BAKAR TA'ADA BOOK 2 Complete Hausa Novel
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA.......*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
Cikin kasala irin wacce b'acin zuciya ke sababa wa, Baban Marina ya ce "waye kuke ganin ba zai auru ba, tamkar Yabina! Wane ne shi?"
Hatta Dada jikinta ya yi lubus da Baban Marina ya ce Yabinsa a akan idon ta da na y'anuwansa. Wanda hakan na alamta ce wa ya kai makura wajen kawaicin da yake yi amma ba'a yi masa kara.
Daga Baban Tsakiya har na Kasuwa ba wanda ya iya cewa kanzil domin sun shiga yanayi na jin nauyi da borin kunya.
Sun fahimci fishin da yake shinfid'e a fuskar yayan nasu ya tunbatsa.
Sai suka yi dabarar kame wa daga jaye jayen maganar.
Bai sake jiran komai ba, ya mike tare da yiwa Dada sallama ya fice.
Yana fita Baban Tsakiya ya ce "Muna cikin wani irin kalubale a wannan duniyar.
Ace ba dama ku tattauna da dan-uwanka ya fahimce ka, shike nan sai ya zama sanadin tabarbare war al'amura?"
Ya yi k'wafa mai nuna takaicinsa muraran.
Baban Kasuwa yana bu'de baki sai ce wa ya yi "To ai irin wannan al'amarin wuya ne da shi. Tuni Ubangiji yasan al'ummar Manzonsa zamu riski wannan zamanin shi yasa ya saukar mana suratul Yusuf dan ta zama izina ga masu hassada da k'yashi. Ta kuma zama gargadi ga masu hankali.
Wani abin kaicon ma mu babu y'an uba a cikinmu, amma babu yadda za'a yi a ha'du a yi hira da walwala cikin farin-ciki saboda kawai ka fi mutum haske?
Gaskiya zan fa'da miki Dada.
Tunda ke kin isa da shi, ba wanda ya cancanci Yabi sai Tijjani, su rufa wa junansu asiri, shine kuma zai iya biyar da ita, ya yi maganin shak'iyancinta".
Baban Tsakiya ya numfasa ya ce "Tunaninmu d'aya Iliya, sai dai ba lallai ne ya amince ba.
Tunda duk iyashegenta bai yarda ja'irar yarinya ba ce. Zai yi wahalar gaske ya ba shi tunda shi lalacewarsa ta bayyana a gida da dawa.
Ita kuwa mu na kusa ne muka fahimta kawai".
Dada ta saki ajiyar zuciya ta ce "Idan haka ta faru kuwa ina da yakinin mai sunan manya zai nutsu domin komin ginshirarsa ba zai kushe ta ba.
Ubangiji ya kyautata halittarta, gata yar shawalwala da zata da'de tana cin zamaninta".
Suka gintse fuska suna fa'din "Kyaun hali da tarbiya ai sune kyaun mace Dada."
Kawai dai ki sanya baki a ba shi ko ma sarara, domin idan shine mijinta zai karya dukkan lagonta."
Basu tashi ba, sai da suka tabbatar ta gamsu bawa Bulkachuwa auren Yabi fa'ida ne mai yawa a garesu bakid'aya.
Baban Tsakiya ya fi kambaba lamarin, a zuciyarsa kuwa so yake a yi a yi a auren ta tunda kusan kullum sai ya yi mafarkin Jabir ya bijire masa ya aure ta.
Sun ki kwamishina ne dan kada haske ya shiga k'ofar dan-uwansu, tunda sun tabbatar nagartacce ne, basa son ya'yansa su yi k'arfi.
Sun fi son a ce su da y'ay'ensu sune masu fa'da aji.
Auren Bulkachuwa kuwa sun san ba wani fiffika da y'ar iskar yarinyar nan zata yi musu.
Tunda a bayyane yake matu'kar mace bata samu miji na gari ba to rayuwarta ta na'kasa.
Washagari da sassafe Baban Marina ya yi sallamah ya ce ya tafi Azare.
***
Na fito sanye cikin uniform, na isa mashigar zauren Dada dan gaisuwa da kuma biya wa Nasiba. Sai na ji magana k'asa kasa daga dakin Bulkachuwa.
Na kasa kunne dan na ji me yake fa'da.
"Bazan sake turo kowa gidanku ba Bilki. Na yarda ki na sona, amma kuma ai ba zaki iya aurar da kanki ba, dole sai da wakilcin iyayen ki. Kema kin san ina sonki, amma tabbas bazan sake turo kowa da zummar a nema mini aurenki ba".
Na yi fakare, jikina ya yi laushi akan abin da na ji.
Waton ba karamin son Bulkachuwa y'anmata suke yi ba.
Bansan me yasa shi kuma yake da jarumtar juya wa soyayya baya ba, matu'kar aka nemi muzanta shi.
Na tsinci kaina da fa'din "Ina ma irin zuciyar Tijjani nake da ita?" Da tuni na yi watsi da tunanin Jabir da soyayyarsa.
Amma ina! Har yanzu ina jin sonsa, kawai na danne ne dan babu yadda na iya.
Na shiga cikin gidan na tarar da Nasiba ta shirya.
Na gaida Dada kamar yadda na saba.
Sai dai amsa mini da ta yi, ya banbanta da sauran watannin baya. Domin tunda kwamshina ya bayyana mini, da karsashi take amsa mini gaisuwa ta.
Amma a yau cikin wani irin yanayi da na kasa tantace wa.
Sai kuma ta zarce da fa'din "Wanda duk ya yiwa mahaifinsa biyayya ba zai tab'e ba. Ina da tabbacin ko wuta na rura na ce da tsohonku ya shiga zai fa'da ne kawai babu tambihi.
Ina rokonku ku dinga yi masa biyayya, ku yarda ya isa da ku, mussaman ke Yabi da tun shekarar da kika iso duniya ya shiga cikin tala jaurar duniya".
Ta fa'da kuka na subuce mata.
Jikina ya mutu murus a dalilin kalamanta, tunanina ya shiga canke canken akwai al'amarin da zai biyo bayan wannan jirwayen na Dada.
Muna tafe da Nasiba duk uban maganar da take yi mini akan Bulkachuwa na kasa ce mata uffan.
A dalilin zuciyata ta riga ta baci da yadda Dada ta ce wai tunda na iso duniya ubana ya fa'da cikin ibtila'i.
Na sani ba yau ake fa'da ba, Mama ta sha fa'da mini ni din tauraruwa mai wutsiya ce, haka ma ya'yanta su Yaya Indo.
Tun ina damuwa har na zo abin ya daina damuna, domin Baban Marina bai ta'ba yi mini wannan izgilancin ba.
Amma a yau sai na tsinci kaina da jin ciwon furucin Dada kwarai da aniya.
Na dinga hasashen me ya janye mini alfarmar da na a samu y'an watannin nan a idonta?
A daren ranar Babanmu ya zaunar da ni da matansa ya fa'da mana aurena da Alhaji ba zai yiwu ba, bisa wani dalili da bai bayyana mana shi ba.
Ya je shi da Alhaji Tanimu sun bashi ha'kuri. Ya gamsu sun yi masalaha, duk da ya shiga rud'ani sosai.
Ya kuma ce ya yafe duk hidimar da ya yi.
Jikina ya mutu, zuciyata ta tsinke.
Na kasa bu'de baki na yi magana.
Ya sallami matansa suka bar ni da shi.
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWIA SAIWOWIN SANYI*
AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU*
*AKWIA SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*
Ya tausasa harshe har ya bani tausayi.
Ya ce "Yabi kinsan Nura dan wajen Babanku Tanimu?"
Na daga kai tabbacin eh.
Ya numfasa ya ce "Madallah! To zai zo ku gaisa, shi na za'ba miki ya zame miki miji. Ubansa tuni yake ro'kon na ba shi ke ya bawa Nura, tunda ya samu labarin abin da y'anuwana suka yi mini, ina ta bagarar da maganar. Saboda ganin Alhaji ya shigo da k'arfinsa.
Amma a yau din nan na amince masa.
Ina ro'kon arziki Yabi, kada ki kunyata ni. Kinga shi namiji ma ubansa yana fa'da masa ya amince da farin-ciki da walwala. Ki kwantar da hankalinki irin k'alubalen da kike fuskanta da kananun shekarunki na alamta cewa zaki samu kyakkawar rayuwa a gaba".
Hawaye taf a idona na ce "Na amince Baba! Allah ya sa hakan shine mafi alheri".
Ya amsa da ameen ikin farin-ciki mai yawa, tare da sanya mini albarka.
Ya sallame ni bakinsa dauke da addu'a a kaina da lamarina.
Ina shiga d'akin Gwaggo na fashe da kuka.
Ta ru'ko ni sosai ta dinga bani ha'kuri.
Wannan rarrashi da Gwaggo ta yi mini ya sanyayya mini zugin da nake ji a zuciyata.
Da na nutsu sai na fahimci ba kukan rabuwa da Kwamshina nake yi ba. Domin ba wani sonsa nake ba, dama na yarda zan aure shi ne, dan na gaji da zaman Gidanmu. Sannan Bulkachuwa ya kitsa mini cewar da na yi kukan takaici a gidan babu, gara na yi a gidan wadata.
Amma sam babu soyayyar da zan yi ba'kin ciki irin haka.
Kawai ina kukan yadda al'amarina ya banbanta da na kowacce y'a a gidanmu ne.
Maganganun Gwaggo sun sake fahimtar da ni ita dama ba son aurena da Alhaji take yi ba, ta yi shiru ne dan gara aurensa akan na Jabir.
Amma ta ce bata fasa addu'a ba, bata fasa nema mini zabin Allah ba.
Dan hakan kuma ya kasance sai ta gamsu Ubangiji ne ya amsa mata.
Kwanki biyu na warware tamkar komai bai faru ba, na cigaba da harkokina.
A yammacin wannan rana ta litinin mun taso daga Islamiya sai ga aike wai ana sallamah da Yabi in ji Nuru Tanim.
Na dan diririce na kasa magana a dalilin yadda ya zamanantar da sunan na shi.
Na dinga canki canki wane ne Nura a y'ay'an, Baba Tanimu? Domin y'ay'an gidan yawa ne da su, matasa sun kai bakwai ko wanne ya isa aure.
Na kasa cankar wane ne shi a cikin jerin matasan gidan.
Inna da kanta ta cewa yaron ya je ya ce "ina zuwa".
Hijabina har kasa na sanya, bayan Gwaggo ta matsa mini na shafa hoda.
Na fita cikin zullumin yadda zan gan shi. Tunda bani da sauran za'bi akan lamarin.
A babban zauren na hango shi sanye cikin shudiyar shadda sosai, kansa sanye da hular da ta dace da kwalliyarsa.
Ko ka'dan ba shi da makusa, ya fi Yaya J cika, tsayi ne dai zasu yi taya.
Batki ne sosai, amma ma'abocin tsabta ne daga ga ni.
Take na ji abin da ya d'aure mini kirji ya fa'da mini domin ban ganshi a cikin mummunan yanayi ba.
Baya aikin gwamnati, amma yana koyar wa a wata firame mai zaman kanta, boobies a sannan yana da shagon caji da turin wakoki ko finafinai a wayar hannu.
Muka gaisa cikin yanayi na babu yabo, babu fallasa.
Muka yi shiru.
Tsawon lokaci kafin ya katse shirun ya ce "Asiya! Zuciyata ta harba domin har cikin raina nafi son a ha'da mini da Yabi.
Na amsa a hankali da "Na'am".
Ya tausasa murya ya ce "Na da'de ina son ki, na sha fa'da wa Babanmu ya taimake ni ya nema mini auren ki, sai ya bada hanzarin dan-uwanki ne yake son ki, ba zai yiwu ya gabatar da maganata ba, tunda akwai nauyi a tsakaninsa da Baban nan gidan. Dan haka ko da kika gan ni anan ba turo ni aka yi akan dole ko biyayya ba, dama ina son ki tun ina zuwa makarantarku".
Na yi kasa da kaina ina sake samun nutsuwa mai yawa.
Ya sake sassauta wa ya ce "Idan har kina da matsala ko kina ganin ban yi dai-dai da ra'ayinki ba, zan san yadda zan yi na zulle wa maganar ba tare da an ga laifinki ba, domin al'amarin aure ba k'aramar tafiya ba ce da za'a yi ha'kurin dole a cikinsa."
Na tsinci kaina da cewa "Babu damuwa Allah ya tabbatar mana da alheri".
Dadi ya kama shi, ya ce" kenan Asiya ta aminta da ni?"
Murya babu amo na ce "Yabi bata da burin yin fatali da burin iyayenta ko da ya ci karo da nata ra'ayin."
Farin ciki ya sake lullube shi. Ya dinga fa'din ma sha Allah! Madallah da Yabi".
Na taya shi murmushi.
Ya ce "da alama kina son Yabi, ni kuma sai nake ganin karamci ne na kira ki da Asiya."
Na cuna baki na ce "Tunda na riga na sami wannan falalar ta zuwa gabas, kawai ka kira ni Yabi domin ina son sunan da dukkan zuciyata".
Ya murmusa ya ce "An gama Yabin Nuru".
Zuciyata ta tsinke yau ga abin da Yaya J ya guda, na jingina wa Yabinsa sunan wani ba nasa ba.
Mun jima muna dan tattauna wa duk da shine yafi yin hirar sosai.
Ya ciro ku'di ya bani, na ki karba.
A sanyaye ya ce "Matu'kar baki karba ba, to alama ce ta ban samu karbu wa ba".
Jin hakan ya sanya na mik'a hannuna duka biyu na karb'a.
Daidai lokacin Bulkachuwa ya shigo a hargitse rigarsa daban haka ma wando daban duk a yamutse. Da alamu ba nisa ya yi ba. Inda a ce d'an wanka ne sosai bansan irin rubibinsa da za'a yi ba, tunda a hakan ma ba'a fasa sonsa ba.
Nura ya mika masa hannu suka gaisa ya wuce babu walwala nasan kuma yana taya kwamshina kishi ne.
A lokacin na sake tabbatar da tsayi da cikar Bulkachuwa ya kai k'ure wa domin sai na ga Nuru bai kai kafadarsa ba.
Daga haka muka yi sallamah ya tafi.
Na shiga gida ana kiran magariba.
Bayan mun idar da salla na bawa Gwaggo ku'din da ya bani sababbin yan dari biyar guda goma cif.
Ta yi shiru sai kuma ta ce "Allah ka sawa al'amarin albarka, ya sa karshen wahalarmu kenan".
Na amsa da Amin a zuciyata domin ni kaina na gaji da yadda komai yake kwace mini.
Gaba'daya shekaruna sha shida ne da ka'dan amma na gaji tunda al'adar auren wuri ne a gidanmu.
Wai duk yadda nake da k'arancin shekarun nan, da yadda nake y'ar tsurut habaicin rashin aurena a ke yi mini, ko a jefi Gwaggo da bak'ar magana.
Har ta kai bani da kalubalen da ya wuce zaman gidanmu a rayuwata.
Rayuwar gidanmu da ta gidan Yaya Ummi ta sanya na k'yamaci zaman babban gida. Wani zaman idan an yi sa'a sai ya zama tsintsiya dan ha'din kai. Wani kuwa sai ya zama tamkar sansanin yaki dan fitina.
Ta sake kallona ta ce "Nasan yaron dan wajen Sahura ne, yana da zuciyar neman na kansa ga shi mai jin maganar iyaye ne, duk cikin matan gidan dakinta yafi na ko wacce fasali da kayan jere mai kyau, kuma duk shi ne yake yi mata, shi ka'dai ne namiji a d'akinta, y'ay'anta duk mata ne, amma da ya ke mai zuciya ne sai tafi mai y'ay'a maza biyar gata da kyan ga ni, ta bar uwar maza je da fankamar ita ce da gida.
Shikenan rabuwarmu da Kwamshina. Ya mini waya washagarin da Baba ya ce ya je Azare. Ya fa'da mini yadda Baba ya je ya ba shi hakuri.
Ya fahimci Baba suka rabu cikin girma da arziki, tare da ro'kon idan auren ya zo a sanar masa zai halarci dauri aure.
Nima ya mini maganganun masu taushi da nuna muhimmancin yiwa mahaifi biyayya.
Duk da ba wani sonsa nake yi ba, sai da na yi kukan yadda kalamansa suka dagargaza ni. Kewarsa ta taso mini ba ka'dan ba.
Ya dinga rarrashi tare da tambayar me zai siya mini na kayan aure dan na yarda ya gode da karamcin da na yi masa.
Na kasa cewa komai sai shine ya ce "Zan aiko miki da sako zuwa satin sama in sha Allah"
Ya k'are maganarsa da fa'din "Allah ya sa ki shiga gidan auren a sa'a, Allah ya zaunar da ke lafiya".
Bulkachuwa a bakin kwamshina ya ji maganar aurenmu ta ruguje.
Rannan da hantsi ya aiko yana kirana.
Zuciyata d'aya na je na tarar da shi a tsakar gidan Dada yana zaune kan kujerar tsuguno. Na zauna akan turmin da yake fuskantarsa.
Ya kalle ni da tarin kulawa ya ce "Asiya Toro me yake faruwa ne? Jiya na shiga Bauchi sai nake jin labarin da ya ki'dima ni a bakin Honarable.
Nasan ba zai mini karya ba, me yasa kika canja?
Me yasa dan Allah?"
Na yi k'asa da kaina haka kawai na ji hawaye ya k'wace mini. Domin idan aka cire yan kofarmu ba wanda ya nuna damuwarsa ko alhini akan shiririce wa da maganar Kwamshina ta yi sai Tijjani.
Na tabbatar bayan soyayyar da yake yiwa lamarin, to akwai kishin wula'kanta ni da aka yi a gidan, shi yasa yake son na yi auren ke ce raini.
Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi ya ce "Ba kuka zaki yi ba, ya ce mini Baba ya gabatar masa da hujja mai k'arfi shi yasa ya ha'kura.
Wacce irin hujja ce wannan dan Nabiyur Rahmati?"
Ya fa'da a matu'kar zafafe.
Kafin na ce komai sai Dada ta rarrafo ta ce "Ni ce nan! Na barranta lamarin, na kwashe masa albarka, ba zai yiwu na ha'da jini da mai kafirtamu ba. Ba zai yiwu ta auri wanda iyayenta suka tabbatar ba mutumin arziki ne ba".
Da kakkausar murya ya ce "Dada me kika yi hakan?
Su waye iyayenta?"
Yana rufe baki ta ce "Su Badamasi mana".
Maimakon na ga ya sake fusata sai kawai na ga ya kwashe da dariyar iyashege ya na fa'din "wannan shine abin dariya kunama ta ciji danwanke. Shi Baban Tsakiya idonsa da kwalli har ya ce wani bai cancanci Yabi ba?
Sanin kowa ne Jabir da Yabi masoya ne tun suna yara k'ananu, amma shi da kansa ya datse soyayyar kuma yanzu Allah ya turo mata wani sai ya ce bai cancanci a ba shi aurenta ba. Wanne irin lamari ne mai kama da k'yashi da kuma hassada?"
Dada ta rabka salati tana fa'din "Kawunka kake fa'din wannan kalaman a kansa?
Mai sunan manya anya zaka yi hankali kuwa?
Kusan ma fa saboda kai ya yi wannan al'amarin amma ka ke sakin maganganun da suka yi daidai da zaginsa kake yi."
Ya sake fashe wa da dariya ya ce "a kaina, ni kuma?
Lallai kuwa, zan ga ta yadda za'a yi, wannan bawan Allan ya nufo ni da wani alheri. Rannan ba abin da bai fa'da mini ba, akan sun je kai mini ku'din aure gidan kananun mutane ba'a karba ba.
Ya dinga cin alwashin ba zai sake shige mini gaba a harkar aure ba. Ni kuma abin da bai sani ba, ai kawu ba uba ba ne, dama dangin uba ne a hakku su nemo mini aure, bare ya ce zan wani damu."
Dada ta sake rangada salati tare da cewa "Mai sunan manya wanne irin dibar albarka kake yi ne haka tamkar ka sha k'waya?"
A tunzure ya ce "Ras nake! Na gaji da fitinar mutanan ne, duk wata fitina su suke kitsa ta.
A gabansu uwar Nasiba ta dinga sakin maganganu a kaina ta barranta y'arta da ni, ba wanda ya ce kala a cikinsu. Haka nan shima har yau ba wanda ya kalubalan ce shi akan hukuncin da ya yiwa Jabir na auren Maijidda saboda yana da cikakken iko a kansa. Akan me zai yiwa lamarin Asiya katsalandan alhalin ba kallon y'a yake yi mata ba?
Akan me zai nemi ya dinga nuna ya isa da ni alhalin akan idon uwata suka kasa yi mini alfarma da kawaici."
Ta ce "Allah ya shirye ka, albarkar mai sunanka shiriya zata sauko maka."
Ya bata fuska ya ce "Tare zaki roka ta zo mana da ke, tunda akan idonki ake yin abubuwa na kura kurai amma ba kya iya tsawatar wa. Rannan na ji wani malami yana fa'din ainihin manufar ma'anar kuyanga ta haifi uwargijiyarta. Sak fatawar da ya bayar tamkar ke ya siffanta haka na dinga ji".
Na zuba ido. Ina jiran ta rushe da kukan da zata tara masa jama'a tamkar yadda take yi mana. Amma sai ta share ta yi mirsisi ta fanshe da cewa "Shi ubanta ai ya yarda na isa da shi, shi yasa ya katse al'amarin babu tashin hankali.
Allah ya shirye ka mai sunan Shehu.".
Ya shareta ya kalle ni ya ce "Yanzu kina son wannan ba'kin yaron ko kuwa dole aka yi miki?"
A hankali na ce "ko bana sonsa tunda Baban Marina ya amince ai maganar ta kare".
Ya girgiza kai ya ce "Baban Marina mutum ne Wlh amma ban son ha'kurinsa, any way Allah ya sanya albarka all the best Asiya Toro".
Daga haka ya mike ya fice yana fa'din da kin ce ba kya so. Wallahi da tsaya miki zan yi, komin sharrin mai sharri ba za'a baki wanda ba kya so ba, domin kema y'a ce ba baiwa ba. Kina da hakkin ki so a kuma so ki".
Wannan abin da ya yi mini sai ya rage tsanar sa a raina.
Dada ta dinga fa'din "Sha sha kamar ba saboda shi aka yi komai ba."
Na rasa gane manufar wannan maganar ta Dada.
Tsawon sati da kulla alakarmu da Nura wanda ya yi zuwa uku kenan.
Mamakin kaina nake ta yadda ya shiga raina sosai.
Ko dan sau'kin kansa da yadda ya iya kwalliya da shirya zan ce ne?
Ga shi ma'abocin kyauta duk zuwa sai yasan me ya ru'ko mini wala na ci, ko na amfani, gwargwadon k'arfinsa.
Mahaifiyarsa da ake kira Yaya itama ba karamin son al'amarin take yi ba. Domin da kanta ta zo da kuma ledarta mai shak'e da kayan kwalliya.
Kusan yini ta yi lamarin da ya takura ni, kunyarta sosai na ji. Wanda ko kusan ban ta'ba jin irin hakan akan mahaifiyar Yaya J ba.
Karba ta samu daga ahalin gidanmu, dan kuwa ko Mama bata yi abin kaico ba, har ta tafi.
Dada ce dai bata wani karbe ta da fuska mai yakanah ba, hatta shi da kansa da ya je gaisheta bai ji da'din karbar da ta yi masa ba.
Hankalina ya fara tashi domin kuwa ba hannu Rabbana ya je mata ba, sai da ya siyo mata lafiyyayun lemo da kankana da ayaba tika tika.
Na dinga fargaba da tunanin wata'kila wannan d'in ma, ta yi mini sanadinsa tunda su Baban Tsakiya kullum cikin fadin Alh Tanimu munafiki ne wai yana nuna wa ya fisu kusanci a wajen Dan-uwansu".
Kuma gaskiyar magana a yanzu da muka shafe satika kusan uku ba k'aramar shakuwa muka yi da shi ba.
Ina matu'kar kad'uwa a duk sadda zuciyata ta ayyana mini muna iya rabuwa. Ban ta'ba kuma shiga irin wannan yanayin a baya ba.
Duk kishin Yaya J a kaina ya ha'kura ya bar ni da Nuru domin da kansa ya ce ba zai hana ni kula shi ba, amma shima kada na ce na sallama shi, ya yarda ni din allura ce cikin ruwa mai rabo ka dauka.
Dan haka zai cigaba da lalube cikin ruwa har Ubangiji ya taimake shi ya damk'e abin da yake nasa ne
KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers*
*08089965176*
*07084653262*
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*MASU BUKATAR YON RIGISTA DA G.H.T. KAKARKU TA YANKUE SAKA DOMIN KUWA FASEELAT ZATA MUKU JAGORA HAR KU FAHIMCI KOMAI CIKIN KYAKKWAR MU'AMALA DA KYAUTATAWA*.
*07039269802*
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya, kusancina da Nuru yana sake shahara. Har ta kai ya goge mini rad'ad'in rashin kwamshina a zuciyata.
Rashin Yaya J ne bai bar ni gaba'daya ba, amma ya yi rauni matu'ka da gaske.
Yayin da Bulkachuwa ya d'ora masa karan tsana haka siddan.
Sau biyu yana ganinmu idan Nuru ya ba shi hannu sai kawai ya d'aga masa, amma ba zai yarda ya ba shi nasa ba.
Na cigaba da zuwa makaranta hankalina ya fara kwanciya. A lissafi saura kwanaki talatin da tara na bar gidan.
Tare za'a ha'da da na Nasiba domin tuni wanda za'a bata ya ce ya kammala gininsa dan haka ba za'a kai bad'in da suka ambata da farko ba.
Lafiya lafiya yan uwan Alh Tanimu suka kawo komai na al'adar aure aka karba, cikin mutuntunta juna.
Saboda Baban Marina ya gayyato yan'uwansu na Lame da Kano kan dole su Baban Tsakiya suka zauna aka karbi bak'i da su.
Gidan Nuru da yake bayan gari k'arami mai kyau shigen na Yaya J.
Irin murnar da nake ciki na barin gidanmu tamkar wacce na girma ba'a gaban uwa da uba ba.
Domin na riga na kai makura wajen son na kauce na bar wa su Baban Tsakiya gidan su tabbata a cikinsa.
Ubaida ce farkon wacce aka kai makaranta kwana a gidanmu.
Idan mai karatun bai manta ba diyar Baban Marina ce itama diyar Inna ta biyu.
Yau an yi hutun zangon karatu na biyu.
Bulkachuwa ne ya taho da ita tunda shi kusan akai akai yake zuwa Bauchi.
Tana GGC Bauchi ne ajinta uku, mutumiyar Ikilima ce haka suke tamkar ni da Nazira sai dai banbanci akwai tazara mai yawa tunda shekaru kusan uku ta bawa Iki. Amma amincin da yake tsakaninsu sai Allah.
Saboda Ubaida, Iki ta nace boarding ita ma zata tafi, duk da dai ta fara day ajin ta d'aya a sakandire su d'in kamar karatunsu ba zai yi sauri irin namu ba.
Tunda a yanzu haka har Dada ta fara maganar auren Ubaida, a dalilin tana da garin jiki, kuma tana shirin shiga shekaru sha biyar ne.
Cikin farin-ciki muke hutunmu, na saje a tsakanin Ikilima da Ubaida tunda ni din ba ni da auki.
Ba abin da yake damuna sai bibiya da nacin yaya J.
Matu'kar kuma na yi saken da muka ha'du yini nake yi babu sukunin a dalilin fama da tsallen badake da zuciyata take yi.
Da yake aurena ba kwatsam ya zo kamar na Nazira ba, Baba ya samu damar siyan dimemiyar katifa mai nagarta.
Ya tanadi labulaye da kafet, da ledar tsakar daki da kuma bargo.
Irin dai kayan da aka yiwa Nazira.
Ya ce idan ya samu dama ko a ranar da za'a kai ni ne idan ku'din gado da kujeru sun samu sai a siya tunda gasu nan a bakin titi ko ina, idan kuma bai samu ba to a hakan zai kai ni arzikin gidan miji yafi na uba.
Ban damu da rashin kayan katako ba, na sani in sha Allah yan'uwana zasu yi mini irin na Nazira.
Sai dai bani da garanti akan manyanmu yan dakin Mama. Domin sun yi nisa a cikin *BAK'AR TA'ADAR* Y'an ubanci.
Su Yaya Salisu ne kawai zasu tsaya mini tunda sun fara daukar albashi duk da dai ba mai wani nauyi ba ne amma dai sunfi da .
Ranar asabar mun dawo daga Islamiya.
Yammaci ne sosai muna tafe da yan ajinmu.
Mun zo daidai wani gida da bai kammala ba, muka ga Bulkachuwa da wata yarinya wacce nafi zaton ita ce Bilkin da na ji yana fa'da a waya kwanaki, sun fito daga cikinsa.
Gajeriya ce, amma fara ce sai dai ko kusa bata kai ni ba.
Sannan ita din yar duma duma ce tamkar su Nasiba.
Kirjinta a cike yake, jikinta irin rugu-rugu ne.
Nan da nan shaidan ya kawo wa zuciyata caffa domin take sai na yi aiki da zato, na zarge su da al'amarin da shaidarsa yana da tsananin tsauri.
Na kalli Nasiba na ga hankalinta na kansu, tausayinta ya kama ni, domin sai yanzu na gane ba son Nasiba yake yi ba, domin ko ka'dan bai yi mata uzziri irin wanda ya yiwa Bilki ba. Ko da yake maganganun da mahaifiyarta ta yi wa uwarsa ne suka yi masa ciwo ba ka'dan ba.
A zuciyata na ce shi kuma Bulkachuwa yana son lukataye masu manyan nonuwa.
Na sake kallonsu na gan shi kamar kullum ba wani wadatatcen wanka, yana cikin yanayin babu yabo babu fallasa.
Amma ni kam duk saurayin da ya zo mini a haka ina da tabbacin ba zan saurare shi ba.
Domin an sanya mini son namijin d'an wanka, haka nan na k'yamaci marar gyara irin Tijjani.
Amma a hakan yake murza zuciyoyin yan mata kintsatssu da watsatssu.
Na sani kuma kyaunsa da zubin k'arfin da yake da shi yake rudarsu.
Gaba'daya a murde yake dukkan physiques dinsa sun bayyana alamun yana motsa jiki yadda ya kamata.
Na ja tsaki muka wuce, yayin da ya yi kamar bai hango mu ba.
Ba zato na ji Nasiba ta barke da kuka mai sauti.
Wani har tsayar da mu ya yi yana tambayar ba'asin kukanta, domin dai ya dauka ta samu labarin rasuwar uwa ko ubanta ne.
Kukan nan na Nasiba ya yi matu'kar dukan zuciyata, domin na san pain din da ake ji na kubuce war masoyi domim ni din katuwar victim ce.
Muna tafe, tana kukan bata fasa ba, duk yadda nake bata ha'kuri da kalamai masu nutsar da zuciya.
Kukan nata sai ya zama sanadin tabarbare war sassaucin da na yi akan al'amarin Bulkachuwa.
Domin na dauke shi a mai son kansa, mai fifita bare akan jininsa.
Sannan fitowar da suka yi daga kongon gidan da babu kowa a ciki ya sanya na sake k'yamarsa da dukkan zuciyata, domin kowa ya shaida shi din mai BAK'AR TA'ADAH ne.
Da k'yar na shawo kanta ta yi shiru.
Amma a k'asan raina haushin makauniyar soyayyar da take yi masa nake yi.
Gaba'daya ta lalace, ta zube bata farin-ciki ko ka'dan da auren da za'a yi mata.
Uwarta kuwa ta ja ta dake akan sai dai ta canja uwa matu'kar ta ce ba zata yi wa mahaifinta biyayya ta so d'an-uwanta da ya za'ba mata ba.
Duk da k'arancin shekaruna na fahimci Tijjani ne kawai mahaifiyarta bata so, domin kuwa mahaifin su Nasiba bai cancanci ya yi irin wannan ikon ba, tunda gaba'daya fita ya yi daga hidimarsu, ba wanda ya taba ganin an kawo musu wani abu daga mahaifinsu, ko danginsa, duk wahalarsu uwarsu ce da danginta.
Amma an zo batun aure ya nuna ikonsa na uba, ita kuma duk ba'kin cikin da ya k'unsa musu daga ita har Dada sun manta.
Abin da nake tambayar kaina shine shi wanda Baba Maryon ta fifita akan dan yar'uwarta tana da tabbacin nagari ne?
Ko dan kawai ma'aikacine, ya kuma gina gidansa?
Na yi imani da ace Bulkachuwa yana da ku'di to ko yafi haka lalace wa za'a ba shi, duk wani na'kasunsa sai an yi masa kwaskwarima ya zama abin uzziri.
Amma da yake bashi da ko sisi, sai take ta akilon y'arta ta nisan ce shi, ta so d'an-uwanta na dangin ubanta, na d'an yar'uwarta kuma ya tabbata a lalace.
Muna isa gida Dada ta hau tambayar makusidin kukanta.
Kai tsaye na shiga rattaba mata dalilin.
Ta yi tsaki ta ce "Kare ya cinye miki zuciya Nasiba. Ina ce jiya a gabana ya tsaya yana miki kashedi akan ki sakar masa kurwarsa?
Bakaken maganganun da ya cusa miki, ai masu cizo ne da kina da hankali.
Domin bai ji kunyar idona ba ya ce miki komin k'wadayin ki shi yafi k'arfin ko dandana shi ki yi, bare kuma ki mallake shi a matsayin miji.
Amma dan lalace wa har ki zauna kina kuka dan kin gan shi da wata? Bayan Allah ya baki mai son ki, nutsatssatse ba irinsa ba. Bayan hakan kuma mai abun hannune ta ko ina ya yiwa mai sunan manya fintikau. Ban da ma darajar jini me zai sa ki so shi haka?
Ko an yi auren ma wahala zaki sha tunda ba sonki yake ba, ga kuma talauci da takaicinsa."
Jikina ya sake mutuwa ina ayyana duk soyayyar da take tsakanin Dada da Bulkachuwa amma take iya fa'din hakan a kansa saboda Nasiba?
To wai wa take so ke nan a tsakaninsu?
Take na yanke hukuncin Nasiba take so.
Na tsinci kaina da jin haushin yadda bai san ciwon kansa ba.
Kullum a fa'din ya daina mugayen dabi'aunsa yake, ashe ba hakan ba ne.
Ina tsaye tamkar gun ki aka fara kiraye kiraye sallar maghariba.
Murya a dashe na ce "sai anjima Dada".
Na tafi na barta tana ta kumfar baki da dan mulmulallen bakinta.
Muna idar da sallar na kalli Gwaggo na hau rattaba mata bayani.
Ina fa'din "Gwaggo ashe har yau Bulkachuwa yana yin iskanci?
Dazun na gan shi da wata sun fito daga kongo".
Ba zato na ji ta gwabe mini baki. Tare da cewa "A ina kika san iskancin?
A ina kika ga yana iskancin?
Kinsan girman al'amarin da kike fadi kuwa?.
Dan sun fito daga kongo shike nan sai ki yi shaidar zurr?
Annabi ya tsananta jan kunnenmu akan shaidar zurr.
Kinsan matakan da sharia ta gindaya kafin a zartar da ce wa mutum ya yi zina?
Sai an ga mutum turmi da tabarya, kuma daga bakin muminai da aka gasgatasu har guda hudu.
Ba dan komai ba saboda kiyaye nasaba da mutunci.
Amma mutanan yau sun manta wasiyyar ma'aiki a kan kazafi da shaidar zurr. Ki kiyayi yada sharri Yabi."
Na kasa ce wa komai a dalilin ba k'aramin azaba na ji ba, domin da k'arfi ta bugi bakin nawa.
Ta zarce da fa'din " Àllah ka shiryi duk wanda ya kauce hanya, Allah ka shirya zuri'ar al'ummar Annabinka. Allah ka shirya Tijjani, ka bashi sana'a, ka tsare shi, ka mayar da shi nagartacce".
Na amsa ameen a zuciyata, ina alkalancin maganganun Dada da na Gwaggo akan Bulkachuwa.
Shike nan sai na kame bakina ban yarda na sake fa'din wannan maganar ga wani ba.
A hakan har aka shafe sati dai-dai lokacin saura sati biyu aurenmu.
An kawo lefen Nasiba.
Lefe kuwa mai kyau, komai sai son barka, domin komin kushen mai kushe na zai kushe kayan ba.
Amma gare ta babu wata murna. Dan ko dazun nan sai da na ga tana wanke wa Bulkachuwa kayansa.
Ba kuma sata ya yi ba. Ajiye wa ya yi a inda ake wankin ita kuma ta jika ta wanke tare da na Dada.
Kwanaki biyu a tsakani aka kawo lefena.
Sun yi kokari kwarai da gaske domin duk ha'duwar kayan Nasiba, nawa sun zarta nata da ka'dan.
Amma abin mamaki ahalin gidanmu basu zuzuta kayana kamar yadda aka yi ta kuranta na Nasiba ba.
A lokacin kuma Dada da y'ay'anta kullum sai sun zauna, Babanmu ne kawai ba'a sa shi a cikin zaman sai Baba ta Bulkachuwa ita kuwa ba a garin take ba.
Saura kwanaki goma sha biyar auren Dada ta zaunar da Babanmu.
Bamu san me ta ce masa ba, amma dai mun ga ya shiga cikin rashin sukuni har washagari.
Ashe ce wa ta yi auren Yabi da Nuru ba zai yiwu ba matu'kar tana da iko akansa.
Ya nemi sanin ba'asi ta ce ya saurare ta zuwa jibi.
Bai sanar da kowa ba, har sai ranar da ta ambata.
Dukkansu suna zaune a dakinta.
Cikin rashin damuwar komai ta ce "Alhaji! Yanzu ya kyautu ace an bar mai sunan manya yana gararanbar neman aure ana hana shi, alhalin akwai yara a gabanku?
Kullum da abin nake kwana, nake tashi, tare da zullumin kar'bar da zaka yiwa al'amarin.
Sai kuma na tuna ikon da shari'a ta bawa uwa ".
A sanyaye ya ce "Hakane".
To maganar auren Yabi da wannan ba'kin yaron ba shirayayya ba ce daga Allah.
Domin mai sunan manya za'a bawa ita."
Wani irin zullumi ya shige shi.
Murya a raunane ya ce "Dada ina ce Nasiba yake so?"
Nan da nan ta ce "Nasiba ai ubanta ne ya yi iko a kanta ya ce dan k'aninsa zai bawa."
Ya ce "Dada ina ro'kon arziki a ba shi wata cikin yaran Badamasi ko na Iliya tunda an riga an karbi komai na aurent a, akwai nauyi mai yawa a tsakaninmu da uban yaron nan ke ma shaida ce".
Ta kai kallon ta ga Baban Tsakiya ta ga ya murtuke fuska.
Nan da nan ta ce "Duk abin da yake tsakaninku da Tanimu ya kai da yar'uwar ka ne?"
Da sauri ya ce "Ba kai ba Dada! Sai dai haramun ne neman aure a cikin aure."
Baban kasuwa ya ce " Ai ba bisa son zuciya ba ne, biyayya ka yi, Allah kuma zai karrramaka tunda ka bi uwa. Idan ya so sai a bawa Nura Kaltume ba shike nan ba."
Baban Marina ya kalli kaninsa da wani irin duba.
Yana mamakin son zuciya irin tasa. Ya dauki y'arsa ya bawa Jabir yasan kuma saurayin Yabi ne. Yanzu kuma a kan idonsa yake fadin zai sake bawa Nura y'arsa tunda yasan akwai mamora a tare da yaron.
A hankali ya ce "To ko zaka lamince na bawa Tijjani Kaltumen kawai?"
Nan da nan ya ce "Ina! Ai ba ita Dada ta umarta ba, so ka ke na shiga fishin uwa?"
"Shike nan Allah ya amsa addu'ar ka, Allah ya sanya albarka a cikin wannan ha'din , ya amintar da lamarin. Na bawa Tijjani Yabi, da dukkan zuciyata"!
Baban Marina ya fa'da cikin wani irin yanayi mai ban tausayi.
Dada ta ce "Allah ya yi albarka".
Har ya yunkura zai tashi sai ya ce "Zan bawa shi Nuran kanwarta. Komai da suka kawo da sunan Yabi ya koma kan Ubaida".
Ya fita yana ha'da hanya.
A zaure suka yi kicibus da Bulkachuwa.
Baban Marina ya kalle shi cikin wani irin yanayi.
Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Dubi gashin kanka, kamar ba bahaushe ba, ka dubi wando jikinka, tamkar babu iyayenka a gidan, yaushe zaka zama cikakken mai kamala ne?"
Ya sunkuyar da kai ya ce "Za'a gyara Baba"
Domin kuwa da dukkan zuciyarsa yake ganin kimar Baban Marina fiye da su Baban Tsakiya.
A dakin Dada kuwa Baban Kasuwa ya dinga fa'din"Dada ai da kin ce a ba shi Kaltume kawai, ina ce ta fi Ubaidan a haife?"
A dan tsorace ta ce "Ga ni na yi zan takura da yawa, sannan dole hankalin mutane zai dawo kanmu".
Ba shakka ya ce "To ya dawo mana! Idan ka daka ta mutane ai ko sallah ba zaka yi ba, domin kana yi suna kallon ka, ba dan su gyara maka ba, sai dan su gano na'kasunka su yi zundenka
Bare kuma akan wani al'amarin duniya da bai zame komai a juya maka manufarka kyakkawa zuwa mummuna ba."
A sanyaye Dada ta ce "Hakane".
Suka tashi ba tare da sun so a bawa Nura Ubaida ba.
Washagari sassafe Baban Marina ya zaunar da matansa ya shaida musu juyin da aka sake yi, da kuma hukuncin da ya yanke akan yin madadi da Ubaida.
Daga Inna har Gwaggo abin bai musu da'di ba. Mussaman Gwaggo da take gani ita ce zata fi shiga cikin tashin hankali, domin matu'kar Yabi bata samu dacen aure ba, to komai ma zai kwace mata ne. Ga Ummi ita ma fama take a nata gidan.
Shike nan a hakan zasu kare ita da y'ay'anta?.
Shirun da suka yi gaba'daya shi ya sake sanyaya masa guiwa.
Ya ce "Kun yi mini zuru?"
Mama cikin walwala ta ce "To me zasu ce Alhaji? Y'ay'anka ne fa ka yi iko da su, sannan ba shawara ka nema ba, tunda an riga da an zartar to wace ce zata yi inkarin hukuncin Dada matu'kar tana son ka rabauta?".
Maganar Mama ita ta sanya wa Gwaggo k'warin guiwa domin ta sani so take ta ganta cikin rashin sukuni da tashin hankali.
Nan da nan ta ha'diye damuwarta, ta murmusa tare da ce wa"Allah ya sanya alheri da albarka, ina fatan Allah ya sa ace gara da aka yi".
Wata irin nutsuwa ta zo wa Baba domin dama uwar Yabi yake ji. Ya sani borin da Yabi zata yi ba zai yi tasiri ba tunda an yi sa'a ita din mai jin maganarsu ce mai kuma kishin kada su kunyata ne.
Ya dinga yaba mata tare da sanya mata albarka.
Ya juya ga amaryarsa Inna uwar Ubaida.
Ya ce "Ke kuma fa?"
Murya babu amo ta ce ", Allah ya sanya albarka".
Ya sake numfasa wa tare da cewa"Yadda kuka kwantar mini da hankali a lokacin da aka jefa ni cikin matsanancin hali, ina rokon Ubangiji ya kewaye y'ay'anku da farin ciki da kwanciyar hankali a wannan aure.
Allah ya sanya alheri mai yawa ya biyo baya. Allah ina rokon a azurtasu ta inda muka zata da
ta inda bamu zata ba".
Suka amsa da ameen cikin juriya. Amma Mama bata ce uffan ba.
Ha'din kai da ya samu daga wajen matansa ya taimaka kwarai wajen kwantar da hankalinsa.
Har dare muna namu yi, ban samu labarin komai ba. Sai dai na lura da rud'anin da Gwaggo take ciki, gaba'daya ta zama wata iri, ta yi zuruzuru.
Na tambaye ta ta ce mini gudawa take yi. Take na gasgata na tura Anas ya siyo mata filagil.
Da daddare bayan dare ya d'an fara tura wa Baba ya kiramu ni da Ubaida.
Na cika da mamakin ha'damu da ya yi.
Muna durkushe a gabansa, shi kuma yana kan kujerar ba'kin karfe irin ta da, da take dakinsa.
Ya kalle ni ya ce "ku zauna sosai. Ina bu'katar hankalinku da nutsuwarku".
"Muka nutsu kuwa, amma gaba'daya zuciyata ta shiga rud'ani sosai.
"Shi da kansa ya jima bai iya yin maganar ba. Ya jima yana juya maganar yana tunanin ta yadda zai iya fa'dawa Yabi a karo na biyu za'a bawa wata saurayinta. Babban damuwarsa irin yadda ya ga ta sanya Nura a ranta.
Ransa ya baci fiye da jiya. Ba'kin cikin y'anuwansa ya mamaye shi. Wai me ya tsare musu a wannan duniyar ne?
Da k'yar ya yi k'arfin halin cewa "Yabi kinsan ce wa a duniya ba wanda zai so ki, ya so cigaban ki irin ni da gyatumarki ko?"
Ba haufi na ce " "Eh Baba".
Ya ce "Madallah! Sannan kuma ba wani abin kaico da zai dunfaro d'a mahaifi ya zuba ido ya cimmasa, sai idan abin ya gagare shi.
Ina son ki fahimce ni, ki mini adalci, ki kuma ninka biyayyar da zaki mini a wannan karon.".
Jikina ya fara tsuma, zuciyata ta shiga zullumi, idanuwa suka cika da ruwa.
Na kasa bu'de baki na ce komai dan tsananin bugun da zuciyata take yi.
Ya numfasa sosai ya ce "Ina son na fa'da miki auren ki da Nura ba zai yiwu ba, ba kuma na son ki kalli hakan a matsayin shirina ko shirin wani, ki yarda shirin Allah ne, shi kuwa idan Ubangiji ya jarrabe ka, ka yi ha'kuri a farkon al'amarin kana da lada da sakamako mai girma".
Take ruwan da ya cika a gurbin idona ya tumbatsa ya fara zuba.
Ina jin nauyin da zuciyata ta yi ba zai kwatantu ba.
Wacce irin Bak'ar kaddara ce nake gudu take bina da gudu shigen na fanfalaki?
Na kasa bu'de baki na ce uffan domin sai na fara hasashen mafarkin da nake yawan yi ne akan aurena da Nura zai iya ruguje wa.
Jin shiruna ya sanya ya ce "Na sani kina sona, son da yake sanya ki son duk abin dana haifa, ko nake so.
Ina ro'ko ki taimake ni, na yiwa mahaifiyata biyayya, ni kuma zan dauwama ina miki addu'ar wanye wa lafiya da kuma rufin asirin duniya."
Cikin rishin kuka na ce "To Babanmu".
Ganin irin rudin data shiga sai wata dabara ta zo masa.
Sai ya ce "Babanku Iliya ya bu'kaci na bawa Nura Kaltume a madadinki".
Na d'ago a matu'kar birkice na ce "Wai me na yi muku ne Baba?
Yan'uwanka suna azabtar da ni, kai kuma ka zuba ido kana kallo, ka kasa kare mini darajata! Ko dai da gaske karayar arzikinka tana damfare da zuwana duniyar nan mai cike da ba'kin ciki mai tsanani?"
Na fa'da ina kuka sosai.
*Auzubillahi! Na yafe miki Yabi! Na sani kina cikin ki'dima ne, ni kaina da na haife ki kiris ya rage ban zautu ba a dalilin wannan al'amarin.
Allah ka sassauta, Allah ka kawo mafita. Allah kada ka jarribi Yabi da jarrabawar da zata bijire mini. Bare ta haifi wanda zai bijire mata."
Na yi kasa da kaina ina kuka kasa kasa.
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
Tsawon lokaci kafin na ce "Na ha'kura da shi Baba. Amma Wallahi indai aka ba shi Kaltume to zan roki Ubangiji ya matso mini da ajalina kusa, domin na sani bazan sake farin ciki ba.
Indai kunyar Babansa kake ji, to ka bashi Ubaida tunda dama saboda kai ya turo d'ansa ya neme ni, ka bashi ita, zai fi mini sauki a maimakon ka rasa suruki nagari irinsa".
Ina rufe baki kawai Babanmu ya fara hawayen da ya daskarar damu.
Wanda na tabbatar na zallar ba'kin ciki da kuma farin cikin yadda nake tsananin son y'anuwana.
Ai ko murya na rawa ya ce "Irin yadda kike son yan'uwanki haka nake son nawa, amma shaidan da son zuciya sun shiga cikin al'amarinmu sun yi kane kane."
Ya daga kai ya ce "Allah kada ka jarrabi ya'yana da rugujewar zumunta".
Jikinmu ya sake yin mugun sanyi ya ce "Ubaida kin ji me yayarki ta ce shin zaki bi bayanta wajen sadaukar da burinki, ki mini biyayyar da ke ma zan dauwama ina yi miki farar addu'a?"
A sanyaye ta ce "Zan yi Baba! Na amince, da ikon Ubangiji ba zan kunyataku ba, komai zan zama kuma a duniya a sanadin auren nan, na sani arzikin Adda Yabi na ci, ba kuma zan juya wa al'amarinta baya ba".
Zan yi zumunci da ita a cikin ko wanne hali da rayuwa zata wullamu".
Daga hakan kuma ta fashe da kuka sosai.
Wanda ita kanta bata san dalilinsa ba, amma dai tana jin na tausayin Yabi ne.
Da ya rasa yadda zai fadi Tijjani ne mijin da aka zaba mata sai ya ce "Yabi ki tsananta addu'ar shiriya ga Tijjani! Ki kuma rage tsananta al'amarinsa ta yadda zaki fahimce shi da kyau, Annabi ya ce "Addu'ar miji akan matarsa karbabbiya ce, haka addu'ar mata akan mijinta karbabbiya ce.
Dan haka ki tsananta yi masa addu'ar shiriya, da kuma a cika kirjjnsa da soyayyar ki da tausayin ki, sannan a buda masa kofofin arziki"
A ki'dime na ce "Baba dan Allah warware mini wannan curarren bayanin, d'an yi mini gwari gwari".
Da matu'kar rauni ya ce "Tijjani zan aura wa ke".
Ai kuwa na dage na zunduma ihu ina birgima, ina fa'din "Wayyo Allah mutuwar tsaye ta samu Yabi! Wayyo Allah nakasa ta zo mini. Yabi zata zama iyalin mai *BAK'AR TA'ADAH*
*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin *Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
Da dukkan k'arfina nake ihu, domin na tabbatar an zartar mini da wananan hukuncin ne dan na tabbata a cikin garari, a kuma jefa mahaifana cikin ba'kin ciki mai dagargaza lafiyar d'an adam.
Babu zato na ji saukar duka ta ko ina a jikina.
Da k'yar Baba ya k'wace ni a hannun Gwaggo yana fa'din "Akan idona zaki dake ta?
Ai abin sai ya yi mata yawa ga mari ga tsinka jaka!"
Da rawar murya ta ce "A wannan daren da ko allura ce ta fa'di za'a iya ji ne zata yi ta mana kururuwa?
Ba ga k'anwarta nan Ubaida ba, da aka zartar mata da hukuncin aure babu zato, bata yi hakan ba sai ita?"
Ya girgiza kai ya ce "Tana cikin rud'ani, rarrashinmu take bu'kata ba fishi da juya baya ba.
Baba ya ri'ke ni a jikinsa yana ce wa "Yi tafiyarki ki bar ni da su ai ban kira ki ba".
Haka kuwa ta fita, ba tare da ta sake ce wa komai ba.
Ya ce "Uwarki mai biyayya ce, mai ha'kuri ce, daure ki gaje ta, da sannu Ubangiji zai yi muku tukuicin alheri.
Allah baya kunya ta masu ha'kuri duk lalace war zamani".
Ya dinga rarrashi da ban baki har ya samo kaina na tsagaita kukan da nake yi mai gigitar wa.
Ubaida kuwa ita ma taya ni kukan take yi.
Da kansa ya raka ni har dakin Gwaggo tare da jan kunnen ta kada ta sake ko murya ta d'aga mini.
Sannan ya raka Ubaida yana ta faman sanya mana albarka.
Wannan dare ni dai duk yadda ake fadin barci barawo ne bai iya sace ni ba.
Kwana na yi ina kukan zuci da na ido.
Wata irin kiyayyar Bulkachuwa ta mamaye ni, har na ji ashe ma da ban washe shi ba.
Yanzu ne nake jin asalin k'insa da k'yamarsa.
Yadda na kwana ban runtsa ba hakan ma Gwaggo.
Sai dai ita kwana ta yi akan abin sallar ta.
Tana ta addu'ar idan wannan al'amarin daga gare shine, to ya amintar da mu akansa, ya kuma sanya alheri da albarka a zamantake war aurenmu, ya shirye shi, ya ha'da zuciyoyinmu, ya kuma saukar mana da arziki.
Idan kuma ba daga shi ba ne, to ya ruguza al'amarin cikin kwanciyar hankali.
Ba addu'ar da nake jin da'dinta irin idan tana fa'di "Allah ya ruguza al'amarin.
Domin har cikin zuciyata na tsani ta ce Idan alheri ne Allah ya tabbatar din nan.
Kwata kwata ba tsarina daya da shi ba, mun yi hannun riga, kyaunsa da farar fatarsa basa rud'ata.
Na tsani halaiyarsa, na tsani yadda nake ganinsa a kaca kaca.
Na tsani namiji fari sol ma gaba'daya.
Washagari duk yadda na so na ha'diye damuwata, kasa wa na yi. Sallah kawai na yi na sake kwanciya.
Ba'kin ciki har mak'oshina nake jin sa.
Na dinga jin wani irin azababben ciwo a kahon zuci.
Na hakaito yadda aka raba ni da Yaya J wanda ciwon hakan ba gushe wa ya yi a zuciyata ba.
Ubangiji ya ha'da ni da kwamishina nan ma aka ce bai cancanci a ba shi aure ba.
Allah ya sake kawo Nura an sake cewa a a.
Wanne irin zalunci da raini ne wannan?
Kuka na yi har idona suka kuje.
Farar fatar fuskata ta zama jawur. Idon sun yi luhu luhu.
Na zabge tamkar mai ciwon tsi da ha.
Kwanaki biyu ina cikin tsananin da ban yi zaton zai wuce a waje na ba.
Gaba'daya na takura kaina, na k'warzabi raina.
Har mafarki nake yi wai Bulkachuwa ya shafa mini S.
Ranar da Babanmu ya tara dukkan ya'yansa ya fa'da musu sauyin da aka yi.
Jikin kowa ya yi sanyi.
Mazan Cikinmu hankalinsu ya tashi da jin za'a ba ni Bulkachuwa.
Yayin da Nazira da Yaya Ummi suka fashe da kuka sosai.
Da k'yar Baba ya hakurkurtar da su yana fa'din da ikon Allah bazan wula'kanta ba.
Su Yaya Indo kuwa na kasa gane inda suka saka dosa. Gasu nan dai ba yabo babu fallasa.
Ba abin da Baba yake ta fa'da mana irin mu taimaki kanmu mu zauna da junanmu lafiya. Mu guji dabi'ar y'an ubanci babu ahalin da suke yin nasara a rayuwar nan alhalin suna da wanan *BAK'AR TA'ADAH*. Allah ne ya tsara namiji ya auri mace sama da guda, shi ya shirya ya haifi y'ay'a daga mata daban daban, ke nan ba laifi ba ne yin hakan. Akan me zamu k'i jininmu dan kawai an fito daga uwa daban daban.
Abin kaico sai yar'uwar ka da kuke uba dyaya ta yki fa'da maka sirrinta ko damuwar da take ciki, amma sai ta fa'da wa k'awar ta da basu had'a komai ta fuskar nasaba ba. Kuma abin ba'kinciki wannan k'awar sai ta fitar da zancen har ya iso kunnunwan wadanda ba kya fatan su ji."
Ya numfasa ya zarce da ce wa "Zaku daukaka ne idan na sama kun tsaya kun taimaki na kasanku, idan kun yi adalci a tsakanin kannenku shakikai da li-abbai, abin da zaku dinga kallo shine.
Gidanku daya, gadonku daya, haka nan nasabarku daya. Ba ruwanku da dauko matsalar iyayenku mata ku jefata cikin al'amarinku.
Ku manyan idan kuka jibanci al'amuran kannenku yau, gobe suma zasu jibanci naku lamuran da na y'ay'anku."
Ya yi shiru sannan ya numfasa ya ce "Mutuwa bata yi mana sallama, dan haka ya kamata mu zama cikin shiri da fa'din wasiyya ko da kuwa lafiyarmu kalau.
Zan nemi alfarmarku duk taku. Ko bayan raina ku yi ha'kuri da junanku, kada ku bar kananun cikinki da kawunansu, ku kuma ku bi manyanku, ku shawarce su. Ku zauna da yan'uwana lafiya, ku gaishe su. Ku mutuntasu.
Allah ya muku albarka, ya saukaka muku hanyar neman halal dinku. Allah ya daidaita muku al'amuranku gaba'daya. Allah ya jefa soyayyar junanku a zukatanku. Sannan dukkanku ku yawaita yiwa Yabi addu'a Allah ya juyar da auren ya zama alheri a gare mu baki daya, Allah ya amintar da mu akan abin da muke ta jin tsoronsa."
Hawaye ya k'wace masa, dukkanmu kowa ya fara kuka domin mun gane shi ma jarumta ce kawai da biyayya da kuma son yar'uwarsa ya sanya shi yin shahadar bawa Bulkachuwa aurena.
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
Zaman bai tashi ba sai da aka tattauna yadda za'a yi wa Ubaida siyayyar kayan daki.
Ni kam an gama da ni tunda ya siyi muhimmai ga kuma freezer da tv bango, da bilanda babba, Honarable ya aiko a bani, da kuma kayan abinci da dubu dari biyu a Baba.
Ya ce ba zai samu halartar daurin aure ba tafiya ta taso masa.
A sadda kayan suka zo ba k'aramin murna na yi ba, domin ba karamin haska mini gidan Nura zasu yi ba.
Amma a yanzu me zan yi da su?
Idan na tuna Bulkachuwa zan aura sai na ji zuciyata ta harba da k'arfin gaske.
Ni dai ban fahimci me suka tattauna ba, nasan dai ya ce "Dubu Darin biyun da Kwamishina ya bashi bai ta'ba ko sisi ba hidimar aurenmu zai yi.
Suka gama aka tashi. Nazira ta zauna da ni dakin Gwaggo tana taya ni jimami domin akai akai take d'auke hawayen idon ta cikin dabarar kada na ga ni na sake karaya.
A daren wannan ranar na Kwankwatsa mafarki wai gashi nan an yi auren amma na sake zama y'ar firit na zama y'ar mitsitsiya ciwon yunwa da na zamani ya kwamushe ni.
A gigice na tashi wani abin mamaki jikina a jike na tashi tabbacin zufar da na ga ni a mafarki ce ta jike ni a zahiri.
Na rasa inda zan tsoma raina. Na kasa tashi na yi sallah na nemi zabin Allah.
Kawai na fi yarda na gudu.
Zuciyata ta buga da na tuno shekarar da za'a aurar da Yaya Ummi ta gudu wajen dangin mahaifiyarmu, da kansu suka dawo da ita, tare da bawa Babanmu ha'kuri. Tsananin da Gwaggo ta fuskanta kuma ba mai sau'ki ba ne domin dukkan gidan ce wa aka yi ita ta zuga ta, ita ta ce ta gudu.
Duk da ina yarinya kankanuwa amma ina tuna irin kukan da Gwaggo ta yi, tare da cewa duk abin da ya shafi al'amarinmu kada wanda ya sake, ya tafi danginta mu nemi dangin ubanmu dan sune a hakku akan mu ba danginta ba.
Jikina ya mutu to ina zan tafi ke nan?
Na numfasa ina tunanin gurin wa zani a Lame?
Wanda suka mana saura a can duk matsayin y'ay'a suke a wajen Dada ke nan ba wanda zai tirsasa ta.
Wanda zasu tsaya mini dama su Baban Tsakiya ne to su kuwa ai babu dausayin imani a ransu. Na tabbatar ma sune suka kitsa wananan fitsarin fakon dan kawai sun tsane ni.
