BAKAR TA'ADA BOOK 3 Complete Hausa Novel
*BAKAR TA'ADA BOOK 3 Complete Hausa Novel
*Na*
*Surayya Dee*
*Marubuciyar Halin Yau*
*Da*
*Sabo da kaza*
61&62.
Har muka isa gidan ba wanda ya yi magana.
Kai tsaye daki ya shige ya yi kwanciyarsa. Ni kuma na shiga kicin na sama wa kaina abin da zan ci. Sannan na yi wanka. Na gyara jikina sosai, na isa dakin na tsaya gaban madubi na bi ko ina na goga turare.
Na tarar da shi idon sa biyu. Na zauna na tausasa murya na ce "Fa'da mini abin da na yi, mu shirya kafin Yaya Ummi ta zo".
Ko motsi bai yi ba, bare ya yi magana.
Na zuba masa ido ina tuna yadda yake rawar jiki da tsoron fishina. Amma tunda ya fahimci na fara fad'awa komar sa shike nan abu ka'dan zai fitittike ya yi mini fishi.
Na kai hannu na fara shafa sumar kansa da nufin lallashi tunda na gane shi mutum ne mai son a rarrashe shi tamkar mace.
Da kakkausar murya ya ce "Bari Asiya Toro".
Nan da nan kuwa na cire hannun nawa domin gargadi ya yi mini mai kauri.
Haka muka kwana duk rai babu da'di.
K'arfe takwas sai ga Yaya Ummi da alamu tare suka fito da yaranta yan makaranta su suka wuce ita ta taho nan.
A falo muka zauna.
Ita ta fara ce wa "Yaya Bulkachuwa ka ga yadda ka koma kuwa me yake faruwa ne?"
Ga mamakina yana bu'de baki sai ce wa ya yi "Ba'kin cikin Asiya ne yake neman kassara ni".
Gabana ya takarkare ya fadi. Me nake yi masa ni Yabi?"
Yaya Ummi ta ce "me ya faru haka Yaya Bulkachuwa?"
Na kasa kunne sosai dan na fahimci abin da zai ce da kyau.
Sai ji na yi ya fara rattabo laifukan da nake yi.
Cikin nutsuwa ya ce "Ummi tunda aka rufe gidan burodi da nake zuwa na shiga yanayin rashin ku'di. Har ta kai bana iya yin abin da ya kamata. A farko rimi rimi Asiya ta ke ha'kuri da duk abin da zan kawo. Tare zata sarrafa mu ci, ko da garin kwakai ne. Amma tafiyar bata yi nisa ba sai ta fara gazawa. Ta fara raina kokarina saboda an riga an cusa mata akidar wata rana ita ce zata rike mini gidan. Komai zan siyo na bata ba zata yi amfani da shi ba. Kwanaki na siyo sabulun wanka Gif har yau bata ta'ba ba. *Sai ta yi odar na Oriflame a wajen wannan jikar kanin Dada Aisha lame 07036662633*.
Duk ban ce komai ba, sai shekaranjiya kuma ta ce mini zata fita, ban zaci wai gida gida zata dinga bi tamkar dilalliya ba. Tun safe da ta fita sai yamma lis ta dawo wai ashe gidaje ta dinga bi tana yin k'unshi ana biyanta saboda kawai ta fahimtar da kowa ita ce take ri'ke da ni!
Ya nisa ya zarce da fa'din tana shigowa ta tarar na yi komai, kamar yadda ta sani tun farko ni aikin gida bai zame mini komai ba, amma kin san me ta ce mini?"
Yaya Ummi ta girgiza kai cikin sanyin jiki.
"Tana bude baki sai ce mini ta yi wai na zama Yabi. Wato na zama mace mai zaman gida, ita kuma ta zama namiji mai fita ya yi gwagwarmaya. Duk yadda maganar ta buge ni hakan na daure na ha'diye maganar na kawar mata da kai!
Ya fa'da yana hucin b'acin rai.
Gaba'daya jikina ya mutu, zufa sai keto mini take yi. Na tabbatar duk abubuwan da ya lissafo ina yinsu tabbas. Amma ko ka'dan a zuciyata ban dauka zasu b'ata masa rai ba. Domin ko ka'dan ban yi da nufin wula'kanci ko da muzanci ba. Asalima ni na yi ne da nufin kyautatawa.
Kafin Yaya Ummi ta ce komai sai ya cigaba da fa'din "Jiya kuma ta ce mini zata fita ban amsa mata ba. Sai kawai na dawo na tarar bata gidan, tun azahar nake zaman jiranta bata dawo ba sai tara saura. Fa'da mini Ummi me ta mayar da ni, me kuma take nufi da ni ne?"
Yaya Ummi ta yi shiru ta rasa abin fa'da domin ta fahimci ransa ba k'aramin baci ya yi ba.
Sai kawai ta buge da ba shi hakuri tare da ce wa"Tabbas ta yi kurakurai amma ka yi hakuri zata kiyaye."
Ya girgiza kai ya ce "Ba fa zan yi hakuri ba tunda ba zan dauki wadannan BAK'AK'EN TA'ADODIN da ta fara tsirarsu tun daga yanzu ba. Gara manya su san halin da muke ciki kada abu marar da'di ya faru ace na bawa marar d'a kunya."
Yaya Ummi ta yi maza ta ce haba dai, haba dai Yaya Bulkachuwa ba abin da zai faru sai alheri. Ai gata nan duk ta ji abin da ka fa'da, za kuma ta kiyaye."
Ya girgiza kai ya ce "Kin san kafiyar ta, ba ji zata yi ba, ni kuma ba zan yarda ba. Kin ga gara komai a yi shi a bayyane ba sai abu ya yi tsananin da rayuka zasu baci da yawa ba".
Ni gaba'daya ma mamaki ya ba ni, ya fitittike akan sai na tafi, ita kuma Yaya Ummi sai wani lallab'a shi ta ke yi. Yo ni ban da ina jin tsoron gorin da zan fuskanta, da ba'kin cikin da zan jefa iyayena da na girgije na bar masa gidansa.
Ta kallo ni tare da mini signal na ba shi hakuri. Na dauke kai na juyar da fuskata. Domin nima na hauro ai komai nake yi domin sa ne. Amma tunda shi ba zan yi masa alheri ya yaba ba, sai dai ya bini da sarhutu to shike nan na daina yin komai. Fita k'unshi da sunan Home service kuwa na soke sai ya nemo wani laifin kuma.
Da k'yar Yaya Ummi ta shawo kansa ya ha'kura da maganar sai mun je gaban Baban Marina. Ta bu'de murya ta ce "Ki ba shi hakuri".
Fuska a daure na ce "Allah ya baka hakuri".
Daga haka na tsuke fuskata da bakina.
Tare muka karya da ita. Sai da zai fita suka tafi tare ya sauke ta a gidanta.
Ban zauna ba sai da na yi abinci na zuba a flask.
Na gyara ko ina, sannan na fara yiwa wata da ta zo k'unshi. Bai dawo ba sai yamma, kafin lokacin kuwa na yiwa mutum hudu duk sun tafi. Budurwa d'aya ce ta rage da yake ita zan mata bak'i da kuma kitso.
Da azama na saki kitson na fita ina yi masa barka da dawowa, domin ya tsani ya dawo ban bar abin da nake yi, na je gare shi ba.
Idan wani ne ya fa'da mini Bulkachuwa zai dinga yi mini irin wannan mulkin mallakar zan k'arya ta shi kai tsaye. Ni da kaina mamakin kaina na ke yi. Na yadda nake rawar jiki a kansa. Wata'kila kuma yadda yake sarrafa ni ne sirrin.
Ya mik'o mini ledar hannunsa mai dauke da karas da atile.
Hannu biyu nasa na kar'ba na dinga fa'din "Na gode, Allah ya k'ara budi.".
Na wanke hannuna, na yi kicin na ha'da abincinsa na kai masa.
Na debo pure water masu sanyi guda biyu na saka a plate. Na ajiye a gabansa.
Na fita na debo masa karas da atilen na zuba a bowl na wanke na sake Kai wa gabansa.
Na dan yi jim na kalle shi yana cin abincinsa cikin nutsuwa. A hankali na ce "zan je na karisa kitso."
Da walwala ya ce "To".
Na fita a raina kuwa sai fa'din nake yi sarkin son mulkin tsiya.
Da daddare ya dinga laluba ta, na maze ban yi masa abin da nake yi masa ba.
Ya fara ce wa "Amma dai kin san bana son haka, sannan kuma kin san kin ci bashina jiya".
Da sauri na ce "Ba wani bashin ka da na ci. Kai ne ka kawar da kai, alhalin ka ce ko mun yi fa'da kada mu saka aurenmu a ciki. Amma jiya sai da ka saka su tsundum."
Cikin kwantar da murya ya ce "Hankalina ne ya tashi matu'ka da gaske. A ce matar aurena tana garanranba a gidajen mutane har almuru da sunan sana'a? Ai k'arshen tozarci ke nan. Amma ai na ha'kura kin san ina sonki fiye da komai Asiya. Ban so wani abu a duniyar nan da ya zarta ki ba. Uwa da ubana ne kawai a gaban ki. Dan haka ki daina damun kanki akan wasu matan. Ba sonsu nake yi ba. Da gaske ba wacce nake so a zuciyata sai ke. Amma zan iya ganin wata ta burge ni ko ta bani sha'awa a dalilin Ubangiji ya sanya sha'awar mace sama da d'aya a zuciyar maza je. Amma kullum ina ro'kon Ubangiji ya tsare ni da sha'awar wata macen fiye da ke. Duk sadda na ga wata zata burge ni ko ta bani sha'awa gida zan garzayo na ga halalina, na yi abin da nake so da ita. Ke dai idan kin gan ni afujajan na dawo miki, to ban da musu da bijire wa da sunan jan aji".
Dan haka ki saki ranki da ni, ke nake so, ke ce halaliya ta, da ke nake fatan na rayu muddin rai".
Na fara k'ananun hawaye na ce "To kuma nufin ka korata da ka yi da daddare a ganduna ne? Ya tafi a bilis?"
Ya tarairayo ni cikin rad'a ya ce "Ai ya wuce tunda da kaina na je na dawo da ke".
Na fara turza kafa ina fa'din "Alkur'an ban yarda ba".
Ya sheke da dariya ya ce "Dole sai kin nuna mini kina da alaka da mutanan Gwaram da Birin kudu domin a bakinsu nake jin wannan rantsuwar".
Na ce "To mahaifiyata ta fito daga yankin ai kuwa kasan jininsu ce".
Ya ce "Haka ne. To yanzu me zan yi ki yarda ki huce".
Na shiru ina tunani sai kawai na ce "Yi mini kukan zakara".
Ya ce "kukan sa wanne a ciki?"
Na ce "oh kukan zakaran kala kala ne?"
Ya ce "Yana cara idan afijir ya keto, yana yi yayin kiran sallar farillah akwai kuma wanda yake yi idan ya ga kaza yana kyarkyarar ta, yana hilar ta dan ya samu hadin kanta".
Kunya ta kama ni na ce "Yi mini wanda yake yi idan alfijir ya keto kawai".
Ya kuwa ce "Alkur'an ba shi zan yi ba tunda nima yanzu kyarkyarar ki nake yi".
Kafin na ce komai ya takarkare ya fara wani irin gurnani yan kur kur sai ya kuma ya yi cara tamkar dai zakaran gaske kafin na ankara ya turmushe ni irin yadda zakara yake dank'ar kaza.
Washagari da walwala muka tashi ya dawo Tijjanin da yake kaffa kaffa da ni.
Sai ririta ni yake yi. Komai shi ya yi har abin karya wa.
Na kalle shi cikin nutsuwa bayan ya d'ora ni akan cinya yana shinshinata tamkar maye. Na kama gemunsa na ce "Wannan shine .... Amma wancan da ya shude na aro ne".
Dariya mai yawa ta k'wace masa ya ce "sabo da Allah little mene ne wani dash dash? Ki ce Tijjanin da kika saba fa'da mana tunda har yau bani da k'imar da za'a sakaya mini suna".
Na yi murmushi na ce "Ai tunda na yi al'kawarin sai na haihu da na saka maka suna to fa sai na haihun. Idan ka matsu kawai nan da sati na fara amai, ka kai ni asibiti ana gwada ni ace ciki ne, tun a ranar zan fara fa'din sunan na ka".
Ya kankame ni sosai yana dariya kwarai da gaske.
Ya ce "Nan da shekaru goma masu zuwa zan tisa ki a gaba ina miki bitar wadannan kalaman a lokacin kin kai ashirin da bakwai.
Na ce "ko zuwa lokacin y'ay'a nawa na haifa?"
Ya zuba mini ido ya ce "Allah yasa sun kai uku"
Na ce "Haba dash dash ina laifin hudu ma. Nifa ina son yara da yawa."
Ya yi kissing din goshina ya ce "Allah ya bamu masu albarka. Nima ina so.
Amma kin san dole control zamu yi bazan yarda ki tara yara da yawa ki man ce da sha'anina ba".
Na yi k'asa da murya na ce "Kai ne fa bebina na farko ta ya ya zan mance ka? To ko y'ay'a dari na haifa kai ne a gabansu. Ni burina na haifo mai kama da kai".
Nan da nan kuma sai na rufe fuskata alamun kunya ta rufar mini.
Shi kuma da'din kalamaina ya yi matu'kar kama shi. Ya samu nutsuwar da gaske ina sonsa yanzu. Ya rungume ni tsam tsam ya kasa ce wa komai.
Ya sakar mini nishin da yake rura mini jiki. Ya ce "Ni kuma na fi son ki haifo mini little girl mai kama da ke. Amma ba mafad'aciya irin Asiya Toro ba".
Na cuna baki na ce "Yo ai ni fa'da na sai an tab'o ni".
*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*
63&64
*Watanni shida a gaba*.
Zuwa lokacin duk kaucen kaucen Tijjani na kada na shiga harkar ri'ke masa gida ta ci tura. Duk yadda baya son ya karbi ku'dina abin ya faskara domin samun ku'di ba k'aramin wahala yake ga talaka a wannan lokacin da aka janye tallafin mai a Nijeriya ba. Mafi yawa masu kananun sana'u sun shiga halin ni y'asu bare kuma wanda sana'ar sa hab'o ce ma'ana sai an samu za'a yi.
Duk da k'arancin shekaruna na fahimci matu'kar Tijjani zai fita ya dawo gida ba tare da ya ru'ko wani abu komai kankantar sa ba, to kuwa a wannan ranar ba zan gane kansa ba. Duk yadda zan yi masa rawar jiki da haba haba dan na samar masa da nutsuwlar bai gaza ba, ba kuma laifi ba ne dan ya fita ya dawo bai samo wani abu ya kawo mini ba. Kullum sai na fa'da masa cinikin da nake yi da nake samun makudan k'udade na yi imani mafita Ubangiji ya kawo mana, domin ba ni ka'dai ba ce wacce ta iya lallai a garin Toro. Amma duk macen da ta tunbatsa, duk macen da ta isa ko ta kai ta kawo to kuwa wajena take yin k'unshi da kitso. Sannan mafi yawa basa ba ni adadin ku'dina sai sun yi mini k'ari.
Idan ya bu'de baki sai ya ce "Ko ke ce Zainab Shamsuna ai ba'a ce na zauna na nad'e k'afar wando ki yi mini komai ba. Ubangiji ya ce na ciyar da ke, na tufatar da ke gwargwadon k'arfina."
Na nisa na ce "Haka ne! To a maimakon ka dinga tayar da hankalinka, nima kana tayar mini da nawa. Mu yi wata ka'ida mana".
Ya zuba mini ido yana saurarona. Na ce "Ka dinga siyar da lalle da mahallabiya da salatip. Ni kuma sai na dinga siya a wajen ka. Pure water ma da nake siyar wa sai ya koma naka ne zan dinga siyar maka".
Ya ce na yarda zan siyar da lalle amma ba zan siyar da ruwa ba tunda ai fridge din ba nawa ba ne".
Na ri'ke hannunsa na ce "Ashe kayana ba naka ba ne? Rannan a kunne na wata cikin y'anuwana take ta fa'din matu'kar mace da namiji igiyar aure ta zarge su ai komai da suke da shi ya zama mallakin junansu. Ta kalli idona ta ce mussaman idan ta haifa masa y'ay'a to ba wani sauran iyaka a tsakanin abubuwan da suka mallaka."
Na nisa na ce "Kana nufin wannan yarfen da aka yi mini, ni da kai ba kamar sauran ma'aurata ba ne? Abuna ba naka ba ne. Kai ma abin ka ba nawa ba ne saboda ni ban haihu ba?"
Na fa'da da rawar murya.
Jikinsa ya yi sanyi ya janyo ni jikinsa ya ce "Kina dai son ki yi mini rikici ne little ban da haka menene abin kuka? Duka ma shekarar ki nawa ne? Ni fa a halin da nake ciki ma ban shirya karban bebi ba. Hidimar ki ka'dai tana gagarata ina kuma da jariririn da bai san babu ba. Amma idan haihuwar ta zo ina so, kawai dai zan so ace bebinmu sun zo a lokacin da komai ya dai-daita mini ta yadda zan musu hidima sosai".
Na yi shiru na ce "Ka sare da yawa ne. Amma da sannu Allah zai kawo mafita."
Ya saki gauron numfashi ya ce "Ai al'amuran k'asar ne ya lalace komai sai da hanya, hanyar ma sai ka biya makudan k'udade kafin ka samu aikin gwamnati."
Na ce "Idan Allah ya k'addara abu rabon bawa ne komin tsanani sai ya same shi".
Da haka na lallaba shi na samu kwanciyar hankali, domin ni rashin ku'dinsa baya damuna irin idan ya takure ya k'i sukuni. Nafi son soyayya, nafi son walwala. Bana kuma samun hakan sai idan yana kawo wani abu, domin ya riga ya k'yamaci ace ni ce nake ciyar da mu.
Washagari da wuri ya fita.
Bai dawo ba sai yamma lis. Wani abun mamaki da buhun sabon lalle irin mai L din nan ya dawo har buhu uku amma d'anye ne.
Na kalle shi na ga ya yi laga laga.
Tabbacin da kansa ya shiga jeji ya samo.
Tausayinsa ya yi matu'kar kama ni.
Hawaye ya cika mini ido, a zuciyata sai addu'a nake yi masa akan Ubangiji ya hore masa hanyar da zai ri'ke gidansa cikin sau'ki.
Da k'yar na ha'diye kukan nawa na dinga yi masa sannu. Ya zauna akan baranda ya ce "Asiya na gaji sosai ga k'aya ta yi ta suka na."
Da tausayi na ce "Sannu, Ubangiji
ya baka lada, ya kuma sanya wa neman ka albarka."
Na dauko masa ruwa ya sha. Na kalle shi ya yi kaca kaca da shi. Har kan gashinsa k'ura ne.
Na ce "Bari na juyo maka ruwa wanka ga shi akan gawayi.
Da kai ya amsa mini.
Na sirka ruwan na kai masa bandaki.
Ya shiga ya yi. Ya fito ya jika kayan da ya cire. Sannan ya shiga daki dan ya shirya.
Kafin nan kuwa na Kai masa abinci falo.
Na zuba omo na sab'e masa kayan na shanya masa.
Ya fito ya ga ina shanya. Ya murmusa ya ce "Ni ina ce Asiya Toro ce ta ce Aji dawun ta yiwa k'ato wanki?"
Kunya ta kama ni domin na sani tsokana ta ya yi, tare da tuna mini sababin da nake yiwa Nasiba idan tana yi masa wanki.
Na dara na ce "Ai har yanzu ma ba zan yi ba, kawai na yi maka ne a matsayinka na mijina kuma bebina".
Ya shiga falon yana ce wa "zo mu yi maganar a zaune".
Yana cin abinci ina masa fifita. Ya ce "Da wayo da wayo dai so kike ki dinga ce mini Bebi ko?"
Na yi gajeriyar dariya na ce "A a ai sunan ka yana zuciyata lokacin kawai nake jira. Amma kai kanka ai kasan bebi ne. Domin abin da kake yi mini ai bebis ne suke yin hakan. Ba dama ka kwanta sai ina kusa da kai. Ko juyi zan yi sai dai mu juya kwanciyar gaba'daya, saboda kana.." sai na kasa fa'da.
Ya zuba mini ido ya ce "Fadi mana marar kunya. Me nake yi? Na daure na ce zuke wa bebis din da zan haifa mana abinsu."
Ya murmusa ya ce "Ai ba nasu ba ne, nawa ne, idan sun zo dai zan dinga sammu su, idan lokacin shansu ya k'are za'a cire su, su bar mini kayana. Ni ai ba zaki taba yaye ni ba".
Na yi dariya na kawar da maganar da ce wa "Wai da kanka ka je yago lallen ne?"
Ya ce "Eh. Baban Marina na tambaya ko ina zan dinga samun lalle ina sara. Sai ya kwatanta mini yankin da Ubangiji ya azurta da lalle. D'an na goro ake bawa digacin yankin sai ka je ka yi ta yanka.
Shine ma ya bani dubu guda duk da shima fama yake da kansa. Da naki karba kin ga b'acin ran da ya yi?
Wai raina shi na yi, shi yasa nake ganin ba zai iya bani abu na kar'ba ba.
Nasa hannu biyu na kar'ba ina ba shi ha'kuri, shi kuma yana ta yi mini fararen addu'oin da suka k'arfafa mini guiwa.".
Na rausayar da kai na ce "Allah ya bada sa'a, yasa a fara a sa'a".
Ya amsa da "Ameen Little".
Kwanaki ka'dan lallensa ya bushe. Da kansa ya zauna ya gyara abinsa tsab. Ya ha'de su a buhu biyu.
Ya fita da su, ni dai bansan inda ya kai ba sai gani na yi ya dawo da shi ya zama gari mai laushi ainun, kuma ya yi auki domin ba k'aramin yawa ne da shi ba. Ya kusa yin buhu guda.
Ganin hakan sai na auni kwano biyu na zauna na k'ulle shi tas. D'aurin hamsin, da d'ari. Duk wanda suka zo k'unshi sai na yi musu tallan ina sayar da lalle, ina k'wabawa mutum yasa a gidansa.
Nan ma sai Ubangiji ya sanya albarka domin duk sati sai na k'ulla kwano biyu, nima kuma a satin ina k'arar da fin kwano uku ma.
Kafin ka ce miye wannan sai jarin Tijjani ya kafu ya samu na siyo mahallabiya da kwalin salatip.
Duk sati kuwa zai je ya yago domin ya gamsu ba k'aramin rufin asiri hakan ya yi masa ba.
Tunda duk sati zan ha'da masa ku'dinsa a kalla dubu goma. Idan ya kar'ba kuwa zai siyo kayan abinci da k'ananun abubuwa. Maganar ku'din cefane kuwa da ku'din pure water muke yi. Duk da hakan nawa yana shiga amma ba mai yawa ba ne. A hakan kuma bai fasa fita ya yi sana'a ba idan ya samu.
Hankalinmu a kwance yake, mun samu rufin asiri. Tunda ya samu ya biya ku'din gidan amma na watanni shida, rabin shekara. Duk nacin ya kar'ba ya biya na shekarar sai ya biya ni a hankali bai yarda ba.
Da na matsa ma sai ce mini ya yi "Allah ya karbi ransa kafin ya ga ranar da zan biya masa ku'din hayar gidan da zai kwana."
Daga haka na ja bakina na tsuke.
Muna cikin wannan rayuwar mai da'di domin dukkanmu mun gamsu da kokarin junanmu. Na yarda ina amfani da duk abin da ya ba ni, ina iyakacin kokarina ban nuna masa ina bu'katar abu sama da k'arfinsa ba, na kuma ajiye dukkan burikana na son na dinga yin suturu masu tsada. Maimakon haka sai na tattara na sayi dan kunnen gold wanda shi da kansa na bawa ku'di ya siyo mini a Jos. Ko zan yi abu a gidan sai cikin dabara ko kuma na kara masa ku'din lallensa idan sati ya zagayo. Shi kuma tunda ya fahimci burina soyayya irin ta indiyawa sai yake ajiye komai ya yi ta kashe ni da kalolin soyayyar da ko indiyawa ma sai a shiri, tunda suma ai shirin fim ne. Shiri kuwa kowa yasan shirya shi ake yi.
Amma a hakan yake lalace mini. Ya zama tamkar mai irin shekaruna. Ko a littafai ba kasafai ake samun irin Bulkachuwa ba. Domin ya iya shiririta kala kala da mata suke son ayi musu. Idan yana gida barin komai yake ya tarairaye ni. Cinyarsa ita ce wajen zama na. Goyo kuwa zai iya goya ni, ya yi shara. Har k'aton baho ya siyo irin tafkeke na masu wankan jego. Ya cika shi da ruwa ya dauke ni ya tsunduma. Ya wanke ni tas.
A shimfida kuwa irin murza ni da yake yi, da da'din da yake jiyar da ni dole ma na so shi na rikice a kansa. Domin har cikin zuciyata na fara tunanin da ba shi na aura ba dan ban more ba. Har jin haushin son da na yiwa Yaya J na fara yi.
Gaba'daya na gama mutuwa a kansa, ba abin da nake so irin na gan shi a gida idan yamma ta yi. Yanzu da baya fita lahadi a gida yake yini. Da kaina na soke yin lalle da kitso. Komin girman mace bana yi a wannan ranar zan fa'da mata maigidan ya hana yi a wannan ranar.
Dan na fahimci ba a daina zuwa ana katse mana jin da'dinmu ba sai nake yawan rubutawa a status d'ina cewar babu lalle ranar lahadi haka ma kitso.
Mun yi kyau, mun shak'u da juna, komai yana tafiya dai-dai mussaman da na daina yi masa rikicin bai yi mini ciki ba.
Da kansa ya dauke ni muka je asibiti da muka cika shekara guda da aure. Dukkanmu aka auna mu aka tabbatar mana lafiyarmu k'alau cikin ko wanne lokaci zamu iya haihuwa. Shike nan sai na daina damuwa illah iyaka ban daina addu'ar ma samu ciki na haihu ba.
Muna cikin wannan yanayin mai da'di Rafi'a ta kammala karatunta na jamaia ta dawo gida gaba'daya.
Kusan kullum sai ta shigo mini. A zuciyata bana so amma tunda uwarta ba k'aramin kirki take yi mini ba. Sai nake share wa mussaman ita din ma mai kirki ce.
Amma haka kawai nake jin fargabar zakewarta a wajena domin na riga da na sani mijina yana son yan lukataye irin ta. Ni kuma yar firit ce. Sannan bazan yaudari kaina ba, zai iya sha'awarta tunda jikinta rugu rugu ne, kuma bayltw damu ta saka mayafi ba. Tunda tana ganin ba sai ta fita waje da ta shigo ba. Bugu da kari ba Hausawa ba ne. Wasu abubuwan nasu da namu akwai banbanci.
