƙe tace"kaga malam karka wani cikani da surutu iba ruwanka dani ne?dawani zaka tsuma bakinka lamarina banason shisshigi tawani hayayyaƙu masa kaman zata cinyesa ɗanye tawu saman ɗakinta,hajia mariya na kiranta amma ko nuna tajita batayi ba"rabu da ita mummy ƴar wahala irinta yaushe zaka tsaya namiji na garata in banda kauyanci ta rashi wayo irin tata wai wanda zamusu auren haɗi take irin wannan haukan akan sa ni wallahi mummy kima faɗawa daddy wallahi karma yace nima ze hadani da wata ƴar abokonsa dwn wallahi ba yarda zan ba. Aisha:sai da mukai sallar magriba sannan kabiru ya dawo dasu khadija da sayayya niƙi niƙi sai murna suka mubaraq ya hau cewa"Anty aisha mun hau lilo da doki kai anty harma da mota ƴar dayiya nayi na maijin daɗin ganin su cikin farin ciki nace"lalle kace yau uncle kabiru yasha surutu dariya yayi khadija tace"wallahi kuwa kaman kinsani anty bakin sa yaki rufuwa har muka dawo gida bebar surutu ba,au anty na mance uncle kb yace kisa mesa a waje,kicin kicin nayi da fuska Anna ta kalleni ta girgiza kai tace"yanzu Aisha ko saboda yanda wannan bawan Allah yake hidima da ƴan kanneki yaci ace kin sassauto da zuciyarki ko bakomai ai zuciya nason mai kyautata mata,gaskiya anna ta faɗa dan duk rashi kulashi danake hakan be hanashi kyautatamun ba,da duk wani abu dayasan zanyi farin ciki yana kokarin yimun sai de indan baya gari dan aikin sa a lagos yake. hijabi na nasaka nafita tsaye nasame shi ya jinjina jikin motarsa yana ƴan danne danne da waya yana hangoni yayi sauri maida wayan aljihun wandon sa fuska sake yake kallo na,ƙasaso inda yake nayi nace"amincin Allah ya tabba gareka,faɗaɗa murmushin fuskan sa yayi yace"amin harda ke gaidashi nayi ya amsa yana cewa lalle yau wace ranace haka?dan ɓata fuska nayi ɗan taɓa hira mukai muna sallama sai ga fadila tana kallona da kabiru tayi kicin kicin da fuska tawuce tashiga cikin gida ba kotsaya ta kalle mu ba,girgiza kansa yayi yace kinga shiga daga ciki dan naga alama wannan ƙawar taki ita ke hana ruwa gudu ɓata fuska nayi zanyi magana yabuɗe kofar mota ya dauko wata leda ƙatuwa mai tambarin wajen sayan kayan yamiƙa mun yace bawa Anna ki isarmun sakon gaisuwata gareta kafin na wuce gobe in sha Allah zanyi kokarin shigowa mugaisa. "Yah kabir bade har komawa zakayi gobe ba?"kinaso na zauna ne?ya tambayeni yana tsareni da ido cike da jin kunya nace"sai da safe mun gode Allah yakara buɗi"Amin yace yana bude motar yashiga nima nashiga cikin gida. Fada Anna tayi tamun maiyasa na amshi kayan duka ai wannan hidima tayi yawa,dakyar tayi shiru ɗaki muka shiga da fadila nan muka baje kolin hira tace"kawata albishiriki amsa mata nayi da goro tace"nasami aiki cike da murna na rungumeta nace"masha Allah kice kin kusa zama mai kudi cike da zolaya nayi maganan,ga mamakina sai naga ta washe baki tace dani"wallahi kaman kinsani dan nasami aiki a wata ƙungiya mai zaman kanta kuma da alama akwai romo a wannan tafiya,kungiya na maimaita a zuciyana nace"kungiya kuma ƙawata nide gakiya ina jiye miki abunda zakizo kiyi da kinsani daga baya. Shiga ƙungiya kinsan ko wace ƙungiya tana da ƙa'idojinta dakuma manufofinta shin macece ƙa'idar ƙungiyar da kika shiga kuma fa idan kinshiga ƙungiya halartar taro wabijinine gareki koda yaushe kuma ko aina za'ayi pls ƙawa nide haka kawai naji sam shiganki ƙungiya be kwantamun araina ba. Ture hannuna tayi daga riƙon da namata tace"gaskiya kinga Aisha ina da burin yin ƙudi bafa zan zauna cikin talaucin nan da aka haifemu ciki muka girma cikin ta ba,kowa da kika gani yana da burin yaga cangi a rayuwar sa dan haka zancan ina fita a ƙungiya be taso ba kede kawai kibini da addu'a ko bakyason ganina cikin canjin rayuwane,na dauka zakiyi farin ciki idan kinji nasamu canji. Jiki a sanyaye nace"ba haka bane kawata Allah yasanya alheri,dariya tayi tace"amin daga nan muka shiga hiran duniya nan naji tace wai ashe matar nan bata hakura ba saida tasake zuwa ɗazu wai so take ki soma aikin wanki gobe asabar zata aiko da driver yazo yakaiki can gidan nata,"amma ke waya fada miki dan ni bamuyi haka da ita ba. "Anna ce take faɗamun yanzu amma dan Allah kawata kar kije,hmmm"haba kemade fadila ai ba abunda ze kaini nida nasami aiki kuma da alama nasamu karɓuwa daga masu wajen mai zai sake kaini wanke ɗan kamfan mace ƴar uwata sabida tsaɓan ƙazanta irin ta ƴaƴan masu kuɗi ko pad idan sunyi amfani haka suke bari jikin pant ɗin saide nina cire"Allah de yabudawa kowa amma talaka naganin tasku a rayuwa dakuma rashin daraja wajen masu kuɗin. "Barcewa haka fadila muma talakan munada daraja bawai bamu da ita bane sannan muna da baiwa da Allah yayi mana saide wasunmu suke zubar da daraja da Allah yamusu wajen maida masu kuɗi ababen bautarsu madadin suroka a wajen Allah amma sai kiga sunje suna rokon masu kuɗin taya zasu ganmu da daraja wallahi fadila matukar mutum yaroƙa wajen Allah sannan ya jajirce wajen neman nakansa da tsayuwa tuƙuru zesami Allah baze taɓa barin sa ba. Washe gari yakama asabar tunda mukai sallah asuba na tasa su khadija gaba muna tilawar al-qur'ani mai girma wajajen karfe takwas muka fatiha muka ci ɗumamen tuwo da anna takawo mana bayan mungama muka daura da ruwan bunu muna hira akai sallama gidan namu daga bakin ƙofa kafin wani daga cikin mu yaleƙa yagani sai ga maman salmanu da tafaɗo mana ɗaki tana washe tace"wani mai motane yake sallama da Aisha wai hajiace ta turoshi,fuska na ɓata nace"amma maman salmanu matsayin mu na musulmai ai yaci kimana sallama kafin kifaɗo mana ɗaki haka idan sallamarce take miki wuyan faɗin to kice gafaranku mana,ƴan soshe soshe tafara cike da kunya ruwan bunun anna ta zuba a kofi ta miƙa mata ta amsa tana kurɓa zata zauna nace kinga tunda ke akabawa sakon koma kice bazan jeni ba,daga Anna har maman salmanu zubamun ido sukai suna kallon na yayin da nikuma jikina yayi sanyi dan gani irin kallon da Anna ke jifana dashi nasan nagargadine..     ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Chapter 12 "Anna yanzu tafiyan zanyi nafaɗa kaman zan mata kuka?"eh tafiya zakiyi ta amsamun kanta tsaye ba tare da tadamu da yanayina ba,sake maimata tambayan nayi amsan de ɗayace eh dole ba dan naso ba saka hajibi na naɗauki jakata inada canji naira ashirin namikawa khadija nace idan kunje islamiya kwasayi sweet amsa tayi tanamun godiya hakama mubaraq suka dauki jakar makarantar su suka fita. Sai sannan anna ta kalleni tace"jeki mana Aisha kinbar bawan Allan nan da jira"amma Anna yanzu fisabilillahi kinsan natsani wannan wanki musamman na hajiyar nan amma sai kika yarda kice naje,ai da naje can gidan nata gwara sukawo kawai nayi anan tunda kin fison....katseni tayi tana cewa"a'a Aisha idan kinga kaman da taƙura yi zamanki dama nace mata idan kin amince zakije idan kinƙi kuma bazan tilastaki ba. Aisha shi rayuwa ɗan hakurine kowa dakika gani yayi nasara a rayuwa to sai da yahaɗa da hakuri dakuma jajircewa kafin yakai ga cin nasara dan haka inason koda yaushe kika sance mai hakuri a rayuwa dan masu iya magana kance mahakurci shikan dama dutse har yasha romonsa,ki koyi shanye damuwarki ko yaushe karki zama mai korafi ko saurin fushi kikuma iya sarrafa fushinki sannan komai zaki gani ki kalla da idon basira idan kuwa zakiyi abu ki auna amizanin addini dakuma al'ada jeki Allah yamiki albarka"amin na amsa mata nace sai nadawo Anna adawo lafiya ta mun. "Ahmad wai lafiyanka kuwa?Ammin sa dake zaune a gefensa tamasa wannan tambaya"lafiya Ammi wallahi kawai tunani nake kan wasu kaya da ake neman su nan da kwana uku wallahi gani nake kaman sabbin ma'aikatan da muka ɗauka bazasu iya ba wallahi,hmmm Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace"in banda abunka ahmad ai sai kamusu bayani tunda dukkansu sun yarda zasuyi aiki dakai kuma kwararrune to meyasa bazaka tuntuɓe suba,kagade yau asabarce ranan litinin idan mai duka yakaimu sai ka tarasu duka kai musu bayani dakuma basu order shikenan abu mai sauki amma kawani tsaya tunani abunda baka taɓayi ba kenan kode wannan karon surukuwa ta acikin su take tunda ana kunyan su tayi maganan cike da zolaya kwafa kawai yayi yana kikewa ya fita daga main falo baki ɗaya dariya ƙannensa sukai bayan fitan sa ganin yanda yayi kicin kicin da fuska. "Mummy kin tabbata yau wannan yar rainin zata zo kuwa tayi maganan tana yamutse fuska?"mai ze hanata zuwa bayan suna da bukata da kudin zata zo yanzun nan...sallamata shiya hana hajiya karasa maganarta juyawa tayi suka kalli juna da basma sai kuma suka kwashe da dariya tsayawa nayi daga bakin ƙofar shiga falon sai da sukai mai isarsu sannan suka tsagaita"shigo mana naji muryar hajiya mariya namun magana ba yanda na iya na shiga ciki gaidata nayi ba tare da na duƙa mata ba,kallona sukeyi a wulakance kaman bazata amsamun ba sai kuma ta amsa tana taɓa baki dacewa haka aka koyar dake ki gaida na sama dake? "hakanma nayi kokari hajia tunda na iya gaisuwan wasukan ai hakan ma basu iya ba,na amsa kaina tsaye a fusace basma ta miƙe tace"kee ni sa'ar kine da kike neman kawomun rai.hmm murmushin dauke a fuskana nace"in banda abunki anty basma na ambaci sunane yanzude ba tare da bata lokaci ba"miƙomun kayan wanki nafara da wuri dan inada wasu aiyukan da nabari a gida uhmm karkuma ki mance ki haɗomun da sabulu kinsan ba saba haɗawa bawa sai kuma robobin wanki sai ki nunamun bakin famfo na kare maganar ko akwalata ban kuma damu da irin kallon wulakanci da suke jifana da shi ba,na juya zan fita waje naji tana cewa"waye ze kwaso miko kayan komo kizo kishiga dakina bayan kin gyaramun bedroom ɗina ki kuma wankemun toilet sai ki dauko kayan wanki a dustbin kizo laure zata nuna miki wajen wanki. Murmushi ɗauke a fuskata nace"anty basma kiyi hakuri wanki kawai hajiarki tace zanyi amma batace harda wani ƙarin ba,idan baki shirya amiki wankin ba zan iya komawa inda nafito?wani irin hayayyako mun tayi kaman zata hauni da duka yanda takemun ihu harta kai saida na ritsa idanuna dan harga Allah zan iya cewa tunda nayi wayo ba wanda yataɓamun tsawa ko ihu irin haka,"meyake going ne anan?naji wani ya tambaya daga bayana"bro wannan ƴar aikine take neman rainamun hankali ina bata command tana neman raina mun hankali"ƴar uban waye ita?da har za bata umurnin yin abu tace ba zatayi ba,cak ya tsaya daidai setin fuskana yana karewa fuskana kallo da tunanin ina yasan wannan fuskar,bude idona nayi a hankali na sauke blue eyes ɗina cikin nasa daya sauke masa wani irin kasala na bude bakina a hankali na kai dubana ga hajia mariya dake hakimce tana zaune tana karkaɗa ƙafa duk wannan hargowar da basma kemun bata ko motsa ba balle nayi tunanin zata tsawatar mata"hajia tunda ba aiki da zanyi sai anjima dan tunda naga kaman baku shirya ba. "to fitararriya yimun fitsara dakika saba,mamaki yakani jin abunda hajia tace wato nice ma nayi lefi duk abunda ƴarta tamun bata gani ba"yi hakuri nace da ita ance faɗan da yafi karfinka kamai dashi wasa"riƙe hakurin ki mara kunya a raina nace ganan mara kunya a gabanki amma a zahiri sai bata hakuri da nake na daura da cewa hajia kefa cewa kawai kikayi wanki amma ya daga zuwana zata tareni da wani gyaran danki da wanke bayi kinga dole ai nace bazanyi ba,kuma harda guzuri zagi nida ba maula ko neman sakada yakawo ni ba ai kinga bazan dauki irin wannan mulkin mallakan ba. "Hohoho mummy dama ashe mai wanki ce?itan wannan saurayin da namara jiya yayi wannan tambaya dan tunda na gansa nagane shi shine bansani ba koya ganeni ko be gani ba,yana wani yatsine fuska kaman yaga wani kashi"eh ai da fari uwarta ke mana wanki kasan halin talauci da rashin cima mai kyau yunwa duka ta karya mata karfin jiki shine taturo wannan dan ta maye gurbin ta,tana magana tana nunani da hannu zuciya tazomun iya wuya kaman zan amayar masu da abunda yake cina a ciki amma na daure dan nasan idan nakoma gida nace ma Anna banyi ba bazata ji daɗin hakan ba"yauwa mummy kawai bani ita tarinƙa zuwa duk week tanamun wanki da guga dakuma gyaramun ɗaki kinga sai muyi jinga da ita biyan wata ko kullum inason ganin irin waƴan nan ƴan mata na aiki karkashina yanzun nan zan saukar mata da duk wani iya shege da takeji na yawo a kanta,kallon sa nayi na murguɗa masa baki ba tare da nadamu da kallon da hajia ke jifana da shi ba ita da basma. "Laure laure naji basma ta kwala kira wata mata tafito daga wani ƙofa da ƴar gudunta tana dukawa gaban ta tace"gani hajia ta amsa mata yatsine fuska tayi tana nunoni kaita ɗakina kinuna mata inda kayan wanki suke zata ɗauka da to matar ta amsa jikinta sai ɓari yake"ki dauko kawai basai nashiga ciki ba ai ɗakin mutum sirrin sa be dace. ..katseni basma tayi da cewa ke kinga wasa a fuskana"nide dan Allah kuyi hakuri me wani na batawa mutun lokaci akan wanki da yanzu ai nayi rabi amma tun dazu abu mai sauki anty basma ki shiga ki miƙomun kinƙi sannan ga wacce zata ɗauko kina katseta wai idan nashiga dakin naki mai zanyi miki idan so kike naga inda kike kwanciya kikeso nayi ai basai kinyi haka ba,tun sanda na fara ganinki nasan kedin ta dabance dan Allah kinga inna laure ɗauko kawai ni yau naga ta kaina wallahi har kaina yafara ciwo. "He hehe wannan saurayin yamun magana kallon sa kawai nayi ban ko amsa masa ba yace,gobe a roud 9am kizo zakimun wanki dakuma gyaramun ɗakina ke harma da wordrobe ɗina duka dan tayi kura sosai kallona yake kaman mayun wacin zaki kana wani lashe baki kaman tsohon maya araina nace maye saide kaci kanka kana kallon sa kasan be san kunya ba"banawa maza wanki na bashi amsa da mamaki hajia take kallona da tafa hannu tace"wace daraja ke ga talakan da talauci yama katutu da har ze zaɓawa kansa kalan jinsin da zewa aiki.....   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "13" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1311711488?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=wpYNlAAYQ3IxPeVPRWtm5DyqJzbgM%2FvLx0yMHk%2FK2f8NkjF0ATEJkK3UhEsQPyN83XUn5liQlQV%2BV3QYloUU7dGIDKA9ptqw19b4Ns0leGWo2QY1rSR%2BYKgHDlgsYhPp ___________________ *AUREN WUCIN GADI* Chapter 13 Tabbas maganar tata ta dakeni idan nace banji zafin sa ba to nayi karya,nasake faɗaɗa murmushi a fuskata nace"ayyah Hajia shi daraja dakike gani Allah shike ba wanda yaso bawai dan yafi sonsa bane ba,ya daraja shi kan wasu bayinsa ya gani shin ze gode masa abisa ni'ima da yayi masa ko kuwa ze daukarwa kansa girman kai dakuma jiji dakai dan kawai Allah ya bashi daraja. "To matsassako mai bakin magana kewai wace iriyar yarinyace komai mutum ya faɗa kin tanadar da amsarta dan Allah ni wuce ki bani waje bancika son yawan magana ba amma sai da kikayi yanda nayi harkin samun ciwon kai,ruwa ta dauka ta kurɓa da daura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana mai maida kanta ga kallon tv dake kunne tun ɗazu tashar mbc 2 suka hasko wani american film xmen. Ni made tsuke bakina nayi basma dake kishingiɗe sai aikomun da harara take niko da mun haɗa ido da ita sai nasakar mata murmushi haushi kaman yakarta shiko sokon yayan nata tsaye yayi ya rungumi hannuwan sa a ƙirginsa sai kallona yake dawasu ƙananun idanun sa,har tsayuwan yafara gundurana saboda idanu da suka zubamun su biyu kaman masu son gano wani nakasa a halitta. Dakyar laure ke jan dustbin ɗin kayan zuwa nayi na taimaka mata muka kama muka fito dashi waje can baya wajen famfo mukai sai da muka ajiye taje ta daukomun robobi sai da natara ruwan wankin sannan nazube kayan duka a ƙasa sai ganin laure nayi ta zaro ido cike da tsoro yana cemun"ƴar nan kika zubur da kayan a kasa? kallon mamaki nake binta dashi murmushin nan de nasakar mata nace"Inna laure idan ban zubar a ƙasan ba ya za'ayi nagane waƴan da zan wanke da omo da wanda zanyi da sabulu kinga da wannan tsoron naki dama zuwa kikayi kika anso sabulun da omon zefi,ajiyar zuciya ta sauke tace"kede ina jiye miki fushin hajia a kanki hmmm na sauke ajiyar zuciya nace"aini da fushin tayi wallahi zamma fi jin daɗi daga nan ban ƙara tanƙa waba ita ma bata sake yimun magana ba dan gani take kaman ƙuruciya ke damuna bansan ciwon kaina ba. Sai da naware komai pant da bra duka na maida mata da abunta cikin dustbin ɗin dan na alkawartawa kaina bazan sake wanke pant ɗin mace ƴar uwata ba,wanki nake tuƙuru sai sha biyu da rabi na rana nagama wanki na ƙwashe wanda suka bushe na linke nakai ciki a falo na tatta da hajia cikin kwalliya kaman mai shirin zuwa anguwa saman kugera nasamu na zube kayan akai nace"hajia barka da hutawa a wulakance take bina da kallo sai can tace"wai da mekike takane da bazaki iya rusunawa kimun magana ba?kin wani tsayamun ƙerere a ka kina sakarmun da wannan murmushin naki na rainin hankali,ganin murmushin nan nawa yana ƙular dasu yasani sake faɗaɗawa nace"kinsan abunka ga wanda be sabayin hakan ba hajjaju saide fa hakuri mtssss taja tsuka mai tsayi tace jeki kitchen kice laure ta baki abinci kici kinsan muna da karamci duk wanda yashigo gidan nan bazamu barshi yatafi beci komai ba. Ƴar dariya nayi nace"da girman kugeranki hajjaju saide fa aƙushe nake da zaki bani hakkina natafi da yafi mun wannan tayin abincin naki a guna kinsan ciki kuma ba lalle cimarku ta zamo ɗaya da tamu ta talakawa ba karna zarme naci dayawa cikina ya ruɗe. A harzuke ta miƙe tsaya dan jin abunda nace saurin riƙe kunnuwana nayi nace afuwan hajjaju ban fadi haka dan naɓata miki rai ba,kawai de nafaɗi iya gaskiyana ne amma idan hakan ya taɓaki yi hakuri,dan Allah yanason bayinsa masu hakuri,komawa tayi ta zauna ta ɗaura kafarta saman canter table tace zauna ki matsemun ƙafata inaji ya ɗanmun tsami. Kaman na kai mata mangara haka nakeji dan haka cike da jin haushin ta na zauna ina jamata kafar a hankali har wani lullumshe ido takeyi saboda yanda take jin daɗin sa,ina cikin ja mata kafar basma ta fito cikin kwalliya ta kalleni ta watsar tace"mummy zanje shoppin zaram na miƙe tsaye nace"yauwa sai ki saukeni bakin hanya yamutse fuska tashiga yi kaman taga kashi niko ko akwalata ta bankamun harara tace"wai nice zan ɗaukeki a motata tayi maganan tana nuna kanta"eh na bata amsa a taƙaice kana nadubi hajia mariya dake kaɗa ƙafa nace to hajjaju zan tafi sai abani hakkina dan musamu nasawa a bakin salati kinsan abunka ga talaka sai yafita zai sami abunda ze saka abaka. Yanda nayi maganan ina karkace kai sai kadauka da gaske nake yinta har zuciya niko iya baka ne"ki tafi zan aika miki tace ba tare da ta kallin inda nake ba"haram hajia da kinsan bazaki biyani hakkina ba ai tuntuni da kin faɗamun da mutum yayi magana sai ace talaka wace daraja gareshi amma ansan yanda za'a tauye masa hakkin....kafin na karasa magana a fusace basma ta cillomun 2k tsugunawa nayi na ɗauka banko kalli inda hajia ke zaune ba balle ita dake ta huci kamar wata macijiya na nufi kofan fita na tsinkayo muryar hajiya na cewa"tsiyar talaka kenan murmushi ɗauke a fuskata na juyo nace"yauwa Anty basma na manta ban faɗa miki ba na barmiki raguwar ruwa da omo a can baya ko zaki wanke kunzugunki naga duk sunyi tsotsa shisa nabar miki dan bazan iya kayan ƙazantar nan ba,ƙila ke zaki iya tunda nakine,mutum yakoyi ɓuye sirrin sa kafin yaga rashin darajan wasu wace darajane ga maccen da bata iya ɓuye sirrin ta ba,koda yake.....bara de nayi shiru kawai nasa kai nafita a falon inajin hajiya nace wa wallahi sai naje gaban wannan tsomararriyar uwar taki sannan na cicci ubanki oho de nide nafita laure da taleƙo zata tambayi hajiya abunda zata dafa a ɗari takoma ciki tana mai zaro idonta waje da rufe bakinta da tafin hannunta tare da jinjina rashin tsoran wannan yarinyar da take kasada da rayuwarta dan tasan wace hajia wajen rashi imani.   2:am Alhaji sunusi yamiƙe tsaye ya kalli dandazon mutane da suka halarci wannan taro na ƙungiya sabbi da tshoffi yace"ina mai farin cikin halartanku wannan taro namu na ƙungiya ba tare da ɓata lokaci ba munason ganin duk wani sabon member namu anan,miƙewa sukayi suka zagaye wani ƙaton ƙwarya dake saman wani rami shi baya sama kuma be zauna a kan ramin ba yanade tsaka tsakiya ya umurci ko wanne cikin su da cewa ya yanke hannun sa ya diga jinin sa cikin wannan kwaryar,bamusu sukai bayan sun gama sai suje gaban wani katon mutum dake zaune cikin jajayen kaya sumasa sujjada(wa iyazu billah Allah yakiya shemu da son zuciya)shi kuma sai ya daura wani abu mai kamada gashin ɗawisu a kansu yayi wasu surutai. Bayan sun gama sannan Alhaji sunusi yace barkan ku da shiga kungiyar asoka muna da sharuɗan mu kafin kazama ɗaya daga cikin mu harsai ka cika wannan sharaɗin kun shirya"eh suka amsa masa bai ɗaya da farko dole halartan kowani taro namu koda baka garin dole kazo dan ka halarta,sannan ko wanne cikin ku wajibine ya sadaukar mana da jinin mutumin da yafi soyuwa aransa,kafin yasamu cikin burin sa,mutukar mutum ya cika sharuɗamu shida talauci saide yagani anayi. Fadila tunda taji sai ta sadaukar da jini take jikinta ya dauki ɓari karkarkarkar miƙawa kowa wani kogo akai duka amsa sukai amma banta ita data lula duniyar tunani da zullumi"kee taji wani kakkausan murya daya sata firgita saboda amsawa da dajin gaba ɗaya yayi karɓi kisha aka faɗa cike da bata umurni kin shigo cikinmu bake ba fita tunda kintsani talauci muddin kika kawo mana wasa cikin lamarin mu jinin iyayenki ya halasta garemu......wani irin faɗiwa gaban ta yayi madadin ta ambaci sunan Allah kawai sai jin bakinta tayi ya ambaci sunan Aisha saboda tunawa datayi da maganan su rannan"AISHA AISHA AISHA taji wajen yaɗauka take tazube wajen sumammiya.     ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: https://www.wattpad.com/story/332566231?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=kkjsc95XxwiP3GV30DMUT103FcdhIcmpFhv%2FOjjfixlNbrYk9G2UUyWdkiqmWi8oz%2B%2BDuDjjl4lySgoa5jMhbh0c39A%2FEeHzTt7KvJQ0dMRPEDc3AE2NLi7cL8gZtM7P ______________________ *AUREN WUCIN GADI* Chapter 14 Daidai wannan lokacin da duk wani mahaluƙi yana ga makwancin sa harta ga tsuntsaye,sai masu neman duniya dakuma bayin Allah salihai masu ganawa da mahaliccin su sune kawai suke a farke, Daddy ishaq dake ɗaura alwala saboda yin nafila kaman yanda yasaba,tar tsatsin wuta yagani a sararin samaniya kaman ana kesta wuta tsai yayi yana kallo sai can yaji dajin duka na amsa sunan Aisha da muryoyi ma bambanta wani irin faɗiwa gaban sa yayi duk da bashi da tabbacin Aishar tashince amma jikin sa yabasa akwai abunda ke faruwa,saurin ƙarasa alwalan yayi ya tashi ya fuskanci gabas yafara gero nafila saida yayi raka'a huɗu sannan ya ɗaga hannu sama idonsa na zubda hawaye yace"Ya Allah gawata baiwarka tana bukatar taimakon ka ya Allah kaceci rayuwarta kakuma tsareta daga hannun waƴan nan azzaluman haka yarinka ƙwararo addu'a yana hawaye dakuma roƙon Allah yakawo karshen su Alhaji sunusi da iri irinsa. Aisha ina baccina mai daɗi kawai sai ganina nayi tsakiyar wasu mutane masu jajayen kaya sun zagayeni ko wannan su hannun sa riƙe da candil dukkan su sun haɗa baki suna karantu wasu surƙullen su da ba gane wa nake ba, Innalillahi Allahumma ajirni hasbunallahu iri irin wannan addu'oin su suka zomun baki kaman yanda suke karanta surkullen su da karfi haka nima nakara ƙaimi ina ɗaga muryata kaman maƙogorona ze yage nakeyi ga wani irin tsoro daya lulluɓeni wanda ya haddasa mun rintse idona dan banason nabude idona nayi arba da waƴan nan halittun dan nama dauka ko mutuwa nayi mala'iku suka zomun sai kuma natuna ai mala'ikun Allah masu tambaya cikin kabari ba da irin wannan suffa suke zuwarma mutum ba,kaman yanda aka koyar damu a islamiya to ina ne nan menayi musu da suke neman halakani,lahaula wala ƙowata illah billahil alim....wata murya ce tadamun tsawa muryar mara daɗin sauraro yana cewa zaki rufe baki kidena waƴan nan addu'oin da kike ko kuwa? Ahmad kwance yake saman royal bed dinsa yayi daidai sai bacci yake bakajin komai a dakin sai ƙaran ac dake aiki,da alama yanajin daɗin baccin nasa dawani irin zabura yatashi sakamakon wani mummuna mafarki da yayi jikin sa yajiƙe sharƙab da zufa kaman wanda yayi wanka dafe kansa yayi da hannun sakamakon sarawa da kan keyima sa. Anna zaune take tana azkar bayan ta sallame nafila kafin tatashi ta sake wani sai ganin Aisha tayi cikin wani irin yanayi da bata ɓace saninta da shi ba,jikin ta sai ƙirma yake gawani irin gumi da ta haɗa har ɗiga yake,amma duk da halin da take ciki bakinta be fasa kiran sunan Allah da addu'a ba,ɗaga kanta Anna tayi ta ɗaura saman cinyarta tashiga kiran Aisha Aisha amma ina Aisha bata masan Anna nayi ba,ruwa Anna ta jayo tana shafa mata a fuska idonta na tsiyayar da ƙwalla kira take ya Allah kaine gagara gasan masu gasa baka ɗaurawa bawayinka abunda bazasu iya ɗauka ka ba,ya wahabu ga ƴata kakare mun ita da kariyar ka ya samadu karka basu ikon cutar da baiwarka ya Muzambil kakarya alkadarin su kamaida musu da sharrinsu garesu,bamu cutar da kowa ba kar kabasu iko akan bayinka ya zul-jalalu wal-ikram kakawo karshe waƴan azzaluma sai kuma ta ɗauki qur'ani tafara karatu tanayi tana kuka ba komai take tunawa ba sai mijinta abun alfarinta ta rasashi asanda yafara irin wannan abunda tagani ga Aisha. Sake kwanciya Ahmad yayi bayan yasha ruwa yayi addu'a kaman yanda manzon rahma(s-a-w)yakoyar mana ya canja gefen sa saide baccin nasa beyi wani nisa ba yasake yin wannan mafarki wannan karon zaburan da yayi har yafi na farkon tashi yayi zaune saman bed din sa yashiga tariyo abunda ya gani a mafarkin nasa ga dukkan alama Aisha na bukatar taimakon sa. Wai meyasa yake damuwa da yarinyar ne tun ranan da yasona ganin ta,wacece ma ita tukunna me wannan mafarki yake nufi. Mafarkin sa na farko Aishan ya gani cikin wani daji mai matukar duhu mai yalwan bishiyu ana janta a ƙasa tana kiran taimako jama'a duk da ba alaman wani mahaluƙi dake rayuwa a wajen,hakan be hanata neman taimako ba, Jin ihun nata yasa shi zuwa wajen da gudu saide kafin yakaiga karasowa gareta tuni an fizgeta anyi gaba da ita,baya ganin kowa sai ita dake ƙasa tana neman abunda zata riƙe ta tokare amma ba komi wajen sai ganyaye. a haka har suka kai bakin wani rami yana miƙa hannu ze riƙota yaji an fizgeta da karfi ta rubta ramin mai matukar duhu tana kira ya ahmaaaad. Sai kuma na yanxu wai yana zabe bakin ramin gwiwa a ƙasa yana kuka sai ga wani mutum cike da kamala ya dafashi yana cewa dashi"kaine wanda ze ceto rayuwar yarinyar nan daga hannun waƴan nan azzaluman amma saika jajirce kuma bazaka sami yin hakan ba,sai idan ta kasance mallakinka wato matar ka ta sunna. Gefe guda kuma sai ga daddyn sa yana cewa karka yarda dashi son karya yake maka karɓi wannan zoben kasaka,shikuma wancan mutumin cewa yake karkasa wannan zoben ita ma yarinyar sun saka mata irin sa kayi ƙoƙarin ganin karabata da shi,daddyn sa kuma sai karyarta mutumin yake tare da cewa my son kasande bazan maka karya ba dan haka karka yarda da wannan mutumin mugune gardama ta ɓarke tsakanin su daidai nan yata shi,a fili ya furta komade mainene wannan mafarkin nawa yana da alaƙa da wannan yarinyar to ita kuma ɗaya yarinyar dake laɓe bayan bishiya ita din wacece?     ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "15" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1312875730?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=EEYRgzwj3FAWdivrfqVCXnioADqgLs6PB0Yn3yZt%2FcWrXTwWZ4xt99l5icplMwBfbHg5XLjk2Myd9hi4pktca5eSi7H1EnR%2FVrL06eTfTvTKSC3dV6X7yS33%2BtGhqg9g ____________________ *AUREN WUCIN GADI*   Chapter 15 Kinran sallan da akasoma shi yadawo da hankalin Aisha ta sauke nannausan numfashi tana gyara kwanciyarta,sai a sannan Anna dake zaune itams hankalinta ya ɗan kwanta tabari idan anyi sallan asuba taza tambayi Aisha taji. Ahmad shima anashi ɓagaren hakane kiran sallane yata dashi daga zaunen dayake yanufi bayi ya dauro alwala raka'atul fajir yayi kafin ya tashi yafita zuwa masallaci bakin get sukaci karo da daddyn sa zai shiga gidan da motar sa,tambayan kansa yayi daga ina daddy yazo a wannan lokacin,nufar motan yayi saide Alh badamasi be bashi wannan daman ba dan be tsaya ba yaja motarsa zuwa cikin gida ganin haka yasa Ahmad saurin fita waje dan jin antada iƙama. Sai wajajen karfe shidan safe Anna ta tadani nayi sallah ko azkar banyi ba nasake ɓegirewa daga wajen na kwanta karfe goma natashi saida nayi wanka Anna tabani raguwar kunun koko da ƙosai da suka ragemun nasha nasake kwanciya ina cewa"Anna wallahi jikina duk ciwo yake mu. Shafa kaina tayi da hannu tace"jiya wani irin mafarki kikayi daya kin firgitani sosai wallahi na tsorata sosai da yanayinki na daren jiya,mamaki ɗauke saman fuskata na dubi anna nace"ni kuma"eh tace dani ɗan jim nayi sai kuma namiƙe zaune kaman mai tunani saide nakasa tunano kamai. Hajia mariya zaune suke da kawayenta biyu da suka kawo mata ziyara ɗaya mai suna karime tace"gaskiya mariya kinyi sake dayawa taya zakice har yau kunkasa shawo kan Ahmad yace yanason basma sai itace ke hauka akansa amma kallo bata ishesa ba gaskiya sai ki tashi tsaye waye Ahmad yo ko uban sa badamasi idan kinason a karkato da hankalinsa kan ƴarki abune mai sauki amma kin tsaya wai wani ahmad yana juya miki ƴa kaman waina a tanda,hmm ta sauke ajiyar zuciya tace"wallahi ƙawata Ahmad yawuce duk inda kikayi zato dan shu'umin kansane shima, Sai kuma hajia balki ta amshe yo kema ai saiki nuna kin fishi shu'umanci tun tuni na faɗa miki kishirya muje wajen bokan nan dake amma kinƙi dan kina ganin kaman kin samu duniya"yo wace duniya tasamu karime ta amshe dacewa ai namiji tamkar Zuma yake saida wuta,ai kullum sai kina service dan inganta aikin ki akansa bawai kitsaya tsakaka baki bude kina ganin kin riga kingama dashi kawai baki ankare ba saide kijiki a salansa wata tayi miki wuf da miji. "Kayya karime bar faɗin haka wannan sai kisa jinina hawa wallahi,dariya suka fashe dashi harda su shewa nan suka saka jibi zasuje wajen boka na gangare kafin su shirya zuwa ogomosho can garin yarbawa. Basma fitan da tayi a gida saida ta biya ta ɗauki ƙawayenta fa'iza da surayya tukunna suka wuce wajen shoppin saida sukai shoppin tamusu sayayya kafin su wuce shan ice cream,zazzaune suke bayan ankawo musu order da sukai suna cikin sha fa'iza ta kai dubanta ga basma da ta shagala kallon wasu miji da mata cike da sha'awa take kallon su ta shagala sosai da kallon nasu saida surayya ta tafa hannun ta da karfi sannan tadawo da kallon ta kansu"sun burgeki ko? "Wallahi kuwa har imagin nake wai ni da Ahmad ne dakuma ɗanmu,ko sai yaushe zan sami kulawa da nake bukata daga Ahmad? Ta kare maganan ta cike da rauni dafata fa'iza tayi tace kawo kunneki ta raɗa mata wani abu danima kaina banji mai tace ba,sai gani nayi basma ta ɗan gwalo ido waje tana kallon fa'iza tace"kina ganin wannan shawaran zeyi"ware mata fici ficin idonta tayi da cewa"mai ze hanashi yuwa. Aisha zaune muke da yamma ina taya Anna tsintar shinkafa muna taɓa hira saide duk yawancin hirar tamu ya ta'allaƙane kan wajen aikin da nasa nan na gyara zama nace"wallahi Anna kingade kwanan nan nafara aiki a wajen amma gaskiya ana ha'intan mai wajen. Kallona Anna tayi tace"taya keda bawani jimawa kikayi sosai a wajen ba. Hmmm"Anna kenan sai kace baki sannin ba,wajen lura da abu dakuma riƙeshi cikin ƙwakwalwata hmmm da ace yau zanga wannan abokin Abban mu mai yawan zuwa garinmu wallahi zan iya ganeshi dan na haddace hoton fuskansa a kaina wallahi mutumin mugune Anna. Bansan nayi wannan magana ba saida Anna tace"kintaɓa ganin yana wani muguntanne Aisha? Wayyo Allah kaga matsalan tsuɓutar baki kenan nafaɗa araina amma a fili sai nace"Anna kece kawai baki sani ba amma duk zuwanda yake akwai abunda yakeson Abbanmu ya bashi shi kuma Abba yaƙi bashi wannan abun shine rannan cikin fushi naji yana cewa Abba zaka gani tunda nabika da lallami kaƙi. Sauke ajiyar zuciya Anna tayi zatayi magana kenan saiga sallamar fadila cike da murnan ganin juna muka rungumi juna har ƙasa ta zauna tana gaida Anna amsa mata Anna tayi da sakin fuska da tambayarta yasu mamarta nan tace kowa lafiya,ledar hannunta mai ɗauke da kayan marmari ta miƙawa Anna tace happy hourn nasu khadija da mubaraq ne godiya Anna tamata sannan muka ranƙaya ɗaki da ita. Kallona tayi cike da rauni tace"ƙawata nafa samu wannan aiki harma nafara zuwa jiya"wow na tayaki murna kice kin kusa zama hamshaƙiya tawan nafaɗa cike da zolaya dariya tayi tace"kwarai kuwa kaman kuwa kinsani tace dani tana miƙomun wani zobe mai shegen kyau da ɗaukar ido kallon zoben nake azahiri amma abaɗini tunanin nake kaman nataɓa ganin wannan zoben,take jinane ya ɗauki rawa tunawa da nayi da mafarkin da nayi jiya.   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "16" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1313627113?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=C9s4QlcX9CBdZ3byiKnCqNHqT1QN1dhU2QILjjdlsrDsv9olvu8YqXvRiVgmEKnLS1h2lAJttNY1ia1DDZ5Nxx8DUbmIwDuZTYxu4gfP1QRFf36u1jc0cEDuy9e4kuNS ___________________ *AUREN WUCIN GADI* Chapter 16 Ki karɓa mana kintsaya kallo harda rawan jiki ta faɗa tana miƙomun zoben,ni kuwa kallon sani nakewa zaben aina wajen waye wannan ne bazan iya tunawa ba. Karɓa nayi da bismillah sauri shammatata tayi ta karɓe tana cewa"kinga mikomun hannunki nasaka miki,hararar ta nayi a wasance nace kinjiki da wata batu saurayina de zai samun zobe a hannu ba wai in miƙa hannu na haka kawai kisamun zobe ni ƴar daɗi zobe ina kare magana nayi saurin warce zoben ina sawa a yatsana bakina ɗauke da bismillah kuwa dumm gaban fadila ya faɗi dan an sheda mata karta bari na anbaci sunan Allah kafin nasaka zobe take wani irin zufa yakaryo mata,niko ko kula da yanayin ta banyi ba,nashiga juya hannuna ina yaba kyan zoben da gudu nayi waje ina zuwa na faɗa jikin Anna. Shafa kaina tayi tana"kai Aisha kede kan bakya girma goɗe goɗe dake zaki fadamin jiki haka dariya nayi nace"Anna inasonki kece komaina kece duniyata jarumar uwa ɗaya tamkar dubu"kai Aisha bakinki kullum baya gajiya da fadi abu ɗaya"Anna kenan taya zai gaji ai sonda nake maki baki bazai iya fadin irin sa ba,khadija da mubaraq suka hada baki wajen cewa"Anty aisha mufa?"ai kune gaba gaba bayan Anna dariya suka fashe dashi cike da farin ciki da murna nace Anna kinga ƙawar amana ta sayo mana zobe ni da ita iri guda kallon zobe Anna tayi tace masha Allah Allah yasanya alheri yakuma haɗa kanku yabar zumunci"amin muka amsa harda fadila da tafito a dakin hannunta riƙe da wayar ta tace Aisha zo kirakani ku gaisa da shi. "da to kawai na amsa dan dama da hijabina ajikina muka fito tare daga cikin gida motarsa na tsaye bakin layin mu babban mutum ne kaman a girme yama girmi baban fadila amma saboda ganin kuɗi wai wannan ne saurayin ta,gaidashi nayi cikin sakin fuska ya amsa da tambayata ummana na amsa da lafiya"Aisha ko gyaɗa kai nayi murmushi yayi yace ai kullum sai kawarki ta ambaci sunan ki lalle tana ji da ke"nima murmushin nayi ina kallon fadila nace"ai nima ainaji da ita dariya yayi sallama nayi musu har najuya yatsaida ni yama miƙamun kuɗi yace ki sayawa ƙannenmu sweet godiya namasa na karba nawuce na barsu tsaye jinjine da mota fadila taso yimun tattaki nace gaskiya kikoma kin bar mutum tsaye dole ta koma gunsa nikuma nawuce gida. "fadee baki da hankaline ko kin mance da sharaɗin shugaba ne?bayan wucewar Aisha yafara yima fadila fada kaman kuwa zeyi duketa, Fadila tayi rau rau da ido tace"wallahi duk shammatar ta danayi amma bansan yanda akai haka ta faru ba. kuma kai kanka shedane hana Aisha ambaton Allah abune mai matukar wuya kade gani koshi kansa shugaba nasan zemun uzuri zuwa gaba. Huumm ya sauke numfashi yace"saura aiki na gaba ki kula wallahi kar asamu kuskure idan ko aka samu kema kinsa sauran kinde ga yanda shugaba yakewa iyayen gidanmu faɗa bare kuma ke wallahi kikai wani kuskure keda yin kuɗi saide gani daga nesa amma bade kiyi ba. Saurin katsashi tayi tana cewa ya kekemun bakine dan Allah daga yin kuskuren farko,hmm"ai ke kike ganin hakan amma shugaba besan uzuri ba kinde ga yanda ranan yake ta balbale Alh sunusi kan wani kuskure da yayi shima kan wani mai irin hali kamande wannan ƙawa taki danko ansha kawo shi matsafa amma wallahi saboda ambaton sunan Allah da kira'a idan yafara kaman a harami har bakin sa ansha ɗaurewa amma baya fasa ambaton sunan Allah a zuci haka har za watsa zaman batare da ankai matsaya guda ba,yau kimanin shekaru takwas ana azabtar da bawan Allahn nan wallahi haryau bata canja zani ba. Dan shugaba yace a kyale shi kawai idan an matsa kungiya zata iya tarwatsewa. Ahmad koda yadawo daga masallaci kwaciya yayi saman sofa dake cikin bedroom dinsa mafarkin da yayi daren jiya shi yarinƙa zuwar masa kaman jin abun yake kaman azahiri haka yafaru ba mafarki bane, Yana cikin tarawa da kwashawa hat bacci yayi awun gaba dashi be tashi farkawa ba sai wajajen karfe 11am bakinsa ɗauke da salati yata yafaɗa toilet wanka yayi yafito ɗaure da towel a ƙugunsa yana yane gashin kansa da karami mayuka masu daɗin kamshi yafashe jikin sa dasu sannan ya saka kananun kaya ya feshe jikin sa da turaruka yanufi main falo dan yunwa yakeji bana wasa ba. Sallama ɗauke da bakinsa yashiga ya tadda amminsa zaune tana kallon sunna tv,maza yayi ya ɗaura kansa saman cinyarta kaman wani karamin yaro yace"ina kwana Ammi shafa suman kansa tayi tana sakin murmushi tace"lafiya lau Ahmadi fatan de yau lafiyanka kayi irin wannan bacci? Toro bakin sa ya ɗanyi a shagwaɓa yace"kwanciyane da banyi da wuri ba jiya yana faɗin haka yace"Ammi yunwa nakeji, Murmushi ɗauke saman fuskarta tace"oya tashi muje nabaka abinci tare suka iso dining table tayi savin ɗinsa saida ya ƙurɓi black tea kaɗan sannan yace"Alhajin ki jiya be kwana a gida ba hala lafiya fitan dare haka? Fuska da alaman damuwa tace"ahmadi wasu lokuta nima kaina abunda Abbanku yake yana damuna ace mutun kullum idan za ayi meetin sai karfe biyun dare kaman wasu matsafa danayi magana ya hauni da faɗa,shiru ta ɗanyi jin kaman takun sawu suka juya dan kallon mai tafiya illa kuwa shiɗinne"gulmar me kuke kun haɗa kai da ɗanki? "Ina kwana Alhaji "Lafiya Ahmad yau baka fita bane? "Eh yau lahadi ya amsa masa a takaice. "Zubomun abincin mana Ammin yara kintsaya sai kallona kike kaman kinga wani sabon halitta a gabanki. Hmmm ta sauke ajiyar zuciya yasan abunda takema shima kuma har ga Allah bayaso yana ɓata mata rai shi kansa besan yadda akai ya tsinci kansa cikin wannan ƙungiya ba tsomo tsoma dan ma shi ba kowani irin sharaɗin su yake bi ba. Dan a cewarsa bashine yashiga cikin su ba susuka jashi. Bayan sun gama sun koma falo da zama,Alh badamasi cikin tsare gida yadube su yace"dama inason magana daku,gyara zaman su sukai suna fuskantar sa,ajiya zuciya yasaauke kana yace"jiya mun tsaida auren yaran nan,a zabure Ammi ta miƙe ta zuba masa ido karon farko daya tsinci kansa da jin shakkarta ya haɗiyi ƴawu mai kauri mukut,yi hakuri ki zauna muyi magana mana ma'arufa ya kira sunan ta cikin sanyin murya. Nunashi tayi da hannu tace"zaman me zanyi saide inaso kasani darajan ɗana yafi asaka ranan auren sa gaban mushirƙai waƴan da suka kwashe kayansu a gaban ma'aiki,shin baka da ƴan uwane koni bani dasu shi uban yariyar da uwar ƴa basuda ƴan uwane da zaku rasa inda zakuyi maganan aure sai karfe biyun dare gaban matsafa to wallahi da ahmad ya auri wannan yarinyar kwara yayi auren wucin gadi a mutunce"enough is enough ya daka mata wani irin tsawa ranshi yakai ƙololuwar ɓaci cikin kakkausan murya yace zancen banza kenan aurene ba fashi nan da wata guda sannan ɗanki shine wanda ze tare gidan surukansa dan yarinya bazata tare a gidan sa ba,wani dummm sukaji maganan nashi katamkar saukar arado.   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Https://arewabooks.com?id=63dbe9c0e999537d82ef5685 Kuyi followin ɗin ta wannan link dake sama☝ Chapter 17 Shirune ya ɗauke su na ɗan wani lokaci kafin Ammi tayi karfin halin cewa"wallahi Alh baka isa ba,tun tale tale ba inda ka taɓa ganin inda ango ya tare gidansu amaryar ,a al'adarmu ta malam ba haushe balle ace yau kan ɗana za fara tana kaiwa nan cike da fushi tazo ta wuce sa fuuu kaman wacce zata tashi sama saboda ɓacin rai da take ciki. Bayan Ammi ta wuce rai a ɓace Alh badamasi ya kalli ɗan nasa da bai gane yanayin sa ba yace"kanaji hajiarku tana ɗagan murya ko?shiru ahmad yayi masa dan shi kaɗan yasan abunda yakeji ganin be amsa shi ba yasa a ɗan hasale yace ina magana kayi shiru. "Yi hakuri Alh amma gaskiya ni yarinyar nan bata cikin tsarin irin macen da zan aure balle takaini da tarewa gidan su. Yana kai karshe da maganan ya miƙe jiki ba gwari yanufi fita daga falon. "Koma ka zauna yace da shi cikin ɗaga murya ba musu Ahmad ya koma ya zauna daga inda ya tashi,kallon sa Alh badamasi yake amma ya rasa ta inda ze soma dan haka hannu yasa cikin aljuhun rigarsa ya fito da wani karamin box mai kyau da ɗaukan hankali ta ajiye a gaban Ahmad ɗin batare da yace komai ba. Shima ahmad a nashi ɓagaren kallon box ɗin yayi ya kauda idon sa"ɗauka mana kagani ina tayaka murnan karin shekara wani irin zabura Ahmad yayi jin abunda mahaifin nasa yace dan tunda yasan kansa zai iya cewa Alhajinsa be taɓa yi masa kyauta dan ya yaƙara shekara ba sai yau. Ɗauka yayi cike da zumuɗi yana buɗe box ɗin zaro idonsa yayi yana kallon zoben cirowa yayi daga cikin box ɗin ya shiga jujjuya zoben a hannun sa yana kare masa kallo kaman yasan zoben amma aina amma tabbas yasan zoben nan kuma yayi masa kyau sauri sawa yayi a hannun sa yana dariya yayi huggin mahaifin nasa yace"love you daddy you're the best dad in the world,dariya shima Alh badamasi yayi cike da jin daɗi sai da yabari ahmad ya gama murnan zoben sannan ya ɗauko masa magana basma. Cikin kwantar da murya yace yanzu ɗana ba zakama mahaifinka wannan alfarman ba,haba my son so kake abokaina sumun dariya suga kaman ban isa da gidana ba,ita ma ta mace ta yarda zatayi biyayya amma kai da mahaifiyarka kuke neman kunyata ni da son nunawa duniya ban isa daku ba shikenan tashi ka tafi na tabbata da khalid ne koda bayaso ze amshi maganata da hannu bibiyu amma kaida na haifa bazaka iya faran tamun ba. Kasan tsakanin ɗan da mahaifi sai Allah nan take ahmad sai yaji jikin sa yayi sanyi ganin yanda mahaifin nasa yayi narai narai kaman ze zubda hawaye. Saurin duƙowa yayi gaban mahaifin nasa ya riƙo hannunsa yace"Alhaji na yarda zan aureta amma saide gaskiya bazan tare gudan su ba,saide ita ta tare kamar ko wacce yarinyar da a kaiwa aure amma zance gaskiya banga abunda ze sani tarewa wancan gidan ba. Fadila ta kallo Aisha tace"kawata ki rakani saloon mana aima tare"kai fadila ban taɓayi ba kuma banda ra'ayi kede kawai idan rakiya kikeso na rakaki tunda bani da aikin da zanyi yanzu. Cikin tsigar zolaya fadila tace"wankin ɗan gidan hajia mariya ba yau bane ba?dariya suka kwashe a tare Aisha tace "tab ai wannan ba wanki yaso ai masa kwartonci yakeson yimun dan naga idon sa a tsastsaye suke wallahi. Shiryawa Aisha tayi suka fito daga ɗanki aisha tace"Anna zan raka fadila wankin gashi daga can zan wuce kasuwa nayi mana ƴan sayayya"a dawo lafiya ku kula da kanku cewar anna tana binmu da addu'a har mun kai bakin kofa muka tsinkayo muryan maman salmanu na cewa Aisha ɗiyar albarka ga murtalata biyar idan kin biya ta kasuwa kisayomin makani da to kawai na amsa na karɓi kuɗin muka fita napep shata fadila taɗauka har wajen wankin gashi tun daga bakin ƙofar shiga wajen nasare na tabbata wajen bana ƙananun mutane bane ba. Ashe a waje banga komai ba abun kallo yana ciki saida muka shiga ciki tunkun nan kan kallo harda na kauyanci nan da nan a kasoma wankema fadila kanta da wanke ƙafa bayan da batayi dani ba,nace ni ban shirya saka mai a kaina ba dan dole ta hakura badan taso ba. Wajen sun iya tarɓa customer dan sun kawo mana ruwa mai sanyi na gora da kuma maltina sai da mukai sallan la'asar anan sannan muka fita,bansan ko nawane cajis ɗin da akai mata ba tunda ATM ɗinta ta bada mamaki fal cikina amma banyi magana saida mukaje kasuwa tun daga kan siyayya da naga fadila nayi kaman bata san zafin kuɗi ba nasare ainun to ina fadila ke samun waƴan nan maƙudan kuɗaɗe haka kode fadila ta soma bin maxane tunda tana da masifan son ƙudi ba abunda ba zatayi ba dan tasamu kuɗi saurin kawar da wannan tunanin nayi daga raina saida muka gama sayayya muka fito mun soma tafiya na dubeta nace"kawata zan faɗamiki wani abu idan yasosa miki rai kiyi hakuri amma kinsan de bani da ƙawa aminaniya ƴar uwa sama dake ko,shiru na ɗanyi dan jin me zatace itama shirun tayi tade maida hankalin ta kaina. Na cigaba da cewa dan Allah kar halin da muke ciki na talauci yasa ki canza halayanki masu kyau dakuma ɗabi'unki dana sanki dashi"me kika gani Aisha?ta tambayen fuskanta sakin hmmm na sauke goron numfashi nayi kana nace "fadila nifa ba yarinya bace irin wannan sayayya da kikayi ko kudin wanke kai dakika biya abun tambayane gareni tunda nasan ba inda zaki sami waƴan nan kuɗaɗe haka. Dafani tayi tace"kwantar da hankalin kawata ai kinsan nafara aiki ko tace dani cikin son na yarda da ita,murmushi nayi ina girgiza kaina nace"fadila wannan kuɗin da kika kashe ai yafi karfin kudin albashinki sannan fara aikinmu daga ke harni yau ko sati biyu bamu rufaba taya zabaki kudi haka fadee haba ƴar uwa dan Allah kar ruɗin duniya ya debeki kizo kina kinsani daga baya. Kin sande hakkina nane....."dakata Aisha tace dani cikin karaji da ɓacin rai ban taɓa sanin ba kyason cigaba na ba aisha sai yanzu saurin katseta nima nayi da cewa"haba fadila ki fahinceni mana ita ma saurin dakatar dani tayi kancewa"bazan fahince ki ba aisha na dauka zakifi kowa farin cikin ganina cikin canjin rayuwa amma sai gashi kece wacce kika fara nuna kyashinki akaina dan me yasa kika ga canji a tare dani cikin ƙanƙanin lokaci ko?"wallahi ba haka bane fadila dan Allah ki fahinceni nan ta hau tsurfamun masifa tarufe ido tacimun mutunci har hankulan mutane ya dawo kanmu wasu dayawa suka rinƙa nuna hasada nake mata har wani matashi na cewa ai mutum mugun icce bazaka taɓa sanin masoyinka da maƙiyinka ba har sai wani abun yasameka yanzu duba ƙawarki amma take nuna hasadan ta akanki kai tirr da masu hali irin naki dayawa sukai tamun tofin ala tsine waƴanda basusan kan zance ba. Ban taɓa fuskankan kunya da tozarci irin ta yau ba,bansan sanda hawaye ya gocemun ba kuka nake riris dakyar na iya bude bakina bace"fadila ni kika ciwa mutunci atiti ko bakomai lokacinki ne amma karki manta karkice ban faɗa miki ba duniyace Allah yabada sa'a nagode bisa cimun mutunci da kikayi saide kisani ko kaɗan kinsan abun duniya be rufemun ido ba,balle nakai ga jefa rayuwata data iyayena cikin wani hali kisani duk abunda kika zama babu wanda besan tushenki ba saide wanda besan suwaye iyayenki ba nabarki lafiya. Na juya ina goge hawayena da suka kasa tsayuwa nakasa yarda wai yau nice fadila tama haka a baynan nasi haka innalillahi nashiga maimaitawa wannan matashin saurayin zai mun kauɗi na ɗaga masa hannu nace"malam ba ruwanka dani baka sannni ba haka bansanka ba,ita wacce kakeson zama ɗan koron natama basanin ta kai ba,wai menene matsalarka shin baka da aikin yine sai zaman kashe wando jibeka wani gaja dakai sai tsamin baki kake kabi ka dami mutane da kaudi sai kace kai kafi kowa baki da iya magana ko banza tare kaganmu da ita sannan anguwarmu ɗaya kaifa?ina kaiwa nan nabarshi baki buɗe matasa yan uwansa nata mishi dariya na tari abun hawa nau tunda na hau napen dinnan ba abunda nake sai aikin rera kuka na kasa yarda fadila wai ni fadila tawa haka yau itace tamun haka a titi innalillahi shine kawai abunda bakina yake iya maimaitawa.....     ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Https://arewabooks.com?id=63dbe9c0e999537d82ef5685 Kuyi following dina ta nan domin samun wannan littafin daga farko. Chapter 18 Zan iya cewa tunda na taso ba taɓa tozartani irin wanda fadila ta mun yau ba,wai shin ina soyayya da mukewa juna yake ina kauna dake tsakanin mu ina aminci da mukewa juwa menama fadila wanda ta zaɓi yamun haka sanin ba mai bani amsa yasani goge hawayena ina mai kokarin tsaida kukanda ke tasomun tun daga ƙasan zuciyata har muka ƙaraso anguwan mu sauƙa nayi nami ƙawa mai napep ɗin kuɗi sai cemun tayi ai wanda ya tsaidashi yabada kuɗin godiya namasa duk da bansan wanda yake cewa yabada kuɗin ba. Sai da natsaya bakin ƙofan gida kaɗan na daidaita nutsuwata sannan nashiga cikin gida bakina ɗauke da sallama khadija dake alwalan sallar magariba ita ta amsamun sallama danayi"sannu da xuwa anty aisha, ""Yauwa khady ina mubaraq?"yaje sallah masallaci ta bani amsa. "Yauwa idan kigama alwalan ɗauki wancan ledar ki miƙashi ga maman salmanu da to amsamun ni kuma na dauki buta alwala nayi nashiga daki na shimfiɗa sallaya na tada sallah. daga ni har Anna ba wanda yatashi saida mukai sallan isha'i sannan add'oin neman tsari na jima ina addu'an neman sassauci kan abunda nakeji a cikin raina dan zuciyata namun zafi har wani irin turirin zafi nakeji,Kasa cin abincin nayi da zaran nakai abincin bakina sai abunda yafaru dani dazu ya faɗomun daga karshe hakura nayi da na wanke hannu na nakoma gefe na zauna,a tsanake Anna ta dubeni tace"lafiya naga bakici abincin ba? Ɗan murmushi yake nayi nace"lafiya anna kawai banajin cin abincin ne Allah ya kyauta tace. Muna cikin hira saiga maman fadila kaman anjehota ko sallama babu kallon ta Anna tayi tace"a'a Rabi kece lale marhabin shigo daga ciki mana...dagawa Anna hannu tayi tace"banason munafinci ai wallahi maman aisha nayi mamaki dama bazaka taɓa sanin masoyinka ba,sai abu yasameka wani irin taimakone bamu muka ba arayuwa haka fadila zata tasani gaba tasa na zubo muku abinci ta dauko ta kawo muku amma saboda baƙin hasada da butulci irin ta ɗan adam shine Aisha zaki rufe ido kiciwa fadila mutunci saboda kawai Allah yarufa mata asiri tasamu aiki mai gwaɓi,to wallahi ahir ɗinku daga ke ha mahaifiyar taki idan ita ke aikoki wallahi wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa. Banzaye dangin tsiya wayasan asalinku wama yasani ko saida aka gama yawun dandi sannan nitsuwa tazo ma akaxo inda ba ba wanda yasanku kuka ɓoye kanku idan ba haka ba ai duk ɗan halas yasan halacci wallahi,tunda tafara surfa masifa ba wanda yace da ita ci kanki daga ni har Anna sau kukan baƙin ciki daya kubce mun nasan nice silar komai da ke faruwa yanzu,da nayi shiru da bakina da ba wanda ya isa yaciwa mahaifita mutunci haka ba tasan hawa ba bata kuma san sauka ba,anzo har gida ana ci mata mutunci ni kaina mamakin yanda fadila ta iya lauye zancen ta maida lefin kai kawai nake banyi mamakin rashin mutuncin mahaifiyar ta ba,dan kowa dake anguwar nan ya kwana da sanin idan tatashi masifa rufe ido take taciwa kowa mutunci. Ahmad Ya kalli ammi da lulun idon sa maikama da wanda yakejin bacci yace"dan Allah ammi kiyi hakuri kinsan ke kaɗaice farin cikin mu...katsesa tayi da cewa"amma ahmad kai baka ganin abunda Alhaji yakeson yi kaman rainane da kuma zubar da mutunci yake neman sayowa kansa,ko so yake mutuncimmu yazube a idon duniya in ba haka ba Ahmad dame Alhaji sunusi yafishi da zaice saide kai ango katare gidan sa gaka ga ɗiyarsa wace irin rayuwar aure zakuyi a gidan ɗaya da surukai ga ɗaki ga ɗaki idan ba dawata manufa aka shirya yin hakan ba. "Ni de dan Allah ammi kiyi hakuri banaso kusamu tsaɓani da Abba akan wannan magana dan Allah yakare maganan kaman ze saka mata kuka,guntun murmushi da bekai ciki ba tayi tace"shikenan zanyi hakuri amma fa saboda kai bawai dan Alhajin naka da abokin nasa dan sunfi karfina bane ba..da sauri Ahmad yace naji saboda ni Ammi shi duk duniya ba wanda yakeso kaman mahaifiyar sa idan kacire soyayya mahalicci data ma'aiki (s.a.w)to cikon na ukun ammin sane dan ko mahaifinsa saide yabi bayan Ammin sa. Amma da sharaɗi maganan ammin shi yadawo dashi daga duniyar tunani da yaɗan lula zuba mata ido kawai yayi tace"zaka auri zaɓina ita ka ajita nan ita kuma matar son sai kabita gidan su tunda kunyarda zuciya kare yacinye. Wani irin zabura Ahmad yayi dan beyi tsammanin jin wannan magana daga bakin Ammin nasa ba,"pls Ammi yace damuwa fal ransa"don pls me ahmad idan kaso nabar wannan magana tasha ruwa ta lafa ba tare da kowa yasan sirrin gidan mu ba to tabbas ka yarda ka amince zaka auri wata matar bayan wanda Alhaji ya zabar maka idan ko bakada ita nice nan zan nemo maka,na baka nan da sati ɗaya kaje kayi tunani kayanke hukunci nima kaina bazan nuna yarda ta da amincewa ta ga Alhaji ba har sai naji hukunci daka yanke akan wannan shin zaka martaba bukatata ko kuwa zakayi fatali da shi. Take zufa ta karyo masa dan sun sakashi tsaka mai wuya bakuma halin yace yafasa duka dan dukkansu suna da wata hope akansa sannan kuma suɗin iyayensa ne waƴan da sukai sanadin zuwansa duniya bazai iya ƙin yimusu biyayya ba. Aisha kallon maman fadila tayi da fuskarta shaɓa shaɓa da hawaye tace"dan Allah mama kiyi hakuri in sha Allah daga yau zan dauke idona akan fadila kaman yanda kikace saide kisani banida ƙawa ko yar uwa sama da ita"dallah rufamun baki idan har abunda kike faɗi gaskiyane meyasa....sauri katseta nayi da"naji mama hakan baze sake faruwa ba"dade yafi miki shegiya sai baƙin jini babu mashinshi wama yasa..."ya isa Rabi Anna ta daka mata tsawa tana nuna mata hanyar ƙofa da hannu bawai kinfi kowa iya masifa bane,karkiga idan kin fara masifarki ana shiru ana ƙyaleki bawai tsoronki akeji ba,a'a hauka aka ɗaura miki dan ba mai ganinki da hankali karki sake aibatamun yara dan sufi naki asali inde asaline karkiga kina zaune da mahaifinsu tare kinemi shegenta mun da yara. Aisha kuma inde nice na haifeta to babu ita babu ɗiyar alheri da kuka mana kuma Allah yabiyaku saide duniyace kubita a sannu watan wataran zakuyi nadama rabi ke saima fita daga cikin gidanki ya gagareki inde irin wannan kuɗin ne. Maganan Anna da alama ya daki mama Rabi dan koda wasa bata taɓa tsammanin Anna zata iya buɗe baki tayi magana ba saboda irin hakurin ta"baki zakimana maman Aisha aniyarku tabiku keda butulun ƴarki nan ta hau tsalle tana buri kan kace kabo tafara tara mana jama'a abunka da anguwan geto,janta wasu mata sukai sukai waje da ita...   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Https://arewabooks.com?id=63dbe9c0e999537d82ef5685 Kuyi following dina ta nan domin samun wannan littafin daga farko. Chapter 18 Zan iya cewa tunda na taso ba taɓa tozartani irin wanda fadila ta mun yau ba,wai shin ina soyayya da mukewa juna yake ina kauna dake tsakanin mu ina aminci da mukewa juwa menama fadila wanda ta zaɓi yamun haka sanin ba mai bani amsa yasani goge hawayena ina mai kokarin tsaida kukanda ke tasomun tun daga ƙasan zuciyata har muka ƙaraso anguwan mu sauƙa nayi nami ƙawa mai napep ɗin kuɗi sai cemun tayi ai wanda ya tsaidashi yabada kuɗin godiya namasa duk da bansan wanda yake cewa yabada kuɗin ba. Sai da natsaya bakin ƙofan gida kaɗan na daidaita nutsuwata sannan nashiga cikin gida bakina ɗauke da sallama khadija dake alwalan sallar magariba ita ta amsamun sallama danayi"sannu da xuwa anty aisha, ""Yauwa khady ina mubaraq?"yaje sallah masallaci ta bani amsa. "Yauwa idan kigama alwalan ɗauki wancan ledar ki miƙashi ga maman salmanu da to amsamun ni kuma na dauki buta alwala nayi nashiga daki na shimfiɗa sallaya na tada sallah. daga ni har Anna ba wanda yatashi saida mukai sallan isha'i sannan add'oin neman tsari na jima ina addu'an neman sassauci kan abunda nakeji a cikin raina dan zuciyata namun zafi har wani irin turirin zafi nakeji,Kasa cin abincin nayi da zaran nakai abincin bakina sai abunda yafaru dani dazu ya faɗomun daga karshe hakura nayi da na wanke hannu na nakoma gefe na zauna,a tsanake Anna ta dubeni tace"lafiya naga bakici abincin ba? Ɗan murmushi yake nayi nace"lafiya anna kawai banajin cin abincin ne Allah ya kyauta tace. Muna cikin hira saiga maman fadila kaman anjehota ko sallama babu kallon ta Anna tayi tace"a'a Rabi kece lale marhabin shigo daga ciki mana...dagawa Anna hannu tayi tace"banason munafinci ai wallahi maman aisha nayi mamaki dama bazaka taɓa sanin masoyinka ba,sai abu yasameka wani irin taimakone bamu muka ba arayuwa haka fadila zata tasani gaba tasa na zubo muku abinci ta dauko ta kawo muku amma saboda baƙin hasada da butulci irin ta ɗan adam shine Aisha zaki rufe ido kiciwa fadila mutunci saboda kawai Allah yarufa mata asiri tasamu aiki mai gwaɓi,to wallahi ahir ɗinku daga ke ha mahaifiyar taki idan ita ke aikoki wallahi wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa. Banzaye dangin tsiya wayasan asalinku wama yasani ko saida aka gama yawun dandi sannan nitsuwa tazo ma akaxo inda ba ba wanda yasanku kuka ɓoye kanku idan ba haka ba ai duk ɗan halas yasan halacci wallahi,tunda tafara surfa masifa ba wanda yace da ita ci kanki daga ni har Anna sau kukan baƙin ciki daya kubce mun nasan nice silar komai da ke faruwa yanzu,da nayi shiru da bakina da ba wanda ya isa yaciwa mahaifita mutunci haka ba tasan hawa ba bata kuma san sauka ba,anzo har gida ana ci mata mutunci ni kaina mamakin yanda fadila ta iya lauye zancen ta maida lefin kai kawai nake banyi mamakin rashin mutuncin mahaifiyar ta ba,dan kowa dake anguwar nan ya kwana da sanin idan tatashi masifa rufe ido take taciwa kowa mutunci. Ahmad Ya kalli ammi da lulun idon sa maikama da wanda yakejin bacci yace"dan Allah ammi kiyi hakuri kinsan ke kaɗaice farin cikin mu...katsesa tayi da cewa"amma ahmad kai baka ganin abunda Alhaji yakeson yi kaman rainane da kuma zubar da mutunci yake neman sayowa kansa,ko so yake mutuncimmu yazube a idon duniya in ba haka ba Ahmad dame Alhaji sunusi yafishi da zaice saide kai ango katare gidan sa gaka ga ɗiyarsa wace irin rayuwar aure zakuyi a gidan ɗaya da surukai ga ɗaki ga ɗaki idan ba dawata manufa aka shirya yin hakan ba. "Ni de dan Allah ammi kiyi hakuri banaso kusamu tsaɓani da Abba akan wannan magana dan Allah yakare maganan kaman ze saka mata kuka,guntun murmushi da bekai ciki ba tayi tace"shikenan zanyi hakuri amma fa saboda kai bawai dan Alhajin naka da abokin nasa dan sunfi karfina bane ba..da sauri Ahmad yace naji saboda ni Ammi shi duk duniya ba wanda yakeso kaman mahaifiyar sa idan kacire soyayya mahalicci data ma'aiki (s.a.w)to cikon na ukun ammin sane dan ko mahaifinsa saide yabi bayan Ammin sa. Amma da sharaɗi maganan ammin shi yadawo dashi daga duniyar tunani da yaɗan lula zuba mata ido kawai yayi tace"zaka auri zaɓina ita ka ajita nan ita kuma matar son sai kabita gidan su tunda kunyarda zuciya kare yacinye. Wani irin zabura Ahmad yayi dan beyi tsammanin jin wannan magana daga bakin Ammin nasa ba,"pls Ammi yace damuwa fal ransa"don pls me ahmad idan kaso nabar wannan magana tasha ruwa ta lafa ba tare da kowa yasan sirrin gidan mu ba to tabbas ka yarda ka amince zaka auri wata matar bayan wanda Alhaji ya zabar maka idan ko bakada ita nice nan zan nemo maka,na baka nan da sati ɗaya kaje kayi tunani kayanke hukunci nima kaina bazan nuna yarda ta da amincewa ta ga Alhaji ba har sai naji hukunci daka yanke akan wannan shin zaka martaba bukatata ko kuwa zakayi fatali da shi. Take zufa ta karyo masa dan sun sakashi tsaka mai wuya bakuma halin yace yafasa duka dan dukkansu suna da wata hope akansa sannan kuma suɗin iyayensa ne waƴan da sukai sanadin zuwansa duniya bazai iya ƙin yimusu biyayya ba. Aisha kallon maman fadila tayi da fuskarta shaɓa shaɓa da hawaye tace"dan Allah mama kiyi hakuri in sha Allah daga yau zan dauke idona akan fadila kaman yanda kikace saide kisani banida ƙawa ko yar uwa sama da ita"dallah rufamun baki idan har abunda kike faɗi gaskiyane meyasa....sauri katseta nayi da"naji mama hakan baze sake faruwa ba"dade yafi miki shegiya sai baƙin jini babu mashinshi wama yasa..."ya isa Rabi Anna ta daka mata tsawa tana nuna mata hanyar ƙofa da hannu bawai kinfi kowa iya masifa bane,karkiga idan kin fara masifarki ana shiru ana ƙyaleki bawai tsoronki akeji ba,a'a hauka aka ɗaura miki dan ba mai ganinki da hankali karki sake aibatamun yara dan sufi naki asali inde asaline karkiga kina zaune da mahaifinsu tare kinemi shegenta mun da yara. Aisha kuma inde nice na haifeta to babu ita babu ɗiyar alheri da kuka mana kuma Allah yabiyaku saide duniyace kubita a sannu watan wataran zakuyi nadama rabi ke saima fita daga cikin gidanki ya gagareki inde irin wannan kuɗin ne. Maganan Anna da alama ya daki mama Rabi dan koda wasa bata taɓa tsammanin Anna zata iya buɗe baki tayi magana ba saboda irin hakurin ta"baki zakimana maman Aisha aniyarku tabiku keda butulun ƴarki nan ta hau tsalle tana buri kan kace kabo tafara tara mana jama'a abunka da anguwan geto,janta wasu mata sukai sukai waje da ita...   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Https://arewabooks.com?id63dbe9ec0e999537d82ef5685 Kuyi following ɗina akan wannan handle ɗin don samun wannan littafin daga farko. Chapter 19 Bayan fitar da maman fadila daga cikin gidan mu da makwabta sukai wasu daga ciki sun shigo har ɗaki suna bawa Anna hakuri akan abunda maman fadilan taxo tamana,yayin da suke kecewa da Anna kawai taraba Aisha da fadilan dan a zauna lafiya tunda ga hanya da yarinyarta ta ɗauko wasu na raɗe raɗen karuwanci ta fara tunda kullum ranan duniya da kalan motar da zata kawota gida gudun bacin suna Aisha kirabu da fadila Allah yasa hakan shine alheri cewar maman kausar da Amin aka amsa baki ɗaya. Nide banda hawaye ba abunda nakiyi bayan duka sun kama gabansu Anna ta kalleni tace"kukan ya isa haka mana Aisha ai sai kanki yayi ciwo. Faɗawa jikinta nayi nasaki sabon kuka da karfin gaske cikin kuka nasoma cewa"dan Allah anna kiyi hakuri wallahi ba....shiiiii tace tana mai ɗaura yatsanta saman bakin ta. "Banason dogon surutu nasanki Aisha nasan halinki a kullum ina alfari da kasancewar ki ɗiya gareni mai tsayuwa kan gaskiya koda hakan zesa aga baƙinki,kwanta kiyi baccin ki tace dani ba tare da ta bani wata daman nayi magana ba. Ahmad duk abun duniya ya taru yamasa yawa kwakwalwansa ya tsaya cak baya aiki,yama rasa wani irin tunani zeyi ta ina zai fara? Khalid da tun dazu yake tsaya yana masa magana jinsa shiru yasa shi matsowa kusa dashi ya dafa kafaɗasa yace"komai yayi zafi maganin sa Allah kamata ka sauƙakawa kanka yawan tunani amma mutum ya zauna sai tunani shin auren haɗi kanka farau ko kanka karau sai kace ba namiji ba ka zauna kana ɓatawa kanka lokaci da tunane tunanen banza wallahi da nine kai ko,hmmm wallahi ko sau daya baxan ɓata lokaci na wajen tunani ba kawai biyayya zanyi bayan aure da ɗan watanni nima nabijiro musu da nawa zaɓin kaga shike nan magana taƙare kalass..yakare maganan yana dan ware hannun sa. Hmmm Ahmad ya sauke nannausan ajiyar zuciya yana gyara zaman sa ya fuskanci khalid sosai yace"bazaka gane bane ɗan uwa"idan ka fahintar dani mai zai hanani ganewa shima ya faɗa masa. Nan Ahmad ya kwashe komai dake faruwa yasanar da shi ta ɗaura dacewa kasan basma kasan halinta na rashin ganin kan kowa da gashi gata da son wulakanta na ƙasa da ita ga rashi iya komai ni fa bana tunanin ko dafa tea wannan ta iya sannan wani karin haushi wai ni zan tare gidan su koda me suke taƙama kuma Alhaji ya biye musu. "Gaskiya abokiya da aiki a gaban mu yanzu de ba wannan ba nifa ina ganin irinsu yarinyar nan Aisha zaka samu idan kasami irinta gogawa zasuyi da basma duk tsiyarta dan da alama bata da tsoro, kallon baka da hankali Ahmad ɗin yamasa ƴar dariya khalid yayi ya cigaba da cewa wallahi Im serious kai bakaga yanda ranan ta shararawa wancan guy ɗin mari ba, Kuma bata burgeka ba ranan? Kadeyi tunani idan kuma bata ma ba nide gaskiya yarinyar tamun tun ranan da nafara ganin ta naji wani abu ya ɗarsu a raina gami da ita kawai zan fara yaɗa munufata kafin wannan shamsu yayi mun tsakiyar da ba ruwa"zubar da aji cewar Ahmad yana jan gajeran tsuka"oho de kwara na xubar da ajin dan barin kashi a ciki baya maganin yunwa wani ajine ga namiji dama duk ajin ka duk jiji da kanka wataran sai karamar yarinya ta zautar dakai tasaka kuka a bed jifansa da pillow Ahmad yayi ya cafke yana dariya shima din dariyar yayi da cewa wallahi khalid baka da kunya. "Basma basma basma Kaman bata jin kira haka ta sauko down stairs ko sleepin dress dake jikin ta bata cire ba,sai wani yatsune fuska take da alama baccin be gama isarta ba"Daddy gani irin wannan kira haka sai kace nayi lefi,ta kare maganan cike da rashin tarbiya Washe bakin sa yayi cike da so da kaunar ɗiyar tashi dan ko kaɗan shi bemaji haushin rashin amsa mishi kiran da yamata batayi ba yace"ki shirya anjima Ahmad ze zo ku sasanta kanku dan mun rigada mun gama komai da babansa ku kawai muke jira ku sasanta sai musha biki....wani irin tsalle tayi ta rungumi daddyn nata tace"luve you daddy"love you too dear maza jeki ki shirya tarɓansa yace da ita da gudu tayi hanyan kitchen tana kwalawa lantana kira dariya hajia mariya tayi tace"oh yaran yanzu ba kunya dubi yanda take murna da zuwan saurayi shima Alh sunisu dariya yayi irin tasu ta manya yace"barta tayi abunta. "Ai ko yanzu ban riketa ba. "Ina da buri mai yawa akan auren nan nasu mariya ki nutsar da ɗiyarki karta kwafsa mana idan komai yayu ina burin mallakan cibiyar nan ta Al-hakk baki ɗayansa yazama mallakina dan haka dole sai mun tashi tsayin daka mun kuma haɗa karfi da karfe wajen ai watar da wannan manufa tamu. "A hayyeh ayyiriririi kace duniya sabu zamu maganan jiji dakan hajia ma'arufa dan daga lokacin da ɗanta yayarda ya tare nan gidan daga sannan kace sunan ta sorry ba ita ba ɗa. Dariya suka kwashe baki ɗaya nan suka zauna sukai ta tsara yanda komai ze gudana. Daddy ishaq Zaune yake bayan ya gama nafilfilun sa kaman de yanda yasaba koda yaushe,dan bashi da abokin hira sai istigfari da hailala da yake kullum dakuma addu'an Allah ya aramasa tsawun rai yaga faɗuwar su Alh sunusi da ire iren sa, A ƙiyasi yau shekara takwas kenan yana tsare kar kashin ƙuntatawa na alh sunusi sannan a ƴan kwanakin nan kullum ya kwanta bacci yana yawan mafarkin Aisha na mawuyacin hali tun randa yaji amon muryoyi suna kiran wannan sunan a filli ya furta"sunusi karshenka yakusa dan wannan hadin aure da zakayi tsakanin ƴarka da ɗan alh badamasi wannan shine kuskure mafi girma da zaka aikata sannan sadaukar da jinin aisha a ƙungiyarku wannan yana nufin tarwatse warku yazo dariya ya ƙyalkyale dashi kaman yana tare da wani ya cigaba da cewa narantse da sarkin da ya busan numfashi bazan fasa kai ƙararka gareshi ba har sai naga durƙushe warka.   ALLAH YASA MUDACE. [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "20" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1317659832?