Take na tuno Baba ta Bulkachuwa ita ka'dai nake da tabbacin zata fahimce ni, ta taya ni kubuta daga wannan auren da gara babu da shi.
Duk da ita ma bata da wannan isar. Amma dai zan gwada zuwa na roke ta ta zo ta rokar mini Baban Marina ya fasa bani Tijjani ya bani ko waye ni kuma zan kar'ba na zauna lafiya.
Nan da nan na samu salama a raina, gari ya yi haske na fito na yi uzzirina yau har da shan koko dan kuwa na samu sukuni.
Gwaggo ta shiga wanka na janyo bankina na bu'de k'wadon na dauko dubu uku.
Na mayar na rufee.
Na saka kayana kala biyu a leda da undis da hijabi daya.
Na boye a sakaden gado.
Daga haka na yi kwnaciyata ina jin raina fes.
Ba zato Baba ya leko ya ce "Yabi yau ki shirya ki je gidan Nazira".
Na amsa da "To Babanmu na gode".
Ai kuwa da'di ya kama shi domin yadda na amsa ya ji alamun sassauci a raina.
Na fito sanye da doguwar riga tsadaddiya cikin ireir kayan kwamshina.
Na yiwa su Gwaggo sallama na tafi.
Na shiga wajen Dada dan na gaishe ta.
Da Bulkachuwa na tarar da ita, suna zaune akan baranda cikin wani irin yanayi na rashin dadi da alamu suka nuna sa'insa suke yi mai zafi a tsakaninsu.
Ganina ya sanya ya yi shiru. Sai kuma ya mik'e ya ce "Asiya Toro wai da gaske ne Nuran ma ba za'a bari ya aure ki ba?
Kuma da gaske Baban Marina ya sake yarda da wannan almarar?"
Na kafe shi da idona da ya ke a kumbure kuma jawur.
Na tabbatar bai san juyin wainar da aka yi mini ba.
Ganin shirun da na yi, ga alamun tashin hankali shinfide a fuskata.
Ya tabbatar masa da gaske an runguza maganar aurena da manemi na a karo na uku.
Ya lailayo ashariya ya danna ya ce "Tabdi jam ahalin wannan gidan ba zasu ga ma'aiki ba, ba zasu ga dai dai ba."
Dada ta ce "Mai sunan manya ka iya bakinka fa! Kada ka zo ka rasa yadda zaka yi da kalaman ka".
Ya sake sakin wata maganar tare da ce wa "Bani na fa'da ba Dada. Annabi ne ya ce "matu'kar mutumin kirki da aka yarda da addininsa ya zo neman aure a ba shi. Hana shi kuwa yana nufin faruwar al'amura marasa dad'i!
Tunda aka hana Kwamshina aure nasan sai bacin rai ya biyo baya.
Yanzu kuma Allah ya kawo wani nagartacce sai a sake hana wa?
Ni yanzu da nake nema ake hana ni ashe ba kwa jin ciwo?
Akan me zaki zuba ido ahalin gidan nan su zama marasa daddako? Me yasa ba kwa yiwa kowa wannan al'amarin sai Yabi? Me yasa ba kya tirsasa kowa a cikin ya'yanki sai Baban Marina?
Me yasa aka mayar da shi k'arami marar yanci alhalin shine kuma babba?
Ya daga hannunsa duka biyu ya ce "Allah ka bani ku'di masu yawa ko dan na yi daraja a idon mutanan yau.
Wai ace a gidanku ma idan baka da komai sai ka zama wula'kantacce?"
Dada ta fashe da kuka amma ba irin na kururuwa ba.
Tana tafa hannu tana fa'din "Duk gatan da nake yi maka, duk soyayyar da nake yi maka ashe kai baka sona, baka yaba mini?
Me yasa ka raina kawunan ka?
To sune suka bada shawarar ayi hakan dan cigaban ka. Su suna son ka, amma kai kana wula'kanta su, kana kallonsu a bai bai.
Nan da nan ya kalle ni, ya juya ya kalle ta.
Kamar zai yi shiru.
Sai kuma ya ce "Wallahi yau kam sai kin fito kin fa'da mini dalilin ki na fa'din hakan, da kuma dalilin ki na ce wa saboda cigabana ake rashin adalci a gidan nan".
Ta kyabe baki ta ce "Sai dai ka je ka samu iyayen ka. Amma ba zaka zage ni ba, sannan ka ce sai na yi maka yadda kake so."
Ya kalle ta cikin ido ya ce "Na yi rantsuwa fa Dada".
Ita ma ta ce "Wallahi ba zan fa'da ba, sai dai ka dauko bindiga ka bindige ni".
Ya kalle ni ya ce "Asiya Toro kina da masaniya akan wannan shaguben tsohuwar?"
Na galla masa harara tare da tsaki hawaye kuma na kwaranyo wa a dukkan idanuwana.
Jikinsa ya mutu, bala'in da yake cinsa ya yi sanyi.
Na kalli yadda yake sanye da riga cukurkude a wanke amma babu guga.
Kansa ya sha dying ya zama brown.
Ga gajeran wando duk a yayyage wai kuma a hakan mai tsada ne.
Raina ya sake baci ta ya ya zan yi alfahari da wannan bawan a matsayin miji kuma uban ya'yana?
Gashi dai da dukkan zuciyarsa yake taya ni ba'kin cikin yankar bayana da ake yi, amma hakan bai sa na ga farinsa ba.
A hankali na ce "Dada ina kwana?"
Ta amsa da lafiya k'alau Yabi".
Na juya na fice, ina ce wa"Sai anjima".
Ya biyo ni yana ce wa "Asiya Toro tsaya ki fahimtar da ni mana, mene ne yake faruwa? Na yi miki al'kawarin wannan karon zan tsaya miki?"
Na sake jan tsaki na ce "Ni da kaina ne zan tsaya wa kaina. Kai har yaushe ka taimaki kanka, bare ka tsaya wa wata?"
Ya hauro ya ce "Ina matu'kar tausayin halin da kike ciki, amma ke na lura sam, ba ki san mutunci ba, ba ki san mai nufin ki da alheri ba".
Na sake jan tsaki na ce "In dai alherin ta sanadin ka ne bana son sa har abada".
Ya yi sukuri ya ce "Asiya Toro me yake faruwa ne, me ya susuta ki hakan, ba mun riga mun shirya ba?"
A hanzarce na ce "A gidan uwar waye muka shirya din?"
Ba zato kuwa ya kawo mini k'arfaffan mari na goce, amma ya samu gefen kunnena .
Yana huci ya ce "Duk rashin kunyar ki kada ki sake gigin yi mini zagin wula'kanci. Idan ba haka ba na rantse sai na illata ki.
Har cikin zuciyata nake jin damuwar halin da kike ciki, ashe Allah ne yasan manufar jaki da bai ba shi k'aho ba.
Da Honarable din ma ya aure ki irin ku ne masu kunyar nuna ahalinsu saboda tsananin butulci da k'ifadi.
A zafafe na ce "Ka jima baka illata ni ba.
Idan ni butulci da k'ifadi kake mini hasashe, kai kuma ina da tabbacin jahilci na damun ka, sannan kai din bara gurbin k'oyi ne a cikin zuri'a."
Ya sake hassala ya dunfaro ni, ko gezau ban yi ba dan tsananin k'insa da yake cina.
Na bu'de murya na ce "Ban da k'aton jahili wanne kato ne zai dinga d'aga wa mace hannu?
Na dire maganar da tsaki da harara tamkar manyan idanuwana zasu fa'do.
Jikinsa ya yi laushi, idanuwansa suka kad'a, ransa ya baci fiye da farko.
Murya babu amo ya ce"Asiya Toro me ya same ki ne, me na yi miki kike son cin zarafina haka siddan?
Da kinsan yadda muka kwashe da Dada a akan ki, da baki mini ko kallon banza ba, ina jin ki tamkar mun fito ciki guda ne".
Da yake akan tsinin kiyayyar auren sa nake sai ban ji kalaman nasa sun yi tasiri ba.
Na sake watsa masa kallon raini na ce "Ina ma cikinmu guda Tijjani? Ka ga da na kubuta daga bala'in hada ni aure da kai".
Nan da nan na ga ya kad'u. Tsawon sakanni ya zama tamkar mutum mutumi.
Ganin hakan da ya yi, ga shi ya kafe ni da ido babu kifta wa.
Ni kuma na yi tafiyata na bar shi cikin tu'ajjibi mai girma.
Ina tafe, Ina kuka har na isa gidan Nazira.
Ganina ina kuka bai sa ta tambayi dalilin zubar hawayen da nake yi ba.
Sai ita ma ta bar komai ta zauna tana kallon yadda na ke yin kuka mai hade da ajiyar zuciya.
Ina yi ina kallon yadda gaba'daya ta susu ce, alamun kukan zuci take yi da yafi nawa ciwo.
Tsawon lokaci muna haka.
Har mijinta ya fito ya same mu a hakan.
Ya zauna yana fuskanta ta.
Ya ce "Asiya na ji duk abin da yake wakana. Abin da nake so ki fahimta daya ne.
Ki fahimci duk wanda ya girmama sha'anin iyaye ba zai wula'kanta ba.
Duk wanda ya yi damarar yin aure saboda Allah, Ubangiji da kansa ne ya yi al'kawarin taimakon wannan bawan. Ki yi ha'kuri Asiya"
Ya yi shiru alamun alhini a dalilin kukan nawa ya sake tsananta, domin har cikin zuciyata nake tsananin ba'kin cikin a ce mini na yi ha'kuri na karbi Tijjani a matsayin mijin aurena.
Ya yi huci ya ce "Ki daure ki karbi auren nan saboda Allah, da kuma biyayyar aure ki ga yadda Ubangiji zai kawo miki dauki.
Annabi ya ce "idan mutum ya shiryu ta sanadinka yafi a baka daular duniya.
Tijjani mutumina ne, idan har an fahimce shi, an mutunta shi. Wallahi mutumin kirki ne, abu ne mai sau'ki ki sauya shi zuwa yadda kike so. Inda zaku samu matsala ki nuna bai isa ba. To anan ne zaki ga isar sa."
Na yi shiru, amma hawaye bai yanke mini ba, ina jin tamkar na ha'diye zuciya na mutu na huta.
Ta Yaya ban kasance fankashaliya ba, amma a dauke ni a bawa wanda ya saba cud'anya da mata daban daban?.
Ni ba rasa manema na yi ba, ba abin da yake d'aga mini hankali irin a gaban kowa, har a gaban Dada. Baba Maryo ta ce "Ba zata yarda a ba shi Nasiba ba. Duk yadda Dada take sonsa kuma bata matsa a ba shi ita a dole ba.
Sai kuma yanzun zata ce a ba shi ni?
Akan wanne dalilin?
Bansan a fili na yi maganar ba, sai da na ji Nazira ta ce "Saboda ke ba jikarta da y'arta mace ta haifa ba ne.
Saboda kuma ubanmu ba shi da abin duniya shi yasa zata tirsasa shi ko da baya so".
Mijinta ya kalle ta ya ce "Assha! Wacce irin magana kike yi haka ne? Maimakon ki rarrashe ta, ki k'arfafa mata guiwa ki kwantar da hankalinta sai ki sake jefa mata wasi-wasi?"
Cikin fishi mai yawa ta ce "Abin ne akwai tozarci a ciki".
Ya murmusa ya ce "Dukkan ku yara ne ba zaku fahimci muhimmimancin ha'kuri mussaman a fuskar zumunta ba sai a gaba.
Ba zaku gane tagomashin da mai biyayya yake samu ba sai a gaba.
Da ikon Allah watarana zata zo da Asiya zata ce Madallah da auren Tijjini indai ta sa Allah a gaban ta".
Ai kuwa yana rufe baki na takarkare na dinga zunduma ihu, ina fa'din "Ba zan ta'ba alfahari da shi ba, in sha Allah sai Ubangiji ya kawo mini sanadin da zan kubuta daga bala'in auren kazamin namiji kuma lalatacce".
Ya mike ya fita yana ce wa"Allah ya kawo mafita ta alheri Asiya! Ki yi ha'kuri, amma kada ki bari zuciya ta rinjaye ki, ki fa'da ba'kin ciki da ya zarta na auren Bulkachuwa".
Bayan ya fita da k'yar Nazira ta shawo kaina ta hilace ni muka ci abinci tare.
Muna sake tuna wariyar launin fatar da Dada ta dade tana nuna wa a tsakaninmu da jikokinta na wajen mata.
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*
Hatta shi kansa Bulkachuwa ya fimu sake wa a gidanmu.
Haka nan akan idonmu zata raba musu abu nasu ya fi namu yawa. Ko kuma ta ce su sammana a hannunmu, ko ta basu ku'di su siyo abin da suke so irin na yara, amma mu ta ce mu tafi wajen iyayenmu mata su bamu.
Da la'asar na bar gidan Nazira na wuce gudan Yaya Ummi.
Da tausayi take ce wa "ki yi ha'kuri, na sani an yi wannan ha'din ne dan bamu da galihu, so ake dole uwarmu ta tabbata a cikin ba'kin ciki, ban da hakan ya'yan wa ake yiwa irin wannan musgunawar?
Haka nima aka yi mini, ina da wanda yake sona amma a ka ha'da ni da wannan tsohon da babu rabon komai a gidansa sai na haihuwa".
Daga karshe ta hakurkurtar da zuciyarta ta ce "Tunda Babanmu ya roki alfarmar ki amince, to kawai ki yi hakuri. Da ikon Allah ba za ki wula'kanta ba."
Na bar gidanta, ba dan na gamsu da shawararta ba, na sani Tijjani mutuminta ne. Ban da haka me yasa zata ce na ha'kura? Dan haka na yanke hukuncin gobe zan bar garin, gara na shiga duniya komai zai same ni, zai fi mini sau'ki akan na auri marar nagarta, wanda ake yi wa kallon biri boko.
Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*Regular 500
Vip 1k via
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers*
*08089965176*
*07084653262*
Dukkan tunanin Bulkachuwa ya tsaya cak.
Tunda Yabi ta tafi ya kasa sukuni, sai ya koma da baya, cikin nutsuwa ya zauna kusa da Dada.
Ya sassauta murya ya ce "Na ro'ke ki, ki fahimtar da ni abin da ake shirya wa. Jiya na ga su Baba Shehu(k'anin mahaifinsa). Sun zo nan.
Tunanina bai bani komai ba, na yi zaton sun zo wuce wa ne suka tsaya dan su gaishe ki."
Ta ja tsaki ta share shi.
Ya sake lank'awasa harshe cikin ladabi, ya ce "Haba Dada ki yi hakuri mana, na ci alfarmar mai sunana".
Nan da nan kuwa ta ce "Kai din ne kayan kuttun ka yawa gare su. To aure suka zo nema maka, an kuma basu".
Ya dan zabura ya ce "wanne irin aure haka Dada? Wa na ce miki ina so da har zaki aika iyayena su zo, su nema mini?"
Cikin rashin damuwar yananyinsa ta ce "Na sani wacce aka baka din ba zaka yi watsi da ita ba, bata da mukusa, duk da dai guntu wa ce, amma jawur ce tamkar tsada, ga kyawuna ta samu domin kamarta nake sadda nake cikin k'uruciya ta".
Ya gintse ya ce "Dan Allah fahimtar da ni kawai".
Ta muskuta ta ce "Saboda soyayyar da kawunan ka suke yi maka suka yanke shawarar a baka Yabi, ni kuma na goya wa wannan kyakkawan kudirin nasu baya.
Dan haka ranar auren Nasiba za'a ha'da da naku, shi mane min nata kuma ubansu ya ba shi Ubaida".
Ya sandare a zaune. Tunani iri iri suka dinga zarya a tsakanin zuciyarsa zuwa kwanyarsa.
Ya sani ko da wasa bai ta'ba furta yana son Yabi ba.
Amma me yasa duk mutanan kirki da suka zo neman aurenta ba'a basu ba, me yasa sai shi? Alhalin babu kyakkawar alaka a tsakaninsu bare kuma alaka ta soyayya.
A karan kansa ya fahimci so ake kawai a kassara rayuwarta saboda ana ganin mai tsiwa ce, kuma ubanta ba shi da yadda zai yi.
Karon farko da takaicin kansa ya kama shi.
Ya tabbatar an yi wannan ha'din ne dan ta tabbata a garari da wahalar rayuwa.
Wani irin bacin rai ya ziyar ce shi, wato ana masa kallon lallatacce marar amfani.
Ya mike ya kalle ta cikin ido ya ce "Amma kuwa Dada zan yi rikicin da kowa zai gane an taba ni. Ban ce ina son ta ba, ba'a taba ganin kankanuwar alamar ina sonta ba, bare k'atuwa. Akan me za'a hana ta wadanda suka bayyana da nufin soyayyarta sai kuma ace za'a yi mana dole gaba'daya?"
Ta sassauta ta ce "Mai sunan manya kada ka k'wari kanka. Yabi bata da makusa, irinsu ne matan da ko shekaru hamsin suka yi jikinsu baya nuna wa. Kalle ni mana yadda jikina ya boye shekaruna da suka tura ainun. Baya ga hakan kai ne muke da yakinin zaka tankwara ta ka yi maganin shak'iyancinta. Muna cike da tsoron kada ta je a sako mana ita bayan ta gama karya darajar gidan nan, kai kuwa ai zaka yi hakuri da ita, kamar yadda zata ha'diye dukkan dabi'unka marasa kyau".
Ya sake tunzura ya ce "To idan na kasa jurewar na sako ta fa?"
Cike da rashin damuwa ta ce "Ai dai ka yanke mata budirci, ba za'a yi ta mata kallon an aurar da sa'aninta har an zo kan kannenta ba".
Ya jijjiga kai ya ce "Zan je na samu wadanda suka kitsa wannan ha'din, basu isa ba, akan me zasu yi iko da ni irin haka alhalin basu dauki dawainyata ta zame musu dole kamar yadda ta y'ay'ansu ta zame musu ba?
Baban kasuwa bai aurar da Jabir ba, sai da ya bashi fili ya tallafa masa ya gina gida.
Amma D'an Baban Marina a gidan haya yake, sannan nima ba wanda ya mini irin wannan taimakon sai kawai ace za'a bani aure, abin ciwon ma ba da kyakkawar manufa aka shirya ba. Ita suna mata kallon tantiriya fitananniya, sai suka ga ba wanda ya dace da ita sai dan-iskan da yake tumbele a gari saboda ya rasa mafad'a idan yaso ni da ita mu tabbata a cikin bala'i.
Me yasa Baban kasuwa ba zai bani Kaltume ba?
Me yasa ya dauki Maijidda ya bawa Jabir?
Me yasa Baban Tsakiya ba zai bani Saratu na aura ba?
Me yasa autarki ta hana ni Nasiba, amma dukkanku kuka zuba ido alhalin kunsan ita take sona nake son ta?"
Jikin Dada ya mutu k'warai da gaske.
Ta kasa kalubalantarsa. Tsawon lokaci ya ce "Na sani matu'kar Allah za'a duba baki da bakin magana. Dada ki yi kokarin gyara wannan matsalolin da suka dabaibaye ahalinki tun kina da sauran dama.
Kuma komai za'a yi bazan auri Yabi ba. Ita din y'a ce ba baiwa ba. Tana da damar ta kawo duk wanda take so a aura mata, ban ta'ba ganin wadanda ake yiwa auren dole a gidan nan ba, sai yaran Baban Marina. Suma ba dai yaran dakin Mama ba. Sai na Gwaggo, sai kuma na Inna da za'a fara daga kan Ubaida. Ita kuwa auren Nura ai tsintar dami ta yi a kala".
Ya numfasa sosai
Ya kaurara murya ya ce "Dada na fa'da mikii ki dakatar da wannan ha'din. Matu'kar a gidan nan za'a bani aure bana so, ba zai yiwu a hana ni wadda take sona fiye da komai ba, a kuma dauki wadda bata saka ni cikin mutane masu daraja a bani ba.
Bani da sana'ar da zan ri'ke Asiya Toro. Tun tasowar ta masu wadata suke zuwa neman auren ta akan me za'a hana su a ba ni, me nake da shi da zan burge ta Dada?"
Cikin rarrashi ta ce "Ita rayuwar gaba'daya tana tafiya ne akan *Lak'ad anan, laja'a anan, lak'as anam*. Aci, a rufe tsaraici, a kuma yi alheri, arziki na Allah ne mai sunan manya".
Duk rud'anin da yake ciki sai da ya yi dariya ya ce "wannan karatun kuma yaushe kika yi sabuwar k'awa makauniya?"
Ta tunzura ta ce "shekarar da nake goyon uwa ka".
Ya juya ya fice yana fa'din kome zaki ce, ina kan batuna".
Kai tsaye dakinsa da yake zaure ya shiga. Ya jangwabu kan katifarsa. Ya shiga zurfaffen tunani, zuciyarsa ta dinga hakaito masa Yabi. Tabbas bata da makusa, mai kyau ce, amma shi kuma yafi son mace mai manyan halittu. Yafi son wacce take tsananin sonsa, yafi son wacce idan ya yi mata mazurai zata shiga taitayinta. Amma ya sani Yabi ba zata ji tsoronsa ba, tunda ita ma k'walluwar kanta ce kuma bata sonsa.
Ya lumshe ido yana ganin ta cikin k'ahon zuciyarsa, bai san ya aka yi ba wani irin tausayinta da soyayyarta suka shige shi da wani irin k'arfi tamkar wadda aka yi masa turensu a lokaci guda.
Ya juya yana jin wani irin al'amarin da bai ta'ba jinsa akan ko wacce mace ba.
Cikin jarumta yake koka wa da abin da yake ji din, yafi son ya danne shi ya hana shi tasiri, baya son a ha'da kai da shi ayi zalunci, zunubin kansa ma ya ishe shi ba sai ya ha'da da zaluntar wata halittar ba.
Amma da yake ikon sarrafa zuciyarsa ba a hannunsa take ba. Ubangiji ne mai juya al'amura yadda ya so, ko da kai baka so ba.
A wannan kwanciyar da ya yi wata irin soyayyar Yabi ta yi masa d'auri fiye da daurin huhun goro.
Jikinsa ya mutu murus. Ido na lumshe sai ji yake ina ma, ina ma?
Ya sake tuno dan tsut din bakinta da ya iya rashin kunya da zaro bak'ar magana.
Ya saki gauron numfashi ya ce "Anan zamu yi ta samun sa'bani da ita matu'kar k'addara ta tabbatar da al'amarinmu. Domin ita marar kunya ce, ni kuma mai son girma ne, mai kuma k'iyayyar rainin wayo ne."
Sai ya tsinci kansa da fa'din "Allah idan da gare ka ne, ka tabbatar da wannan ha'din, ka sanya alheri da albarka, ka bani k'arfin zuciya. Idan kuwa rud'ani ne na shaidan Ubangiji ka sassauta mini wannan soyayyar da ta shiga dukkan zuciyata da gangar jikina, Allah ka ha'da kowa da rabonsa na alheri".
Ya mik'e da k'yar. Ya fita waje tafiya yake yi amma shi da kansa bai san inda za shi ba.
Ya sha kwana ke nan suka yi kicibus da Baban Marina.
Bai san ya aka yi ba sai ya ji kunyarsa ta rufar masa. Sannan bai so ya gan shi cikin wadannan kayan da kuma yadda kansa yake kuma babu hula.
Karon farko da Bulkachuwa ya ji nauyin a gan shi cikin wannan yanayin, domin shi a ganinsa ba wai ya saba wa sharia ba ne al'adar bahaushe ya bata wa, to shi bafulatani ne ba shi ke nan ba?
Dada ce dama take yawan yi masa fa'dan ya gyara, ita kuwa kai tsaye yake fa'da mata bai saba wa ka'ida ba ta bar shi ya yi yadda yake so. Sai kuwa Baban Marina da shi ma yake yawan yi masa nasiha. A gabansa zai nuna zai gyara, sai dai ba dan zai gyara din ba.
Amma a yau sai ya ji tamkar ya ruga da gudu dan tsananin kunyar da ya tsinci kansa a ciki.
Da walwala sosai Baban Marina ya amsa gaisuwar da yake yi masa.
Ya zarce da fa'din "Dama ina neman ka, mu je, idan babu inda zaka je".
Da nauyi sosai ya ce "Dada ce ta aike ni, amma da zarar na dawo zan zo Baba".
Baban ya k'ada kai ya ce "To hanzarta ka tafi, ka bari sai na dawo bayan isha sai ka zo".
"To Baba"
Bulkachuwa ya amsa da ladabi fiye da na kullum.
Ya tafi yana ayyana ashe surukuta gaskiya ce?
A da beken abokansa yake gani idan suna sun sun da kai idan sun ga iyayen matansu mussaman abokinsa Salisu yayansu Yabi.
Har da kansa ya ji yana mamakin kansa me yasa baya jin kunyar iyayen yan matansa, me yasa baya jin kunyar Baba Maryo uwar Nasiba?
Zuciyarsa ta harba domin ya gasgata su din ba sonsu yake yi ba sha'awa ce tunda ya sani shi din yana cikin jerin mazan da suke tsananin son kasance wa da mace.
Amma a yanzu ya fahimci son Yabi yake da dukkan na'kasunta domin shi yafi son cikakkun mata ba kwailaye ba, bugu da kari bai son mai tsiwa sannan kuma bai son auren zumunci.
Amma a yadda yake jin Yabi tana bin ilaihirin jikinsa da zuciyarsa tana sake yin kane kane a cikin ko wanne dakika ba zai iya tankwabar da al'amarinta ba. Duk da bata zo a yadda yake son ace ta zo masa ba.
Yana tafe yana murmushi a dalilin har ya fara hango ta dauke da cikinsa.
*
Har na iso gida ina tufka da warwara, ina ta tunanin inda zan tafi.
Gaba'daya tunanina ya tsaya a waje guda domin na fi gamsuwa na je wajen Baba ta Bulkachuwa.
Ana magariba na iso gida.
Da daddare duk ana zaune akan katuwar tabarma a dalilin d'an zafin da ake yi.
Baba ya gama cin tuwo yana jin radio.
Ni kad'ai ce a daki. Amma ina jin duk abin da suke yi. Kwatsam sai jin muryar Bulkachuwa aka yi yana kwada sallama. Bansan dalili ba, zuciyata ta harba da tsananin gaske.
Da sakakkiyar murya Baba da su Gwaggo suka amshe shi.
Ya gaishe su cikin nutsuwa ina hango shi sai da ya zauna sannan ya gaishesu sabanin da da yake gaida matan a tsaye kerere, kai duk gidan ma Baban Marina kawai yake dukawa har kasa, amma ko su Baban Tsakiya dan risinar da kai yake yi ka'dan.
Amma a yau hatta Inna ma sai da ya duka mata bare kuma ace Gwaggo ce da kanta.
Wani irin takaici ya shake ni wato dai a wannan duniyar samun mai kaifi daya ma'ana mai magana daya sai an tona sosai.
Daga dan ambata ha'di a tsakaninmu shine ya tattaro siffar mutanen kirki ya yaba a jikinsa?
Tamkar dai ba shine ya gama fa'din zai tsaya mini na auri wanda nake so tamkar ko wacce y'a ba?.
Na sake kad'uwa a dalilin kayan da suke jikinsa.
Wata farar shadda ce tar a wanke a goge. Ni da kaina duk adawar da nake da shi na sani shi din mai kyau ne, sannan halittarsa a cike take ga shi ingarma ne.
Ba k'aramin karbarsa shaddar nan ta yi ba. Ga kamala ya shinfida a dukkan jikinsa.
Matan gidan suka tashi suka basu guri.
Gwaggo bata shigo daki ba, sai ta nufi baya inda take tatar koko, ta kira Iklima tana taya ta.
Na sake kasa kunne na ji dalilin zuwan nasa da kuma wannan sauyin da ya yi farat daya.
Cikin nutsuwa Baban Marina ya ce "Na kira ka ne dan na fa'da maka jiya su Alhaji Shehu sun zo nema maka auren Yabi.
Na kuma basu babu jayayya, har na ji ban ji da'din yadda aka taso su suka zo cikin gidan nan wai nema maka aure ba".
Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*
Zuciyata ta sake tsinke wa, hawaye ya b'alle mini. Shi ke nan dai da gaske wancan kazamin halittar ne mijina".
Kuka ya nemi subuce mini da karfi.
Na yi maza na danne bakin da filo.
Ina cikin kukan sai jin Bulkachuwa cikin rawar murya da alamu suka nuna gaf yake da rushe wa da kuka.
Yana fa'din "Madallah da kai Baba! Kafin wannan lokacin ban ta'ba sanin ina da gata har hakan a wajen ka ba. Ban yi zaton zaka iya mini irin wannan sadaukarwar ba.
Ban san ce wa zaka iya rintse ido daga dukkan nakasuna ba sai yanzu.
Hakika na sani dole aka yi maka akan ka ba ni aure, na kuma yi imani zaka iya bacni aure ko da ba'a yi maka tilas ba.
Ina da yakinin idan ba wanda ya riga ni son Ubaida da zaka bani babu haufi. Ni da kaina da aka zabe ni aka ce a bani ita, na kad'u matu'ka da aniya Baba.
Da dukkan zuciyata na karbi auren nan, ban karba akan dole ba sai dan ina so.
Al'kawarin da zan yi maka daya ne, zan ri'ke ta irin rikon da uba zai yiwa y'arsa, zan kuma ri'ke ta irin rikon da miji nagari zai rike matarsa.
Zan sassauta mata, zan yi dukkan iyawata na hana ta zubar da hawaye a dalilin ba'kin cikina.
Ina maka al'kawarin komin nisan zamani sai Yabi ta ce Madallah da aurena In sha Allah".
Ban san ya aka yi ba, na fita a guje na tsaya kusa da shi, cikin kuka sosai na ce "Har abada ba zan yi alfahari da auren ka ba Tijjani! Cuta dai an gama cuta ta, da ikon Allah kuma duk mugayen da suka kitsa wannan ha'din sai sun ga tozarcin duniya."
Ashe har Baba ya tashi ya samo tsabga ban ankara ba.
Sai kawai ji na yi ya wancakalar da ni, na zube k'asa, sannan ya saka k'afa ya take ni sosai, ya shiga shaud'a mini tsabgar nan babu tausayi.
Na kuwa dage dukkan murya ina canyara ihu, tare da shure shuren neman tsira.
Bulkachuwa sai fa'di yake "Bar ta Baba! Yarinya ce. Yi hakuri, yi mini hukuncin a madadin ta.
Yayin da Mama da Inna suka tsaya cirko cirko, suna fa'din Alhaji yi hakuri mana, yi hakuri, Gwaggo kuwa ko kusa da wajen bata zo ba.
Ganin ba zai bar ni ba.
Ya sanya Bulkachuwa yin rumfa a kaina Baban Marina kuwa ya shiga labta masa babu sassauci.
Amma abin mamaki ko gezau bai yi ba.
Illah fa'di yake "Ka yafe mana, ka huce, ka gafarcemu Baba".
Duk yadda ya yi mini rumfa dan ya hana dukan Baba samu na, ban ji kamshi a tare da shi ba. Haka nan kuma ban ji yana hamami ba.
Sabanin Yaya J idan yana waje sai an gane saboda yadda kamshi ya kama komai nasa.
Sai da ya mana lilis sannan ya yar da bulalar yana cewa "Gobe idan ina magana da na gaba da ke ki zo ki saka mini baki.
Idan kuma an yi auren ki ha'diye zuciya ki mutu, ai kin sani sarai ina da irin ki, sama da bakwai. To mene ne zai dame ni, akan idona kike zagin y'anuwana da fatan tsiya a garesu?
Ki bi a sannu Yabi.
To ina cikin wad'anda suka kitsa maganar sai ki hada har da ni a muguwar addu'ar ta ki!
Sannan ki sani daga ranar da aka daura miki aure da Tijjani yafi kowa hakki akan ki har ni Uban ki.
Idan kin kwantar da hankalinki kin zauna lafiya, kin taimake shi, kin rufa masa asiri, kema da ikon Ubangiji Allah zai miki fiye da hakan.
Idan kuma kin tasa shi gaba da bala'i da cin mutunci da tashin hankali ke ma ba zaki samu kwanciyar hankali ba In sha Allahu"
Na sake rushe wa da kuka mai tsananin gaske.
A ki'dime Bulkachuwa ya yi maza ya rufe mini baki da hannunsa yana fa'din "Yi shiru Yabi kin ga Baban Marina baya son kuka irin wannan, kada ya sake cuda miki jiki".
Gaba'daya jikin kowa ya mutu ana tu'ajjibin irin soyayyata da aka ga ni a dukkan jikinsa da ayyukansa.
Gwaggo ta shige daki, yayin da Inna take fa'din "ki yi ha'kuri komai zai wuce kamar ba'a yi ba.
Mama kuwa ta wuce tana fa'din "Ikon Ubangiji! Wata'kila yanayin Tijjani ne ya sanyaya mata jiki.
Baban Marina kuwa ya ce ",Tashi ka tafi na sallame ka da alamun ka sullutun namiji ne kai".
Bai ce komai ba ya risina yana "Fa'din na gode sosai Baba Allah ya saka da alheri, ya shirya maka zuri'a. Allah ya hana ni kunyata a idon ka".
Baba bai amsa ba shi kuma ya tafi da sauri.
Bayan fitarsa Baba ya dinga yi mini fa'da tamkar harshensa zai tsinke.
Hakan ya sake rura wutar k'iyayyar Bulkachuwa a raina, domin a kansa mahaifina ya ta'ba duka na.
Na kwana ina juyi ina hawaye, yayin da Gwaggo ta kwana akan sallayarta, da ta fara gyangyadi zata zabura ta sake doro alwallah.
Na sani kuma ni take faman yiwa addu'ar zabin alheri.
Duk da ina cikin yanayin kunci, sai da kawata Rukayya ta fado mini da uwarsu ta rasu bara.
Ko waye zai musu addu'a irin wadda Gwaggo take yi mana?
Hawaye ya balle mini na tausayin Gwaggo da kuma duk wata macen da bata da uwa.
Hakika y'a mace bata ta'ba fita daga marairaicin rashin uwa duk girmanta kuwa.
Cikin Sa'a na doro alwallah na yi shimfida a gefenta, ba abin da nake roka irin Ubangiji ya yiwa Gwaggo alheri mai yawa a rayuwarta.
A fili nake fadin "Allah ka amsa addu'ar Gwaggo! Allah ka yarda da ita, ka bata aljannah.
Haka nake ta nanata wa, sai kuma na ce Allah ka jibanci al'amarin marayu, Ubangiji al'kawarinka baya tashi, Allah ka sanya farin-ciki a zuciyar duk wanda ya rasa uwa".
A karshe na ce "Allah ka yiwa Yabi zabin alheri".
Sai kuma na fashe da kuka sosai.
Kamar ba zata tanka mini ba, sai kuma ta ce "Ai kin gama magana, share hawayen ki tunda kin bar wa Allah ya yi miki za'bi.
Na ha'diye kukan amma nauyin kirjina bai sassauta mini ba.
Da safe na tashi da kuka. Baban Marina ko ta kaina bai bi ba, da k'yar ma ya amsa gaisuwar da na yi masa.
Hankalina ya sake tashi na dinga tsine wa Bulkachuwa domin dai a dalilinsa ubana ya yi fishi da ni irin wanda bai ta'ba yi mini ba.
Wato ko auren ma aka yi hakan zai dinga zuwa yana bata ni a wajensa?
Na diga kuka irin na sharbe.
Ai kuwa na shammace mutan gidan bayan Baba ya fita, nima na fice da ledar kayana da na zuba tun jiya.
Kai tsaye na yi bakin titi na shiga motar da zan sauka a Bulkachuwa.
Na isa da azahar.
Baba ta dinga marabta ta, cikin wata irin soyayya da farin ciki mai yawa.
Gaba'daya kaina ya kulle aka shafe mini ita ce ta haifi Tijjani.
Cikin kuka nake rattab'a mata halin da nake ciki tare da ro'kon ta je ta rokar mini Baban Marina ya canja mini Tijjani da ko wanne namiji, domin shi dan iska ne kuma k'azami, har mafarki na yi ya shafa mini s.
Ta yi sakare tana kallo na. Cikin sanyi jiki ta ce " Share hawayen ki, ki ji mai zan fa'da miki."
Cikin kuka sosai na ce "Ni dai bana son sa, ki ji tausayina duk dangin Babanmu ke na yarda zaki taimake ni. Ki ji k'aina ko daga haka kar ki sake taimakona a rayuwata, indai kika mini hanyar da na kubuce wa auren nan kin mini karshen zumunci".
Murya Babu amo ta ce "Ai kuwa zan yi dukkan iyawata na kubutar da ke, ba zai yiwu ki zabe ni, ki mutunta ni, ki taho wajena sannan na kasa yi miki adalci ba, sai idan abin ne yafi k'arfin azancina".
Tana rufe baki sai ganin Bulkachuwa na yi, ya fito daga cikin kicin dinta da yake falon.
Take na tuna dangantakarsa da Baba ta Bulkachuwa. Wani irin tashin hankali ya sake ziyarta ta. Kunya da ki'dima suka rifar mini, na rasa yadda inda zan tsoma raina.
Na kalle shi, na ga alamun damuwa a tare da shi, haka da na kalli Babar sai na ga ita ma tana cikin zullumi.
Kunyar yadda na zo gabanta ina fa'din bana son dan cikinta ta nemi zautar da ni, domin ban san ya aka yi ba na zabura na tsallake kwanukan abinci da na ruwa na yi waje a guje.
Ina jinta ta biyo ni tana fa'din Yabi! Yabi!".
Ina, ko takalmi ban saka ba.
Har na fita waje ina juyo ta tana k'walawa Nasir kanin Bulkachuwa k'ira tana fa'din zo ka taro mini ita, ka hanzarta mana, kada mota ta buge mini ita, a ki'dime take kuma ta nufi titi".
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN DA G.H.T. KAWAI KI TUNTUBE TA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
Jin hakan ya sanya na sake kwasa a guje sosai, duk karancin shekaruna na ji kunyar Babah irin wacce ban ta'ba jin ta akan kowanne mahaluki ba. Dan hakan nake sake azamar gudun dan na kubuta da sake tsaya wa a gabanta.
Amma da yake hanzarin mace da namiji ba d'aya bane.
Sai gashi ya cimma ni da taimakon k'anwarsa Ihisan suka mayar da ni har falonta duk yadda nake tirje wa ina kuka, ina fa'din su sake ni suka ajiye ni a gabanta.
Bayan Bulkachuwa a zafafe ya ce "Nasir sake ta."
Nan da nan kuwa ya sake ni.
Na zauna ina ha'da kaina da guiwa ina kuka sosai.
Babah ta ce "Jira ni mu tafi tare. Ai ba zai yiwu na bar ki ki tafi ke ka'dai ba.
Yi shirunki, tashi ki je ki yi wanka ki ji sanyi a ranki.
Da kaina zan mayar da ke, na kuma roki Yaya a fasa wannan ha'din."
Kunyar maganarta ta sake rufe ni. Na sake k'ara wa kukana sauti.
Da k'yar na mike na nufi dakinta da zan wuce na dan kalli Bulkachuwa da yake zaune a kujerar kusa da dakin yana shan abu a kofi, idanuwan sa sun k'ada amma ya maze tamkar baya wajen, ko kwakkwaran motsi yak'i yi.
Hakan da ya yi ya sake bata mini rai.
Ba dan komai ba saboda jiya ya kare ni a gaban mahaifina, sannan ya dinga rarrashina, har kowa ya zaci matsanancin sona ya kama shi farat daya.
Amma anan ya yi kamar ma bai sanni ba, ashe dama maza ma sun iya makirci?
Ko yaushe ma ya zo garin?
Na wuce ina cigaba da kuka rurus.
Da taimakon Ihisan na yi wanka. Na sauya zuwa doguwar rigar da na zo da ita a leda.
Sai da ta ga na nutsu sannan ta bar ni, ta tafi Islamiya.
Sa'armu ce, ni na girmeta da watanni biyar.
Da la'asar Babah ta leko ta ce mini zasu shiga barka da taaziya mak'wabta.
Yanzu zata dawo na fito falo, na yi kallo.
Nasir yana d'aya dakin yana guga.
Na sani kuma dan ya mata gadina ne ta zaunar da shi tare da saka shi gugar kayanta da na Ihisan.
Ina jin yana kunkunin shi ba zai goge na Ihisan ba.
Yayin da Babah ta rantse sai ya goge.
Shi bai ga irin hidimar da take yi ba?
Kullum ita take girkinsu ya d'ebo ya ci babu godiya.
Sannan ita ce mai gyara dakunanta da falo ya zo ya zauna har ya bata wajen.
Shin shi ba zai dinga ji tausayin mace bane?
Ta sake cewa "idan baka ji tausayin mace ba me zaka yi mata Nasir?
Allah da kansa ya ce mata raunin su mai yawa ne.
Ka koyi kyautata mata, da jin tausayinta, sai ka ga idan an baka amanar mace ta hanyar aurenta baka musguna mata ba, domin dama ka saba. Mene ne dan kana mata wanki da guga?"
Bulkachuwa da yake zaune a kusa da shi, bai ce k'ala ba.
Domin yana wahalar gaske ta kula shi.
Amma shi da kansa ya sani magana mai harshen damo take yi.
Ta fita tana fa'din "sai mun dawo".
Tare suka ha'da baki wurin fa'din "Ku dawo lafiya"
Nima a hankali na ce "A dawo lafiya".
A zahiri kallon nake yi. Amma gaba'daya tunanina yana gida. Ko ya suke ciki?
Zuciyata ta harba da wanne idon zan kalli Gwaggo?
Ya ya Babanmu zai kalle ni?
Na dinga jin nadama tana kama ni.
Hawaye ya dinga zuba tamkar ba kwana na yi ina yi ba.
Haka dazun ma na yi kuka tamkar idona zai kafe.
Ba zato na ga Bulkachuwa zaune a kujerar da take fuskantar wacce nake zaune.
Murya babu amo ya ce "ya kamata ki yi kuka fiye da haka Asiya Toro".
Wani malolon ba'kin ciki ya makure ni, na ji zafin fa'din Asiya Toro fiye da koyaushe.
Ya sake yin k'asa da murya ya ce "na raina wayon ki Asiya! Jiya akan idona Baban Marina ya zane ki har nima fishin ya shafe ni. Da zan d'aga miki rigata da kin ga yadda bayana ya farfashe saboda kare ki da na yi.
Na dauka wannan bacin ran da kika sanya shi ya isa ki kwantar da hankalin ki, ki saki ran ki, ki yi masa biyayya, a gefe kuma ki yi ta addu'ar kada Allah ya k'addara miki aurena idan babu alheri. Amma sai kika kwaso jiki kika gudo wajen yar'uwar sa, kin kuma san k'anwa ce a wajensa idan har da tarbiya ba zata je gabansa ta yi inkarin hukuncinsa, ko ta goya miki baya ki bijire masa ba.
Amma dan baki da mutunci ki zo har gabanta kina fa'din ba kya sona! Ke ba ki ji a ranki sai maganar ta bugeta ba? Ba ki ji furucin zai iya janyo wa ta washe ki ba?
Tunanin ki bai fa'da miki ita ta kawo ni wannan duniyar ba, ko kuwa tsabar wula'kanci da rainin wayon ki ne ya kai k'ure wa?"
Duk tsiwata sai na kasa tanka masa domin idan har gaskiya zan bi, to zahirin gaskiya yake furzar wa.
Hawayen takaici da ba'kin ciki suka ci gaba da tsere a kumatuna.
Ya zarce da fa'din "k'iyayyar da kike yi mini ta saka kin manta da neman zabin Allah, ke dai ba kya so na, ke dai a kubutar da ke aurena.
Abin mamakin ni namiji ban yi irin wannan asaranci ba sai ke mace?
Ko kin ta'ba ganin wata alama da take nufin ina son ki?
Amma saboda tausayin ki da nake ji, saboda kimar Baban Marina sai na ajiye komai, na amince da ke, nake kuma yi miki tanadin alheri da gata."
Cikin kuka na ce "ka ri'ke tanadin ka Tijjani.
Sanin baka son nawa ne ya girmama ba'kin cikin da nake ciki. Domin ba a ha'da ni da kai ba, sai dan ana nufin kassara ni.
Ina da masoya birjik, amma aka hana ni aurensu, ake neman lika mini kai, tun bamu je ko ina ba ka fara fa'din baka ta'ba sona ba."
Ya watsa mini lalataccen kallo ya ce "Ko ina son ki ai dole son zai zagwanye.
Me zan yi da wacce zata zo har d'akin uwata ta tozarta ta?
A akan idon ta, da kunnen ta kika ce zan shafa miki S? Ashe ke din kin kere tunanina da nake miki kallon yarinya kankanuwa. Kin ringa kin san komai.
Dan haka ki janye tunanin zan cigaba da yi miki sassauci!
Wallahi sai kin biya wannan rashin kunyar da kika yi mata. Ki rubuta ki ajiye, matu'kar kaddara ta zargemu a matsayin ma'aurata sai kin yi tuba akan wadannan kalaman naki na raini da iyashege. Da ikon Allah sai kin ji kunya da nadama idan kika tuna wannan ta'asar da kika yi."
Na cuna baki ina fa'din "Ba ruwan ka da shirgina, kuma bana son ka so ni, dan Allah kada ka sake yi mini sassauci Tijjani".
Ya jijjiga kai yana fa'din "Yanzu ba ni da lokacin ki, sai kin zama mata ta zaki ga rashin sassauci, kuma ki ga karshen rashin kunya".
Na ja tsaki mai tsananin gaske tare da cewa "Dutse a tsakanina da auren ka. Ban da mugunta ta ya ya za'a yi wannan ha'din, kana nan tamkar Basumade! To na yi ya ya da kai?"
Ya sake girgiza kai ya ce "Za ki ga yadda zaki yi din. Watarana har kuka zaki yi akan son Basumaden".
Bansan ya aka yi ba, na tattaro yawun bakina na watsa masa a fuskar sa.
Tare da fa'din "Aniya bi Aniya! Har abada ba zan ga wannan bak'ar ranar ba".
Ransa ya b'aci k'warai da gaske.
Ba zato ya d'auke ni da marin da ya shige ni tamkar na saki sayi a wajen tsabar ki'dima.
Na k'walla k'arar da ya sanya Nasir fito wa a guje yana cewa "Mene ne Yabi?"
Ganin yayansa a tsaye a wajen ya sanya ya kasa magana. Sai kallommu yake yi.
Cikin fishi ya nuna ni da yatsa yana ce app lwa "Tashi ki dauko ragga ko tissue ki share mini wannan k'azantar da kika watsa mini, ko na nada miki na jaki".
Cikin kuka sosai na ce "Bazan share ba, ka kashe ni k'arewar duka irin na jaki.
Kuma wannan marin Wallahi baka ci bulus ba. Dan na zo gidanku ba shine dalilin da zaka dinga dukana ba."
Na fa'da ina matsanancin kuka.
Takaici ya kama shi ya dunfaro ni, ganin yanayinsa ya sanya na kankame jikina ina kare fuskata da dukkan hannayena.
A hanzarce Nasir ya ce "Rabu da ita Yaya ba k'arfinku daya ba".
Bai tanka ba, ganin yana shirin damkata ya sanya na sake canyara ihu fiye da na farko tare da rufe idanuwana.
Ba zato na ji ya ja hijabin jikina yana goge yawun fuskarsa da shi.
Daidai lokacin Babah da abokiyar zamanta suka shigo a matu'kar birkice saboda ihuna da ya cika kunnuwansu tun daga waje.
Ganinsa a tsaye a kaina ga hijabina a hannunsa.
Ya sanya ta fusata, ta dinga zaginsa irin na tsamar nama.
Ya kasa cewa kala kanzil bare ya kare kansa.
Ta juya ta kalli Nasiru ta tambaye shi ba'asin ihuna.
A sanyaye ya ce "Rashin kunya ta yi masa ta tofa masa yawu a fuska shine ya mareta, ya ce ta goge masa, ita kuma ta k'i shine ya goge da hijabinta."
Cikin kuka sosai na ce "Allah ya hana hubbul ra'as Yaya Nasir. A Ina na yi masa rashin kunyar?
Ba shine ya zo ya same ni ina zaune yake ta yi mini sababin wai na yi miki rashin kunya ba. Kuma har yana kirarin idan an kai masa ni sai ya kusan kashe ni tunda na zo gabanki na ce bana sonsa.
Dan na ce "Ai ke din uwata ce shikenan ya rufe ni da duka, wai ta ina kika zama uwata?"
Na fa'da ina jan majina.
Ta juya kuwa tana masa ba'kin kallo ta ce "Ta zo ta fa'da mini din shasha da baya girma! Idan ka ji haushi ka gyara munanan ta'adodin da ake k'yamarka saboda su.
Sannan ita din y'a ta ce har a kiyama kuwa! Zuwan data yi wajena ba k'aramin kara mata daraja ya yi a idona ba.
Ta karrama ni, daga nan har k'asa ta rufe mini ido kuma zan yi ta karrama ta ina yiwa kuruciyarta adalci".
Umma kishiyarta ta ce "To daina yi masa zagin yara a idonta. Wannan ba sharia kike yi ta gaskiya ba. Bangaranci kawai kike yi".
Da takaici Babah ta ce "Ban da shasha ne yana ganin halin da take ciki, maimakon ya dinga rarrashi da hila har ya samu ta sauko a samu daidaito a tsakaninsu sai kuma ya tisata a gaba da cin zali da alwashin razanar wa iri iri?"
Na sake fasa kuka ina cewa "Babah dazu kin ce za'a fasa auren, yanzu kuma kin ce ya rarrashe ni?
Ni Wallahi ba zan karbi rarrashinsa ba.w
Ya cire hular sanyin da ya kifa a kansa ki ga yadda sumarsa take.
Sannan ya dauki wannan tafkeken hannun nasa ya mare ni, gaskiya ni dai ki rama mini kawai".
Umma ta mini dakuwa tana fa'din "ungo na ki, ja'irar yarinya, Tijjani za'a doka?"
Na kara fashe wa da kuka.
Yayin da shi kuma ya koma gefe ya sunkuyar da kai.
A yau ka'dai na fahimci nauyin juna, Babah suke ji ita da Tijjani.
Bata kula shi a dalilin shine d'an fari.
Shima kuma baya iya katabus idan tana wajen.
Wata irin nutsuwa yake yi a gabanta.
Wadda ni ban fahimci hakan ba sai yau.
Kafin wayewar gari na fahimci Babah irin iyaye ne da basa sakarwa yaransu fuskar da zasu rainasu .
Haka nan yaranta maza ma suna aikin gida ba sai iya mace ba.
Kullum cikin jaddada musu, idan basu saba da jin k'ai da tallafa wa mace tun yanzu ba, sai yaushe zasu fara?
A wannan zaman na gane ita ce ta mayar da Tijjani Toro dan lalacewarsa da zata fi muni a gabansu tunda ubansa baya son damuwarsa.
Wannan rashin fuskar da bata ba shi tun yana yaro ya sake yin tasiri a mua'amalarsu.
Sannan na fahimci ita din wata irin uwa ce da son y'ay'anta bai hana ta yi musu sahihiyar tarbiya ba.
Ma'ana bata ta'ba dora ra'ayinsu akan nata, dole sune zasu bi tsarinta ko da basa so kuwa.
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*MASU BUKATAR YON RIGISTA DA G.H.T. KAKARKU TA YANKUE SAKA DOMIN KUWA FASEELAT ZATA MUKU JAGORA HAR KU FAHIMCI KOMAI CIKIN KYAKKWAR MU'AMALA DA KYAUTATAWA*.
*07039269802*
Washagari sassafe muka dauki hanyar Toro.
Muna kusantar garin zullumin da nake ciki na sake tsananta.
Nadamar gudun da na yi, na yi ya fi sau dubu.
Kafatalin ahalin gidan Marina mu yaran Gwaggo ne muke guduwa idan za'a aurar da mu.
Duk da cewa mu ka'dai ake yiwa auren dole a gidan.
Na tuna daren shekaranjiya inda take fa'da mini tsananin da ta fuskanta a auren Yaya Ummi.
Komai sai ace ita ce ta saka ta.
Ta ro'ke ni na daure na kwantar da hankalina, domin tunda aka ambata aurena da shi bata sake kwanta ta yi barci mai nauyi ba.
Idan kuwa har addu'ar uwa tana tasiri akan ya'yanta ta tabbatar ba za'a juyar da addu'ar da take yi mini ba.
Na sake tuna rarrashin da Baban Marina yake yi mini a kullum, duk abin da zai yi dan ya sanya farin ciki a zuciyata shi yake yi mini a tsukun nan.
Amma shekaranjiya sai da ya zane ni dan ya tabbatar mini babu fashi akan al'amarin Bulkachuwa.
Amma washagari na saka kafa na fice na barsu.
Na kuma yi imani duk inda zan je ba zan sami daya bisa darin soyayyarsu ba.
Daga jiya zuwa yau Àllah ka'dai yasan ba'kin cikin da suke ciki, dan ma Babah ta yi hikimar skaa Bulkachuwa ya juya da yamma dan ya sanar da mutan Gidanmu ina wajen ta.
Tunda ta kasa fa'da musu ta waya.
Na dinga kuka ina shessheka. Ita kuma tana ta rarrashi da yi mini nasiha.
A motar na bata hakuri, na kuma roki alfarmar kada ta ce da Baban Marina komai, na ha'kura zan yi biyayya".
Ta dinga yi mini addu'a da fatan alheri a dukkan sha'anina.
Har muka iso Toro misalai iri iri ta dinga yi mini na irin aurena.
Da kuma dabarun ri'ke namiji a hannu. Har na dinga jin nauyi da kunyarta.
A k'ofar Dada muka fara sauka.
Ta amsa gaisuwar Babah, amma tawa gaisuwar ta share.
Kamar ba zata tanka ba sai kuma ta zabura ta ce "Mandiya hamshakiya! Wai ke tabbataciyar marar kunya, kuma marar kirki. Idon ki babu kunya ko ka'dan, har ke ce zaki tafi wajen Hauwa ki fa'da mata ba kya son auren mai sunan manya?
Da me kika fi shi?
Sanin kan ki ne ban da ya mayar da kansa abin da ya zama ba, da ke baki isa ko kallon ki ya yi da sunan soyayya ba."
Na zum'bura baki ainun na ce "To kawai a bar shi ya auri wacce take son sa ta kuma dace da shi din.
Ni ma a bar ni da masoyana".
Ta kawo mini duka da mafici, ban goce ba, domin na riga na kai makurar fusata da al'amarinta.
Ba dan idon Babah da take zaune ba, da na zage na fa'dawa Dada gaskiyar magana. Amma ido mashi ne, mussaman da yake muna cikin zamanin da inka cika fa'din gaskiya sai ya zama rashin kunya a idon manya.
Mun jima a wajen Dada sannan muka isa k'ofarmu.
Muka tarar da Baban Marina yana gida ya dawo cin abinci.
Da walwala ya marabci k'anwarsa yana fa'din "Lale da mutanan Bulkachuwa". Ta zauna kusa da shi cikin nutsuwa da murmushi sosai.
Ta gaishe shi a ladabce.
Ya amsa mata da sakakkiyar fuska.
Ina gefe a takure tamkar mujiya cikin tsuntsaye.
Na gaishe shi kaina a kasa.
Ya share tamkar yadda Dada ta yi mini.
Na sake yi a karo na biyu.
Ya sake dauke kai tare da daure fuska.
Nan da nan na fara kuka sosai, ina ba shi ha'kuri.
A dan tsorace Babah ta ce "Ka yi ha'kuri! Da kanta ta ce na rakota ta baka ha'kurin fitar da ta yi baka sani ba."
Ya girgiza kai ya ce "To mai gaisuwarta zata yi mini?
Me zata fa'da mini?
Na zuba mata ido ta yi duk abin da ta ga dama tunda ni ban isa da ita ba.
Sannan ni ba tafiyar da ta yi ba ne ya bak'anta raina ba, wajen ki da ta dosa ne ya b'ata mini. Akan me zata je wajen dangina tunda ni din da zata ci arzikina a wajen ki, ta nuna mini iyaka ta?
Ban da hauka da kuma idonta babu ruwa a ciki ta ya ya zata doshe ki?
A sanyaye Babah ta ce "Yaya dan Asiya ta zo waje na sai ya zama aibu?
Akan wannan yaron ne kake ganin rashin kunya ne ta zo waje na?
Ni bana raba tsakanin yarana da naka.
Sannan na gode mata ta zo wajevna, da wani wajen ta yi fa?"
Ya murmusa ya ce "Da kuwa da kanta za ta dawo domin ai duniya ta ishi kowa darasi, a lokacin da za ta dawo daga gudun ni kuma a lokacin zan guje ta da ni da dukkan ahalina".
Kukana ya tsananta domin a lafuzzan Babanmu na fahimci girman bacin ran da na sanya shi.
Ina kuka, ina bavshi hakuri tare da ce wa "Na yi kuskure Babanmu".
Ya yi shiru bai ce k'ala ba.
Babah ta ce "Ka huce! Ka yi mata afuwa dan girman Allah. Ta ci arzikin rakota da na yi."
Ya saki gauron numfashi ya ce "Na yi mata afuwa, amma bazan huce da ita ba, sai an yi auren ta kwantar da hankalinta, ta kwantar da hankalin mijinta. Yardata tana d'amfare da yardar mijinta akan sha'aninta.
Ban da ke Hauwa, da ko kallonta ba zan yi ba. Domin ai ga Ubaida nan k'anwarta ce ta sosai, bata son auren da zan yi mata amma ta ha'diye komai. Amma ita Yabi da yake ta isa, kuma uwarta bata k'wabarta ai kin ga d'anyen hukuncin da ta dauka na guduwa ta kai k'arata. Ban da k'arfin addu'ar da kullum nake yiwa iyalinmu ai da duniya ta yi niyyar shiga".
Babah ta dinga fa'din "Da Ikon Ubangiji ba zamu ga haka akan ahalinmu ba! A yi ha'kuri Allah ya shirya mana su.
Ta dinga godiya da addu'a, akan alheri mai yawa ya biyo bayan auren.
Sai kuma ta fashe da kuka wanda ni dai bansan na menene ba.
Na dai ji Baban Marina yana ce wa "Yo Hauwa ban da dai muna cikin wani irin zamani da dan-uwanka yake zama tamkar makiyinka menene abin godiya? Komai zan yi miki ai kaina na yiwa. Tijjani d'a ne ko yafi hakan lalacebwa idan duniya da adalci bai kamata mu din mu hana shi aure ba.
Tunda mune muke zuwa nemo masa auren y'ar wasu. Kebnan idan da adalci sai mu ba shi tamu.
Fatana dai ki tsananta yi masa addu'ar shiriya, bakinki yafi na kowa tasiri a kansa."
Tana goge hawayen idonta tana fa'din "Ina yi Yaya, zan cigaba da yi. Allah ya shirye shi, ya sanya wannan auren ya zame masa sanadin shiriya da albarka a rayuwarsa gaba'daya.
Yabi kuma Allah ya bata hakuri da juriya."
Ya kalle ni ya ce "Tashi ki bamu waje. Na mike sum sum Babu nauyi. Domin hakan da Babanmu ya yi mini ya tabbatar bai huce da ni ba.
Ina shiga d'akin Gwaggo na tarar da ita tamkar wacce take fama da tsi da ha. Gaba'daya ta rafke, gata fara ce amma ta yi wani irin baki sosai.
Na zauna na gaishe ta ta amsa ba tare da ta kalle ni ba.
Nan da nan kukan da nake yi ya dawo sabo.
A fusace ta ce "ki rufe mini baki tun baki tunzira ni, na yi miki mummuna baki ba. Ai hakan kike so
Shike nan ni kuma duk sadda aurenku ya zo a lokacin watan bakin-cikina ya kama.
Kin ji da'di da ubanku ya jingina guduwar ki da ce wa ni na saki.
Allah shine shaidata, ban isa da ke ba ne, domin da na isa ko k'ofar gida zaki je sai kin fa'da mini.
Amma saboda ki jefa ni cikin kunya da ba'kin ciki shine kika gudu! Har kin yi girman da zaki gudu ki bar iyayen ki saboda sun miki laifi?
Ta share hawaye ta ce "
Da nasan hakan zaki yi mini Wallahi da ban kawo haka a cikin gidanku ba. Da na dauke Ikilima tun shekarun baya na yi tafiyata na bar wannan k'addararren zaman".
Na dinga kuka ina bata hakuri, domin fishinta da kukanta yafi d'aga mini hankali fiye da fishin Babanmu.