Haka dai nake ta daure wa ina ta k'ok'arin ban bar shi da kewa ba. Komai yake so sai na yi masa. Ba kuma na tab'a k'osawa da al'amarinsa duk da nima ina son harkar. Amma bana ja masa rai saboda kada ya ga ni a waje ya yi sha'awa. Ba kuma na nunawa ya gundure ni.
Ana cikin haka aka tashi bikin. Ihsan k'anwarsa. Tun saura sati biki na tafi, saboda a fara komai da ni, sannan ni ce zan mata k'unshi da kitso.
Babah sai ina ka saka take yi da ni. Yadda ta ga na murje na yi kyau ba karamin da'di ta ji ba. Na sani kuma da a ce da goyo na je mata da tafi haka murna.
Shi da kansa ya kai ni. Washagari ya tafi akan sai nan da kwanaki ka'dan zai juyo. Komai sai da na bar masa, hatta miya sai da na soya masa, na yi masa cincin. Kawai tafasa farar taliya ko shinkafa zai yi sai kuwa shayi.
Ana gobe biki y'an Toro suka iso. Aka yi hidima cikin rufin asiri taro ya tashi lafiya.
Kwanaki biyu a tsakani ya zo muka tafi shake da kayan biki masu yawa.
Tunda muka yi aure bamu ta'ba nisa da juna ba sai wannan karon.
Duk da dai a Bulkachuwan ma ranar biki sai da ya faki ido ya jani muka je wani waje ya yi abin da zai yi sannan ya dawo da ni.
Amma muna isa gida ko hutawa bamu yi ba. Daki ya ja ni bamu fito ba sai da ya samu nutsuwa.
Da daddare ina zaune a cinyarsa sai ce mini ya yi "Little baki da nauyi, shafal ban ji kin danne ni ba".
Na zabura na kalle shi, gabana ya fa'di sosai. Da rawar murya na ce "Sai yau ka fahimci haka? Wa ka d'ora a cinyar da yanzu baka ji yadda kake so ba?"
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
Ya daburce ya ce "Wallahi babu kowa Yabi".
Fa'din Yabi da rudun da ya shiga sai yasa na kasa gasgata shi amma kuma na danne na ha'diye saboda babu kyau zargi.
Duk yadda na so na bar maganar amma a zuciyata sai wasi-wasi nake yi. Na kasa samun nutsuwa. Hakan ya fara shafar walwalata. Ban sauya masa ba, ba kuma na bijire masa amma kuma babu shiriritar da nake yi masa a baya.
Rannan na ce masa ina son na je gida na yini. Da rawar baki ya ce "To, yaushe zaki je?"
Domin ya takura da rashin walwalata.
Na ce "Duk ranar da ka ce".
Ya ce "To gobe sai na kai ki"
Haka kuwa da kansa ya kai ni, muka fara isa k'ofar Dada muka gaisa. Tana ta barkwancinta da karatunta. Ban wani jima ba na tashi na nufi k'ofarmu."
Ya shigo suka gaisa ya ce mini zai tafi da yaushe zai zo ya d'auke ni?
Na ce "ko yaushe ma".
A k'ok"arinsa na son ya kyautata mini sai ya ce "Tom idan an idar da Isha zan zo".
Na ce "Allah ya kai mu".
Ya tafi. Na yini cikin iyayena cikin nutsuwa da walwala.
Da yamma lis Gwaggo da Inna zasu je duba yar kanwar Mama da ta haihu kusa da unguwarmu ne.
Dan haka Baban Marina ya ce "Asiya sai ku je tare ki rakasu idan kin dawo sai ki shige gidanki".
Na amsa da ce wa "To Babanmu, domin idam Gwaggo ta fita ba jin da'din zaman zan yi a dakin ni ka'dai ba, tunda Ikilima ta tafi Islamiya, shima kuma Baban fita zai yi. Mama kuwa babu wata ma'amala mai yawa a tsakaninmu.
Dan haka muka tafi tare. Da muka dawo na yi lungun da zai sada ni da gidana, su kuwa suka mik'e suka koma nasu gidan.
Haka kawai nake jin nauyin jiki na saukar mini. Wani irin b'acin rai ya ziyar ce ni da na karyo kwanar da na fara hangen gidanmu. Haka nake tafe ina ta jin fargaba. Ina kuma ayyana abubuwa marasa da'di a zuciyata.
Nan da nan na fara ta'awizi ina kore shaid'anin da yake son yin wasan kura da zuciyata. Har cikin zuciyata ina son Tijjani, ina son na rayu da shi. Domin a zaman da muka yi na shekara daya da kusan rabi na tabbatar yana da kyawawan dabi'u. Na farko shi mutum ne mai mutunta sallar farillah. Sannan mai yawan tsayuwar dare ne na shaida hakan. Domin duk lokacin da zai shafe yana tiritiri da ni da daddare, to da zarar k'arfe uku ta yi kuma zai tashi ya yi wanka. Ya yi ta yin munajati da Ubangijinsa, wani lokacin ya matsa mini na tashi, wani zubin kuma ya k'yale ni na yi barcina. Sau tari kuma idan ban tashi ba, da asuba idan ya tashe ni sai ya ce "Tashi ki yi sallar farillah akan lokaci, na raba dare ina roka miki alherin duniya da lahira my little".
Bayan hakan na karance shi yana da matu'kar son ya kiyaye ka'idojin da shari'a ta d'ora masa mussaman na ri'ke gida da kula da tarbiyata. Sannan ba shi da mugunta ko ka'dan har yau din nan Tijjani bai ta'ba saka mini ido akan ku'dina ba. Asalima kullum cikin k'ara k'auwame kansa yake yi da abin hannuna.
Sannan ya iya Soyayyar da duk taurin zuciyar mace sai ya dargaza ta. Ga kuma girmama iyaye, yana mutuntata manya kwarai da gaske. Wadannan dabi'un da ya siffantu da su ya sanya nake hakuri da inda yake kuskure mini, hakan ne kuma dalilin da yasa na k'i yarda na k'arfafa wa kaina zargin ko ya koma Bak'ar Ta'adar sa ta baya.
Na shiga zauren na ga kofar tamu a rufe ruf. Na fara tunanin ai ban fito da mukulli ba, tunda mun yi shi zai zo ya dauke ni.
Na zaro waya da nufin na k'ira shi ya zo ya bu'de mini, sannan na wuce k'ofar Maman Safiyanu na jira shi. Sai na jingina da k'yauren k'ofar ga mamakina sai na ga ta bud'u.
Na tura a hankali na ga sakata a ture tabbacin an saka bata shiga ba ne.
Na shigo a hankali. Amma sai na ci birki na tsaya cikin tsananin tu'ajjibi da mastanancin mamaki mai yawa.
Jikina ya d'auki b'ari, zuciyata ta yi nauyi ainun. Amma idona ya bushe k'amas.
Na saka hannuna na murtsike idanuwana da tunanin gizo yake yi mini, tare da fatan ace sak'e sak'en zuciyata ne da wasi-wasi irin na shaid'an.
Amma ina zahiri nake ganinsu. Tijjani zaune akan baranda yayin da Rafi'a take kan cinyoyinsa da manyan mazaunanta. Ta kwanta luf a kirjinsa, shi kuma idonsa na kan k'irjinta yana kallonsu. A zahiri iya abin da na gani ke nan amma zuciyata sai ta shiga wassafo mini cewar yanzu ma suka sanya tufafinsu.
Na ki'dima ainun, amma na kasa yin kwakkwaran motsi, na tsaya cak ina kallonsu tamkar mutum mutumi
K'arar faduwar wayata ne ya ankarar da shi.
Ya d'ago da fuskarsa ai yana ganina ya yi wani irin zabura ya wancakalar da ita, ta hantsilo ta fa'do kan guiwowinta.
A matu'kar rude ya k'araso gare ni.
Ya rasa mai zai ce, sai kawai ya zube a gabana guiwa bibbiyu. Ya ru'ko hannuna na kalle shi na ce "Tijjani gizo idona yake yi, ko mafarki nake yi?".
A ki'dime ya ce "Zan so a ce mafarkin kike yi Asiya".
Daidai lokacin Rafi'a ta zo ta shige sum sum tamkar k'wai ya fashe mata a ciki.
Na dinga jin tukukin ba'kin ciki da tashin hankali. Amma kuma idona a soye duk yadda nake son hawaye ya zubo mini abu ya ci tura.
Na sunkuya na d'auki waya ta na k'wace hannuna na yi d'akina ina jin jiri na katantanwa da ni.
Kai tsaye na hau cire rigar cikina domin zafin da nake ji a zuciyata har jikina yake kutso wa. Zufa sai yanko mini take yi.
Na cire komai na d'aura zani. Na zauna amma ban daina jin zafin jiki ba.
Na fita har lokacin yana durk'ushe a inda na bar shi.
Na dauki botiki na nufi rijiya. Da azama ya tare ni, ya ce " Bana hana ki jan ruwa da kan ki ba?".
Ban ce komai ba na matsa gefe ya janyo mini ruwan. Ya kinkima ya kai mini band'akin.
Na shiga na yi wanka. Amma dana fito ina goge jikina da tawul, zufar na sake keto mini.
Na dauki rigar barci marar nauyi na saka, bayan na saka gajeran wando ta ciki. Na d'aure kaina da dan kwali mai taushi.
Kicin na fa'da na hau girki, ina yi ina hailala. Gaba'daya jina nake yi tamkar ba ni ba. Na yi matu'kar kad'uwa da abin da na ga ni a cikin gidan aurena.
Ban san falalar kuka ba sai a yau, domin gaba'daya hawayen ya k'i zuba.
Shi kuma ya takure, a gefe tamkar ka ce k'yat ya zura a guje. Cikin lokaci k'alilan nadama mai tsananin gaske ta bayyana a dukkan jikinsa. Ya kasa sukuni, da alamu kunya ce ta hana shi sukuni. Tunda ni dai ban bu'de baki na ce masa komai ba.
65&66.
Na gama komai na kai falo kamar yadda na saba. Shi kuma ya zama mutum mutumi.
Na fito na ce "Ga abinci ko sai ka dawo daga masallaci?"
Ya zuba mini ido ya rasa abin fa'da.
Ya tashi ya ce "Da sauran lokaci ai."
Na zuba mana kamar yadda na saba. Amma gaba'daya mun kasa ci sai faman juya shi muke yi.
Gara ni na ci loma biyu na ji mak'oshina ya cushe na ajiye. Shi kuwa yama kasa kaiwa ba'kin nasa.
Ya gaji ya kalle ni ya ce "Asiya dan Allah ki yi ha'kuri, ki yafe mini".
Ba ja in ja na ce "To".
Daga haka kuma ban sake ce wa komai ba. Ya yi maganganu na ban ha'kuri da nuna nadama masu yawa amma ban ko kalle shi ba. Aka kira sallah ban yarda na bu'de baki mun yi magana kamar yadda yake fata, ya yi alwala ya tafi masallaci.
Har muka kwanta ban bu'de baki na ce k'ala ba. Duk jaye-jayen maganarsa kuwa. Da muka kwanta ya fara lalubata ban hana shi ba, amma ko kwakkwaran motsi ban yi ba. Ya yi duk abin da zai yi dan na motsa ko na mayar masa martani amma tamkar an shuka dusa.
Ya gaji ya koma ya kwanta yana fa'din "Innalillahi wa ilaihir rajiun" .
Ya ru'ko ni da rawar murya ya ce "Asiya ki yiwa Allah, ki bu'de baki mu yi magana".
Yana rufe baki na ce"To".
"Asiya ki yi ha'kuri, ki yafe mini, dan Allah, dan Annabi, ki yafe mini".
Na yi shiru. Ya sake ce wa Ban san me ya same ni ba Asiya. Dan Allah ki mini uzziri ki yi ha'kuri ki yafe mini".
Nan ma na ce "To".
Ya yi iya ban hakuri, amma ban yarda na ce komai ba.
Da gari ya waye da wuri ya dawo daga masallaci ya hau hidimar gyaran gida.
Ya yi abin karyawa. Har d'aki ya kawo mini amma ina ci sau daya ban sake kai wa na biyu ba, na ce na koshi. Ya yi shiru ya rasa yadda zai yi.
Bai fita ko ina ba. Yini aka yi ana zuwa lalle amma ban iya yiwa ko mutum daya ba. Sai ha'kuri nake basu tare da uzzirin ce wa ba ni da lafiya ne.
Hakan da ya ga ni ya sake rib'anya tashin hankalinsa. Domin yasan yadda nake matu'kar son sana'ata. Bana son abin da zai hana ni yin lalle ko kitso.
Amma da bakina nake sallamar mutane yasan al'amarin da yake zuciyata ba k'ank'ani ba ne.
Kwanaki uku muna cikin wannan halin. Daga ni har shi, mun yi matu'kar rame wa tunda bama iya cin abinci ga rashin nutsuwar zuciya.
Ya yi juyin duniya mu yi magana na k'i, domin har yau ban yarda na yi masa k'orafi ba. Komai kuma zai ce sai na amsa da "To". Kullum safiya zan gaishe shi, zan kuma amsa sallamar sa idan ya shigo. Daga hakan kuma bazan sake yarda na ce komai ba. Rashin yin lallen har zuwa lokacin ya fara ta'bamu tunda shima baya iya fita, ko ya fitan ma baya nisan kiwo zai dawo.
Ranar da aka yi kwanaki biyar da faruwar al'amarin Tijjani ya zauna ya ba ni hakuri tamkar yawun bakinsa zai k'afe. Har da k'wallarsa. Amma ban ce komai ba, sai ma murmushi mai ciwo da na yi na ce masa "To me ka yi ne Tijjani?"
Duk da k'arancin shekaruna amma na fahimci shirun da na yi masa ba k'aramin dafa shi take yi ba. Ba abin da yake so irin na yarda mun yi magana ko da rashin kunya ne na yi masa. Amma ban yi hakan ba. Ni a karan kaina so nake na yi kuka, na caccaba masa maganganun da zasu gasa masa zuciya tamkar yadda ya yi dalilin da tawa zuciyar take gasuwa, amma na kasa.
Tsawon sati guda muna cikin wannan matsanancin halin, daga ni har shi mun zama wasu iri. Gidanmu ya koma tamkar na zaman makokin mutuwar uwa mahaifiya.
Sannan na k'i yin k'unshi har lokacin. Al'amarin da ya sake damalmala mana komai.
Tijjani kam kawai k'arfin halin da aka san maza da shi ne. Amma kana kallonsa kasan yana dandanar kudarsa da shiruna. Yadda bana cin abinci haka shima baya ci. Gara ma ni da daddare na kan yi barci, amma shi duk juyin da zan yi zan gan shi kan sallaya ko yana zaune ko kuma yana sallah.
Da asuba ya dawo ya tarar har na koma na kwanta.
Ya zauna a bakin gadon. A sanyaye ya ce "Asiya wai a haka zamu rayu ne? Bazan iya wannan rayuwar ba. Ki yiwa Allah da ma'aiki ki bu'de baki ki fa'di duk abin da kike so. Na ro'ke ki ba dan ni ba, da Allah nake ha'da ki."
Ko motsi ban yi ba.
Ya tsananta da magiya. Sai kawai ji na yi cak ya dauke ni ya yi nufin d'ora ni kan cinyoyinsa. Ai gaba'daya wani irin k'arfi mai tattare da matsanancin fishi ya taso mini. Da dukkan zuciyata na fisge na ingiza shi ya fadi k'asa warwas.
Na dinga huci mai zafi, amma na kasa bu'de baki na yi magana.
K'irjina sai harbawa yake yi da tsananin gaske.
Ya mik'e ya kafe ni da ido, cikin kad'uwa da tashin hankali. Ya ce "Dan Allah bu'de baki ki yi magana Asiya. Fadi me zaki ce, idan kuma na zauna ki mini duka zai fi mini akan irin halin da nake ganin ki, ki yafe wa mijinki, ki yafe wa masoyinki, ki yafe mini, kaddara ce ta hau kaina Asiya".
Na juya na kwanta ba tare da na ce uffan ba.
Kukan kuma bai zo ba.
Ya kasa hakuri ya sake biyo ni inda nake kwance ya hau lalubata, ban hana shi ba, ban kuma yi wani yun'kurin da zan tankwabar da shi ba. Ya yi abin da zai yi. Yana gamawa na lalubi zanina na daura na fice.
Wanka na yi, sannan na dawo na kwanta.
Shi kuma yana kwance sai fa'din "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya ke yi da k'arfi.
Yau duk jarumtar sa kasa yin ayyukan gidan ya yi. Dan haka na yi abuna. Na yi abin karyawa har na gama yana kwance. Na d'aga labule na ce "Ka zo mu karya."
Yana daga kwancen ya ce "Ko na zo d'in ma ai ba ci muke yi ba. Ki yafici abin da zaki ya fita ki rufe".
Wasa wasa yana kwance har azahar, ko wanka bai fito ya yi ba. Abin da ban ta'ba ganin ya yi ba, zama da janaba. Komin dare baya kwanciya sai ya yi wanka. Ko da kuwa zai yi second round. Amma yau safiyar Allah kuma ba barci ba, amma yana nad'e ya kasa tashi bare ko ruwan shayi ya kurb'a. Na sani fishin nawa ne ya fara k'ure malejin jarumtar sa.
Ina zaune ina tunanin al'amurar rayuwa sai na ga fitowarsa, daure da tawul da k'yar yake daga k'afafuwansa rauni gaba'daya ya bayyana a jikinsa.
Da ya tashi dawo wa daga masallaci sai ga shi da Malam liman da Malam mai Tafsiri.
Ganin dattawa kuma manyan Malamai na shiga marabatarsu da girmamawa. Shi da kansa ya yi musu jagoranci zuwa falonmu.
Na zuba ruwa a k'aramin tray na ajye a gabansu. Na gaishe su cikin ladabi. Suka amsa suna saka mini albarka. Na yun'kura zan tashi na basu waje dan a tunanina wajen Tijjani suka zo.
Sai kawai na ji sun ce "Ina zaki kuma, ai zuwan na ki ne".
Gabana ya yanke ya fa'di to me ya kawosu waje na ni kuwa?"
Malam liman ya yi gyaran murya ya yi addu'ar bude taro, ya nemi tsari daga sharrin shaidan da rundunarsa. Sannan ya ro'ki Ubangiji ya sanya albarka a abin da za'a tattauna.
Aka amsa da ameen.
Ya zarce da ce wa "Asiya mijinki ne ya same mu ya kawo k'arar kansa da kansa gabanmu. Da bakinsa ya ce ya yi miki laifi da ya amsa sunan laifi. Amma yana ro'kon mu zo mu baki ha'kuri a madadinsa".
Na yi k'asa da kaina, ban ce komai ba.
Domin ba k'aramin nauyi na ji ya kama ni ba. Akan me zai dauko mini manyan mutane irin haka?
Malam liman ya zarce da ce wa "falalar hakuri yawa ne da shi Asiya. Mijinki ya yi nadama, irin wacce ake so mumini ya yi. A wannan zamanin idan mutum ya yi kuskure ya yarda ya yin ma, har yake bada ha'kuri ba k'aramin mutumin kirki ba ne. Abin da yasa na yarda na zo ke nan da bakinsa ya ce ya miki k'aton laifi. Sannan na ga rauni mai yawa a tare da shi, wanda idan ba'a ba shi dauki ba zai iya kwantar da shi. Ki gode wa Allah da ya baki miji mai kiyaye sallah. Sama da shekara da zuwansa unguwar nan ban ta'ba fashin ganinsa a sahun gaba na sallar isha da asubahi ba. Annabin Rahma ya ce wadannan sallolin munafukai basa kiyaye ta. Ki yi hakuri da inda ya gaza mutumin kirki ne, na shaida hakan".
Sai lokacin kuka mai tsananin gaske ya k'wace mini, irin kukan da yake ki'dima duk mai sauraronsa, kuka mai dafa zuciya mai sawa a shid'e.
Kowa ya yi shiru, illah Tijjani da yake fa'din "Alhamdulillah! Alhamdulillah cikin wani irin yanayi. Domin ya sani rashin kukan da ban samu na yi ba. Da rashin furzar da maganganu. Ya sanya na taurare nake dafa shi ta hanyar zuru.
Malam mai Tafsiri da yafi kusa da ni, kuma yafi tsufa, domin ya tsufa ainun, na tabbatar ya haifi kamar Babanmu.
Ya d'ora hannunsa a kaina yana shafa mini, cikin muryarsa ta girma ya ce "Yi hakuri jikata. Kara hakuri, Innallaha ma-assabirin. Ki daina irin wannan kukan zai janyo miki ciwo. Yi salati ki samu nutsuwa. Tsawon lokaci yana shafar kaina tare da maganganu masu taushi har na samu nutsuwar.
Hannunsa na kaina ya ce "Shin Asiya ta huce ta ha'kura ta yafe wa mijinta?"
Da rawar murya na ce "Akan me zai dauko mini ku? Ni bai mini komai ba, kuma nima ban ce masa ya yi mini wani abu ba."
Da azama kuma da cikin rawar murya ya ce "Na yi miki Asiya! Ni nasan ban kyauta ba. Amma ki dubi Allah ki yi ha'kuri. Ki bani dama mu tattauna, mu rufe maganar nan ta wuce".
Na kalle shi hawaye na zuba mini na ce "Tunda ka kafe ka yi mini laifi, fadi laifin da bakinka. Fa'da musu su ji".
Ya yi k'asa da kansa ya kasa ce wa komai.
Na juyar da fuskata na ce "Kun ga ni ba. Ai bai mini laifi ba. In ma ya yi Allah ya yiwa, na tabbatar kuma ya nemi gafarsa tunda kwana yake yi yana ibada. Ni kuwa bai mini komai ba."
Malam liman ya ce "Ga shi da bakinki kike shaidar yana kwana sallah anya bai cancanci ki yafe masa ba. Kin san darajar wanda yake munajati da Allah fil lail kuwa?"
Kamar na ce "Amma ibadar tasa bata hana shi ya yi barna ba, bata hana shi ya tozarta ni ta hanyar yin bak'ar TA'ADAR mua'amalantar wata macen da bai aura ba a gidan aurena ba.
Amma na kasa bu'de baki na fa'da musu hakan.
Ban san da gaske ina son Tijjani ba sai yanzu. Domin bayan matsanancin kishinsa da yake cina, sai na ji bazan iya tona masa asiri ba.
Bazan iya fa'dawa wani mahaluki abin da na ga ya aika ta ba.
Malam liman ya sake ce wa "Ki yi ha'kuri kin ji Asiya. Ki yi koyi da mai sunan ki Nana Asiya. Annabi ya fa'da mana falalar ta. Abin da kuma ya janyo mata babban rabo a wajen Ubangiji imaninta da hakurinta akan mijinta ne. Ki yi hakuri, da sannu Ubangiji zai daidaita muku al'amuranku."
Jikina ya mutu tubus. Na ce "To".
Suka dinga saka mini albarka da godiya. Malama liman ya mike ya ce "Tunda ta amsa ta huce ai shike nan, kai kuma ka kiyaye, kada ka sake aikata laifin ka."
Da sauri Tijjani ya ce "In sha Allah! Na gode amma Wallahi bata ha'kura ba, kuna tafiya zata cigaba da fishinta. Ni ma ta ce mini to yafi a k'irga."
Jin haka Malam mai Tafsiri ya sake d'ora hannunsa a kaina ya ce "Asiya na yafe wa mijinki a madadinki, na rufe wannan maganar har abada, shin zaki yi mini wannan lamini, zaki mini wannan mutuntawar?"
Yam jikina ya amsa. Wani irin abu ya tsriga mini a zuciyata wadda tun ranar da abin ya faru ya tokare ni.
A sanyaye na ce "Shike nan Malam na yarda, na kuma yafe masa". Bulkachuwa na jin hakan.
Da k'arfi ya ce "Alhamdulillah! Allah na gode, Allah ka taimake ni, ka tsare ni."
Ya matso yana fa'din "na gode Asiya".
Na galla masa harara na ce "Wallahi ba dan Malam ne ya yafe maka a madadina ba, da har ka tsufa kamar sa baza ka sake ganin walwala a fuskata bare dariyata. Ba kuma zan sake aminta da kai ba. Amma yanzu ka ci darajar masu daraja".
Ya matsa kusa da Malam din ya ce "Na gode sosai Malam. A kuma taya ni da addu'a Allah yasa k'arshen al'amarin ke nan. Na gode muku, Allah yasa ku gama lafiya".
Suka tafi suna mini godiyar yarda da na yi sun isa da ni. Sai addu'ar mu samu haihuwa mai albarka suke yi mana.
Shi kuwa jan kunne da tunasar da shi girman hakkina da yake kansa suke yi.
Suna ta jaddada masa indai ya musguna mini da gangan ba zai ga haske a al'amuran sa ba.
Ya jima bai dawo ba, da alamun dai har gidajensu ya musu rakiya.
Ya dawo ya tarar da ni a falo. Na amsa sallamar sa na d'auke kaina.
Ya shigo da d'an kuzarinsa. Ya kalle ni ya ce "little me kike son ci na dafa miki?"
Ba walwala a fuskata na ce "Babu".
Ya matso ya durk'ushe tamkar mai neman gafara. Ya ce "Kin amsa kin yafe mini, kin amsa kin rufe maganar me zai sa kuma ki basar da ni? Na ro'ke ki dan darajar Annabi ki yafe mini, dan Allah. Shirun ki bala'i ne. Ki fa'di komai na zuciyar ki, zan ha'diye, na sani ban kyauta ba, amma nima ban san me ya same ni ba."
Da kuka na ce "Tun yaushe kuke yin hakan?"
Da rawar murya ya ce "Ranar ne kawai, Wallahi shine na farko kuma na k'arshe Asiya."
Na ce "Ban yarda ba. Ina ce dama kafin ranar ka ce mini ni bana danne ka yadda kake so?".
Ya daburce ya ce "Billahillazi kawai na fa'da ne, amma ba dan ina d'ora wasu ba ne. Ki yarda da ni, ki bani wata damar, kada ki yanke aminci da yarda a tsakaninmu dan Allah".
Ya fa'da hankalinsa a tashe matu'ka.
Ya ru'ko hannuna ya ce "Ki ji tausayina little. Zuciyata zata iya bugawa idan kika cigaba da share ni, na yi tuba a wajen Ubangiji, ke ma ga ni durk'ushe a gaban ki, ki yafe mini"
Na kafe shi da ido hawaye na zuba. Shi ma ya zuba mini nasa da suka kada suka yi jawur.
Da kuka na ce "Kana tunanin zan samu nutsuwa idan kuna rayuwa da Rafi'a a gida daya, kana ganin zan iya mance wa idan ina ganin gittawar ta?"