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=%2F6okSRwVD0nvAJ81JL%2F%2BU2IXFhoBI%2Fe4AzJ33wVr%2FTJRrW2ZKFNRSF%2Br0aKEmK6BMFFcbde75GdKzmPruwhO4X3XV16jUGDi0QXcsCmXCYZNs1baBlLYZlQ6VshBdYdV ____________________ *AUREN WUCIN GADI* Chapter 20 "Oga mungama shirya komai na barinka wajen nan a daren yau,muryar gaja ne ya katse masa magana da yake,wani ƙayatattaccen murmushi yayi yana kallon gaja yace"ya kai da sauran karnukan farautan nasu? Wannan tambaya ta bawa gaja dariya saida yayi mai isar sa sannan ya tsagaita yace"sai oga ishaq ai komai ya kammala nan da awa guda zakabar zaman nan ina maka fatan nasara dakuma fatan saduwa da iyalanka dan inaji a raina kun kusa haɗawa da juna bansan abunda yasaba amma akwai wata yarinya da nake gani a duk sanda zan ganta sai naji kaman tanada alaƙa da kai. Da sauri daddy ishaq yace"ya kaman ninta suke kuma aina zan sameta?sosa kai gaja yayi yace"gaskiya oga bansan inda take ba,amma ina yawan ganinta a A&b travel kasan wajen ranan nacema na ɗan Alhaji badamasi ne mai suna Ahmad kuma shi alh sunusi yakeson bashi auren ɗiyarsa, To cikin wajen a yanda bincike na yanuna bayan motocin safara da suke dashi akwai wajen ɗinki saboda shahara dakuma gwarewar ma'aikatan wajen kayansu order ake garigari harma da kasashen ƙetare ina kyautata zaton wannan yarinya a wajen take,sannan akwai informer da muke da iya awajen zamu sami dukkan bayane da muke bukata wajenta saide har yanzu tace yarinyar bata sake da ita sosai ba,dan acewar ta kamar bata da sabo da mutane. Gwaron numfashi daddy ishaq ya sauke yace"ya batun wannan flash din? Mika mishi gaja yayi da kuma cemasa duk wani ƙarin bayanin da kake bukata zaka samu cikin sa oga sannan duk sanda wani abu ya shige maka duhu kiyi alart ɗina ta turamun da sakon lambobi a hargitse,hannu daddy ishaq ya mika masa sukai musabaha cike da jin daɗi yace"in sha Allah kuma kaima zanyi iya yina dan ganin nasama maka da duk wasu bayane da kake bukata daga gareni. Alhaji shehu tunda ya daura idon sa akan aisha yakasa samun tsuwa da sukuni zuciyar sa da zaran ya kwanta ita yake gani ya tabbata ya kamu da soyayyarta mai karfi,ɓangaren fadila kuwa komai yana tafiya mata yanda take so,tasamu yanda takeso rayuwa ya canza mata yanda takeso tana juya naira yanda taso,gashi ba abunda suka nema a rayuwarsu suka rasa. Tasaka an rushe musu gidan ana yi musu ginin zamani ginin bulo da bulo yanda tasaki kuɗi aiki ake ba dare ba rana cikin ƙwana biyar har antada katangar gidan dakuma ɗaki ciki da falo da bayi na mamatar an fanti yanxu haka ɓangaren babanta da na yayunta maza biyu ake gini dan dama gidan nasu yana da girma,zaune suke da mamarta sun baje sunacin shawarma suna korawa da ruwan lemo mai sanyi mama rabi ta kalli ɗiyar tata cike da kulawa da so da kauna tace"shegiya naira masu gidan rana,yanzu kiga rayuwarmu ta canza lokaci guda waima fadila wani kalan sana'a wannan Alhajin keyi dan tamusu karyar Alhaji shehu shiya ɗauki nauyin gina musu gida kafin ayi maganar auren su, Allah de yasa ba ɗan yankan kai bane. Ɗan harararta fadila tayi a ƙaikace sai kuma tace"yankan kai kuma mama ai rabin kuɗin nawane dan nima sana'a nake nema nake tuƙuru saboda huce haushin talauci da mukai abaya,yanzu kuma lokaci yayi da zamuji daɗi muma musakata mu wataya cikin daula"fadila kaji tsoron gamuwarki da Allah suka tsinkayo muryan babanta daga baki ƙofan falo,ki guji duniya da abunda ke cikin ta dan wannan arziki da kikayi lokaci ɗaya kin saka mutane ana zargin ko kuɗin jini...katse shi mama tayi da cewa"haba malam bantaɓa sanin baka da hankali ba sai yau,idan baka gode mata ba ai bata cancanci haka daga gareka ba,shikenan ba dama mutum yayi abun kansa sai ansa masaka ma ido,mutum daya sami canji kaɗan a rayuwarsa sai sunsan abunda sukace akan ka kawai baƙin ciki ake dan anga munsamu canji a rayuwa malam toshe kunnenka zakayi gajin irin waƴan maganganun mutanen. So kawai mutane suke su ringa kallon mu jiya i yau garin tuwo na gagaran mu haka sukeson ganin mu muna yawon neman aikatau kororo kororo ana zaginmu,shiru yayi mata yana sauraronta dama gwanace wajen masifa da son abun duniya dan tun can idan tafara surfa masifanta a gidan ba mai kulata,yanzu ma saida takai ayaa sannan malam inuwa wato mahaifin su fadila ya sauke gauron numfashi ya kalleta cike da ɓacin rai yace"kingama? Wannan tambaya da yayi mata ya bata haushi dan haka a hasale ta hau bambamin bala'i ai hasada yake wa ƴarta dan kawai ita Allah ya ɗaukaka cikin su so kawai yake yarinka ganin su cikin ɓakin talauci idan ba haka ba,ya kwantar da hankali yaci arziki amma kullum mutum kana fama da wankin hula yarinya Allah yahure mata bazaka sanya albarka a abun ba,yanzu duba ko a iya gyaran gidan nan ta tsaya ai abun burgewa da tunƙahone agareka ace ɗiyarka Allah ya azurta tas....wani irin wawan tsawa daya daka mata hakan yasa tayi shiru tana ta muzurai nunasu yayi da yatsaya yace"ni ko farko banyi farin cikin gyara mun gida da sukazo mun da shi ita da wawan mutumin can bari kiji rabi Allah ya rufamun asiri bazaki nemi tonamun ba,ya kalli fadila yace kice masu gyaran nan su tattara subarmun gida,shi arziki nufine na Allah idan yayi zakayi to ba wanda ya isa hanawa,haka idan bebaka ba ba wanda ya isa yabaka duk duniya. A kullum ina godewa Allah daya rufamun asiri keda kike ganin wannan abun burgewane a wajenki kuje can kukarata kar wanda yasake cemun komai gidade nawani ba uban kowa ya saimun ba,bara kiji rabi duk wanda ya hau motan ƙwaɗayi a tashar wulakanci za sauke shi yana kaiwa nan yayi ficewar sa a gidan,kuka fadila ta saka ganin kaman mahaifinta yanason kawo mata cikas a fasowa gari da tasomayi. Ahmad zazzaune suke bayan sun gama cin abincin dare hira suke da ƴan uwan shi cike da raha meera autar ammi ta kalle shi tace"yah Ahmad ranan munga wasu dogin riguwa a status ɗin yah khalid ya daura masu masifan kyau"shine kikeson kalansa ko?yakare maganan yana jan hancinta dariya tayi tace"wallahi yah ahmad kaman kasani kuwa fadwa ta amshe da cewa"kuma kinji yah khalid yace wannan kayan bana sayarwa ko kyauta dasu bani saboda....kinga ruwafa mutane baki da shegen surutun tsiya faɗi ba tambayeta ba, Tura baki tayi tana magana ƙasa ƙasa shide ahmad shiru yayi be sake bi takan zancen nasu ba. Alhaji badamasi ne yashigo falon rai aɓace sannu da zuwa yaran sukai masa amsa musu yayi ciki ciki ya ƙurawa ahmad ido shiko ahmad ƙasa yayi da kansa kaman ma besan shi mahaifinasu ke kallo ba alhali kuwa yana yana ankare da irin kallon da yake masa yanama autar ammi wasa hakan yasake ƙular dashi koda ammi tace"Alh sannu da zuwa ga ruwan wanka can na haɗa maka muje kayi sannan kaci abinci. Harara ya watsa mata yace"ai dole kice nayi wanka tunda gani kifi sarki ruwa shi wannan ya maisheni mahaukaci ina magana yayi buris dani,sannan ke kuma kizo kina wani zancen wanka to ba za'ayi wankan ba,yafaɗa a hasale"Allah yabaka hakuri alh"nabi hakurin da gudu nace nabi hakurin da gudu shiru ammi tayi bata sakeyi masa magana ba. Fadwa da meera kuwa miƙewa sukai suka wuce dakin su,sai sannan ahmad ya dago ya kalli ammi data dauke kanta tana kallon tv shiko alh badamasi tsaye yake ƙiƙam kaman wanda aka dasa miƙewa yayi yace"ammi sai da safe ko,kallon sa tayi da murmushi a saman fuskarta tace"ahmad harzaka tafi?to Allah yatashe mu lafiya. Ganin da gaske wucewa zeyi yasa alh badamasi daka masa tsawa yana cewa"oh ga ɗan iskanan kowa sai guduwa yabarni dan kun maisheni mahaukaci ko?to maxa koma ka zauna. Komawa ahmad yayi ya zauna"saboda baka ɗaukeni bakin komai ba baka ganin girmana ɗazu da zan fita nace kaje kasami wannan yarinya ku tattauna shine kaƙi tafiya ita mace ma tayi biyayya ta yarda da auren ka sai kaine zaka nemi watsamun ƙasa a ido ko. "Au dama yanzu duk wannan ƙucin ran da kake sabida ahmad beje gun basma ba kake yinsa to Allah ya kyauta daga haka tamiƙe tsaye tabar falon rakata da ido yayi shi kaɗai yasan halin da ze shiga idan tayi fushi kafin ta sauko. Sake yin kasa ahmad yayi da kansa cikin kwantar da murya yace"haba Alh mai yasa kake hakane gashi yanzu kasa ammi tayi fushi sannan idan zanje wahen yarinya zance ai baku iyaye zaku saka mana rana da lokacin haɗuwa ba,sai kace ƴan 80c ai yanzu zamani yanza duk sanda mukai zamu haɗu bada saninku ba zamu haɗu kumama ni yanzu aiyuka sunsha mun kai bana tsamanin zanje cikin yan kwanakin nan saide namusu zuwan bazata,har yamiƙe sai kuma yace an Alh gaskiya koda zan aurin yarinyar nan da sharaɗin nima zaka bani nawa daman dan auro wacce nakeso ta kwantamun arai zatamun biyayya kuma zata zauna da mahaifiyata ta ringa taimaka mata da ayyukan gida,daga haka be bawa alh badamasi daman cewa wani abu ba yayi shigewar sa,bayan ya shige daɓas alh badamasi ya zube saman ɗaya daga cikin kugerun falon yana mai dafe kansa da tuna yanda sukai yarjejeniya da alh sunusi daga ɗiyar sa Ahmad ba zaikara wani auren ba,sai gashi ba aje gayin auren ƴar tashi bama ahmad ya bijiro masa da zance karin aure take wani irin zufa ta karyo masa yama rasa meke masa daɗi     ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Chapter 21 Yaso dakatar da Ahmad amma gani yayi koya dakatar dashima kaman aikin banzane shi bayama tsammanin ze saurare shi yakuma fahince sa,dan haka miƙewa yayi ya nufi ɗakin Ammi taddata yayi tayi wankanta tayi shirin kwaciya sai baxa kamshi take kallo ɗaya tamasa ta ɗauke kanta. Gani yayi bazata kulashi ba inde bashine ya fara yi ba,takowa yayi a hankula tsaɓanin yanda ya faɗo ɗakin zama yayi bakin gado ya riƙo mata hannu cikin ƙasa da murya yace"yi hakuri Ammin yara ɗazun rainane a ɓace yanzu ina ruwan wanka dan sulhu yake nema da ita,banza tayi masa,riƙe kunnensa yayi ya duka da gwiwansa kasa yamarairaice fuska yace pleasa wify yanda yayi kaman karamin yaro yasata sauke ajiyar zuciya tamiƙa hannunta ta kamo nasa tace"shikenan nayi hakuri ammafa badan wai na huce bane kawai zanyine saboda banason yaranmu su fahinci akwai wani abu narashin jituwa tsakanin mu,kuma dan Allah idan ranka yaɓaci kariƙa ƙoƙarin ganin kasarrafa fushinka karka kasake mun irin haka a gaban yara dan su yara iyayensu sune madubinsu banson munayin irin haka suke gani suma su ɗauka. Aisha dake zaune tana ma nusaiba yankan kayan ankon bikin yayanta,kallon ta nusaiba tayi tace"kefa kinji da dadinki Aisha "Da akai mefa? "Ba ruwanki da komai gashi kin mai da hankalinki wajen aikinki gaskiya rayuwarki tana burgeni saboda kin riƙe talaucinki kwata kwata abun duniya be rufe miki ido ba. Murmushi ɗauke saman fuskata na kalle ta nace"ai kema haka rayuwarki take ba ruwanki da shiga tsabga da bata shafeki ba,ƴar dariya tayi tana girgiza min kai tace"kai Aisha baki da dama kekan,nima dariyar nayi nace"sai hagu ko,dariyar muka sakeyi baki ɗayan mu. Can ta kalleni tace"Aisha nikan mutuniyarki kinga yanda ta koma kuwa? "Wace kenan? Damamaki ta kalleni tace"fadila mana ko kina da wata mutuniyarce bayan ita,ɗan ajiyar zuciya na sauke zuciyata namun zafi dan tunawa da nayi da rashin mutunci da atamun nace"ayyar nusaiba aikinsan yanayin aikin mu daga ni har ita,lokacin da nake gida ita tana wajen aiki ko ita tana gida ni kuma ina wajen aiki balle kuma ita aikin ta da ba weekend. "Hakane kuma fa Aisha amma kuwa kinga wani irin mahaukacin mota da take hawa kuwa,hmm ina faɗa miki aisha wannan rushesshen tsohon ginin gidan nasu ai yau bakiga yanda aka rushesu ya dawo sabo ba,wallahi aisha kuɗi yayi a rayuwa muma Allah yabamu"mai albarka zakice nace da ita"amin aisha wannan haka hake mai albarka"amma aisha ke bakya zarginta da shiga ko irin ƙungiyarnan ta matsafa? Ɗagowa nayi ina kallonta sannan na maida hankalina ga abunda nake nace"yaka mata murinƙa kyautata zato ga ƴan uwamu zato haramun ne koda yazama gaskiya,katseni tayi amma Aisha nima katseta nayi ina cewa"kinga nusaiba kinsan yanda muke da fadila nafi kowa sanin abunda zata iya da wanda bazata iya ba,sannan na fiki sannin inda take aiki dakuma irin aikin da sukeyi ba abun mamaki bane idan tace miki tana samun dubu ɗari kullum"to ke aisha ke mai yasa bazata miki hanyan inda take aikin ba, "Nusauba kenan ai ni ɗinki da kika gani inayi shine burina soyayyata da ɗinki daga jinina yake kuma ina alfahari da kasancewata tellah wata ran kina zaune saide ki ganni ana haskoni a tv ko kiganni a jarida an hasko da hotona wacce tayi fice a duniya ƴar africa talle ta mace dariya tasaka tace Allah yasa nace amin daga nan mukaci gaba da hira amma ƙasan zuciyata ina tunanin maganan nusaiba da tayi na ƙungiya da fadila take. Fadila ta kalli alh shehu da rinan nun idanunta tace"amma alhajina kana cikin hayyacinka kuwa? Kasan abunda kake cewa kuwa? Aisha fa Aisha kace kanaso kasan alaƙata da ita kuma kasan kuma nariga da na sadaukar da jininta wa ƙungiya shin baka...."kinga fadila wannan ba abun ɗaga hankali bane ai tun randa kuka zo ta gaidani naji duk duniya ba wacce nakeso tamun sama da ita,kuma zancen sadaukar da jininta da kike wannan abu mai sauƙine kawai ki shirya fansar da ita da wanda yafi kusanci da ke, zaro idonta tayi waje kaman zasu faɗo kasa tsaban firgita da ruɗani da tashiga dakyar cikin rawan murya ta buɗe baki tace....wallahi ko ƙasa da sama zasu haɗu bazan taɓa bari kasami aisha ba...kuma jinin ta ai nariga da na sadaukar tunda nasaka mata wannan zoben kuma kullum sai nasha kufi ɗaya duk dare kaman yanda shugaba ya bukaceni nayi wani irin zabura yayi ya damƙo wuyarta ya shaƙeta...   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Chapter 22 Fadila taji shaƙa sai muzurai take tana jujjuya kai kashedi sosai Alh shehu yayi mata sannan ya yadata gefe faɗi ƙasa tayi tana maida numfashin wahala can ta miƙe jiki ba ƙwari ta saka kayanta ta ɗauki jakarta saida takai ƙofan fita daga falon ta waigo ta kalle sa tace"ni kawa haka ko?to wallahi kasaka a ranka fansar wannan shaƙarda kamun akan aishan zan ramata saide duk abunda zakai kayi amma wallahi ba abunda ze canzan ra'ayina dan tun farko kaine wanda ka ɗaurani wannan hanya kuma a haka zan tafi,tana kare maganan tasaka kai ta fice a falon biyo bayanta yayi ta kwasa aguje tayi waje. "Basma wai haryanzu kukan kike? Cewar mummynta data gaji da rarrashinta ta fita zuwa falo amma zuciyarta ta kasa hakura ta sake dawowa ɗakin still samun ta tayi kwance saman gado tayi rubda ciki kawarta salaha na xaune gefenta sai bata baki take amma taki yin shiru. "Bass tashi muyi magana cewar salaha data gaji da bata baki miƙewa tayi zaune fuskanta a kumbure idanunta yasake ƙanƙancewa sabida kuka data sha. tambayanki zanyi amma dan Allah karki ɓoyemun komai dan musan inda mafita take,gyaɗa mata kanta tayi sannan salaha ta gyara zamanta ta cigaba da cewa tunda kike da ahmad ya taɓa ɗaukan waya yakiraki da karan kansa? dan yaji lafiyarki ko irin kuyi hiran nan? Shiru basma tayi mata bata bata amsa ba, Ok to na fahinta cewar salaha amma yana tura miki sako irin na morning ko na good night? "A'a ko sau ɗaya baya kirana ko ya turamun da sako idan ma nakira shi a waya gaskiya baya ɗagawa idan ma ya ɗaga wayan saide yace mun ze kirani yanzu yana busy sannan idan natura masa da sako ba reply basma ta bata amsa wasu hawayen nasake bin ƙuncin ta. Shiru ɗakin ya ɗauka daga salaha har basma ba wanda yasake yin magana,numfashi salaha ta sauke sai kuma tace"gaskiya basma abunda zance dake anan ahmad baya sonki ne ko baya ra'ayinki idan da aca yana sonki wallahi idan shine agogo sarkin aiki idan yaga kiranki ajiye komai nasa zeyi yabaki lokacin sa idan sako kika tura masa kuwa sai yayi gaggawan maida miki da amsa ba wai ya shareki ba. riƙo hannun salaha tayi idanun ta na zubda wasu hawaye masu ɗumi tace"dan Allah salaha ya zanyi wallahi inason ahmad idan narasa shi...rufe mata baki salaha tayi da tafin hannunta tana girgiza mata kai,hannu tasa tacire hannun salaha da tarufe masa bakinta tace"barni kawai nafadi abunda yake raina salaha wallahi da ban kamu da soyayyar sa bane da sauki amma meyasa zeyimun haka bayan zuciyata tagama kamuwa da soyayyar sa. "Saboda bashi ke sonki ba haɗaku akai kuma ƙila shi wannan haɗin beyi masa ba,idan da ace shike sonki hakan bazai faru ba,sannan be dace ace iyayene zasu zama masu haɗa connetion a tsakanin ki da shiba,dolene muyi ƙoƙari wajen fidda iyaye dake kai kawo tsakanin ku,kun sa santa kanku inaga hakan zefi. Hakade suka cigaba da tattauna matsalan su da kuma yanda zasu magance komai. "Khalid gaskiya wannan yarinyar akwai abunda ke tattare da ita wannan nakasa fahinta, "Wacce yarinya kake magana akaine? Cawar khalid dake tura sakonni wa abokin kasuwancin su-Al bazz dake kasar sudan. Tsuka yayi dan besan yayi maganan bama da yake abun nacin sa a rai saboda yawan ganinta da yake amafarki tana neman taimakon sa,abun yana daure masa kai dan duk sanda ya kwanta da irin mafarki da yake wani ya tashi a firgice wani kuma yatashi yaji jikinsa yayi masa weak. Kiran suhail ne yashigo wayan sa ɗagawa yayi suka gaisa nan suhail ɗin ke cewa dashi"haba Ahmad dan Allah waƴan nan dogin rigunan nake so sun mun kyau ko nawane kafaɗa mun fashisu wallahi zan biya munada gasan da za'ayi watan gobe inason muyi amfani da su nasan kuma zamuci wannan gasan kuma kaine wanda ze samu wannan ɗaukakan...dakuma tellah data ɗinka wannan yakan ko yaɗinka please mana ahmad dan Allah karkace a'a wallahi na ƙwallafa rai a wannan kayan tun ranan da ka daura a status ɗinka. Dariya khalid dake zaune a gefe yayi dan shima yanzu chattin da suka gama yi da Al-bazz kenan akan waƴan nan kayan,dayake wayan a hand free ahmad din yasaka khalid yanajin komai"zanyi shawara ahmad kawai cewar ahmad ya kashe wayan yana mai dafe da kansa dake ɗan sara masa kaɗan kaɗan sakamakon bacci da besamu yayi jiya ba. "Dazu naji kace yarinya wacce yarinya kake magana akanta sannan wani irin taimako zamu iya mata? Shiru yayi kaman baze ce komai ba sai kuma can zuciyarsa ta bashi shawaran kawai ya fadawa khalid kawai. "Khalid ina cikin wani hali da nakasa tantancewa akan wannan yarinyar Aisha jin ya ambaci sunan da beyi tsammanin ji daga bakin sa ba hakan yasa shi maida hankalin sa kaco kan kansa"Aisha kuma broo a iya sanina dakai ban taɓa ganin ko magana tana haɗaka da ita ba bayan na aiki ba. Numfashi ya sauke kaman ba zai sake yin magana ba har khalid ya fidda rai da zeyi maganan can kuma sai yace"kawai basirarta na bani mamaki dan ban taɓa ɗaukan ma aikaciya wacce take da abun mamaki da ban al'ajabi irinta ba. Shiru khalid yayi dan yasan ba haka yayi niyan faɗa ba,kawai ya canza zancen ne. Fadila cikin ƙunan rai da takaicin wai Alh shehu aisha yakeso ba ita ba,bayan ɓata mata rayuwa da lokaci dayayi yanzu zexo ya wani ce,hmm wallahi bazata tsaɓoba. Dadare Aisha na kwance bacci ya ɗauke ta Anna dake zauna tana tofa mata da addu'a dan yanzu ita abun na Aisha ya fara bata tsoro mutum ace kullum daren duniya bashi da lafiya amma da gari ya waye kuma yatashi lafiyar sa garas sai ɗan abunda ba rasa ba,kuma a tambayeta bazata iya tuna komai ba. Tayi nisa cikin tunani kawai ta tsikayo muryan Aisha na magana da karfi tana bige bige tana kaukawa,sunan da taji Aisha ta ambata yasata miƙewa a zabure ta riƙe hannun Aisha tana jijjigata da kiran sunan ta.   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "23" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1320187307?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=Advp8slQ59vfvcigMi22Hv73xwHWJiGI2qIX%2Bxk8zrto8j2kKnss6pnAyGD6XlFXXh3AHmnHSDIn%2FfmTWHgOsjEcWkzUPKYFAYA%2Frady0NbHCEsiFmLrvBTsRp39E2jO ________________ *AUREN WUCIN GADI* INASON NAYI AMFANI DA WANNAN DAMA WAJEN JAJANTAWA ƳAN UWA DA ABOKAN ARZIKI DAKE GARIN MAIDUGURI BISA IFTILA'IN GUBARA DAYA TASHI A KASUWAR MONDAY MARKET HAKIKA ANYI BABBAN ASARA BILIYOYIN DUKIYAR AL'UMMA ALLAH UBANGIJI YA MUSANYA MUSU DA MAFIFICIN ALHERIN SA YAKUMA MAIDA MUSU DA ABUNDA YAFI WANDA SUKAI ASARAN. WANNAN ALHINI TA SHAFI DUKKAN GARIN TA MAIDUGURI DAN KASUWAR GARINE GUDA SAI WANDA YAGANI YASAN GIRMA DAKUMA ASARA DA AKA TABKA ALLAH YABADA DANGANA AMIN. Not editing Chapter 23 Kasa kunnen Anna tayi dan son tabbar da abunda kunne ta ke jiyo mata illa kuwa haka ɗinne dan Aisha kira take"Abba karka tafi kabarmu muna bukatar ka kazo garemu. Fadila ranta in yayi dubu to ya ɓaci dan haka cikin ɓacin rai da ƙunan zuciya tanufi wajen shugaba tana zuwa ta zube gaban sa tayi sujjada,ta bude baki dakyar cike da taƙaicin abunda Alh shehu yamata tace"ya shugaba gani gabanka ina mai roƙon ka da a saukar da jinin Aisha ga dodo koda yau yau din nan ne ashirye nake dayin duk wani abu da kasani yanzu bani da haufi. Dariya shugaba ya kece dashi sai da yaɗan tsagaita da dariyan ya gimtse fuska ya jawo wani kwarya dake gaban sa ya miƙa mata,karɓa tayi wani ruwane a ciki kaman jini karɓa tayi ta kafa kanta tashanye shi tass ta ajiye kwaryan masa wani madubi dake gefen sa ya jawo yayi wasu ƴan surutan sa ya watsa wani abu kaman hoda saman madubin madadin taga Aisha acikin sai ganin mahaifiyarta tayi,a razane takurma ihu ja da baya tayi tashiga girgiza kanta tana cewa"haba shugaba kaima kasan hakan ba zatayu ba,wannan fa dakake gani innata ce ko ita kanta Aishan da kyar na danni zuciyata na amince zan bada fansar jinin ta gaskiya a sake duba wannan lamarin kai ina. Wani irin tsawa ya dakamata dayayi sanadin girgizan gidan baki ɗaya,cikin kakkausan murya yashiga cewa"jinin innar taki dodo ke bukata,bakece zaki zaɓawa kinki abunda yayi miki ba anan mu muke bada umurni kuma dole mutum yayi idan yanason zama lafiya acikin duniyar sa,maza tashi ki ɓacemun da gani kinɗauka kina kwance zakiyi kuɗi ba tare da kinbi ƙa'idojin mu ba. Daddy ishaq Tafitan dare yayi lokacin da yafita daga cikin gidan lokacin da yafita mai gadi yana baccin saida yayi ɗan tafiya sannan ya isko motar da datake jiran sa ɗan nesa da gidan. Shiga cikin yayi suka dauki hanya suna gaisawa da wanda ke zaune a bayan motan,mutum mai suna balami bayarabe ne cikin gurɓatacciyar hausar sa yace"oga ishaq ina tayaka murna fito fatan zamu ɗaura aikin mu daga inda muka tsaya? "In sha Allah ya amsa mishi sannan ya ɗaura da cewa balami abu na farko da nakeson fara sani shin Alh sunusi wani irin harkallah yakeyi har yanzu? Sannan inason nasamo iyalina dan ina kyautata zato suna cikin garin nan ta kano tunda goga ya shaidamun ko last week sunje garin namu da alh sunusi harma yamun vedio iyayena da ƴan uwana na gansu suna cikin ƙoshin lafiya nakuma ji babana tsawon wannan lokaci yana koken rashina data iyalina baki ɗaya hakan yana tabbatar mun da cewa basa tare kuma har yau Alh sunusi besan inda suke ɗin ba bare ya cutar da rayuwar su. "Karka damu oga damamu kaine damuwar mu tunda gaka kafito mun sameka sauran aikin neman iyalinka ya ratayane a kanmu dan haka karka damu zamusa abun yi. Sauke ajiyar zuciya yayi kana yace"Allah yamana jagora yakuma bayyanar mana dasu cikin sauki"ameen balami ya amsa. Safiyar litinin ranace da ko bature ance soronta yake,a gaggauce nake shiryawa duk da Anna jikin nata ba kwari,bayan su khadeeja sun wuce makaranta sannan na ɗan zauna kusa da Anna nace"Anna ni zan tafi gashi yau jikin naki sai a hankali dan kin matsa inje ne amma da ba abunda zesani yau in fita in barki gashi ba wayane a hannuna ba balle indan na fita nakira naji ya kike. Murmushin karfin hali tayi sai dakyar ta iya cewa"Aisha idan kin zauna a gidan ma me zakiyi? Kawai kijeki Allah ya tsareki yakuma bada sa'a. Cikin jin daɗi na amsa da amin ina mai rungumarta har nakai bakin ƙofa najuyo nace"Anna jiya nayi mafarkin Abbanmu ya dawo faɗada fara'arta tayi tace"to Allah ubangiji yakaddara saduwarmu Aisha amma ni harna cire rai da sake ganin Abbanku duba da yanda muka dauki shekaru mai tsawo kuma ko labarin wanda yace yaga komai kama da shine bamuji ba,duk da yanda mukai ta bibiyar labarin gidan. Cike da rauni ta kare maganarta nace"Anna karki cire tsammani dan inaji a raina Abba ze dawo kuma zamuyi rayuwarmu kar ta da. "Jeki aisha karki makara tace dani nasan maganarce bata so duk sanda mukai maganan Abba sai ta shiga damuwa amma nikuma a duk sanda natuna wani abu dq mukai da Abban mu ko a can garinmu sai nace Abba kaza da kaza kokuma garin mu kaza. Ban samu abun hawa da wuri ba,dan haka dole tasaka ni takawa da kafa kafin na nasami abun hawa kaman daga sama wata mota ash colour tazo taja ta tsaya a gabana bude kofar akai a hankali sai ga wani hamshaƙin mutum dattijo ze kai kimanin irin ɗan shekara hamsin ko da dauriya amma kasan cewar sa cikin hutu jikin sa be nuna shekarun sa ba. Da fara'ar yatare ni yana"a'a malama Aisha kece da sassafenan kice yau ni mai sa'ane tunda nayi tozali dake da safen nan,kallon sa nake cikin rashin sani amma duk da haka saboda girmansa da rusuna har kasa nace"barka da safiya. Washe baki yayi kaman wanda akama bushara da gidan aljanna yace"yauwa Aisha tashi ki miƙe karki sakeyi mun haka ai irin wannan gaisuwar anbar yayinsa kaman baki gane ni bako?"Eh ina saurine nafaɗa ina miƙewa tsaye dan nafara ƙosawa da surutun sa. "Ayyarh sunana Alh shehu nine wanda kwanaki muka gaisa dake da naje wajen ƙawarki"wayyo dan Allah alh kayi hakuri wallahi bangane ka bane kasan ranan dayake darene ban sheda fuskarka ba. Ɓangaren Alh shehu kuwa ya shagala da kallon bakin ta yanda take mutsasu dakuma yanda take ɗan karkaɗa jikinta tana yarfa hannu yatafi can wani tunanin sa na daban harta aisha tagama bashi hakuri bisa rashin ganeshi da bata yi ba ta fara tafiya sannan ya ankare yace"am jima aisha cak natsaya daga tafiyar da nafara zo kishiga mota na rage miki hanya dan naga yau kaman ana wahalan abun hawa saboda tsadar man fetur da akeyi. "Nagode amma kabar shi kawai zan samune yanzu kar kaima na ɓata maka lokaci nace dashi ina mai barinsa wajen tsaye dan harga Allah banason wani abu da ze shiga tsakanina da fadila har mamarta tasamu daman zuwa tama Anna rashin mutunci da tun farko nagane shi ba abunda zesani tsaiwa harna gaidashi ni ɗaya sai faɗa nake aciki zuciyata sai magana nake abuna ina ta buga sauri har Allah yasa nasamu abun haya sauke ajiyar zuciya na sauke lokacin da nashiga na zauna cikin napep din. Ina sauka bakin ma'aikatarmu shima motarsa na tsayuwa a bayan napep ɗin kudinsa na miƙa masa na soma shiga ciki daidai motar Ahmad shima nashiga, saurin shiga ciki nasoma danma kar yace zemun magana amma ina duk girman shi da shekarunsa haka ya ajiye a gefe shima cikin sauri ya tunkareni yasha gabana. Ja nayi da baya na tsaya ganin kaman ze fadamun jiki"aisha kitsaya ki saurareni da alheri nazo gunki ba dawani mugun nufi ba tun ranan da naje wajen kawarki muka gaisa naji kinshiga raina a takaice de inasonki kuma aurenki zanyi. Awani irin zabure ahmad ya juyo yana kallon alh shehu daya tsare aisha da ido jin maganar nasa yayi tamkar anbuga masa guduma akai saida yayi tagaga kaman ze faɗi Allah ya bashi ikon tsayuwa da kafafunsa da sauri yabar wajen dan bayama so ya tsaya yaji wani amsa aisha zata bashi zuciyarsa ta buga. Aisha ma dagudu batar wajen tana mai girgiza kanka hawaye nabin ƙuncin ta.   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "24" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1320559642?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=MKLCtIyT%2FdDN6lxJ6rrseKhWUNck5VkbXHopuj5RCPdkp29dgolVtJr5CaGKLYEFRnfYuWZE0A6VjuuTIxSMX18rvdL2xpVOf3DKE6912DOnIjX2GnDzlQeXOggYy4Ef _____________ *AUREN WUCIN GADI* Chapter 24 Yanda nake sauri har bana iya ganin gaba araina kuwa faɗi nake mai wannan tsohon yake nufi dani ne,shiɗin saurayin ƙawatace wanda take mutuwar so sabida ƙudin sa to wai meke shirin faruwa danine kode yafaɗi wani abu akaina ne yasa ta zaɓin yimun rashin mutunci ranan kuma tasaka mahaifiyarta tazo har gida taci mana mutunci harda yi mana gorin alherin da sukai mana abaya,idan kuwa hakane haƙiƙa sunyi kuskure daga shi har ita dan ni rayuwata ba soyayyar mai kuɗi acikin. Banyi aune ba sai jin na bugu da abu nayi taga taga nayi kaman zan faɗi runtse idona saboda na gama saddakarwa faɗiwa kawai zanyi,jin ban kai ƙasa ba yasani buɗe idona da sauri na sauke a fuskar wanda ya rikoni yana kallon cikin idanuna wani irin ajiyar zuciya na sauke tare da yin saurin zame jikina daga nashi ina daidaita zaman hijabina ba tare da nasake kallon inda yake tsayen ba,jikina sai ɓari yake saboda yaune karon farko da wani ɗa namiji ya taɓa taɓa riƙemun hannu. Wuce shi nayi ba tare da nasake waiwayo shi ba,kawai de inaji ajikina kaman ana kallo na,harna wuce nayi shigewata hall ɗinda muke ɗinki. Fadila jiki a sanyaye ta dawo gida dan jinta take wani iri tunda shugaba yace mata jinin innarta dodo yakeso kawai taji duk wani abun duniya da take da burin tasamu ya fita mata a rai. Jiki ba ƙwari haka ta shigo gidan cikin sanyi jiki da ta shigo gidan innarta sar zuba take tasaka ƙanwar fadila mai suna harira ta kawo mata jalof ɗin macarooni da yasha bandan kifi sai turirin yake tashi da kunun aya mai sanyi,kasaci fadila tayi,sai kallon innarsu take cike da so. Kallonta mama rabi tayi tana ta washe baki dan yanzu fadila bata lefi a gidan tunda tana da ɗan abu a hannun ta"kici abinci mana kin zauna kin tasa abinci a gaba sai ya huce tukunna ta kare maganar cike da kulawa"mama wallahi bana jin cin komaine mama wallahi raina a ɓace yake yau ta amsa mata batare da kalli inda mamar take zaune ba"me yafaru? Waye taɓa mun ke ƴar albarka,duk kusan a tare jero mata da tambayan. hmmm tasauke ajiyar zuciya ganin yanda mama rabi ta ruɗe yasa tayi ƙokarin ɓuye tata damuwar ta tace"bafa wani abunda zaki tada hankali akansa bane kawai Alhajina ne yace yanason Aisha kinji....."kan bazawara ba gashi mama rabi ta katseta da fadi yo akwai abunda yafi wannan tashi hankali ne amma anyi tsinanniyar yarinya yanzu duk jan kunne dana musu ita da uwarta saida tabi ta ƙarƙashin ƙasa danta rabamu da farin ciki kawai dan anga canji a rayuwarmu to wallahi bazata tsaɓo ba sai naje har gidan nasu na cicci musu mutunci wallahi takare magana tana hucin ta ƙaici. Dama tun fil azal saida namiki magana akan ƙawancen ku kikace ba komai yo ina kika taɓa ganin inda abotan ƙyakkyau ya ɗaure data mummuna,ai duk wanda zece yana sonki da zaran ya ɗaura ido akanta sai yaji hankalin sa ya karkata gun,haka mama rabi ta karaci faɗanta karshede taji bazata iya hakuri batare da taje ta sami maman Aisha tamata jan kunne ba,idan ko ta ƙiji to wallahi bazata ƙi gani wallahi ko tsirara zatayi yawo a doron duniya ƴarta bazata bari ƴata tashiga damuwa ba. Ahmad office ya koma ya zauna duk yarasa abunda yake masa daɗi,kawai maganan wannan mutumin ke zo masa cikin kunnen sa inda yake cewa,Aisha inasonki kuma aurenki zanyi. Watse yayi da duk kayan da ke saman table ɗin dake office ɗin nasa sai huci yake yadafe kansa dake sara masa da hannu,jin kaman fashewar abu yasa khalid daya hana Alh shehu bin bayan aisha shigowa daga ciki dan ce masa nan wajen aikine alh ba dandalin soyayya ba dan haka kayi hakuri idan ta koma gida kasameta a can wannan ba girman kane ba. Gaskiya abunda khalid ya fadamasa da alama ya shige sa dan shi ko ɗaya be kawo hakan a ransa ba kawai aisha dake gaban sa idon sa yake gani gani yake kaman shigan da tayi bazata fito ba haka yakeji a ransa. "Bro lafiya kuwa? Ya tambaye sa lokacin da ya faɗo cikin office ɗin a guje,turus yaja yatsaya ganin yanda ya maida office din. Meke fatuwa anan? yasake tambaya cikin sanyin murya sanda ya karaso tsakiyan office ɗin sosai,zama yayi saman kugera yana ta maida numfashi ba tare da ko kalli khalid dake juro masa tambaya ba. Ruwa mai sanyi khalid ya dauko masa daga cikin freezer sai da yabude goran ya miƙa masa karɓa yayi ya kafa kansa saida yama goran tass sannan yayi jifa da goran ya jinjina da kujeran da yake zaune yamai da idon sa ya lumshe kaman mai bacci amma duk yanda yaso ya ƙice fuskan wannan banzan mutumin a ransa kasawa yayi,dan Allah mai zatayi da wannan tsohun dawani tumbi kaman randa"au bro to kai ina ruwanka da tsufan sa da tumbinsa tunda ba sonta kake ba,kumama ai farare bugun abuja. Bude idonsa dake lumshe ya zubasu fess saman fuskar khalid daga masa gira khalid din yayi haka ya tabbatar masa da zance zuci dayake yafito fili.   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "25" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1321069479?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=4Oxdc%2B1wpFVlyhYspb%2B%2F%2FQNZ7JLkabzLCAvgD7uA9r3z7eu%2FjICMnKgqq9By28HJc3c7SUkPZnDqbHkET6gvLLN9e9LUrISlMB6u0yClGkP%2BTYu%2BsvlyJ24J3727zZZX __________________ *AUREN WUCIN GADI* Chapter 25 "Idan yana da farare bugun abuja shi besan dacewa a rayuwar sa bane? Jibe shi fa tsofe tsofe dashi yawani biyo yarinya karama yana furta wani banzan kalma wai so mtsss yaja tsuka abun ko daɗin sauraro babu wallahi. Dariya khalid ya fashe dashi harda riƙe ciki ganin da gaske abokin nasa kishi ke cin sa dan yana gani cikin kwayar idon sa,sai da ya tsagaita da dariyan sannan ya kalle sa yace"a iya sanina sai da so ake kishi...katse kalid yayi dacewa"bawani kishinta da nake kawai de banason wannan mutumin ya lalata mata rayuwane ko banza karkashina take aiki hakkin kare mata mutunci ya rataya ne a wuyana. Ba tare da khalid yasake bi takansa ba yace"ni kaga bara nage na turo maka da ita...saurin katse khalid yayi yana cewa"excuse me watsa masa wani kallo yayi"ni dan Allah kadena yimun irin wannan kallon naka zuwa zatayi ta gyara nan kafin bakin mu su karaso kasan tun dazu na aiki dauda dauda wato shine mai shara da goge gogen office ɗin Ahmad. Aisha tunda na shiga hall ɗin da muke ɗinki kasa taɓuka komai nayi ba komai ya jamun wannan mutuwar jikin ba illa kuwa kalaman wannan mutumin saboda rashin hankali wai yana sona kuma aurena zeyi, Shin fadila bata faɗa masa alaƙar dake tsakanina da ita bane? Idan ko hakane akwai gagarumin yaƙi a gaba dan mama rabi bazata taɓa barin mu muyi rayuwar salama da mahaifiya ta ba,saboda bala'i zata yi,ko ita kanta fadilan sai inda karfinta yakare akan wannan mutumin da suke gani shine ginshiƙin rayuwar su ya fidda da su daga kanjin talauci. Maganan khalid yadawo dani daga duniyar tunani dana lula idan de ba kunne nane baji da kyau ba kaman naje na share office ɗin oga Ahmad yace"ni kuma ya khalid na tambaye shi cikin rawan murya ina dafe kirjina da hannu dan jin yanda zuciyata ke bugawa kaman ze faso ƙirjina ta fito,innalillahi shine kawai kalla dake fitowa daga bakina. "Aisha ki tashi muna da baƙin da zamuyi suna tafe yi abu da jikin ki,miƙewa nayi tsaye na nufi kofan kamar kazar da kwai na aciki na fita daga hall ɗin tsinkayo muryar laila dake cewa haba"Aisha kaman wacce akace za yankaki irin wannan tsoro haka wallahi da nice nasami shiga haka da gudu zani dan bazan tsaya sanyin jiki ba. ban tanƙa kata ba nayi wuce wata kayan shara na fara ɗauka sannan na shiga office ɗin bakina dauke da sallama jin shiru ba amsa naji sanyi a raina dan na tabbata ogan muzurai baya ciki har nagama abunda zanyi be shigo ba,tattara kayan da ya watsar na fara a raina ina mamakin garin ya ya hargitsa office ɗin haka shi ba karamin yaro ba aiko yarone karami ba zaiyi irin wannan abun ba. Saida nagama na adana komai a muhallin da yadace duk da bansan tsarin komai na office ɗin ba amma made nayi bakin ƙoƙarina dan ganin komai na ajiyeshi bisa tsari sannan na shiga tsince glass cup dana gani tarwatse a ƙasa saida nagama tsicewa tass ba tare da na kula ba nakai hannu na ɗauki tsinsiya ashe akwai glass ajiki ban kula ba na damƙi tsinsiyar da karfi wani irin zafin raɗaɗi ne ya ziyarci hannun na harma da kwakwalwata jifa nayi da tsintsiyar nashiga yarfa hannun na,ganin glass ɗin cikin fatan hannun nawa yasake rikitani da kuma jini dana gani ai kawai sai na fashe da kuka nama kasa nutsuwa na zare glass ɗin sai yarfa hannun nake ina hawaye da dan shasshaka kaɗan kaɗan. Bazato naji hannun mutum saman nawa da nake yarfawa,waro idona nayi ina kallon sa yanda yariƙe nin sai ya haifarmun da wani irin tsoro da fargaba jikina sai kirma yake a hankali yakai ɗaya hannun sa daya da nufin cire glass din dake maƙale cikin hannun nawa wani irin zabura nayi zan miƙe damƙoni yayi yanda bazan iya kwace kaina ba yacire glass din sai hawaye nake yashiga huramun iska ta bakin sa luf nayi sai sauke ajiyar zuciya nake tissue ya ciro ya goge mun wajen sai da ya tabbata ba wani raguwar jini sannan ya sakemun hannun sauri mikewa nayi tsaye da nufin karasa abunda nazo yi"ki barshi kawai naji muryansa kaman wanda akasa dole sai yayi magana"zan iya na amsa mishi batare da na kalli inda yake ɗin ba,saida nagama nazo na goge saman babban table din dake tsakiyar office ɗin naji yana magana cikin kakkausan murya"maza kije ki kuri wancan sokon tsohun ya janye gwangwanin motar sa nan ba wajen wasan yara bane ko dandalin masoya ba kice masa nan ɗin wajen aikine kuma kar yasake zuwa nan ya parka mun mota idan ba haka ba....hannun sa ya matsa yabada wasu irin ƙasa ƙara rass tunda yafara magana jikina sai yasake ɗaukar wani irin rawa kaman mazari kwasa nayi zan fita da gudu ya dakatar dani ta hanyan cewa"wa ze kwashe miki kayan sharan komawa nayi zan ɗauka yariƙo dantsen hannuna da karfi zafin da naji a ƙashin hannun nawa har saida na furta ouuuch kalleni nan yace ƙin kallon sa nayi sai jin sa nayi yace wallahi koda wasa nasake ganinki da wannan tsohun ko naji labari kin gama yawo. Tsaban tsorata danayi da abunda yace na karshe wallahi da kayan sharan a hannuna na shiga hall ɗin da muke dinki sai safa da marwa nake nama rasa abunda yake mun daɗi ashe duka waƴan da suke zaune kowa ido yaxuba mun yana kallona dayawa waƴanda muke hall ɗin tare idan ka cire laila da shamsu bada kowa naje mu'amala ba iya kata da kowa gaisuwa amma ganina cikin wannan hali dayawa suna mamaki to mai yasameni firgici na fita hayyacina lokaci ɗaya. "Wacece Aisha? ana kiranta a waje muryan wani security dake bakin get yayi magana daga baki ƙofan shiga hall ɗin muke. Saurin bin bayansa nayi da kayan hannuna saida nakai bakin get sannan na tuna na ajiye a wajen masu gadi na nufi inda yake tsaye jinjine da jikin motar sa jallabiyace a jikin sa tunna ɗaxu da safe da alama ko gida be tafi ba kenan tundazu. Yana hangoni yafito da saurin sa a cikin motan sa niko nasake tamƙe fuskata nayi ban bari yayi magana ba nashiga cewa"haba dan Allah bawan Allah menaka na shigowa rayuwata dan Allah karabu dani anriga da anmun miji kuma ko da ace babu bazan taɓa son abunda aminiyata keso ba,idan ma ni nafara son abu tace tanaso wallahi ni mai iya sadaukarwane gareta dan haka na haɗa hannuna guɗaya alaman roƙo nace kabarni nafuta,awannin ƙalilan da shigowarka rayuwata kasani nafara fita hayyacina inaga idan kuma muka ƙulla inaga hankalina gaba ɗaya zan rasa daga haka na juya koma ciki ina ta sauke ta gwayen ajiyar zuci kaman wacce tasha kuka shiko anashi ɓagaren Alhaji shehu sake baki da hanci kawai yayi yabita da kallo dan koda wasa betaɓa tsammani yarinyar nan tana magana haka ba.   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "26" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1321786057?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=r7LuHJ7HoP8f96xaRheBeiOlydynbwHFa9XDgIJZ2ldqH7nSQa1%2Bn%2Fn0oPsWogTzkPLRQ1mziNM9svRNgrYx3%2BPU18jny%2BLB8EkqTGD9MIRRUgxyyiGl5QpKmjkQiHQJ __________________ *AUREN WUCIN GADI* Chapter 26 Raina wasai na kama gabana ko ba komai ya rabu dani dan a rayuwa banason mutum yace ze taɓamun mahaifiyata wallahi duk girman sa danake gani daga ranan da yataɓa mun Anna ta wallahi mun raba hanya dashi na fahinci ta dalilin sa fadila tazaɓi wulakantani ranan sannan mama rabi tazo har gida tayita zaginmu harda yimana gorin taimako da suke mana a baya,wallahi koda shine autan maxa daya rage a duniya bazan kulasa ba,balle ma tsohu dashi daya gama expire. Aikina naje naci gaba dayi kusan azahar sai ga manyan ɓaki da alama ba ƴan nan kusa bane duba da yanayin su farari sol kaman larabawa dukkan su su ukun sanye suke da suit ɗaya daga cikin sune ya hau yimana vedio kowa kagani sai gyara zaman sa yake sau ɗaya na ɗago na kalle su shima haɗa ido da mukai da wani kyakkyawan cikinsu bansake gangancin ɗagowa na kalli inda suke ba,saboda yanda yamun kwarjini dakuma yanda zuciyata take dukann tara tara dan bazan iya cewa uku uku ba saboda yafi karfin hakan. Muryan wannan mutumin naji tsaya kusa dani yana tambayata yanda na koyi ɗinkin irin wannan kaya,Ahmad ne cikin kame fuska ya fassara mun abunda mutumin yace cikin harshen hausa dayake shi wancan da turanci yayi magana,kaina a ƙasa nafara yi masa bayani ahmad na faɗa masa abunda nace ta harshen turanci shikuma sai murmushi yake yana yaba kwarewata dakuma yanda nake magana cikin nutsuwa,sake tambayata yayi cikin harshe larabci ko mantawa yayi oho,nan nashiga yi masa bayani ta larabci dan ina jin larabci sosai turanci ne de sai a hankali gaba ɗaya zubamun ido sukai suna kallona tunda basu taɓa jin ina magana da wata yare bayan hausa ba,shi ɗinma bada kowa nake magana ba,oga Ahmad kuwa rungume hannun sa yayi a kirginsa ya gyara tsayuwar sa yana mun kallon gorillah muryanane yafara rawa saboda rashin sabo da yanda kowa yake kallona. Jeho mun da wata tambaya yayi da yasani ɗagowa na kalli fuskar sa wanda ya yalwan ta da murmushi"shin zaki iya bina garin mu?shine abunda yace dani Kai kawai na girgiza masa alama a'a duk yanda yaso nasake yi masa magana ƙin yi nayi dan ni anawa ganin wannan tambayar tasa baya bukatar amsa. "Ba magana ake miki ba kinyi shiru"tambayar tasa bata bukatar amsa shisa banbasa amsan ba,na faɗa kai tsaye ba tare da wannan tsoron shi danake ji ba,kodan ban dago nakalli fuskan sa bane oho,juyawa yayi naji yana cewa da mutumin suhail mutafi ko,har sun juya sun fara fita sai mutumin nan da naji oga Ahmad yake kira da suna suhail ya ciro wani card mai kyau cikin aljuhun suit ɗin jinkin sa ya ajiyamun saman kekena idan kin yanke abu ɗaya ki nemani shine kawai abunda yace ya juya bazato naga oga Ahmad ya yasa hannun sa ya dauke wannan card din ya jefa a aljuhun sa bayan ya watsamun wani kallo da saida hanjin cikina ya kaɗan saboda tsoro. Karfe biyar muka tashi mun fito da laila da kuma shamsu inda suke ƙodani da cewa wallahi Aisha bakiga yanda kika burgeni ba da kika fara zuba larabci sai ma kinga yanda oga yake da hararanku keda wannan mutumin hmmm kawai nace dan bani da baki magani sai kuma shamsu ya amshe yana"to wai da oga ya dauke card ɗinda mutumin yabaki mai zeyi dashi? "Shide yasani kunga bara nayi sauri na tafi dan nabar Annata tana zazzaɓi yau nakare maganar ina yin gaba na barsu a wajen. Suhail bayan sun fita daga hall ɗin sun koma office ɗin oga Ahmad nan yake kara yabon tsarin wajen da kuma ta yanda ya wadata ma'aikatan sa da kayan aiki irin na zamani tare da zaɓan kwararro waƴanda suka san aikin su,Ahmad yaji daɗin yanda abokin kasuwancin nasa ya yabesa gyara zama suhail yayi ya fuskanci ahmad dakyau bayan ya ɗan kurɓi ruwa mai sanyi yace"gaskiya abokina wannan yarinya tamun wallahi idan zaku bani ita zan iya zuwa 9ja da zama,kallon baka da hankali ahmad ya jefasa dashi shide yasan bawai yanason yarinyar bane amma duk sanda wani yanuna yanason ta sai yaji kaman an hura masa wuta acikin zuciyarsa koda kallonta wani namiji yayi wallahi shi kaɗai yasan yanda yakeji daurewa kawai yake shisa ma jiya yayi magana da khalid kan cewa zasu canza tsarin nasu za mai da matama wajensu daban haka ma maza. Bakace komai ba suhail yakatsa masa tunani,ɓoyayyen ajiyar zuciya ya sauke kana cikin nutsuwa da nuna irin i dont care ɗin nan yace"indai kasami soyayyar ita yarinyar to ni mai nawa aciki saide kawai nabiku da addu'a murmushi suhail ɗin yayi najin daɗi daga haka yamiƙe yana ɗan duba agogon hannun sa yace"kamata muje ka rakamu airport nan da minti talatin jirginmu ze ɗaga. Ƴar dariya khalid yayi cike da neman magana yace"kuma kace idan zamu baka mata zaka iya zama garin nan yanzu kuma kana shirin komawa ba tare da....ahmad be bari khalid ya gama maganar ba yace"kana da matsala wallahi shima suhail din kawai yafaɗi hakane dan yaji daɗin bakin sa amma barin kasarsa ya dawo nan da zama ba abune mai sauki ba. Alhaji sunusi waya ƙange a kunne sa sai gani nayi ya zabure yamiƙe tsaye amatukar yazane yana"ina gaja bashi waya"hello oga gaja ya amsa a ɗaya bangaren"riƙe hello ɗinka ashe gaja baka da hankali kai kafi kowa sanin hatsari dake tattare da kuɓutar ishaq daga hannun mu kace na tara ƙattin banza ina ci daku baku da amfanin komai to wallahi na baku nan da awa 24 duk inda yashiga koda karkashin kasane kufito dashi sannan ku kashe shi dan..."nashiga uku alh wa za kashe muryar hajia mariyah tadaki dodon kunnen sa,katsa wayan yayi ya juya ya kalleta rai aɓace ba tare da yayi mata magana ba yayi ficewarsa waje yana sake kiran wayan duk yaransa yace su taru gayanan zuwa yanzu. Minti goma tasada shi da tangamemen gidan gonan nasa rai a ɓace yake kallon su dukkan su majiya karfi gasu manya"aikin banza yanzu duk girman ku ace ishaq yatsare baku sani ba amma kun bani kunya mai amfani ci daku da nake"ɗaya daga cikin su yace sorry oga akasi aka samu daren jiya mun shayune da yawa shisa hakan tafaru amma zamu nemosa da yardan ka. Fuska murtuƙe alh sunusi yayi tattaki gaban wanda yayi maganan yashaƙo wuyasan yace"banza har yanzu mayen be sakeka ba da yardan Allah zakace tuff ya tofa masa ƴawu a fuska ran wannan gayen yayi bala'in baci da abunda alh sunusi yayi masa dan haka yabude baki ciki kakkausan murya yace"ni katufa ma ƴawu alh?cikin ɓacin rai alh sunusi ya juyo gaba garesa yace"an tofa maka mezaka iyayi yafaɗa yana pointin ɗin sa da bindiga,ganin haka yasa sauran suka shiga bashi hakuri dan sun san Alh sunusi ba imanine dashi ba yanzun nan sai yakashe mutum kuma yakashe banza. sai yanzu gaja ya motsa daga inda yake zaune tun zuwan alh sunusi wajen nasu"kashesi zakayi? Shine kaɗai tambaya da yama Alh sunusin da mamaki alh sunusi ya ɗago yana kallon gaja fuska a murtuƙe cike da ɓacin rai mai tsanani dan kubcewar ishaq daga wajen su babban bara zanace gareshi dama rayuwar sa baki ɗaya. Sharce gumi daya gama jiƙashi yayi yabude baki dakyar yace"amma kasan...be barshi ya karasa abunda yayi niyan faɗi ba ya ɗaga masa hannu yace"alh munan dukkan mu haihuwar mu iyaye sukai bawai mun faɗo daga sama bane,kasan muna aiki tuƙuro amma duk sanda kuskure daya tasamu mune da kuskure idan kuma nasarace takace hakan ba zeyu ba,kakawo mana kayan maye munsha to yakakeson muyi in ba bacci ba,kuskurene ya faru tun a waya mun gama magana zamu nemo sa amma kazo kana wa mutune wulakanci to kasa ranka a inuwa zamu nemo sa mukawo maka shi amma da sharadin sai ka haɗo mana da ɗanka usman cikin tawagarmu tashi hankali da basa masa rana ba jagob alh sunusi yazube gaban gaja..   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "27" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1322464236?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=ZbWnkE0LS0hpeGa2d84njJH3fJ5Sl1i47RX%2ByoAFRCKiD%2BDSb4CAj83hTiB9AEf1qs8vwskwLB7S7hz1bDYD1jGn1XY4i0cz%2FUClWRtRVV%2FfqSlKCPSWRmGjFVuG%2F5ip _________________ *AUREN WUCIN GADI* Chapter 27 Saida yashaƙi wani iska sannan yatuna aahefa shine boss ɗin dan haka miƙewa tsaye yayi cike da izza yace"gaja karka kawomun wasa cikin lamurata kuma usman da kuke magana akansa ba zan kawoshi nan ɗin ba koda wani abunne kuma? Shirune yabiyo baya ba wanda ya iya cewa komai dashi sai muzurai da suke ganin basu bashi amsa ba yace"ina goga? Sai a sannan goga yamiƙe daga kwancen da yake saman benci yace"gani mugu uban mugaye ya akai? Murmushin jin dadin kirarin da akai masa yace"kanajin wai mai yaran nan suke fadi kuwa? Eh inaji yafaɗa yana takowa tare da dafa kafaɗan gaja yayi sannan yasoma magana a hankali ai gaskiyar magana gaja wato alhaji gaja yayi matukar kokari kasan yafini basira ga ƙwanya dakuma hangen nesa inaga idan tafiyan nan kasako ɗanka ciki zamufi jin daɗin ai watar da komai karkaji komai Alhaji dakyar da tsiɗin goshi Alhaji sunusi yashayo kansu suka yarda zasuyi aikin ba tare da ɗan saba amma da sharaɗin muddin wasake yi musu irin haka wallahi zasu baryi masa aiki ya yarda dan yasan watukar sukayi ta waye dashi to asirin sa yana gab da tonuwa tunda goga da gaja na hannun daman sane kuma sunsan dukka sirrikan sa sai waƴan da baza'ara ba. hajia mariyah waya ƙange akunne ta magana take tana cewa"yaude kan nagaji da gafara sa wallahi aminiya naɗauki shawararki na shirya tsaf dan zuwa gida malamin nan dakika faɗi,dariya akai mata a ɗaya ɓangaren saida ta sassauta dariyar tata tace"wayagaya miki borno gabas take ai da kintsaya kallon ruwa kwaɗo yamiki ƙafa"hmm kede bari ɗan iskan yaro so yake zautarmun da diƴa wallahi bazan masa da sauki ba. Hahaha akai dariya dayin shewa tace"gobe alhajina zeyi tafiya idan yaso sai mu ɗauki hanya amma fa da ita yarinyar zamu kuma yana da sharuɗan sa"sharuɗa kaman ya? Hajiya mariya tayi tambayar a ɗan ruɗe hmmm hajia balkisu ta sauke numfashi tace yakan sadu a mace kafin yafara mata aiki"nashiga uku ni maryama"a'a karkiji komai ai yana maidawa da budurwa budurcin ta idan ta rasa"taya? Ki fahintar dani ta yanda zan fahinta cewar hajiya mariya dan ita tama kariya da akace sai yasadu da mutum kafin yabada magani. "Yana amfani da kwalba ne wajen siddabarun sa...a'a bar wannan kawai tayi saurin katseta batama bari takai karshe. maganan nata ba,inda wani sai muje amma banson wannan ina dalili garin neman gira a sara ido i hajia balkisu kinfi kowa sanin banson harka dazace sai da saduwa nan na tsani jin sunan ta ma balle aikatata kawo wata shawarar amma wannan batayi ba. Ahmad tunda sukai sallama da suhail khalid ya tafi kaisu airport haka kawai yakasa samun nutsuwa duk wata motsi da zeyi idanunsa aisha yake gani tanama suhail magana tare da murmushi rintse idon sa yayi da karfi yana cewa wai meke shirin faruwa da nine? Daidai basma tashigo office batare da neman izini ba sai ji yayi anyi hoggin ɗinsa tabaya saurin maro manyan idanunsa yayi yana uziyya wanda yasa basma cikin halin ko in kula da yanda yayi ɗin ta juyo zuwa gaban sa tace"my how fa?   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "29" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1323875043?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=spZN6kMyexB8%2BUiiY4h25fG6xbbTQmT%2Bo1bx6LnC7jA1cLgDK4TrELbZQH8rL9LPIbNgT%2FZlLqoDprt7CP3OTsHmn%2FacNkQvehGwfpxRZ0e3rGYEEv%2BC8Xl57WUavP2%2B _______________ *AUREN WUCIN GADI* Chapter 29 Zumbur ya mike kaman wanda aka tsikara da allura yanufi cikin ɗakin dayake jiyo ihun hajia mariya da gudu ita kuma tana shirin fitowa dan neman masu taimako,saura ƙiris yafaɗi da abunda idon sa suka gane masa basma yagani ƙwance idanunta duka a kakkafe bakinta na fitar da wani irin kumfa. Batare daya tsaya ɓata lokacin sa wajen tambayan dalilin ba kai tsaye yanufi bakin gadon ya kinkimota yayi waje da ita dagudu hajia mariya na mara masa baya bayan mota yasaka ta hajiya mariya ma tashiga shima yazaga yashiga mazaunin driver yajasu a guje yafita daga gidan wani asibitin kuɗi yatafi yana shiga harabar asibitin ko parkin beyi daidai ba yafito daga motar yabude kofar baya ya kinkimota dagudu yayi ciki yana kiran"dr dr dr ganin yanda yake a ruɗe yasa kowa hanya yake bashi kafin wasu nurse biyu suka fito ɗauke da gadon ɗaukar marasa lafiya emergency room aka shiga da ita,kafin dr uku suka rufa masu baya tare da kullo ƙafan. Tsakanin Ahmad da hajiya mariya an rasa wanda zeba dan uwansa hakuri itakan hajiya mariya sai kuka take riris shiko ahmad sai safa da marwa yake aranshi kowa Allah Allah kar ƴar mutane tamutu ta sanadin sa,awa uku curr suka ɗauka a wannan yanayin kafin aka buɗe ƙofar wani dr yafito da sauri suka tunkarosa da tambayan ya'ake ciki? "Kusameni a office yace dasu cike da fargaba suka rufa masa baya saida yasamu waje yazauna sannan yamusu nuni da wajen zama,zama sukai jiki ba kwari gyara zaman glass ɗin sa yayi sannan ya kallesu yace"kune kune kuka kawo wannan yarinyar"eh eh suka hada baki wajen amsa masa dan sun kagu yafaɗa musu halin da take ciki. Numfashi ya sauke yana mai kafe ahmad da ido yace"mijin tane kai ko? "A'a ya amsa a gajarce"mamarta ce ni hajiya mariya ta amsa da wuri"ok amma me kukai mata dazafi haka wanda har take ƙokarin illata kanta? Wai maiyasa sam wani lokaci iyaye bakuda kula akan lamuran yaranku wajen maida hankali akan me sukeso dakuma wanda basa so,kuma gode Allah ya takaita kunyi saurin kawota akan lokaci badan haka ba da yanzu saide tashin zance ƴan rubuce rubuce yayi a farin paper ya ɗago yada kallon sa garesu yana cigaba dace musu su kula da ita sannan a kiyaye duk wani abu daze jefa rayuwarta cikin hatsari idan ma saboda saurayi tayi hakan to a gaggauta mallaka mata da abin da takeso dan gujewa faruwan irin haka nan gaba. Aisha A ɗari na shiga cikin gida tun kafin na karasa ciki nake iya jiyo yanda anna ke wani irin tari ba kakkautawa maman salmanu sai jera mata sunnu take,sauri karasowa wajen nata nayi na rungumeta jikina ina kuka da tambayan maman salmanu"meya sameta? Me fadila tamata da tafita yanzu naruɗe har nasara meke mun daɗi sai sumbatu nake ina wallahi idan wani abu yasami anna wallahi bazan yafema fadila ba. Sai kuka nake can da kyar muka su tarin ya lafa tayi matukar jiƙata sai numfashi take saukewa akai akai sake maimaita tambayar tawa nayi me fadila tazo yi gidan mu bayan mamarta ta shata mana layi,da mamaki naga suna kallona khadija ce ta iya bade bakinta dakyar tace"anty aisha ai ba wanda yashigo ina kuka haɗu da anty fadilan dakike ta ambatar sunan ta tun ɗazu? Sakato nayi ina kallon ta to inba ita nagani ba wa nagani yanzu har mukai magana kode nafara samun matsalan ƙwakwalwa ne tun ina mafarkin dare karde ace zaucewa nayi nafara ƴan gane gane. Dafe kaina nayi da hannu biyu dake wani irin saramun nama rasa wani irin tunani zanyi nide nasan tabbas naga fadila kuma harma munyi magana da ita baki da baki ya salam na furta da karfi. Dafani maman salmanu tayi tace"gaskiya khadija tafaɗi ba wanda yazo gidan nan tun bayan tafiyanki aiki jikin mamar taku ya matsa ko makaranta yaran nan basu samu zuba,nayi tunanin yi miki aike kidawo gida saboda jikin nata amma ta hana kiranki,yanzun nan tafara tari muna zaune tare. Tunda maman salmanu tafara yimun wannan bayani jinta kawai nake amma bawai da ina fahintarta ba ganin kaman bana cikin nutsuwa yasa tayi shiru ta barni na kafe Anna da ido kaman me son gano wani abu ajikin ta,amma duk ƙwaƙwafina ba abunda idona suka gane mun tattare da ita,ba wai dan nayarda da abunda suke cewa ba nadeyi shiru ne kawai. Hajiya maryama ta kalli ahmad bayan sun fito daga office ɗin likita fashewa masa tayi da sabon kuka cikin kukanta take cewa"na haɗaka da Allah ahmad ki taimake mu badan halin mu ba kaceto rayuwar basma,yanzu haka ceto rayuwarta ya ta'allakane a wuyanka saurin ɗagota yayi ganin tana neman durkusa masa kafin yayi magana wayansa tayi ƙara cirota yayi daga aljuhun sa yana karawa a kunnen sa,a ɗaya ɓangaren akasoma magana kaman haka"iba kashigane tuntuni muna kiran wayanka baka ɗagawa? Numfashi yafesar mai zafi bakin sa ɗan waigowa yayi ya kalli hajia mariya da sannan matsan ƙwalla take cikin sanyi murya yashiga faɗawa Ammin nasa abunda ya tsaida shi'cike da jimami tace yanzu wani hali take ciki ita basman? "Alhamdulillah ya amsa mata dashi sannan yafaɗa mata sunan asibitin da suke tace gata nan yanzun nan yana kashe wayan ya koma wajen hajiya mariya yace"hajia kiyi hakuri kibar zubda hawayen nan haka komai zezo da sauki kuma in sha Allah inde nine na amince zan aureta saboda ceto rayuwar ta kaman yanda kika bukata. Cike da jin daɗi tawashe bakin ta sai sanya masa albarka take phamacy yanufa dan sayo musu magunguna da likitan ya rubuto masu yana barin wajen takira Alh sunusi ta sanar dashi abun da yake faruwa,aruɗe yanufo asibitin kan kace me asibitin yacika da ƴan uwa da abokan arziki zuwa dubiya kowa kaga fuskansa da damuwa bama kaman alh sunusi dan rufe idonsa yayi yama Ahmad faɗa harcewa yake wani irin zuciyace gareka da batada tausayi sai kace zuciyar kafiran farko yajuya yakalli hajia ma'arufa yace yanzu fisabillahi saboda ba ƴarki bace baki damu kota mutu ko tayi rai ba,kingade halin da ƴar nan tashiga kuma duk a saboda son da takema ɗanki matsayin ki na uwa ki kaddara idan ƴarki ce take a wannan hali wani mataki zaki ɗauka? Ya zakiji abun a ranki? Dan Allah kisawa ranki salama matsayinki na uwa kima ɗanki magana dan sai yafi jin naki magananki dana mahaifin sa. Jiki a sanyaye Ammi ta kalle sa tace"bakomai wallahi Allah yabata lafiya yakuma sanya albarka a abun dama can ni ba hanawa nayi kawai de yanda kukayin ne bemun ba ina lefin tunda dukkan ku kuna da ƴan uwa kamata yayi aje neman aurenta itama kaman yanda addini dakuma al'adarmu ta tanada. Washe baki alh sunusi yayi yashiga da bata baki dan hararo nasaran cikin lamuransa,daga haka sukai masu sallama suka koma gida tare da fatan samun sauki har mota hajia mariya ta raka Ammi nata ta zuba mata godiya. "Aisha koda dare yayi kasa rintsawa nayi saboda abubuwa da sukaima kaina yawa,tabbas nafaga fadila ido da ido amma kowa cewa yake beganta ba a gidan,dan waigowa nayi na dubi sashin da Anna ke kwance"bakiyi bacci bane Aisha? Natsinkayo muryarta"eh nace a sanyaye na daura da cewa Anna aikema bakiyi baccin ba,hmmm ta sauke ajiyar zuciya tana kai gyara kwanciyarta tace"Aisha ɗazu hajia ikilima tazomun da wani batu kuma kinsan yanda muke da ita ba abunda zata nema aguna matukar bamufi karfin abun ba zamuyi mata shi alal hakika zancen da nake dake yanzu an daura aurenki da ɗan yarta ɗazu kuma nasan bazaki zuban kasa a ido ba zaki....bata iyata karasa maganan nataba dan ganin Aisha bata cikin hayyacin ta idanun ta akafe sai wasu irin sammatu take"innalillahi na shiga uku ni nafi wai make shirin faruwa da rayuwar ɗiyar nan ne daidai ta karoso ta rungumi Aisha zuwa jikin tana sakin wani irin kuka mai cikin rai.   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "28" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1323023441?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=axHeNiDjm%2BD%2BoRcFzVn7MM9XJHcRnKt0s%2Be0kDmBhfrXJGAUSf1kQaZMRUoqAWZohf5dqGYZ5UMo7YYdrkssR5gA%2B8cehKyphyLXRImhRhSXo64Q0vK8cboWdUjrRHX3 _______________ *AUREN WUCIN GADI* Chapter 28 Lumshe idanun sa yayi sannan ya budesu tarr saman fuskarta da tasha make up tayi shar da ita"fine ya amsata a gajarce yana mai miƙewa tsaye yasoma tattare kayayyakin sa mikewa tayi ita ma ganin kaman fita zeyi kuma be nuna wani ze kulata ba yasa tace"fita zakayi? "Eh ya amsa a gajerce faɗawa tayi jikin sa tasaki kuka mai tsanani Allah yana gani tana masifar sonsa bazata rayuwa ba tare dashi ba,wani irin ƙanƙamesa tayi tana kuka irin mai cin ran nan"why ahmad? Why meyasa kake hakane? Me lefina dan nace kai nakeso ka kaddara ƙawarka ce ni ko wata ƴar uwarka kace ni yazakaji aranka idan wani yana mata irin yanda kake mun? Shikenan tace tana ɗagowa daga jikinsa wallahi zan kashe kaina shikenan kaima ka huta da taƙura ta saide kasani kafin na mutun sai nabar wasiya cewa kaine silar mutuwata ta kai karshen maganarta bata bashi daman cewa da ita komai ba,tayi waje a guje tana kuka. Jikin sa yayi sanyi sosai dan shi mutum ne mai tausayin mata Allah ya ɗaura masa tausayin su saboda raunin su,iska mai dumi ya fesar yana sake dafe kansa da yakejin yaɗauki dumi dan ya marasa wani irin tunani zeyi zumbur ya miƙe yana mai furta cewa a fili"dolene. na dakatar da wannan yarinyar da sauri yamike yafita daga office ko tsayawa rufewa beyi ba motar sa yanufa cikin sauri yashiga ya tadata da wani irin gudu yabar harabar ma'aikatan nasu dan so yake ya isa dawuri dan dakatar da ita aiwatar da wannan mummunan ƙuduri nata nason kashe kanta,yasan tafaɗa masa hakan kuma shi bega alamun wasaga maganarta ba. Fadila fitowarta gidan su Aisha yayi daidai dashawo kwana da aisha tayi kallo kallo suka shiga yiwa junan su sai aishace ta kauda da komai takira sunan ta. A yatsine fadilan ta juyo tana kare mata kallo daga ƙasa har sama kaman yaune ta soma ganin nata sai can ta buntsure baki tana"a'a kece dama wajenki nazo amma rashin samunki da banyi ba yasa na barmiki sallaho wajen gyatuma idan kin shiga ciki kyaji amma duk da haka bara in faɗa miki abu ɗaya kiyi hankali dan bakin rami ba wajen wasan makaho bane. Kaman bazan tanƙa taba sai kuma naga yana da kyau tagane shirun danayi bawai na tsoro bane ba,fadila naji abunda kikace amma kinfi kowa sanin koni wacece bana haɗa uwata da duk wata shashanci dan ita ɗin duniya tace ita zan kuma iyayin komai akanta duk wani tsegarecinki ya tsaya kaina karki kuskura insake ganin ƙafarki a gidan nan harma da mamarki da bata iya riƙe girmanta ba,kaman yanda tashata layi tsakanina dake ai har yanzu ban tsallake layin ba kode bata faɗa miki tashata layin bane? Hmmm fadila kawata ina tausaya miki irin rayuwa da kika ɗauka sannan karkiji da wai nasan komai kuma kifaɗawa daƙiƙin alhajin nan naki yabar bibiyata dan ni ba kashin dankali bace da duk wani shakatafi ze tayani a karshede ina mai gargadin ki da kitsaya iya limint ɗinki karki wuce ina ganin ƙimarku a idona karki bari yazube dan duk halin da zaki tsinci kanki ciki koda bama tare zanfi kowa shiga damuwa saboda kaunarki a gareni daga haka gida nashiga nabatta nan tsaye tana mai jin haushi da tsanata mai tsanani. Ahmad wani iko Allah ne kawai yakai shi gidansu basma lafiya yana parkin motar sa ko tsayawa kasheta beyi ba yafito da gudu yafaɗa cikin falon gidan bakinsa dauke da sallama ihun hajiya mariyah dayaji daga saman ɗakunan yasashi sankarewa yakasa motsa koda dan yatsansa ne balle ya iya yin wani yunkuri saboda take wani irin kasala yarufesa kansa sai ɗaukan dumi yake. Zubewa yayi agun yana ambato innalillahi sabida son daidaita kansa. ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "30" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1324858585?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=y%2FzFwCXdgt9AGSNAxVcwFBPMHKTRxO77shksd5rtfXNSDRv%2BFni%2F7wBHshg%2FwzefrvXypMVdTj5qh2iXmxqONtlS9UrHMUJ%2BAkBtjLX8ljXQwZXcnlwPGQM%2BoflktDSs _____________ *AUREN WUCIN GADI* Chapter 30 Duk yanda Anna taso danne zuciyarta kasawa tayi saboda yanda Aishsn ke wasu irin maganganu kaman mai aljanu,sai kira take innallahi Anna shikenan mama rabi ta mutu anmata kisan gillah Anna kalli nan kigani na shiga uku sun kasheta suna taran jinin cikin wata ƙatuwar ƙwarya lahaula ya ilalil alamina Anna harda fadila cikin wannan aika aikan kalli kukama take saboda munafinci. Rufemata bakin Anna tayi dan bazata iya sauraron wannan kayan taƙaicin ba cike da tausayin ƴartata tasoma cewa"ya'isa Aisha kiyi shiru ki nutsu bude idonki ki kalleni nan sai kuma tashiga dan marin ƙuncinta a hankali ta yanda bazataji zafin marin ba tanayi tana kiran sunan ta. Duk yanda Anna taso Aisha tayi shiru batayi ba sai wajejen asubah bacci mai nauyi yayi awun gaba da ita. Washe gari muka tashi da mummanan labarin mama rabi ta amsa kiran Allah,sakamakon amai da gudawa cikin dare kafin akai ga zuwa asibiti rai yayi halin sa. Anna tasha kuka sosai da ta tuna da maganganun Aisha na daren juya sai ta ɓarke da kuka karshede sai zazzaɓine mai zafi yarufeta ta lulluɓa da abun rufuwa sai rawan sanyi take kar kar kar. Kwanan basma uku a asibiti zuwa wannan lokacin jikin ta yayi kyau an kuma tsaida lokacin biki sati biyu zo kaga murna da rawan kai wajen basma yayinda ita ma hajia mariya ta ɗaga dubai ranan da aka sallame su a asibiti da dare domin sayayyan kayan gado da kuma kitchen na gani na faɗa acewar ta bikin ƴar gata za'ayi. Ammi zaune take tayi jigum saboda tunani neman mafita wa ɗanta damasu baki ɗaya dan ita harga Allah bata yarda da wannan haɗin ba gani take kaman da wani abun a ƙasa. Kasa hakura tayi saida ta kira ƴar uwarta hajia ikilima ta waya dan su sami zama, Bayan sunyi waya kaman da minti ashirin sai gata dama a hanyarta da zuwa gidan takira ta. Bayan gaishe gaishe Ammi ta gabatar mata da ruwa da lemu da ɗan abun motsa baki sannan suka zauna zaman tattaunawa. Nan ta fayyacewa ƴar uwatata komai"yanzu ikilima ina mafita cikin wannan lamarin nifa gani nake kaman da akwai wata a ƙasa sannan narasa gane kan Alhaji inde magana tashafi Alh sunusi wallahi hankalin sa baki ɗaya bacewa yake bashi da ra'ayin kansa saita wannan bawan Allah wallahi ikilima bana tantama wannan mutumin ze iya kashe rai dan biyan bukatar sa. Nisawa haj ikilima tayi ta kalli ƴar uwartata tace"yaya ni a tunanina mafita shine munewa Ahmad wata ƴar wacce zata kula dashi ya aura. "Anƴa kina ganin Ahmad ze yarda da wannan? Ko wannan da za'ayi yanzu fa saida yarinyar tanemi ta kashe kanta shine fa ya yarda amma tun tuni Alh yana maganan auren yayi biris. guntun murmushi haj ikilima tayi tace"AUREN WUCIN GADI zamu masa kuma na tabbata kafin wa'adin yacika ze sota ya kaunace ta saboda kyawawan ɗabi'un ta sannan wannan yarinya zata maxa kariya gareshi haka shima ze zame mata kariya. "Taya ƴar uwa? Kawo kunnen ki nan tama Ammi wasu maganganu cikin kunneta sai ga Ammi tana sakin murmushi dacewa"inde wannan ce na yarda nabaki wuka na baki nama sai yanda kimayi. "Wuka da nama kika damƙawa ikilima anƴa baza'ayi abun arziki awajen. Dukkansu a tare suka juya dan ganin mai maganan alh badamasi ne da yasako kai falon yake tambaya dan jin maganan Ammi. "Au ashe kana kusa dama maganar lefe naxo muyi dariyar jin daɗi yayi yace"a'a lalle yau anyi abun kirki ashede kin fara hankaltuwa,yakare maganar cike da zolaya. "Au da me kaɗaukeni? Fuska a washe ya amsa mata da cewa"ai ke dince maciji sari ka noke. "Lalle Alh ai kaikan ka kasani idan nayi sarata bana nokewa dan nasan a gaɓanda nakeyi. "Yanzude barwannan ai ni ina jinjina ƙoƙarin kabiru daya iya hakuri zama dake tsawon wannan shekarun batare da anji kanku ba. Saida tayi dariya sannan ta amsa masa da"saboda ire irenku masu bacci da ido yasa kuke kashe abun tare bunne tare batare da kunjimu ba kadeji. Saida suka ɗan taɓa raha sannan ya cake musu maƙudan ƙudi dan hada lefe acewarsa lefen ƴar gata nan yayi musu sallama yafita Ammi tana masa adawo lafiya. Yana fita sai ga Ahmad ya danno kai falo yana waya magana yake ƙasa ƙasa da harshen turanci be kula da haj ikilima dake zauna sana sake tattaunawa da Ammi ba saida yaxo tsakiyar falo sannan ya lura dasu kashe wayan yayi. Yanufo su yana huggin dinsu da ɗai ɗai yana sakin fuska gaidasu yayi a tare sannan ya juya kallonsa ga haj ikilima yana cewa"Anty hajja yaushe a gari? Da kulawa take kallon sa tace"daren jiya Amminka ta hanani sakat dole na hawo jirgi nazo. Maida kallon sa yayi yana kallon Ammin yana marairaice fuska kaman wani karamin yaro"nide dena bina da irin wannan kallon dan ina kan bakana karkaga na amince da auren ka da wancan ɗin nayine saboda tausayi kuma a matsayina ta uwa. Sauke numfashi yayi yace"dan Allah anty hajja kice wani abu mana,cike da shagwaɓa yayi maganan yana kwaɓe fuska. Shafa kansa tayi"tace ai yanzun ma magana da muke kenan,tsayawa zakayi a kan kalaman ka nason matarka ta tare a gidan ka bawai kai kabita gidan su ba. Matukar tanason ka zata yarda ta biyoka gidan ka,sannan kuma kaman yanda ka yarda ka amince kakuma amshi wannan auren to itama yaya so take kayi mata wannan biyayyar kaman yanda muka sanka da biyayya a baya to yanzu so muke gobe za daura maka aure da wata kuma insha Allah zakayi alfahari da wannan zaɓin. A zabure ya miƙe wani irin gumine ya jiƙashi sharkaf tuni yanemi ƴawun bakin sa yarasa muƙushin sa yabushe riƙo hannun sa haj ikilima tayi ta zauna dashi kusa da ita sannan ta soma magana cikin taushin murya tace. "Ahmad kanitsu ka saurare mu da farko de dalilin mu nason yi maka aure ba wai dan mu saka rayuwarka cikin ƙunci bane,munfi kowa son muganka cikin farin ciki da walwala arayuwar auren ka. "Amma anty hajja kubarni naji da abunda yake damuna mana bawai ku sake dauramun wani ba haba anty hajja na dauka zaki rokarma Ammi ta janye da batun auren nan amma sai naga kaman ke kinma fita son ganina cikin damuwa. "Ba haka bane Ahmad ta amsa da sanyi murya. "To yayane anty hajja wallahi ni kaɗai nasan irin ƙunci da nake ciki da maganan wannan aure. "Yauwa Ahmad tsaya kaji dalilin mu muma nason yimaka wannan auren da farko de kai bakacin abinci ƴan aiki. Sannan gyara maka makwanci dakuma wanke maka irin ƙananun kayanka irin gajeran wando dade sauran su sai matar ka kula da duk wasu kananun abubuwan cikin gida. Kasande ɗakin kwananka sirrinka ne kai mai gida be dace ace wata wai ƴar aiki tashiga dan ta gyara ko tashere maka ba sai matar ka. Amma idan kana ganin matar taka zata iya kula da dukkan waƴan nan abu buwan dana lissafo to shikenan. Ammi ta amshe tana cewa"ina fa zata iya yarinya da akace ko pant tacire nan take bari sai mai aikine zata dauke mata yo ina kike tsammanin zata yiwa miji saide idan ko shime xe zaje yayi kayansa amma wannan ƴa bana tunanin ko ruwan shayi ta iya dafawa. "Ai yaya karin wani ta kaicima sai kingani wallahi har pad idan tayi amfani barin sa take cikin pant ɗinta sai mai wankine ze cire ya yar shisa duk mai wanki da suka ɗauka idan yayi sau daya baya sake dawowa dan gudun kayan ƙazanta,tunda suka fara magana shiru yayi yana jin abunda suke tattaunawa akai ɗin xuciyar sa takasa yanke masa abu guda. Sai maganan haj ikilima ne yadawo nashi inda take cewa"kede yaya bari kawai inaga kawai AUREN WUCIN GADI zamu masa idan yaga kamun ludayin matarsa nan da wata uku saiya sauwake ma yarinya takama gabanta koya kikace? Hakane amma kinyi tunani mai kyau yaxamu da iyayen yarinya kode zamu faɗa musi manufarmu ne. "a'a yaya kawai matsayin ƴar aiki zamu daukota sai musami wani malami ya daura auren. "Anty hajja wannan wanj irin magana kuke dan Allah. "To kai ina ruwanka ina kai kasan ita din matsayin matarka take yo mai aciki dan ita bata sani ba. Kawai mu kalla daya muke jira a wajenka wato na amince shikenan sauran komai kabarshi a hannun mu. Sauke numfashi yayi yana duba agogon dake daure a hannun sa yace"ni zantafi inada abu yin sosai amsarku kuma shine yaɗan kalli ammin sa yanda ta zuba masa ido tana jiran taji wace amsa ze bada gyaɗa kai kawai yayi batare da ya iya furta komai ba saboda yanda yaji bakinsa yamasa dauyi lokaci guda. Kabbara da Ammin tayi yasashi dan bude idonsa daya lumshe yana zubasu saman fuskarta hango farin ciki dayayi kwance saman fuskarta tana ta sakin murmurshi da sanya masa albarka yasa yaji sassauci cikin zuciyansa koba komai tu da mahaifiyarsa tana farin ciki koda shi ze shiga ƙunci yayarda gwamma yarasa nashi farin cikin ita ta dauwama cikin ta. Karfe goma daidai aka kai mama rabi gidan ta na gaskiya Allahu akbar duniya kenan budurwar wawa duniya gidan kashe abu,shikenan mama rabi antafi kenan saide muce Allah yajikanta da rahmarsa. Mutane da yawa sun halarci jana'iza ciki harda irin su Alh shehu Alh sunusi dama wasu manyan da dama mutane dayawa suna mamakin ganin irin manyanda suka halarci jana'izan saide wajen wasu ba abu mamaki bane duba da yanda fadila take bin manyan mutane. Sanda Aisha ta matso kusa da fadila dayi mata gaisuwa da jajanta mata kan rashin mama rabi da sukai kuka mai tsanani fadila taɓarke dashi wanda tunda akace mama rabi rai yayi halinsa bayi irin sa ba sai yanzu. Rike hannun Aisha tayi gam ida kadai tasan abunda takeji a ranta dangane da ido hudu da sukai da Aisha dakyar Aisha tamu ta kwace hannunta daga irin riko da tayi mata sukai sallama ita da Anna da tafita jikin Anna duk yayi sanyi haryanzu zazzaɓin be saketa ba,suna fitowa bakin ƙofan gida kaman ance da Anna ɗago kanki kawai sukai ido biyu da Alh sunusi dake kokarin bude mota cak ya tsaya daga bude motar"Na...na..nafi yakare maganan da in ina Anna kuwa nan take taji zazzaɓin yasake wani karfine yazo mata ta fizgi hannu Aisha suka ranta ana kare....   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "31" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1325206030?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=AxH4QZTV8l6xdHt3va0ZpbGAuLv6krYRhFRhd%2BUp9UqdUyfpzh8ezwHxZvg6I7YHEtU0oEegpdSWKFQu4zFzZFomfRfnJCgibWtGNQrrSvZaftGNdzw%2FlZS58su2%2Bhlo ____________ *AUREN WUCIN GADI* Chapter 31 Gudu kawai Anna take tana janye da hannu Aisha wacce batasan dalilin gudun nasu ba. Saida suka shiga wani lungu sannan suka tsaya Anna tana haki ita ma Aishan haka kallon Anna tayi kafin tayi magana Anna ta rigata fadin. "Aisha kiyi maza ki barnan kuka karki kuskura kice zaki juyo duk abunda kunnuwanki zasu jiyo miki,kuka Aisha ta fashe dashi tace"dan Allah Anna ni ki nutsu kimun bayani ta yanda zan fahinta, Waye wannan din damuke gudun na sa? Kuma meye alakarmu dashi dakika saka muke wannan gudun domin sa? Dan Allah Anna kicire ni a duhun nan ta yanda zan iya fuskantar sa,idan yafi karfin ki ai befi karfin hukuma ba. Maganganu mutane da suke jin yana kusonto su shiyasa Anna yin karfin hali cewa da Aisha"maza kitashi ki tsiratar da rayuwarki data ƴan uwanki amsan waƴan nan tambayoyin naki zaki samesu gida cikin tsohuwar akwati dake cikin ɗaki hanzarta kije ki dauki ƙannenki kije gidan haj ikilima. Aisha sai kinzama jaruma kafin ki iya yakan sa wannan yaƙin na mahaifinkine ki kaddara a ranki tamkar muna tare dakene maza miƙe.....kafin Anna takai ga karshe maganan ta suka jiyo wani dargagegen ƙato yana cewa sauran"kuzo gata nan jin haka yasa Anna ture Aisha dake kuka ta ƙankameta tana"wallahi ni ba inda zani nabarki. Da karfi Anna ta tureta daga jikinta tana"yazame miki dole Aisha kimun alkawarin zaki kula da kanki dama yan uwanki kizamo mai hakuri da mutune ita duniya makaranta ce mai zaman kanta maza gudu karki kuskura ki juyo sugane fuskarki. Atare suka mike tsaye Anna tayi kudu da gudu dan son daukewa wayan nan kartin hankali yayinda Aisha tayi arewa tana kuka tana gudu kaman ranta ze fita kukan rabuwa da Annanta haka suka rabu kattin nan suka rufawa Anna baya. Ahmad zaune yake yayi zurfi cikin tunanin sa har besan sanda Abokin sa faisal da khalid suka shigo office ɗin nasa ba,saida faisal yabuga table din gaban sa sannan yayi firgigit yadago yana kallon su. Yatsine fuskan sa ya ɗanyi yana mikawa faisal ɗin hannu suna musabaha zama sukai saman kujera"guroom to be abokina yafaɗa yana dariyar shekiyanci. Khalid ya amshe da cewa"karshede wani ze angonce sai mucire shakkun ko aljana ta aure shine saboda naga kaman matan ma tsoron su yake. Dariya suka fashe dashi a tare taɓe baki yayi yace"kai kasani de da shegen gulma ba abunda ka iya sai kai kawo da ƙule ƙule katashi daga ɗan kasuwa kanason komawa dallalin haɗa aure. Sosai maganar tasa tasaka khalid dariya dan yasan kan suhail yake magana shiko yanzu daya shigo nan ɗin dan suna tare da faisal ne yasa be nemata ya haɗasu a waya kaman yanda suhail ɗin ya bukata tun jiya yadame sa da kira ba. Rike baki faisal yayi yana mai cewa"kace basai na wahala wajen neman mata ba kenan. "Raba kanka da sharrin sa faisal da ina dillancin hada aure ai da banbari ya amince da wannan chewin gum ɗin tasa ba,kaide kawai ayi sha'anin ne. "Sai naji abun alheri abokina cewa faisal yana ɓagarar da maganan Ahmad din nacewa na khalid dillalin haɗa aure. Taɓe baki yayi yana wani basarwa kaman badashi yake maganan ba. Damuwa fal ransa yamasa wanda ze tunkara da wannan abun,wai kaman sa ace za aura masa mata har biyu amma ba zaɓin ransa ko ɗaya ciki. Gwara basma yasanta amma wancan ta WUCIN GADIN fa? "Gaskiya an cuceni yafurta hakan afili ba tare da yasan ya furta hakan ba,dan yanda abun yake cinsa arai haka shi kaɗai yake ta surutu a ransa kaman wani zautacce. "Lafiya abokina? suka haɗa baki wajen tambayan sa cike da kulawa dan ganin yanda ya faɗa lokaci ɗaya kana ganin sa kasan yana cikin damuwa kawai faɗine baze yi ba. Shiru yayi musu batare daya iya cewa komai dasu. Dafashi khalid yayi yana cewa"na ɗauka munzama ɗaya bakada wasu waƴan da suka fimu meyasa bazaka iya share damuwarka damu ba. Shin muda muke faɗama tamu damuwar bamusan muɓoye maka bane? Kode baka ɗaukemu kaman yanda muka dauke kabane"ashe mu bamuda hankali ko bamusan ciwon kanmu bane muke fada maka tamu damuwar ko. Faisal ne yafaɗi hakan cikin ɓacin rai ganin kaman ransu yaɓaci dashine yasa shi fesar da iska mai zafi ta bakin sa yace. "Wallahi ba haka ne? "To yayane suka hada baki wajen tambayansa. Hmmm yasauke ajiyar zuciya yana cewa"wallahi bansan ta inda zanfara bane kuma bansa wanda zan tunkara da wannan abun danake ganin sa kaman a shirin film. "Oh ashede haryanzu baka daukemu a matsayin ƴan uwanka ba kenan? Cewar khalid. "Haba khalid meyasa kake cewa haka kaima kasan bani da kamarku yayi maganan da tsigar lallashi. Hmmm"karya kake damuna da wannan matsayin a gunka bazamu zauna muna tambayanka damuwarka kake wala wala damu ba. Faisal kan yacika harya batsa saboda fushi ya dauki wayan sa daya ajiye saman table yamike tsaye yana mika musu hannu batare da yayi wata magana ba kana gani kasan fushi yayi. Riƙe hannun sa Ahmad yayi ya zagayo gaban sa suna fuskantar juna yace"yanzu faisal fushi kake dani? Ninefa abokin da kazaɓa tun muna yara a bainar jama'a. Murmushin gefen baki faisal yayi yace"ko wancan lokacin ma ƙuruciyace tasani zaɓanka me za'ayi da aboki irinka mu idan mun ɗauki damuwarmu ko matsalarmu da muke tun kararka ai bamu da wayone kuma bamusan ciwon kanmu bane. "I'm sorry F Hmm kawai faisal yace yana mai zare hannun sa daga rikon da yamasa yanayin gaba. "Ai nace kai hakuri ko? Dan Allah khalid kasa baki yayi hakuri yazo mu zauna muyi magana nidinma ai bani da kamanku kawai de banson tada muku da hankaline ku ma. Yayi kalan tausayi abunka da ɗan uwa kuma abokan juna dole suka zo suka zauna su kai shiru suka zuba masa ido danson jin abunda ze fito daga bakin sa. ********* Aisha gudu take tana kuka baiwar Allah haka tanufi gidan nasu tana zuwa bata tsaya ɓata lokaci ba dan bata da nutsuwar tsayuwa tayi tunani ko dayakar wani abu. Tana shiga ɗakin kai tsaye wajen akwatin karfe tanufa tana budewa wani kundi taci karo dashi bangon sa an rubuta mai DERTINY da manyan harufa harta dauko zata rufe akwatin idon ta yasauka kan wani album na hoto dauka tayi idanunta yana tsiyayar da hawaye harta kai bakin ƙofa tasake waigowa tayi wa gidan dakuma ɗakin su kallon karshe abubuwan da suke agida tare da Annanta da kannenta yana fadomata arai sauri fita tayi a gidan gudun kar maman salmanu tafito ta ganta ta tsareta da tambaya dakuma tuna maganan Anna. "Allah yakaremun ke Anna ya kuɓutar dake daga hannun waƴan nan azzaluman sai inda karfina yakare wajen wannan yaƙin koda zan rasa rayuwata ne saina cikawa Abbana burin sa,daga haka tasakai fita.     ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "33" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1326082248?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=C4QDeYFqby%2FMM04Ia2QhhGo2uX4B3hd%2BPHkG5d%2FZMOm8RlHjoVVLNkvvTccA11u5Zdi%2F9zo9e2l%2Fc9V2JbzAqm0MstcMaY5lBK3iSS9D%2FoHBduM4YqoYSNhDSkAIpJSK _______________ AUREN WUCIN GADI Chspter 33 Diro a motan da su goga sukayi suka nufo wanda Alh sunusi ke ciki suka bude masa kofa gaja yace"Alhajin Allah fito fatan ba abunda ya sameka ko? Eh eh yace duk ya rudewa iya ruɗewa idan akwai abunda ya tsana a duniya shine mutuwa"Alhaji wannan tafiyan batada sana'a kawai mukoma abari zuwa wani lokacin idan ka matsa bamusan abunda zamu tadda gaba ba. Ya gamsu da bayanin gaja dan haka sauya mota yayi yashiga nasu sukuma suka shiga nasa daya bige suka juya baya. Basma da ke zaune tsakanin ƙawayen ta wasu nashan syrup wasusun na afawa dan kunsan yawancin matasan mu nayanzu wasu suna ganin hakan kaman wani wayewa ne. Allah ya shirye mu baki ɗaya. Nan sukai ta tattauna yanda zasu shirye party bikin sun tsara taron da zasuyi har tsawon sati zasuyi suna shagalin bikin su,wanda wasu a cewar su dole sai ango ya halarci shagalin. Ahmad cikin sati ɗayan nan duk ya faɗa damuwa fal ransa yanaji ajikin kaman yayi kewar wani abu amma kewan menene de besanin ba saide tabbas yana jin yayi kewa acikin zuciya da ruhin sa. ****** Aisha yanzu de tazama ƴar gida saboda yanda kowa yake ƙoƙarin sa dan ganin sun sake dasu Alhamdulillahi ta ɗan sake saide abun da ba'arasa ba,kullum daren duniya sai tayi mafarkin Anna saide takanyi mafarkin ne tana ganin ta cikin kyakkyawar yanayi tsaɓanin da datake yawan mafarkin abin tsoro ko kuma ana azabtar da ita. Taɗan sake ba lefi amma haryau jiknta akame yake dasu kwara ummu salma tafi sakewa da yarinyar saboda akwai da shiga rai gata da ɗan banzan surutu irin yaran nan ne masu suturu. Kitchen ta nufa nan ta iske hajia ikilima da ɗiyarta malika suna ta kiciniyar haɗa abun kari,gaida hajia tayi sannan ta gaida malika amsa mata sukai fuska sake. "Amm hajia me zankama miki? fuska dauke da murmushi hajia ikilima ta kalle ta tace"amma ai saikin cire wannan hijabin naki dariya malika tayi tace"wallahi ni Anty hajia mamaki ma wannan ɗiya taki take bani mutum kullum kumshe a ɗaki idan anyi sa'a ta fito saide da zumbuleliyar hijabi wannan mijinta zesha fama duk tabi ta ɓoye abubuwa. Dukanmu dariya mukai atare jin abunda malika kecewa"kai Anty malika nace ina ƙoƙarin cire hijabin dan saka musu hannu a aikin nasu sannan nikaina ina da bukatar koyan kalolin girke girke tunda ban iya abu dayawa ba saboda matsalan rayuwa da muka taso. Wanke wanken farayi inayi ina ɗan kallon yanda suke sarrafa komai nasu cikin gwarewa"Anty malika inaso fa ki koyamun girki irin taku ta ƴan gayu yanda nakare maganan saida ya basu dariya"to ai gidanta kikazo inde koyan girkine ganan oganniyata nan tafaɗa tana nuna hajia. Koba komai na ji daɗin yanda suke jana aji ba nuna bambanci su ƴaƴan masu kuɗine,komai ake agidan sai an sako dani dan son nakara sakewa dasu. Da yamma ina zaune can bayan gidan cikin wasu furanni wajen yana da daɗin zama musamman ga irin waƴan da suke bukatar keɓewa,nayi zurfi cikin tunanin ta inda zanfara. Zumbur na miƙe kaman wacce ta mitsina ɗakin da aka ware mana nida ƴan kannena na nufa,wani baƙin riga da wando da malika tabani nasaka na daure gashin kaina baya,nasaka hijabi har ƙasa sannan na nufi falo na tadda Anty hajia ita kaɗaice zaune tana kallon tashar saudiyya a tv har kasa na duka nace"barka da yamma Anty hajia. "Barkade Aisha ina kika shiga dazu na leka ɗaki bakya nan? "Eh wallahi ina can bayane na amsa mata. Maida hankalinta tayi kaina tace"Aisha inaso kisawa ranki salam kuma in sha Allah ba abunda ze faruda mamartaku sai alheri Alh yasaka jami'an sirri suna yin aikinsu ba dare ba rana mukanmu addu'a ya kamata mubisu dashi Allah ya bayyana mata da ita duk inda take cikin ƙoshin lafiya"Amin na amsa idanuna na tare kwallah. Ba kuka zakiyi ba Aisha lokacin kukanki ya wuce yanzu lokacine da zaki zama jaruma ki koyi juriya sannan ki karfafawa kanki gwiwa wata zuciyar ta bata amsa. "Share hawayenki kinji karki bari hawayenki ya zube abanza idan da wanda kike zargi ko tuhuma ki faɗamun zan sa ayi mana binciken sirri dan yayanku faisal jami'in sirrine na farin kaya kina iya tuntuɓan sa ze tamaka miki dari bisa ɗari bani da haufi kansa. "Babu Anty hajia kuma nagode da kulawarku kanmu ba abunda zance dakun sai fatan Allah yasaka muku da mafificin alheri yabiyaku da gidan aljanna"amin ta amsa tana maijin daɗin addu'ar har cikin ranta kuma take tausawa yaran nan da mahaifiyarsu tuntuni take da niyar daukan dauwayniyar karatun su dakuma bukatunsu na yau da kullum Allah ne be nufeta wancan lokacin ba dan komai baya faruwa sai da nufin sa. "Anty hajia inason nazan ɗan leƙa anguwar mu ingani wala Allah ko wani yaga Anna nayi maganan cikin sanyin murya da mutuwar jiki. "Ok Aisha amma dole ki canza taku dan bazaki fita haka ba,faisal ne ke magana dan shigowarsa falon yaji ina tambayan fita,kallon kaina nayi nagade shigar da nayi bata da wani aibu tattare da ita maida kallon nayi kansa ga mamakina sai cewa yayi cire hijabinki. "Wai me haka faisal? Hajia tayi tambayar tana kafesa da ido shima kallon nata yayi yace"come Anty hajia wani aiki zamu fara da ita daga yau yanzuma kuwa dole saita canja takunta tatashi a wannan amai sanyin takoma mai zafin. "Aiki na maimaita maganan a fili?"yes aiki dan haka kisameni a garden zamuyi magana yana kaiwa nan yamiƙe yayi waje a sanyaye nakime jiki ba kwari,karfamun gwiwa Anty hajia tashiga yi tana cewa"ki daure Aisha nasan zaki iya kuma na yarda da faisal bazai saka rayuwarki cikin hatsari ba. Kowace rayuwa dakike gani tana da irin tata kalubale harda ma masu kuɗi dakike gani wasu tasu ƙalubalen idan an daura miki akanki ko an fayyace miki sai kin kwana sallah kina godewa Allah da ni'ima da yayi miki,jinjina mata kai kawai nashiga yi dan bani da wani karsashi daya saura mun ajikina. Ina isa garden ɗin na hangosa tsaye yana goye da hannun sa a kirjinsa,sallama nayi ya amsamun fuska sake yana karemun kallo yace"zamu fara wani atisaye dake mai suna CIKAN BURINA. "Cikan burina na nanata"yes ya amsa or operation AS ko ince dake operation Alhaji sunusi,wani irin wuntsulowa nayi idanuna suka firfito idona masu haske da girma barakallah waje ina mai dafe kirjina wacce take mun wani irin lugude kaman zata faso girjina ta fito,kallon sa nake saboda tsaban mamakin yanda akayi yasan wannan shine cikan burina kasa magana nayi saboda yanda bakina yayimun nauyi ƴawun bakina yakafe sai ido wirkil warkil danake binsa dashi nazama kaman wata mutum mutumi.   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "32" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1325618003?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=trb2kxQA0CfzjFUiFnM0ZsVflepU5E0QBvDl%2B3JARypk2DP9m%2ByvaWIPI4%2FLmojlfrYEeZDvhD4e5w8CUGmP9T8sVowGbrTI6QYASc3glq5nH%2BiEgHxf%2FZJSPg1yQg0S _________________ AUREN WUCIN GADI Chapter 32 Tana tunkarar waje ta aro jarumta ta yafawa kanta dan gudun zargi har ta isa makarantar su khadija bata sha wani wuyan ba wajen batasu su fita a ƙafa suka doshi gidan haj ikilima. Duk yanda ƴan ƙannen nata sukaso ta fadamusu ina zasuje bata amsa musu ba. Saima kara ƙami da take wajen yin sauri sun gaji sun kuma galabatu kafin su isa anguwar da haj ikilima take basu sha wahala ba mai gadin yabude musu ƙaramar kofa dake jikin get ɗin suka shiga dayake yasan fuskar Aisha. Sallama dauke a bakunan su suka shiga falon gida haj ikilima da itama dawowar kenan daga gidan yarta,ta amsa musu da sallamar fuska sake"lale marhabin da manyan baƙi Aisha yau kece a gidan namu kushigo ku kushigo ta kama hannun mubaraq tana cewa maigida ba cefane yayade? Aisha ina mamar taku fatan tana lafiya sai a sannan tasamu tasake kukan da take ƙokarin riƙewa tun daxu ya kubce mata a rikice haj ikilima ta juyo tana tambayan ta, Lafiya Aisha? Mesamu Anna? Kimun magana mana Duk tabi ta kiɗime dawowa tayi da tambayar ta kansu khadija dasuma kukan suke ganin Aisha nayi yasasu,wai meyake faruwane khadija meyasamu mamarta ku? Cikin kuka tace"haj wallahi muma bamu sanin abunda yafaru ba kawai de Anty taxo ta daukemu a makaranta mun dawo nan amma ki tambayeta ko zata iya faɗa miki. Jinjina kai kawai haj ikilima tayi taciro wayanta daga cikin hand bag dinta ta dannawa faisal kira lokacin suna zaune Ahmad yasoma faɗa masu abunda basma ta aikata na son kashe kantakanta. harda barazana data masa harda da amincewar da yayi kan wannan auren da yake gani kaman a shirin film wai shine zai tare gidan su amarya saide shi yatare can kaman wani mara galihu ko mara gata. Wayan hajiar sa shiya dakatar dasu daga tattaunawa da suke"duk abunda kake kabari kazo gida yanzu shine abunda kawai tace dashi ta kashe wayan hankali tashe yamiƙe yana tace dasu"ni zan wuce gida hajia ce tayi kiran nakuma ji muryarta kaman arude tayi magana. "Ya salam suka ce a tare kode zamu tarene Ahmad yafaɗa yana kokarin fita waje"da kabarshi kawai zamuyi waya duk yanda ake ciki kasan halin antyn taka abu kaɗan yake sata rikice. "Ok kawai yace yana dan bubbuga kafadan sa sai najika. Daga haka sukai sallama har bakin mota sukai masa rakiya da khalid sannan suka juya zuwa ciki khalid nufar hall ɗin ɗinkin yayi tunkan yakarasa shiga ya hango bata nan. Time ya duba har sha biyu ta gota laila ya kwallawa kira"na'am yaya khalid ta amsa tana karasowa inda yake saida suka gaisa sannan yake tambayarta"Aisha fa? "Wallahi nima najita shiru yau ko lafiya?amma bata saba kaiwa wannan lokacin haka ba,saide jiya tayi magana kaman mamarta bata batada lafiya Allah de yasa bajikin bane. "Amin ya rabbi Kinsan gidan nasu kuwa? Ɗan jim laila tayi sannan ta amsa tana cewa"gaskiya bansan gidanna su ba amma nasan nguwar su sannan idan ka tambaya kace gidan su malama Aisha ta Nurul huda ba wanda baisanta ba ko ƙaramin yaro ka tambaya. "Nagode yace da ita yana barin wajen. Alh sunusu Lokacin da yayi tozali da Anna yashiga tashin hankalin iya tashin hankali saboda girgita da ganin ta da yayi har wayan da ke ƙange a kunnesa saida tasubuce ta faɗi ƙasa kasa nutsuwa yayi har saida ya kira sunan ta cikin rawar murya. Ganin taƙi tsayuwa yasa yaransa subita su ɗauko masa ita yana bukatar ta a raye,yasan muddin yasame ta to lalle yagama da ishaq duk inda yashiga koda karkashin ƙasa yashiga tabbas zefito. Motan sa yashiga cikin rashin nutsuwa yabi bayan yaran nasa saide neman duniya sukai mata basu ganta ba kaman wata mai rufa ido ta ɓace musu ɓat. Suhail Kiran khalid yayi daga jiya zuwa yau besan adadin kiran da yamasa ba,yanzu ma cikin rashin nutsuwa zuciya data ruhin rashin jinta yasake kiran khalid ɗin,yana ɗaga wayan ko sallama be barin sunyi ba yafara cewa"nasan warhaka tazo dan Allah khalid bata wayan naji muryarta ko zuciyata zata samu nutsuwa. Dafa goshi khalid yayi kaman yana ganin sa yace"ok maida kira video sai kaji dadin kallon,ba musu ya maida shikuma khalid beyi ƙasa a gwiwa ba yasake komawa hall ɗin har sannan batazo ba. Hasko masa da wajen zamanna ta yayi yakuma sake tambaya akace masa bata dazo ɗin ba"kade gani ko wallahi tun safe nake zarya daga office dina zuwa nan amma bata zo ba in sha Allah zuwa anjima zan binciko maka gidan su"promise suhail yace a sanyaye"sure khalid ɗin ya amsa masa. ***** Aisha yini tayi tana kuka tambayan duniya haj ikilima ta mata amma ba wani amsa dan koda faisal ya karaso gidan dan kiran da hajiar tasa tamasa,shima tambayan yayi amma ganin ta kasa bude baki tayi magana da zaran tabude baki da niyar basu amsa sai kawai taji sabon kuka ya kubce mata. Faisal ya kalli hajia ikilima da duk ta damu yace"hajia ina ga a barta kawai tasamu nutsuwa kila ta iya faɗin koma menene ke faruwa dasu,amma yanzu idan ance sai tabude baki tayi magana ze iya zama kaman taƙurata ake. Aisha tashi kishiga ɗaki kikwanta ki huta dan Allah kibar kukan nan haka karwani ciwon yakamaki. Ɗaga kanta kawai ta iya yi gashi kanta yayi wani irin nauyi dakyar take iya bude idanunta saboda nauyi da sukai mata,miƙewa tayi harwani irin dish dish take gani saboda jiri data ke gani miƙewa tayi hajia ikilima da duk tadamu ta taimaka mata wajen mikewar album din da tadauko dakuma diary ne suka faɗo daga saman cinyarta ƙurawa bangon littafi dake rubuce da DESTINY faisal yayi kan yayi yunkurin kai hannu Aisha ta duƙa a sanyaye ta ɗauki abunta. BAYAN SATI ƊAYA ___________________ Aisha ta dan sake a gidan dan hajia iklima da mijinta dama yaran baki daya suna zaune a falo ranan da suka ciki sati a gida,Alh auwal yabude da addu'a sannan yayi musu nasiha sosai akan riƙe gaskiya da amana yakalli ƴaƴan sa faisal shine babba sai malik da malika ƴan biyu sai fadil da sa'id sai autar su ummu salma,yace faisal ganan Aisha da kannenta cikin mu Allah ne yakawo ta cikin ku kuriƙeta tamkar ƴar uwarku ta jini kutsaya mata duk abunda take da bukatar a tsamatan babu ƙyara ko tsunguma itama dayace cikin mu. Kallon Aisha yayi dakan ke duƙe yakira sunan ta amsawa tayi cikin sanyi murya yace"inason ki kwantar da hankalin ki kuma kidawo da nutsuwarki ki karfafa gwiwanki gaduk abunda kika saka gaba karki kalli faɗiwa a rayuwa kullum ki kalli nasara wannan shi zai kaiki ga nasaran sannan ganan ƴan uwanki duk wani abu daya taso miki ki samesu zasu tsayamiki ki daukemu tamkar iyayenki waƴan nan kuma ƴan uwanki hajia kuma mahaifiya. Tuni kuka ya kubce mata tana fadawa jikin hajia iklima. Alh sunusi jin Anna taɓace musu yakai gwaro yakai naushi sai cizon hannun yake kawai yakira su goga da gaja a waya yana cewa su shirya yau garin ƴar daje zasu"lafiya de ko gaja ya tambaye shi"eh kawai ya amsa mishi a gajarce. Da yake tafiyar gaggawace be koma gida ba kawai waya yayi yasanar da hajia mariyah duk da bata garin suka dauki hanyan daura tunda suka dauki hanyan waya kawai yake akai akai duk bayi da nutsuwa sun fita garin kano sunyi tafiya mai nisan zango kaman daga sama yaji motar da yake ciki tadaki wani dotse dake gefen titi wani irin ihu ya saka yana kiran goga na mutu.   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "34" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1326430067?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=Fhw3IXV3t7pACUlTsoUisXeWxsghQyXm9bOlIjg%2BaxkMUxcqwU9Si6cYHZF8b52UndP1xcuDiJxUalSqUP3vHBYP2xU6QMYgEmyzs8%2BIhCCyPNpwh3zLL4gMcRWIShOt __________________ *AUREN WUCIN GADI* Chapter 34 "Kinyi mamaki ya'akai nasan wannan ko? Shiru nayi masa wannan kundun yanuna mun yans cigaba da cewa wannan shine amsan ki,rannan da kukazo gidan Anty hajia takira ni da nadawo gida sanda kika tashi tsaye yafiɗo ajikin ki. Tunda daga kan rubutun bangon littafin danayi a ganin farko na fahinci zan masu sirrika da muka daɗe muna nema bamu sane sa ba. Dalilin wannan nayi ta bibiyarki kafin kisake dani dakyar nasamu na dauki littafi shafi biyu kawai na karanta a ciki sauran aikin kece zakiyi nikuma huras wace tawa saide aiki yanada hatsari tunkarar mutum kaman Alh sunusi. Numfashi nasauke sai yanzu nasami daman yin magana nace"shidin ba mutum bane? Murmushi faisal ya sakarmun yace"mutum ne shi amma ba kaman kowa ba,sabida dalilai da yawa,abu nafarko da nakeso kisani kuma ki zauna kiyi tunani akai shine taya mutum mai imani da sanin yakamata ze saka rayuwar abokin sa aminin sa cikin hadari bayan bashi da kaman sa ya rabashi da ahalin sa na tsawon rayuwa yacutar dashi zekuma kashe rai dan biyar bukatar sa bakomai bane a wajen sa yin haka. Alhaji sunusi Duke yake gaban shugansu duk yabi ya haɗa zufa yana cewa"ya shugaba abu lamarin nan wallahi kuɓutar ishaq da matarsa hatsarine gare,nayi kokarin bin bayan ta amma wallahi kaman mummunan kadamine ke bibiyata mota ta hanani tafiya. Aduba mun ko zasan inda suke"hhhhhhh dariya shugaban ya tuntsure da ita yace"kaga kwantar da hankalin ka ishaq mun gusar masa da hankali baze iya tuna kansa bama balle wani koya ya iya tona maka asiri, sannan ita matar ai tuni tayi hadari ta mutu garin gudun ceto mota tabi ta kanta matso nan kagani. Matsowa Alh sunusi yayi yayi wani tanƙamemen ƙwarya dake gaban sa mai cike da wani irin ruwa mai yauƙi ne ya bayyana yana leƙawa kowa sai ga wata mata tana falfala gudu taxo daidai bakin gwalta wata mota kuma tazo da karfi tabi ta kanta,ajiyar zuciya yasauke yana cewa duniya sabuwa yanzu bani da wani saura fargaba. "Nuna masa wata ƙwarya shugaban yayi da hannu ko beyi magana ba yasan me yake nufin da yayi tuɓewa yayi yasa alƙalamin sa cikin wannan ƙwarya wani irin turirine yake fita ta dukka ƙofofin jikin sa dukka wannan abun saboda son duniya yake yinta. Allah yakare mu da son zuciya koda yaushe kasa mufi karfin zuciyar mu kakaremu da imanin mu ja kyautata karshen mu Allahumma amin. ****** Yau tun safe ta shirya dan ta fita aikin ta kuma a yaudinnan take son fara yin suwa bincike dan gani take sau da yawa ana ha'intar Ahmad ba tare da sanin sa ba. Shiga ta alfarma tayi da daya daga cikin kayan da malika ta bata light me up tayi tayi rollin kanta da tsiriyar gyale ta fito hannun ta rike da hand bag ɗinta tun kafin ta karasa shigowa falon ƙamshin turen da tafesa yadaki hanci ƴan falon da kallon suka bita dan ba karamin kyau tamusu ba yau"masha Allah malika ta furta tana yaba kyaun da tayi yau,malik kuwa kallo ɗaya tamata ya dauke kai yana taɓe baki da cewa"sai wani zuzutata kuke kalen son yarinya fara raina mutane,dariya hajia ikilima tayi tana cewa"a to mutum koya ƙyasa saide yayi hakuri dan ba bashi diyata zanyi ba. "Allah ya sauwake wallahi narasa wacce zan so hajia sai wannan kucakar yarinyar,yafada yana nuna Aisha da hannu ku kuke sawa ta raina mutune. Miƙewa yayi yanufi ƙofa yana kaɗa makullin motarsa"yaya malik dan Allah idan fita zakayi karage mun hanya zazzaƙar muryarta mai dadin sauraro ya daki kunnen sa. Tsuka yayi"dan Allah yaya malik cewar malika "mutafi amma wallahi idan kin ɓatan lokaci da wannan yauƙi naki tafiya zanyi na barki. Tunda ya doshi bakin get ɗin ma'aikatan nasu ake ta kallon su dan basaba ganin ta da irin wannan shiga ba,sannan a wani ya kawota da mota kai koda wani namiji daban shisa abun yazame musu kaman sabon abun ita kanta jitake banbarakwai wai namiji da suna larai. Motar Ahmad ne yadoso tasu tunda ya doshi inda suke tsaye ya kafeta da ido jiyake kaman ya sauka ya hauta da duka dan haushin ganinta tare da wani haka kawai yaji wani mololon abu ta tsaya mashi amaƙoshi. Shi be zaice yana sonta ba amma duk sanda yabude ido yagata tare da wani ɗan namiji suna hira tasake fuska tana murmushi ko dariya sai yaji wani abu mai kama da kishin ta yataso masa. Yanzu ma hakance ta faru fashi ganin ta da malik yayi mamaki ba kadan ba ina malik yasanta kode budurwar sace"kai ina ko faisal yaushe yake da budurwa balle malik yaro dashi nawa yake,haka shi kaɗai yayi ta surutansa kaman wani zautacce har ya karaso yayi parkin motarsa daidai khalid daya iso inda suke yana cemata"nagode Allah sister yaude gaki ina kika shigane tsawon mako guda ba sanarwa suhail yana neman kasheni da kira. Fari tayi da ido tana sake kallon sa tace"yaya khalid ina kwana shima malik yamika masa hannu sukai musabaha sannan ya zagayo suka gaida da Ahmad daya kafesu da ido. "Ya karatu? Ahmad din ya tambayi malik"Alhamdulillahi ya amsa masa yana cewa dama wannan kwailar nan take aiki ashe? "Uhmmm kawai ya iya yacewa batare da yasake kallon inda suke tsaye da khalid dake ta zuba ba. Shi kaɗai yasan abunda yakeji a zuciyan sa,sallama malik yayi masa yadawo inda khalid ke tsaye yamasa sallama harya kama murfin motar ze bude ya shiga yaji tana cewa"yaya malik injira ka anjima zaka dazo?yanda tayi magana tana wani shagwaɓe fuska sakin murfin motar yayi yayi kanta ai kuwa dagudu ta ranta tayi ciki tana dariya shikuma yakoma yana zan gamu dakene yarinya. Tana dariya tashiga balcony da ze sadata da ainihin hall ɗin da suke ɗinki batayi aune ba taji an damƙo mata hannu bude baki tayi da nufin kurma ihu kaman yasan abunda zatayi yayi saurin rufe mata baki da ɗaya hannun nasa,gwalo ido tayi waje saboda tsoro dakuma mamakin wanda tagani ɗin.   ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Chapter 35 Ɗaukan ta yayi be direta ko ina ba sai a tsakiyar office ɗin sa yashiga kallon ta daga sama zuwa ƙasa dakyar ya hadiye wani abu daya tokare masa a maƙoshin sa, Cike da taƙaicin ɗaukarta dayayi kafin yayi magana tariga shi cike dajin haushin sa a tsiwace tace"wai me hadina da kaine daxaka wani kinkimo ni haka saikace wanda ya dauki matar sa? Wani abu yaji yana yayo tun daga saman kansa zuwa babban yatsan kafarsa dakyar ya iya daidaita nutsuwar sa fizgo maganar yayi yace"wani irin shigane wannan da kikayi? Mamakine yacika Aisha a fakaice takalli kanta sai kuma ta maida kanta gefe ba tare data tanka mishi ba,ganin tamasa banza yasake jeho mata da wata tambaya data sata ɗago kanta ba tare data shirya ba,zuba masa idanunta tayi sai ta murguɗa masa baki tana dauke kanta daga kallon sa. Takowa yayi gareta cikin takun nan nasa na ƙasaita baya baya tasoma yi yana biye da ita saida tajin gina da bango takowa yayi daf da ita tokare bangon yayi da hannuwansa duka biyu ritse idanunta tayi da karfi ganin yanda yatsaya daf da ita har suna iya jin hucin numfashin junan su, zubama baby face ɗinta ido yayi yana kare mata kallo wani abu yaji yana taso masa tundaga babban yatsan kafan shi har zuwa tsakar kansa. Wani abu yakeji mai kaman mayen karfe yana jansa zuwa gareta besan sanda yakai hannun sa ɗaya ya dago haɓarta ba,sai jin saukan tattausan leɓenta tayi saman nata. Waro manyan idanun ta tayi bata sauke ko ina ba sai saman fuskan sa da idanun sa suke kulle,wasu zafafan hawaye na zallah takaici da tsanar sane suka shiga zubo mata daga ƙwarmin idon ta. Ɗumin hawayenta dasuka zubo masa saman fuskan sa shiya ankarar da shi kuka take saurin saketa yayi yana ja da baya,ganin ya saketa yasata duka awajen tasaki wani kuka maicin rai kaman ranta zebar gangan jikita tanayi tana goge bakita da gyalen dake kanta tana tofar da ƴawu. Saida ya daidaita kansa sannan ya iya buɗe bakin sa yace,matukar kika sake irin wannan kwalliya kikazo to wannan shine hukunci da zanyi miki,sai na tsotse jan bakin tass...Ɗagowa tayi a zafafe ta banƙa masa harara kaman idonta ze faɗo kasa ta murguɗa masa baki tace"ɗan iska kawai kace kawai iskanci kake neman yi mun. Wani irin zabura yayi jin abunda tace ɗin ƙwasa tayi da gudu tayi waje kaman zata kife,komawa yayi ya zaune saman kugera haka kawai ya tsinci kansa da sakin murmushi da besan dalilin sa ba,dacewa yarinya bar ganin kun tsira zamu haɗune dake. Saida tayi nisa da office ɗin nasa taje can ƙarkashin wani bishiyar maina sannan taji wani irin kuka mai karfi yataso mata,saida tayi mai isarta sannan ta tashi jiki baƙwari tanufi hanyan fita dan tafiya gida. Tana ƙokarin fita wata baƙar mota ta shigo wajen haka kawai zuciyarta ta bata tabi sa komawa tayi da baya ta laɓe bayan wani mota tana kallo wani mutumi yafito daga cikin motar bayan ya faka yanufi ciki wajen direbobi dake lodin kaya suna kaiwa gari gari bayan ɗan shuɗewar minti shida zuwa bakwai sai gashi da wani daya daga cikin direbin sun iso wajen motar tasa a tare shiga ciki sukai sai gashi wannan direban ya fito riƙe da wata baƙar jaka rike a hannun sa sai washe baki yake yana dafe da aljunun sa da alama kudi aka bashi yasa sallama sukai yashiga ciki dan komawa inda yafito shikuma wacan mutumin yaja motar sa yafita da uban gudu. Wallahi tunda take bata taɓa taƙaicin rashin riƙe waya ba sai yau"yama zama dole nafara riƙe waya a hannuna tace dafata taji anyi da sauri ta juyo cikin tsoro. Wannan direban ne ashe tunda suka zo da wacan mai motan yalura da ita a wajen shiyasa yace sushiga cikin mota shine yanzu ma yazago yazo"me kikeyi anan? Ya jeho mata da tambaya,fuskarsa ba rahma yake kare mata kallo ta tsorata da irin yanda yake binta da kallon dukda ta tsorata da irin kallo daya binta dashi amma bata bari tsoron yayi tasiri a ranta ba ta aro jarumta tace"gudowa nayi ta bashi amsa tana barin wajen. Tsaidata yayi ta cewa"in ma leƙen asiri aka aikoki kiyi rayuwarki zaki saka cikin hatsari dan haka shawara tarage naki kiyi shiru ko ki fallasa abunda kika gani. "Barazana kakemun da rayuwata kenan? "Yaro man kaza bazaki san rayuwarki tana da mahimmanci ba sai randa kikayi gigin shiga hurumin da be shafeki ba. Kafin nayi magana natsin kayi muryan khalid yana cewa"wai ina kika shiga tundazu sai nemanki nake suhail ya addabeni da kiran waya in bashi ke. Saida yakaraso wajen namu sosai tukunna ya kula da bani kaɗai bace,da mamaki yake kallon mu yace"malam balarabe lafiya de ko? Me kefaru anan naganku tsaye koda wani abunne. Sauri cewa nayi"guduwan aiki nayi shine fa dan ya ganni zaune anan yake tambayata ko wani abu nake nema. "Da eh eh ya amsa a ɗan rude,murmushi khalid yayi yana cewa"ai tana daya daga cikin telolin da mukeji da ita anan masana'antar ina ga gudun fadan oga yasata gudowa nan taɓuye kasan ogan nan naku idan yafara faɗan nan nasa musamman ga wanda yayi fashin zuwa aiki. Ajiyar zuciya nasauke a ɓoye ina markin fuskan mutumin kuma araina ina da yaƙinin tanan zan samo bakin zaren. Tare da khalid muka juya dan barin wajen saida nayi gaba harna juya ina kare masa kallo ganin sa kaman ya tsorata dani hannu nasaka a wuya masa alama da zan yankaka murmushin dan bansan ma'anarsa ba ya suɓuce masa yana kaɗa kansa. "Basma yanzu kina ganin zuwa musami wannan mutumin shine mafita kinfa sanni da rashin hakuri bazan juri wulakaci daga miskilin mutumin nan naki ba. "Allah kuwa daya daga cikin ƙawayen nata ta amshe kinsan Allah salaha ni har mamaki basma kebani akan wannan dan rainin hankalin saurayin nan nata. Duk yanda take gwara kan maza amma namiji ɗaya yake wanata kaman sitarin mota. "Kanku akeji wai an tsikari kakkausa ni ahaka naga abuna kuma nakeson sa,kinga irin miskilan mutanen nan miskilanci baze barshi yadaga kai ya kalli wata macen bama balle ta burgesa dagani yarufe ƙofa. Dariya suka kwashe dashi hardasu shewa nan suka shirya ita dasu dan suje office ɗinsa suyi magana akan tsare tsaren da tayima bikin da kuma irin party da dakuma mawaƙa da zasu gaiyato dan katawa abun armashi. Wanka ta dauka iya wanka tayi shigar wata material ɗinki ya bala'in tsuketa kaman idan tayi ƙwaƙkwaran motsi ze yage. Motar ta suka shiga ita ke driven abinta salaha na zaune kusa da ita raihana na bayan mota suna hira sunƙure sauti cikin wakar justine biba duk inda motar ta gilma sai anbita da kallo yanda take gudu dakuma yanda sautin kiɗi ketashi. A harabar ma'aikatar sukai parkin motar suka fito suna takun katsaita cikin son nuna isa dakuma izzar tata data saba,saida suka kai bakin office ɗin sa harta kama handle ɗin ƙofan zata buɗe raihana tayi saurin dakatar da ita akan suyi nockin tukunna. Badan tasoba dan ita neman izini kafin kashiga guri badamuwar ta bace,saida tayi nockin sau uku sannan akayi magana daga ciki hakan yasa cikin zumuɗi ta tura ƙofar tashiga saide tun daga kallon da Ahmad ɗin ya jefeta dashi taji gwiwarta naneman tsagewa,zama sukai inda yamusu nuni da hannu salaha da raihana suka gaisheshi a gajarce ya amsa musu ita ko gimbiyar jira take shi ya gaisheta dan haka be sake bi takan su ba aikin sa yake cikin systerm ɗinsa saida sauka dauki kimanin minti hudu a haka sannan ya ɗago yadube su"me zakawo muku? Saurin amsa masa tayi da nothing"ok and? Saikuma yayi shiru cike da yanga dakuma yauƙi ta ɗago ta zuba masa ido irin na riƙaƙƙun ƴan duniyar nan tace"gami da party da muka tsare na shagalin bikin mu"hmmm yace kawai ba tare da ya kalle taba. Nan tashiga zayyano masa kusan party aƙalla sunkai kala goma kuma wai duka so ake ya hallarta,saida yagama sauraron ta sannan ya sauke ajiyar zuciya yabude baki dakyar yake motsa lips dinta cike da jan aji yace"all this for what? A mamakince suke kallon sa dukkan su kana ya daura da cewa duk abinda zakiyi kije kiyi amma karkiyi tsammanin zuwana dan bani da time a mean ina nufin wannan lokacin bana kasar zamuyi tafiya sai ana jibi biki zan dawo so idan tanine walima kaɗai ya wadatar mukirayo malamai suyi wa'azi da faɗakarwa sabida neman albarkar auren koya kika gani tawajena yakare magana cike da zolaya. Miƙewa tayi tace"wallahi my kai baka isa karusa mana shiri da tuntuni mukeyi akan wannan auren ba,kuma ba wani walima da za'ayi kuma wallahi dole ka halarci dukkan event ɗin da zamuyi kai da ƴan gidan ku,tsaye take sai zazzaga masifa take sabida rufewar ido tama mance da wanda take duk yanda ƙawayen nata sukai ta jan hannun ta kan tayi shiru ta zauna taƙi saida ta sauke duka abunda yake kanta sannan ta zauna tana fashe masa da wani sabon kuka. Shigowar Aisha daya aika khalid yamasa kiranta ne yasashi bude idanunsa da suke kulle tun sanda basma ta soma masa masifarta yasauke su akanta"ɗauko mun ruwa mai sanyi ya umurceta tunkafi ta ida shigowa ruwan ta ɗauko tana miƙa masa nuna mata inda zata ajiye ruwan yayi gaban basma dake kuka. "Ɗauki ruwan kisha sai muyi magana yamata magana kaman bashine yayi ba ya maida kallon sa kan Aisha data gama shan jinin jikinta tsoronta karyace ze sake yimata iskancin da yamata ɗazu amma wani ɓari na zuciyarta ta ɗan yimata sanyi tunda taga da mutane cikin office ɗin ai duk iskancin sa baze yimata gaban su ba. "Meya hanaki zuwa aiki harna tsawon mako guda batare da kinsanar ba. Wani irin ashariya basma dake kuka ta lailayo ta yaɓa ma wacce yake ma tambaya tunkafin ma taga ko wacece,tayi cilli da goran ruwa tana miƙewa sauke idonta tayi saman fuska Aisha wani irin bugawa zuciyarta tayi"uban me kikeyi anan mai wanki. Murmushi dauke saman fuskarta duk da taji ciwon zagin uban da tayi mata amma ta dake tana"anty basma ashede kece wani kallon mai cike da tsana da kaskanci take binta dashi"faɗamun abunda kikeyi anan zakiyi bawai iskancinku na ƴaƴan talakawa nace kimun ba. Ƴar dariya Aisha tayi tace"aiki nake kinsan nafi kwarewa wajen iya wanki to nan din ma aikin shara dakuma bama oga abinci nake kinsan saboda kuɗi ba abunda mutum ba zeyi ba,na gaji da wankin ɗan kanfen mace ƴar uwata shisa naga gwara nayi nabuje ko ba komai wataran zan samu.....ji kake tasss . ALLAH YASA MUDACE [5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published "38" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1339200412?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=OZqMHKm4wEPJCOQ1%2BOj8aOK5tQC2vhgUb%2BlXSKemzCXzcQcM32BRwkUlEkuQnZ9SbsseGV%2FNSZgN%2BBGe080k%2FTZfR%2FVcdU%2FqD00FJE8z8gQ5RSOSza07h7D9amDgqa08 _________________ *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 38 Saurin riƙo hannun ta yayi be bari tafita da gudu kaman yanda ta bukata ba. Ta faɗo jikin sa yayi saurin ya rungumeta kaman dama jiran haka yake kiciniyar ƙwantar kanta tasoma cike da taƙaicin taɓa mata jiki da yake da zallah masifa tace"dallah malam cikani. Ta faɗi haka ciki da tsoro a muryarta"idan naƙi sakin naki fa mezaki iyayi? Yayi maganar cikin ƙaramin murya kaman na mai raɗa a cikin kunnen ta,ƙirjinta ne yasoma wani irin bugawa da karfi jin sauti yake cikin jiki da ɓargon sa wanda haka shima ya haimar ma nashi zuciyan sauya bugun ta. Wani karfine yazo mata bazata ta ture shi tama mai share fuskarta da hannuta na dama tabude baki da ƙyar tace dashi"Allah ya isa taɓamun jiki da kayi kwarto kawai,tana kare faɗin haka ta kwasa da gudu tayi waje. Komawa yayi yazube saman wani kushun da aka tanada saboda hutawa yana mai jin haushin kansa. Basma Kasa tuƙi tayi sai raihana data miƙawa key din motan kuka take riris kaman karamar yarinya tasan iyayenta nada wani shiri akan aurenta da ahmad kuma sunkashe maƙudan ƙuɗade dan ganin burin su yacika,amma da alama ze kawo musu cikas dan yanda yake tsaye tsayin daka da alama duk aiki da akai masa be kamashi ba. Idan ko hakane akwai aiki ja a gabanta ko tace a gabansu da iyayen nata dan ita Allah yana gani tanason Ahmad bilhakki da gaskiya zata iya koma menene dan ta samu ta mallaki zuciyar sa. Amma ta ya? Sannan wace alaƙace tsakanin sa da wannan ƙaskan tacciyar ƴar aikin? "Ina da bukatar sanin wace alaƙace tsakanin ta da Ahmad? "Bakida matsala cewar Salaha gobema zan saka a bincika mana amma kinsa aikin ɗan kunama sai yaji dumus a hannun sa. Harara ta maka mata tana mai cewa"matsalata daku kenan bakusan zaman tare ba komai sai kuɗi mtssss takare maganan tana tsuka. ***** Ya alhaj gafa sabuwar yarinya da nake faɗa maka nan zatayi aiki damu dan tana da ƙwazo sosai takuma iya takunta,dan dama tajima tana aikin saida syrup da tabar wiwi tana kuma da ɗaure gindin wasu daga cikin jami'ai musamman ta NDLE. Duka wannan magana da mutumin yake idon ya Alhaj nakanta saide duk ƙwafƙwafin sa nason ganin ainihin fuskarta abun ya faskara saide shigar da tayi na baƙaƙen kaya sun matukar burge shi. "Kina da sa'a ƴan mata a rayuwarki da kika haɗu dani kai tsaye. Hmmm tace tana sakar masa da murmushi mai sauti ta amsa masa da cewa"dama can niɗin da sa'ata nake tafe saide zan iya cewa kaine kayi sa'an samuna matsayin wacce zatayi aiki daku. Takuwa burgeshi dan kanta tsaye take maganarta ba tare da nuna tsoro ko shakkan sa dan ganin yanda yake zagaye da guggan ƴan daba ba. "Wannan gwarin gwiwa taki da yanda kike maganarki kanki tsaye ya burgeni"hmmm haka nake dama ta bashi amsa tana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannun ta lokacin tafiya ta yayi ko zan iya tafiya. "Baki da matsala ya amsa yana ƴar dariya da cewa yaushe zamu haɗu naga kaman kina sauri dan inada sharaɗuna kafin ki soma aiki damu. "Zanso hakan dan nima inada nawa sharuɗun kafin na karɓi aiki dan nasaba cin gashin kaina ban saba zama karkashin ƙwarin bariki ba shi sa. Dala dubu goma yamika mata yace"kyayi kuɗin mota kafin musake haduwa dake kafin sannan inason sanin sunanki da kuma address dinki? Dan shiru tayi sai kuma ta sakar masa da murmushi mai sauti kana tace"sunana NATASHA address kuma duk sanda ka bukaci ganina zan bayyana a wajen dan bana da address taƙa maimai ɗaya tana kare faɗin haka ta amshi kuɗin daga hannun sa ta daga masa ƴan yatsun hannun ta uku alamun bye. Da ido ya Alhaj yayima wani dake kusa dashi alama da yabi bayanta. Saide kash ta katse masa hanzari wajen cewa dashi"Alhaji ba sai ka wahal da kanka wajen sawa a bibiyeni ba idan kana da shakku a kaina kabar aikin kawai dama ni ba wani damuwa nayi da sainayi aiki karkashin wani ba. "noo noo noo hajjaju Natasha bazamuyi haka dake ba yafaɗa cikin rawar jiki da ido yama yaran nasa alama da suja da baya. A ransa kuwa mamakinta ne fal ransa ya akai ta gane yasa a bibiyeta idan kin sa wata baki san wata ba ya faɗi haka a ransa yana sakin murmushin mugunta. Ɓangaren Natasha bayan barinta wajen cikin sauri ta faɗa motar da yazo ɗaukanta saida ta daidaita zamanta motan tabar harabar wajen ta cilla hancinta kwalta sannan ta sauke ƙatuwar ajiyar zuciya tana cire face mark ɗin fuskarta ta gurgar gefe tace"wai dakyar nasha gaskiya ya faisal bazan iya tunkarar waƴan mutanen kaitse haka ba. Dariya faisal yayi harda buga sitarin motar yace"haba hajiya natasha kenan bazaki iya tsayuwa tsayin daka kijajirce dan ganin kin cika burin uncle ishak ba? Idontane ya ciko da kwallah tunawa da wannan shine azzalumin da yasaka rayuwarsu shiga garari ya maishe su marayu karfi da yaji. Yaya faisal nashirya koda zan rasa rayuwanane zanyi komai dan ganin wannan azzulumin da kuma ire iren su sun kau a doron duniya.   Fatan anyi sallah lafiya Allah ya amshi ibadun mu yasamu muna daga cikin salihan bayin sa Allah maimaita mana na baɗi Allah yasa muna daga cikin salihan bayin sa Amin     ALLAH YASA MUDACE [5/2, 12:51 PM] Xeenat: I just published "39" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1339755305?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=F91THsvJXukxVrDQ76eRIUDsw1qK8sldrUaP5NNqWBKfsFM60ftv1yxgntlWsb8%2BzdAI125vjxkLdZDUTWGdo1pnNbwo8bqO9u82Tx73SnmryyVHy01tExTcVZWx5VAF ________________ *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 39 Kuka take sosai dayayi sanadin samun gefen titi ya parka motar,ya juyo ya fuskanceta da kyau ya sauke gauron numfashi yakira sunan ta da Aisha. Bata amsa masa ba sai kallon sa datayi da idanun ta masu tsiyar da hawaye"kiyi shiru ki share hawayenki idan har wannan aikin da nakeso muhaɗa karfe da karfe dan ganin mun taimakawa al'umma waƴanda ake zalumta da ƙananun yara basuji ba basu gani ba ne be miki ba sorry ki dena kukan haka is ok zanyi komai da kaina dan ganin na gurfanar da waƴan nan azzuluman gaban ƙuliya. Aisha sun maida ƙananun yara da dama marayu sun maida mata dubun dubata zawarawa haka zalika sun kashe marasa lefi sunyi garkuwa da wasu sunwa wasu kisan gilla. Aisha ko kinsan mahaifinki yana raye be mutu ba tsayon wannan shekarun. "What Shine abunda yafita daga bakin ta hawayen idonta yatsaya cak ta waro idanunta kaman zasu faɗo kasa. Alhaji shehu Cikumo fadila yayi da iya karfinsa ya shaƙe mata wuya yace"oya faɗamun me kikawa Aisha da zakice mun ta ɓace tsawon wannan lokacin basan idan suka shiga ba. Fadila ido ya raina fata taji shaƙa iya shaƙa sai kakari take sannan ya saketa ta faɗi kasa jikake tadafe wuyanta sai tari take. Faɗamun abunda kikayi mata yafaɗa cikin daka mata wani gigitacce tsawa dayasa hanjin cikinta hautsunawa ba shiri ta shiga cewa"ni ni ban mata komai ba asalima tunda suka zo mun gaisuwar mutuwar innata bansake jin ɗuriyarsu ba,kumama ai ni bance zan mata wani abun ba. "Karya kike baƙar munafuka ya katseta da faɗi haka cikin nuna jarumta ta yunƙura ta miƙe tsaye daga duƙen da kake tace"naji ni munafuka ce kai kuma fa? Karfa ka manta kaine nan wanda ya canzan ra'ayina kan ƙawar da bani da kamarta. Saida ka gama da ni da rayuwata yanzu kazo kace Aisha kake nema zaka aura kaima kasan muddin ina numfashi a doro duniyar nan to wallahi wallahi ko Auren wucin gadi baka isa ka auri Aisha ba. jikake ta tass sauka mari daya hanata karashe maganan bakin ta,isowar yayanta Sani wajen yasa Alhaji shehu barin wajen ba tare da ya bashi amsan tambayansu da yake ba. **** Kace mahaifina yana raye? "Kwarai ya amsa mata "Taya zan yarda da maganarka? Shin idan da gaske mahaifina yana raye ina yake yanzu? Kaga dan Allah yaya faisal idan kanason amfani dani dan cimma wani manufarka ta aiki karkamun karyar mahaifina yana raye ka yaudaren ta wannan. Tana kaiwa nan ta rufe fuskarta da tafukan hannun ta ta shiga raira kuka ina mai tsuma zuciyar mai sauraro ba komai take yiwa kuka ba sai famin miƙi da yanzu akai mata na rashin mahaifinta sai kuma tunawa da tayi da Anna uwa ɗaya tamkar a dubu yanzu ko ina take? Shin tana cikin ƙoshin lafiya ko ya? Kode itama waƴan nan azzaluman sunyi nasaran kamata sunyi garkuwan da itane. "La la la la la ina hakan sam ba maiyuwa bane ta furta da karfi sai kuma tashiga marin kanta da kanta tana kuka takoma masa tamkar wata mahaukaciya sabon kamu duk tagama birkice masa,tayi daya sanin sanar da ita yayi duk da dama abokin aikin sa samuel tun farko ya gargaɗe sa da karya kuskura ya sanar da ita harsai sun samu gamshesshiyar bayani akan yana rayen ko sun ganshi sannan ne. Amma gashi yanzu yazo ya ɓata goma be gyara ko daya ba. "Aisha ki nutsu karki bari hankalin ki ya gushe akan abunda ni nasan gaskiya nake faɗa miki kuma na miki alkawalin haɗaki da mahaifinki muddin na binciko nasamo inda yake koda ba zakiyi aikin nan da mu ba. "Kaga yah faisal karabu dani da banzan ƙudurin ku na aiki,ni nasan da ace mahaifina yana raye da bazamu ɗauki tsawon shekarun nan bamuji ɗuriyar sa ba. Anna tasha faɗamun duk ranan da Abba ze bayyana kansa to tabbas zeyi wani abu da ze girgiza waƴan nan azzaluman koda ta hanyan fallasa wani sashi na sirrin su ne. Anna tasha faɗamun haka wannan dalilin yasa koda yaushe nake cikin kasa kunne na saurari labarai duk da bani da waya amma koda yaushe ina tambayan mutane wani sabon topic ne wannan yake bada wuta a media amma shiru kakeji. Sai yanzu kawai dan ka karanta wani shashi na ƙundin sirrimu kace xakayi amfani da wannan daman wajen son juyamun da hankali Yanda ta birkice masa dole tasa ya kyaleta dan yasan tana bukatar hutu ba ita dake da ƙarancin shekaru ba komai yawan shekarune ba lalle ne ya yarda da shi lokaci guda ba. Alhaji sunusi Suna zaman meetin da wasu manyan abokan harkallan sa,daya daga cikin mai suna Alhaji hamza ya kalle su yace"gaskiya Alhaji ba yanda za'ayi musaka maƙudan kuɗaɗen mu munaji muna gani muxo muyi asarar su ba. "Haba Alhaji hamza wani irin asara kuma? Bayan ba tun yau muke wannan sana'a da kuba,ko ba haka ba Alhaji ɗahiru? Numfasawa Alhaji ɗahiru yayi yace"gaskiya Alhaji sunusi maganan Alh hamza yana kan hanya karfa muzuba kuɗaɗen mu daga baya muzo mutashi a tutan babu wato ba tsuntsu ba tarko. Kayi sake Alhaji ishaq ya kubce daga hannun ka ka kuma san wannan babban barazanace garemu baki ɗaya,kaxo kace kaga matar sa harda ɗiyarta itama kayi sake sun gudu ba gansu ba. Kafasan ance jada baya ga abokin faɗa ba tsoro bane wata ƙila shiryawa zasuyi kuma kasan duk sirrin ka yana tafin hannun Alh ishaq kai ba kai bama hatta mu damuke tare dakai dakyarne zamu tsira idan ƙwan tafashe. Sharce guminsa yayi yace"ina da plan sosai akan wannan ba abunda ze samu kuɗin ku sannan wannan aure da nakeso na haɗa tsakanin ɗiyata da ɗan Alh badamasi shima yana daga ciki dan cibiyar alhakk zata dawo karkashin kulawarmu sai yanda mukai da shi karshe shikuma mu turashi inda bazuwa idan yace ze kawo mana matsala hhhhhhh dukansu suka kwashe da wani irin dariya wasu bosawa.   ALLAH YASA MUDACE [5/10, 7:42 AM] Xeenat: I just published "40" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1342048441?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=PmISWgeA6kHrWG0z7W%2F7jrIqwm5oCMdpXqyxlwHo08SWeXv8I6D2Z5DeZcpw4rfI5L1CWsGXQVE5lC3sowTgKMWZ%2FwmqEwzbER7CWdZhwLydnObbyoG5AYwcTSV7XuNe ____________ *AURE WUCIN GADI* CHAPTER 40 Saida ya sassauta da dariyar dayake sannan ya dubesu ɗaya bayan ɗaya yace"kafin sannan na san kai Alh hamza kasani cewa koda giwa ta faɗi tafi karfin.....be barshi yakai karshen maganan ba yace"haba haba ya alhaj karkaji komai ba wata matsala kawai de mundan shiga ruɗune kasan sha'anin kuɗi ba abun wasa bane ba. Alhaji ɗahiru ya amshe da cewa"kuma kaima kanka Alhaji sunusi kasan harka ta kuɗi kaman yanda bakason wasa dasu haka muma dan idan mutum yace ze shiga tsakanin mu da samun mu to wallahi yanzu ne zamuyi uwar watsi da shi. "Aisha yakira sunan ta. Ɗaga masa hannu tayi murya na rawa tace"kaini gida kawai ba lalle ne karamin kwakwalwata ta iya ɗaukan abunda kake cewa ba. A karancin shekarun nan nawa ba lalle na fahinci mai kake cewa ba,da kace mahaifina yana yaraye gwara kace dani anga mahaifiyata wannan shine abunda zan iya yarda da shi. "Amma Aisha kinsan bazan miki karya ba ko? Yafaɗa yana tsareta da ido. Saida ta share hawayen da ke kwaranƴa a idanunta sannan tace"aiko yanzu yaya faisal bance karya kayi nun ba,amma menene dalilin ka nacewa mahaifina na raye? Tsawon wannan lokaci shekara goma fa ba kwana goma bace ba? Abu ɗaya nasani shekara tara baya an tsinci motar sa ta ƙone hakan yana nufin be tsira da rayuwar sa,idan ko yana raye yaci ace tsawon wannan lokacin wani ya gansa koda hatsari yayi ya kamu da cutan mantau wata ƙila wani yagansa ko ayi cigiyar ƴan uwansa amma ina anyi haka? Idan kuma bayani kake so na baka gami da abunda yashafi aikin ka ba wai sai kabi dani ta nan ba zan faɗa maka iya abunda nasani,zanyi hakan ne dan cikan burina dakuma ta iyayena amma zancen wata NATASHA kabarta nan daga haka taja bakin ta ta tsuƙe duk yanda Faisal yaso ta bashi haɗin kai suyi magana taƙi dole bawai dan yaso ba ya ƙyaleta dan bata daman tayi tunani. Ahmad zaune yake a main falon gidan su yana tura wasu samfuran kaya wa customer ɗin sa,Ammin sa dake zaune gefe tana kallon tashar sunnan tv ta ɗan maida kallon ta kansa tace"kasan yaune kai lefen ka ko? "Nasani ya amsa mata cikin halin ko in kula. Kallon sa tayi da mamaki ganin bema nuna damuwar sa ko wani zumuɗin sa kan wanna. auren ba,cigaba tayi da maganan nata tasake cewa"wani tanadi kaiwa bikin naku dan naga Alhaji yaɗauki abun da mahimmanci sosai. Sannan kuma dama ina tason muyi magana da kai gami da yarinyar da nace zan zaɓa maka to Alhamdulillahi an rigada an ɗaura auren ka da ita tuntuni da wani irin sauri ya ɗago da kansa yana kallon Ammin nasa dake magana saide duk kwafkwafinka baka isa kace ga yanayin da yashiga ba. Tuni yaji ƴawun bakin sa ya ɗauke magana yake son yi amma yakasa furta koda kalla gudane. Sai cigaba da magana da Ammi tayi bata damu da sai yace komai ba,Ahmad na tabbata zakayi alfahari da wannan auren,nan gaba dan yarinyace mai hankali da sanin yakamata na yaba da tarbiyarta da kuma hankalinta shi yakaini ga sha'awan aura maka ita. Idan kasamu lokaci zaka iya zuwa gidan Antinku hajia tana can da zama tun bayan daura aurenka da ita zamanta ya koma can. Kafin ta sake wani magana Alhaji badamasi ya banko ƙofar falon ko sallamar kirki babu yashigo cikin falon yana aunawa Ahmad din harara shiko Ahmad ƙasa da kansa yayi dan yasan kwanan zancen"lafiya Alhaji? Ammi tayi tambayarsa dan ganin yanda yake huci,da mugun kallo yabita dashi yana cewa"eh dole ki tambayeni ko lafiya tunda kin iya saka shi gaba ki zugashi. "Wai meka faruwane? Alhaji daga tambaya sai cibi yazama ƙari Allah yabaka hakuri. "Dole kice haka wato ma'arufa kiji tsoron Allah dama ke kike zugashi dan kawai inason ƙulla zumunci tsakanina da abokina amma wannan yaron saboda bashi da mutunci shine ze ce baze halarci duk shagalin biki da za'ayi ba? "Au dama wannan duk wannan kakewa fushin to shi shagalin bikin farillace da sai Ahmad ɗin ya halarta ni naga jaraba kowa nason ganin farin cikin nasa amma banda kai Alhaji. "To to to yanzu nagane kice kekika hanashi kuke son maisheni karamin mutum kai da uwarka eh? Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba saida yayi mai isarsa sannan yayi shiru. Ganin ba wanda ya tanƙa shi sai kuma abun ya hasala shi yashiga cewa wato ga mahaukaci nan ina magana kuna jina kunyi shi to wallahi Ahmad bara kaji narantse maka da rawanin kakana na kande muddin baka tsaya anyi komai dakai ba to kanemi gidan wani uban bade nan ba. Zuba mishi ido Ahmad yayi sannan yace"wai kai Abba mai yasa ko wani uba yana son ganin farin cikin ƴaƴansa amma banda kai,shi wanda kakeyi dan shi be goyi bayana ko ya tambayi dalilina na cewa bazanin ba,bayan ɗiyar sa yagoya amma kai yanzu duba daga zuwa ka hau Ammina da zagi batasan hawa ba batasan sauka ba bama tasan anyi hakan ba. Kaga Abba ina da tafiya mai mahimmaci a gabana kuma zanyi kwana shida kafin nadawo dan haka ni ban hana kowa yin party ba,suyi shagalin su yanda suke so saide Abba kasani kaman yanda tace dole ƴan gidan mu su halarci wajen wannan ne bata isa ba. Kuma Abba zancen tarewa ta can gidan babu dan ni ba lusari bane sannan kafadawa abokinka baka haifi lusari da ze tare gidan surukan sa. Kafin na dawo daga tafiya Ammi kisaka a gyara wannan site ɗin idan sunada buƙata suzo suyi jeren su idan kuma basu da buƙata ok fine ya ɗage kafaɗansa cikin halin ko inkula yayi gaba. "Kina gani ko nace kina gani ko yaron nan yana neman zagina wato ban haifi lusari ba nine kenan lusarin uba ko? Danma anason yimaka gata kai kakai Alhaji sunusi ya tsaya neman alfarma a wajenka ne idan ba dan kaci darajan so ba. Murmusawa Ammi tayi ganin yanda Alhajin nata yake ta bambami tace"a to kyan ƴa mace ɗakin mijinta Allah ya huremana banga abunda su zasu nuna mana na lalle lalle sai yaro ya tare a gidan su ba,saide inda wata a ƙasa,ai wallahi idan ka matsa sai Ahmad ya tare gidan surukan sa wallahi sai malam mai babban riga yajimu da kai wato ƙanin baban shi Alhaji badamasin kenan. ****** Aisha suna komawa gida ko tsayawa daidai parkin bata bari yah faisal yayi ba ta ɓalle marfin motan tafita tashiga ciki da gudu tana tare kukan da yake son kufce mata. Bata taradda kowa a falon ba da alama anti hajia fita tayi malika bata dawo daga skul ba hakama malik dasu ummu salma. Ɗaki su tashiga tana shiga ta faɗa saman gado tayi rub da ciki dasaki kuka,saida tayi mai isarta sannan taji dama dama nauyi da takeji a ƙirjinta ya ragu baccine ya dauke ta daga kwancen da take ba ita ta farka ba sai karfe biyu da rabi a gurguje tatashi ta shiga toile wanka tayi tare da dauro alwala tafito daure da towel bata tsaya shafa jikinta da mai ba,ganin yanayi zafin garin sallah tayi taba tashi a wajen ba tanan zaune a wajen tana tilawa bata tashi ba saida tayi sallan la'asar sannan ta miƙe ta naɗe sallayar ta adanata tare da ninke hijabin hula tasaka a kanta tafito falo. Harde sannan ba wanda yazo dan haka kitchen tanufa ta daura musu girkin dare sannan itama tasha freesh milk towun semo da miyar ɗanyen kuɓewa da yasha nama ta taura musu take gidan ya kaure da daddaɗan kamshin girkinta sai daf da kiran sallan magariba ta gama ta haɗa musu juice ɗin abarba da kwakwa tasaka a frige sannan ta fito dan gabatar da sallah magariba da aka fara kira. Shiganta falo da coolar abinci a hannun ta yayi daidai da zuwan su ahalin gidan baki ɗaya harda su khadija. Sannu da zuwa tama anty hajjia da malika suma yaran suka mata barka da gida"a'a mai aka girka mana ne haka duk gida ya game da kamshi haka cewar Anty hajjiya da fara'a ɗauke a fuskarta. "Tuwone Anty ta amsa tana ajiye cooler"waw kice yau mubude ciki mu kwashi girki kaman ko kinsa bamuci wani abun kirki ba tun fitan mu. "Wash wallahi na gaji tafaɗa tana cilli da jakar hannuta"kai anty malika bade lalaci ba ince ko noma kikayi"hmmm Aisha baxaki gane bane aiko wanda yayi noma yau baze nunamun gajiya ba. Nida nasan irin wannan gida zamu wallahi da a gidan Ammi nayi zamana shegu sai son nunawa mutane su wasune amma tarɓa baƙi common wannan basu iya ba,sunzo sun wani taremu da juice da snack sai kace ce musu mukai muɗin ƙwaɗayayyune mtssss taja tsuka. Bayan gaba dayan su sunyi sallah sun zo sun halarta a taburin cin abinci Aisha tayi saving kowa cin abinci suke ba mai magana saida suka kammala khadija da Aisha suka kwashe komai suka maida kitchen sun dawo falo sun zauna kenan aka hasko hoton gawar wata yarinya ƴar makaranta wacce ta ɓace sati biyu baya. mahukunta sunce ana amfani da yaran ne wajen basu hodar iblis ana safara dasu gari gari itama wannan bincike yanuna cewa ansamu akasi ya fashe acikin cikin ta shine yayi sanadin rayuwarta sannan saboda rashin tsoron Allah aka farke cikin bayan ta mutu aka cire sauran hodan. Da kuka Aisha ta ɓarke tana cewa"wallahi nasanta ajinmu ɗaya a islamiya samira ce Allah yasaka miki Allah yatoni asirin waƴan nan azzaluman. "Aisha asirin su ze tonune harsai ansami mai tamƙa musu wanda ze zaƙulo ko ya banƙaɗo da sirrikan su,wata zuciya ta amsamata da haka. Tana cikin kuka da zance zuci ta tsinkayo muryar Anty hajjiya na cewa"ai waƴan nan mutane saide muce Allah ya ruguza su amma cutakan suna cutan bayin Allah duka saboda duniyar su. Sun lalata rayuwar ƴaƴan mutane da dama sun maida ƴan mata bila adadin karuwai ƴan ƙwaya karfi da yaji duka dan samun duniyar su. "Anty hajjia mai amfanin hukuma da muke dasu muna da police soja civil difence ndlea harma da ƴan banga amma ace anrasa wanda ze kamasu da hujja dan gurfanasu gaban ƙuliya. Dafa kafaɗan ta tayi tace"Aisha waƴan nan mutane sun wuce tunanin ki suna aikine da tsafi sannan duk wanda yayi yunƙuri magana kan abunda suke tuni zasu aikashi barzawu ko su ɗauke maka ɗan wannan yasa ba wanda ya isa tanƙamusu suke tsula tsiyarsu son ransu. Shekarun baya ansamu wanda ya fito yayi magana da kuma rubuce rubuce a kansu amma daga baya shima yaɓace ɓat.   Alkalami ️ yafi takobi⚔️ ALLAH YASA MUDACE [5/11, 8:09 PM] Xeenat: I just published "41" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1342459751?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=h81c4fj1iTp8JKwxGh5dDAfwZwvq7T5Sq%2FBWRihWyTIDb7G4UdjbUktXIH6T8ZU6WkgrJxHWSHKrmaNFqXKNOWjTw0nx%2FrRHvjXj4CklGYSmyP9rqmBaPclyAuGQup0k ______________ *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 41 Ɓacewa kuma Anty hajia?"eh Aisha tunda yayi wani yunƙuri akan safaran yara mata da akeyi hukuma tashiga cikin abun kaman fa da gaske daga baya shiru kikeji shikenan aka rufe babinn sa. "Amma Anty hajjia su jami'a da muke dasu a ƙasar me amfanin su? "Kina kallon movies?ta tabayita madadin ta amsa mata da tambaya da tayi"eh ina kallon ya amsa fuskarta dauke da mamakin ƙin amsa mata tambayarta da batayi ba. Wata zuciyar tace yo ya zata baki amsa bayan mijinta da ɗanta duka suna cikin hukuman kuma ana damawa dasu. Katse mata tunanin tayi da fadi"kaman de yanda kike gani a movies haka abun yake,hmmm ta sauke ajiyar zuciya tare da miƙewa tsaye tana cewa"zanje na kwanta sai da safen ku. "Da wuri haka karfa kisa abun a ranki ya hanaki sukuni abubuwa dasuke faruwa a wannan ƙasa tamu sai du'ai"in sha Allah shine kaɗai amsa data iya bata tayi wuce warta ɗaki. Ahmad tunda ya baro sashin Ammin sa ya dawo part ɗinsa yasamo zarya cikin falon yama rasa meke masa daɗi,wani irin tunani zaiyi shifa ba yaro bane da zamasa auren haɗi wai ace amasa aure har biyu ciki ba zaɓin sa ko ɗaya aciki. Harma gwara Basma tunda yasanta kuma tana sonsa shine de kawai sai a hankali,to ita wanda Ammin sa ta zaɓa masa fa? Idan yarinyar ta kasance nakasasshiya ko bata daga tsarin macen da yake so fa,kai ina yayi saurin ture wannan tunanin. ƴanya ze iya hakura ya amsheta a duk yanayi da ze ganta kuwa,kode zuwa ze yasamu ya lallaɓa Ammin sa a ware wannan auren tunda ba wanda yasan dashi. Amma fa kai gaulane yama za'ayi kaman ka yaro ɗan kwalisa da kuɗinka da ajikan kana da kyau sannan ka haɗa duk komai wanda ko wace ƴa mace zata soka amma ace ka kare a auren haɗi gaskiya beyi ba. Ire iren abubuwan zuciyar sa ke injiza shi dakyar ya iya shiga toile ya sakarwa kansa shawer ya jima tsaye a haka ruwan nabin jikin sa kafin ya kashe tap ɗin ya fito ɗaure da towel a ƙugun sa yana kuma tsane ruwan kansa da karami towel din ji yayi kaman yayi tuntuɓe da abu yasa shi janye towel yana binta da wani irin kallo wanda yasa jikinta yin sanyi cikin yauƙi da duniyanci ta miƙe tsaye tana cewa"haba my saura kwana nawane ashafa"sai kibari ashafa tukunna. Rungumar sa take sonyi yayi saurin dakatar da ita ta hanyan daga mata hannu cike da ɓacin rai yake magana"sau nawa zance miki banason wannan ɗabi'ar yahudancin na rungume rungumen nan. Please fita kikoma falo zan shirya kaina"haba my to mai aciki dan ka shirya a gabana ai yanzu munriga da mun zama ɗaya kazama ni nazama kai aiko nida nake ƴa mace ba wani abu bane dan nashirya kana kallo na. Tunda tasoma magana yakafe ta da lulu idon sa kaman na maijin bacci saida takai karshe da magana da take kuma ba alaman zata fitan haka ya nufi clothes set ɗinsa ya dauki kayan sa yakoma toilet yasaka sannan ya zo. Gaban tangamemen mirrown dayake jere da mayuka masu tsada da turaruka masu kala kala jere suke rurus kai kace kashiga kanti saida su,saida ya tsaya ya zaɓa sannan yafeshe jikinsa da turare kala uku duk ƙwakwafinka baka isa kace ga ainihin kamshin turare da yake ba. A falo yasameta"me zaki sha akawo miki? Shine tambayan da yamata sanda yake kaiwa zaune. "Nothing ta amsa masa a taƙaice kafaɗan sa yaɗaga cikin ko in kula. Ganin bazai tambayi dalilin zuwan nata ba yasata tasowa inda take zaune tazo da zauna kusa dashi ta ɗaura kanta saman kafaɗan sa tace"wai me yasa baka sona? Me zanyi na burgeka a rayuwa harkaji kana sona? Tabbas yasan basma na son sa kuma tana hakuri da duk wani halin ko in kula dayake nuna mata dan ko bakomai yasan sonda take masa tasa ta juran duk wasu rashin kulawa daga gareshi. "I know yanzu de faɗamun meke tafe dake nasan de haka kawai bazaki zo a wannan lokacin ba? Dan murmusawa tayi tace"ai tare muke dasu mommy na,sauri ɗaga kanta yayi saman kafadan sa yana cewa"shine kuma tuntuni baki faɗamun ba. "Ba gashi yanzu kaji ba,dama zuwa mukai suga tsarin part ɗinda zamu zauna jibi idan Allah yakaimu masu dec_za suzo su duba suga ya yanayin tsarin zai kasance. Kansa kawai ya gyaɗa mata yana mai cewa"kenan sun amince da tarewarki nan?meya canza ma daddynki ra'ayi lokaci guda haka? Yakare maganan yana mai kamewa da ƙin sakin fuskan sa. "Muje ka gaisa dasu mommy na,tafaɗa tare da miƙewa tsaye tana mai riƙo hannu sa. "No kibarshi next time zan haɗu da itane,ɓata fuska tayi. Riƙo hannunta yayi ya maidata xauna kusa dashi abunda be taɓa yi ba kenan cikin sanyin murya yace"kinga be dace sai ta tako taxo har gida sannan naje nace zan gaisheta ba,kuma kinga irin kayan da ke jikina. ****** Aisha kusan kwana tayi tana tunanin abun bacci duk gwanin iya satan sa ranan be ɗauketa ba. Kusan raba dare tayi tana tunane tunane karshe kawai taji kuka ya kubce mata da wani tunani ya faɗo mata na ko Abban ku shima irin wannan mutuwan yayi. Shassaƙan kukanta shi yatashi khadija dake bacci cikin sauri tamiƙe zauna tana subhanallahi Anty Aisha lafiya kike kuka warhaka kode haryanzu mutuwar samiran ne? Rungume khadija tayi sai kawai itama khadija tasaka kuka duk da batasan abunda yayar tata kema kukan ba. Dakyar sukayi shiru Aisha ta riƙo hannun khadija murya na rawa tace"khadija yanzu muma irin mutuwar da iyayenmu sukai kenan? Tureta khadija tayi tana mai girgiza mata kai tana cewa"a'a Anty aisha iyayenmu basu mutu ba. "ki nutsu khadija bani da kowa sai keda mubaraq kune kaɗai dangin dake gareni khadija ina ji ajikina kaman wani babban al'amari ze faru dani wanda ze nisan tani daku. "Dan Allah Anty aisha kibar faɗin haka ba abunda ze rabamu kuma Anty akwai abunda baki sani ba amma yazama dole ki sani Abban mu be mutu ba yana raye. Tureta tayi daga jikinta tana girgiza kanta hawaye na fareti saman kyakkyauwar fuskanta"karki soma khadija kode kema sun juya miki tunanin ki ne? Kinga idan zaman mu anan ze kawo mana matsala to yanzu basai gobe ba zamu bar musu gida tunda amfani suke da ƙarancin tunanin mu dakuma rashin gatan mu. Tana kaiwa nan da maganar ta tanufi wordrobe dinsu ta soma zazzago da kayayyakin su ƙasa kaman wata zautacciya haka takoma sai kuka take tana surutai duk yanda khadija tayi kokari dan ganin yayar tata ta nutsu abun yaci tura tun sunayi su biyu har hayaniyar su yatada mubaraq dake bacci shima yashiga taya ƴan uwan nasa kuka duk da besan abun da suke wa kukan ba,ganin Aisha na haɗa musu kayansu cikin wata ƙatuwar jakka tana kuka yashiga cewa"Anty aisha ina zamu je? Ko kema zaki tafi kibarmu kaman Anna. Jin abunda yaron yace batasan sanda tasake kayan dake hannun ta yafaɗi ƙasa ba,jawo shi tayi ta rungume shi tasaki wani kuka mai sauti. Ganin haka ita ma khadija tazo ta faɗa jikin su Aisha tahaɗa su duka ta rungume su kuka sukeyi sosai Anty karki tafi kibarmu shine kawai abun yaron yake iya cewa"ba inda zani na barku kaji yi shiru ka kwanta na fasa kankameta yayi sosai gani yake kaman idan yasake ta zata tafi ta barsune har barci yayi awun gaba dasu baki ɗayan su a haka. WASHE GARI Diran mikiya Ahmad yayi ma gidan Antyn nasa dan son gani wacce mai kasada ce ta yarda da auren sa. Lokacin da yazo gidan yaran suna shiga motan malik ze kaisu makaranta mamaki shimfiɗe saman fuskan yake binsu da kallo ina Anty hajiya ta samu waƴan nan yara musabaha sukai da malik har ƙasa khadija ta zauna tana gaidashi hakama mubaraq fuska sake ya amsa dan tarbiyar yaran yabirgeshi haka kawai yaji kaunan yaran yana tambayan malik"ina Anty tasami kyawawan yara haka? Dariya malik yayi yana cewa"kyauta daga Allah ku ba kunƙi kuyi aure kutara musu jikoki ba,dukan wasa yakai masa yana gocewa sallama sukai yashiga ciki su kuma suka shiga mota suka wuce. Sallama ɗauke a bakinsa yashiga falon,bakowa sai tv dake aiki shi kaɗai wulga idon sa yasoma yi can sai ya hango kaman gilmawar mutum dining room haka kawai yaji zuciyarsa na ingiza shi zuwa wajen. Cikin takunsa na jaruman maza isa zuwa wajen,be kaiga ganin fuskarta ba saide tsuran jikinta kawai daya gani yaji tsigar jikin sa na tashi daure take da towel iya gwiwa kanta ba ko hula sai gashinta dake ɗaure da rebon tsaye take taba ƙofan baya da alama yunwa takeji sosai ko kuma sauri take soyayyan dankalin turawa ta zuba kaɗan cikin plate tana tauna a hankula jutawa tayi da nufin ta tafi ɗaki kawai ta ga mutum tsaye ba zato tasaki wani irin gigitaccen ƙara tana sakin plate ɗin hannun ta yafaɗi kasa tare da saurin ƙanƙame towel ɗin datake daure da shi dan karya faɗin. Shikansa Ahmad wani irin abu yaji kaman electric shock ya jashi nunata yake da yatsa yanason magana amma ya kasa sai zuba mata ido kawai da yayi ba lalle ka gane yanayin da shiga ba.     Alkalami ️yafi Takobi⚔️ ALLAH YASA MUDACE [5/12, 6:57 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Chapter 36 Kafin tasauke hannun ta nima nakai mata maruka dama da hauni ba ita ba hatta Ahmad abun yaba shi mamaki dan betaɓa tsamanin zata iya rama wannan marin ba duba da yanayin tazaran shekaru dake tsakaninta dasu dakuma wayewa uwa uba ƴaƴan manya. Zafin marin be gama sakin salaha ba ta tsinkayo muryata nama basma magana cikin ladabi kaman ba itace tayi wannan abun ba yanzu"anty basma kifayi hakuri kinsan ni bana barin bashi komai ƙankantar sa,bare kuma ga taɓamun lafiyata tunda nake ko uwar da ta haifeni ma bata taɓa saka hannun ta ajikina ba bare kuma wata,ɗan dafe gishinta tayi kaman wacce tayi mantuwa sai kuma ta ɗan kalli salaha tace sorry fa kawar Anty. Wani irin malolon abune ya takare makoshin ta harma ta kasa cewa uffan. Juyowa tayi ga Ahmad dayake hakimce saman kugera duk wannan abu kaman baya gun,saboda ya maida hankalin sa kacokan saman systerm ɗin sa, Azahiri kenan amma a baɗini duk abun nan da ake yana ganin su"gani tace dashi ba tare da tako kalli inda yake ɗin ba,banza yamata kaman ma besan da wata halitta mai suna Aisha a wajen ba. "Ok basma kuna iya tafiya dan ina da aiyuma masu tarin yawa"kuttt yanzu My saboda wannan kucakar ƙasƙantacciya ƴar wanki shegiya wacce...."ya'isa taji an katseta a tsawace yanda tsawan yashigeta har saida taɗan zabura abunka da wanda yataso ba gwaɓa. "Ya'isa ya'isa tasake maimaita hakan cike da ɓacin rai dakuma baƙin cikin yanda wasu masu kuɗi basu ɗauki talaka bakin kamai ba,mai zan so ga wannan saurayi naki ƙwala ƙwalan idon ko kuma farin fatan,Allah ya sauwake mun keda kike ga abun burgewa a gun kyayi,amma bar wani haɗani da wannan abun ko kusa. baya daga cikin gerin miji da nakeso in kina abunki yatsaya tsaka ninku amma kibar sakani cikin tsabgarku,duk talauci da ƙaskancina Alhamdullahi bantaɓa zuwa gidan masu kuɗi danyin bara ba,gumina nakeci kuma ko wanki da kike goranta tamun bafa sata nake ba balle naji kunya sai na wanke miki ɗan kamfe harma da ƙunzugu sabida rashin sanin dajara a hakanma sai na tsaya tsayin kada kafin abani hakkina ko da saura bayan wannan? Wani irin zabura rahaina tayi cike da borin kunya kunyata kawartasu da wannan yarinyar tayi dakatar da ita nayi da cewa"haba raihana ke kuwa mai naki na zabura haka kode neman suna kike? Da kin tsaya matsayinki da baki ɓata lokacinki wajen daukar jakar mace ƴar uwarki ba wallahi kuke saka ana raina mu ƴaƴan talakawa saboda ƙwaɗayi da rashin sanin ciwon kai. Daga haka ta juya da nufin barmusu office ɗin harta kama handle din kofan zata buɗe taji ance"waya baki izinin fita? Sake handle ɗin tayi a hankali ta juya ta kalle shi shima ita ɗin yake kallo hartayi ƙasa da kanta jin idanunsa masu kaifi a kanta saide tunawa da tayi da abunda yamata ɗazu hakan yasata banka masa harara ta juya da sauri tafita waje tana rufe masu ƙofa da karfi daya ba sautin garammm. Rintse idonsa yayi shi kaɗai yasan abunda yakeji akanta,amma ƙwarin gwiwarta da rashin tsoron ta yana burgeshi besan sanda murmushi ya suɓuce masa ba. Ganin murmushi saman fuskansa abunda tunda take dashi take mararin ganin sa dashi amma bata taɓa gani ba sai yanzu,hakan yasake tunzurata ta fashe masa da wani sabon kuka tana cewa"wato abunda wannan ƴar sharan tamana ma be ko dameka ba,sai ma murmushi dakake binta dashi tunda nake dakai bantaɓa ganin ka dashi ba,kullum kazo guna fuska cunƙushe kaman wanda aka faɗawa sakon mutuwa. Wallahi daddy zankira in faɗa masa beyi yunƙurin hanata kiran ba dan yana ganin alama tanan tafi kauri kai ƙara abu kaɗan daddy be gama tunanin da yakeyi ba ta miƙomasa wayan tana ƙananun kuka. Karɓan wayan yayi a hannunta ya kara kunne sa,sallama yafara masa madadin amsa masa da sallama da yayi sai tsinkayo muryar Alh sunusi yana masa faɗa da tada jijiyoyin wuya beyi kunkurin katse shi ko bashi hakuri ba,saida yakai aya a maganar tasa sannan cikin ladabi Ahmad din yace"sorry Alhaji ban hanata party ba inma duniya zata gayyata sani yarage nata nine de bazan samu daman halarta ba saboda wani aiki mai mahimmanci danake dashi a wannan lokacin. Da mamaki basma take kallon sa dan batayi tsamman tsaurin idon ahmad ɗin yakai yima mahaifinta musu ba. Bata sake tsinkewa da lamarin nasa ba saida taji yana cewa gaskiya Alhaji wannan abun yafimun wannan shagalin dama auren baki ɗaya bana jin zan fasa wannan tafiya tawa,shiru yayi da alama yana sauraron abunda Alhaji sunusin ke cewa sai kuma taga yamiƙa mata waya yana cewa dasu salaha ku ɗan bamu waje zamuyi magana simi simi sukayi waje kaman wasu munafukai. Rufe kofar yayi sannan yatako zuwa inda take tsaye kallonta yake ido cikin ido har saida taji kallon da yake mata yafara gundurar ta ita tasoma jaye nata idon dan bazata iya cigaba da kallon cikin idon nasa ba. Basma yakira sunan cikin murya mai amo"ya zama yaune rana na farko kuma karshe dazaki kai karata wajen mahaifinki,dan na yarda da aurenki hakan bawai yana nufin zakuna juyani yanda ranku keso ba. Sannan zance tarewa a gidan ku dakuka tsara matukar kina sona kuma kin shirya zaman aure dani to kishirya tarewarki a gidana,idan gidane muma muna dashi idan kuma ɗakine inada shi bana bukatar komai daga iyayenki ke kaɗanki kin isheni komai. Wannan umurni nake baki kai tsaye bawai shawaranki kota tsuffinki nake nema ba. Tunda nake a tarihin duniya bantaɓa ganin inda akace ango yatare gidan surukanka sa ba,dan haka baxa fara wannan rashin M ɗin akaina ba. Tunda yafara magana tasake baki tana kallon sa saida yakai karshe sannan tasake fashe masa da sabon kuka tana cewa"yanzu ni yakake son nayi kasan inasonka kuma wannan abunda kake magana akai......kice musu ke mijinki zaki bishi dan zakufi sakewa can dashi yakatseta da faɗin hakan. Rugumesa tayi tana"amma kasan inasonka kuma zan iya komai saboda soyayyarka ko? "Eh nasan zaki iya ya bata amsa. "Amma gaskiya baxan ɓata musu shirin su ba. Tureta yayi daga jikinsa yana karemata kallo dayasa tasha jinin jikinta,ta duburburce tace"ina nufin shirin su nason haɗa kan family ɗinsu waje ɗaya aikama kana ɗaya daga cikin mu yanzu ko? Shiru yamata tabbas akwai wata a ƙasa kuma bazai nuna mata komai ba. Dan haka saiya saisaito da muryar sa yasake shigar da ita jikin sa da kyau takoyi luf tana sauraron bugun zuciyarsa. "Basma inason kisan wani dan na aureki hakan bayana nufin nine zan tare gidan ku ba,matsayin ki na ƴa mace kece wacce zadauka akaita gidan mijinta kamar ko wace ƴa. Kaman yanda shi mahaifin naki yakeson ganin ya haɗa kan family ɗin sa nima nawa mahaifan suna so"amma ai daddy yace da amincewar daddyn ka tafaɗa tana sake shigewa jikin sa. Burin mahaifina yasha bamban da tawa burin dan ni burina befi na ganni zaune da iyayena da ƴan uwana da matata dakuma yarana dukkan mu family ɗaya zaune saman dining munacin abinci a tare ba dan haka muddin kina sona bakya son kiyi aure kikare rayuwarki a gidan ku ba to saifa kin tare gidana dakina mushimfa rayuwarmu kaman ta sauran ma aurata. "Amma ai....."wannan shine burina bazan kuma canza zance na ba,kaman yanda nafaɗa miki mutuncin ƴa mace akace ɗakin mijin ta. To kinga bafa faƙiri bane ni dazan biki gidanku saboda wani abu na mahaifinki kingane ko bawai ina alfahari bane,a'a inason kisan cewa ko dako zanna dauko ɗan abunda de zannemo matata da ƴaƴana suci Allah bezai hanani ba. Balle kuma Allah yawadata ni na tsaya da kafafuna bana dogoro da dukiyar daddyna,na baki awa 24 kije ki zauna ki nutsu kiyi tunani shin wannan tsarin da suka dauko na son tarewa ta gidan ku yayi kokuma na tarewarki gidana shine mutuncinki? Kawayenki nawa akayiwa aure shin ba gidan mazajensu aka rufe musu kai aka kaisu ba? Kokuwa gidagen su angwayen suka bisu? Ke akaran kanki tarewarki gidan mijinki shine ƙimarki ko kuma shi mijin yatare gidanku ɗakinki gaban iyayenki wace irin rayuwa zakuyi wace irin sakewa zakiyi da mijinki al hali kina zaune cikin gidanku gaban iyayenki. Idan ko kinƙi janyewa daga wannan ƙuduri nasu karshe kece zaki wahala dan ni mijin mace huɗune ina daman ƙara aure kefa? Kinga saide kikare rayuwarki a gidan ku ke ba bazawara ba ke ba ga mijin ba. Yana kare fadin hakan yarabata da jikinsa yayi gaba wayan sa kawai ya dauka yafita yabarta a office ɗin tsaye ƙiƙam kama wata wacce aka dasa a gun. Aisha tana fita daga office Ahmad ta hango khalid tana ganin sa ta daidaita kanta miƙo mata waya yayi sabuwa dal a kwalinta yace"Suhail yamatsa shine yatura ƙudi naje nasayo miki ta,kiduba idan batayi miki ba sai muje tare kizaɓi wanda yamiki akwai sim aciki da karfe biyar ɗin yamma ze kiraki kinga nima yanzu na huta da kira yakare magana yana ƴar dariya,yana dan sassauto muryar sa yace wai ƙanwata menene sirrin wannan farin jini haka na kwara kan zaratan maza haka. Murmushi kawai na nasakar masa nace"masha Allah waya tayi kyau ya khalid gaskiya ka iya zaɓe. Murmushi shima yasaki yana ɗan bubbuga kafadan sa. Daren yau kaman yanda basma bata rintsa ba,tana ta tufƙa da warwara karshe de topic tasaka a social media wanda matasa da samari suka shiga tafka muhawara kan wannan maudu'in. Ahmad ma nashi ɓan garen hakance ta kasance dan daya kulle idon sa Aisha yake gani yana sumbata yaja karaman tsuka yana gyara kwanciya a ransa ko cewa yayi idan ma aljanace ke to haka zaki barni. Aisha kuwa hankali kwace tatafi da wayanta gida koda tanuwa su,anty hajia da anty malika murna suka tayata malika ita ta zauna ta tura mata Apps da tasan zata bukata,dadare bayan sun kwanta suhail yakira suka sha hirar su.   