Murya na rawa take fa'din "da yake ita Innarku ta iya haihuwa, ai ga shi nan Ubaida bata kunyata ta ba, bata janyo mata ba'kin jini a wajen Babanku ba".
Tsigar jikina ta tashi sosai. Na dinga ganin wautata.
Da muryar kuka na ce "Dan Allah ki yi ha'kuri Gwaggo! Kaina ne ya kulle ainun. Na shiga rud'u mai girma. Amma da ikon Ubangiji komai zai daidaita, zan iyakacin bakin kokarina na ga ban sake janyo miki bacin rai ba. Ki sake ninka addu'ar da kike yi mini. Kullum ina sake jin tsana da k'yamar Tijjani a zuciyata".
Kuka na sosai ya k'wace mini.
A wannan karon sai ta kasa ce wa komai illa ido da ta zuba mini sosai.
Wata'kila rauni ne irin na uwa, wata'kila kuma tausayi na bata sosai.
Ta aro jarumta ta ce "Sau tari alheri yana zuwa mana ta inda bama so. Sai ka k'i abu tare da hasashen bai cancanta ba, sai kuma ya zame maka alheri. Sai ka so abu tare da hasashen za'a dace sai kuma ya zame maka fitina.
Ina fatan komai zai dunfaromu Ubangiji ya juyar da shi zuwa alheri.
Tashi ki d'oro alwallah, ni na yi tun dazu".
*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers*
*08089965176*
*07084653262*
*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
Ina alwallah ina kuka. Ba abin da ya sake karya mini zuciya irin yadda na jiyo Baban Marina yana cewa Baba "Ni fa ki daina ro'ko na Hauwa! Tuni na yafe mata, amma walwalata ce ba zata ga ni ba, har sai ta kwantar da hankalinta an yi hidimar nan lafiya lafiya. Sannan kuma ta zauna lafiya da mijinta kamar yadda y'anuwanta suke zaune lafiya.
Ina ce Ummi gidan mai iyali aka kai ta? Ga kuma mijin ya d'orawa ransa masifar son abin duniya. Ba ya sauke hakkin da shari'a ta wajabta masa.
Duk k'uncin da take ciki yau shekaru kusan takwas da aurenta, bata ta'ba zuwa gabana da nufin wata matsala ko da zummar na taimake ta ba.
Na sani kuma tana bu'katar a taimake ta, amma da yake ta dauko ha'kurin uwarsu ta shanye komai tana zaune da y'ay'anta, sai kuma ta yi tabarar koyon sana'a cikin cire girman kai da buri.
Shiyasa ni kuma ban ta'ba yin sallah ban roka mata sassauci a wajen Ubangiji ba.
Duk kuma wanda Allah ya ba shi nisan kwana zai ga yadda Allah zai albarka ci zuri'arta. Allah sai ya yi mata tukuicin hakuri da biyayyar da ta yi da ikon Allah".
Da k'yar na tokara na tashi zuwa daki na tarar da Gwaggo tana share hawaye.
A sanyaye na ce "Gwaggo baki huce da ni ba ne?"
Ta girgiza kai sai kuma ta ce "Ina mamakin duk alherin da mace zata yiwa namiji na ha'kuri da juriya akan al'amarinsa ko na ahalinsa. Amma idan d'anta ya yi laifin da ita kanta bata sani ba sai ya shafeta.
Ko sai yaushe uwa zata kubuta daga irin wannan kalubalen a k'asar hausa?
Duk lalacewar uwa ba zata so d'anta ya zama marar tarbiya ba. Na sani akwai uwayen da basa son laifin ya'yansu, amma me yasa aka fi yiwa masu hakuri da kawaici raddi?
Yanzu duk laifinki a kaina ya k'are. Yana wahalar gaske Babanku ya yaba ha'kurin da nake yi a gabana sai dai a bayan idona. Shikenan ita mace ba za'a yabe ta a kurzanta ta ba?
Ba za'a yayata alherinta ba, amma kuskuren da ba ita ta yi shi ba ma sai an yi mata tuya a kai".
Ta fa'da hawaye na sake k'wace mata.
Na taya ta kukan da take yi domin na sani sanadin tafiyar da na yi ne.
Da rawar murya na ce "Ki k'ara hakuri Gwaggo! Idan kika yi sa'a Ubangiji ya yabi ha'kurinki shikenan kin gama dace wa."
Ta zuba mini ido sosai ta ce "Kema na hore ki, ki yi hakuri, ki yi juriya, ko bana raye shine tsanin da zaki ri'ke, ki tsallake dukkan k'alubale a wannan duniyar".
Jikina ya sake sanyi. Domin kalmar ko bata raye ta yi matu'kar dukana.
Na ha'diye kukan na tayar da sallah.
Sai dai hawaye bai yanke mini ba, na idar da sallar ina zaune ina lazimin Ya ladifu da fatan na samu sau'kin halin da nake ciki.
Washagari sassafe Babah ta koma Bulkachuwa.
Ala dole na ha'kura na zuba ido aka cigaba da shirin aure, wanda yake sake k'arantowa.
Duk da na ha'kura amma wata irin rama nake yi mai tayar da hakankalin masu kallona.
Na sake zama wata yar sumoli da ni.
Ba annuri a fuskata.
Na kasa yiwa jama'a kitso bare kuma lalle.
Idan ba k'ure wa ta yi ba yana wahalar gaske na yi magana. Na zama very silent.
Makarantar boko ma na daina zuwa duk da a shekarar k'arshe muke.
Kwatsam sai ga Yaya J ya dawo daga Bauchi.
Bai samu labarin aurena da Bulkachuwa ba sai a jiya.
A ki'dime ya iso gidan Marina. Ya gurfana gabana Dada yana fa'din "Dada wanne irin abu ne haka?
Ta ya ya za'a dauki Yabi a bawa Bulkachuwa! Saboda Allah Dada wannan daidai ne?
Me yasa aka hana shi Nasiba baki tsawatar ba?
Me yasa aka tirsasa ni na auri Maijidda?
Akan me ita kuma za'a yi mata hakan? Ciwon abin ba shi ya yana sonta ba.
Idan saboda kada na sameta ne kuka k'ulla wannan al'amarin, na sadaukar da soyayyar da nake yi mata, na janye, bazan sake furta sonta, ko a bani aurenta ba. Amma ki yiwa Àllah Dada kada ki kassara mata rayuwarta.
Waye bai san BAK'AK'EN TA'ADODIN da yake yi ba?
Ta ko ina basu dace da juna ba.
Yabi mai son sana'a ce, yayin da Tijjani bai damu da ya gina kansa ba, irin mazan da suke barwa mace hidimar da shari'a bata dora musu ba ne.
Tijjani manemin mata ne, yayin da Yabi ta kasance mai tsananin kishin gaske.
Tijjani fari ne, Yabi bak'i take so.
Tijjani mai zafi ne. Yabi mai tsiwa ce.
Ta ina zasu ji da'din zama?
Ta ina suka dace?"
Kafin Dada ta ce wani abu Bulkachuwa da yake tsaye a bakin k'ofar Dada ya ce "Bamu dace da juna ba Jabir. Sai dai ka sani Ubangiji ne yake jujjuya al'amura, yake kuma k'addara afkuwar komai ko da bamu tsara faruwarsa ba.
Maganganunka sun yi matu'kar ta'ba zuciyata. Tabbas gaskiya ka fa'da, duk da na ji na muzanta. Da a ce son Yabi bai yi mini kamun kazar kuku ba.
Dana tirje wa aurenta. Sai dai an jarrabe ni akan ta cikin kankanin lokaci."
Ya numfasa ya sake fa'din " Na gode da ka ankarar da ni, duk inda sana'ar da zan gina kaina take zan nemota zan kuma yi duk wahalar ta.
Laifin da ka jingina mini kuma na neman mata wannan kai da Allah! Domin baka ta'ba ganina na yi ba.
Allah ne shaidar na yi tuba, Allah ne shaidar tunda na yarda aka zartar da hukuncin da ya yi a kaina ban sake yi ba.
Amma kun rike abu kuna ta faman jifana da shi."
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
Ya fa'da cikin wani irin yanayi na bacin rai mai tsananin gaske.
Dada ta zuba masa ido cikin son ta nazarce shi.
Ta k'asa ha'diye abin da ta fahimta akan sa cikin dak'ik'a.
Ta nisa ta ce "Mai sunan manya, shin ka fa'da komar Yabi ne har haka?"
Takaicin ta ya k'ume shi.
Bata ce da Jabir komai ba, da yake faman sakin maganganun da suke nufin tozarci a gare shi.
Amma tana neman shiriritar da maganar. Bai ce mata k'ala ba ya juya tamkar ya tafi, sai kuma ya toge a jikin bishiyar zogalen da take gefen dakunan ka'dan. Cikin bacin rai na sosai.
Yayin da jikin Jabir ya yi sanyi domin ya fahimci ba k'aramin son Yabi Tijjani ya afka ba. Sannan ya ji kunyar maganganun da ya ji yana yi a kansa.
Dada ta kalli Jabiru ta ce "gara ma da baka auri Yabi ba Jabir. Na fahimci irinsu ne matan jaraba. A kansu ba abin da namiji ba zai yi ba. Mafi yawa haka zaka gansu yan firit amma suna murza mazaje ingarmai. Yadda kake sanyi k'alau din nan ba zaka sarrafa ta ba. Ko mai sunan manyan da yake a tsaye, tun komai bai gitta a tsakaninsu ba, ga shi nan yanayinsa ya nuna ta riga da ta shiga ransa ta yi kane kane".
Cikin jin nauyin maganarta Jabir ya ce "wacce irin magana ce haka Dada da girman ki?"
Ta nisa ta ce "Gaskiya ne mana! Kawai murnar da nake yi masa d'aya ce. Ta iya sana'ar samun ku'di, dolenta ta fito da ku'di su ci abinci. Idan ku'din da suke saka ta yiwa iyayenta raini basa zama mata ai ta nutsu ta girmama manya".
Tana rufe baki Jabir ya ce "Haka su Baban suka fa'da miki shiyasa kika tirsasa aka yi wannan bahagon hadin?"
Ta yi dan tari kafin ta ce "Gaskiyarsu ne ai! Sannan shi mai sunan manya tunda ba shi da sana'a asirinsa zai rufu".
Jabir ya ce "Gaskiya kun kassara rayuwarta, amma akwai Allah. Ina fatan alheri ya biyo baya, sai dai har yau din nan ban hakura ba. Na sani *Hannu daya* baya daukar jinga. Bazan ha'kura da ita ba har sai na ga ranar da aka shafa fatiharta da wanina. Daga ranar na zubar da makaman nemanta. Amma matu'kar ban mutu ba idan an kaddara mini cikar burina zai zama gaskiya. Idan da rabona zata dawo mini, ni kuwa zan aureta komin tsufanta, domin ita nake so ba wani abu a tare da ita ba".
Dada ta kyabe baki ta ce "Idan k'asa ta rufe mini ido komai ma sai ku yi tunda ban ga ni ba".
Tijjani da yake jinsu zuciyarsa ta dinga bugawa da k'arfin da ya zarce ka'ida.
Yana son ya je ya fa'da wa Dada duk lalacewarsa bata kai mace ta ciyar da shi ba, bai yi mutuwar zuciyar da macen aurensa zata dauki nauyin kanta da nasa ba. Sannan ta fahimtar da y'ay'anta hakan.
Amma sai ya daure ya ha'diye. Ya ja jikinsa ya fa'da dakinsa ya fa'da kan katifarsa.
Wani irin yanayi na shigar sa na tsananin bacin rai da ya sababa masa k'arfin zuciya.
Domin gaba'daya ji ya yi hatta dako na daukar buhun gero da na su wake zai iya yi, dan ya ciyar da Yabi da guminsa ba wai ta ciyar da su ba.
Idonsa ya ciko da hawayen tausayinta domin ya gane k'iyayyar da ake yi mata ne ya sanya aka bashi aurenta.
Ya yi shiru yana nazari wato saboda ana ganin shi din lalatacce ne. Ana ganin shi ba zai amfana wa kansa komai ba, bare ita ta amfana da shi. Ana kuma fatan ya dauwama cikin lalace wa da mutuwar zuciya.
Sai ya tsinci kansa da tambayar shi da Yabi wa aka fi tsana ne a gidan Marina?"
Take ya muskuta ya janyo wani kwali.
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*
*Lame fa garin su Yabi ne*
Ya dauko memo da biro, ya yi rubutun magananun Jabir, da wanda su Baban Tsakiya suka yi da ya ji a harshen Dada.
Da irin manufar ba shi Yabi. Da yadda ake fatan ta tabbata cikin halin ni 'ya su.
Sai kuma ya je shafi na gaba sosai ya rubuta "Zan yi komai na halal dan na sauke nauyin da yake kaina.!
Allah ka sani ban sake aikata zina ba! Allah ka taimake ni ka cigaba da tsare ni.
Allah ka fahimtar da ni sarrafa mace ta yadda Yabi zata rayu cikin farin-ciki a hannuna.
Allah ka hore mini kofofin arziki ta yadda zan sauke nauyinta ba tare da tallafinta ba.
Na sani al'kawarin ka baya tashi, da kanka ka yi al'kawarin taimakon wanda ya k'udire niyyar aure saboda kai. Ga ni bawanka, Ibnu bawanka cikin kankan da kai, ka taimake ni, ka kubutar da ni kunyata a idonta da na dangimu. Allah ka hore mini lafiya, ka sanya mini hakuri akan sha'anin ta, sannan a mallaka mini zuciyarta da tunaninta." Sannan ya rubuta kwanan wata.
Ya rufe yana jin girman k'alubalen da yake gabansa.
Wani irin son ta da tausayinta yana sake bin dukkan jikinsa yana kutsawa.
Har yake jin anya akwai wanda ya so mace kamar yadda yake jin son Yabi ya sake shak'e shi a yanzu?
Domin shi son ta yake yi babu wani dalili na sha'awa ko na burge wa.
Na farko yafi son manyan mata masu manyan halittu. Yabi kuma yar mitsil mai k'ananun halittu, maimakon ya ga ba hakan yake so ta zo ba. Sai yake jin ko bata da komai na cikar mace yana sonta a hakan.
Na biyu yafi son mace mai sanyin hali, mai kawaici.
Amma daga ranar da aka jefa masa sonta shikenan ya ji da tsiwarta zai yi amfani wajen kutsawa dan ya sami kusanci a zuciyarta.
Ya sani ba zai yarda da rashin kunyar da ta wuce ka'ida ba.
Amma yana fatan a cikin rashin kunyarta ya dinga isar mata da sakwanni masu girma.
Na uku akan abin da aka yi mata na tirsasa Jabir auren Maijidda, da kuma yadda uwar Nasiba ta ture komai na zumunci ta fadi maganganu marasa dad'i a gaban mahaifiyarsa! Shike nan ya k'yamaci auren zumunci.
Amma a yanzu yadda yake jin Yabi zai iya yin komai dan ya same ta.
Ya gamsu tausayi da sonta sun masa rubdugu.
Ya rufe littafin ya mayar da shi ma'adaninsa.
Ya jima a zaune yana ta tunanin sana'ar da zai fara.
Ya saki gauron numfashi! A fili kuma sai ya ce "Allah ka hana Tijjani sanya Yabi kuka! Allah ka hana ni zaluntar ta. A hore mini ita ya Ubangiji".
Ya zabura ya mik'e yana ganin lokaci ya yi da zai daina buga buga ya samu tartibiyar sana'ar da zai dogara da ita tunda nauyi mai yawa ne zai hau kansa, wata'kila ma badi war hakan yana shirin zama Abba.
Murmushi da kunya suka subuce masa ya dinga sosa k'eyarsa tamkar yana gaban manya ne.
A fili ya furta wa ya ga "Yabi as uwa?"
Sai dariya ta sosai ta kama shi, har bacin ran da Jabir da Dada suka cusa masa ya yi sauki.
Ya fito ya nufi wajen Alh Tsoho magini dan ya ji ko zai masa hanyar samun aikin ginin.
Yana tafe sanye da yadi na wando da riga bata kai guiwar sa ba.
Kamar kullum a wanke suke amma fa babu guga.
Sannan ya saka hular sanyi ya rufe gashin kansa.
Domin tunda aka furta za'a bashi auren Yabi. Bai sake yarda an ganshi da gashin kansa ba, duk da ya ki aske wa.
Ba wanda yake jin kunyar ya ganshi da sumar irin Baban Marina. Domin ya sani baya so, ya sha tisa shi a gaba ya saka a masa askin akan dole.
A yanzu kuwa wata irin kunyarsa yake ji ta sosai domin bayan kawunsa ne da yake yi masa adalci, yanzu shirin zama surukinsa yake yi.
Bulkachuwa da kansa ya yi amannar ba dan zuciyar Baban Marina irin ta daddako ba ce da ba za'a yi masa wannan k'arfin akan diyarsa ba. Ba dan alherinsa mai yawa ba ne, da ba zai ba shi aure ba, komai za'a yi kuwa.
Amma ya yi shahadar ba shi, babu dogon turanci. Yana tafe yana fa'din "Allah ka fitar da Tijjani kunyar Baban Marina".
Ya sha kwanar shiga cikin wani kwararo sai kawai ya fara jin k'amshin turaren da yake ji a jikin Yabi da kuma wanda yake shaka a jikin Jabir.
Ya shiga sai kuwa ya hangosu kowannensu jingine a garu.
Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi.
Kishi mai tsananin gaske ya dabaibaye shi.
Tamkar ya juya sai kuma ya tsinci kansa da tunkararsu.
Ya zuba musu ido. Yabi na kuka sosai yayin da Jabir idonsa ya kad'a ainun.
Sau d'aya za'a kallesu a gane suna cikin tsananin soyayya da kuma halin cankacakare.
Ya kalli Jabir da yake tsab da shi cikin shadda ruwan toka ta sha guga. Farin gilass ya mak'ala.
Ga k'amshi mai da'di na tashi a jikinsa domin komin hassada baka isa ka ga wani abu na rashin tsabta ko gayu a tare da Jabir ba.
Yayin da Yabi take sanye da hijabanta har k'asa sai dai duk ya b'aci da hawaye har da ba'kin kwalli.
Kishi sosai ya turnike Bulkachuwa.
Har ji ya yi zukar numfashi na neman yi masa turjiya.
Amma a hakan ya motsa k'wanjinsa ta hanyar cewa "Jabir na tabbatar babu jahilci a tare da kai tunda ka yi zurfi a ilimummuka daban daban. Sai dai abin mamaki sanin naka bai amfana maka komai ba, tunda zaka iya tsayawa da wacce kwanaki kadan ya rage a daura mata aure a cikin lungu inda babu sawu.
Ni ba zan yi maka rashin adalci na yi maka kazafi irin yadda ka yi mini ba.
Sai dai na sha fa'da kai din azzalumi ne, ba masoyi ba. Ta ya ya an baka aure ka karba, dan kwadayin albarkar iyaye ita kuma ka dinga hure mata kunne da ga yiwa nata tsohon biyayya? Ban da ita din sakara ce har wanne kalami ne a bakinka da zaka tsara mata da yafi na ubanta da kannensa tasiri?".
Jabir ya sandare ya zuba wa Bulkachuwa ido, yana jin wata irin fargaba from no where tana shigarsa.
Yayin da ni kuma na dago ido jage jage da hawaye na watsa masa kallon kiyayya da raini na ce "Ba ruwan ka da ni Tijjani! Na saurare shi din, domin shi nake so, nake fatan kasance wa da shi".
Ga mamakina sai kawai ya ja kakkuran tsaki tare da ce wa "Ai ke din shasha ce! Kuma kin ji na saka maganata da ke?
Da shi na ke wanda na gamsu da hankalinsa da iliminsa, kawai adalcinsa ne bai gamshe ni ba. Amma ke da baki da hankali ina ruwana da ke?
Jiyan nan na gan shi da matarsa a asibiti yana ri'ke da ita. Yana faman tattalinta. Wai matar da ya aure ta ba dan yana so ba yake yiwa irin wannan son da adalcin, amma ke kullum yana cikin dama miki lissafi. Da yake ya mayar da ke shargalle marar tunani."
Ai kuwa yana rufe baki kuka ya k'wace mini sosai.
Jabir ya kasa magana domin ya tabbatar Bulkachuwa ya gansu a asibiti ba k'arya ya yi masa ba.
Bulkachuwa ya sake yin k'uta tare da nuna Jabir da yatsa ya ce "Neman aure cikin aure haram ne in ji ma'aiki (S.A.W).
Da ku'din aurena akan ta, ko ba zaka yi mini kawaici irin na zumunci ba, to ka yiwa ka'idojin shari'a biyayya. Ka fita mini a harkar Asiya! Ubangiji ya baka Maijidda wacce ita ce mafi alheri a gare ka. Amma bar mini Asiya Toro domin ina da yakinin akwai babban al'amari a tsakanina da ita. Daga ranar da aka tabbatar mini an ba ni ita, na fara addu'ar na yi nisan kwana mai yawa dan na tabbatar ni kad'ai na mallake ta".
Still Jabir ya kasa magana domin gaba'daya almarin ba k'aramin bugunsa yake yi ba.
Kishin Bulkachuwa ya shak'e shi k'warai da gaske. Domin idan gaskiya zai fa'da ya ga son Yabi a idonsa irin wanda bai yi zaton Tijjani zai yi mata ba. Mussaman yadda bai dauki soyayya da muhimmanci ba. Mace tana bata masa rai zai juya mata baya duk yarda yake da ita kuwa.
Ina kuka, ina kallon Yaya J. Na sani dan na yi ba'kin ciki ya sanya Bulkachuwa sako maganar Maijidda. Ban da haka mene ne dan ya nuna kulawa akan matarsa ta aure?
Nan da nan zuciyata ta hassala cikin rawar murya na ce "Mene ne dan ya kula da lafiyar Iyalinsa? Tabbacin nima zai kula da ni ke nan tunda har ya yiwa wacce baya so adalci to ina kuma a ce ni ce da yake so? Kai sau nawa ana ganinka da tambadaddun matan banza?"
Take jikin Yaya J ya yi k'wari domin yasan yadda nake da kishi na gaske, maganar Bulkachuwa na iya tunzura ni na yi masa fishi. Dan haka ya dan murmusa. Sannan ya ce "Ko yanzu na mutu a sanadin rashinki ba ni da kaico tunda kin mini kyakkawar shaida Yabin J".
Da rawar murya na ce "Idan ka mutu, kuma ka bar ni da wa? Wanne irin ba'kin fata ne, akan me zaka mini fatan irin wannan asarar haka?"
Tijjani ya harzuka ya ce "Ba zaka mutu ba ka ga yadda Asiya Toro zata manta da al'amarinka ba Jabiru.
Ya sake sakin tsaki sannan ya ce "Idan kuwa har ka mutu ba wanda ya yi asara irin abin da yake cikin Maijidda, sai kuwa ita Maijiddan, da zata shiga takabar mijin da yake sonta yake gudun bacin ranta".
Na sake fasa kuka ina fa'din "Allah ga Tijjani nan ya takura ni, ya fitine ni haka siddan, ka sani bana sonsa, ka gaggauta cire mini shi a duniya ta".
Sai lokacin Yaya J ya ce "Yi hakuri kin ji Yabi! Ko zan mutu ba yanzu ba, da saura In sha Allah".
Na wuce na fara tafiya a hankali.
Bulkachuwa ya ja tsaki ya ce "k'aryar banza! Dan Allah ka mutu yanzu Jabir. Da an ga tsiya domin kuwa ana dawowa daga rufe ka zan lallaba na koma. Tamkar wanda zan yi maka addu'a. Nan kuwa fitsari zan tsula maka a kabarinka ta yadda sai ka shekara a kwance kafin addu'ar jama'a ta riskeka, mussaman ta Asiya Toro. Kai da addu'a ta riske ka sai damina ta zo. Idan na so k'eta ma, daminar na dauke wa na sake tsula maka wani. Kuma idan juninka tsiya ne Maijidda na haihuwa zan aure ta. Na ha'da su da Asiya Toro su yi ta faman buga competition a kaina".
Na juya da nufin na yi masa raddi ya nuna mini yatsa ya ce "Idan kika kuma tozarta ni sai na fasa miki bakin ki domin ban yi da ke ba, marar kishin kai".
Jabir ya yi hanzarin ce wa "Kar ki ce komai Yabi cikin yanayi na kad'uwa sosai.
Ya kalli Bulkachuwa ya ce "Har zaka iya yi mini fitsari a kabarina Bulkachuwa? Sannan ka ce "zaka auri matata akan idona?"
Wani irin murmushi Bulkachuwa ya yi mai dauke da nisha'di da ma'anoni.
Ya ce "In dai son Asiya ya zama ajalinka zan tabbatar na hana adduarta riskar ka.
Sannan dan na auri Maijidda ai rufa maka asiri na yi tunda tare da abin da ta haifa zan ha'da na rikesu. Idan kuwa kana kishinta kamar yadda yanayinka ya nuna har ka kasa ha'diye hakan a gaban wacce kake kirarin kana so. To kawai ka k'yale mini Asiyata.."
*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
"Shikenan idan ka yi haka ba zan maka fitsari idan ka riga ni mutuwa ba. Ba kuma zan aurar maka bebinka ba, tunda wani irin so kake yi mata wanda baka iya b'oye kishinta a gaban kowa"
Ba'kin ciki mai tsanani ya lullub'e ni.
Na kasa bu'de baki na ce komai domin na tabbatar yana iya fasa mini baki kamar yadda ya fa'da din tunda baya fa'dar magana da zummar wak'e.
Na juya na tafi, ina tafe ina hawaye, ina kuma ha'da hanya. Domin idan akwai abin da yake ci mini zuciya bai wuce a mini zancen Maijidda ba.
Na kuma fahimci Bulkachuwa yana son bani labarin irin tarairayar da J yake yi mata.
Na tuna tun kafin zancen aurena da shi ya b'ullo, ya sha fa'da mini yana ganin Yaya J goye da Maijidda a mashin dinsa.
Har na isa gida kukan sharbe nake yi.
Na shiga dakinmu na zauna bakin gado ina kuka sosai.
Domin abin ya ha'de mini, ga bacin ran auren dole da mutumin dana tsana ga kishin Maijidda da yake azalzalata tamkar zuciyata ta fa'do kasa.
Gwaggo ta kalle ni ta yi k'wafa tare da fa'din "ki yi ta kuka har hawayen idonki su k'afe, aure kuwa kinsan babu fashi".
Ta fice ta bar ni.
*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
*Dada*
Bulkachuwa zaune a kusa da ita kan baranda sai faman bacin rai ya ke yi.
A hankali ta ce "To menene zaka tisa ni a gaba kana ta faman k'unci kaki fa'da mini damuwar ka?"
A hankali ya ce "Jabir ne mana ba dama Yabi ta fita sai yasan yadda ya yi ya tare ta. Gaskiya abin ya fara tayar mini da hankali, ki fa'da masa ya bari".
"A sanyaye ta ce "zan fa'da masa kaima ka kara hakuri duka kwana nawa ya rage ne? Ai da zarar am shafa mata fatiharka dole kuma su kiyayi juna."
Bai kai ga amsa mata ba, ya ga masu aikin gini da fenti sun shigo da kayan aiki sun shige k'ofar ciki".
Ya kalli Dada ya ce "me suke yi a ciki ne?"
Da walwala ta ce "Tun dazu suke fama, sallah suka je yi. Kawunanka suka saka a gyara maka wajen sun ce bai kyautu su barka da neman muhalli ba".
Ransa ya baci ya ce "Shi Baban Tsakiya ne zai ce haka?
Me yasa bai mini gini irin na Jabir ba?
Idan kuwa Baban Kasuwa ne me yasa ya hana Salisu zama a lokacin da ya roki a bashi ya zauna kafin ya samu sararin yin nasa?"
To bana so, na sani kuma Yabi ba zata so wajen ba, ya yi tsufa da yawa".
Daga haka ya tashi ya barta tana faman buga salati tare da fa'din "Ni Binta ina kallon wuyar zama irin ta y'ay'an yau. Komai aka yi musu babu mutunci bare su yi godiya.
Wannan zamani da wuyar sha'ani yake".
Ta yi k'wafa sannan ta sake cewa "Allah na yi tuba, kai ne mamallakin zamani. Allah ka shirya".
Har washagari bani da sukuni, a kuma wannan ranar aka kawo mini lefe daga Bulkachuwa.
Sosai aka zuba kaya a lefen tamkar na masu wadata. Na sani kuma y'anuwan ubansa da Babah ta Bulkachuwa suka hada kayan, sisinsa bai yi ciwon kai ba.
Maza ne suka kawo kayan dan haka ba ayi gayya ba.
A k'ofar Dada aka taru aka ga ni, masu fatan alheri na yi, masu shagube na yi.
Sai da ya kwana ya yini a wajen Dada sannan ta saka aka kawo kofarmu.
Hatta Babanmu sai da Inna ta bu'de masa kayan ya ga ni, ya yi addu'ar alheri tare da fa'din "Oh haka suka yi wahala mai yawa?"
Ni kuwa ko kallon kayan ban yi ba, bare na ga mene ne a ciki.
Da yamma ina zaune ina k'ulla wa Gwaggo siga.
Sai ga Anas ya shigo ya kalle ni ya ce "Dada ta ce ki je yanzu".
Na bata rai na kasa amsawa domin na tsani na je kofarta saboda dalilai masu dama.
Na farko haushinta nake ji.
Sannan bana son ganin mawuyacin halin da nake ganin Nasiba a ciki. Domin sosai ta mak'ala wa zuciyarta son Bulkachuwa. Kishina sai ya galgalata yake yi, duk da bata bu'de baki ta mini maganar ba, sai ma murnar da ta yi mini na samun miji irinsa wacce na ji tamkar ta caka mini wuk'a ne. Wannan shine daidan wani, karkataccen wani.
Sannan kuma ina sake k'in shiga wajen Dada ne saboda kada na ga Tijjani. Shi yasa ma bana zuwa gaishe ta sai hantsi ya yi sosai.
Gwaggo ta ce "Je ka ce tana zuwa".
Ya ce "To" ya tafi.
Akan dole na dauki mayafi na nufi shashin Dada.
Ina hasashen menene dalilin kiran?
A zauren Dada na tarar da shi a tsaye. Zuciyata ta tsinke sosai. Na yi kamar ban gan shi ba. Na wuce da nufin shiga cikin gidan.
Ya bu'de baki ya ce "Ni ne mai kiran na ki ai".
Na tsaya cak. Ba tare da na iya ce wa kanzil ba.
Ya saki gauron numfashi kafin ya ce "Ga ni na yi abu ya matso kusa sosai amma babu fahimta a tsakaninmu bare nasan abubuwan da kike bu'kata".
Na ja tsaki na ce "auren so ake yiwa irin wannan tagomashin".
Fuskarsa ta yamutse kadan. Ya ce "To na biyayya fa?"
Nan da nan idona ya ciko da hawayen takaici. Na yi k'asa da kaina na kasa ce wa komai.
Murya babu amo ya ce "Abokina da muka yi karatu a Gad'au gobe zai zo.
Ya dame ni akan na ba shi lambar amarya ko na kawarta dan ya ji irin yadda ake sallamar amarya da kwayenta a nan, da kuma abubuwan da kike bu'kata".
Na ja tsaki tare da ce wa "Komai zai fito ta hannun ka ko ta sanadin ka bana sonsa ba kuma zan kalle shi ba."
Ya zuba mini ido sosai cikin damuwa mai yawa.
Cikin wani irin yanayi ya ce "Asiya Toro alfarma d'aya nake so ki mini, ko da kuwa ita ka'dai ce alherin da zaki yi mini. Ki taimake ni kada ki tsinka ni, ki yi mini wannan arzikin dan Allah".
Ban san ya aka yi ba, jikina ya yi sanyi, mussaman yadda na ga ya yi kalar tausayi tamkar ba Bulkachuwa ba.
Na yi shiru amma fuskata a cukune sosai.
Ya sake ce wa "ki bani lambar wacce zai yi magana da ita Asiya. Sannan idan sun zo mini ranar daurin aure kada ki wula'kanta ni a gabansu. Na yarda bayan sun tafi ko menene ki yi mini, zan jure".
Na sake gallah masa harara tamkar idona zasu fa'do k'asa. Tare da ce wa ban iya Yaudara ba, ba kuma zan fara yanzu ba. Ai na sha jin kana fa'dawa abokan naka ba macen da zaka aureta alhalin kasan bata sonka. Ba ayi macen da zata ce baka yi mata ba, sannan ka nace sai ka aure ta, duk wanda ya sanka yasan wannan alwashin na ka. To me yasa yanzu ka yarda zaka aure ni alhalin kasan bana son ka, bana farin-ciki da al'amarinka gaba'daya?"
Kuka ya k'wace mini sosai.
Murya babu amo ya ce"Kaddara ta ce a hakan Asiya! Ni kaina na kasa gane kaina.
Wata'kila cika bakin da na yi ta yi ne, ya sanya aka jarrabe ni da son auren wacce ta washe ni, wata'kila kuma Ubangiji ne zai mini wani alherin ta sanadin ki shiyasa ya jingina mini sonki mai yawa."
Na sake jan tsaki na ce "Ba wani alheri domin da zan ga sadda zai tunkare ka zan karkatar da shi na bawa wanda suka fika mutunci da so na".
Ya girgiza kai ya kasa magana domin ransa ya baci idanuwansa har canja wa suka yi.
Tsawon sakwanni bai iya ce wa uffan ba.
Ni kuma sai fama nake da kuncin zuciya. Sannan sai yanayinsa ya sanya na ji babu da'di, domin duk yadda na tsane shi. Sai na ji ya d'an ba ni tausayi ka'dan.
Muna haka Baban Marina ya dawo, ya zo wuce wa ta babban zaure ya hango mu a zauren Dada.
Ina kallon yadda yake murmushi yana amsa gaisuwar Bulkachuwa da walwala.
Ni kaina a wannan lokacin ya sace da fishin da yake yi mini. Domin da murmushi a fuskarsa ya amsa barka da zuwan da na yi masa.
Har yana fa'din "Sannunku Yabi"
Kunya ta saka na yi nufin shige wa wajen Dada. Sai ce wa ya yi "Dawo ku cigaba da tattaunawarku. Allah ya yi muku albarka. Allah ya sa ku zamo abin alfahari, Allah ya shiga al'amarinku".
A hankali Tijjani yake amsa wa yayin da ni kuma ban amsa ba ko da a zuci ne.
Yana shige wa ya kalle ni a sanyaye ya ce "Asiya Toro Baban Marina bai dauki auren nan namu da wasa ba fa. Mu ha'da kanmu, kada mu ba shi kunya dan Allah".
Na ja tsaki tare da ce wa "Ni Malam na gaji tafiya zan yi".
A sanyaye ya mik'o mini wayarsa ya ce "Saka mini lambar"
A tunzure na ce "Ba ni da k'awa".
Da sigar lallashi ya ce "Yanzu duk ro'kon da na yi miki?
Farin cikin da Baban Marina ya yi a dalilin ganinmu bai sa zuciyarki ta rusuna ba?"
Na murguda baki na ce "To ai dai kasan ba ni da k'awaye, Adda Nazira ce kuma ta yi aure, sai kuwa Nasiba ita ma kuma ai auren ta za'a yi ko?"
Ya girgiza kai ya ce "Hakane! To Ina wannan fara mai dan jikin nan da yanzu kuke dawowa daga boko tare? Sannan tare nake ganinku a wajen koyon kwalliya".
Na zuba masa harara na ce "Tsabar sawa mata ido har ka gane halittar ta?
Har abada ba zaka burge ni ba Tijjani. Ba kuma zan baka lambar ba, domin dai da bakin ka ka tabbatar mini nema cikin nema haramun ne. Bari na shaida maka tuni an kai ku'din aurenta. Dan nasan kana iya lallabawa wajen ta".
Ya yi sororo sai kuma b'acin ran fuskarsa ya ragu.
Ya ce "Bana ma son lambar, na fasa, zan ba shi lambarki sai ki fa'da masa ta yadda zai turo miki ku'din kunshi da na kitso, ya damu akan a sallame ki ke da kawayen ki ne".
Na yi shiru ban ce komai ba.
A hankali ya ce "ya yi miki hakan?"
Na sake yi masa banza.
Ya sassauta ya ce "please mana Asiya Toro".
Na harzuka na ce "Gaskiyar magana baka yi mini adalci, idan ina kaunar yadda kake gatsa sunana ha'de da na garina Allah ya tsine mini!.
Ya dan murmusa ya ce "Da sannnu idan kin kwantar da hankalinki zan daina fa'da, na samo miki sunaye masu da'di da tsuma zuciya".
Ba'kin ciki ya sake turknike ni. Na ce zuciyar waye din zata tsumu?"
Ya make kafa'da ya ce ta "Asiya Toro".
Na yi kwafa na ce "Ai na gane zuciyarka babu alheri ne shi yasa kake k'yashin ce mini Yabi. Da'din abin ma dubun ka suna fa'da mini cikin girma da arziki".
Ya ce"Nan da lokaci ka'dan komai zai zama tarihi. Kin ga dai na nemi arzikin ki, ban kuma mayar miki da martanin bakaken maganganun da kika yi ta yab'a mini ba. Ina sake ro'kon ki idan abokina ya kira ki, ki taimake ni kada ki bayar da ni."
Ban amsa ba. Ya sake cewa dan Allah Asiya Toro".
Cikin fishi na ce "Na ji".
Da'di ya kama shi ya dinga fa'din "Na gode sosai. Ina fatan na ga ranar da zaki fahimci irin tarin alkhairorin da suke zuciyata mussaman akan lamarin ki".
A hanzarce na ce "Ai kuwa dai ba zaka ga ranar ba".
Ya girgiza kai tare da ce wa "Babu damuwa time will tell".
Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ina son na tambaye ki, zaki iya zama a wanccan daya bangaren na Dada?"
Maimakon na yi masa magana da baki, ai sai kawai na d'ora hannu aka na fashe da wani irin kuka na tashin hankali.
Murya na rawa na ce "wato dai a cikin masifar gidan nan zan tabbata? Idan kuwa har a cikin gidan nan ake nufin na zauna da sunan zaman aure Allah ya dauki raina kafin hakan ya tabbata. Na shiga uku ni Yabi".
Ya rikice ya hau fa'din yi shirun ki dama na fa'da mata wajen ya miki local da yawa, sannan baki samu sauyin muhalli ba. Yau din nan duk inda gida yake zan nemo kafin dare. Da ku'di a hannuna.
Yi hakuri ki daina irin wannan kukan. Kin ga yadda kika koma kuwa Asiya?"
Da k'yar ya lallaba ni, na yi shiru.
Ya zura hannunsa a aljihu ya ciro cakulet manya masu da'di da tsada k'waya biyu ya mik'o mini.
Bansan ya aka yi ba na fashe da dariya ga kuma hawayen ba'kin ciki na ziraro mini.
Da yake d'an duniya ne sai kawai shima ya fashe da dariyar yana cewa "Ni nasan Ubangiji zai cusa miki soyayyata dan yasan yadda ya gina ki a tawa zuciyar. "
Da k'yar na samu dariyar ta tsaya.
Da hawaye a idona na ce "me zan yi da wannan abar?"
Ya zuba mini ido yana wani lumshe su ya ce "Wai fa dan kada na zo hannu na dukan cinya ya sanya na taho miki da su"
Na rasa me zance masa tsabar takaicinsa da ya d'ada makure ni.
Na ce "To ajiye idan ka ga Yarinya k'arama ka bata amma ba ni ba".
Ya waske ya ce "Asiya Toro maraina ka'dan fa barawo ne. Kowa ba iya karfinsa zai yi kyauta ba?
Kin san wahalar da na sha kafin na samo miki wannan cakulet din a garin nan? Saboda nasan kina son ta ne. Amma ban burge ki ba? Idan kin yi hakuri wataran katon zan siyo na ajiye miki."
Da sauri na ce "da dai ace ba hannun jinjirai ne da kai ba tsabar rowa."
Ya nuna kansa da yatsansa ya ce "Ni ne mai hannun jarirai? Lallai kuwa zan baki mamaki Asiya Toro local government. Bauchi state of Nigeria".
Ko kula shi ban yi ba na wuce shi na tafi na bar shi a tsaye. Tsabar takaicinsa da ya sake kular da ni.
Ya d'aga murya ya ce "Sai gobe zan dawo, ko da anjima ma na dawo?"
Da kansa ya bawa kansa amsa da ce wa "To zan dawo da daddaren ran ki ya da'de."
Har na isa k'ofarmu mamakin Bulkachuwa kawai nake yi. Ban da dai ya riga ya same ni a araha ya rasa me zai kawo mini sai cakulet k'waya biyu. Shi ko kunya bai ji ba? Amma da na tuna halin rowarsa sai kawai na janye mamakinsa. Na shiga tambayar kaina wanne irin zama zamu yi ne da shi?
Na tabbatar sassaucin da ya yi dan baya son na yarfa shi ne.
Amma da tuni ya baje mini kalolin rashin mutuncinsa.
Na zauna na fara kokarin cigaba da k'ullin sigan.
Zuciyata ta shiga hakaito mini kayan jikinsa.
Shadda ce a jikin sa kalar ganye wato kore sosai. Ya d'ora hular sanyi mai tambarin kungiyar Manchester United. Na sani kuma d'an ya boye wa Baba curarriyar sumarsa ne tunda zafi ake yi ba sanyi ba.
Daga ni tun farar safiya ya sanya kayan a hakan kuma shi ya k'ure malejin kwalliya ne.
Na ja tsaki tare da ce wa "Idona ya saba ganin samari ma'abota wanka da gayu. Irinsu Yaya J da Nuru Tanim. Ta ya ya Bulkachuwa zai burge ni?."
Gwaggo ta shigo ta ce "me ya faru da kika je?"
Na yi kasa da kai na ce "Ba Dada ba ce ashe".
Ta ce "To waye?"
Na bata rai duk da kan nawa yana kasa na ce "Tijjani ne".
Daga hakan bata kara ce wa komai ba ta dauki abin da zata dauka ta fice tsakar gida.
Washa gari da azahar ina kwance a tsakar daki sai ga Nazira ta zo. Karon farko da ta zo gida tunda aka yi mata aure. Duk rud'anin da nake ciki sai da na tashi da azama na rungume ta.
Muka haye k'aramin gadon Gwaggo da muke kwana a kansa ni da ita tun fil'azal.
Da murmushi a fukskata na ce "Yau Adda Nazira ce a gidanmu?"
Ta d'aka mini duka tare da cewa"oh har kin cire ni a cikinsa, to kema kwana nawa ya rage miki mu yi kunnen doki?"
Na bata fuska sosai. Ta ce "daga wajen Dada nake suna can, suna artabu da Yaya Bulkachuwa akan inda zaku zauna.
Wai akan me zai je ya kama haya tamkar ba shi da kowa a Toro?
Shi kuma ya kafe ba zai zauna a cikin gidan nan ba.".
Na bata rai na ce "Ai Wallahi na fa'da masa indai ya yarda da tsarinsu to kuwa sai dai a tsine mini dan bazan zauna a gidan nan ba'kin ciki ya karasa ni tun ajalina bai zo ba"
Adda Nazira ta ce "Haba ashe tirjiya ya samu daga gare ki, kin ga yadda ya fitittike akan ba zai zauna a wajen ba?
Dada har da kukanta wai sai da ya bari su Baban Tsakiya sun gama gyara masa wajen sannan ya ce zai fita ya kama haya tamkar wanda bashi da galihu a Toro? Shi kuma kinsan shi ya ce "Salisu da yake hayar rashin galihu ne ke nan?
Ashe ashe Gimbiya Yabi ce ta saka ya rikice ya turje.
Ya kama miki gida mai kyau a bayan sakatariya. Ba ki ga gidan ba. Yanzu muka dawo a mashin dinsa ya goye ni muka je ya nuna mini gidan. Ni Wlh har na ji na daina k'insa. Kin ga rawar jikin da yake yi. Sai fa'di yake ya kika ga wajen Nazira? Nasan idan ya burge ki to zai burge kanwar ta ki ma.
Gaskiya Yabi ke d'in mai sa'a ce. Gaba'daya kin rikita namiji irin Yaya Bulkachuwa. Murna nake yi, da dukkan zuciyata nake jin addu'armu ta karbu. Da ikon Ubangiji sai kowa ya yi mamakin alherin da zai biyo bayan wannan auren."
Na tab'e baki na ce "Hmm ai ni dai an cuce ni kawai. D'azu muna maganar k'awayen amarya. Na ce masa ba ni da k'awaye, ke ce to kuma kin yi aure.
Yana bu'de baki da yake shi d'in bunsuru ne sai ce wa ya yi wai ina k'awata fara mai dan jiki. Kin san wa yake nufi?"
Kafin ta ce komai na zarce da ce wa "Shafa'atu yake nufi fa. Har ya k'yalla ya ga halittu a tare da ita shine zai silala me za'a yi da Tijjani ne. Na fa'da cikin kunan rai.
Ga mamakina sai ganin Nazira na yi ta k'yal-k'yale da dariya sosai. Sannan ta ce da wuri haka Yabi?"
Na bata rai na ce 'ban gane ba?"
Ai kuwa cikin ido ta ce" tun yanzu kin fara kishin Yaya Bulkachuwa ina kuma idan kin shiga hannunsa?"
Hawaye ya b'alle mini ina ce wa "Allah ya sauwake, ashe ba ki fahimce ni ba Adda Nazira?"
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBE TA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
"Tunda Kika kasa gane abin da yake zuciyata ba wanda zai fahimce ni dai-dai".
Na fa'da cikin kuka sosai.
Ta maze ta ce "Ai kuwa dai kinsan na sanki tamkar yunwar cikina. Wata'kila kuma y'an watannin da muka yi ba tare ba ya sanya na soma mance ki. Amma tunda kin ji bacin rai a dalilin maganar ki yi hakuri da wasa nake yi shikenan?"
Da haka na fara goge hawayen idona.
Sai yamma lis ta tafi. Na rakata hanya ta hau abin hawa.
Ina kan hanyar dawowa sai ganin mutum na yi tamkar daga sama yana biye da ni.
Bai yi magana ba, bare ni kuma. Har muka iso gida sannan ya ce "Asiya Toro manyan mata. Na wuce shi na yi shigewa ta. Ina ayyana shi bai san ya kintsa kansa idan za shi wajen budurwa ba.
Ina shiga na tarar da Babanmu a zaune.
Ko hijabi ban cire ba, sai ga yarinya cikin yaran Baban kasuwa ta shigo ta ce "Adda Yabi Yaya Bulkachuwa ya ce "sauri yake yi ki je yanzu sakon zai fa'da miki".
Ba'kin ciki ya tokare ni, wai shi nan masharranci.
Na fito babu b'ata lokaci na fita ba dan komai ba sai dan Baban Marina yana zaune ba dan haka ba sai dai ya bushe a wajen.
Da fishi shinfide a fuskata na isa.
Ya kalle ni ya ce "Me kuma ya faru dan Allah. Dazun nan fa na ganki kina ta murmushi har na yi zaton ko labarin gidanki da Nazira ta gano miki take baki ya saukar miki da farin ciki mai yawa."
Na d'ago na kalle shi ina rasa ma ajin da zan ajiye Tijjani. Na lura kusan halin mahaifina ne da shi. Zaka yi musu abin takaici sai su waske su nuna basu gane ma me kake nufi ba, bare su nuna sun damu a karshe kuma sai su yi maka abin da kai ne zaka shaki takaici cikin salama.
Na wuce shi na yi tafiyata.
A hakan har kwanakin suka zo ya rage saura kwanaki biyu daurin aure.
A wannan ranar kuma aka yi mini jere.
Da yake Yaya Salisu ya na aiki bansan yadda aka yi ba an ce dai an yi mana gado da kujeru ni da Ubaida.
Na tuna irin yanayin damuwa da Nura ya shiga a dalilin rashina. Da hawaye a idonsa yake fa'din "Na tafka asara Yabi! Tijjani ya zama mai sa'a. Na yarda da kaddara. Na kuma karbi auren kanwarki da hannu biyu in sha Allah kuma zan yi mata adalci.
Allah ya sanya alheri. Allah ya sanyamu cikin masu biyayyar iyaye da ha'kuri saboda shi".
Da alhini mai yawa muka rabu.
Kimanin kwanakin sati kenan.
Na nisa ina sake hakaito wa ban da y'an kofarmu ba wanda ya yaba lefe ko kyaun gidana na rasa irin wannan masifar.
Har gara ma an dan yaba gidan Ubaida kadan duk da gidanta gida ne mai kyau sosai.
Amma da yake da ahalinmu aka fi adawa ba a wani yaba an zuzuta kamar yadda aka kurzanta na su Maijida da Firdausi ba.
Haka gidan Nasiba aka yaba aka kod'a lefenta tamkar me? Amma namu mukus kake ji.
A hakan har asabar din da ta yi daidai da 20 ga watan 5 ta zo aka daura aurena da Bulkachuwa, sannan aka daura na Ubaida da Nura.
Daga nan aka d'unguma gidansu Nasiba aka daura nata.
Fa'din halin da nake ciki na damuwa ba sai na fa'da ba.
Amma dai ji na yi tamkar na sheka barzaku.
Ina takure a dakin Gwaggo Nazira sai kai komo take yi cikin kwalliya. Ga cikin jikinta da ya fara tasawa ya kara mata kyau sosai.
Ihisan k'anwarsu Bulkachuwa ta shigo wai na je abokan ango na jirana.
Akan dole na yarda na bita bayan na ce sai dai ta tsaya ni idan mun je.
Haka na dinga yak'e ina gaisawa da su. Ala tilas na yarda aka yi hotuna. Shi kuma ganin ya samu dama har da sawa ayi mana daga ni sai shi.
Cikin rufin asiri aka yi hidimar bikinmu.
Ubaida aka fara rakawa da yake bamu da nisa.
Ni kuwa Baban Marina hannuna ya kama ya damkawa Babah ta Bulkachuwa.
Ya ce "Rakata dakinta Hauwa! Allah ya kawar da dukkan abin da muke tsoron faruwarsa a cikin aurensu. Ki kula da ita, ko bani ne na haifa miki ita ba, ta zama y'arki tunda surukuta ta mayar da ke uwa a gareta. Bare kuma ni din cikinmu guda. Ina ro'kon ki duk kuskuren da zata miki a zamantakewarku kada ki mata hukunci cikin zato. Kada kuma ki bari shaidan ya rinjayar da aibunta a zuciyarki. Yarinya ce ita din a gaban ki koda kuwa ta kai shekaru hamsin a duniya. Na damk'a miki ita, cikin gasgata cewar na bayar da ita a amintaccen hannun da ko bana raye za'a yi adalci da sassauci. Ina fatan wannan ya zama sanadin karin zumuncinmu ba wai sanadin tabarbarewarsa gaba'daya ba".
Duk da fuskata a rufe take amma na lura da yadda jikin Babah ya yi lakwas. Domin ta kasa bu'de baki ta ce uffan. Na dai ga tana goge fuskarta da na tabbatar hawaye ne.
Tsawon lokaci ba wanda ya yi magana a tsakaninsu.
Sai Baban ne ya katse shirun ta hanyar fa'din "Ki saurare ni da kyau Yabi.
Aurenki ya banbanta da na dukkan y'ay'an gidan nan. Ina fatan kuma ya zama mafi da'din misali a cikinku.
Ki dauka ibada zaki yi. Kinsan kuwa ibada wajibi ce ba wai ra'ayi ba. Ina ro'kon ki zauna lafiya da mijinki.
Ina alfahari da ke tabbas Asiya. Amma zan sake alfahari da ke ne idan har kika taka muhimmiyar rawa wajen mayar da Tijjani yadda muke son ganinsa. Na sani babban aiki ne mai nauyi. Amma tunda an yi sa'a yana sonki to matu'kar kin kwantar da hankalinki za'a samu dai-daito.
Ina fatan na ganku da iyali masu yawa kuna cikin rufin asiri. Tashi ki je, Allah ya bada sa'a ya maki albarka".
Ina kallo yadda Babah ta tashi da k'yar amma bata yarda ta saki hannuna ba tunda Baban Marina ya damka mata.
Ta tayar da ni ta fita da ni har lokacin kuma bata iya cewa komai ba.
Har muka shiga mota, muka isa gidan tana rike da ni.
Da kanta ta shigar da ni dakina bayan ta jira ni na karanta falaki da nasi da attahiyatu har zuwa inda ake yin sallamah a bakin kofa. Ita ce ta bani umarnin yin hakan wanda sai lokacin na ji ta yi magana, rawar da muryarta take yi ya sanya na gane kuka take yi sosai.
Duk yadda jama'a suke shiga da fita na ganin dakin amarya bai sanya Babah ta tafi ko ta saki hannuna ba.
Matan gidanmu duk wacce ta shigo ta ga Babah sai ta yi turus.
Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*
Hatta mamah da matan Baban Tsakiya da suka rakoni tare da ita sai da suka tsokane ta suna cewa "To ko dai ba zaki bar ta a dakinta bane kamar yadda aka yiwa kowa?"
Duk da hakan kuma bai sa ta bar ni ba. Har sai da Aliyu ya dauko mata Bulkachuwa cikin abokansa da suke dakon a gama watsewa su rako shi.
Yadda mahaifina ya damka mata ni a hannunta, bata saki hannuna ba duk tsawon lokacin nan.
Ta kamo hannunsa ta ha'da da nawa ta damk'e cikin nata.
Ta ce "gata nan ubanta ya bani amanarta na kawo maka ita da kaina saboda ya nuna mini ita ce tawa ba kai ba.
Na karbi amanarta, ni kuma na baka amanarta. Ka dinga tuna dalilin ha'da wannan auren. Ka zama cikin mutane masu halarci da kuma sakanta alheri da alheri.
Ban ta'ba farin ciki irin na yau ba. Ka sani na ha'diyi takaici da wahalolinka daban daban. Zan mance komai na yi alfahari da kai har ma na daga maka sawuna ka shiga aljannah idan Yabi ta kubuta daga tozarcinka da gangan.
Ko bana raye idan ka kyautata mata tamkar ni ka yiwa.
Albarka da farin-ciki zasu kewaye ka.
Ka kula da tarbiyarta, kada ka bari ta bijire wa ka'idojin shari'a. Amma ka zama mai sasauci da kawaici domin dai yarinya ce y'ar k'arama.
Ina fatan auren nan ya bud'a maka k'ofofin arziki da kuma fahimtar rayuwa daidai. Àllah ya shirye ka ya shirya maka iyali.
Allah ya albarkaceku gaba'daya".
Ta mik'e ta bar shi a durk'ushe yayin da nake kan gado, hannunmu kuma suna sark'e.
Sai da na tabbatar ta yi nisa na fincike hannuna, na ja tsaki na koma gefe.
Murya a dushe ya ce "Na yafe miki Asiyata! A gabanki Babah ta ce amanarki ta bani, na tausaya miki, na kuma yi miki sassauci."
Na sake jan tsaki fiye da na farko.
Ya mike ya fita bayan yan tsirarrun kawayena sun fara hayaniyar ba'a sayi baki ba dare na yi.
D'aya ce ma k'awata a ciki ragowar hudun duk wanda suka zo daga Kangire ne wato cousin dina na dangin Gwaggo. Sai kuwa Ihisan k'anwarsa. Ita kuma a takure take a dalilin yayanta ne angon.
Ba jima wa suka zo. Suka taba barkwancinsu, sannan aka yi nasiha da addu'a.
Suka gwangwaje k'awaye da ku'din sallama mai auki. Sannan suka tafi da su.
Ina ganin sun fita, shi kuma ya bisu da niyyar rakiya.
Na tashi na rufe kofar dakina.
Da ya dawo ba yadda bai yi dan na bu'de kofar ba na ki.
Ta windo ya leko ya ce "Ga leda nan ki dauka ki ci nasan da yunwa a tare da ke".
Washagari ina jin ya fita sallah na yi maza na fita na doro alwallah a bandaki, takaicina daya bandaki a tsakar gida yake ba a cikin daki kamar yadda na ci buri ba.
A gurguje na kammala uzziri na koma na rufe dakina. Ina idar da sallah na yi kwanciya ta. Sai tara da kadan na bu'de k'ofar dakin, domin barci na yi mai nauyi.
Ina bu'de wa kuwa ya shigo da sauri.
Ya ce "Kin tashi? Sannu ya kwanan bakunta?"
Uffan ban ce ba.
Amma wani irin bakin ciki ne ya turnike ni. A dalilin rashin bandaki a cikin daki.
Na hakaito kusan duk wadanda muka taso tare ko wacce band'akinta a dakinta ne.
Na tuna gidan J da na Nura, hatta Nasiba band'akinta a dakinta ne sai ni ce na samu dakuna tamkar na Islamiya tunda na ga falon ma daban ne ba'a hade suke ba".
Sai kawai na fashe da kuka mai sauti sosai.
Ya diririce ya ce "Daga tashi sai kuka Asiya?
Tun dazu fa nake zaman jiran ki tashi ki karya.
Ina son na fita muyi sallama da abokaina zasu koma garuruwansu".
Ban ce masa komai ba. Illah kukan da nake yi mai tsananin cin rai da nuna k'ololuwar ba'kin cikin da mai yinsa yake ciki.
Ya dinga rarrashi yana Fa'din "Ki yi ha'kuri Asiya komai zai dai-daita, daure ki tashi ki yi wanka anjima ka'dan zaki fara yin baki, duk wadanda zasu tafi yau sai sun biyo sun gan ki. Ina ganin kafin Babah ta wuce Bulkachuwa ma sai ta zo, idan ta ganki a hakan kinsan ba zata ji da'di ba."
Gaba'daya ya rikice ya ce wannan ya saki, ya ce wancan.
Da kuka na ce "Ni ban ta'ba hasko zan shiga gida mai bandaki a waje ba. Gaskiya an cuce ni, an gama da ni. Na saka fashewa da kukan da yafi na farko tsanani.
Hankalinsa ya tashi domin a ki'dime ya tattaro ni.
Na zabura na k'wace ina sake jin taikacinsa tamkar na rufe shi da duka. Jikina har bari ya dauka domin lokacin ne karon na farko da jikin namiji ya rab'i jikina irin haka.
Da muryar kuka na ce "kada ka kuma ta'ba ni. Bana son ka, bana ko son ganin ka".
Ya rasa yadda zai yi da ni. Ya zauna a gefena cikin rashin abin yi.
Tsawon lokaci ina shesshekar kuka.
A hankali ya ce "Ko na samo miki katon baho sai ki yi wankan anan idan kin gama sai na dauke na gyara wajen".
Yadda ya yi maganar sai na ji wani irin abu mai kama da tausayinsa yana neman kama ni.
Na sassauta kukan nawa. Amma ban kula shi ba, bare na tanka masa.
Ya sake lank'awasa harshe ya ce "Ki yi ha'kuri Asiya! A yanzu bani da halin irin gidan da kike mafarkin samu. Ban ta'ba jin takaicin ta'adin dukiyata da na dinga yi ba irin yau. Amma ina ro'kon arziki ki yi mini ha'kuri . Da ikon Allah zan yi aiki tukuru dan na cika miki burin ki. Na miki al'kawarin matu'kar rayuwata da taki ta kai lokacin da zan yi miki ginin da zai dace da ke, to ke zan bawa zabin yadda za'a fasalta ginin".
Na ja tsaki na ce "Duk kana nufin ina nan tare da kai, ina kuma dakon ganin wasikar jaki irin taka?"
Idonsa ya kad'a ya ce "Ni na sani Allah zai taimake ni, dan haka ba wasikar jaki nake yi ba".
Na ja bakina na tsuke. Ya dinga magiya tamkar zai fashe da kuka akan na je na yi wanka.
Da k'yar na yarda na tashi sai dai ban yarda na tube kayana akan idonsa ba.
Sai da ya fita. Sannan na cire. Na dauko sabon zanina gyauto guda. Na daura na saka hijabi. Na bu'de akwatin da na shirya kayana a ciki.
Na ciro soson wanka da sabulu da burush, hadi da makilin. Na ajiye tawul akan gadon.
Na fito na tarar da shi zaune akan baranda duk jikinsa ya saki babu kuzari a tare da shi tamkar ba Bulkachuwa wanda baya barin ta kwana ba.
Yana ganin na fito ya mik'e ya dauki botikin da yake gabansa cike da ruwa.
Ya nufi band'akin.
Na dakata ya fito, ya kalle ni ya ce "yanzu na janyo miki a rijiya da dumi tunda garin da zafi."
Ta tafasa ban ce ba.
Na shiga na turo kofar na sanya sakata.
Ina wanka ina ayyana, ina ma a cikin daki bayin yake?
Dan karami amma ko ina tayals ne.