Ya yi shiru. Na ce "ko ina son na manta ba zai yiwu ba. Dan haka zan fa'da maka gaskiyar magana. Sai dai ka zabi daya a ciikin ni da ita".
Ina rufe baki ya ce "wanne irin zabi ne wanda babu azanci a cikinsa? Ta ya ya zaki ce na zaba a cikinku? Ai ke ce tawa, ke nake so, ke nake burin rayuwa da ke, ke kike burge ni."
Da rawar murya na ce "Ita kuma tana baka sha'awa, kana son ka ji manyan mazaunanta a k'asanka, kana son kama manyan non..".
Ya yi maza ya rufe mini baki jikinsa na bari irin na zullumi.
Ya ce "Na zabe ki, ke nake so Asiya Ubangiji ne shaidar ban so wata mace kamar yadda nake son ki ba. Na kuma yi imanin ba zan so wata sama da ke a bayan ki ba."
Na goge hawayen idona na ce "muhimmi a gurina ka zama kamamme, idan har son da kake yi mini bai yi tasirin da zai kange ka daga ta'ba haramun ba ai banzar wannan son Tijjani".
Da rawar murya ya ce "Allah ka mayar da ni kamamme. Allah ka yafe mini, Allah na tuba".
Tausayinsa ya kama ni yadda yake daga hannuwansa yana ro'kon da dukkan zuciyarsa.
Na nisa na ce "Mu fuskanci gaskiya. Idan da gaske son ka nake yi to akwai bu'katar na baka gudumawar da zaka tsira daga fa'dawa halaka. Na yarda na kuma gamsu kana sona. Nima kuma idan gaskiyar zan fa'da ina son ka. Amma na sani ban zo maka a yadda kake fatan matarka ta zo maka ba. Na yi amanna jikina bana manyan mata ba ne. Nan da shekaru goma ma ba zan yi girman Rafi'a ba. Dan haka ka aure ta kawai".
Ya zabura ya ce "Kin san me kike fa'da kuwa Asiya?"
Idona ya sake cika da hawaye na ce "Na sani mana, kuma har cikin zuciyata nake nufin hakan"
Ya sake ni ya na girgiza kai ya na fa'din bana sonta, bana burin na aure ta, ko ina da halin k'ara auren ma kamammiya nake so wacce bata san namiji ba sai a kaina tamkar yadda na same ki".
Maimakon na ji da'di sai na sake shiga rud'u.
Da rawar murya na ce "ka tabbatar ba budurwa ba ce? Tijjani ba iya abin da na ga ni ya gitta a tsakaninka da ita ba ke nan?"
Cikin ido ya kalle ni da dukkanin gaskiyar sa ya ce "Na rantse da Ubangiji ban sake yin zina ba tun sadda aka yi mini bulalar haddi. Amma kuma duk macen da bata san namiji ba ai ba zata dinga shige masa ba. Ba ni na je inda take ba, ita ta kawo kanta. Ko da ina son ta zauna a jikina ai sai ta amince, kin ga ni kuma ba dole na yi mata da son ranta ta zauna, na tabbatar ba ni ka'dai take yiwa hakan ba, ba ni ka'dai take sakarwa ba. Dan haka ina cikin nutsuwata bazan auri shasha ballagaza ba".
Y'anmata kalubalenku abin Bulkachuwa ya fa'da shine gaskiyar magana, saurayin nan da kike amince yake ta'ba ki ba zai aure ki ba, sai tsananin rabo. Idan rabon auren ya rantse kuwa har ki tsufa a hannunsa ba zaki fita daga zargi da wula'kancinsa ba.
Ba shakka wayewar da ta sanya kika bar shi yake lalube ki, to shifa a ballagaza wacce ta saba cudanya da maza daban daban yake miki kallo.
Ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali ya yi wanka.
Na daskare a zaune, wato duk tantirancin namiji shi kamila yake so.
Duk yadda zaki sadaukar masa da komai da sunan soyayya shi fa a zuciyarsa ba haka ba ne.
A yau na k'ara fahimtar darasin rayuwa. Na kuma k'ara gode wa Allah da na tsallake sirad'in yanmatanci lafiya.
Na kalle shi cikin tu'ajjibi na ce "To ka sani Wallahi bazan zauna a cikin gidan nan ba. Matu'kar kana son kwanciyar hankali da walwala to kuwa bana son gidan, ba kuma zan zauna a cikinsa ba."
A rikice ya ce "Asiya kin san dai da yadda aka biya ku'din rabin shekara yanzu wata guda tal muka yi, ta ina zan fara neman wani gidan?"
Ido cikin ido na ce "koma ta ina ne, na baka nan da sati if not Bilhiillazi bazan ha'kura ba. Sai dai ka nemi ni ka rasa shike nan sai ta tattaro ta maye maka gurbina."
Ya yi muk'us ya kasa zaburo mini.
Ya nisa ya ce "Haba little nan da sati me zan yi na samo ku'di? Kin san dai ba dawo mini da kudin zasu yi ba, bare na kama wani".
Na ce "Sai na baka aro, ka karbi zobena ko dan kunne ka siyar, sai ka biya ni idan ka samu hali".
Ban san ya aka yi ba kawai ya fara nuna ni da yatsansa cikin sababi yana fa'din "Nafi karfin ki kama gida na zauna a ciki Asiya. Ba zan yi wannan lalacewar ba, har abada da ikon Allah."
Na kafe shi da ido tsawon lokaci har ya fara kame kame. Na nisa na ce "Tijjani ni kake yiwa wannnan shouting din?".
Na girgiza kai na ce "Ba laifin ka ba ne. Laifina ne da na yarda da afuwar da Malam ya yi maka ba tare da na bayyana tozarta ni da ka yi ba. Afuwar da aka tilasta ni na yi maka ne ya baka kuzarin yi mini sababi irin haka ko?
To Wallahi bazan zauna a gidan nan ba. Komai za'a yi da ni kuwa".
Na mik'e na bar shi, ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye shi. Domin ya ga na koma Yabin Marina marar sassauci.
Ban jima da shiga d'akin ba sai ga shi ya biyo ni jikinsa a sanyaye. Ya zauna kusa da ni ya tausasa harshe ya ce "Ke little ba ki fahimce ni ba ne. Ki yi hakuri, zamu tashi, amma pls ba nan da sati daya ba dan Allah."
Na ce "To".
Ai kuwa nan da nan ya hau fa'din "Na rok'e ki fa Little. Ban son irin wannan to din na ki".
Na share shi. Ya dinga jaye-jayen magana amma ban tanka masa ba.
Sai kuma ya bani tausayi yadda ya yi shiru ya rasa abin yi.
A zuciyata sai hango girman gatan da Ubangiji ya yiwa mazaje nake yi. Domin duk girman laifin da zasu yi wa mace sai Ubangiji ya sanya hakuri da sassauci had'i da rauni a zukatan mataye. Nan da nan mace zata yafe ta kuma manta musganwar miji.
Na tuna ranar da ya rufe mini gida dan kawai na je na na yi sana'ar da zan samo masa ku'din da zamu rufa asirinmu. Amma har washagari yana sababin sai na tafi gida.
Amma ni na fita unguwa na dawo na tarar yana shek'a ayarsa. Na girgiza kai domin nasan da ace ni ya ga ni a cinyar Yaya J sai ya masa dukan mutuwa tunda ba k'arfinsu daya ba. Ni kuwa zai yi wahalar gaske idan bai sallama ni ba.
Na kalle shi na ce "Na tambaye ka?"
Ya d'aga mini kai tabbacin eh.
A hankali na ce "Idan ni ka ga ni a cinyar wanin ka ya zaka ji?"
Ya ce "Wata'kila zuciyata bugawa zata yi, wata'kila kuma na had'u da mummunan hawan jinin da zai kanannad'e ni."
Na sake zuba masa ido na ce "Amma me yasa baka yi zaton nima sakamakon hakan zai iya samu na a dalilin ganin wata a jikin ka ba?"
Ya fara sosa k'eya. Da k'yar ya ce "Ban san ya aka yi hakan ta faru ba. Ni gaba'daya am upset ma".
Na girgiza kai na ce "Hmmm".
Muka yi shiru sai kuma na ce "Kuma zaka zauna da ni idan ka gan ni a irin yanayin da na gan ka?"
Ba ja in ja ya ce "Ba zan iya ba".
Na zuba masa ido ina masa kallo mai tsananin gaske.
Na kaurara murya na ce "Amma kuwa son zuciyar ka azimin ne Tijjani."
Bai yi inkari ba. Bai ce komai ba, na kuma tabbatar da dukkan zuciyarsa ya bani amsar.
Kamar daga sama sai na ji ya ce "Mace daraja ne da ita sai wacce ta wula'kanta kanta. Duk matar auren da zata bada k'ofar da wani namijin zai mata waya, ko doguwar gaisuwa dama ai ba kamammiya ba ce. Ba kuma yadda za'a yi mijinta ya gasgata ta. Bare kuma a ce har ya ga ni da idanuwansa, tabbas ba zai zauna da ita ba, ko kuma idan ya ri'ke ta din ma bisa wani dalilin to fa har abada ba zata ji dadinsa ba."
Na sassauta na ce "Amma shi namiji idan yana sharholiyarsa ko da kuwa a cikin gidan aurensa ne dole ne matar ta yi hakuri ta zauna da shi ko?"
Ya kasa amsa mini.
Na zarce da ce wa "Ana rudarku da cewa duk abin da namiji ya yi ado ne, na mace ne kaico. To ka saurare ni da kyau abin da zan fa'da ka sani sai dai zan sake yi maka matashiya ne na kuma kafa maka hujja tunda yanzu ka sanya an tursasa ni na yafe maka.
Laifin namiji baligi da na mace baliga a banagaren barna duk daya ne a fuskar addini tunda duk hukunci iri d'aya Ubangiji ya zartar.
Al'amari irin wannan kuma bashi ne in ji Annabin Rahma. Idan mutum ya bata y'ar wani, shima za'a bata tasa. Idan ka yi da matar wani, kai ma za'a yi da taka.!
Na kaurara murya na ce "Na yarda baka yi zina ba Tijjani. Amma kana kusantar ta. Kana bin hanyar da ta bi. Ka sani kuma Allah da kansa ce wa ya yi kada mu kusance ta, ba wai kada a aika ta ba. Ina ro'kon ka, ka daina kusantar ta bare tsautsayi ya sanya ka fa'da yin ta da auren ka. Ina jin tsoro da zullumin kada na fara haihuwa a b'ata mini yara. Ina cikin fargaba kada laifin ka ya jefa ni cikin had'arin a lalata ni da aurena".
Ya zabura ya ce "To y'ar sarkin mugun fata da jawo bak'in alkaba'i."
Na kalle shi na ga ya shiga rud'u a dalilin furucina sosai. Kishinsa ya bani mamaki ainun.
Ban ji d'ar ba na ce "Gaskiya na fa'da maka, wacce Annabi ne ya fad'a tun gabannin kakaninmu su iso duniyar.
Bayan haka kuma ina son ka sani laifin da ka yi tabbas na ha'kura. Amma ina tabbatar maka idan na sake kama ka da irin wannan laifin to fa ka sani ka kuma ri'ke a zuciyar ka ba zan sake zama da kai ba Wallahi".
Ya matso kusa da ni ya rungume ni sosai yana fa'din "Da ikon Ubangiji bazan sake ba Asiya. Ki taya ni addu'a. Ina kuma ro'kon ki sake hakuri, ki shafe wannan al'amarin a zuciyar ki. Wallahi summa Tallahi iya abin da ya faru ke nan, kuma a wannan ranar na ta'ba yin hakan, kada shaidan ya rinjayar miki ce war na saba yi din ne.
Na kuma fahimci Ubangiji ya so ni da alheri ne shi yasa ma asirina ya tonu."
Na saki ajiyar zuciya mai nauyi na ce "Shike nan Allah ya yafe mana gaba'daya."
Ya sake ri'ke ni sosai yana fa'din "Na gode sosai, Allah ya sanya ki cikin bayinsa da yake kar'ba daga gare su."
Hawayen da ban san dalilinsa ba ya dinga zuba mini.
A hankali na ce "Ameen".
Shike nan muka rufe maganar. A ranar ma mutum uku suka zo lalle amma hakuri na basu da gabatar da uzzirin ban warware ba. Domin gaba'daya na rasa karfin zuciyata. Rauni mai yawa nake jin yana bina. Sannan wata irin karaya da al'amarin Tijjani ya haifar mini da gajiya da kasala masu nauyi a zuciyata wanda gangar jikin ta rasa k'arfi da kuzari.
Bai ce komai ba. Amma jikinsa shima ya mutu domin ya fahimci k'arfin halin da nake yi iya gangar jikina ne kawai.
Da daddare ya ri'ke ni, ya dinga rarrashi, da ban baki irin wanda sai masanin falsafa ne zai dinga harhada kalaman masu nauyi a mizanin masalaha.
Na amsa da ce wa "Na ha'kura da gaske."
Ya ce "To me yasa ba zaki y lalle ba Asiya? Na sani kuma ke ma kin sani, rufin asiri ne mai yawa sana'ar taki take yiwa jama'a."
Murya na rawa na ce "Zuciyata ta karye, jikina babu k'wari."
Sai kuma na ke ce da kuka fiye da wadda na yi a gabansu Malam.
Ya kasa ce wa komai tsawon lokaci mai yawa ina kukan, shi kuma yana shafata tamkar jinjira.
Na jima ina kuka bai hana ni ba. Har sai da kukan ya tsaya cak dan kansa. Na koma ina ajiyar zuciya mai d'auke da shesshek'a.
Ya sassauta murya ya ce "Kin yi kuka Asiya da ikon Ubangiji ba zaki sake kuka akan irin wannan al'amarin ba. Ki yi ha'kuri, wannan rufin asirin da kika yi mini, ni ka'dai nasan yadda na sake jin ki a raina. Ni ka'dai nasan yadda girman ki da nauyin ki suka yi mini rubdugu. Ke yarinya ce k'arama amma hankalin ki na manya ne. Kin yi k'ank'anta kin tsunduma cikin irin wannan bak'in-cikin. Ina ro'kon Ubangiji ya sanya wannan ne kukanki na karshe akan wannan matsalar a dukkan rayuwarmu gaba'daya".
Na amsa da"Ameen" a hankali.
Murya babu amo na ce "Bana son wannan gidan, ba zan yi farin-ciki a cikinsa ba. Ka samo mini wani ko daki daya ne zan zauna".
A hankali ya ce "Da ikon Allah zan samo miki, amma ki d'aure zuwa lokaci ka'dan kin ji".
Na ce "To shike nan".
Ya dinga fa'din Na gode sosai my little. Allah ya bani dama da zan jiyar da ke da'di mai yawa".
Na ce ni "Ka tsare mini mutuncina da naka da kuma soyayya da tattali nake so fiye da komai".
Ya ce "zan miki Asiya, zan yi kokarin kiyaye ko wacce irin BAK'AR TA'ADAR da zata sanya ki kuka. Yanzu yaushe zaki fara yin k'unshin dan na tabbatar kin huce kin kuma yafe mini?"
Na shagwaba na ce "Sai ka yi al'kawarin ba zaka dinga yi mini sababi akan k'aramin abu ba. Bana son shouting".
Ya numfasa ya ce "Zan dinga k'ok'arin ina yin fa'dan a hankali. Amma bazan yi al'kawari ba, kin san wani lokacin ha'kurinmu k'wace wa yake yi, abin da zaki fahimta shine sab'awa a zamantakewar aure ba k'iyayya ba ce, matu'kar kuskure ne irin na zaman yau da kullum ko kuma sab'anin ra'ayi".
Na ce "Tom shike nan jibi zan fara yi In sha Allah"
Ya tsananta rik'on da ya yi mini yana fa'din"Thank you my little girl".
Daga hakan kuma ya shiga bai baye ni da zafaffar soyayya mai goge dukkan tsatsar zuciya.
Washagari muka yini cikin nutsuwa da walwala mai yawa. Tun safe kuma na yi status da cewar gobe idan Allah ya kai mu zan fara k'unshi.
Shike nan na ha'kurkurtar da zuciyata na manta komai.
Na rungumi mijina da sana'a ta. Illah iyaka na yanke mua'amala da Rafi'a. Mahaifiyarta kuwa ban fasa gaishe ta ba, ban fasa mutuntata ba. Illah iyaka shiga ne bana yi. Ita ma kuma Rafi'a din ta daina shigo mini.
Wata biyu da faruwar hakan na fara wani irin zazzabi mai zafin gaske. Domin kwana nake yi mutsutsukun ciwon jiki. Gaba'daya ji nake tamkar ana kwankwatsa mini kasusuwan jikina. Ga bana iya cin abinci.
Haka nake kwana ina yini cikin wannan halin. Sa'armu d'aya akwai kayan abinci tare da mu. Sannan yana k'ulla lallen da siyar da ruwa. Babu matsalar babu sosai a tare da mu. Kwana biyu ina ta shan maganin zazzabi da na rage rad'ad'in ciwo. Amma babu sau'ki kullum gaba ciwo yake yi.
Hakan ya sanya shi fita ya yi buga bugarsa ya samo ku'di ya ha'da da wanda muke da shi, ya kai ni asibiti.
Yini muka yi domin sai da aka k'ara mini ruwa. Aka yi mini gwaje gwaje.
Da yamma aka sallame mu bayan sun tabbatar ina da ciki na wata daya har da sati biyu.
Duk yadda nake jin rashin kwarin jiki amma sosai na yi murna. Ni da Tijjani ban san wanda yafi murna da zumudi ba.
Muna isa gida na dauki waya na k'ira layin Gwaggo.
Tana dauka ta ce "Yabi ya jikin dai?"
Da azarbabi na ce "Hmmm Gwaggo ashe duk wannan wahalar da murkususun da nake yi ciki ne da ni!"
Ta yi shiru, sai kuma ta ce "Ni kika kira ki fa'da wa hakan Yabi? Wacce irin marar kunya ce ke haka?"
Na yi sakare domin ni ban ga wani laifin ba. Ita ce uwata bani da wacce ta fita a halin yanzu. Ita ce mafi kusa na tattauna dukkan farin-cikina da ita. Zan yi kokarin na boye fa'da mata damuwar da nake ciki domin na yi amanna damuwata zata tsayar mata da dukkan farin-cikinta ne.
Na sanyaya murya na ce "Gwaggo ki yi ha'kuri. Ina cikin murna ne. Kin san kwanaki a gidan nan aka fa'da mini ce wa Tijjani ya gama zubar da yaransa a titi ni bazan haihu ba. Sannan kuma ke da bakinki kika ce sai na haihu da ki zo ki ga muhallina".
Ta sassauta ta ce "To ba sai ki bari na fahimta ba, ko na ji a bakin yayarku ko kuma Nazira".
Na ce "To sake yin hakuri Gwaggo ai yanzu na fahimta. Idan zan yi ta biyu, bazan fa'da miki ba. Sai dai kawai a ce miki Yabi ta haihu"
Ta ja tsaki ta ce "Allah dai ya baki lafiya" tare da kashe wayarta.
Tijjani da yake gefe yana ta faman murmushi ya ce "Burinmu ya cika.
Yanzu fa'da mini sunan nawa?"
Na yi dariya na ce "Ai sai na haihu".
Ya girgiza kai ya ce "Kin ce da zarar kin samu ciki zaki fa'da mini fa".
Na ce "Haka ne".
Ya ce "To fa'da mini na ji".
Na murmusa ka'dan na ce "Abbanta".
Ya kwashe da dariya ya ce "Wanne irin suna ne wannan? Duk yadda kika kwadaita mini zakuwar samuwar cikin a iya wannan sunan zan k'are?
Abbanta kuma. Wace ce?"
Na jingina a jikin kujerar na ce "Bebin mana."
Ya sake fa'dada dariyarsa ya ce "To idan namiji ne fa?"
Na ce "Ai kuwa sunan da zan fa'da maka mai wuyar samu ne indai namiji na haifo tunda na fa'da maka mai kama da kai nake so".
Dadi ya kama shi ya ce "Allah ka kula mini da Asiya. Ka taya ni son ta, ka shiga dukkan kasafinta. Duk al'amarin da zai dunfaro ta, Ubangiji kada ka bar ta da iyawar ta.
Na ce "Ameen" a gajiye domin wai maganar da na yi har na gaji na fara haki.
Haka nake kwana da yini babu lafiya. Duk dare bama barci kwana muke muna fama. Domin gaba'daya ni dai babu sau'ki. Kwana nake magogo. Haka kuma Tijjani baya runtsawa. Tausa yake yi mini, da fifita idan babu wuta. Tin a lokacin muka fahimci zama iyaye ba karamin al'amari ba ne. Duk yadda na zaku na samu ciki sai da na fara sare wa. Murnata ta fara koma wa ciki dan tsananin wahalar da nake ciki.
Al'amura suka fara yi mana tsauri a dalilin ku'di ya fara yanke mana.
Haka da safe idan ya tallafa mini na yi wanka, ya shafe mini jiki da man zafi zai fita ya dan yawata. Idan an yi sa'a ya samu aiki ya samo ku'di, zai siyo mini 'dan abin kwadayi. Watarana kuma hakan zai dawo.
Baya kuma nisan kiwo, ko ya fita hankalinsa na kai na.
Sai na samu sau'ki, sai kuma jikin ya sake rikice wa.
Na fara gazawa. Rannan Baban Marina da ya zo duba ni, ya ga yadda na koma gaba'daya na yi yaushi.
Ya bashi umarnin ya kai ni gida, ko shima ya d'an huta.
Bai musa ba kuwa washagari da hantsi ya dauke ni da jakar kayana ya kai ni gida. Har da siya mini su maltina da madara da indomi da zan dan yi kwanaki ina ci. Wanda na tabbatar ya ha'da da bashi.
Da k'yar na shiga muka gaisa da Dada wacce bayyana farincikin da ta yi a dalilin samuwar cikin bata lokaci ne.
Ya kira Ikilima ta ri'ke ni zuwa cikin gida. Na sani kuma dan ya mutunta iyayenmu ne ya sanya bai ri'ke ni da kansa ba.
Yadda Tijjani ya ha'do ni da shirgi da maganganuwana. Sai ka rantse har cikin zuciyarsa yake nufin na zo na yi goyon ciki a gida.
Kwana na biyu a gida na fara samun sau'ki tamkar a gidana ciwon yake. Domin ina barci, da safe kuma ina shan koko na ci dumame.
Sannan Gwaggo da kanta take daddana mini jikina. Har gasa mini jiki take yi da tawul. Ga shi duk abubuwan da nake son ci na gargajiya ina samu.
Kwatsam ranar da na yi kwana uku sai ga shi ya ce shi ya gaji da rashina sai dai mu koma gida.
Na tubure akan sai na ji k'warin jikina.
Shima ya kafe. Kuma wai ni ce zan ce ina son komawa gidana.
Nan da nan na rantse akan bazan fa'da ba.
Ya jijjiga kai ya ce "Shike nan tunda babu taimako da fahimta a tsakaninmu. Ni zan fa'da wa Baban akan na gaji ina son ki koma dakinki. Dama kunya da nauyinsa ne suka sanya na kawo ki."
Da yamma ya dawo akan na taimake shi mu koma gida. Ya kasa fa'dawa Baban zai tafi da ni. Na ce "Ni dai na fi son zaman nan".
Nan da nan ya tunzura ya ce "Saboda bani da ku'di ko Asiya?"
Na kalle shi a razane. Ya ce "Haka ne mana. Inba hakan ba wace ce ta taba zuwa gida dan bata da lafiya a gidan nan?"
Na ce "Ubaida bata dawo ba?"
Da hanzari ya ce "Amma duk jinyar da ta yi da ciki ai bata dawo ba. Sai da ta haihu. Ke kuwa ai ba haihuwa kika yi ba. Idan ba gazawa ta aka ga ni ba. Mene ne zai sa ayi mini wannan umarnin?"
Na sake kallonsa cikin tu'ajjibi na ce "Baban Marina kake fa'dawa hakan ko kuwa wa?"
A tunzure ya ce "Asiya na ke fa'dawa saboda ita ce zata ce masa ta samu sau'ki."
Idona ya ciko da hawayen takaici na ce "To".
Daga hakan na k'ulle bakina ban ce masa komai ba.
Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi. Ya ce "Ya muke ciki?"
Ko kallonsa ban yi ba.
Ya gama zamansa ban sake kula shi ba.
Da daddare ma ya dawo, ban yarda na kula shi ba. Domin idan akwai abin da yake b'ata mini rai da shi idan muna magana ya dinga sako babun shi ne. Na kuma lura idan ban taka masa birki ba, ba wanye wa k'alau zamu yi ba. Tunda yana nema ya mayar da ita sara.
Washagari sassafe sai ga Babah ta Bulkachuwa ta dira a gidan. Ina daga daki na ji suna gaisawa da Baba. Ya ce " Hauwa kamar ba kwanaki ka'dan da suka shud'e kika zo duba y'arki ba. Me ya sake dawo da ke kuma yanzu? Mata kuna da son sabgar yawo.
Ta ce "Ba hakan ba ne Yaya. Shi ne ya mini waya wai jikin Yabi ya yi tsananin da ka ce ya dawo da ita gida. Sai ya ro'ki na zo na zauna masa da ita. Ni kaina hankalina ba kwanciya zai yi ba idan ba zuwa na yi na ganta ba."
Baba ya numfasa ya ce "Ai shi Tijjani bai gamsu zan kular masa da iyali dan karan kansa ba, sai ya zargi na yi masa fin k'arfi saboda y'ata ce?".
Ta diriri ce ta ce "Haba Yaya ni Wallahi har kasa na ji babu da'di."
Ya ce "To ki ji mana. Ban da dai ke ma kin banbanta ta ya ya zaki zo ki ce mini "Zaki dauki matar Tijjani a gaba na?"
69&70
Ta shiga ba shi ha'kuri, shi kuma ya dinga yi mata sababi. Yana fa'din "Da kam nan da kwana biyu na yanke zata koma zan ha'da ta Mamarsu ta je ta zauna da ita ko na sati ne kafin jikinta ya yi k'wari. Amma yanzu na fasa ba zata koma ba. Ki fa'da masa na ri'ke ta, sai ta haihu tunda ba shi da kunya, ya banbanta, ya nuna uwarsa ce ka'dai zata yi wa iyalinsa hidima.
Ai kuwa Babah ta dinga ba shi hakuri, ta lallaba ta zame kanta ta bar Tijjani tsundum cikin maganar.
Ta shigo d'aki ta duba ni. Ta bani leda mai d'auke da soyayyun kaji. Da kuma soyayyar awara da ta sha yaji mai da'di fal leda (K'ara'i).
Na fahimci duk yadda Babah bata shiga al'amarin Bulkachuwa Amma bata dauki abin da ya shafe ni da sau'ki ba. Samuwar cikin jikina kuwa sai na fahimci k'arfin soyayyar da take yi masa. Domin farin cikin da take ciki duk wanda ya rab'e ta sai ya gane hakan. Kusan kullum sai na amsa k'iran abokan arzik'inta. Suna mini sannu da jiki. Daga samuwar cikin zuwa yanzu na manta adadin da ta zo duba ni.