ALLAH YASA MUDACE [5/12, 6:57 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* Chapter 37 Yanda suhail yake zayyano mata da sirrin zuciyar sa da kalamai masu sanya farin ciki karshe har bacci ya dauke ta suna kan waya saida yaji saukan numfashita sannan ya sumbashi wayan shima yakwanta. Hajia mariya suna tattauna yanda tsarin komai ze kasance musu a bikin ita da kawarta hajia bilkisu dan bikin ƴar gata za'ayi acewar ita hajia mariyan"dole ƙawata ƴar gwallin gwalin ai dole a gwada mata gata saide kawata wani hanzari ba gudu ba. "Uhmmm ina jinki hajia mariya ta faɗa tana maida hankalinta ga ƙawartata dan tasan da magana a bakin ta. "Yauwa dama batun tarewar angon a nan gidan naku duk da banso saka bakina acikin lamarin ba amma gani nayi mai ze hana tunda yaron shima naga kaman da rufin asirin sa kiyi magana da Alhaji ya bari ayi mata jere a ɗakin ta kinsan bakin mutum mugun abu kuma ko dan saboda ƙawayen mu da ƴan gulma da ƴan bani na iya dole sai kanayi kana canza taku kinsan haka kawai wasu gulma da tsugu didi ke kawusu zuwa gidan biki kinga idan ko yarinya bata tare ɗakin miji ba yo mai amfanin zuwa dubai sayomata kayan gado kinga ai asara ne tunda basu fita cikin gidan naku ba. Nisawa hajia mariya tayi ta kalli kawartata tace"kumafa balki magananki tana kan hanya,amma kibari kawai zanyi magana dashi Alhaji idan yaƙi zan haɗa da babba yayansu tunda yana jin maganan sa. ******** Aisha ta dauki wanka tana zaune tsakiyar gado suna video call da suhail sai zuzuta kyanda tamasa yake"Aisha wai menene sirrin wannan kyawun naki? Fari tayi da ido ta dan tura baki cike da yanga tace"kaine sirrin ƴar dariya yayi cike da jin dadi yana shafa kansa da hannu nockin kafar ɗakinta akai tana daga kanta sukai ido hudu da Malik dayayi kicin kicin da fuska yace"dallah malama kifuto mu tafi kin tsaya kina batan lokacin saboda rainin wayo kin barni ina jira kaman wani drive kinzo kin zauna kina ta zuba a waya. Langwaɓe kanta tayi cikin siririyar murya tace"sorry gani nan zuwa yanzu,dalla mata harara yayi ya juya yana banƙo mata ƙofa dayin ƙwafa. Ajiyar zuciya ta sauke"lafiya?Suhail ya tambayeta ta daya bangaren dan ganin mood ɗinta ya canza lokaci ɗaya"aiki zani shi kansa sai yanzu ya tuna suna da meetin da wasu baƙi gashi kuma tun ɗazu yana ganin kira daga P-A ɗinsa daga ɗaya daga cikin wayoyin sa amma ya gagara ɗaga kiran"yanzu sai yaushe kuma? Nasan idan kin tafi aiki ba lalle nasame ki a waya ba,kuma gaskiya baxan iya yini ba tare da nasake jin muryarki ba. "Mayi waya data yaya khalid amma fa banda vid call saboda kasan yanayin aikin mu"ok yanzu de zaɓamun kayan da zansa nafita,waro manya idanunta tayi tace"ta ya? Clothes set ɗinsa yanufa yafara ɗaga kayan gasunan burjik kaman zaka buɗe kanti saboda yawansu,can ya ɗago wani blue suit sunyi mata kyau a ido tace wannan sai kuma waje net tie shima ta zaɓa masa sai agogo sai kuma takalmi saida ya kewaya yasaka kayan ya feshe jikin sa da turaruka yafito fes dashi sai zuba murmushi yake haka kawai yatsinci kansa cikin nishaɗi gani habibty sa tazaɓa masa kayan gani yake kaman tunda yake be taɓa shiga data amshi shi irin ta yau ba. Anty malika ce ta leƙo tana cewa"to tsuntsuwar soyayya ai sai kizo ki wuce kin dasamun ɗan uwa ke kina zaune nan hankali kwance kuna shan soyayya cike da kunyarta tamiƙa mata wayan ta dauki jakarta tayi waje a guje duk kiran da Anty malika take na ta tsaya ta karɓi wayanta ƙi tayi,gaisheta da Suhail yayi shiya an karar da ita ashe bata ma kashe wayan ba,amsa masa tayi cike da kunya tace"yi hakuri na kora maka ita ko? Labas dama shirin sallama muke kika shigo ki gaidamun da su ummi zasuji ta amsa ta kashe wayan a ranta tana yaba kyaun Suhail ko ina Aisha ta tsinci diamond haka. Ahmad ya gama ciki yana batsewa ganin yanda lokaci ya ƙure Aisha bata zo ba,gashi yana son yau tayi masa wasu ɗinkin dan ita kaɗai ya yarda duk cikin ma aikatan nasa dan yasan ita bata saka wasa a aikinta komai yinsa take tsakanin ta da Allah bata saka ganda ko son jiki komai wuyan ɗinki idan yabiyo ta hannun ta yinsa take ba tare da ƙorafi ko cusgune fuska ba. Tana sauka a motar tana sake marairaice murya tana bama malik hakuri ganin yanda yake fushi tace"haba yaya malik a haka zan baka lil sisi ta kana irin wannan cinmun magani haka aikuma na baka hakuri ko. Besan sanda murmushi ya kubce masa ba yace"kin ganki ko? Ki kiyayeni Aisha wallahi kiyayi ranan da zan damƙoki ko wannan mai jan kunnen naki be......"sai kifito ai duk makara da kikayi kuma still kin tsaya kina.....Ahmad ne yake magana tsaye yake bakin kafar motar"barka da safiya yah Ahmad shima malik ya katse masa faɗan daya zo da ita. Miƙa masa hannu yayi sukai musabaha"lefin kane ko?ya tambaya yana tsare malik din da ido. "No ya amsa masa yana kallon Aisha data marairaice fuska alaman ban hakuri. Maida idon sa yayi kan Ahmad daya tsare shi danson jin mai zaice"hajia sai kifito tunda mun ƙaraso jiki ba ƙuzari ta fito daga motar ta raɓa gefen Ahmad zata wuce ƙamshin turaren data shafa mai sanyin ya daki hancin sa,lumshe idon sa yayi kafin yabuɗe su harta ɓace masa shama malik yashiga motar sa yana kokarin ta dawa a ranshi cewa yake wazai iya da wannan muzuran naka. Tana shirin shiga hall din ya katseta da cewa"biyoni office. Wani irin abu ta hadiya mukut dan ita batason wani ƙeɓewarsu dan taga alama iskanci yakeson koya nata. Shiga hall din tayi kaman bataji shi ba,tanufi saman keken ta tana gaisawa da abokan aikin nata"kee Aisha aka kirata daga bakin kofan yanda taji murya sa ba wasa ciki hakan yasa ta miƙewa ta tako cikin takun ta ta nufosa ganin tana zuwa yasa shi yin gaba,binsa tayi a baya har cikin office ɗin sa tun kafin yayi magana ita tafara bashi hakuri. "Dan Allah oga Ahmad kayi hakuri wallahi bazan sake makara ba. Shagala yayi da kallon ƙaramin bakin ta dake motsawa gwanin sha'awa kai Ahmad kai controlin kanka karkabada kanka ga ƙaramar yarinya ta rainaka. Wata zuciya ta gwaɓe sa,murtu fuska yayi kaman wanda aka aikowa da tsakon mutuwa yace"menene hukuncin wanda ya tsaɓa yarjejeniya? Da mamaki take kallon sa dan ita iya sanin ta batasan da wani yarjejeniya dake tsakanin su ba. "Ni bamuyi wata yarjejeniya da kai ba. "Ni kike turawa baki Eshow yanda yakira sunan saida gaban ta yafaɗi. Bata ankara ba taji ya canko bakinta ya haɗa da nata yana tsotsa kaman wanda yasami lollipop hawaye zallah ta ƙaicin abunda yake mata takeyi dakyar tasamu ta tureshi gefe tana mammashe leɓen ta saboda zafi da yake mata. Allah ya'isana nide kalle ka kaman mutumin karki a ido amma cikin ka fal iskanci ba abunda ka iya saison koyamun kawai saboda ka lalatamun rayuwata kacuce ni narasa wanda ze aureni. Shi maganarta na karshe har dariya taso bashi. "To ba gani ba tunda nine nayi barnan sai na aureki idan kin rasa mai auren,yafaɗi haka cikin halin ko in kula. "Allah ya sauwake wallahi ta faɗa tana fita da gudu dafe goshin sa yayi yana furta"ya salam wai meke shirin faruwa dani ne? Akan wannan ƴar yarinyar bana iya controllin kaina akanta kuma bana jin haka ga kowace mace sai ita Allahumma ajirni..     ALLAH YASA MUDACE [5/16, 8:25 AM] Xeenat: https://www.wattpad.com/1343772748?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=o7G1IJmPv%2Fwl9VoFVbNxN9A%2Bu%2FPktBI8lNVxI7oFgayXd5RMgi31H9zmLxenpbJhNMnmx1OSV5wvuR8gLQ1i2WcPxB54ccT18SltmfIEVjHfs1MKsSIMWez6CSYHxnsx ______________ *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 42 Harya kai hannun da nufin damƙota sai kuma yayi saurin dunƙule hannun nasa saboda wani abu dayaji ya tsargar masa tsigar jikin sa. "Lafiya? Suka jiyo muryar Anty hajjia a bayan su wannan ya bawa Aisha daman kwasa da gudu bako tare da tabi takan tambayarta da Anty hajia keyi ba tayi waje. Ikon Allah kaji wani shashanci kuma komai yake damun yarinyar nan oho ta faɗa tare da ƙoƙarin juyawa tasake jinjina wa a ranta komai ya tsoratata harhaka,idanta ne yasauka kan mutum dake tsaye kaman an dasashi tace kai kuma yaushe kazo nan kode kaine dama ka firgitamun ƴa? Ɗaga mata kafaɗansa yayi yana cewa"ni kuma anty hajiya yo mai haɗina da ita. Wacece ita? Naga kyawawan yara da zam shigo tare da Abdul malik gaskiya sun burgeni sosai? "Na tambayeka madadin kabani amsa sai ka bige da sake tambayata. To itade wannan da kagani yanzu sunan ta Aisha waƴan can yara da kagani kannentane suɗin,ai yaran sun samu tarbiya sosai wallahi uwarsu mutuniyar kikece data kawaici idan kaji ance jajirtacciya to wannan ta amsa wannan sunan. Ai Aisha da kake gani yarinyarce tsayayya abun duniya be taɓa tsone mata ido ba fatan da burinta kullum ta nemi nakanta da gumin ta aima tajima tana aiki ƙarkashin ma'aikatanja fannin ɗinki,wallahi ba yanda banyi da ita ta koma makaranta ba bayan dawowarta nan da zama amma cemun kawai tayi ita burinta be wuce ƙannenta suyi karatu ba. Shiru kawai yayi yana sauraron ta sai data dire sannan yace"wai anty ina su ummu salma da malika ne? A baɗini basu yayi niyar tambaya ba kawai de yatsinci bakinsa da furtawane duk kokawa dayake da zuciyarsa. "Ai tuntuni suka fita,Faisal kuma tun safe be shigo nan ba yana can yana fama da aiki ya tasa computer gaba. Nan ta hau bashi labarin yanda aka tarɓrsu jiya a gidan surukan nasa dasuka kai lefe,shide sai binta yake da e'e kawai a fakance yake wulwulga ido yaga ta inda zata ɓullo dan yanason sake sakata a ido haka kawai yaji yana mararin sake ganin ta. "Anty ni zan wuce"to to to dawuri haka idan can company zaka ɗan ragewa ɗiyata hanya yau bata shirya ba malik yayi tafiyar sa ya barta. Yatsune fuska yayi yana duba agogo daya ɗaura nai shegen tsada da kyau da kallo sai kuma ya miƙe tsaye batare da yace da ita komai ba,yana cewa"wai Anty wace yarinyace da Ammi ke magana a kanta da zan fito a gida. "Aisha ce ko batayi maka ba,tako bashi amsa kanta tsaye dan koda wasa batayi tsammanin Aishan ta fito ba. "What ya furta da karfi yana mai kafe Aisha da itama ƙirjinta yabada sautin dum to mai tayi kuma karde zargi datake musu yazama gaskiya kuma wace irin alaƙa ce tsakanin su ƴan gida da oga Ahmad. Duk wannan magana a zuciyarta take yinsa yayinda jikinta ya ɗauki rawa karrr karrr karrr. Maganan sane ya daki dodon kunneta da yake cewa"haba Anty gaskiya batamun ba kalleni fa kalli wannan yarinya da ba komai a cikinta sa tsiwa da rashin kunya kumama nide nake da buƙatar mace wacce ta amsa suna mace ƴar jami'a mai aji ina zankai wannan jaririyar yarinyan rainonta zanyi,ina ina gaskiya ku canja tunani banda wannan idan kuwa kun matsa saide na zauna da ita na WUCIN GADI wato de ina nufin AUREN WUCIN GADI,dan zata taimakamun kota fanin aikace aikacen gidana ne. Can na hango Alhaji sunusi cikin gawani rumfa da alama wajene da aka keɓe dan shan iska wasu ƙatti ne majiya karfi dake tsastsaye zagaye dashi suna gadin sa,gefe ɗaya kuwa harkar business ɗinsa yake yana kallon komai dake gudana cikin systerm dinda ke gaban sa,kasan yanzu duniya ta cigaba kana zaune a wani kauyenku dako sunan sa zeyi wuyan fadi bakin wasu amma saikayi kasuwanci da wanda yake birnin sin ko dubai da England kuma kuna kallon junan ku kaitsai. Yana cikin wannan sai wayan sa dake ajiye kusa dashi taɗau burari neman agaji daga maishi ganin mai kiran nasa nasa sashi cewa da wanda yake magana dashin"zan nemaka zuwa anjima"ok sir aka amsa masa daga can ɓangaren rufe systerm din yayi sannan ya ɗauki wayan da harta katsa yana shirin bin kiran aka sake kiran sa. Saurin ɗauka yayi yana kara wayan kunne"hello aka faɗa a ɗaya ɓangaren kafin Alhaji sunusi ya amsa yaji ansake cewa"oga ansamu matsala fa Miƙewa tsaye Alhaji sunusi yayi daga zaunen da yake dan shi a rayuwarsa ya tsani yaji an kira masa matsala"what Mashi mai kake cewa kode kunnuwa nane basuji da kyau ba. Yafaɗa yana sauke wayan a kunnen sa da ɗansaka yatsa cikin kunnun yana kaɗawa,dasake maida wayan kunnen sa fatansa de be wuce yaji Mashi yace ba abunda yaji da farko bane. "Eh oga dan wallahi wani sabon jami'ine yakame mana dukkan nin kayan da mukai order jirgin yana dawowa gaɓan teku kawai sai ganin mutane mukai daga sama da alama kuma mu suke jira kode nace sunsan komai gami damu.....wani irin ashar ya lailayo yaɓa wanda yasaka Mashi dole dakatawa daga yi masa bayani da yake. Cikin kumfar baki yace"to mai amfaninku bazaku bude musu wuta bane? "Haba oga ya kake cewa haka wani wuta zamu bude bayan mudin ma nace maka daga sama suka faɗo mana ba tare da munsan da su ba,kuma wayasan yawansu. "Waye wannan mai son wasa da rayuwarsa ya shiga gonata? Eh Mashi wannan karon a zafafe yayi maganan kuma da karfu tsaɓanin ɗazun har saida Mashi ya sauke wayan a kunnensa. "Wanine wai sunan term din nasa operation sari ka nuke kuma su kansu su CP wannan yankin yace besan da wannan tsarin ba,dan da alama umurni suka samu daga sama amma yace ze bincika idan ya gane wanda ya jagoranci wannan aikin ze tuntuɓe mu,oga rayuwar mu tana cikin hatsari zamubar wannan yanki daren yau idan munsami mafaka zan kiraka. Faɗin halin da Alh sunusi ya tsinci kansa wannan lokacin ɓata bakine,dan karshe cire hulan sa yayi ya shiga firfita da shi saboda tsaban rikicewa,kai karshema cire babban rigar yayi yashiga zarya cikin ɗan rumfarda yake tare da tunanin wani ɗan kasadan ne yashiga rayuwar sa lokaci gudan dan son tarwatsa shi. WAYE WAYE WAYE? yakare faɗi da karfi yana watsi da kayan teburin dake gaban sa. "Easy sir ɗaya daga cikin guard ɗinsa yafaɗa. "Nabi easy da gudu ba wando nace nabi easy da gudu ba wando ko baka jini bane"sorry oga ya faɗa kansa duƙe a ƙasa. Kirane ya shiga wayan sa,saurin duba wayan yayi fatan sa CP mambila ne sai tsaɓani hakan ya gani Alh hamza ne ke kan layi ƙoƙarin daidaita nitsuwar sa yayi yan ɗaga kiran tare da salama. "Riƙe sallaman ka Alh duba wayanka ina ganin bakasan abunda ke faruwa ba ko,to duba wayanka kagani kitt ya katse wayan ba tare da yabashi daman tambayan sa ba. Hannu na rawa ya kunna datan wayan sa,abunda yagani saida yasa numfashin sa daukewa na wucin gadi,wati duk wani order da sukai ankame kuma ganan wani shegen jami'i yabawa ɗaga manyan kifi dake cikin kwando ko ince kwanduna yana bude cikin kififayen tare da ciro hodar iblisi wato koken yana ajiyewa ƴan jarida sunyi caa akansa da tambayayo. Wanine yamai tambaya kaman haka"shin waƴan dake safaran miyagun ƙwayoyin da sanin hukuma? "Kwarai kuwa dan bakin su ɗaya da wasu guɓatattatu cikin mu sune masu daure musu karƙashi suke tsula tsiyarsu lokaci yayi da zamu karya ƙasusuwar su sai mun sakakasu guduwa wanda yake da niyar gyara ya gyara dan akwai cuta acikin garin nan dama ƙasar tamu baki ɗaya dayake bukatar magani. Daɓas Alh sunusi yakai zaune wani irin zufa na karyo masa. ******* "Anty hajia me naji wannan yana cewa..au...au...auren wucin gadi dani kuma wayyo Allah wayyo Anna mairaici beyi ba a rayuwa,mai yasa Anna kika tafi kika barmu a lokacin da mukafi bukatarki. Wannan duk yana daga cikin rashin gata da rashin galihu da bamu dashi,na shiga uku dan Allah Anna kidawo ki daukemu daga nan gashi ana shirin ha intar miki ni. Tana fadin haka tariƙo hannun Anty hajia tashiga raira kuka cikin kukan take cewa dan Allah anty hajia ki ceci rayuwata karki bari son zuciya ya kaiki ga cutar da rayuwa na ki tuna nifa marainiyace ba abunda nasani na daɗin rayuwa face rayuwar talauci da gwagwarmayar rayuwa indan saboda muna zaune gidanki ne zaki yanke irin wannan hukunci kiyi wallahi yanzun nan zambar miki gidan ki da ƴan uwana dan tsiratar da rayuwata dama Anna ce tace nazo nan gidan da zama bayin kaina bane amma bazan tsaya inaji ina gani a mun auren dole ba,kisani kema fa uwace kin haifa idan ƴarki akawa haka ya zakiji aranki? "Ki nutsu Aisha Anty hajia ta fada tana kokarin sata a jiki ta rungumeta,da sauri ta janye jikinta daga gareta tace"ina ni ina sauran nutsuwa vayan inaji kaman rayuwata tazo karshe wani har yana ikirari auren wucin gadi dani kai ina. Faisal daya doso main falon gidan dan samawa kansa abunda zai saka acikin sa yafita aiki yasoma jin hayaniya natashi da sautin kuka. Dan haka da ɗan sassarfan sa ya karasa shiga ciki ja yayi ya tsaya ganin Ahmad dake shirin fita Aisha ta ciƙwaikuye masa riga ta baya tana kuka harda jan majina tana cewa wallahi ba inda zashi saiya saketa idan ma anɗaura idan ko ba daura ba dole sai yafaɗa da bakin sa bayayi su anty hajia su janye banzan magarnar tasa na auren wucin gadi. "AUREN WUCIN GADI Faisal ya maimaita kkalman ƙasan maƙoshi.   Alkalamiyafi Takobi⚔️ ALLAH YASA MUDACE [5/17, 10:23 PM] Xeenat: I just published "43" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1344213731?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=RrkNWlQzq%2Bhb4MWfILuS8lowPUuKpKPOfvmiz190yzBty1EnxfJaUfX%2BznVk4MTmhIcE6jvlWe%2BhdPL7PVpIjf3bY%2FQdwXcxPXfYYWnV%2B9UXG%2FgoXnQgfEqwU9cDeWRw ______________ *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 43 Yanda ta cuƙwiƙuye masa riga tabaya har jikin su na gugan na junan su yayin da Ahmad yashiga wani irin yanayi mara misaltuwa dan ji yake kaman da gayya da saninta take masa hakan,amma saboda miskilanci irin tasa baka isa cewa ga halin da yake ciki ba. "Aisha taho ki zauna muyi magana dake amma sai kin nutsu kin maida hankalinki jikin ki,girgiza mata kai tayi kana tace"a'a Anty hajiya dama kadai yake jira ya tafi alhali tunda yafurta hakan to kuwa aiwatarwa a gunsa abune mai sauki ban shirya gantalar da rayuwata ba haka kawai yamai sheni karamar bazawara da wani auren sa na wucin gadi kai ina,duk wanda yake da saka hannu cikin wannan abun naringa jaa masa Allah ya...saurin rufe mata baki yah faisal yayi be bari takarasa fadin abunda ke bakin ta ba. Yana girgiza mata kansa alama karka sake cewa wani abu,kuka mai karfi yataso mata irin mai cin rannan tun daga ƙasa zuciyar ta tashiga rerawa jikinta har rawa yake,tasoma cewa"wayyo Allah Anna kin tafi kin barni a lokacin da nafi bukatarki kusa dani ni marainiya ce bansan rayuwar daɗi ba saina rufin asiri bansan mai duniya take ciki ba lokaci ɗaya farat ɗaya narasa mahaifiyata farin cikina shin tana rayene ko bata raye na tabbata da tana tare dani yanzu da hakan bata faru dani ba nayi rashin kafaɗa da zan daura kaina nafaɗa mata damuwa ta nayi rashin cinya da zan kwanta nayi kuka waye ze sharen hawayena wayyo Allah gani gareka bani da karfi bani da mataimaki sai kai ka taimakani ka kuɓutur dani daga zalumcin wannan bawa naka rintse idanunsa yayi da karfi yana mai dunƙulu hannun sa wani irin turin bakin cikin da zallah taƙaici yake taso masa har hucin sa da wani irin zafi yake fita. Hajia ikilima ma kuwa jagwaf ta zube saman ɗaya daga cikin kugeran da sukama falonta nata ƙawanya tayi tashiga sharan ƙwallah,ganin haka yasa Aisha sakin Ahmad tazo ta zube gwiwa biyu gaban ta tana cewa"dan Allah anty hajia kiyi hakuri kidena zubda hawayenki kaina,ke tamkar uwace gareni hawayenki musibace gareni na yarda zan iya daukan komai amma banda wannan maganan auren na wucin gadi nan idan ko kema kika goyi da bayan yin hakan to wannan yana nufin rasa dukkan nin farin cikina ne. Ahmad dake tsaye be juya ya kalle su ba,yayi ficewar sa yah faisal na biye dashi abaya. "Boo wai meke faruwa ne?narasa gane kan wannan abun naku,naji kai kana kiran auren wucin gadi ita kuma tana kukan bata yarda ba wai me? Numfashi daya gumsa a bakinsa ya fesar yana mai saka hannuwansa cikin gashin kansa yana yamutsawa idanun sa rintse ya datsa leɓansa na ƙasa da karfi kaman ze fudasu saboda ƙunci dayake ciki can kaman ba zeyi magana ba har yah faisal ya fidda tsammanin zaiyi magana sai kuma yace"nima kaina bansan abunda ke shirin faruwa da ni ba,tako ina ba sauƙi ɗan uwa. Rana zafi inuwa ƙuna,inda nake tsammanin samun sassauci garesu suma kaga inda suka ɓulomun,dafashi yah faisal yayi yana cewa"boo kakara hakuri in shaa Allah zakaci riban hakuri da biyayya,daga haka yarakashi yashiga mota yatafi shi kuma yana mai tausayawa ɗan uwan nasa aure biyu lokaci daya kuma duk babu zaɓin ka aciki abun da ciwo amma idan kayi hakuri sai kaga alheri. Alhaji sunusi yashiga tsaka mai wuya dan ba ƙananun ƙudi yasaka a wannan harkan ba,waya yake hankali tashi sai faɗi yake"mambila wai wani dan kasadan ne wanda bayason rayuwan sa yakeson wasa dashi? A ɗaya ɓagaren naji wanda aka kira da mambila yana cewa"Alh gaskiya saide kayi hakuri dan koma wanene ba karamin tanadi yake dashi kanka ba,dan da alama be fara wasan ba sai da yashirya kuma duka cikin hukumanmu babu wani wanda yake da masaniya kansa,da alamade umurnine daga sama kuma kafin ya turo da kayan nan zuwa head quater saida duniya tasan da labarin nan kaga bamu da ikon yin komai akai idan akwai abunda zance maka befi nace ka tsagaita na ɗan wani lokaci ba. Dan abu kazan uban nan yafaɗa da karfi yana baya baya kaman ze faɗi Allah yabashi ikon tsayuwa da ƙafafunsa,yanzu mambila kana nufin mutsaida komai saboda wannan banzan da be bayyana kansa ba? "Kwarai kuwa Alh bakaji ance kaji tsoron abokin gabanka na ɓoye ba,dolene mu canza tsarin komai idan ma yana bibiyar komai namune to yanzu zamu canza tsarin komai duk wani jadawalin na farko zamu kansale. ***** Rarrashin duniya nan hajia ikilima tayi amma babu wani canji wajen Aisha dan sai cewa take saboda anga ni marainiya ce akaimun haka ai da iyayenta na tare da ita ne ko banza zasu bukaci jin ra'ayinta. Karshe saida hajia ikilima ta ɗauki waya takira Ammin tana dagawa ko gaisawa bata bari sunyi ba tace"yaya akwai matsala? Miƙewa tsaye hajia ma'arufa tayi tanufi hanyan ɗaki dan tana tarene da ƙawayen hajiya mariyah da suka zo jere lokacin,saida tashiga ɗaki yarufe kofa harda murza key sannan tace"matsala ikilma ta mefa? Nan Anty hajiya takwashe komai daya faru ta sanarwa yayatata ta kara da cewa"yanzu haka aikin rarrashi nake amma ko kadan taƙi saurarata bansan ya zanyi ba,Ahmad yaxo duk ya dagula komai tafaɗa kaman zatayi kuka. Dafe goshinta tayi tana mai cewa"dama fitan da yayi ɗazun gidan naki yaje?barshi ze zone yasa meni yaro besan ana masa gata ba,hmmm"kede yaya bari kawai wai har cewa fa yayi zamu aura masa jaririya ko rainon ta zeyi. Dan dariya hajia ma'arufa tayi kana tace"ze gane rainonta zeyi ba zai taɓa sanin gata muka masa ba shi da uban sa ba sai nan gaba,kinsan Allah ikilima baki bani bashin rantsuwa ba amma kwata kwata jinake ban yarda da wannan haɗin auren na Ahmad da ɗiyar Alh sunusi ba,gani nake kaman da wata a ƙasa wallahi shisa nadage kai da fata saida aka daura da Aisha sannan naɗanji dama dama ko ba komai zata zamewa ɗana garkuwa haka nakeji a raina. "Kwarai kuwa yaya haka,amma ya akai mutanen naki suka canza shawara suka yarda da tarewar ɗiyarsu bayan da sunce saide Ahmad ya tare gidan su?"Allah masani ikilima banace ba,ko sunga kaman zargi ze shiga tsanine suka canza taku oho kin kuma san halin ɗanki tunda ya tirje bazashi ba to bazashin bane dan haka sukai da uban inaga koshi sa suka canza tsarin nasu mude Allah muka rika mutum ko tashi sama yake saboda tsafi da yardan Allah ba abunda ze samemu,na cikaki da surutu jeki lallaɓa mun ɗiya da zaran ɓakin nan sun tafi zaki ganni. "Tom yaya sai kin dawoɗin sukai sallama koda ta waiga taga wayam ba Aisha dake zaune dan haka hankali tashe ta nufi ɗakin su nan ta cammata ta haɗa kai da gwiwa sai kuka take. Zama tayi kusa da ita tasaka hannu ta ɗago da fuskarta da yayi caɓa caɓa da hawaye tace"sai kika tunomun da yayata sanda aka ɗaua mata aure da mijinta wato mahaifin su Ahmad kinsan yanda tayi kuwa? Bata jirayi amsa gunta ba taci gaba ta cewa"haka tasaka kakarmu gaba da kuka da bori kamande yanda kikayi ɗin nan karshe wasu daga cikin ƴan uwa suka yanke shawaran kawai ya sauwake mata tunda bata ra'ayin sa,sai wani dattijo yace ku kira ita yarinyar muji ta bakinta kafin a yanke hukunci. Koda yaya tazo da wannan dattijon tsohon kakannamu ya tambayeta kaman haka"ma'arufa shin wannan miji naki bayi miki ba a warware auren a maida gawani wanda kike so kukuwa? Buɗan bakin yaya sai cewa tayi cike da ƙuruciya nide gaski Alhaji babba bawai shiɗinne beyi mun ba kawai ina kukane idan natuna wannan ƙatuwar tumbi nasa nace wa ƙawayena wannan ne mijina aisai sumun dariya karshe suma idan ba sa'a akaci ba susaka shi waka a dandali ai Aisha batasan sanda da fashe da dariya ba harda riƙe ciki......     Alkalami️yafi Takobi⚔️   ALLAH YASA MUDACE [5/19, 9:13 AM] Xeenat: I just published "44" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1344604973?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=8eXA3ZPoSp1gMVBOZePIasu2LeMHsv6rcblZGAZsSP92LL6Op0eB%2FApEd9f1Pt%2BdVd10joyDBVu%2BAd41AYWC58OWL3u8Ii2PW2NTGyw3uLTpdtVK3gfbupGXQEXX79Ih __________,,____ *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 44 Sunjima Anty hajiya na bata labarin ban dariya harta sake sosai kaso hamsin cikin ɗari na damuwarta sai taji ya gushe,suna cikin hira sai ga sallamar Ammi daga falo tare suka miƙe suka isa gareta har kasa Aisha ta tsuguna ta gaidata amsamata tayi fuska sake tana kamota ta miƙarta ta zaunar da ita kusa gareta tana kara godewa Allah daya sa Aisha ta zama surukuwarta sannan tana addu'an Allah yasasanta tsakanin su yakuma dasa musu soyayyar junan su a zukatan su. "Aisha Ammi takira sunanta cikin sanyi murya. Na'am Ammi ta ansa mata kanta duƙe. "Nazo da kaina ne domin baki hakuri bisa kuskure da muka aikata miki,karki ga kaman dan rashin gata mukai miki haka a'a munyi hakanne saboda munyaba da tarbiyyarki kamalarki sannan uwa uba nasabanki da yarda kuma da amincewar mahaifiyarki mukai wannan abun asalima itace ta jagorance mu wajen wani Baban Abba shiya wakilci dauri auranki. Idan kinga munshiga rayuwarki ne kiyi hakuri Allah yana gani kuma shiya dasa mana kaunarki harmukai wannan tunani,idan ma so kike na duƙa a gabanki nabaki hakuri wallahi Aisha ashirye nake dayin hakan. Nasan mun miki lefi dan Allah ɗiyata kidubi girman Allah kiyafe mana...Aisha jitayi duk jikinta yayi sanyi yanda Ammi take mata magiya jitayi duka ta muzanta mace kaman Ammi da girmanta da komai amma tasauke kai take bata hakuri ba tayi la'akari da ƙanƙantarta shekarunta ba,sunyi kalan tausayi kaman zasu saki kuka daga Ammin har Anty hajiya kallon fusko kinsu tayi ɗaya bayan daya sai ta sauke kanta tace"Ammi karkiji komai matsayinki na uwa dan kinyanke hukuncin kan ɗiyarki ai ba lefi bane kawai de naji babu daɗine da yaxo yake cewa dani sai kuma tayi shiru saboda nauyin Ammi da takeji yanzu. Shafamata kai tasoma yi tana mai cewa"Allah yayi miki albarka ɗiyata ubangiji Allah ya bayyanar mana da Nafi aduk inda take yakare mana ita da lafiyarta"amin Anty hajia ta amsa daga nan suka shiga hiran su nan takejin satin sama auren sa da basma wani irin abu taji yadaki ƙirjinta zuciyata ta gwaɓeta da ina ruwanki da auren sa da har zakiji wani haushi keda aurenki dashi na wucin gadine to haushin me zakiji,miƙewa tayi tanufi ɗaki duka bin bayanta sukai da kallo tare suka sauke ajiyar zuciya kowanne cikinsu da abunda yake aiyanawa aransa. Ahmad koda ya tafi company kasa sukuni yayi lokaci zuwa lokaci sai yaja tsuka da kallon tangamemen agogo dake maƙale a office ɗin nasa,a wannan halin khalid yashigo yasame shi yayi mamakin ganin sa a wannan lokacin dan besaba shiga company a wannan time ɗin ba shisa ko knockin beyi ba yashiga turus ya tsaya yana kare masa kallo"man lafiya na ganka a wannan yanayin? "Me kagani? Ganin raina masa hankali yakeson yi kawai sai yace"dama suhail ne yakira yace an dage wannan taron sai next 2weeks kai kawai yajinjina masa,sai kuma ya daura da cewa waƴancan kayan na suleiman Ghana gobene fa alkawarin mu kuma naga har yanzu Aisha bata shigo ba. "So "Nagade ita keda alhakin wann...katseshi yayi ta hanyan cewa"daga yanzu na canza tsarin tafiyan ba ita ba yin wasu aiyuka masu kaman daa,kallon kataɓune khalid yamasa kaman zeyi magana sai kuma yayi shiru yana dage kafaɗa yayi ficewar sa yana amsa kiran da suhail yamasa ya tambaya mai yasami mutuniyartasa baya samunta ta waya. "Ai yau kwata kwata bata shigo ba nima tunani da nake yanzu ko llafiya amma kwantar da hankalinka zan bincika inji,a ɗaya ɓangaren suhail kaman zeyi kuka yake cewa khalid din dan Allah ina jiranka idan da wani abu ka taɓoni jinake kaman nayi tsuntsu na ganni a garin naku. Dariyama abun yabama khalid dan haka saida yadara kana yace"kasan mu ƴan africa musamman nageri ƴan matan mu daban suke da sauran. Shima suhail din dariya yayi yana cewa"gashi nagani karamar yarinya duk ta dagulamun lissafi nakasa samun sukuni idan banji muryarta ko munyi video call ba jinake manan rayuwata ce takusa barin gangan jikina"kai mr suhail dama ance ku labarawa kunfi kowa iya soyayya da iya tattalin mace. wannan kan sosai yasaka suhail darawa yace"kai khalid ai bakasan matsalanku ku ƴan africa baku iya sauke kai ga mace bane alhali ko ta fannin halitta halittarmu ba ɗaya da nasu bane sannan kaga mu yanzu anan koda mune da gaskiya sanda mace ta hau 90 tayita faɗa tayi kuka to karshe zamu zauna mu sauke kanmu mubata hakuri da sayo mata ɗan fure ko wata ƴar sarƙa komade mainene abunda ze faranta mata raide hakade tare da kalamomi masu sanyaya zuciya da nuna mata zallah soyayya amma ku maxan africa baƙwayi masamman ma ku hausawa. ********* Aisha kuwa koda tashiga ɗaki duk yanda taso kawar da abun aranta kasawa tayi karshema fashewa tayi da kuka mai tsanani ita fa a ganinta duka rashin gatane yajamata haka,tana haka su khadija suka dawo daga makaranta suka isketa hankalin yaran yayi ƙololowar tashi da ganin halin da yayar tasu ke ciki,cikin kuka khadija ta rungumeta tana cewa"Anti aisha me akai miki daya yake saki kuka? Gaskiya idan har zamanmu anan ɗin be kwanta miki a rai ba mu masu binki koda dokar daji murayu dake matukar hakan zesaki farin ciki. Kallon fuskar ƙanwartata tayi sannan ta miƙawa mubaraq hannu yaro dama kaman jira yake yazo da dan gudun sa ya faɗa cinyarta yana sauke ajiyar zuciya,shirune yaɗan ɗauke su na ɗan wani lokaci kana Aisha ta dubi khadija tace"khadi nasan kina da hankali dakuma lura duk da ƙarancin shekarunki bani da kowa da zan faɗawa damuwa naji sassauci acikin zuciyata sai ku,nasan wani abun idan kin fahinta wanin ba lalle ki fahinta ba,khadi aure aka ɗaura mun kuma da alama ya kwan biyu bansani ba. Wani irin zabura khadija tayi ta waro idanunta waje tana kallon yayar tata baki na rawa ta maimaita kalmar"Aure "Eh aure kuma nan takwashe yanda sukai dasu Ammi ta faɗamata. Saida ta gama sauraronta sannan tace"anty aisha dan Allah ki kwantar da hankalin ki mubi komai a hankali ganinki cikin damu yana taɓamun zuciya da hanani sukuni. Nan tashiga kwantarwa da Antyn tata hankali da kalamai masu dadi nan shima mubaraq yashiga bata labarin makarantar su da yanda uncle malik yake sayamai kayan dadi yace"Anty harma wajen wasan yara kaini yake muhau lilo tare ya goyani Anty har wasan doki da ƴan ɓoye ɓoye munayi dashi jin yanda kannen nata ke ta fadin alherai ga ahalin gidan yasa xuciyarta dan sassautawa amma fa batajin zata sassautashi kan uban gayya tunda ya furta da bakinsa auren wucin gadi to lalle sai ya furta yajanye kalaman sa sai yazo ya duka gabanta dan neman yardan ta da soyayyarta. Ya faisal kansa duk ya dauki ɗumi aiki yake tuƙuru amma bawani haske cikin lamarin nasa wacce yake tsammanin wani haske ta wajenta itama tamasa mummunan fassara zaune yake yana rubutu a saman wani dan takarda inda ya rubuta LION da manyan harufa yakasa gane kan abun yaja tsuka yafi akirga Aisha ce ta doso wajen ganin takarda iska ya dauka tayi sauri kamowa tana ajiye masa gaban sa dacewa"Ya faisal da alama hutu kake bukata dubi yanda iska yayi filla filla da takardun dake gabanka amma kagaza yin komai ta ajiye masa saman dan karamin tablr dake gabansa tayi shigewar ta cikin garden. Bude idon sa dake lumshe yayi ya sauke su saman table din da nufin tattara komatsan sa yashiga ciki ya huta kaman yanda tace din,kwayan idon sa yasauka saman paper data ajiye masa LION taya juya upside down yabashi abunda yake nema tsawon kwanaki wato NOI7 besan sanda wani irin ƙayataccen murmushi ya suɓuce masa saman fuskar sa ba....tare da furta kalmar Alhamdullahi acikin ransa.   Alkalami ️yafi Takobi⚔️ ALLAH YASA MUDACE [5/21, 3:57 PM] Xeenat: I just published "45" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1345295536?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=srYvvcIgPVOzbuJC0L%2Fe8M9q3rPr1z9kCUkzyc90b%2BA3jsd%2B8ZR3fr9Yh4HcEjMyaHsLlnA4yd86vO3zJ4po5ZfNjymq9suCaSwAqlBMmspgmJgH1jKzwSYB%2FQSioraF _______________ *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 45 Aisha koda tashiga garden ɗin zamanta tayi dan wajen yana da daɗin zama ga shukan furannin da kuma kukan tsuntsaye ga wani iska mai ni'ima dake kaɗawa kamshi furanni dake tashi waje luf tayi tana tunanin wai yanzu ita matar aurece,yanzu bata da hurumin yin komai sai da izinin wancan banzan kwarton mai halin bunsuraye kai ina kilama su Ammi dan basusan halin sa bane yasata zo tayi ta rokonta alfarma da tasan halin ɗanta ai baxata wahal da kanta wajen zuwa bata baki ba,yanzu ya xatayi da suhail ita fa shine wanda zuciyarta ta aminta dashi badan kuɗi ko kyansa ba saide dan kyan halin sa da ganin girma da darajan ɗiya mace. Hajiya mariyah da kawarta hajiya bilkisu gurfane suke gaban wani ɗan tsamurmurin tsohun bokan sun gurfana gaban sa kaman masu neman gafara,hajia balkine cikin rawar jiki tabuɗe baki wajen cewa"ran boka ya daɗe wannan itace ƙawata danake baka labarin ta mungurfana gabanka domin neman taimakonka da agajinka cewar hajia balki bude baki hajia mariyah tayi da nufin koro masa bayani yayi saurin ɗaga mata hannu cikin kakkausan muryarsa mara daɗin sauraro yace"basai kinyi mana bayani ba munsan da zuwanki tunkafin ku zo auta ya sanar dani bukatar ki saide kinyi sake dayawa yaron da kuke son aura masa ɗiyar ku ba ɗiyar taku bace arayuwarsa wata yarinyar ce ta daban. Wani irin zabura hajia mariya tayi batasan sanda tabuɗe baki ta furta"ya rasulu manzon Allah ba,wani gigitaccen tsawa bokan yadoka mata yana ƙara jaddamata karta kuskura ta sake irin wannan gangancin anan,tsuƙwi da kai tayi tana mai neman gafaran sa. Wani ƙwarya ya miƙo musu dan madaidaici cikinsa cike yake da ruwa yace"ku kalli ciki ku gani,a tsorace suka leƙo da kawunan su Ahmad ne tsaye sai wata yarinya da basa iya hango fuskata tsaye saide suna iya kallon ta rungume da towel ta juya masa baya. "Kan bala malam mezan gani? Karde ace auranta yayi asirrance ita kanta bata san sanda bakinta ya subuce wajen fadin hakan ba. Girgiza mata kansa yashiga yi yace"ko ɗaya saide sakacin ɗiyarki zesa hakan ya kasance,cikin rawan baki hajia bilki ta amshe da"yanzu malam ina mafita? Bushewa yayi da dariya saida yayi mai isarsa sannan ya dubesu da ƙananun idonsa yace"mafita ɗayane zan baku magani kuba ɗiyar taku tayi tushe dashi kuma ta tabbata taja ra'ayinsa ya kusance ta sannan duk abunda yafito ta jikin sa ta goge da farin ƙwalle ku kawo nan. "Amma.....kallon da yawatsa mata yasata haɗiye maganan da takeso tayi hajia balki kuma na zungurinta tayi shiru dole ta haɗiye abunta muƙut.....nunatayayi da yatsansa yace"nan ba wajen gardama bane kuma ba wajen yimana musu bane duk abunda muka faɗi anan gaskiyace bama fadin karya saide mufaɗa ba daidai ba. Mijinki yana cikin wata ƙungiya to kice dashi yatashi tsaye yayi sake ɗan zaki ya girma akwai wata gagarumar ƙalubale dake tunƙararsu kungiyar tasu zata ruguje kaman ba'ataɓa yinta ba sannan ze dawo faƙirin sa kaman yanda yake daa sakamakon cin amana dayayi. Hhhhhhhhh yasake kecewa da wata iriyar dariya mara daɗin sauraro da amonta ya amsa duka cikin dajin tsoro fargaba duka yarufe su hajiya mariya"kutashi ku tafi ansallameku kufita da baya ahankali karku take yaran aljanu sukaji wata murya daban wanda bata bokan ba,kululu cikin su duka ya ɗuri daruwa itako hajia mariya har gudawa takeji kaman ze zubo mata saboda tsaban firgici da take ciki. ******* Aisha shagala tayi zaune a garden harbatasan adadin wani lokaci ta ɗauka ba kaman daka sama iska ta kaɗo wani hoto takafaɗa saman cinyarta,ganin takarda mai kaman hoto yasata saka hannu ta dauka ta juyar da fuskar na cikin hoton sosai tana kare masa kallo ko kiftawa babu can tasaki murmushi ganin anyi rubutu kaman hakan WANTED"aikin banza ta furta a fili suna xaune cikin AC suna saka mutane wahala alhalin su kansu sunsa inda wayan nan miyagun suke dama. "Aishatu bakiga wani hoto ba,wallahi ina tsaka da tattarewa iska ta barbazasu. Yah faisal ne ke magana yana ƴan dunbe duben sa a bayanta saida ta juyo taga ashe hotunan suna dayawa bama ɗayan nan bane"gashi nan ta faɗa tare da miƙo masa hannu yasa yana karɓa yace"wallahi aikin nan duka yasani gaba gashi lokaci da aka ɗibarmun harya kusa cimmini amma haryau bawani karin haske daga kowace kusurwa. "Inako zakaga karin haske bayan dasaka hannun manyanku ake aiwatar da komai"what mekikace? Yafaɗa yana samun waje yana zama a ɗaya daga cikin kugerun wajen da aka tanadasu dan shan iska. "Ni bance komai ba,tafaɗa tana ƙoƙarin miƙewa ta bar wajen dan saida yayi maganan tagane ashe fa zancen zucin da take yafito fili. "Please dan Allah Aishatu kisake maimaita abunda kikace,kinga wannan case ɗin saura mako guda a amsheta daga hannun na kuma wanda za bawa kowa yasan ba mutumin kirki bane ƙilama idan case din yakoma hannunsa komai sai yafi na yanzu lalacewa Aishatu nashiga wannan aikinne da zumman kawo canji kasata da garina amma wallahi tunda na fara aiki nake fuskantar bara zana da rayuwata wataran har tsoro nake karwani abu yasami ahalina duka ta sanadina,yanzu haka na aiyana araina matukar nafaɗi kan wannan bincike zan bar aikinne baki daya dan banga amfaninta ba tunda bazamu iya ceto rayuwar ƙananun yara daga hallakaba bazamu iya ceto yaruwar ƴaƴa mata da ake lalatawa ba,gamu muna amsa sunan jami'ai amma bamuda amfanin komai a kasarmu saide kawai mushiga mota mukunna jiniya muna yawon yin bincike amma babu nasara. Yaƙare magana yana dauke ƙwallah daya taru a idonsa tare da miƙewa ze bar wajen. Tausayinsa ne ya darsu a zuciyar Aisha tabude baki dakyar tace"shi na wannan hoto nasan inda yake yana shagon aski JB barbin saloon kusada babban shagon rufaida yogouth shago mai NO17 zaka sameshi kimanin karfe biyar da rabi na yamma dan mafi akasari idan mun tashi a wajen aiki nan muke yawan ganin sa zaune dukda bansan abunda ke kawoshi wajen ba,amma yana da yawan kallon mutane kaman be yarda dasu ba,zan iya taimaka maka idan har kabani daman hakan dan ganin kakamashi amma banson koda munje waje kai kafito daga cikin motanka dawuri sannan karka tafi da motar da aka sanka da ita dan o ready manyanku sun rigada sun basu bayananku dama fuskokinki amfani suke daku dan cinma manufofinsu idan ko kun kamasu wahalan banza kukesha cikin awa da be gaza biyu zuwa uku ba zasu saka kubarsu to me amfanin wahal da kanku dan ganin kunkawo canji,yah faisal canji nan fa baze samu ba harsai muda kanmu munkankare tsatsan dake zukatanmu sannanne canji zezo mana. "Like father like dauther shekarun baya haka mahaifinki ya tsaya gaban manyan jami'an tsaro da manyan dattawa masu faɗa aji akasar harma da sarakuna yayi wannan maganan saide ko wata biyu ba rufe ba mukaji labarin wai yafita ba ganshi ba. Ahmad ne dake zaune duk tunanin duniya ya taru yama kansa yawa gashi yau wannan ƙwailar ko gilmawarta be gani ba karde tace zata bar aikinta dan kawai taji ance an aura masa ita tace zata goga ƙafaɗa da kafaɗa dashi hmmm ya sauke ajiyar zuciya daidai secretary ɗinsa mai suna jamila ta buɗe ƙofan office din sa ta shigo sai wani yauƙi take kaman karkashi ita adole ta burge ogannata koda ze kyasa.   Hajiya mariya koda suka dawo gida shiganta bayi uku sannan ta ɗan tsahirta koda Alh sunusi yadawo haka ya taddata kwance saman doguwar kugera tayi rajab"mariya lafiya na ganki haka duk kinwani susuce? "Hmm ba lafiya ba Alh jin amsa data bashi yasashi komawa ya zauna yana cewa"ina sauraronki amma dan Allah kadaki sake dauramun wata damuwan. Kallon sa tayi ta watsar tana cewa"dadina dakai rashin hakuri to gashi gashi abunda malamin yace da mukaje ɗazu da bilkisu gwara musan nayi tun kafi komi ya kare mana.   ALLAH YASA MUDACE [5/24, 11:43 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 46 Ba tare daya dago daga abunda yakeyi ba yace"jeki ki dubomun Aisha cikin musu ɗinki,wani irin tuƙuƙin bakin ciki taji ya turnuketa tama rasa meke mata daɗi koba komai ai yabari yaji dame taxo amma sai wani shamƙamshi yake duk uban kuɗin data ɓata wajen yimasa kwalliya dan ganin ta burgesa amma a banza. Saurin juyawa tayi ta fita tana jawo kufar da karfi yabada sautin garammm ɗan tsuka yayi ya cigaba da abunda yake. Yau asabar anwayi gari da labarin ɓacewar wasu riƙaƙƙun ƴan ta'adda da hukumar ƴan sanda ke nema ruwa a jallo,wannan abune daya tsorata sauran ƴan click ɗinsu dama manyansu kai duk wani ɗan mafiya ya tashi da tsananin tsoro da fargabar yake da ɓacewar manyan yaransu har guda hudu LION da akafi sani da NO17 sai junior sai kuma kaska da bazuka ɓatansu ya girgiza manyansu dama ƙasa baki ɗaya dan ba wanda yasan taƙa maiman wanda ya ƙwamushe su,hukuman ƴan sanda tuni sukai zaman gaggawa dan acewar su wannan abun kunyane ace suna aiki ba dare ba rana amma ace sungaza kama waƴan nan mutanen saide kawai suji labari agari wai wani ya kamesu ba su ba,wannan abun kunyane gare sosai cikin ɓacin rai IG yamiƙe yana tada jijiyoyin wuya yana faɗa cikin tsananin bacin rai yace yabasu nan da awa 48 dan ganin sun kamo wanda yayi wannan aika aikan kokuma suda aka kaman wannan umurnina yafaɗa da kakkausan murya. Duka amsa masa sukai da yes sir. Duk da sunsan abune mai matukar wuya ace susamo waƴan nan mutanen cikin kwana biyu dan duk wanda yayi wannan abun ba karamin shiri yayi ba. "Alhaji ya ina faɗamaka ga abunda boka yace kana ɓagarar da zance wallahi wannan bokan aikinsa kaman yankan wuƙa yake baya karya duk abunda yace ze faru to ba makawa saiya faru. A fusace ya ɗaga mata hannu rai aɓace yafara magana"haba mariya sauraramun da zance bokan nan mana haka tun dazu kin isheni da magana ɗaya waima in tambayeki mana"ina jinka ta amsa masa a daƙile. "Shin da izinin wa kika ɗauki ƙafa zuwa wajen bokan? Tambaya daya mata a bazata kame kame tasoma yi dan bata da amsa guda dazata bayar dan kare kanta ita kanta sai yanzu ta tuna da katoɓarar da tayi dan tun tuni Alhaji sunusi ya haneta da bin malamai ko bokaye acewar sa idan kishiya take tsoro shi bashi bayi mata ƙari sannan yara wanda ta haifa masa sun isheshi rayuwar duniya shisa suke cin duniyarsu da tsinke duk abunda tanema yimata yake wani abun ma saide kawai taga yasayo mata. "To daga yau kika sake wanke kafa kikaje wajen wani boka kiyi kuka da kanki idan kinyi wasama ita ƙawar taki mai baki shawara zuwan zanyi muku katanga tsakanin ku,fuuuu yawuce ciki cike da fushi abu ya game masa goma da ishirin. Suhail duk ya tashi hankalin sa dana ƴan gidan su baki ɗaya da rashin samun sahibar tasa a waya kwana biyu da beyi ba,kira dubu zema khalid amsar ɗayace ba tazo aiki ba koyaje gidan su besame su ba,ganin sa cikin damuwa ya tashi hankulan ahalin sa baki ɗaya musamman ummin sa,yanxun ma zaune yake wayansa riƙe a hannun sa kaman wanda ze ganta taciki ɗagowa yayi yace"Ummi kibani izini inason zuwa Nigeria a yau ɗin nan dan son ganin meyasame ta nasan haka kawai bazata kashe wayarta ba inma wayar tata tasamu matsalane ai dole zanji daga khalid tunda kullu yaumin sai taje aiki,kafin ummin tayi magana suhaiham dake zaune dan nesa dashi ta taso tazo gaban sa tazube gwiwa a ƙasa tace"yanzu akhi dama duk saboda mace ka shiga wannan halin damuwar dan Allah faɗamun dame tafini,kyau ko asali naɓata lokacina akanka nakori duk wasu samarina masu sona da aure nace sai kai irin sakaiya da zakamun kenan kawai sai ta daura kanta saman cinyarsa tafashe da kuka saida tayi mai isarta sannan ta ɗago tariƙe masa hannu tace dan Allah kasoni ka kaunaceni koda kwata kwatancin sonda nake makane wallahi idan kagujeni koka juyamun baya mutuwa zanyi kawai sai tari ya tsarƙe mata tasomayi ba kakkautawa take duka sukai kaita kira suke suhaima suhaima cikin tsananin tashin hankali ummi take kira ɗaukota muje asibita amma tuni tatafi luuuuuu sai tarota yayi sumamiya cikin tashin hankali ya ɗauketa da gudu yayi waje da ita sakata mota yayi Ummi tashiga ta daura kanta saman cinyarta sai hospital. ******* Aikinki yana kyau ƙanwata dan murmushi tayi tace"karka damu akwai manya manya boma bomai daxasu tarwatse nan gaba saide tarwatsewar ba zaiwa mutane da yawa daɗi ba. "Ai wannan ɗinma beyi musu daɗin ba ya amsa mata da faɗin hakan"hhhhh ƴar dariya tayi sannan tace wancan ɗin fa gunduma gunduma ne tashin sa saiya girgiza ƙasan baki ɗaya"Allah de yasa bamu aciki dan gaskiya nayi mamakin aikin da ya ɗaukeni tsawon wata shida inayi amma ke cikin awa ɗaya kika gamashi kai keɗin ta dabance naso ace kina ɗaya daga cikin mu. "Hmmm bani da ra'ayin aikin ɗan sanda sabida cin hancinsu yayi yawa"kai Aisha bafa duka aka taru aka zama ɗaya bafa"kaga time na ƙurewa zoka maidani gida kar Anty hajiya taga daɗewata dan cemata nayi zani duba ƙawata. yau yakama mondaya kowa kagani shirin fita yake ƴan makaranta nayi masu aiki nayi. Cikin shiri fita aiki take dan yau haka kawai ta tsinci kanta dason leƙawa tun a cikin gida malik yake mata surutun shifa bazata shiga masa bayan mota ba dan shiba driver ɗinta bane,ƴar dariya tayi tana cewa"sha kuruminka malam wanda ma yafika da komai zan dauka driver nan gaba kaɗan wanda kaida kanka iidan kaganshi yana buɗemun mota sai kayi ƙass da kanka ai kaikan a wannan gaɓan saide ko mai gadina zan daukeka"kutt wani irin wawan mangari yakai mata tayi sauri guduwa bayan Anty hajia tana ɓoyewa"kwafa yayi yana cewa"wallahi anty hajjya ashe kekike daure ma yarinyar nan ƙarƙashi take raina mutane. "Yo kaiko Abdul malik ba dole na nadaure mata ƙarkashi ba surukuwa wasace takare faɗin hakan cike da zolaya,Aisha kuwa rufe fuskanta tayi cike da kunya tana shirin barin wajen shikuwa malik ya ɗauka da yayansa faisal Anty hajiya ke nufi dan haka yayi dariya a ransa yana cewa shisa kwanan nan nake kallon sa makale da ita ashe ba banza ba. Karfe goma daidai motar sa ya shiga company haka kawai yaji zuciyan sa badadi yau,duk inda ya gilma sai ma'aikatan sa sunzube kasa suna kwasan gaisuwa yauko ɗaga musu hannu dayakeyi bayayi saida direct office ɗinsa yanufa kaman kullum jamila ta tsaftace komai saida ya zauna sosai sannan yashiga duba cctv ɗinsa,tsaye ya hangota tana ɗagawa mai mota daya sauketa hannu da murmushi ƙwance saman fuskarta take yaji wani abu kaman mashi ya sokeshi. Waya ya dauka idon sa nakan tv yakira mai gadi yana daukawa beko tsaya amsa masa gaisuwa dayake ba"yace turomun wannan yarinyar ya ajiye wayan,tsuke fuskanta tayi kaman wacce aka faɗawa sakon mutuwa kaman bazata ba sai kuma tanufi office ɗin nasa sallama tamasa ƙasan maƙoshi ta tsaya tsakiyar office ɗin batare data rufe ƙofan ba tace"gani saida ya mula kaman badashi take maganan ba sannan ya ɗauke kansa daga allon tv yakalle ta kallo na tsanake"natsani yawan kallo wallahi a rayuwa mutum sai shegen kallon kaman ƙwarto tayi maganan ƙasa ƙasa tana turo bakinta sarai yaji mai tace amma ya shareta. Saida ya gaji da kallon nata dan kansa sannan yace"meya hanaki zuwa aiki kwana biyu? "Bani da ra'ayine shisa banzo ba,ta amsa masa kanta tsaye shi wasu lokutan har mamakinta yake wajen tsaurin idonta da son mai dawa mutum magana kanta tsaye ba tare da shakku ko tsoro ba. "Iska yafesar ta bakin sa yace"amma kinsan ka'idan aikin ko?"eh mana duk wanda yayi fashi zaka zabtare masa albashi sai kuma me? Tamaida masa da tambayan nufota yayi bata ankara ba taji ya damkota yariƙeta da kyau sannan yace"shikuma wanda ya saukeki a mota yanzu da izinin wa ya ɗaukoki ko kika shigar masa mota. Marmar tafara yi da ido kaman zatayi kuka duk da haka bakin be mutu ba cike da tsiwa tace"idan tambayata zakayi katsaya inda kake amma mutum kullum saboda kwartanci sai ya raɓi jikin mutum sannanne zakaji daɗin masa magana ai wannan haramune. Ɗalle mata baki yayi da yatsa"mugu kawai ai wannan ma cin zaline ta faɗa tana kunkuni"eashow nikike kira ƙwarto ko bara yau nanu miki ni cikekken kwarton ne nan gaba kyaji daɗin kirana da sunan beyi wata wata kawai ya haɗe bakunan su guɗaya yafara tsotsan lips ɗinta kaman wanda yasamu lolilpop gashi ya matsata sosai jikinsa ba ta yanda zata kwaci kanta sai hawaye dake fareti saman kyakkyawar fuskanta a haka jamila tashigo ta gansu mutuwar tsaye tayi dan batasan sanda file ɗinda take riƙe dashi yafaɗi ƙasa ba,shi kuwa khalid murmushi yayi kawai yana mai komawa da baya kaman ma bega maike faruwa a gun ba dan shi yajima da sanin abokin nasa yadulmiya ƙogin soyayya ba tare daya sani ba. Alhji auwali da su Alh hamza harda oga Alh sunusi zamane sukai na sirri kan abunda yake shirin tunkarosu nan Alh auwali ya dubi Alhaji sunusi yace wai shin"ya akai hakan ya farune shin sakacin mune yajawo faruwar hakan kode cikin mu akwai mai mana zagon ƙasane? Nan suka shiga kallo kallo a tsakanin su kowa da abunda yake kissimawa a ransa"nimade abunda nake tunani kenan gashi ita kanta hukuman ƴan sandan bata da masaniya balle ayi yanda aka saba cewar Alh sunusi ya daura da cewa kama kame waƴan nan yaran namu bafa karamin hatsarine garemu ba"dole akwai masu bibiyarmu Alhaji hamza ya amsa da faɗin hakan"kunfa san yau kwana biyu da kame mana kaya a malesiyya kuma haryau ita kanta hukuman tace bata san mai alhakin yin wannan aikin ba,gashi yanzu lokaci ɗaya aka kame mana yara har hudu kai abun faa abun dubawane. Alhaji surajo ne ya amsa da cewa"ni abun ms mamaki yake bani wai wata yarinyace taje tasai kaya kusan na dubu ɗari uku zata masa tranfer yaƙiyi shine fa yace tazo suje pos daga nan shikenan ba ita bashi. "Yarinya kuma? Har rige rige suke wajen tambayan sa"eh ya amsa su yaɗaura da cewa na LION ba sukuma sauran ance anyi amfani da wayan shi LIONɗin wajen kiransu ɗaya bayan ɗaya da faɗa musu inda zasu haɗu shike nan. Dolene mutashi tsaye dan kaganin mun kare kawunan mu dama dukiyar mu baki ɗaya,kuma yazame mana dole muyi idon fara dan ganin mun binciko masu bibiyarmu. Duk wannan tattaunawa dasuke yana kallon su ta tv dake gaban sa kaman ma tare dashi sukai wannan tattaunawar dariya yayi sosai sannan ya miƙe tsaye yakira ɗaya daga cikin yaran sa yana mai bada umurnin"ku binciko mun wanda yakama LION ance yarinyace mai alaƙan ita wannan yarinyar da waƴan nan mutanen ina bukatar sani"angama oga aka amsa masa ɗaya ɓangaren yana barin wajen dan cika aikin ogan nasu. RUGA FULANI CIKIN WATA BUKKA Hango wata mata nayi kwance kaman bata numfashi kwance saman katifat yayi gefenta kuma wata ƴar yarinyace zaune tana wasa"ruwa ruwa ruwa matar dake kwance saman katifar yayin ta ambata amma idon ta arufe,kallon ta yarinyar tayi sai kuma ta kwasa da gudu tayi waje tana kira"inna muddibo ƴarɗo kozo yau matar nan tayi magana dukkan su kusan atare suka yo hanyar bukkan harsuna turarreniya gun shiga.   Alkalami️yafi Takobi⚔️ ALLAH YASA MUDACE [5/27, 4:42 PM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 47 Suna shiga cikin ɗakin sukaja suka tsaya ganin ba wani alaman wannan mata ta motsa,inna fure ce ta kalli boɗɗo cikin harshen fillanci ta kai dubanta ga boɗɗo tace"anƴa bakarya kika mana ba matan nan ta motsa kuwa? Cike da yarintar ankirata da makaryaciya ta shiga dirza ƙafa tana mustsuke ido ta ƙwaɓe baki tasaki kuka kai da gani kasan kukan shagwaɓane cewa tayi"am inna aide naji tace ruwa ruwa inma karya nake kutashe ta ita zata faɗi,kanta modibo yashafa yace "yi shiru boɗɗon Abba ai nisan bakya karya inna inaga mubata ruwan taimakawa inna fure yayi suka ɗan ɗagota suka shiga bata wani ruwan jiƙon magani da Abba yanemo cikin daji ya jiƙa,sunyi mamakin yanda tasha ruwan dadama,inna fure kasa hakuri tayi fuska ƙumshe da annuri tace"da alama fa lafiya tafara sumuwa tunda tsawon wannan lokaci data ɗauka cikin wannan hali dakyar ruwa yake wucewa ta maƙoshinta amma duba yau kaga hamdullahi tasha dadama wannan ma wata nasara ce. ***** Daddagewa tayi da datsa masa cizo a harshen sa ai kuwa besan sanda yature ta daga jikin sa ba idon nan nasa sunkada sunji jajur,share hawayenta tashiga kana tace"kwarto anfaɗa kwarton saika tsireni ta kwasa a guje tayi waje bangaje juna sukai da jamila dake laɓe tana dakon fitowarta ai kuwa batayi wata wata ba ta damƙota ji kake fass fass ta sharara mata ruka har sau biyu,ita ma Aisha cike da jarumta dan ita bataga dalili da za'a mareta haka ba,tunda bada saninta taxo ta bigeta ba. Ramawa tayi tana nunata da yatsa tace"idan kina cin kasa kikiyayi ta shuri bada sani na bangajeki ba amma kiyi hakuri harta juya ta fara tafiya sai kuma ta dawo da baya tace bafa hakuri akan marin da narama nake baki ba a'a hakuri akan bangazan ki danayi ne. Baki sake jamila ke binta da ido dan kusan suman tsaye tayi ita kan ta bata taɓa kawowa a ranta wannan ƴar ficikar yarinyar zata iya ɗaga hannu ta rama marin da tamata ba,dan haka tanaji tana gani Aishan tabar wajen harta ɓacewa ganin ta bata iya yin komai akai ba. Alhaji badamasi zaune suke da abokin sa Alhaji manzo nan Alh manzo ya ƙurɓi lemon mai sanyi saida ya ajiye cup din hannun sa kana yadubi abokin nasa dacewa"kaman naji kishin kishin wai an ɗaurawa Ahmad aure da wata bayan ƴar gidan Alh sunusi da kowa yake tsammani,wani irin zabura Alhaji badamasi yayi yace"mai nakeji kake cewa ne kode nine banjika da kyau ba. "Karde kace dani bakasan abunda ke tafiya a gidan naka ba,to inde haka lalle da.....sai kuma yayi shiru take zufa yakaryoma Alh badamasi inda yatuna maganan su da Alh sunusi na karshe inda yace dashi nayarda ƴata zata tare gidan ka bisha wasu dadilai amma kasani auren ɗanka da ƴata ba saki babu kishiya babu taƙura duka abunda takeso shi zatayi matukar ɗanka ya tsallaƙe daya daga cikin wannan sharuɗan jinin sa ya halatta dan zamu sadaukar da jinin sa wa dodon mu. Yana kawowa nan da tunanin sa kawai ya miƙe zumbur yashiga safa da marwa yama rasa tacewa sai shi Alh manxo ne daya ƙara dacewa"yanzu me mafita kasan sharaɗin da Alh sunusi ya ginɗaya maka kuma a gaban dodo akai wannan yarjejeniyar nima kaina da wannan labarin ya zomun na kaɗu sosai nasan tabbas ba'a saninka hakan yafaru ba. Amma kajeka kabincika a hankali cikin hikima zaka tunkari ita hajiar dan tanada masani komai tunda nima abakin mai ɗakina natsinta. Da haka suka rabu da Alh manzon inda ko sallaman kirkiri betsaya yi da abokin nasa ba yanufi motarsa driven sa na ganin sa ya nufosa da sauri yabuɗe masa murfin motan saida yashi ya xauna da kyau shima drivrn ya zajaya yashi yama motar key sannan cikin ladabi da biyayya yace"Alh ina muka nufa? Muje gida ya amsa masa a gajarce Koda isarsu gidan be tsaya jiran sai anbude masa motan ba yabude da kansa yanufi cikin fuskar nan tasa hade kaman hadarin gabas zuciya tamasa nauyi har wani huci yake,ko sallama be tsayayi ba,saboda rufewar ido bemaga waƴan da suke zaxzaune a falon ba yana shiga kawai kan Ammi yasauke idon sa. "Ma'arufa yanzu sabida kinmai sheni mijin hotiho ɗan nawa saide na tsinci labarin kunmasa aure a titi,shin mekike ɗauka kanki dashine ko yanada wani uban bayan ni. Waima wani ishafeffe da mai ɗinne da harya isa ɗaurawa ɗana aure ba tare da ƴawuna ni ubansa ba. "Sai ni aka amsa masa daga bayansa a mugun figice ya juya dan jin muryan da beyi tsammanin ji koda wasa ba,ido hudu sukai da tsohu mai rankarfe wato baffan sa wanda suka kira da malam mai babban riga zaune ya hakimce saman daya daga cikin kugerun da sukaima falon ƙawanya sai gefen sa wansa yakubu da kanin sa nafi'u zaune daga ƙasan carpet sai gefe guda kuma ma'aruf wato dan uwan hajia ma'arufa sai kuma yarta yaya bara'atu da kawunta ita hajiar Aminu gefe guda kuma ga setin akwatuna biyu masu kyau da daukan hankali ajiye ganin idon malam mai babban riga be hana Alh badamasi fidda abunda yake ransa ba. Saida ya daura da cewa ta tabbata ashe gaskiya ake faɗi ba rade raɗe bane to wallahi ma'arufa muddin nine na haifi Ahmad ba wani ya haifamun ba to a yau yau kai yanzu yanzu basai anjima ba ze rubutamun takardar sakinta ya bani a hannuna idan ko ba haka ba....."Ta tabbata ashe abunda ake faɗi kanka gaskiyane ba karya ba,to wallahi kasani kafita harkar sunusi idan ko ba haka ba akwai ranan nadama ina jiye maka wannan rannan dan abotanka dashi ba abunda ze kareka dashi. Kuma yaro kaika haifi abunka ba wanda ya haifama saide kaman yanda kake da iko kansa kake kuma da hakki hakama ita uwarsa tana dashi aure de anɗaura ba fashi saide kasani muddin kace zaka raba wannan aure to wallahi kasani ƴar gwal din da kakeson aura masa baxe taɓa auren taba saide ayi biyu babu"dan Allah baffa kayi hakuri yafada sanda yake zama daɓas a gaban baffan nasa wallahi idan ance dole sai anyi wannan abun zamu iya rasa Ahmad ɗin....duk falon ido suka zuba masa suna kallon sa shi kansa besan yayi wannan katoɓarar ba saida yafaɗa sannan yarufe bakin sa da duka hannun sa yana ta muzurai rashin gaskiya. Hajia mariya ɗaki tashige bayan wucewar Alhajin cikin rawar jiki tashiga laluɓen wayan kawartata wato bilki saida tayi mata kira biyu sannan ta ɗauka wata ƙatuwar ajiyar zuciya hajia mariya ta sauke tana cewa"ƙawata akwai matsala. "Mecece matsalan? "Akwai matsala. "Faɗamun matsalanki koda yakai dutsen auhudune baki da matsala tunda kina dani kwantar da hankalinki kaman kinma sarki karya. Dariya suka kwashe kusan a tare harda shewan su sannan hajia mariya ta kwashe komai dasukayi da Alhajin nata tafaɗa mata. Ajiyar zuciya Alhaji balki ta sauke sannan tace"kewaya faɗamiki idan anje wajen irin wannan ana faɗawa miji"tabb kice na tabka kuskure fadin hajia mariya"ba ɗanka ɗan ba kuwa dan ai maza basason mace tasan sirrin su idan kuma kina tafiya ire iren wannan wajen yanzu idan bamuje wajen ba zakisan yana wata kungiya ne? Kai tashiga jijjiga mata kaman suna tare ta daura mata dacewa to bara kiji da kibude kunnenki da kyau ki saurareni yanzu duniya ta canja anfita daga rayuwar duhuwar kai idan kana da kai ka ƙara da wanka idan kina kissa wajen riƙe miji sai kinhaɗa da biyebiyen nan dan samun malakan kansa. "Kai kawata "Hmmm kina mamakina to bara na faɗa miki yanzu haka na mallaki gidan kaina kai gidaje ma zance miki bada sanin Abbansu usman ba ina da motoci har uku da akemun aiki dasu keke napen goma duka nayi tanadin abunane dan karta ɓaci,yanzu ke me kika mallaka naki nakanki. Hammm hajia mariya ta sauke ajiyar zuciya tace"gaskiya nifa ba abunda na mallaka nawa na karan kaina banda ƴan gwal gwale daya saimun da kansa ba abunda nake dashi . "Tabb kina ruwa ashe ni ina kallonki wayayya ashe da sauranki,waya fada miki yanzu mata suna zama hannu rabbana dole kitashi tsaye ki yakice rabonki kinji abundade boka yace wallahi kika tsaya kallon ruwa sai ƙwaɗo yamiki ƙafa daga nan sallama ta mata ta kashe wayanta,tabar hajia mariya da sake saken xuci dan ita ko keken kanta bata mallaka ba,ashede mata na samun kuɗi ita ta zauna sai abunda aka yaga mata takeda lalle dole nima nashi tsaye abunda take tsakawa aranta kenan sai zarya da take cikin bedroom ɗinta tana bubbuwa wayan a hannunta. Tunda Aisha ta fita yaxube saman kugera sai maida numfashi yake ruwan gora mai sanyi ya dauka saida ya shanye goran tass ya lumshe ido shiyama rasa mema yake jansa zuwa gareta yarinya da nonuwanta ko lemun tsami basu wuce ba,yama rasa wata jarabace ke damunsa ga manyan mata amma yaɓige da laluɓan ƙwaila ai wannan ma zubda ajine idan wani yagansa sannan sayama kansa rainine wajen ƙaraman yariya da haifuwar kajine ya haifi irinta. Aisha kuwa tana barin wajen saida ta saita nutsuwarta sannan ta nufi cikin hall dinda suke dinki cikin sakin fuska ta gaggaisa da abokan aikinta nan suka shiga hira da laila nan take ce mata"wai ke me sirrin ne kwana biyu baki zoba sai kinga yanda oga yake zarya zuwa nemanki,tafaɗa tana ƙasa da murya da ƴar dariya kadan kaɗan. "Duka takai mata a wasance tana cewa"laila yaushe kika fara sharri"wallahi bawani sharri gaskiya nake faɗi,tsakanin sa da khalid bansan wanda yafi zaryan zuwa tambayanki ba,danma shi oga baya magana sai muzurai"Allah ya kyauta tace tana dauka wani yadin material ta yanka tabada zizza kafin ta haɗa wata doguwar riga data dauki hankalin duka abokan aikinta inda nan take suka sakata jikin ƴar tsana suka shiga haska mata hoto kowa kagani burinsa yariga ɗan uwansa yin postin kan kace me,sai ga kira daga costomers irin big girl din nan kowacce burinta ace itace wacce zafara ganin wannan kayan ajikita,basma na zaune da salaha suna cikin abinci a gidan cin abinci salaha dake daddanna waya ita tafara cin karo da wannan post ɗin a IG ganin ruwan comment da yanda dinkin rigar yatsaru saida ta bibiyi waje ta tabbata sannan ta miƙawa basma wayan tace kalli nan ki gani"wai me kinsanfa ni bana saka kaina sabgar media. "Kede karɓi kigani tafada tana sake miƙa mata wayan. Karɓa tayi tana kallo ai batasan sanda ta saki wani ihu ba,har saida hankulan mutane dake cikin wajen ya dawo kansu,sauri miƙewa tsaye basma tayi tana laluɓen numbar wayan Ahmad dan sanar masa da bukatan ta. Gudu gudu sauri sauri tajeta tabiya kuɗin abincin harsuka shiga mota kiran wayansa take amma be dauka ba,kai tsaye company tanufa ko tsayawa kashe mota batayi ba,sai salaha ce kashe cike da yauƙi tashiga office ɗinsa ko neman izini babu ya lafe jikin kugera idanun sa a lumshe kaman na bacci sai sauka kiss dinta yaji a ƙuncinsa bazato. Dan tureta yayi yana waro idon sa akanta"sau nawa zan faɗa miki banason wannan ɗabi'a ta yahudancin,cikin ko inkula tace"sorry saura kwana nawane a shafa. To sai kibari sai anshafan kyayi"yanzu de ba wannan ne yakawo ni nan ba,wayan ta miƙa masa karɓa yayi yana ware idon sa saman hoton basarwa yayi yana maida mata da wayan"nagani sai me? "Yamunne inason ɗinkin nafison nazama nice wacce zata fara sakashi jibi a wajen party ko wacce classic girl maiji da kanta saide ta gani ajiki na kuma banason asake dinka irin sa cikin kwanakin nan harsai nasaka. Taɓe bakin sa yayi danshi bega abun zaƙewa anan ba. ""Ok bara naduba nagani ko wayayi wannan dinkin danni banima da masaniya akansa,yana faɗa yana gyara zamansa da kyau ita dinma zaman tayi ta zuba masa ido tanajin wani irin abu mai karfi gami dashi gira ya ɗaga mata alaman yade"ina son ka shine abunda yafada tana tsare shi da ido jin ko ze tanƙa amma sai taga ya maida da hankalinsa ga wayan da yakeyi tadeji ya ambaci "Aisha kuma ok turamun ita yanzu daga haka yakashe wayan. Minti biyar tsakani sai gata tashigo bakinta ɗauke da sallama fuskarnan tata tsuke danma kar yace zesake gwada mata rashin M"gani oga tace dashi tana sakeyin ƙasa dakai,nuna mata basma yayi sai sannan ta waigo gareta"barka da warhaka hajia tafaɗa batare data kalli yanayin fuskarta ba,saida tasha ƙamshi tana ƙarewa Aisha kallon dan tayi wani irin freesh taga kamanma ta ƙara mata girma a ido daɗa taɓe bakinta tayi tare da ɗaga kafaɗanta tace"kaya nagani kuma inaso konawane zan biya sannan dole a mallakamun tunda nace inason. Ba Aisha ba shikansa Ahmad yanda tayi magana cikin isa da nuna iko abun yabashi mamaki saide besaka musu baki ba asalima basarwa yayi kaman baya wajen. "Bansan wani kaya kike magana akai ba ta amsa mata cikin sanyi murya daya zame mata jiki,tura mata wayan tayi gabanta zata kai hannu taɗauki wayan tayi sauri daukar wayanta tana cewa"ba irin ƙazamai ke taɓamun waya ba,maganan tama Aisha zafi dan haka itama kanta tsaye ido cikin ido take kallonta sannan tace"kuma ƙazaman su suka ɗinka kayan da kika wanko ƙafa kikazi nema,kan kizo dubunki sunzo dan haka wannan kaya ba mallakin kowa bane mallakina ne sai yanda nayi shi koshi kansa mai faɗa aji na wajen bashi da iko akan wannan kaya kina iya ɗauka tsamin kafanki kibar waje dan bazaki taɓa saka kayan nan wajen ba dan dukkanmu masu aikin taron ƙazamanne sai aje can anema awani jen.......     Alkalami️ Yafi takobi⚔️   ALLAH YASA MUDACE [5/29, 3:33 PM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 48 "K kinsan waye ubana da zaki tsaya gabana ina faɗi kina faɗi? Kallon kasa da sama tamata sannan ta danyi wani juyi da ɗan miƙa kamande da gayya tayi haka illa kuwa sakon ya isa gawanda takeson isarwa dan kusan mutuwar zaune yayi dukda ƙokarin sa nason basarwa dayake dan yamai da hankalin sane kacokan kan systerm din dake ajiye a gaban sa idan baka sani ba sai kaɗauka wani aiki yake mai mahimmanci saide a baɗininsa hankalin sa gaba ɗaya yana kansu dan kallon kasan ido yake binsu dashi"na sani mana ta amsa mata a ƙaikaice mutum ne shi mai hannu biyu kafa biyu ido da baki da hanci sunan sa SUNUSI takare faɗi da tafa hannu sai me? Dawani irin mugun sauri ya daugo kansa yana kare mata kallo anya yarinyar nan tasan waye mahaifin Basma da harta iya kiran sunan sa tsirara haka,maganan da yakeyi a ransa kenan yayin da Salaha dake laɓa bakin ƙofan shiga office tayi saurin dafa bakinta da hannu tana jan kafarta takoma da baya dan baxata so suyi ido biyu da ƙawatata ba,dan ita tasan waye uban nata a rashin imani. Ita karan kanta anata ɓangaren mutuwar tsaye tayi dan wannan shine zata iya cewa karon farko datayi kuri da mahaifinta wani mahaluƙi ya kira sunan sa tsirara haka bawani ɗan kara wai wannan yarinyar da haifuwar kaji ma zata iya cewa ta haifi irin take tsaye gabanta ido cikin ido ta kira mata sunan mahaifi haka. "Waye ubanki anan garin? Waya ɗaure miki gindi dahar kika samu gwarin gwiwan kiran sunan mahaifina a tsirara haka? Yanda tayi maganan kawai ze tabbatar maka da ranta na ɓace sosai da hakan. Itako Aisha ko ajikinta saima cewa da tayi"koba haka sunan sa yake ba? Nagade sunan da akai masa yanka da ita kenan yo mai nawani nuna damuwa dan ankira mutum da sunan sa,taɓe baki tayi ta cigaba da cewa ni banga abun damuwa anan ba. Idan dama saboda wannan kika kirani to kinga ninayi nan,takare dafita daga office dinma baki ɗaya,a fusace ta juya kan Ahmad dayayi kaman ma baya wajen cikin muryar kuka take magana"yanzu MY rashin darajata har yakai kana waje ana gayan magana bazaka iya tsawatarwa ba,kanajin fa yanda wannan ƴar mitsitsiyar yarinyar nake takira suna daddy haka gatsar bawani kara ko girmamawa,kawai sai tasaka masa kuka datake ta dannewa tuntuni. Numfashi ya sauke yana mai ture systerm ɗin gefe yacire eyeglass dayasama idon sa danson kare masu kallon ya ije gefe sannan ya harɗe hannun sa guɗa yana kallon yanda ta dage tana risgar kuka"wai kukan duka na me? Ya tambaya kaman ma besan meyafaru tsakaninta da Aishan ba,sake sautin kukanta takara batare da tama kula shiba ganin bata da niyar amsa masa yaɗaga kafadan sa yana cewa"anyway tunda bazakiyi shiru ba shike nan inada meetin jirana ake yanzu haka zsn iya tafiya idan kin kuma gida kimiƙa sakon gasuwata ga hajia. Saurin shangaban sa tayi ganin dagaske fitan zeyi bata tsaya wata wata ba ta rungumesa cikin kuka take cewa"wato baka damu da damuwata shine bazaka kirata ka tsawatar mata yanxu taci bulus kenan duk rashin kunyar da tamun,ni akullum sai sake linƙaya nake a kogin soyayyarka amma kai ko oho saima kakkaucemun dakake wai mazanyi kasoni koda ƙwatancin yanda nake sonka ne. "Hmmm Bass matsala yafaɗa can kasan maƙoshi yana zameta daga jikinsa kamo hannun ta yayi ya zaunar da ita saman kugera data tashi goran ruwa mai sanyi ya ɗauko yamiƙa mata bamusu ta karɓa tasha dan ita kanta tanada bukatar ruwan,ajiyar zuciya ta sauke tana kafesa da ido,kaman bazece komai ba sai can kuma ya motsa lips ɗinsa a hankali yace"abunda nakeso kikasani mu ƴan kasuwane bawai ƙarƙashin wani muke ba balle ya mulkemu. Sannan a harka ta kasuwanci ba nuna ma mutum iko akan abunsa,bakibi hanya daya dace ki mallaki wannan kaya ba,da farko kin nuna kinaso kuma dole a mallakamiki wannan dole ya tsaɓa ka'idan mu ƴan kasuwa,sannan kinnemi mai abun kina bukatar abu awajenta amma kina nuna ita bakomai bace face wata ƙaskantacciya. Yama za'ayi ta saurareki,da ace sari zakiyi ko pieces dubu kikace kina bukata kunyi ƙudi kinbiya wannan kina da ikon abunda zakiyi dasu koda kingani a jikin wata kafin yaxo gareki hakkinkine kibi diddigi. "Amma MY dan naga abu nan wajenka inaso bani da matsayi da zaka mallakamun wannan abun matsayina na wacce zaka aura,tafaɗa tana kafesa da ido dan son jin amsa da ze bata. Be bata amsa ba asalima bashi da niyar sake ce mata komai dan yana ganin yayima kokarin tsayawa yin dogon magana. "Shikenan ta faɗa tana gyara fuskarta tada ɓaci da ruwan hawaye mikewa tsaye tayi tana kallonsa ok ina bukatar pieces ɗari daga nan zuwa gobe warhaka nakeso kasan idan kuɗine ba matsalata bane,wani shu'umin murmushi yasake mata wanda takasa gane ma'anarsa yana ɗage mata kafaɗa yace"anyway zaki iya zuwa kisami mai kayan sai kuyi magana da ita dan ni kaina saida kikazo nasan da kayan an danko yadinda akai amfani dashi bama dashi anan company....saurin katseshi tayi tana cewa kace kawai bazaka saka baki wannan ƴar matsiyaciyar ta bani kayan ba kenan,to wallahi kasani ko ta halin yayane sai na mallaki wannan kayan fuuuu tafice a fusace tayi hanyan barmasa office ɗin tana mai daddanna wayanta danson dialing Number ɗin daddynta dan ita fa dole saita mallaki wannan rigar dan tunda mummynta ta haifeta bata taɓa nagani abu tanaso rasaba dan haka wannan ma tagani tanaso kuma dole ta mallaka dan ta nan ne kaɗai take ganin zata nunama ƴar matsiyatar nan bambanci dake tsakaninta da ita. ALH BADAMASI Zubewa yayi gaban mai babban riga duk yaruɗe yana bada hakuri kan dan Allah a rusa batun auren Ahmad da wata bayan wanda ake saka ran yinsa,yanda yaruɗen kadai ze tabbatar maka ba cikin hayyacinsa yake ba kamande bawa da shugaban sa wajen ƙin tsaba umurni. "Shikenan zauna ai kabari ko gaisawane mayi ko yayansa yakubu yafaɗi haka kaman bega yanda kanin nasa yaruɗe ba,sai sannan ya maida hankalinsa ga waƴanda suke zazzaune a falon take wani irin kunya ta lulluɓesa dan rabon daya yaje garinsu ziyara koya kirasu ta wayane yaji lafiyan harya manta. Ƙasa yayi da kansa mai babban riga yasoma gaisarwa sannan yaya yakubu da yaya bara'atu nafi'u da ma'ruf shima suka gaisheshi ruwa mai sanyi da juice mai sanyi Ammi ta gabatar masa beyi musu ba yakuwa sha sosai fiye da rabi sannan ya ajiye kallonsa Malam mai babban riga yayi ya gyara zaman sa dayau yace"badamasi³sau nawa nakira sunan ka? "Sau uku baffa ya amsa masa,gyaɗa kansa yayi ya cigaba da cewa yaushe rabonka da zuwa dubomu ko waya? Shiru yayi yakasa amsa masa da tambayan sai hakuri dayaci gaba da badawa"a'a riƙe hakurin ka ai mutum idan Allah ya ɗaukakashi gani yake ƴan uwa da abokan arziki da basuda shi ba ajin sa ba yanxu ya wuce sanin. Kagode Allah daya baka mace tagari mai son zumunci badan ita ba da mun daɗe da mancewa da munada wani ɗa,amma Allah yabaka mace wacce take tsaye kai da fata dan ganin wannan zumuncin namu be ruguje ba,dan duk wani abu kama daga bikin aure suna ko mutuwa tana zuwa wani bin da yaran baki ɗaya wani bin kuma takanyi mana aike ko suje da ƴan uwata bata taɓa wofintar da duk wani abu namu ba,ko wannan zuwan muzone dominta da ɗanmu Ahmadu bawai saboda kai nayi tattaki daga kazaure zuwa nan kano ba,sai ya dan tsahirta. "Aure kuma anɗaura bamu da hurumin raba abunda Allah ya hada dan bamusan abunda Allah yaɓoye cikinta na alheri ba,yaya yakubu ne ke wannan magana. "Ai wallahi kaman yanda matar uban gidan naka take kurin sunfi karfin kishiya to mu kuma zamu nuna mata cewa sunnan ma'aiki mukebi, faɗin(Allah subuhanahu wata alah)cewa ku aura daga biyu uku hudu idan ko bazaku iyayin adalci ba ku auri ɗaya,to danmu adaline da yardan Allah aurene anyi ba fashi saide idan mutum ze mutu dan baƙin ciki ya mutu. Wannan magana ta yaya bara'atu kaman ta watsa masa tafashesshen ruwa haka yake jinsa,shi kaɗai yasan irin tashin hankali dayake shirin fuskanta dakuma tarin kalubabe dake tunkarosa. Shide Alh badamasi banda hakuri ba abunda yake badawa saida nafi'u kaninsa da ma'aruf suka saka baki wajen bawa mai babban riga hakuri da yaya yakubu sannan ya hakura ƙarshe nasiha yashiga yimasa mai ratsa jiki cikin hikima da wayo dakuma dabara irin tasu ta manya,kwarai jikin Alh badamasi yayi laushi dajin yanda mai babban riga yake yi masa nasiha kalma bisa kalma harafi bisa harafi ba wani hargowa ko ɗaga hankali,karshe yasake jaddada masa da kula da zumunci sannan ya daura da cewa masa"karka shiga hurumin da banaka ba,bamusan abunda Allah yaɓoye na alheri cikin wannan auren ba dan haka karmuzama masu ɓata abunda Allah yahaɗa Allah yayi muku albarka ma'arufa kikara hakuri kuma koshi beje kaimana ziyara ba ke karki bar wannan zumunci Allah yanason masu sada zumunci da masu yawan yin alheri. "Ina shaa Allah malam bazamu taɓa barin kuba aikune madubin dubawan mu baki ɗaya,sannan dan Allah malam ina neman alfarma abar su Inna delu suzo mana wannan karon ranan asabar kaman yanda aka saka shine ranan ɗaurin auren Ahmad da basma sannan kuma tarewar ita ɗayan ma. Murmushi yayi irin tasu ta manya yace"ai ma'arufa kinfi karfi haka duk ma zasu zo harma da waƴanda baki nema ba,ai koni banzo ba yakuba zasu dawo dasauran yan uwa,ai kosu waƴanda suke masa ganin bashi da ƴan uwa zasu ganema idonsu shiɗin dan dangine gaba da baya dan ya wofinta dasu na. Mutum idan ba rashin hankali ba kana tsaye da kafafunka mutum yazo rana tsaƙa yaraɓeka amma yace shine wanda ze juyaka katsaya kana rawan jiki baka da kataɓus akan komai sai yanda akai dakai,shide Alh badamasi kansa a kasa fatansa kawai kowa yatafi yabarsu yasamu zazzagema Ammi jakar tsaɓa kanta. ALHAJI SUNUSi Lokacin da Basma ke kiran wayan sa shikuma daidai sannan yana wani ɗaki yana ganawa da shugaban su bayan sun gama aikata masha'arsu(wa'iyazu billah Allah yakiyashe mu)dan neman duniyarsa goge jikin sa yayi da wani farin kwalle shima Alhaji sunusi yagoge duburansa a tare suka jefa kwallen tsumman cikin wani tukunyar kasa dake gabansu wuta naci aciki,rufe idon su sukai suna karanta wani dalamirai na tsafi can wutan ta tashi sama kaman an zuba mata fetur ciki a tare suka zabura cike da fargaba shugaban ya dubi Alha sunusi yace"matsala ta samu andaura auren surukinka da wata yarinya muddin wannan yarinyar tana cikin rayuwar sa bazamu taɓa samun yanda yamuke so ba,dan zata lalata mana komai namune akwai inuwan dake bibiyarta haryanzu bankai ga gane inuwar na waye ba. INUWA INUWA INUWA kawai yashiga maimaitawa kaman wani zararre sabon kamu yana cewa shugaba kode inuwar Ishak da nafi ke bibiyar rayuwata yake son hanani kaiwa ga nasara bayan nasan duk wani sharaɗin dodo nacika harfa mamata ka kwanta da ita tsawon kwana arba'in haka nabaka budurcin ƴata ɗaya tilo nabaku jinin ɗana abun kaunata haryau uwarsa batasan baya duniya ba,ya zauce sai surutai yake"nutsu ka saurara wani murya ne yaratsa inda suke"yi maza kasamo mana jinin budurcin wannan amaryar surukinnaka a daren da aka kaimasa ita,idan karasa darenta na farko kanada dama harzu daren kwana uku dazatayi a ɗakin mijin ta maza tafi kuma cikin dare dodo yanason kakawo masa ƴarka na tsawon kwana uku dan cikan burin ka na har abada.   