Na fahimci sabon gini ne mune muka fara zama a ciki.
Sosai na yi wanka.
Sai da na alwala da kuma brush sannan na fito. Na shiga daki na tarar da tsintsiya a hannunsa tabbacin shara ya yi mini. Ga gadon ya gyara tamkar gyaran mace.
Daga kasa kuma kwanukan abinci ne.
Ko kallonsa ban yi ba, bare na yaba masa ta hanyar cewa sannu ko na gode.
Ya kalle ni ya ce "Bari na baki wuri ki shirya".
Ya juya ya fice.
A hankali nake shafa mai tamkar mai ciwo sannan na goga powder. Na shirya cikin sabuwar atamfa ta Buyers Batik. Doguwar riga ce amma dinkin ya yi kyau domin a Jos aka dinko mini.
Gata shudiya ce sosai aka yi mata yarfen ja.
Tsaya fa'din yadda farar fata ta haska atamfar bata lokaci ne.
Na goga rol on din Nivea a raina sai tsaki nake yi ina fa'din da an bar ni da kwamishina ko Yaya Jabir da tuni roll on din oriflame zan dinga tu'amalli da shi dama sauran product dinsu gaba'daya.
Tunda su zance a zubo mini a lefena.
Na fesa turaren Far-away, na shafawa lebena jan baki mai jan duhu.
Gefe na ajiye jan mayafi Wanda ya dace da atamafar.
Da yake yanzu a hutar da mata bata lokaci wajen daura dankwali ana ta yin huluna.
Nima hular aka yi mini.
Ai kuwa na kafata a kaina na isa gaban madubi ina daidita zamanta.
Ni da kaina na dinga fa'din "Fatabarakallahu ahsanul khalik'in.
Sosai na yiwa kaina kyau.
Maimakon na zauna sai na tsinci kaina da son yin walaha tunda na yi alwallah kafin na fito a band'akin.
Na idar na tsaya ina kallon dakin.
Madaidaici ne sannan kayan gadona suma matsakaita ne masu sau'kin ku'di. Amma sun yi kyau babu laifi.
Labulayen sun fi komai dqukar hankalina, ledar tsakar dakin ma mai kyaun aka saka mini wacce za'a kwana biyu bata fatattake ba.
Na bude akwatin na dauko wayata na kunna. Na koma bakin gadon na kishingida ina dakon ta gama daidaita.
Ina cikin dube dube ya shigo shima tamkar alamara ya sanya shudiyar shadda irin shud'in atamfar jikina.
Zuciyata ta harba da tsananin gaske. Domin komin k'in da nake yi masa tun fil'azal nasan yana cikin yan ka'dan da Ubangiji ya yi masa kyaun fuska da kuma ciakken zati.
Da walwala ya ce "Amarya kin sha kyau. Nan gaba fa idan zuciyoyinmu suka zama aminai ba karamin gidan farin ciki zamu gina ba.
Tun yanzu zabin zuciyoyinmu ya zo d:aya.
Mun sanya kaya iri daya ba tare da mun shawarci juna ba".
Na zabura na cire hular na bu'de akwati ina laluben wasu kayan.
Da sauri ya karaso kusa da ni.
Ya ce "Dan Allah! Ba dan ni ba. Dan alfarmar Annabi ki bar kayan ki, sun miki kyau ainun. Ina ta fa'da miki baki zaki ta yi yau. Ni fita ma zan yi".
Magiyar da ya yi ta sace mini guiwa na fasa canjawar.
Ya bu'de flask din abinci ya ce "Wannan doya ce da kwai Salisu ne ya aiko mana.
Ya bu'de d'ayan kuma masa ce itin tamu ta mutanan Bauchi da kuli kuli.
Ya ce wannan kuma daga gida aka kawo ga kuma kunu".
Yana nuna mini jug din.
Ya sake cewa "Na tafasa miki shayi na dauko miki?"
Ina kallonsa amma ko motsi ban yi ba bare na tanka shi.
Bai yi fishi ba, ya mike ya dauko flask din shayi wanda nawa ne a cikin kaya ya dauko.
Ya koma ya dauko kofina da kayan hada shayin a leda wanda alamu suka nuna siyowa ya yi.
Ya zauna ya ce "Sauko to mu karya".
Na sake sharewa.
A hankali ya ce "Da ace kin ji nasihar da aka yi ta yi Miki, iya ta jiya kacal da kin raga mini, domin dai ko ya ya nake ni din Ubangiji ya za'ba miki ya zame miki miji. Shi kuwa miji komin kashinsa ai daraja ne da shi."
Na yi kamar ban ji ba, na cigaba da danne danne wayata.
Ya karya, ya kwashe kwanukan da ya yi amfani da su.
Ya dawo ya ce "Zan fita Asiya. Zamu je yiwa iyayenmu ban gajiya. Nasan ba zaki yini da kewa ba yau".
Ya sake cewa sai "Na dawo".
Daga hakan ya juya ko uffan bai sake cewa ba.
Sai tashin mashin dinsa na jiyo.
Yana fita na sauko na karya.
Na kai ragowar kicin.
Na tsinci kaina da son karewa gidan kallo.
D'akuna biyu ne a jere akan baranda.
Sai kuwa guda daya daga can gefe kusa da bandaki.
Sai kicin a dayan gefen.
Gini ne ba laifi gashi ya sha fenti. Kan barandar ma tayals ne. Haka kicin dinma.
A fili na ce "ko me ya hana a saka tayal a dakin?
Na kalli yadda aka k'awata
mini kicin din da kayayyaki. Na sani kuma mafi yawa dangin mahaifiyata ne suka zo da kayan.
Da sauri na nufi d'akin da yake mak'wabtaka da dakina wanda na tabbatar shine falon.
Ina shiga na ji sau'kin takaicin da nake ciki.
Domin dai falon ya yi kyau daidai na masu karamin buri.
Kujera ce irin mai L din nan. An saka ta a bango guda, da yake falon ma an saka tayals sai aka saka madaidaicim kafet a tsakiyar falon.
Ga kuma TV an mak'ala a bango, sai fridges daga can gefe.
Shikenan sai labulaye kalar kujeru da kafet din wanda suka kasance royal blue ne. Ga katon agogo mai kyau shima an kafa shi.
Na zauna ina jin da'din yadda na ga wajen. Na sani da ace Yaya J ne mijin tabbas da na kasance cikin farin-ciki mai yawa.
Na kunna fanka ganin da akwai wuta.
Na fita na nufi daya dakin da ya fi kusa da band'aki.
Na leka na ga bashi da girman wanda aka saka mini gado a ciki.
Ba komai sai labule. Gefe kuma akwatin kayansa ne da tarkacensa sai takalmansa.
Na janyo kofar kamar yadda na ganta a sakaye na fito.
Na koma falo ina jin dau'kin tv na kama ni.
Duk kokarina na kasa ha'da ta.
Dole na hakura na kashe na jona wayata a caji.
Na zauna iska.lr fanka tana kad'a ni.
Ina haka sallamar babbar mace ta saka na zabura ina amsa wa.
Na marabce ta da sakin fuska duk da dai ban gane fuskarta ba. Sannan a kallon farko na fahimci ba bahaushiya ba ce, tunda ga siffarta har tsagun da suka cika faffadar fuskarta
Na gaishe ta da girmama wa tunda na ga zata haife wacce ta fini ma.
Ta ce "Ni ce a waccar kofar. Suna na Gadatu. Ana kirana Maman Safiyanu. Mijina bara ya rasu, ina da yara maza da mata. Allah ya sanya alheri.
Allah kuma ya zaunar da mu lafiya.
Na yi k'asa da kaina. Na tashi na kawo mata cin cin da dubulan.
Bata ci ba. Na juye mata a leda ta tafi da shi.
Bata Jima da tafiya ba sai ga y'arta da alamu suka nuna zata girme mini. Gata da garin jiki. Doguwa ce sannan a koshe take ainun. Ta ce "wai Mamansu ta ce na bada kasko a kawo mini garwashi ko zan yi turare.
Na dauko na bata, fuskata a sake.
Ta kawo mini kuwa. Na tambayi sunanta ta amsa mini da cewa "Rafi'a" Na ce "To na gode miki".
Na zuba turare nan da nan gida ya kaure, ya zama na amaryar sosai.
Ba jima wa kuwa jama'ar Kangire suka zo motarsu guda, suka dinga addu'a da jan kunnena akan bawa marar d'a kunya na zauna lafiya da mijin da Allah ya za'ba mini.
Daga haka suka tafi wanda kai tsaye Kangiren suka wuce.
Haka kuwa aka dinga shigi da fice.
Hatta Babah ma ta zo kafin ta tafi Bulkachuwa ta dinga yaba yadda ta gan ni.
Tare da su Nasiru da Ihisan ta zo.
Da kulawa mai yawa ta ce "Duk abin da zai miki kada ki biye shi waya kawai zaki dauka ki sanar da ni, ni kuwa zan miki maganin matsalar. Ki yi hakuri, ki yi biyayya, ki yawaita addu'a. Sannan ban da rashin kunya.
Allah ya yi miki albarka."
Kuka kawai nake yi. Kukan da bansan dalili ba, ban saniba ko dan na ga ita ma hawaye take yi. Bansan kukan da take ta faman yi ba, na farin-ciki ne ko na tausayina ko kuwa na yadda aka juya al'amarin ne oho.
Ashe tare suke da shi ya coge a tsakar gida.
Sai da suka fito sannan ya bi bayansu ya rakasu.
*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers*
*08089965176*
*07084653262*
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*.
37&38.
Da yamma lis sai ga Yaya Ummi da tarkacen su tsintsiya da sauran kayayyaki har da su kuloli masu kyau da zannuwan gado na sani wanda aka samu na gudunmawa ne aka karo zabo mini masu kyaun cikinsu.
Ta sake gyara mini kicin din. Na bata tarkacen robobi da wani flask din roba irin mai biyun nan.
Kayan lefena kuwa turamen atamfofi biyu na bata da hijabi hadi da kayayyakin kwalliya.
Ta dinga yi mini addu'ar Allah ya zaunar da ni lafiya.
Ta bu'de jakar hannunta ta dauko wata yar roba mai dauke da garin magani kore. Ta sassauta murya ta ce ko zaki dinga shan wannan a cikin madara ko yoghurt?"
Na kar'ba na ce "Na menene?"
Ta yi k'asa da kai ta ce "farin ciki da dokin juna zai sanya muku"
Na yi maza na mayar mata cikin jakarta. Tare da cewa "Da dai ba irin wannan mutumin aka aura mini ba."
Ta ce "shikenan da har da INGANTATUN SAIWOWIN DAHUWAR GIMBIYAR KAZA. Amma zan ajiye miki. Na sani wataran zaki nema da kan ki.
Idan kuma na yi amfani da su, sai a kawo miki wani ta hannun kanwar kawata Aisha Lame mai siyar da kayan kwalliya masu daraja (oriflame).
Tasan Surayya Dee da take kawo su daga chadi.
Baki na tab'e baki, ina kallonta kawai, domin har abada ni Yabi bazan yi wani abu dan na sanya Tijjani farin ciki ba.
Muna haka ya shigo, suka gaisa sosai cikin walwala da tsokanar juna.
Bai jima da dawowa ba, ta yi haramar tafiya nata gidan.
Da yake mutumiyarsa ce.
Ya ce "Ta jira ya kai ta a mashin".
Ta galla masa harara da cewa "Ni zaka goya Yaya Bulkachuwa?Wallahi ba zan sake biye wa tsokanar da kake yi mini ba, dan ka riga ka zama k'anina".
Ya kwashe da dariya ya ce wannan kuwa shine tatsuniyar gizo da k'oki. Ke yanzun nuna mini kika yi Asiya Toro ta fini a wajen ki?"
Ta mak'e kafa'da ta ce "Ato Wallahi ka kama k'afata dai".
Ya tsugunna a gaban ta ya ce "Dai-dai ina zan kama Ummi?"
Ta yi gaba ta bar shi tana fa'din "Hmm sai ka yi kai ka'dai".
Ta goyi y'arta shi kuma ya d'aukar mata ledar kayanta.
Ya yi gaba ya na jiranta.
Da k'yar muka rabu. Cikin lallashi take ta nanata "Ki zauna lafiya, ki kwantar da hankalinki da na iyayenmu dan Allah. Kin ga dai an riga an yi auren nan. Allah ya taimake ki, ya hore miki shi. Nan da wata daya ki cigaba da sana'ar ki, domin mace mai neman na kanta ta huce takaicin babu".
Ta bata rai ta ce "kinsan dai ba'kin cikin da na kwankwada a dalilin bani da yar'uwar da aka aurar da muke daki daya. Yanzu murna nake yi kema an aurar da ke na samu abokiyar ha'di. Komai ya taso miki ni ce a hakku saura ki ce zaki bayar da ni a wajensu ta hanyar nunawa duk daya muke ni da su a wajen ki.
Gasu nan su hudu ne dakinsu daya."
Nima na bata rai na ce "To idan hakane ita kuma Ubaida dawa zata hada kai kenan?
Ko so kike ita ma ta fuskanci tsananin da kika fuskanta? Ni fa dukkan y'ay'an Babanmu ina sonsu da dukkan zuciyata".
Ta zaburo mini ta ce "Ban ce kada ki so su ba, amma ai wata kusan tafi wata".
Na yi dariya na ce "To kawai ki ha'da ni da Nazira da kuma Ubaida ki jamu a jikinki, ki dai-daita su da ni. Shikenan Kinga kin samu k'anne uku aurarru tashi guda.
Da sannu suma manyan sai su dawo cikinmu mu zama madaurin tsintsiya".
Ta yi gaba tana fa'din "To uwar Iyah! Ta ya ya zan ha'da shakikiyata da dan uba su zama duka daya ne?"
Na k'yal-k'yale da dariya tare da fa'din "Yaushe zaki dawo?".
Ta ce "sai an kwana biyu".
Na zauna ina nazarin Yaya Ummi mutumiyar kirki ce, amma rashin adalcin da manyanmu suke yi mata da kuma yadda kishiyarta ta jefa yan'ubanci a tsakanin y'ay'ansu ya sanya ta k'yamaci dan uba. Na yi mata uzziri domin ita da yaranta suna fuskantar zazzafan yan'ubanci.
Ina fatan watarana duka y'ay'an Babanmu mu zama abu guda, ina matu'kar son mu gane girman nasaba irin ta uba daya.
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
***
Bai dawo ba, sai da ya sallaci Isha.
A falo ya tarar da ni, na yi wanka na zira doguwar riga cotton mai zuwa da mayafi babba.
Na shafa turaren oudi(concentrate).
Ya kalle ni ya ce "Ranki ya da'de Asiyata".
Na galla masa harara na ce "Ba taka ba ce".
Ya murmusa ya ce "Ta Ummi ce shikenan?"
Na yi shiru domin so nake na fa'da masa abin da zai bak'anta masa rai.
Amma tunda ya saki maganar bari na k'yale shi sai idan ya sake katobarar cewa ni tasa ce zan tabbatar masa ba tasa ba ce, ba kuma zan zama tasan ba.
Ya ajiye ledar hannunsa ya fita.
Sai gashi ya dawo da kananun bowls da kuma fork biyu.
Ya zauna kusa da ni.
Ya bude ledar kamshin hadadden balangu ta buge ni.
Ya juyo mini dauri guda ya turo mini gabana. Tare da robar yogurt madaidaiciya mai sanyi, da kuma robar ruwa shima mai sanyi.
Sannan ya juyo nasa daurin. A hankali ya ce "Bismillah Amarya".
Ban kula shi ba. Na gama yaukina na dauka na fara ci. Sosai naman ya yi mini da'di, sannan kuma mai laushi ne.
Na cinye tas na bu'de yogurt na fara sha. Rabona da abinci tun karyawar safe.
Duk da an kawo mini daga gida amma ban iya ci ba.
Ganin na cinye yasa ya turo mini nasa ya ce "Kara Asiya".
Na yi kamar ban ji ba.
A sanyaye ya ce "Ba kyau a yi magana mutum ya yi kamar bai ji ba".
Nan ma tamkar ba na wajen.
Ya yi k'wafa alamun ya k'ulu.
Ganin hakan ya sanya na tashi na bar shi na yi dakina ko kwanon da na ci ban kawar ba, bare na kawar da nasa.
Ina shiga kuma na sanyawa dakin sakata.
Na cire mayafin rigar na haye gado na yi kwanciya ta.
Tunda na kwanta ban farka ba, sai da asuba shima kwakwasa mini kofa ya yi.
Kafin na fito tuni ya bu'de gida ya wuce masallaci.
Yau kam har na gama barcina na tashi k'arfe goma. Da na bu'de kofa na fito a zaune na same shi akan barandar. Babu alamun gaggawa a tare da shi.
Yana ganina ya mike da sauri yana fa'din "Bari na janyo miki, na roba da sanyi, na rijiyar kuwa dumi ne da shi.
Ya bu'de bandaki ya dauko botiki ta nufi rijiyar.
Na bishi da kallo. Mamaki nake yi dama Tijjani zai iya yin laushi haka?
Duk wula'kancin da nake yi ba ya fasa yi mini hidima.
Na sake bin kayan jikinsa da kallo. Alamu sun nuna ya yi wanka. Sabon yadi ne a jikinsa amma ba alamun karin guga. Na tabbatar yadda tela ya ba shi hakan ya saka su.
Na ja tsaki sosai. Dai-dai lokacin kuma ya zo daf da ni.
Ya ce "Asiya Toro wata rana za'a wayi gari a ga kin zama tsaka fa".
Ban kula shi ba, bare na tanka ya samu sanadin da zai jani da surutu.
Ya wuce ya kai mini bayin.
Na shiga na yi wankana na fito.
Yauma atamfa na dauko koriya Shar. Doguwar riga ce da ta manne a jikina.
Na gyara sosai.
Na gyara d'akin, na zauna. Ya yi sallamah na amsa a dole. Ya ce "Na shigo?"
Na ja tsaki, na kame bakina na tsuke.
Jim ka'dan ya shigo. Na daga kai na kalle shi. Fuska a daure na ce "Na baka izinin shigowa ne?"
Da walwala ya ce "Tunda baki zabura kin ce kada ka shigo mini ba, ai nasan kin kammala adana yan kananun abubuwan da kike yi mini k'yashin ganinsu".
Ba'kin ciki ya turnike ni.
Na murguda baki na ce "A a kiyasai ne k'arewar kankantar".
Ya zauna bakin gado ya ce "Ban da samun guri irin na ki Asiya. Ta ya ya zaki dinga rufe mini kofa, kina hayewa gadon da ba'a siya miki ba sai saboda ni, ni kuma ki bar ni da kwanan kasa. Kwana nake yi ina artabu da sauro. Amma ke babu ruwan ki, ba kya gudun maleriya ta yi mini illah?".
Na ki kula shi, bansan me yasa yake bani haushi ba, baya burge ni ko ka'dan.
Ya sake yin k'asa da murya ya ce "Ki yi kokarin kyautata lahirarki Asiya. Babu ruwan alkalami da cewar ba kya sona. Matu'kar ina kwana da ba'kin ciki ki sani kina cikin fishin Ubangiji".
Na rasa me zance masa domin dai ya sako wanda ban isa na fa'di bak'ar magana a kansa ba.
Kan tilas na share ban ce komai ba.
Ya tashi tsaye ya ce ki taso ki karya ga abin kari can a falo.
Bauchi zan je. In sha Allah ba zan wuce la'asar ba.
Za'a kawo miki abinci da rana. Ki shirya gobe zaki fara yin girki".
Sai lokacin na fashe takaicinsa da cewa "Ba zan yi ba.
Har abada ba zan dora tukunya saboda kai ba".
Babu damuwa a tare da shi ya ce "Babu laifi. Lokaci zai fayyace komai ai".
Ya juya ya tafi bai sake cewa komai ba.
Har shad'aya ina daki ban fita falon ba. Sai da cikina ya tsananta yi mini kartan yunwa.
A dole na fita. Na tarar da waina a karamin flask. Sai kunu a jug. Daga dukkan alamu siyowa ya yi.
Kan dole na zauna na karya.
Ina zaune har aka fara kiran sallar azahar. Na idar kenan sai ga almajiri yana kwankwaso kofar shigowa wajena. Da yake ni ce a farko su kuma su Mama na can ciki.
Bamu ha'da komai ba, sai kofar shigowa gidan.
Da sauri na fita na bu'de masa. Ya mik'o mini flask din abinci babba mai kyau. Wai wani ne ya bashi ya kawo wannan kofar.
Na kar'ba ba tare da na ce komai ba. Na sani abincin da ya ce za'a kawo mini ne.
Sai da na zauna a falo na bude na ga alalan gwangwani ya ji manja.
Da alamun kifi a ciki. Na ji wani iri a dalilin yunwa nake ji ba ka'dan ba. Ni kuma bana iya cin alala na koshi. Tabbas an gyara shi ne dan a burge ni. Na rufe, ina sake jin yunwa na taso mini gadan gadan.
Na yi shiru ina nazari. Sai na ji wayata na k'ara. Ina dubawa na ga Tijjani ne domin ina da lambarsa tun lokacin kwamshina da muka fara dan gaisawa. Na ki amsawa har ta katse. Ya sake kira ban dauka ba. Bai fasa ba, sai a karo na hudu na dauka a fusace na kan ga a kunnena, bayan na danna alamar amsa wa.
"Yaro ya kawo miki abinci?"
"Eh".
Na fa'da a gajarce.
Ya ce "kin ci na safen kuwa?"
"Wai ni kam jinjira ce ne da zaka dinga mini tambaya tamkar kankanuwar yarinya? Idan ma ban ci ba ai cikina ne ko? Tunda baka shawarce ni akan abinda zan ci ba, ka ajiye mini wanda ya yi maka".
Ya nisa ya ce "Asiya Toro kenan!
Cikin kuka na ce "Komai zaka ce Allah na ganinka ai".
A sanyaye ya ce "Kukan na menene Asiya?"
Na sake tsananta kukan na ce "Akan me za'a kawo mini alala? Ni bana ci".
Ya tausasa murya ya ce"Alalan gwangwani ne, saboda ke har kwai da kifi aka saka a ciki. Daga gidan abokina Abdul aka kawo miki fa, kema kuma kinsan matarsa mai tsabta ce".
Da kukan na ce "To ni ina ruwana, ni dai ba zan ci ba, kuma yunwa nake ji tunda kunun ma ban iya sha ba, ya riga ya yi sanyi k'arara."
Ya diririce ya ce "Ki yi ha'kuri bari na sa a kai wa Ummi macaroni da kayan miya sai ta daho miki yanzu. Hakan ya yi miki?"
Na yi shiru. Ina harara tamkar yana wajen.
Ya sassauta ya ce "Please mana Asiya ki ce to".
A shak'e na ce "Yanzu d'aya da rabi. Idan ya wuce uku da rabi bazan ci ba, gara yunwar ta kashe ni".
Ya dinga fa'din"Na gode sosai, bari na saka a kai mata yanzu. In sha Allah ba zai wuce hakan ba."
Ya katse wayar.
Na ri'ke wayar, haka kawai sai na tsinci kaina da mamakin yadda Tijjani yake rawar jiki a kaina. Gashi tunda na zo ban ta'ba yi masa wani alheri ko da ta magana mai da'di ba ce.
Yadda ya lank'awasa harshe yana rarrashi tabbas yana yi ne tunda ga kasan zuciyarsa. Na fara gasgata sona yake yi ba sha'awa ba.
Mintina biyar a tsakani ya sake kira.
Na dauka bayan ta kusa tsinkewa.
Da sauri ya ce "An tafi kai mata. Na ja mata kunne, na ce ta bar komai ta girka miki, tunda Nina sanya ta. Biyu da rabi zan aika a karbo mini. Dan haka zuwa uku za'a kawo miki in Allah ya yarda".
Na yi shiru. Ya numfasa ya ce "Asiya ba ki ce komai ba".
"A hankali na ce "Ina ji ai"
Ya yi kasa da murya ya ce "Me zan taho miki da shi?"
"Bana bu'katar komai na ka".
A sanyaye ya ce "Shikenan, amma na siyo miki abin da nasan zaki yi murna".
Na kyabe baki tare da fa'din "Hmm to ya yi".
"Baki ce na dawo lafiya".
A gajiye na ce "Tijjani ni na aike ka ne? Ka dame ni, in ta nine ma kada ka dawo".
Kada na dawo Asiya? Saboda ke na yi tafiyar fa! Amma idan na dawo zaki ga ni".
Ban bashi amsa ba na kashe wayata.
Na ajiye ina jin wani irin abu da bansan menene ba yana mamayata.
Uku saura na ji ana buga k'ofar.
Na zari hijabi na nufi k'ofar.
Yaro ne ri'ke da madaidaicin flash.
"Gashi in ji wani a waje".
Ya fa'da a hanzarce da alamu sauri yake kada ya yi latti tunda kayan Islamiya ne da jikinsa.
Na kar'ba na tura kofar.
Kicin ma fara shiga na dauko plate.
Sai lokacin na lura da kwalin taliya, macaroni da galan din mai dana manja.
Sai wani katon bokiti sosai mai murfi. Na bu'de na ga garin masara ne a tankade.
Daga kantar kuwa an jere robobi masu dauke da kuka, kubewa daddawa da yaji.
Sai kunshin bakar leda mai dauke da Maggi da onga da kuma gishiri.
Na yi tsam da raina. Ina jinjina wannan kokarin. Na sani Kuma Babanmu baya irin wannan al'adar domin shima baya bari a dorawa ango hidima mai yawa.
Na tabbatar a kaina aka fara irin wannan hidimar ni din ma saboda Tijjani ya yi.
Daga can gefe na sake hango buhun gishiri a cike amma kuma d'aure bakin aka yi. Na saka hannu na ta'ba na ji don na tabbatar ba gishiri ba ne.
Ina tabawa kuwa na gane shinkafa ce a ciki.
Na girgiza kai ba tare da na furta komai ba.
Na dauki abin da zan dauka, na fice.
Na zauna ina cin abincin da ya yi mini da'di ya ji kifi da albasa.
Na bu'de fridge ga mamakina sai n ganshi cike da pure water da lemon fanta da coke da kowanne zai yi shida.
Take na fahimci katon daya ya siya aka hada masa kaloli.
Na dauki ruwa da lemo na rufe.
Ina ci ina nazarin yadda Tijjani yake ta rawar jiki a kaina.
Wayata ta hau kuwwa. Kamar ba zan dauka ba sai kuma na dauka din.
Da sauri ya ce "Network dina ne ya dauke. An kawo miki abincin, kin ci?"
A shak'e na ce "Ni ban ci ba, yaji ya yi yawa, ga shi salam babu gishiri ko maggi ne oho".
Ya diririce ya hau fa'din "haka Ummi zata yi mini? To a kawo miki yoghurt. Kafin na dawo na miki girkin da kaina".
Na yi shiru.
Cikin rarrashi ya ce "Pls Asiya Toro".
Na tunzura na ce "Ai da zaka bar Toron baka tuna da cikina ba. Saboda bani da daraja. Akan me yanzu zaka fitine ni da buge bugen waya da tambayar na ci abinci ko ban ci ba. To bazan ci ba, idan na mutu ma ai baka da asara."
Ya harzuka ya ce "Botsarriyar yarinya kawai! Ana taro ki, kina sake nausawa, to kar ki ci din. Allah ne shaidar na yi bakin kokarina".
Ai kuwa na zunduma ihu tamkar gaske. Na katse wayar.
Ya dinga kira amma naki d'agawa.
Ya kira ya kai sau biyar ina gani ban dauka ba.
Daga can sai ga text message.
Kamar bazan bu'de, sai kuma na bu'de din.
"Asiya Toro ki ji tausayina! Ki daina mini irin haka. Kinsan yadda zuciyata take bugawa a dalilin kukanki da kin daukar kirana?
Ki yi ha'kuri bazan sake yin tafiya na barki hakan ba. Kuma indai na iso lafiya da kaina zan dafa miki komai kike so".
Jikina ya yi sanyi. Tsawon lokaci na kasa gane yanayina, tausayi ya bani ko kuwa mene ne?
Na bu'de what'sapp na ga anan ma ya turo mini sakonni.
Na kasa bu'de wa domin bana son na sake jin fiye da kasalar da nake ciki.
Da yamma lis sai ga shi ya dawo. Na bu'de masa kofa ya shigo dukkan hannuwansa ri'ke da ledoji.
Ban yi yun'kurin kar'ba ba. Da walwala ya ce "Asiya Toro babu oyoyo sai kallo mai kama da harara?"
Na gintse fuska na yi gaba, na bar shi.
Ya biyo ni falon dana shiga. Ya ajiye mini a gabana.
Ya fita da sauri sai gashi ya kinkimo kwanon satellite ya ajiye a tsakar gidan ina hango shi ta windo.
Da'di ya yi matu'kar kama ni. Domin na kagu na fara kallo.
Ya sake fita ya dawo rungume da kwali a kirjinsa da na yi zaton receiver ce. Dayan hannun kuma leda ne.
Na yi maza na gyara zamana na yi kamar harkokina kawai nake yi.
Ya shigo da sallama na amsa a hankali.
Ina mamakin yadda Tijjani yake da yawan sallamah.
Ya zauna a kasa a gabana tamkar uwargida da yaronta. Amma girmansa da cikar haibarsa ya sanya bai yi kama da yaron gida a gabana ba.
Tunda ni din yar mitsil ce.
Yanayinsa yafi kama da na wadda yake neman a amince masa, a gamsu da lamarinsa.
Da barin jiki ya tashi ya dauko roba a kicin, da yar wuka hadi da bowl karami irin plastic din nan mai k'wari.
Ya debo ruwa a cikin robar. Ya shigo, ya bu'de ledar da tafi kusa da ni.
Apple ya ciro guda biyu ya wanke a cikin ruwan, ya saka su a bowl din tare da yar wuk'ar ya miko mini ya ce "Fara da wannan Asiya. Ki rage yunwa kafin na gama miki abincin.
Maghariba ta kawo kai sai na dawo daga sallah zan d'ora miki. Me kike son ci?"
Ban kar'ba ba, ban kuma tanka ba.
Ya ce "Ki kar'ba mana, me yasa kike yi mini haka ne?"
Yadda ya yi maganar a dan tunzure, bansan ya aka yi ba, na tsinci kaina da mika hannu na kar'ba.
Ya sassauta ya ce "ko na yanka miki?"
Ban amsa ba, illah hannu da na saka a cikin robar na wanke.
Sannan na dauki Apple din na fara gutsura da bakina.
Ya zuba mini ido yana kallon yadda nake cinsa cikin yanga tamkar me cin magani.
Ya murmusa ya ce "Yabi yanga".
Karon farko da kunne ya ji ya kira ki da Yabi.
Na dauke kai na ce "Tsabar adawa da kake yi da hajjina shine ba zaka ce Yabi ba. Yau kuma da bakinka ya subuce ka fa'da din sai da ka ha'da da bita da k'ullin yanga?"
Ya fashe da dariya sosai ya ce "Kamar kinsan subutul kalam na yi. Tun fil'azal nafi son ce miki Asiya domin sunan na matu'kar burge ni. Yanzu kuma tunda Jabir haka yake ce miki, na sake kauracewa sunan. Bana adawa da hajjinki, amma fa bazan kira ki da Yabi ba.
Ina fatan na samu damar da zan kai ki sauke faralli Asiya. Sai ki zama Hajiya ta sosai tunda hakan shine burinki."
Na dauke kai, na gutsuri apple na ce "Da wanne ku'din zaka kai ni Makkah?
Ai indai ina tare da kai babu wani alherin da zai same ni, bare alheri irin na zuwa Saudiyyah".
Tsawon lokaci ban ji ya ce mini komai ba.
Na juyo da kallona gare shi. Na ga jikinsa ya mutu. Duk kuzarin da ya zo da shi ya gudu.
Gaba'daya ya zama tamkar an kwara masa ruwan sanyi.
Ni kaina sai na ji jikina y mutu lakwas.
Tsawon lokaci muna haka tamkar masu zaman makoki.
Da k'yar ya yun'kura ya mike ya ce "Na tafi masallaci".
Na bishi da ido, ina jin abin da nake ji a kansa na sake mamaya ta. Na kasa gane tausayi yake bani ko kuwa menene?
Nasan dai ko ka'dan babu digon sonsa a raina.
Da zai dawo ya shigo da k'aramin gas (3kg).
Daga bakin kofar falon ya tsaya bayan ya daga labule ya ce "Me zaki ci Asiya?"
A hankali na ce "Ni na koshi, akwai macaronin nan a kicin".
Bai ce komai ba. Ya saki labulen.
Da kansa ya zubo abincin.
Sai dai wannan karon a kujerar nesa da ni ya zauna. Bayan ya dauko ruwa da lemun coke.
Na kalle shi tamkar wani mai wadata ya hakince ya saka ruwa da lemu a gaba.
Ya kammala, ya dube ni bayan ya ha'diye fishins ya ce "Ki dinga jin tsoron Allah Asiya. Yanzu abin da kika yi ya yi daidai kenan? Ki saka na k'ira Ummi na balbale ta da sababin bata yi mini aikin da na saka ta da kyau ba. Ashe ma kin ci kin cika cikin ki, tsabar fitina, da son ki tayar mini da hankali shine ya sanya kike kuka da fa'din abincin bai yi da'di ba?".
Na zum'bura baki, na kasa cewa komai.
Ya yi k'wafa, bai ce komai ba.
Ya sauko ya zauna kan kafet din ya bu'de reciver ya ce "Gashi na siyo miki."
Ganin ban amsa ba ya sanya ya cigaba da bude ledojin da ya shigo da su. Kusan duk kayan abinci ne dangisu shinkafa, taliya da macaroni. Sai katon din indomie da kayan shayi. Sai kuma leda mai dauke da sabulun wanki da su omo, makilin da maganin sauro na kunnawa.
A hankali ya ce "Ku'din da abokaina suka ha'da mini ne na siyo miki settlite da gas, shine na karo kayan abinci dan mu dan tura sosai kafin su kare."
Na juyar da fuskata na ce"Madallah".
Ya yi sororo murya a dakushe ya ce "Ba zan yi wani abu da niyyar na sanya ki farin-ciki ki nuna mini kin ji da'di ba Asiya?"
Cike da iyashege na fara wage baki, dukkan hakorana a waje, ga idona na zazzarosu tamkar mai motsi a k'wak'walwa.
Ina yin hakan, ina cewa "Na yi murna Tijjani. Ka burge ni Tijjani, na ji da'di Tijjani".
Sannan na dawo yanayina na zuba masa ido na ce "shike nan?".
*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*.
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*
Ya girgiza kai, bai ce uffan ba, ya tashi ya kwashi kayan abincin ya nufi kicin da su.
Ina hangen sa ya dauko farantai ya juye kayan miya da ya barsu a tsakar gida.
Ashe har da doya guda uku manya. Sai da ya jide ya adana komai.
Sannan ya daga murya ya ce "Zan je sallar isha."
Bai jira amsata ba yasa kai ya fita.
Na tokara na dauro alwallah dan nima na sallaci isha.
Na idar na jima a zaune sannan na shiga daki na yi shirin wanka.
Na fito na shirya a nutse. Na dawo falo da nufin na sha ruwa. Aka dawo da wuta. Na kalli receiver dokin a ha'da mini ita ya kama ni.
Ina tsaye na gan shi ya dawo, na tsinci kaina da lekensa ta windo.
Na ganshi da bargo irin mai sau'kin ku'di da kuma pilo guda daya.
Kai tsaye dakin da kayansa suke ciki ya shiga da su.
Na dan ji wani iri. Na tsinci kaina da tambayar kaina da cewar wato bai damu sai ya zo dakina ba. Duk da k'arancin shekaruna ni din ma'abociyar karatun littafan Hausa ce mussaman da nake da babbar waya nake karatun littafan online. Ina ganin yanayin yadda angwaye basa daga kafa a wannan fagen. Sannan da yawa an yiwa kawayenmu aure da muka kammala k'aramar sakandire, muna jin labarin zumudin angwaye.
Amma shi wannan ko oho. Nan da da nan zuciyata ta baci a dalilin na hakaito*BAKAR TA'ADAR* Da ya saba yake yi!
Na ji tsanarsa ta sake tsananta a zuciyata.
Na dinga jan tsaki. A haka ya shigo ya same ni. Ya miko mini leda ya ce "Ga shi". Na juya baya ba tare da na kalle shi ba, bare na kar'ba.
Ya iso kusa da ni ta yadda muke jin hucin juna.
Kamshina ya mamaye wajen, da ace yana shafa turare da sun cakude sun bada kamshi na mussaman.
Baya wari, amma kuma ana dan jin tsamin maza ka'dan a tare da shi, wanda rashin tu'amalli da turare ke sababawa.
Takaici ya sake k'ume ni. Hawaye ya cika mini ido.
Ya nazarce ni. Ya nisa ya ce "Wai menene haka kike mini? Tsabar tsanarsa sai na ji hucin bakinsa mai bashi ne. Zuciyata ta taso na ji tamkar na sheka amai.
Na fa'di kan kujerar da bayana na fashe da kuka sosai.
Ya matso da sauri da nufin rike ni, na k'walla k'ara sosai. Ya yi maza ya janye hannunsa ya fasa.
Ya sassauta ya ce "ki daina yi mini irin haka Asiya. Ubangiji ya sanya mini k'yamar na ji kukanki. Fa'da mini me nake yi miki?"
Tsawon lokaci yana dakon amsa ta.
Ya kosa da shiruna ya ce "Ki yi ha'kuri komai zai dai-daita mana".
Cikin matsanancin kuka na ce "Wallahi ba zai daidaita ba. A hakan ne komai zai dai-daita?
Dube ka dan Allah! Ni gaba'daya baka burge ni".
Ya murmusa ka'dan, ya mike ya ce "Wata rana zan burge ki In sha Allah".
Har ya kai bakin kofa ya ce "Ki ci nama ne, idan kuma ba zaki ci yanzu ba, ki bu'de shi domin akwai albasa a ciki kada ta lalata shi. Ki kara ha'kuri Asiya".
Ina ganin ya fice na dinga kuka sosai mai dafa zuciya.
Ina jinsa yana ta kiciniyar jawo ruwa a rijiya.
Bayan kamar mintina talatin ya dawo ya zauna kusa da ni. K'amshin sabulun wanka kawai na ji a tare da shi ba na turare ba.
Cikin rarrashi ya ce "Kuka har yanzu Asiya?
Ba zaki yi hakuri ba! Ko wanne bawa da kaddararsa, ba ke ka'dai ba ce, ki tsananta addu'a."
Cikin kuka na ce "Addu'a sau milyan nawa zan yi?
Ai kaine matsala ta ni kam."
Ya yi shiru can ya ce "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!
Na mike da sauri na bar shi a wajen.
Ina shiga d'akin na rufe kofar da k'arfin gaske.
Na jima kafin barci ya sure ni.
Bansan yadda ya kare a inda na bar shi ba.
Washagari kuwa tunda na yi alwallah da asuba da na rufe kofata har shad'aya ina kwance duk da ba barci nake yi ba.
Sau biyu yana kwankwasa k'ofar. Amma na share shi.
Ban fita ba sai wajen shabiyu da rabi.
Shima uzzirin shiga band'aki ne ya uzzira mini. Kan dole na yi shirin wanka.
Na fito na tarar da shi a saman katanga yana ta daura kwanon setelite.
Ya ha'da zufa sharkaf. Na ja tsaki na shige band'aki.
Abin mamaki sai na tarar bayan robar band'akin da take a cike. Ya cika mini botikin wanka ya ajiye a inda ya saba ajiye mini.
Na yi shiru ina wasi-wasin yadda saurin fishi irin na Bulkachuwa baya yin tasiri akan sha'anina.
Na hakaito yadda yake ta ha'da zufa wanda na tabbatar dan ni yake yi.
Abin da nake ji mai kama da tausayinsa ya sake tsananta a tare da ni.
Bansan me yasa idan yana kusa da ni nake jin zafinsa ba. Amma ga dukkan alamu rashin iya wanka da gayunsa na cikin cikas dinsa a wajena.
Na gama uzzirin na yi wanka sosai.
Sadda na fito a falo na hango shi ya kunna talabijin yana ta kokarin saita tashoshi.
Na shirya tsaf. Kamshina ya cika dakin.
Na hau kakkade dakin.
Haka kawai sai na ji tamkar ana kallona. Na juyo ai kuwa sai ganinsa na yi yana jingine da bango ya yi mini zuru.
Na b'ata fuska na juya na cigaba da aikina.
Ya shigo ya ce "Asiya me zan miki ki daina mua'amalanta ta irin haka?
Ko arzikin gaisuwa bani da shi a wajen ki? Me ya yi zafi ne?"
Na share shi.
Ya tausasa harshe ya ce "Burodi na siyo. Na dafa shayi, na kawo nan, ko zaki fito falo?
Da kin daure ma, sai ki zo falon kina karyawa kina kallon tashar da kike so".
Ban d'ago ba, na ce "Kallo bai dame ni ba."
Ya yi shiru na sakwanni sannan ya saki ajiyar zuciya ya ce "Bari na kawo miki nan to".
Ya fita ba tare da ya jira amsa ta ba.
Bai jima ba, ya shigo da da biredi da robar butter. Ya ajiye, ya sake juya wa.
Ya dawo da kofi yana turiri.
Ya ajiye a gabana. Na kalli shayin na ga hadin kauri ya yi masa na sosai.
Amma wani sashe na zuciyata ya k'alubalanci had'awar da ya yi. Akan me ba zai kawo mini na ha'da da kaina ba kamar yadda ya mini jiya da shekaranjiya ba?
Take na yarda wani k'ullin ya shirya mini.
Ya zauna daga k'asa da rarrashi ya ce "sauko ki sha kada ya huce nasan ba kya son shayi idan ya huce."
Na zo na zauna kamar da gaske shan zan yi, na dinga juya cokalin cikin shayin.
Ya zuba mini ido yana kallon yadda gown din material din Umm Nihla kalar k'wanduwar k'wai ta karbi farar fata ta, dinkin kuma ya yi kyau sosai ya zauna mini.
*Umm Nihla mazauniyar Malaysia ce, daga can take turo kayanta masu aminci da rahusa zuwa Kano*
*Tana bada daya tana bada sari yadda ke ma zaki sami alheri*
*Tuntube ta manhajar Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*
*07020695644*
Ba zato kawai na tuntsurar da shayin.
Nan da nan kuwa shayin ya fara gangarawa inda yake zaune.
Ya zabura ya tashi. Ko ban kalle shi ba na sani ya kai k'ololuwar fusata tunda ya ga ba cikin kuskure ya zube ba.
Murya na rawa irin ta tsananin b'acin rai ya ce "Wanne irin wula'kanci ne haka? Idan ba zaki sha ba, ki bar mini mana. Almabozaranci babu kyau. Kin yi dan ki b'ata mini rai, ki saka ni ba'kin ciki! Tabbas hak'kar ki ta cimma ruwa. Raina ya baci k'warai da gaske. Sai dai ki sani, bazan sake yi miki irin wannan kyautatawar ba.
Yau kwanan ki uku a gidan nan. Daga yau kin fita daga bakunci a ka'idar shari'a. Dan haka ki fito ki dora abincin rana yunwa nake ji, ko kuma na bar ki da Ubangijin da ya wajaba miki yi mini biyayya".
Na fashe da kuka sosai domin ban zaci abin da zai biyo baya ba kenan.
Tun fil'azal na tsani ace za'a bar ni da Allah.
Cikin kukan na ce "Akan me zaka ha'da mini ba a gabana ba? Na sani ko ka jefa mini wani
abu a ciki".
Ya ja tsaki mai tsananin gaske. Ya ce "oh ina ganin tala jaurar duniya. Wai ke nan kina zaton zan miki wani abu a dole?
Ya girgiza kai ya ce "Babu macen da zan mata hakan. Sai kuma ya fashe da dariya mai sauti sosai.
Da murmushi ya ce "Asiya Toro manyan mata. Ki yi ta abu tamkar wata babbar mace. Dan Allah duka shekarun ki nawa ne?
Kin wuce sha biyar?
Ni kallon kwaila nake yi miki wacce bata gama fitar da halittun ta ba. Wacce bata kai wankan girma ya hau kanta ba. To me kike zaton zan miki da har zan baki wani abu na rashin gaskiya a cikin abin sha?"
Ba'kin cikinsa ya sake makure ni. Na sake fashe wa da kuka mai tsananin gaske.
Ya sa kai ya fice yana jaddada idan ban zo na dafa masa abin da zai ci ba, ya bar ni da Allan da ya kallafa mini yi masa biyayya.
Na jima ina zaune ina kukan ba'kin cikin takaicin da ya cusa mini.
Ga cikina sai kiran ciroma yake yi.
Ala tilas na tashi na fita bayan na goge fuskata da tissue.
Har lokacin yana ta faman hade wayar satellite din a jigin bango.
Na wuce shi fuu na fa'da kicin din.
Na tsaya ina nazarin me zan dafa ne?
A yadda nake jin yunwa zan fi son jalaf din taliya mai dan ruwa ruwa.
Dan haka na zabi kayan miyan da suka fara yin laushi na wanke na fara jajjege dan na rasa inda gireta take, duk da akwai wuta zan iya blanding dinsu. Sai dai na fi son na gansu a jajjegen.
Na yanka albasa mai yawa.
Na bare maggi duk na ajiye a kusa da ni.
Na tashi na daurayo tukunya, ya kalle ni, na galla masa harara.
Ya yi murmushi tare cewa "The great Asiya a kicin dinta".
Na share shi, na shiga falo na dauko naman da ban ci ba a fridge.
Na duba na ga ya cire albasar ciki.
Na nufi kicin din. Na zuba mai a tukunya. Na zuba albasa. Na jere komai na bu'kata a gabana.
Na kalli gas din da yake tsaye sabo dal da shi. Na fara tunanin yadda zan kunna tunda zancen gaskiya ban ta'ba kunnawa ba. Bamu taba amfani da shi a gidanmu ba.
Na yi shahadar murda wa sannan na fara kokarin kyasta ashana.
Sau biyu ashanar tana karyewa saboda rashin k'warinta.
A karo na uku ta k'yastu, na nufi bakin gas din da ita. Ai kuwa gas ya yi wani irin but da karfin gaske! Na furgita, na tsora ainun, na mike na dinga karo da fatali da kayan da na jere a gabana na yi waje a guje cikin ki'dima mai yawa.
Ya fito a band'aki ke nan, ya gan ni a guje na yi dakina.
Ya biyo ni da sauri. Fa'di yake "mene ne, mene ne?"
Ya zuba mini ido yana kallon yadda jikina yake kyarma irin na tsoro sosai.
Da sigar salama ya ce "Asiya! Nutsu ki fa'da mini. Mene ne ya ki'dima ki haka?"
Ganin na kasa magana ya tashi ya nufi kicin din.
Ya tsaya a bakin k'ofar yaga yadda ruwa ya jiqa kasan kicin din. Komai a wancakale tabbacin ta kansu ta bi.
Ga gas kuma yana ta yi fahh.
Ya rage karfinsa. Sannan ya dora sanwar. Domin ya saba girki tun yana makaranta.
Ya gyra wajen. Bai bar kicin din ba sai da ya tsaida ruwan girkin tunda ya ga taliya ta yi niyyar dafawa.
Ya koma ya zauna kusa da ita a bakin gadon. Zuwa lokacin ta dan shiga nutsuwar ta.
Ya sassauta ya ce"Asiya wai mene ne? Kadangare kika ga ni ko tsaka?"
Na zum'bura baki na ce "Wutar abin nan ne ta yo kaina gaba'daya".
Ya kwashe da dariya sosai. Hakan kuma ba karamin kular da ni ya yi ba.
Cikin bacin rai na ce "Yi dariyar ka son ran ka Tijjani, ai ko k'onewa na yi baka da asara tunda ba sanin darajata ka yi ba".
Na fara hawaye. Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi. Nan da nan ya gintse dariyar da yake yi.
Ya ce "Very sorry Asiya Toro. Abin ne ya bani dariya yadda kike yar gayu kuma wayayyiya amma gas ya yi miki wula'kanci irin haka?".
Sai kawai ya sake tintsire wa da dariyar da ta fi ta farko k'arfi.
Ba'kin ciki har mak'oshina nake jinsa. Na rasa me zan yi na sanya takaici akan zuciya da fuskarsa.
Kafin na yi magana ya yunkura ya tashi a dalilin kamshin da ya fara cika hancinmu wanda alamu ne na ya tafaso.
Bai dawo dakin ba, sai da girkin ya kammala.
Ya dawo da plate biyu a hannunsa. Ya dire a k'asa, ya sake fita. Kaamshin girkin ya cika d'akin, hakan ya sake sabunta mini yunwar da nake ji.
Ya dawo dauke da pure water da lemo akan tire.
Hannunsa kuma da fork guda biyu.
Ya zauna ya ja plate daya gabansa ya bu'de murya ya ce "Bismillah Amarya".
Na bata rai na ce " Asiya Toro dai. Ina na kai darajar amarya bayan ni din yarinya ce kwaila kuma kankanuwa".
Ya murmusa ya ce "Oh wai maganar ciwo ta yi miki ne?
Tsakani da Allah ba gaskiya na fa'da ba? "
Na girgiza kai ba tare da na kula shi ba.
Na sauko na ja abincin da yake jirana.
Na kai bakina duk kushena ban isa na ce ga inda girkin yake da tasgado ba.
Na dinga zura loma.
Sai da ya ga na kusa cinyewa ya kaikaice ya ce "Asiya Toro iyashegen ki yawa gare shi. Jibi yadda kike zabga loma kina zare ido. Me ya janye tunanin zan zuba miki wani abu a ciki Kuma?
Kunya ta kamani ka'dan. Amma na daure na yi kamar ban ji komai ba.
Na share shi. Sai da na gama na yi gyatsa, na kalle shi na ce "Na tabbatar da Yaya J ne ya dafa abincin nan, zubowa zai yi a waje daya. Sannan ya manta cikinsa har sai ya tabbatar nawa cikin ya cika."
Na saci kallonsa na ga har wata zufa ce ta karyo masa.
Zuciyata ta fara harbawa da tunanin hukuncin da zai yi a dalilin yadda yanayinsa ya nuna maganar ta buge shi.
Ga mamakina sai kawai ya yi yak'e ya ce "Ba ki yi karya ba Asiya! Domin jiya mun je gidansa ni da Salisu a dalilin an sace mashin dinsa.
A gabanmu ni da Salisu yake tarairayar Maijidda akan ta daure ta ci ayaba. Kinsan cikinta ya tsufa ba komai take iya ci ba.
Ai Jabir kam yana mutuntunta maganar tsohonsa akan Maijidda. Sosai yake sonta yake tattalinta. Har mamaki na dinga yi tare da shakkun idan har ya taba son wata mace kafin ita.
Ita ma bata jin kunyar mu din yayunta ba ne sai tabara take yi masa son ranta.
Take na gano mata irinsu ba zasu ta'ba barin mijinsu ya yi tunanin wata macen ba. Wanda duk ya samu irinsu ya gama morewa, ga cikar halitta ga shagaba ga kuma biyayyar iyaye da aure. Wanda bai samu irinsu ba ai zai dauwama cikin cizon yatsa ne.
Sannan tagomashin biyayyar da suka yiwa iyayensu ya sanya gidansu ya zama gidan farin ciki."
Maimakon na b'ata masa rai, sai ya zamana nawa ran ne yafi b'aci. Bayan kod'a Maijidda da ya dinga yi, tare da kwarzanta ta, sai na fahimci yarfe yake yi mini akan ban yiwa nawa tsohon biyayya na mutuntata aurena ba.
Na yi shiru na kasa cewa uffan. Ya gaji da jiran kalamina, ya tokara ya tashi. Bai dauke kwanon da ya ci ba, bare ya ha'da da nawa. Ya bar gidan ba tare da ya yi mini sallama kamar yadda ya saba ba.
Tun da ya fita bai dawo ba, sai bayan sallar isha. Ga mamakina sai na ji haushin hakan. Rashin dawowar tasa ta mintsinin zuciyata sai dai ban bari ta bayyana akan fuskata ba.
Ya leko ni, ina zaune a daki. Bai shigo sosai ba. Ya ajiye mini leda ya juya bayan ya ce "Sai da safe".
Bansan ya aka yi ba kuka ya k'wace mini.
Ni da kaina ban san dalilin kukan ba.
Amma so na yi ya shigo yana lallaba ni, da ro'kon na ci abin da ya siyo, ina botsare masa.
Ko duba ledar ban yi ba, na yi kwanciyata bayan na rufe k'ofar dakin.
Cikin dare na tashi da wata azababbiyar yunwa.
A gigice na janyo ledar na hau cin awara irin manyan nan ga kabeji. Da k'yar na iya janyo leda a lungun gado. Maman kawata Shafa'atu ce ta je Kano ta siyo yajin Annur food mai dan karen dad'i. Shine ta ba ni roba d'aya.
*Annur food Delicious*
*Ba iya yaji ba har da garin danwake da man Shani, da yajin daddawa*
*Tuntube su a wannan lambar dan k'arin bayani 08039183880*.
Na sani sadda ya kawo da zafinta.
Sai da na cinye tas, sannan jikina ya daina rawar yunwa. Take na tuno ashe jiya iya taliyar nan kawai na sanya a bakina.
Na jima barci bai dauke ni ba. Sai kawai na yanke shawarar na doro alwallah na yi nafilah. Na mike ina da tabbacin Gwaggo na kan sallayarta a irin wannan lokacin da bayi suke barci.
A hankali na zare sakatar na fita. Abin mamaki sai na ga Tijjani akan barandar yana sallah. Yana sujjada. Na dakata ya idar tunda ba zai yiwu na wuce ta gabansa ba.
Na jingina da kyauren kofar dakin nawa. Ina kallon yadda ya kyautata sujjadar. Tsawon lokaci bai dago ba.
Wani abu ya sake tsirga mini a kansa. Na tuna a duk sadda Gwaggo ta tashe ni cikin dare dan mu yi nafila. Cewa take yi daure ki tashi ki nemi yardar Ubangiji Yabi. Irin wanna lokacin sai zababbun bayi ne suke rabauta da yin ibada. Duk kuma abin da mai yin ibadar dare yasa a gaba sai ya ga sau'kinsa.
Allah da kansa yake saukowa sararin subhana yana shelar ina mai bu'kata na biya masa?"
Zuciyata ta sake harbawa domin ni kaina da bana son Tijjani. Kallonsa yana sujjadar nan sai da na ji wani irin abu, to ina kuma Ubangijin da ya kyautata sujjadar saboda shi.
Har lokacin kuma bai dago ba.
Na sake tuna jawabin Gwaggo da take fadin kada ki ce sai kina cikin damuwa ko bu'kata zaki yi sallar dare. Domin idan ta zame miki dabi'a, to lah shakka duk wata bak'ar k'addara da zata zo miki, sai ta zo da sau'ki, sannan komai kika roka zaki ga biyan bu'kata duk nisan jinkiri. Ban da ma dai dan adam mai shagala ne, ai ya kamata ace yana yawan yin godiya ga Ubangiji bisa dinbin niimomin da ya masa.
An yika musulmi, an baka lafiya, an kuma hore maka abin da zaka ci komin kankantar sa.
Ashe kuwa ba sai da damuwa za'a yi ibada ba.
Na nisa ina jin na fara gajiya da dakonsa.
Har zan koma daki sai kuma ya d'ago.
Na dinka fatan ace sujjadar karshe ce ba zai koma wata ba.
Ai kuwa sai na ga ya zauna, alamun attahiyatu yake yi.
Ina ganin ya sallame na yi maza na wuce a dalilin fitsari ya kama ni ba ka'dan ba. Yana zaune har na fito na shige shi. Sai dai Ina wuce wa ya sake mikewa tabbacin dama ya jinkirta mini ne na wuce.
Raka'a biyu na yi mai dauke da gajerun surori.
Na yi yan adduoina. Ban san me yasa na kasa addu'ar da nake nacin yi ba.
Na Ubangiji ya tarwatsa aurenmu. Na tsinci bakina da fa'din Àllah ka mini zabin da zai fi mini alheri. Karon farko da na yi addu'ar da dukkan zuciyata.
Na yi addu'oi, na yiwa mahaifana addu'a, na ha'da da al'ummar ma'aiki.
Na koma na kwanta ina fa'din "da wanda yayi doguwar sujjada, da wacce ta yi gajeriya, Allah dai ake yiwa, to Ubangiji ka karba mana gaba'daya".
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES.*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
Ina kwance ina jin dukkan k'uncin da yake raina yana zagwanye wa da kaso mai yawa.
Ban makara sallar asuba ba, a dalilin ya buga mini k'ofa na tashi.
Wajen k'arfe takwas da rabi na ji ana kwankwasa k'ofar dakin.
Na tashi na bu'de.
Na gan shi a tsaye. Ya kalle ni ya ce "Ki zo ki d'ora mini abin karyawa na fara jin yunwa."
Na yun'kura da nufin na yab'a masa bak'ar magana. Amma ina ganin yadda ya d'aure fuskar . Sai ya yi mini kwarjini sosai.
A sanyaye na kawar da fuskata na ce "Ni bazan sake kunna shi ba".
Ga mamakina sai ya sassauta ya ce "Wanko fuskar ki zo na kunna miki. Ai jiyan ma shi kika fara kunnawa kafin ki kyasta ashana. Sa'a ma kika yi ai da gaba'daya jkinki zai bi.
Na sake tsorata na ce "gaskiya ka siyo mini gawayi. Idan baka nan wa zai kunna mini?"
Ya murmusa ya ce "Zaki iya a hankali."
Ya dakata na yi brush, na wanke fuskata, sannan muka nufin kicin din.
Cikin nutsuwa ya ce "Sai kin gama hada komai na girkin ki, sai ki kyasta ashana sannan ki murd'a gas din ki.
Amma a fara kunna gas da sakwanni kafin a k'yasta ashana hatsarinsa yafi na had'arin mota muni."
Ina tsaye ya kunna. Sannan ya fita yana cewa "Sai ki dora abin da zaki yi".
Na yi jim ina nazarin abin da zan yi. Sai kuma na yi azamar daukan tukunya na dauraye na d'ora bayan na zuba citta da kaninfari.
Na sake nutsawa cikin nazarin me zan yi ne.
Idona ya sauka akan doyar da ya zo da ita.
Na dauko wuka na yanki ka'dan tunda manyan ne sosai.
Ina gama ferewa shayin ya tafasa.
Na juye, na mayar da doyar.
Ina zaune ina fatan na soya doyar nan ta yi kyau.
Zancen gaskiya ba saba soya doya da kwai muka yi ba.
Amma kwanaki mun kalla a wata tashar girke girke a YouTube mun gwada a gidan Nazira kuma ta yi kyau.
Na dudduba na ga babu k'wai a kicin din.
Na fita na gan shi yana ta faman janyo ruwa a rijiya.
Na cuna baki na ce "Kwai za'a ba ni".
Da walwala ya ce baki kula da shi a fridge ba?"
Ban ce komai ba. Na koma kicin na dauko bowl, na nufi falon da shi.
Na debo guda hud'u.
Cikin ikon Ubangiji na kammala aikin lafiya, kuma ta yi dadi da kyau, k'amshi ya cika gida.
Na zuba masa a plate mai zurfi irin na dafaffiyar roba, na dauko robar yaji na zuba masa a gefe. Na dauki flask din shayi na kai masa falon.
Na dawo na dauki kofin shayi da cokali da kuma cokali mai yatsu, na kai, sannan na rufe nawa a kicin din da zummar sai na yi wanka.
Na fito, na ga ya yi wanka ya shirya yadda ya saba.
Ma'ana kaya babu guga.
Takaici ya mak'ure ni. Nan da nan idona ya kad'a a dalilin tausayin kaina da ya kama ni.
Ni d'an gayu nake so wanda ya iya wanka da soyayya ba marar kintsi irin Tijjani ba.
A shak'e na ce masa "Na ajiye maka a falo".
Ya share tamkar bai ji ba. Na shige band'akin na rufo kofa da k'arfin gaske.
Ya yi sakare domin ba karamin haushi ya ji na wannan tumbatsar da take yi ba. Sannan ta yi magana tamkar da yaronta, bugu da kari ta buga masa kofa tabbacin raini na gaske ta yi masa.
Ya ha'diye bacin ran da ya taso masa.
Ya isa falon, ya tarar da wani sabon bacin rai.
An ajiye masa abinci a bude babu sayawa. Sannan duk farantan tangaran din da ya ga ni ta kasa zuba masa a ciki ta rufe sai a wnanan?