A dakin Gwaggo ta shigo ta same ta suka hau cakar juna, tunda k'anwar miji ce. Gwaggo ta ce "Oh ni Asma'u ina ganin kananci a wajen Hauwa. Kina zazzame wa akan sha'anin yara. Amma tunda kika ji zaki yi jika sai b'are b'are kike yi da sintiri a hanya tamkar a kanki za'a fara yin jika".
Ta ce "kya yi kya gama. Y'ay'ana nawa ne suka haihu? Yanzu ina ce duk sa'anin aurenta sun haihu dama wandanda suka riga ta auren. Duk ba jikokina ba ne?"
Gwaggo ta ce "wace ni na ce ba jikokin ki ba ne. Gani na yi Ummi yar hutun ki ma baki ta'ba zuwa dubiya idan tana laulayi ba, sai idan haihuwa ta yi. Amma Yabi kin zo ganin ta, sau ba adadi sabo..".
Ai bata jira saboda me Gwaggo zata ce ba. Ta sunkuci jakarta ta fice tana wani irin murmushin farin-ciki. Tare da ce wa "sai ki yi da wata ai. Ke da ake ganin shirunki da hak'urinki, nan kuwa ba'kinki fal zan ce da bita da k'ulli ne".
Washagari ta shiga mota ta juya ba tare da ta ce wa Tijjani komai ba.
Ai kuwa kwanaki biyu ya dinga wata irin zarya a cikin gidanmu ta ban mamaki. Baban Marina ya share shi.
Rannan da daddare ya murje kunyar sa ya ce "Baba gobe zan zo na d'auki Asiya."
Baban ya gyara zama ya ce "Ai haba?"
Ya yi wani irin tare da sunkuyar da kansa k'asa ya kasa amsawa.
Baba ya numfasa ya ce "Ai k'ure rashin kunyar ka zan yi Tijjani. Wai kai magidanci kada a ga gazawar ka. Shine ka turo mini uwarka dan ka nuna mini ita ce zata maka hidima kai tsaye ko?"
Ya yi k'asa da kansa tare da ce wa "Ba haka ba ne Baba".
Ya ce "Ya ya ne? Fada mini ina jin ka".
Tsawon lokaci bai tanka ba.
Baban ya ga ji da shirun sa ya ce "To uwar taka ma da soyayyarka ta rude ta, ta zo zata mini rashin kunya na fatattake ta, bare kuma kai karamin alhaki. Ai tunda ka nuna mini da wajena da wajen Hauwa da banbanci, ni kuma zan nuna maka da kai da Salisu d'aya ne a waje na. Bazan baka Asiya ba sai ta haihu ta yi arba'in".
Ya kalli Baban ya ce "Idan na baka hakuri fa Baba, zaka ha'kura ka bani ita?"
Kai-tsaye ya ce "Bazan hakura ba."
Tijjani ya ce "To ka yi ha'kurin kuskuren da na yi".
Ya ce "To na ha'kura Allah ya yafe mana. Ku daina banbanta iyaye. Dukkanmu d'aya ne."
Ya ce "To Baba zan kiyaye."
Suka yi shiru.
Can Tijjani ya ce "Baba ko zaka yi hakuri ka janye zancen sai ta haihu, nan gaba a k'ara wata biyar fa, kafin ma ta haihun".
Ya ce "To na ha'kura Tijjani. Allah ya yi muku albarka. Allah ya k'ara ha'da zuciyoyinku. Ya kuma hore maka ikon kula da iyalinka". Ya amw.sa da "Ameen Baba".
Washagari da yamma ya zo muka tafi, ni kuma sai fishi nake yi.
Muna isa gida ya rungume ni sosai yana ta sakin ajiyar zuciya.
Ni kuma na sha mur, na kawar da fuskata gefe guda.
Ya ce "Tunda mun dawo ai sai ki huce. Yau kwana uku ko hudu kina mini fishi. Gidan fa gaba'daya zafi ya yi mini da ba kya nan."
Nan ma ban kula shi ba.
Sai da ya dinga rarrashi da ban baki sannan na bu'de baki na ce "Ai dan ka ga na damu da kai ne shi ne kake musguna mini ta hanyar ce wa dan baka da abin duniya ne nake yi maka wani abu. Tunda haka zaka dinga yi mini kawai ka k'yale ni, kowa ya yi harkarsa".
Ya dinga fa'din "ki yi ha'kuri na daina, dan Allah ki huce haka nan". Ya shafa cikina da ya fara tasa wa. Ya ce "Ya bebinmu?"
Kawai sai kunya ta kama ni na ture hannunsa na rufe fuskata da hannuwana.
Ya sani a jikinsa ya ce "Asiya ina son ki, ina son kasance wa tare da ke muddin rai. Jikina ya yi sanyi na kasa ce wa komai. Amma kalaman sun yi matu'kar tasiri a zuciya da gangar jikina gaba'daya.
Ban samu kaina ba sai da cikin ya shiga wata biyar. A lokacin kuma ya fito sosai tamkar ba cikin fari ba.
A kan dole nake yin k'unshin, amma sai muka tak'aita iya mutum uku kawai nake yiwa a rana.
Amma ina yiwa masu son bak'i da tunda shi babu durk'ushe sosai. Sannan ina yin kitso. Ana kuma siyan lalle.
Dai-dai lokacin kuma Tijjani ya fara zuwa Bauchi cikin kasuwar Muda lawal. Ya samu Alhaji Auta aminin mahaifinsa tare ma suke kasuwancin. Kawai dai da tafiyar ta yi nisa sai bai cigaba da bibiyar iyalin marigayin ba. Amma hatta katon fiilin da ya fito a gadon Tijjani a jere suka siye su. A yanzu hakan ma shima nasan filin yana nan. Wajen ya rayu, ya yi daraja ainun.
Cikin cire girman kai Tijjani ya yi masa bayanin yana son ya zama cikin yaran shagon ko da ciccire ribabbun kayan miya ne. Domin ya fahimci idan Yabi ta haihu ba k'aramin nauyi ne zai sake hawa kansa ba. Ga shi kuma, kullum rayuwar k'ara tsananta take yi ga talaka.
Da sakin fuska ya karb'e shi ya kuma babshi wani bangaren da zai dinga kula da shi.
Dan haka sai Tijjani ya zama sai bayan kwana uku yake zuwa Toro. Duk sadda zai je kuma zai je da kayan miya, da kayan abinci.
Sannu a hankali yake bin kasuwar yana kuma yin biyayya.
Amma ba'a dauki lokaci mai yawa ba sai ya fahimci yadda *BAK'AR TA'ADAR* hassada ta yi katutu a zuciyar jama'a. Mafi yawa yaran shagon sun ha'de masa a dalilin suna ganin maigidan nasu ya daukake shi. Sannan ba ya yarda a yi aikin ha'inci da shi. Domin mafi yawa suna satar kayan su siyar ba tare da sum saka ku'din a shagon ba. Zuwansa sai k'udaden shiga suka karu dan haka Alhaji yake bud'a masa yake yi masa Ihisani.
A yanzu da ya wadata su da abinci sai ya koma siyan kayan haihuwa. Duk sadda zai tafi sai ya sayi riguna unisex guda biyu, baya damuwa ko da iri daya ne matu'kar dai kala ta banbanta su. Da ya tara riguna da yawa sai ya koma sayan ragowan kaya.
Yau ma Sai da ya biya ya siyi setin robar wanka mai sau'kin ku'di. Ya kalli rukunin masu tsada mother care. Ya ji sun ba shi sha'awa. A fili ya ce "Allah ka hore mini wata haihuwar na siya wa Asiya irin wadannan".
Ya kara da setin mai na Nycil. Ya tafi ya hau mota. Bayan ya siya mata tarkacen su fruits dangin mangwaro da su abarba.
Sannu a hankali muke rayuwa, har cikina ya shiga watan haihuwa, zuwa lokacin kuma ya canja mini gidan, amma shima na rabin shekara ya kama tunda ya fara tunanin mu koma Bauchi da zama, amma ya ce sai na haihu tukun.
Kowa ya kalle ni sai ya yi maganr girman cikina. Har rinjaya ta yake yi.
Idan ya tafi Bauchi sai Iklima ta dawo gidana. Sai ya dawo sannan ta tafi.
Cikin sa'a haihuwa ta kama ni yana gari, kuma da daddare. Dan haka ya samo abin hawa, muka tafi, sai da aka karb'e ni, aka bani gado. Sannan ya tafi gida ya fa'da. Take Baban Marina ya ha'do shi da Mama akan ta zauna da ni.
Har asuba ban haihu ba ina shan azabar duniya. Na yiwa Gwaggo addu'a yafi cikin carbi. Sai da na gama galabaita sannan aka fahimci bazan iya haihuwa da kaina ba.
Nan da nan aka shirya ni zuwa d'akin tiyata. Amma muna shiga ciwo ya sake tasowa fiye da ko wanne. Na dinga kururuwa ina salati, tare da fa'din a ce wa "Gwaggo ta yafe mini."
Likitocin da zasu yi mini aikin suka rufu a kaina. Ai kuwa sai ga haihuwa gadan gadan. Suka taimaka wajen zaro jinjiri. Yana fito wa ya xika dakin da kuka mai tsananin gaske tamkar gyare. Na fara maida numfashin wahala da gajiya. Ai sai wani sabon ciwon ya taso, gaba'daya na rasa karfina. Take kuma likitocin suka tabbatar ba mabiya ce kawai a cikin ba, akwai sauran halitta.
Na fara kuka domin na tabbatar bazan iya sake haihuwa a yanzu ba. Ina kuka ina fa'din "Summa sabila yassara".
Daga haka ciwo ya tsananta, na birkice, ga shi na kasa nishi mai tsanani. Da taimakon Allah da na likitocin na biyun ya iso duniya bayan sun k'ara ni. Wahala kan wahala na yi kafin na rabu da cikin da na kwashe watanni tara ina tiriri da shi cikin kalubale kashi kashi.
Ban gama wartsake waccar azabar ba, aka shiga yi mini dinki tamkar k'warya. Duk yadda aka yi mini allura kashe rad'ad'i sai da na dinga jin ciwon har cikin kaina.
Sai da suka gyaramu sannan aka karbo kayan Bebi a wajen Mama sannan aka fito da mu.
Sai hamdala nake yi a zuciyata. Ina sake girmama sha'anin Ubangiji. Ba a taba ce mini tagwaye ne a cikina ba.
Na tarar y'anuwa sun zo asibitin da yawa.
Na dan ji da'di domin kaf y'ay'an Babanmu da aka aurar da su. Ba wacce ban ga ni ba, har Ubaida kuwa. Ko Yaya Indo da bata sake taka gidana tun ranar da aka kai ni ba, na ganta a wajen. Idona ya cika da k'walla ina ayyana duk yadda shaidan yake shiga cikin al'amarin zumuncin yau, jini yana da tasiri k'warai da gaske.
Ina ta waige waige domin zuciyata so take ta ga jariraina, so take kuma ta ga uban y'ay'an.
Amma ban gansu ba gaba'daya.
Na ha'diye na yi shiru na cigaba da kallonsu d'aya bayan d'aya.
Tare da amsa sannun da suke ta faman yi mini.
Na jima kafin barci ya sure ni. Na dai farka na tarar da Babah ta Bulkachuwa zaune a gefena tare da Mama.
Sannan Inna da Yaya Ummi suna ri'ke da jariran da aka nad'e su da zani iri d'aya.
Dada na gefe tana mulmular goro a bakinta, tana kuma jan tasbaha.
Da suka ga na farka, suka hau fa'din "sannu, sannu Yabi".
Dai-dai lokacin kuma ruwan da ake k'ara mini ya k'are.
Wata jamiar kiwon lafiya ta shigo a daidai ta cire mini, tana mini sannu.
Da walwala ta ce "Mrs Bulkachuwa ina taya ki murnan samun wad'annan kyawawan jariran. Allah ya rayasu ya baki lafiya".
Na yi shiru su kuma ahalina suka amsa da fa'din "Ameen mun gode".
Ta kalli Mama ta ce "Zo ki ri'ke ta, ki taimaka mini mu zaunar da ita.
Yaranta suna bu'katar nono".
Da dabara suka zaunar da ni. Sai da ta tambayi na ji da'din zaman ko na takura a gyara ni?"
A hankali na ce "Ya yi".
Dada tana ganin malamar asibitin ta karbi yaron hannun Inna. Ta zabura ta ce "Dakata dafta".
Kowa ya mayar da hankalinsa kan Dada da ta jawo ledar da ta zo da ita, ta fito da k'ok'o tare da gorar mirinda da kuma wani ruwan maganin a wata gorar daban.
Ta yun'kura da k'yar tana dunduk'e ta nufo gadon.
Ta kalli jami'ar kiwon lafiyar da take shirin kwantar da jaririri a jikina ta ce "gafara ka'dan".
Cike da girmamawa ta kauce tana ce wa "Sannu tare da mamakin me zata yi.
Sai dai su yan d'akin sun san me zata yi.
Ta saka k'ok'o a cinyata, ta d'aga rigata. Duk da y'an k'ananun nono gare ni, amma tunda cikina ya fara girma suka ciko. Yau kuwa da ruwan nono ya zo sai suka yi girma suka tsaya k'yam tamkar kwakwa.
Karon farko da aka bu'de mini nono a bainar jama'a ban kuma ji nauyi mai yawa ba.
Ta daidaita ta dinga zuba ruwan robar ta kuma saka hannu tana wanke mini su.
Sai kuma ta fara k'ok'arin matsesu tana fa'din sai an cire mataccen nonon da yake lalata jinjirai kafin a basu su sha. Dukkansu babu wanda ya yi inkarin hakan domin suma akan wannan Ta'adar suke.
Nan da nan malamar asibitin ta ce "kin wanke Dada ya isa haka".
Ta d'ago ta ce "Yarinya me kike fa'da ne? Kina son ki ce wai dak'ashin za'a bari su sha?".
Cikin girmama wa ta ce "Eh Dada. Domin alfanunsa mai yawa ne a jikin jariri. Shine rigakafi na farko da Allah subhanahu wa ta'ala ya fara yiwa dan-adam da shi."
Dada ta bar komai ta kafe ta da manyan idanuwanta ta ce "To sannun ki, amma su wadannan baza su sha datti ba. Kullum a cikin yiwa Allah da ma'aiki k'arya ku ke. Allah dai ya shiryeku idan zaku shiryu".
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWIA SAIWOWIN SANYI*
AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU*
*AKWIA SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.
Ta sake rank'wafawa da nufin yin abin da ta yi niyya. Ma'aikaciyar ta ce "A a Dada daure ki yi hakuri. A yanzu Asiya ba a hannunku take ba. Tana hannun gwamnati ne da kuma hukumar lafiya. Dan haka duk abin da za'a yi mata dole zai kasance k'arkashin kulawar hukumar asibiti ne. Bijire wa hakan kuma yana iya sawa mu gurfanar da mutum gaban kuliya. Dan haka ki yi ha'kuri ki bar hukuma ta yi aikinta.
Wannan karon kam a zabure ta ce "ke yarinya kar ki mini iyashege kin ji. Dan Allah falfala da gudu ki kirawo mini hukumar mu yi arangama domin mutuwa ce ka'dai zata hana ni matse wa Yabi mataccen nono marar amfani, ba ku da kuke yiwa masu jajayen kunne bauta ba."
Ta murmusa ka'dan ganin Dada ta kufula da yawa. Ta ce "Dada abin bana b'acin rai ba ne. Ki Fahimci bayanina. A da an rayu cikin duhun kan cewar nonon farko mai kalar rawaya matacce ne kuma mai illah. A yanzu da ilimi ya cika duniya masana kimiyya sun gano d'inbin amfanin da Allah ya ajiye a nonon uwa. Mussaman na awannin farko da haihuwa. Yana rigakafin ciwon hanta, k'oda, huhu. Yana hana tasirin ciwon k'yanda da tarin fuka, da shawara. Yana k'arawa jariri kaifin k'wak'walwa, yana kuma daidaita k'asusuwansu".
Dada ta dauki salati tare da cewa "Ni Binta ina ga ni da sauraron kinaya. To da kunsan da hakan amma kuka sake k'ak'alo allaurar da ake daukar watanni ana yiwa yara babu tausayi bare imani da sunan rigakafi ce. Yanzu wanne ne gaskiyar magana kenan?"
Malamar ta yi murmushi ta ce ko wanne gaskiya ne Dada".
Ta ce "To ku ri'ke gaskiyarku, amma ni ban yarda da ita ba, bare kuma na yi muku biyayya"
Da walwala ta ce "Shike nan Dada ki ri'ke fahimtarki. Amma tunda har aka kawo Asiya asibiti to wajibi ne abi ka'idojin hukumar lafiya. Idan ba hakan ba zamu sallame ku ne. Komai ya biyo baya kuma babu ruwanmu. Kafin haka kuma, zan rubuta tirjiyar da kuka yi, idan abu marar da'di ya biyo baya ke ce da d'aukar alhakin komai. Domin na tabbatar za ki ga ni".
Nan da nan Dada ta d'auki salati tare da fashe wa da kuka ta koma gefe tana ce wa "Yau ko da wa kike tak'ama sai na yi sharia da ke tunda kika ce zan ga ni."
Ita kuwa bata damu ba, da alamu ma dariya Dadan ta bata. Domin sai guntse bakinta take yi. Ta kuma d'ora mini yaron tana nuna mini yadda zan tallafe shi a duk sadda zan shayar da su gudun kada su dinga kware wa ko su kasa samun iska.
A lokacin da yaron ya fara tsotso wani irin rad'ad'i ya ratsa ni. Na zabura ta ce "Sannu".
Na kasa amasawa, kunyar idon su Babah ya hana na yi kwarmato. A daddafe ya sha. Ta dauke shi, ta dauko d'ayan.
Ya fara sha ke nan Tijjani ya iso da kayayyaki a hannunsa. Ya ci birki ya tsaya yana kallon yadda take rurrufe ido tana cije wa ga yaro yana sha. Farin cikin Asiya ta zama uwar y'ay'ansa har biyu tashi guda yana matu'kar saka shi tsumaye.
Amma ganin Dada na kuka ya takaita masa murnar da yake ciki.
Ya ajiye kayan a gefe ya isa kusa da da ita.
Yasa hannu ya ru'ko hannunta da take share hawaye. A tausashe ya ce "Dada kukan me kike yi haka ne? Ina ce d'azu kika dinga rangwad'a murnar alherin da ya samu a cikin alhalinki na samun tagwaye?"
Cikin kuka mai yawa ta ce "Ayyah mai sunan manya ai wannan ja'irar yarinya tana neman mayar mini da murnar tawa ciki. Ba yadda ban yi ba kada ta bawa yaran nan dattin nono amma sai da ta kafe ta basu suka shanye. Idan an yi sa'a sun rayu, to tabbas zasu tashi da kukan da baya jin rarrashi ga yawan kumburin ciki, sannan mafi muni suna iya samun tawaya a hankalinsu". Ta ke ce da kuka mai tsananin gaske.
Fargaba ta shige shi ainun. A ki'dime ya ce "jariran aka yiwa sanadin raunin k'wak'walwa Dada?"
Ta kad'a masa kai tabbacin eh. Tare da ce wa "Kuma Wallahi tunda ta ce mini zan ga ni, sai na yi shari'a da ita ko da me take tak'ama kuwa. Ba zata lahanta mini tattaba kunne, sannan ta bini da mugun k'ulli na kuma ha'kura ba. Ko waye ubanta a garin Toro da kewaye sai mun je gaban gatan marar gata wato kuliya".
Ya sake ta ya isa gaban su yana leka yadda a ke bawa yaron nono. A gigice ya ce "Baiwar Allah ya zaki dage sai sun sha abin da zai zame musu illah?"
Ya fara k'ok'arin karb'e yaron.
Babah ta Bulkachuwa ta yi wani irin tari mai kama da kashedi. Nan da nan ya ankara ya fahimci gargadi ta yi masa.
Ya d'aure ya saki yaron. Ya koma gefe amma zuciyarsa ta dinga wani irin tsalle.
Dada kuma ta sake tsananta kukan tana fa'din "Duk wannan iyakacin da aka nuna mini akan y'ay'an nan baki ji ciwo ba ashe? Ba ki hana ta ci mutuncin uwarki ba, baki hana ta nakasa rayuwar y'an mala'ikun Lillahi ba. Shi ya zo zai kwatar mana yancinmu ni da su shine zaki hana shi?
Eh lallai! To ki je na barwa hukumar asibitin ke, ranar da zamu yi shari'a da su ki zame musu shaida ki kwaye wa uwarki da jikokinki baya".
Ta juya ta fice tana kuka bilhakki.
Yayin da Babah da Inna da kuma Mama suka bita da nufin lallashi da ban baki a gare ta.
D'akin ya yi saura daga mu sai Yaya Ummi.
Ya d'auki yaron ya rungume shi tsam tsam. Yana ta tofa masa addu'ar da ta zo bakinsa. Ya kalle ni ya ce "Sannu Asiya! Ubangiji ya yi miki albarka, ya baki lafiya, ya baki hakuri da kuma juriyar raino da tarbiya".
Na kalle shi ina jin wata irin soyayyarsa na kekketa ni fiye da ko wanne lokaci. Wata'kila kuma kasancewar sa uban y'ay'an da nake jin kaunarsu har a cikin b'argona yana da alak'a da sake jin ninkin soyayyar sa.
Na murmusa na masa ameen a zuciyata.
Ya mik'awa Yaya Ummi wanda yake hannunsa ya karbi d'aya yaron da ya kammala sha yanzu a hannun malamar.
Cikin nutsuwa ta kalle shi ta ce "Mr Tijjani kada Kaka ta rikita ka." Ta shiga fado masa muhimmancin fara bawa yaro nonon uwa a farkon awanninsa a duniya. Ta sake ce wa "Tunda mu musulmai ne mun yi sa'a kuma muna d'abbaka sunnar manzo. Da zarar uwa ko uba sun tauna dabino sun guntsawa yaronsu a baki bayan sun yi Bismillah. Ba abin da zai fi dace wa da lafiyarsa illah wannan nono da mutanan jiya suka tafi a fahimtar ce wa cuta ce. Babban sirrika ne da Ubangiji ya zuba a ciki".
Ya gyada kai cike da gamsuwa. Ya yi mata godiya sosai tare da bata ha'kuri akan maganganun Dada. Ta murmusa ta ce "Ai babu komai nima kafin na fito sai da muka haura da tawa kakar. Sai ana yi musu uzziri. Da zarar sun kai shekarun girma irin haka, sai an sake yin hakuri da sha'aninsu ana mayar da komai zasu ce a matsayin girma ne. Shi kuwa tsufa ba k'aramin nauyi ne da shi ba. Domin Allah da kansa sai da ya yi ta jan kunnenmu a cikin kura'aninsa mai girma akan idan iyayenmu suka kai shekarun girma kada mu fa'da musu munanan kalamai, komai zasu yi mana, kada mu ce musu uffan, balle a yi sa'insa da su".
Ya sake ce wa "Haka ne. Na gode sosai".
*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*.
Ta tattara kayanta ta fice ta bamu waje.
Ya matso ya zauna a gefen gadon da nake kai. Ya zuba mini ido tare da ce wa "Sannu little. Ban zaci zaki iya haihuwa da kanki ba. Mussaman da na ga Ubaida da Nasiba masu garin jiki sun gaza haihuwar da kansu".
A hankali na ce "Haihuwa ikon Allah ke sawa a yi ta lafiya ban da haka kam da iyayenmu basu taramu da yawa haka ba".
Ummi da take gefe ta murmusa ta ce "Yabi an je kusa da lahira an dawo."
Ya ce "Ummi ai ni da kaina na tausaya mata, haihuwar yara biyu tashi guda, sannan ki gansu manya tamkar ba tagwaye ba? Wani ikon Allah bamu yi zaton yan biyu ba ne, Ubangiji ya boye su ko sikanin din da aka yi bai nuna ba."
"Ikon Allah ya fi ga hakan ai" Yaya Ummi ta fa'da a hankali.
Ya sake kallona ya ce "Asiya kin ga yaran nan kuwa, kina ganin yadda Ubangiji ya mana kyautar da ba kowa yake yiwa irinta tashi guda ba?"
A hankali na ce "Ai ban gansu ba, ba'a bani na ga ni ba, kunya kuma ta hana ni na tambaya".
Ya yi hanzarin sake matso wa kusa da ni tare da d'ora mini yaron akan cinya a hankali. Cikin nutsuwa yake ce wa "kalle shi da kyau Asiyata. Kalli ki ga yadda suke kama da ni. Kalle shi, ki masa addu'a, ki kuma gode wa Ubangiji bisa d'inbin baiwar da ya yi mana".
Na zuba wa yaron ido. Ina son ga ne kammannin da Tijjani yake fa'da. Amma na kasa tantance wa, domin ni kam bana ga ne kammannin jarirai. Na tsananta kallonsa, ina jin wata irin nutsuwa da kaunar yaron na shigata sannu a hankali. Na saka hannu ina duba yatsun hannunsa da na tabbatar irin nawa ne.
A hankali Tijjani ya ce "Yusuf ke nan (Baban Bulkachuwa) ki masa addu'a, shi ne babban".
A fili na furta "Allah ya raya shi, ya saka shi cikin bayinsa da yake sonsu. Allah ya masa kyakkawar rayuwa. Allah ya bashi basira da azanci, ya saukaka al'amarinsa, ya kuma ba shi kyakkawan rabo a lahira".
"Ameen ameen" Tijjani yake fa'da cikin wani irin yanayi.
Da azama ya ce "Ummilolo kawo shi, shi ma ya samu tabararakin addu'ar uwa."
Ya dauke wanda ya kira da Yusuf. Yaya Ummi ta d'ora mini na hannunta ta koma gefe. Ya gyara rikon na hannunsa ya ce "Kin ga yadda suke kama da juna ko? Tagwaye ne masu kama da juna kwabo da kwabo(Identical twins)".
Na gasgata shi, domin ni kaina idan aka jere mini su bazan iya banbanta su ba a yanzu.
Na zuba masa ido tamkar yadda na yiwa d'anuwan sa. A hankali Tijjani ya ce "Muhammad Sani ne wannan(Baban Marina)."
Haka kawai na ji tausayi yaron ya shige ni. Kaunar sa ta shiga mamayata.
Cikin rauni na ce "Allah ya raya shi, ya sanya shi cikin bayinsa da yake kar'ba daga garesu. Allah ya saukaka al'amarinsa, ya kimsa masa ilimi da azancin sarrafa harshe. Ubangiji ya sa ya dace da kyakkawan rabo a lahira".