Alkalami️ Yafi takobi⚔️ ALLAH YASA MUDACE [5/30, 4:11 PM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 49 Hankalin Alh sunusi yayi ƙololuwar tashi dajin abunda dodon yanema a wajen dan haka kai tsaye yace"a gafarceni dodo wannan abunda kanema gareni yayi mun tsauri banajin wannan karon zan kawo ƴata nan duba da yanda aurenta ya gabato banaso tasamu matsala a gidan aurenta bason tayi kuka dani daga baya banason iyalaina suyi Allah wadai dani bazan iya ba bazan iya ba. "Tashi kage ka'aiwatar da abunda muka saaka bama son gardama ko musu anan haka jiki ba ƙwari yafito daga wajen yana maida tufafin jikinsa daya cire sannan yanufi motar sa driver ya jashi suka fara tafiya sunyi tafiya madan nisa harsun fara shiga cikin gari yasa baƙo driver cike da tsoro da yanayin na uban gidan nasa yau yace"ranka ya daɗe Basma takira wayanka tunɗazu"uhmmm kawai yace kaman bazece komai ba sai kuma yace mai tace tana bukata?"ranka yadaɗe ban ɗaga wayan ba yasake amsa masa. "Ok baƙo kiramun ita yanzu muji mai yake faruwa dan bata kirana a waya haka kawai,kiranta baƙo driver yayi saida yaji anɗaga sannan yamiƙa wayan wa Alh shikuma ya cigaba da tuƙi,bansan de abunda tace masa ba saide yanda Alh sunusi ya amsa cike da ƙaraji zai tambatar maka da antaɓa ƴar lelensa,yana kashe wayan yace"baƙo kaini company wajen Ahmad harni zama rashin mutunci auta taga abu tanaso ace bazata samu ba,me amfanin dukiyata idan har bazan iya siyamata duk abunda takeso ba haka yayi ta bambamin sa. Kusan motarta data daddynta a tare suka shiga harabar company daidai kuma Ahmad da khalid da wasu ɗaiɗaiku sun fito daga masallaci sallar la'asar,khalid ne ya hangosu yana nunawa Ahmad cike da son zolayarsa yace"gafa Amaryarka da surukinka kode takasa hakura sai an ɗaurane yak....dukan wasa Ahmad din yakai masa yana dariya tare da kaucewa wannan ya hanashi karasa maganan nasa,nufosu sukai Alh sunusi na rungume da basma jikin sa itako sai shagwaɓa take zuba masa harda hawayenta abunda yake sake dagula ma daddyn lissafi ganin hawayenta,har kasa suka zube suka gaidashi. Amsa musu yayi adaƙile"daddy da kanka da waya kai basai kazo ba khalid yayi maganan da ƴawun Ahmad harara ya bankawa khalid ɗin yana cewa"kuna ganin girman mutun ne daza kiraku ta waya ace kuyi kuyi"sai hakuri daddy yanzun ma khalid dinne yayi magana Ahmad kan tsaye yayi ya goyi hannunsa a ƙirjinsa yana kallon wani bangaren daban hakan dayayi saiya sake tunzura Alh sunusi"ina kayan suke? "Wasu kaya kuma ranka yadaɗe?khalid ya tambaya cike da rashin sanin kan maganan. "wai kai menaka sai ana magana kai tasaka baki kaman an kasa dakai basma ke cewa khalid hakan"yi hakuri Amarya yafaɗa yana ɗan bubbuga kafaɗa Ahmad tare da lumshe idonsa yasa budewa alaman rarrashi,lips ɗinsa ya ciza da karfi yana warr da idonsa wucesu khalid yayi dan barmusu wajen. Hango Aisha tayi da laila dake shigowa ciki da alama suma ɗin daga masallacin suke suna ƴar hirarsu suna takawa sannu a hankali suna ƴar dariyar da alama sunajin dadin zancen dasuke"yauwa daddy ga yarinyar can itace wacce tayi ɗinki kuma daddy har agabansa takira sunan ka tsirara amma be tsawatar mata ba ta faɗa tana kumbura fuska tanuna ahmad ɗin da hannu dayayi kaman bashi a wajen. "Yakuwa ze tsawatar da ubansa badamasi takira ai da yayi magana,da karfi ya rintse idon sa yana danƙule hannunsa. "Keeee ƴar matsiyata mai wanki zo nan daidai sanda su Aisha sukaxo zasu gifta ta gefensu su wuce tafaɗi hakan,ja tayi ta tsaya batare da tace da ita komai ba. Kallon ido cikin ido sukaiwa juna sai itace taji bazata iya juran kallon ƙwayar idon Aishan ba ta janye nata da sauri danjin yanda tsigar jikinta nawanj mimmiƙewa ga wani abu mai kama da tsoro na ɗarsu a zuciyanta. "Kece? Batayi magana ko tanuna tasan da ita yake ba,wai ko kurmace?yasake tambayarta a karo na biyu yanzun ma shiru tamasa bata tamƙaba. "Ke mara mutunci ƴar matsiyata ana miki magana kinyi shiru,murmushin gefen baki ta mata sannan ta bude idon fes kanta tace"kinsan anmun tarbiya da zan tsaya ina musayar ƴawu da manya bane shiyasa kece inaga zan kusa yi dake tunda tazarar dake tsakani na dake bawani abun azo a gani bane. A ƙufule Basma ta maida kallon ta kan daddyn nata tace"kagani ko daddy? "Eh nagani yace yana sake kallon Aisha sosai da taki kallon sa koda sau ɗayane yace"kee wakike da suna komade yane inason yanzun nan kije ki ɗauko kayan da tagani tace tanaso ko nawane inde harka ta kuɗine zanbiya dan farin cikin ƴata,mai amfanin neman kuɗin idan bazan sama mata dukkan abunda take so ba dashi. Yakare maganan sa yana sake jawo basma zuwa jikin sa ita ko sai sake shegewa jikin sa take tana ta taɓara ita ala dole shagwaɓaɓɓiya. "Yi hakuri malam tafaɗa da muryarta mai sanyi dakuma daɗin sauraro. "Malam malam kuma yasake maimaita sunan. "Oh Alhaji tasake faɗa ganin kaman ya raina malam dinɗa takirashi dashi,tana dan dafa goshinta alaman mantuwa. Jinjina mata kai kawai yayi amma ransa fal mamaki yake shida ko maza ƴan uwasa basa iya musamasa idan yafaɗi magana idan ko yace tanason wani abun jiki na rawa ake masa,ita wannan ɗin wacece? Suwaye iyayenta? Dole yana son sanin wani abu daga gareta,kaf rayuwansa mutum ɗaya ke iya tsayuwa gabansa ya kallesa ido cikin ido yafaɗi abunda ya gadama kuma shiɗima yanajin yagama da rayuwan sa to ita wannan yarinya wacece,tunani dayake tuntuni kenan har saida Basma ta taɓashi sannan ya dawo daidai. Inda Aisha ke cewa dashi"bafa komaine kuɗi ke iya saya makaba,akwai abunda koda kudin ka saida rabonka kafin ka mallaka yana dakyau yaran masu kuɗi nan yawancin su susan da haka,dan haka nima anawa ɓangaren hakane koda kuɗinku...sai kuma tayi shiru cike da jin haushi Alh sunusi ya hayayyaƙo kaman ze daketa dan haushi yace"zan baki 5m nasan ba kuɗin kayanki bane kawai zan bakine dan kije ki rage zafin talauci dake damunku keda iyayenki da yawanku dama talakawa idan talauci yamuku ƙatutu ganin kuna samun dama kaɗan kan masa hali zaku so nuna isarku. Hmmm"Alh kenan banso kai da kanka da girmaka kafaɗi haka ba,amma amsan bazata gagara ba,riga de mallakinane kuma nike da ikon sai dawa ko bada kyautarsa ko kuma na kyakketa nazubar duk yana...."ke dakata ko ubanki be isa ja da niba balle ke wannan umurni nake baki kai tsaye ba wai dogon surutu ba kuɗin kikeso zabaki jeki kawo kayan yanzu yafaɗa cike da bada umurni yana sake murtuƙe fuska kama hadarin gabas yanda fuskar tasa takoma lokaci ɗaya duk wani dake waje tsaye saida ya tsorata amma abun mamaki Aisha ko ako aƙwalarta dan addu'an neman tsari kawai take cikin zuciyarta fal tsorone kaman tasaki gudawa dan tsoro amma bazaka taɓa gane haka akan fuskarta ba. Hannu ta haɗa waje ɗaya alaman ban hakuri tace"anty basma wannan abu tsakaninmu ne yo mai nasa mahaifinki aciki gashi kinsa namasa rashin kunya,rigane kingani kinaso saide kalma guɗa daya takk shine ya hana na mallaka miki wannan riga kuma ba abunda ze sa kisame sa. "Zaki kuwa rasa wani naki yafaɗa cikin fushi"na daɗe da rasasu saide idan karan kaina zan rasa,zuwa yanzu kuwa tafara tsorata da Alh sunusin. Saurin ɗagowa shima Ahmad din yayi dan jin abunda Alh sunusin ya faɗa akan riga zarasa rai yafaɗa azuciyan sa amna azahiri sai cewa yayi"dan Allah daddy ayi hakuri abun bekai ga haka ba"ya kai mana MY kabani mamaki tunɗazu ka tsaya shiru kaman bakai a wajen ƴar mitsitsiyar yarinyar nan daddy na faɗi tana faɗi saikace sa'anta dolene a koya mata hankali,wani mugun kallo ta watsa mata daya sata yin shiru tana kunkuni...... Alkalami️ Yafi takobi ⚔️ ALLAH YASA MUDACE [6/4, 7:35 PM] Xeenat: *AURE WUCIN GADI* CHAPTER 50 Jan hannunta laila tayi itako sai wani turjewa take cike da jarumtar da tanemo ta yafawa kanta amma ƙasan ranta fal tsorone dakuma fargaba dan cikin ta hautsina mata yake kaman zata saki zawo sabida tsorata da tayi da kalman wannan Alhajin na rashin imani. Suna kaiwa bayan wasu motoci tasaki wani irin mahaukacin ajiyar zuciya tana dafe da setin ƙirjinta dake mata wani irin lugude sai numfashin wahala da take saukewa, akai akai saida ta seta nutsuwarta sannan ta ɗago da dubanta ga laila tace"kinceceni wallahi dakyar nasha. Dariya laila ta fashe dashi saida tayi harda riƙe cikita tana mai nuna fuskar Aisha tace"kalli fuskarki gaki da tsoro amma bakin ki baya mutuwa nide abunda kawai zance dake ki kula ba ko ina zakina sake baki kina magana ba,irinsu Alh sunusi basu da imani wallahi zasu iya iyin komai saboda farin cikin su data iyalansu. Ahmad dan sussunar da kansa yayi cike da ladabi yace"dan Allah daddy kai hakuri akwai yarinta tattare da ita be dace kaida kake babba kabiye mata ba,dan biyematan da kaine yabata daman sakin maganganu haka batare da ta tauna abunda zata faɗi ko kula da kaiɗin babba bane ba,daddy kasan sha'anin ƙuruciya"kai dallah rufama mutane baki anfaɗa maka ƙuruciya haukace toh nabi ƙuruciya dagudu ba wando nace nabi ƙuruciya dagudu ba wando tuntuni yariya tana ta zuba iya shegenta bakai magana ba sai yanzu zaka wani kashe murya kaman karuwa taso damfara kana wanu cewa sha'anin kuruciya. To wallahi muddin bata farantawa shalelena rai ba kuwa itama bazata taɓa samun kwanciyar hankali ba,kwanciyar hankalin ta ɗayane kawai takawo kayan sannan tazo ta bani hakuri yanzun nan,ya kare magana yana huci kaman wani zaki. "eh wallahi daddy sai takawo kayan nan kuma ta gogemun takalmi da hijabin ta sannan ta duƙa har kasa tabani hakuri basmace ke wannan magana shiko daddyn nata sai wani washe baki yake kaman gonan auduga,karshe Ahmad tafiya yayi ya barsu tsaye a wajen dan kansa har sara masa yake dan kwata kwata ya tsani tashin hankali da hayaniya arayuwar sa,ko meetin sukeyi da ma'aikata ko abokan kasuwancin sa yawanci khalid ke wakiltansa shike gudanar da komai. Taku yasoma yi dan barin wajen cike da izza da ƙasaita kai kace jinin sarautane shiɗin"kai Ahmad Ahmad ina zaka baka kirata tazo ba,da karfi Alh sunusi yake kiran sunan sa yana masa magana dan ganin kaman yanufi parkin lot,bema nuna yaji shi yayi tafiyarsa yana isa wajen yabude motarsa ze shiga sai ya hangota duƙe dafe da kirjinta fasa bude motan yayi yanufi inda suke yana zuwa be tsaya yimata magana ba kawai ya damƙi hannunta yanufi bakin motarsa yabude yatura ta ciki da karfi sannan shima ya zagaya yashiga mazaunin driver key yama motan sannan ya figeta da wani irin karfi ya bar wajen wani irin tsorone yasake kama Aisha ji take kaman ta saki futsari awando tawani waro ido cikin in ina tasoma cewa"da Al lah kamun rai karage gudun nan dani wannan gudun wallahi banshirya mutuwa ba,akwai buruka da yawa da nakeson cikawa kafin mutuwa ta. Banza yamata saima kara gudun motar daya sake duk inda motar su ta gilma sai mutane sun bisa da kallo masu abun hawa kan saide sune suke kauce masa hanya. Ganin hakan da Aisha tayi sai yasake tsoratata dan Aisha duk jarumtarta da rashin bari takwanan ta amma akwi tsoro dan ko adaidaita ta hau idan taga driver na gudu sai tayi masa magana tayi yanda yaraje gudun dan ita anata ɗan ƙaramin tunanin duk wani hatsari dake faruwa gani take gangancin driver ke jawowa da suna kula da yin tuƙi cikin nutsuwa da hakan bazata yawaita faruwa. HAJ MARIYA tunda jiya dasukayi maganan nan da ƙawarta Haj balkisu hankalinta ba akwance yake ba,dan haka yau koda Alh sunusi yafita daga gidan ita ma shiryawa tayi ta nufi gidan kawartata dan tun daga bakin ƙofan shiga falon take ta ƙwaɗa sallama mai aikin gidan ne ta amsa mata tana mai bata hanya ta wuce a wulakance take kallon matar"hajiya fa?Tayi tambaya kaman wacce akace dole sai tawa matar magana. "Tana ciki ƙaraso mana hajiya kya tsaya anan matar ke magana cike da girmamawa kaman bataga irin kallon da hajiya mariyan ke binta dashi ba. "A'a lale marhabin kece tafe da sanyin safiyar nan shigo shigo da alama de akwai labari?hajia balkisu kenan dake zaune a falo hannunta riƙe da jarida take wannan magana. Dan sakin fuska hajia mariya tayi tana ƙarasa shiga ciki nan suka shiga gaisawa inda hajia mariya ta kalli ƙawartata tace"ba dole kinganin nan ai tunda mukai maganar nan ta jiya hankalina ba aƙwance yake ba,kece ina can nasaki baki ina bacci ina baza izzar ƙarya inci in zubda masai ashe ku kuna nan kunama kanku tanadi kun barni baki hangame. Dariya hajia balki ta kwashe mata dashi sannan tace"kai kawata ashede kanki na jaa yo aina dauka duk shekarun nan da mukai dake keɗin ƴar hannuce bansan ba haka kike ba ai da tuni munɗaura ki a network yanzu ma bata ɓaci ba inde kin shirya cin duniyarki da tsinke bismillah kafin nan zan gabatar miki da wata ƙungiya da muke da ita. "Ƙungiya kuma? Tafaɗa kaman maijin tsoro,cikin ko in kula da yanayin da taga hajia mariyar tashiga na shock tace"eh amma fa bata komai bace ta huce taƙaicine muna da ƴan shawalwalan ƴan mata da samari domin huce haushin ragon miji,ajiyar zuciya haj mariya ta sauke jin abunda ƙawartata ke fadi tace"yanzude ba wannan ba ai sai kanada yan canji zakaji daɗin huce haushin yande faɗamun hanya mafi sauki da zanbi dan ganin nima na yagi rabona kafin maganan wannan boka ta tabbata kinga ƙwara na tsira da wani abun nima dan gudun gori. Aisha duk tasha jinin jikinta saima kanta data saka tsakanin cinyarta tasaki kuka bata yarda ta ɗago koda wasa ba amma tanajin yanda yake sharara gudu da kakkaucewa ababen hawa dakuma yawan horn dayake hakan na tabbatar mata da cewa haryanzun gudu yake,can aji yaci wata mahaukaciyar burki dasata furta"innalillahi shikenan yakashemu Allah yajiƙaina. Maganar tata yaso bashi dariya duk da yanayin fushi dayake ciki amma ya danne bata ankara ba,taji an fuzgota da karfi har hannunta yana buguwa da murfin motan"shikenan wayyo Allah Anna gawani nan ze kashe miki ni takare magana cikin gunjin kuka. Tsawa daya daka mata shiya nitsar da ita"dama kina da tsoro kika tsaya kinawa mutane rashin kunya ko,ɗan shiru yayi ganin de har yanzun kuka take kuma tamaƙi bude idonta ta kallesa. A hasalale ya cigaba da cewa ba jininki rashin kunya ba,to kuwa zaki mutu ba tare da burukan naki son cika ba wawuyar yarinya dubeki mitsitsiya dake amma cikinki fal rashin kunya to kuwa inde irin su Alh sunusi zaki taɓa kuwa kishiryama mutuwa,yana kare faɗin haka yayi shige warsa motan ya baɗeta da ƙura,a rikice ta buɗe idonta ganinta ƙofan gida yasata sauke ajiyar zuciya tana murguɗa masa baki da cewa"oho de nasan kaji haushi daga kai har ita matar da zaka aura da ɗan tsohu wai harda wani cewa yi maza kije ki dauko kayan nan ki kawo yanzu ta kare faɗa tayi shigewarta cikin gida tana sake riƙe rigar da kyau ashe dama ɗamara tasha da rigan da zasu yin sallah. Dariya tasake kwashewa dashi kamar wata mahaukaciya sabon kamu taƙara da cewa daman kaine Alh sunusin makashin iyayena to kashirya ma uƙubarka dan ina nan tafe gareka. ALH SUNUSI Bayan barin Ahmad m'aikata kiran Alh badamasi yayi cike da fushi yana dagawa yashiga magana"yanzu badamasi wai har kamata yaron nan ze wulakanta ya shanyamu a rana? Alh badamasi jin abunda abokin nasa ke faɗi yamiƙe tsaye cikin rawar murya data jiki yace"wai wani yaro kake magana akaine? Alh dan Allah yi hakuri kamun bayani dalla dallah. "Kabari kawai badamasi raina aɓace yake zucitarta sai tafarfasa yakemun yanzu kaman Ahmad wai shalele taga wani ɗinkin kaya daya ɗauki hankalinta tace tanaso amma yamurza toƙa a idon sa yanuna bema santa da ba. "Shi Ahmad ɗinne yama haka Alh badamasi ya tambaya daga ɗaya ɓangaren"kwarai kuwa karya zanma ne badamasi kakira sheɗanin ɗan naka kaji inda yake"yanzu kuwa yafaɗa tana kashe wayan yashiga kiran Ahmad ɗin daya sauke Aisha yana hanyarsa ta komawa gida. Saida yamasa kira uku sannan ya danna bluetooth dake maƙale a kunne sa dukda besan waye mai kiran nasa ba. "Asslamu alaikum yafaɗa madadin amsa masa sallamar da yayi saijin saukar manyan boma bomai da mahaifin nasa keyi sauke masa,magana ta karshe inaso kakoma yanzu kayi masa duk abunda yake bukata inde kanason ganin farin cikina yana kaiwa karshe betsaya jiran jin ta bakin Ahmad ɗin ba yakashe wayansa yana sauke numfashi dacewa yaro anama gata amma baka gani. Ahmad kuwa cike da ɓacin rai yakira wayan Basma wacce tacika tayi fam kaman zata fashe dan fushi ganin kiran nasa ta juya ta kalli daddyn nata dake tsaye yahaɗa zufa sai gogewa yaki da hancky tace"laa daddy kalli yakirani tafaɗa tana nuna masa scream ɗin wayan nata"dauka muji mai kuma zaice mana haɗa fuska tayi taɗaga madadi bata hakuri da tayi tsammani ko rarrashinta daga gareshi saɓanin haka tajj dan tana ɗaga waya yace"kiyi maza kija mahaifinki kibar wajen kafin nazo nasameki idan kuma muna abu kika sake saka iyayenmu ciki abun baze mana daɗi ba,idan ke bakisan girma da ƙimar naki iyayen ba ninasan nawa dan haka......sai kitt taji alaman ankashe waya sakato tayi tana karewa wayan kallon ganin yanda daddyn nata ya zubamata idon dan son jin meke faruwa sai cewa tayi"daddy yace mutafi gida kawai"dan abu kazan ubansa ni yaron nan ze nunawa duniyanci to wallahi yama ubansa badamasi dan ko shi daya kawoshi duniya be isa musamun magana ko na faɗi abu yaƙi yi ba to wallahi yama ubansa dan ni daidai nake da ubansa yi hakuri shalele mutafi kina zaune ubansa ze sakosa a gaba har gida zezo yabaki hakuri idan ko beyi ba to sunana ba sunusi ba...       ALLAH YASA MUDACE [6/6, 3:57 PM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 51 "Ransane yayi mugun ɓaci da abunda Ahmad ɗin yayi masa dama gashi cikin ɓacin rai yake yauɗin tunda yabaro wajen shugaba,laluɓen wayansa yasake yakira Alh badamasi dashima yake zaune zaman jiran jin shin Ahmad din zebi umurnin sa ya aiwatar da abunda ya umurce shi yayi koko bazeyi ba? Kiran yashiga wayan sa saurin dagawa yayi tunma kafin Alh sunusi yayi magana yashiga bashi hakuri yana cewa"wannan takadarin yaron beje ko Alh amma kayi hakuri kabarni da shi anjima da kaina zan tasosa gaba nakawo shi har gidan naka amasa afuwa kasan sha'anin yaran zamani yarane ba duk abunda mutum keso sukeyi ba. Yanda Alh badamasi ya marairaici murya da kaskan da kai kaman ɗalibi yama malaminsa lefi zai zanesa yana bada hakuri haka shima yayi abun gwanin tausayi gwanin ban haushi kai kace bashine Alh sunusin yake nema daga gareshi ba tsaban yanda ya asirce shi. HAJ MARIYA "Sauke numfashi tayi bayan ta gama sauraron ƙawartata tace"yanzude kawata duka ba wannan ba wace hanyace kike ganin zan samu natatsi Alh rabona cikin ruwan sanyi. "Yanzude magana zaki masa zaki fara kasuwanci sarin kaya daga dubai china mukuma tsoffin yan kasuwa zamu samo miki da customers kinga daga haka sai kifara zaran rabonki idan yashigo da ƴaƴan banki cikin gida,ke ba ruwanki da nau'in kuɗi bata kasarnan bane kawai zara zakiyi"anƴa kawata kina ganin bazai zargeni ba,ta faɗa cike da tsoro. Murmushi Haj balki ta sakar mata tace"kingani ko wannan tsoron naki bazai taɓa bakirinki kiyi abun arziki ba,jeki kawai duk sanda kika shiryawa neman nakanki sai kisake zuwa muyi zama na musamman idan takamama muje dake can ƙungiya inyaso ƙyaji ta bakin sauran manya mata idan kin shirya zama babbar mace wacce zadama dake to sai taware mata hannunta idan ko baki shiryama tafiyan nan shikenan sai kiyi ta zama kinashan Ac ki ci zaji kisha juice ki juye a masai wannan shine ribarki. FAISAL "Wai ya ake cikine haryanzu yau tsawon kwana uku da ɓatan ƴan ta addannan waƴan da hukuma ke nema ruwa a jallo amma ace waƴansu zasu samu nasanar sacesu abun kunyane garemu baki ɗaya mene amfanin mu? "Sorry muna iya bakin ƙoƙarin mu dan ganin munsamo bakin zare"a hakan kake wani cewa kuna kokari ina ƙokarin take anan?faisal har tsawon wani lokaci ya daukeka dan ganin ka kamo ɗaya daga cikin su shin kayine?kamal kenan shike magana cike da fushi dan yaso abashi wannan case amma aka hanashi aka bawa faisal shisa yasaka yaranshi cikin tawagan faisal din batare dashi faisal ɗin yasani ba suke kawo masa dukkan wani mutsin faisal gefe guda kuma yahaɗa kai da ƴan ta'addan shike basu bayanai har suke samun zarran tsallake duk wani tarko da ake ɗana musu. Murmushi mai ciwo faisal yayi ba tare da yakalli sashin da kamal din ketsaye ba yafara magana kaman haka"yallaɓe muda muke da bara gurbi cikin mu masu fitar da duk wani motsinmu suna saidawa ƴan ta'adda akan farashi mai sauki tayaya kake ganin zamuci nasara akansu har mukai ga kamesu bana zaton haka ko gaba dan cikin mu masu sanye da uniform waƴanda sukai rantsuwar kare rayuka da dukiyoyin al'umman ƙasa amma suke daƙile layukan wayoyin mu bamu isa muyi magana koda ta sirrine da iyayen mu ko abokan aikinmu ba face sai waƴan nan ƴan ta'addan sunji komai. Kaima kanka kasan nasaran mu bazata samu ba inde a hakan zamuyi tafiyar harsai mun wanke dauɗan dake tattare damu,sannan maganan sace su LION a gaskiya ni banyarda sace su akai ba kawai anawa tunanin gani nake kaman sun ɓoye kansune saboda sunason wasa da hankulan ƴan sanda nide a nawa ganin kawai rabuwa zamuyi da su basai mun sha wahalan cewa sai mun nemo suba ko sai lalle munsan inda suke ko wayan da sukai wannan aikin ba,kawai mu maida hankulan mu kan wasu aiyukan daban masu mahimmanci. Cike da gamsuwa da bayanan faisal din IG yajinjina kai shiko kamal kwafa yayi ganin ba wanda ya kula da zance sa shide haka kawai yaji yana zargin faisal akan bacewar su Lion ɗin tunda manyansu irin su Alh shehu da Alh sunusi sunnun lalle lalle yabinciko masa wake da hannu cikin kame musu yara kuma abun mamaki kosu ƴan rahoton nasa basusan da wannan zance ba to waye da alhakin wannan aikin. Ahmad bayan yagama waya da basma kashe wayan nasa yayi baki ɗaya yakuma juya akalan tukin nasa zuwa wani gidansa dayake sauke baƙi gidane ɗan madaidaici kuma ginin gidan ya tsaru dan wani tafiya da yayi turkiya acan yasayi zanen gidan,horn yayi mai gadi ya bude masa kofa saida ya tsaya suka gaisa da maigadin sanna yanufi ciki ya parke motan direct falon yashiga yasamu komai tsaf bawani ƙura tunda akwai mai shara wato matar mai gadin ita ke wannan aiki kuma yake biyansu albashi ita da mijin nata. Saman kugera yakwanta hutu yake buƙata na ɗan wani lokaci cire rigar jikin sa yayi yamiƙe madadin hutun da yake bukata gakuma kansa sai sara masayake kaman yarabe gida biyu,sai kawai yashiga tunani wai yama akai daddynsa baya tsayawa koda yaushe matukar abu ya danganci Alh sunusi yayi tunani ko yabi abun a hankali ne sai kaganshi duk yasusuce kaga kaman yayi lossin main dinsa,dan ko Amminsa bayajin daddyn nasa yana ɗagawa ƙafa inde abu yashafi wannan mutuminne. Wai yaushe masukayi irin wannan sabo haka idan be manta ba shekaru biyar da suka wuce suka haɗu da shi da matarsa dakuma ƴarsa a airport sunje taro ƴartasu wato basma shima kuma Ammin sa da daddyn sai faisal khalid da autar Ammi wato saima dasukaje tarɓansa nan suka haɗu sanadiyan musayan jaka dasukai da ita basman. AISHA yanda take tasakin murmushi ita kaɗai abun ma gwanin ban dariya Anty malika ce tafito daga cikin falo zata fita motartake kiciniyar budewa ganinta yasata dan tsayuwa tana tsura mata ido Anty hajia ma data biyo bayan malikan dan tare zasu fita kallon ta ta tsayayi ganin ma kaman bata gansu ba,zunguranta tayi tace"wai ke lafiyanki kuwa sai sakin murmushi kike ke ɗaya? "Anty hajia inaga kode sun daidaita da broo ne irin wannan murmushi haka Anty malikace ta kare da faɗin haka bayan Anty hajiya tayi tambayarta. Dan sosa kanta tayi tana tura baki tace"Anty hajia kinga Anty malika ko?"eh to nima de tambayan da nakeson yi miki kenan,lumshe idonta tayi tasake budewa tace Anty hajiya zanbiku inda zakuje"a'a ba inda zaki bimu sai kintambaya an barki tukunna. "Wazan tamvaya kuma bayan gaki tafaɗa cikin rashin fahinta"Ahmad zaki tambaya tunda yanada igiyar sa uku a kanki Anty malika ta bata amsa da hakan. Cinno bakinta tasakeyi tace inde sai na tambayi wancan ɗan uwan naki zanfita to na hakura mema akai akai AUREN WUCIN gadi da zabashi wannan mahimmanci ai idan kinji ana neman izini sai auren so da kauna ba auren haɗi haɗinma irin namu da maishi be wani daukeshi da mahimmanci ba. Sai kuma ta juya wajen Anty hajiya tace"wato yau na fusata wani fusataccene tsuntsune shisa nake jina cikin wani irin farin ciki tawani ware hannunta tana tsalle sake baki sukai su dukkansu biyu suna kallonta garin tsala tsalanta rigan data ɗaura acikinta yasince ya fadi ƙasa duƙawa tayi ta dauka tana warewa sai kuma komai ta tuna saita kwashe da dariya tana cewa wannan rigar aradu ƙwalelenki.......     ALLAH YASA MUDACE [6/9, 10:17 PM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 52 "Waini keda waye? Anty hajia ta tambaya ganin yanda take ta fara'a Anty malika kuwa warce rigan tayi ta warware tana kare masa kallo. "Hmmm Anty hajia yau ina cikin farin ciki na fusata wani fusataccen mutum daya ɗauka dukiya zata iya saya masa komai saide nanu masa cewa ba komaine zaka iya mallaka saboda kana da dukiya ba. "Wow wow wow Anty malika keta faɗi sanda ta warware rigar ta ƙare masa kallo nan take taciro wayanta cikin jakanta tashiga duba screenshot da ƙawarta ta tura mata ɗazu datake faɗa mata yana trendin a media yau, cikin zumuɗi takai dubanta ga Aisha tace"kai sis aina kika samu wannan kayan daya kawo wuta a media yau ɗin nan kinga ruwan liking da comment kuwa cikin abunda be wuce awa ɗaya da daurasa ba hmmm kice nice first person da zansa wannan riga ranan dining broz Ahmad nasan za'ayi karya awajen dan harkace ta big big girl tafada tana ƴar dariya. Warce kayanta tayi daga hannun Anty malika dake ta zuba kaman bishiyar kanya tace"tabb ai kuwa Anty malika saide kiyi hakuri dan bakisan irin gurmin da na haɗa yanzu bane nan tashiga maida masu yanda suka da basma da mahaifinta dakuma gargaɗinta dayayi dakuma kawota gida dayanzu Ahmad din yayi. Ajiyar zuciya suka sauke dukkan su kusan a tare salati Anty hajia tayi tasanar da ubangiji tana tafa hannu tace"ai Alhaji sunusi inde akan ƴaƴan sane ba zance ba zaiyi haka ba zeyima fin haka dan wallahi watannin baya bakiga wani takadarin ɗansa daya biyo ummu sa'ad ƙanwace ga Ahmad gida wai yana sonta ba,yaya ma'arufa tayi faɗan tayi lallamin amma a banza daga karshe hadashi tayi da Ahmad yamasa jan ido sannan ya ɗauke kafarsa da zuwa gidan daga baya kuma mukaji labarin wai an fiddashi kasar wajeyin karatu niko nace umma ta gaida assha yaro ko anan ma ya lafiyan kura balle kuma anbude masa hannya,haka de Anty hajia yayi ta basu labari karshe ma sai Aishan ce tace"kode zaku fasa fitan mukoma daga ciki muci gaba da hiran mu naga kaman zefi armashi ko? Yanda takare maganan cikin zolaya yasa Anty malika kaimata dukan wasa tana cewa"oya mutum tashiga ciki tayi zaman yimana gadi kafin muzo aini wallahi nama gode Allah da mutum baze iya fita ko nan da can batare da yanemi izini ba wallahi kunnuwa nama sun futa da jin taƙulla taƙullan nan shima mai jan kunne yaje yanemi daidai shi. Ɓata fuska Aisha tayi tana kunkunni tayi shigewarta ciki tana cewa cikin ɗaga murya"ai wallahi duk bakin cikin mutum nida suhail mutu karaba takalmin kaza,dan wannan auren na dan uwanki na wucin gadi aini ban ɗauke sa abakin komai ba wallahi"kede kika sanda wannan amma mu namu auren waya faɗa miki na wuncin gadine ai daga nan gidan duniya har gidan aljannan mutum de yadena wani botsare mana dan kardaga baya mutum yaji kunya. Murguɗa mata baki tayi tana cewa"ana maganan zuman farar tsaka kinzo kina wani....."yi hakuri Aisha ɗiyata Anty hajiyace ta katseta dafaɗin rabu da wannan Antyn taki danma an musu alfarma idan ba hakaba su harsun isa takara da balarabe shiga ciki kiyi wanka kici abinci kafin mudawo cikin tsigar rarrashi Anty hajiya tayi maganan tana makawa Malika harara. Zumbura baki Aisha tayi tana cewa"wallahi Anty hajia kimata magana nide,gwalo anty malika tayi tana shiga mota ta barsu dan ita tasan aikin gama ya gama tunda an daura da sannu zaku so junan ku,magana take aciki ranta ita kaɗai. ALHAJI SUNUSI. Rayuwarsa ta ɓaci zuciyarsa tayi baƙi wani tukuƙin baƙin ciki kaman ya karsa wai yau shine aka samu wata ƴar mitsiyar yarinya ta tsaya a gabansa take faɗa masa abunda ranta yake so waye ubanta a garin nan shida ko maxa ƴan uwansa jira umurninsa kawai suke cikawa ne nasu cikin gaggawa amma amma sai kuma yayi ƙwafa da jan tsuka mai tsayi yana maida dubansa gefen titi"kaini Al hakk yace da drivern sa,shi kaɗai yasan irin tuƙuƙin bakin cikin da yake ji cikin ransa na gamida da abunda Ahmad ɗin yamasa harma gwara yarinyar dan yasan ƙila ita batasan kowaye shi ba,amma shi kumafa? Uban sane daidaini bashi karamin mara kunya ba,koda motar tasa da shiga cikin harabar company tunma kafin yafito daga cikin motan nasa Alhaji badamasi ya tunkaro sa yana tabashi hakuri kaman ze zube kasa dakyar da tsuɗin goshi ya hakura da sharadin dole sai yakawo masa Ahmad da yarinyar sun ba shalelen sa hakuri da sauri Alhaji badamasi ya amince da sharadin nasa nan yamasa rakiya yakoma mota tare da alkawarta ma daya koma gida ze tistsa ƙyeyar Ahmad yakaisa har can gidan yabasu hakuri kuma ya mallaka ma shalele rigar da ta bukata ko kuma rankowa ya ɓaci da haka suka rabu. Hajia mariya koda ta koma gida haka tashiga zarya dan neman mafita,dan kuwa tasan tabbas hajia balki gaskiya tafaɗa mata gwara ta yagi yabonta ashe mata suna can suna juya dala zuwa naira suna hawa jirgi daga wannan ƙasa zuwa wancan da sunan kasuwanci suna murza sitarin mota da sukaga dama amma ita anbarta da yawo da driver abun dubu goma bata iya tama kanta ba sai tayi karamar murya,ashe izzarta da mulkinta duka abanza tunda iya masu masu aikin gidanta take yiwa hamm manya mata suna can inda suke ashe duk wayewa da nake ganin inada ita ashe har yanzu ni baƙauyiya ce ina bara ta saɓuba bindiga a ruwa bara Alhaji yaxo tukunna ta faɗa a fili daidai basma tada fado falon kaman wacce aka jefo tayi cilli da takalmin dake kafarta sannan tayi jifa da jakar hannunta ta faɗa saman kugera tana sakin kuka maikarfi yaune rana ta farko a rayuwarta data taga wani abu takwallafa ranta akai kuma tagaza samun sa kuma har mahaifinta da take tutiya dashi kan komai ze iya sayamata matukar kuɗi ze saya sai gashi tanaji tana gani karon farko a rayuwa kaman wannan alfarin nata bazeyi mata amfani ba. "Ke wai lafiya kin wani shigowa mutane da kuka kode wanine ya mutu?tambayar da Hajiya mariya take mata kenan ba tare da rarrashi ko lallaɓata kaman yanda tasaba yi mata da ba. Kawai saita sake fashe mata da sabon kuka tana cewa"yanzu mummy kiganni cikin damuwa amma kigaza rarrashina"iko cewa hajia mariya yanxu ke basma yarinyace da zaki faɗomun falo haka da kuka ni kinsan halin da nake cikine to nima da kike ganina babba yau da zansamu kukan zanyi dan fuce taƙaici......   "Ma'arufa ma'arufa Alhaji badamasi ne keta kwallah mata kira kaman wanda ze bar garin,zubur Ammi tamiƙe itako Anty hajia gyara zamanta tayi dan cewa tayi bataga abun tada hankali anan ba tunda tariga tasan kan zance tasan tatsuniyar gizo baya wuci ta ƙoƙi. Illa kuwa hakane dan ko ida shiga falon beyi ba yashiga faɗin"yanzu saboda yaron nan be daukeni a bakin komai ba nine zanbashi umurni yaƙi karshema dan nayi masa magana ze kira yarinyar nan yamata cin mutunci bakiga yanda ran Alh sunusi yaɓaci dashi bane yau. Ajiyar zuciya ammi ta sauke tana faɗawa sanan kugera tare da dafa goshinta tashiga kaukawa da numfashinta dan ba karamin firgici ta shiga ba dataji irin kiranda yake mata. Ina magana kinyi shiru kin mai sheni mahaukaci to wallahi kisani bazan lamunci wannan ba da ran Alh sunusi yaɓaci gwara ran kowama yaɓaci yafaɗa yana huci. "Iko sai lillahi yanzu shi Alh sunusin ne yace maka Ahmad ya ɓata masa rai a hakan kuma kuke tunanin haɗa zuri'a tsakanin ku wane irin zama za'ayi anan? Saida yaji muryata ma sannan yasan cewa ashe ba ita kaɗai bace"yauwa ikilima yafaɗa yana nufarta yanzu dan Allah abunda yaron na yayi daidaine? Kaman zeyi kuka yake tambayarta tare da daura cewa kuma fa shine surukinsa na gobe. "Hakane amma yah badamasi kamata kanemi shi Ahmad din kaji ta bakin sa dan Ahmad yarone mai biyayya baze so bata maka rai dagangan ba,sannan shi abokin naka meyakaisa shiga tsabgar yara yanzu idan anyi auren ma haka zena zuwar musu gida yana tambayar ƴarsa matsala kai kuma idan ankawo maƙara ƴar siyasar nan ta baka baka iya ba sai ka hau zuciya kayi ta masifa ba tare da ka bincika ba,kowa fa son farantawa nasa yake amma duba kaga yanda kashigo gidan nan a hargitse kaman wanda akace maka Yayah ta zagi iyayenka. "Ai ikilima hakama zakice yo ba gwara ma'arufan tazagi kaf dangina ta ɓata musu rai data taɓa mutum mai ƙima kaman sunusi kai da kaga yanda yake maganan kasan da iya gaskiyarsa yakeyi dan ba alamun wasa ko sassauci a fuskan sa"ALLAH ya kyauta idan kaga Ahmad ɗin cene mai inason ganin sa tana faɗin haka ta miƙe tanufi hanyan ɗakinta batare da ta ko kalli inda yake tsayen ba. "Kagani kaɓata ma matarka rai akan wani banz...."kul kika zagesa ikilima dan yanzu sai muhau sama dakene.   ALLAH YASA MUDACE. [6/11, 10:16 PM] Xeenat: O *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 53 "To aiga irin tanan ana baka kana roƙa kai zaka iya batawa da kowa akansa dan farin cikin sa amma shikuma baze iya batawa dako ɗiyar da ya haifaba saboda farin cikinta na sama da kowa awajen sa,sai kakira Ahmad ɗin kaji ta bakin sa amma inde a haka zaku tafi bana tunanin wannan aure da kukeson kullawa zeyi tasiri dan shi Ahmad mutumne mai kafiya da tsayuwa kan magana ɗaya shikuma Alhaji sunusi mutumne daya fifita bukatarsa saman komai a duniya kai kuma bazaka iya ƙetare maganan shi ba kaga kuwa Ahmad dinne ze sha bakar wahala dan wannan yarinya bana tunanin ko ruwan zafi ta iya girkawa. Ganin tagama maganan tana shirin miƙewa"koma ki zauna ina kuma zaki ikilima ai sai kitsaya ki saurareni tunda nima danake babba sama da ke natsaya na saurari ta bakinki,kawai de zance dake inde kisan da bakin ki ko dana ƴar uwaki Ahmad yasa Ahmad yin haka wallahi kuyi gaggawan cemasa ya janye daga kudirinsa yakuma dawo gida in kuma yayi wasa wallahi insa yau dinnan adaura masa aure da basma kowama ya huta. Ƴar dariya Anty hajia tayi tace"yayah amma kanada abun dariya yo idan aure zaka daurawa Ahmad sai kazo ka nemi fada mana yo mume namu ciki,bakaga muda mukasan zafinsa dakuma sanin abunda ze faranta masa ai sai ji kawai kayi mundaura masa aure da wacce tafi dacewa da rayuwarsa wacce kai da kanka sai kazo kana alfahari da zamowarta surukarka. "Oh ta haka kula ɓulo to bari kiji wallahi wallahi dande kun saka malam cikine badan haka ba da tuni nasaka ya rattaɓa mata saki ai ni ku yanzu wannan auren ban ɗaukesa aure ba auren wucin gadi kinsan abunda ake nufi da na wucin gadi to haka na daukesa lokaci ƙanƙani nake jira"Antyn yara aka kira daga bayansu tare suka juya jin muryar Ammi yasa Alh badamasi yin kicin kicin da fuska itama haɗe fuskarta tayi ba alamun wasa tace zoki wuce ki tafi gida mayi waya anjima. HAJIA MARIYA Ganin kukan na basma bana karewa bane tashiga rarrashinta harta samu ta shawo kanta tayi shiru ta faɗa mata damuwarta,murmushi tayi ta kamo hannun ta tariƙe tace"basma kefa ba yarinya bace karama haryanzu da komai sai daddynki yashige miki gaba sannan zaki samu. Keko ƴar kissarnan ta ƴan matan zamani baki iya ba kice komai sai da izza zaki mallakeshi kisani wani abun karfin izza data mulki kuɗinki shi zesa ki mallakesa ba, wani abun saida ƙaskan da kai sannan ne ze kaiki ga samun abunda kikeso. Yanzu duba kigani da kinje masa da lallami da tausassan kalma da yanzu kinsami biyan bukata amma kinje kinyi masa wannan haukan naki taya ze saurara miki shin baki taɓa jin shikansa daddyn naki yana faɗi a harka ta kasuwanci babu sani ba sabo ba,yanzu gashi kinge kinsaka daddynki ciki ƙila yace koda karfin kuɗi saiya samo miki wannan riga saboda farin cikin ki amma shi Ahmad ɗin naki kinɓata masa.....shiru tayi tana sauraron mummyn tata a can karkashin ranta kuwa tunani take yaushe mummynta tazama haka take magana cikin sanyi. Ganin kaman tana tunani yasa mummynta dan tabata kamanko tasan abunda take magana aranta tace"kinga bar wahalar da kanki sai kinsan komai kibar komai yanda kika gansa yanzu de tashi kishaga kisamu kiyi wanka ki kira Ahmad ɗin a waya ƙila yasauko daga fushin da yayi ki kalallamesa karkuma ki dauko masa zance rigan mude samu yasauko da fushin tukunna musan abunyi da haka tasamu ta korata ɗaki ita kuma ta zauna zaman jiran Alhajin nata. Aisha koda tashiga ciki wanka tasamu tayi hankali kwance,tafito bedroom dinta daure da towel saida ta tsane danshin ruwan jikinta sannan ta zauna zaman shafa jikinta da lotion masu kyau da daɗin kamshi tana gama shafa man ta jawo turaruka ta feshe jikinta dashi light makeup tayi sai kawai taji aranta ranason saka wannan rigan kai sai ta jawo abarta tasa tashiga juyi a gaban mirrow ita kaɗai sa sakin murmushi take kawai sai dauko wayanta da kasheta ta ajiye tun kwanaki takunna saida ta gama searching sannan tashiga camera tasoma haska kanta da hotuna saida tayi mai isarta sannan ta tsagaita abunda bata taɓa yiba daura hoto a media shine yau tayi na musamman amma a IG dan nan sukafi ɗaura tallan kayansu idan sunyi sabbin styles imoji tasa daidai kan fuskarta sannan tayi rubutu kaman haka dayaja hankulan mutane musamman matasa ƴan uwanta masu sana'ar dinki. _kowa da kudinka saida rabonka bawai ina magana kan kaina bane a'a ina maganane kan wannan riga dake jikina matsayina na ɗiyar da nakowa ba ban isa na mallaki wannan kayan ba,Abu na Allah wai budurwa da jika kasancewa ta telah sai gashi na dinka abata na nasaka ina alfahari da sana'ata ta telah muba abun rainawa bane kaman yanda wasunku suka daukemu neman gumin mu muke bawai roƙo ko bara muke ba,kaman yanda wasunku suke ɗaukan mu kawai sukawo muna kaya mu ɗika musu subamu kuɗinmu idan kuma akasamu akasi rashin gama musu ɗinkinsu akan lokaci su rufe idonsu suci mana mutunci basa tunanin gobe ma zamu sake gamuwa sude ganin su ai kuɗinsu ke aiki dan haka bamu da saura mutunci awajen su tunda kudi suke biyanmu. Tellah ba ƙasƙantacce bane mu teloli jajirtattune jinjina ga telolin da ke faɗin duniya baki ɗaya dan ko shugaban ƙasa ayau da bazarmu yake taka rawa dan sai mundika sannan ze saka tufafin da zefiti jama'a suyaba na jinjina mana matasa ƴan uwana kumu riƙe sana'armu hannu bibiyu watarana ze kaimu inda bamuyi zato ko tsammani ba mukasance masu cika alkawari sabida girmanta_ Tana turawa sai kawai kira yashiga wayan ta ƙirgijinta ne yashiga lugude yana dukan tara tara dan yafi karfin uku uku bata taɓa jin faduwar gaba irin haka ba,idan yakirata koda yaushe takan tsimayi kiransa cike da zumuɗi take ɗaga kiran har Allah Allah take lokacin kiransa yayi susha hira amma yau itace rana ta farko da taji hakan a ranta kuma ta tabbata ba komai yasa tashiga wannan yanayin ba sai girma igiyan auren mutumin da bema dauki abun dawata daraja ba akanta wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauke daidai kiran ya katse wani kiran yasake shiga. Ƙuntum bala tayi wajen dauka wayan tayi takara a kunne batare da tayi sallama ba,ajiyar zuciya taji yasauke mai karfi cikin sanyi murya kaman na wanda bashi da lafiya yafurta"so keki kikasheni ko hamaira? Batasan sanda kuka ya kubce mata ba,kawai sai ta fashe masa da kuka jin kukanta yasa hankalinsa ya dugunzuma wajen tashi ji yake kaman yajawota tacikin wayan yabata hakuri"Ana asif ya habibi shine kawai abunda take iya faɗi cikin kuka. Kusan minti goma tadauka tana kuka shi kuma yana sauraronta,abu biyu takewa kuka na farko mahaifiyarta da har yau bata da yaƙinin shin tana rayene ko kuwa wane hali take ciki shin tana cikin ƙoshin lafiya ko tana halin jinya shin tama samu taci abinci ko tana can tana bara su suna zaune anan hankalin su kwance duk daren duniya sai tayi kukan rashinta atare dasu,abu na biyu kuma shine Suhail dole ta fito ta faɗa masa gaskiya bazata rufesa ba ko dan darajan soyayyar gaskiya dayake mata. Cikin rawan murya tace"Suhail kai hakuri dan Allah badan halina ba banyi hakan dan na ƙona maka rai ba,saide inaso matsayinka na musulmi wanda yayi imani da Allah da kuma kaddara maikyau ko akasinsa Suhail kaine wanda nafara so tun bansan menene so ba,inaso kamun alkawarin duk abunda na faɗa maka zaka daukesa matsayin kaddaranmu bazaka kuma yimun mummunan fassara ba"cike da zaƙowa yace nayi duk da wani sashin na zuciyarsa tana faɗa masa wani abu abu mara daɗi amma haka ya daure yace yayi. Dakyar ta aro jarumta tasakawa kanta tasan wannan itace hanya daya dazata faɗa masa gaskiya kafin yaji abakin wani yadauketa mayaudariya"inaso ka auri ƴar uwarka Suhaima dan itace ta dace dakai. Wani irin miƙewa yayi tsaye dayajawo hankulan iyayensa da ƴan uwansa duka dake zaune a falon dan tattauna ta yanda zasu ɓullowa abun ganan suhaima ta kusan kamuwa da ciwo zuciya sanadin sonda take masa shi ance ya hakura a aura masa ƴar uwarsa yanzu in yaso daga baya suje nigeria neman masa auren wacce yakeso yaƙi yace shifa sai idan ansoma nema masa auren Aishan in yaso ayi na suhaima daga baya. Ita kuma suhaima cewa tayi inde ze aureta koda na wucin gadine ta yarda muddin zata amsa sunan matar sa yaje ko Aisha uku ze auro ya auro. Jikinsa sai kyarma yake kaman mazari besan sanda ya faɗa saman kugera daya tashi ba,umminsa ce ta karɓi wayan daga hannun sa tasaka ta hands free tayanda kowa zeji. "Habibi kai ɗin ka kasance masoyin gaskiya dakai nake kwana dakai nake tashi acikin raina tunaninka betaɓa gushewa acikin raina kodana na diƙiƙa ɗayane ba,saide bazan yaudare ka nakuma yaudari kaina mufaɗa cikin fushin ubangiji saboda son zuciya ba. An dauran aure da waninka bansan ya ze karɓeni matsayin mata ba,shin zan dace da auren koko? Nide nayi bibiyane nasan kuma duk wanda yama iyayensa biyayya Allah ze dubi lamuransa,Anta mahbub da'iman kukane yaci karfinta ta yanda baxata iyayin wani maganan ba sai sautin kukanta dake karaɗe kunnuwan su tsit kakejin falon shikansa suhail ba zakasan awani yanayi yake ciki ba saboda kasa dayayi da kansa,suhaima ce ta rarrafa tazo ta faɗa jikin sa tasaki kuka mai karfi tana cewa"akhi kaje kazo da ita itaɗin masoyayiyar gaskiyace hakiƙa ni naza maison kaina nasan Aisha ta gujeka ne kawai sabida goranta mata launin fata dakuma kiranta da kwaɗayayya mara asali da nayi yasa ta yanke wannan hukunci,tabbas ita ɗin mai zuciyar zinarice tunda bata taɓa faɗama irin cin mutunci da zaginta danakeyi a waya ba,bayan sakon txt dake rubutawa na cin mutunci da tozarci danake tura mata bata taɓa maidamun da amsa koda sau daƴane ba nasan hakkin wannan abunda namata shike bibiyata Allah yajifa mun soyayyarka acikin zuciyata gashi tana bara zana ga rayuwata wacce na raina nake ganin nafita dakomai ita tayi nasaran mallakan zuciyarka dan allah akhi alfarma ɗaya zakamun koda na rasa rayuwata kazamo....sauri rufe mata bakinta yayi da tafin hannunta yana girgiza mata kansa dagowa yayi da rinan nun idanunsa dasuka kaɗa sukai jajir dasu fuskar nan tasa ita tayi jaa sabida tashin hankali dayake ciki,miƙewa yayi batare da yace komai ba,yayi hanyan ɗakin sa sai juwa dake kokarin kadashi saurin miƙewa ummi tayi dan bin bayansa amma sai Abbiy ya katse mata hanzari yace"barshi yana bukatar keɓe kansa ku barshi ya huta,da haka taron ya watse sai suhaima da aka bari falo tana rizgar kuka da kiran duka lefinta ne ita tajawo Aisha ta guji suhail tayi da tasanin bin shawaran kawaye datayi sosai. ALHAJI SUNUSI Sai gabda kiran sallar magariba sannan yazo gida koda yazo ɗakinsa yawuce direct saide yana bude kofan ɗakin wani kamshi mai daɗi yabugi hancin sa,lumshe idonsa yayi dan shifa gani yake tunda yake a rayuwarsa betaɓa jin kamshin turaren daya tafi dashi irin wannan ba. Haj mariya dake laɓe bayan labule tafito cikin takun katsaita tazo ta rugumesa tabaya take yaji wani irin azabebben feeling wanda betaɓe jinsa ba akanta rugumeta shima yayi nan labarin yasha bamban nima mai dauko muku rahoto sai fitowa nayi naja musu ƙofa dan fa abun na manyane. Ahmad Baccin sa sha sai karfe biyar ɗin yamma yasamu daman farkawa da azaban ciwon kai lallaɓawa yayi yafaɗa toilet wanka yayi tare da dauro alwala yazo ya gabatar da sallan la'asar da besamu yayi ba karamar wayansa yaɗauka wanda bakowa keda wannan lamba ba yakira Ammin sa lokacin tana ɗaki zaune ta rabka tagumj hannu bibiyu ita tarasa meke damun mijinta kowa nason ganin farin ciki da walwalan ƴaƴansa amma banda shi,gashi yanzu yaɓatamun rai amma bemasan yayi ba yanzu haka jira yake naje nabasa hakuri wallahi wannan karon baxan bada hakuri ba tunda kan wannan mutumin ne. Wayanta dake ringing ne ya katse mata hanzari dagawa tayi batare da tasan wanda ke kan layin ba"Assalamu alaikum Ammi yafurta cikin sanyi murya. Wani irin dadine ya ziyarci xuciyar ta har hakan ya bayyana a muryarta amsa masa tayi da"wa'alaikum salam Ahmad ina kashiga ne duk katamun da hankali. "Ammi kwantar da hankalinki tafiyace ta kamani na gaggawa zanyi sati kafin naxo"Allah yakamaku ashe keke zuga yaron nan yake mun iya shegen da yaga dama bani shi bani shi yafada yana warce wayan daga hannun Ammin saide kafinma yakai wayan kunnesa Ahmad yariga daya kasheta baki ɗaya tunda yaji muryarsa yakuma daura damarar yakan Alhaji sunusi da fiddashi cikin rayuwr mahaifin nashi......ja'irin yaro yakashe wayan yafaɗo rike da wayan a hannun sa.     ALLAH YASA MUDACE [6/13, 11:53 PM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 54 "Ai dama tunda naga wancan fitsararriyar ƙanwa taki taxo nasan dawata a kasa ashe keke sashin yimun rashin kunya,to wallahi bazan lamunta ba"wai Alhaji fisabilillahi ace mutum da ɗansa baze iya zama kona minti ɗayane ya fuskanci matsalansa ba kai kullum da kun haɗu kaman musa da fir'auna ai ba haka akeyi ba. "Saiki faɗamun yanda akeyi yafaɗa a fusace kaman zekai mata bugu"Allah yabaka hakuri ya huci zuciyarka bana nufin ɓata maka nafaɗi hakan ba kuma Ahmad dakake magana kansa tun safe daya fita anan bansake sakashi a idanuna ba,sai yanzu daya kira yake cewa tafiyar ujulace ta kamashi jin faɗanka yasa shi kashe wayan sa. "Karya yake yana nan ɓuyewa kawai yayi daga gareni ungo anshi wayan ki kiramun shi dan nasan inkece kikayi kiransa yanzun nan ze ɗaga niko danake maƙiyinsa bagashi yayi blocking wayana ba. Ba yanda ta iya haka tasaka hannu ta karɓi wayan tashiga kiran sa saide kaman abun tsafi duka layinsa a kashe,ajiyar zuciya ta sauke tana maida waya ta ajiye bakin gado sannan tawuce tafita falo ta barshi a tsaye a ɗakin ƙerere kaman dogari,saida yayi tsayuwar kusan minti uku bayan barinta ɗakin sannan ya fito cike da fushi dan shi kadai yasan abunda yashirya ma Ahmad ɗin yana zuwa falo ya isketa zaune tana kallin tv labarun cikin gida kwafa yayi harya gifta ze wuce sai kuma yaja ya tsaya jin wani kanun labarin da yadauki hankulansu daga shi har Ammi. Miƙewa tsaye Ammi tayi tana nuna tvn da yatsa"Alhaji mai nake gani haka? Shima tsura mata ido yayi tana girgiza mata kansa kaman bashine yanzu ya gama tijare ta ba,kana nufin cemun bakasan abunda yake faruwa a company ba kenan? Nan ma ɗaga mata kansa yayi dan shi kansa yashiga cikin matsanancin ruɗani"ana zargin cibiyar magunguna ta AL HAKK da fitar da gurɓatattun magunguna ba bisa ka'ida ba,dan haka hukumar nafdac ta ƙasa ta bada umurnin rufe wajen harsa tagama bincikenta. Gumine yashiga karyo masa shide yasan basa sarrafa ko wani irin magani ba bisa ƙa'ida ba to meke shirin faruwa dashi?tambaya dayama kansa kenan kira yafara samu daga ƴan uwa da abokan arziki wasu jajanta masa sukeyi wasuko gulmace kawai yasasu kiransa haka ita kanta Ammi duk wanda yagani a labarai sai yakirata ita damuwarta ɗaya Ahmad ina yashiga gashi wayansa a kashe baya shiga,Anty hajiace takira itama jajen tawa yayar tata tayi sannan tadaura da cewa zatama faisal magana insha Allah daya shigo zata turashi can gidan naku yagana da Alhajin dan sanmu matsaya guda kafin sunan company sa yaɓaci godiya Ammi tayi ta zauna ta rabka tagumi,shi kansa Alhaji badamasi yama rasa mai zeyi dan kwata kwata jiyake ƙwaƙwalwarsa ta tsaya cak. Alhaji sunusi yakira yana ɗauka yace"wai mai nake gani yanzu a labarai ne? "Kaman yanda kake gani nima yanzu haka abunda nagani kenan narasa wake shirin ɓatamun suna company wallahi,na raini company na tun yana jariri harzuwa girmansa ban taɓa samun tangarɗa ba,nasha wahala kafin nakai wannan matsayi amma rana tsaka wasu da bansa kosu waye ba suke neman ɓatamun suna bani da maƙiyi kowani dana taɓa sa'insa dashi,ya kare maganan sa cike da rauni ƙwantar masa da hankali Alh sunusi yafara dan yasan koma waye yayi musu wannan abun to tabbas yasan sirrin abunda akeyi a wajen to amma waye shine de besani ba amma zeci gaba da baza yaransa dan su binciko masa gasu goga yanzu basama a ƙasa ko wace uwa duniya suka tafi oho tunda sanda yamusu rashin mutunci akan ɓacewar Ishak suka samu saɓani suka watse sukabar masa daban sa. Haka yayi ta magana aransa amma a zahiri cewa yayi"ko zamu haɗu anjima da dare kaman yanda muka saba haɗuwane dan zuwa wajen shugaba ya taimaka mana koda wani abun. Juyawa yayi yakai dubansa ga Ammi da take zaune shiru be ɗauke idonsa daga kanta ba yace"gaskiya sunusi bazan iya zuwa ba dan iyalina tafara zargina gami da fitan dare da nake. Tsuka mai tsawo Alh sunusi yayi daga can ɓangaren yace" aikin banza kenan ai tun tuni saida nace dakai a mata aiki ta yanda koda mutum tagani kana yankawa bata isa tayima magana amma kaƙi,ni kaganni nan wallahi iyalina bata isa ta buɗe bakinta ta tankareni da koda makamancin irin wannan magana ba. Sauke numfashi Alh badamasi da duk abun duniya suka nemi tsaya masa yayi yace"kabar wannan maganan yanzu mayi zuwa wani lokaci dan yanzu bana cikin yanayin da zan iya fahintan inda zancen ka yadosa daga haka ya kashe wayan ya barshi sororo riƙe da waya a hannu wai yau shine badanasi ke kashewa waya zanyi maganin ka yace.   Ahmad dake can gidan sa kwance besan me ake ciki ba tunda yabi kashe dukkan wayoyin sa kuma be kunna tv ba balle yasan abunda ke faruwa a gari. ******** Aisha kuwa bayan gama wayanta da suhail jin bemata magana ba gani take kaman taci amanan soyayya dan haka kuka tayi kaman ba gobe karshe wani irin zazzaɓine yayi nasaran rufeta har haƙoranta suna kaduwa katkatkat. Anty hajiya da tadawo gida har kusan sama da awa biyu jin shuru bataji ɗuriyar ta ba yasata miƙe tanufi hanyan bedroon ɗin nata dan ganin ko lafiya kuma ta faɗa mata abunda yake faruwa da surukin nata dan ta jajanta samunta tayi lulluɓe sai rawan sanyi take dan haka da sauri tanufi bakin gadon tana yayi duvet data rufa takai hannu ta taɓa jikinta zafi taji rau"Aisha baki da lafiya shine bazaki kirani awaya ki fada mun ba. A matukar ruɗe ta ɗagota ta rungumeta dukkanta ajikinta saide jin yanda zafin jikin nata ke ratsata tayi saurin tallaɓota tana kiran"malika fito da mota muje asibiti jin yanda Anty hajia ke kwala mata kira cikin rashin nutsuwa yasa malikan fito aɗaki aruɗe tambaya take"Anty lafiya? Yanda ta ganta da Aisha yasata ƙarasowa wajen nasu da sauri tana taɓa jikin nata jin yanayin zafin jikin nata yasata furta"ya Allah wai meke damunta ne ba ɗazun nan muka rabu lafiya lafiya ba? "Yi sauri mukaita asibiti yanzun ba lokacin tsayawa surutu bane musamu wannan zazzaɓi yasake tukunna musan abunda ke damunta shigana ɗakin kenan na taddata lulluɓe sai rawan sanyi take takare magana kaman zatayi kuka. Wani karamin asibitin kuɗi suka kaita taimakon gaggawa aka shiga bata anmata allurai da karin ruwa takuma samu tayi normal bacci,saida likitan yafita yake cewa"hajia ku kwantar da hankalinku komai normal tasamu tayi bacci yanzu"zazzaɓin fa?ta katseshi da tambaya. "Shima ya sauka hajia"wai meke damunta harya haddasa mata mata wannan zazzaɓi lokaci guda malika ta jeho masa da tambaya,gyara zaman glass dinsa yayi yana kare mata kallo gaskiya ba karya bebin ta haɗu takuma takuma burgeshi da yanayin nutsuwarta kana kallonta kasan classic baby ce duka wannan a ransa yake magana"ina ganin kaman tana cikin damuwa shine abunda ya jawo mata wannan zazzaɓi kaman kuma tayi jima tana kuka saboda yawan sauke ajiyar zuci da take amma fa karku damu in shaa Allah normal zata tashi daga bacci daya dauketa amma dole yau zamu riketa da takwana sai munga yanayin jikin nata tukunna"ai wannan ba matsala bane dakta cewa Anty hajiya takara da cewa ko zamu iya shiga inda take?"show bakomai idan kuna da bukatan wani abu pls lemme no yafaɗa yana kafe Anty malika da ido kauda kanta tayi tana cewa natsani yawan kallo a rayuwa wallahi mutum har mutum gaka idan anganka wayayye amma sai shegen kauyancin kallo haka sarai yaji mai take cewa cikin harshe turanci tayi maganan Anty hajia kan tuni tayi shegewarta ɗakin da aka kwanta da Aisha bata masan abunda sukeyi ba awajen. Da yamma koda Malik ya dauko yaran daga makaranta yana zuwa mai gadi yake faɗa masa ai Aishace ba lafiya hajia babba da hajia karama malika yake nufi sun tafi kaita asibiti basu dawo ba laluɓosu awaya kaji inda suke. Haka ko akayi dan wayan yakira yamayi sa'a anty Malika ta tafi da waya nan take fadamasa asibitin da suke,shima yah Faisal malik yakira shi yake sanar dashi duk da tarin aiyuka dayake dasu a gaban sa haka ya tsallake yaje asibitin dan duba halin da suke ciki. Alhamdullahi jikikan da sauki dan ba yanda sukai tsammanin samunta ba suka sameta anan malik yakoma gida da Anty hajia da yaran gida akabar Anty malika ta zauna da ita zuwa gobe in yaso yanzu malik ze kawo mata da duk abun bukata. Tsaye yake ya kafe allon talbijin ɗinda yakusa rabin bangon falon da ido saboda girman sa,kanun labaran da aka gaba badawa ya kalla sai kuma yayi dariya yace"sunusi ruwa takusa karewa ɗan kada. Yaron sa dake tsaye a bayan sane yayi magana"kwarai oga wannan karon sai mun rusa karfin ikon sa na zalumci da yarda Allah. Shima ɗayan dake zaune ya miƙe tsaye cikin ƙunan rai yace"sai mun tabbatar anma iyayenmu adalci wannan karon koda zamu rasa rayuwarmu amma in shaa Allah sai an wanke mana iyaye a idon duniya. Sai kuma wani da yashigo yanzu falon da sallama amsa masa sukai yashga bawa ogan nasu bayani akan aiki da aka sakashi. "Oga yarinyar da kafaɗa haƙiƙa ɗiyar kace da wani irin sauri ya juyo dan tun dazun be juyaba yabasu bayane eh oga yace kana ya daura da cewa yaran su ukune Aisha itace babba sai khadija mai bimata sai kuma karamin su mubaraq suna zamane gida Alhaji suleiman mai fata amma bincikenmu yanuna kaman basa tare da mahaifiyarsu yanzu sun dawo zama wannan gidan ne watanni uku dasuka wace,ita Aishan tana aikine karkashin company A&b travel agent fanin ɗinki take awannan wajen sannan naji kaman jiya Alhaji sunusi yamata barazana kan wani riga data ɗinka ɗiyarsa tagani tanason wannan kaya amma bata samuba saboda Aisha ta nuna mata bakomai kuɗi ke iya saye ba,daga baya kuma ita Aisha ta daura wani rubutu a shafinta na IG inda take sanye da wannan rigar gashi nan. Yamiƙa masa wayan dake hannun sa cike da ladabi saide duk ƙwafƙwafin sa be iya yaga fuskar ta ba sabida imoji data daura yarufe mata fuska"like father like dauther ya furta ciki ciki,maida masa wayan yayi yana cewa"ka binciko mana mahaifiyarsun ina take rasuwa tayi kokuwa? Bayan yafurta hakan kuma sai yaji wani abu mai nauyi yazo ya tokare masa maƙoshi tuni launin fuskarsa ta canza zuwa ɓacin rai komawa yayi ya zauna saman kugera yana lumshe idonsa ganin hakan yasasu suka barshi shi kaɗai dan sunsan yana bukatar hutu. Alhaji shamsu da Alhaji sunusi sai Alhaji bala inda sukai zama na ujula a wani gidan gonan shi Alhaji shamsun nan Alh shamsu yamiƙe tsaye yana cewa"sunusi wani mai ke faruwane? "Kaman ya ya tambaya daga zaunen da yake. "Oh bakama sani ba kenan to bara na tunatar dakai maƙudan kuɗaɗe muka saka wannan harka kuma kai da bakinka ka tabbatar mana da bawata matsala yanzu gashi matsalan ta fara kunno kai"kwarai faɗa masade ko yafi jin naka ankame mana kaya na miliyoyin dalalo a malesiya yanzu gashi gida nan ma matsalan tarafa kunno kai ina mafita. Sauke ajiya zuciya yayi sannan ya dubi abokan nasa yace ku kwantar da hankulanku nan fa 9jace kuɗi zamu tura yanzun nan sai kaji an canza zance kuma wannan company tana gab da zama mallakinmu"kaman yaa suka furta a tare file dinda ke gabansa yatura masu budewa suka suna zaro idanu waje dan ganin abunda yaƙusan...     ALLAH YASA MUDACE [6/15, 11:32 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* CHSPTER 55 Dariya suka kwashe dashi gaba ɗayansua tare kaman wasu bosawa saida sukayi mai isarsu suka buɗe kwalban barasa shamfe suka shiga kwankwaɗa nan Alh sunusi yake sanar dasu ƙudurinsa"saka hannun wannan mai taurin kan ɗan nasa nake bukata fiyot a wuce wajen. "To ita kuma ɗiyar taka ya zakayi da ita kasan yaran zamani da shegen hange hangen su wai SO kartaƙi yimana yanda muke so saboda soyayya kasan soyayya ba abunda baya sawa mutum yaƙiyi soyayya maida maƙiyi masoyi. "Nabi soyayya da gudu ai bazan bari soyayyar ɗan miƙiyina ya tasirantu a zuciyar ɗiyata ba dole itama ta fifita buƙatana sama da komai na duniya dan wallahi ko ɗan yatsan hannuna ne naga ze shiga tsakanina da nasarata da muradina to wallahi guntule shi zanyi kagako ba abu mai wahala bane kawar da duk wanda ze nemi kawo mun cikas ko yun ƙurin cin amanata daga doron duniyar nan,mukut su biyun suka haɗiyi wani ƴawu mai kauri dan Alh sunusi idan ya furta abu ba makawa to kuwa zeyine kamande yande ya samu nasaran kawar da abokan kasuwancin su da dama ace warsa maciya amana ne. BAYAN KWANA BIYU Yau aka sallamo Aisha daga asibiti da tarin magunguna Aisha dake zaune bakin gado ta zubawa guɗaya ido da alama tunani take yayinda Anty malika kuma tashiga harhaɗa masu kayansu dan tayi waya da Anty hajia ma tace tayi zamanta yanzu suma za suzo tunda an sallame su,dr sufyan nagani zaune a office ɗinsa sai rubutu yake a wata doguwar paper yana rubutawa yana sakin murmushi dr irfan daya shigo ya'iskesa yayi murmushi yana girgiza kansa dacewa"lalle iska yana wahal da mekayan kara. Ɗagowa yayi ya banka masa harara sannan yasake maida kansa ya cigaba da rubutun da yake,zama dr irfan yayi kan kugera dake fuskantar abokin nasa yace akan wannan zaman rubutu da kake mai ze hana kaje ka tunkareta gaba da gaba da bukatarka kasan fa yau shine last chace ɗin dan yanzu haka na barota sai haɗa kayansu take kaga kuwa tafiya zatayi sunan ta kawai kasani ba address ba ba ba ba...yakare da zolayarsa zunbur dr sufyan yamiƙe yana kallon dr irfan da shima shidin yake kallo yace"karkace mun haka"to shike nan tsaya kallon ruwa ƙwado yama ƙafa. Be ma sake bin takan dr irfan dake faman yimasa tsiya ba yayi waje da mugun sauri shiko dr irfan mai zeyi inba dariya ba yana cewa hmm su so manya daa idan ance akwai so kaine kan gaba wajen musawa mutum babu so yanzu ko wace ƙaniyarce kuma wannan yana kare faɗin shiɗin ma fita daga office din yayi yaja masa ƙofa dan dama zuwa yayi ya faɗamasa mutuniyar tasa fa sai faman haɗa kaya take. Hajia mariya nagani zaune sai zabga murmushi take wato bukata tabiya kenan ta dauki waya takira aminiyarta Hajia balki a waya kira ɗaya ta daga kaman dama jira take"kawata kice tasamu kenan kira a wannan lokaci haka? Dariya hajia mariya ta kwashe dashi tana cewa"oshe ita hajia balkin dariya tayi daga nata ɓangaren tana gyara zamanta saman gado tace ban nasha da dumi dumin sa. "Ƙawata komai yayi daidai wato wannan magani da kika bani bala'ine wallahi musibace bakiga yanda Alhaji ya susuce akaina ba wallahi,ai bayan komai ya lafa ina kawo masa buƙatata be wani ja zancen ba sai cewa yayi ai dama can gani yayi kaman nice banida sha'awa yin kasuwanci take ya cakemun 10m inja jari ke in faɗa miki harda babban shago dakuma store ajiye kaya. "Wayyo daɗi kice duniya sabuwa ƙawata yanzune zaki faso gari,yanzu yaushe kike ganin yadace muje mufara miki sari kinsa ance da zafi zafi ake dukan karfe. Ɗan jim tayi kaman mai tunani sai can kuma tace"ca nayi mubari harsai an gama bikin basma tukunna kinsan wannan satin ne kuma inajin kaman gobene zasu fara wasu event din. "Shike nan hakanma yayi amma kisamu kizo mukoma wajen bokan nan ta yanda zaki samu kan Alhajin sosai duk da shima tsaye yake amma bazaki zauna ki zuba masa ido ba. Ahmad sai yau ya shirya zuwa gidan su karfe goma daidai na safe yasame shi a ƙofar gidan saida yashiga ya daidai ta parkin din motarsa ya fito yana tafiya kaman wanda bashi da laka ajikinsa main falon gidan nasu yanufa kansa tsaye bakinsa dauke da sallama. Auta meera ce tamiƙe da gudunta tana masa oyoyo daukanta yayi ya ɗagata sama yana juyata kaman wata bebi itako sai dariya take Fadwa ma tazo ta faɗa jikin sa tana cewa"ya Ahmad ina kashiga kwana biyu baka nan kullum Ammi sai tayi kuka gashi kuma daddy bashi da lafiya wai wai ....sai kuma tayi shiru tsareta da ido yayi zuciyarsa dake faman bugawa da sauri da sauri meera ce ta amshe da cewa"a school dinmu ba wai kawayen mu cemana suke daddyn mu macucine yana cutan al'umma da saida musu da ƙwaya da sunan magani shiyasa aka rufe masa company da muka faɗawa uncle Sam sai yace ai gaskiya aka faɗa mana mu yaran maci amanan kasane yau kwana biyu bamuje school ba saboda ko munje yara da malamai zagin mu suke. Besan sanda ya dire meera ƙasa yanufi ciki ɗakin Ammi da sassarfa ba,zaune ya taddata ta saka daddy gaba da ban baki yasha koda tea ne,amma yaƙi amsa yayi baƙi kirin ya rame cikin kwana biyu kaman wanda ya kwanta ciwon shekara,zuba masa ido sukai suna kallon sa"Ammi wai me nakeji daga bakin yaran nan yanzu? Ajiyar zuciya ta sauke tana maida kanta kan Alh badamasi dake zaune cikin sanyi murya tace"wai ana zargin sa da sarrafa miyagun ƙwayoyi ba bisa ka'ida ba,shine aka rufe wajen. Kai ina kashiga kwana biyu wayanka baya shiga ina kake tsawon kwana biyu baka da labarin abunda yake faruwa a garin?ta tambaya tana tsareshi da ido"yanzu de ba wannan ba Ammi shi daddyn wani irin mataki ya dauka dan kare mutuncin kansa dama companyn nin baki ɗaya. "Babu nadeji ɗazu yana waya da Alhaji sunusi yana cewa zasu sami manyan akan maganan? Wannan ba yi vane Ammi Kallonsa daddyn nasa yayi yace"kadamu danine da katsallaƙe kayi tafiyarka kwana biyu batare da ka waiwaye mu ba? "Yi hakuri daddy yanzu ba lokacin yin wannan magana bane inason sanin shin akwai waƴanda suka saka hannu jari a company ko kuwa? Shiru yayi dan yasan da zaran yace Alhaji sunusi yanzun nan zasu haushi da masifa shisa ma koda faisal yazo jiya du tambayan da yayi masa be yarda koda wasa ya ambaci sunan sa ba. Jin shirun yayi yawa yasa Ahmad miƙewa rai a ɓace yace"daddy zanyi duk iya yina dan ganin nakare mutuncinka da martabanka da ƙimar wannan gida tamu koda zan rasa raina ne amma fa hakan baze samu ba harsai ka bani haɗin kai,daddy idan har ba wani abu mara kyau a wannan company naka ba bukatar bin manya da basu cin hanci. "Ahmad company nawane ko naka? Alhaji badamasi ya tambaya rai aɓace dan wani mugun haushin Ahmad yakeji,abu yau kwana biyu bayanan sai yanzu ne ze zo masa dawani zancen banza. "Naka Ammjn ta amsa masa "To inde nawane ba ruwansa"da ruwan sa harda tsakin sa dan hakkinsa ne kare mutuncun gidan nan matsayin sa na magajin ka. Banga dalilin da wani bare da ze saka bakinsa cikin wannan magana ba,idan bada wata a ƙasa ba mai nawani cewa za bada kuɗi abi manya dan kawai son rashin gaskiya idan ba wata a ƙasa abar jami'an tsaro suyi aikin su kaman yanda suka bukata idan kuma dama kasan da wata aƙasa kayi gaggawan fayyace mana ta yanda zamu gane. Menene alaƙanka da Alhaji sunusi dan shi kaskane raɓi...."ya isa yafaɗa a tsawace da daurawa da cewa kufita kubani waje. "Zamu fita yanzu kaman yanda ka bukata saide abu na farko kuma ba karshe da zan faɗa maka shine babu zancen wannan bikin na Ahmad cikin wannan sati kaman yanda kuka tsara harsai komai ya daidaita dan baza'ayi biki aure ana cikin wannan hali ba tana kaiwa karshen maganan ta taja hannun Ahmad daya kafawa daddyn nasa ido suka fita daga ɗakin. ******* "Aisha Aisha Aisha har sau uku Anty malika na kiran sunanta amma bataji taba saboda nisa datayi da tunani da take,barin abunda takayi tayi taxo ta zauna saman gadon kusa gare tana mai dafa kafadanta firgigit tadawo hayyacinta tana ƙakalo murmushi da iya kacinta kasan saman leɓɓen tane tace"Anty malika karde hankin gama? Gyaɗa mata kai tayi cike da tausayinta tariƙo hannunta tace"nasan da wuya ace rana tsaka karabu da abunda kakeso dakuma ciwo amma idan kika saka hakuri aranki kika kuma dauki abun da sauki saiyazo miki da saukin. Hawaye datake ƙokarin tsayarwa ne yasamu nasaran xubo mata daga gurbin idanunta tace"Anty malika hakika nayi rashin masoyin gaskiya shin faɗa masa gaskiya danayi kafin yaji abakin wani yaɗauka na yaudare sane kuskurene yin hakan? "Bakiyi kuskure ba koka ɗan hakan da kikayi shine daidai"to amma Anty meyasa koda sau ɗayane be tsaya ya saurari abunda nake faɗa masa koya nuna yajini ba sai shirun da yayi kinko san yaren shiru kuwa Anty malika wannan shiru yana neman kasheni naso ace koma yayane ya tsaya ya fuskance ni nide wallahi an cuceni da wannan auren wucin gadin nan wallahi ta faɗa tana sake fashewa da sabon kuka,dr sufyan daya zo shiga ɗakin yaji dukkan abunda suke tattaunawa baya yayi a hankali batare dasun san da tsayuwar sa awajen ba. Suhail tunda yashiga ɗaki yarasa meke masa daɗi yasan tabbas gaskiya Aisha ta faɗi dan betaɓa kamata dayi masa karya kokuma wasa irin haka ba,shin awani mizani yakamata yaɗaura kalamanta cin amana ko yaudara"la la la yafurta a fili to ma waye wannan dayayi musu ƙatsalandan shiga cikin rayuwarsu bayan sun riga sungama tsara yanda zasuyi rayuwarsu ƙarƙashin inuwar aure. Kukansa yayi mai rai da lafiya dan yasan kukan ne kaɗai ze iya saukar masa da abunda yajiki a ransa gwara yayi ko ze samu sassauci da salama a zuciyar sa amma de yasan yayi rashi rashi irin wacce bazai taɓa maida irin sa ba.   