Duk yadda doyar ta yi masa kyau a ido, ga kamshin da ya cika hancinsa. Duk irin yunwar da yake ji sai ya ji ba zai iya cin doyar ba.
Ya mik'e ya fice ya bar gidan gaba'daya.
Na fito na shirya tsaf. Sannan na shiga falon da nufin kwashe kayan sannan na zubo nawa.
Sai ganin abincin na yi yadda na bar shi.
B'acin rai ya sake baibaye ni. Wato dama ba yunwa yake ji ba? Tsabar k'yashi da adawa da barcina yake yi kawai?
Na ja k'wafa.
Har zan zauna na cinye, sai kuma na yi tunanin ko sallamah aka yi da shi, ko kuma wani uzziri ya fita, zai dawo ya ci.
Na zuba nawa abincin, har na gama bai shigo ba.
Dan hakan na dauke, na kai kicin na rufe. Amma zuciyata tamkar ta fa'do k'asa.
Na hau shara, ina yi, ina hawaye tare da tir da auren dole.
Ina cikin mopping barandar ya shigo da leda a hannunsa. Kai-tsaye dakinsa ya fa'da jim ka'dan na ji yana fa'din"Asiya Toro".
Kamar bazan amsa ba, sai kuma na amsa d'in tare da ajiye aikin na nufi inda ya ke.
Daga ba'kin k'ofa na ci burki a dalilin yadda kuka yake neman k'wace mini.
Ganinsa na yi yana cin masa da k'uli k'uli ga kunun gyad'a a leda yana zuk'a.
A tausashe ya ce "Samo abu ki diba idan zaki ci".
Na rasa inda zan saka raina, da ba'kin cikinsa.
Murya na rawa na ce "Dama ka katse mini barci dan kawai ka saka ni aikin da ba ci zaka yi ba?"
Cikin rashin damuwar komai ya ce "Ci zan yi mana".
Na kasa bu'de baki na ce uffan, na juya ina jin tamkar na yi ta rusa ihu da kururuwa.
Kirjina ya yi nauyi ainun. Na dinga hawaye ina share wa. Tsawon lokaci ina zaune akan barandar nan, na kasa cigaba da aikin.
Ya fito da ledar ya kai shara. Ya wanke hannunsa, ya kalle ni ya ce "Sai na dawo Asiya Toro".
Ko kallonsa ban yi ba, bare na tanka masa.
Shima bai tsaya ba, yasa kai ya fice.
Na dinga kuka tamkar dukana ya yi.
Yini na yi akan barandar nan. Ina kaico da auren Bulkachuwa.
Sallah kawai nake tashi na yi.
Sai da na yi sallar la'asar yunwa ta uzzira mini.
Na ha'da shayi mai kauri na kwankwada.
Ina kallon doyar da ya bar mini bai ko taba ba, amma ban ci ba.
Sai bayan isha sosai ya shigo. Hakan ba karamin sake fusata ni ya yi ba.
Ina zaune a dakina ido ya yi jawur, ya kumbure saboda kukan dana yini ina yi.
Da azama ya iso gare ni yana fa'din "Asiya Toro me ya same ki, kin ga yadda kika zabge kuwa? Ga idon ki tamkar mai fama da matsanancin ciwon apolo. Mene ne yake damun ki?"
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
Da zafin rai na ce "Kai ne ka fitine ni, irin fitinar da ko maki'yata bana fatan a fitine ta irin haka."
Na sake rushe wa da kuka tamkar an fa'da mini mutuwar mahaifina.
Ya ki'dima ya ce "Me na yi miki? Fa'da mini dan Allah".
Takaicinsa ya nemi sark'e mini numfashi. Na kasa magana illah hawaye da yake zuba tamkar famfo.
Tsawon lokaci ya yi shiru yana sauraron shesshekar kukana.
A sanyaye ya mike, murya babu amo ya ce "ki k'arantawa kan ki k'iyayya ta Asiya! Bai kamata ki kuntata wa zuciyoyinmu irin haka ba.
Ki cigaba da addu'a da sannu komai zai wuce."
Har ya kai bakin kofa ya ce "kin ci abinci kuwa?"
Cikin fishi na ce "Bazan sake cin abinci ba, sai yunwa ta mayar da ni gawa In sha Allah!
Ya girgiza kai ya ce "Babu laifi".
Maimakon ya yi kwanciyarsa sai na ji yana ta buruntu a kicin.
Shude war mintina talatin sai ga shi da bowl yana fa'din "Ki dubi Allah da ma'aiki ki tashi ki ci, ba dan ni Tijjani ba. Dan Allah".
Na sassauta kukan domin Gwaggo ta cusa mana yin uzziri matu'kar aka ce saboda Allah.
Ya zauna kusa da ni sosai ya miko mini.
Cikin rarrashi ya ce "Allah ka yarda da Asiya, ka sata cikin bayin da ka yarda da su".
Jikina ya yi sanyi.
Na kar'ba, na fara cin indomien da ta yi da'di tamkar ba girkin namiji ba.
Ni da nake fa'din bazan ci ba, sai gashi na share ta tas. Da hanzari ya karbi kwanon ya mik'o mini ruwan hannunsa mai rangwamen sanyi.
Take na nemi jirin da nake ji na rasa.
Na yi gyatsa. Sai kawai na gayra na kwanta. A hankali ya ce "da kin daure kin dan yi tattaki kafin ki kwanta".
Ban kula shi ba, a haka barci ya sure ni.
Bansan sadda ya tafi nasa makwancin ba.
Washagari mirsisi na k'i yin abin kari.
Bai matsa mini ba. Ya siyo kosai da kunu ya kawo mini.
Kwanaki suka yi ta shud'e wa, har na samu sati a gidan aurena.
Har lokacin kuma ban yarda na sake d'ora tukunya ba.
Shi kuma ko ya yi fishi, ba ya jure ganina ban ci abinci ba. Kan dole sai ya nemo mini.
Ranar da na cika kwanaki goma ya fara gazawa da al'amarina. Ga shi ku'din hannunsa sun tasar ma k'are wa.
Ya zaunar da ni ya sassauta murya ya ce "Asiya yanzu a ce abincin da zamu ci ba zaki dinga girka wa ba?
Kina kallon kayan miyan can da yawa sun lalace. Ya kike so na dinga yi ne? Idan na fita tun safe na dinga bulayin abin da zan yi na samu taro da sisi dan asirinmu ya rufu amma bazan dawo na tarar da kwanciyar hankali ba? Yini nake cikin zullumi da fargabar halin da kike ciki, da abin da zan dawo na tarar.
Me yasa bani da wata alfarma ne a wajen ki?"
Na zum'bura baki ainun.
Tsawon lokaci ban ce komai ba.
Ya numfasa ya ce "Pls Asiya na roke ki, mu zauna lafiya ki kwantar da hankalinki dan Allah".
Tsawon lokaci ya dauka yana rarrashi, akan na ce masa na yarda zan dinga yin girki.
Amma ban yarda na ce masa komai ba.
Ya harzuka ya ce "Allah kai ne shaida ta."
Ya tashi ya bar ni.
A hakan na cike sati biyu.
A wannan lokacin kuma aka fara zuwa mini lalle da kitso. Na rasa a inda zamu dinga zama. Domin tsakr gidan babu bishiya kuma babu rumfa.
Baranda kuma idan rana ta bude babu dadin zama.
Dakin da kayansa suke nan ne yafi dace wa ya zama dakin da zan dinga yin sana'a ta.
Dan haka na shiga na tattara masa kayansa gefe d'aya, na kunna turaren wuta a dalilin kayansa masu datti na zube a k'asan. Na ha'da na d'aure su waje guda.
Yini na yi ina lalle. Sai yamma ya dawo gidan da ledar abincin da ya siyo mini.
Kallonsa kawai na yi, na gane ya ji haushin cika masa daki da na yi da mata.
Ya ajiye abincin ya juya.
Sai dare ya dawo lokacin babu kowa. Tuni kuma na share dakin na kintsa shi tamkar ba'a ciki muka yi ba.
Fuskarsa a daure ya tarar da ni ya ce "Asiya Toro kada ki kuma shigar mini daki da nufin yin kitso ko lalle".
Na cuna baki na ce "Idan na kuma fa?"
Ya girgiza kai ya ce "To ki kuma din".
Washagari da hantsi sai ga Rafi'a ta shigo mini.
Da walwala na karbe ta.
Ta dinga fa'din "Amarya ashe haka kika iya kunshi da lalle?"
Da murmushi na ce "Ina koya dai, idan kina so sai ki zo na yi miki".
Da babbar muryarta ta ce "Ai kuwa na gode sosai".
Tijjani na fita na shiga d'akin muka fara yin kunshin.
Kafin na gama mata har mutum ukun sun zo.
Da azahar ya dawo gidan, ko d'ar ban ji ba, balle na yi fargabar na karya dokar sa.
Ga mamakina bai shigo ba, bare ya dauki matakin da nake son ya dauka.
Amma sai na ji ya bu'de murya yana kiran Rafi'a daga falon.
Ita kuma ta shiga da saurin ta.
Wani irin abu ya d'an mintsini zuciyata.
Amma na sanya jarumta na boye abin dana ji din.
Ina dan jiyo maganganunsu, har na fahimci sun saba dama tunda yayanta abokinsa ne.
Bansan me ya ce mata ba, na ga ta fito ta shiga kicin.
Abin ya sake buguna.
Ban ankara ba na ji ta fara jajjage.
Wata babbar mace da na gama sanya wa lallen.
Ta kalle ni babu alamun wargi ta ce "Je ki karbi hidimar mijinki a hannun waccar yarinyar tun baki janyo wa kanki sanadin bacin rai ba".
Na yi yak'e na ce "Ai tare muke da ita, k'anwarsa ce."
Ta saki gauron numfashi ta ce "Tau ya yi babu laifi, na dauka babu sidi bare sadada a tsananinku. Amma dai kada ki fara saka wani lallen, tashi ki je ki marabce shi, ki bashi ruwa sai ki dawo.
Ki kula da auren ki da kyau kin ji".
Ganin ta haife ni, dan na tabbatar tana da yaran da suka zarta ni.
Hakan ya sanya na tashi na yi tamkar na je wajensa, nan kuwa dakina na shiga na zauna bakin gado.
Tamkar mai jirana sai gashi ya shigo mini.
Ya kaurara murya ya ce "Asiya Toro ba ki ji kashedin da na yi miki ba akan shigar mini daki da mata ba ko?"
Na murguda baki na ce "Ban ji ba Tijjani! Ba kuma zan ji ba".
Ya ce "Shike nan"
Na riga shi barin dakin.
Ina kallon yadda ta shirya masa abincin a tray, cikin flask mafi kyau a kicin din.
Plate din na tangaran ta saka. Maimakon da ta kai ta fito, sai ta yi zamanta suna hirarsu.
A daddafe na kammala lallen. Dan da wata ta zo ma ha'kuri na bata, na ce ina da ayyuka mai yawa ga kuma maigidan na nan.
Wani irin makakin ba'kin ciki nake ji har cikin mak'oshina.
Duk da bana son Tijjani amma na ji zafin kiran Rafi'a da ya yi. Mussaman umarnin yi masa girki da ya bata.
Ina da eani irin kishi tun ina karama ta. Har ta kai Gwaggo kullum cikin yi mini addu'ar samun sassauci take yi.
K'asan zuciyata kuma ban yarda kishinsa nake yi ba. Tunda ba wai ina sonsa ba ne. Kawai wula'kanta ni da ya yi ne ya mini ciwo.
Sai da ya gama ta fito da kwanukan abincin.
Da murmushi ta ce mini "Na gode sosai Amarya. Sai na sake shigo wa".
Ga mamakina na kasa yi mata ko da yak'e ne.
Murya a dakushe na ce "Madallah".
Da daddare ina falo, ina kallo ya dawo. Sai da ya yi wanka, sannan ya shigo ya zauna.
Cikin nutsuwa sosai ya ce "Asiya na ce kada ki kuma shiga mini daki da nufin yin lalle ko kitso amma baki ji ba ko?"
Yana rufe baki na ce "Tijjani ban ji ba, ba kuma zan ji ba, ka yi abin da zaka yi marar tsoron Allah kawai".
Ya yi mini k'uri ya ce "Me na yi miki na rashin tsoron Allah? Ni ban fa'di hakan akan ki ba, sai ke zaki fa'da mini hakan?"
Babu fargaba na ce "Ina da tabbacin bana aikata kaba'ira, kai kuwa kaba'irori nawa kake aikata wa? Tsabar shaharar da ka yi a BAKAKEN TA'ADODI har gidan auren ka ma bai tsira da sharholiyar ka ba".
Ransa ya baci. Amma da ya fahimci kishin Rafi'a ne ya k'ume ta, sai farin-ciki ya maye gurbin bakaken kalamanta. Da alamun da Rafi'a zai yi amfani ya dinga rama wula'kanta shi da take yi.
Ya girgiza kai ya ce "Sharri dai dan aike ne. Mussaman wanda aka ginasu akan zato da jita jita."
A kufule ainun na ce "Ba batun sharri a lamarinka. Iya karshen cuta an yi mini. Amma na barwa Allah al'amurana"
Na fa'da hawaye na subuce mini".
Ya kasa cevwa komai.
Tsawon lokaci mun yi jigum jigum! Sai hawaye da suke tsere a kan fuskata. Babu kuzari ya taso ya dawo kusa da ni sosai ya sassauta murya ya ce "Kinsan bana son kukan ki Asiya!
Na tari numfashin sa a zafafe na ce "A gidan uban waye baka son kukan nawa? Makaryaci, mugu, bunsuru..!
Ai ban karasa ba, na ji wani irin gigitaccen mari a fuskata. Wanda ya sanya na zunduma ihu a matu'kar ki'dime.
Cikin fishi mai yawa ya ce "Kin ci uwar karya kin kwana da yunwa Asiya. Kin yi ka'dan ki zagi ubana, ki wanye lafiya. Ashe togaciyar da na yi miki kwanaki a zauren gida baki ji ba?
Wallahi ki mutunta ta kan ki, ki kame bakinki daga zagina. Ni zaki ce wa a gidan uban wa? Ubana zaki zaga? Baki isa ba, rashin kunyar ki ya tsaya a kaina. Ni da kike ganina nasan mutuncin iyayena da gaske, ba wai yaudarar ina sonsu a baki ba, amma na kasa kare musu martabarsu a bayan idonsu ba."
Ya mike tsaye ya ri'ke kunnensa alamun gargadi.
Da kumfar baki ya ce "Billahillazi kika kuma yi mini lalle a daki sai na wula'kanta ki, ke da gayyar ta ki.
Sannan yau ne rana ta karshe da zaki yi gigin zagin iyayena. Ki bari, bana so! Idan kuma kin ki ji, lah shakka ba zaki k'i ga ni ba".
Ya tafi ya bar ni ina kuka mai tsananin gaske, domin ba k'aramin shigata marin ya yi ba.
Tunda ga wannan lokacin gaba ta k'ullu a tsakaninmu mai tsananin gaske.
Ya fita daga al'amarina gaba'daya. Baya bin ta kaina, yana dawowa daga sallar asuba zai fice tun gari bai yi haske ba. Ba zai dawo ba sai wajen Tara. Nan ma yana gama uzzirinsa zai sa kai ya fice. Ba zai dawo ba sai dare.
A hakan na fuskanci wajen gini yake zuwa. Fitar asubar ne bansan me yake yi ba. Zuciyata har kissima mini take yi lalata yake fita yi. Dan haka na sake wasarsa, na sake jin haushinsa.
Bana girki sai dai na saka almajiri ya siyo mini, abincin siyar wa tunda ana yi a makwabta.
Ina samun lalle da kitso. Ban kuma fasa yi a dakin nasa ba. Sai dai kafin ya dawo sun tafi, ni kuma zan gyara masa dakin, sai dai k'amshin muhallabiya ya kama dakin.
Bai ta'ba magana ba. Ban sani ba, ko dan bai dawo ya tarar da mu a ciki ba. Ko kuwa ya hakura ne?.
Cikin wannan yanayin da muke ciki na yi matu'kar rame wa. Na yi baki. Kullum cikin kuka da b'acin rai na ke.
A ranar da na cika wata guda a ranar Dada ta zo ganin dakina.
Bulkachuwa da kansa ya dauko ta a mashin ya kawo ta.
Ta dinga yaba tsarin dakunan.
Amma ta kasa gamsuwa da yanayinmu. A sanyaye ta ce "Mai sunan manya Yabi ta sake kankace wa, ta yi duhu, duk da ita fara ce kal.
Kai ma dube ka, babu wani annurin angwanci tare da kai."
Ga mamakina sai ya sassauta murya ya ce "Kowa da yadda yake fuskantar kalubalen duniyar nan ai.
Me nake da shi da zan jiyar da Asiya da'di bare na samu nutsuwa da ita. Na barwa Allah komai. Idan na mutu Dada na yafe miki wannan ha'din da kika jagoranci aka yi. Cike nake da fargabar kada auren namu ya sake d'aid'aita zumuncin gidan Marina."
Dada ta dauki salati tana fa'din "Ashe har yau baku shirya ba? Ashe ba kalau kuke zaune ba, shi yasa ka dinga zille wa idan na ce ka kawo ni gidan ka?".
A hankali ya ce "k'alau muke Dada."
Ta kalle shi ta ce "Tashi ka bamu wuri."
Bai yi musu ba, ya fita din.
Ta kalle ni ta ce "Haba Hajja Yabi. Me yasa ba zaki kwantar da hankalin ki ba? Mai sunan manya son ki yake irin son nan mai tsananin gaske. Ban ta'ba ganin abin da ya sanyaya shi irin lamarin ki ba.
Tun wanccan satin na je gidan Ubaida tana zaune k'alau da mijinta. Sai ke ce zaki kunyatamu?"
Na rushe da kuka sosai na ce "Ita mijinta ai baya wula'kanta ta, baya yi mata sanadin da zata kwana ta yini da yunwa. Mijinta mai kamun kai ne. Amma ni kuwa fa?"
Kuka ya ci k'arfina sosai.
Duk son kan da Dada ta wanzu tana yi a tsakaninmu da su Bulkachuwa a wannan ranar na ga damuwa mai yawa akan fuskarta. Na ga alhinin halin da ta gan ni a ciki a jikinta
Ta bu'de baki ta kira shi. Ya amsa ya shigo.
Ta ce "Me ka ke yiwa yarinyar nan haka? Ai farkon zaman bata birkice ba, tunda kowa ya zo sai ya ce Yabi tana zaune cikin walwala kamar ba ita ba. Me ya jefa ta cikin wannan tashin hankalin?"
Da rashin kuzari ya ce "Zagi irin na tsamar nama ta yi mini. Hakurina ya k'wace na mare ta. Shike nan fa! kuma yau zancen nan an kai sati biyu. Amma ta taurare ta k'i barin abin ya wuce."
Ya fa'da cikin damuwa mai yawa.
Dada ta ce "Ai baka rarrashe ta ba. Baka ha'diye fishin ka dan ka kawo masalaha ba."
Da sauri ya ce "To na yarda, na yi kuskure, taya ni bata hakuri. Bazan sake dukan ta ba, amma ita ma kada ta sake zagi na".
Tausayinsa ya cika Dada domin ta sake fahimtar ya fa'da matsanancin soyayyar Yabi.
Ta nisa ta ce "kin ji abin da ya ce Yabi. Ki yi ha'kuri, komai ya wuce ba zai sake ba.
Na cigaba da kuka sosai. Ina son na fa'da mata ni girkin da ya sanya aka aka yi masa ne, yafi nukurkusa ta fiye da marin. Amma bansan dalilin da ya sanya na kasa fadar wannan maganar ba.
Ta dinga rarrashina tamkar ba Dada da bata yi mini sassauci ba.
Sai da na yi shiru. Sannan ta kalle shi a zafafe take yi masa magana.
"Idan har ka kuma dukanta, to ka tabbatar zan aikawa uwarka ta zo, tunda ka nuna ban isa ba. Ai ba'a baka ita dan ka dinga gwada mata k'arfi ba. Duka duka ma nawa take ne Yabin? Ba zaka yi hakuri da kuruciyar ta ba?"
Ya yi shiru ya kasa bu'de baki ya fa'di abubuwan da nake yi masa.
Karshe ya buge da bata hakuri da al'kawarin zai canja.
Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*.
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES.*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
Tsawon lokaci kafin su samu na yi shiru.
A kokarin Dada na son na warware sosai, sai ta fasa tafiyar ta ce ya yi tafiyarsa sai yamma ya dawo ya mayar da ita gida.
Ya fita, sai kuma ya bu'de baki ya ce"Asiya".
Na yi shiru kamar ban ji ba.
Dada ta sassauta ta ce "Kiran ki yake yi fa Yabi.
Ki na son ki k'one ne? Girman sa yawa ne da shi a wajen ki fa".
Na tashi bayan na cuna baki tamkar na buta.
Da fishi sosai na tsaya a gabansa.
A sanyaye kuma murya k'asa ya ce "Zan je na samo ko kifi ne, ki yi girki dan Allah".
Nan da nan na ce "Wallahi bazan dafa da kai ba".
Ya ce "Shike nan ki yi muku. Hakan ma na gode sosai".
Ya fita na bishi da harara. Ba'kin cikin yadda na takarkare na yi masa doya da k'wai ya k'i ci, ba k'aramin cizo na yake yi ba har yanzu.
Sannan girikin da ya sanya aka shigar mini kicin aka yi masa, sai ya gane ni ba irin matan da za'a yi musu hakan ba ne.
Bai wani jima ba, ya dawo. Sai da ya shiga kicin din sannan ya fito ya yi dakina.
Dada ta zuba mini ido alamun na tashi na bi shi.
Akan dole na je din.
Ya mik'o mini leda mai d'auke da sink'in sabulun wanka da kwalin TURAREN
Ismiyaki.
Na kar'ba galala.
Ya ce "Idan zata tafi sai ki bata".
Na gatsina baki na ajiye a bakin gadon ban ce komai ba, na fita na bar shi a tsaye, ya yi wani iri abin tausayi!.
Ya fito ya dan tsokani Dada sannan ya fice.
Zafi ya sanya na yiwa Dada shimfida a baranda.
Ta fito, muna hirarmu ina gyaran kayan miya.
Ina tunanin artabun da zan yi da attaruhu yayin greting. Don kuwa indai na murtsika attaruhu sai na kwana na yini hannuna na yin mini zugi.
Kwatsam aka kawo wuta. Cikin karambani da giggiwa na ha'da bilandar na fara markade.
Sai da na zuba shinkafa a dalilin ruwa ya tafaso.
Sannan na koma wajen Dada.
Da murmushi ta ce "Oh ashe dai da rabon za'a samu mai tu'amalli da injin markade na zamani a jikokina".
Na yi dariya tare da cewa "Dada kenan.
Bari na zauna ki d'ora mini karatu, ina kewar karatun ki."
Ta gyatta, na zauna kusa da ita.
Ta ce "Tunda Ubangiji ya sanya na ga auren ki har ga ni a gidan ki.
To zan 'dora miki karatun da har abada kin wuce yin boranci a idon namiji. Ban ta'ba koya wa kowa wannan addu'ar ba, saboda jarraba namiji ake yi da ita k'warai da gaske. Kema dan ina son ki tsare mijin ki, daga sharholiya ne!".
Ban ce komai ba.
Ta yi waiwaye dan ta sake samun tabbacin babu me jin abin da zata furta.
Ta matso kusa da ni ainun.
Murya k'asa kasa ta ce "A yayin da kuka shiga mayafin aure sai ki yi Bismillah ki ce "Allah daraja, MA'AIKIN Allah daraja a taimake ni akan aure. Zan jarraba y'an maza wane.. Ibnu wance.
Ki kamo ainihin sunan sa da sunan babar taku, sai ki tofo yawun bakinki akan yatsan sai ki yi matsi da wannan yawun addu'ar. Amma a zuci, zaki yi fa". Ta fa'da da dukkan zuciyar ta.
Duk da na saba jin karatun Dada wannan ya yi matu'kar sanya ni mamaki da dariya.
Amma na sanya jarumta na maze, na yi k'asa da kaina a zuwan kunya ce ta hana ni sukuni.
Ta kuwa dage ta ce "Ba kunya zaki ji ba Yabi! Na baki wannan fahamin ne dan na taimake ki, ku zauna lafiya. Amma fa kada ki yarda ki dinga jansa a k'asa. Domin k'arfin addu'ar yawa ne da shi tamkar yankar wuka take".
Na k'yal-k'yale da dariya saboda bilhakki take maganar zan jarabta shi da wannan karatun surkullen.
Sai da dariya ta tsagaita mini na ce "Allah ya bada lada Dada. Amma ni bazan yi a kansa ba. Baya sona, bana sonsa. Kowa harkar gabansa yake yi."
Ta dauki salati tana fa'din"Ashe har yau baku zama d'aya ba? Tisa ki yayi a gaba yake kallon ki kawai?
To idan na tafi zan fara tsayawa wajen Malam Nata'ala na ji ya ya matsayin aurenku.
Domin nasan duk ma'auratan da suka shafe kwanaki arba'in basu hadu ba, tabbas aure ya haranta. To ku kwanaki talatin da biyu da aurenku. Zan je na sake jin fatawar kada aje ko auren ya b'aci ba'a sani ba".
Na yi shiru domin na kasa gane bayanin na ta. Ban ce komai ba, domin kuwa ban ta'ba jin makancin hakan ba.
Ta numfasa ta ce "Yabi kin san duk macen da ta ki d'agawa mijin auren ta k'afa. Zata zama makamashi ne a cikin wutar jahimu?"
Na yi shiru tare da b'ata fuska. Ta sake ce wa "Wannan hukuncin lahira ne. A duniya kuwa babu ita babu ganin hasken rayuwa tunda malaiku dubu maitan ne zasu yi ta kabarbari suna d'ebe mata albarka. Kin san kuwa ko limamin unguwarku ne ya tsine miki, kin yi hannun riga ke da walwalar rayuwa bare kuma ma'asumai irin malaikun Allahu".
Jikina ya yi sanyi da wannan karatun na karshe. Wanda babu kuskure ko shaci fa'da a cikinsa.
Amma da na tuna ai bai ta'ba nema na hana ba, ke nan bana cikin tsinuwar malaiku, sai na samu sau'kin tsoratar da na yi.
Kafin ta sake magana na zabura na tashi ina ce wa "Bari na duba girikina".
Na tace shinkafa, na yi k'asa da wutar na mayar.
Na duba ledar da ya ajiye na ga salak da kuma ledar soyayyen kifi.
A gurguje na yanka na wanke da gishiri na bar shi a kwandon tsane wa bayan na rufe.
Daidai lokacin na sauke sanwar, na d'ora ta miya.
Na juye a flask na fito da tukunyar na jika ta da ruwa.
Na ce "Dada mu shiga ki yi kallo. Rana ta fara kusantomu.
Ta ce "Zan tashi dai saboda rana, amma ba dan na yi kallon shagala ba.
Na kunna na kamo mata wa'azin Malam Guruntun tana saurare can ta nisa ta ce "ya iya karatu kuwa. Amma dai wannan ba namu ba ne ko Yabi?"
Cikin k'arfin hali na ce "Musulmi ai d'anuwan musulmi ne Dada. Bare wannan bijimin Malami ne. Ke dai ba ki ji abin da Allah da ma'aiki suka ce ba ne na ki?"
"Ta kyabe baki ta ce"Masu daddagen wando ai tsakaninmu da su sai a lahira. Tunda suna raina karamar shehu".
Dariya ta kwace mini. Na dinga yi sosai.
Na canja tashar cikin sa'a kuwa sai ga sheikh Mak'ari yana bayani irin wanda ta gamsu da shi.
Na gama abinci tsaf. Bamu ci ba sai da muka yi salla sannan na kawo mana. Tare ta ce na zuba mana. Muna ci tana yaba girkin nawa.
Tana kuma ta yi mini maganganun da suke nuna girman da miji yake da shi.
Ban ce uffan ba, sai da ta ce "Ki kwantar da hankalinki ki zauna lafiya. Nan da kwanaki ka'dan zan sake kewayo ku. Idan har kika bari kwanakin auren ki ya kai arba'in baki bari ya ri'ke hannun ki ba. Tabbas zan fa'dawa mahaifin ki. A san halin da kuke ciki. Kada ku fara zaman haranci".
Na fara kuka tare da ce wa "Ba ruwan ki Dada! Kada ki ha'da ni da ubana, kada ki janyo mini fishin sa."
Ga mamakina sai ta sassauta ta ce "Idan kuwa har irin haka kike gudun fishin uban ki. Kamata ya yi ki guji fishin Allah fiye da hakan. Ai ba Babanku ba ne ya hukunta faruwar al'amarin ba. Allah ne da kansa. Fishin Ubangiji akan bawansa kuwa yana nufin tabarbarewar dukkan al'amuran rayuwa".
Na kasa bu'de baki na ce "Bai ta'ba nuna wa yana da bu'katar hakan daga gare ni ba. Saboda yana samu a waje. Sai kawai na sake tsananta kukan da nake yi. Domin har ciki mak'oshina nake jin ba'kin cikin halin da nake ciki.
Har la'asar ta kawo kai, bata fasa sakin maganganu ba. Wasu na gaskiya, wasu na barkwanci wasu kuwa masu nauyi ne. Ita kuwa ko a jikinta.
Ina kuka sosai amma bata damu ba sai ce wa ta yi "Da kin san kanki ai da tuni kin mayar da shi bita zaizai. Mata irinmu masu k'aramin ruwa ai mafi yawa murza maza muke yi. Kin ga duk haiba da siffar mijin ki. Da kin kwantar da hankalinki, kina masa biyayya, kina ba shi kanki ai wataran ma sai ya shirya zai fita, idan kika ce kada ka fita ce wa zai yi to."
Na cuna baki na ce "Da dai ba dan-iskan duniya ba ne".
Ta kuwa zabura ta jefe ni da kofin kusa da ita.
A ki'dime ta ce "Mijin ki kika zaga kai tsaye babu nadama bare shakka?
Tabbas kin kafurta, kin halaka Yabi. Dole sai kin sake karban shahadar shiga musulunci.
Na kasa kunshe dariya ta. Na k'yal-k'yale da dariya sosai.
Ranta ya baci k'warai da gaske. Ta shiga share hawayen takaici.
Murya na rawa ta ce "Ki aikata kaba'ira sannan ki yi dariya? Saboda ku yaran yau babu darhamin imani a zuciyarku?"
Na ha'diye dariyar a dalilin kukan gaske take yi.
Da sanyin murya na ce "Ki yi hakuri Dada."
Ta ce "Na ha'kura amma, ai dole ki sabunta musuluncinki Yabi. In kuwa ba hakan ba, tabbas kin zama arniya.
Cikin k'arfin hali na ce "Ba ni kalmar shahadar na sabunta din."
Ta rike baki ta ce "Wace ni na shiga sahun Malamai. Ni almajira ce me neman sani. Gaban babban malami za'a kai ki ya baki shahada ki kar'ba. Ko kuma ki yi tuba a gaban mijinki ki nemi afuwa sannan ya baki kalmar ki kar'ba".
Na bata rai na ce "Haba Dada tunda ba'a gabansa aka yi ba, ina dalilin sai ya ji. Tunda kin ce na sabawa Allah. Ki bari na ce Astagafirillah! Amma kada ki fa'da masa. Dukana zai yi, son girmansa yawa ne da shi".
"To shikenan bazan fa'da masa ba.
Amma ki tsananta intigifari Yabi".
Daga haka muka yi haramar sallar la'asar.
Na tattare kwanukan na share wajen kafin ta fito daga bayi.
Mun jima da idar da salla sannan ya dawo.
Kallonsa kawai na yi na gane bai ci abinci ba.
Dada ta dinga yi masa barka da dawowa. Ya amsa yana murmushi wanda na tabbatar na yak'e ne.
Ta zuba masa ido ta ce "Ya na ganka haka ne?"
Ya ce "Babu komai. Sauri nake yi kada ki ce ban zo da wuri ba."
Bata ba shi amsa ba ta kalle ni.
A dole na ce "Sannu da dawo wa".
Ya amsa da walwala sosai".
Ya ce "Na kai ki yanzu, ko na watsa ruwa?"
A tausashe ta ce "Yunwa kake ji, ka fara cin abinci, nasan baka shiri da yunwa".
Ya yi k'asa da kansa. Bai ce komai ba.
Ta ce "Yabi ki kawo masa ruwa da abinci mana".
Na daure fuska matu'ka da gaske sannan na ce "Baya cin abincina ai".
Ta fara fa'din "Allahu Akbar kabiran, wa subhanallahi bukuratan wa asila. Wanne irin zama kuke yi ne na kafirci ni Binta?
Baya cin abincin ki sai na wa to?"
Da yake abin na yi mini ciwo sosai. Cikin rawar murya na ce "Sai na y'ar iska mana."
Dada ta kalle ni da kyau tamkar me yin nazari. Sannan ta mayar da kallonsa kansa. Gaba'daya ya yi laushi tabbacin ya buga bai samu abin da ya sanya a bakinsa ba.
Tsawon lokaci ta ce "Kira mini lambar Alhaji. Da alamun al'amarin naku ya yi munin da ba zan iya gyara shi ba."
Tana rufe baki na fashe da kuka Ina cewa "Saboda son kai sai ki kira mahaifina ki bata ni a wajensa, ki tayar masa da hankali. Alhalin tunda na zo gidan nan ba abin da nake ga ni sai wula'kanci da tozarci. Ai ni an cuce ni karshen cuta kuwa".
Na fa'di hakan cikin kuka mai tsananin gaske.
Ta saki ajiyar zuciya ta ce "To kira mini Hauwa tunda ita din kin yarda uwar ki ce".
Shima cikin sauri ya ce "A a Dada kinsan dai bayan ta zata bi. Sannan fishi zata yi da ni! Yanzun ma ya nake fama ne a rayuwar nan bare kuma ace ina cikin fishin uwa. Rabu da ita kawai Dada. Idan na fa'di na mutu ba shi kenan ba. Sai ta je ta auri wanda take so."
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWIA SAIWOWIN SANYI*
AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU*
*AKWIA SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.
Yadda ya yi maganr ya yi matu'kar dukanmu. Ko ni da ba sonsa nake yi ba. Ya bani tausayi kwarai da gaske. Bare Dada da kowa yasan bata jure ganinsa cikin damuwa.
Ta rasa inda zata tsoma ran ta. Ta kasa cewa komai.
Can ta ce "Tashi ki kawo masa abinci".
Na zum'bura baki ainun na ce "Ba fa ya ci Dada. Akan me zaki ce sai na ba shi, salon ki sa zuciyata tafi hakan b'aci tunda barinsa zai yi".
Da sauri ya ce "Wallahi bazan bar shi ba Asiya. Ci zan yi, yunwa nake ji rabona da abinci tun daren jiya. Na gaji da abincin siyarwa, ban saba ba, tun fil'azal."
Jikina ya mutu murus.
Cikin murya marar amo ta ce "Kin ji ya rantse zai ci".
Na sake d'aure fuska ban tanka ba.
Ta kalle shi ta ce "Kai me yasa idan ta dafa kake k'in ci?"
A hankali ya ce "Zubin wula'kanci ta yi mini. A bu'de kuma a farantin roba".
Dada ta fara ce wa "Eh dole ranka ya b'aci, duk namiji sarki ne a gidansa komin kashinsa kuwa. Lalle Yabi wula'kanci da tozarcin ki kabiran ne".
Nan da nan ya ce "A a Dada ya kuma zaki sake ankara ta. Ai ban ce ki tayar mata da hankali ba. Ke dai kawai ki rarrashe ta, ai dazu ma kin ce yarinya ce zata daina ne".
Ta yi sukuri tana kallonsa cikin tu'ajjibi mai yawa.
Jin ya fa'di hakan, na k'ara kukana na ce "Bar ta ta yi son kan da ta saba yi a tsakaninmu.
Kuma kai ma dan me baka fa'da mata ka kira budurwarka har falona kun yi hira ba. Me yasa baka fa'da mata bayan hakan da ka yi, bai ishe ka ba. Har umarnin ta yi maka girki a kicin d'ina ka bata?"
Na fada cikin kuka sosai.
Dada ta dauki salati tana ce wa "A cikin gidan auren ki, ya yi irin wannan ba'kin zunubin? Eh lallai ba laifin ki ba ne, nasa ne. Wato ni a lokacin da nake kamar ki yaushe za'a mini hakan na bar al'amarin salin alin ba tare da na fitarwa da ja'irar jini ba. Na goge hawaye na ce "Ban yi komai ba na kai k'ara wajen Ubangiji. Sannan kuma har abada bazan sake ba shi abincina ba. Ba kuma zan huce ba, daga nan har na tsufa".
Dada ta yi maza ta ce "Eh to ba dan ina jin tsoron kada kwanaki arba'in din ta cika auren ya samu karaya ba. Dana goyi bayan wannan tutsun na ki. Amma yanzu ki yi ha'kuri, ki yafe, ki huce! Ubangiji yana son masu afuwa da sassauci. Idan ya kuma ni da kaina ne zan sanar da iyayenku. Ai bazan yarda ki yi irin wannan zaman na kuttu ba".
Na girgiza kai na ce "Ai Dada babu maganar huce wa. Babu ni babu sake shiga shirginsa tunda juninsa wula'kanci da nema mini raini ne".
Kafin Dada ta yi magana ya yi fit ya ce "Ban san zaki ji haushi ba Asiya. Na rantse ban yi da gayya ba. Amma tunda ban kyauta ba. Allah ya baki hakuri. Ba zan sake ba."
Na dauke kai ina harara tamkar idona zasu fa'do k'asa.
Ya ce "Dada ki ce ta yi hakuri mana."
Ta nisa ta ce "ki yi ha'kuri kin ji. Ta shi ki ba shi abincin ba dan halinsa ba. Dubi Allah, ki duba Manzonsa."
Ban sake ce wa komai ba. Na mik'e din.
Ban san ya aka yi ba, da na isa kicin din na samu kaina da d'auko plastic plates masu fadi guda biyu.
Na zuba masa na rufe na dora cokali a kai. Na dauka na nufi falon. Ina jin Dada na fa'din "kada ka sake kuskuren saka wata ta yi maka girki. Ban da sakarci ma ina kai ina doguwar magana da ita, bare har kasa a yi maka girki akan idon matar ka. Ai gwara da ta murd'e maka. Kasan halin fa'dan ta ai, bare kuma an tsokano ta".
Murya ba amo ya ce "ki bar maganar nan, sai na zo dakin ki. Yanzu dai lallaba mini ita Dada kawai".
Na shiga na ajiye a gabansa. Ya saki murmushi ya ce "
"Madallah da Asiya". Na cuna baki na dauko ruwa na ajiye masa a gabansa na koma gefe na zauna.
Ya dauki abincin ya dinga ci tamkar bai ta'ba cin abinci irin hakan ba. Cikin kankanin lokaci ya tashi da uban abincin da na danne farantin da shi.
Fanka na kad'awa amma zufa sai yanko masa take yi.
Ya ta'ba ruwan ya ji sanyi sosai.
A hankali cikin kwantar da murya ya ce "Asiya idan kina da ruwan Lipton taimake ni da shi mana please" .
Na dauke kai, kamar bazan amsa ba, sai kuma na tashi na fita ba tare da na ce komai ba.
Dada ta bini da ido tana fa'din "Kasaitacciyar mace. K'aramar halitta mai babban al'amari".
Sai da na isa kicin na yarda na yi dariya.
Na dauko kofi da cokali. Sannan na dauki filas din ruwan zafin.
Na sake ajiye wa a gabansa ba tare da na ce komai ba.
Na zauna na dauki waya ta ina danne danne.
Dada ta ce "Ba ki kawo masa sigari ba."
Kafin na yi magana ya ce "Idan zata dafa take zubawa, dan rage masa tasiri."
Ta murmusa ta ce "Yabi mutanan turai".
Shi ma ya taya ta murmushin. Ni kuwa ban ce komai ba.
Ya kammala, ya yi gyatsa tare da hamdala.
Ya ce "Har na ji ni a duniya. Na gode sosai Asiya. Allah ya yi miki albarka."
Ban amsa ba. Dada ta amsa da sauri tare da fa'din "Barka da arziki Yabi! Kin rabauta tunda kika samu farar addu'a daga mijin ki".
Na yi shiru ban tanka ba. Yayin da shi kuma ya mik'e yana cewa "Bari na canja riga na zo na mayar da ke."
Yana fita Dada ta ce "Yabi maganar nan ta wuce. Ku zauna lafiya. Ko makaho ya zo gidan nan sai ya gane mijin ki na son ki".
Cikin fishi na ce "Baya sona Dada. "
Ta murmusa ta ce "Yana son ki. Ke ma da gangan kike inkarin hakan. Yanzu bazan fa'dawa kowa ce wa ba k'alau kuke zaune ba.
Amma fa idan na dawo gidan nan, na fahimci baku shirya kanku ba. Ku tabbatar sai na ha'da muku iyayenku da Malamai. Dan bazan yarda da zaman kafirci ba."
Na dinga k'unk'unin babu ruwanta da shiga al'amarin da bai shafe ta ba.
Ta gyada kai ta ce "komai zaki ce Yabi ki fa'da. Amma ki sani, ni bazan ha'inci shari'ar musulunci ba. Tilas ne ku bi ka'idojin shari'a a kan aurenku."
Ya lek'o daga bakin k'ofa ya ce "kin gama Dada, ko na je na dawo bayan maghariba sai na kai ki?"
Ta yun'kura tana fa'din "Na gama, yinin ya isa, ba sai na kai almuru a waje ba."
Nima na bi bayan ta muka fito. Na kalle shi ya sanya jallabiya. Ko mai bai shafa ba, bare tuarare. Àllah ya sani ina son na dinga jin k'amshin na tashi a jikin mutum.
Na shiga daki, na d'auko ledar kayan da ya siyo. Na dauki dubu guda a cikin ku'din da na tara na lalle. Na saka mata a ciki. Na k'ulle. Na sake k'ara wata ledar.
Na tarar har sun kusa fita.
Na bu'de baki na ce "Dada mun yi sallama ne?"
Suka dakata na isa garesu. Na mika mata tare da ce wa "Ga shi Dadarmu na gode da ziyarar ki. Amma Wallahi bakin ki k'anin kafar ki akan sha'aninmu Dada. Idan kuwa kika fa'di wani abu, sai dai a neme ni a rasa."
Ta sassauta ta ce "Ayyah Asiya me na ga ni ma ban da alheri? Ai ko da na ce zan fa'di baku zauna lafiya ba. Dan ban fahimta ba ne. Yanzu da na fahimci shine da laifi, ai na fa'di gaskiya. Kawai da ke da shi ku yi kokarin d'abbaka sunna, kada auren naku ya b'aci ba'a ankara ba.
Kunya ta yi matu'kar kama ni. Na rasa yadda zan yi, sai kawai na juya da sauri na yi ciki na barsu.
Shi kuma ganin hakan ya sanya ya ce "Allah yasa dai ba sai yanzu kika yi mata wannan bitar ba Dada?
Domin a zaune zaki yi mata ba a kurarerren lokaci irin haka ba. Idan kuma zaki fasa tafiyar sai bayan Isha da na fi haka gode wa Dada".
Ta nuna shi da yatsa ta ce "Tabataccen marar ta ido. Oh ni Binta ina kallon shak'iyanci. Ai gara ma da Asiyan ce matar ka, ita ce maganin ka. Haba kana da fitina Wallahi".
Ya yi gum. Ta d'aga murya ta ce "Na tafi Yabi, na gode Allah ya yi albarka.
A ci gaba da hakuri."
Ina zaune ina kallonsu ta windo har suka fice.
Suna tafe a hankali yake jan mashin d'in gudun kada ta subuto tunda ba iya hawa ta yi ba.
A hankali take fa'din "Ashe haka zaka yi mana? Akan me zaka kawo wata har gidan auren ka?"
Ya ce ba ni na kawo ta ba. Wajenta take zuwa fa.
Kuma kunshi take yi, wai ni rage mata aiki nasa aka yi"
Ta hassala ta ce kaniyarka da rage mata aikin. To bata so. Kada ka kuma wannan d'anyen aikin."
Ya ce "To bazan sake ba, da gaske."
Suna isa ana kiran magariba. Dan haka da ya kafe mashin din a zaure bai shiga gidan ba, ya nufi masallaci.
Da nutsuwa ya isa kofar Baban Marina ya gaisa da su Gwaggo cikin kunya da girmama wa.
Kansa a k'asa ya ce "Gwaggo idan uniform din Asiya na nan wai a bata zata fara koyon dinki"
Da sauri ta shiga daki tana ce wa "Sabon yana nan. Tsohon dai Ikilima tana amfani da shi."
Jimawa ka'dan ta kawo masa a bak'ar leda.
Hannu biyu ya sanya yayin karba.
Ya yi godiya, ya yi musu sallama ya tafi.
A gurguje ya yiwa Dada sallama ya wuce gidansa. Yana Jin zumudi da d'okin zama kusa da Yabi.
Yana son yi mata ba zata. Yana son ya shawo kanta, ya d'ora mata girma ko zata rage tsiwa da zafin kai.
*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers*
*08089965176*
*07084653262*
✍️.
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES.*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*Tallah Tallah Tallah*
Shaharriryar marubuciyar nan wacce tanishaɗantar ku a littafin ta mai sunan
SAMHA```!
```Ta sake sabon shirin ta, wajan ƙara faranta maku rai' tazo maku da sabon book ɗin ta Wato KECE SANADIN [rayuwa]```
```Masoyana kufito ku nunamin ƙaunar da kuke cewa, kuna min```
```farashin KECE SANADIN ₦500 0nly```
```wacce bata shirya ba kada tamin magana```
```masu san fara pyarment da wuri gashi, 810353370 kimin screen shot ki turo ta wannan no 08138012334```
```masu kati kuturo ta wannan layin 08108353370```
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
45&46.
Ya shiga da kuzari. A falo ya tarar da ita tana kallon tashar Bollywood.
Yana wahalar gaske ya ga tana kallon tashoshinmu. Har gara tana kai wa Sunna TV sa'i zuwa sa'i.
Ya manta da uniform a cikin but din mashin din.
Ya zauna kusa da ita.
Ya sassauta ya ce "Asiya Toro babu magana, babu yi mini barka da zuwa?"
Na galla masa harara na ce "To ni ina ruwana da kai da zan yi maka magana? Ba gaba mu ke yi ba?"
Ya ce "mun shirya ai. Na baki hakuri, kakarmu ta baki, mene ne kuma ya yi saura?"
Na ja tsaki mai tsananin gaske na ce "Da wa din ka shirya? Ai ni duk mutumin da zai tozarta ni, ya kuma ta'ba lafiyata da sunan duka to babu ni, babu shi har gaban abada".
Na fa'da cikin matsanancin fishi.
Jikinsa ya fara mutuwa. Ya numfasa ya ce "Ashe duk maganganun Dada basu shige ki ba? Daga tafiyar ta Asiya zaki fara d'aga mini hankali, mene ne nak'asuna ne da kika washe ni har hakan?"
Yana rufe baki na ce"nak'asunka ai birjik ne. Mafi muni baka da kamun kai.".
Ya zuba mini ido ya ce "sai me kuma Asiya?"
Kai tsaye na ce "Baka burge ni ko kadan. Domin bana jin k'amshi a tare da kai. Baka iya kwalliya ba. Kullum kayan ka babu guga. Kalli faratan hannun ka.
Kullum na kalle ka ba'kin ciki ne yake kama ni maimakon farin-ciki."
Jikinsa ya yi sanyi kwarai da gaske. Idanuwansa suka canja launi sosai.
Murya a dashe ya ce "Sai me kuma?"
Na ce "Idan na tuna, na fa'da maka".
Ya numfasa ya ce "Duk zan gyara indai sune cikas dina a wajen ki. Idan na sauya din shi ke nan zaki daina tsananta mini?"
Na sake shan kunu ban tanka ba.
Ya ce "To nima ina da damar da zan fa'di abubuwan da kike yi mini da bana sonsu?".
Kamar bazan kula ba.
Sai kuma na ce "Baka da damar domin ni ba so nake sai na burge ka ba. Ba kuma so nake ka zauna da ni akan dole ba.
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Shike nan! Amma ina ro'kon ki kada ki sake shiga mini da mata dakina".
Na tunzura! Na tashi zaune sosai na galla masa harara na ce "Sannu mai d'aki. Komai dakinka, dakinka. To sai na shiga d'in.
Shima ya hassala ainun ya nuna ni da yatsa ya ce "Kada ki fasa Asiya. Ai tunda na gane ba kya son sulhu da sassauci, to mu zuba tsiyatakun mu ga wa zai janye wa wani".
Na ja tsaki na ce "Ai ka k'oshi shi yasa ka samu kuzarin yin musayar yawu da ni".
Ya juyo a tunzure, ni kuma na zabura na yi shirin kai masa naushi.
Dariya ta kama shi ya ce "Wai dambe zaki yi da ni? Ko da yake ai mai hali baya fasa wa."
Na ce "oho dai."
Ya fita ban sake jin sa ba, sai da asuba ya tashe ni.
Da safe ba yadda bai yi ba akan na tafasa masa wani abu, duk da ya shigo da burodi a safiyar, kawai bai dame shi ba ne. Na yi tsallen bad'ake na ce bansan zancen girki ba, gara mu cigaba da zaman doya da manja kawai.
Ya shiga ya tafasa farar taliya ya zuba yajin *Annur food* da manja. Ya ci ya fice bai bi ta kaina ba.
Sai da na gama komai sannan na d'ora shayi.
Na karya na yi wanka. Ina zaune babu wuta, kuma babu kowa.
Sai da azahar sai ga y'anmata uku sun zo k'unshi.
Muka shiga d'akin da ake ta mini kashedin kada na shiga na fara yi musu.
Na gama wa mutum d'aya sai ga Hajiya babbar mace sosai. Dan zata haife ni. Mun saba tuntuni, wani lokacin har gidanta ina zuwa na yi mata, sanadin haka suka saba da Gwaggona.
Na marabce ta da murna.
Na kammala saka musu. Na kammala yiwa Hajiya a hannu.
Sai ga shi ya dawo. Ban san me yasa ba, na ji faduwar gaba ainun. Wata'kila ko dan ya yi ta jaddada mini kada na shigar masa d'akin da nufin yin kunshi ne?
Ya lek'o ya tabbatar ban ji maganar sa ba.
Ya juya ko gaisuwarsu bai amsa ba.
Ya dauko bokiti ya janyo ruwa.
Hajiyar ta ce "tashi ki je ki masa sannu".
Na ce To" ba dan ina so ba, na yun'kura na fita. Na gan shi ya gama cika bokitin, ya dauko na tsaya ban ce masa kanzil ba.
Zuciyata ta tsinke a dalilin yanayinsa ya koma na Bulkachuwa na asali, ba na yanzu da ya koyi sassauci ba. Ya shige ni bai ko kalli inda nake ba. Ya kai ruwansa band'aki. Nima na koma na cigaba da lallena.
Mintina biyar sai ga shi ya shigo d'akin babu sallamah. Y'anmatan suka fara gyare gyaren jikinsu yayin da Hajiyar ta rasa yadda zata yi a dalilin duk na yiwa hannuwanta k'unshin.
Ba zato ya cire rigarsa ya mak'ale. Zuciyata ta tsinke. Wani irin abu ya tokare ni. Kafin na wartsake sai kawai ya zame dogon wandonsa, ya yi saura daga shi sai singileti da gajeran wando. Hankalina ya kai k'ololuwar tashi lokacin da ya cire singletin.
Ya dauki tawul din da yake rataye ya daura a kugunsa. Ban san me ya hana shi zame gajeran wando ba. Yasa kai ya fice zuwa band'aki.
Na yi kasa da kaina hawaye ya b'alle mini.
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBE TA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
Gaba'daya y'anmatan suka bi shi da kallo. Wani irin mak'aki ya tokare ni. Na sani zai burgesu tunda Ubangiji ya masa kyakkawar sifa kwarai da gaske. Motsa jikinsa da yake yi, ya sanya jikinsa ya ginu sosai.
Wanne irin wula'kanci Tijjani ya yi mini yau? Na fa'da a zuciyata.
Matar ta ce "Cire mini lallen nan. Ai bansan maigidan baya so ba. Na tabbatar ba da izininsa kike wannan sana'ar ba. Shiyasa ya dauki wannan k'azamin matakin.
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Yau na ga lukutar tsiya ni Hadiza."
Ta fa'da cikin kad'uwa.
Na fara kuka sosai, ina yi, ina cire mata. Ai kuwa ina gamawa ta ja ni jikinta ta mak'ure ta rufe ni da duka tana cewa "wanne irin shak'iyanci kike yi masa da ya janyo miki wannan d'anyen hukuncin. Shin baki da makusanta da suke fa'da miki gaskiya ne? Kowa ya kalle shi yasan yana tsananin son ki. Me kike yi masa?"
Dama so nake na yi kukan sosai, ko na samu sau'kin zugin da kirjina yake yi mini.
Dan hakan na bu'de baki na dinga canyara ihu. Ita kuwa sai dukana take tamkar ita din Gwaggo ce.
Sai kuma ya fito a bazame. Dan ya ga me ya sani irin wannan kukan. Ganina a hannun Hajiyar ta matse ni tana ta mintsini na ya sanya shi ce wa "Na ha'da ki da Allah ki bar ta haka nan Hajiya, k'yale ta"
Ai kuwa ta k'yale ni. Ya tsaya daga ba'kin k'ofar ya mika hannu ya d'auko jallabiyarsa da take rataye. Ya yi baya, ya sanya.
Ya dawo ba'kin kofar ya ce "Darajar wannan baiwar Allah kika ci, tana gidan. Na rantse miki da yau kin ga k'arshe taurin kai da tsiya."
Ya kalli Hajiya ya ce "Na gode sosai, amma dan Allah kada ki sake ta'ba ta. Ki yi ha'kuri".
Yasa kai ya bar gidan gaba'daya.
Y'anmatan nan suka kasa ce wa komai amma dai gaba'daya sun shiga rud'anin al'amarin da ya faru.
Ta tashi, ta fita tana fa'din "Zan je har gidanku na sanar wa Gwaggonki baki shirya zaman aure ba. Gara ta sani kada rana daya ta gan ki kamar jifa kin koma gabanta. Ke ko tunanin halin da take ciki ba kya yi? Tare da kanwar ki aka aurar da ku. Tana zaune k'alau, amma ke kin fitini kanki kin fitine shi."
Na dinga kuka ina bata hakuri akan kada ta fa'da wa Gwaggo fishi zata yi da ni.
Da k'yar ta yarda ba zata fa'da ba.
Bayan ta ce na kira mata shi a waya.
Akan dole na kira shi. Na danna speaker.
Yana dauka sai ce wa ya yi "Bebina kin daina kukan? Ki yi ha'kuri kin ji. Ai da nasan mutumiyar kirki ce irin haka da bazan yi hakan a gabanta ba".
Ba'kin cikinsa ya nemi kassara ni. Na mika mata wayar cikin b'acin rai.
Jin muryarta ya sanya ya shiga cikin nutsuwa sosai.
Bai bari ta ce komai ya fara bata ha'kurin abin da ya yi.
Ta ce "Tambayar ka zan yi. Baka son ta yi k'unshin ne?"
Da sauri ya ce "Ina so. Ai bazan hana ta sana'ar da ta kafu da ita ba. Amma dai dole ta bar abin da na ce mata. Na ce kada ta kuma yi mini lalle a d'akina, ta je ta yi a nata d'akin. Shine kawai rikicina da ita".
Ta ce "To shike nan. Magana ta k'are."
Ta kashe wayar ta murd'e mini kunne tare da ce wa "Dama can dakinsa ne, amma kike masa k'unshi a ciki?
Saboda ke tabbataciyar marar kunya ce?
Amma yanzu ai kin ga 'karshen tsageranci."
Ta saki kunnena ta tashi ta bud'e wadrof d'ina ta ga dukka kayana ne babu nasa ko daya. Ta sake kai kallo ga d'akin ta ga babu alamun hula ko wani abu na miji a ciki.
Ta daure fuska ta ce "kwanta na duba ki, wato har yanzu ke budurwa ce ko?"
Na rushe da kuka wiwi. Ina fa'din Dan Allah ki yi ha'kuri sanin da na yi ita din mai zafi ce. Sannan ba mai wargi ba ce, y'ay'anta ma shakkarta suke yi ainun.
Ta cije ta ce "Kin san Allah sai na ga ni. Ko kuma yanzu na saka Salisu ya dauko mini Gwaggonki tunda ni ba ni da mutunci a wajen ki."
Na sake tsananta kukana ina fa'din "Dan Allah Hajiya ki rufa mini asiri. Dama fushi suke yi da ni. Mussaman Babanmu, ki yi hakuri. Kuma ni akan wannan ba laifina ba ne. Na yarda na yi kuskure akan maganar d'akinsa, ba kuma zan sake maimaita wa ba.".
Ta saki ajiyar zuciya ta ce "Shikenan na hakura. Amma na baki daga nan zuwa kwanaki uku ki kwaso kayansa ki dawo masa da su nan.
Sannan ki kwantar da kai, ki roke shi ya baki iznin zama a d'akin tunda gidan naku babu bishiya ko rumfa.
Ba sai na fa'da miki muhimmanci sana'ar ki ba. Komin wadatar miji neman na kai da'di ne da shi. Zaka yi harkokinka kai-tsaye ba sai ka jira an yi maka ba. Bare ke da kika saba yiwa iyayenki hidima a cikin sana'arki".
Ina kuka na ce"To. Domin dai na gamsu da maganganunta.
Ta sake ce wa "Ki ajiye komai ki rungumi auren ki, kowa da kaddararsa Yabi. Ke taki ma da kyua. Tunda mijin na ki yana son ki da alama kuma yasan me yake yi tunda soyayyar bata rufe masa ido ya sarayar da yancinsa na miji ba. Ki shiga taitayinki. Wadanccan y'anmatan zarata kallon so da fatan ace nasu ne suke binsa da shi. Ki ribaci damarki. Ki rike darajarki tun baki tankwabar da ita ba. Idan a yanzu da yake neman zaman lafiya da ke, kika yarda kuka zauna, to har tsufanku ya dinga kaffa kaffa da ke. Ban ce ba zai bata miki ba, ban ce ba zai kuntata miki ba. Amma dai zaki samu sau'ki, zai kuma din ga shakkar ki botsare masa. Kada ki yarda ki koya masa jure wa fishin ki Yabi".
Cikin kuka na sake ce wa "To" Wanda ban san dalilin da ya sanya na kasa daina wa ba.
Ta nisa ta sake ce wa "Ban da ma ke din sakarya ce ai cikin hikima zaki gaje can din. Da kin nuna masa nan ne dakinsa ai shike nan. Yanzu kuwa can din da kika raina sai ki ga ya samu wacce zata yarda ta zauna a cikinsa. Sai dai ki ji an kawo masa amarya."
Ba k'aramin dukana wannan maganar ta yi ba. Na k'ara sautin kukan da nake yi. Ta ce "Sha sha a haka kamar wayayyiya amma bagidajiya ce. Baki iya komai ba sai kishi. To wai wannan kishin na mene ne tunda ba sonsa kike yi ba? Ya auro uku mana me zai dame ki? Na so bana gidan yau, ya tub'e ya zauna cikin mata na ga yadda zaki yi. Kin san kuma duk masu hankali baza su sake zuwa miki ba. Marasa tunani kuwa sun dinga zuwa, dan su k'ulla alaka da shi".
Bata bar gidan ba sai yamma lis, bayan y'an matan sun cire nasu sun tafi.
Sai bayan Isha ya dawo. Ya same ni a dakina ina kan abin sallah duk na takura tsabar takaicinsa da yake dafa ni.
Ya zauna a kasa kusa da ni. Ya ce "Barka da gida Asiya Toro".
Na kasa bu'de baki na ce masa uffan.
Domin yadda zuciyata take tafasa sai na ji tamkar na yi ta k'unduma masa ashariya.
Yasa dukkan hannunsa ya ru'ko ni yana fa'din "Ba kya gajiya da kuka ne Asiyata?"
Ai kuwa ba zato na fara kai masa duka a ko'ina. Ya dinga fa'din"ki yi a hankali kada siraran hannuwan ki su ji ciwo."
Na bar dukan domin tabbas hannuwana ne suke mini zafi tunda jikinsa a murd'e yake k'warai da gaske.