Shi da Yaya Ummi suna ta fa'din "ameen".
Ya sake kusantowa gare ni. Ya ha'demu gaba'daya ya rungume. A fili ya ce "Allah ga ahalina, ka so su, ka taya ni kula da al'amarinsu, ka tsarkake mini su. Ubangiji ka basu kariyar da ni ba zan iya basu ba. Ka zame mini jagoran wajen sauke nauyinsu da ka d'ora mini. Allah ka bawa uwarsu lafiya da juriyar raino da tarbiya. Ina ro'kon ka saukar da albarka a cikin gidanmu da rayuwarmu gaba'daya".
Ya dinga kaiwa kuncina da goshina sumba.
Jaririn da yake hannuna ya fara mutsu mutsu da k'ananun kuka tabbacin an takure shi. Da azama Tijjani ya janye daga gare ni.
Yaya Ummi ta matso da nufin d'aukar yaron. Ya ce "Ashe ba ki fita rarashin Dada ba Ummilolo? Da kika ga sun fice ai sai ke ma ki bi bayansu ki bamu waje".
Ta ce "ka gama borin kunyar ka dai".
Ya matse ya ce "To ba daukarsa zaki yi ba. Taimaka wa zaki yi ya sha. Da alamu yunwa yake ji sai tsotson hannu yake yi".
A hankali ya na ce "A a ai ya d'an sha d'azu. Zafi Wallahi!.
Cikin tausayi ya ce "Ki yi ha'kuri, zafin na d'an lokaci ne k'alilan".
Kan dole na yarda na ba shi. Shi kuwa yaro sai zuka yake yi babu jinkiri da alamu sai yafi d'an uwansa tsotso.
Ana hakan na hannunsa shi ma ya fara nasa sukur sukur din.
Ya mike ya saba shi a kafa'da, yana dan juyawa.
Daidai nan su Babah suka shigo. Ta kalle shi ta ce "Bawa Ummi shi, ka zo ka tafi. Ka zo ka yi kane kane ko kunyar iyayen pka baka ji".
Ya bada yaron ya fice ba tare da ya sake ce wa komai ba.
Kwana na yi da yini sannan aka sallame mu. Yara lafiyarsu k'alau.
Kai tsaye gida aka zarce da mu. A dakin Gwaggo muke yin jego. Hidima kan hidima Tijjani da mahaifiyarsa suke yi. Har sai da Baban Marina ya ce "Ka bi a sannu Tijjani kada ka yi bashi". Tun kafin ranar suna aka lankayawa Yusuf(Hanif). Muhammad Sani kuma (Hamim)
Har ranar suna ta zo aka yi taron sunan tagwaye cikin rufin asiri. Na yi kwalliya da leshi, da kuma kyawawan sabbin material din Umm Nihla....
Har kala biyu. Kyaunsu da sau'kinsu ya sanya Tijjani ya siya mini kala biyu. Leshi kuwa a cikin na lefena na dauka na dinka.
Fayyace irin kayan da muka samu ni da yan biyu bata lokaci ne. Domin gadajen Gwaggo duka biyu sai da suka cika da kayayyakin barka.
Babbar matsalar da ta fara damuna rashin warke wa ta. Tafiya ta a bubbude. Na je asibiti sun ware d'inkin. Suka ce na dinga kama ruwa da ruwan dumi da dan gishiri a ciki zan warke.
Sosai Gwaggo take kula da ni. mun warware mun ciko ni da yara. Na murje tamkar ba yara biyu nake shayarwa ba.
Matsala biyu ke damuna ta farko kukan yara. Domin idan dare ya fara nisa suka fara kuka, babu me yin barci a k'ofarmu. Da daya ya fara, d'ayan ma zai dauka, su taru su kidamamu. Basa dainawa sai an yi assalatu.
Dada kuwa sai fadi take yi "Ai kuka ma basu fara ba, tunda an riga an yi musu sanadin wahala. Waye zai sha mataccen nono ya share k'alau?"
Matsalar ta gaba kuma nake jin na bu'de. Ina jin yadda iska ke shigata. Nasan na karu amma ban yi zaton dinkin ba zai ha'de ni ba.
Ga shi ban fasa kama ruwa da ruwan zafi ba. Na kasa jin da'din kaina. Na kasa fa'dawa Gwaggo. Yaya Ummi na zuwa na fa'da mata. Ta ce "na sa a kawo sassake da saiwowi kalakala da ake kawo wa daga chadi."
A kunya ce na ce "Na gode.
Kwana biyu a tskani sai ga ta dawo da kayan. Da kanta ta dafa mini, ta ware mini butar da zan dinga zuba maganin.
Dan kama ruwan da na yi da ruwan maganin har na fara jin da'din jikina. Da zata tafi ta hada kan kayanta ta tafi da su. Ina son na ce ta bani koren maganin da na dafa kazar, amma na kasa a dalilin kunya ta yi mini k'awanya.
Na tuna ranar sunan Ubaida yadda su Nasiba da su Maijida suke koda kyaun kayan da suke siya daga Kano ta hannun Yaya Ummi. Na tuna sadda ta bani ina amarya na ki kar'ba.
*Masu bu'katar kayan gyara na chadi gangariya, su yi mini magana. 08032773332*
Amma da yake Yaya Ummi yar'uwa ce ta gaske sai da ta bani kayan nan duka. Kazar ma ta ce zata daho mini idan na kusa arba'in. Cikin dabara na kirgi ku'din da na samu a barka na sawa y'arta mai d'an dama a aljihunta.
A haka na kwashe sati hud'u da haihuwa. Tijjani ya fara rawar kai da son na koma gidanmu haka nan. Tunda na warware.
Idan ya fara wannan maganar shiriritar da ita nake yi.
Da safe an yiwa yara wanka suna ta barci tamkar basu ne masu kwana ido biyu suna kuka mai tsananin gaske ba. Amma da gari ya waye ba za'a sake jin motsinsu ba. Yini suke suna barci.
Ranar da muka yi kwanaki talatin ya iso daga Bauchi. Ya zaune kan sallaya a tsakar d'akin Gwaggo. Ya ci abincin da aka kawo masa. Ya kalle ni ya ce "Little ki girmama al'kawari. Ba irin cika bakin da baki yi mini ba akan idan kin haifi namiji suna na mussaman zaki saka mini. Cikin ikon Ubangiji kin haifo har biyu amma har yau ban ji sunan nawa ba. Anya kin yi daidai kuwa?"
Na dauke kai ina murmushin kunya. Tare da ce wa "gaggawa ne da kai. Ka bari sai mun koma gidanmu zan fara fa'da maka."
Ya yi murmushi ya ce "Gaskiya na matsu fa'da mini na ji kawai".
Na yi dariya na yi shiru.
Ya zuba mini ido sosai ya ce "So nake ku koma, mu yi kwanaki ka'dan kafin mu fara ha'da kayanmu. Kin san mun kusa cika wa'adin kudinmu. Bazan sake biya ba. Idan na samu dama a Bauchi nake son na samu k'aramin gida mu koma can. Zirga zirgar zata mini yawa ga tsadar ku'din mota. Zan fa'da wa su Baba zamu k'aura zuwa Bauchi."
A sanyaye na ce "Allah ya k'ara budi."
Domin na shiga zullumin yadda zan rasa jama'ar da nake da ita, tunda bazan samu jama'a a Bauchi kamar yadda na yi shura a Toro ba.
Ya ce "Ameen Asiyata! Amma fa ban bar waccar maganar ba.
Dai-dai lokacin Haneef ya fara kuka da alamun razana ya yi. Da azama ya dauko shi, ya shiga tofa masa addu'a. Sai kuwa ya yi shiru. Ya bu'de idonsa kirr yana kallon Babansa. Da murmushi Tijjani ya ce "Halo Babana, how you doing today?"
Na murmusa na ce "Kana jiran amsa ne?"
Ya ce "ko bai amsa ba, ya ji ni. Yasan yana tare da Babansa ba ki ga ya yi shiru ba?"
Na ce "Hakane".
Daga hakan ya tsoma hannu a baki ya fara tsotso.
Tijjani ya ce "shima shan hannu ya fara?"
Na ce "Eh! Shi ne ma yake yi kawai. Hamim din da ya fara, yanzu ya gane nono, baya yarda ya sha hannu, wannan yafi shi hakuri".
Ya d'aga shi ya ce "To ba shi ya sha kada a dinga amfani da hakurinsa ana barinsa da yunwa."
Na karb'e shi na gyara na fara shayar da shi. Tijjani ya tsura mini ido yana kallon yadda k'irjina suka cika, suna tsaye tunda k'ananu ne.
Ya kasa hakuri ya dauko Hamim da yake barcinsa ya ce "Ka ji Momi ta ce "Ba ka da hakuri. Baban Marina da ka ci sunansa kuwa hakurinsa mai yawa ne".
Shi bai bu'de ido ba. Barcinsa kawai yake yi.
Ya ce "Ta shi kai ma ka sha".
Na ce "kana shigowa, ina kwantar da shi. A koshe yake."
Ya kankace ido ya ce "Ba kya kewata ko little?"
Na ji kunya irin sosai. Na kawar da fuskata ba tare da na ce kanzil ba.
Ya yi kasa da murya ya ce "Na yi matu'kar gajiya. Na matsu sosai".
Na kasa amsa masa.
Ya sake ce wa "Yaushe Baba ya ce zaki koma?".
Murya babu amo na ce "idan mun yi arba'in mana. Ai yanzu ma saboda kukan yaran nan ne ya barmu da ana yin sati uku zai tattaramu."
Ya nisa ya ce "Idan ta kukansu ne ai zan iya da su Asiyata."
Na yi dariya na ce "baka san kalar kukan da suke yi ba ne."
Ya ce "Da gaske nake yi miki, zan bar komai na ji da su. Kinsan yadda nake jinsu a raina kuwa?"
Na girgiza kai na ce "Ina zan sani? Amma ni da su waye a gaba?"
Ya tillike da dariya sosai ya ce "Yanzu kishin ki har da y'ay'an ki Asiya?".
Na cuna baki na ce "Yo daga tambaya sai ka hau sarhutu".
Ya murmusa ya ce "Yaushe zasu fiki, to wa ya haifa mini su?"
Na murmusa ka'dan.
Ya ce then fa'da mini sunan da kika ce".
"Oh Allah! Bari na fa'da maka tunda kai gajen hakuri gare ka. Baban 2. Shike nan?"
Da'di ya kama shi, ya washe baki dukkan hak'oransa suka bayyana ya ce "Na gamsu da suna na mussaman ne. Ke kuma Maman 2?".
Na juyar da fuska ina murmushi na ce "A a ni ba Mama ba ce."
Ya ce to me ce ce?"
"Yaya".
Ya sake cewa wanne irin Yaya kuma?. Ko da yake tare zaku taso tunda kin yi haihuwar wuri. Amma dai su ce miki Ammi tunda ba kya son Mama".
Na ce "To."
Su Hanif basu bar kuka ba sai da muka kusan arba'in. Kafin lokacin kuwa sun yi girma na ban mamaki tamkar sun yi watanni biyu. Amma tunda ana fa'din da Bulkachuwa suke kama dole su yi girma.
Ana jibi zamu yi arba'in Baba ya ce a shirya ni, domin ranar da na cika arba'in zan koma dakina.
Haka Gwaggo ta hau shirya mini kayanmu, tana ha'de su waje guda. Sannan k'anwar mahaifiyarta ce zata zo ta zauna ta taya ni rainon tagwaye har su dan yi k'wari.
Ranar da muka yi arba'in tun da sassafe Tijjani ya zo daukarmu, ko kunyar su Baba baya ji.
Baban kuwa bai yarda ya tafi da ni ba. Kayanmu dai ya yi ta diba yana kaiwa. Mama Baba ya ce ta rakamu, bayan ya dauko shatar mota ta fara kaimu asibiti a yiwa yara allurar rigakafi. A cewarsa baza mu hau mashin da jinjirai a kwasar musu sanyi ba.
Mamah ta tab'e baki ta ce "Alhaji da alamu dai y'ay'an Yabi sun zarta na kowa daraja a wajen ka".
Kai tsaye ya ce "To ai su tudu biyu suka ci, kin san Tijjani ne ubansu. Jikokin Hauwa ne fa".
Takaici ya kume ta ainun.
Ni kuma na dinga mata kallon ko sai yaushe zata daina Bak'ar Ta'adar rashin ri'ke girmanta. A shekarun ta ai ta wuce ta dinga irin k'ananun maganganu marasa kan gado. Wanda babu azanci a cikinsu sai tarin k'yashi da hassada.
Akan dole ta raka ni, a asibitin duk inda muka wulga sai an yi sha'awar tagwaye tare da yi musu addu'a. Wajen goma da rabi na safiya muka gama da asibitin sannan muka zarce gidan.
Muka tarar da gidan a gyare tamkar ina ciki. Ban yi mamaki ba domin ya riga ya saba da gyaran gida.
Jimawa ka'dan ta yi mini sallama tabi motar ta tafi abin ta.
Tijjani ya tisa ni gaba da rawar jiki. A sanyaye na ce "Duk gajiyar asibitin da na sha. Ka bari mana dare ya yi".
Ya hau jijjiga kai yana fa'din "Ba zan iya ba. Na yi hakuri Asiya! Ke ma kin sani. Kawai ki bani hadin kai. Da daddare rainon twins zan yi, ke kuma ki yi barcinki son ran ki".
A hankali na ce "Dama dai ba Baban 2 ba ne".
Ya yi dariya ya ce "me kika ce?"
Na girgiza kai tare da cewa "Ban ce komai ba".
Ya mikar da ni, ya ja ni zuwa d'akin. Na yi turus ganin su Hamim kwance akan sabuwar katifa madaidaiciya daga gefe. Hakan ya saka dakin ya cike. Na zuba ido ina kallon yadda ya shimfida zanen gado sosia, su kuma ya jere su, duk da akwai tazara a tsakaninsu. Na ce "wannan katifar fa?"
Ya ce "Tasu ce. Tunda ba ni da halin siya musu gado, shine na siya musu katifa. Kinsan ba yarda zan yi su dinga shiga tsakiyarmu ba. Can ne makwancinsu. Idan sun yi kuka zan koma na kwanta a cikinsu".
Na yi k'aramar dariya ban ce komai ba.
Ya ja ni jikinsa ya rungume tsam tsam yana shakar kamshin jikina. Al'amarin da ya biyo baya ba mai sau'ki ba ne. Na gamsu ya yi kewata, na kuma gasgata shi da ya ce a matse ya ke. Duk yadda na takura a dalilin yadda kayan chadi suka saka na matse, na daure na bar shi ya samu nutsuwa.
Shi kuma sai fa'din "anya ba cs aka miki ba little? Ni ban ji alamun tana nan twins suka fito ba".
Ni dai ban bude baki na ce masa uffan ba, amma ni da kaina na gasgata kyaun saiwowin da na yi amfani da su. Na ji dadin maganin sanyin da na sha ba ka'dan ba.
*Domin samun naku kayan gyara na mussaman, ko maganin sanyi sadidan.*
*SAIWOWINE da ake kawo su daga Chad da Sudan gangariya. Ku tuntu'be ni a kai-tsaye ta manhajar WhatsApp*
08032773332.
73&74
Kwana biyu da komawa ta Muna ta barzar amarci. Yaran kuwa tamkar almara basa kuka. Da sun yi ka'dan suka sha nono sai su yi kwanciyarsu sai an idar da sallar asuba zasu farka.
Yana dawowa kuwa zai d'ora mana ruwan wanka. Da aka sa zai juyo, ya taya ni mu yi musu wanka.
Ni da kaina na tabbatar zai yi wahalar gaske a samu miji irin Bulkachuwa. Domin duk aiyukan gida ba zai zame masa komai ya yi ba.
Ina jin dadin Supplement din FASEELAT. Sun taimake ni wajen gyara mini ruwan nono da sake hade ni. .G H.T duniya ne na yarda *07039269802*.
Rainon yaran nan kuwa ba abin da ba ya yi. Kafin na yi musu hidima d'aya ya yi musu biyar. Ko pampars suka bata, ba ya jin komai zai cire ya wanke musu ya saka musu wani. Idan sun yi barci, sai kuma ya dawo yana tiritiri da ni.
Tun tafiyar tamu bata yi nisa ba na fara fa'din madallah da aurensa a zuciyata. Ban dai furta a fili ba ne.
Kwana duk da kuwa yana da na'kasu, sai dai alherinsa yafi tsiyatakum yawa.
Kwana biyar da komawa. Baba Lami ta zo daga kangire. Wacce matsayin kaka ce a wajena. Tunda k'anwar mahaifiyar Gwaggo ce uwa daya uba daya.
Ranar da ta zo, a ranar ya koma Bauchi.
Cikin sau'ki da rangwame nake rainon yan biyu. Basu da fitina. Sannan Baba lami mace ce mai kazar kazar ainun. Abin da nake yi ka'dan ne. Watana biyu da haihuwa na koma kan sana'a ta.
A hankali kuma Tijjani yana samun rufin asiri a zamansa a baucy. Tunda abinci dai baya yanke mana. Iyakar kokarin jarfinsa yana yi. Duk sati zai taho musu da Pampers. Ni kuwa kayan shayi duk sati ne. Idan na ce "Basu kare ba".
Ya dinga fa'da akan me bazan dinga shan shayi mai kauri ba, alhalin ina shayar da yara har biyu. Ga su nan su sun yi girma ni kuma na sake zuke wa.
Watarana Baba lami ta ce masa ba rashin cin abinci ba ne, wasu matan idan suna shayarwa hakan suke yi. Sai sun ya ye sannan su yi kumari.
Baba Lami bata tafi ba sai da muka kwashe watanni kusan biyar a tare. Lokacin su Hanif na da watanni shida.
Muka ha'da mata alheri sosai. Sannan suka tafi da Gwaggo da Yaya Ummi bikin da za'a yi a can Kangire. Na so zuwa, amma ya yi mirsisi ya hana.
Sannu a hankali muke rayuwa, bamu cika samun matsala ba, tunda kwanakin da yake yi a Bauchi sun fi wanda yake yi a Toro.
Kullum idan ya dawo sai ya ce "ki tsananta yimini addu'a little. Mahassada sun kewaye ni a kasuwar nan. Ga shi an rasa gane inda matsalar take kullum Alhajin da muke wajensa sai karayar arziki ya ke samu.
Ina jin tsoro k'warai da gaske.
Cikin tausayi na ke kwantar masa da hankali da kalamai masu taushi.
Wani zuwa da ya yi, ya ce "mu
shirya zai kai mu Bulkachuwa mu yi sati.
Na dinga murna domin rabona da zuwa tun kafin na haihu. Ga shi yazu watannin su tara har sun fara tsayawa. A yanzu kam na gasgata kama suke yi da Bulkachuwa. Domin suma haka suke dogaye, masu gaba manya. Ba wanda zai ce ni ce uwarsu. Domin manya ne sosai, sannan ni yar tsurut ce sosai. Kawai faratuna suka diba, da kuma yan k'ananun kamanni. Amma kammanin ubansu yafi yawa a tare da su. Tun yanzun kuma halayyarsu ta banbanta. Haneef mai sanyi da hakuri ne. Sai ya yini baka ji kukansa ba. Kafin ya nemi nono sau daya Hamim ya nema sau uku.
Zai yi wahalar gaske ya damuki d'anuwansa yasa shi kuka. Amma Hamim kullum cikin nukurkusrsa yake.
Ga shi da shegiyar kiwa. Ko wajen Babansu sai ya akan dole yake zuwa. Ko idan ya ga ya dauki Hanif zasu fita.
Shi dai kullum yana jikina. Ko k'unshi zan yi, sai dai na ha'da masa kayan wasa a kusa da ni.
Ko ya ce ",sai na goye shi.
Sabanin Hanif da ba ya yin kiwa. Kowa ya mika masa hannu zuwa yake yi.
Shiyasa ma na fi kai shi gidan Yaya Ummi ya yini tunda yanzu ba ni da nisa da ita.
Kullum Bulkachuwa sai ya ce halina ya kwaso. Domin mafad'aci ne na gaske, ga kuka. Idan ina mita akan halinsa Gwaggo ma ce wa take yi hakan na yi mata. Haka ta sha fama a goyona. Bana yarda a dauke ni. Ko band'aki zata shiga sai an yi artabu da ni.
Da yammaci muka isa Bulkachuwa. Babah sai ina ka saka take yi da ni da yara. Komai ta mika hannu a kai sai ta dauko ta ajiye a gabana. Yara kuwa kayan wasa sabbi sun fi kala uku tamkar dama a wajenta suke. Na kasa ha'kuri na ce "Babah wadanda kayan wasan fa?". Domin ihisan ba a garin take ba. A cikin Bauchi take bari na yi zaton na yaranta ne.
Da walwala ta ce "Tunda ya ce zaku zo na siya musu, tunda na ga mai sunan yayan nawa rigimamme ne. Shi dai bai kwaso halin mai sunansa ba. Hanif ne ya kwaso halin mai sunansa."
Nasir da yake gefe ya ce "Su Babah ana yabon sunan masoyi".
Ya bani dariya na rufe fuskata na dinga yinta. Ta mike sabe da Hanif tana fa'din ja'iran yara bari na baku waje.
Shi dai Tijjani bai ce komai ba. Asalima matse wa ya yi ko dariyar bai yi ba.
Kwana biyu ya yi, ya barmu ya wuce Bauchi.
Bayan dakina da na Gwaggo ba inda nake samun natsuwa irin a dakin Babah. Domin wata irin mua'amala take yi da ni mai dadi da tattali. Bata taba nuna surukunta a tsakaninmu ba. Sai ni ce ma nake jin kunyar yin wasu abubuwan a gabanta. Ita kuwa da taga hakan zata balbale ni da fa'da tana fa'din bata son rashin kunya. Har yaushe na zama matar tasa da zan ture ta a uwa na mata kallon suruka. Na sake na yi komai yadda nake so kamar yadda nake yi tuntuni.
Da kanta ta dafa mini kazar da na tabbatar ta mata ce. Kunya ta kama ni. Ita kuwa fadi take ci ki sha romon. Tun lokacin haihuwar na siya na dauka zaku zo yawon arba'in. Tunda baku zo ba. Na ajiye nasan a can ma za'a gyara ki."
Na rasa yadda zan yi, ita kuwa ko a jikinta.
Ranar da Bulkachuwa ya dawo. Da daddare an hadu a falonta ana ta hira cikin walwala ya kutso da maganar yana son mu koma Bauchi gaba'daya.
Ta ce "ka dai kafe. Yanzu kam tunda yaranta sun yi k'wari ba zan hana ba. Allah ya bada sa'a.
Dama har da tunanin yadda sana'ar ta zata durk'ushe ne. Amma In sha Allah a can din ma sannu a hankali za'a santa."
Ni kuma sai kawo masa abinci abubuwa nake yi. Gaba'daya na kasa sukuni. Babah da kanta ta gane yanzu kam sonsa nake yi da dukkan zuciyata.
Washagari ana zaune bayan mun karya. Sai kawai ya kalle ni ya ce "A irin wannan ranar ta shekaru uku baya kika zo har nan kika ce ba kya sona Asiya".
Nan da nan na ji tamkar k'asa ta tsage na shige. Kunya ta rufar mini. Na rasa yadda zan yi. Sai kawai na fara kuka ina ce wa "Idan juninka tashin tashina ne, da son sai ka kunyata ni, to ni ba damuwa zan yi ba, kai ne zaka ji kunya Wallahi".
Nasiru ma cikin dariya ya ce "Ai kuwa nima na tuna yawun da kika kwalbana masa a fuskarsa. Yau kuwa sai faman girmama lamarinsa kike yi".
Na sake rushe wa da kuka ina ce wa "Ai kai dama baka fa'din gaskiya".
Babah ta ce "Yo ni ke kika fi ba ni haushi, to kukan na mene ne? Ware wa zaki yi ai ku yaga, suma ki nutsu ki fadi irin nasu al'amarin da baza su so a taso musu shi ba."
"Nasiru ya ce "Ni dai babu abin da zata fa'da a kaina, sai dai ko akan mijinta".
Tijjani dai tunda ya kunyata ni bai sake ce wa ba.
Jimawa ka'dan Babah ta mike ta shiga cikin gida.
Nasiru ma ya mike yana ce wa "Hajiya Yabi bari na fece tun Babah bata zo ta fa'da miki wani abu a kaina ba."
Ko kula shi ban yi ba.
Yana fita na kalli Tijjani na ce "Na gode sosai Baban 2"
Ya yi murmushi ya ce "wannan godiyar fa! Ta mece ce?"
Na matso hawaye na ce ",Na gode da kunyata ni da ka yi, na gode da wannan sakayyar".
Ya dara ka'dan ya ce ",Kin san na fa'da miki lokaci zai zo da zaki ji kunyar abin da kika yi".
A hassale na ce ",To mene ne zaka tayar a gabanta? Gaskiya kada ka sake yi mini irin haka. Idan kuwa ba hakan ba kasan kai ma ka mini laifin da ban ta'ba bude wa an ji ba".
Nan da nan ya shiga nutsuwarsa ya ce "Ai ni ba da bacin rai na fa'di hakan ba. Amma ba zan sake ba, mu rufe maganar haka nan.
Na girgiza kai na juyar da fuskata gefe. Ya shiga kiran sunana a hankali, na ki juyowa. Ya diririce. Ya ce "Asiya wasa fa nake yi miki. Me zai sa
mu yi fa'da a gaban Babah".
Na ce "Ai so kake ka bakanta ni a wajen ta, shi yasa ka dauko wannan maganar".
Ya marairaice ya ce "Billahillazi ba hakan ba ne. Gaba'daya ya rikice jin na lauya magana zan tado da tashin hankali.
Ya dinga lallaba ni da son sai na dawo da walwala ta.
Ni kuma ina sane na yi masa hakan.
Bamu bar garin Bulkachuwa ba sai da muka shafe sati biyu.
Da zamu tafi, tamkar wanda muka je fatauci saboda kayan da muka samu.
Lafiya k'alau muka isa Toro. Kwana biyu a tsakani ya koma Bauchi.
Kwatsam aka tashi da mutuwar mijin Nasiba. Wannan mutuwa ta bigemu, domin babu jinya sai mutuwa. Ashe kasurgumin dan shaye shaye ne. Can wajen sharholiyarsu rikici ya kaure tsakaninsa da abokinsa ai kuwa ya daba masa kwalbar a kahon zuci ya mutu a wajen nan take.
Gaba'daya maganar ta cika Toro da kewaye.
Na tausayawa Nasiba kwarai da gaske, duk da dama ba zaman dadi take yi da shi ba. Duk cikinmu ita ce bata samu sukuni a gidan aurenta ba. Yaranta biyu Muhsin, da kuma Maryam da bata fi watanni shida da haihuwa ba.