ALLAH YASA MUDACE [6/25, 10:10 PM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 56 Suna gama wayan ta sauke jiki a sanyaye take sanar dasu abunda ke faruwa da mijin yayar tata kowa dake wajen sai da jikinsa yayi sanyi kuma sun kaɗu dajin wai cid aka jedashi wannan yana nuni da cewa case ɗin ba karami case baneba tunda harda su cid aciki"Anty hajia ko zaki kira yah faisal ki sanar dashi abunda yake faruwa cewar Aisha"nima abunda zancd kenan kika rigani inji malika. Koda Anty hajiya takira wayan faisal cemata yayi yanzu haka suna cid office shida Ahmad amma bawani feedback tunda aka shiga dashi ciki kuma sunnemi gabawa da manya amma babasu wannan daman ba ajiyar xuciya ta sauke kana tace"karka bar ɗan uwanka shi kaɗai katsaya dashi dan ganinka tare dashi ze bashi kwarin gwiwa,amsa mata yayi da In shaa Allah Anty hajia bazan taɓa barin sa shi kaɗai ba duk yanda ake ciki zan kasance dashi,daga haka yakashe wayan. Yana ɗan kallon Ahmad dayake waya da comm [7/15, 3:58 PM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 57 NAGODE DA ADDUO'IN KU GARENI MASU KIRANA TA WAYA KAI TSAYE DA MASU TURA SAKON KARTAKWANA DAKUMA MASU YIMUN MGN TA WHTAPP ALHAMDULLAHI NAJI SAUKI ALLAH YABAR KAUNA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA Suna gama wayan ta sauke jiki a sanyaye take sanar dasu abunda ke faruwa da mijin yayar tata kowa dake wajen sai da jikinsa yayi sanyi kuma sun kaɗu dajin wai cid aka jedashi wannan yana nufi da cewa case ɗin ba karami case baneba tunda harda su cid aciki"Anty hajia ko zaki kira yah faisal ki sanar dashi abunda yake faruwa cewar Aisha"nima abunda nake son cewa kenan kika rigani inji malika. Koda Anty hajiya takira wayan faisal cemata yayi yanzu haka suna cid office shida Ahmad amma bawani feedback tunda aka shiga dashi ciki kuma sunnemi ganawa da manya amma babasu wannan daman ba ajiyar xuciya ta sauke kana tace"karka bar ɗan uwanka shi kaɗai katsaya dashi dan ganinka tare dashi ze bashi kwarin gwiwa,amsa mata yayi da In shaa Allah Anty hajia bazan taɓa barin sa shi kaɗai ba duk yanda ake ciki zan kasance dashi,daga haka yakashe wayan. Yana ɗan kallon Ahmad dayake waya da commissioner ƴan sanda dayake mutumin daddyn sane amma sai ce masa yayi"Ahmad kayi hakuri sannan kuyi ta addu'a ba abunda zan iya yimaku dan case ɗin na Alhaji babban case ne akwai kuma lauje cikin naɗin daga haka ya kashe wayansa yana mai bawa Ahmad din hakuri. Shiru Ahmad yayi idanun nan nasa sun kaɗa sunyi jajur jijiyoyin kansa sun tashi rudu rudu saboda ɓacin rai,bakin nan nasa yabushe kai kace yashekara besha ruwa ba,case din Alhaji akwai lauje cikin naɗin shine abunda yake ta maimaitawa waye? Waye wayake son ganin yaɓatawa mahaifinsa suna tawannan hanyan waya zaɓi ɓatasu a idon duniya ta wannan lalle maishi koma wanene yayi babban kuskure. Dafashi faisal yayi dan ganin yanda yake kai komo yana maganganu yace"lafiya? Girgiza masa kai yayi sannan ya labarta masa yanda sukai da commissioner shiru faisal yayi sai can ya dago yana kallon Ahmad yace"kai me kafahinta anan?"babu saide inason fahintane dan wallahi nagano koma wanene yakeson jafa daddyna cikin wannan mawuyacin halin saina kasheshi da hannuna yakare magana a fusace. Murmushi faisal yayi yadaura da cemasa dadina dakai saurin fushi amma katsaya kayi tunani a tsanake zero sai shegen zuciyar banza data wofi yanzu kai baka tunanin da saka hannun wasu ko wani shin baka zargin wani cikin wannan abun? Shiru sukai duka kaman masu tunano wani abu sai can Ahmad ya dago yana kallon faisal ɗin yace"gaskiya bana zargin idan ma zan zargi wani to Alh sunusi ne amma fa ko shiɗinma bana tsammanin zai ɓatawa daddyna suna ko dan saboda abotansu. "Hmmm bro kenan irin su Alh sunusi zasu iyayin komai saboda biyan buƙatar kansu yanzu de abu ɗaya nakeson kaimun dan son samun bakin zaren ni kuma zanyi aiki da ƙwarewata dan ganin mun kama duk wani mai hannu cikin wannan case din amma da sharadi"wace irin sharaɗi fadi koma wacece zanyi dan ganin anyi released daddyna kuma an wankeshi a idon duniya. Gyaɗa kai faisal yayi cike da gamsuwa yace"yanzu de ɗauki wayanka kakira shi Alh sunusi kace ka amince da auren basma dama tsarinsu na tarewarka gidan sa,kallon baka da hankali ahmad yamasa eh ta nan kaɗai zamu samu kama masu lefin a hannu da shi Alh sunusi shike sarrafa cocaine a company ta Al hakk bincikemun yanuna shike amfani da mazuban capsule dakuma tambarin Al hakk ɗin waje guda suka ware suna wannan aikin a binciken da mukai saide bamu da ƙwakƙwaran hujja dazamu gabatar koda mun kamashi. Cike da gamsuwa ya gyaɗa kansa cemasa zakayi yanzu ga halin da daddayn ka ke ciki kana neman alfarman a ɗan ɗage auren zuwa lokacin da zaa saki daddynka idan zargina akansa daidaine to dazaran yaji haka zaka ganshi ya dawo nan kuma ze tsaya tsayin daka dan ganin yafito da daddy yau din nan tunda yasan manya sosai. Alhaji sunusi zaune suke a guest house ɗinsu suna shakatawa gefe guda kuma ga ƴan mata nan birjik suna sha'aninsu wasu na tikar rawa wasu na zazzaune suna zukar shisha wasunsu kuma na ƙwaƙulal junan su gefe kuma samarine matasa manyan Alhazawan nan ke hakewa ba kunya ba tsoron Allah,Allah yakiyashemu wayan Alh sunusi ce tayi ringin yana kaganin mai kiran nasa saida ya kwashe da dariya kaman wani boss yace"yaro man kaza sannan yayi pickin call ɗin yakara a kunnen sa"sallama Ahmad yamasa amsa masa yayi kaman bayason amsawa ya daura da cewa"ya iyayen naka?rintse ido Ahmad jin tambayan da yamasa daurewa yayi yace"suna lafiya yadaura da cewa dama nakira na sanar dakaine ina bukatan a karamun koda sati daya saboda matsala da daddyna nake ciki kafin sannan ƙila musamu ko a warware idan komai ya daidai ta satin sama sai a daura auren idan yaso zuwa weekend idan baƙi sun watse sai natare a gidan naku kaman yanda kabukata"wace matsala Alhajin ke ciki?muna nan ai bazamu bari ya tozarta ba yanzu faɗamun meke faruwa da Alhajin yafaɗa ai abunda yashafi Alhaji yashafeni koba komai shidin abokinane sannan mutumin kirkine shi yanda yake tambayan kai kace kuka zeyi nan Ahmad ya labarta masa abunda ke faruwa da inda suke ba kunya ya kaɗa baki yace dayake rabona da sauraro ko new paper tun shekaran jiya bansan abunda ke faruwa ba amma gamunan yanzu zamuzo kuma in shaa Allah yau Alhaji gida ze kwana ai wannan tozarcine kashe wayan yayi yakai dubansa ga abokan sa yana washe baki yace plan A tayi yanzu zamuje ga plan B get ready to play yanzu wasan yasoma. Cikin abunda be wuce minti ashirin ba su Alhaji sunusi da muƙarraban sa suka hallara a cid office yana fitowa daga cikin motarsa waya kange a kunnesa sai magana yake a fasace sude su Ahmad sundeji yana cewa"Alhaji badamasin ne baku saniba kode kawai kunason tozarta shine bana bukatar hakurin ku kawai ku hadani da manyan ku yanzu gani nan harabar wajen yana kare fadin haka yakashe wayan yanufi inda ya hango su Ahmad"wanene na kusa da Ahmad din nan ya tambaya?"wannan ai shine faisal din nan jami'in da kadade kana nema Alh shehu ya amsa masa"wace alaqa ke tsakanin sa da Ahmad din?"kila ta abotane yanzun Alh bala ne ya amsa da fadin haka. Koda suka karasa hannu suka mika musu cike da ladabi da biyayya shikansa Alh sunusi yaji daɗin yanda yaga Ahmad din yabashi girma ko ba komai yasan aikin da akai masa yasoma kamashi dariya yayi aransa yana cewa sai na juyaka kaman waina a tanda kai da uban ka,amma a zahiri yanu alhinin da rashin jin dadin abunda yafaru da Alhajin yakuma ce in shaa Allah yanzun nan zafito dashi waƴan nan yanuna Alh shehu da Alh bala yace manyan membobine a ƙungiyarmu muna cikin meetin ɗin karshen wata kiranka ya iskeni shine muka katse meetin din mukazo nan dan wannan ba abunda zaka zauna kace sai daga baya zaka zo ba dan shi kansa Alhaji ba mutum daya bane idan wani abu yasamu dan kungiyarmu koda matashine tsayuwa yake sai yaga komai ya daidaita sannan hankalin sa ke kwanciya"ai Alhaji ba mutum ɗaya bane wajen nuna tausayin sa ga waƴanda suke tare dakuma taimakonsa ga kungiya cewar Alh bala"wannan haka yake Allah de yakare shi yakuma shiga tsakanin sa damasu son ganin bayan sa cewar Alh shehu Amin su Ahmad suka amsa sauri zungurin sa Alh sunusi yayi yana masa alama da ido mecece na addu'an. Zuwan su ba jimawa sai ga Alh badamasi da mutanen da suka je gida suka zo dashi sun fito dashi suna ta bada hakuri kan kuskure sukai rai ɓace Ahmad ya kalle su yace"bawani kuskure da kukai saide ku faɗawa shi wanda yasaku cewa da Allah muka dogara kuma da yardan Allah baze taɓayin nasara akanmu ba idan yana da wata bukata to yatun ƙaromu gaba da gaba wannan shi ze nuna shidin namijine bawai sari kanoke ba kuma wallahi ko da wasa wani daga cikin wannan hukuma taku tasake taka ƙofar gidanmu bada wata ƙwaƙƙwaran dalili ba wallahi kotu zata rabamu dashi dan ko yanzu cctv na tanaɗi komai kuma zan ajishi hujja saboda gaba daga haka yayi gaba yabarsu baki sake shikansa Alh sunusi dake rugume da Alh badamasi yana nuna murnan sa amma hankalin sa yanaga maganan da Ahmad din keyi da mutanen wannan yaron wannan yaro anyi hatsabibi yafiɗi haka yafi a kirga a ransa. ******* "Ammi amshi ruwa kisha ki ƙwantar da hankalin ki in sha Allah yanzun nan zakiga daddy yadawo karɓan ruwan tayi ta kurɓa tana cewa"ɗiyata Aisha ni ba kame Alhaji da akaine damuwata ba damuwata ɓata masa sunanan sa data sana'arsa daya ɗau shekaru yanayi yasha wahala kafin yataka wannan matsayin amma lokacin ƙanƙani wani yazo daga sama yaɓata masa suna kinsan abun da cin rai. "Hakane ammi amma idan kika fauwalawa Allah komai kika miƙa masa da ƙogon baranki sai kikaga ya amsa miki addu'arki kuma kinsan addu'ar mata ga mijinta addu'ace karɓaɓɓa dakuma iyaye ga yaransu musamma uwa idan kika dage da kaiwa Allah kukanki dakuma yawaita sadaka sai kiga komai yazo da sauki. "Gaskiyarki ɗiyata kin sake tunatar dani abunda namanta in shaa Allah zandage dakaiwa Allah kukana nakuma gode da Allah daya bani ke matsayin surukuwa fatan zaki zauna da Ahmad kikuma karɓesa matsayin miji dan inaji ajikina zakuyi farin ciki da wannan haɗin namu naga.....rufe fuskarta tayi da tafin hannunta cike da kunya"wai yaya me kuke tattauna da ɗiyarki haka sai faman rurrufe fuska take Anty hajjia ce ke tambaya tana kokarin zama ganin yasa Aisha miƙewa ta zura ɗaki da gudu daidai su faisal dake shigowa falon da sallama miƙewa Ammi tayi ba tare da jin nauyi ko kunyan kowa ba tanufi Alhajin ta tarungume sa ta saki kuka...   ALLAH YASA MUDACE [7/18, 9:14 AM] Xeenat: AUREN WUCIN GADI CHAPTER 58 Tsunkayar dakai Ahmad da faisai sukai cike da kunya suko su Alh sunusi abun ba karamin burgesu yayi ba,bubbuga mata bayanta yashiga alaman rarrashi ƙuri suka zura masu ido suna kallo can Anty hajia tayi gyaran murya tana murmushi tace"to su yayah abawa baƙi hanya sushigo. Sai a sannan ma takai hankalinta garesu cike da kunya tasaki daddy tana cewa dasu"a'a Alh kune tafe ashe sannunku da zuwa kushigo daga ciki ta fada tana raɓawa ta gefen daddy data sake tayi cikin falo shigowa sukai suka zazzauna kafin aka gabatar musu da ruwa da lemu da dan abun motsa baki. Bayan yan gaishe gaishe nan Alh sunusi ya gyara zama ya fuskanci su Ammi sosai yace"hajia wato maganace nakeso muyi da ku akan auren yaran nan sai kuma ya danyi shiru"to to ko wani abunne kuma akace yafaru? Saurin amsa mata yayi da"ko ɗaya saide abubuwa dake faruwane kamande yanda kikaga wannan abun yafaru da Alhaji dande Allah ya takaitane da bamusan inda ze tsaya ba,Allahde yakare gaba"da amin sauran suka amsa sannan Ammi ta dubi Alh sunusi da kyau tace"Allah de yakare gaba amma ko yanzu dole ne mubibiyi masu son yimana zagon ƙasa dan dole dasaka hannun wasu tayu makusantan mu komade manene...sai kuma tayi shiru"mai kike nufi Hajia ko kina zargin wanine?yanda yayi tambayan kaman tana ɗan firgice dan murmushi yaƙe tayi tace"banace ba saide kawai nafaɗi hakanne saboda duniya ba gaskiya wanda kayarda da shi shine ze cuceka kokuma ya haɗa kai damasu son ganin bayanka,duk ba wannan ba mukoma ga maganan da kaɗauko Alhaji dan ina ganin kaman zatafi wannan ɗin mahimmanci. Ba haka yasoba daso samune yaso yaji kode tana zarginsa ne ya canza taku,sai yan kame kame kawai daya fara yakasa samun nutsuwa zuciya data ruhi yayi danyin magana haka kawai yatsinci kansa da shakkar hajia kwarjini yaji tana masa tacika masa ido da kwarjini abunda tunda yake mutum ɗaya yakeji yana masa irin wannan aduk sanda ze masa magana ko wani saide yakan haɗa da karfin zuciya wato ishaq tunawa dayayi da shi take yaji zufa yakaryo masa ajiki dukda sanyi Ac daya cika falon amma shi zufa yakeji,sai Alh shehune yace"ranki yadade hajia wato munriga mun gama magana da shi Ahaji badamasi tun tuni dama yardan yaro dakuma naki muke jira to Alhamdullahi yanzude zamu iya cewa komai kaman yazo karshe tunda shi yaro ya amince da auren dakuma tsarin tarewan sa can gidan ta bakin ki kawai mukeson ji. Duk yanda Ammi taso ƙin amincewarta da wannan tsarin nasu marairaice mata Ahmad yayi dole tayi shiru badan ta so hakan ba,amma duk da hakan saide tace"Alhaji tunda sun fini yawa na amince nima duk da ba haka naso ba,daso samune naso ace nima na zauna da ɗana da surukuwata tare amma hakan beyu ba amma fa kasani Ahmad yanada wata matan bayan basma dan tarewarta kawai muke jira saboda haka inason kasani dole ze raba musu kwana inma ƙwana ɗai ɗaine ko biyu biyu duk de yanda yatsarawa kansa amma kasani bazan sake yarda da wata tsarin bayan wannan ba,tana kare faɗin haka tamiƙe tanufi ɗaki Anty hajia ta mara mata baya. Bayan barin Ammi falo ijiyar zuciya suka duka dusan a tare kana Alh sunusi yayi kasa da murya yace"Alh badamasi ashe taurin kan Ahmad ba ƙasa yadauko ba,saide inason kasani kokuma ince kafi kowa sanin wanene ni dakuma abunda zan iya aikatawa da wanda bazan iya aikatawa ba,kajawa matarka kunne idan tace zata kawomun matsala zata iya rasa rayuwarta"karka kuskura kasa Ammina cikin matsalan nan dan ita ba abunda tasani illa soyayyar mijinta da ɗanta tanason ɗanta fiye da yanda kakeson ɗiyarka dan haka katsaya iya inda yadace ba ruwana da suruki koda mahaifina ne yace ze cutarmun da uwa sai inda karfina yakare yana kkare maganarsa yayi gaba dan maganan sa yayi cikin hocky voice dinsa dakuma murmushi kwance saman fuskan sa sai karantse abun bedame sa ba,saida yayi magana sannan Alh sunusi ya ankare ashe dashi awajen kafin yace zece wani abu dan kare kansa tuni yaɓacewa ganin sa yafita a falon faisal na mara masa baya. Dafe kansa yayi tashin hankali goma da ishirin dole yaje yagana da dodo a yauɗin nan dan wannan vabban al'amarine ba abunda ze tsaya sanya ba,idan yace ze tsaya yin sanya sai wankin hula ya kaishi gayin dare. "Kaga irinta ba,wai meya kawo wannan maganan yanzu idan hajiya taji fa duk yabi yaruɗe sai masifa yake dole de Alh sunusi karshe shiya kwantar dakai suka bawa Alh badamasi hakuri sannan sukai sallama suka katafi tun a hanya yakira basma a waya yamata albishir wani irin ihun murna tasaka dayasa shi dole sauke wayan akunnen sa,nan tashiga kiran ƙawayenta tana faɗamasu auren next week ba fashi nan danan gida ya dauki harama kasan abunka da masushi tun saura kwana biyar ƴan uwa na nesa suka fara zuwa. Ammi tana komawa ɗaki takai gware takai mari tama rasa yanda zatayi shin kuka zatayi ko daura hannu zatayi aka tayi ta ihune,dafata Anty hajia tayi tace"yayah dan Allah ki kwantar da hankalinki abi komai a sannu bamusan me yasa Ahmad din amincewa haka dawuri ba,addu'a zamuyi masa Allah yakare shi daga sharrin sa ina ganin akwai wani abu da yasani mu bamusani ba ko kuma yakeson ganar da mahaifinsa"hmmm Allah gamu gareka Allah kakare mun ɗana daga sharrin masu sharri"Amin yarabbi yanzude zama be ganni ba dole zanje ni nima nafara shirri ɗiyata kar abarmu abaya. ******** Shirye shiryen biki ake daga kowane ɓangare ba kama hannu yaro amarya basma ansha gyara ciki da waje dan ba karamin kuɗi hajia balki ta ansa ga wajen ƙawartata ba acewarta na gyarane,haka shugaban kungiya yaso Alh sunusi yakawo basma tayi kwana biyu dasu amma wannan karon ya tuɓure yace saide kungiya tayi hakuri yayi masa alkawarin daren farkon auren ahmad ze amshi budurcin ɗaya matar yakai musu jinin budurcin kaman yanda suka bukata,da wannan suka hakura. Ma aikata da aka ɗiɓo masu girki da masu kula da baƙi dade sauran su ciki kuwa harda daddy ishaq da yaransa inda sukai shigar ɓat da kama yana daya daga cikin masu kula da sashin ɓaki shige da ficensu dakuma abunda ya danganci abincin su da abun shan su. Aisha tana ɗaki ƙudundune kwance taƙi ci da sha sai aikin kuka da take,Anty malika da su ummu salma dasu laila har khadija ba barta a baya ba sunje sunyi ƙunshi da gyaran gashi amma amarya taƙiyin komai saima zazzaɓi daya rufeta tayi luf cikin bargo ba abunda yake sake sakata kuka idan ta tuna wai aurenta za ayi ba dangin uwa balle na ubanta ba saka albarkarsu ina Anna ta take ga ranan da kike ta ƙulafucin gani Allah yakawo amma ba ke ina kike Anna wayyo Anna nayi rashinki kusa dani nayi kewar ɗuminki nayi kewar komai naki naso ace kina tare dani dukda auren naɗan wani lokacine amma nasan zakiyi farin ciki daganin wannan rana,haka tayi ta sumbatu tana kuka. Ɓangaren amarya basma kuwa yau suke party da ƙawayenta a wani hotal da ganin yanda aka tsara wajen kasan naira tayi kuka basai an faɗama ba,wajen kansa sai kanada get pass sannan zaka wuce taso ango ya halarci wannan taron saboda abokanta da suka zazzao daga nesa wayanda sukai karatu tare amma yaƙi kaman zatayi kuka haka tasamu daddynta da magana ya rokar matashi koda minti ashirinne yabata cikin lokacin sa. Lokacin da Alh sunusi yakira wayan sa yana hanyansa ta zuwa gidan Anty hajia dan Anty malika ta kira ta faɗa masa tun safe Aisha take kuka taƙi cin komai kuma ko ƙunshi taƙi yarda amata da yaso basarwa amma ganin tanada hakki kansa yasa shi yace gashin nan"da sallama ya ɗauki wayan bayan sun gaisa sai Alhaji sunusu yace"am kana jina ko? "Eh inaji Alhaji "Dama ina neman wata alfarmarce dan Allah ko zaka aramana minti goma lokacinka idan ba damuwa? Dan shiru yayi be amsa masaba sai da yasake cewa"hello ko baka jina ne? "Ina jinka saide ina da abunda nake yanzu ko zamuyi magana a waya ina sauraron ka? "No ba maganan waya bace dama cewa zanyi ko zaka halarci party da basma zasuyi yau na yau ɗaya kafiddata kunya saboda abokanta da sukazo na nesa,cikin ƴar ƙaramar murya yayi maganan. "Banajin zan iya halartan koma wani kalan party ne dan munriga da mun yi wannan magana da ita tun farko,inma duniya gaba ɗaya zasu halarci partyn ta to karta saka dani so yanzu banga abun damuwa ba. "Amma abunda zakayin yafi zuwa kafiddata kunya mahimmacine? Alh sunusi yasake tambayansa danson yaji mai ze hanashi zuwan. "Eh Alhaji kusan hakane dan yanzu haka ina hanyata ta zuwa kai matata ƙunshi ya amsa basa cikin halin ko in kula. Daga basma har mahaifinta suman wucin gadi sukai sannan basma ta fizge wayan daga hannun mahaifin nata tasaka masa kuka a ganinta ko ze tausaya mata yace zezo......manage this   ALLAH YASA MUDACE [7/23, 9:04 AM] Xeenat: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 59 Fizge wayan hajia mariyah tayi daga hannunta tana kallonta cike da fushi tace"amma anyi shashashan yarinya wallahi bakiyi kuka a gidan ubanki ba sai ga gadin miji tunma kafin kishiga wannan idan kuma kin shiga ciki yakenan? Faɗawa tayi jikin umman nata tace"dan Allah mummy kiyi wani abu wallahi ina sonsa zan iya yin komai saboda shi,bansan abunda yasa yatsani har haka ba wallahi mummy dan Allah koke zaki gwada kiransa a waya ki bashi hakuri yaxo ya fiddani kunya. Kallon baki da hankali tamata sannan ta juya ga Alh dake hakimce tawatsa masa wani muguwar harara tace"wallahi Alh kabani mamaki har yaushe zaka biyeta ka zubar da ƙimanka ga wannan yaron mara kunya da besan mutuncin na gaba dashi ba,idan kai bega girmanka ba ai yasan girman uban da ya haifesa kai kuma kana da iko da uban nasa kira ɗaya zaka masa kafin nan nikuma yanzu zani wajen mai charbin ƙwai ba matarsa ba har uwar da ta tsuguna ta haifesa inaga sai yanance sunan ta bare wata mata tashi kishare hawayenki jeki kici gaba da shirinki zuwane kaman yayi kai kuma sai ka amshi wayan kakira uban nasa dolene ya turasa. Daga haka tasa kai yafita daga falon tana magana da ƙawarta hajia shema a waya kan su haɗu a hanya dan zuwa gidan mai charbin ƙwai. **** Aisha ƙudundune take cikin duvet tayi luf tana sauraron yanda kanta ke sara mata ji tayi anyaye mata lulluɓin saurin runtse idonta tayi dan duk a zatonta ta ɗauka anty malika ce da tun ɗazu ta dameta data tashi ta wanke bakinta koda tea ne tasamu tasha saide tsaɓanin tunaninta jin ƙamshin turaren sa"oya tashi yafaɗa mata muryar sa ba wasa ciki miƙewa tayi zaune dafe da kanta dake barazanar rabewa biyu. Amshi nan miƙa mata kufin hannunsa yayi ɗan kauda kanta gefe tayi zaki karɓane ko sai namiki ɗaure yanzu yafaɗa da kakkausan murya,tura bakinta tayi tana ɗan mutsu mutsun kaman mai magana oh zagina kikeyi ko? Sake tura bakin tayi batare data amsa masa ba,wayansa ne yayi kara hakan yasashi fita daga ɗakin bayan ya dire mata da kofin tea yana cewa minti goma nabaki ina jiranki kisame ni waje karki kuskura nasake shigowa nasamu baki shirya ba,daga haka yasaka kai yafita yana amsa kiran. "Assalamu alaikum daddy barka da warhaka yafaɗa kaman yana kallon sa cike da ladabi. Madadin daddy ya amsa masa sallamar sai cewa yayi"to sannu ishasshe nace sannu ishesshe tun daga nan ya fahinci inda daddyn nasa yadosa dan haka cike da zolaya yace"Alhaji wai lafiya kuwa irin wannan fusatan haka kasanfa ni yau nake ango dan yanzu haka ina shirin kai surukuwarka wajen ƙunshi gashi naga kaman...."dallah rufamun baki wanda besan inda yake masa ciwo ba,yanzu Ahmad saboda Allah ga inda akeson yima gata amma kaɓige da shashanci"wai Alhaji mai akace nayine? "Yanzu kaman Alh sunusi yakira yana neman alfarman yau kaɗai kaje wajen taron yarinyar nan kona minti goma amma ka iya bude baki kace masa bazaka ba wai....katse mahaifin nasa yayi yana cewa"daddy dama saboda wannan kka fusata nifa na mijin mata biyune Alhaji yakare magana cike da zolaya. Jin abunda yake fadin yasake tunzura Alhaji badamasi sai faɗa yake ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba karshe yarufe da cewa kashirya anjima karfe bakwai na dare kutafi kodasu khalid ne wannan umurni nake matsayina na mahaifinka idan ko kaki tafiya to wallahi ran uwarkane ze ɓaci dan nasan ita ke zugeka. saka Amminsa ciki yasa shi yaruntse idonsa cike da ɓacin rai zuciyarsa na masa suya can yace"Alhaji tun tuni munyi da ita bazan halarci ko wani irin taronsu ba,kuma ta amince sannan kuɗina ko kwandala na bazeyi ciwon kai ba"ai idan naka beyi ciwon kai ba ni nawa sunyi dan duka party goma da sukayi nina ɗau nauyin bakwai daga ciki kama daga abunda zaci awajen da abun sha da biyan kudin hall da zasu gudanar da taron kai harma da makaɗa da za gaiyato duka"yanzu Alhaji a wannan marran dakuma halin da kake ciki shine...."dakata mun Ahmad yakatse sa cike da fushi wai kaine ka haifeni ko nine na haifeka? "Kai ka haifeni ya amsa cikin sanyi murya. "To inde ni na haifeka to kashirya zuwa ba ruwanka da halin da nake ciki abun kunyane gareni ace ɗana ze auri kaman ƴar Alhaji sunusi amma ina da kuɗin nakasa ɗaukan ɗawainiyar komai na barmasa,sannan ita wancan mata taka ban amince da tare warta nan kusa ba,duk da dama ni banwani dauki auren nan a aure ba dan nafi daukansa da auren wucin gadi kokuma auren jingina. "Alhaji yanzu bakaji kunyan tattauna irin wannan da danka ba,kai da yaka mata kaimasa addu'an Allah yatayashi riƙo amma kake wani zance mara dadin ji da sauraro to wallahi kasa aranka cewa wannan da kakewa fatan auren jingina ko na wucin gadi in sha Allah itace wacce zakayi alfahari da ita gaba,dan wannan ƴar gwal ɗin taku da ubanta ba komai suke yiwa ba sai abun hannun ka ina kyautata zaton akwai abunda wannan mai ido a tsakar kan yakewa bazaka taɓa ganewa ko kayarda ba sai lokaci ya ƙure maka idanma bacci kake ka tashi wallahi ko wannan abunda yafaru dakai bana zargin kowa sai shi tabbas dasaka hannun sa ciki wallahi Allah ko kaffara bazanyi ba,sannan kuma bincike da ake shine ze kara tabbarwa da shidinne da sannu zaka gane bason Allah yake maka ba. Tunda Ammi ta soma magana yayi saroro yana kallonta ko kiftawa bayayi saida ta dire sannan yasamu zarran cewa"amma ma'arufa bantaɓa sannin ƙiyayyarki da Alhaji sunusi yakai kimasa sharri ba sai yau yana fadin haka mikewa yayi yayi wucewarsa daki. Hajiya mariyah da kawarta hajia shema ne gurfane gaban wani gajeren mutum mummuna da wagege baki hanci kaman ƙofan kasuwa..bude baki tayi da nufin tamasa bayanin abunda yakawota saurin dakatar da ita yayi da cewa"tun ma kafin kuzo anfaɗamun so kuke yaron nan yanuna musu wani ƙwaya dake gaban sa cike daruwa matso kugani matsowa sukai ai kuwa azabure suka ja baya ganin Ahmad tsaye jinjine jikin mota waya kange a kunnesa yace ko bashine ba. Saurin amsa masa sukai cikin rawr murya da"wallahi shine"ai kinku mai saukine amma sai kunsamo mana sunan ita matar tasa da kuma ta mahaifiyarsa sai kuma bayan ita mahaifiyarta sa akwai wata ɗaya da ita ke juya uwar yaro bata iya tsalleke maganarta ba. Ina zuwa tace sannan ta kira wayan mijinta yana dauka tace"Alh wai ya sunan mahaifiyar yaron nan ne dan malam yace sai an samo sunan su sannan aikin zeci,dan jim yayi kaman mai tunani sai can yace"marfu'at ne ina ji"kana tantamane?kode ka tabbata karfa asamu matsala Alh"hakanne ma ita kuma matar tasa kibari zan tambayo badamasi idan yaso ko a waya kyafada masa zuwa gobe"tom ta amsa tana kashe wayan. Cike da kwarin gwiwa ta faɗawa malamin sunan sannan ta daura da cewa"sunan ita matar tasa zuwa gobe zankira ka ko ta waya idan yaso nasanar dakai"ba matsala yace. Dan Allah malam aiki mai zafi nakeson ai mun akansu so nake wannan yaron yamace akan yarinyata sannan inason a dasa tsana mai tsanani tsakanin sa da iyayensa shikuma yazama bashi da maganan kowa saita basma duk abunda yasamu da wanda ya mallaka duka ya mallaka mata. "Wannan shiyafi komai sauki amma kafin sannan duk yanda zakuyi kuyi dan ganin be tare da matarnan tasa sunyi taraiyar ba idan ko ya tare da ita duk aiki da mukai ze karye karshe komai ze koma kanku dan haka ku kiyaye kunisanta shi da duk inda kukasan yarinyar take idan baya ganinta baze taɓa tunawa da ita ba. Kayan aiki muna bukatan hantan baƙar karya da huhun cinnaka sai maniyin sauro da sune za haɗa maganin. "La'ila ha illallahu"yimun shiru yadaka mata wani gigitaccen tsawa dayasa duka dajin amsawa rai a mugun ɓace yacigaba da cewa kinsan da Allahn kika kawo kanki wurin mu"tuba nake ran malam yadaɗe ruɗewa nayi"ki kiyaye gaba dan duk wanda kika gani anan ya kauce hanyane ɓatacce kaɗai kanzo nan. "Tuba muke baza kara ba suka faɗa kaman zasuyi masa sujuda. "Yawuce yanzude ku chake kuɗin da zabada dan nemo muku kayan aikinku aikinmu kaman yankan wukane"munsani ran malam yadade amma dan Allah aimana sassauci kar atsuga mana kuɗi dayawa shekara da shekaru muna tare. "Hakane yanzu de kuɗin kayan da nafaɗa dubu ɗari biyar zaki bada sannan zaki bada dubu ɗari da hamsin kuɗin kafin alkalamin aikinki idan aiki ya kammala saiki cikatomun da dubu hamsin. Jiki na rawa ta ciro damin kuɗi cikin jakarta ƴan dubu dubu sabbi kar dasu ta ajiye masa daukan kuɗin yayi yana shinshinawa yana babbaƙewa da wani irin dariya mara daɗin sauraro saida ya tsagaita da dariyan sannan ya ɗaga hannun sa sama saiga wani ƙullin magana ya miƙa mata yace duk yanda zakiyi kiyi yau din nan ki tabbata kin bada anzuba masa a abinci ko abin shansu dan yau shine ranarki ɗan tsuku yana kan aiki shi kuma yaron ze zo taron da tawagarsa dan haka amshi nan hanzarta kar asamu matsala kuma duk yanda zakiyi kisa ƴarki ta tambayo sunan matar tasa kutashi kutafi,kufita da baya da baya kutaka a hankula karku taka mana yara suna wasa duk sun tsure baramma hajia shema da bata taɓa zuwa irin wannan wajen ba. ***** Aisha tunda Ahmad ya fita a ɗakin zaune tayi bakin gadon dafe da kanta yafi minti talatin kafin yasake shigowa ɗakin yanda yabarta haka yashigo yasameta tunma kafin ya karasa shiga dakin yasoma tattare hannun rigarsa kaman mai shirin kaukawa da gefe idon take kallon yanda yake takowa da karfin sa fuskar nan tasa ba alamun rahama a tare da shi take taji cikin ta yasoma kugi kuuuuuuuuu wani kakkauran ƴawu ta haɗiye mukut miƙewa tayi da hanzarin ta dan shiga toilet tama kanta maɓoya saide tana miƙewa taku ɗaya biyu taji anyi sama da ita buɗe bakinta tayi da nufin fasa ihu kaman ko yasan abunda zatayi yayi saurin rufe mata baki da ɗaya hannun sa.   ALLAH YASA MUDACE [8/13, 4:56 PM] Xeenat: https://www.wattpad.com/1366365575?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=MH6%2FgYRjdzvQHp3kuIwmYWnw1bbyj4AA6GwB6tkm80Cdg2uzJFh0PfLUUGOy8NI2D6OCLkXYfxsWaRHeV2wjpel017eJ7tYg%2FAbhVbW8giNKLXbkkDbG1Cbu%2B1Gwt6XI ____________ *AURE WUCIN GADI* CHAPTER 60 Zaro idonta tayi kaman zasu faɗo ƙasa tasoma wutsul wutsul da kafanta ba bakin magana saboda rufe mata bakinta da yayi da tafin hannun sa ɗaya sai"um um um kawai ta iya cewa. Falo yanufa da ita a hakan daga ita sai ƴar riga mara nauyi da tasa na shan iska"me zan gani haka ni ikilima yau sauke mun ƴa Anty hajia ke magana daidai shigowan sa falon ɗauke da ita kaman wata ƴar tsana. Kusan duka waƴanda suke zaune a falon miƙewa tsaye sukai idan kacire yah faisal da kallo ɗaya yamasa yacigaba da aikin da yake a systerm din da ke saman cikinyan sa fuska ƙunshe da murmushi. "A'a Anty hajia dan Allah karki tsaidani taurin kai takeson yimun idan bata bini a hankali ba wallahi fitan da zanyi da ita ta tafi kenan wai kaman ni zan bata umurni amma yarinyar nan saboda taurin kai ko motsawa batayi daga inda take zaune ba,almost 30mnt nabata dan ta ƙimtsa amma tayi kunnen uwar shegu da maganana"to naji yanzu de sauketa yi hakuri ta fada tana nufosa dole yasa yadireta badan yaso ba,sake tamke fuska yayi yana kallon wani direction ɗin yace"hijabi kawai zata ɗauka tazo mutafi kokuma...."a'a bazayi haka ba ta dakatar dashi dafaɗin haka yanzu de dan barmun ita tayi koda breakfast ne. "Ai taƙoshi kuma anty hajia idan ba abunki ba ina kika taɓa ganin ango bayar amaryar sa da yunwa ai tattaleta zanyi ai gwara ni na zauna da yunwa da in barta dashi ki yarda dani yakare maganan cike da zolaya. Sannan ya ɗan kalli faisal da khalid dake tsaye ƙiƙam kaman dogari yace bros anjima around 8 zaku rakani wajen taron wancan yarinyar,baki sake suka bisa da kallo"wace yarinya? Khalid yayi karfin halin tambayan sa duk da yafahinci wa yake nufi amma yaga tunda suka fara shagalin su ba wanda ya hallarta"daddy yakira yanzu yake tamun faɗa dan nace bazani ba yasake faɗin haka da damuwa kwance saman fuskan sa. Ke malika ki haɗo mun da kayan da zata canza kuma na gayyace ku dasu umma salma gaba ɗayanku kuje,murmushi faisal yayi ya ajiye aikin da yake gefe sannan yace"kai akeson gani ba wasu tarin yara akeson gani ba har kana wani gayyato su auta kaide kawai zamu maka rakiya dan fidda kai kunya gani ga khalid sai nawwar zan kira dr sapwan a waya anjima inaga mun wadatar ko?kai kawai ya gyada masa. Amma zancen wayannan yaran barsu a gefe sannan ita Aisha kabarta su tafi da malika tunda....saurin katsesa yayi da fadin nine zan kaita ai taƙi tafiya dasu malikan tun tuni yana gama mafadin haka yaja hannunta tana turjewa tana me yafita da ita,saida yasata mota ta zauna ya kullo ƙafar sannan shima yaxaga yashiga ta ɓangaren driver yaja suka fita daga gidan dan duk yanda Anty hajia taso sutafi da malika tare ƙi yayi daga karshema sai ce mata yayi wai anti hajia tsoron me kike?nagade matatace ina da hakkin keɓewa da ita da sauri anty hajia tashiga tattaɓa kunnenta da hannu tana cewa"kaide baka da kunya sai ku tafi amma ka maidomun da ƴa da wuri dan bazan lamunci...."haba anty hajia ki barsu su tafi kina ɓata musu lokaci cewa malika dake zaune tana daddana waya wani irin harara Aisha ta zabga mata ganin kaman tana sake zugashi. Tunda motan yafita daga cikin gidan ya hau saman titi kawai sai taji hankalinta ya tashi tashiga rera masa kuka duk yanda yaso basarwa kasayin hakan yayi dan jin kukan nata yake harkasan ransa,samun gefen kwalta yayi ya faka motan ya juya ya kalleta fuskar nan tasa tamƙe kaman hadarin gabas yace"idan baki rufemun bakin kindena wannan ɗan iskan kukan bako to wallahi tafiya da zanyi dake kin tare kenan har sai randa zamanki na wucin gadin ya kare sannan zan maidoki,mukut ta haɗiyi wani abu mai kauri tashiga kunkuni yasanta da tsiwa dakuma rashin tsoro maidawa mutum martani inde abu beyimata ba,tada motan sa yayi yasoma tafiya sai ya tsinkayi muryanta cikin kuka tana cewa"ai wannan zaluncine auren rashin gata dan kawai anga iyayena basa raye har kana wani ikirari da cewa auren wucin gadi zakai dani dan kawai anga bani da gata saboda rashin sanin darajan mace,jin yanda ta taƙarƙare sai zuba take yasashi dakatar da ita ta hanya cemata"ba gwara ni ba ko banza kina kasarki ta gado kuma ai zaman namu naɗan wani lokacine da zaran nasamu abunda nake nema kinga sai nasallameki kikoma ga wanda kikeso kafin sannan kinyi girman da zaki iya rayuwa koma a inane,amma da yanxu na bari mai jan kunnen nan ya aureki kinga nafarko barin ƙasar zeyi dake sannan abu na biyu ba lalle ƴan uwansa su amsheki matsayin surukuwa ba saboda bambancin launin fata,gani nayima taimakonki nayi tunda banbijire wa Ammina ba na amince da aurenki na amsa ai godemun yakamata kiyi. Wani tuƙuƙin baƙin cikine ya turnuƙe mata zuciya ita akaima aure ana rokonta alfarma tayi hakuri ta zauna dashi amma yanzu saboda yafita baki harze wani ce taimakonta yayi Allah sarki suhail masoyin gaskiya ko ina yake? Ya zeji idan akace tayi aure tunawa da masoyinta na gaskiya yasata sake barke masa da wani kukan har batasan sanda suka iso ba,saida taji yace"to ai sai ki sauko sannan ta bude idonta da tunɗazu tarufe da tafin hannu ta kai dubanta ƙofa ashe harya zagayo yabude mata ƙofa yace kinga ni ai mutumin kirkine maison kyautatawa na ƙarkashin sa,batade ce masa komai ba sai ƙoƙarin saukowa datake saurin dakatar da ita yayi ta hanya cewa koma ki zauna kawai yanzu a hankanki zaki fita kowa ya kalleki,kallon da tamasane yasashi ankarewa da ɓaram barama da yayi sai kawai ya fuske da cewa karki dauka wai kishinki nake nop kawai kinsan ko banza da igiyar aurena akanki dole na kare abuna dukda auren na wucin gadi ne. Batasan sanda tasaki wani mugun tsaki maitsawo ba mtsssssss aduk sanda yabude baki yace auren wucin gadi yayi da ita ji take kaman ta shaƙo masa wuya harsai yadena numfashi ta barsa. Yiyayi kaman beji abunda tayin ba,saima wayansa daya ciro a aljuhun wandon sa yashiga kiran wata numbar itade taji yace gamu nan a waje sai ya kashe wayan ya dan juya ya kalleta yace saura kuma kiyi mata taurin kannan da kika saba idan baki bari anyi miki komai abunda yadace ama amareba wallahi wallahi kinde ji na rantsa miki ko daga nan sai.....sauri katse shi da cewa"ni nacema bazan tsaya amun bane ai ko jiya danaƙi binsu anty malika kaina kemun ciwo mutum bashi da magana sai ta tarewa wama yace maka zamu taren ai bazamu taɓa tarewar nan ba kaman yanda kadauki auren nan a na wucin gadi haka kuwa ze kare a wucin gadi kaida ganin tarewa kuma saide ta wancan mai maka da zabiyan naka,takare magana tana cinno bakinta. Daidai wata mata da ganinta kaga shuwa da fara'arta ta nufosu gaisawa sukai Ahmad sannan Aishama ta dubeta ta gaidata cikin sakin fuska ta amsa tana cewa wannan itace? "Eh itace hajia ya amsa. "Ok to shikenan taho ƴata mushiga ciki ta faɗa tana riƙo hannun Aisha datake tsaye ƙiƙam tana kallon su"hajia duk abunda kikaga yadace ayi mata to ayi sai anjima zanzo ɗaukanta yafaɗa yana dan sosa kansa alaman kunya dariya matar tayi tace"baka da matsala Alhaji in sha Allah zaka yaba da aikinmu sannan ta daura da cewa hala amaryace ko? Dan kallon inda Aisha ke tsaye yayi sai yaga itama ta kafesa da nata idon donson jin amsa da za bama matan sai ji tayi yana cewa"a'a kanwa tace kuma itace babbar ƙawar amaryar da zan aure kinga dole in fitar da ita saboda harkace ta manya ko zansamu mai tayawa wani irin tuƙuƙin taƙaicine ya turnuƙeta har batasan sanda ta gallah masa uwar harara ba tace da matar"hajia mushiga daga ciki bana juran yawan tsuyuwa daga haka matar tamasa sallama suka shiga cikin shagon nata,babban shagone sunayi gyaran jiki lalle ja da ɓaki halawa dilka wanke gyashi suna kuma sayarda turarukan humra dasu turaren wuta nasawa a daki dana turara kaya da ƴar tsugunne kana shiga wajen kamshi da sanyi wajen kawai ze sauke maka da wani irin ni'ima da nutsuwa haka ya kasance da Aisha dan duk wani tura haushin da Ahmad yamata sai taji tanemasa tarasa sai wani irin nishadi da ta tsinci kanta ciki wajen haɗu iya haɗuwa ga ma aikatan wajen sun iya tarɓan bako ga faran faran da jama'a snack da lemo mai sanyi aka fara bata taci tasha lemon kafin a wanke mata kai sannan daga bisani aka daura mata jar lalle daga gama lalle Aisha ta ɓingire a wajen sai bacci tayi bacci sosai kafin ta tashi sallati dauke a bakinta tayi mamakin yanda tadauki lokaci tanayin baccin saide ba abun mamaki bane duba da yanda bata samu tayi bacci daren jiya ba. "Kin tashi matar ta tambayeta?cike da kunya ta amsa da"eh wallahi tashi tayi daidai matar takira wata mai suna larai zo kicire mata lallen nan tayi sallah cike da cika umurni wacce aka kira da larai tazo tacire mata lalle masha Allah suka faɗa atare duba da yanda lallen yakama yayi maroon shar dashi ga kuma yanda yankan gum din ya zauna raɗau tashu Aisha tayi larai ta nuna mata toilet tashiga tayi alwala taxo tayi sallah sannan matar nan da kanta ta jata wani ɗaki na daban ta bata xtra zani ta daura sannan ta umurceta data zauna saman kujera ƴar tsugo zama Aisha tayi wannan hajiyar tashiga mulketa da nau'in abubuwa kala kala shafa wannan goga wancan lakuta wannan saida tagama dirza mata jiki tass sannan ta kawo ruwan lalle tamata wanka da shi sai kuma ta saka itacen dorot data magarya saina habil tasake cewa Aisha tazo ta zauna saman wata kugerar wacce tsakiyarta da huji zama tayi bayan hajiyar nan tasa waƴan nan ice dana lissafo cikin wani rami ta zuba garwashin wuta ciki take wani hayaki mai dadin kamshi yafara fitowa daga cikin ramin bargo ta dauko ta lulluɓama Aisha sai kanta kawai data bari waje tun Aisha na daukan abun da sauki harta soma gajiya da zaman sai wani irin zufa datake ssaida aka dauki akalla minti talatin sannan hajiyar tazo ta yaye mata bargo ta mika mata zani ta daura suka fita a ɗakin zuwa wani ɗaki na daban,sannan tamika mata wani kufin sulba cike da kunu amsa Aisha tayi dukda batasan kunnun name nene ba amma taji dadin kunnun tana gama sha aka tsantsara mata bakin lalle saman jan ba karya ko ita kanta taji bambanci sosai ajikinta ga wanj irin fitinannen kamshi dake tashi ajikinta sai sheƙi data gashin kanka nayi mata gyara namusamman kana ganinta taga amarya Aisha haka kawai ta tsinci kanta da farinci sai sakin murmushi take ita kaɗai idan ta dago ta kalli kanta ta cikin madubi dake cikin ɗakin. Hajiya mariya suna zuwa gida ana kiran sallan magariba saboda nisan da dajin da bokan yake da cikin gari a gurguje taje ɓangaren ma aikata tana shiga inda ake girke gurke duka ma aikatan suka zube suna gaidata amsawa tayi da tambaya ina ogansu wani farin dattijone yafito ta wani ƙofa sanye yake da farin kaya da wani dogin hula gaisheta yayi yana cewa"gani hajia wani abu kuke bukata kallon sakon goma tamasa sannan ta amsa"da eh dama inason ganin me da me kuka shirya na tarɓa baki kasan nan da kaman awa daya za fara gudanar da party ko?"eh nasani ranki ya daɗe anma gama komai ya amsa mata cikin rawar jiki"ok mugani wucewa yayi tana biye dashi a baya yafara nuna mata komai ta kuwa yaba yajidaɗin yaba musa datayi godiya yayi harze juya tace"jimana komowa yayi ya tsaya kansa duƙe yana kallon kasa kuɗi taciro cikin jaka tamiƙa masa tace wannan nakane sannan inason zakamun wani aiki zan maka sallama mai tsoka dazaran kamun yanda nakeso"wannan ba komai bane hajiya ya amsa mata cike da jin dadi ta ciro ƙullin magani cikin jakar hannunta tamika masa tace wannan nakeson kazuba ma angon cikin abunci dana sha da anjima za bashi dan Allah kada kabari wannan dama tawuce ni,yanda ta marairaice masa kaman zatayi masa kuka yasashi amsa dan idan yace bazeyi mata ba besan abunda ze biyo baya ba dan yasan irin wayan nan matan daba Allah ne a zuciyarsu ba zata iya masa wani sharrin tunda yasan tasan sirrin sa.     ALLAH YASA MUDACE [8/13, 4:56 PM] Xeenat: https://www.wattpad.com/1368788145?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=Es%2FpDd6QfWsguCJy8Xl3clX5MAEfLOAl918L4Z7n%2FKzK1sjbc4fXDKmctA75qklPBs%2BWm5DZKKxGX7m%2FcWzCwC5zOKajc4E9r63sykA4d%2Beb7su211hiMeRlL18l%2FqdU ____________ *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 61 Jujjuya ledan data tamiƙa masa yafara sai can yace"hajia gaskiya aikinki mai saukine sannan da wuya abunda yasa nace haka nide nawa zubawa ne kawai amma sakashi yaci wani abun ko yasha wannan badaga ni bane dan haka shine wuyan da nace,dole sai annemi wanda ze ja hankalin sa yaci abincin ko kuma yasha juice ɗin,shin kina da wanda ze aiwatar miki da wannan ko babu idan babu ko kinga xubawan asarace. Saurin ƙatseshi tayi ta hanyan ɗaga masa hannu tace"banason jin an anbaci asara nan"to hajia ga shawara kice da amaryar tayi iya yinta dan ganin ta bashi koda juice ne yasha"shawara mai kyau tace dashi harta juya zata tafi sai kuma ta juyo tace dashi ka kula wajen zubawan kar wani yagani"baki da matsala inde wannan ne kede kiyi ƙoƙarin dan ganin yasha ko yaci wani abun shine kawai daga haka sukai sallama da cewa sai yajita. Tana barin wajen daddy ishaq ya ƙwashe da dariya yaron sa kamilu ya matso kusa dashi yana cewa"oga da alama waƴan nan mutanen basuda imani haryanzu idan bacin haka yaushe asiri yake tasiri aiko yayi naɗan wani lokacine"ai kamalu basu sani ba kuma bazasu san kuskure da suke tabƙawa ba harsai ranan da reshe ya juye da mujiya tukun zasu sani,ai yanzu idona nakan duk wani motsin su kafin a gama wannan bikin ko zan samu nasaran ƙusawa cikin masarautar su ko kuma sai yayi shiru....."karka damu oga in sha Allah saikayi galaba a kansu wannan karon Allah yana tare da mai gaskiya yafaɗa cike da bashi gwarin gwiwa"hakane ya amsa yana komawa ciki. Hajiya mariyah gaskiya keɗin gwaskace shiga irin wannan ƙatsurgumin dajin wallahi tunda muka tafi bansamu nutsuwa ba harsai da naga munshigo gari kuma cikin gida sannan naji hankalina ya kwanta,dariya sosai hajiya mariya tayi tana kallon hajia shema tace"ai bari shema nima kaina dayace mu fita a hankali karmu taka musu yara suna wasa wallahi karfin hali kawai nayi amma da kin lura lokacin zakiji yanda cikina yake ƙuji wallahi dariya suka kece dashi a tare sannan hajiya mariya ta kwalawa mai aikin ta kira ta kawo musu abinci da abun sha,saida sukaci sukai nak sannan suka daura sabon hira dakuma yanda zasu ɓullowa basma tabawa Ahmad koda juice ne yasha kada asamu matsala dan sanin halin basma da shashancin kartasa muyi zuwan banza. "Kaman kin shiga zuciyana kin gani abunda nake tunani kenan nima shema tunda boka yabani maganin hanyan da zanbi nazuba masa a abinci nake ta tunani to wannan an wuce wajen dan fitan da nayi da muka shigo ai naje nasami wanda zemun wannan aikin ne saide shima ce mun yayi nashi mai saukine wanda zesa ya danci wani abu ko shan waje abun shine kawai. Ɗan shiru sukai kaman masu tunanin wani abun sai can hajia shema tace"yauwa gawani shawara ki kira ita basman yanzu,ba musu kuwa hajia mariya ta dauki waya ta kira basma bugu daya biyu sannan aka ɗaga tunma kafin tayi magana tace"kisameni a ɗakina yanzu"to mummy kin dawone?"eh na dawo yi sauri kizo karki batan lokaci muna tare da mummynki shema kuma tafiya zatayi yanzu"tom mummy gani nan zuwa daga haka ta katse wayan tana kallon salaha tace"ina zuwa yanzu mummy nakira na daga haka tasa kai tafita daga dakin tabar ƙawayenta da mai makeup dasuka gayyato. ********* Wow kinga yanda ƙunshin nan yamiki kyau kuwa?gaskiya na dade banga wanda gyara ya amshi jikinta ba farat ɗaya irin ki,takare faɗin haka fuska ƙunshe da murmushi. Murmushin ita Aisha ta maida mata tace"kai hajia karki saka kaina ya kumbura naringa jina a sama,dariya tayi tana riƙe haɓa tace oh ƴar nan dan ma kinsamu na yaba to bani ba bari wanda yakawokin yazo dan nasan shima kansa sai yayaba yakuma karamun da tuƙwici dan wannan gyaran babbar harkace dukda yace keɗin ƙawarsace amma ba komai nasan ze yaba kuma dan Allah ko raran aurenki karki mance da nan kizo ko gayyatana kiyi har gida zanje namiki gyara na musamman na amare tsawon sati biyu zamuyi wallahi sai kinga yanda jikinki ze dawo tamkar balarabiya ai ingaya miki munan bama wasa wajen inganta aiyukanmu kayan mu masu ingancine dan daga sudan muke oder nasanma dole yallaɓe yayaba irin kyaun da kikayi"hajia kenan kita wani yayaba aiko be yababa ni nasan aikinki yayi tunda naji wasu ƴan canje canje ajikina ba karya. Gyara zama tayi tana fuskantar ta tace"yama kike da suna?"Aisha ta amsa mata da Aisha"yauwa Aisha kinganni nan niba karamar yarinya bace dazaku raina mun hankali kuna wani ɓoɓɓoye mun shi yace ke ƙanwarsace amma irin kallon da yake miki yafi karfin yah da kanwa,zakice na fadamiki wataran tabbas akwai soyayyarki na gani a kwayan idon sa,ƙila shima besan yakamu da son naki ba,amma nide abunda zance dake shine ki kula karkiyi wasa da wannan daman naki,sau ɗaya tak kake samun dama a rayuwa dan haka karkiyi sake wannan daman yabarki. "Kaman yaa hajia?bayan mudin ba wasu masoyan bane babu komai tsakanin mu kaman de yanda kika fada ina ganin kawai hasashe kawai kikayi amma ina ni ina auren mutum kaman Ahmad ina ga gami,ai kinsan yafi karfina kota wani fanni,dariya hajiar nan tayi sosai saida ta tsagaita sannan tace"lalle Aisha har yanzu kina fama da yarinta amma in banda haka ina ruwan so da matsayi kyau ko muni so ba ruwansa da wannan karkiga matsayin da kikaga Ahmad yana da ya tsorata ki haƙiƙa ninasan koman daren dadewa Ahmad ze furta miki kalman so kar gayun sa da kuɗinsa ya tsorataki abu daya zan faɗamiki shine ki kasance wayayya ki kuma kasance ƴar gayu dan mace da gayu akasanta sannan kiyi kokarin sanin me dame yafiso me yafi birgesa sannan kuma meyafi sha'awa wani irin abinci ko abun sha yafiso arayuwarsa wani irin kwalliyane yafi burgesa ga ɗiya mace shin ma'abocin son saka ƙananun kayane ko yafi sha'awar kayanmu na hausa wani irin ƙamshin turarene yafi burgesa da ɗaukan hankalin sa,sannan uwa uba ki iya girki wannan shine babban makaminki ƴa mace duk kyaunki da iya ɗaukan wankanki idan vaki iya girki ba kinzama hotiho baki da sauran amfani sannan muhallinki yazama ko da yaushe ashare cikin ƙamshi. "Hmmm wai hajia meyasa kike faɗamun duka wannan abun?kanta tsaye tace"saboda nasan wataran zeyi miki amfani kuma inason kifara rihazal daga yau ai tsakanin mata da mijinta babu shamaki idan yace yafison yaganki daga ke sai ɗan kamfai yi kokarin ki zauna masa hakan dan faranta masa"hajia mubar wannan maganan kawai dan ko ɗaya bana fahintarki,tafaɗa cike da ƙosawa dakuma gajiya da maganan dan hajiyar nan idan kabiyeta irin matan nan ne masu shegen surutu da son jin ƙwakwafi da son shiga sharo. Basma tafiya take ma aikatan dake aiki a gida sai zubewa suke suna gaisheta duk inda ta wulga amma ko kallo basu isheta ba,tana gab dashiga ɗakin hajiarta suka kusa cinkaro da lantana mai aikin gidan nasu tafito daga ɗakin ɗauke da kayan dasu hajia suka gama cin abinci batayi wata wata ba ta zabgawa lantana mari da hankaɗata gefe tanunata da yatsa cikin ɓacin rai take magana"wace iriyar yarinya ce ke?kina tafiya kaman tunkiya kai a ƙasa tashiga dudduba jikinta taɗaura da kinyi sa'a da baki batamun jiki ba da yau sai kin raina kanki. Lantana data maru dan marin yashigeta gashi kuma da tray a hannun ta balle tasamu zarran dafe ƙuncin ta sai hakuri take bata a zahiri amma a zuciya sai Allah ya isa datake jamata tare dayi mata mummunan fata a gidan auren ta"ɓacemun da gani sai warin baki kike anƴa yau kinma wanke bakin kuwa?cike da jin haushi lantana ta amsa mata dacewa"dayake man wanke bakin da kika sayumun sun ƙare tun wancan wata,dakamata wani irin gigitaccen tsawa tayi dayasa lantana zabura ta kwasa da gudu saura kaɗan ta ɓarar da kayan hannun ta,ganin yanda ta kwasa a guje yasa basma taɓe baki tana cewa kaga wani shashanci kuma. "Kedawa?Mominta ta tambaye ta sanda ta bude ɗakin ta shiga dan ganin yanda tayi kicin kicin da fuska"ni da wa in banda wannan shashashar mai aikin naki mummy wallahi bakiji yanda take hamami ba"kinga zauna nan ya'isa ni banji wani hamami da take ba,sannan kamata kibar wannan ɗabi'ar nan naki na wulakanta ƴan aiki tunda kinsa hakan yana daga cikin abunda Ahmad yatsana ke bazaki iya controlling temper ɗinki bane ba"mummy takira sunan tana wani marairaice fuska"to ai shikenan amma hakan yana daga cikin abunda bazamu nema miki mai aiki ba,dan gudun samun matsala tsakanin ki da mijinki,zatayi magana tayi saurin katsata da ga mummyn ku nan ki gaisheta tafiya zatayi yanzu dan su hanan su zo akan lokaci. "Ina yini mummy ta gaisheta bayan ta juya tana fuskantar ta"lafiya lau baby ta amsa da fara'a kwance saman fuskanta taci gaba da cewa yau kuna da party babban harka tunda yau ango ze halarci wajen,dawani irin sauri takai tubanta ga hajia shema ta zaro ido danson jin ƙarin bayani eh ai ɗazu daddynki yakira mahaifin sa yamasa fata fata dan haka umurni yasamu daga wajen daddyn sa kai tsaye anjima zaki ganshi amma me kika tanadar masa dan ki burgesa? Ajiyar zuciya ta sauke fuskanta dauke da mayalwacin murmushi tace"ai ni mummy nama rasa tacewa"ok to ni bara na baki nawa shawaran idan yazo kiyi kokarin ganin kinci dashi daga wani abu a wajen koda na shane daga hannunki hakan yana kara dankon kauna"inde wannan ne mai saukine zanyi kokarin ganin nabashi inde hakan ze burge shi,takare maganan cike da farin ciki"mezai hana ki burgesa saide idan bakiyi masa hakan ba cewar hajia mariya"haba mummy me zai hana inbashi wallahi bansan irin farin ciki danake ciki ba gaskiya mummy shema ba karamin burgeni kikayi ba yau ai wannan albishir ɗin naki yafi kugeran makka a wajena takare fadin haka tana miƙewa dan tafiya tasoma shiri dan a cewarta shirin na yau na musamman ne,tana komawa ɗakinta tafaɗa kan salaha tana dariya itama salahan tayata dariyan tayi dukda batasan me takema ba amma tasan komade mainene abun farin cikine yasami kawartata"salaha tayani murna yau mine zezo ya halarci partyn mu"wow karkice cewan salaha"wallahi kuwa ƙawata dalilin kiran da mummy tayimun yanzu kenan kede dole mu cancell wasu tsarin kicire wine dakika saka ciki dan ganin wine a wajen babban barazanace gareni sannan dan Allah ƙawata yi kokarin sanar da sauran yanzu babu shigan ƙananun kaya suyi amfani da wannan dogon rigar nan ta material dan mukara burgeshi ganan wayata ɗauki ki kira nakira kisanar dasu duk ta ruɗe take takasa tsaye takasa zaune gu ɗaya. ******** Saida akai sallahn magariba sannan Anty malika takawo mata riga da zata saka,wannan dogon rigar ta material da sukai faɗa akansa da basma haɗe da takalmi golden colour sai mahaɗan sa hand bag da ɗan yalolon gyale,Aisha na ganin Anty malika ta dan ƙwaɓe fuska kaman zatayi kuka cike da shagwaɓa tace"shine sai yanzu kika dawo bayan kinsa ko kuɗin motan komawa gida banda. Ƴar dariya Anty malika tayi cike da zolaya tace"rabani da wannan ƙanwa ina ni ina shiga tsakanin mutum da matarsa,ko yanzu ma saida yakira yace nazo nakawo miki kaya kishirya sai kuma tayi ƙasa da murya tace dan Allah ki nutsu ayi miki kwalliya na burgewa dan so nake yau ki ƙarasa haukata wancan wawiyar kinsan hankali be gama isarta ba. Kallon ta kawai tayi batayi magana ba dafa kafadanta tayi tace ke kwantar da hankalin ki bawani abun damuwa bane,nima kinga da shirina nazo dan so nake naje naganewa idona abunda takeson yayah Ahmad sai yaje dan haka so nake kiyi gayu iya gayu kamande wacce zata gasar kyau,ganin kaman Aisha bata da niyan tashi yasa Anty malika riƙe mata hannu tana tayi mata magiya kaman zata saka mata kuka har hankulan mutanen dake wajen yafara yuwa kansu saiga hajiar nan tanufo su tana tambayan yaya maike going anan ganin Anty malika yasata washe baki tana cewa ƴan biyu ashe kece"eh wallahi hajia ya aiki?ta amsa da fadin hakan tana kallon Aisha"lafiya lau fatan kin kawo mata kaya dazata canja?saurin amsawa malika tayi da fadin"eh hajia gashinan idan tasaka ayi mata makeup mara hayaniya dan yanzu nan zezo ɗaukanta. Itade Aisha zaune take ko motsawa takasayi sai aikama Anty malika da harara take"Aisha tashi muje daga ciki ai da zafi zafi ake dukan karfe karki tsaya yin nawa haryazo yatsaya tsayuwar jiranki,wani irin haushi yake tasoma Aisha aranta kuwa cewa take mutum inba ya raina ma mutane hankali ba,me nawani sa muje shagalin bikin sa da wata,take taji wani abu nataso mata tun daga ƙasan zuciyarta yana lulluɓeta take tayi saurin kawar ta abun aranta tana faɗin toma wai ina ruwa da wani shagalinsu dama ita mai shagalin baki ɗaya dazan wani ji haushin su. Rigar tasaka yayi mata ɗas a jiki yakuma fitar da shape ɗin ta saida akai mata makeup sannan hajiyar da kanta tayi mata ɗauri daya zauna mata daidai a kanta mayafin ta yafa mata a kafadanta takalmin tasaka irin half cover ɗinnan ce sai mahaɗanta hand bag masha Allah shine abunda ke fita daga bakin hajiar dama wacce tayi mata kwalliyar wankan turare akai mata gakuma ƙamshin turaren wuta dana dorot daya kama mata jiki,ita kanta Aisha sanda ta kalli kanta a madubi tsintar kanta tayi da sakin murmushi daidai tana kara juyawa gaban madubin tana karewa kanta kallo tare dakuma godewa Allah subuhanahu wata ala dayayi ta dakyan tsari da fasali maikyau badan wayonta ko dabaran ta ba,turo ƙofan ɗakin Anty malika tayi saida ta zarana da irin kyaun da taga Aisha tayi mata yau a ido duk da tasan ita din kyakkyawace amma bata taɓa sanin kyaunta yakai haka ba take ita ma tafara fadin masha Allah ke kinga yanda kikayi kyau kuwa wannan ai sai kisaka yah Ahmad fasa zuwa wajen shagalin ko kuma idan yaje yamance sunan amaryasa saide kawai muji yana kiran eashow eashow,dukan wasa Aisha takai mata ita kuma na gocewa tana dariya tace kidaurawa ƴar mutane hawan ruwa a banza cike da zolaya take maganan hajia ma tasamu abunda take so sai kaɗa baki tayi tana tambayan Anty malika"ince ko shidin shine wanda ze aureta?ƴar dariya Anty malika tayi duk yanda Aisha ke mata alama da ido kartayi magana amma saida ta tanka tace"hajia wato de zan iya cewa shiɗin mijinta tane duk da dukansu basu dauki abun da mahimmanci ba,haɓa hajiyar tarike kafin tayi wata magana sai wayan Anty malika yayi ringin tana dubawa taga yah Ahmad ne bisa layi tana dagawa bebari ko amsa sallamar da tayi masa yayi ba yace"ku fito muna waje daga haka yakatse kiran,kallon Aisha tayi datayi tsuru ta zuba mata ido tayi tace"mutafi ko kirarin da hajia tasoma matane yasata saurin fita daga ɗakin tanufi kofan fita waje daga babban shagon nasu Anty malika na biye da ita da ledar kayanta data canza riƙe a hannun ta sai hajiyar nan dake ta washe baki biye da ita tasan yau irin kyaun da Aisha tayi dole tasamu sallama mai kyau wajen ogan tunda taji ance matar sace. Fitowa Ahmad yayi daga cikin motarsa yana daddan na wayan sa khalid dake zaune cikin mota shiya fara hango xuwan su Aisha kafeta da ido yayi a ransa yana ma abokin sa dariyar mugunta dan haka fitowa yayi daga cikin motar dan son ganewa idonsa wani irin yanayi abokin nasa ze shiga dan kullum bashi da magana sai cewa wannan ƴar jaririyar yarinyar su Ammi za suce matarsa saide ya yarda ze zauna da ita na wucin gadi kafin nan kowa ya kama gaban sa,gyaran murya khalid yayi da fadin"a'a malika harkun fito kenan tun ɗaxu muna jira kunason ɓata mana lokaci kaman bakisan yayan nan naki bayason yawan jira ba. Yafadi haka amma idonsa nakan Ahmad daya sake baki da hanci ya zubawa Aisha ido tunda khalid yayi gyaran murya yakafe ta da ido besan sanda yafurta"wow beautiful ba.   ALLAH YASA MUDACE [8/13, 4:56 PM] Xeenat: https://www.wattpad.com/1372620081?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=xXYMe%2FWZPQP%2BWqSoBHDlnNIhvRqz3MEnyfWrD%2Fbw9GuxTY8IWcwGUnEPSLVq5cV205z%2FdvBNVVDvbK68S%2BibXtedeLop1j%2FaweaVWwDyMV0EA5u0aYdT2I4V85kxLmlh _________________ *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 63 Can waje tafita inda bayawan hayaniya taje ta zauna haka kawai takejin tsanar basma har karkashin zuciyarta,tsana da da batajin tana mata irinsa wani irin baƙin ciki takeji aranta yanda ta ƙanainaye Ahmad dashima yake biya mata ko kunya babu da sunan rawa tsuka tayi tasakeyin ƙwafa taja tsaki yafi aƙirga duk yanda taso cire abun aranta kasawa tayi sai kawai tamiƙe tasake shiga can baya inda batajin motsi tana nan zaune tunani duk yayi mata bake bake acikin zuciya to wai ma mai hadinta dasu data zataringa damun kaita a kansu,wata zuciya tace kode kishi kike. "Ina ina Allah ya sauwake nayi kishi a kan ma wani dalili zanyi kishinsa? saboda yana auren ki wata zuciyar ta bata amsa kinga kuwa dolene kiyi kishinsa hakade ta ringa surutai kaman wata zautacciya ita kanta batasan adadin lokacin da taɗauka nan zaune a wajen ba,ƙusƙus datake ji a bayan wasu motoci shi yaɗauki hankalin ta miƙa tanufi in takejin kaman magana na tashi daga inda take tsaye tana iya ganin mutane biyu duk da bata ganin fuskokin su suna tattauna wani abu abunda taji suna magana akai baƙaramin tada mata da hankali yayi ba,take hanjin cikinta hautsina taji wani jiri naneman ɗibanta kaman zata faɗi da sauri takoma baya dan karsu ganta bigewa tayi jikin madubin wani mota hakan yajayo hankalin su wajen daya daga cikin mutanen biyu yashiga cewa"waye waye a wajen? Dube dube suka shigayi ita kuma tana ja da baya jin ɗaya yana cewa daya"karmu bari koma wayene ya kufce mana sai mun kamosa dan tabbas maishi yaji abunda muke tattaunawa,a ɗan rikice ɗayan yake magana yana cewa"dama saida nace maka muhadu a wani wajen kaƙi to gashinan yanzu asirin mu yana gabda to nuwa"kai shiru nace kai shiru ya dakawa ɗayan tsawa ganin yanda ya diririce duk ya firgice kai ba namiji bane abu kadan sai kanuna tsoronka a fili sai kace wata mace wallahi ko mace ba zatayi hakan ba,amma dubeka dan Allah abu ɗan ƙanƙanni sai kabi duk katada hankalinka sai kace kaine ɗaya mai rai ran nan fa guda ɗayace kuma kowama ɗayan gareshi. Jin yanda ɗayan yakema ɗan uwan nasa faɗan yanutsu yabata daman rarrafawa dan neman wa kanta maɓoya tasan muddin tabari suka ganta to kashinta yabushe idan tace komawa zatayi inda tafito dole su ganta kuma su kamata idan suka kamata batasan abunda zasuyi mata ba,sannan yanda take ganin idon waƴan nan kashetama za su iyayi kuma sukashe banza ba abunda ba zasuyi ba dan kar asirin yatonu. Neman maɓoya tashiga yi yayinda suma suke dube dube ido rufe dan ɗayan yana sake tabbarwa ɗan uwan nasa karka sake murasa koma wa Rarrafawa tasomayi tana jada baya suma kuwa gadan gadan cike da tashin hankali suke nemanta bayan wanj mota tasamu taɓoya tana mai ajiyar zuciya can kuwa ta tsinkayo muryansu suna waya suna sanar wasunsu ansamu matsala akawo musu ɗauki dan basason koma waye ya kufce musu,ai kuwa tuni cikin Aisha ya ɗauri ruwa gashi bata da waya a hannu balle tayi tace akawo mata ɗauki,cikin abunda befi minti goma ba saiga zugan wasu ƴan daba da makamai rirriƙe a hannun su sai kafa wuƙaƙe suke suna kiran yau zasu sha jini,ji tai inama bata fito ba tayi zamanta ai ba lalle sai ta kalli inda suke rawan ba. "Inason ku bincika mun nan sosai kar maishi yatsare mutum ne kai koma addabane sai kun gurfanar mun dashi nan dan barin maishi haƙiƙa hatsarine garemu,oya rufe bakin sa keda wuya waƴan nan matasan samarin su takwas suka shiga neman ta harƙarkashin mota sai sun leƙa mota kuwa kona uban waye sai sun buɗeta sun duba in kaga basu duba mota ba ka tabbatar a kulle motan take,kaman yanda suke kusantota haka ita ma takeyin baya tare da canza inda take zuwa wani wajen duk ta tsure suna cikin wasan ɓoyan nan kawai ɗaya daga cikin su ya hangota ta madubin wani mota buɗe wagegen bakinsa yayi yana cewa"oga gatanan naganta dago kannan da Aisha zatayi sukai ido huɗu da wanda ya gantan miƙewa tayi takwasa a guje suna biye da ita a baya. Ahmad da tun fitan ta yake hankalce da ita saide Basma ta kanainaiye shi taki barisa balle yasamu daman binta a baya,malika dake masa liƙi yama magana tabita abaya saide koda malikan tafita bataga inda tayi ba,harma parkin lot ta tafi amma bataga koda mai kama da Aishan ba,harma ta ƙarasa bakin get din hotel ɗin ta tambayi mai gadi koya ganta amsa mata yayi da gaskiya shi bega yarinya mai irin wannan kaman nin da ta ambata ba,tade sake dubawa ta aciki. Komawa Anty malika tayi cikin hall din da ake gudanar da shagalin txt massage ta turawa Ahmad dake zaune kusa da amaryar sa sannan ta sanar da yah faisal Aisha fa tafita tun dazu kuma tafita ta duba bata ganta ba."what tun taushe tafita ya tambayeta da damuwa saman fuskan sa"wallahi yayah nima bansan sanda tafitan ba,dan sanda a kakira ango da amarya nace tazo muje muyi liƙi tace bazata ba toni najeni sai yah Ahmad ne yace mun yaga tafita naje naduba ina zata,nabi bayan ta kuma ban ganta ba har bakin get naje batanan nama tambayi mai gadi yace bega mai kama da ita ba,takare maganan hawaye na taruwa a idanun ta"riƙo hannunta yah faisal yayi yana yace"cmon za ganta ne ba inda zataje kode takoma gida ne kinkira su kinji ko taje?"nah tace dashi amma bara yanzu nakira ciro wayanta dake cikin puse ɗinta tayi takira wayan Anty hajia har sau biyu tana ringin taƙatse ba'aɗagawa hakan yasa ta maida akalan kiran nata ga malik bugu daya biyu ya dauka ko sallamar sa bata amsa ba tace kawai yaduba mata gida ko Aisha tazo"batazo ba ya amsa mata kansa tsaye yadaura da cewa tundazu ina gida Anty hajia sun je kai kayan lalle gidan Alh sunusi sauran yaran kuma na gidan Ammi amma lafiya kike tambayan Aisha ko batare take da ku ba?"tare da mu take saide tun ɗazu tafita bamu ganta ba,danAllah twince ɗan duba kagano mana ko tashigo bada saninka ba,duk yanda ake ciki kasanar da mu"ok ya amsa yana mai miƙewa dan duba dakin su ko tana ciki bega shigowantan bane. Ahmad dake zaune kusa da amaryarsa ta saƙale hannunta da nasa hannun duk shige da fice da faisa da malika keyi akan idanunta zuciyar fal murna dan cewama take tafi ruwa gudu yarinya duk tazo ta tarwatsamun farin cikina,amma yanxu ganin yanda ta hango damuwa saman fuskokin su haka kawai ta tsinci kanta da farin cikin kuma tafiyan nata saiya wanke mata da duka wani taƙaici da shiga dazu,miƙewa Ahmad yayi danufi zuwa gunsu yaji sake rike masa hannu tayi cike da kissa tana cewa"mine kaɗan zauna mana ganan ƙawayena xuwa muɗauki photo kafin ka tafi duk yanda yaso zullewa abun ya faskara kaman hadin baki dan ƴan mata da samari layi layi suke zuwa a dauki photo kowa kagani riƙe da ƴar wayar sa a hannu da kyar Ahmad yasamu kansa yamike yanufi su inda su Nawwar ke zaune shiɗinma karfi hali yayi bawai dan yan daukar hoton bs karewa sukai ba. Da murmushi saman fuskar sa amma kana gani kasan ina kanta fuska shima Nawwar din maida masa da murmushin yayi fuskansa da alamun damuwa yace"haryanzu basu ganta ba sannan anyi waya gida ancbataje gidan ba,bama kowa a gidan sai malik to ƴar uwar tace yashiga yaduba ɗakin su ko tana nan bega shigan ta bane yanzun nan yakira yace gaskiya bata zo ba kuma har mai gadi yafita ya tambaya shidin ma cewa yayi yau tunda garin Allah ya waye beganta ba. Da sauri yanufi kofa Nawwar namara masa baya sai latifa da itama takebiye dasu dama tuni khalid da sapwan na tare da faisal din. ******** Aisha da tun zuwan yah faisal da Anty malika na farko ta hangosu amma wani saƙandamin ƙato ya rufe mata baki saboda rashin imani wasu biyu daga ciki suka riƙe mata hannuwanta gudun kartayi wani ƙwaƙƙwaran motsin da zajita. Nan da nan suka jata zuwa bayan wasu shuke shuken fulawa sukayi maɓoya acan lokacin da Ahmad ya nufo wajen da nawwar duka akan idon Aisha da wayan nan da samarin ƴan daban,haka suka shiga bube bube suka haɗu duka dasu faisal amma ba Aisha ba labarin ta har tsakankanin motoci Ahmad yaje har kusa da fulawowin saura kaɗan ya hangota kiran da malika tayi masa yasashi saurin juyawa gareta,wannan yabasu daman sake canza wani maɓoyan koda yasake maida hankalin sa wajen bega komai ba. Faisal ne yaƙara so wajen yana cewa"kaga kai kaje gida tunda Anty hajia na gidan ku ko taje can ɗinne,ni kuma yanzu zanje office nakai wani report duk yanda ake ciki sai kaimun waya"ok ya amsa a taƙaice yana mai sake duba cikin fulawan nan shide haka kawai yaji yakasa yarda da wajen. Haka duka suka fita suka shiga motocin su suka tafi sai a sannan wayan nan samarin suka sauke ajiyar zuciya itako Aisha wasu hawayene masu dumi suka shiga zubo mata tabbas tasan tata takare,ɗaya daga cikin sune yashiga cewa"maƙwa bara nafita bakin get nagani ko sun tafi dan naga kaman wannan gayen yaso ramfomu yanda yake yawan juyawan nan kaman ze sake zuwa nakeji."Ko nima haka har jikina yafara sanyi da wannan lamarin anƴa ma kuwa ba cinnaka a cikin su?cinnaka suna nufin police"nimade abunda nagani kenan kiran sunan su yashiga yi ɗaya bayan ɗaya"jaami moro magaa bagaa duka kuyi sauri kufita daga nan kafin a ganomu mu muhaɗu a mahaɗa kai kuma bad boy yi maza ka kawo mana motan nan nan muyi maza mubar nan kafin susuke zuwa,yana gama fadan haka kaman kiftawa da bismillah duka suka watsa Aisha na ganin abun da suke niyar yi tayu yunƙurin guduwa saide ko taku biyu mai kyau batayi ba,wani ƙoto ya kwarfeta jikake timm tafaɗi a ƙasa tasaki wani gigitaccen ƙara wani irin zafine ya ziyarci hannunta data faɗa akai har ƙwaƙwalwanta taji wannan zafin. Mota suka cusata yayin da wanda taji ankira sa da makwa yafizgi motan a 360 yafita daidai wata mota kiran honda baƙa tashigo wajen kaman zasu daki wannan motan driver yayi saurin ɗauke kan motarsa ganin hakan wanda yake bayan wannan hodan yace da driver sa"yi maza kayi reverse mubi wannan mota da alama basu da gaskiya"angama ranka ya dade ya amsa sannan shima driver wannan hondan ya juya kan motar cike da kwarewa ya mara musu baya gudu suke saman kwalta duka ababen hawa hanya suke basu ganin yanda suke shara gudu kai kace tsaren mota suke kaman a cikin shirin american film ɗin nan fast&furious ganin ana binsu a baya makwa yayi yaza yadau waya yakira ogan nasu da yabasu aiki wayan tana shiga dama shikan sa kiran nasa yake jira yana dauka"oga ansamu matsala ganan wani mota tana da bamusan ko waye ba yana biye damu abunda yasamu cewa kenan ga ogan nasa daidai motar tasu ta daki wata daf data lalace tana dauke da lodin kaya ji kake kiiiiiiiiiiiiiiii kau... Masoyana abun Alfahari dake bibiyar wannan littafi a duk inda kuke a faɗin duniya ina muku fatan alheri. Sannan ina mai neman afuwanku bisa jina shiru da kuke hakan yasamu asalina sabida rashin karfin jikina. ALLAH YASA MUDACE [8/13, 4:57 PM] Xeenat: https://www.wattpad.com/1371145203?