Kawai sai na fashe da kuka tare da ce wa "Sai Allah ya bi mini hakkina da ka keta a gaban jama'a. Baka da buri irin ace an kai k'arata gaban iyayena. Ka je na barka da Allah ya bi mini kadin zaluncin da kake yi mini. Ban da ka mayar da ni banza ka yi mini hakan? Bayan kwanaki akan idona ka saka aka yi maka girki. Idan tak'amar kicin da kayan abincin naka ne. To kwanukan da tukwanen fa? Ai da sai ka siyo ka kawo mata, ko ta debo na uwarta."
Da sauri ya ce "Amma Dada ai ta kashe wannan maganar. Na baki hakuri kuma."
Na ja tsaki mai tsananin gaske tare da ce wa "Ri'ke ha'kurin ka bana so. Tunda ka nuna ba ni da iko a cikin gidan da ake ce wa wai nawa ne, sai ka fa'da mini inda zan dinga zama da jama'ata, tunda ka sani a gidan ubana ma ina da inda aka ware mini nake zama na yi sana'ata."
Ya koma gefe ya ce "Gidan ki ne ba wai ba ne".
Da rawar murya na ce "Wallahi ba nawa ba ne. Domin da nawa ne ba zaka tozarta ni irin haka akan d'aki ba."
Ya nisa ya ce "Tsakanin ki da Allah sau nawa ina gargadinki akan dakin? Ai ba sana'a na hana ki ba. Dakin ne ba zai yiwu ace mata suna shigar mini ba. Tunda dai shine dakina zan yi iyakacin kokarina na ba shi kariya irin yadda ake bawa dakin mijin da yake da daraja.
Ki zo ki yi anan dakin, ko a falo ba ni da matsala da hakan. Amma wancan dakin baki isa ba, ba ki biyo hanyar da zai zama k'arkashin ikon ki ba Asiya".
Na ji tamkar na sharara masa mari. Amma da na tuna maganganun Hajiya. Da alwashin da ta yi na zata fa'da wa su Gwaggo halin da nake ciki. Ya sanya na ha'diye dukkan fishina na ce "Ai shike nan".
Ya mik'o mini ledar awara tare da ce wa "Ga shi na san baki ci abinci ba.".
Ban kula shi ba. Ya mike ya ce "Sai da safe, yau na gaji likis."
Kwana na yi, ina nadamar yadda zan dawo da Tijjani dakin nan alhalin bai nuna yana son ya dawo ba".
Washagari bayan na idar da sallah barci me nauyi na yi. Sai wajen goma saura na farka. Na tashi na ga ya ajiye mini burodi. Na ga kuma kusan duk kayansa har wanda ban ga ya sa ba, ya wanke su, ya shanya su a igiya reras.
Ashe fitar da yake yi da asuba aiki ya samu a gidan burodi. Kullum ya je suka yi aikin kwabi da d'aure wa. Za'a bashi babban burodi d'aya da donot guda hudu, da ku'di dubu da dari biyar.
Idan ya dawo kuma ya huta sai ya fita gurin aikin saka tiles ko na gyaran setlite ko had'awa. Duk abin da ya samu a ranar zai yi. Na burodin ne sau hudu a sati.
Dan haka baya rasa yan k'udade hidimar yau da kullum tunda ya k'i jikinsa. Mafi yawa kullum sai ya shigo da taliya daya ko macaroni. Wani lokacin kuma magi rabin leda sai da na ga robar maggin ta sake cika duk da bamu cinye kayan abincin namu ba.
Da na yi tsam sai na fahimci baya son kayan abincin su k'are ne.
Shi yasa kullum sai ya siyo wani abu ya ajiye akan kayan abincin, duk da har yanzu girkinmu ba kankama ya yi ba, sai na ga dama nake dafa wa.
Jiya da garin rogo ya shigo rabin kwano. Ban ce masa komai ba, da na ga ni. Amma har zuciyata na fara gamsuwa Tijjani ba zai bar ni da hidimar gidansa ba, kamar yadda ake hasashe. Sai dai bazan yi saurin shaidar hakan ba sai nan gaba.
Shiru bai dawo ba, yan k'unshi suka zo. Na rasa yadda zan yi, rana ta take barandar ba zata zaunu ba tunda inuwa bata zo wajen ba. Ni kuma ina k'yashin yi a falona.
Na kasa samun mafita. Kan dole na ce musu "Ba ni da lafiya bazan iya yi ba.
Suka tafi suna mini fatan samun lafiya, tunda sun san ni, sun ga kuma ramar da na yi.
Suna fita yana shigo wa da alamu sun yi kicibus ma.
Na kalle shi na dauke kai. Ya zuba mini ido ya ce "Sai yaushe zaki fara yi mini oyoyo da barka da dawowa ne?"
Na gatsina fuska na ce "Eh ai ka yi mini sallama da zaka fice, bare ka saka ran zan yi maka sannu idan ka dawo".
Ya girgiza kai ya ce "kullum fa sai na yi miki sallama Asiya. Yau ma sai da na leko na ga barcin na ki ya yi nauyi. Ni kuma wai kada na katse miki shi yasa na fita. Amma ki yi ha'kuri".
Na dauke kai na ce "To".
Ya mik'o mini leda tare da ce wa "Ungo nasan ki da son gurjiya, ganin ta na yi manya manya da ita. Shine na siyo, na taho na kawo miki".
Na kar'ba a hankali na ce "Na gode". Karon farko da na yaba masa har na yi godiya.
Da'di ya kama shi ya ce "Nima na gode miki. Ko na zauna na bare miki ne?"
Tausayinsa ya kama ni wanda nake kasa gane dalilin raunin da yake kama ni akan sha'aninsa. A hankali na ce "Na hutar da kai"
Dadi ya sake kama shi, walwalarsa ta karu. Ya zauna kusa da ni ya ce "Fa'da mini sunan turare mai k'amshi, kuma mai sau'kin ku'di."
Kamar bazan kula shi ba. Sai kuma na bu'de baki na ce Dagmar".
Ya zuba mini ido sosai sannan ya ce "Na tsani turaren nan, duk yadda yake da dadi mai nutsar da zuciya Asiya. Ya mike ya girgiza kai ya ce "Na gode da wula'kanci! Ai na sha ganin kwalin turaren a dakin Jabir. Shine kike son nima na saka saboda ki dinga jin kamshinsa a tare da ni?"
Ba'kin cikin da yake zuciyarsa ya kasa boyuwa. Ya juya ya bar gidan gaba'daya.
Kafin na tashi, sai ga shi ya dawo ya kwashe kayansa ya shiga da su dakin ba tare da ya tsaya ninke wa ba.
Ya fito a hanzarce ya fice tamkar kububuwa.
Abin mamaki sai na ji babu da'di. Yadda idonsa ya canja launi duk sai na damu ainun.
Ga shi ban roke ki shi ya bar ni na dinga zama a dakin da yake yi mini tijara a kansa ba.
Na tashi na shiga d'akin. Na ga ya zube su akan tabarmar da take shinfide a k'asa.
Kamar na ninke sai kuma na fasa.
Na janyo na rufe masa.
Da yamma sai ga shi ya dawo da cakwal da gawayinsa a leda. A tsakar gidan ya yi shimfida. Ya fita ban san inda ya samo rushi ba. Na ga dai ya zo ya zuba gawayi akai.
Tunda ya fara gugar nan bai tashi ba, sai da ya kammala tsab.
Ya kalle ni ya ce "kin dafa abincin, ko baki yi ba?"
Ba walwala na ce "Na dafa". Ya ce "To a dan bani".
Ya fa'da fuskarsa a tamke.
Na tashi na zubo masa, na rufe sannan na kawo. A wajen ya ci. Sannan ya kwashe kayansa ya yi dakinsa da su.
Zuciyata ta yi nauyi tabbacin da gaske ba zai bar mini dakin ba.
Ya fito, ya shiga wanka. Ina zaune a barandar ya fito cikin farar shaddarsa wani irin kamshi sai dukan hancina yake yi. Kamshin da ban ta'ba jin irinsa ba, mai matu'kar da'di.
Ya yi kyau tamkar wani hamshakin attajiri.
Zuciyata ta buga da irin haduwarsa, ya taje sumar kan nasa da take cike. Gashi bai sanya hula ba. Shaddar ta gogu.
Kuma babu dying tunda ya sake waccar mai cibiri cibiri lokacin bikinmu, bai sake b'ata ta ba. Ya dai tara amma babu rini ko murde wa.
Na kasa gane me nake ji. Na gan shi a yadda nake son ganinsa.
Bai wani tsaya ba ya ce "Sai na dawo ya fice da alama masallaci za shi.
Amma ga mamakina bai dawo ba sai da tara ta gota.
Sannan da ya shigo ina jinsa da Rafia a zaure da alamu ita ma unguwa ta je a lokacin ta dawo. Da k'arfi ta ce "Ka gaida amarya kwana biyu bana zama ne shi yasa ban shigo ba".
Ban ji me ya ce mata, tunda bai daga tasa muryar ba.
Wani irin abu mai tsananin gaske ya tokare ni. Shaidan ya shiga zuciyata ya ayyana mini tare suka dawo. Shashanci suka je suka yi abunsu.
Hawaye ya b'alle mini. Ya tarar da ni ina matsar k'walla.
A rikice ya zauna kusa da ni ya ru'ko ni.
Na fizge cikin kuka sosai na ce "Ka je kun gama iskancin kun dawo shine zaka ri'ke ni?"
Ya zauna ya ri'ke kansa. Ya kasa ce wa komai. Amma ba k'aramin kidima ya shiga ba.
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWIA SAIWOWIN SANYI*
AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU*
*AKWIA SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.
✍️
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*
Tsawon lokaci ina kuka shi kuma ya kasa ce wa komai. Da k'yar ya nisa ya ce "Asiya Toro son ki ya zame mini jarabta mai girma. Daga ranar da aka ambata mini za'a bani ke daga ranar ban sake samun y'ancin zuciyata akan lamarin ki ba. Me yasa zaki yi mini irin wannan mummunan zaton?"
Ya fa'da cikin b'acin rai matsananci dan har wani haki yake yi.
Na cigaba da kuka ban kula shi ba.
Ya damk'e ni sosai cikin tsawa ya ce "Ina miki kallon yarinya k'arama kina mini kallon biri boko.
Gaba'daya shekarun ki nawa ne a duniya. Ina tausayin k'ank'antar ki, amma ke abin da kika sani ya zarce na manyan y'anmata masu shekaru ashirin da biyar.
Kin ture dukkan ka'idojin shari'a, kina ta musguna mini. Babu ragayya a tsakaninmu. Ai ko ban ci darajar aure ba ya kamata na ci na jini. Wallahi na yi zaton ko wani kika ji ya jefe ni da wannan al'amarin sai inda k'arfin ki ya k'are. Amma har da ke a cikin jerin wadanda suke mini yarfe dan na tozarta na yi ba'kin ciki.!
Ya numfasa yana maida numfashi tamkar mai mura.
Jikina sai bari yake yi a dalilin na shiga zullumin irin damk'e ni da ya yi.
Nasan dalilin da ya sanya kike iya kallon idona kike jingina mini wannan Bak'ar TA'ADA. Saboda ban nemi hakkina ba.
Ashe tunda ke ba yarinya ba ce kamar yadda nake miki kallo kuskure na yi, da na dauke kai.
Tunda kin san kishi kin kuma iya har a kaina da ba sona kike yi ba shike nan, magana ta k'are zan d'ora miki girman da zai sanya ki dinga jin nauyin fa'da mini duk abin da ya zo bakin ki."
Na yi muk'us ban da b'ari ba abin da jikina yake yi.
Ya sake ni, ya fita. Ai ina ganin ya fita, na zabura na rufe k'ofar da sakata.
Na yi shiru ina ta zare ido domin har lokacin zuciya ta bugawa take yi da tsananin gaske.
Can na ji yana kwankwasa k'ofar. Na yi bakam a zuwan barci nake yi.
Bai tsananta ba, ya juya ya tafi.
Da asuba ban yarda na fita ba duk yadda fitsari ya matse ni, sai da na ji fitarsa masallaci sannan na yarda na bu'de k'ofar.
Har ya je gidan burodi ya dawo barci bai dauke ni ba.
Kamar daga sama na ji muryar Baban Marina a tsakar gidan.
Zuciyata ta tsinke sosai. Gumi ya dinga yanko mini. Gaba'daya na tsorata na tabbatar Tijjani ne ya kai k'arata.
A sanyaye na bu'de k'ofar, na taya Tijjani marabtarsa.
A falo muka sauke shi. Ya amsa gaisuwa ta da walwala na d'an samu kuzari. Domin na lura babu bacin rai a tare da shi.
Ganin hakan ya k'arfafa mini guiwa na mike na bu'de firij na d'auko ragowan k'wai uku da ya ragu.
Na soya masa a gurguje tunda nasan da burodi.
Kafin na gama shirya kofina a tray har shayin ya kusa juyawa.
Na dauka na kai gaban Baban.
Ina dawowa kuwa shayin har ya tafaso na juye a flask na kai masa.
Cikin soyayyar da na kwana biyu ban ga ni ba a dalilin fishin da ya yi da ni akan auren Tijjani.
Ya ce "Sannu Yabi. Allah ya yi miki albarka. Na ji da'din yadda na tarar da ku, kuna cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Allah ya dauwamar da aurenku, ya baibayeku da albarka ta inda kuka zata da ta inda baku zata ba. Wanzuwar aurenku na cikin burina a wannan duniyar. Ki zauna lafiya, ki yi ha'kuri da kawaici irin na uwarki."
Kaina na k'asa amma hawaye nake yi. Tabbas idan da Tijjani zai bu'de baki ya yi masa bayanin yadda muke zaune da bai yi wannan farin-cikin ba. Da bai sanya mini albarka irin hakan ba.
Tijjani ya ha'da masa shayi ya ce "Bismillah Baba ka ci abincin Asiya".
Da murmushi ya ce "Na riga da na karya, amma tunda Ubangiji ya nufe ni da zuwa gidanku zan ci abin da kuka ba ni. Ina fatan Ubangiji ya buda maka k'ofofin ciyar da iyali cikin sau'ki Tijjani".
Nan da nan ya masa da "Ameen Baba".
Yana kurb'an shayin Tijjani na yankar biredin yana cusa masa k'wai a ciki, yana mik'a masa.
Ba wani sosai ya ci ba. Amma ya shanye shayin. Ya yi hamdala ya ci gaba da sanya albarka cikin marari.
Ya ce "Tijjani ina fatan dai lafiya kuke zaune babu damuwa?"
Jikina ya d'auki rawa.
Amma ga mamakina sai ya ce "Lafiya k'alau muke zaune Baba. Ai Asiya har bayan idonka tana kiyaye tare da girmama umarninka".
Da'di ya k'ara kama shi. Ya ce "Alhamdulillah! Allah ka so Asiya, ka sanya soyayyarta da tausayinta a zuciyar mijinta. Shi kuma ka bashi lafiya da jarumta da arziki mai gudana. Àllah ka zaunar da su lafiya, ka basu zuri'a dayyiba."
Daga haka ya mik'e ya gyara rigarsa ya ce "Nurun ala nurun a dukkan rayuwar da zaku yi".
Tijjani ya bishi suka fita, yayin da na bisu Ina fa'din "A gaida mutanan gidan, Allah ya k'ara lafiya mun gode".
K'aran mashin din Tijjani ya tabbatar mini ya tafi mayar da shi ne.
Bai dawo ba sai wajen k'arfe d'aya da rabi na tabbatar kuma sai da ya yi sallah.
Kai tsaye wanka ya yi, ya sanya jallabiya ya shigo falon, k'amshin turaren da ya tsiri sawa ya bugi hancina.
Ya zauna. Na yi kokarin kyautata fuskata na ce "Sannu da dawo wa."
Ya kalle ni ya ga na yi kwalliya cikin wani fitinan material.
*Wanda Umm Nihla mazauniyar Malaysia take odarsu.*
Tuntube ta akan wannan lambar ta *manhajar Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa.*07020695644*
Ya ce "Wow Asiya kin yi kyau tamkar yar tsana. Na murmusa na ce "Na gode".
Ya numfasa ya ce "Wannan sannun ta ki nasan kin yi saboda rufin asirin da na yi miki ne".
Na cuna baki na ce "Yo kai ma ai na rufa maka naka asirin ai".
Ya matso kusa da ni ya ce "Fa'da mini rufin asirin da kika yi mini, ni da kin fallasa da ba hakan ba".
Na dauke kai ina hura hanci irin na ta'bara da shagwaba.
Ya sake susucewa ya ce "Saboda Allah me zaki ce masa ina yi miki na musguna wa?"
Cikin yanayin tab'ara na ce "Abubuwa masu yawa, yo ni abubuwan da ka yi mini ban da dai ni din mai hankali ce, da tuni ba'a yi b'atacciya ba".
*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
Ya maze ya ce "Ni nasan hankalin ki yawa ne da shi ai".
Na sake ce wa "Ban da dai ina tsoron fishin Baba ai da tun ranar da ka sanya aka shigar mini kicin da tun ranar zan bar maka gidan, ita sai ta zauna kawai a madadina".
Da sauri ya bar kan kujerar ya gurfana a gabana, ya ru'ko dukkan hannuwana ya sassauta murya ya ce "Asiya" cikin wani irin yanayi.
Na kasa amsa wa, karon farko da ya ri'ke ni ban fizge ba. Domin gaba'daya maganganun Baba ya dagargaza ni, ya fahimtar da ni zama da Tijjani tilas ne.
Zamana lafiya a gidan aurena yana nufin farin-cikin mahaifina na tabbatar Gwaggo ma ba zata so ta gan ni a gabanta da sunan mutuwar aure ba.
Na zum'bura baki na ce "Uum".
Ya yi kasa da murya ya ce "kalle ni".
Na sake juyar da fuskata ba tare da na kalle shi ba.
Da wata irin murya ya ce "Pls mana Asiya Toro".
Na zakuda da sauri, na fara kokarin cire hannuna a nasa. Ina ce wa "Ai dai kasan bana son gatsa mini sunana da kake yi."
Da azama ya ce "Indai zaki daina yi mini rashin kunya ai daga yanzu na daina fa'da miki. Kwanaki kin ce mini bana goge kaya, bana saka turare. Yanzu na fara yi dan kisan ba abin da bazan yi dan na samu aminci da nutsuwar ki ba. Amma ko ki nuna kin gane na canja, balle ki yaba mini na ji dadi".
Na bata rai na ce "Akan me zan yaba? Bayan ba dan ni ka yi ba. Ina ce jiyan da ka fita sai da dare ya raba kana zan ce, idan ta yaba maka ai shike nan"
Ya kame baki ya ce "Tabdi jam!
Ya bar maganar ya canja da ce wa "Yanzu zan sake ba ki hakuri, ki manta maganar shiga kicin din ki. Na yarda na yi kuskure, dan Allah ki shafe ta a zuciyar ki. Nima na yafe miki zargina da kika yi jiya. Kin ga dai murna da addu'ar da Baban Marina ya yi. Kamata ya yi mu ha'da kanmu mu zauna lafiya".
Na bata rai na ce "To ai kai abin haushin ka yawa ne da shi Tijjani. Bana son na ga namiji ya cika kule kulen mata, kai kuma kana tafiya a mashin ma kana iya tsayawa ka yiwa mata magana ko baka sansu ba".
Ya sake ru'ko hannuna sosai ya ce "Billahillazi a da ne Asiya. Tunda muka yi aure bana yi, na rantse miki da Allah. Mussaman da kika ce mini mai kamun kai kike so, sai na sake kame wa sosai".
Na yi shiru ya ce "shike nan komai ya wuce zamu zauna lafiya, zaki yarda na zama mijin gaske ba na wai ba?"
Na ce "Sai ka yarda wanccan dakin ya zama zan yi yadda nake so a cikinsa".
Ya ce "Kin san ban iya yaudara ba. Idan kin yarda na zama mijinki na sosai, ai gaba'daya ma ya zama naki, to me zan yi da shi?"
Na ce "Ban gane ba?"
Ya jima yana kallona har sai da jikina ya amsa sannan murya a dashe tabbacin ya shiga cikin shauki sosai.
Ya ce "Idan dakinki ya zama shine nawa, kayana sun koma ciki, kin adanasu tamkar yadda kika adana na ki, sannan a ciki zan dinga kwana, a ciki zan yi komai. Shike nan dakin ya zama na lallen ki da duk bak'on kwana da zamu yi".
Gabana ya yanke ya fa'di tamkar yanzu na fara jin ya kamata ya dawo dakina".
Na yi k'asa da kaina na kasa ce wa komai.
Ya marairaice fuska ya ce "Ki ce to Asiya, na matsu ki zama matar aure ta sosai, na k'osa ki zama babba."
Kunya ta kama ni, na rasa yadda zan yi, sai kawai na fara kananun kukan shagwaba tare da ce wa "Ai yanzun ban girma ba kake nufi?"
Da sauri ya ce "kin girma mana, shi yasa nake son na sake mayar da ke babba sosai".
Na sunkuyar da kai na k'asa domin kunya ce ta sosai ta yi mini k'awanya.
Ya dinga murza mini tafin hannuna wanda hakan ba k'aramin abu ya haifar mini a gangar jikina ba.
Haka shima gaba'daya ya yi sanyi ido ya canja.
Kunya ta sake kama ni. Kan dole sai da ya sake wanka kafin ya tafi sallar la'asar.
Nima dai abin da na gani na kasa gane wanka zan yi ko tsarki. Dan haka sai na yi wankan gudun kokwanto.
Na dinga mamakin lokacin da muka cinye bamu nemi ko abinci ba.
Na shiga kicin na dauko plask din abincin wanda jallof din shinkafa ne.
Na koma na dauko plates da cokula.
Ya dawo ya tarar da abinci. Ya ce "Kamata ya yi muci a plate daya Asiya".
Ga mamakinsa sai ya ji na ce "To."
Na zuba mana, muna ci yana yi mini hira kala kala.
Muna gamawa ya kalli agogo ya ce kwaso kayan ki na wanke miki".
Na girgiza kai na ce "Bar shi zan wanke da kaina".
Ya mike ya na ce wa "Bari na debo da kaina.
Kan dole na bar masa wankin nan ya yi, ina baranda yana ta faman zuba mini hira. Ni kuma na kasa tanka masa, sai dai eh ko a a.
Da daddare yana tafiya sallar isha na rufe k'ofata. Da ya dawo ya ga na rufe. A hankali ya dinga buga mini tare da kiran sunana, amma na kasa bu'de masa. Wata irin fargaba ta dinga ratsa ni. Kan dole ya hakura ya bar ni.
Da safe da na fito ya amsa sallamar da na yi masa, kansa na kan doguwar rigata da yake goge wa.
Tausayinsa ya tsirga mini, duk yadda na rufe masa k'ofa, kuma ban yarda na bu'de masa ba, bai sanya ya fasa goge mini kayana ba.
Gasu nan birjik a gabansa da alamu ya jima yana yi. Tunda rigar da yake kan yi ne ta k'arshe. Sai da na yo brush na ce masa "Ina kwana?".
Ya amsa babu yabo babu fallasa"
Da ya gama zai fita na ce "Zaka dawo ne da rana?"
Ya girgiza kai tare da ce wa "To me zan dawo na yi?"
Na yi shiru sai na ce "To idan an zo k'unshi zamu shiga d'akin, kada ka zo ka dizga ni."
Ya girgiza kai alamun bai yarda ba.
Ya bu'de baki ya ce "Ban yarda ba. Kada ki fara, idan kuma kin ki ji, to ki tabbatar zaki ga abin da baza ki so ba".
Na Kwakkabe fuska tare da fa'din "Amma dai kai ne ka ce zai koma nawa".
"Na fa'da tabbas. Amma ai na fa'di sharadina. Baki yi abin da na ce ba, dan haka kada ki sake ki kai mini mutane d'aki".
Daga hakan ya fita. Ina gama abun da zan yi. Na fara tunanin yau laraba, zan samu masu kunshi sosai har zuwa gobe. Ina matu'kar son sana'a ta, ina samun nisha'di da walwala a cikinta. Sannan ina son na dinga aika wa iyayena wani abu. Idan bana sana'a kuma bazan samu wannan alherin ba.
Na tabbatar kuwa matu'kar da kayan Tijjani a dakin da nake son ya zama na zaman sana'ata, to kuwa da sannu zai kore mini jama'a.
Na zabura na shiga dakin na dauko jakar kayansa. Na kai ta d'akina. Na sake dauko kwalin makorinin da ya zuba takalmansa a ciki.
Na fito da shi tsakar gida na bu'de. Kafa hudu ne da alamu biyu a lokacin aurenmu ya siyesu tunda sabbi ne.
Na goge su na kai su daki.
Jallabiya da tawul din da suke rataye, na fito da su na shanya tunda da danshin ruwan wanka a tare da su.
Bargo da filon kawai na ninke na barsu gefe daya.
Na dauko kaskon turaren wuta da yake ci a dakina na saka na sakayo k'ofar.
Cikin sauri na d'ora shinkafa da wake.
Na kammala na ji almajiri yana bara.
Na kira shi na bashi naira dari ya siyo mini salak da kokomba, domin kayan ganye sau'ki ne da su a Toro tunda muna kusa da Jos.
Nan da nan ya siyo mini, na bashi guntun burodin jiya.
Ina tsaye na yanka na wanke na rufe shi.
Na ha'da kwanukan da na bata na wanke.
Na shiga wanka. Na shirya cikin doguwar riga cotton mai gajeran hannu.
Na saka hular da ta dace da rigar.
Na kalli agogo na ga shad'aya ne da rabi.
Ai kuwa sai ga wata ta zo kunshi da kitso.
Na bude dakin muka shiga, na fara yi mata lallen, cikin kankanin lokaci na gama saka mata. Na dauko kujera a kicin muka fara kitson.
Mun yi rabi sai ga tawagar yan mata wajen su bakwai har da amarya.
Murna ta kama ni, domin ku'di zan samu ba ka'dan ba.
Sannan bana cikin zullumin wula'kancin Tijjani.
Ina gama kitson na fara yiwa amaryar tunda nata yafi wahala na salatif ne.
Na gama yi mata, na fara yiwa daya cikin kawayen na ji k'arar mashin dinsa.
Ya shigo da sallama. A zabure na mike na fita y'an dakin suka bini da kallo.
A bakin kofar na tare shi da ce wa
"Sannu da dawowa".
Bai amsa ba ya sha kunu ya fara kokarin shiga d'akin duk da na tare k'ofar.
Baki na rawa na sake ce wa "Sannu da dawo wa, muje ka sha ruwa, ka ga ni".
Bai musa ba. Ya yarda ya bini zuwa d'akina. Na nuna masa jakar kayansa da take gefe akan kwalin takalmansa.
Na ce "Babu kayan ka a dakin Wallahi. Ka ga tawul dinka ma?" Na d'aga labule ya gan shi akan k'ofa.
Ya daure fuska ya ce "Indai a hakan zaki bar mini su, to kawai ki mayar mini abina can."
Idona ya ciko da hawayen takaici. Murya na rawa na ce "Kawai dai sana'a ce baka son na yi Tijjani. Ban da haka, ga yadda ka ce na yi, zaka bar mini d'akin, na yi kuma ka ce ba haka ba".
Ba wasa ya ce "Ai ba ki adana mini su kamar yadda kika adana na ki ba. Kin ajiye su tamkar suna wancan d'akin dan haka mayar mini su can din kawai."
Da sauri na bu'de masa durowar na ce "Ka ga inda na bar maka fa, bana son na bu'de maka kaya ne baka nan. Da sai dai ka dawo ka tarar na jere maka".
Ya saki fuskar ya ce "To shike nan. Amma kin yi sallah kuwa?"
Na ce "dama d'aya zan k'arisa wa sai na yi kafin na fara yiwa wata".
Ya kalli agogo ya ce kusan uku saura, kina neman duniya baki yi abin da aka halicce ki yi ba? Yau ne rana ta k'arshe da za ki ji ana kiran sallah baki bar k'unshi kin yi ba".
Na ce "To".
Ya ce "Je ki yi alwallah ki zo ki yi sallar a nan".
Na fita ban ce komai ba.
Yayin da Tijjani ya cigaba da ambaton *RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN.* Cikin farin cikin ganin tasirin addu'ar akan lamarin Yabi. Domin tunda ya ga al'amarin ta babu ragayya, babu soyayyar sa ko kad'an sai ya nace wajen yin wannan adduiakan al'amarin. Ya kuma fara ganin sassauco mai yawa. Mata ku rik'e wannan addu'ar sirrikanta yawa ne da shi.
Na idar, na mike na kai masa abincin falo. Na dawo na gan shi kwance shame shame akan gadona. Gabana ya yanke ya fa'di. Saboda ya tube riga daga shi sai gajeran wando. Wani irin tsoronsa ya kama ni a dalilin duk jikinsa gashi ne. Kirjinsa kuwa yafi ko ina gashi.
Ranar da ya tub'e a gaban su Hajiya da yake a kidime nake ban ga gashin irin haka ba. Na dauka iya kirjin ne kawai.
Murya na rawa na ce "Abinci yana falo".
Muryarsa a dashe tabbacin yana jin barci ko wani al'amari daban.
Ya ce "Sannu da aiki".
Na amsa da ce wa "Na tafi".
"Tom, idan na ci zan fita, nasan ba son na lekoku zaki yi ba".
"Na ce "Eh. To sai ka dawo din".
Na saki labulen na je na cigaba da yi musu.
Bai fita ba sai da la'asar ta yi.
Sai wajen biyar na gama yi musu tunda na yiwa mutum biyu kitso a cikinsu.
Ina gamawa na karkade jikina na wanke hannuna da sabulu.
Na shiga kicin, na ga akwai donot sai kawai na dafa shayi na cika filas tunda akwai ragowar abincin rana da na yi
Ana kiran magariba suka tafi bayan sun bani kudina.
Na kirga na ga alherin da na samu ba ka'dan ba ne. Na ha'dasu na adana.
Na yi sallah, sannan na shiga wanka. Nasan sai ya yi isha zai dawo.
Amma abin mamaki har goman dare bai shigo ba. Haka kawai sai na fara jin zuciyata tana b'aci. Sai shad'aya saura ya dawo lokacin na gama fusata.
Ya shigo ya ga ban ko kula shi ba. Na hau na yi suntum. Ya ce "Asiya na yi ta kiran wayarki a kashe."
"Uhum" kawai na ce na kame bakina.
Ya ce "Wallahi Maijidda ce zata haihu, haihuwar ta zo da matsala, zan taho, Dada ta ce na kai ta asibitin ta gano ta. To abin ba da'di, ganin mawuyacin halin da take ciki ya sanya Dada kasa barin asibitin, nima kuma sai na yi alkunya na zauna jiranta kada ta ce dama a dole na kai ta".
Na ce "Sannu! zaman jiran matar da kake jiran a mutu ka aureta ta haihu ai wajibi ne.
Na mike zan bar masa d'akin. Ya yi maza ya ru'ko ni. Ya ce haba Asiyata wacce irin magana ce wannan?"
"Na ce k'arya na yi, baka fa'da ba?"
Ya ce "Allah ya sauwake, ai na fa'da ne saboda kishin hure miki kunne da yake yi. Amma ni ko d'aura mini wata macen aka yi ba fincike wa zan yi na zura a guje ba."
Na saki raina ka'dan. Ya ce "Dazun nan Dada ta gama ce wa yau watan aurensu goma da kwana goma.
Cikin Ikon Allah gasu da y'arsu a hannunsu. Baki ji yadda ake ta saka musu albarka tare da diyarsu ba. Su tun a ranar suka manta da komai suka rungumi junansu". Ban kula shi ba. Maimakon ya yi shiru sai ya sake ce wa "Ni da na duba key holder din aurensu na lissafe sai na ga a lissafin bature watansu tara ba kwana uku ma".
Kuka ya kwace mini, na ce "Na gode sosai da yarfe Tijjani".
Ya marairaice ya ce "Mene ne abin yarfe Asiya? ".
Na k'wace na koma gefe ina gunjin kuka.
Ya numfasa ya ce "Amma kin san dai bana son kukanki ko?"
Na zabura zan ce a gidan uwar wa? Ai ina tuna barin makauniyar da yake yi mini idan na fa'di hakan, na yi maza na ha'diye maganar na buge da jan tsaki da kara k'arfin kukan nawa".
Shi da kansa ya a fahimci da zaginsa zan yi, sai kuma na fasa.
Ya murmusa ya ce "Ban da abin Asiya Toro wai mene ne abin kuka saboda Allah? Ina ce da kin ji duk abin da ake fa'da miki da yanzu kina da cikin da ya yi daidai da kwanakin auren ki. Kina haihuwa sai dai a fahimci ke ma kin yi biyayya, kin manta da wanda ya manta da ke".
Na mik'e na bar masa d'akin. Kai-tsaye band'aki na shiga. Na juyo zan rufe k'ofar na hango shi ya daga labule yana kallona.
Sai da na ci kukana, na wanke fuskata na fito. Na ga ya koma ya bar ba'kin kofar.
Na lallaba na shige falo na saka sakata na yi kwanciyata akan doguwar kujera bayan na kure gudun fankar.
Ina kwance ba abin da nake so irin barci ya sure ni. Amma na kasa, zuciyata sai k'unci take yi. Ban san dalilin k'uncin ba, tunda na laluba ba haihuwar Maijidda ce ta dame ni ba.
Jin shiruna ya yi yawa ya sanya ya biyo sawu.
Ganin da ya yi k'ofar bayi a bude, ya sanya ya shiga d'akinsa. Nan ma wayam bata ciki.
Ya nufi falo ganinsa a rufe, ga fanka na kad'awa da k'arfin gaske ya tabbatar da tana ciki.
A fili ya furta "Bilhiillazi an jarrabe ni akan wannan azinanniyar yarinyar. Allah ka hore mini ita".
Ya koma ya kwanta, amma barci ya yi masa tutsu. Idan ya tuna jaririyarsu Jabir sai ya ji tamkar ya wayi gari ya ga Yabi ta haifa masa tasa.
Ya saki ajiyar zuciya tare da cewa "Wannan yar darun ma, ko sai yaushe zata bari ta girma, rimi rimi na fara shawo kanta, ta sake botsare wa tamkar me bugun aljan.
Ya muskuta sai kawai ya tuno uniform din ta da ya karbo sai kawai ya murmusa sosai. Tare da ce wa "gobe da ikon Ubangiji zan rage wannan tutsun na ki na iyashege. Na riga na gaji da kallon ki tamkar hoto".
Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES.*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
Washagari ko da na fito na tarar ya tafi gidan burodi.
Dan haka na k'ira layin Gwaggo.
Ta amsa tare da ce wa "Inji dai lafiya kika k'ira ni da duku dukun nan?"
Na ce "K'alau Gwaggo. Na gaishe ta, ta amsa. Na k'ara da ce wa "Ki turo mini Anas ya zo ya karbi ku'di, za'a siyo mini lalle da mahallabiya. Sannan salatip din mai kala za'a siyo mini.
Zan bashi da ku'di, dubu biyu naki ne, dubu uku kuma ki bawa Baba ya yi cefane, sauran kisa mini a bankina".
Ta amsa da "To" tare da saka albarka mai yawa.
Sai kuma ta ce "Zan dauki dubu a cikin wanda za'a jefa a bankin na bawa abokan zaman nawa,kowa drmaei biyar ko omo ne sa siya Yabi".
A dole na ce "To domin dai mama idna yaranta suka kawo asafi sau tari ma ba'a ji. Idan kuwa an ga ni ma, to mafi yawa baka sanin yadda aka yi da shi.
Na kasa komawa barci. Sai kawai na tsiri shara, na gyara ko ina.
Sanin zai dawo da burodi ya sanya ban yi haramar dafa wani wani abu ba.
Na yi wanka, na shirya, na zauna a falo. Babu wuta bare na yi kallo.
Ina ta sake sake har ya dawo.
Ya shigo ya kalle ni ya ce "Asiya Toro kina da kunnen k'ashi. Wata'kila dai kin fi son sai na fito na fa'di gaskiyar yadda muke zaune".
Na sha kunu ban tanka masa ba.
Ya zauna ya ce "Abin da kika yi jiya ya yi dai-dai ke nan? Kin b'ata mini rai. Amma na yafe miki, sai dai ki sani idan kika sake bazan yafe ba".
Na sake yin shiru.
Ya tashi yana ce wa ni fa yunwa nake ji".
Na fito, ganin yana janyo ruwa na tabbatar wanka zai yi, tunda sai zufa yake yi. Bayan aikin k'arfi da da ya yi nasan kuma da gudu gudu yake dawowa saboda ya saba da atisaye.
Na duba ledar da ya ajiye, burodin ne da donot din. Sai madara da milo na sacet ko wanne guda daya.
Tausayinsa ya kama ni, nasan ni ya siyo wa, shi kuwa sai ya sha ba'kin shayi abinsa.
Muka karya, yana ta jana da hira amma na d'ad'are.
Ya zabura ya fita da hanzari, alamun ya tuna wani abu.
Sai ga shi ya dawo da leda ya mik'o mini.
Na kar'ba, na bu'de ganin uniform din makarantana ne. Ya sanya na kalle shi da neman k'arin bayani.
Kai-tsaye ya ce "Na karbo miki ne saboda ina da sha'awar ki samu takardar kammala sakandire.
Tuni an gama ristar Waec. Amma ta Neco da saura. Idan Ubangiji ya hore mini zan biya miki ki zana.
An kusa fara yin tumfirint zaki je ki yi nan da sati biyu".
Wani irin farin-ciki ya kama ni marar misaltuwa.
Na dinga fa'din "Na gode sosai Tijjani". Domin ban ta'ba hakaito hakan ba, tunda dama ni karatun ba damuna ya yi ba. Amma na ji da'di, zai zama ni ce mace ta farko a gidanmu da nake da takardar kammala sakandire.
Ya ce "Amma fa idan kina mini rikicin banza, da rufe k'ofa haka siddan zan fasa ne, tunda alheri misaye ne".
Da sauri na ce "Na daina, amma kai ma ka daina yi mini yarfe".
Ya kwashe da dariya ya ce "Lallai Asiyata ba yarinya ba ce tunda tasan yarfe har tana jin ciwo idan an yi mata."
Na b'ata fuska na ce "Kallon dai mahaukaciya ka ke yi mini kawai".
Ya ce "Haba ni yanzu idan za'a tambaye ni kaf gudan Marina wa cece ta fi hankali kina ganin zan tsallake matata ne?"
Na dauke fuska ina motsa bakin ni ban yarda ba, da'din baki ne kawai.
Ya yi murmushi ya ce "Asiya kin same ni da yawa. Kin shiga zuciyata kin yi kane kane, sai wahalar da ni kike yi. Ko tausayi babu a lamarin ki".
Na cuna baki na ce "Gwano baya jin warin jikinsa ai".
Ya basar ya ce "Nan da sati uku zan je Toro daurin auren diyar Baba Shehu. Jibi ma zani daurin auren abokina amma bazan kwana ba, idan kuma na ga zan yi dare zan kwana d'aya.
Na washe baki na ce "Ka ce na shirya kawai."
Ya zuba mini ido ya ce "ke yanzu sai ki bi ni?"
Na ce "Ai na je ma na gama. Ya shiga girgiza kai ya ce "Bazan je da ke ba, bana son rikici, wata'kila dai nan da sati ukun na tafi da ke."
Na b'ata rai na ce ", Gaskiya ni dai zan je".
Ya ce "gaskiya ba zani da ke a hakan ba. Haka kawai ki janyo mini b'acin rai. Babah tana kallon ki zata gane ke d'in budurwa ce kin kuwa san ai ranta b'aci zai yi, ta yi mini fishi mai tsananin gaske".
Kunya ta kama ni. Na yi kasa da kaina. Bakina ya mutu murus.
Ya sake ce wa "Wata'kila dai bikin Salima na tafi da ke, idan na gamsu da zamanmu".
Ban yarda na sake yin magana ba.
Ya ce "Ki shirya da yamma idan na dawo zan kai ki, ki yi barka".
Babu walwala na ce "Tom".
Muka karya, ya yi wanka ya fice.
Yau ma na samu y'an lalle, dan ma wasu hakuri na basu, tunda zan fita. Anas ya zo ya karbi sakon. Sai da ya ci abinci sannan na na bar shi ya tafi.
Wajen k'arfe biyar ya dawo na shirya na yi fes da ni l.
Sosai na yi kyau, rashin nauyin yadin yana sani d'oki sanya shi.
Riguna guda biyu masu kyau muka siya a wani plaza sannan muka wuce.
A k'ofar gidan muka tarar da Yaya J.
Da kansa ya yi mana iso.
Ina falon Maijidda su kuma suna tsakar gida suna hirarsu.
Zuciyata sai girgiza take yi. Ga shi dai Bulkachuwa ya kere shi a kyaun sifa da k'irar k'arfi. Amma so ba k'arya ba ne.
Haka na baro gidan ban yarda na kalle shi sosai ba.
A hanya Tijjani sai ce wa yake yi ba ki ga yadda jinjirar ta yi maki kyau a hannunki ba. Ba ki ji sha'awar ki samu ta ki ba?"
Ba tare da na zurfafa tunanin komai ba na ce "Na ji mana, sai na ji kamar su bani na tafi da ita".
Da sauri ya ce "Maijidda ba zata ba ki ba. Kawai ke ma ki dage ki samu ta ki".
Na ce "To Àllah ya ba ni"
"Ameen dai Asiyata. Oh har na hango ki kina bata nono".
Kunya ta kama ni na yadda ya fa'di sunan mama gatsar gatsar.
Duk yadda na dinga ro'kon sa akan muje gidan Marina. Bayan Isha sai mu koma namu gidan k'i ya yi.
Da zai shigo gida bayan isha sai ga shi da kaza da yoghurt.
Ya tisa ni gaba da zantuka masu nauyi, masu nuni da ya kai k'ololuwar gajiya da zuba mini ido.
Na rasa yadda zan yi, domin gaba'daya ya hana ni samun damar da zan gudu na rufe kaina. Tunda ko bandaki da zan shiga bina ya yi ya tsaya a bakin k'ofar.
Duk yadda na share lokaci mai yawa ina ciki. Da na fito a zaune na gan shi yana dakona bai gaji ba.
Ya ru'ko hannuna. Har cikin dakinmu. Zuciyata sai harba wa take yi. Gaba'daya harshena ya yi mini nauyi.
Ya ja ni jikinsa ya rungume sosai tamkar zai mayar da ni ciki. Gaba'daya ma b'oye ni ya yi a jikinsa, tunda ya yi mini rumfa saboda tsayinsa da zatinsa.
A hankali ya ce wannan karkarwar da kike fa Asiya? Nutsu, bazan cutar da ke ba".
Ni dai na kasa bu'de baki na ce k'ala kanzil.
Sallar da ya sanya ni dole. Na bishi ne mun yi babu nutsuwa a tare da ni. Akan sallayar ya shiga b'are b'are.
Ina ji, ina gani ya salube mini rigar jikina.
Na shiga ki'dima a dalilin abubawan da yake da sassan jikina. Na fara kuka. A ki'dime ya ce "Kada ki zalunce ni, kukan ki na tayar mini da hankali. Na riga, na ku'dira aniyyar yin aure yau, kada ki janyo wa kanki tsinuwar mala'iku.".
Jin hakan ya sanya na saddak'ar babu tsumi babu dabara.
Yau sai yadda Allah ya yi da ni.
Yana jagwalgwala ni yana ce wa "Ai Baban Marina tuni ya dauka mun saba tsintar kanmu a cikin wannan yanayin.
Shi yasa ya dinga farin-ciki da roka mana albarkar rayuwa."
Da rawar murya na ce "Ka yi mini girma Tijjani, tsoro nake ji kada ka fasa ni".
A kunne kamar mai rad'a ya ce "Za ki dauke ni, Ubangiji ne ya shirya komin girman namiji baya gagarar mace ta dauke shi".
Da wayo, da rarrashi, da dabara ya samu ya kai ga gaci.
Amma ni din ba k'aramin galabaita na yi ba. Domin kuka da shure shurena bai hana shi komai ba, sai da ya tabbatar ya kai inda yake son kai war."
Sosai shimfidar ta baci. Wanda bamu lura da hakan ba a lokacin.
Ni kam bayan na samu ya rabu da ni, sosoai na bu'de baki nake kuka domin ji na yi k'asan na zugi tamkar an watsa mini borkonon tsidugu.
Sannan haka siddan na ji wata irin fargaba ta yanko mini tamkar ina cikin tsaka mai wuya. Dan haka na dinga kuka tamkar raina zai fice.
Tun yana rarrashi, har ya hakura ya zuba mini ido. Ya rasa yadda zai yi. Kan dole ya hakura ya bar ni ya je ya yi wanka. Ya dawo kenan aka kawo wuta. Dan haka ya yi sauri ya jona ruwa a yar karama butar dumama ruwa wacce tafi kama da matsakaicin jug.
Da k'yar da makyarkyata na yarda zan yi wankan. Ai ina gwada yin tafiya sai kawai na durk'ushe na sake fasa ihu. Domin zafin da ya sake ratsa ni mai tsananin gaske ne.
Bai tsaya bata lokaci ba, caraf ya sure ni ya kai ni bayin da kansa.
Ya surka mini ruwan sannan ya fice.
Ruwan zafi sai ya zama tamkar garwashi dan haka ban yarda na zauna sosai ba.
Na watsa na fito.
Yana jin bu'de k'ofar ya karaso. Ya sake surata, yana tafe yana manna mini kises bai ko damu da kukana ba.
Ina gunjin kuka har barci ya wuce da ni.
Ya jima yana kare mata Kallo. A ransa yake tambayar kansa duk barnar da ya yi a baya sai a kuma aka bashi kamilar mace wanda wani namijin bai ta'ba kusantar ta ba. Wata'kila kuma dan ya yi sahihiyin tuba ne.
Ya tsinci kansa da fa'din ", Astagafirillah".
Ya shinfida sallaya ya fara salla tunda ya yi alwallah da ya yi wanka. Sannan ukun dare ta gota.
Ba abin da bai roka ba, inda yafi maimaita wa a addu'ar tasa sai a hore masa lafiya da arzikin da zai sauke hakkin ciyar da Yabi da sauran dawainyarta.
Ya dinga ro'kon a cika zuciyarta da sonsa kwatankwacin yadda aka cika tasa zuciyar da kaunarta.
Har aka fara kiraye kiraye sallah bai runtsa ba.
Yana gaban Ubangiji yana godiya tare da neman rabauta.
Sai da ya sallaci raka'aitainil fijir sannan ya tashi Yabi.
A hankali ya jata jikinsa ya rungume. Ai kuwa yadda ta yi barci da kuka.
Sai kuwa ta tashi da kukan.
Ya kankame ta ya ce "Is ok kukan ya isa hakan. Mu je ki yi alwallah, bana son na tafi ban taimake kin yi alwallah ba."
Cikin kuka na ce "Da ina da band'aki a ciki ai da ko da rarrafe ne zan je da kaina, ba sai an taimake ni ba".
A hankali ya ce "Ko akwai ma zan taimaka miki. Ai nuna kulawa da yabawa a lokacin da ka samu alheri a tare da mutum abu ne mai kyau."
Ganin bai tunzura ba, da na yi maganar bandaki sai kawai na rushe da kuka ina cewa "Wayyo bandaki a d'aki nake so ni ".
A raunane ya ce "Haba Baby girl, kin shayar da ni farin-ciki, ai bai kamata kuma ki rikita ni irin haka ba.
Ki yi ha'kuri, zan miki daki mai bandaki In sha Allah. Amma yanzu ki yi hakuri kin ji".
A daddafe dai na yarda ya kai ni, na yi alwallah.
Sannan ya tafi masallaci.
Ana idar wa ya dawo, duk da yau ba zai je gidan burodi ba, da wucewa zai yi atisaye.
Amma ko tashi ban yi akan abun sallata ba.
Da rawar jiki ya sure ni, yana ce wa "Barka da safiya My Asi beauty."
Ya ta'ba jikina ya ji zafi. Ya fita da sauri, jimawa ka'dan sai gashi ya dawo da kofi mai dauke da shayi, hannunsa kuma da Panadol. Da magiya da ban baki na sha shayin, na ha'diyi magani sannan ya rungume ni tamkar jinjira, muka kwanta.
Barci muka yi ainun. Dan kuwa sai bayan shad'aya muka tashi.
Shi ya dafa mana indomie. Ya saka kazar jiya a ciki. Da lallashi ya sanya ni yin wanka. Da na fito duk yadda nake ture shi, sai da ya ware tawul din ya shafa mini mai
Na runtse idona a dalilin kunya da takaicin sun yi mini rubdugu.
Amma shi ko a jikinsa sai yaba laushun fatata da k'oda farina mai kyau ne irin nasa. Ni dai ban kula shi ba. Asalima runtse idona na yi tunda ya riga ya tube ni, yana kare mini kallo tamkar tsohon maye.
Yinin ranar bai fita ko'ina ba, sai masallaci wannan kam da azama yake fita. Hatta wayoyinsa kashe su ya yi.
Yayin da ni kuma na lanjare, ko motsin kirki na k'i yarda na yi. Yan k'unshi kuwa sai zuwa suke yi. Da kansa ya ke fa'din bata jin da'di, kuma tafiya ma zata yi sai satin sama zata dawo. Dana gaji da jin wannan bayanin nasa, sai na ce shin ina zan tafi ne?".
Kansa tsaye ya ce "Hutun lalle zaki tafi. Dan ba zai yiwu muna amarci ana damunmu ba."
Na girgiza kai domin kuwa zan ga yadda za'a yi na sake yarda ya gana mini azabar da na sha a hannunsa jiya. Na tabbatar da gayya ya nuna mini rashin tausayi.
Kamar jifa ya tafi sallah la'asar sai ga Hajiyar nan.
Tana ganina ta gane yanayin da nake ciki. Ta dinga murna tana ce wa "To ko ke fa? Yanzu zai kara son ki, zai kara manne miki. Ke kuma ki yi juriya, ki yi biyayya shi kenan sai ki damk'e shi a hannun ki. Duk wanda zai musguna miki zaki ga ba zai yi k'ima a wajensa ba."
Na kasa jure wa na ce "Amma gaskiyar magana ya yi mini yawa Hajiya".
Na fa'da ina rusa mata kuka. Ta yi shiru ta ce "Ke kam ranar da zaki haihu da kallo."
Ganin da gaske nake kukan ta sassauta ta ce "Iya na yau ne. Da zarar kin zama y'ar gari shi kenan sai rawar kai da falli, da zai dauki lokaci bai nemi ta'ba ki ba sai an ji kanku".
Da kuka na ce "Allah ya kyauta na yi hakan Hajiya. Ni bana sonsa, amma an takura, an tursasa ni"
Jikinta ya yi sanyi ta ce "ki yi ha'kuri da sannu zaki so shi ne. Kuma ina tabbatar miki kina sonsa ko ya ya ne. Tunda na ga kishi a idon ki ranar da ya yi miki wannan iyashegen."
Na yi shiru ba dan na gamsu ba, sai dan ta wuce na yi musu da ita.
Ta dinga rarrashina da nasiha. Har ta samu na nutsu. Ta tafi tana ta yi mini addu'ar alheri. Na sani kuma saboda kirkin da Gwaggo take yi mata ne ya sanya ta damu da lamarina.
Ta fito da leda a jakarta ta miko mini. Ta ce ki dinga shan wannan, wannan kuma ki dinga shafawa.
Na zuba wa magaunnan ido na tabbatar masu daraja ne,na manyan mata ne mussaman da na ga G.H.T. product ne.
Ta ce "suna da kyau a wajen wata baiwar nake siyansa, ita ce ta zaba mini su, yayarku Sajida nake siyawa. Shekaranjiya na siya, jiya ta Sako mini a mota. FASEELAT da cika alkawari take, ga shi zata baka kaya masu kyau. Ga lambarta Dan nasan watarana zaki so ki sake siyansu"
*07039269802*
Na dai ce na gode, amma ba wani abu da zan yi akan Tijjani.
Ta tafi babu jimawa ya dawo da leda a hannunsa. Ya zauna kusa da ni. Ya bude kamshin hadadden tsiren da ya yi shura a garin Toro ya bugi hancina. Yawun bakina ya tsinke. Amma na maze tamkar bai bani sha'awa ba.
Sai da ya dinga ro'kona sannan na yarda na ci.
Da daddare muka kwanta, bai nemi komai ba sai rungume ni da ya yi.
Washagari da zai fita sallah ya ce zai wuce wajen aiki sai ya dawo.
Na amsa da adawo lafiya.
Na bi shi na sanya sakata.
Sai wajen tara ya dawo. Shi ne ya tashe ni tunda k'arar kiran wayata da ya yi ne ya tashe ni.
Yau bayan madara da milo har da k'wai guda hudu a ledar.
Sai da ya yi wanka ya shirya cikin shudiyar shadda da ta sha guga, ga k'amshin turaren da ya fara sanyawa mai da'din kamshi ya baibaiye hancina.
Yauma shi ya shiga kicin. Ya soyo kwan. Ya hado shayin da burodi ya kawo gabana.
Muka karya. Sannan na yi nawa wankan.
Da yake tsamin da jikina ya yi da sau'ki, kwalliya na yi mai sauki. Na kalli fuskata na ga ta d'anyace. Na sake yin fari.
Shi kuma baya gajiya wajen kawo hannunsa jikina. Tun lokacin na gane jarabarsa ba k'arama ba ce. Washa gari ya yi sammmako ya fita. Duk tunanina gidan burodi ya tafi. Amma bai dawo ba sai gaf da maghariba. Kayan jikinsa ya tabbatar mini ba a wajen aiki yake ba. Ya mik'o mini ledar hannunsa tare da ce wa "Ga shi in ji Babarki."
Ina jin hakan na fasa masa kuka har da dirowa daga kan kujerar. Ya tarairayo ni a gigice. "Saboda Allah fa kin girma Asiya. Yanzu ai kin wuce irin wannan kukan."
Da kuka na ce "Amma na ce maka za ni, shine ka tafi babu sallama?"
Ya sake rungume ni sosai. Ya sanya kansa a kan wuyana. Cikin rad'a ya ce "Sorry Asiyata. Daga yau bazan sake ba. Takanas ma zan shirya mana zuwa Bulkachuwa. Kwana nawa zaki yi?"
A hankali na ce "Sati biyu".
Ya lank'awasa harshe yana ce wa "Sati d'aya dai Sweetie".
Daga hakan ya dinga kissing dina, har sai da na ji jikina ya amsa sosai, na zame na koma kan kujera.
A hakan muka kwashe kwanaki hudu ban yarda an sake ba. A wannan ranar kuma ya rikice akan ya yi iya ha'kurin da zai iya. Kusan k'arfi ma ya sanya mini. Sai me? Gaba'daya sai na ji babu banbanci da na farkon wajen zafi da radadi, na rasa yadda zan yi. Na tattaro dukkan k'arfina wai akan na ingije shi, amma abu ya faskara.
A wannan ranar kam har cizo na yi ta gasa masa. Amma bai sanya ya k'yale ni ba, sai da ya yi yadda yake so ya gama.
Kukan da na yi a wannan dare ya zarta na ha'duwarmu ta farko.
Hankalinsa ya yi mugun tashi. Ya rasa inda zai tsoma ransa. Ya gaji da rarrashi ya zuba mini ido.
Can ya nisa cikin rauni sosai ya ce "Asiya irin wannan bacin rai kamar wanda na yi miki fyade. Kin san k'uncin da nake ji kuwa. Kin san yadda kika tayar mini da hankali. Me zan yi miki kin rangwanta mini k'iyayyar da kike yi mini?"
Jikina ya yi sanyi. Amma rad'ad'in da nake ji ya hana ni na daina kukan.
Ya numfasa ya ce "Ki yi hakuri ko wacce mace da hakan ta girma."
Da rawar murya na ce "Billahillazi bazan yi hakuri ka sabauta ni a banza ba. An yi na farko, an yi na biyu to kuwa ba za'a yi na uku da ni ba. Na riga na sani, baka iya yi da y'an k'ananun mata irina ba. Ka saba danne tima tima masu manyan halittu shi yasa nima kake gwada mini rashin imani kana ganin tamkar babbar mace ka samu".
Jin ya yi shiru ya sanya na d'ago na kalle shi.
Zuciyata ta tsinke a halin da na gan shi. Gaba'daya idanuwansa sun yi jawur tabbacin zuciyarsa ta b'aci ainun da kalaamina.
Bai ce komai ba. Ya tashi ya bar dakin.
Wanka ya yi, ya dawo dakin ya shimfida abin sallah ya tayar.
Yanayinsa ya saka kukan ya tsaya cak. Na rasa gane tausayi yake bani ko kuwa mene ne?
Washagari bayan ya dawo daga gidan burodi ya gama duk abin da zai yi mana.
Ya kawo mini abin karyawar har d'aki.
Fuskarsa babu walwala ya ce "Sai na dawo".
Ban amsa ba. A dalilin kuttun da ya shak'e ni. Don me zai fita? Ba zai zauna ya kula da lafiyata ba.
Ya tafi bai jira amsawa ta ba.
Na dinga kuka. Zuciyata tana kissima mini ai ya samu abin da yake so shi yasa bai damu da ya tsaya na yi wanka ko na karya ba .
Da rana ya dawo, ya zauna ya kalle ni. Yayin da ni kuma na d'aure fuska sosai.
Ganin hakan ya mik'e shima fursakarsa a d'aure ainun ya ce " Ban samu ku'di na siyo abin da zaki ci ba. Me kike son ci na dafa miki?"
Cikin son na wahalar da shi na ce "Faten doya da wake. Sannan da alaihu da kifi a ciki."
Ya nisa ya ce "Ba ni da kudin da zan sayi kifi yau. Zan dai je na siyo alaiyahun. Ya fara tafiya da nufin fita.
Na bu'de baki na ce "Zo ka kar'ba. Ni ina da kudin".
A zafafe ya juyo "Cikin kaushin harshe ya ce "Asiya Toro baki da kudin da zaki yi mini cefane matu'kar ina da lafiya, ina kuma kan k'afafuna. Ba zaki yi ku'din da zaki aike ni, na siyo abu sannan na zo na girka miki ba, har abada kuwa".
Ganin yadda ya rikice ya koma Bulkachuwan sa sai na yi maza na kame, domin na sani yana iya dauke ni da mari. Na laluba na kasa gane fishin me yake yi tun dare. To me na yi masa? Ni da ya ganawa azaba ma ban yi masa zafin kai ba sai shi zai dinga yi mini muzurai da hargagi?.
Ya yi k'wafa ya fice bayan ya jira na tanka, amma na yi muk'us.
Ina ta jin b'ab'atunsa a kicin. Ga mamakina sai ga shi ya kawo mini lafiyayen faten doya da wake a ciki. Ya ji alaiyahu da albasa mai lawashi.
Nabi bayansa da kallo. A dalilin bai zauna ba fice wa ya yi.
Ina jinsa a kan baranda ya zauna yake cin nasa.
Haka kawai sai na ji guiltiness na kama ni to me na yi masa?. Da ya gama bai lek'o ba. Daga inda yake ya ce "Sai anjima".
Na rasa gane manufar wannan abin da yake yi.
Da daddare ma da ya dawo bayan ya yi wanka. Ya dube ni ya ce "Zaki ci donot da tea ne, ko kuwa da abin da kike son ci?"
Cikin kuka na ce "Bazan ci komai ba Tijjani. Na hutar da kai" Na cigaba da gunjin kuka.
Da farko kamar ba zai tanka ba.
Sai kuma ya kasa jarumtar share ni. Ya ce "Wannan kukan fa? Ko dan na fa'da miki bana so shi yasa kike ta yi, tunda burinki ki kassara ni da ba'kin cikin ki".
*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
"Na tsagaita da kukan na ce "Akan me zaka dinga yi mini fishi, alhalin ni ya kamata na yi".
Ya zuba mini ido yana yi mini kallo mai tsananin gaske.
Cikin b'acin rai ya ce "Idan a duniya akwai abin da na k'i to a jingina mini waccar Bak'ar TA'ADAR ne.
Ta yaya kina matar aurena zaki dinga kallon idona kina fa'da mini maganganun da suke neman sabauta ni. Ban da dai kin mayar da ni shasha marar mutunci kya fa'da mini na saba danne mata akan idona?"
Jikina ya yi sanyi ganin yadda yake cikin fishi sosai idonsa ya kad'a har k'walla ne kwance a cikinsu. Tabbacin ba karamin k'ona masa rai na yi da kalamun nawa ba.
Ban san ya aka yi ba na ce "Allah ya baka hakuri Tijjani".
Ina rufe baki ya matso jikina ya ce "Shike nan na yafe miki duniya da lahira. Na huce".