*Watanni bakwai a gaba*
Zuwa wannan lokacin mun koma Bauchi da zama. A satin nan kuma na yaye yara. Bulkachuwa aka kaiwa Babah su. Kwance nake ina fama da zazzabin da ciwon nono ya zuba mini. Ga kewar yara, abin sai ya hadu ya kwantar da ni. Nasan Hanif ba shi da matsala, amma Hamim kam sai Allah. Rashinsa ya fi takura ni.
Tijjani kuwa sai tsokana ta yake da fa'din Hanif ne kawai zai dawo, Hamim ya zama dan Bulkachuwa.
Bana ce wa komai amma na sani zolaya ta yake yi.
Sai da na sha allurai sannan na warware.
Sannu a hankali na shiga saboggina tunda anan Bauchi ma na fara sanuwa a wajen k'unshi da kitso, sai dai ba kaman Toro ba.
Matsakaicin gida ya kama, cikin madaidaiciyar unguwa.
Cikin nutsuwa da rufin asiri mukr rayuwarmu. Har yau din nan Bulkachuwa tattala ni yake yi. Baya kaunar abin da zai ha'damu rikici sai dole. Baya mini fishin da ya wuce na kwana d'aya. Ni ce dai nake jarumtar share shi na lokaci mai yawa.
Duk da ni din ma karfin hali nake yi.
Yanzu haka Tijjani yana da nasa teburin a cikin kasuwar ma'ana ba k'arkashin Alhaji yake ba. Watanni uku ya karbi ku'dina ya mallaki wajen flda zai ajiye teburinsa. Zobena daya muka siyar. Yanzu haka jiya ya kai ni na zabi wanda nake so ya siya mini a madadin nawa.
Na sani ba dan ya samu damar biyan ba ne, sai dan yana son ya biya ni ne.
Hakan kuma bai sa sun rabu da Alhaji Auta ba.
Ana cikin haka guda cikin kamfanin sadarwa ya nemi kafa turakan ayyuknasu cikin unguwar da filin Tijjani yake. Gaba'daya mutanan da suke da fili a wajen kowa fata yake a ce su karbi nasa, tunda haya zasu kar'ba.
Alhaji Auta har addu'a ya baza a yi masa ko ya samu ya d'an farfado.
Kamfani har yanzu zagaye yake tare da wakilinsu da suka san ilimin kimiyya suna ta auna inda zasu fi samun sabis.
Gaba'daya Tijjani bai sa hankalinsa a wajen ba. Gara ma jiya ya ce mini ku'din da mutum zai samu a shekara d'aya kacal ba k'ananu ba ne.
Ina bu'de baki na ce "Idan akwai alheri a cikin samun da za'a yi, Allah ya saukar a kan filinmu".
Ya ce "Kayya! Amma tunda Allah kika ce ai magana ta k'are. Ameen".
Muka bar magana a hakan.
A wannan tsukun auren su Yaya Ammar da na Yaya Rabiu da su Kaltume ya zo.
Muka shirya muka tafi tare. A can muka tarar da Babah da y'an yayenta. Hamim na ganina ya cakume ni, ya cukuikuiye hijabina wai bazan gudu na bar shi ba. Hanif kuwa kawai kwantar da kansa ya yi a jikina. Tijjani ya kalle shi ya ce "Kai ma ka bi bayan d'anuwan ka, baka ta tawa ko?" Ya kalle shi kawai. Ya yafice shi tare da ce wa "zo mana Babana".
Ya kuwa isa gare shi ya kwanta. Yayin da Hamim ya rikice sai ya sha nono. Da k'yar Tijjani ya yane shi suka fice.
Babah ta ce "Ai ban yi zaton darun d'anuwana ya kai haka ba sai yanzu".
Na ce "Ai ba shi da sau'ki Babah. Hanif ya fi sassauci". Ta ce "Babu hadi ma. Allah ya musu albarka ya tsare su. Ki yawaita yi musu addu'ar tsari da kuma kambun baka".
Cikin na ce "To".
Duk inda na shiga sai an kalle ni. Da na juya baya za a hau zancena. Haka Ikilima ta jiyo mini gulmar da sa'anina da muka taso tare su Saratu su Maijida. Suna fa'din ",Ai gaba'daya Bulkachuwa tsorona yake ji saboda ina da ku'di. Duk kafafar da nake yi da burgar kwalliya da yadikan yan gayu na Umm Nihla collection. Ni nake yiwa kaina ba shi ba ne. Su kuwa sun gode Allah mazajensu ne suke dawainiya da su yadda Allah ya hukunta. Barin Maijidda da a yanzu suke Kaduna. A dalilin Yaya J ya samu aiki a kwalejin kimiyya ta kaduna(Kad-poly).
Gaskiya ne duk ta fimu d'aukar ido. Amma kuma ba wai ta fi kowa kwanciyar hankali ba ne. Ko wacce ita tasan yadda take zaune a gidanta.
Nasiba tuni ta sake dawowa gidanmu gaban Dada. A yanzu da bata da aure ma tafi walwala da kwanciyar hankali. Tunda yayanta Ammar na kula da ita daidai gwagwado. Sannan iyayen mijinta suna ri'ke da Muhsin cikin kulawa, Maryam din da take shan nono ma sukan yi mata aike lokaci zuwa lokaci. Gaba'daya ta murmure ta dawo da jikinta da ta rasa a baya. Sai daga baya aka gane komai na d'akinta ashe ya siyar tunda mashayi ne kuma dan caca. Da ace wata a k'ofarmu hakan ta same ta da anyi yamididin halin d atake ciki. Amma wannan shiru ake ji.
Tallafin da take samu ya sanya take figa take yin y'an sitturu da kayan kwalliya dan haka fes take bata da makusa.
Na yi tsuka na ce "Basu da abin yi ne, koma a ya ya na ke rayuwa ai babu ruwansu, tagayyara da ake mana fata kuwa ba zamu shige ta ba in sha Allah."
Amma a tunzure nake kwarai da Maijidda. Na kuma ku'dire indai ta sake ta mini maganganun banza yadda ta saba yi mini, idan mun hadu a taro, to a wannan karon zamu sake gwada yar kwanji dan na tuna mata baya.
Ta fitine ni da yawa. Nazira da take gefe ta ce "Sanin kina da daraja ne a wajen mijinta ya sanya ta washe ki, ban da haka kina matar wani, ta shafa miki lafiya mana, tunda tasan a musulunci mace bata auren miji biyu. Da a ce Nasiba ce ke, ai da tuni Maijidda ta kusa zama gawa, domin ba abin da zai hana mijinta fitowa neman auren ki, tunda har gobe yana son ki".
Da hanzari na ce "Allah suturi bukui. Ai sai yanzu na fahimci tun asali ba wani sonsa na yi ba, shak'uwa ce da soyayyar k'uruciya. Yanzu da na saba mua'amalantar barden namiji irin Baban 2, mai zan yi da dan karamin sauron mijinta? Su je can su k'arata har abada ba zai sake burge ni ba."
Dadi ya kama Adda Nazira ta fashe da dariya ta ce "Ina komawa zan fa'dawa Baban su Abid tun yanzu Yabi ta fara fa'din madallah da auren Yaya Bulkachuwa".
Kunya ta dan rufar mini na ce "eh ki fa'da masa".
Haka aka yi bikin aka gama lafiya. Baba Maryo da kanta wani gani gani take yi mini da ban san dalilinsa ba. Ba dama ta ga Babah ta yi mini wani abu sai ta ce "Ba hakan aka barki ba, da aka tashi kame mata Tijjani har da uwarsa aka ha'da ban da hakan irin wannan gudun zuciyrta da kike yi har ina? Yara na son zuwa wajen uwarsu kin kanekane kin rikesu kina fa'din ta je ta yi hidimar jama'a. Ke kuma kin zama mai raino'.
A lokacin da take fa'din haka ina tsaye, wata irin fargaba ta kama ni, domin na hango kishina ke cinta ba ka'dan ba. Na laluba ko na yi mata laifi ne, amma ban ga na yi mata komai ba. Wata'kila zamana lafiya a gidan aurena ne yake mintsinarsu. Tunda da safen nan ma sai da Baban Tsakiya da na kasuwa suka tambaye ni, wai na fa'di irin zaman da nake yi, idan babu dama sai a ha'kura ramar da nake yi ta yi yawa.
A dakin Dada a gaban kuma Babah.
Na kalle su ina mamakin manufarsu. Domin ni dai jefi jefi Tijjani na matsa mini na kira na gaishe su, ina kuma yi tunda tisa ni yake yi a gaba. Amma su kam tunda na yi aure ba wanda ya ta'ba kirana ya ji lafiyata, ko ya ji ya ya na ke? Baban Marina ne kawai yake mini hakan a cikinsu.
Amma abin mamaki sune da fa'din wai na rame tsabar sun saka mini ido suna kuma adawar sun jimu k'alau ni da Tijjani.
Na bu'de baki cikin nutsuwa na ce "Satin jiya na yaye yara, na yi fama da zazzabi a dalilin haka. Sannan ni ba ni da matsalar komai ina cikin rufin asiri mai yawa. Allah ya saka muku da alheri bisa bawa Tijjani aurena da kuka yi. Bana fatan sauyi ko a aljannah ne".
Baban Kasuwa ya ce "To ya isa zabiya! Mun ji, mun ga ne ba sai kin zarce da rashin kunyar da kika saba ba."
Baban Tsakiya kuwa ya ce "Na tashi na basu waje sun sallame ni, dama sun nuna kulawa ne dan sun gane muna zaginsu a bayan idonsu akan basa kula da sha'anin yan k'ofarmu. Amma zan fara yi musu rashin kunya da iyashege."
Na fito zan shige Babah da take bawa tagwaye koko da kosai.
Suka fashe da kuka wannan karon kukan har da Hanif.
Murya babu amo ta ce "Zo ki zauna, yunwa suke ji".
Na dawo na zauna shi ke nan kuma suka yi shiru. Suka ci gaba da cin abincinsu.
Muna haka Tijjani ya shigo dan haka na sid'ad'a na fice tunda suna ganinsa.
Washagari muka koma, daga ni har Tijjani so muke mu tafi da yaranmu. Tunda sun yi sati biyu. Amma kowa ya kasa fa'dawa Babah da ta daure fuska bayan ta fahimci take takenmu.
Sai da zamu tafi ta biyo ni har zaure tana fa'din "Zan dawo muku da su, amma sai kin warware kin murje. Kina ganin dai yadda ramar ta ki ta janyo cece kuce. Ki kwantar da hankalinki, nan da wata ma zasu dawo."
Kunya ta kama ni, na shagwabe fuska na cuna baki na ce "Ni fa Babah ban damu da su ba, su zauna ma gaba'daya a wajen ki, ba ni da matsalar komai".
Ina rufe baki Tijjani ya yi maza ya ce "Bilhiillazi karya take yi miki Babah."
Ta gwale shi da ce wa "ko k'arya take yi, ai ta saya, kai da baka da kunya ai ka bu'de ka nuna na baku yaranku".
Nan da nan ya yi shiru, ni kuma na yi dariya tare da yi masa gwalo.
Da hakan muka rabu, ta koma cikin gida, mu kuma muka tafi.
75&76.
Da wuri muka shiga Bauchi. Ya taimake ni muka gyara gidan, muka yi girikin abin da zamu ci.
Dai da yamma ya fita.
Kwanci tashi asarar mai rai, kwanaki suka yi ta shud'ewa har muka samu sati da dawowa daga Toro.
Daga ni har Tijjani bama jin da'din rashin yaranmu a tare da mu. Kewarsu muke yi sosai. Amma dukkanmu kowa ya bar abin a ransa, mun bisu da addu'a.
Muna cikin hakan ba zato sai aka kira Tijjani tare da albishir din filinsa kamfanin sadarwa yake bu'kata. Zasu karbi hayar wajen na shekaru uku. Idan wa'adin ya cika, wata'kila su siya gaba'daya ma, matu'kar mutane sun karbi sabon kamfanin da hannu biyu.
Farincikin da muke ciki ba ka'dan ba ne. Mussaman da Tijjani ya tabbatar mini ku'din ya isa ya sayi gidan da muke ciki da kuma mota golf da ake yin sufuri da ita.
Cikin Ikon Allah kuwa bayan cike cike, da kai komo suka tura masa ku'dinsa cas ta asusunsa na banki. Hassada da bak'in-cikin a wajen masu filaye a wajen tamkar su jefa shi wuta. Hatta Alh Auta bai iya boye ba'kin cikin da ya ji ba.duk da Tijjani ya bashi kyautar dubu dari a cikin ku'din amma hakan bai sa ya gode ya ha'diye ba'kin cikinsa ba.
Wani k'aramin gida da yake gabanmu ka'dan, Tijjani ya siya. Sabon gini ne, fenti ne kawai ba'a yi ba.
Mai gidan ya d'aga gidan xai siyar a dalilin ya samu wnada ya fishi yalea zai siya.
Da yamma muka je na ga gidan.
Karamin guda ne ainun. Sai dai kuma an tsara shinda kyau. Kafin udan an shiga daga farkon akwai daki mai dauke da band'aki. Wanda tsarinsa yafi dace wa da na maigidan.
Daga ciki kuwa k'aramin tsakar gida ne, sai falo mai dauke da dakuna biyu, ko wanne da bandakinsa.
A tsakar gidan akwai kicin da kuma wani band'akin daga gefe.
Gidan ya sake kawatuwa a dalilin an zuba masa tayal ta ko'ina. Ta bayan dakunan kuma akwai doguwar hanya, bata bille wa, amma dakuna zasu sami iska, sannan za'a iya daura igiyar shanya a wajen.
Farin ciki ya mamaye ni. Yau ga ni zan yi d'aki mai dauke da band'aki a cikinsa. Lallai komai lokaci ne.
Ya kalle ni da murmushi ya ce "Ya yi miki?"
Na bu'de baki na ce "sosai ma kuwa Baban 2. Ubangiji ya k'ara arziki, yasa rabo ne."
Da walwala ya ce "Ameen, tunda ya yi miki bari na je wajen dillalan, mu nemi shaidu a je a biya".
Na fa'da jikinsa ina jin farin ciki na walagigi da ni. Na dinga jera masa fararen addu'oin da suke sanya shi farin ciki.
Ba'a dauki lokaci mai yawa ba, ciniki ya fa'da ya yi fentin da ba'a yi ba.
Ya sayi katifa ya saka a d'akinsa.
Dakina kuwa aka shirya kayan gadona bayan an musu kwaskwarima, katifar gadon muka bari a tsohon gidan kafin mu tare. D'akin yaran kuwa aka saka musu katifarsu da ya siya musu yun suna jarirai.
Kujera ya canja mini, tawa ta tsufa da yawa, tunda ba mai tsada ba ce dama. Yanzun ma mai L ce amma mai daraja sosai. Aka makala tibinmu a bango shike nan, domin a kicin a saka firij tunda da fili.
Gida ya fito ras. Na dan yi siyayyar kayan kicin wanda zan iya. Na sayi kafet da labule kalar kujerar.
Muka ja gida muka rufe. Da kansa ya je Bulkachuwa ya taho da Babah da yara. Ta zo ta ga gidan da Ubangiji ya mallakawa Tijjani cikin sau'ki.
Ta dinga hawayen farinciki, tare da addu'ar Ubangiji yasa likkafa ta cigaba. A fili ta ce "Da ikon Allah sai kun yi arzikin da kowa sai ya ci arzikinsa. Ina da yakinin Ubangiji ba zai juyar da addu'ar da nake yi muku ba".
A ranar ta tafi, duk yadda muka so ta kwana tare da mu, amma fir ta ki. Ta bar yara, tare da zolayata wai gasu nan su mini sati biyu, zata turo Nasiru ya dauke su.
Haka ya je Toro ya sanarwa da iyayenmu alherin da ya samemu, tare da basu Ihisani. Mota guda suka taho ganin gidan da su Baban Tsakiya nasu gasgata Tijjani ya siya ba.
Tun wuri ya kawo mini kayan miya da nama ya ce "Ki yi abinci da yawa Asiya. Yau mutanan Toro sun taho ganin gidanmu. Nasiba ta ce mini har da Dada".
Na dan ji babu da'din yadda ya ce Nasiba ta fa'da masa. To waya suke yi ko kuwa ya ya?
Na daure na ha'diye ban tuhume shi ba.
Na hau hidimar aikina. Shi kuma ya ri'ke hannun yara suka tafi siyo ruwa da lemo.
Na kammala abincin na yi wanka. Ina cikin shiryawa na ji tsayuwar mota, a gaggauce na gama shirina.
Na fito ina marabtasu.
Na ri'ke hannun Dada ina yi mata maraba ta mussaman. Tuni su Baban Marina, da Baban Tsakiya har da Baban kasuwa suka isa falo. Baba Maryo na cikinsu.
Tare da Tijjani muke ta ajiye musu kwanukan abinci da abin sha.
Yadda muke shige da fice muna hidimarsu tare, abin ya yi matu'kar burge Dada da Baban Marina. Domin sai addu'ar alheri suke bin mu da ita. Su kuwa ragowar wani irin kallo suke bin mu da shi wanda na rasa gane inda suka dosa. Domin ba wanda ya taya Dada da Baban Marina albarkar da suke sanya mana.
Sai da suka ci, suka gyatse. Suka je masallaci suka yi azahar. Sannan muka d'unguma ganin sabon gida.
Dada sai hamdala take yi, yau Ubangiji ya gwada mata ta ga gidan mai sunan manya.
Baba Maryo kuwa da ta shiga falon ta leka ta ga dakuna biyu, ko wanne da bayi a ciki. Tana bude baki sai ce wa ta yi "Gida kuwa a yalwace. Ban da wuyar zama irin ta y'ay'an yau. Mace biyu ma sai su yi zamansu wata bata takura wata ba. Tunda akwai turakar maigidan".
Zuciyata ta yi matu'kar bugawa, domin na fahimci akwai k'ulli a zuciyarta game da ni, tunda muka je biki na ga tana rawar jiki wajen Babah tare da bagarar da ni, nasan akwai abin da take nufi da ni.
Maganar da Tijjani ya fa'da mini dazu na ce wa Nasiba ta ce tare da Dada suka taho, ta sake dawo wa ta rib'anya zullumin da na shiga.
Na daure ban ce komai ba illah yak'e da nake yi. Gaba'daya Dada da Baban Marina ne suke yin murna ta fisabidillahi a cikinsu. Baban kasuwa da ya bu'de baki sai ce wa ya yi "To Tijjani gida ya yi kyau. Amma ku shiga a hankalinku, ku dinga jin tsoron Allah. Harkar nan ta neman maza ta zama ruwan dare a tsakanin matasa. Kada ku bari manyanku su rude ku su dinga baku kudade kuna b'ata gobenku".
Na kalli Tijjani na ga ya yi kasa da kansa yana fa'din"Da ikon Ubangiji zamu kiyaye iyakokon Ubangiji."
Zuciyata ta dinga tsallen na mayar masa da martani. Amma idon Baban Marina, da na Tijjani suka mini cikas. Domin na sani dukkansu baza su mini ta da'di ba, idan na yi masa rashin kunya a gabansu.
Ban gama jimamin isgilancin Baban kasuwa ba, sai kuwa Baban Tsakiya ya ce "Haka KUMA a kiyaye cin riba, da shiga kungiyar masu daukar bindiga suna kwace wa jama'a rayukansu da dukiyoyinsu suna azurta kansu. Wannan zamani da wuya ya ke."
Dada ta ce "Ina addu'a akan duk rintsi kada a jarrabi iyalina da aikata kaba'ira.
Ban san me ya hana Baba Maryo sakin nata bakaken ba. Tunda ita ma bata nufinmu da alheri.
Shi dai Baban Marina bai ce musu kala kanzil ba. Sai da suka gama. Ya nisa ya ce "Ubangiji ya yiwa neman ka albarka, ya tsare ka, ya baka arzikin halali mai yawa. Ubangiji ya saukar da farinciki a kanka da iyalinka. Allah ya tsareku gaba'daya, ya shirya muku zuri'a."
Na daddage da k'arfi na ce "Ameen Babanmu. Ameen dattijon arziki, uban marayu, har masu uban ma.."
Baban Marina ya faki idonsu ya galla mini harara. Gane nufinsa ya sanya na ha'diye sauran maganar da na yi nufin zubarwa.
Baban Tsakiya ya kalle ni cikin fishi ya ce "Shi ka'dai ne Ubanku?'
Da azama na ce "Duk nan ina da uban da ya fika ne Baba? Kai ne ka d'aura mini aure fa".
Ya furzar da iskar baki ya ce "Na dauka kin manta saboda kina ganin kun fara shigo wa gari ai"
Kan dole na yi shiru. Ban sake ce wa komai ba. Amma dai kam zuciyata a tunzure take ainun.
Muna dawowa suka shiga mota suka tafi. Bayan Tijjani ya saka musu kwanduka kayan miya, ya kuma biya ku'din man da suka zubo a motar.
Kan dole nabi bayansa wajen yi musu godiya da addu'ar sauka lafiya. Dan kuwa ba dan tsoron Baban Marina ba da iya shi da Dada zan ware na yi musu godiya da fatan su sauka lafiya.
Tunda abin nasu babu arziki. Ban da fitina daga zuwa ganin abin arziki, babu saka albarka, babu fatan alheri, babu nasiha mai da'di. Sai mugun k'ulli ya biyo baya. Har da jinginawa mutum mafi munin zunubi irin luwadi. Kaico ga mutanan da basa furta alheri. Hasara da tabe wa ga masu hassada da k'yashi. Àllah ka shirye masu shiryuwa kawai.
Tunda suka tafi Tijjani ya kasa tafiya kasuwa. Kwanciya ya yi har dare, sallah kawai ke fitar da shi. Na sani kuma maganganunsu ne suke dafa shi. Duk da bai yarda ya biye ni mun yi zancensu ba.
Kwananki ka'dan muka tare sabon gidanmu mallakinmu ba wai haya ba.
Cikin dare mun gama mua'amalarmu, mun yi wankanmu a cikin d'akinmu. Munana kwance ya kankame ni, a kunne ya rad'a mini "little kamar yau kike mini kukan band'aki a daki kike so. Na ce miki da sannu zan miki, a wanccan lokacin baki gasgata ni ba, sai kika ce wasikar jaki nake yi. Tun daga waccan rana ban sake yin sujjada ban ro'ki Ubangiji ya bani damar da zan miki band'aki a cikin d'aki. Sai ga shi a kusa na samu damar ba tare da zato ko iyawa ta ba."
A hankali na ce "Baban 2 kana da tashin tashina Wallahi".
Ya yi dariya ya ce "Indai ba sharri ne da ni ba ai da sau'ki Maman 2".
Ban gama wartsake wa daga kunyar da ya saka ni a ciki ba. Ya sake baro wata maganar. Ta hanyar ce wa "Na k'osa ki yi ciki little kada ki fara yi mini borin idan ban miki ciki ba zaki tafi ki bar ni".
Na kai masa duka a k'irjinsa ina kukan shagwaba tare da fa'din "Bana son irin hakan da ka ke yi mini Baban 2".
Ya ri'ke ni yana dariya ya ce "Ba gaskiya na fa'da ba? Kin ga twins sun yi wayo, suna gudunsu ko ina, idan kin samu ciki yanzu babu damuwa, kafin ki haihu sun sake girma. Na ga kuma Babah so take ta rabamu da su. Idan kina da wani a hannun ki ba zaki wani damu ba".
Ban ce komai ba. Domin kunya ta yi mini k'awanya.
A wannan tsukun da'din da Baban 2 ya jiyar da mu ba ka'dan ba ne. Domin suturun da baya samun sukunin yi mini sai da ya mini matsakaita kala biyar. Kusan karamin lefe ya yi mini. Tunda komai sai da ya siya mini daidai misali. Haka yara ma ya yi musu siyayyar kayan sawa da kayan wasa.
Cikin nutsuwa muke rayuwa, ina mutunta shi tare da girmama shi. Haka shima yake kaffa kaffa da ni. Idan ya ga zan rikice masa, zai bar komai ya rarrashe ni, ya kwantar mini da hankali. Domin budin da ya samu, ya sanya shima ya sabunta suturunsa, ya sake zama hadadden gaye. Tunda yanzu ne ya cika shekaru talatin. Ma'ana yana cikin shekarun samartaka da k'arfi. A lokacin ni kuma nake shirin shiga shekaru ashirin.
Gaba'daya na kwarzabi raina, domin ina ganin zai iya samo zabgegiya ya aura.
Ban ta'ba bu'de baki na yi masa k'orafi ba. Amma a ankare nake matu'ka da gaske.
Ba a jima ba motar da ya siya ta golf ta iso.
Ya zaunar da ni ya fa'da mini zai fara kai kayan miya garuwa ranakun kasuwanni. Tunda zaman kasuwar yana neman gagarar sa. A dalilin yadda Alh Auta da sauran wadanda suke ganin ya je ya same su a wajen amma ya kere su. Sun ki fahimtar Ubangiji ne yake raba arziki a sadda ya so.
Cikin nutsuwa na ce "Wai filin nan naka babba ne da suka karbe shi da ku'di masu nauyi irin hakan?".
Shima a nutse ya ce "Babba ne ainun. Idan raba shi za'a yi zai yi fuloti uku manya. Sannan wajen ya yi daraja baya ga hakan a bakin titi wajen yake. Kar kuma ki manta tsawon shekaru biyu suka biya.
Shiyasa nake son na juya ku'din da ya yi saura mu dinga samun na abinci da sauran bu'katun yau da kullum.
Yaranmu gaba ka'dan makaranta za'a sasu, boko da Islamiya, kin ga duk hidimar ku'di ce. Ga yadda kullum rayuwar take sake tsananta. Akwai bu'katar na yi aiki tuk'uru. Sai na barwa Allah ya taimake ni a inda zan gaza".
A sanyaye na ce "Da ikon Allah na zaka gaza ba Baban 2. Ubangiji ya yiwa kokarinka albarka. Ya tsare ka da dukkan sharrin masu sharri. Allah ya raba ka da sharrin karfe da titi."
Ya rungume ni sosai ya ce "Ameen Maman 2. Ina son ki, ina alfahari da ke. Allah ya barmu tare cikin aminci".
Da rauni na ce "Ameen. Amma kasan ina shiga zullumin kada wata ta zo ta k'wace mini kai?"
Na fa'da hawaye na ziraro mini. Ya tsananta rik'on da ya yi mini ya tausasa harshe ya ce "me yasa kika karaya haka Asiya? Ban ji akwai wata mace da zata firgita ki ai. Ni naki ne, a hannunki na ke. Ki daina damuwa da abin da yake gaibu ne. Al'kawarin da zan miki d'aya ne. Har abada kin wuce wula'kancina. Kina da alfarmomi masu yawa da babu wata macen da zata samu irin alfarmomin ki a waje na."