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=9mW7ekzQIFtKuljbQFDiDxAD1pkMHmC8CxSp7JWgtdQjE9XgdT%2B60qHbqx2BGSaMUT3UeLb7Q6seKFr9cn8S9aboM4gMj5jx%2Bj0SuOcdXHJzwg81S3A%2Fm%2BeSoFTtZkd7 ______________ *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 62 Masha Allahu walaƙuwata ubangiji yayi halitta anan besan sanda ya furta hakan a fili ba,yana nan tsaye de har suka zo Aisha ta gaida khalid ya amsa yana zolayarta da cewa"kode gasan kyau zaki bamu sani ba ƙanwas murmushi kawai ta sakar masa tana jan hannun Anty malika dake tsaye saida suka dan gilmashi sannan khalid dake tsaye yana kallon sa yaɗan bigi saman motar da karfi nan Ahmad yayi firgigit yadawo daga duniyar tunani daya tafi sake kallon hanyan babban shagon yayi hajiya hanas din yayi murmushi hajia hanas dake tsaye a gaban sa ta sakar masa dole ya maida mata da murmushi yaƙe ganin yanda yake dan kalle kalle yasata cewa"gasu can sun wuce. Wayancewa yayi yana cewa"oh na gansu bani acct dinki,ba musu ta karanto masa yasaka nan take sai ga alart zaro ido hajia hanas tayi cike da jin daɗi irin wannan kyautan hakan yasake tabbar mata dacewa lalle aikinta yayi kyau kuma wanda akai domin sa yayaba,dama ance yaba kyauta tukuwici gashi kuwa tagani godiya tashiga yi masa har tana haɗawa da khalid cewan yata yata godiya wajen Alhaji sannan ta juya baya tanasake jaddada masa duk sanda madam takeda bukatar gyaran jiki lalle ko wankin gashi dama ƙitso ko waya kawai yayi ba matsala ko gidane zaje aimata godiya yayi mata ta koma cikin shagon ta cike da murna irin wannan kyauta da tasamu. Shiko Ahmad ganin yanda khalid ya tsastsare sa da ido yana ƴar dariya ƙasa ƙasa yasake haɗe fuska shi ala dole bayason wargi yace"me kawani tsareni da ido kaman zaka haɗiyeni? khalid besan sanda wata irin dariya da karfi ya kubce masa ba ganin raina masa hankali Ahmad kesonyi kaman bashine yanzu yagama kallon yarinya dayake kiran Auren wucin gadi yayi da ita ba. "To malam me nawani haɗa rai ai sai kaje kakira ta mutafi kasan tun tuni su faisal na can mu kaɗai suke jira amma mutum kawani sake baki kana kallon gwailan yariyan da banaji ko ƙirgen dangi ta gama kaida za kawo maka classic lady me nawa westin time kan wannan abar yakare magana yana ɗauke kansa daga kallon inda Aisha da malika ke tsaye jikin motar malika kuma yayi hakan ne kawai dan son kunno da abokin nasa ai kuwa ya kunno,dan wani irin tuƙuƙin bakin cikine ya turniƙe masa zuciya besan sanda yayi kwafa yana ce masa to me zan gani anan ɗin karkaga dan nakawo ta nan anyi mata ƙunshi kadauka wani abunne wannan din hakkine akaina banason ana taron baki yazama itace kaɗai batayi ba,yana kare fadin haka ya yafito malika da hannu shikuma fuuu yakoma cikin mota duk takaici yagama isar sa yama rasa abunda ke masa daɗi khalid ma ya kalle ta haka ina ga wasu kenan haka ake kallonta ji kawai yayi kaman yafasa ma tafiyan da ita wajen yace da malika kawai su koma gida,amma kuma idan ta koma shirin sa ze rushe haka ya danne zuciyar sa. Malika na isowa yace"jeki kirawota kinsan koma amma kinason ɓatamun rai"yi hakuri bro wallahi tun ɗazu nake fama da ita amma ta kafe bazata wajen wani party da wannan shigar haka ba saide a nema mata hijabi. Besan sanda yaja wani gajeran tsuka mtsss yana cewa"matsalata da irin waƴannan yaran kenan rashin wayewa to wama ze kalleta a wajen idan munje ana ta manyan mata wake ta gwaila irin dallah malama kizo karki batan lokaci,yanda yayi magana har saida yabasu dariya amma duka suka waske basuyi ba,sai ma khalid ne yace"bara na taimaka maka da wannan yanufi bakin motar malika yasami Aisha tsaye yace"ƙanwas kefa muke jira tuntuni kuma kinzo kin tsaya anan,marairaice fuska tayi tace"wallahi yaya khalid banajin zuwa wajen partyn ne haka"ina ina kanwas saide fa yau ɗaya kiyi hakuri yah faisal ma yace yana jiranki a can gakuma kawarki laila ita tana bakin hanya tana jiran muje madauke ta dan haka kiyi hakuri keɗin kibi motan Ahmad kuje tare nikuma da malika zamu biya ta inda laila ke jiranmu muɗauke ta"amma yah khalid i zamu iya zuwa tare mu dauketa ko?"naa ba zauyu muje dukkan mu mubar ba kede muje kawai kutafi muma gamunan tafe. Haka Aisha ta hakura zatabi motan Ahmad amma badan saboda tanaso ba dande kawai karta kafe khalid yagani kaman taƙi jin maganar sa ne,har bakin motan ya rakota saida yabude mata gidan gaba tashiga ta zauna khalid harda gyara mata riga saboda tsokala ai kuwa ya tsokalo dan yana ɗagowa yasamu guzurin mugun kallo daga oga Ahmad dake tsaye murmushi yasakar masa dacewa a kular mana da ƙanwa banda tuƙin ganganci dan naga kaman ka haura sama"dallah malam ware kukesa kananun yara suna raina mutane surinƙa ganin kansu daya dakai dakayi magana,dariya khalid yayi malika natayasa duk da tana ɓoye dariyar tata kar yayan nata yagani amma abun ya gagara dan saida dariyar ta fito fili,daƙyar ta danne dariyar tana cewa"yaya in banda abunka ai koda ƙwana daya ka girmi mutum ai ka girme sane balle kaida kaba da shekaru shima yah khalid ɗin yafaɗi hakane kawai dan ya tsokaleka kuma kai kanka kasani har abada ba raini tsakanin mu dakai wallahi ko ita Aishan ma banajin zatayi tunda ba halinta bane,wayan Ahmad ne tayi ringin wannan shine kiran da faisal yamasa na biyar kenan tunda sukazo daukar su Aisha ɗaga wayan yayi yana cewa to malam sauri ba wajen zuwa gamu nan yanzun nan na daukota kasan sha'anin mata komai ƙanƙantar mace wajen wanka kadai sai taɓata a ƙalla minti talati wajen shafa mai ma haka sannan wajen kwalliya wannaan itace uwa uba dan sai taɓata awa guda sannan......"yaushe kazama haka Ahmad faisal ne ya katse shi dafadin hakan murmushin gefen baki Ahmad yayi yana maikafe Aisha dake zaune a mota da ido duk da kallon gefen ido yake binta dashi sai kawai yakashe wayan yana maida abun sa cikin aljuhu shima yashiga motan ya zauna saida yamata key yabata wuta sannan ya cillata saman kwalta dama tuni khalid sun tafi da motar malika tunda yasa Aisha a motar Ahmad ya anshi key daga hannun malikan bayan yagama tsokalan Ahmad yatafi. Saida ya daidai nutsuwar sa sannan ya kalli Aisha yana taɓe baki yace"wannan wace iriyar shigace dako tsari babu,ɗagowa tayi ta kalleshi ganin ya zuba mata ido ko kifyawa bayayi tayi saurin cewa"na shiga uku kalli gaban ka yanda tayi dole yasa ka tsorata kokai wayene ai kuwa da sauri Ahmad yamai da duban sa gaba yana kaucewa wani mai mashin ajiyar zuciya duka sauke a tare tana tura baki gaba tana cewa mutum in be iya tuƙi ba ai ba dole sai yayi ba. "Magana kike na? "A'a ni bance komai ba ta amsa tana kauda kanta gefe ganin taƙi kallon inda yake shikuma be gama kallon kwalliyar tata ba,tuki yake da daya hannun sa sannan yakai daya hannun ya kamo hannun ta yakai bakin sa yamanna mata kiss yana dan kallon jan ƙunshin yatsun hannun ta da zanen fukawan sun zauna ɗas gwanin burgewa yace"inason ganin hannun mace da kunshi ba karamin burgeni yake ba,ko sanda ina yaro duk sanda Ammi na tayi kunshi haka zan sakata gaba ina kallo shisa koda yaushe nake addu'ar Allah yabani mace mai son ƙunshi"ai kuwa addu'ar ka bata harɓo ba dan ni bana daga cikin masuson yinta koda ina so kaima kanka kasan bazanyi duk wani abu da ze burgeka a zaman wucin gadi da zamuyi ba,ta ƙatseshi da fadin hakan. Shi Ahmad har mamakin Aisha yake duk sanda kafaɗa mata wani abu kaman dama amsan na bakinta nan take zata baka kuma ta fuske abunta kaman ba itace tayi maganan ba. Yana riƙe da hannun nata yana murzawa a hankali hankali duk yanda taso ƙwatan hannun nata hanata yayi ƙarshema cemata yayi sadakin da su Ammin sa suka bada yake taɓawa ai ita din halalin sace dole ta haƙura amma duk yasakar mata kasala dan wani irin yanayi da batasani daba tasoma tsintar kanta cikin muryan menuna mutum yanason yin kuka tasoma magana"ai wannan kwartonci ne aina aka halasta maka yin hakan wannan ai rashin sanin darajan mutum ne kawai kanason ɓatani a banza kabari ma bagade yanzu zamuje wajen wacce kakeso take sonka sai kayi mata amma a ƙarancin shekaruna kakeson koyamun abubuwan banza na rashin ɗa'a sai ga hawaye sharr sharr sun soma zubomata daga ƙurmin idonta,parkin motan yayi dayake yariga da yashigo cikin hotel din da ake gudanar da party,dan waigowa yayi ya kalle ta kaman bazece komai ba ganin kukan take bilhakki da gaskiya yace"malama ai saiki goge hawayenki mushiga ciki saura kinuna ƙauyancin ki a fili ɗan riƙe miki hannu kawai danayi duk kinwani sake kaman fulawa da tasha bugu,wani irin haushin maganan nasa yabata sai kawai tasake fashe masa da kuka na gaske watom itace ma takai kanta gareshi ganin yanzun kan da gaske take kuka dole yashiga rarrashinta yace"wai ke ɓakisan wasa bane nifa wasa da wasa nake miki ai kedin mai sa'ace tunda kika sameni matsayin miji kinyi goshi saiki gode Allah batasan sanda ta ɓalla masa harara ba tace"ko kuma kaine kayi sa'an samu na matsayin mata ba badan wannan kaddararren aurenka na wucin gadin nan ba da yanzu haka ina dubai tare da mijina abun sona amma saboda wannan auren naka gani a inda basan darajata ba sa....wani irin tsawa ya dakamata saurin rufe bakinta tayi da tafukan hannunta duka biyu ta zaro idon ta waje kaman zasu fado kasa,matseta yayi jikin set ɗin yasaka hannun sa cikin rigarta ta baya bayan ya zuge zip din rigar a rikice Aisha yasoma yimasa magiya"dan darajan iyayen ka kayi hakuri wallahi kuskurene bakina ne ya tsubuce bazan sake maka rashin kunya ba na tuba nabi Allah nabika yaya Ahmadin Ammi. Dariya ma maganan tata taso bashi amma ya fuske yace"a'a bari kawai nayi maganin bakin rashin kunyan yana faɗa yaciro hannun daga bayanta yayi mata wani irin kyakkyawan runguma ringin ɗin wayansa shiya katsashi daga abunda yayi niya sai da yasaita kansa sannan ya dauka murya ashake kaman me mura y amsa da gamu a parkin lot yana gama fadin haka ya kashe wayan a dayan bangaren faisal rike wayan kawai yayi yabi screen din waya da kallo kaman ze ga Ahmad din taciki to mai yake damun Ahmad kuma yafadi haka yafi akirga sai can ya wayance yana kallon khalid yayi yar dariya yace"kaida malika kuge can parkin lot ku taho dasu sai mushiga dukka mu atare. Haka kuwa aikai suna isa suka iske Ahmad yayi tsaye yana maida numfashi ita kuma Aisha ta hada kai da gwaiwa sai kuka take suna zuwa khalid yace"me kayima ƴar mutane take irin wannan kuka haka? Kallon kai waye Ahmad ya jefi khalid dashi sannan yace"tambayeta mana me zanyi da wannan gwailan mema takeda da zantaɓa ajikinta mamuni grass dinta dako lemun tsami bekai ba zantaɓa kome? Duka shiru sukai jin abunda yace ba lefin kabane lefi nane dana tursasa mata binka amma ba damuwa cewar khalid da ranshi yagama baci da rainin hankalin Ahmad din kasa yarinya mutane kuka amma idan an tambayeka kanuna bakasan komai ba. Dakyar malika ta rarrasheta tare da khalid ta hakura malika tasake gyara mata fuska sannan ne tafito daga cikin motan suka nufi zuwa inda sauran abokan sake jiran su duk wannan abun da akeyi na rarrashi Aisha Ahmad na tsaye yaki tafiya Anty malika ce ta duka daidai kunnen ta taraɗa mata wani abu data sakata sakin fuskanta tana murmusawa a haka suka jera suka karasa ciki tun daga wajen ajiye motoci zai tabbatar maka da bikin na ƴar gatane duba da yanda aka faka motoci masu kyau da dama sanda suka isa inda su faisal ke tsaye tun dazu dr sapwan yana ganin su yace"sannunka da shukamu da kai tundazu kata nadi abunda cewa gun amaryarka tunda acike take dakai saura kaɗan ta fashe...zungurinsa da nawwar yayi shiya sashi yin shiru duk da besan ma'anarsa nayin hakan ba gaishe su Aisha tashiga yi daya bayan daya suna amsa mata cikin sakin fuska bayan gama gaisuwar su suka dunguma zuwa ciki inda ake gudanar da fatin ai suna sako kai DJ yasaki kiɗa Mc kuna nasanar da karasowan ango da tawagan sa take hankulan mutane baki ɗaya yayo kansu Ahmad shine a gaba hannunsa sarkafe dana Aisha dake neman yanda zata kwaci hannun ta bayan sa dr sapwan ne da bebinsa latifa sai khalid da laila sai kuma nawwar da malika daka mara musu baya sai faisal shine karshe tunda Ahmad yasoko kai hall din baka iya ganin komai sai hasken camara da aka soma haska su tako ina madu waya nayi masuyin video ma nayi rikicewa Aisha tayi had batasan sanda ta kankame hannun nasa ba,yanda suka shigo wajen duk kushen mai kushe karyansa yace basuyi kyauba kuma gasu sun dace da junansu kai kace itace ma amaryan saboda yanda ta haɗun sannan yanda suka shigo da tsari basu da yawa da gani kasan antsara abunne cikin wayewa. Ahmad saida yakai Aisha yanema mata maxauni yaja mata kugera ta zauna sannan suma sauran yan tawagan nasa suka samawa kansu wajen zama,sannan ne ango yanufi inda amaryar sa ke zaune tacika tayi fam kaman zata fashe gefe daya kuma kus kus kakeji kananun maganganu suna tashi. Ahmad sobada iya taku yana ƙarasawa inda amarya basma take ya riko hannunta ya sumbata yana cewa"amun afuwa bisa rashin ganina da bakiyi a kan lokaci ba,kafin basma ta amsa sai ga wani ɗan jarida yaƙaraso inda suke yana cewa"Ahmad Alh badamasi a ƙa'ida akanga ango atare da amaryarsa yayi gudanar da wani irin shagaling biki tsaɓanin kai da yanzu muka ganka da wata ko zamu iya sanin wace alaqa ke tsakaninka da ita? Kallon inda Aisha ke zaune yayi sannan ya maida duban sa ga basma data kafesa da ido sake sumbatar hannun nata yayi a karo na biyu yana kallon cikin idonta yace"ita din takasance Abokiyata ce "Abokiya ɗan jaridan ya maimaita sannan yace amma mr Ahmad Abota iri irine wanne kake nufi daga ciki? Murmushin gefen baki yayi sannan yace"duk wanda kaga yadace to shine ze sake magana ya ɗaga masa hannu yace karka sake mun wata tambaya idan kana da shima zaka iya adana abunka dan zema amfani wani jiƙon. Dole dan jaridan yabar wajen bawai dan gamsu da amsan da Ahmad din yabashi ba,bayan barin dan jaridan wajen basma zatayi magana Ahmad yarigata da cewar wala tajassasu kada ki cika son bincike dan idan kikace zakiyi hakan wataran zaki binciko abunda ze hanaki bacci. Daga haka suka maida hankulansu wajen da ƴan mata da samarin dake rawa hannuwan su sarkafe da najuna lokaci lokaci Ahmad yakan ɗago ya kalli Aisha dake zaune dasu malika da laila itama kuwa kaman baki duk sanda yadago ze kalleta sai sun haɗa ido,mc ne yawage baki cikin loudspeaker yana kiran ana neman ango da amaryarsa nan take suka bayyana tsakiyan fili inda akasake kiɗa nan da nan abokan ango da amarya suka taso suka soma liƙi yayinda amarya basma tazage tatiƙi rawarta kaman ba gobe dan ace warta idan batayi yau ba yaushe zatayi maƙale Ahmad tayi ta juya masa baya tana goga masa maxaune tana wani irin rawa matsari Aisha dake zaune taƙura masu ido haka kawai taji ranta naɓaci da abunda basma keyi da sunan rawa tsab tamike tafita daga wajen basma tabita da wani irin mugun harara dan dama duk motsinta tana hankalce da ita,kuma ko rawan da gayya tayi.     ALLAH YASA MUDACE I just published "64" of my story "AUREN WUCIN GADI". https://www.wattpad.com/1374360963?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=R5k868o21aqv1GZpTnj0yWnti2xLoJ2NKMAR7KLxTxkNgWnVKU9v%2FpUs75MTEex9HX%2FrNl8mOZAady1gcuJnvTfRCX5%2BMBrCf1x8s6dLBMj5qZNjkv7vlJsyQQt708tG ________________ *AUREN WUCIN GADI* CHSPTER 64 A guje drivern babban motan da yaron matan sa dama bakaniki dake gyara motan sukabar wajen dan tsiratar da rayuwar su,karkashin babban motar tasu motar tashiga gaba ɗaya sun rikice sun kuma ɗimauce dan ganin mutuwa sukai muraran a gaban su saide Allah ya taƙaita musu daf ɗin a tsaye take da tafiya take sunan su sorry ta bakin bature. Duka cikin motan ihun suke idan kacire Aisha da bakinta dake adaure sai ido ba abunda takeyi sai zikirin da take cikin zuciyar ta,tare da rintsa ido dan so take inma mutuwarce ta dauke ta idonta rufe ba tare da taga irin mutuwar da zasuyi din ba,amma tanajin yanda kartin ke ihun sai kuma taji dif bata sake sanin inda kanta ke ba. Kaman kiftawa da bismillah haka wayan nan katti sukayi dif suka ɗauke wuta na ɗan wani lokaci kafin kuma suka fara babbaƙewa da wani irin dariya ganin sun tsira da ransu shiko maƙwa da kansa ya daki glass ɗin gaban motan tattaɓa jikinsa yashigayi da hannu saida ya tabbatar da lafiyan sa sannan yashiga yin dariya saide nan da nan dariyar tasa ta dauke ganin wayan da suke tsaye gefe da gefen motan nasu. Ance ko a gidan giya kake akwai babba to hakance takasance dasu maƙwa ko bakin magana shikan be samu ba saijin saukan naushi daya dauke masa jinsa da ganin sa besake sanin inda kansa yake ba,daddy ishaq dake zaune bayan wannan honda dake biye dasu Makwa dasuka dauke da Aisha sanda motar tanufi shiga karkashin daf ɗin nan"innalillahi wa'inna ilalhir raju'na Allahumma ajirni Allahumma ajirni yashiga faɗi saboda yanda zuciyarsa ta tsinke ba abunda zuciyar sa keyi sai wani irin luguden bugawa da karfi da karfi idan kana zaune kusa dashi zaka iya ganin yanda zuciyar tasa ke ɗagawa yama kasa ƙarashe addu'a daya ɗauka rintse idonsa yayi da karfi yanajin wani irin faɗiwar gaba dan ganin ƴarsa kuma yana ganin kaman ze rasata wannan shi ake kira ga ƙoshi ga ƙwanan ƴunwa. Faisal na fita a hotel ɗin nan haka kawai yaji yakasa yarda da nan wajen parkin space ɗin gani yake kaman Aisha na wajen dan sanda suka isa wajen da malika yaga wani matashin saurayi mai tsukakken wando suna haɗa ido da wannan saurayin yaga ya rikice ya duririce yama rasa me yadauke masa hankali lokacin sai yanzu ma abun yazo kansa dafe kansa yayi yaɗan bigi bencin dake gabansa yamiƙe da sauri yana ma abokin aikin sa magaba suka fita duka a tare. Ahmad tunma kafin yaje gidan nasu yashiga kiran Ammin sa a waya saide harta ƙatsa ba wanda yaɗauka sannan yamaida akalan kiran nasa ga ƙanwarsa fadwa tana ƙauka beko saurari sallama datake masa ba bare ya amsa jifa mata tambaya yayi"Aisha tazo gida"a'a batazo ba yayah amma lafiya ko?meya sami Aishan?ba tare akace take dakai ba?duka wannan tambaya lokacin ɗaya ta jeromasa"shikenan sai nadawo karkice da kowa komai yana cewa haka ya kashe wayan,maida akala kiran nasa yayi ya kira faisal da shima hankalinsa yake a tashe suna mota tare da abokan aikin sa guda biyu kan hanyarsu ta komawa hotel din sai ga kiran Ahmad Faisal na ɗaga wayan yashiga cewa"kana ina?"gamu kan hanyar mu ta koma hotel din wani abunne ko Aishan takoma gidane?"No bata koma ba saide nima gani na juyo dan komawa can ɗin dan inajin kamsn Aishan na can ina kuma ji ajikina kaman wani abu na shirin faruwa zuciyata takasa tsayuwa gudaya"kwatar da hankalin ka ba abunda ze sameta in sha Allah,a sanyaye Ahmad ya amsa da Allah yasa yanda ya amsa da rauni shi kansa Faisal sai yaji dan uwan nasa yabashi tausayi. a tare suka ajiye wayan dukkansu ko wannen su da abunda yake aiyanawa a ransa tare sukai parkin din motan su faisal yafito da abokan aikinsa daga nashi motan haka shima Ahmad da sauri ya nufo su faisal ko tsayawa kulle motan sa beyi ba yana cewa da faisa"ɗazu naso ganin kaman mutum a nan a ɓoye kuma naso ganin kaman kalan rigar Aisha na fara zuwa wajen kaga harma nazo nan yana nuni da inda ya tsaya sai malika tamun magana to juyawar da nayi gareta koda nasake juyowa banga komai ba zama kaga sanda kace muje gida muduba zakaga yanda nake ta waiwayan wajen idan ka kula"hakane nima koda muka tafi nayi tunani wani abu dan sanda muka iso nan da malika naga wani matashin saurayi muna hada ido dashi naga duk ya firgice da ganina ban kawo komai a raina ba,dan hankalina yatafi ga rashin ganin Aisha da bamuyi ba wallahi saida na isa office tukun abun yazo mun,yanzu de bara mu fara dubawa,"tom kawai Ahmad yace sannan yanufi wajen shuke shuken nan shima faisal umurni yabawa abokan aikansa biyu daya zo dasu din suka shiga dube dube nan Ahmad yaga warin takalmin Aisha ɗaya a wajen kwalawa Faisal kira yayi aikuwa sai gashi shida abokan nasa ganin Ahmad yayi riƙe da takalmi wari ɗaya yana ganin faisal yashiga cewa"wallahi takaminta ne wannan ɗazu nasa malika takawo wallahi natane nan faisal yace da abokan nasa sufa bincikawa sannan ya juya ga Ahmad dib yace"kwantar da hankalinka in sha Allah zamu ganta yanzu de bara mufara da bincike nan suka rarrabu suka fara takan security suka fara amma duk wanda aka tambaya cewa yake shi bega mai kama da wanda suke tambayan ba,karshe dole suka fara amfani da wayansu suna nuna hoton ta amma shiru ba wanda yace ya ganta harma suncire tsammani sai wani dattijon mai gadi yace"yan samari bande ga yarinya da kuke faman nema ba amma ɗazu wata mota tafita anan da mugun gudu kaman marasa gaskiya kana wani mai mota ƙirar honda baƙa dashiganta nan kenan tamarawa mai wancan mota baya suka fita anan yaro idan kaga yanda suke shara gudu ko waye kai sai kabisu da addu'an Allah yatsare mukanmu da muke zaune anan munyi zargin mai motan farko da yafita kaman bashi da gaskiya,duka zubama dattajon ido sukai suna masu sauraron abunda yake cewan sai wasu mutane dake zauna kusa da shi suma suka amshe suna cewa ai wannan driver jar motan dagani kasan ɗan wiwi ne bakinsa baƙi ƙirin idanun nan nasa jajir dashi dagani saida ya maku yafara tuƙin na gefen sa ya amshe da"kai baka kula bane amma ni saida nayi ƙuri na ƙurewa bayan motan idon kaman mace nagani maza biyu sun sata tsaƙiya bakinta bakinta kaman a daure"kai Kallah kaji tsoron Allah cewa ɗayan"wallahi kuwa modi bakaga ina tama nhu nhu nhu ɗazun nakasa magana sai alama amma daga kai har baba ba wanda yagane me nake nufi. Susu uku suke zaune a falon ga kugeru na alfarma an ƙawata falon dashi gefe guda wani mutumine kai da gani kasan yana jindaɗi duba da yanda jikinsa yake freesh harma baka iya ganin tsufansa rai a ɓace yake kallon mutanen biyu dake zaune sunyi tsuru dasu suna jiran hukucin daga ogan"wannan ai shashancine mekukeyi dahar yarinyar nan taji abunda kuke tattaunawa shin kunma san fitan wannan abun kaman mun daɓawa kanmu da kanmu wuƙane?"wallahi oga saida nace dashi yabari sai mun haɗu a wani wajen amma yaƙi"dallah malam rufamun baki karka wani ce zaka ɗauramun lefi ca nake da kai kamu tsaya munemi dukma wanda yamana leɓe da kanmu amma sai ɓari kake kaman wanda aka kaɗawa gangi kakasa tsayuwa ka nutsu gu ɗaya sai wani cewa kake dama saida nace....."kumun shiru yadaka musu tsawa cikin kakkausan muryar ogan ya katsasa hakan ya hanashi ƙarasa abunda yafara yanzu de zama be ganku ba ku tabbata ba samu wata matsala ba muddin aka samu matsala to wallahi kuyi kuka da kanku karkuma wanda yace yasanni a cikin ku....Alhaji surajo kenan kutashi ku bani waje yafaɗa musu yana maui juya musu baya cike da ƙunan rai sannan ku tabbata yau din nan kunkawo yarinyar nan tunda kunce tana hannun yaran da kuka bawa aiki da tom suka amsa dukkan su haka suka miƙe jikin ba ƙwari Alh bala da zuciyarsa ke cike da tsoro sannan ga fargaba kafin su fita falo yakira numban Maƙwa daga cikin yaran da suka saka aiki ringi daya biyu aka dauka"halo Makwa wai haryanzu shiru murya yaji an amsa masa dashi ne yasa wayan hannun sa tsuɓucewa yafaɗi kasa saurin juyowa Alh surajo da Alh sunusi sukai suna duban sa tare da tambayar sa.......     ALLAH YASA MUDACE [8/23, 8:53 PM] +234 903 826 7959: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 65 Kansa sukayi da mugun sauri har rige rigen tambayasa da"lafiya lafiya?shide Alh bala ba baki sai ido wuƙil wuƙil ganin suna tambaya sa be amsa musu yasa Alh surajo ɗaukan wayan yaduba yagani shi dawa,lokacin da Maƙwa yasha wannan naushi be gama zuwa daidai ba wayansa rayi ringin ganin numba ce basuna hakan yasa Goga ɗaukan wayan danson sanin waye keda hannu cikin ɗauke musu ƴar oga shima Alh bala yakira ne yaji haryanzu basu ƙaraso bane koya dan shi yana gudun samun matsala kasancewar sa matsoraci dakuma raunin zuciya tsaɓanin su Alh sunusi da oga kwata kwata Alh surajo dan su zama suyi kisa dan ganin cikan burin su. Muryansu yaji sanda suke tambansa lafiya hakan yasashi kashe wayan yana ɗan tafa fuskan Maƙwa dayayi suman wucin gadi yana bude idon sa yamiƙa masa wayan da masa alama dayayi magana idan ko yakuskura yayi wani abunda zesa sugane da wata matsala yamasa alama da yankashi zeyi,ai kuwa cikin rawar murya data jiki yashiga bawa Goga hakura yana hada hannuwansa guɗaya yace"dan Allah oga kayi hakuri wallahi bansan wannan yarinyar ta wajenka bane da ban karɓi wannan aikin ba. Suɗin banza suɗin wofi wallahi ko nawa zasu bani baxan amshi aikin nan ba,taɓa wannan yarinya hatsarine gareni amun afuwa maigida wallahi duk abunda kakeso zanyi mashi da yardan ka dakuma amincewar ka maigida babban oga da girman kugeranka oga yanda yakema Goga kirari kaɗai hakan ze tabbar maka da yasansa farin sani,shide Goga shiru kawai yayi yana sauraron sa yana cikin zuba aka sake kiran wayan a karo na biyu bayan kashewan da Goga yayi ɗazu"wani ɗan balamin ne?muryan Alh sunusi ta daki dodon kunne su dayake wayan a hands free yasata"oga nine Makwa ya amsa"kaine wa?"nine wanda kabawa aiki ko baka ganeni bane?ajiyar zuciya Alh sunusi yasauke yana duban Alh bala da ɓacin rai yace"kadeji da kunnen ka amma katashi ka ɗaga hankalinka dama namu baki daya. ****** Aisha bata tashi farkawa ba daga suman da tayi ba sai can cikin dare,daddy Ishaq duk hankalin sa a tashe yake yasata a gaba yana zaune bayan tafiyan dr daya kira yaduba ta,yakuma sanar masa da ta farfaɗo saide anmata alluran bacci dan tana bukatar hutu sabida firgita datayi kuma yasake tabbatar masa da zata farka lafiya yayi ƙuri ya zuba mata ido bayaso ko kiftawa yayi,salati dauke a bakinta tashiga buɗe idon ta a hankali a hankali ta sauke shi saman fuskarsa zabura tayi zata mike yayi saurin riƙeta jikinta ne yashiga karkarwa wani irin rawa jikin ta kiyi zuciyarta sai sama da ƙasa yake tsananin rudewa datayi sakamakon ganin sa datayi rintse idon ta tayi tashiga karanta duk addu'a da tazo bakin ta karfi dan ita a tunanin ta fatalwa take gani dan fa bata yarda da Abbanta na rayeba tasan tabbas idan yana raye baze taɓa barinsu tsawun wannan lokaci batare da sunji labarin sa ko yanemi inda suke ba koda khadija ranan da tace yana raye jinta kawai tayi badan ta yarda dayana rayen bane ko faisal dayace mata babanta na raye jinsa kawai tayi dan ganin kaman yanaso yayi amfani da faɗa mata hakan dayayi dan aikin da yasa gaba saboda ita tasan wasu daga cikin abunda yake aikin akai kuma tace dashi zata taimaka masane akan aikinsa dan son ceto rayukan ƙananun yara daga shiga maraici sannan da tsiratar da mata daga shiga zawarci ko banza tasan idan aka kawo karshen su Alh sunusi yakasance tamkar guɓane daga cikin al'umma. Luuu tayi zata koma baya saurin tarota Daddy ishaq yayi yashiga kiran sunan ta"Aisha Aisha Aisha bude idanunki ki kalleni nine Abbanki Aisha karki sake ritsa idonki ina da bukatarku kusa dani riƙo mata hannu yayi yashiga tofa mata addu'a duk yarikice yama rasa abunda zeyi kawai sai yafara zubar da hawaye matsowa lukman yayi yace"oga kayi hakuri ka karfafa zuciyarka kama gode Allah dayasa basuyi mata komai ba,na tabbata akwai abunda Aisha tasani na sirrin su ƙila hakan yasa suka farauce ta. Jin yanda suke tabashi baki hakan yasake tabbar mata da ba fatalwa bane ashe yana raye to idan yana rayen ina yashiga tsawun wannan shekaru ya barsu yabar Anna da wahala da ɗawainiya dasu tsawon wannan shekarun. Bude idanunta da yake tsiyayar da ruwan hawaye tayi tasauke a kansa tabbas Abban tane bazata taɓa manta wa dashi ba,koda shekara dawa suka ɗauka basa tare dashi batasan sanda ta fada jikinsa tasaki kuka ba cewa take"ina katafi kabarmu tsawon wannan lokaci dama kana raye Abba ashe kana a raye kabarmu mukai maraici Abba Anna tasha wahala akanmu ina kashiga sai kuka ita kuka shi kuka ta ƙankame shi sai risgar kuka suke gwanin tausayi suma kansu yaran nasa saida suka shiga matsan kwallan zallah tausayin su dakyar suka tsagaita da kukan Goga ne ya motso yakawo musu ruwa mai sanyi ba musu Daddy ishaq ya ansa yaɓalle marfin goran yamiƙama Aisha ganin ta kasa ansa sai shasshaka take yashiga share mata hawayen yana cewa"kinga yi shiru kuka ya ƙare yanzude sharuwa sai kibani labari ina Nafeesa?tana lafiya ko ina khadija ƴar baba?me nafeesa tahaifa yaro ko yarinya tahaifa duka waƴan anan tambaya ajere yayisu ga Aisha wani sabon kuka tafashe dashi tana sake faɗawa jikin sa tace"baba muma kanmu bamusan inda Anna take ba yanzu. Dagata yayi daga jikinsa yana kallonta da idanunsa da suka kaɗa sukai ja kansa yashiga girgizawa da karfi jin kannasa yake kaman ze rabe gida biyu saboda sarawan da yake masa"a'a Aisha a'a karkice karkice narasa nafee haka yadawo kaman zautacce,zaman da yayi na ƙunci tsawon shekara takwas daya dauka yana ƙillace yadan taɓa lafiyar ƙwaƙwalwar sa abun yakan tashi masa lokaci zuwa lokaci kasancewa ya fuskanci zaman ƙunci da wahala wajen Alh sunusi ganin halin da yashiga yasake tsorata Aisha ƙanƙameshi tayi tashiga kiran"Abba dan Allah kadena abunda kakeyi din nan wallahi tsoro kake bani Anna bata mutuba tana gida tana jiranka dawowarka tsawon wannan lokacin"kin tabbata zaki kaini inda take"eh eh tace tana sake fashewa da sabon kuka shiko jin tace zata kaishi wajen nafeen sa yashiga washewa yana kallon yaran nasa yana cewa"ai dama na fadamu ku nafee zata zo gareni sai kuma yashiga dariya yana cigaba da cewa sunusi ka ƙwashe mun komai nawa ka rabani da kowa nawa ka kawoni tsakar daji ina rayuwa cikin dabbobi inda ba kowa sai kuma ya kalli Aisha dake kuka kaman ranta zefita yace waye ke.......allura da wani daga cikin yaran nasa yasa masa sai kuma ya ɓingire a wajen yafara bacci kallon su Aisha tayi fuska faca faca da hawaye tace"me yasami Abbana "kwantar da hankalin normal ze tashi yanzu   ALLAH YASA MUDACE [8/23, 10:23 PM] Xeenat: https://www.wattpad.com/1376329959?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=cwi8uKh4%2ByzPlkMkVemdvKnrGc6VHwaoZtO52Xm8dlZamUg8YUz%2BJDJ4DESRgIxVZRvJyKb1jzpkIud%2BS327zvWpa4BpXtJf4AT4fC1vhDD0vGapxJSDokkbJislCTxt ___________ *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 67 Dole ne kisan meke tsakanin sa da ita ko itace yarinyar da akace uwar sa ta aura masa. Saurin ɗagowa basma tayi tana kallon mummyn ta jin abunda tace ɗin"Aure kuma mummy?waye uwarsa tamasa auren?ta tambaya taba kafe hajia mariyah da ido,ganin mummyn tata taƙi tanƙata yasa ta cigaba da magana tana fadin bade kina nufin kice Ahmad nada wata matan bayan ni da ake shirin mana aure,kai ina ina tace tana girgiza kai abunda bezai taɓa yuwaba kenan Ahmad bashi da wata matan bayan ni inma auren akai masa to saide AUREN WUCIN GADI naɗan wani lokaci ƙanƙani da zaran nashiga gidan ita kuma zanyi checking nata out taƙare maganan tana huci tamike zata tafi. Hajia bilki tayi saurin dakatar da ita tana cewa"ina kuma zaki ai sai kitsaya kiji dalilin kiran da mukai miki ko?batama juyo ba balle susa ran zata saurare su tace"kuna iya faɗawa mummyna koma mainene amma ni banajin zan iya sauraronku a halin da nake dan raina a ɓace yake daga haka tasa kai ta fita daga falon salaha namara mata baya,salaha ce tayi ƙasa da murya bayan sun fita daga falon tace""gaskiya basma be dace kice dasu hajia haka ba,duk abunda zasu faɗa miki ina ganin abunda ze amfane kine amma gaskiya amsa dakika basu be dace ba kwata kwata naso ace kintsaya kiji da wacce suka zo nasan sabida nema miki mafita suke zaunen"look salaha ki ƙyaleni kina kara batamin raine da wananan maganganun naki yama za'ayi mutumin da nakeso yake shirin zama mijina ace bikin mu dashi saura kwana uku amma ranan tsaka yazo da wata kucaka yaɓatamun party. Yanzu kuma azo anamun faɗa kaman basuga halin da nake ciki ba,na dauka kirana sukai su lallasheni wallahi da nasan kirana sukai dan sumun faɗa wallahi baxan je ba. "Wai meke faruwane sai wani cika kike kina batsewa?"kide bari ramla ba dole tariƙa cika tana batsewan ba tayi tacika mana baki karshe de....bata kaiga kareshewa ba basma ta daka mata tsawa duka ƴan matan da ke wajen dariya suka kwashe dashi suna shewa hakan da sukai yasake tun zura basma ta hau zage zage salaha na bata hakuri karshe kawai sai ta fashe da kukan baƙi ciki. Alhaji sunusi da Alhaji bala tare suka nufi inda Makwa yakwatan ta musu,suna ta aiyana irin azaba da zasu gana mata saide tun kafin sukarasa gun Alh bala kasancewar sa matsoraci duk magana da Alh sunusi ke masa kawai amsa masa yake da eh ko a'a amma hankalin sa kacokan yana kan hanya tun daga nesa ya hango wata mota daban ba wanda su Makwa suka zo da ita ba,"tsaya yace da driven cikin rawar jiki kafin driven ya ida tsayawan yace yi maza kajuya mubar wajen da sauri yi maza yi maxa kajuya haka yarinƙa uzzurawa driven har saida yajuya kallon sa Alh sunusi yayi damuwa kwance saman fuskar sa yace"lafiyan ka bala?irin wannan ruɗewa haka sai kace wanda yayi arangama da zaki ko damusa"ansamu matsalane Alh wancen motar ba tasu bace kuma wanda yake tsaye kusa da motan baya daga cikin su banma taɓa ganin sa ba. Take zufa yashiga tsastsafo ma Alh sunusi dan shi kansa yanzu yafara tsorata da alamarin sa dan komai nasa lalacewa yake duk abunda yasa hannu ciki yanzu zasamu matsala ko daga gareshi hakan yake faruwa ko daga wanninsa shide har yanzu yakasa ganewa dolene daren yau a zauna meeting koda a maƙabartane duk da wasunsu basason tattaunawan maƙabartan amma yazama muso dole duka wannan magana yanayin sa a zuciyan . ********* Aisha zaune tayi tasaka Abbanta gaba sai kallon sa take ko kiftawa batasonyi"Aisha taji ankira ta ɗagowa tayi ta kalli mai kiran nata wanda yama Abban ta allura ɗazune yamiƙo mata ledan dake hannun sa karɓa tayi ta ajiye bata bude ba,shima zaman yayi kusa da ita shiru sukai dukkan su kaman na minti biyu zuwa uku sai can mutumin yakatse shirun yana fadin"karkiji komai nan da karfe sha biyu zakiga ya tashi normal,gyaɗa masa kanta tayi cike da damuwa kaman bazatayi magana ba sai kuma tace"tun yaushe yake fama da irin hakan?kaidin likitane kokuwa....sai kuma tayi shiru ganin yanda yake kallon ta sai yamata ƙwarjini...."ko likitan bogi ko?shima yafada yana murmushi riƙe bakin tayi da hannu tace"nide bance ba"faɗaɗa fuskar sa yayi yana cewa"eh bakice ba amma nasan zakice din ne ai,murmushi tayi ganin yanda yasake da ita kaman dama can yasanta"sunana isma'il hashim kuma na karanci likitanci na gama karatuna garin neman aiki wani attajiri yana ganin takadduna ba kunya ba tsoron Allah yace"wannan takardun da ɗansa na'im suka cancanta badani ba,jin abunda suke tattaunwa akai yasani daukan kayana nabar waje to kinsan halinda kasar mu yake nazalunci shuwagaban ninmu su komai ƙanƙantar shugabanci da kabasu sai sunci amanan ƙasar data al'ummanta to wallahi ina faɗa miki hargida aka biyoni cikin dare aka tafi dani,nima kuma dama kaman nasan za'arina tunda naji wannan Alhajin yana kiran million 20 ze bayar nasan za ayi haka dan haka da dare nabawa ƙawanta takardun wajen yayana,ni kuma akai garkuwa dani sai naba da takarduna harfa gidan mu saida sukabi dare sukaje ba inda basu dubaba amma basu samu ba,hakan yasake tun zura Alhajin shine yamun barazana da kisa idan naki bada takardun ba nau'i na azaba da basu ganamun ba Aisha niko nace wallahi ko kasheni zeyi ba zan bayar ba kawai dan anga iyayena su ba kowan kowa bane sannan bamuda idon sani a gomnati shine sukaci gaba da tsareni harma Allah yahaɗani da mahaifinki ...."tab lallai kaga tasku jiwani karfin hali kai da wahalan karatu su da shan ramo cewa Aisha sai kuma tace amma lokacin da ka haɗu da Abbana a wani irin yanayi kagansa?shiru yayi kaman ba zece kamai ba sai kuma yace"gaskiya Aisha nasame shi cikin mawuyacin hali da a kullum da akwai wani likita da ake turowa yana nasa allura ashe alluran na birkita masa ƙwakwalwa yake zuwa yamasa kullum baya cikin hayyacin sa,saide wani ikon Allah duk lokacin sallah idan yayi yakan tashi yayi sallah cikin nutsuwa,abun yana bani mamaki kuma ba wanda zan tambaya balle nasamu amsa,da kwai wani mutum dake zuwa wajen sa duk ranan alhamis dadare ze zauna ya aske masa kansa sannan ze yanka masa farace sai ya tafi da gashin dakuma farcen cikin wata jar ƙwalle akwai xuwan da yayi naji yana cewa"Ishaq kai wani irin hatsabibin mutum ne duk asirin da nake maka yau tsawin shekara shida amma haryau baya tasiri akanka allura da nasaka anayi makama banga alamum yana aiki a jikin ba gashi ƙungiya tace bata bukatar jininka yanzu saina ahalinka idan ansamu sai da jininsu sannan asirinmu zeyi tasiri kanka,ga kai kuma sabida tsabar wayo bansa wace duniya kakai iyalan naka ba. tun daga nan nafara bibiyar duk lamuran sa karshe alluran da ake masa na danne likitan naƙwace bayan namasa dan banzan duka nace sai nayi masa na daureshi a ɗakin da muke shine fa dayaga ba sarki sai Allah yabini hakuri na barshi yakuma yimun alkawarin ba ze sake yimasa ba amma ze rinƙa zuwa yana masa wanda zerinƙa sakashi bacci ƙwaƙwalwarsa tasamu hutu yakuma kawomin magunguna ina bashi yana sha ban yarda dashi ba,saida na anshi wayan sa nashiga browser nayi searching sunan magani da alluran a ta google nagani sannan na yarda nabarshi da yace dani idan yace baxeyi ba wayan nan mutanen nan sawa zasuyi a kasheshi kuma yarda gaskiyane sa dan basu da imani bazance ba zasuyi ba zasuyi komai ma dan biyan bukatan su sannan duk sanda yakawo alluran ni nake masa magunguna kuma idan yashi yin sallah nakan bashi bayan nasa ya ɗanci abinci kinji handa akai ɗago kanda zeyi kawai sai yaga Aisha hawaye faca faca a fuskarta na tausawa Abbanta hakuri zakiyi Aisha kima gode Allah dayasa suka barshi da ransa. Share hawayen ta tashigayi tace"mun gode sosai da taimakon da kai ma Abbanmu Allah yabiyaka da mafificin alher"amin ƙanwata yanxu de bude kici abincin karya huce"tom kawai tace sai kuma ta waiga ta kalli su Goga dake zaune suna lido a waya tayi ƙasa da murya tace"sukuma wayancan fa?ɗagowa yayi sukayi ido biyu da goga yana murmushi yace"sune waƴan da suka ƙuɓutar damu nan din da muke zaune ma gidan sune sannan su din sunsan sirrin komai na Alhajin da yakama Abbanki hatta sirrin gidan Alhajin idan akwai wanda basu sani ba to ɗai ɗaine"kun haɗa kai kuna gulma ko?"gulma kuma suka faɗa atare sai goga yace"eh in ba gulma kuke ba to me kuke kun hada kai tode kuyi a hankali kar ɗayanku ya ciji kunnen ɗan uwan sa ehem karkuce ban faɗa muka ba,dariya sukai dukan su banda Aisha data ɗan murmusa. Ahmad kaman wani zautacce haka yakoma sanda yazo gidan Anty hajiya yaga halin da take ciki kaman yayi kuka yaɗauki lefin duka yadaurawa kansa cewa yake kiyafeni Anty hajia duka nina jawomuku shiga wannan halin da kuke ciki da nasan haka ze faru da bange da ita ba"kai ma ganganci kai Ahmad kai da uwayenka duka baku daukeni abakin komai ba har aure zasu maka kuma saboda rashin hankali irin naka kadauke ta kaje da ita wajen sha'anin bikin ƴar Alhaji sunusi kayi tsammanin kaci banza ai wannan wasane sai kuma ya kwashe da dariya yace wannan auren ai na wucin gadine kaman yanda kukayi shi a gantale haka ze kare a gantalen dukkansu sakin baki sukai suna kallon sa harda Ammi dake rungume da Malika suna kuka. "Alhaji amma kanka ɗaya kai wai mai yasaka baka da tunani shin baka ganin halin da ƙanwata keci ne?harkake irin wannan magana to bari kaji inde Alhaji sunusi ne kai kanka ba barin ka yayi ba dan ƙaidinsa yawa garesa yamafi mata karkayi zato ko tsammanin katsira daga kaidin sane,kaima a'a baka tsiraba munanan wataran zamu ganku a rana kai da shin,kai da anyi magana idan tashafe sa karinka tada hankalin kana tada jijiyar wuya karka manta idan ma kamance ni bara na tunatar da kai shine wanda yajefaka halin da kake ciki yanzu amma duk da haka baka hankalta ba da zaran kaji an ambaci sunan sa jikin ka har rawa yake aure kuma da kullum kake kiran auren wucin gadi to bara kaji saide wanda kake shirin yimasa shine na wucin gadi amma wanda kake kira mu uwayansa mun masa kai ma kanka saikayi alfahari da ita dan sai yayi karƙo saboda nariga da nasawa abun albarka kuma albarkata saitayi ta bibiyarsu. "Ma'arufa ni kike gayawa magana haka saboda kawai nafaɗi gaskiya,Ammi zatayi magana Ahmad yayi saurin cewa dan ALLAH Ammi kudena haka mana idan shi be damu da halin da Anty hajia ke ciki ba ke ai ƙanwarkice kuma be kamata ki biye masa kuna musayan nƴawu anan mutane na ganin ku ba. [8/26, 10:05 AM] Ummahani: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 68 Shiru Ammi tayi badan tasoba ta zubawa ƙanwarta dake kwance saman gado ido duk ta rame ta zube lokaci guda kaman wacce ta kwanta jinyar kwanaki,sauke ajiyar zuciya tayi sai kuma ta kalli Ahmad dayayi zuru da faisal dake gyawa mahaifiyar sa kwanciya tace"yanxu ya'ake ciki? "Eh Ammi yanzu haka nayi report tun tuni harma an baza jami'an tsaro dukkan nin madakatai tashan mota harma da airport jami'an mu na nan dakuma dukkan nin checkin point faisal ya amsa mata da faɗi haka. "Allah ya bayyanar da ita yasa asame mata cikin aminci da salama"amin suka amsa"su kuma waƴan da suka ɗauke ta Allah yatoni asirin hegu"hmmm ƙwafa Alh badamasi yayi haryasa kai ze fita sai kuma yatsaya jin Ammi na tambayan Ahmad"kai meyakai ka tafiya da ita wajen shagalin su,bayan kasan uban yariyar nan yayake yanzu a wani hali ma ƴar mutane keciki?"shin tana hannu nagari kokuwa?Ahmad ina jin tsoro gaskiya bazan ɓoye maka ba ina jiyewa ƴar nan tsoron wa annan azzaluman sai kuma ta ɗaga hannun ta sama tana tacewa ya Allah ga baiwarka nan Aisha hannun ɓata gari ya Allah karka bawa duk wanda yakeson ya cutar da ita dama,karka basu daman da zasuyi galaba a kanta. "Wai ke ma'arufa mekike nufi da Alh sunusi ne?nasan duk wannan abun washi kikewa,shin wani abu yataɓa haɗaki dashine?kinfa saka bawan Allan nan gaba haba haba ko dan suru....ɗaga masa hannu tayi bata bari yaƙare maganan sa ba tace"yanzu me nace Alhaji fisabilillahi kokaji na ambaci sunan wani anan sai kuma ta juya ta kalli Ahmad tace mundin ba'asami ƴar mutane ba wallahi kadeji na rantse maka ko ƴar sarkin makka ce jibi baza'a ɗaura wannan auren ba. Dasauri Alh badamasi ya juya yana kallon ta baki buɗe shide Ahmad be'iya cewa komai ba saima ƙasa daya sakeyi da kansa dan shi kadai yasan abunda yakeji acikin zuciyar sa. Basma saida tayi kukanta taƙushi sannan ne salaha da tunɗazu ke bata baki tasamu daman ta kulata tace"yanzu me wancan kucakan take da wanda ni bani dashi,eh salaha kiga yanda mine ya tozartani a bayyanan nasi?ai wannan ma tozarci ne ke kinsan irin yanda nariƙa cika baki a cikin ƙawayen mu amma abunda zemun kenan irin sakayya da ze mun kenan dan yaga inason shi nasan tunda yace bazezo ya halarci partyn mu ko ɗaya ba matsawa danayi akan sai yazo na haɗa da daddyna yama daddynsa magana yazo shisa yamun haka ba komai taƙare magana. tana share guntun ƙwallan idon ta"amma ke yanzu bade kina nufin daga shi har itan sunci bulus ba?kallon salaha tayi tace"ban gane mekikeson kice ba?"ina nufin yanxu tashi zamuyi idan akwai kuɗi a hannun ki muje wajen wani malami da zeyi mana aiki akan sa dama ta ita yarinyar ta yanda koda akwai wani alaqa tsakanin su a raba adasa musu tsanar junan su a zukatan su sannan a dasa soyayyarki a zuciyar sa ta yanda zeji duk duniya ba wanda yakeso da kauna sama dake koda uwar da ta haifesa sai abunda kikace zeyi mata. Hmm tasauke ajiyar zuciya basma tayi cike da jin daɗi abunda salaha tace saide zuciyata taso rabuwa kashi biyu ɗaya zuciyar tata na hani gareta yayin da ɗayan ke ingizata ga tabi shawaran salahan da nuna mata ta hakane kaɗai zata rama abunda sukai mata wajen maida Aisha ƴar aikin ta shikuma Ahmad sai yanda tayi dashi dan ko wanka idan taƙi sai tace ya ɗauketa yaje yamata tana wannan tinanin kawai ta ssaki murmushi tamiƙe a hankali tayi taku ɗaya biyu tayi wani juyi tace"hmmm waya ganni ina juya mine yanda nakeso,ƴar dariya salaha tayi sannan tayi ƙasa da murya tace idan kinaso yin haka zakiyi kede kawai shirya muje gobe dawuri dan musamu zuwa da wuri saboda nisan waje kinga yanzu dare yayi amma gobe karfe shidan safe zamu fita dan musamu isowa dawuri"amma daddyna fa tafaɗa da alaman tsoro agareta"sai kisan karyar da zaki musu,abu mai sauki ma ce musu zakiyi zamu je raba iv kinga bazasu tuhumeki ba,ajiyar zuciya ta sauke tana cewa"amma gaskiya salaha kin iya law sosai dama ace law kika kiranta,dariyar jin daɗi salaha tayi itako basma toilet ta shiga cike da ƙwarin gwiwa ta wanko fuskarta tafito tazo gaba tangamemen madubi ta dake jera kayan shafe shafe dakuma turaruka masu sanyin kamshi dakuma tsada ta gyara fuskanta sannan tafito zuwa falo wajen ƙawayen ta dasuke zazzaune ana hiran yaushe gamo fitowarta yasasu yin shewa da dariya itama biye musu tayi tsaɓanin ɗazu dasukai mata irin haka tasaka musu kukan haushi yanzu ko samun waje tayi ta zauna a kacigaba da hiran da ita. Hajia mariyah duk kunya ta lulluɓeta da abunda basma tayi,shuru sukai dukkan su ko wannensu da abunda yake ayyanawa aran sa sai hajia shema ce ta katse shiru da cewa"gaskiya hajia mariyah bazan ɓoye miki ba sam baku bawa yarinyar da tarbiya daya dace da ita ba,wannan shine abunda zatakai gidan mutane irin abunda zataje tayi ma surukan ta kenan,amma kinfi kowa sanin hajia ma'arufa ba macece tsayayya a gidanta dan ko abinci bata yarda da ƴan aiki su dafa mata ba,ita keyin koman ta amma ni banga alamun ko ruwan shayi basma ta iya dafawa ba. "Taya kuwa zata iya dafawa bayan sun sangarta yarinya bata ganin kan kowa da gashi idan ba haka ba ina basma zata tsaya tana kallon tsaban idon mu tace mufaɗawa uwarta abunda zamu faɗa mata idan yaso ita tafaɗa mata daga baya,hajia balki ce ke wannan magana. A ƙule hajia mariyah ta miƙe tsaye tace"ya'ishe ku haka me haka ai be kamata kurinƙa faɗin irin haka a gabana ba,ita din yarinyace karama zata denane wataran. ********* Bayan kwana biyu Aishace zaune a babban falon gidan dasu Goga da safe jama'an gida gaba ɗaya sun hallara suna karin kumullon safe dan dama wannan yaxame musu ɗabi'a duk safe tare suke karyawa kafin kowa ya kama gaban sa kuma anan duka suke kawo report din abunda suka samo. Goga dasuke tattaunawa da daddy ishaq yamasa nuni da Aisha da take zaune tayi shiru sai jujjuya kofin shayi datake riƙe dashi da cokali take"Aisha Abbanta yakira sunan ta"na'am Abba ta amsa masa sannan taɗago tana kallon sa"kinason komawa gida ko? Tsunkuyar da kanta tayi kasa ba tare data amsa ba yacigaba dacewa yanzu mustapha ze mai daki saide karki manta da duk abunda na gayamiki jiya,komai ze tafi yanda muka tsara karki mance da komai yarana zasuna bibiyarki suna tare dake ako ina kuma duk sanda kikaso ganina zaki iya sanar da yarana dake tare daku sukawo ki inda nake koda wasa ko ƴar baba karkice mata kin gannin(khadija kanwar ta yake nufi)"meyasa Abba?batasan sanda bakinta tafurta tambayan ba"sai lokacin hakan yayi tukun na. Mustapha ne yashiga bayan ya gaida su yasamu wajen zama ya zauna yana haɗawa kansa abincin ɗan dungurin sa goga yayi yana cewa"ummm mustapha acici kode aci towa ba cewar goge yana dariya dan sunan da suke kiransa tun yana karami dan baya wasa da cikinsa wajen cin abinci shiyasa suka saka masa suna aci towu. Saida yagama cin abinci yacika cikin sa sannan yakoma ya zauna yana fuskantan daddy ishaq yace"oga akwai matsala"wace irin matsala kuma mustapha?suka haɗa baki wajen tambayan sa"eh oga dan hajiya mariƙiyar Aisha bata da lafiya jininta ya hau sosai ta tashi hankalin ta sosai bata da aiki sai kuka da kiran yar amana take,taƙi kwantar da hankalin ta balle asamu jinin nata yasauka. Sosai Aisha taruɗe jin halin da Anty hajia ke ciki"kinga kwatar da hankalin ki yanzu za maidaki Abban nata yafada amma ina duk yanda yaso Aisha nitsu kasa nitsuwa tayi daga karshe kuka tasaka masa dole yace to shiga kishirya kixo ya kaiki aiko da sauri tamiƙe tanufi ɗaki da take. Ajiyar zuciya suka sauke duka kana suka maida hankalin su kan mustapha bayan shigar Aisha ɗaki"muna jinka yauwa ajiya da darene aka kawoma Alh badamasi takardan sammaci daga babban kotu,sannan a daren yau ne Alh sunusi dama yan kungiyarsu baki ɗaya suka shirya taron gaggawa"aina zasu gudanar da taron nasu wannan karon?"meyasa kakeson sanin inda zasuyin tafiya zakayi?"gogane yayi tambayan farkon yayinda shima goge ya tambayeshi yaji shin zashine dayake tambayan"eh zani kasan darene sannan akwai wasu abubuwa da bazamu sani ba sai wani cikinmu ya halarci taron nasu mafi akasari sunfi yinsa karfe biyun dare sa'ilinda ƙafa yaɗauke. "An mustapha ina wannan na'ura dana baka jiya"oga nabawa sani yama ajiye a falo karkashin centar table dake tsakiyar falon"good cewar daddy ishaq"very bad sir kallon goga yayi dan son jin ƙarin bayani"eh saboda centar table ɗin na glass ne kaga dole a gani oga,dan jim sukai duk sai kuma goge ya kira sanin a waya dan yace ya canza ma na'uran waje,bayan sani ya dauki wayan suka gaisa sai goge yace"kana jina sani?"eh ina jinka oga yauwa wannan ɗan abun da mustapha yabaka jiya ka dauka kamai dashi can jikin tv dake falon ka maƙala ta wajen baƙin jikin tv ta yanda baza'a gani ba"angama oga ya amsa sai kuma goge yace bawata matsala ko ta wajen naku"yanzu de babu saide ina ga kaman yau dukkan su a ruɗe suke barin ma Alh bala"ko kaji me yaruɗar dashi"gaskiya bankai gasanin abunda yake faruwan ba amma zan saka ido nagani idan naji zanyi alert dinka"yauwa hakan yayi daga haka suka kashe wayan a tare basa bukatar karin bayani dan wayan a free hand yake sunji komai dasuke tattaunawan daidai nan Aisha tafito dan haka miƙewa mustapha yayi. Kallon ta Abban nata yayi fuska ƙunshe da murmushi yace"Aisha ki kikula sosai sannan maganan wani natasha da wancan jami'in yayi miki bashi inajiye miki tsoron faɗawa tarkon sunusi dan ba imani ne dashi ba,ze kuma iyayin komai saboda biyan buƙatar sa ta duniya. Shi faisal bashine babba wajen aikin suba yana da nagaba dashi sannan umurnin su yake jira a kowani lokaci,kinga kuwa bazeyu yace zeyi wani aikin shi kaɗai ba tare da sanin su ba,idan ma yayin akasamu akasi ya turaki kinge can shikuma yasamu kiran gaggawa kinga dole umurnin manyan sa zebi ya tafi kiran da akai masa ke kuma fa?shiru yayi ita ma Aishan batayi magana ba amma ta gamsu da bayanin sa ɗari bisa ɗari,dan haka ya daura da cewa kibar zancen natashan nan kiyi abunda muka saki kawai aikin ki ze farane daga jibi a gidan muna da yaran mu can kama daga maigadi da mai wanki da guga harma da matar da take aikace aikacen cikin gida dukkan su yaranmu kinga ko zasamu matsala abun zexo da sauki"in sha Allah Abba bazama asamu matsalan ba wannan karon sai kayi nasara sai duniya tasan waye Alh sunusi dakuma abunda yake aikatawa Abba na barku lafiya,tace dasu daga haka tanufi kofan fita tana share hawayen da take ta kokarin riƙisu. Ko a mota batama mustapha magana ba rufe kanta tayi da dan kwalinta tashiga yin kuka saida tayi mai isanta sannan tayi shiru tashare idon a hankali ta maida dubanta kan mistapha dake tuƙin sa hankali kwance tace"kai ni A&B daga haka tayi shiru shima be nemi sanin meyasa tace yakaita can din ba,suna shiga layin sun danyi tafiya kaɗan sai tace tsaya anan yayi parkin motan nesa da wajen saida ta fita tace"zaka iya juyawa saboda akwai cctv camera a can din banason a ganmu tare,daga haka tanufi takawa a hankali tana ɗan share hawayen ta dayaƙi tsayawa harta ƙarasa shiga ciki tun daga bakin get maigadi yadinga kallon ta yana mata sannu tana shiga ciki khalid ne yasoma ganinta aikuwa kaman ƙaramin yaro yakwasa dagudu sai office ɗin ahmad yana haki beko tsaya yin knocking ba kwai sai ganin sa sukai yafaɗa daidai basma dake zaune tafara aiwatar da abunda boka yace tayi dan daga wajen boka suke ko gida bata je ba tabiyo ta nan din,ta buɗe wani ɗan karamin ƙwalba ta daura saman babban table dake cikin office din ta ɓoyeta bayan jakarta zata zuba maganin ciki kenan Aisha ma tafaɗo office ɗin wani irin zabura basma tayi garin miƙewar da zatayi kawai kwalbar ta faɗi ƙasa sai ji kake tatasss......   ALLAH YASA MUDACE [8/30, 8:12 PM] Ummahani: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 69 Saurin duƙawa ƙasa Aisha tayi ya yinda xuciyar Basma yashiga dukan tara tara dan yafi karfin akira shi da uku uku dan tariga da ta saddakar ƙwalbar Aisha zata ɗauko tatona mata asiri saide ga mamakin ta sai ganin Aisha tayi duƙe gabanta tana mai bata hakuri ɓoyayyen ajiyar zuciya ta sauke sannan ta maida dubanta kan Aisha dake duƙe a gabanta cike da ƙaskanci take kallon Aishan nan ta tuna da maganasu da boka. Kina nan zata zo tabaki hakuri daga nan kiwuce kai tsaye wajen angon naki dan ai watar da aikin da muka baki yanzu haka yana zaune a office din sa yana tunanin wata yarinya da ban bake ba. "Kan bala boka wacce asararrarce takeson shiga gonata?"shine bamu sani ba dan bama ganin abunda cikin zuciyar mutum shikuma wannan zuciyar sa arufe take ruf,har wani irin huci take naɓacin rai tasake cewa"ita kuma yarinyar da nazo amun aiki akanta fa?da wani mahaukacin dariya boka ya kece wanda saida dajin ya'amsa amon dariyar nasa daya wage wagegen bakin sa dayake fidda wani irin ɗoyin wari saida tsagaita dayin dariyar ya kalle ta yace"itama yanzu haka mun tura aljani ɗan tsaiko kuma a namu ɓan garen zamu turnzura miki ita yarinyar a duk inda take zata biyoki ta baki hakuri nan ke kuma zakiyi amfani da daman wajen juyata yanda kike so kirama abunda tamiki saide ki kiyaye abu ɗaya shine duk sanda zakiyi amfani da maganin mu ba kiran sunan Allah dan duk wanda yaxo wajenmu ɓatatcene wanda yariga yakwashe kayan sa gaban ma'aiki sannan kiyi ƙoƙarin gano mai ke tsakanin ta da shi mijin da zai auraki idan kika gano sai kizo ayi musu farraƙu ta yanda zamu raba tsakanin su rabuwa ta har abada. Basma tare suka je office ɗin Ahmad da salaha sunko taki sa'a yana ciki,tun daga bakin ƙofar shiga office ɗin ta ciro wani ɗan ƙaramin ƙwalba acikin jakarta ta shiga shafa wani abu mai kama da turare a fuska sau uku kaman yanda bokan yace mata kuma shafarwa da zatayi ba duka face din bane a'a cross zata zana dan haka cikin sauri tayi sannan suka shiga ciki. Cikin son nuna isa da son nuna ita watace tana yatsine face da bintse baki tace"zan hakura amma da sharaɗi,da sauri Aisha ta amsa da"wani irin sharaɗi?dazaki zauna dani a gidan mu har tsawon wata biyu bayan aurena zaki zamemun ƴar aiki idan kin yarda da hakan to kuwa tabbas zan tafe miki zan kuma yin miki kyauta mafi daraja"zan duba yuwuwar hakan gareni,cewar Aisha tana fadin haka tajuya zata fita batare da takalli ko inda Ahmad ɗin ke tsaye yana ta kallon ta a mamakance ikon Allah waime kedamun yarinyar nan ne yafiɗi haka a ransa yafi aƙirga. Alhaji badamasi komawarsa gida kenan daga dubiyar Anty hajia zuciyar sa sai tafarfasa yake ga miki da sa'insa dasukai da Ammi duk haushinsu yakeji yana nan zaune a falo maigadi yayi sallama yashigo ya duƙa ya gaida dashi amsawa yayi yana kafesa da ido yace"Alhaji dama wasune sukazo suna son magana da kai,dan shiru yayi sai kuma yace"cene musu sushigo,mikewa maigadin yayi yama mutanen iso har bakin kofan shiga falon sannan yajuya bakin aikin sa,da sallama suka shiga amsa musu sallaman Alh badamasi yayi yana cewa"bismillah ganan waje ku zauna. Bamusu suka zauna bayan sun gaisa ne yane yake kallon su cike da rashin sani ɗaya daga cikin su biyun yace"Alhaji baka ganemu ba ko?'eh wallahi kallon da nake muku kenan kaman naso ganeku kaman kuma ban taɓa ganin kuba,"eh kwarai tayu kasanmun miƙa masa wani farar takarda dake linke yayi yace"daga kotu muke wannan sammacine kallon su Alh badamasi yake a razane yanda yarazanan nan da a tsaye yake da tabbas daya fadi kasa sa'ansa guda a zaune yake,take wani irin zufa ya karyo masa,sabida tsaban rudewa da yayi ko sunan Allah ne yakasa ambata hannu yakai ya dauki ruwa dake a jiye cikin juk dake saman wani ɗan karamin table yakafa bakin sa a juk ɗin saida yasha kusan rabi sannan ya maida juk din a jiye gaban rigan sa duka yajiƙe da ruwa,kana ganinsa kasan duka a ruɗe yake ganin yanda yaruɗe ɗayan daga cikin su biyun yace"yi hakuri Alhaji bafa komai bane idan kana da gaskiyanka ko ina aka kaika gaskiyanka shin ze ƙwaceka kaide kawai abunda zance dakai karka ɓoye komai abunda kasani kuma karka zama mai magana biyu duk tambaya da zamaka kasa nutsuwa a ranka kafin ka amsa tambaya da zamaka wannan gudumawa nane daga haka sukai masa sallama suka tafi duk magana da mutumin yake masa ba abunda daya fahinta abun yake iya ganewa illa kalman sammaci saboda tsaban tsoro da ruɗewa ko takardan kasa budewa yayi yagani balle yasan ko akan me ake tuhumasa. Da sauri Ahmad yamara mata baya ganin tamaƙe bata ko kalle saba balle yasa ran zata masa magana saima wani abu datake kaman drama wa basma shi abun natama daure masa kai yayi"ina tashiga kwana biyu ta barsu da zullumin wani hali take ciki suna yawon nemanta tun fitowar rana idan sun fita sai fadiwarta suke dawowa gida tunda ta ɓatan nan yau kwana biyu ko ruwa bayajin yasha ya tsargemasa ciki baccin sama ragaggene ga anty hajia na kwance ba lafiya amm.....tunanin sa ya katsane ganin ta nufi bakin get gadan gadan ba tare da ttama kula kowa ba. "Hajia mariyah kishirya na kaiki wajen malamin gangare neman taimako nasan kuma zeyin dan kinsan aikin sa kaman yanka wuka yake,hmmm hakane hajia bilki shiyasa nake yinki dan baki taɓa bani shawaran banji daɗin sa ba,yanzu zamu ko?"eh idan akwai dumus a hannunki ai muje kawai kinsa ance abari yahuce shike kawo rabon wani gwara de kawai muje yanzu dan a wuce wajen. Hajia shema tace"tom nide balki zan koma gida kinsan yau nike da Alhji kwara naje dawuri"gaskiya kan ki kasa ki tsare kodan saboda wannan munafukar kishiya taki"ai kede bari ina ganin barukanci kala kala wajen wannan figigiyar matan"kice har yanzu kina fama?"ai saima abunda yaƙaru mariyah kwanaki fa harni Alh yakalli tsaban idona yake cewa wai in saida masa da kwanana zaije gunta dan tafini daɗi,zaro idanunsu sukai dukkan su suna haɗa baki wajen cewa"me "Eh"kuma kika sayar din?lalle balki ashe bakisan wace shema ba kawai cemasa nayi idan maɗacice ni haka zayi idan yaso ranar girkin ta taje yasha zuma amma bazan sayar ma ƴar iskar nan kwanana ba. Dariya suka kwashe a tare suna shewa tare da tafawa kai kace yarane yan sweet sixteen saida suka shirya zasu fita sannan hajia mariya takira Alh sunusu a waya yana dauka tace zasu fita dasu hajia balki zata karbo sako sai kin dawo kawai yace yakashe wayan sa. Aisha na gaf da zata fita bakin get Ahmad ya cimmata yana zuwa yasa hannu yariko hannunta ɗaya"kacikani tace dashi batare da juya ta kalle sa ba. "Eashow yakira ta cikin sanyin murya bata amsa masaba shima be damu da ta amsan ba,kinko san halin da muka shiga da bamu ganki ba?"musu shiga de suka shiga waƴanda suka damu da ɓatata amma bakai dake zaune kuna tsara yanda bikinku ze kasance ba"what eashow kina da hankali kuwa?kinsan abunda kike cewa kuwa?kinsan matsayinki wajena aiko dan igiyar aurena dake kanki dole na damu a fusace Aisha ta juya tana kallon sa tace"Aure aure hmmm ai na wucin gadine naɗan wani lokaci da zaran kayi aurenka da wacce kake so zaɓinka ba xaɓin kowa ba ni kuma saika sauwake mun dan nasamu na aure wanda nakeso yake sona wani irin fizgota yayi bata ankara ba sai jinta tayi ta faɗa ƙirgin sa daidai basma sun fito tana dariya Aisha itako Aisha fashewa masa da kuka tayi basma ko batasan sanda jakar hannunta yatsuɓuce yafaɗi kasa ba......     ALLAH YASA MUDACE. [8/31, 10:41 PM] Ummahani: https://www.wattpad.com/1378779979?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=xXtCJtVVeX0aFRhZgChjPK5QXYBpFk9TS13cjSFrhoroQOhcGWB629ZoJRMZdiBZk%2BPonTbi76KfA29ABFg56t1aQoR0oZToW10NLHMD8vKnx9AWPiDV%2Fy7tL0zz33JI ______________ *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 70 Murtsuƙe idonta tayi wai ko bata gani da kyau bane,amma still koda tasake buɗe idon haryanzun de suɗin take gani hannun su sarƙafe dana juna wani abu mai kauri daya tokare mata makoshi tahaɗiya jikake mukutt take tasoma gani duhu yana neman rufe mata ganin ta,hannun salaha dake tsaye gefenta ta damƙa da karfi harsai da salaha taɗanyi karamin ƙara"aucch ƙawata lafiya?kika damƙeni haka tayi tambayar tana idon ta na kallon inda basman take kallo. "Kina kallon abunda nake gani kuwa?kode ido na kemun gizo kaman yanda yasoma yimun daga jiya. Takai dubanta inda basma kenuna mata,sai kuma tasauke ɓoyayyan ajiyar zuciya ganin bataga kowa a wajen ba,tasan halin ƙawartata yanzune zata tada mata da bore tace aikin da bokan yamata beyi ba kuma su samu matsala da ita dan itake kaiwa da bokan customer's yana ware mata kasonta yawan kudi daya samu awajen mutum itama yawan biyan da zeyi mata. Abunda basma bata sani ba shine sanda take wa salaha magana Ahmad ya fixge hannun Aisha duk da turge masa da take ta cusata mota da khalid ya kawo wajen,suka fita. Alhaji sunusi zaune suke da tare da Alhaji surajo suna tattauna yanda meetin din nasu ze kasance shi Alh sunusi yaso ayi zaman meetin din daren yau yayinda Alh surajo yace"gaskiya sunusi bazeyu muyi zaman meetin yau ba dan ita kanta zaman tana da dalilinta dakuma ƙa'idan ta,dan haka dolene sai an zauna a ƙungiya an tattauna batun kafin a zauna idan shugaba ya yarje mana yin hakan. Cike da ɓacin rai Alh sunusi yamiƙe tsaye yana kallon Alh surajo rai a ɓace yake magana"ammade kasan abunda ke shirin tunƙaro mu ko?"eh nasani same?shima ya amsa masa cikin halin ko in kula. "oh baka damatsala tunda kasan yaranmu da aka kame babu naka ƙo ɗaya acikin su sannan ba wanda yasan fuskan balle yanuna ka,shisa baka damu da damuwar tamu ba. "Eh same ?idan nadamu da damuwar taku,a kufule Alh sunusi yace"karka dauka idan rubtawane mu kaɗai ze rubta damu a'a harda kai cikin kuwa. Daga zaunan dayake ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallon Alh sunusi daya cika yana batsewa yace"inason kasan abu guda duk rashin imanina ni surajo maci amana bane dan haka idan ma ruftawance zatazo mun da sauki tunda banci amanan kowa ba amma kai fa?yanuna Alh sunusi dake ƙame kaman andasa shi,dan haka kaje dukma abunda zakayi kayi saide kasani duk tsuntsu dayaja ruwa shi ruwa ze ja. ****** Aisha duk mutsu mutsun son kwace hannun ta da take kasawa tayi yana zurata mota khalid yaja suka tafi,matseta yayi ya kawo fuskansa daf nata harsuna iya jin numfashi junansu saboda yanda kusancin su yake numfashi mai ɗumi yafesa mata saman fuskarta hakan saiya haddasa mata rawan jiki baya tayi niyar ja amma be bata daman yin hakan ba saboda yanda ya matseta jikin kujeran motan rintse idanun ta tayi da karfi jikin ta sai ƙyarma yake take taji jikinta yaɗauki ɗumi kaman mai shirin kamuwa da zazzaɓi. Shima anashi ɓangaren hakace ta kasance dashi wani irin kasalane yaji yasaukar masa yanda bugun ƙirjinta dayake sama da ƙasa yake gogan nasa ƙirjin take yaji wani abu ya tsargar masa tun daga tsakar kansa har zuwa babban yatsan ƙafar sa. Kai hannun ta tayi da niyar tureshi saukan tattausan fatan hannunta kaman na jariri saman fuskar dokin wuyan hakan yasaka shi wani irin shock besan sanda ya ƙanƙameta ba. Yana haɗiye wani abu mai wuyan haɗiya jikake mukut besan sanda yakai kansa tsakanin wuyanta yana shaƙan kamshin turarenta mai sanyi dakuma daɗi hakan sai ya haifarmusu da wata iriyar kasala yayin da bugun zuciyar su ya tsanan ta. Hajiya mariya da hajia bilki gurfane suke gaban malamin su hajia balki tace"ranka yadaɗe malam aiki zakawa kawata ƴarta zata aurar to ranka yadade yaron ne haryanxu muka rasa gane kansa auren su saura kwanaki kawai sai gashi dawata yarinya kuma ita wannan yarinyar ƴar aikin ita amaryar da ze aurene to shine mukeson amana aiki akanta ita yarinyar ta yanda za dasa tsanarta a zuciyar shi angon adasa masa tsananta yaji duk duniya ba wacce yatsana kuma bayason gani sama da ita. Sannan munaso shikuma ango a dasa masa soyayyar ita wanda ze aura ta kare maganan tana langwaɓe kai. Gyara zama malamin yayi yace da hajia mariya tamatso ta ɗauki ɗaya daga cikin carbin daya ajiye,dauka tayi tamiƙa masa karɓa yayi daga hannun nata yana kallo yana jujjuya kansa"lafiya malama?hajia bilki ta tambaya ganin yanda yake jujjuya kannasa kaman wani kadangare mai jan kai yace"hajia aikin ki da sauƙi sannan da wuya. A ruɗe suka amsa masa"kaman ya malam ka ambaci sauki da wuya lokaci ɗaya"eh sauki shine yanda ƴarki zata mallaki zuciyar mijin ta,wuyan kuma shine yarinya da kuka kawo aiki akanta a tsaye take ma'ana bbata wasa wajen yin ibada dakuma addu'a samunta baxeyi sauki a gare ku ba,har sai idan zaki iya kai laya da zan baki makabarta ki binne shi da kanki cikin dare karfe sha biyu daidai,idan kimyi hakan.....ai basu gama sauraren abunda ze faɗa musun ba hajia mariyah tabude baki murya na rawa tace"kalen inje garin binne laya suriƙeni.....ba hajia bilki da suke tare ba hatta shi kansa malamin nasu saida yaƙura mata ido yana cewa"dama wayace miki neman duniya yana da sauki haka jeki tambayi mijinki maza kutashi kubani waje yafaɗa rai aɓace yana nuna musu hanyan.     ALLAH YASA MUDACE [9/5, 6:44 PM] Ummahani: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 71 Sosai su hajia mariyah suka tsorata da yanayin malamin take hajia bilki da tafi hajia mariyah sanin halin sa tazube gaban sa tana mai shimfiɗa hannuwanta tana roƙon sa ganin haka itama hajia mariya tashiga bashi hakuri dakyar de suka samu ya hakura yace sukoma su zauna,komawa sukai suna nazama yadube su dukkan su ganin yanda sukai laushi yasashi gyaran zaman sa yana kallon su yace"shikenan da nace kece zaki aiwatar amma yanzu nayi duba naduba naga bazaki iyayi da kanki ba,zaki iya sawa aimiki. Amma da sharadi zaki bawa duk wanda zeyi muku aikin amma ki tabbatar kina tsaye saiyaje ya burne sannan zaki je ki kwanta wannan shine idan zaku iya to idan ko bazaku iya ba kutashi kubar mun waje. Da sauri suka ce wallahi zamuyi yanda kace malam mude ka taimaka kar asamu matsala"bakuda matsala matukar kukai yanda nace gashi wannan layace yama sunan su? Nan suka faɗa masa sunan ya rubuta jikin laya daga nan yamiƙa masu tace sutashi sutafi ajiye masa maƙudan kuɗaɗe sukai kafin suyi gaba zuciyoyin su cike da jin daɗi. ****** Jikinta sai mazari yake cikin nuna jarumta da rarrabewar murya tace"dan Allah wai me haka kake yine? Buɗe gajiyayyun idanunsa wanda suke ruɗata yayi yazube a kanta kaman bazeyi magana ba sai kuma yabude kaman wanda akasa dole yace"inane kika tafi tsawun kwana biyu? Kallon sa tayi tamaka masa wani zazzafan harara tare da murguɗa masa baki tawatsar dashi tana mai kai kanta gefe batare data amsa tambayarta dayayi ba. Direct asibitin da aka kwantar da Anty hajia khalid yanufa dasu,zaune suka tadda ta saman gado Ammi na fama da ita kan koɗan shayine tasha Faisal dake tsaye daga fege yace"haba anty hajjia dan Allah ki daure kisha ko kaɗan ne zama da yunwa ma kanta itama wata cutace inde Aisha ne ki kwantar da hankalin ki in sha Allahu namiki alkawari za'aganta zatazo garemu cikin aminci....sallamar da khalid yayi musu daga bakin ƙofar dakin shiyasaka suyin shiru suna kallon ƙofan khalid ne a gaba sai Ahmad dake biye dashi daga bayansu kuma sai Aisha,wani irin zabura Anty hajjia tayi sai gata tadiro ƙasa daga saman gado a sukunce ita Aishs ta karasa shiga ɗakin daga tsaƙiyan ɗakin suka rungumi juna suka fara kuka ita de Anty hajia sai Alhamdulillah take ta nanatawa hakan yadauke su kusan minti biyu sannan Anty hajia ita tafara janye jikin ta daga na Aisha tana binta da kallon tuhuma. Ganin yanda take kallon nata yasaka Aisha tsunkuyar da kanta ƙasa tayi tana wasa da zoben hannun ta"inane kika je kika barmu da zullumin ba inda bamu nemeki ba amma ko labarin wanda yace yaga mai kama dake ma bamuyi ba. Itade Aisha taƙi ɗagowa ta kalli kowa dake ɗakin sai sharan hawaye da take,ganinta hakan yasa yah faisal gyaran murya yace"Anty hajia ki bari ta nutsu tukunna yanzu zauna kisha koda shayi ne ko,cewar Ammi komawa tayi saman gadon ta zauna hannun ta rike dana Aisha kaman zaƙwace mata ita"yanxu kan zansha yayah haɗamun harda abincima zanci dariya duka sukai mata tanaci ana ɗan taɓa hira da ita Ahmad ko ya tsurawa Aisha ido kaman maison gano wani abu,duk ɗagowa Aisha zatayi sai sun haɗa ido dashi idsn yakashe mata ido ita kuma ta murguɗa masa baki duk abun nan dasuke Anty hajia na hankalce dasu. Anty hajia na kammala cin abinci tace"kai tadago tana kallon su tace"ai sai akira likitin ya sallamemu mutafi gida ko"ggida suka haɗa baki wajen tambaya. "BAD kace kai kaga yarinyar ko? "Eh ranka yadaɗe Alhaji na ganta ido da ido wallahi zuciyata tafarfasa take Alhaji idan natuna dalilin ta yasaka bansan inda ƴan uwana suke ba,yakare maganan yana hucin bacin rai. "Kwantar da hankalin ka Bad tunda kaganta ai komai ma yazo da sauki kaga gobene ƴan matan zasu gudanar da bikin kamu tom inason ka kasance a wajen ko Allah zesa taje"Alhaji inaga fa duk yanda akai da ita wannan yarinyar ake ɗana tarko wajen kame mana yara duba fa kagani ko su lion wayanda suke wajen sunce yarinyarce taje wajensa tasayi kaya daga zuwa pos shikenan labarin yasha bambam yanzu kuma su maƙwa abun nan fa yana bani tsoro Alhaji,Alhaji bala ne yakema Alhaji sunusi maganan shiko Alhaji sunusi bazaka gane yayinda yake ciki ba saboda bushewar zuciya. Basma afujajan ta faɗo falon mummynta fa zuwansu kenan daga gidan malamin nasu ita da ƙawarta hajia bilki tana shiga falon tayi cilli da takalminta kallon ta sukai a tare cikin karfin hali hajja mariya da jikin ta ke rawa tabude baki dakyar tace"ke lafiya kika fadowa mutane a bakatatan? Rushimata tayi da kuka tana cewa"mummy kiyi wani idan nasara shi mutuwa zanyi"ke nutsu kimun dalla dalla yanda zan fahinta,nan ta kwashe komai tafaɗa mata tana karewa tasake fashewa da sabon kuka. "Kwantar da hankalin ki inda wannane matsalarki to daga yau anwuce wajen dan yanzun nan zuwanmu daga gidan wani malami muke neman taimako ki kaddara cewa kawai matsalanki daga yau yazo karshe kokuma kice yaƙare gaba dayama hajia balki takare magana tana sakin murmushi,cike da farin ciki basma tashga share hawayenta tana dariya miƙewa tayi tsaf daga inda take zaune taje ta rungumi hajia balki tana cewa"nagode mummy maganin kukan mu ni da mummyna dariya ita ma hajia mariya tayi dan ba abunda takeson gani aduniya sama da farin cikin ɗiyar nan tata. nan sukaci gaba da tattauna yanda zasu gudanar da aikin su,waya hajia bilki ta dauka takira wata lamba ring ɗaya biyu aka ɗauka daga daya bangaren aka shiga cewa"da girman kujeranki hajjia saida sukayi yar wasa da dariya sannan hajja balki tashiga rattabo masa da ƙudurinta shiru tayi saikuma ta juya tana kallon mariya datayi luƙus tana kallon ta dan sonjin abunda suke tattaunawa shike nan zamu baka dubu ashirin ok shikena saida suka gama tattaunawa sannan ta kalli hajia mariya da tayi sakoto tana jiran jin yasukayi da wanda taƙiran taƙagu sugama maganan tamata bayani ganin yanda ta zaƙo hajia balki ta kashe wayan tana kallon ta tace ya yarda anjima zakuje tare ke kitsaya daga bakin ƙofa shikuma ze shiga ciki. Zaro ido tayi waje kaman ze faɗo tashiga faɗin"amma hajia ke meyasa kika aminci masa kan zamu tare bayan kisani kuma ai ko malam cewa yayi ya amince amun kawai. Hmmmm mariya kenan inaga baki shirya ƙwatowa ɗiyarki ƴanci ba,ca nake a gabanki malam yace wani ze iya aiwatar miki amma kina tsaya agun idan ko baki shirya ba shikenan idan nice ke wallahi ba abunda ze hanani zuwa hakade tayi ta zugata harta yarda ta bata lambar mutumin sai sannan sukai sallama ta tafi gida. Itako hajia mariya tun tafiyan hajia balki takasa samun nutsuwar xuciya data ruhi sai safa da marwa take a haka har Alh sunusi yazo gida ta taddata haka shima dayake da tasa damuwar yazo be kula ba balle yagane sauyin dake tattare da ita yana zuwa ɗaki yashiga yace kuma kar wanda yatashesa yana bukatar hutuwane dan haka itama tata ɗakin tashiga kowace daƙiƙan daidai yake da bugun zuciyarta sha ɗaya da rabi daidai ta shirya ta fito samun sa tayi yazo yana jiranta bakin get shi yaja motan suka tafi parka motan yayi dan nesa da makabartan suka fito baysn sun kulle motar suka shiga takawa da ƙafa zuciyar hajia mariya ba abunda yake banda tsalle har suka iso bakin ƙofar maƙabartan ja tayi ta tsaya daga waje tana miƙo masa da layar saida ya karbi layan sannan ya kalle ta yace"gaskiya hajia saide fa mushiga tare idan yaso kitsaya daga ciki gardama ya balle tsakanin su dakyar de ta yarda suka shiga dan ce mata yayi wallahi muddin bazata shiga ba shima baze shigan ba saide sukoma,dole tabiyoshi suka shiga ciki tare tsorace take ciko tafiyan sa yake ba alaman tsoro ko dar saide ko tashiga ciki basuyi sosai ba hajia mariya ta taka wanj rami kasancewa damunane kuma anyi ruwan sama da rana kafarta ɗaya ya rufta ciki,take tasaki wani ƙururuwan ihu harda fitsari saida yakufce mata tana kiran"ma tattu natuba dan Allah karku riƙeni wallahi idan kuka barni yanzun nan zankoma ban shirya zama cikin ku ba layarma na hakura......wayyoooooni daga nan ta sume. ALLAH YASA MUDACE ALLAH YASA MUDACE [9/6, 9:25 PM] Ummahani: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 72 Hajia mariya bata tashi farkawa ba saida sanyin asuba ya kaɗata a zabure tafara"kiran dan Allah matattu kuyi hakuri wallahi ban shirya zama dakuba idan kuka barni baxan sake xuwa inda kuke ba,baba inna kullu inna hajara baba babba ku kun daɗe cikin su kuce suyi hakuri duk wannan iface ifacen da take taƙima bude idon ta balle tasan a inda take ita a tunanin ta harsan nan a can ɗin take duk ta jiƙe da zagumi sharƙaf ta firgice ta ɗimauce"mariya mariya buɗe idonki ke idan anyi mafarki addu'a akeyi ba ihu ba,cewar yayarta hajjo da sukazo auren. Jin muryan yayarta hajjo hakan yasata ta buɗe idonta ɗaya tana kannewa tare da tsoron abunda zata ganin addu'a take ita anata sai karanta "baa sin mi aa ra take da iya karfinta itafa a dole addu'a take idan ka tambaya, sai maimaita take da karfi itade fatan ta karda ta ganta wajen jiyan"ke wai me haka kikene addu'a akace kiyi ba karatu ba,cewar yayah hajjo. Bude idon ta shigayi ga mamakin ta sai taganta a gida kwance saman gadon ta ganan yaya hajjo zaune gefen ta tana mata faɗan tayi addu'a sai gwaggo tani dake zaune itama a kasan saman carfet tana kurɓan shayinta hankali kwance tana ƙarawa da soyayyar ƙwai sai ta cika bakinta da kwai soyayye sannan take korawa da shayi tana cewa"yanzu hajjo irin daula da mariya ke ciki kenan amma kiduba shine mu tabarmu a kauye muna fama da rayuwa Allah yatsine arzikin da zakaci kai ɗaya batare da ƴan uwa ba. sai kuma ta fashe da matsanancin kuka ta cigaba da cewa hajjo duba kiga tunda mudawo yau kwana biyu kenan nama saide muci iya cinmu muture amma bawai dan yaƙare a gidan nan ba,haka kaza daya amsa sunan kaza shima saide muci muture mai ramo ko soyayya kai harma da gasasshe,duba kiga wannan kwaice guda goma nasa wancan mai aikin nasu ya soyamun kalli shayi mai kauri haɗin majinyaci amma Allah yasa tsakanin mu dake mariya kina irin wannan abun kin barmu da cin tuwun dawa arniya mai shockin(miyar kuka kenan) kullum mukenan cin abu ɗaya da dare kaci kayi ɗumamen sa da safe"dan Allah gwaggo tani kiyi hakuri kiyi shiru ke taci kike niko ta lafiyar ƴar uwata nake ki bari dan Allah idan ta dawo hayyacin ta kya faɗa mata koma menene dan Allah badan ni ko ita ba kiyi shiru kinjide abun da likitan yace ɗaxu dayazo duba ta ko"sai kawai ta gyada mata kanta tana cigaba da cin kwai da shayi. Jin wannan maganganun nasu yabata daman buɗe idon tar da kyau saide tayi mamakin ganin ta gida a ɗaki kuma saman gadonta kwace take a komai abunda yafaru da itane yazo mata kaman yanzu akayi,zumbur tamiƙe zaune tana. Tana faɗin nashiga uku waya kawoni sai kuma ta ɗaga kafarta ɗaya daya maƙale jiya a cikin rami tagade lafiyansa lau sai kuma tasake ɗaga ɗayan taga shima lafiya ganin tana lafiya lau tasauke ajiyar zuciya sai kuma ta kalli yayarta tace"yaya hajjo waya kawoni nan? Kallon juna gwoggo tani da yaya hajjo sukai sai kuma suka maida kallon su kanta yaya hajjo tace"amma kanki ɗaya mariya?mafarki kikai ko kuma wani abun kika aikata kike kiran matattu yardasu baba?Take zufa yakaryo mata da jin irin tambayar da yayar tata tamata cike da tuhuma. *********** Su Aisha suna nan a asibiti sai bayan magariba suka koma gida tare da anty hajia datace ita fa tawarke kawai a sallameta,dole likitan yayi sallama dan angwada BP yasauka,koda suka koma gida bedroom ɗin anty hajia suka shiga da Aisha tare da Ammi suka sakata tsakiya da tambaya ko anmata wani abu"bude bakin tayi cikin rawar murya hankali idon ta natara ruwan ƙwalla nan take suka tuna mata da Annanta ta sande duk duniya uwace kadai wacce zata shiga damuwa akan ƴarta dakuma tsoron kowani abu yasame ta,sai gashi Allah yabata ahali masu sonta da kaunarta masu damuwa da damuwarta. Faɗawa jikinsu tasaki kuka tanayi suma nayi su tsoron su kartace wani a taɓata itako kukan take na tuna mata mahaifiyarta dasukayi saida sukai mai isarsu sannan sukai shuru dan kansu bude bakinta tayi tace"wallahi anty hajia Ammi ba abunda akaimun ba wanda ya taɓani kawai ina kukane tunawa danayi da Annata banyi tsammanin zan samu waƴanda zasu mayemun gurbin ta ba. Wannan ne yasani kuka,share mata hawayenta Ammi tayi tace"Aisha bakomai ai ɗa nakowa ne tashi kije kiyi wanka sannan ki huta ƙannenki suna can gidan namu anji malik ze dawo dasu munyi waya,da tom ta amsa cikin sanyi jiki tafi ta koma ɗakin su koda ta koma wanka tayi tafito daure da towal da karami riƙe a hannun ta tana tsane ruwan jikinta zama tayi saman stool din gaban mirrow tana shafa jikinta da tsadaddun mayukan ta masu kyau da sanyin kamshi ta murza turare a jikinta saida tabi lungu da tsaƙo na jikinta tamulke da turaren sannan tamiƙe cikin takunta da nutsuwarta ta nufi canza kayanta data ajiye saman ƙofa taji an turo ƙofa,saurin ɗago da kanta tayi tana sake rigar da ta dauka ƙasa. Saboda tsaban rudewa da tayi batasan sanda ta duƙa kasa gaban mirrow ba tana ƙanƙame jikin ta gada kallon da yake binta dashi,tanajin idanuwan sa masu kaifi dake yawo akanta,takuwa yayi a hankali cikin takunsa mai nuni da shiɗin cikakken namijine isowa yayi inda take yakai hannun sa danufin ya ɗagota tayi saurin make masa hannu tana sake riƙe towel dinda take daure dashi. Sake kai hannunsa yayi a karo nabiyu cikin rawar murya dake nuni da tsoro tace"dan Allah kafita idan wani yashigo ya ganmu a haka fa? Taɓe bakin sa yayi yace"to mai aciki mutum da matars...kafin yaƙara sa yaja masa wani dogon tsaki....ai kafin tadire ya fuzgota cikin fushi yace"ni kike jawa tsaki ko?yau zanyi maganin wannan bakin na tsiwa ta yanda gobe idan ance kima wani ba zakiyi ba. Tun kafin yakare maganan nasa ta fizge daga rikon da yayi mata zata gudu ko toilet ne ta ɓoye kanta,taku ɗaya biyu yayi karaf ya caf kota ya matseta da jikin bango ɗakin yamata rumfa da faffadan kirjinsa hannun sa yakai cikin zafin nama ya fizge towel din da take ta rirriƙewa ai batasan sanda ta kwalla ihu ba. Sa'ansa ɗaya ƙofar ɗakin a rufe take da abude yabarta ba abunda ze hana su anty hajia dake zaune a falo jin ihun nata. Faɗawa jikinsa tayi ta rungumesa da karfi so tight dan gudun karya kallar mata jiki wani irin shockin kaman na wuta lantarkine yajasu dukkansu su biyun take zuciyoyinsu yashiga sama da ƙasa kusan a tare dana juna zuciyar tasu ke bugawa,ɓagaren Ahmad wutane ya dauke masa itako Aisha a ruɗe take saboda yanda ta ruɗen jikinta harkaɗawa take kaman mazari. Sun dauki a kallah minti uku zuwa hudu a hakan tuni hawaye masu ɗumi sun wankema Aisha fuskarta na tsaban takaicin abunda yamata,gashiya gama kallen mata jiki badaman tace zata bar jikinsa a yanda take tsirara ganin baze gane ya barta ba kawai sai tadaga murya tashiga raira masa kuka,kukan tane yadawo dashi daga shockin ɗin da yake ciki. Saurin tureta baya yayi tasake fadawa jikin sa tana kuka tana cewa"wallahi nide banyafe maka kallan mu jiki da kai ba kuma kabani towel dina kuma saina haɗaka da Anty hajia ai ni ba ƴar iska bace da zaka shigo mun ɗaki kana neman.....saikuma tayi shiru bata ƙasara ba tana sake ƙanƙame shi. Tureta baya yasoyi amma taƙi barin sa cike da jin haushin kansa da kansa waime yagani gawan nan ƴa yarinya dabaya iya rike kansa harsaya dangana gareta(niko nace so da kauna) Ganin taƙi sakin sa kawai a zuciye saiji tayi anyi sama da ita be direta ko ina ba sai saman gadon dake ɗakin yana jefata yabi ya danneta rintse idonta tayi da karfi gashi yasake mata duka karfin sa badaman tayi koda motsin kirkine ba bakin tsiwa sai hawaye batayi aune ba taji saukan tattausa lips dinsa masu danshi da dumi saman nata yashiga tsotsan bakin ta kaman wanda yasami lollipop da zafi zafi yake tsotsan ganin yana neman rasa nutsuwar sa yayi saurin sakinta yana mirginawa gefe tare da sauke tagwayen ajiyar zuci, tayi saurin jan zanin gadon tayi tarufa har saman kanta tana kuka dajin haushin abunda yamata. Saida ya daidaita nutsuwar sa sannan ya sauka daga saman gado saida yayi taku ɗaya biyu yafara mata magana yana cewa"gobema kika sake mun tsiwa haka zan miki wannan shine hukuncina ko kuma yacinye bakin tsiwar nan naki yana gama fadin haka yasa kai yafita daga dakin yayi sa'a be samu kowa a falon ba dan haka yafita waje.   