Na ce "Amma zan fa'da maka gaskiyar magana".
Ya ce "To ina sauraren ki."
Na kawar da fuskata na ce "Gaskiya baka iya wannan abin ba. Ba haka ake yi ba, sannan ba haka k'awayena da aka yi musu aure suke ji ba. Domin ni dai ko a littafi idan ina karantawa ba'a shan wannan azabar da kake gana mini. Na tabbatar da haka kowa yake ji da Adda Nazira ta fa'da mini. To ina ganin iyawa ne kawai baka yi ba gaskiya".
Ya sake kallona, ba tare ya ce uffan ba, na tabbatar ya rasa me zai ce mini ne.
✍️
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*
*BAKAR TA'ADA*
51&52.
Me ya tuna oho. Na ga dai ya ha'diye dukkan fishinsa da mamamkinsa ya ce "Nasan ke ma baki iya ba, bare na kwantar da kai ki koya mini."
Na dauke kai na ce "Mu y'an kananu ba'a d'aukar lokaci mai yawa tare da mu."
Ya murmusa ya ce "Shike nan next time zan kiyaye."
Na sake dauke kai na ce "Ni fa ba zan sake yarda ba".
Ya murmusa ya ce "Ai hakan ma na gode".
Bai sake tayar da maganar ba. Ya dinga ririta ni.
Muka kwana lafiya lau.
Washagari zai fita bayan mun karya tunda babu zuwa gidan burodi.
Na kalle shi na ce "Ina son zuwa gidan Adda Nazira".
Ya girgiza kai ya ce"Ba yanzu ba Asiya".
Na bata rai na ce "To sai yaushe?"
"Ta kusa haihuwa ai, sai Allah ya sauke ta lafiya. Kya je ganin abin da ta haifa miki".
Na tsuke fuska na ce "Gaskiyar magana fa Tijjani ba irin wannan rayuwar nake harin samu ba.".
Ya girgiza kai ya ce "Ki gode Allah dai".
Na zum'bura baki na ce "Kullum cikin godiyar na ke. Amma yanzu an daina irin wannan takurar fa".
Ya kalle ni ya yi murmushi tare da cewa "Asiya Toro manyan mata".
Daga haka ya tafi ya bar ni.
Kwana hudu a tsakani na warware na cigaba da harkokina har da sana'ata.
Shi kuma ya daure bai sake takura ni ba.
A haka muka sake kwashe sati. Har lokacin kuma ban sake yarda mun ha'du ba, duk jarabarsa kuwa.
Ya rasa yadda zai yi da ni. Domin duk dare sai na sanya panties uku, sannan na saka dogayen wanduna biyu. Na sake saka riga a kai.
Duk hilarsa ya kasa cimma ni.
Ya gaji da rara-gefe ya koma rarrashi.
Amma fir na k'i domin gaba'daya na tsora ta. Da gaske rad'ad'in da nake ji ya wuce misali.
Rannan da daddare ya kasa barci.
Ya tashe ni, a marairaice yake lallaba ni.
Murya a raunane ya ce "Ina jiye miki tsoron tsinuwar mala'iku Asiya."
Rai a bace na ce "Ni gaskiya bazan yarda ba, haka kawai ba komai a ciki sai azaba. Daga gunka ne matsalar, tunda ai ba haka ake ji ba, ni ce nake jin hakan."
Ya ru'ko ni a diriri ce ya ce "Allah zai taimake ni. In sha Allah yau ba zaki ji zafi ba. Ki yi ha'kuri kin ji. Da ace kin bu'de mini zuciyarki ba zaki ji zafin har haka ba".
Duk yadda ya ki'dime da son na aminta da shi fir na bijire, da na ga zai saka mini k'arfi ma. Kuka na dinga yi masa mai tsananin gaske.
Ya k'yale ni.
Amma barcin da bai yi ba ke nan.
Washagari ya tashi da azumi. Amma me?
Da ya dawo daga gidan burodi sai gani na yi, ya fito mini da tarkacen filillinkan lallena da na saka aka kawo mini su daga gida. Hatta robar da nake k'wabin sai da ya fito mini da ita.
Ya shigo d'akina ya kwashi wasu daga cikin kayansa.
Ya mayar can.
Ina kallonsa ban ce komai ba. Amma dai kam na shiga damuwa. Domin an jarrabe ni da son sana'a tun ina k'aramata. Ina samun nisha'di a cikin yin lalle da kitso.
Na sani kuma ba zai yiwu na mayar da falona wajen dabdalar yin k'unshi da kitso ba.
Ya gama uzzirinsa ya yi shirin fita. Ya same ni har cikin falon da nake zaune.
Fuskarsa babu walwala ya ce "Asiya kada ki shigar mini daki, ina bu'katarsa. Domin kwanan cikinsa zai fiye mini masalaha ga lafiya ta".
Na kalle shi. Yadda ya tsare gida ya sanya na kasa sakar masa bakaken maganganu.
Na tsuke fuskata na ce "Al'kawarin ke nan? Ni ba Tijjani ne ya ce ya bar mini d'akin na yi yadda nake so ba?"
Ya girgiza kai ya ce "Tijjani ne ya fa'da, yanzu kuma ya fasa sai ya ya?"
A kufule na ce "Sai hukuncin mai sab'a al'kawari ya hau kansa".
Ya ce "Ya hau din. Tunda dai ba tsinuwar mala'iku zata hau kaina ba ai da sau'ki".
Na sake hassala na ce "Wai na tambaye ka mana?".
Ya ce "Kunne na jin ki".
Babu tsinkaye na ce "Ni a siffofin munafiki ai har da sab'a al'kawari ko?"
Da budaddiyar murya ya ce "Eh" , sai kawai ya shammace ni ya dauke ni da mari".
Na zunduma ihu ina ce wa "Manzallazi ya saka mini akan wannan zaluncin da kake yi mini".
Ya ce "Idan zaki zage ni sau dubu. Ni kuwa zan d'aga miki hannu sau dubu. Shege ka fasa a tsakaninmu. Kuma idan kin cika marar kunya ce ke, to ki shiga mini d'aki da nufin yin k'unshi, ki ga kalar tawa rashin kunyar".
Na kasa ce wa komai illah kuka sosai da nake yi.
Bai damu da kukan ba, ya saka kai ya fice.
Asarar da na yi, a yinin wannan ranar ba ka'dan ba ce.
Domin kuwa mutane sun fi goma da suka zo k'unshi ina sallamarsu.
Gara ma na yiwa yara uku kitso a falo.
Sau uku yana kewayo wa ko zai tarar na shiga, ya wula'kanta ni. Sai kuma ya ga duk zuwan da zai yi bai ga kowa a ciki ba.
Kwana biyu muna wannan takun sak'ar.
Ga shi na ji a bakin Rafi'a ana ta tumfirint din Neco.
Kwana na uku na same shi a d'akinsa da daddare na zauna na sassauta murya na ce "Tijjani ka ce "Zan yi Neco ga shi ana fa'din an kusa rufe yin rigista da tumfirint din".
Kai-tsaye ya ce "Na fasa fas. Dama ai ba wai karatun ya dame ki ba ne. Ni ne a kokarin na sanya farin ciki a zuciyar ki ya sanya na ce zaki yi. Ina kuma da sha'awar mace mai ilimi. Yanzu kuma na fasa tunda baki da abin wula'kantawa, sai ni".
A sanyaye na ce "Dan Allah Tijjani tunda ka saka mini rai ka bar ni."
Ya ja tsaki ya juya ya cigaba da kwanciyarsa. Na tsura masa ido ina jin zuciyata tamkar ta fa'do. Wato ko wanne namiji ya iya tsiyataku masu k'ona rai. Na dinga mamakin me zai sa wula'kancinsa ya yi mini ciwo ne?".
Na tashi na bar shi, zuciyata tamkar ta fa'do k'asa.
Kullum fishin nasa gaba yake yi ba baya ba.
Gaba'daya ya fitittike ya koma wanccan Bulkachuwan da yake dauke kai ga mace in ta nemi yaga shi. Magana ma da k'yar yake yi mini. Tsakaninmu ya shigo mini da cefane. Idan ya samu sararin siyo kayan masarufi kuwa, sai dai na ga yawansu ya k'aru. Ya daina sauraron abincina. Ya kuma daina tambayar me zan ci. Da ya gama uzzirinsa zai sa kai ya fice, nasan dai bai ta'ba fashin kawo mini cefane ba. Sannan bai damu sai na ba shi idan na girka ba.
Ranar da babu gidan burodi kuma bai samu aikin da zai yi ba. Zai dawo ya ce mini ki yi wake da shinkafa ko ki dafa taliya da manja.
Shi kuwa sai ya jika garin rogonsa ya sha, ya sake fice wa. Wani lokacin tausayinsa ya hana ni sukuni. Na rasa yadda zan yi da shi, ya k'ulla gaba mai yawa a tsakaninmu.
Rannan ya ce mini "Ya tafi Bauchi. Da'di ya ratsa ni, domin zan samu na dan yi k'unshi kafin ya dawo garin. K'warai na takura a halin da nake ciki.
Ai kuwa mutum uku suka zo, na kai su dakin bayan na kintsa masa kayansa gefe guda.
Na dauko bedsheet na rufesu.
Na gama yiwa mutum biyu, ina cikin sakawa ta uku. Tamkar jifa sai buga k'ofa na ji. Ban kawo shine ba. Tunda ya ce ya tafi Bauchi. Nasan kuma sai wajen dare zan gan shi.
Na fita da sauri ina zaton ko Anas ne.
Ina bu'de kofa kawai na ga mutum a tsaye.
A gigice na ce "Tijjani ba ka tafi Bauchin ba?"
Fuska a daure ya ce "Allah bai yi ba".
Na tare hanyar shigowar. Ya ce "menene haka, ba ni hanya band'aki zan shiga".
Na diririce. Baki na rawa na ce "Dan Allah, dan darajar Annabi Tijjani ka rufa mini asiri, ka yi hakuri kada ka shiga d'akin lalle.
Ya galla mini harara ya ce "Yau munafurci ya tabbata a kan ki, kuma zaki ga k'arshen rashin mutunci Wallahi".
Na zabura na ri'ke shi sosai. Murya na rawa na ce "Ka yiwa Àllah da Manzonsa kada ka yi mini haka. Na yarda komai ka ke so zan yi, amma kada ka sake tozarta ni Tijjani".
Ya zuba mini ido yana kallon yadda hawaye yake tsere akan fuskata.
Ya jijjiga kai ya ce "Shike nan".
Sanin bai iya yaudara ba, ya sanya na sake shi ya shiga, ina bin sa a baya. Domin da zai shiga d'akin, ba zai nuna mini ba zai shiga ba.
Kai-tsaye falo ya dosa. Na samu nutsuwa a zuciyata.
Tsabar nutsuwar da na samu har ruwa na dauko masa.
Na kawo masa abincin da na dafa zan ci.
Ya hakince tamkar wani basarake. Yana cin magani, komai isa isa yake yinsa.
Haka dai na lallaba shi, ya koma harkokinsa.
Yana fita na saki gauron numfashi. A fili na ce "Oh Allah. Menene damuwata ne akan abin da zai yi a d'akin da nake shiga zullumi idan zai shiga din?"
Na kasa bawa kaina amsa.
Na kalli mashin dinsa da yake gefe wanda bai fita da shi ba.
Yana fita wasu zugar suka zo. Dan haka har kusan magariba sannan na gama saka musu.
A gurguje na yi wanka.
An fara kiran isha wacce na saka wa a karshe ta cire ta tafi. Na dinga jin da'din ku'din da na tara. Da na nutsu sai na gane, idan ban dauki matakin dai-dai to a tsakanina da Bulkachuwa ba. Asarar da zan dinga yi a kullum ba ka'dan ba ce.
Ba'kin cikin rashin bishiya ko rumfa yana cina.
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWIA SAIWOWIN SANYI*
AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU*
*AKWIA SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.
Ga shi yanzu yanayin damina ne. Idan ruwa bai zuba ba rana ake yi, idan kuma an yi ruwan ba damar zama a waje.
Ya shigo na ha'diye haushinsa na yi masa sannu. Na kawo donot da flask din shayi. Sai da muka kammala. Na dauko dukkan cinikin da na yi a ranar. Na tura gabansa.
Na sassauta murya na ce "Tijjani ka ga cinikin da na yi yau ka'dai. Na ro'ke ka daina hana ni. Na yarda kullum kana da kaso a cikin ku'din da zan samu".
Ya fusata irin sosai din nan.
Ya nuna ni da hannu.
Ya ce "Ke ce kike mutunta ku'di irin haka. Na kuma sha fa'da miki ce wa baki da kudin da zan sa ido akansu bare har ki yi mini iyashege saboda su. Ya jijjiga kai ya mike tsaye bayan ya dangwarar da kofin shayin.
"Da nasan zaki kalli idona ki yi mini irin wannan tayin na raini Billahillazi da dazu ban yarda na karbi ban hakurin ki ba. Amma shike nan. Daga yau din nan bana bu'katar ayi mini lalle da kitso a gidan nan gaba'daya ma".
Ina jin hakan na takarkare na ce "Bilhiillazi ba zai yiwu ba, komai kake ji da shi Tijjani, baka isa ka hana ni sana'ar da ka gan ni da ita ba! Duk masifar ka kuwa".
Ya murmusa ya ce "Lokacin da aka dauke ki aka ba ni babu shawarata ai ba a ce mini mata zasu dinga yi mini zarya a gida ba. Dan haka yanzu da na ga bazan iya d'auka ba, na dakatar da su".
Na sake hassala na ce "To wai dole aka yi maka ka zauna da ni?
Na ce ba na sonka, kai ma baka sona, to mu rabu mana. Mugunta ce kawai ta sanya ka ri'ke ni, kake musguna mini."
Ya ce "Shike nan bar shi a muguntar ne kawai. Sai dai ki sani na riga na samo wa kaina mafita. Ki saurari abin da zai biyo ba. Ban karbi auren ki ba sai da na kudire wa zuciyata komin rintsi bazan bari mugun halinki ya sanya na kunyata Baban Marina da Babah ba.
Ki je ki karaci diban albarkar ki. Ai Ubangijin adalci ya riga ya samar mini mafita a cikin wula'kanta ni da kike yi tun kafin a halicce ni".
Daga haka ya fice.
Gaba'daya na kasa gane manufar maganganunsa. To wacce manufar ya samo?
Na kwana ina tauna maganganun Tijjani. Zuciyata ta yi nauyi a wajen son na fahimci inda ya dosa.
Ko dokar da ya sanya mini ta hana ni sana'ata bata tokare mini wuya ba. Irin son na gane mafitar da ya samo.
Kwanaki biyun da suka biyo baya, zaman namu ya sake yin tsami bisa dalilai guda biyu. Na farko ya tire kan ra'ayinsa na kada a ayi masa lalle a cikin gidansa. Sannan ya tsiri ya yi wanka ya sheka kwalliyar da ni na koya masa yin ta. Da daddare zai dauki wankakken kaya kuma gogagge ya fesa turaren da duka gidan sai ya amsa tsabar bulbulawar da yake yi, sannan ya fice ko kallon inda nake ba zai yi ba bare ya yi mini sallama.
Ba zai dawo ba sai goman dare ta shud'e.
Wannan al'amarin ba k'aramin ci mini kwarya yake yi ba.
Na rasa inda zan tsoma raina da ba'kin cikin da Tijjani yake guma mini. Mussaman na barina a gida da daddare ni ka'dai kamar mayya.
Ranar da muka yi sati a cikin wannan halin. Na bugawa Yaya Ummi waya, ji na babu kuzari ya sanya ta dinga fa'din "Mene ne, me ya same ki Yabi?"
Na kasa bu'de baki na ce mata uffan, illah kukan da nake yi mai cin rai, mai kuma sauti sosai. A lokacin kuma dare ne sannan yana gidan.
Ya ji ni sarai, tunda a lokacin yana falo. Amma ya yi kamar bai ji ba.
Washagari da asuba sai ga Yaya Ummi ta diro mana gidan.
Tausayinta ya kama ni. Yargale yargale da ita. Da alamun ma kukana bai barta ta yi barcin kirki ba.
Ta same ni kad'ai a dalilin bai dawo masslaci ba.
A gigice take tambayar me yake damuna?
Murya a dashe tsabar kuka na ce "Tijjani yana shirin kashe ni da raina ne. Haka siddan ina zamana ya saka mini rai zai mayar da ni makaranta na samu shaidar kammala sakandire.
Yanzu ya zo ya ce ya fasa. Hakan bai ishe shi ba sai ya ha'da har da soke sana'ata. Sannan dan yasan Baban Marina ba zai saurare ni ba, sai yake amfani da hakan yake musguna mini. Fiye sati yana gaba da ni. Sannan kulllum dare sai ya sheka wanka sannan ya fice ya bar ni a gida sai dare ya raba zai dawo. Ni nasan Bak'ar TA'ADAR sa ya koma. An cuce ni Yaya Ummi."
Na fa'da ina rushe wa da kuka sosai.
Daidai lokacin kuma ya dawo, amma kukan da Yabi take yi tamkar na mutuwa shi ya hanasu jin motsinsa. Ya zauna a barandar yana son fahimtar abin da yake faruwa.
Jikin Yaya Ummi ya yi sanyi. Ta ru'ko hannuna ta ce "Yabi nutsu ki ji ni. Shin me kike masa yake yi miki hakan?".
Cikin kuka na ce "Bana yi masa komai".
Ta numfasa ta ce "Me yasa kike gaba da shi? Da kina gaishe shi, na tabbatar Yaya Bulkachuwa zai masa miki."
Na yi shiru dan kuwa gaskiya ta fa'da.
Ta sake ce wa "Da kin ja shi a jikin ki, da ba zai iya fitar da yake yi ba. To me zai yi a wajen bayan yana da d'anyar amarya mai cike da shiriritar kuruciya?"
Na bata rai na ce "Kawai saboda ke da shi akwai amana da yarda shi yasa kike shaidar sa a bayan idonsa ni kuma kike bani laifi a kan idona ko?"
Na fa'da hawaye na ziraro mini.
Ta tsananta ri'ke mini hannu ta ce "Gaskiya ai bata bu'katar ado Yabi. Babu ruwan alk'alami akan kina so ko ba ky so. Kawai girman hakkinsa da ya rataya a kan ki za'a duba. Idan baki sau'ke ba Wallahi halaka zaki yi Yabi. Ni yanzu son nawa mijin nake yi? Amma na yarda kaddara shi ta zaba mini. Dan haka na yi hakuri nake yi masa biyayya, duk da shi din ba duka yake sauke hakkin da shari'a ta gindaya masa ba. Amma na sani ina rabo mai girma a wajen Azza wa jallah".
Na tsananta kallonta domin gaskiya ta fa'da. Har zuwa yanzu da ta zarce shekaru goma da aure bata son mijinta, ni shaida ce akan hakan, amma kuma ha'kuri da biyayyar da take yi akan sha'aninsa mai yawa ne.
Ta numfasa ta ce "Yabi ba kya yarda da Tijja
Yaya Bulkachuwa. Su kuma maza da kike ganinsu komai zaki yi musu na kyautata wa matu'kar ba kya mutunta shinfidarsu, to fa komin kokarin ki a banza ne a idonsu. Saboda haka ki d'auki matakin gyara a tsakaninku."
Na nisa na ce "Baya gamawa da wuri Yaya Ummi. Ni gaskiya bazan iya ba."
Ta ce "Ahab dama da labarin neman auren da yake yi ya riske ni, sai da na ce na tabbatar ke ce silar k'arin auren sa. Ai sai ki yi tunda al'amarin kishiyata bai saka kin k'yamaci kishiya ba".
Wani irin abu ya soki k'irjina, ban san mene ne ba. Amma gaba'daya ji na yi tamkar zan shid'e.
Na rushe da kuka mai tsananin gaske.
Ta ce "Ai indai kika cigaba da tafiyar da shi a hakan, tabbaskuka na gaba. Ba ki ga Bilkin da yake zuwa wajenta ba, gansamemiya ta yi biyu da rabin ki."
Da rawar murya na ce "Me za'a yi da mai BAK'AR TA'ADAH irin ta Tijjani. Aure ko rufa wata biyu ba'a yi ba har ka fara neman wani auren. Na rantse Yaya Ummi sai dai a tsine mini. Amma bazan taba zama da wata macen a k'arkashin ikon Tijjani ba".
Ta sake ru'ko hannuna ta ce "Idan kina son ki zauna lafiya, ki yi sana'arki, ki cigaba da tallafa mana. To ki zauna lafiya da mijin ki, ki daina gudunsa, ki yi hakuri da shi watarana sai ki ga kun kai ga babban bigire. Ni fa na dauka ma ciki ne da ke. Jiya nan na je gidan Ubaida na tarar tana ta kwarara amai. Da kaina na rakata asibiti aka tabbatar ciki ne da ita. Kin ga kuma ai kanwar ki ce duk k'uruciyar ki ai kin fita a haife. Jabir din da kike ta kulafacinsa matarsa wata tara ta haihu. Sai ke ce zaki zama shasha wacce bata san me yake mata ciwo ba. Da ace kin kwantar da hankalinki da wata'kila ke ma da na ki cikin a jikinki".
Kunya ta rufe ni, na ce "To yanzu dai ki fa'da masa ya bar ni na yi sana'a ta."
Ta ce "A yanzu bazan yi masa magana ba. Idan kin canja kin daina gudunsa, bai bar ki ba, sai na yi masa magana. Amma yanzu ai ke ce zaki fara zuwa da gyara".
A sanyaye na ce "To".
Amma k'irjina tamkar ya fa'do a dalilin nauyin da yayi akan batun tsohuwar budurwar Bulkachuwa wacce aka kai masa ku'din aurenta aka k'i karb'a. Tun lokacin ya fita a harkarta amma ita take ta nacin ya yi hakuri.
Tijjani da ya yi bakam yana sauraronsu. Ya saki gauron numfashi yana k'ara ganin hankalin Ummi. Sai dai mamakin da ta bashi a ina ta ji yana zuwa wajen Bilki?
Shi yasan tunda aka yiwa su Baban Marina wula'kanci bai sake taka gidansu ba har yau. Idan Ummi ta fa'di hakan da nufin yiwa Yabi barazana. Ya tabbatar liki ta b'allo masa.
Duk yadda Yabi take kirarin bata son sa amma kuma kishi take yi akan lamarin sa ba ka'dan ba. Duk da dai ya yi amanna kishi dabi'arta ce.
Amma ya tabbatar wannan maganar sai ta ri'ke ta a ranta.
Ya saki gauron numfashi yana fatan a sami dai-daito a tsakaninsu.
Tsawon lokaci yana sauraronsu, yana jin irin yadda Ummi take ta wasa shi tare da ban baki a madadinsa. Wanda hakan ba k'aramin kaunarta ya k'ara ji ba.
Jin tana haramar tafiya ya sanya shi mike wa ya maze tamkar bai ji me suke fa'da ba.
Da murmushi ya ce "Ummilolona ke ce da sassafen nan?"
Ita ma da walwala ta ce "Eh Yaya Bulkachuwa barka na je nan gabanku ka'dan, shine na biyo na gaisheku ko na yi laifi?"
Da sauri ya hau girgiza kai tare da fa'din"kin yi daidai Ummi. Allah ya bada ladan zumunci".
Ta ce "Ameen."
Ya bita suka fita da kafarsu. Wata'kila har gidanta ya rakata domin ya jima bai shigo ba.
Hadari ya hadu mai k'arfin gaske. Daidai lokacin ya dawo tamkar jifa.
Sai da ya rufe k'ofar d'akin da yake yi mini isa, ya rufe tagogin falo.
Sannan ya shigo d'akina. Na kalle shi na dauke fuska domin haushinsa ya sake kama ni sosai.
Ya zauna a gefen gadon ya sanyaya murya ya ce "Albarkacin zuwan Ummi na ajiye fishina. Na huce, komai ya wuce".
Na yi kamar ban ji ba. Ya matso jikina sosai ya ru'ko ni, na fizge a fusace na ce "Bana son ka huce Tijjani. Domin dai ni bana ha'da sabgata da marar imani bare kuma tausayi."
Ya sassauta ya ce "me na yi na rashin tsoron Allah Asiya?"
Murya na rawa ina shirin kece wa kuka na ce "Ban da ka tabbata baka da tausayi mene ne zai sa ka jajibo aure alhalin ko wata biyu baka rufa da yin auren ba. Mene ne hakan inba rashin tsoron Allah da rashin imani ba?."
Ya sake matsowa jikina ta yadda bayansa na shafar cikina.
Ya yi k'asa da murya ya ce.
"Wallahi Asiya Toro tsoron Allah nake ji sosai. Shine shaidar hakan. Asalima saboda ina tsoronsa ya sanya na fara neman auren. Ya zan yi? A d'an zaman da muka yi ya kamata ki fahimci bazan iya ri'ke kaina alhalin ina ganin ki, muna kwana gida d'aya ba.
Ke kuma gaba'daya kin bijire , kin k'i saurara ta, tunda ba sona kike yi ba. Sanin zan iya fa'dawa halaka ya sanya na samu wata bazawara mai gajeran buri muke tattauna wa. Idan Allah ya yi zan aure ta. Kin ga shike nan na magance tashin hankalin da yake tsakaninmu, sannan na samu mafita daga hatsarin fa'dawa zina da aurena".
Yana rufe baki ba zato na mik'a hannuna na d'auko wata doguwar robar mai ta kokobota. Na kwad'a masa a goshi. Ina kwada masa tare da ce wa "Allah ka yi mini tsari da mugun k'ullin da yake zuciyar wannan bawan naka. Bilhiillazi kana da fitina Tijjani."
✍️
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
*Assalamu alaikum Bayin ALLAH, kun san ce wa FREE PAGES na littafin ƘALUBALEN RAYUWA ya ƙare? Wanda cigaban littafin KUSKUREN SO na? Kun san dai yadda na nishaɗantar daku a labarin Nafeesar Sufyan? Kuma dai kun san yadda na nishaɗantar DAKU a littafin ISHARA labarin Zainabun Sameer? Littafin ƘWAƊAYI fa? Labarin Zainabun alamaramma? Na san baku manta RAHEELA MAI ƊAN BUJE ta cikin littafin RUGUNTSUMI? Jamaa na rubuta kun karanta kuma kun shaida, alƙalami ne da babu tantama a cikin shi, Jamaa yanzu ma tafe da nake da ɗaya tankar dubu, salon na daban ne? Ba zan so ya wuce ku ba, shiyasa na maku promo ku biya 300 madadin 400 kacal ta wannan hanya 9994468172 Access bank fiddausi musa tare da shaidar biya ta 08036953516 ko 07042277401, domin mu tafi tare, na maku alƙawari, labari ne da zai tsaya zukatan..*
53&54.
Ta ko ina nake jifan sa, gaba'daya na hargitse dakin.
Da k'yar ya samu ya ri'ke ni ya dauke ni caraf ya d'ora a cinyar sa ya rungume ni tsam tsam.
Gaba'daya na shige jikin na yi luf, sai kukana kawai yake tashi, wanda na shagwaba da kishi ne.
Cikin rad'a yake ce wa "So ki ke ki illa ta ni ne?"
Da k'arfi na ce "Eh. Wata'kila dan ka ga kana da kyau ne ya sanya kake ganin ko wacce mace ka ce kana so, ba zata tankwabar da kai ba. To gara na rugurguza ka. Tunda ni kyaun naka bai rud'e ni na makance akan ka ba"
Ya sakar mini wani irin nishi a kunne, sannan ya dan cizar mini shi ka'dan. Yar na ji jikina ya amsa. Na fara fizge fizgen bazan yarda ba, sai nima na cije shi a nasa kunnen.
Shi kuma ya dinga dariya yana cakuma ta son ransa.
Babu zato ruwa mai k'arfi ya goce.
D'akin ya yi duhu saboda ko ina rufe yake gudun kada ruwa ya shigo.
Wannan yanayin ya sake susuta Tijjani. Ni kuma na dinga koke-koken jan rai. A ki'dime yake rarrashina.
Fa'di yake "ki yi ha'kuri I will be soft and gentle."
Ni kuwa sai botsare wa nake yi. Tare da ce wa "Ni dai ba da'de wa zaka yi ba."
Da rawar murya ya ce "Nà yarda amma idan kika cije ni, ko kika yi mini fallashasshen kuka. Ki tabbatar kina cikin komar mala'iku".
Na yi shiru. Amma zuciyata sai harbawa take yi. Domin har zuciyata nake jin tsoron al'amarin.
Ina ji ina ga ni, ya shiga yin yadda ya ga dama da ni.
A farkon tafiyar gaba'daya na kankame jikina ina sauraron jin matsanancin zafi.
Amma ga mamakina sai ban ji ba. Har na sakankace na saki jikina. Wanda hakan ba k'aramin dadi ya yi masa ba. Ya k'ara haifar masa da kuzari mai yawa.
Dan haka lokacin da ya shafe yana abu daya, bai dame ni ba.
Bayan ya nutsu. Ya rungume ni yana ta faman sakin kalaman yabo da soyayya.
"Asiya da hakan kike yi mini, to me zai sa ma na yi fishi da ke? Bare har na yi tunanin k'arin aure. Na gode sosai, Ubangiji ya sanya albarka a rayuwar ki gaba'daya."
Na yi shiru. Amma zuciyata sai kai kawo take yi akan abin da nake son amayar wa.
Na kasa jarumtar ha'diyewar murya babu amo na ce "Yo ni ai tunda wula'kanci ka shiryo mini daga yin aure za'a ka fara neman wani dan kawai ka nuna wa duniya bani da wata kima a idonka. Wallahi ba zama zan yi ba. Zaka wayi gari ne ka ga na bace maka."
A diririce ya sake ru'ko ni sosai tare da ce wa "Kar ki tayar mini da hankali dan Allah.
Na fasa, dama dan na rasa yadda zan yi ne. Amma yanzu indai kin daina yi mini abubuwan da kike yi. Wallahi bazan sake tayar da maganar ba. Ke ko hanyar da ta bi, bazan sake bi ba".
Cikin kuka na ce "Daga baya ke nan. Wadanda suka ganka kana zuwa tadi ai tuni sun san baka son Yabi. Dan haka kuwa ba yarda zan yi ba. Ka je ka cigaba da abin da kake yi, ni ma zan samu mafita Wallahi".
A raunane ya ce "Bana son kukan ki Asiya! Amma sai ki ta yi mini, dan kawai ki gigita ni. Ban iya yaudara ba. Na ce miki, na fasa, na janye, to ba shikenan ba?"
A zabure na ce "Ba shike nan ba".
"Da azama ya ce "To fa'da mini yadda za'a yi, me kike so na yi dan ki gamsu?"
Na dinga gunjin kuka da na tabbatar yana jijjiga shi.
Ya dinga shafa kaina, yana fa'din " Sorry Asiyata! Na ce bazan sake ba, ki yi ha'kuri da gaske na fasa. Dan Allah mu rufe maganar nan haka. Me kike son ci na dafa miki?"
Na fara kokarin fizgewa daga rugumar da ya yi mini, amma na kasa.
Cikin tab'ara na ce "Bazan ci ba. Yau kwana nawa rabon ma da ka tsaya ka saurare ni akan maganar abinci. Ko na ci, ko kada na ci ai babu ruwan ka".
Ya sake sassauta murya ya ce "Wula'kanta ni fa kike yi. Ta ya ya zuciyata zata ji da'din kyautata miki? Yanzu kuwa ai komai yi miki zan yi da kaina".
Na cuna baki na ce "Abar maganar abinci. Ka tashi tunda ruwan ya tsaya, ka kwaso kayanka da ka kai mini wanccan d'akin dan kawai kana nema na da jidali".
Ya zabura ya tashi. Ya lalubo jallabiyarsa ya d'ora akan gajeran wandon bai ce komai ba ya fice.
Ya kwaso su tsab. Ya mayar dasu inda suke.
Ya juyo ya ce "Na kwaso, shike nan?"
Na bata rai na ce "Ba shike nan ba. Kada mu samu sabani ka sake yi mini hakan. Tijjani ba ruwanka da d'akin can. Nan ne dakinka. Idan kuma zaka dinga fitina ta akan dakin to ka sani zan tattara kayan gadon na mayar maka can din. Tunda nan d'akina ne da shari'a ta ce ka bani shi tilas. Idan anan nake sana'ata ban shiga cikin dakin ba, ai na tsira ko?"
Ya yi wani irin murmushin da na fahimci mai harshen damo ne.
Ya numfasa ya ce "Namiji ai ba yi masa shamaki a gidansa. Dan haka mu zauna lafiya mu mutuntata juna shine kawai. Amma bazan yarda ina tattala ki, ke kuma ki ce zaki dinga wula'kanta ni, sannan kuma na yi miki yadda kike so." Ya girgiza kai ya ce "Ba haka Tijjani yake ba. Ba kuma zai zama hakan ba".
Na kura masa ido na tabbatar iyakacin gaskiyar sa ya fa'da. Na rasa me zance masa domin na tabbatar duk bala'ina. Idan ya kunsa mini ba'kin ciki daya tak kwana zan yi na yini cikin ba'kin ciki mai tsanani.
Dan haka sai kawai na buge da sake fashe wa da kukan.
Daga inda yake tsaye, ya ce "Allah dai ya taimake ni ki hau ko na samu sau'kin wannan rikicewar da gangan. Idan kina ganin baby a hannunki wata'kila kya daina yi irin wannan sakalcin."
Yana rufe baki na fara nuna kaina cikin kuka ina ce wa "Tijjani ni ce sakaliya?"
Kafin ya amsa mini na rausayar da kai na ce shike nan na gode da wannan tukuicin".
Ya taho da sauri yana kuma dariya. Ya rike k'afafuna ya ce "Ina nufin sakaliyata fa".
Na yi tsuka na juya.
A sanyaye ya ce "Bana son tsuka Asiya. Amma na yafe miki, ban yi fishi ba".
Daga hakan ya koma ya fita. Na tabbatar kuma kicin zai shiga. Ni dai daga nan barci ya sure ni.
Sai bu'de ido na yi na ganshi ya yi wanka ya shiraya tsab. D'akin ma ya cika da kamshin turaren nasa.
Yana daga jikin sif din yana saka links ya ce "Yanzu dama zan tashe ki, na kai miki ruwan wanka".
Ban ce komai ba, na tashi, na daura zani a kirji sannan na saki zanin gadon na sauko.
Ya kalle ni babu riga a jikina. Ya ce "Asiya Toro a gabana babu riga. Sai na sake ganin ki wata yar kwaila, a hakan tamkar ba zaki iya komai ba. Nan kuwa al'amarin da yake tare da ke azimin ne".
Na cuna baki na ce "Ai ni na gode Allah ma da aka baka yar mitsil din. Kai da rusa rusan mata sai kallo daga nesa. In juninka cusawa mutum takaici ne. Har abada kai da zunduma zunduman mata".
Ya murmusa duk da dai yana kokarin shanye dariyarsa.
Ya ce "Wato baki ji da'din yabon da na yi ba, sai kika dauki abin da bai yi miki da'di ba, kika yi raddi?"
Na share, na dauki tawul na fice abina.
Na dawo na tarar da shi ya gyara gadon tsab. Ya share dakin. Na kasa hakuri na ce "Tijjani wai a ina ka iya gyaran gado ne, tunda kullum dakinka na gida a hargitse yake, sai asarrariyar can ta gyara maka shi yake yin fasali".
Ya dauko mai yana murmushi ya tarar da ni a bakin gadon. Na yi kamar na hana shi shafa mini mai din sai na fasa kuma.
Domin a dan zamanmu na fahimci yana matu'kar son ya shafa mini mai, kafin na sanya komai a jikina.
Ina ji ina ga ni ya dinga shafe ni da sunan shafar mai wanda ni kaina ina matu'kar jin sakon nasa a dukkan jikina.
Yana cikin murzar tafin kafata. Wanda kafin ya zo kafar ya shafe mintina sha biyar.
Murya dakushe tabbacin so yake ya koma ruwa ya ce "Nasiba ce asarrariyar Asiya?"
Na fizge kafata na tashi. Na ce "Ina dalilin gatsa sunan matar wani ne Tijjani? Kusan mintina ashirin da yin maganar ashe duk yadda na barka kake yin yadda kake so da sunan shafar mai, zuciyarka na tunanin suntumemiyar halitta ko? Wallahi bazan iya da bala'in ka ba Tijjani!
Ganin da gaske na fitittike, zan birkice masa.
Jikinsa na bari ya ce "Allah ya baki ha'kuri, na yi kuskure. Sai dai ya kamata ki mini shaidar tun ma kafin a mini babban alherin ba ni auren ki ai na fita a dukkan sha'aninta. Bare kuma yanzu da take matar wani. Dan Allah mu bar maganar, bana sonta. Ki yi hakuri."
Ya dauko mini wata riga ya ce "Ga gifts din ki na zama matar aure, tun first night dinmu nw so baki, to bata iso a lokacin ba."
Cotton yar kanti. Gaba'daya rigar tafi dacewa da yara y'an shekaru goma. Domin har da teddy wacce aka yi jakar goyo da ita. Sannan da hula irin mai malafar nan.
Kalar ruwan hoda (pink )da yarfin filawa mai ruwan lemon tsami (lemon green) ce. Ba karamin kyua ta yi ba.
Ya mik'o mini sabon pant. Ya ce na saka miki?"
Na juyar da fuska. Ban amsa ba. Sai da na shanye kunyar na na ce "Tijjani da gaske dai kallon yarinya kake mini. Ban da haka wannan rigar ai ta yiwa Iklima ka'dan bare ni. Kasan kuma Anas ne yake bina ba ita ba."
Kai-tsaye ya ce "Na sani. Sha'awa ta bani, shine na yi kundubalar d'auko miki ita, rabin ku'din na bayar. Abokina yake kawo su daga China. Ta kusa dubu ashirin, sonta nake yi, saka kawai".
Na ce "Tsakani da Allah da atamfa ka siyo mini, yanzu wannan ina zan saka na je da ita?"
Ya ce "Ba dan ki sa ki fita na siyo ta ba. Dan ki saka mini na kalle ki a yadda nake son ganin ki ne".
Ganin ya b'ata fuska ya sanya na juya na saka pant din. Ina juyowa ya bani sabuwar breziya yar mitsil kalar wando da alamu set ne tare suka zo. Ban ce komai ba na kar'ba. Ina ayyana wato ya riga ya gama gane wacce zata yi mini. Domin duk na lefena sun yi mini yawa duk da k'ananu ne sai dai ko nan gaba. Domin da na aikawa Gwaggo akan ta bayar, dawo mini da su ta yi, ta ce nan gaba zasu yi mini na adanasu.
Sai da na shafa hoda na goga jan baki kalar ruwan hoda.
Sannan na zura rigar. Ta shige ni tsab. Ta d'an zarce guiwata da ka'dan, kasancewar ba ni da tsayi. Ya ce "Wow This is Asi beauty lady".
Na dan yi murmushi. Ban ce komai ba. Da kansa ya sa mini hular ya d'auko sabon turare a cikin kayansa da aka rubuta Active woman. Ya bu'de ya hau fesa mini.
Kamshin turaren jikinsa da wanda ya fesa mini suka hadu suak bige ni. Suka isar da wani irin sako akan Tijjani a cikin zuciyata.
Shi kuma ganin na koma masa wata yar yarinya kankanuwa ya sanya ya sure ni. Ya yi falo da ni. Yana ta sakin maganganun da suke da nauyin bayyana wa.
Komai da barin jiki yake yi mini. Ya ajiye ni akan kujera ya ce "Bari na kawo miki abincin Little Angel."
Har cikin zuciyata na ji da'din sunan. Duk sunayen da Bulkachuwa yake fa'da mini babu wanda na ji dadinsa irin little. Domin ya dace da ni k'warai da gaske.
Shiru shiru bai dawo ba. Sai na yi kamar na leka shi, sai kuma na fasa.
Can sai gashi da tray da ya jero kayan abincin.
Da walwala ya ce"Sorry little na bar ki ke ka'dai, ga shi babu wuta bare kallo ya hana ki gundura da zaman jiran kukun naki"
Na k'yal-k'yale da dariya na ce "Wai kai ne kukun?".
Cikin gamsuwa ya ce "Ba ki aminta ba? To mene ne aikina ban da na fita na yi aiki tukuru dan na nemo miki abin da zaki ci.
Idan kuwa ina gida, idai baki bata mini rai ba. Still aiki zan miki dan na hutar da ke shiga kicin kullu yaumin".
Na murmusa ba tare da na ce komai ba, domin na yarda da dukkan zuciyarsa ya ke yin maganar.
Ya bu'de kwanon abincin ga mamakina sai ganin fanke na yi subu-subu sun soyu sun bada kala mai daukar hankali.
Na kalle shi da mamaki na ce "Tijjani yaushe ka iya fanke haka?"
Ya saki murmshin jin dadi ya ce "Ki bari sai kin ci sai ki tambayi na iya ko kuwa makwaki na yi".
Na sauko ya ha'da mini shayi mai madara da milo. Shi kuma ya zuba bak'i.
Muka fara cin fanke wanda ba karamin dadi ya yi ba. Na kalle shi na ce "Ya yi da'di sosai. Na ji har da k'wai da madara ka saka. Maimakon ka bar madara ka zuba a shayinka."
Ya rausayar da kai ya ce "Ke dai ki sha my little".
Ya kashe mini ido sannan ya ce "Ai ina ganin amfaninta. Addu'a nake yi sosai na samu damar da zan daina siyo miki ta sacet. So nake kullum ki sha ta ruwa gwangwani guda. Ta yadda ba zaki dinga gazawa da al'amarina ba".
Kunya ta yi matu'kar kama ni. Na sanya dukkan hannuna na rufe fuskata, ina wani irin murmushin da bansan ta inda yake bullowa ba.
Da k'yar na cigaba da cin abincin bayan ya ce "Duk a wajen Baba na koyi girki. Yadda kika ga Aliyu da Nasiru suna hidima irin ta y'ay'a mata nima irin wannan goyon ta yi mini.
Kullum fa'di take yi, tunda bata samu mace ba, ba zai yiwu a ce ba zamu tallafa mata da kaomai ba.
Kullum cikin fa'da mana take yi mu koyi aikin gida dan wataran mu taimaki iyalinmu. Annabin Rahma da yafi kowa daraja yana tallafawa iyalinsa. Ba mallakewa ba ne dan namiji ya yiwa mace hidimar girki, wanki, ko ta shara ba. Amma kuma ta ce "Ban da wanke wanke wannan na yan daudu ne".
Muka k'yal-k'yale da dariya domin kuwa munsan kawai ra'ayinta ne amma babu aibu idan mutum ya yi. Ya ce "rigar nan fa ta yi miki kyua my little. Tamkar na dauwama ina kallon ki".
Na murmusa ka'dan tare da ce wa"Thank you" a gayance.
Na marairaice na ce "Ya maganar tomfirint din?"
Cikin nutsuwa ya ce "zuwa wani satin zan kai ki da kaina".
Na fa'dada murmushi na ce "Na gode Tijjani".
Ga mamakina sai na ji nauyin gatsa sunan da na yi, ta mamaye ni. Karon farko da na ji hakan a rayuwata.
Na lura shi kuma yana cikin maza yan ka'dan da basu damu da a fa'di sunansu kai-tsaye ba.
Tas muka cinye fanken.
Na kwashe kayan dan nasan idan ya mike zai kwashe ne.
Na kai wajen wanke wanke na ajiye.
Na koma wajensa na ce "Wai da yaushe ka yi kwabin ne?"
Ya nisa ya ce"kina barcin gajiyar da na tara miki. Ni fa duk kallon jaruma nake yi miki. Ashe a tsiwa da dambe da sana'ar k'unshi kike da jarumtar".
Na girgiza kai na ce "oh haka ka ce? Ai shikenan next time zaka gane ashe dazu ba karamin jarumtar na yi ba".
Ya jani jikinsa ya ce "Kin san bana wasa a wannan fannin tsokanar ki nake yi, idan akwai abin da yafi jarumta kin yi dazun".
Na kalle shi cikin nauyi nauyi, kunya kunya na ce "ka ji tsoro?"
Da sauri ya ce "Na ji".
Bai fita ba sai da ya dawo daga sallar azahar.
Muka ci abincin da tare muka yi da shi.
Sannan ya fita zuwa gidan Alh Ado Naira zai yi musu gyaran satellite tunda aka kawo wuta suke ta yi masa waya.
Kamar ana jiran ya fita aka fara zuwa lalle da kitso.
Shike nan muka shirya da Tijjani. Wata irin soyayya yake gwada mini mai wuyar samu. Da ya ga na canja fuska zai fara susuce wa, ya dinga jaye jaye magana, ko fita ya yo sai ya dawo. Matu'kar ban ware masa ba, ba zai samu nutsuwa ba. Ni da kaina na sani an jarrabe shi a kaina. Domin gaba'dayana a tsaye ban fi iya ruwan cikinsa ba. Duk zafin ransa baya son mu yi fa'da. Cikin rarrashi yake tafiyar da ni.
Komai da rawar jiki yake yi mini. Kullum safiya ya wajaba kansa share duka gidan. Ya sa tsintsiya ya wanke band'akin, sannan ya tashe ni na yi wanka. Mafi yawa da safe da burodi muke karyawa. Dan haka shayin ma sai dai na gan shi a filas ya riga ya dafa.
Da nutsu sai na ga ne tunda na daina gudunsa a shimfida shike nan ya tattara dukkan hankalinsa a kaina da lamarina.
Baya taba yin dare a waje.
Ana idar da sallar isha zai dawo ya rufe gidan shike nan sai gobe.
Idan kuwa uzziri ya yanko masa sai ya bugo waya ya sanar mini yana waje kaza. Na ce to tare da addu'ar ya dawo lafiya.
Ranar da yan rikicin suke kusa kuwa, na botsare masa idan ya dawo.
Ya yi ta barin jiki wajen rarrashi na.
Tuni muka fara jarrabawa har mun kusa kammalawa. Da kansa yake kai ni. Idan mun gama sai na yi masa waya ya zo ya dauke ni.
Muna tsaka da jarrabawa Nazira ta haifo d'anta lafiyayye.
Dan haka zarya nake yi tsakanin makaranta da gidanta. Har aka yi suna yaro ya ci sunan wan mahaifin mijinta Ahamd. Ni da kaina na lank'aya masa Abid.
Sosai na yi mata hidima ita da yaronta.
Ranar suna wanda a lokacin watan Maijidda biyu da haihuwa, y'arta Sajida ta yi gubibi da ita.
Tana hannuna ina kare mata kallo. Na rasa gane da wa take kama a tsakanin itayenta Jabir da Maijidda.
Saratu da Firdausi suka shigo. Ita Firdausi ta haihu. Saratu ce ta ke ja itama yau ko gobe.
*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
Na kallesu da murmushi na ce "Ni kam da wa Sajida take kama ne?"
Kafin na rufe baki Maijidda ta ce "Da Abbanta mana. Yo ko makaho ya shafa ai yasan kama take da Honey. Shiyasa yake kara sonta domin kullum ya dauke ta sai ya ce mata "Ta zabo uwarta da kanta".
Gaba'daya jikinmu ya yi sanyi domin kuwa kowa yasan neman magana kawai take yi.
Dan haka sai na mikawa Firdausi yarinya na shiga hidimar raba abinci. Amma k'asan zuciyata ya yi nauyi akan lamarin Maijidda. Har aka watse ban sake yarda na zauna a cikinsu ba.
Har dare duk mana gidan Nazira.
Muna zaune sai ga yaro ya zo ya yi sallamah ya ce "Wai Asiya ta fito su tafi".
Na kasa boye masa abin da Maijidda ta yi.
Tun a hanya na hau rattaba masa abin da ta yi mini.
Maimakon ya bi bayana ya fa'da mini maganganun da zan ji da'di. Sai ce wa ya yi "To mene ne na bacin rai a ciki? Ke ma Ubangiji ya za'ba miki wanda yafi mijinta son ki, to sai me kuma? Ki bar maganar nan inba so kike na ga ne kishinta kike yi har yau ba".
Takaici ya kama ni goma da ashirin. Na kame bakina na yi dif. Amma na riga da na harzuka k'warai da gaske. Ga mamakina sai kawai shi ma ya share ni. Muna isa gida ya gama uzzirinsa ya yi kwanciyarsa ya rabu da ni.
Ba'kin cikin hakan ya sanya na dinga kukan sharbe. Bai ko motsa ba, bare ya nuna ya ga ne halin da nake ciki. Da kaina na kwanta. Da asuba bayan ya dawo nan ma kwnaciya ya yi bai nemi ni ba kamar yadda ya sabar mini. Ai sai kawai na fashe masa da kuka mai sauti.
Ya janyo ni jikinsa ya ce "Yi shiru, na baki hakuri kin ga".
Cikin kuka na ce "Akan me zaka yi fatali da ni?"
Da rauni a muryarsa ya ce "Akan me har yau baza ki bar kishin Jabir ba? Kina tunanin zan ji dadi idan na ga ne har yau ban yi nasarar shafe shi a ranki ba?"
Na yi shiru sai shesshekar kukana ne yake tashi.
Haka ya ajiye fishin nasa ya dinga rarrashi tare da shafata cikin nutsuwa. Daga hakan kuma ya shiga yin abin da baya gundara da yinsa.
Sannu a hankali muke rayuwa. Duk yadda Bulkachuwa yake tarairaya ta, akwai abin da yake mini wanda yake ci mini tuwo a k'warya.
Duk yadda na so na dinga saka mana kifi ko nama a cikin girkinmu ya k'i yarda. Idan kuwa har na bayar aka siyo na girka to zai ci iya abincin ne ya bar mini nama ko kifina.
Rannan da na nuna b'acin raina.
A zafafe ya nuna mini yatsa. Ya ce "Iya abin da nake da shi zan ba ki, ba kuma zan zauna ki shiga cikin lamarin rik'on gidana ba. Ke dai tunda kina samun ku'di fiye da ni, komai kike so ci akan abin da nake da ikon ba ki, ba zan hana ki ba. Amma ni kada ki ajiye, ko ki ba ni, bana so".
Ganin da gaske baya so din, sai na daina. Iya abin da ya siyo shi zamu ci. Da na bi yadda yake so, sai muka samu dai-daito. Domin duk ranar da ya ga kifi ko nama alhalin ba shi ya siyo ba. To fa yini zai yi babu sukini da walwala. Sai dai wani zubin na kan auni mangyada ko manja na zuba a galan din namu, ko na sayi ledar maggi. Wannan bai cika fahimta ba. Tunda wani lokacin zai siyo gwangwani biyu a leda ya juye a ciki.
Dan haka a duk lokacin da ya samu sararin siyo kwalba, kwanaki ka'dan nima zan sake siya na zuba. To baya ankarewa da hakan.
Abin da na lura bai dauki maganar da aka yi na ce wa ba zai iya ciyar da mu ba da sau'ki.
*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
✍️
.
*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers*
*08089965176*
*07084653262*
*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633
55&56.
Ranar asabar ya dawo da rana. Sai ga shi da macaroni guda biyu hakan ma taliya, da shinkafa mudu guda. Sai sauran kaya danginsu maggi da sauransu.
Na karb'e shi da walwala kasancewar ba kasafai nake yin k'unshi asabar da lahadi ba. Sai kitso ne yafi yawa a wadannan kwanakin, saboda ana hutun karshen mako.
Doguwar riga ce ta yadin material din *Umm Nihla collection*
*07020695644*
A lokacin kuwa watanmu kusan bakwai da aure.
Da na lura sai na ga kamar ba a cikin nutsuwarsa yake ba.
Na gabatar masa da ruwa da abinci.
A hankali ya ce "sai na dawo zan ci. Dauko mayafinki mu je gida".
Gabana ya takarkare ya buga. A ki'dime na ce "Me ya faru?"
Ya numfasa ya ce"Dada ce ta.."
Kafin ya karasa na katse shi ta hanyar saka salati mai tsananin gaske. Tare da ce wa "Ta rasu?" Na fara k'walla ina cewa "Dada yau kwana ya k'are Innalillahi wa inna ilaihir rajiun". Allah ka gafarta wa Dada!
Ya bu'de baki ya ce "Yaushe na ce "Ta mutu? Kin san yanzu damina ta tsananta. Ta je zagaya wa ne sai shaddar ta rufta da ita. Allah ya sa an ji k'arar ruftawar, da ba haka ba kam, da tuni ba wannan maganar ake yi ba. An ciro ta amma baki ga ba, duk ta daddauje sosai."
Bansan ya aka yi ba dariya ta sosai ta k'wace mini.
Na dinga k'yal-k'yale wa. Ya yi sak'are yana kallo na. Can ya kasa jurewa dariyar da nake faman yi babu k'ak'kautawa.
Ya kalle ni ya ce "Ban da dai lamarinki akwai k'uruciya mene ne abin dariya a ciki? Dada fa na ce miki ta fa'da shadda. Da kuma rai ya yi halinsa me zaki yi?"
Cikin dariyata na ce "Kuka zan yi mana. Baban Kasuwa nake yiwa dariya da ya kasa gyara band'akin gyatumarsa da take nuna masa soyayya ta daban shi da ahalinsa."
Gau na ji ya hambare mini baki. Ya d'aure fuska ya ce "Idan zaki iya yiwa k'anin ubanki rashin kunya, to amma kuwa ba a gabana ba. Domin kawuna ne k'anin uwata na kuma yarda k'aninta ne. Da zuwa na yi na dauke ki, ki gaisheta ganin kusan kowa na gidan har Ubaida. Amma tunda zaki dawo da rashin kunyar ki, sai ki zauna ki yi ke ka'dai".
Ya mike ya fice. Na bishi da gudu. Murya a marairaice na ce "Zan bika Tijjani dan Allah".
Ya zuba mini ido yana yi mini kallo mai tsananin gaske. Na sani so yake na ba shi hakuri, ni kuwa ban ga me na yi ba. Ai gaskiya na fa'da. Bayan haka ai ya buge mini baki, dan haka na waske na k'i ban bada ha'kurin.
Kallon ya shige ni, na fara bubbuga k'afa. Ina ce wa "Saboda Allah me na yi maka?"
Ya jijjiga kai ya yi tafiyarsa, ba tare da ya ce uffan ba.
Ni kuwa da na hasaso Dada a masai sai na sake tuntsire wa da dariya.
Sai yamma lis ya dawo. Kai tsaye falo ya shiga. Na bi shi ina masa sannu. Na zauna. Ya ce "zubo mini abincin".
Na fita na kawo masa, ban zauna ba sai da na dauko masa ruwa a fridge.
Sai da ya gama cin abincin. Sannan na kalle shi bayan na d'aure fuska na ce "Ya jikin Dadan kuwa?"
Kai-tsaye ya ce "Da sau'ki. Amma ta samu tagarde a hannunta."
Na sake yin kalar tausayi na ce "Ayyah! Allah ya bata lafiya."
Ya amsa da "ameen" yana daddana wayarsa.
Can na nisa na ce "Tijjani wa ya yiwa Dada bik'in kashin da ta kwaso?"
Kamar ba zai yi magana ba. Sai kuma ya ce "Gwaggo ce".
Na zabura na dafa k'irjina na ce "Gwaggota?"
Kansa na k'asa ya ce "ita fa".
Kawai sai na fara kuka ina cewa "Na rantse da ina nan bazan bari ba. Duk yadda take tsangwamar ta sai kuma ta zo ta yi mata irin wannan wahala alhalin tana da y'ay'anta birjik?"
Kansa na kan wayarsa dai, ya ce "Ai da yake tana mutunta mijinta ne. Baban Marina aikin ya kama, da yake ita mace ta gari ce, sai ta fanshi mijinta".
Na zabura na ce "Wallahi ba shi ya kama ba. Ina ce ga Baban Tsakiya nan, ga kuma dan k'wai Baban kasuwa, dukkansu suna da matan auren kuma".
A fusace ya ce "To basu yi ba, ita Gwaggo ita ce ta yi domin tafi dacewa ta yi aikin".
Na harzuka na ce "Ban gane ba Tijjani. Wato ita ce kaskantacciya kake nufi ko me? Ai ba ita ce babba ba, ga Mama nan".
Ya dago ido cikin ido ya ce "Asiya na ce miki da ita aikin yafi dacewa shiyasa ta yi d'in".
Na mike na ce "Wallahi aikin bai dace da ita ba kai ma ka sani. Y'ay'an cikinta ne a hak'ku. Baba Maryo fa?" Ga mamakina sai na kasa ambato Baba ta Bulkachuwa.
Shima ya mike ya ce "jikinki na yi miki k'aik'ayi Asiya Toro. Bilhiillazi kika yi gigin zaginsu a gabana sai jikinki ya fa'da miki. Bazan dauki wananan mugun halin ba. Ke abu ba zai wuce a wajen ki ba? D'azu dukkansu sai da suka tambaye ki, amma ke kin k'wafesu a cikin zuciyarki".
Na ja tsaki na ce "Kana yi mini dukan da jikina ya fa'da mini. Ka tabbatar kai ma sai naka jikin ya fa'da maka. Domin kuwa dai ka daki aurenka tunda shine lasisinka na dukan jikin nawa".
Ya kasa ce wa komai. Amma na lura ba k'aramin b'acin rai ya shiga ba.
Ya kewaye ni ya fice. Bai dawo gidan ba. Sai wajen goma. Ni kuma tuni na sake fusata. Dan haka da ya dawo ya shigo d'akina ban ko kalle shi ba, bare nasan me yake ciki.
Ga mamakina shima bai kalle ni ba, ya koma k'arshen gado ya kwanta.
Washagari ma da asuba ya fice, k'ofar d'akin ya buga da k'arfi. Wanda na gane tashina ya yi dan na yi sallar asuba.
Ya dawo ya ajiye burodi. Ya ha'da nasa shayin ya karya ya fice.
Na yi abinci na ajiye masa na rana, amma bai dawo ba.
Da yake lahadi ne. Mutum biyu sun zo lalle, haka kitso ma mutum uku na yiwa. Kafin la'asar babu kowa.
Duk da zuciyata babu da'di a dalilin yadda na lura Tijjani ya tsananta fishin da yake yi.
Wayata na dauka na shiga manhajar WhatsApp. Sai ganin Umm Nihla ta yi posting hadaddun materials daga Malaysia. Ina matu'kar son irin yadukan. Ba don komai ba, sai dan basu da nauyi, sannan gasu da taushi, ga kuma sau'kin ku'di ainun. Abin burgewa kuma basa kodou sai da ka gaji da su ka bayar.
Wani yellow da blue suka tafi da ni. Kai tsaye na ce mata ina sonsu. Ga mamakina duk ku'din basu yi tsanani ba.
Ta tambayi a wanne garin nake? Na bata amsa da Toro. Ta ce to sai a saka miki a motar Jos kenan?. Tunda kunfi kusa akan Bauchi.
Na ce "A a akwai sister ta Aisha Lame jakadiyar oriflame. Ita zaki aikawa zasu same ni.
Ta yi mamakin cewar nasan Aisha Lame.
Na ce "To ai yar garinmu ce. Sannan muna da alaka ta wajen kakata da ta haifi Babana.
Umm Nihla ta turo emojin mamaki ta ce "Ai kuwa Aisha na da kirki, kafin na bar Nigeria a wajenta nake siyayyar kayan kwalliya da spices. Farashin kayanta mai sau'ki ne ainun".
Cikin alfahari na ce "Ai ko anan haka ahalinsu suke, mutane ne masu kirki kwarai da gaske. Nima da aurena ta bani kyautar fame wash. Yanzu kuwa na tura mata ku'din wani zan siya saboda na gane muhimmancinsa".
Daga haka ta turo mini asusunta da zan tura ku'din.
Sai mamakin yadda duniya ta samu cigaba nake yi. Ina Toro amma na sayi kaya a hannun wacce take zaune a Malaysia. Har na tura ku'din, ta tabbatar mini ta ga ni. Nima kuma ina da tabbacin zuwa gobe zan ji Aisha Lame ta karba mini. Na saki gauron numfashi.
Na fara lissafin ku'dina domin so nake na yi k'undubalar fara shafa man oriflame. Idan nafi haka sheki da d'aukar ido zan fi daukar hankalin Tijjani fiye da yanzu.
Haka na lalubo lambar Aisha Lame cikin sa'a tana online, ita da kanta ta za'ba mini Wanda yafi dacewa da farare. Itama take na tura mata ku'dinta. Na fa'da kuma za'a kawo mata material d'ina ta ha'do ta aiko aiko mini. Muka yi sallama.
Yau ma sai bayan Isha ya dawo. Ban kula shi, shima bai kula ni ba.