Bai bar ni ba. Sai da na samu nutsuwa. Can kuma ya ke ce da dariya ya ce "Ubangiji yana ta kama mini Asiyata. Kamar yau take fa'din me zata yi da Basamude irina. Kin tuna amsar da na baki a ranar?"
Na k'yale shi domin yanzu ya riga da ya lakanci tuno mini abubuwan da suke kunyata ni.
Bai bar maganar kamar yadda na barta ba sai da ya ce "A lokacin na ce miki akwai ranar da zaki yi kuka akan son basamuden nan. Sannu a hankali komai na fa'da a kanki Ubangiji yana zartarwa. Na share ban yarda na tanka shi ba.
Cikin Ikon Allah Tijjani ya fara safarar kai kayan miya kasuwanni daban daban na cikin jahar Bauchi da makwabtanta irin su Jigawa.
Da wuri yake fita. Ya je ya kai. Idan zai dawo kuma sai ya lodo mutane. Gaba'daya ya ajiye girman kai, da tunanin yana da kwalin digiri.
Ba'a dauki lokaci mai yawa ba, muka rabu da matsalar babu. Domin sosai yake samun ku'di tunda ba balance yake kai wa ba. Ni ce ma na koya masa dabarar ya dinga ajiye wani abu a banki saboda ko watarana motar zata bukaci gyara. Ko wata lalurar zata gitto bakatatan. Ba ja in ja ya yarda da shawara ta. Akai akai yake yiwa mahaifiyarsa da Baban Marina sako. Dada ma bai barta a baya ba. Wani lokacin idan ya je Jos sai ya tsaya ya musu alheri, sannan ya taho. Hatta su Baban Tsakiya yakan yi musu alheri kai musu kayan miya ko doya.
Ku'di ne dai baya basu.
Wannan rufin asirin da ya samu ya sanya masu yi masa kallon banza suka shiga nan nan da shi. Akai akai ake bugo masa waya, sabanin lokacin baya da ba'a saka shi cikin mutane bare a tuna da shi.
Rannan kwatsam sai ga shi ya dawo da Nasiba tare da akwatinta shake da kayan da suke nuni zata jima tare da mu.
Na gama nazarinta. Gaba'daya ta goge ta yi fes da ita. Ta cika ko ina dam tabbacin yanzu tafi samun nutsuwa.
Ni ce shaida muka akan son da take yiwa Baban 2.
Na ha'diye komai na yi mata uzziri tunda shi so Ubangiji ne yake kitsa shi a zukatan bayinsa. Sannan a lokacin da aka zartar da aurena da shi bata yi mini koamai ba, sai fatan alheri duk da kuwa yadda al'amarin ya buge ta. Dan haka nima a yanzu zan mata kawaici ka'dan. Amma ban da aurensa. Wannan kam bazan iya ba. Na kuma tabbatar da niyyar hakan aka turo ta. Uwarta zata yi komai dan ganin Tijjani ya aure ta ba tare da ta jin kunyar ubana ba. Ta manta yadda ta ture komai ta yi sanadin datse soyayyarsu. A yanzu kuma da ake ganin ya samu mamora shine za'a lika masa ita. Ko kunyar ha'damu kishi bata yi. Kiri-kiri take nuna mini tsana tamkar wadda agola ce ni a gidan haka take yi mini.
Da daddare muna kwance gaba'daya na kasa sakin raina. Har shi ma na ji haushinsa ya turnik'e ni, akan wanne dalilin zai dauko ta tunda ga Toro su taho Bauchi?
Ya kasa ha'kuri ya ce "Little wai mene ne?"
Na yi masa banza. Ya tunzura ya ce "Amma dai kin san na tsani na miki magana ki share ni ko?"
Na kasa bu'de baki na ce mass komai a dalilin kuka nake yi irin na sharbe.
Jin shesshekar kukana ya sanya ya shiga rud'u.
Ya dinga tambayar ba'asin kukan nawa. Sai da na tabbatar na rikita shi matu'ka da gaske sannan na ce masa "A kan me za'a sa ya kawo mini Nasiba gida ba tare da yarda ta ba?"
A hankali ya ce "Dada ta ce na taho da ita ta mana kwana biyu. Ita ma kuma ta da'de tana fa'da mini tana son zuwa ta ga sabon gidanmu. Shine yau da ta ce zata biyo ni na ce to".
Na tashi na zauna na ce "Hakan ya yi. Wato har waya kuke yi ko Tijjani?"
Ya zuba mini ido sosai domin yasan tunda na gatsa sunasa gatsal to zan iya yin komai na rikici a tsakaninmu.
Ya sassauta ya ce "Dan ta zo mana bakunta mene ne a ciki?"
A tunzure na ce "akwai komai ma. Bana son bakuntar ta, ba kuma zata zauna mini a gida ba".
Ga mamakina sai ce mini ya yi "Wai gidan na ki ne?"
Na kad'u matu'ka da gaske. A matu'kar sanyaye na ce "A a naka ne mantawa na yi, amma ka tabbatar ba zan yarda da kai alhalin ina ganinku a gida daya ba." Na koma na kwanta, shi ma ya kwanta bayan ya juya mini baya da alamu ya yi matu'kar fusata da na ce Ban yarda da shi ba. Ya sani kuma ina da hujjar da zan guji zamansu a gida daya, mussaman karamin gida irin namu.
Washagari muka tashi kowa na ganin laifin d'anuwan sa. Na yi matu'kar boye wa Nasiba halin da muke ciki. Tare da ita muka karya a kwano daya. Tunda shi ya fice bai saurari abincin ba.
Da daddare ma hakan muka sake kwana babu jituwa. Domin nasan jira yake na ba shi hakuri, na kuma rarrashe shi. Ni kuwa al'amarin da yake cina ba k'arami ba ne.
Ko magana bama yi ni da shi.
Ba dan bana son ta fahimci akwai matsala a tsakaninmu ba da ko dakinsa ba zan je ba.
Amma ina zuwa bayan mun sha hira ni da ita.
Ranar da ta yi kwanaki biyu da daddare mun kwanta. Na bu'de baki na ce "Tijjani gobe bakuwarka zata yi kwanaki uku a gidanka. A ka'idar shari'a kuma bakunta ta kwanaki uku ce. To kasan yadda zaka yi ta bar maka gidan a gobe, ko kuma ka ga abin da baka so".
A tunzure ya ce ",Tun yaushe na ga abin da bana so Asiya? Ai tunda babu yarda a tsakaninmu magana ta k'are. Ba kuma zan kore ta a gidana ba. Ni da kika gan ni bana manta alheri komin tarin kalubale da rashin kirkin mutane. Dan haka komai zaki yi Bismillah".
Na ce "Hakane. Madallah da Tijjani".
Kasan zuciyata kuwa tamkar na tashi na cinnawa gidan wuta haka nake ji.
Washa gari ya saka kai ya fice bayan ya amsa gaisuwar ta a tsaitsaye ba tare ma da ya kalle ta ba. Haka kuma yake yi mata tunda ta zo.
Mun gama karyawa na kalle ta na ce "Nasiba zan je Kangire dubiya. Wata'kila na kwana, wata'kila kuma na dawo. Na tafi da yaran nan ko na bar miki su?"
Zucyarta daya ta ce "Ki barsu mana indai baza su yi rikici ba. Idan suna ganin Babansu baza su yi kuka ba ai babu damuwa".
Na ce "Hakane.
Na shirya kayana set uku a dan k'aramin akwatina, na yi sallama bayan na yi dabarar tura tagwaye kwaso shanya a baya. Na fice a hankali, bayan na ce mata na bar ki da wahalarsu kuma".
Ina jin ta tana fa'din 'yayanki ba nawa ba nawa ba ne ke nan Yabi?"
Ban tsaya bata amsa ba gudun kada su fito, su ga tafiya ta.
Da azahar ya koma gidan a dalilin ya dawo daga Dass.
Ya tarar da yara na kukan neman Amminsu. Ya fahimci Yabi ta fice ta bar gidan babu izininsa. Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi, ransa ya baci ainun.
Cikin hikima ya ce "Da nasan da wuri zan dawo ai bazan bari ta fita ba.".
Nasiba da take kicin ta ce "Nima da ta ce mini zata iya kwana a can na shiga zullumi."
Ya mik'e ya ri'ke hannun yaran suka fita, ya rasa inda zai tsoma ransa da wannan tashin hankalin da ya kewaye shi.
"Sha'anin mata yana da gigitarwa. Mene ne abin tafiya ki bar dakinki idan ba kalen masifa ba little?" Ya furta a fili a kuma ki'dime.
77&78.
Tsawon lokaci yana tunanin abin yi. Ya rasa inda zai dosa meman ta. Ya tabbatar ba zata nufi Toro ba.
Ya tambayi kansa to ina zata tafi har tana fa'din idan dare ya yi zata kwana?.
Kukan Hamim na sake rib'anya tashin hankalin da yake ciki.
Ga haushinta, ga zullumin fishinta gaba'daya sun ha'du sun yi masa rubdugu.
Ya mike ya shiga gidan, ya tarar ta kammala abincin da take yi. Ransa ya sake b'aci da abin da Yabi ta yi, wato manufarta ta bar musu gidan su yi komai ma.
Cikin rashin sukuni ya ce "Ha'da kayan ki zan kai ki tasha ki koma gida. Tafiya ta same ni zuwa gadar mewa. Ba zai yiwu kuma na bar ki ke ka'dai a gidan ba."
Cikin nutsuwa ta ce "To". Amma yaran fa?"
Cikin rashin sukuni ya ce "Zan kai su wajenta daga can, tunda hanya ce".
A hankali ta ce "To ko zamu tafi gaba'daya ina ajiye mu a wajenta sai mu dawo gobe da ita".
Da rawar ya ce "A a, mu je dai na kai ki tashar, ba zai yiwu na yi ta yawon kasuwa da ke ba."
Tunda ya ajiye ta a tasha yake gararanba a titunan Bauchi. Gaba'daya ya rasa ta inda zai fara nemanta.
Nasiba kuwa da ta Isa Toro a gidan Marina ta tarar da gyatumarta tare da Dada.
Cikin mamaki Dada ta ce "Ke da kika ce sai an gan ki kuma sai ki dawo, duka duka yaushe kika tafi ne?"
Cikin nutsuwa ta ce "Yabin ce ta tafi Kangire dubiya. Shi kuma ya ce na taho tunda kwana zata yi".
Dada ta ce "Ikon Allah. Ga kuma uwatata bata fadi wani abu ya samu ba, bare mu yi mata ja je".
Sai lokacin Baba Maryo ta ce "Hmm Wallahi ba abin da ya faru, kawai zamanta ne bata so a gidan. Shi kuma da yake salallamamme ne shine ya ce ki taho. Yarinya k'ank'anuwa sai azabar iya barikanci. To duk shure shuren kaza baya hana a dirza mata wuka. Yabi akwai tuggu Wallahi shi yasa na washe ta, bata da kunya ko kad'an bare mutunci".
***
Da azahar na dira a Bulkachuwa. Babah sai ganina ta yi kwatsam. A sanyaye ta shiga yi mini barka da zuwa. Sai da na yi sallah ta bani abinci da ruwa, na ta'ba ka'dan na rufe. Ta zuba mini ido ainun. Ta ce "Wai mene ne damuwar ki ne Yabi? Maimakon tunda yanzu ba shayarwa kike yi ba, ki murje ki cike, amma kullum sai fige wa kike yi tamkar wacce ake tsakurarki?."
Na yi k'asa da kaina, ba tare da na ce komai ba. A tausashe ta ce "Yanzu me yasa kika taho ba shiri ba komài?"
Na fara hawaye, ba tare da na bu'de baki na ce komai ba.
Ta ri'ke hannuna ta ce "Da ke da Ihisan daya nake jinku. Dan haka zan fa'da miki gaskiya. Gaba'daya aure hakuri ne. Ba yadda ake so ake ga ni ba. Idan Ubangiji yasa farin yafi ba'kin yawa a cikin zamantakewar sai a yi ta gode wa Allah. A kuma yi hakuri da inda aka kuskure. Idan kuwa ba hakan ba sai ki ga gidan aure ya zama tamkar kurku dan tsanani. Adadin mutuwar aure ya yi ta tunbatsa. Yin sassauci da kawaici babban jigo ne da yake rike da gidajen aure.
Cikin kuka na ce "Wallahi ina yi."
Ta ce "Na sani. Yanzu fa'da mini abin da ya yi miki har kika kasa hadiye wa"
Cikin kuka na tsara mata yadda muka yi da shi, ban yiwa al'amarin kwaskwarima ba. Da kuma kafewar da ya yi sai ta zauna da mu saboda tana da alkairai masu yawa a idonsa. Cikin kuka na ce "Ni kuma Wallahi bazan yarda na zauna da ita ba".
Ta yi shiru, na tsawon lokaci kafin ta ce "Tashi ki je d'aki ki yi kwanciyar ki. Kar kisa wannan maganar a ranki. Kina da gaskiya dan hakan zan tsaya miki, da kuwa baki da gaskiya da a yau zan mayar da ke dakinki".
Dad'i ya kama ni. Babah ta fahimci irin rad'ad'in da nake ji. Ina kwance ta shigo ta ce "Kuma sai kika bar mata yaran?"
Fuska ba walwala na ce "Eh". Ta ce "Da kin taho mini da su, ina cikin kewarsu ainun. Amma bar masa din da kika yi akwai hikima mai yawa tunda ba sha suke yi ba. Kukan Hamim kadai ya ishe su ai. Ki yi zamanki ba wanda zai san kina nan tunda Umman gidan nan tana garinsu tafi wata a can. Ko Nasiru ma baya gari. Aliyu ne ya ce zai zo yau, to kuma ya fasa sai satin sama, saboda zasu je Ibadan".
Ta dauki abin da zata dauka ta fice. Tana fa'din "Da ni yake zancen".
Sai da dare ya fara ja sannan ya koma gida. Bayan Nasiba ta masa text din ta sauka lafiya. Tunda ta kira shi ya fi sau biyar yana gani amma bai dauka ba.
Da asuba ya kira wayar Yaya Ummi.
A d'an tsorace ta ce "Yaya Bulkachuwa barka da asuba"
Murya na amo ya ce "Ummilolo taimake ni ki bani lambar mijinki na nemi izinin aikenki yanzu zuwa gidan Marina".
Ta ce yana jinka ma yanzu haka, na saka ta a sifika ka tambaye shi."
Ya bu'de murya cikin ladabi ya gaishe shi. Ya kuma roki alfarmar zai aiki Ummi zuwa gidan akan wani al'amari da tayar masa da hankali.
Nan da nan ya ce "Babu komai na amince ta je. Ya mika wayar ga Ummi.
Ta ce "Ya ya ne Yaya Bulkachuwa?".
Cikin zullumi ya ce "Asiya ce ta yi mini yaji Ummi! Tun jiya ta fice ta bar mini gidan da yara."
A zabure ta ce "Subhanallah a kan me Yaya Bulkachuwa?"
A sanyaye ya ce "Hmm! Kawai mu bar maganar tattauna wa ki tashi yanzu ki je gidan, ki duba ko ina. Idan kin ganta kada ki nuna komai kawai ki dawo gidanki. Ki fa'da mini sai na taho".
Yana rufe baki Ummi ta ce "Gaskiyar magana ban jin Yabi zata iya zuwa gidanmu da sunan yaji. Ta tsani yamididi, tana kuma matu'kar tsoron bacin ran Baban Marina".
Ya fesar da iskar damuwa ya ce "To saboda Allah ba kisan inda take ba Ummilolo?"
"Wallahi ban sani ba, ko waya bamu yi da ita ba. Amma bari na je sumame gidan Nazira".
Da sauri ya ce ",Yauwa Ummilolo, na gode, hanzarta dan Allah".
Ta ce "Zan sallami mutanan gidan da abin karyawa tukun".
Akan dole ya ce "To."
A hanzarce ta gama dumame ta sallami kowa.
Kusan da sanda ta shiga gidan Nazira domin ta tabbatar mijinta baya nan. Amma bata ga wata alama mai kama da rashin gaskiya ba. Suka gaisa ta tambayi yara.
Ta ce "Daga ina Yaya Ummi?"
Ta ce "Mafarkin ki na yi Nazira shi ne na taho dan na ganki, na ga lafiyarki".
Da'di ya kama Nazira. Ta ce "Madallah da Yaya Ummi. Kin kuma tarar da ni lafiya, har na karya na yi hidimar gida".
Ta mike tana fa'din "Alhamdulillah! Tunda na ganki lafiya bari na tafi".
Ta hanzari Nazira ta yi kicin dinta ta juyo mata dafadukan macaroni mai dan dama a madaidaicin filas. Ta ce ga shi ki kaiwa yaran nawa. Na maigidan ne bai tsaya karyawa ba. Ana ta jiransa zasu je Lame. Ya dai sha kunu a tsaitsaye."
Ta karba da godiya ta tafi. Maimakon ta zarce gidan ta, gidan Marina ta yiwa tsinke. Duk wani bin kwakkwafinta bata ga ko ganin wata alama da take nuna sun san Yabi bata gidanta ba. Dan haka suma ta yi musu sallama ta tafi ba tare da ta bu'de musu komai ba.
Sai da ta isa gidanta sannan ta kira Bulkachuwa ta tabbatar masa Yabi bata zo Toro ba. Ya lalube ta anan Bauchin.
A rikice ya ce "Yanzu Ummi abin da Asiya ta yi mini dai-dai ne?"
Kai tsaye ta ce "To ai bansan me ya faru ba Yaya Bulkachuwa".
Ya ce tsaya ki ji, ki fa'da mini inda nake da laifi, ki kuma fa'di shin ta kyauta mini kenan?"
Ta ce "To zan fa'di gaskiya tsakanina da Allah kuwa".
Ya numfasa ya shiga koro mata bayani tiryan tiryan na gaskiya.
Bata katse shi ba sai da ya gama tsaf ya ce "kin ji abin da ya faru".
Ta numfasa ta ce "Ka yarda gaskiyar magana zan fa'da?"
Da sauri ya ce na gasgata ki Ummi. Komin tasirin jini na sani zaki yi adalci domin ke din mai kauna ta ce na shaida."
Ta ce "Na gode sosai. Amma gaskiyar magana kai ne baka kyauta ba. Kasan Yabi tasan akwai tsohuwar soyayya tsakaninka da Nasiba. Yanzu Kuma bata da aure. Akan wanne dalilin zaka dauke ta da kanka ka kai ta gidanka da sunan ta zauna, ba zama irin na bakunta ba.? Me yasa da Yabi ta ce bakuntar kwanaki uku ta amince ta yi muku baka yarda kun fahimci juna ba? Me yasa ka ankarata ta hanyar ce wa Nasiba tana da darajar da ba zaka kore ta a gidan ka ba?. Tsakanina da Allah wannan maganar ta yi nauyi a zuciya. Ai da sai ka ce mata ita ta kore ta, shi kenan magana ta k'are."
A sanyaye ya ce "Na gode na kuma yarda na yi kuskure. Amma me yasa ta zarge ni?"
Kai-tsaye Ummi ta ce "Kai ka bada k'ofar. Me yasa dan Nasiba zata zo gidanka sai ta hannunka zata biyo? Ba Yabi ce matar gidan ba? Me yasa sai da kanka zaka kai ta? Me yasa ka kausasa harshen ka akan zamanta?"
Ya ce "Yanzu dai Ummilolo Yabi ta yi dai-dai da ta fice ta bar gidan babu izinina?" Ta numfasa sannan ta ce "A fuskar shari'a bata kyauta ba. Amma tunda ni mace ce nasan yadda take jin zafi a zuciyarta bata yi laifi ba, tunda ka nuna wacce bata zama dolen ka ba sai ta zauna mata a gidan ko tana so, ko bata so, ba tare da rarrashi ba".
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Na gode sosai Ummi. Na kuma gamsu da wannan gaskiyar ta ki babu son kai a cikinta. Kuma yanzu hakan tun jiya na saka Nasiba a mota ta dawo Toro. Na sallame ta a kurarerren lokaci ko?"
Nan ma Ummi ta ce "Eh, baka girmama ra'ayin matarka ba, sai da ka bari ta yi maka tutsu, hakan kuma zai haifar muku da tazara da tsatsar zuciya mai yawa".
Cikin karaya ya ce "Na gode bari na shirya yaran nan, mu fita nemanta, ki taya ni addu'a, gaba'daya yarinyar nan ta gigita ni. Wato Yabi jidalinta mai girma ne."
Ummi ta kwashe da dariya ta ce ni fa ban ga laifinta ba Yaya Bulkachuwa. Haka kawai za'a lallaba a yi mata kutse mai dafa zuciya, da saka jinya a gangar jiki".
Ya numfasa ya ce "Allah ya sauwake, ni Wallahi babu tunanin komai a zuciyata akan hakan".
Ta ce "Kai kasan hakan, mu ina muka san zuciyar ka?"
Ya ce "Shi kenan bari na saka d'ambar neman ta."
Suka yi sallama, ya kashe wayar tare da zurfafa a tunanin ta inda zai fara nemanta.
A daddafe ya yi wanka saboda azabar kukan Hamim. Domin a bakin band'akin ya zauna yake kuka na tashin hankali. Hanif kuma sai ri'ke shi yake alamun wai ya yi shiru.
Dan haka ko da ya fito a rikice ya shirya, ya dauki yaran da yake ta gunjin kuka.
Yasan kukan neman Amminsu yake yi. Allah ya zuba masa k'ulafacin uwa. Ya gama shawo kan Hamim ya yi shiru, sai kawai Hanif ya fa'di ya dan bugu a goshinsa. Ya fara kuka shi ma.
Hamim da dama kukan ba daina shi ya yi gaba'daya ba, sai kawai ya bu'de baki yana taya Hanif. Suka rikice masa ainun.
Ya jima kafin ya samu su tsagaita. Shi da kansa ya fahimci d'a sai uwarsa. Duk da yadda ya iya raino. Amma rashin Yabi a tare da su sai komai ya k'wace musu daga shi har y'ay'an sa.
Har suka bar gidan bai yanke shawarar inda zai dosa ba.
Amma yana hawa titi zuciyarsa ta fi rinjayar masa ya je Bulkachuwa.
Dan haka gidan mai ya shiga ya sha mai. Ya siya wa yaran yoghurt da cake. Sannan suka dau hanya. Yana yi yana daukar fasinja dan ya samu sau'kin tsadar mai.
Da walwala Babah ta karb'e su. Tana ta tambayar ya aka yi suka baro Yabi a gida ita kad'ai?
Ya dan diririce, bayan ya ga rashin wasa a fuskarta. Murya babu karsashi ya ce "Bata jin da'di ne shi yasa bamu taho tare ba, nima kayan miya na kawo nan Dambam".
Ta ce "Ayyah me ya same ta? Ko zazzabin damina ne da ko ina yinsa ake yi".
A sanyaye ya ce "zazzabin cizon sauro ne, amma da sau'ki rashin k'warin jiki ne kawai."
"To Ubangiji ya bata lafiya". Ya amsa da Amin cikin damuwar to ina Yabi ta fantsama kenan?
Ya kasa ko da shan ruwan da yake gabansa bare kuma abinci. Yara dai suna ta cin abincinsu.
Ta zauna tana fa'da masa sati mai zuwa Aliyu zai je Ibadan yin jarabawar zama likita, tunda karatun likitanci yake yi a jami'ar Jos.
A gajarce ya yi murna da fatan alheri. Ta fahimci rudun da ya shiga amma ta matse ta yi kamar bata gane ba.
Ya sassauta murya ya ce "Tafiya zan yi, zan bar yaran a nan, zuwa jibi zan dawo".
Cikin nutsuwa ta ce "Haka kawai ka dauko su babu shirin zasu zauna ka bar mini su? Uwarsu ba zata ji dadi ba".
Ya basar ya ce "Ko ba wajen ki na kawo su ba, har ta yi mini inkarin inda na kai su bare kuma wajen ki ne".
Da azama ta ce "Wallahi ba zaka bar su ba, tunda kai ma ba da nufin su kwana ka taho da su ba. Kaya kala daya ka sako musu a leda. Nasan kuma idan sun bata na jikinsu a sauya musu ne iya yau. Ka bari idan ka shiryo su da kayansu sai su zo mini, amma ba haka kawai a shiga hakkin uwa da y'ay'an ta ba".
Ya rasa yadda zai yi, a kan dole ya kwashe su suka juya.
Ni da nake mak'ale a daki, zuciyata sai tsalle take yi a kan na ga yarana. Da k'yar na daure ban fito ba.
Da suka tafi kuwa sai na ji tamkar na ruga a guje na ce "Ga ni nan".
Na kwanta lamo. Ina kallon silin. Babah ta shigo yanayin da ta ganni a ciki sai ta yi turus. Ta iso ta zauna a gefen k'afafuwana. Ta sassauta murya ta ce "Nasan zaki so yaranki a tare da ke. Amma ki daure ba jimawa zaki yi ba. So nake ya rikice gaba'daya, ta yadda da kansa zai zo da bakinsa ya fa'da mini ba kya tare da su.
Har da ce mini wai kina gida zazzabi kike yi".
A hankali na ce "Idon Hamim ya yi ja?"
Ta galla mini harara ta mik'e ta na ce wa "Ban sani ba. Idan kuwa haka zaki mini, ki kuntata kanki sai ki zo ki bi bayansu kawai".
Ta fice tana ta sababin masifar son y'ay'a da iyayen yau suka mak'alawa zukatansu.
Da gaske dai mace tana saurin yin afuwa ga namiji a dalilin yaranta. Domin tun yanzu na fara kewarsu. So nake na bu'de ido na ga suna wasan hawa da sauka a jikina.
Na fesar da iskar damuwa. Na sani daga shi har yaran suna cikin kewata mai yawa. Barin ma sarkin kuka da k'ulafaci Hamim.
Haka na zauna, ina jin wani irin abu na bina.
**
Bulkachuwa kuwa da k'yar ya isa Bauchi domin ya shiga rudun inda zai ga Yabi. Ya kira wayarta yafi sau goma ana fa'da masa a kashe take. Amma ya kasa dainawa.
Suna isa gida, dakinta ya dire. Yaran da suka waiwaya basu ganta ba, suka dinga kuka a tare. Shi kansa ji yake tamkar ya bare baki ya tayasu. Gaba'daya azanjinsa ya k'are. Da k'yar ya shawo kansu suka yi shiru. Kwanaki biyu yana tiritiri da su. Sa'ar da ya yi ma ya riga ya saba da hidimarsu. Jiya a Toro suka yini, yana bulayin yiwa gidajen mutane dirar mikiya ko zai ga Yabi. Amma shiru tamkar Malam ya ci shirwa.
Komai ya tsaya masa cak. Kan dole ya sake komawa Bulkachuwa da su.
Ya rasa ta yadda zai fa'dawa Babah Yabi ta gudu ta barsu.