Wayane kare akunne yayinda sauran abokan nasa ke zazzaune mikewa yayi a zabure yana nace"what abunda yayinne ya jawo hankalin sauran kansa duka miƙewa suke suna tambayan sa ko lafiya. Ai besan sanda wayan ta suɓuce ta faɗi ƙasa ba take zufa ya yanko masa dukda uban ac dake kunne a falon sannan ga fanka"bala bashir karshen yazo watan talaucewar mune yakama an kame mana. Yana faɗa musu haka suka shiga zagaye falon sai jikike ƙwarr sun gora kansu dana junan su,dama gashi Alh bala shi be iya shiga tashin hankali ba yanason cewa Alhamdulillahi sai kawai yaɓige da faɗin ALI YAMUTU LILLAHI....   ALLAH YASA MUDACE [9/9, 11:16 PM] Ummahani: *AUREN WUCIN GADI* CHSPTER 73 "Wa'in wa'in wa'in shikuma Alh bashir haka yaketa fadi shikuma Alh sunusi sai kiran labbaika labbaika yake saboda tsaban ruɗewa cikin su ba wanda ya iya ambatan Allah dukkan su sunbi ruɗin duniya,sun mance da Allah belle sukira sunan sa. Sunɗauki lokaci mai tsawo cikin wannan yanayin kafin daga bisani Alh sunusi ne yayi karfin halin fadin"dole mu haɗau da boka najadu a yau ɗinnan dan ya kawo mana dauki cikin lamuranmu(wa'iyazu billa mutane suna mancewa da Allah suriƙe wanin sa dan neman taimako ko biyan buƙatarsu,duk wanda yabar Allah yakama wanin sa haƙiƙanin gaskiya yataɓe Allah yasa mudace yakare mu da imanin mu amin) "Mummy mummy mummy turus tayi tsaye tana kallon su ganin mummynta kwance saman gado tayi zuru zuru duk tafaɗa kaman wacce ta shekara kwance lafiya naganki kwance shame shame kaman me shirin haihuwa? Tayi tambayar ta cikin ko in kula da halin da taga uwar tata,duka kallon ta sukai cike da taƙaici gwaggo tani tamata daƙuwa tana cewa''ungo wannan ja'irar yariyar irin wannan tarbiyar da iyayen naki suka baki kenan ko? Yo in banda shashanci wani ɗan albarkane zega uwarsa kwance haka hankalin sa be tashi ba,ban dake shashashace angaya miki uwa abun wasace ai duk wanda yarasa uwarsa haƙiƙa yayi babban rashi arayuwa. "Kinga tsohuwa badake nake ba dan haka kishafa mun lafiya ko yanzun nan kijiki a waje road kizo kina...."ke basma ki iya bakin ki baki taɓa ganin wanin mu yazo gidan ku da nufin cin arziki ba yanzun ma dalili yakawo mu ki bari idan kingan mu jibi bayan auren ki sai kimana rasharin kunyar taki yayah hajjo ce ta katseta da fadin haka ranta a mungun ɓace take maganan sai kuma ta juya tana kallon ƴar uwartata tace kinga irinta ko,saboda baki ɗauke mu bakin komai ba yasa ƴarki....katse ta hajia mariya tayi bata bari taƙare abunda takeson cewa ba tace"haba dan Allah yaya hajjo barcewa haka basma ai yarinyace yarinta ke damunta wataran idan kince tayima ai bazata yi ba. mugun haushin hajia mariyan tabata dan haka miƙewa kawai tayi tafita daga ɗakin tana cewa"kinga gwaggo taso kibarmusu ɗakin da alama tattaunawa zasuyi da ƴarta,kafin gwaggon ko hajia marian ɗayan su yayi yunƙurin yin magana tuni tabar dakin,kallon ta gwoggo tayi ita miƙewa tayi tafita tabar musu ɗaki da harara basma dake tsaye ta raka gwaggo dan mugun haushin tsohuwar takeji dama. Ahmad yana fitowa motarsa yafaɗa ko sallama betsaya sunyi da mutanen gidan ba gida yawuce kai tsaye,koda ya isa parka motarsa yayi yafito a nitsu yanufi ɓangaren sa dake cikin gidan,wanka yayi tare da ɗaura alwala yafito ɗaure da towel a ƙugunsa saide betsaya wani ɓata lokaci ba kaya yasaka marasa nauyi na zaman gida ya feshe jikin sa da turare sai baza kamshi yake yanufi ɓagaren iyayen nasa tunda bakin ƙofa shigowa falon yakejin kaman ƴar hayaniya dan haka cikin sauri yakarasa shiga Ammi ya hango da farar takarda a hannun ta tsaye shiko Alh badamasi sai kumfar baki yake,take kirjinsa yabuga dan shi zaton sa takardar saki Abbansa yaba Ammin sa. Da sallama abakin sa yakarasa shiga falon amsawa Ammin tayi tana cewa"yauwa gashi nan ma yaxo take zuciyarsa tabada sautin rasss cikin rarrabuwan harshe yace''la...la....fiya Ammi? Takardan hannun nata tamiƙa masa hannunsa na rawa yamika hannun yakarɓa yana karantawa saida yagama karantawa yaɗago da kai yana kallon mahaifin nasa yace"Alhaji wai meke faruwane haka?ni nakasa fahintar komai kaman akwai abunda yake faruwa da bakason musani ninayi wannan tunanin tun randa akazo aka tafi da kai cid office da zuwan abokanka belin ɗinka nasan dawata a ƙasa bayan kafin zuwansu bayan da banyi ko da dpo ne nagani sunƙi yarda ba amna da zuwansu sai gashi kira ɗaya tak yayi akace wai an barka batare da wani tambaya ba case close kaima kasan wannan ba abunda hankali ze dauka bane amma kake ɓoyuwa Alhaji shin idan mu baka faɗamana ba wakake da waƴanda suka fimu?yakare maganan yana tsare mahaifin nasa da ido. "Ai cewa mayayi kar'a faɗamaka sai gaka kaima kazo,cewar Ammi. "Kar'afadamun kuma?yasake tambaya da mamaki"eh ninace karta fada maka saboda banason katada hankalin ka,kumama menene dan an fadama din amfanin me jinnaka zeyi?eh sosai sukai mamaki da yanda yake magana duk ya birkice sai yanzu ma Ahmad ta lura da yanda falon yake a hargetsa. Ɗagowa yayi ya zubawa Ammin sa ido itama shiɗin take kallo idonta na cikowa da ƙwallah"dawowata kenan daga gidan ikilima na tadda duk ya birkita komai bama falon kadai ba hatta da ɗakin kwanan sa sai kaga yanda yayi filla filla da komai duk ya birkita komai kaman mai neman wani abun, waya Ahmad yaciro bayan yagama sauraron Ammin nasa yakira family dr dinsu da yazo yaduba Alhajin ko alluran baccine amasa. Ba ɗauki lokaci mai tsawo ba kuwa saiga dr balami yazo wayan Ahmad din yakira yace gashi a ƙofan shigowa falo fitowa Ahmad yayi yashigo dashi saida ya gwada masa bp ɗinsa sannan yamasa alluran bacci,yace bara zeje ya haɗo masa magani yatafi kawowa shikuma Alh badanasi be jima ba bacci yayi awon gaba dashi nan suka sauke ajiyar zuciya Ammi ta sauke. ****Aisha kallo nan juyawa tayi tana kallon abunda ake nuna matan" jarida kuma?tafaɗa tana karɓa a hannun anty malikan head line ɗin kawai ta kalla. Cikin zaro ido tana dan rufe bakinta da hannu tace"Anty malika dama haryanzu ana safaran mutane kaman wasu kaya bayan ta miyagun ƙwayoyi da akeyi? "Nimade abunda nagani kenan abunne da daure kai wallahi Aisha yanzu a yanda ƙasarmu take muna da ƴan sanda soji mobil ace ana irin wannan abun kuma wai ace basu da masaniya ai akwai ayan tambaya suma akansu. "Yanzu anty malika idan na fahinceki daidai kinason cewa jami'an tsaron mu na ƙasa basa aiki yadda ya kamata kenan? "Kusan hakane Aisha?"to yanzu idan basu din bane suwaye suka kame waƴan nan din?tayi tambayan dan son kore zargin ta"wasune da ba'asan ko suwaye ba Aisha ai wannan ma abun taƙaicine kiduba irin yanda yah faisal yake aiki tuƙuru ba dare ba rana amma ace wai wasu daba jami'ai bane zasuyi wannan aiki daya dace ace sune sukai. "Kinga Antya malika shirya dawuri muwuce kar ayi bamu wajen kuma magana dakike ai ko ke zaki iya saukakawa jami'an tsaro nauyi idan kinga wanda baki yarda dashi ba ko kinga ana wani abun da baki yarda ba sai kiyi shiuttt dan a kamesu"hmmm Aisha kenan wai yanaga kaman yau kinma fini zumuɗi da zuwa gidan su antyn takine wai me sirri?takare tana ɗaga mata giranta ɗaya'kawai de inason zuwanne saboda inga yau kuma wacce ƙaryar za'ayi"kede faɗi gaskiya hajia kode kode"a'a wallahi anty ko wancan na sameta nabata hakuri kuma ita ta buƙaci naje ɗin,shiru Anty malika tayi dan kanta ya kulle"kika bata hakuri kikace? "Eh anty "Kan wani dalili kika bata hakuri kuma yaushe kuka haɗu da ita kode ita tasa akayi kidnapin dinki?"anty duka wannan tambayan lokaci guda wanne kike son na amsa miki"duka tace tana tsareta da ido kafin Aisha tayi magana saiga khadija tashigo da gudu tana cewa"anty wai kuyi sauri inji yah malik. Da sauri Aisha ta miƙe tayi waje dan gujewa amsa tambayar anty malika tana cewa"kisamemu waje daga haka ta riko hannu khadija sukai waje saida suka biya ta ɗakin anty hajia sukai mata sallama tana sake jaddadawa Aisha takula da kanta banda keɓewa ke kaɗai ki zauna cikin mutane inma kinji bazaki iya zaman ba to yi zaman ki a gida. Aisha dake da target akan tafiyar tayi sauri tana cewa"karki damu anty hajia zan zauna bazan tashi ba,tafaɗa nan anty malika tasameta tare suka fita inda malik ƙe tsaye da mota yana jiran su. Tare suka shiga bayan mota da ummu salma autan anty hajja khadija ce tashiga gaban tafiyar minti ashirin ya kaisu gidan Alh sunusi inda anan zasuyi taron,kasancewar gidan babba gidane anƙawata inda za'ayi taron amarya da ƙawanta duka sun saka kaya iri ɗaya sai taka rawa suke mai kiɗan ƙwarya nayi amarya na zaune hakimce. Gurin amarya suka fara zuwa sukai ggaisa sannan suka koma gefe suka zauna suna tafi can Aisha ta duna agogo dake daure a tsintsiyar hannunta tayi tsuka tasake yin tsukan akaro na biyu kallon ta anty malika tayi tace"lafiya ke kaɗai kike ta tsuka?"fitsari nakeji kuma banson tafiya ni kaɗai. in banda abunki ai nan cikin gidane kinga jeki kiyi kidawo,mikewa Aisha tayi tanufi cikin gidan bayan tasaka face mark ɓaki tana shiga falon tafara ƴan dube dube Alh sunusi ne ya leƙo daga can saman beni yana tambaya"waye anan ɗin? cikin kamewarta tajuya tana kin kallon sa tace"nice fitsari zanyi bayi nake dubawa. Zonan ki biyoni yafada yanayin gaba bin sa abaya tayi tana hawa benin tanabin ko ina da ido bayan ta seta cameran dake jikin veil ɗinta wata kofa yanufa tana biye dashi a baya mutum ukune sune zaune a ɗakin tagane Alh shehu saurayi fadila kawarta daya kamo yace ita yakeso,sai Alh sunusin da kansa ɗayan ne bata sanshi ba. Shiga can ki haɗo mana coffee akwai komai gyaɗa masa kanta kawai tayi batare da tayi magana ba,tana shiga inda yanuna mata tafara jin kaman nishi tawani ƙofa dake kulle ta cikin kitchen din jikinta ne yaɗauki bari take wani irin zufa yashiga karyo mata ta ƙofofin gashi dake jikinta. A hankali take takawa harta isa bakin ƙofan dakin leƙawa tayi ta ɓulin makulle"kee yi sauri kikawo magana da tajine ya hanata lekawa taga komai aciki komawa tayi da sauri kunna gas tayi ta haɗa masu ta zuba cikin flaks tahaɗa da kofi ta dauka ta kai musu,tana ajiwa tamiƙe jiki na kyarma ta nufi fita daga ɗakin"ina zaki bayan kin gane mana sirri saura kaɗan Aisha ta saki zawo yanda cikin ta yamurɗa ganin yanda ta ruɗe yasa suka kwashe da dariya dukkan su Alh shehu yana nunata yace"kalli fuskarta jeki wasa muke miki ya sunan ki?saboda yanda ta ruɗe batasan sanda tace izawaka'a ba sabida tsaɓan ruɗewa tana fita a ɗakin da gudu,bayan fitan ta Alh sunusu ko me yatuna oho yamiƙe tsaye kaman wanda aka mitsina yace"kai ina da tantama akan wannan yarinyar izawaƙa'a take ko ya?gudu gudu sauri sauri yamiƙe yabiyo bayan ta amma bega kowa ba harde wajen taron yan matan yashiga yana kiran"izawaƙa'a da babban murya ita ko Aisha sai sake lafewa take bayan anty malika.   ALLAH YASA MUDACE [9/12, 8:11 PM] Ummahani: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 74 "Izawaka'a yasake kira cikin ɗaga murya kaman ze tsage bakin sa hakan sai ya jawo hankalin ƴan tsirarun da hankalin su baiyo kansa da farko kowa kallon sa yake da mamakin me kuma yakawo shi nan? Waƴan da basu san koshi waya ba kuma suka shiga tambayan junan su wannan ɗi waye?idan ance daddyn basma ne sai kaga sunyi shiru suna kallon sa yanda duk yake a firgice to idan wannan shine Alhaji sunusin da sukejin sunan sa da labarin sa to meya firgitashi haka tambaya dasuke ma junan su kenan. Yayarsa mai suna balara ce ta matso inda yake ta riƙo hannun sa tana masa alama da ido yanda duka mutanen wajen suka maida hankulan su kansa saurin barin wajen yayi duka a birkice yake,amarya basma kuwa ji take kaman ta daura hannu aka takurma ihu takeji ganin yanda daddyna ta yazo ya yarfata cikin jama'a sai kiran izawaƙa'a yake sai kace mai bitan karatu. Ammi ce takira kanwarta Anty hajia a waya take sanar mata da rashin lafiyan Alh badamasi nan anty hajia tamata Allah yakara masa lafiya takuma cewa"in sha Allah gobe zan shigo dubashi zamu kuma tsara yanda bikin zamu gudanar da komai cikin tsarin wayayyu tunda yace bayason ayi bidi'a a biki kingani ko ta ɓangaren mu kuma gashi saura kwana uku auren yaya kuma banji kince komai ba. "To ikilima mai kuwa zanyi bayan kinfi kowa sanin bafa son abun nan nake ba"yaya kenan ko baso kikeyi ba kinsande baza fasa auren nan ba,dan haka zefi kyautuwa kawai kisaki ranki ayi abun nan kede kawai kisawa abun albarka,cike da ƙosawa da maganan ƙanwartata tace"kede sai kinshigo goben,daga haka ta katse wayan tana sauke ajiyar zuciya Ahmad dake zaune a falon yana aiki a systerm ɗinsa maida kallon ta kansa Ammi tayi tana gyara zamanta tace"saura kwana uku a ɗaura auranka da basma ko?"ummm kawai yace yana maida hankalin sa kan aikin da yake ta systerm din sa. Washe gari kaman yanda suka saba bayan yin sallan asuba Aisha da anty malika tare suka shiga kitchen don hada abincin karin safe nan Anty malika ta kalle Aisha dake jujjuya miya tace"yau saura kwana uku auren mutuminki haka kawai taji baganta ya faɗi tayi saurin waskewa tana basarwa tace"eh nima haka nakeji . "Kikeji kuma?da mamakin anty malika tayi magana"eh to mai hadina da auren da zan dami kaina?"ke ko kike da haɗi da auren tunda kece matar sa ta farko kuma zaɓin Ammin sa mafisoyowa a ransa. "Hmmm lalle kan Anty malika karfa ki manta idan kin manta natunatar dake nan gaban Anty hajia da kowa yace auren wucin gadi yayi dani tunda baze iya cewa Amminsa a'a ba"amma Aisha kinsan...katseta tayi tana faɗin"ba abunda nasani Anty malika nide kawai abunda nasani oga Ahmad yayiwa Ammin sa biyayya ne tunda baxe iya ce mata a'a ba na wucin gadi yake zaune dani da zaran yasamu sarari sakina zeyi nama gode Allah da basa muntare dashi gida ɗaya ba balle ya maisheni karamar baxawara sanadin wannan banzan auren nasa na wucin gadi tana kare faɗin haka jitayi kuka nashirin ƙwace mata hakan yasa. Da gudu tafita a kitchen din tayi ɗakin zuciyarta na tafarfasa duk sanda da tuna wai da auren wani a kanta auren ma na wucin gadi jinta take kaman tayi hauka sabida baƙin ciki kuma ko shekara ɗari zatayi a hakan bazata iya nunawa cewa bata son auren ba kodan saboda yanda anty hajia tariƙe ta da ƴan ƙannenta zata iya yimata komai ciki kuwa harda hakura da wannan auren da mai shi ke kira da na wucin gadi. Ta jima a ɗakin tamarasa me yakamata tayi kan wannan kaddararren auren gashi ko sanda Allah yayi haɗuwarta da Abban ta taɓoye masa zancen auren dake kanta batasan me yasha mata kaita ba. Tana nan zaune tana karantar wasikar jaki khadija data fito daga wanka tayi shirinta na zuwa skul ta kalle ta tagade kaman hankalin ƴar uwatata baya tare da ita. Matsowa tayi ta dafata tace"anty komai fa yayi zafi maganin sa Allah, akan ki zauna kina wannan tunane tunanen zefi kyautuwa ki fauwala ma Allah lamuran ki idan kuma Annanmu kike tunani addu'a zamuci gaba dayi mata kaman yanda kika koyar damu Allah ya bayyanata aduk inda take yasa tana cikin ƙoshin lafiya,ajiyar zuciya ta sauke mai sanyi ta ƙaƙalo murmushi da iya karta fuska bekai ciki ba ta dafa kafaɗan ƙanwartata cikin so da kaunarta dan ita kaɗai take gani taji sanyi a ranta sai mubaraq tace"jeki karki ɓatawa yah malik lokaci kinsan shi bayason ashiga lokacin sa ko. "Aisha a kayi kiranta daga bakin ƙofa,ɗagiwa tayi tana amsawa da Na'am anty hajia "To yi maza kifito dan nasan halinki yanzu sai kice zaki zauna bakiyi breakfast ɗin ba harsai ya huce. Fitowa tayi hannun ta riƙe da jakar makarantar mubaraq tana biye dashi duka kallon ta suke ganin yanda jikinta yake a sanyaye"lafiya?meke damunki?ko wani yamiki abunda bakya sone Aisha? Duka wannan tambayan ajere tayi mata kuma a ruɗe take da ganin sauyawar nata dan tana matukar kaunar yarinya saboda kyawawan ɗabi'unta. Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙaƙalo murmushi tare da sakin fuska tana tattara nutsuwarta tace"la Anty hajia wallahi bakomai kawai de natsaya ina shirya mubaraq ne yau da kaina. Numfashi ta sauke tana cewa"to haɗa muku breakfast din"ke fa anty hajia bazaki ci komai bane?"ƴar dariya tayi tana jan hancin mubaraq dayayi maganan tace yau tare da ƴar uwata zamuyi kari a gidanta"Anty nima zan biki gidan Ammi yafaɗa cike da yaranta. Malik ne yaɗan kalle sa yace"sannu ayawo wayace maka ana zuwa yawo ranan skul"D nimafa inason zuwan dande kar na magana ne kace nafiye son yawo cewan khadija dake zaune ummu salma namata dariya tace"to ai yanxu gashi kiyi maganan hararan ta khadijan tayi tana cewa"to ke wayasa bakin ki ai badake nake ba "To ai....kallon da malik yayi matane ya hanata yin magana ta dauki shayinta tana kurɓa dariya Aisha da malika suka kwashe dashi ganin yanda tayi Aisha tace"kwantar da hankalin ki autar Anty tawaje na bagani ba,tafaɗa tana nuna kanta takare da cewa bama harka da masu muzurai ganin yanda Aisha tayi tana kwaikoyon yanda malik yayi yabata dariya sai gashi tana kyalkyalewa da dariya dayiwa khadija gwalo murmushi anty hajia tayi. Bayan duka sun fita Aisha ta gyara inda suka ɓata ta tattare komai takai kitchen ta wanke duka a jiye komai a ma'adarsu ta wanke hannun ta tana gogewa da towel anty malika tashigo kitchen din cikin shirinta nafita shigowa kitchen ɗin tayi tana kallon Aisha da murmushi a saman fuskanta ita kuma Aisha kame fuska tayi taƙi kulata dafa kafaɗan ta tayi tabude bakin ta a hankali tace"Aisha dan Allah kiyi hakuri naga kaman fushi kikeyi dani banyi haka da wata manufa ba. "Bakomai tace tana kauda kanta daga barin kallon ta"haba ƴa uwa dan Allah fa nace tafaɗa tana marairaice fuska tanayin kalan tausayi,vashiri tasakar mata murmushi mai sanyi tace karki damu ya wuce saide naji ba daɗine lokacin dakuma duk sanda na tuna da auren wani a kaina wanda besan darajata ba balle ya mutantani,balle ta auren da akayi mana hmmm koda yake na wucin gadine kaman yanda yace din yaɓata mun lokacina ya rabani da wanda yakemun soyayyar gaskiya kukane ya kubce mata dagudu tafice daga kitche din ta faɗa ɗaki tana kulle ƙofan tare da nufan toilet shima ta kulle ƙofan. Komawa ciki Alh sunusi yayi a mugun hargitse zuwa cikin falon nasa a inda yabar abokan nasa nan yazo yasame su duk miƙewa sukai Alh bala da Alh shehu cikin matsanancin tsoron mai kuma yafaru Alhajin duk yabi yabirkice daga fitan yarinyar can haka"lafiya? Zubewa yayi saman kujeran dake falon yace dafe da kansa kaman zeyi kuka yace"ku baku gane komai tattare da yarinyar da tafita yanzu bako? Harsuna haɗa baki wajen cewa "a'a ba mugane komai ba"ina kyau tata zaton wannan itace yarinya da take bibiyar mu,kuma ina tsammanin taji duka abunda muke tattauna wa akai"shisa ashe naganta duka a firgice inji Alhaji shehu yafaɗa yana sharce zufa yana kakkaɓe babban rigarsa miƙewa duka sukayi suka shiga zage falon ko wannan su yana cizon ɗan yatsa ganin abun harinsu wacce suke nema ido rufe amma basu ganeta ba harsai da tabar wajen"inde hakane akwai gagarumin matsala Alhaji. Allah de yasa bata leƙa cikin wancan ɗaki taga wani ba,cewar Alhaji bala aikuwa be gama rufe bakin sa ba suka miƙe suka nufi kitchen din a guje.   ALLAH YASA MUDACE [9/13, 8:10 PM] Ummahani: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 75 Harsuna ture ture wajen shiga kitchen ɗin ja sukai suka tsaya ganin ƙofan ɗakin abude,sauri shiga ɗakin sukai zuciyoyin su na bugawa a mugun tsorace baki na rawa Alhaji sunusi dayayi baya yana neman faɗiwa ya dafa bango kansa na mugun sarawa yace"wannan wani irin musiba ne daga wannan sai wannan wannan watan ba watan sa'ar mu bace ba,yana karasa fadin haka juyawa yayi da gudu zuwa waje yana ce kunsa fa idan muka bari wannan matar ta gudu a kwai matsala babba ma kuwa. Ammin na zaune falo bayan ta haɗawa alhajin ta abinci yaci ta bashi magani yasha yaɗan kishingiɗa kan kugera,Ahmad da shigowan sa kenan gaishe da Abban nasa yayi tare da yimasa yajiki"amsa masa yayi a daƙile kaman wanda a kamasa dole. Juyawa yayi ya gaida amminsa ita amsa masa tayi da sakin fuska da tambayan ya yakwana"lafiya lau Ammi ina fadwa da meena fadaɗa murmushi dake kwance saman fuskarta tayi tana cewa"kamanta yau akwai makaranta. Dafa kansa yayi yace"wallahi kinga namance shaff kuma yau inada haɗuwa da wasu baƙi karfe shaɗaya dan ma khalid yana nan ze kula komai kafin naje. Suna cikin magana sai ga sallamar Anty hajia da farin ciki Ammi ta tari ƙanwarta mafi soyuwa a ranta tace"irin wannan sammako haka ikilima? Ƴar dariya tayi tana cewa "ai yau cewa nayi ba zanci komai a gida ba dake zanyi kari muna hira kina samun abinci abikina ina ci ina baki labari dariya suka kwashe a tare dan tunawa dasukai da ƙuruciyar su. Zama tayi saman kugera tana gaida Alhaji badamasi dayayi idon fara tun shigowar anty hajia amsa mata yayi yana miƙewa zaune suna ɗan taɓa hira yace"lalle kunaji da juna keda ƴar uwarnan taki wato dan yau zakizo shine ko abincin ma ƙin tsayawa ci kikayi"wallahi kuwa ta amsa masa. Ahmad dake zaune saman dining ne ya shigo cikin falon yace"ina kwana Anty"lafiya Ahmad dama baka fita ba ta tambaye shi tana gyara zaman ta"eh wallahi anty yanxu ma fita zanyi ya amsa mata yana kokarin miƙewa. "Dan dakata koma ka zauna tace dashi komawa yayi yana zama,gyara zaman ta tayi ta fuskance sa sosai ta cigaba da cewa ai gwara da Allah yasa baka fita ba nazo nasame ka a gida gaka kuma ga Alhaji gwara aiyi komai a gaban sa yanzun ma karyace mu mukai. Shima Alhaji sunusi gyara zama yayi yana kallon su da sauraron kuma dame sukazo masa wannan karon"dama nace ya maganan tarewar ita ɗaya matar taka? Dif Ahmad yaɗauke wuta ma ɗan wani lokaci ƴawun bakin sa yakafe,ya shiga zazzara ido kaman wanda aka kama yana aikata abu mara kyau. "Kayi shiru Ahmad Ammi tasake tambaya sa tana son su haɗa ido dashi amma yaƙi ɗagowa ya kalle ta. "To me kukeson yace?ai bashi da abuncewa kunsako yaro a gaba kun masa auren dole badason ransa ba wannan ba ƙa'ida bace,sannan yanzu kunzo kunason yimasa dole wajen tarewa wai ku waya muku dole kan naku auren ne?eh da zama a gidagen ku....katse sa anty hajia tayi tana cewa "A'a Alhaji ai sai kace.....kinga ikilima kike ko wace wannan magana ta ahaline..itama katsashi tayi da cewa idan ma ta hanjine ba ahali ba,to dole Ahmad ya tarewa da matar sa tunda addini ya halasta masa igiya uku nasa ya hau kanta kuma dol....miƙewa Alhaji badamasi yayi a fusace yana cewa idan ni na haifi Ahmad dole yasaki wannan yarinyar idan ko besake ta ba wallahi wallahi kundeji na rantse muku ko?saide yanemi wani uban bani ba. Itama Ammi miƙewa tayi a mugun fusace tace"ni kuma idan nice na haifi Ahmad dole ya tare da matar sa ko kokuma ya fuskanci fushina tana kare fadin haka tayi ɗakin ta tana kulle ƙofan dakin. miƙewa yayi dafe da kansa dake sara masa yana barazanar rabewa gida biyu ga jijiyoyin kannasa duka sun miƙe ruɗu ruɗu har wani jiri yakeji zuciyarsa kaman zata faso ƙirjinsa ta fito miƙewa yayi yasoma takawa yana haɗa layi kaman ze fadi kasa sabida dishi dishi dayake gani da sauri ya dafa bango yana ambatan sunan Allah. Kalaman iyayen nasa biyu su suke masa amsakuwa a kunne kaman yanzu suke maganan"inde ni na haifi sa dole yasaki wannan yarinya,idan nice na haifi Ahmad dole yatare da matar sa ko kuma ya fuskanci fushina"innalillahi ya'ilahil alamina kakawo mun ɗauki cikin lamurana dakyar ya iya lallaɓawa yafita daga cikin falon yanufi ɗakin sa ya faɗa saman gado notinan kansa duka sun kunce yarasa wani irin tunani zeyi yama rasa a wani irin ma'auni ze ajiye maganan iyayen nasa biyu shin maganan Ammi ze dauka yabar na Abban sa ko nasa ze dauka yabar nata rintse idonsa yayi da karfi yana rasa abunyi jikin sa na daukan zafi kaman zazzaɓe ze kamasa yanda jikinsa ya dauki zafi hakama zuciyar sa ke daukan zafi. Alhaji sunusi duk ya rude ya ɗimauce yana neman zarewa gun maigadi yanufa buguzum buguzum dasauri kaman ze tashi sama mai gadin na hangosa yanufo sa da sauri yana zubewa ƙasa dan gaidash...katsesa yayi yana cewa"baka ga wata mata yanxu tafita waje ba?cikin inda inda mai gadin yasoma cewa"ranka yadade wato kasan yau ai ranar sune masu shige da ficen suna da yawa bazan gane ba,wani irin mahaukacin kallo Alhaji sunusi ya watsa masa ya juya yana cewa"bansan amfanin zamanka a nan ɗin ba,tunda baka gane masu shige da fice,daidai nan suka bangaji juna da wani matashin saurayi a fusace Alhaji sunusi ya ɗago da rinan nun idanun sa cikin faɗa yake cewa"baka ganine kai mahaukacin inane kawani zo kana bangaje mutane kaman wanda yasamu sa'an sa"yi hakuri Alhaji ba danufu nayi ba yana cewa haka yafice zuwa baki get da sauri,bayan ya fitane Alhaji sunusi yaji kaman abu a hannun sa yana dubawa kuwa sai yaga ashe takarda wannan matashin yasaka masa hannu yana dubawa yaga anyi rubutu kaman haka.   Kada kabawa kanka wahala wajen neman ta ni kaman guguwa nake matukar nayi niyar bayyana a waje zan bayyana kainane ta yanda mutum baiyi zato ko tsammani ba kaduba wayan ka zakaga sako Alhaji sunusi ruwa yakusa karewa ɗan kada boom. Ai Alhaji sunusi besan sanda yasaki wayan hannun sa ƙasa ba tsaban rikicewa. Da yamma Ahmad ya lallaɓa yafito daga ɗakin sa dan sallan azaha data la'asar duka a ɗakin sa yayi yana fita wajen motan sa yanufa kai tsaye yashiga motan yamata key horn yake ba kakkautawa da gudu gudu mai gadi yabude kofan yasan yau ba lafiya ba irin wannan horn din da Ahmad ke masa dan ze iya cewa tun zaman sa a gidan be taɓa yimasa irin haka ba,yana budewa ya ɗaga masa hannun dayimasa fatan Allah yatsare kaman yanda yasa ba amma ko kallon inda yake Ahmad din beyi ba. Saida ya hau kan titi sosai yakira wayan faisal yana dagawa be bari ko sallama sunyi ba yashiga cewa ina hanyata ta zuwa gidan ku yau ɗinnan zankawo karshen matsalan nan,kafin faisal yasamu zarafin cewa wani abu tuni ya katse wayan yana tafiya gidan ba kowa sai Aisha kaɗai dake kwance saman kugera a falo yana shiga falon ko sallama babu kansa tsaye yanufi dakin ta saide ganin ta falo ya nufota ita ma sauri miƙewa tayi sanda ta shaƙo kamshin turaren sa tamiƙe zumbur daidai yana juyowa basuyi aune ba ƙirjinsu ya haɗu dana junan su sauri yin baya tayi amma kafin tayi baya tuni taji anyi sama da ita.   Wani iri shock suka shiga dukkan su su biyun ta dalilin haɗuwar gangan jikinsu dakyar ta samu daidaita nutsuwar ta tace"me haka malam saukeni wani hancky yaciro daga aljuhunsa ya daura mata a fuska daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba. Bayan barin Ammi falon kallan sa a wulakance Anty hajia tayi tana taɓe bakin ta tace"idan wani abu yasami yaran nan tasanadin ka bakar zuciyar ka zanyi shara'a dakai daganan har sai inda karfina yakare hakama ƴar uwata kafin yayi yunkurin yin magana tuni tabar masa falon tanufi kofan ɗankin ammi dayake a garƙame tana buga ƙofar tabude amma taƙi saurarota. Wayanta ne yayi ringin tana ddubawa gani mai kiran yasata dauka tana karawa a kunnenta ta kk sallama beyi mata ba yashiga cewa"anty hajia fatan kina gida?"a rude ta amsa masa da bana gida amma lafiya?jin muryansa kaɗai yanuna ba lafiya ba. "Ahmad yamun waya ina tsoron karyama yar mutane wani abun dan najisa kaman yana cikin fushi kuma kinsa idan yana fushin nan ze iya yin koma ai bata bari yakare maganan nasa ba tace"innalillahi nashiga uku ni ikilima wannan wani irin .........sai [9/16, 7:47 PM] Ummahani: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 76 Gudu yake shararawa shide fatan sa ya'isa dawuri kafin wannan hoda data shaƙa yasake ta,sai daf da sallan isha'i suka isa suna shiga garin ya sauke ajiyar zuciya direct wani katafaren gida yanufa yanayin horn mai gadi leƙo yana ganin sa yabude masa yashiga da motan sa yayi parkin kai tsaye bakin tap din dake tsakiyan wasu furanni yanufa alwala yayi yafita zuwa masallaci sai da yayi sallah sannan yazo. Har sannan bata farka ba,saida ya geshi ya bude ƙofan wani falo sannan yazo bakin motan yabuɗe bayan mota ya dauko ta kaman wanda yadauki ƴar tsana ya shiga da ita hadaɗedden falon da bakajin komai sai sai sanyi ac da wani dadɗan kamshi daya cika falon kwantar ta saman kugera 3sitter harya miƙe tsaye ze tafi yaji ta riƙe masa hannun komawa yayi yazuba idanun saman kyakkyawan fuskarta kallon ta yake ko kiftawa babu beta sanin yarinyar haka take da sassanyar kyau ba sai yau ya shagala da kallon ta jin zuciyan sa na motsawa yasashi saurin kai ɗaya hannun sa ya zare daya hannun sa cikin nata ya mike yashiga toilet dan watsa ruwa. Alhaji sunusi yashiga mummunan tashin hankali ko yanzun duka sun halarta a guest house dinda suka saba haɗuwa duka sun halarta idan kacire Alh badamasi . Alhaji surajo ne yamiƙe rai a ɓace yake magana inda yake cewa"sunusi nasan kafi kowa sannin manene ƙa'idan ƙungiyar mu kasan wace irin tafiya muke amma koda yaushe anfi samun matsala ta ɓangaren ka"amma ranka yadaɗe oga kasan ba lefina bane ko?nima badason raina hakan ke faruwa ba. "Dallah rufa mana baki Alh bashir yace rai a ɓace ya daura da cewan kuma kasan ɓatan Ishaq yana daga cikin mummunan kaddara mu barin sa wajen mu kasan barin sa yana rayuwar ƴanci babban barazana ce garemu dama dukiyar mu baki ɗaya"kuma saida akace dakai mukaishi matsafa ko dawanau mubarshj can arinka masa alluran mahaukata amma kaƙi tunda kace bakason yanzu a kashe shi,alh shehu ne yake wannan maganan. Miƙewa Alh sunusi yayi tsaye yana cewa"ina ganin dr da muka bawa contrack ɗin alluran nan yaci amanar mu,ni sai yanzu ma nake tunawa da sharadin shugaba yazama mun dole in nemo Ishaq ko wani dake da alaƙa dashi. "Ya batun saka hannun da alh badamasi ze wa wannan takardun kasan fa idan basaka hannunsa muka samu da farko ba komai namu baze tafi daidai ba"kaman de yanda ishaq yayi maka tsawon lokaci da muka dauka muna ƙillace dashi sai daga baya muka gane takardun duka kaddarorin sa dukka sunan matar sa dakuma babbar ƴarsace har yanzu munkasa sani ina suke aina suke rayuwa kai ko kamanin ita yarinya ba wanda yasani cikin mu balle musaka anemo mana ita. "Sannan ita ma matar damuke ta murnan munsameta sakacin ka da rashin kulawanka yasa munrasata rana tsaka,kuma duk da hakan baka tunanin komai kai auren ƴarka kasa gaba,tom bari kaji yanzu haka alh badamasi an aiko masa da sammaci daga babban kotu"kotu ya ambata a kiɗime"eh kotu yasake amsa masa kuma baka da labarin wannan ɗin ko? Saida ya sharce gumi daya tsastsafo masa a goshi ya haɗiye wani ƴawu mai kauri tukun ya gyaɗa ma ogan nasu kai. Wata uwar harara Alh surajo yamasa yace"dama tun farko saida mukace baza muyi wannan tafiya da kai ba kanace kace zaka iya gashi baje ko ina ba asirin mu naneman tonuwa. Yakare maganan yana huci cike da bacin rai idan yatuna cikin ƴan watanni sunyi asaran million of naira sai yaji mugu mugun haushin sa gashi duk abunda ƙungiya ta ginɗiya masa ba wanda yacika cikin sharuɗan ta. "wai kai surajo me matsalan ka danin ne alh sunusi yace yana miƙewa rai a ɓace dama tun shigowata ƙungiyar nan nasan basona kake ba,take faɗa ya kaure tsakanin su kaman zasu bawa hammata iska saida shugaban su ya tsawatar sannan suka nutsu suka zazzauna bayan ya umurcesu da haka. Kallon su yayi ɗaya bayan ɗaya sannan yace" hukumar NAPTIP tasakomu gaba kan wannan harƙalla tamu duk da ba wanda yasan mune muke aikata abubuwa da suke zargi amma ina jiye mana tsoron faɗi wannan karon dukda tunda muke bamu taɓa faɗiwar ba,kuma bazamu yarda mufaɗin ba gaban maƙiya suma dariya. amma ɗazu nakejin labari da ɗuminsa kan cewa akwai jimi'insu mai ƙwazo da hazaƙa idan yakama aiki bayaji baya gani harsai yaga karshen abun harin sa. Sannan baya karɓan cin hanci matukar akan aikin sane gobe zeyi resume a office dinsu dake abuja dan haka inason kai Alh sunusi katura idon mujiya ya gane mana shin waye shi?ya sunan sa yake dakuma hoton sa adireshin inda yake da zama duka harma da sunan da yakekan card dinsa ya amsa da"an gama oga sannan suka miƙe baki dayansu banda ogan nasu dakuma alh surajo. Ahmad bayi yanufa yana sakarwa kansa shower saida yagama cuɗa jikin sa da sabulun sa mai daɗin ƙamshi da tsada sannan ya dauraye jikin sa da ruwa yafito jikin sa daure da towel yana goge kansa da ƙarami gaban dressin mirrow yanufa ya dauki oil dinsa mai tsada dakuma ƙamshi yasoma shafawa sama sama saida yagama ya dauko jallabiyan sa milk colour ya feshe jikin sa da turare yafito zuwa falon har zuwa sannan Aisha bacci take bata farka ba. Kaman de ze zauna sai kuma ya fita daga falon zuwa compound ɗin gida yanufi wani part dayafi girma cikin gida dan gidan part uku ne dashi amma dayan nan shine babba dan nan part din mai gidan ne da iyalan su,ɗaya na kusa da wanda Ahmad yake ciki kuma na babban yaron gidan ne kuma abokin ahmad din sai bq da masu aikin gidan ke zama a ciki,matar gidan ƴar uwace gun alh badamasi ƴar gwaggon sace kuma ita ɗayace a gidan sai yaranta da mijinta wanda kusan yawanci baya garin yafiye tafiye tafiye yau yabaya garin nan gobe baya garincen hakade yake harkokin sa da yawan tafiya ƙasashen ƙetare. Ahmad yayi zama a wannan gidan sanda yazo wani aiki tsawon shekara biyar kafin ya dan tsagaita da aikin nasa sakamakon bayanan su da wasu daga cikin su ke fitarwa ga abokan adawan su ana dan basu ihsani sukuma suna bi suna kashe masu mutane wannan dalilin yasa hankalin Ammin sa tashi ganin yanda akewa ma'aikatan na NAPTIP kisan gillah tare da iyalansu,dan haka ta matsa dole yabar aiki ya koma gida da zama shine fa yabude A&B travels agent da A&B fashion dakuma boutique shekara uku kenan yanzun ma zeyi join aikin ne saboda kawo karshe masu aikata ta addancu da mumanan ɗabi'u safaran miyagun ƙwayoyi safaran yara mata kai harma da maza dakuma ta makamai masu linzami,ya dauki alwashin sai yakama koma wanene saiya shefe babinsu a doron duniya. Saikuma ya wanke mahaifin sa daga zargin da akemada mahaifin sa yanason ya wanke shi a idon duniya. Duk dashi mahaifin nasa yaɓoye masa bayason yasani amma faisal yatura masa da komai in details yakuma karanta komai daki daki koda ze rasa nashi rayuwan yayi alkawari sai yakawo karshen GAGARA BADAU da akace shine shugaban wannan tafiyar. Ya tsaida tunanin sane sanda ya ƙaraso ƙofan babban falo gidan hannu yakai a hankali yabude yashiga da sallama wata mata macece aƙalla zata kai shekara hamsin hakimce tana zaune saman ɗaya daga cikin kugerun da sukaiwa falon ƙawanya tana kallon wani movies da ake haskawa a mbc2 gefen wata yarinya buduwarce kwance ta daura kanta saman cinyar matar tana danne dannen da wayan ta. Amsa sallamar tasa sukai kusan a tare fuskokinsu yana nuni da zallan mamakin su"yaushe a gari amadi?inji matar itako yarinyar ƙwaɓe fuska tayi cike da shagwaɓa tace"shine baka ko gayamun a waya kana hanya na gyara ma ɗakin ka ba. Neman waje yayi ya zauna yace"ina yini hajiya mun sameku lafiya?"ƙalau ta amsa masa a taƙaice ta ɗaura da yasu Ammin naka da ɗan uwana"suna gaidaku ya amsa a gajarce yana ƙoƙarin miƙewa saiga baby safna ta rugo da gudu ta faɗa jikin sa tana dariya ɗagata sama yayi yana juyata sai dariya take ya sauke yana cewa"a'a bebin daddy angirma dariya tayi tana cewa"uncle A sai kawai katafi kayi aurenka kabar anty fauza kullum sai tayi kuka kuma tace ba zatayi aure ba ita kai zata jira....zaka jirata kaima? Takare faɗin haka cike da yarinta dif wuta ya daukewa mami da ita kanta fauzan shiku Ahmad yi yayi kaman beji abunda tace din ba. Shirin miƙewa yayi yana bawa fauza amsan tambayar da tamasa"ai zuwan bazata nayi wani aikine yataso mun,ɗaki kuma basai kin wahal da kanki ba nayi waya da sajid yasa saminu driver ya share,har yakai ƙofa hannun sa riƙe dana baby safna data maƙale masa mami ce tayi karfin halin yin magana ganin ze fita tace"bara yanzu nasa takawo maka abinci"ok yace yana fita sai kuma ta daura da cewa da kabarta kaga darene sannan kaida kayi dogon tafiya kana bukatar hutu ba surutu irin na safna ba kasanta da shegen surutu kaman aku. Murmushi yayi yana kai kallon sa kan safna data noke kafaɗa sai kuma ya ɗago yana cewa mami idan takai abincin sai tadawo da ita daga haka yafice zuwa nasa part din deep down na zuciyar sa kuma yana ta tunano maganan safna duk da tafaɗa masane cike da yarinta tabbas hakane dan yanda yaga sauyawar mami da ita kanta fauzan sanda safna ke faɗamasa kenan tun tuni fauza sonsa take shi bemasan tanayi ba idan ko hakane akwai aiki dan zaman Aisha gidan nan ba lalle taji daɗi zama da su ba. Yana shiga falon Aisha na farkawa tamiƙe zaune tafe da kanta tashiga dube duben dan ganin inda take take taware idonta dasukai mata nauyi ta zubesu a kansa tana dafe kanta dayayi mata naune"ina kakawoni?ina nane nan?tasake faɗa murya na rawa kafin yayi yunkurin cewa wani abu harta miƙe tsaye jiri taji na neman daukan ta tayi saurin komawa ta zauna sai kuma tarushe da kuka. Baby safna sai kallon ta take idan ta kalli ahmad dake tsaye ko motsawa beyi ba sai kuma ta kalli Aisha dake zaune ta haɗa kai da gwiwa tana kuka''uncle A ita ma wannan kukan take dan bakajira ta ba kayi aure? Tambayar tazo masa a bazata dan safna irin yaran nan ne masu shegen surutu. Sai kuma tashiga takowa a hankali inda Aisha ke zaune tana kuka tace"kiyi hakuri kinji anty haka uncle A yatafi yabar anty fauza itama kullum sai tayi kuka kuma tace ba zatayi aure ba zata jira sa kema jiran nasa zakiyi? Cak Aisha ta tsaya dayin kukan ta ɗago kanta tana kallon yarinyar waye kuma hakan?_wave kuma fauza?wa take jira duka wannan magan tana yinsane aranta ba kuma me bata amsa yanzu koda ta furta sannan kuma bata bukatan sanin. idanuntane yasauka kan wata kyakkyawar budurwa ajin farko ƴar gayu kana kallon ta taga ƴar hutu hannuta riƙe da wata basket da aka rufe da farin ƙwalle ta shigo falon idanun ta kan Aisha da fuska caɓa caɓa ta jiƙe da ruwan hawaye"who is she?ta tambayeshi cikin sanyin murya. shiru yayi mata kaman ma bashi take tambaya ba yanufi ɗaki yabarta tsaye baki bude ai fauza batasan sanda ta saki basket din hannunta ba tayi baya da gudu tana tushe bakin ta dan kar kukan datake riƙewa tun ganin sa datayi ya kwace mata a gaban wace batasan matsayinta agunsa ba ganin abunda fauza tayi hakan yabawa Aisha daman sake fashewa da sabon kuka tana cewa"tunda kasan auren wucin gadi mukai ba auren nunawa dangi ko wani abu bato to me naka nadauko ni kakawo wani gidan ka tashi ni kamaini inda kadauko wallahi ko yau na hana kowa bacci a gidan nan. Ya faɗa tana miƙewa tsaye daga zaunen da take tanufi wani flower vase ƙato dake jirke a gefe da kyar ta kinkima daidai Ahmaf na fitowa daga ɗakin dan sabida kukan da take"K ..K kafin yakaraso inda take tuni taratse ta da ƙasa ji kake tasssss.   ALLAH YASA MUDACE. [9/18, 9:29 AM] Ummahani: *AUREN WUCIN GADI* CHAPTER 77 Kafin ya karasa gareta tuni ta rotsa da ƙasa ya fashe sake raruman ɗaya dake can kusurwan falon tayi ta ɗauka tasake rosashi da ƙasa,ganin abun nata na neman wuci makaɗi da rawa yasa shi takowa a hankali inda take takai hannu zata dauki plasma tv yariƙe mata hannu sannan ya zuba mata idanun sa masu rikita ta yana kallon ta,ya kai babban yatsan hannun sa ya dauke hawayen ta data kasa tsaida su cikin lower voice yace"ki a danasu za suyi miki amfani nan gaba kaɗan an kaya dakika fasa kuma ki lissafa ki a jiye dan zaki biyani ne ƙwandala ta bazeyi ciwon kai ba...yana kaiwa nan yasaki hannun nata. Warin mugun takaici ne ya ƙumeta tama rasa me za tayi gashi kukan ma ta yi har taji ba daɗi hawayen ma yaƙi zuwa sai zafi da zuciyan ta ke mata zubewa tayi kasa jagwab a gun. Kukan ta keson yi amma takasa ta dauki a kalla minti uku a wajen zaune sannan ta miƙe ta nufi tsaƙiyan falon inda ta tadda shi zaune saman kujera ya daura kafa ɗaya kan ɗaya yana waya hankali kwance. Tana zuwa ta shiga cewa"ni kata shi kamai dani inda ka dauko ni"shiiiii yayi mata alama da tayi shiru yana daura ɗan yatsan sa saman bakin sa. Ai ba tasan sanda wani hawaye masu dumi ya shiga ziraro mata saman kyakkyawar fuskarta ba,bata damu data goge ba ta shiga babbuga ƙafa irin ta yara tana kukan. Koda ya gama wayan maida a bunsa yayi ya aje ya ƙima kallon inda take jawo basket din da fauza ta kawo yayi ya dauki a plate da cibi ya shiga zuba a bincin sa hankali kwance ganin da gaske bashi da niyar kulata ya sata wage ɗan karamin bakin ta tace"ni ka kulani,dariya ne yataso masa amma yayi kokarin danne wa dan bayason taga daman sa ta raina shi"ok yace yana maida hankalin sa kanta yaɗan waro idanun sa masu firgitata. Turo ɗan mitsitsin bakin ta tayi tace"ni ka dena kallo na ka zura mun ido har kasa na mance abunda nake son faɗama. Da hankali tayi maganan cike da tsiwa harga Allah ta dauka be jita bane shiko sarai ya jita yi yayi kaman beji me take cewa ba. Sake maida kansa yayi kan a bunda ya keyi,ta dan ɗaga murya tace"ba zaka kulani ba kuma? Ajiyar zuciya ya sauke ya maida plate din inda ya ɗauko ya maido da kallon sa ka cokan kanta yace"yarinyar nan kina bani ciwon kai ya faɗa yana kafeta da ido"ciwon zuciya ma zan baka ba nakai ba ta faɗa ƙasa ƙasa sai kuma taɗan ɗaga murya ta yanda ze jita da kyau tana cewa ni ka dena kallo na haka ɗaga giran sa ɗaya yayi alamar tambaya. Murguɗa masa bakin tayi sai kuma tace"to ai ni fitsari nake ji,beyi tsammanin haka zata ce ba,dan haka nuna mata ƙofan ɗakin yayi da yatsa sai kuma yace"idan kin gama sai kiyi alwala kirama salloli da ba kiyi ba. Zaro manyan dara daran idanun ta masu haske da kallon su ke haddasa masa kasala tayi tace"Allah na tuba ka yafe ni ganan wanda ya bugar dani har lokacin sallah ya wuce banyi ba,kuma wallahi sai Allah ya saka mun zalumta ta dakai kuma bazan kwana a nan ba saide kata shi kamai dani gida wallahi ko kuma in yi ta kururuwa in ce sato ni kayi,yanda take maganan kawai saiya tsurawa ɗan karamin bakin ta ido yana kallon yanda take motsasu. "Yi kururuwan inda wanda ze ji ya kawo miki a gaji sannan ki nutsu karna sake jin bakin ki a nan idan ko ba haka ba,kinga wallahi can waje ɗakin bingo zan maida ki ku kwana dan ba zaki zauna ki hanani bacci ba,a ranta tace bingo kare yake nufi kenan ita a rayuwar ta ba a bunda take tsoro kaman kare dan tsuƙe bakin tayi. Mukutt ta haɗiye ƴawo mai kauri a hankali cikin karyar da kai tayi kalan tausayi cikin sanyi murya tace"to i nane bayin sake nuna mata ƙofar dakin yayi da yatsan sa manuniya,har zata shiga ciki sai kuma ta ja ta tsaya tace"to da me zanyi sallan yanda tayin sai ta bashi tausayi amma ba yason nuna mata dan yanzu yana nuna tausayin sa kanta sake botsare masa za tayi kai tsaye yace ta shiga tayi alwala yanzu ze sa a kawo mata kaya. Harta kama handle din ƙofan zata bude sai kuma ta fasa ta juya tace"wallahi nide in a gun wacan zaka karɓo mun banaso nama fasa"ai baki isa ba yanzu nan kika gama haɗani da Allah sannan ki zo kice ba zakiyi sallan ba keee bude kunnen ki da kyau ki jini kafin mubar garin nan kika sake ta damun da hankali ko sai nayi(..)sai kuma yayi shiru. "Na shiga uku mutum yayi magana ace yayi yayi shiru a cuce shi ni wallahi bazan yarda ba ai koda can cewa anty hajia kai ni ba kalan matar da za ka aura bace ba,sannan ka zo kace auren wucin gadi ai ba'ayi dakai cewa duk inda zaka ka tafi dani ba. Yanzu ka ɗauko ni ka zo dani wata duniyar mai kake son a cemun bayan ni ma naci bakin ba sonka nake ba,kawai kasa mutane sumun kallon ƴar iska,shiko Ahmad mamakin ta yake yanda magana baya mata wuya idan ta soma babu aya balle waƙafi saide ka jita faaa harsai ta je inda taga yayi mata. "Mtsss ƙaramin tsaki yayi dan surutun nata ya fara gundurar sa yace to ni ɗan iska ne kinji ko?ya faɗa yana miƙewa tsaye zuwa kofan falon dan amsan sako daya bada ganin kiran da ya gani a wayan sa. Ranta da gudu tayi dan ita duk a zaton kamata ze yi ya daka saboda ta cika shi da surutun banza duk da hakan bakin nata be mutu ba saida tace. "Nide bance ba ta faɗa tana share kwalla daya zuba mata,ɗakin ta shiga bata tsaya kallon ya tsarin ɗakin ba da yake shine a gaban ta ba,ƙofa data gani a ciki ta buɗe ta shiga fitsari tayi tayi tsarki sannan tayi alwala tafito tana batun tada sallah ya shigo da wata leda ya aje mata ya fita yana cewa"idan kin gama ki fito ina jiran ki daga haka ya juya ya fita ita kuma jawo ledan tana duba wa hijabaine guda uku sai dogin riguna suma uku sai rigar bacci da mayukan shafawa da turare sai bra da pant,taɓe baki tayi tana ɗaukan daya daga cikin hijaban ta saka sannan ta tada sallah bayan ta shimfida sallaya. Alh badamasi wallahi banyi tsammanin haka daga gareka ba?"daa()? be karasa a bunda yayi niyar faɗa ba yayi shiru,hakan sai ya kara fusata shi ya cigaba da cewa ai dole kayi shiru dan baka daukeni a bakin komai ba. Shiru yayi masa kaman ba zeyi magana ba,sai kuma ya magantu da cewa"sunisu bansan a bunda kake magana a kai ba ni yanxu damuwa ta barin gida da ɗana yayi shine kaɗai damuwa ta...a furgice Alh sunusi ya ɗago yana kallon abokin nasa yace"ban gane ba,bade ahmad yabar gida ka keson cewa ba . To idan yabar gidan ina ya je?waye kuma waze auri basma daya gudu yabar gida a na aure saura kwana uku eh ? "Kai wannan ce damuwar ka wanda ze auri ƴarka to bara ka ji ahmad yabar gidan ne dan gujewa abun kunya..."wace irin kunya kuma kode wani abun kunya yayi ya gudu to Allah de yasa ba ciki yawa wata ba. "Kul kul kasake dangan tamun ɗa da mugun nufi,cike da ɓacin rai ya faɗi hakan yana huci kaman kububuwa zaune yake amma besan sanda ya miƙe ya tashi tsaye ba sanda ya ji kalma da alh sunusu yake ji fan ɗan nasa da shi. "Badamasi yau ni kake wa tsawa haka ya faɗa cike da mamakin abokin nasa yana nuna kansa dan yasan mugun ƙulli da sukai masa ko a gaba ba ze iya musasa ba balle ta kaisu ga ɗaga masa murya lalle a kwai aiki a gaban sa idan har haka ya cigaba da faruwa a tsakanin su. Yana cikin tunani yatsinkayi muryar alh badamasi inda yake cewa"ahmad be wa ƴar kowa ciki ba,kuma ba ze yi ba ko nan gaba idan kaga ya yiwa wata ciki to ka kaddara halal din sace,ya cigaba da cewa wato sunusi sai yanzu nake da nasanin jan ka jikina da nayi. Yau a sanidin ka na zama tamkar mujiya cikin tsuntsaye kowa guduna yake duniya tana neman juya mun hatta da yarana basu isa suje makaranta suyi karatu su dawo gida hankali kwance,ba tare da an samu wani ya goranta musu ubansu maci amanan kasa ba da alummar sa ba. Yau ɗan da nahaifa ma gudun abun kunya da na aikata yake,ni nasan ahmad ya gujewa zaman kotu da za'ayi ne bayason ganin ba,abun kunya dana aikata ze riskane bayaso."dakata badamasi ai sai kace...shima katse shi yayi yana cewa kaga sunusi ka tafi kawai ka tafi banson ganin ka balle jin mai ze fito daga bakin ka,kuma ko a kotune ni na daukarwa kaina alkawari ba sunan wanda zan kira balle binceke yabi ta kansa zan sauƙaƙa wa kotu dama kaina baki ɗaya kar kaji komai nasan tsoron ka kar sunan ka ya fita ko?to sunan ka ba ze fita ba,ba ma naka ba,har dana sauran yana ƙare faɗan haka ya wuce sama benin inda ɗakunan baccin su yake. a falon ya barshi tsaye yana rasa abun yi.   Saide a bunda basu sani ba dukka su biyun wannan musayar ƴawu da sukai kan idon Ammi sukai,ɗagowar da ze yi sai cikin na ta idon data ke tsaye bakin kofan kitchen wani irin kwarjini ta masa fiye ma da yanda take masa a baya. ****** Bayan ta idar da salloyin ta anan saman abun sallan tayi zaune ga yunwa na nuƙurƙusar ta dan rabon ta da cin wani abu ko sha tun breakfast ɗinta na safe shima ɗin ba wani abun kirki taci ba. Tana nan zaune sai gashi ya shigo dauke da basket ɗin ɗa zun,a jiye mata yayi gaban ta,shi kuma ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito ɗaure da towel ta gaban ta yazo wuce wa ya ji tane magana ƙasa ƙasa be ji me tace ba,amma ƙaramin tsaki da tayi hakan ya ankarar dashi take ko dan ta gan shi ba kayane ko me? Har ya wuce sai kuma ya koma da baya daidai ta miƙe tana batun barin wajen sai kawai taji ta faɗa jikin mutum kyakkyawan riƙo ya mata tana kiciyar kwace wa daga rikon da ya mata ba zato ta ji saukan lips ɗinsa a nata wani irin tsotsa yake musu cike da mugun ta kaman ze cinye mata bakin. Dama hawayen ta a kur kusa yake sa kawai suka shiga fareti saman fuskarta suna gangarowa nasa,duk da yanda take kukan ga jikinta daya dauki zafi da kuma kyarma da yayi kaman zazzaɓi na neman kamata be saketa ba saida ya tsotse mata baki ya gaji dankan sa ya sake ta,ya koma gefe yana sauke ajiyar zuciya. sulalewa tayi a gun tasaki kuka mai cin rai tana taɓa bakin ta da yatsunta biyu jin yanda suka soma tasowa. "Idan kika sake mun tsaki ko tsiwa saina cinye bakin rashin kunyar nan yace yana barin ɗakin.   ALLAH YASA MUDACE [9/22, 1:16 PM] Ummahani: *AUREN WUCIN GADI* ✨ *GORGEOUS WRITERS FORUM*✨ ✨ G.W.F✨ *HOME OF GORGEOUS,INTERLLIGENT,AND EXPERT WRITERS, WE THE BEST AMONG THE REST* CHAPTER 78 Saida tayi kukan ta ta ƙoshi sannan taja jikin ta takoma inda tayi sallan ta kwanta,a ƙudundune tana rufe jikin ta da hijabin ta. Wai meke damuna ne?me saya bana iya riƙe kaina muddin ina tare da ita ne,anƴa zan iya cika alkawarin da na daukawar kaina kuwa? Cigaba da hakan bayana nufin sayawa kaina raini daga ƙaramar yarinya ne?haka yayi ta sakawa yana warware wa harde daga ƙarshe yasamu waje ya zauna. Knocking kofa da a kai yasa shi tara hankalin sa gu ɗaya yana bada izinin shigowa,a hankali ƙofar ta bude ya kafe ƙofar da ido dan son gani wa ze shigo sallama dauke a bakinsa ya sako kai falon fuskar sa ƙawace da murmushi,amsa sallaman yayi yana miƙewa tsaye ya nufe sa shi ɗin ma fuskar sa a sake ƙawace da murmushi kwance saman fuskokin su. Rungume juna sukai ko wannen su yana mai farin ciki haɗuwa da ɗan uwan sa,zama sukai a tare suna sake gaisawa da tambayan juna ya bayan rabuwa,nan fa hiran yaushe gamo ya ɓarle tsakanin su ko wannen na yana bawa ɗan uwan sa labarin bayan rabuwar su. Nan sajid ya dubi Ahmad yace"hala aikin ka kakoma? "Nap ban koma ba tukun na de gaskiya har yanzu ya faɗa yana ya mutse fuskan. "Oh ai naji labarin wai akwai wanda a ka turo zeyi resume a office gobe a can ma'aikatar kasan wana kawo a raina kuwa? Ya faɗa yana kafe Ahmad da ido. Girgiza kansa yayi,faɗaɗa murmushin sa yayi yana nuna ahmad da hannu yace"wallahi kai nakawo a raina"hmmm saboda?be karasa ba yayi shiru()"eh sabida ma'aikatar ku yana da bukatar jajir tattu irin ka masu tsayawa kan gaskiya. "Sannan anfi kashe ire iren mu ba ya tari numfashi sa da fadin hakan,saboda ana ganin kaman muna katsalan dan cikin rayuwar wasu,kana ganin shekarun baya yanda ake farautan rayuwata ba, dan de Allah ya tsare ne da yanzu saide tashin zance,saboda kawai mun kame wasu gurɓa tattun da miyagun ƙwayoyi masu illa dakuma miyagun makamai da muka kama shekaran me ya biyo baya?sai da aka kashe mana jajir tattun yaran mu mutum uku sai daga baya dana bincika ashe ma'aikatar mu ita ke saida bayanan ta na sirri ga waƴan nan yan ta 'addan,ba kuma ko wace uwace zata zauna tana gani ta rasa ɗan ta ba. Uwa ita ke daukan ciki tsawon wata tara da kwanaki sannan tasha azaban naƙuda haifuwa dakuma shayarwa ta kuma bashi tarbiya amma ace rana tsaka wani ya kashe mata ɗan nan nata wani irin raɗaɗi ganin wannan uwa zata ji? Wani irin hali wannan uwa zata shiga?Ammina tana ɗaya daga cikin iyayen da basa son su rasa yaran su yasa ta hanani aikin kwata kwata,kuma na hanu. Yanzun ma wani aiki ya kawoni garin nan,ai kwanaki na faɗa maka irin sana'a da nake ko? yayi hakane dan son ɓangarar da wancan zance. "Eh kafada mun to munyi da wasu costomer's shine nazo haɗuwa da su kuma inason ganin wajen su don musa mu bunƙasa sana'ar tamu. Dariya sajid yayi har yana bubbuga ƙafa yace"kasan Allah Ahmad a shekarun baya idan a kace dani zaka iya sana'ar nan zan musa koma wayene saboda jarumtarka,murmushi gefen baki yayi yana cewa"ai maza sun faɗi kaide yanda nakeji da wannan sana'ar tawa kana ganin zan komawa aikina ne?ai ina koda NAPTIP zasu rinƙa bani linki abunda nake samu na riba bazan ba,zande cigaba da lallaɓa rayuwata,hakade sukai ta hira basu suka ta shi ba saida suka kai sha biyun dare suna hira. "Ke wai me haka zaki shigowa mutane kina kuka wani abune ya faru tsakanin ku? Cikin rawar murya tace"ai da sai nafi kowa farin cikin haka,kasake mami tayi tana kallon ƴar tata cikin rashin fahinta sai kuma ta bude baki da kyar tace"ba bangane me kike son ce wa ba? Sake fashewa da kukan tace"mami ashe duk jiran nan danayi ma yah Ahmad a banza nayi shi,malaman ma dakike zuwa wajen su dukan su ma karyata ne karya suke miki ba gaskiya ko daya cikin maganan su sai cuta. Zaro idonta tayi tace"ke banson sakarci ni duk kinsani a duhu yi mun dalla dalla yanda zan gane"to mami yah Ahmad da matar sa yazo yanzu haka yarinyar tana cikin gidan nan kuma ɗaki ɗaya za su kwana yau na shiga uku. zufa ne ya shiga tsastsafo mata a goshi tana kai komo cikin falon ta dun ƙule hannun ta ɗaya tana kaiwa iska naushi tace"ya akai nayi missin target bayan malam yace mun aure tsanin sa da basma babu shi koda kuwa a mafarkine balle a zahiri to wacece ita wannan me son wasa da wutan? Kede shiga ki kwanta ki kwantar da hankalin ki tunda muka samu ya dawo nan komai yazo gidan sauki kede ki kiyaye dukkan sharuɗan da malam din yace. ******* WASHE GARI: Bayan tayi sallan asuba zama tayi tana yin azkar dinta kaman yanda ta saba tana nan zaune saiga shi ya shigo ɗakin da sallama ƙasa ƙasa ta amsa ba kuma lalle ya jita ba,miƙewa tayi da kyar tana dafe da kanta da har sannan yake sara mata kaɗan kaɗan. Kallon ta yayi kaman ba zeyi mata magana ba sai kuma ya ga hakkin sane kula da lafiyar ta da tsare mutuncin ta tunda ya rabota da kowa ya kuma dauko ta ya zo da ita inda batasan kowa ba sai shi,a jiyar zuciya ya sauke yace "Ya jikin naki? A mamakance ta juyo tana kallon sa ko ba tayi magana ba ya gane mamaki take ta yanda yasan bata da lafiya,kaman ko ya shiga zuciyar ta ya gani yace"jiya da daddare koda na shigo na taddaki zazzaɓi ya rufeki shine na miki allura. A hargitse ta juya tana kallon sa jin abunda yace na ya mata allura kenan ya gama kallar mata jiki"ba fa abunda kike tunani bane kawai alluran namiki ya faɗa yana shiga toilet. Falo ta koma ta zauna shiru tayi tana tunanin yanzu a wani hali ƴan ƙannen ta suke na rashin ta kusa da su,duk da tasan anty hajia anty malika malik ya faisal dukkan su ba za su bari suyi kukan rashin ta ba,amna ita dole tayi kukan rashin su kusa da ita idan ta tuna da wa take tare da. Fitinannen kamshin nan nashi shiya fara isar mata da sakon zuwan sa kafin shi,yana daura agogo a hannun sa ya karasa shigowa falon ko kallon inda take zaune beyi ba yace"ki shirya zamu shiga ciki mu gaisa da mami yana fadin haka ya zauna saman ɗaya daga cikin kugerun falon ya daura ƙafa ɗaya kan ɗaya ya dauki remote yana kara gudun ac. A sanyaye ta miki ta shiga ciki wanka tayi ta fito ta shafa mai ta ɗan murza hoda a fuskar ta,ta feshe jikin ta da turare ta dauki ɗaya daga cikin unders din da ya siyo mata tasa tayi mamakin yanda bra din sukai mata cif cif ya akai yasan size dinta?ganin zata ɓatawa kanta lokacine wajen tunane tunanen banza yasa ta ture komai gefe ɗaya ta saka doguwar riga daya daga cikin.wanda yakawo mata jiya kalan sun mata kyau takalmi shima data gani cikin ledar ta saka ta ɗan murza turaren misik kaɗan ta fito tana yane kanta da gyalen kayan. Yana ganin fitowar ta yamike yayi gaba ta rufa masa baya, duk da beyi mata magana tasan nufin sa nayin gaban babban part wanda take ganin kaman yafi sauran girma ya nufa tana biye dashi a baya saida yayi knocking sannan ya tura ƙofan ya shiga tunda suka doshi nan haka kawai takeji faduwar gaba tana ta addu'a a ranta. shiga cikin falon tayi da ƙafar dama bakin ta dauke da addu'a zaune take a kan kugera da gani wannan zatayi izza kallo ɗaya Aisha ta mata ta sauke kanta kasa ta zube a gaban ta tana gaidata ganin idon Ahmad yasa mami amsa mata tana tambayar gajiyar hanya itade Aisha kanta a ƙasa. Bayan sun gama gaisawa Ahmad ya miƙe ita ma saurin miƙe tayi,ganin kaman fita za suyi mami ta rigasu magantuwa tace"bade komawa zakuyi ba? Sosa kansa yayi yana cewa"dama maidata zanyi ni akwai inda zani ne. "Amma ai ka tsaya kuyi breakfast kafin ka fita,ta faɗa tana tsare shi da ƙananun idonta kaman na ƴan china a ranta kuwa addu'a take na Allah yasa karyaƙi ci take. Har ta miƙe da nufin su je dining amma sai Ahmad ɗin yayi sauri katse mata hanzari dacewa"sauri nake mami karna bar mutane na jirana"to me aciki african time ne fa akeyi kuma ba lalle su din ma sun ()bata ƙarasa ba wayan tayi ringin ya kara a kunne yana cewa "on my way nan da minti goma zan iso daga haka ya kashe wayan yana dan kallon ta dan ta koma inda ta tashi ta zauna"ok mami sai na dawo a dawo lafiya tamasa tana cewa amma nan zaka bar mana ita har sai ka dawo ko?"da ba matsala ya amsa yayi saurin fita. Aisha komawa tayi ta zauna a hankali tana jin zuciyar na tsananta bugawa haka kawai taji wani abu mai kama da tsoro na ɗar suwa a zuciyarta haka kawai.taji matar ba tayi mata ba. Sun zauna shiru tsawon minti uku sai mami ta muskuta ta gyara zaman ta ta kalli Aisha a wulakance tana yatsne fuska tace"yarinya ya sunanki? Aisha ta amsa mata da"Aisha Hmm"Aisha suna mai daɗi tafaɗa tana kafe Aishan da ido da ita kuma tayi kasa da kanta tana wasa da zobe hannun ta. "Me haɗinki da Ahmad? "Eh Aishan tace ganin kaman bata gane tambayan ba yasa ta sake cewa"in nufin shiɗin me hadinki da shi? Miji?ko saurayi?ko kuma aboki?duk da kin masa ƙanƙanta amma zan so sanin wanne daga cikin wanda na lissafa kike? Kai ta girgiza ta alama babu'babu kike nufi ta daka mata tsawa ganin kaman raina mata hankali takeson yi gashi taƙi ta bude bakin ta tayi magana. Safna da tasowar ta daga bacci kenan ta fito tana ya mutse fuska ta tsinkayo muryan mami tana magana a tsawace ta ɗaga murya tana cewa"kode zaman daduro suke? Kallamar daduro nan tama Aisha zafi dan haka mikewa tayi tsaye ta zabgawa safna wani mugun kallon tace"daduron ma iya wace wani inya isa yayi mu gani ta faɗin haka tayi ficewar ta daga falon biyo ta safna tayi tana cewa"gidan ai bana ubanki bane dan haka ba zaki kizo ki kawo mana raini ba shegiya ƴar matsiyata da gani asiri kika masa idan ko ba haka ba me yah ahmad zeyi da ke du beki fa. Ta fada tana nuna Aisha tana mata kallon sama da kasa. Ita de Aisha bata sake cewa kala ba,mami ce ta fito tana tafiyar nan tata kamar ta agwagwa cike da izza tace"ke Aisha zo ki bata hakuri. Ko kallon inda suke Aisha bata sake yi ba,zuciyar ta namata suya ji take kaman zuciyar tata za tayi mata bindiga ta faso amma haka ta rinƙa tausan kanta da kanta"Aisha jeki ki bata hakurin tsunawa wada ba gajiyawa bace abunda gefe ɗaya na zuciyar ta take faɗa mata kenan. Aisha be kamata da haduwarki da mutane ki nuna halin rashi hakuri ba yi hakuri ki bisu a sannu ta hakane kawai zaki san inda suka dosa tana kare wannan tunanin ta nufo su ta tsuna tace"yi hakuri "Ban jiki da kyau ba. Kiyi kakuri tasake faɗa cikin ɗan ɗanga murya daidai Ahmad da yayi mantuwa ya shigo gidan ta ƙaramin ƙofa ya ga komai nan ita ma wasu hawaye masu dumi suka shiga zarya saman kumatun ta. Mami da safna dariya suke ɓaɓɓakewa dashi harda su tafawa kaman wasu ƙawayen juna,juyawar da za suyi idanun su ya sauka kan Ahmad dake tsaye goye da hannun sa saman ƙirginsa ya zuba musu ido.     ALLAH YASA MUDACE [9/27, 10:43 PM] Ummahani: *AURE WUCIN GADI* STORY ZAHRA ALI ABDULLAHI _______________ ✨GORGEOUS WRITTERS FORUM✨ ✨G.W.F✨ GORGEOUS,INTERLLGENT,AND EXPERT WRITTERS,WE THE BEST AMONG THE REST. ________________ CHAPTER 79 A hankali cikin dabara ta share siririn hawayen daya zubo saman fuskar ta,jin sunyi shiru sun dena dariya da duke babbakawa dashi ta gefen ido ta kalli inda suka mai da hankulan su tsaye yake yana goye da hannuwan sa saman kirjinsa yana kallon wani wajen idan duk kwabkwafin ka baka iya ga inda ido yake gani ba. Kallon gefen ido tayi masa tsaye yake kyam ba zaka gane yanayin sa ba miƙewa tayi tana ƙaƙalo murmushi tace"hajia fatan actin ɗin nawa yayi kaman yanda kika bukaci nayi? Da ƴar dariya mami ta shiga amsa mata da"eh eh yayi sosai kinyi yanda ake bukata ke din nan zaki iya zama babbar jaruma kinga yanda ki kai kaman wata KATRINA KAIF jarumai Kasar India din nan,tana kaiwa karshen maganan fashewa sukai da dariya,amma kana ganin fuskokin su kasan dariyar tasu iya fuska ce da zaka kalli zukatan su tsoro ne fal lullube da su. "Murmushi ta sakar musu tana dan juyo wa inda yake tsaye tace"sannu Oga ba de harka dawo bane? Kai ya gyada masa yana laluben hannun ta cikin dabara ta zame hannun ta daga nashi yace"ki daukon mun wasu file dana mance yana nan zaki gan shi saman centar table,kai ta gyaɗa masa tawuce zuwa ciki dan ɗauko masa tana takawa a hankali cikin sanyin nan nata daya zame mata jiki ta nufi ciki dan ɗauko masa da file din. Binta da ido Mami da Fauza sukai wani irin tukuƙin baƙin ciki yana turnuke musu zukatan su dukkan su biyun a tare. (Masu karatu kumun afuwa a shafin da ya gabata madadin nace Fauza sai nace Safna) Mami ce tayi karfin hali ta soma kame kame kunya duk gama lulluɓeta tace"am Ahmad dama dama nace ko zaka tsaya ka ɗanci wani abu tunda ka zo. "Nap mami in nafita zan samu abuda zanci ba haka taso ji daga gareshi ba,amma ba yanda za tayi dole tayi shiru tunda ance tabarmar kunya da hauka ake naɗe shi,kallon sa take sanda yake maganan ita de zata iya cewa ko a fuska ba zata ce taga wani canji tattare da shi ba,saima gwarjini da kara mata a ido. Zungurin Fauza mami tayi tana mata alama ta masa magana,daidai ta kanta tayi daga barin kallon Aisha data ɓacewa ganin ta,tana far da ido ta matse murya tace"Yah Ahmad baka ci komai bafa tunda jiya da kaxo,Abinci dana shirya maka da dare ma baka taɓa komai ba.ta kare magana cike da shagwaɓa. Ba tare daya kalle inda take ɗin ba yace"dama ita na nemawa kuma bata ci ba,jin maganan nasa tayi kaman saukar aradu. Basma duk ta birkice sanda tasamu labarin barin Ahmad garin kaman tayi hauka. Gashin kanta daya sha kari an mata ƙiso blue da ja kitson bob marli duk ya barbaje kuka take riris idon ta duk ya kumbura bayan ta gama fashe fashen ta,kallon Mum dinta tayi da itama bata da aiki sai kiran matattu da basu hakuri Ya hajjo tayi tambayar duniya amma taƙi cewa komai,ƙawarta Hajia bilki ma koda tazo taga halin da take ciki bata sake zuwa ba gudun zargi. Gwaggo Tani ko idan ta zauna sai ta rabka tagumi tayi nishi uhmmm tace"ikon Allah ni Tani ta Malam Tanko tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin inda Mutum baligi mai cikekken hankali yake neman yafiyar gun wanda ya mutu ba. Kallon ta Alh sunusi da shigowar sa kenan tayi da shima duk abun duniya ya ishe sa komai yana neman dagule masa yace"wai Gwaggo tun yaushe take akwance koma ba ara wanda ze faɗamun a cikin ku,hararar sa tayi saida ta gutsuri ɓarin goro ta tauna sannan tace"kaidin ina kake da zabika a faɗamakan? Ni narasa wani irin zama kuke ƴan birni da iyalan ku,sam bakwa bawa iyalan ku lokacin ku, lokutan ku duka na neman kuɗine data neman duniya ne . Yo in banda haka mutum da gidan sa da matar sa da ƴar sa ace besan komai nasu ba,tunda mukaxo ni koda wasa banga kashigo nan ɗin ba,ko irin ƴar shawarar nan a kan wannan biki banji kuna yi da junan ku ba,mu ba haka muke a karka ba idan mutum yayi magana ace be waye ba,idan ko hakan da naga kunayi shine wayewa to Allah tsine....."haba Gwaggo kiyi shiru haka dan Allah. Yah hajjo data fahinci Gwaggo ba shiru zatayi ba tayi saurin cewa"yau kwana uku kenan bata da maganan komai sai matattau. "Amma Hajjo ba inda taje ta kafin faruwan wannan?kuma ba wanda yaxo gunta? Ɗan shiru tayi tana kallon ƙanwar tata dake kwance saman gado cike da tausayin ta tace"to kasan mu kallon ƴan ƙauye take mana amma de sun fita da wannan ƙawar tata mai yawan zuwan nan wata zaka ganta ƴar duma duma haka gajera baƙa to ina kyau tata zaton ita tasan komai,ni tsoron ma nake idan ba Maƙabarta sukaje ba. "Maƙabarta kuma Hajjo? A ɗan ruɗe yayi tambayan jin inda tace sunje ɗin,ta amsa da"eh yanda na fahinta kenan tunda can ɗinne de maƙwancin matattu idan ko ba a can ɗin ba ai nane zata ga wasu Matattu da har zata ruɗe ta zauce lokaci ɗaya,shiru yayi sai kuma yace"ita kuma Basma a wani hali take yanzu? "To itama yanzu ta barnan bayan ta gama wa uwar kuka,rintse idon sa yayi yana jin zafi halin da suke ciki a ransa bata da maganan komai sai ta Ahmad yatafi ya barta ɗazun nan saida tasaka mukaje har can gidan su yaron amma halin da muka iske Mutanen gidan ya tabbar mana da kaman Gidan ba lafiya.dan mun tadda likita yana duba Mahaifin sa sannan ita Mamar Yaron wata Mata ko ƴar uwar tace tana zaune bata baki akan tayi hakuri ta cigaba da masa addau'a Allah yakare sa aduk inda yake,ni narasa wani irin hau ne wannan. Kaman waƴan da suke tsaɓawa Allah wannan abun naku gaskiya abun dubawa ne,ganin yaƙi cewa komai sai ta daura da cewa jekaga halin da Basma ke ciki dan ita ma halin da take ciki abun dubawa ne,dan sai sumbatu take idan ma kunsan kuna aikata ba daidai ba kamata ku koma ga Allah tun kafin lokaci ya ƙure maku baki ɗayan ku,da sauri ya ɗago ya kalle ta,jin jina masa kai tayi tace kana mamakin abun da nace ko?to karkayi mamaki bansan komai a kanku ba amma ɗan zamana gidan nan naku naɗan fahinci wani abun dan gane da yanda kike zaune daga kai har iya mariya. Ba kwa bawa junan ku lokaci ko kaɗan ace Mutum da gidan sa da matar sa da ƴar sa amma ba zaka iya zama ko na minti biyune da su ka fuskance su suma su fuskance ka ba,ko wannen ku tsabgan gaban sa yake. Be barta ta karasa maganan ba ya wuce yana ficewa daga ɗakin yana cewa"ki kimtsa ta zam turo likita yaxo ya dubata daga haka ya fita daga ɗakin. Ɗakin Basma yanufa yana tura ƙofan ɗakin yayi saurin rintsa idon sa ganin yanda ta hargitsa ɗakin ita kanta a birkice take kaman mahaukaciya sabon kamu. Rufe kofan yayi ya nufeta da sauri yana kiran sunan ta,tasowa tayi ta faɗa jikin sa tasa kuka saida tayi mai isanta sannan tayi shiru tana ture shi tana komawa saman gado ta zauna. "Mai haka baby? Kinga yanda kika maida kanki kan namiji ɗaya. Idan shi ya gujeki ai zaki samu wani bawai ii zauna kina irin wannan haukan ba. Sauri ɗagowa tayi tana kallon sa da jajayen idon ta da suka kumbura saboda kuka tace"mahaukaci ya. Ka kirani dan ina nanu alhinin rasa masoyi da nayi. Daddy ka kasani bani abun da nakeso,ka kasa cikamun burina na mallakan Ahmad matsayin miji ka..."ya isa haka baby..ita ma katse shi ta tana cewa barnj nayi magana barni na faɗi abun da yake raina ko zan samu saukin abun da nakeji,baka taɓa sakani ban yima shi ba,koman wuyan sa koda raina bayason abun nan zanyi shi saboda cikan burin ka. Amma yau ka kasa bani abun da nake so kasa cikin mun burin dadday idan nasara shi kowa ma ze rasa tana kai karshen maganan ta ta fita waje da gudu mara mata baya yayi tare da kiran sunta.   Masu karatu dan Allah kumun afuwa rashin jina kwana biyu wasu uxururruka ne suka tsaidani .   ALLAH YASA MUDACE   ALLAH YASA MUDACE

Post a Comment for "AUREN WUCIN GADI Complete Hausa Novel"