Kwanaki uku muna fishi da juna. Abin na cina a zuciyata, amma na daure na matse na share shi. Mussaman da bai shata mini layi da dakin sana'ata yadda yake yi a watannin baya ba.
A kwana na hudu Gwaggo ta yi mini waya a lokacin ina tare da masu lalle.
Muka gaisa ta ce "Yabi ba zaki zo ki gaida Dada ba ne? Kaf yaran gidan nan kowa ya zo ban da ke. Kuma kullum sai Tijjani ya zo ya duba ta. Amma daga ke har shi baku yi hankalin ki zo ki duba ta ba. Sai ta mutu ki zo gaisuwa ne?"
Jikina ya yi sanyi na ce "Zan zo. Shine bai ce na zo ba".
Da sauri ta ce "Ke ma k'aramab niyya ce da ke. Nasan Tijjani ba zai hana ki zuwa gaida Dada ba".
A sanyaye na ce "Ki yi ha'kuri zan zo In sha Allah".
Ta saki gauron numfashi ta ce "Ya dai kamata".
Sannan ta kashe wayarta.
Kamar almara ana idar da azahar ranar sai ya dawo.
Cikin sa'a na gama yiwa wacde nake sawa. Saura mutum biyu su kuma dama sai mun yi sallah.
Ban yi abinci ba tunda ba dawowa yake yi ba. Ko cefane ne idan ya kawo mini. A k'ofar gida zai bawa yaro ya shigo da shi, ya yi juyawarsa.
Na bishi falon. Murya a dakushe na ce "Sannu da dawowa".
Ya amsa babu walwala.
Sannan ya ce "yunwa nake ji. Me kika dafa?"
Na dauke kai na ce "Ban yi komai ba, tunda nasan cikina kawai zan yiwa".
Shima tasa fuskar a daure ya ce "To sai ki dora yanzu. Sauri nake yi kuma".
Ban ce komai ba, na juya na shiga kicin din. Na dora farin ruwa dan nasan ina da miya a fridge.
Daga nan na nufi bayi dan yin alwallah.
Sai da na zuba makaroni sannan na yi dakinmu dan yin sallah.
Bayan na idar na shiga falon na dauko miya. Na tarar ta nuna. Na ta ce na dauraye. Na dora miyar dan ta d'umama.
Na shirya a tire na kai masa. Bai nemi na zauna muci kamar yadda muka saba ba. Nima kuma ban zauna di'n ba. Na tafi na cigaba da yin lallena.
Ya gama ya fita.
Har dare ina ta sakar yadda za'a yi a gobe na je na gaida Dada.
Muna kwnace kowa na k'arshen gado. Dukkanmu mun kasa barci da alamu akwai abin da ya damemu. Ni dai nasan yadda zan fita gobe nake ta tufka da warwara.
Tsawon lokaci muna hakan. Sai kuma na ga ya mirgino ya same ni a jikin bangon da na lafe.
Bai ta'ba ni ba. Amma ya mannu da ni sosai. Murya k'asa k'asa ya ce "Asiya Toro idan muna fa'da ai bai kamata mu sanya aurenmu a cikin rikicin ba. Kawai mu yi harkar aurenmu. Allah bar shi da safe muci gaba da gabarmu tunda bani da darajar da zaki mini laifi ki bani hakuri".
Nan da nan na gano jarumtarsa ta kare ne. So yake mu kebe. Maimakon na yarda tunda nima na kosa da gabar sai kawai na kwabse na ce "Sawa na nawa kuma? Ai tuni ka sanya shi a ciki. Yau kwananka nawa da yin fatali da shi?"
Ya ru'ko hannuna a hanzari ya ce "To yau na cire shi Asiya. Mu shiryasu kin ji. Mu din ma, ko yanzu kika bani hakuri mun shirya. Kin bata mini rai. Wai har ki ce mini zan doki aurena. Ai ban zaci har yau ba kya sona ba Asiya".
Yadda ya yi maganr sai ta yi matu'kar ta'ba ni. Ban san me yasa yake yawan bani tausayi ba.
Na numfasa na ce "Nima ai ka bata mini rai. Akan me zaka dinga duka na? Ko ka dinga yi mini barazana da duka. Ai na dauka ko wani ka ga zai dokar maka jikin nan nawa sai yadda karfinka ya k'are, ba wai kai da kanka ba".
Da sauri ya ce "Bilhiillazi ba wanda zai doke ki a duniyar nan na bar shi ya kwashe kalau. Sai ko Gwaggo da Baban Marina. Amma kowa ye zan motsa k'wannjina a kansa. Ni kuma ai ba haka siddan nake dukan ki ba. Sai na ga zaki kuskure. Sannan kuma ai ba mai yawa nake yi ba".
Na cuna baki duk da a duhu ne na ce "To ni dai bana so, ka daina".
Da sauri ya ce "To. Amma kema ki daina yi mini taurin kai da rashin kunya. Idan na ce miki ya isa, ko bari. To ki bari din kawai".
Ban amsa ba, amma na ji, zan kuma kiyaye.
Ya nisa ya ce "To me zaki ce mini?"
Na fara tirza kafa ina kukan shagwaba tare da cewa"Ai tunda ka buge mini baki shikenan an yi zuza. Kuma ba sharri na yi musu ba. Gaskiya na fa'da.".
Ya ru'ko ni ya ce "Amma tunda raina ya baci, kuma har na fa'da miki ba, sai ki rarrashe ni, ki kwantar mini da hankalina ba?"
Na dinga k'unk'unin ina fa'din "Ni ba wani rarrashin k'ato da zan yi".
Da yake bai ji me nake fa'da ba.
Ya jani jikinsa ya rungume. Ya dinga shinshinata tare da sakin maganganun masu nauyi.
Ni kuma na cure jikina, na dunk'ule. Na dinga ja masa rai. Ban yarda na sallama masa ba. Sai da na ce "Yaushe zan je na gaida Dada?"
Murya na rawa. Ya ce "Kina ce mini sorry gobe zan kai ki tun safe ki yini a can".
Da murna na ce "idan ban ce maka ba fa."
Ya ce "Zan kai ki, amma minti talatin tana cika zan tiso ki a gaba mu dawo gida".
Sanin da na yi da gaske yake yi, ya sanya na bu'de baki cikin walwala na ce "Ka yi hakuri Tijjani".
Nan da nan ya sake rungume ni sosai ya ce "Thats my little girl. Na huce, na kuma yafe miki. Daga Nan abubuwan da suka biyo baya masu nauyi ne. Domin Ni da kaina na tabbatar na yi missing Tijjani da jagwalgwalonsa masu sanya ni tsumaye. Abin da ban yi zaton zan yiwa Tijjani ba, sai da na yi masa a wannan daren. Wanda ba karamin gigita shi na yi.
Da safe ya tashi ya dinga yi mini hidima da bare-bare. Ni kuma kunya ta yi mini k'awanya.
Da wuri muka shirya ya kai ni gida da kansa. Ya kuma ce sai an yi sallah isha zai zo mu tafi. Sai da zamu shiga gidan ya bu'de but din mashin d'insa ya fito da lemon maltina guda biyu da lucozade shima biyu a leda. Ya mik'o mini ya ce "Ki bata".
Na kar'ba tare da cewa "Na gode! Ni ban yi tunanin na siya mata komai ba".
Bai ce komai ba, muka shiga gidan. Nan kuwa jakar hannuna cike take da omon viva 85kg zan bawa su Gwaggo. Da kuma alwar da zan raba wa kannena.
Tare muka gurfana da shi a gaban Dada muna gaisuwa cikin tausayi da alhini. Bansan ai haka ta jigata ba. Kanta har a lokacin a suntume ya ke. Ga hannu a targade ya sha nadi da bendeji. Ga fuska da k'afafuwa duk sun kuje sosai.
Duk yadda ta ji jiki, har jikin ya yi yaushi amma bakinta ras. Ta kalle ni ta ce "Ai Yabi Allah ne yasa da sauran kwana a gaba. Gaba'daya ji na yi tamkar wadda k'asa ta dare na afka. Kai wato wanda yake yawaita ro'kon Allah da neman kariya daga tsautsayi da asara zai ga sassauci a lamarinsa. Ni nasan k'addara bata sauya wa. Amma k'arfin addu'a yana rage zafinta. Na gode wa Rabbani da ya sanya ni cikin bayinsa masu yawan ambatonsa masu kuma yawan gode masa."
Tijjani ya ce "Haka ne Dadarmu".
Ta muskuta, na kalle ta tausayin ta ya sake kama ni a dalilin nasan bata ji dadin zaman ba.
Ilai kuwa kafin na yi wani abu. Sai cewa ta yi "Mai sunan manya matso ka gyara mini zaman nawa. Gaba'daya a takure na ke."
Da sauri ya matsa cancakat ya cira ta. Ya ce "Asiya sa hannu ki gyara mata zaninta".
Na gyra mata din cikin azama".
Ya mayar da ita ya tokare mata baya da filo mai tauri. Ta ce "Allah ya yi maka albarka mai sunan manya. Allah ya tsare ka daga tsautsayi da asara. Allah ya sa kafi karfin magauta. Ubangiji ya bu'de maka k'ofofin alheri".
Ya dinga amsawa cikin walwala.
Na k'ulu, wato Tijjani kawai zata yiwa addu'a.
Na daure na ha'diye ban fashe ba.
Can ta zuba mini ido. Sai kuma ta koma ga Tijjani ta ce "Mai sunan manya da alama komai ya dai-daita. Wannan haske da sheki da cikar da Yabi ta yi ba iya na abici ba ne kawai. Ana takar ta sosai gaba'daya ta fara bude wa"
Ba ni ba, hatta shi kansa maganar ta yi masa nauyi ainun. Ya yi maza ya sunkuyar da kansa ba tare da ya ce uffan ba.
Ita kuwa ko a jikinta sai faman murmushi take yi tana fa'din "Alhandulillahi. Allah kasa zan ga jininka kafin duniyata ta kare".
Na mike bayan na tura mata ledar gabanta na ce "Ga shi nan Dada. Allah ya k'ara lafiya bari na tafi inda nima za'a yi nan nan da ni. Kin riga kin saba da hubbu ra'as. Tunda muka zauna ba kya ta tawa. Sai mai sunan manya, mai sunan manya. To na barku ku k'arata".
Ta k'yal-k'yale da dariya bayan ta ja ledar tana ce wa "Wayyo Yabi mai dogon hannu. Da'dina da ke akwai ungo. Duk cikin jikokina na d'aki ke ce kika kawo mini tsarabar dubiya. Ko wacce da sun zo da mijinta ta ga ya bani dubu ko dari biyar shike nan sai ta ja ta tsuke. Wai suna nufin mazansu sun fanshesu. Har Nasiba haka ta zo mini hannu na dukan cinya. Ita kam mijinta bai zo ba, bare ya bani.
Amma mijinki kullum ne. Sai ya kawo mini kunshin nama, ko lemo da ayaba. Ai yanzu na ga ne biki mai zuciya a ke fa'dawa ba mai dukiya ba".
Na ce "Ke kuma Dada da son a baki ki ke. Ban da haka ina lafi ma da aka zo aka duba ki?"
Na kalli Tijjani na ga ya kyafta mini ido, alamun na bar maganar haka".
Na sanya takalmi na ce "masa na yi cikin gida. Sai ka shigo".
Na tafi na bar shi tare da ita. Ina jin tana cewa "Ah yarinya ta yi bundum ta yi cikar daki. Ni dama nasan ruwan wankan aure duk zai sanya muku nutsuwa."
A zaure muka yi kicibus da Yaya Anwar yayan Nasiba. Na gaishe shi da mutunta wa domin shi d'in kamamme ne.
Ya amsa tare da ce wa "Yabin Bulkachuwa yau a gidan Marina? Tunda aka yi aurenku ke ce ban ga kin zo ba. Bulkachuwa ya rufe ki ruf. Ma sha Allah! Allah ya k'ara ha'da zuciyoyinku".
Kunya ta kama ni. Na wuce ban ce komai ba. Amma sunan da ya kira ni da shi ya sanya mini wani irin shauki a zuciyata. Duk kame kamena na fara gasgata cewa na fara son Bulkachuwa. Irin son nan mai shiga a hankali ya yi karfi mai tsananin gaske. Ga shi wani irin kishinsa nake yi irin wanda ban ta'ba jin irinsa akan ko wanne namiji ba.
Kawai ina waske wa ne dan kar ya fahimci halin da na ke ciki. Tunda shima na fahimci mai iyashege ne.
Ina shiga k'ofarmu aka dinga yi mini oyoyo tamkar ba Yabin da kowa ya ga ji da ita ba. Hatta Mama sai da yi mini barka da zuwa cikin sakakkiyar fuska. Inna kuwa sai kiran kananun y'ay'anta take yi tana fa'din "ku je ku yiwa Adda Yabi oyoyo."
Na fito da alawa na dinga bawa kowa a hannunsa. Tun fil'azal kyautar alawar da nake yi musu ya sanya suka fi sakewa da ni. Dakin mama na fara shiga na gaisheta na ajiye mata omonta zare guda. Sannan na shiga na Inna na bata nata.
Sai kuma na dawo dakinmu na baje.
Na fa'da kan gado na fashe da kuka a hankali.
Ta zauna jikinta na rawa ta ce "Duk yadda jikinkinki ya nuna kina zaune k'alau ashe ba hakan ba ne. Daga zuwanki zaki daga mini hankali, ki shafe murnar da na ke ciki ta ganin ki, cikin yanayi me kyau?"
Na share idon na ce "Ai ke ce "Baki taba zuwa mini ba. Kowa a gidan nan ya je amma ban da ke. Ko har yau fishi ki
ke yi da ni Gwaggo?"
Ta ri'ke hannuna ta ce "Ba komai a zuciyata game da ke sai alheri mai yawa Yabi. To me zan je na yi miki ne? Babanku ya je. Mama ta je, Inna ta je, yayarki tana zuwa. To su duk kin raina k'ok'arinsu?"
Na juyar da fuska na ce "Ban raina ba Gwaggo. Amma ina so ki zo".
Ta mike ta ce "Zan zo. Amma sai kin haihu."
Na rufe fuskata domin kunya na ji irin sosai din nan.
✍️
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*
57&58.
Yini na yi cikin farin ciki. Domin Baban Marina tunda ya dawo cin abinci da azahar, bai fita ba. Zama ya yi muke hira ni da shi domin ba k'aramin da'din ganina ya yi ba.
Sai da aka fara kiran sallar la'asar sannan muka yi sallama ya fice.
Sai dare kuwa muka tafi kamar yadda ya yi mini al'kawari. Albarka na sha ta daga wajen mahaifana har da Dada ma.
A k'ofar gida ina shirin d'ale wa mashin din, sai ga Baban Tsakiya. Na yi kamar ban gan shi ba, na dauke kai. Tijjani ya mini inkiyar na gaishe shi amma na waske. Sai shine da kansa ya ce "Tijjani wannan ba Yabi ba ce?".
Kafin ya ba shi amsa Na rusuna ka'dan na ce "Baban Tsakiya ina yini".
Ya ce "Ai har yanzu ba zaki daina kama suna da inkiya ba?" Ban ce komai ba daga hakan. Na haye mashin d'in ko kunyarsa ban ji ba. Duk da yana kallona haka na dafa Tijjani da zan hau din, tunda har yau ba zai shafa mini lafiya ba.
Ya kad'a kai ya ce "Tijjani Allah ya k'ara maka hakuri da juriya".
Ya kasa amsa masa, amma gaba'daya na ga ya yi wani iri.
Kafin ya ja mashin din sai ga J ya fito da alamu tare suke da mahaifin nasa.
Ya mika wa Tijjani hannu suka gaisa.
Hasken solar da gwamnati ta kafa akan layika ta haske fuskokinmu tunda muna da ita a k'ofar gidanmu.
Karon farko da na kalle shi ban ji wani abu na so ko na burge wa ya taso mini ba.
Domin ko ranar da muka je gidansa yin barka sai da tsumin sonsa ya taso mini.
Na bu'de baki na ce Yaya J ina yini, ya Baby?"
Da wani irin yanayi ya ce "Lafiya k'alau Yabi. Ya kike, ya ruwa?"
Na amsa da Alhamdulillah".
Daga haka Tijjani ya ja mashin dinsa muka wuce.
Lafiya k'alau muka isa gidan, muka gama uzzirinmu muka kwanta. Tsawon lokaci ina jiran na ji hannunsa a jikina shiru. Na dinga mutsu mutsu, amma bai motsa ba. Da k'yar na samu barci ya sure ni. Da asuba ma hakan ya yi, ga shi ya riga ya sabar mini da al'amarin dare da asuba basa wuce mu sai idan fashin sallah nake yi. Shi ma sai mun yi abubuwan da zamu samu nutsuwa.
Na rasa yadda zan yi, domin kunya ta hana na fara kai hannuna gare shi.
Na daure dai nima na share. Muka koma barci. Ni na fara tashi, na gyara gidan, na duba na ga akwai taliyar hausa. Nasan kuma yana sonta sosai. Sai kawai na d'ora jolof d'in ta.
Ina shirin gamawa na ga ya fito ya yi band'aki. Can kuma ya fito da brush dinsa ya zauna daga gefe ya yi, sannan ya mayar ya ajiye.
Maimakon ya shigo kicin ya taya ni mu k'arasa kamar yadda ya saba sai kawai na ga ya yi falo.
Na fara jin wani iri a dalilin sauyinsa. Na dinga tunanin me ya faru. Amma na kasa gano ko na yi masa wani abu.
Na gama, na tafasa shayi. Na ha'da komai na kai falon.
Muka fara karyawa amma babu doguwar hira yadda ya saba mini.
Muna zaune, jigum jigum yaro ya yi sallamah daga ba'kin k'ofa ya ce "Wai ana sallama da Tijjani".
Na zabura na ce "Kai shigo". Ya shigo na kare masa kallo, gaba'daya ba zai wuce shekaru takwas ba.
Na zare masa ido a dalilin na ji haushin gatsa sunan da ya yi. Na ce "Ba zaka ce ana sallama da maigidan ba sai ka wani gatsa sunasa tamkar sa'an ka. Zaka iya fa'din sunan Babanku gatsal?"
Yaron ya yi shiru yana kallona da alamu ma tsorata ya yi kada na rufe shi da duka.
Sai lokacin Bulkachuwa ya ce "Kai je ka ce "Ina zuwa".
Ya mik'e ya bar ni.
Tunda ya fita sai yamma ya dawo. Bai ce mini ga inda ya je ba, nima ban tambaya ba. Na gabatar masa da ruwa da abinci na yi tafiyata wajen k'unshina. Domin na fara jin haushin daddaurewar da yake yi mini haka siddan.
Haka da daddare ma ya sake matse wa bai ta'ba ni ba.
Kwanaki uku ke nan, muna haka, na fara k'osawa domin gaskiya ya riga ya yi mini sabo a harkar, tun ina turjiya, ina raki har na zama yar hannu da al'amarin nasa. Sannan na fahimci nima irin halittarsa ce da ni. Ina son harkar, ina jin da'din ta.
Ban sani ba ko ya fahimci hakan ne shi yasa zai fara yi mini gayya.
Sai na yun'kura zan tambaye shi dalilin sauyinsa sai na yi maza na fasa. Ina jaddada wa zuciyata na ja ajina. Shi da yake namiji ma ya yi jarumtar runtsi idonsa daga gare ni, sai ni mace ce zan k'osa?.
Dan haka na yi hakuri, na zuba masa ido, amma gaba'daya bana cikin nutsuwa. Mussaman idan ya shek'a kwalliya ya baza turare sai na ji tamkar na yi tsalle na mak'ale shi.
Sai ya fita nake samun damar na yi kukana. Ina ayyana wai ni Tijjani yake yiwa wannan wula'kancin haka siddan dan ya fahimci na fara sonsa.
Na fara zargin akwai abin da yake yi a waje da ya sanya yake iya kawar da kansa a kaina.
Gaba'daya na rasa sukuni. Na yi wani iri.
Ranar da muka yi kwana hudu a cikin wannan halin. Gaba'daya ya juye mini, tamkar ba shine mai rawar jiki da tsoron ganin fishina ba. Tamkar ba shine mai kulafacina kamar me ba.
Ranar da wuri ya shigo. Na yi wanka na sanya riga da wando silky. Wando iya guiwa rigar ma iya tsayinta kenan wando kawai ta rufe.
Na taje gashina da yake a tsefe na mulke shi da man gashi na kwakwa da asalain man alaiyadi. Na dauko turarena na mai maiko na oudi na murtsike hannayena da jikina har ma da gashin. Na sake dauko turaren active woman da Tijjani ya canja mini na bi jikina na feshe. Na saka hula marar nauyi kalar kayan barcin nawa.
Na fita na same shi yana kallon labaran NTA Bauchi.
Na zauna ya dago ya kalle ni. Domin na tabbatar kamshina ya kai masa caffa mai yawa.
Na sassauta na ce "Wai mun b'ata ne?"
Cikin nutsuwa ya ce "Da yaushe?"
Na yi sakare ina kallonsa. Na numfasa na ce"Ai tambayar ka na yi."
Ya girgiza kai ya ce "To ke mun b'ata ne?"
Na rasa me zan ce masa ma. Na nisa na ce "Nasan bamu b'ata ba. Amma na ga ka sauya ne".
Ya daure fuska ya ce "Tun yaushe na canja d'in?"
Na ce "Tun kwanaki hudu, tun ranar da ka kai ni gida".
Ya yi shiru tsawon lokaci kafin ya bu'de baki ya ce "Kuma sai yau kike bu'katar sanin dalilin sauyin nawa saboda baki d'auke ni a bakin komai ba?"
Ga mamakina sai na shiga rud'u na ce "To ai kai ne zaka fa'da mini."
Ya girgiza kai ya ce "Babu damuwa ki cigaba da zaman jiran na fa'da miki".
Idona ya ciko da k'walla. Na zuba masa ido sosai na nuna kaina da yatsana na ce "Ni kake wula'kantawa saboda kawai ka shiga ka fita kasa na saba da kai ko?.
Ai shike nan na gode".
Daga hakan na kifa kaina a hannun kujerar na fashe da kuka mai tsananin gaske.
Ya taso da azama ya zauna kusa da ni. Ya ru'ko ni na fizge tare da ce wa "Ba ruwanka da ni, komai kake yi na barwa Allah. Ka cigaba da yi mini wula'kanci komai lokaci ne ai, watarana ba zaka yi ba".
Ya sake tarairayo ni jikinsa yana kamo weak points dina. Jikina ya fara tsuma. Amma na sake k'wace wa na mike, cikin muryar kuka na ce "Bana so Tijjani, ka bari na fa'da maka".
Na fice na yi d'akina ina kuka sosai.
Sai da ya yi wanka sannan ya shigo d'akin har lokacin kuma ina dukunkune ina kuka sosai.
Sai da ya yi shafa'i da wutiri sannan ya tarar da ni a gadon.
Bai kwanta ba. Ya zauna ya kaurara murya ya ce "Asiya tashi mu yi magana."
Na share shi, na k'i na nuna ma na ji shi.
Ya saka hannunsa biyu ya d'aga ni ya zaunar da ni.
Na sake yun'kurin koma wa na kwanta dan na nuna masa ba ni da lokacinsa, sai kawai na ji ya bu'de murya sosai ya ce "Wallahi idan kika kwanta idan ranki sun kai dubu ki tabbatar sai na bisu d'aya bayan d'aya na b'ata su."
Jin ya rantse sai na zauna din. Amma na tattaro dukkan fishi na yab'a a fuskata.
Ya jima yana kallon yadda nake tunbatsa.
Shima ya d'aure tasa fuskar ya ce "Ki saurare ni da kunnen basira Asiya Toro".
Jin ya fadi wannan sunan na sake hassala ainun.
Ya furzar da iskar baki ya ce "Ranar da muka je gida kin wula'kanta ni, kin tozarta ni!
Watannin baya na fa'da miki, ba zai yiwu a gabana ki wula'kanta iyayenmu ba. Idan kin ture girmansu na k'annen mahaifinki ne, to ki sani baki isa ki ture nasabarsu da ni ba. Ina kuma da hak'kin ki mutunta iyayena. Dole ne, wajibi ne Asiya ki mutunta mini dangin uwata matu'kar kina son mu zauna lafiya. Ba zai yiwu ina aurenki kuma in zuba miki ido ki dinga yin rashin mutunci ba. Bilhiillazi wannan ne karon k'arshe da zaki ga wani cikin iyayenmu ki k'i gaishesu, ko ki yi musu gaisuwar je ka na yi ka".
Na fara kuka ina ce wa "To ina ruwanka ne kam. Kai baka ga irin k'iyayyar da suke yi mini ba? Saboda baka kishina, saboda kai sun yarda gyatumarka yar'uwarsu ce shiyasa kake ganin bekena. Duk abubuwan da suke yiwa ubanmu baku da kaico. Ai ka sani ba sai na fa'da ba, ko auren nan nawa sun yi sanadinsa ne dan kawai suna ganin bazan cigaba ba.
Amma da sun tabbatar zan samu nutsuwa a cikinsa a sai sun rugurguza shi. Yanzu ma kuwa nasan akwai lokacin da zai zo da zasu rabamu tunda zuciyarsu mai k'yashi ce."
Ya buge mini baki ya ce "Kada ki kuskura ki fa'di maganar banza a kansu a gabana. Dole fa ki mutunta su a matsayin surakanki tunda ke kin yanke nasabar da ta hada ku".
Cikin gigita na ce "To ka sake ni, bana son yin surukuta da su. Kai ma bana sonka Tijjani".
Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
Jikinsa ya yi sanyi domin ya ga matsanancin fishi a tare da ni.
Ya numfasa ya ce "Na sani ai ba kya sona Asiya. Ban manta ba, amma na sakankace a d'an zaman da muka yi, zaki iya mini kawaici da alkunya akan abin da kika san zai musguna mini tunda kin sani sarai an jarrabe ni akan son ki. Amma yanzu na gane da gaske ba kya sona tunda akan idona kika k'i gaida Baban Tsakiya cikin mutunci duk da kashedin da nake yi miki da ido. Sannan kika gaida Jabir cikin falli har kina kiransa Yaya alhalin kin kankare zumuntar da ubansa."
Na yi shiru domin kam jikina ya yi tub'us.
Ya cigaba da ce wa "Saboda shi kina sonsa, kuma yafi ni ku'di shi yasa kike ce masa Yaya ni kuma ki gatsa Tijjani gatsal duk da na girme shi kuma ni ne mijin ki. Asiya ba zamu tab'a daidaita wa da ke ba alhalin kin ri'ke BAK'AK'EN TA'ADODI. Yanzu duk k'uruciyar ki ai k'iris ya rage ki yi sha bakwai. Kin san kuma hukuncin wacce ta bu'de baki ta ce mijinta ya sake ta ba tare da gamshasshen dalili ba. Sannan kina da ra'ayin ruk'au na k'ullaci. Hakan kuma ba siffar mace ta gari ba ce. Kamata ya yi zuciyar mace ta zama mai taushi da sassauci ba mai tauri da tsanani ba."
Na ji kunyar kalamansa mussaman akan J.
Na tabbatar shi ba na ce masa Yaya. Amma ban da yau ai nafi wata ban kama sunansa ba, sai dai na yi masa magana kawai. Domin na da'de da daina fa'da a dalilin kunya na kama ni tare da nauyin gatsa sunan nasa.
Na tura baki na juya baya. Cikin k'unk'uni na ce "To ai kai ma kana da Bak'ar Ta'ada din, akan me tun a ranar ba zaka fa'da mini laifina ba, sai kawai ka k'ulla ce ni, ka tsiri fishi. Ni ba Allan musuru ba, ta ina zan san kuskurena?"
Ya matso jikina ya ce "Da kina sona ai tun a lokacin zaki fahimci sauyin nawa, sai ki shawo kaina ki ririta ni, ki mantar da ni b'acin ran da nake ciki. Amma saboda am nothing to you ai share ni kika yi. Kika tattara kika yi wurgi da ni".
Na cuna baki na yi shiru. Ya mik'e dukkan k'afafuwan sa. Ya janyo ni ya kwantar a kai. Ya shiga wasa da gyararren gashina. Murya a dak'ushe tabbacin yana cikin kewa ya ce "Bana son abubuwan da kike yi a gabansu. Su din iyaye ne. Ta ko wacce fuska sune a sama da ke.
Zan yi hakuri da komai akan sha'anin ki, amma ban da na fito na fito da iyaye, bana so, ki bari."
Na yi shiru ban amsa ba.
Ya sassauta murya ya ce "kin yi shiru."
Na sake yin shiru still.
Ya zame ni daga jikinsa ya juya baya ya yi kwanciyarsa.
Ina ganin hakan ai kuwa na tak'ark'are na zunduma masa fallashasshen kukan da baya so.
Ina ce wa "Tunda juninka k'ullaci ne ka mayar da ni gidanmu kawai".
Ya juyo da azama ya ce "Asiya ki cigaba da wula'kanta ni. Amma ki sani komai zaki yi ni ba zan mayar da ke ba, domin ina son ki, ke da ba kya sona sai ki tafiyar ki, hakan kuma ba shine k'arshe farin-ciki a gare ni ba."
Na sassauta kukana domin na ga ya hassala sosai.
Na dinga yinsa kasa kasa irin mai cin rai din nan.
Da ya gaji da jin kukan nawa ya saka hannunsa ya ja ni jikinsa ya ce "Yi shiru Asiyata, amma ba zamu shirya ba sai kin ba ni hakuri dole".
Duk yadda na k'agu mu shirya fuska na yi da ce wa "Ai ban maka laifi ba. Sannan ba dan komai nake ce wa Jabir Yaya ba sai dan yana ce mini Yabi ne. Amma kai sai ka dinga ce mini Asiya Toro babu ko sha'awa ma".
Ina rufe baki ya ce "Har abada ba zan ce Yabi ba, idan ya so ba Tijjani kawai ba, ki fa'di cikakken sunan nawa Tijjani Yusuf Bulkachuwa! Marar kunya. Shine rannan kika yiwa yaro sababi akan ya k'ira ni da Tijjani to ke d'in kin saya ne bare ki ji ciwon wani bai saya ba. Kuma ni ban damu sai kin saya d'in ba".
Na nisa na saki ajiyar zuciya irin wacce ake yi idan an ci kuka sosai. Na ce "Ni fa tuni na samo maka sunan da zan fa'da maka, amma sai na haihu".
Maganar ta zo masa a bazata. Ya ru'ko ni ya ce "Kina son haihuwa ne Asiya?"
Da sauri na ce "Ina so sosai, domin duk wanda muka taso ko wacce ta haihu. Wadanda aka yi aurenmu tare Nasiba da Ubaida dukkansu ciki ne da su, ni ce kawai ba ni da shi".
Na fa'da da karyayyar murya.
Ya sassauta ya ce "Asiya haihuwa lokaci ne da sannu ke ma wataran zaki gan ki da naki cikin. Tunda kin daina guduna, sannan nima ina iyakacin k'ok'ari, kawai mu dinga addu'a".
Na ce "To. Ka ga Gwaggo ma ta ce ba zata zo gidan nan ba sai na haihu".
Ya rungume ni sosai ya ce "In sha Allah zaki haihu Asiyata. Mace kike so ko namiji?"
Kai tsaye na ce "Ni dai na samu cikin nafi so. Ko mai na haifa ina so ba ni da za'bi."
Ya yi dariya ya ce "Tom shike nan Allah zai bamu In sha Allah! Kawai ki kara zama jaruma, ko sau nawa za'a yi kada ki yi musu ko ki ce kin gaji".
Na ce "Da gaske idan na yi haka zan samu cikin ko dai wayo zaka yi mini?"
Ya k'yal-k'yale da dariya ya ce "Ba wani wayo gaskiya nake fa'da miki Asiyata".
Daga hakan kuma ya shiga kissing d'ina tare da zafafan sakonni masu rikita ni. Sai da ya tabbatar ya rura mini jiki. Sannan ya sake ni ya kwanta tare da ce wa "Au ashe baki ba ni ha'kuri ba fa, bamu shirya ba".
A hankali na ce ", Mun shirya mana, ba har ka yi dariya ba yanzu".
Ya ce "Ai ba ki bani hakurin da na ce ki ba ni ba".
Na fara kukan shagwaba, ya juyo ya ce "To fa'da mini a kunne na ji".
Cikin kuka kuka na ce "Allah ya baka hakuri".
Ina fa'din hakan ya rungume ni yana cewa"Ameen little girl na ha'kura na huce gaba'daya".
Daga hakan kuma ya dinga b'arin jiki a kaina, komai ha'dama ha'dama yake yinsa har na gamsu k'arfin hali ya yi a kwanakin amma ba samu yake yi a waje ba. Domin duk kulafacina sai da na k'osa amma shi bai k'osa din ba".
Haka muka cigaba da gurgurawa ciikin rufin asiri. Dai-dai gwargwadon k'arfinsa yana yi mini komai.
Matsalar da ta fara damuna har cikin zuciyata rashin samun cikina gashi watanmu goma da aure Nasiba jiya ta haihu Ubaida kuwa har an saka ranar da za'a yi mata tiyata(c.s).
Da aka sanar mini da haihuwar yini na yi cikin sanyin jiki.
Sai kuma matsalar Rafi'a. Wata guda da kammala karatunta na digiri ta tattaro ta dawo gida gaba'daya.
Kusan ko yaushe a k'ofata take. Idan ina k'unshi sai ta hakince a falo da sunan kallo. Ko Tijjani ne ya dawo ba zata tashi ba, sai ma ta yi ta jansa da zancen makaranta su yi ta hirarsu. Ko idan ta ga ya fita sai ita ma ta bi shi su fita tare.
Ranar da na yi masa k'orafi ya balbale ni da sababin wai na raina shi, ban yarda da shi ba.
Na kame baki na yi shiru, kuma sai da na ba shi hakuri akan hakan.
Tunda ya ja ya tsaya ba shine yake zuwa wajenta ba, ba shi yake kiranta ba, tunda bana so ta zo mini gida to na hanata zuwa kawai.
Na rasa ta yadda zan kore ta domin dai gaskiyar magana uwarta tana mini kirki da alheri mai yawa a matsayin ta na babba. Bayan haka ita kanta Rafi'a din kirki ne da ita. Bai zame mata komai ba ta yi mini gyaran gida ba. Kawai ni yadda take shige wa Tijjani ne bana so, domin na riga da nasan shi akan lutayen mata.
Wadannan matsaloli sai suke neman sauya zaman aurenmu. Domin ni a k'arancin shekaruna dauka na yi Tijjani ne ya ki yi mini cikin kawai. Sannan yana son Rafia.
A hankali na fara janye masa, abubuwa suka fara sauya wa a tsakaninmu.
Na daina sauraronsa ko na saurare shi ma to kuwa sau daya ne shima ba cikin da'din rai ba.
Ranar da na dawo daga sunan Nasiba kuwa. Kuka na zauna na yi masa mai d'aga hankali k'warai da gaske. Ina yi ina ce wa "Akan me zaka matsa mini sai ka ta'ba ni bayan bana so, na riga na gane ba cikin nan zaka yi mini ba, dan haka na gaji da nukurkusata da kake yi babu sassauci babu kuma wani abu da zan samu."
Ya zuba mata ido yana kallon yadda take kuka bilhakki. Ya tafi tunanin shekarunta. Watan da ya shud'e ta ciki shekaru sha bakwai.
Ke nan akwai k'uruciya mai yawa a tare da ita. Bai kamata kuma ya biye mata ba, domin ya fahimci da dukkan zuciyarta take ganin shine bai mata ciki ba.
Ya numfasa ya saki gauron numfashi kafin ya ce "Asiya Allah ne fa mai bayarwa, kuma ba mantawa ya yi damu ba. Kika san tanadin da yake yi mana?"
Cikin kuka na ce "Ba wani, ni kawai ciki nake so, ai ko wacce ta haihu saboda mazansu suna sonsu, sai ni ce kawai saboda baka sona, kowa wani gani gani yake yi mini ba'a yi mini ciki ba".
Dariya ta so subuce masa, amma ya maze ya ce "Asiya zai yi wahalar gaske a samu wacce ake takarta irin yadda nake yi miki a cikinsu. Kin san da yawan yi ne sanadin samun ciki da yanzu kin haihu sau uku.
Amma shi samuwar ciki ai ikon Allah ne."
Da rawar murya na ce"Ba wani kawai dai ni ce baka so na samu ba, ga Ubaida nan yarinya da ita jibi za'a ciro mata d'a ko y'arsu, kai ma da su Nasiba ka aura ai da tuni ka yi musu.
Ina goge idona na ce "Wallahi na baka nan da wata d'aya, idan ban samu ciki ba to ba zan zauna ba".
Ya sake zuba mini ido cikin mamaki mai yawa. Ni kuwa ko d'ar ban ji ba.
Ya ha'diye komai ya ce "Shike nan Allah ka taimaki Tijjani ya yiwa Asiya Toro cikin y'an-uku".
Na yi maza na ce y'an uku tashi guda? Y'an biyu ko daya ma ya isa."
Ya fara ta'ba ni, na bige hannun na ce "Ni fa yau na gaji Wallahi".
Ya ce "To shike nan Asiya Toro Allah ya kai mu gobe, tunda ciki kike so ki sani fa babu ke babu hutu, amma na yarda ki huta yau din".
*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
✍️
*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
59&60.
Haka al'amuran suka ci gaba da gudana.
Aka ciro wa Ubaida kyakkawar jaririyarsu mai cike da koshin lafiya. Ita kam gida aka tafi da ita. Tunda bata da lafiya.
Sai da aka yi sati biyu da haihuwar sannan aka yi taron suna.
Ranar sunan na ga dukkan y'anmata da muka taso har ma da k'anwata kowa da d'a ko y'a a hannunta amma ban da ni. Na shige d'akinmu na dinga kuka. Yaya Ummi ce kawai ta gano ni. Dan kuwa ita Gwaggo ma bata dauki hakan a matsala ba ne. Yaya Ummi ce ta dinga ba ni hakuri tare da cewa gaba'daya ma auren naku wata shad'aya ne fa Yabi. Sannan shekarunki shabakwai. Ban da an miki auren wuri ai har yanzu baki isa auren ba, bare aje ga zancen haihuwa. Wadanda suka zarce shekaru goma babu haihuwa fa sai su ce da Ubangiji me? Ki shiga a hankalin ki fa".
Sai da ta shawo kaina sannan muka fita cikin jama'a.
Watanni uku bayan haihuwar Ubaida mai gidan burodi da Tijjani yake zuwa ya rasu. Magada sun yi yawa a kai dan hakan suka siyar da shi. Wanda ya siya kuwa kabila ne dan haka ya sallami galibin ma'aikatan ya debo nasa y'anuwan ya zuba.
Cikin wadanda aka sallama kuwa har da Tijjani. Ban gane aikin da burodin da yake yi rufin asiri ne mai yawa ba, sai bayan an rasa shi. Domin ba'a dauki kwanankin sati ba sai da muka ga gurbinsa. A da bamu da matsalar abin karya wa tunda burodi har yawa yake yi mana. Ga kuma donougt da ita ma bata yanke mana. Ko baki na yi zan basu. Sannan da daddare ba kasafai muke cin abinci ba, sai kawai muci da shayi mu yi kwanciyarmu.
Sannu a hankali rashin samun ku'di ya dabaibaye shi k'warai da gaske. Tunda aikin saka tiles sai an samu. Haka na satellite shima hab'o ne.
Tsawon wata biyu muna cikin wannan yanayin. Ga shi ya k'i yarda na taimake shi, tunda ni kullum kasuwancina tamkar ba iya mutane ne suke zuwa mini kitso da lalle ba. Saboda yadda Ubangiji ya ba ni jama'a.
Tunda kayan abincinmu suka k'are kullum cikin dirka mana garin rogo ko wainar fulawa yake.
Tausayi yake ba ni saboda gaba'daya ya zama desperate kullum cikin yawon neman abin da zai yi yake. Wani lokacin na ga ya fita da takardunsa, wani lokacin idan ya fita tun safe sai azahar zai dawo, haka kuma yake dawowa sai dai na gan shi da garin rogo da siga a leda. Ni kuwa sai ya bani filawa a farar leda ya ce ki yi abin da zai samu da ita, ki mini hakuri dan Allah"
Rannan na gaji da bin ra'ayinsa muna kwana da yini cikin yunwa.
Na ha'da kan ku'din da na samu na kwanaki biyu na rubuta koamai da nake bu'kata a takarda na bawa almaajirina na ce ya je ya ce nawa ne kudinsu. Jimawa ka'dan ya dawo ya ce "Wai dubu sha bakwai da dari shida".
Na kirga na ga har da canjn dubu uku ya rage mini.
Dan haka na cire canjin na ba shi ya tafi ya karbo mini.
Na duba na ga komai ya cika. Na kinkima na kai kicin na shiryasu.
Na ba shi gudar dubu akan ya siyo mini gawayi rabin buhu, da kuma danyar kubewa. Domin na tsani siyan abu dan tsurut a leda kullum. Ina da gas amma na bar shi sai iya da safe zamu dinga amfani da shi.
Ya siyo mini bushasshe kuma manya dan jos haka ma kubewar. Na ce "To je ka dawo anjima ka'dan."
A lokacin kuwa yammaci ne sosai. Dan haka na ha'da wuta na dora tuwon garin masara wanda yana cikin siyayyar da na yi d'azun.
Na gama na kwashe na mayar da miya. Magariba tana yi ina kammala wa.
Sai da na yi sallah, na yi wanka sannan almajirin ya dawo. Na zuba masa ya tafi. Sai ga Tijjani ya dawo. Ya kalle ni na ci kwalliya ko'ina kamshi ke tashi. Ya kalle ni da alamun tausayi ya ce "Sannu da gida. Ya mik'o mini ledar hannunsa wacce awara ce. Na kar'ba tare da godiya.
Na tashi na gabatar mana da abinci, na zuba mana a plate guda.
Na ce "Bismillah".
Ya girgiza kai ya ce "Na gode".
Na zuba masa ido murya na rawa na ce "Ba zaka ci ba, bayan na tabbatar da yunwa a tare da kai!
Da rauni sosai ya ce "Ni ni ne mai ciyar da ke, ba wai na zauna ki ciyar da mu ba".
Na tashi na koma kusa da shi na ru'ko dukkan hannuwansa na sassauta murya na ce "Ba ciyar da mu zan yi ba. Ubangiji zai buda maka k'ofofin da zaka samu ka sauke nauyin rik'on iyali tunda shi ya wajaba maka. Kana kuma da niyyar yi d'in. Abin da nake so ka fahimta ko aure bai ha'da mu ba, ai jini ya ha'damu. Ko ina wani gidan idan ina da ikon kula wa da iyalinka ai zan yi, bare kuma ni ce iyalin naka, to mene ne amfanin sana'ar da ka bar ni nake yi alhalin ba zata yi maka rana ba?"
Ya yi shiru bai ce komai ba, na sake sassauta murya na ce "Dan Allah ka yarje mini na yi iya abin da zan iya yi".
Ya saki gauron numfashi ya ce "Idan na amince ya tabbata dai da aka ce ke ce zaki ciyar da mu Asiya. Shike nan zan rasa yancina na mai gida, shike nan zan zama mata, ke ki zama mijin".
Ya fa'da murya na rawa ainun.
Na durk'ushe a gabansa na ce "Wallahi ba zaka zama ba. Yadda muke hakan zamu cigaba da tafiya kai ne miji. Ni ce mata, zan dinga karban umarni daga gare ka, abin da kake so hakan za'a yi.".
Ya yi shiru yana nazari bai ce komai ba.
Na matse hannunsa na ce "Pls mana" cikin sigar shagwaba.
Ya zuba mini idonsa da ya kad'a sosai ya ce "Asiya zuciyata ba zata nutsu ace kina siya mini abinci a gidan nan ba. Gara dai ki bari na dinga baki abin da aka yassare mini, idan ma zaki kara da abin da kike so to bazan hana ki ba, tunda ban wadatar da ke ba. Amma ni kada ki yi da ni. In sha Allah ko da bashi ne dai bazan kasa baki abin da zaki saka wa ba'kin salatinki ba. Sai idan kin raina".
Na kalle shi na gane da gaske yake yi.
Na yi k'asa da murya na ce "Anya kasan kalubalen da yake tare da cin bashi kuwa mussaman a waje? Kawai ka yi hakuri tunda dai Ubangiji ya baka matar da ya bata sana'ar hannu mai k'arfi. Ina fatan Ubangiji ya kawo maka aiki ko sana'ar da zaka dogara da ita."
Ya girgiza kai tabbacin bai gamsu ba.
Na ce "To shike nan ka dinga karban bashin a wajena."
Ya gyara zama ya ce "Nawa kika kashe a hidimar tuwon?"
Na ce "mu je kicin a lissafa.
Ya mike muka je. Na nuna masa komai da aka siyo wanda a k'alla zamu kai wata muna ci a talau ce.
"Nawa kika kashe a wannan siyayyar?
Na ce dubu sha bakwai da dari shida na. Sai gawayi na dubu daya."
Ya ce "To kub'ewar fa?"
Na ce "A bar wannan".
Ya girgiza kai.
Da sauri na ce "Ta naira dari ce."
Ya ce "Sha takwas da dari bakwai ke nan ko?"
Na ce "Eh" ya ce "In sha Allah zan biya ki, matu'kar ina shakar numfashi."
Muka koma falon muka ci abinci ina ta yi masa hira dan ya ware sosai.
Wannan kayan abincin da muke da shi sai ya rage masa damuwa mai yawa. Duk da hakan kuma bai yarda ya zauna a gida ba. Kullum sai ya fita. Rannan ya yi sa'a ya samu hada saltelite har gida uku. Da k'arfinsa ya dawo ya mik'o mini dubu biyar ya ce "Ga shi, na rage miki bashin ki. Ya fita ya dawo da leda mai d'auke da soyayyen kifi.
Na kar'ba tare da addu'ar Allah ya kara budi.
A wannan tsukun gaba'daya a takure nake domin maimakon na samu ninkin tattalin da yake yi mini kafin mu shiga tsananin da muke ciki. Sai ya zamana ni ce nafi rawar kai a kansa domin dai na samar masa nutsuwar shine mijin. Tunda na lura yana kame wa ne dan kada na samu dama a kansa. Na dinga mamakinsa domin gaba'daya ban yi zaton zai mini kallon zan raina shi dan ya shiga halin babu ba.
Ya takura kansa sosai, komai kaffa kaffa yake yi.
Idan na yi kamar zan yi masa magana sai na ha'diye.
Na dinga hakuri ina lallabawa ina binsa a hankali.
Hidimar da ta karu a kaina sai ya zama ina ta kokarin fa'dada kasuwancina. A dalilin an kawo wa Tijjani takardar biyan ku'din gida tun kwanakin baya.
Na fara tunanin yin Home service domin na samu na tara masa ku'din kafin lokacin da suka diba mana ya cika.
Na kalli yatsun hannuna guda biyu gold ne. Daya na wajen kwamishina ne, dayan kuwa da sana'ar tawa na siya.
Jiya na bashi daya na ce ya siyar ya biya ku'din ya ce "Ba ya so, kada na sake na siyar da kadarata akan al'amarin da ba hakkina ba ne. Idan kuma na siyar to ba zai karba ba.
Da zai fita na tambaye shi zan fita, zan je bayan layinmu. Bai hana ba.
Tunda na fita da hantsi ban dawo ba sai yamma lis tunda asabar ce ban cika samun k'unshi a ranar ba sai kitso.
Na dawo na tarar da shi a gida. Ya gyara ko ina.
A falo na tarar da shi yana kallo. Na yi masa murmushi ya mayar mini a gajarce. Ya kalle ni ya ce "Daga ina kike na ji sai k'amshin muhallibiya kike yi"
Zuciyata daya na ce "Wallahi lalle na yiwa wata babbar mace da ahalinta zasu je biki Abuja.
Na fito da kudina dubu sha biyar na ajiye masa na ce "Idan Allah ya yarda a satin nan zamu ha'da ku'din da zaka biya gidan".
Ya zuba mini ido galala sai kuma ya kad'a kansa ya ce "Babu laifi".
Ni ban kawo komai ba. Na tashi na yi kicin da nufin dora girki. Sai na tarar da ya girka ya juye a flask. Ga shi ya mayar da ruwan wanka kan gawayin. Na bu'de na ga ya yi zafi ainun. Na dauko babban flask din da nake zuba ruwan zafi na cika shi. Na ajiye sannan na juye ragowar na shiga wankan.
Sai da na shirya na ha'da Mana abincin na kai ina cewa "Yau dai ka zama Yabi, na dawo na tarar ka yi komai sannu da kokari".
Ya sake yi mini wani irin kallon da ban gane ma'anarsa ba.
Duk da dai yanzu ya canja amma ba musguna mini yake ba, kawai walwala da sukuninsa ne suka ragu, sannan yana yawan yi mini abubuwan da suke kona mini rai ta hanyar shata layi da abin hannuna.
Na kalle shi na ce "Sauko mu ci to".
Ya girgiza kai ya ce"ci, ni ba yanzu zan ci ba".
Na marairaice na ce"To zo ka dinga bani a baki na gaji sosai Wallahi".
Ya sake kafe ni da kallon da yafi wadanda ya yi mini. Bai kuma ce komai ba. Na rasa gane manufar hakan sai kawai na fashe masa da kuka mai tsananin gaske.
Ya taso ya zauna kusa da ni ya ce "Me na yi miki zaki yi mini irin wannan kukan?"
Da kuka sosai na ce "To akan me zaka dinga yi mini kallon tuhuma? Akan me ba zaka zo mu ci abinci tare ba? Na riga da na gane ka tunda ka fahimci na fara sonka shikenan ka nade kafar wando fara yi mini wula'kanci kala kala".
Ya matso jikina sosai ya kwantar da ni a kirjinsa ya ce "Da gaske kina sona Asiya?"
Na ture shi na zum'bura baki na juyar da fuska gefe.
Na kasa bu'de baki na ce uffan.
Ya saki gauron numfashi ya ce "Shikenan na daina yi miki wula'kanci, duk da nasan ba na yi din".
Da kansa ya zuba mana abincin. Lokaci zuwa lokaci kuma zai debo ya bani a baki. Ko ruwa da ya bula ledar bai sha ba, bakina ya nufa da shi. Na zuke tas na bar masa leda a hannu. Sai wani ya bu'de.
Da yake ina siyar da pure water, saboda masu zuwa lalle kawia na tsiri siyar wa kuma sai nake yin ciniki sosai.
Na yi gyatsa "Na yi hamdala. Gaba'daya sai jikina ya mutu murus gajiya ta taso mini, ba abin da nake so irin na kwanta na yi barci. Ga shi maghariba ta kawo kai.
Na kalli agogo na ga za'a kai minitina arba'in da biyar kafin a kira sallah.
Na mik'e na kwashe kwanukan, na hau zaga tsakar gida dan abincin da na ci ya dai-daita. Na koma falon na kwanta a kujera na yi daidai iskar fanka na kad'a ni. Ya taso ya fara bin gabbobina yana dannawa sannu a hankali nake jin da'di a jikina.
Ban ankara ba sai kawai ya sure ni yana cewa "mu je daki na wartsake miki gajiyar gaba'daya. Na fara shure shure shi kuma ya ri'ke ni gam. Fadi nake yi "No bazan yarda ka dora mini wata gajiyar ba gaskiya".
A kunne ya ce "Amma kinsan na ce idan kina yin gardama komin kankantar ta cikin ba shiga zai yi ba".
Nan da nan kuwa na yi muk'us domin har zuciyata so nake na ganni da ciki, so nake na ganni da baby a hannuna kamar yadda nake ganin su Ubaida.
Har aka fara kiran sallar Bai samu nutsuwa ba. Kan dole ya tsallake ya bar ni. A gurguje ya yi wanka ya nufi masallaci.
Ni kaina a dole na sake wanka na sauke farali.
Yau da wuri muka kwanta domin ana idar da sallar isha da ya shigo ya rufe gidan, ni dama a kwance ya tarar da ni. Sai da ya karasa abin da bai ida ba sannan muka yi wanka, muka kwanta wajen tara da rabi. Washagari lafiya muka rabu, da zai fita na ce "Idan fita ta kama ni zan fita. Bai ce komai ba, ni kuma ban yi zaton bai amince ba.
Da yake na dora cewar na fara Home service akan status dina. Sai kuwa na dinga samun k'ira akan ana bu'kata ta a wuri kaza.
Na za'bi gida biyu, na bawa guda biyu hakuri akan wasu sun rigasu.
Na kammala gyaran gidan tsab.
Na fice. Wannan ranar har dare sannan na koma gida. A k'ofar gidan na tarar da shi, cikin wani irin yanayi. Yana ganina ya zabura ya mik'e.
Ni kuma ganin a waje muke yasa na zarta shi na shige. Sai kawai na tarar da k'ofar tamu da sabon kwad'o.
Na jinkirta amma bai shigo ba. Na gaji da tsayuwar jiransa. Na fara hassala ya gan ni amma ya kasa shigowa, yasan kuma ya canja kwad'o.
Na gaji na fita na tarar da shi yana zaune tamkar dutse ko motsi ba ya yi.
Na ce "K'ofar a rufe take fa".
Ko kala bai ce ba.
Na sake fusata. Na ce "Ka zo ka bu'de mini".
Nan ma tamkar da Dutse nake magana.
Allah yasa ma babu kowa a wajen. Zuciyata ta hauro matu'ka da gaske. Duk fa'din tashin da nake yi dan asirinsa ya rufu shi bai ga hakan ba. Murya na rawa na ce "Ni kake yiwa wula'kanci haka?"
A fusace ya ce "Wace ce ke? Gida ne bana bu'katar ki a cikinsa ba, ba sai ki koma inda kika fito ba, kin ga kin yi maganin wula'kancina, nima na huta da rainin da kike yi mini".
Jikina ya yi matu'kar sanyi, hawaye ya b'alle mini. Murya na rawa na ce yanzu a daren kake so na tafi gida?"
Shima murya na rawa ya ce "Ai ni a daren kika dawo mini gida. Dan haka ki koma inda kika fito ko ki je inda zaki, ai dai babu sisin ki wajen kama gidan har yanzu, bare ki yi mini sabon isgilanci".
Na fara kuka na ce "Na rantse da Allah Tijjani kai bahago ne na k'arshe. Duk tunanina mu ha'du mu rufawa kanmu asiri wani bai ji ko ba'a gane halin da muke ciki ba, amma gaba'daya ka murde ka canja, ka ki da'din azanci. Dan Allah ka fahimce ni, nifa ba jin da'din yadda kake yi nake ji ba".
A tunzure ya ce "Yo dama ni ina da abin da zan jiyar da ke da'di ne?"
Na yi sakare ina kallonsa gaba'daya ya juye ya koma wani azababben mutum.
A hankali na ce "To zo ka bu'de mini, tunda dare ya yi."
Ya girgiza kai ya ce "bana son ganin ki a cikinsa."
Na juya na ce "Shike nan na gode".
Na fara tafiya ni kad'ai ga shi wajen ba kowa, tsoro ya kama ni, da na ji kamar ana bina. Sai da muka iso wajen hasken solar na juya sai na ga shi ne yake bin bayana.
Na tsaya na ce "To mene ne kuma, ba dai ka kore ni ba?"
Da sanyin murya ya ce "Bakin titi zan raka ki, kada karnu ka su biki".
A tunzure na ce "Allah yasa ma kuraye su kama ni, su cinye ni!
Bai ce komai ba, har muka isa inda zan bi na yi gida. Na kalle shi na ce "Yanzu me kake so na fa'dawa Baban Marina?"
Kai tsaye ya ce "ki fa'da masa gaskiyar abin da ya faru kawai".
Na marairaice na ce "Tunda har ka rako ni nan, nasan ka huce, mu koma gida ka fa'da mini abin da na yi, ba sai ka ce na baka hakuri ba, zan nemi afuwarka".
Ya girgiza kai ya ce "A a bana bu'katar ki a gidan ne, ki je gida, ko ki je ki kwana a wajen neman ku'din ki".
Ganin zai sake tunzura da yawa yasa na tafi din. Amma tafiya kawai nake yi, bana ko sanin inda zan jefa k'afata. Tashin hankalina ace na je gidan Marina da sunan bacin rai. Na sani masu murnar ganina sai sun fi masu yin jajjabi yawa. Kuka nake yi sosai. Me zan cewa Baba da Gwaggo ni Yabi? Ko Ubaida k'aramarmu ba'a taba tura ta gida da sunan ta yi laifi ba sai ni? Ni kuwa dama akuyata ta yi shura.
Ina ganin hanyar da zan bi na isa gidan, amma sai na bi wanda zata kai ni gidan Yaya Ummi.
K'arfe tara da rabi na shiga d'akinta tamkar jifa. Cikin sa'a mijinta ya je Jos d'aurin auren yar kaninsa sai gobe litinin zai dawo.
Ganina a wannan daren ga kuka ina yi, duk sai ta diriri ce ta dinga fa'din mene ne, daga ina kike?"
Ina kuka, na fa'da mata Tijjani ne ya ce "Bazan shigar masa gida ba."
Ta dauki salati ta ce "To ke da ina kika je?"
Na fa'da mata gaskiya.
Ta yi shiru ta ce "Tsakani da Àllah laifinki ne Yabi. Tunda bai amsa miki ba, ai kinsan ba wai yana so ba ne. Sannan me yasa kika yi dare har wajen tara?"
Na yi shiru sai kuka kawai nake yi. Domin tskani da Allah ban san ina son Tijjani sosai ba sai yanzu da ya yi min irin wannan hukuncin. Ji nake kamar na yi ta zunduma ihu har kowa ya fahimci rad'ad'in da nake ji. Baya ga haka kuma fishin da na ga ni shinfide a kan fuskarsa ya sake dagula mini lissafi.
Cikin kuka na ce "Ni bana son na je gida Yaya Ummi. Baba fishi zai yi da ni, haka ma Gwaggo. Ga magauta su tasa mu gaba da dariya da zunde".
Ta nisa ta dauki k'aramar wayarta ta ce "ku'din ciki babu yawa, amma bari na gwada na ga ni.
Bugun farko ya dauka tamkar me jira a k'ira shi.
Ta gaishe shi da walwala.
Sai kuma ta ce "Yaya Bulkachuwa sai ga Yabi ta zo mini a wannan daren, kuma abin mamaki ta ce wai kai ne da kanka ka koreta, ai da sai ka yi hakuri da safe ka tura ta gidan."
Dake a sifika ta saka sai na ji ya ce "Na kasa yin wannan tsinkayen Ummilolo. Amma yanzu taimake ni ta kwana a gidan ki, gobe sai ta wuce gida".
Da sauri ta ce "A a kasan ni dakina daya ne. Zan dai rako ta, ko mene ne da safe zan dawo mu tattauna tunda dare ya fara yi".
Ya yi shiru tabbacin bai gamsu ba.
"Ka yi shiru Yaya Bulkachuwa".
Ya ja gauron numfashi ya ce "Kunyar ki nake ji ne Ummilolo. Kada ki shiga wannan maganar. Ba ke ce zaki yi alkalancin nan ba. Domin ban dauki al'amarin da sau'ki ba".
Ta sassauta ta ce "Ai tunda na gan ta na sani baka dauke shi da wasa ba. Amma tunda na yi maka waya ai sai ka mini lamini tunda ni da kai ai kasan tun fil'azal bata b'aci."
Ya ce "To shike nan".
Da walwala ta ce"Yauwa Yaya Bulkachuwa rabin raina na gode".
Daidai lokacin kuma ku'din wayarta ya k'are. Ta ce "Ai bu'kata ta biya."
Kafin ta yi mini magana, sai ga shi ya biyo bayanta. Tana dauka ya ce "Yi zaman ki Ummi ai ba zai yiwu ki fito b'akatatan a wannan lokacin ba. Bari na wakilce ki, na zo da kaina. Amma ki fa'da wa mijinki gobe, ki zo mu zauna".
Ta ce "Na kuwa gode! Gobe da ikon Ubangiji da wuri zan zo".
Ya ce "Na gode, ki gaida yaran namu".
Ba a wani dauki lokaci mai yawa ba, sai ga shi ya k'ira ya ce ya zo.
Ta raka ni har soron gidan sannan ta juya tunda k'ofar gidan nasu tamkar kasuwa yake shaguna ne reras gefe kuma teburan masu sayar da nama na gaba kuma masu kayan miya.
A mashin dinsa ya zo. Na haye ba tare da na ce komai ba.
*End of part 2.*
*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers*
*08089965176*
*07084653262*
Post a Comment for "BAKAR TA'ADA BOOK 2 Complete Hausa Novel"