Ya gama kame kamensa ya fa'da mata gaskiya sun samu sabanin fahimta da Yabi ta yi yaji, ya kuma neme ta ya rasa tsawon kwanaki uku kenan.
Ta dauki salati mai tsananin gaske. Ta dake ta ce "Yarinyar da ubanta ya damka mini amanarta a hannuna ka yiwa sanadin da ta gudu ta fantsama duniya?"
Ya yi tsumu ya rasa me zai ce. Ta ce "Sai ka fa'da mini abin da ka shuka mata har ta kasa ha'diye wa ta bar maka wadannan yaran da suka shiga ranta. Ta tafa hannu tana skae kambaba girman lamarin. Fadi take yi "Duk uwar da tafi ta bar k'ananun y'ay'anta ai ba'kin cikin da take ha'diye wa ba ka'dan ba ne. Tura ce ta kai bango".
Ya kasa ce wa komai. Illah zufa da take yanko masa tamkar mai hadiyar kunama.
Cikin bacin rai ta ce "Ya ya ina magana ka mini shiru sai zare ido ka ke yi irin na rashin gaskiya".
Murya babu amo ya ce "Wallahi ba komai na yi mata ba. Nasiba ce ta zo shike nan ta kwarzabi kanta."
"Ta kwarzabi kanta kamar ya ya?"
Ta tambaya cikin wani irin yanayi na bacin rai mai yawa.
Ya numfasa ya ce "Ce wa ta yi sai na kore ta. Ni kuma na ce bazan kore ta ba. Shi kenan na dawo na tarar ta bar gidan".
Ta rausayar da kai ta ce "To ai Yabi
ta yi adalci. Sai da ta fa'da maka bata son zamanta. Kai kuma ka nuna kana da bu'katar ta zauna a gidan tunda naka ne. To mene ne kuma dan ta fita ta bar muku gidan ku tabbata a ciki?".
Ransa ya baci ainun. Ita ma bata fahimce shi ba. Su duk haka mata su ke da kishi ne?. Basa fahimtar komai matu'kar akan kishi ne.
A hankali ya ce "Yanzu dan Nasiba ta zo shi kenan sai ya zama masifa? Ta ce sai ta bar gidan? Duk zamanmu da ita bata gasgata ni ba ke nan? Ni ba kula ta nake yi ba, bare ta ce ta fahimci wani abu a tsakaninmu. Wallahi saboda sababin Yabi ko kallon inda ta ke bana yi. Amma hakan bai yi mata. Shin Nasiba ba zata zo gidana ba, ba yar'uwa ta ba ce?".
Babah ta girgiza kai ta ce "K'warai yar'uwar ka ce ta gaske tunda har ka zabi fishin matarka akan ta. Madallah da Yabi bata za'bi zaman muzanci ba. Ta daga hannuwanta sama ta ce "Allah kasa yarinyar nan tana hannu na gari. Allah kasa tana Kangire ko kaduna gidan Jabir".
Nan da nan ya muzanta. Ya kasa yin shiru ya ce "Kaduna! Ya fa'da cikin takaici mai yawa.
Ya kasa yin shiru da rawar murya ya ce "Na rantse idan aka same ta a Kaduna duk masifarta sai ta ga ne bata iya komai ba".
Ta galla masa harara ta ce "To me zaka yi ne? K'arshe dai ka sake ta. Ni kuwa Wallahi tana gama idda zan bada aurenta ga saurayi ma, don bazan yarda ta fita daga ahalina ba."
Idonsa ya kad'a ya yi jawur. Da rawar murya ya ce "Babah a gabana kike nuna zaki bawa k'anina auren matata?"
Ta bu'de murya ta ce "Na fa'da na ji ruruf!".
A matu'kar ki'dime ya ce "Allah ya huci zuciyarki. Allah ya tsare ni aikata irin wannan BAK'AR TA'ADA din".
Ya bata tausayi ainun. Amma ta cije ta ce "Akan idona uwar Nasiba ba abin da bata fa'da akan ka ba. Ita ta hana a baka aurenta saboda suna ganin ka baka da mamora. Amma Yaya Sani ya juyawa dukkan nak'asunka ya tursasawa Yabi auren ka sai kuma dan ka fara samun dama, ka fara shiga sahun mutane sai a yi maka shunen ta har cikin gidan Yabi! Ta yi shiru. Saboda yadda zuciyarta take jin tsananin zafin yadda aka tado mata tsumin bacin rai na tsawon lokaci.
Ta zuba masa ido wanda rabon da ta yi masa haka ya manta.
A kaurare ta ce "Nasiba ba matarka ba ce, ko bayan raina ba zata zama matarka ba. Shari'a ta halasta ka aure ta babu aibu a cikin hakan. Amma kuma shariar da kanta ta ce "ku girmama ra'ayin iyayenku sama da naku. Matu'kar ina da hak'ki akan ka Wallahi na haramta maka ita. Soko marar tunani. Har ka manta tozarcin da uwarta ta yi mini akan maganarku?"
Hankalinsa a matu'kar tashe ya ce ", Wallahi Tallahi ba ni da manufar komai akan ta. Dan Allah ku fahimce ni mana"
"An k'i a fahimce kan. Ban da sakarci me ya kai ka taho da ita tunda ga Toro har Bauchi ku ka'dai ka kawo ta gidan ka. Ai sai a rasa gane wace ce matar gidan tunda sai ta goyi Yabi da zani tsab. A kan wanne dalilin da ta ce ba zata zauna mata a gida ba, ka kafe sai ta zauna d'in? Ban da munafunci irin na ku na maza. Na gode wa Yabi da ta fahimci bata da daraja a wajen ka. Ta fice ta bar maka gidan".
Da rawar murya ya ce "Allah ya huci zuciyar ki. Na yi kuskure a yafe ni dan Allah. Tun ranar kuma Nasiba ta tafi, da kaina na ce tafi din"
Ta ja tsaki mai tsananin gaske tare da fad'in "Ta baya ta rago".
79&80
Ya yi shiru ya kasa ce wa komai. Haka ita ma. Yara ne kawai su ke ta wasa a tsakaninsu. Sai iskar fanka da take kadawa da karfi sosai. Amma hakan bai sa zufa ta daina yanko masa ba. Gaba daya ya shiga rudani mai yawa. Ya rasa inda Yabi ta gudu. Ga magaganun Babah masu tsauri. Wanda hakan yake alamta masa yana cikin fishinta.
A sanyaye ya sake bata hak'uri tare da matsar da jakar kayan yaran gabanta. Ya mik'e ya faki kallon yaran da suke wasan tsere a tsakaninsu. Ya ce "Zuwa gobe zan dawo".
Galala ta kalle shi ta ce "Dauki jaka da y'aya'nka. Ai ba zai yiwu ka kori uwarsu da baki cikinka ba. Sannan ka saka rai zan maka wahalarsu. Wato na zama shasha ma!
Ya koma ya zauna ya sassauta murya ya ce "Haba mana, dan Allah ki ji tausayi na. Gabadaya nutsuwa ta yi mini tutsu. Idan na barsu ma ba wai hutawa zan yi ba. Neman ta zan cigaba da yi. Gobe Kaduna zan tafi".
Cikin rashin nutsuwa ta ce "To ka tafi da su, ko ka fara kai su Toro wajen Nasibar sai ka wuce. Amma Wallahi ko gwaggonsu ka kai wa yaran nan, ni da kai ne".
Ya yi shiru, idon sa ya kad'a ainun, ya koma ya zauna. Murya babu amo ya ce "Ki yi hakuri dan Allah Babah."
Ta jijjiga kai ta ce "A kan Yabi Bilhillazi zan yi matukar saba maka. Zan fita a sha'anin ka gabad'aya."
Ya yi shiru. Amma ransa suya yake tamkar ya fad'o kasa.
Me ya yiwa Yabi da zata janyo masa irin wannan jidalin?
Ya dinga bata hak'uri. Da k'yar ta ce sai ya gano Yabi idan ta huce, sannan ita ma zata hakura." Ya mik'e da sauri yana fad'in "Na gode sosai. Bari na tafi neman ta da ikon Allah zan nemo ta".
Daidai lokacin Hamim ya fasa kuka yana nuna windo. Tare suka isa gare shi, suna fad'in mene ne?"
Shi dai Hanif yana tsaye, yayin da Hamim yake kuka tare da nuni da saitin windo. Nan da nan zuciyar Baba ta tsinke domin ta gano kayan Yabi yake nuna wa akan igiya. Ma'ana ya gane kayan uwarsu, a ba shi ya rik'e mata.
Nan da nan ta dauke kai, ta shiritar da Tijjani da ce wa "Tofa masa addu'a mana, watak'ila shaid'anu ke son bude masa ido. Allah ya tsaremu daga sharrin abin da bama kallonsu".
A gigice ya hau tofa masa falaki da nasi. Yaro kuwa sai zabura yake akan zai je ya dauko abin da yake ganin na uwarsa ne. Yayin da Babah take ta hirji tare da addu'ar kada Yabi ta kasa jure kukan Hamim da yake d'ada canyarwa tamkar gyare ta fito. Ita da kanta ta gane irin kukan da Yabin ta yi tana yarinya ya gado.
Ta ce "Dauke shi ku tafi. Idan ya ga kun shiga mota zai yi shiru."
A raunana ne ya ce "Yadda ya razana hakan zan tafi da shi? Ki yi hakuri na bar su a nan, gobe ko jibi da ikon Allah zan dawo na dauke su. Ko ban ganta ba.
Ta ce "A a ba fa zan rike su ba. Ai idan kasan zan rik'e maka yara ka dinga shagulatin bangaro da auren ka kenan. Ina ce lokacin da suke hannuna ka fi uwarsu nuna zalamar na baku su? Yanzu kuwa ba zan karbe su ba."
Kamar zai rushe da kuka ya ce "Gobe Kaduna zan je Baba."
A gajar ce ta ce "Tafi da su ka kai wa Ihisan. Idan ka dawo ka je ka dauke su".
A kan dole ya sunkuya ya dauki Hamim. Ya rike hannun Hanif. Bayan ya saba jakar kayansu. Yadda ya d'ebi yaran da jakarsu sai tausayinsu duka ya kama ta.
Suka fita, sai da suka jima da fita. Sannan ta bude dakin da Yabi ta ke. Ta tarar da ita zaune akan gado tana faman goge idonta tabbaccin kuka take yi.
Ta k'arisa kusa da ita. Ta ce "Yabi kuka kike dan ina kokarin ya fahimci muhimmancin ki a rayuwar sa da ta y'aya'nsa?"
Da wata irin tab'ara da kuka na ce "Ai da sai ki karbe su. Kukan Hamim kad'ai abin dubawa ne".
Ta yi galala ta zuba mini ido ta kasa ce wa uffan.
Na kuwa matse na ce "To ni dai na huce tunda haka ne. Ai ya yi ta zuwa, na kuma san yana cikin tasku, sai ki zaunar da mu, a mayar da zan ce, ki yi masa fada, mu tafi."
Ta jijjiga kai tare da ce wa "Ban yi hakan ba Yabi. Ba kuma zan yi ba".
Na kuwa juya na kwanta ina kunkunin bazan sake yin yaji na zo nan ba, tunda ba sulhu zata yi ba".
Ta dinga salati tana tafa hannu. Tare da ce wa "Ban ga laifinki ba. Amma zaki ga karshen iyashege. Dauko hijabin ki, ki bisu. Na bata rai tare da daure fuska ainun. Ta sassauta ta ce "Ba fishi na yi ba. Tunda laifin kaina zai juye to kawai ki bisu. Duk tsamin ran da nake taya ki, baki yaba ba, bare ki bani hadin kai mu yi maganinsa da kyau".
Murya na rawa na ce "To ai da sai ki karbi yaran Babah".
Ta bude murya ta ce "Na ki karbar tasu. Ina ce ke kika barsu a gidansu? Kuma ba a hannun ubansu suke ba tabbatacciyar marar ta ido!"
Na yi shiru amma dai fuskata a daure.
Kafin ta yi magana sai kukan Hamim muka jiyo tabbacin sun dawo. Kafin Baba ta fita har sun shigo falo.
Da azama ta fita tana mini kashedin kada na fito da hannu.
**
Turus ta yi ganin Hamim na rike da riga da hijabin Yabi a hannunsa, ya kuma sassauta kukan da yake yi. Sai ajiyar zuciya yake faman saki.
Kafin ta ce komai Hanif ya ruga ya dauko takalman Yabi da suke gefen falon. Shi ma ya rik'e.
Tijjani ya samu nutsuwa domin ya tabbatar tana gidan.
Yayin da Babah ta kasa ce wa komai.
Cikin nutsuwa Tijjani ya ce "Ashe ba shaid'anu ya ke nuna mana ba. Kayan ta ya ga ni. Har mun fita ya tsananta kuka, ya kuma k'i yarda ya shiga motar. Sai hannuna yake ja. Na yarda na biyo shi muka dawo, sai kawai ya kai ni baya wajen kayan. Anan na fahimci kayan Yabi ya ga ni. Dan Allah Babah ki yi hakuri, ki ji tausayinsu ki basu uwarsu."
Ta yi kicin kicin ta ce "Idan ka ganta ba sai ka daukar musu ita ba. Ai tunda har zaka wulakanta Yabi irin haka, tabbas nima zaka wulakanta ni. Dan haka ba zan zuba ido ka fara mata cin kashi bayan ta gama shanye wahalar ka ba".
Ta rik'e hannun yaran ta tura su cikin dakin. Domin sun bata tausayin yadda suka rik'e kayanta gamgam. Kayan da shafa'a ne ya sanya aka barsu har yaran suka ankarar da ubansu.
Suna shiga ta janyo k'ofar ta zauna akan kujera, ta tsare gida ainun.
Ya rasa ta yadda zai fara yi mata magana.
Tsawon lokaci kafin ya tausasa harshe. Ya ce "Ina sake baki hakuri. Tunda wannan ne karon farko da ta kawo miki karata a zamanmu da ita. To ki yi mini uzziri a wannan karon . Ni kuma na miki alkawarin ba zata sake kawo miki karata akan wannan matsalar ba. Ki yi hakuri dan Allah".
Jikinta ya yi sanyi. Mussaman da ta zuba masa ido ta ga ya fada ya kuma birkice gabadaya.
Ya dinga magiya. Da ban baki tamkar zai rushe da kuka tsabar tsananta rokon da ya yi.
Rauni irin ma uwa ya shige ta. Ta furzar da iskar takaici. Ta ce "Ba dan ta yi hankalin tahowa nan ba. Da an yi ta yamididi da murnar ka yi kudi ka fara wulakanta ta. Da wanne idon zamu Kalli iyayenta da suka yi alkunya da kawaicin baka auren ta? Ta dinga yi masa fada da togaciya tamkar zata bige shi. Yayin da shi kuma yake fad'in "Ki yi hakuri zan Kiya ye da ikon Allah".
Ta tashi ta nufi daki. Ya yi maza ya mik'e ya bi bayan ta a d'arare tare da fargabar kada ta dakatar da shi.
Tana tsakiyar gadon. Yayin da Hamim yake kwance kan cinyarta. Hanif kuwa sarkin hakuri filo kawai ya yi da cinyar jikinsa na kan gadon. Daga ita har yaran kowa ya yi shiru tabbacin suna cikin alhini.
Baba ta sassauta murya ta ce "Yabi ga shi nan ku sasanta. Idan kin ga zaki yi hakuri ki bisu to, idan kuwa kin ga ba zaki bisu ba. Ba zan matsa miki ba. Ban san me kike hadiye wa ba".
Ya rasa inda zai tsoma ransa. Murya babu amo ya ce "Amma na baki hakuri fa".
"Dan ka bani hakuri sai na tirsasa ta?"
Ta jijjiga kai tabbacin ba zata mini dole ba.
Ya sassauta murya ya kalle ni ya ce "Asiya ki yi hakuri da abin ya faru. Na yi kuskure duk da dai fahimta ta ne baki yi ba".
Yana rufe baki na ce "Ba zan fahimta ba."
Babah ta yi shiru tana kallonmu. Watak'ila kuma mamakina ta yi na yadda na kame kamar ban gan shi ba tamkar ba yanzu na gama yin tijarar na huce ba ".
Ya munfasa ya ce "shi kenan ki yi hakuri." Ya furta a hankali.
Babah ta zame ta fice.
Yana ganin hakan ya matso kusa da ni ya zauna. Ya rage murya ainun ya ce "Saboda Allah little ya kamata ki bar dakin ki babu iznina?"
Na galla masa harara na dauke kai ban ce komai ba.
Ya sake tausasa harshe ya ce "Tashi mu tafi, idan mun je gida sai ki yi mini ko wanne irin darun ni kuma zan yi ta rarrashin ki, da kalolin soyayya masu tsayawa a rai."
Na ja tsaki tare da fad'in "Na bi soyayya da gudu. Ni yanzu bana son ka, kai ko ganin ka bana kaunar na bude ido na yi".
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Tom shi kenan, ki dawo dakinki dan yaran ki, ko ban ci arzikin komai ba ki dawo dan y'aya'n ki".
Na dauke kai na ce "Idan na mutu zasu fasa rayuwa ne?".
Ya rik'e kafata da tafi kusa da shi. Na goce da sauri. A tunzure na ce "Kada ka kuma tab'a ni. Ka je ka cigaba da damukar wadanda suke da daraja a wajen ka".
A zafafe ya ce "Na cigaba Asiya?".
Na dauke kai na ce "Eh".
Murya na rawa ya ce "Kin ga na damuk'e ta ne? Me yasa kike son jifa na da wannan mummunar maganar ne?"
Ba ja in ja na kalle shi na ce "Saboda ina da hujjoji na gaskiya. Sannan idan ba hakan ba, me yasa zaka kawo mini wannan suntumemiyar cikin gida? Har kuma kana kumfar bakin ba zaka ce ta tafi ba, saboda ta yi maka alkhairai. Fada mini alherorin da ta yi maka dan kuwa ban sansu ba".
Ya kafe ni da ido. Cikin matsanancin bacin rai ya ce "saboda kin fahimce ni a baibai shi yasa kika taho babu izinina, sannan kike kallon idona kike jifana da alamarin da kika san na tsani a jingina mini. Me yasa kike son ki dinga tayar mini da hankali ne Asiya?"
A tunzure na ce "Saboda ba ni da alheri a wajen ka sai sharri. Yanzu ba sai ka sakawa Nasiba da kalar naka alherin ba. Ni kuma ka bini da irin nawa sharrin ba".
*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Saiwowin maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
Ya jima bai iya ce wa komai ba. Da alamu kokawa yake da zuciyarsa. Domin fishin da ya ke shimfide a fuskarsa ya kai intaha.
Tsawon lokaci mun yi shiru. Yaran kuwa duk sun yi barci.
Ya munfasa ya ce "Ki yi hakuri. Na baki hakuri. Tashi mu tafi, na yafe miki".
Na sake hade rai na ce "Ba na son ka yafe mini, domin ban maka komai ba. Ban zalunce ka ba. Kai ne ka ke shirin zalunta ta. Shi yasa na saukaka maka hanyar rabuwa da ni. Kawai ka sallame ni, ba zan iya zaman zullimi da fargaba ba. Tunda ka fara samun kudi ka ke canjawa. Nan gaba bansan yadda zamu kwashe ba. Gara tun wuri na barka tun baka gama barina ba ".
Murya babu amo ya ce "me nake yi miki Asiya?"
Baka yi mini komai. Son ka ne ba na yi! Ko dole ne?"
Ya mik'e tsaye ya ce "Babu dole, to ba ni yarana".
Na rungume Hamim da yake ta barci yana sakin ajiyar zuciya. Na ce "Ba zan bayar ba, dauki Hanif shi kenan an raba."
Nan da nan ya hau rantsuwar ba zai bar shi ba. Ba zai raba su ba. Na dage tamkar har cikin zuciyata da gaske nake yi. Sosai muke yin takaddama.
Sai da na gama famfa shi. Ya sakankan ce bazan iya yarda ya tafi da su ba.
Sai kawai na ce "Dauke su ku tafi, Allah ya shiga al-amarinsu."
Nan da nan ya yi turus. Jikinsa ya yi sanyi ainun. Ya zuba mini ido tsawon lokaci, ni kuma na yi kamar ban ga ni ba.
Ya koma ya zauna a maimakon mikewar da ya yi, yana kumfar bakin sai na ba shi y'aya'nsa.
Ya sassauta murya ya ce "Na baki hak'uri fa little. Ki mini uzziri mana".
Murya na rawa na ce "Sau nawa ka ke yi mini laifi ina share wa?"
Da sauri ya ce "Da yawa. Ina kuma gode miki. Na kuma dha fad'a miki kina da alfarmomi masu yawa a waje na. Yanzu ki mini hakuri dan Allah. Bazan sake yin hakan ba."
Na hirgiza kai tabbacin ban karbi ban bakinsa ba.
Ya marairaice ya ce "Haba mana my little angel. Ki huce, kin san fishin ki kassara ni yake yi".
Sai lokacin na ji kuka ya zo mini. Na dinga yinsa bilhakki. Tsawon lokaci sannan na daina. Ya saki gauron numfashi ya ce "very sorry little. Nasan kin huce, tashi mu tafi dan Allah".
Na girgiza kai na ce "Ni kam bazan koma ba fa. Ai tunda har waya ka ke yi da ita, nasan akwai abin da zai biyo baya. Dan haka ka je na bar mata kawai."
Ya diririce ainun. Ya fara musun basa waya.
Na zuba masa ido na ce "Waye ya ce mini Nasiba ta ce da Dada za'a zo ganin gida?"
Ya ce "Ni ne".
"Me yasa ni bata fada mini a wayar ba? Me yasa kullum sai ta kira ka? Me yasa sai kai Tijjani? Tunda bata kirana, bata kiran Yaya Salisu da ragowar. Na tsani rashin kame wa".
Ya kasa magana tsawon lokaci. A sanyaye ya ce "Ba ni da bakin magana , am speechless. Abin da zan iya ce wa biyu ne. Ki mini uzziri, ki yi hakuri."
Na yi shiru. Cikin rarrashin ya ce "Wallahi duk hasashen da kuke yi ni ban tab'a d'arsa shi a raina ba. Amma na gamsu kin fini gaskiya. Idan kika yarda muka tafi yanzu kuma. Na miki alkawarin har kasa ta rufe idona babu magana mai tsayi a tsakanina da ita bare soyayya ko aure, In sha Allah ".
Na yi k'asa da kaina, ban ce komai ba, amma kuma k'ullin zuciyata ya hau warware wa".
Ganin rarrashin ya fara tasiri. Ya sake tausasa harshe ya ce "Ai ni na dauka babu abin da zan yi miki, ki yi mini yaji. Tunda baki kai hakan ba ma, na miki babban laifi, kika rufa mini asiri kika yafe mini. Amma yanzu kuma a kan zato da zargi kika tozarta ni. Me yasa zaki munana zato a kaina? Me yasa kika zabi ki janyo mini fishin Babah?"
Yana rufe baki na ce "saboda ka fahimci ban dauki alamarin da wasa ba, ka kuma gane yanzu hankali ya fara ratsa ni. Ba komai zan lamunta ba".
"A karo na ba adadi ina sake baki hakuri. Allah ya huci zuciyar ki. Dan Allah mu rufe wannan matsalar. Wallahi bazan sake yi miki hakan ba, babu ruwana da ita, ko kallon inda take bazan sake yi ba. Ko na ganta a wajen Dada idan ta gaishe ni, zan amsa ne ba tare da na kalle ta ba, bare na gane me take ciki".
Na yi shiru. Ban tanka ba. Ya ce "Haba mana Little"!
Na cuna baki na ce "To kuma wayar da kuke yi fa?"
Da hanzari ya miko mini wayar yana fad'in duba ki ga ni. Na share lambarta. Na kuma jefe lambar a black list ta yadda ita ma ba zata same ni ba".
Na yi shiru ya ce "please mana Little ki ce kin huce, ki ce komai ya wuce".
Na dauke kai na ce "To kuma iyakar da ka nuna mini fa? Da ka ce gidan ka ne ba nawa ba?"
Da rawar murya ya ce "Kinsan An nadamu ala ma fata? To hakan maganar ta ke. To ni me ma zan yi da gidan da babu ke a cikinsa? Idan wannan maganar ne ta sake b'ata miki rai to ki huce. Na baki gidan ma gabadaya. Ki yi yadda ki ke so a cikinsa. Shi kenan?"
Na ce shi kenan, amma bazan koma yau ba".
Da hanzari ya ce "A a kada mu yi hakan, yanzu zamu tafi idan ba so kike hankalina yafi hakan tashi ba."
A hankali na ce "To kawai sai Babah ta ga zamu tafi? Ka bari idan na fada mata jibi sai ka dawo mu tafi".
Da azama ya ce "Wallahi bazan iya ba, kada ki zalunce ni, kin sani bazan iya ba. Tunda mun shirya ina ruwanta da mu?"
Ya mik'e yana ce wa "bari na je na fada mata zamu tafi".
Na bi bayan sa da kallo. Ina jin fishin da na yi da shi yana warware wa.
Na zuba wa yaran ido. Ina rasa ga ne wa nafi so a cikinsu. Dukkansu Abu guda nake ji a kansu. Amma na fi jin tausayin Hamim haka siddan duk da shine fitinanne kuma marar hak'uri.
A fili na furta "Allah ka rayamu tare da yaranmu, ka tsare mana su, ka yiwa rayuwarsu albarka".
Ina kallon Hanif da yake barcinsa akan gado illah kansa da yake jikina. Ina ayyana mutane masu karamci da sadaukarwa tun suna kananu ake fahimtarsu. Yana wahalar gaske ya ture d'an-uwansa a jikina. Ko abu ya dauka da Hamim ya fara kuka zai ba shi. Haka nan baya damuwa idan na goyi Hamim shi na rik'e hannunsa.
A raina sai nake ganin shine yafi dace wa ya amsa sunan Baban Marina. Ko da yake bansan ko Baban Bulkachuwan shi ma haka yake mai hak'urin gaske ne.
Na shafa kansa ina ce wa "Allah yasa ka zarce da hak'uri da yakanar ka. Allah ya saukaka muku rayuwarku gabadaya".
Na yi shiru ina jin wani irin abu na tsirga mini da bansan ko mene ne ba.
A hakan Babah ta shigo, Tijjani na biye da ita a baya.
Ta kalle ni ta ce "Wai har kin hakura kin ce zaki bi shi Yabi?"
Yadda ta yi maganar sai na kasa amsawa.
Nan da nan ya ce "Ta hakura mana Babah. Dan Allah kada ki sauya mata shawara. Na bata hak'uri, ke ma ina sake baki hak'uri."
Ta ce "Idan ta ce zata koma ai shike nan. Amma idan ta ni ne ko zata koma sai na kira maza sun taya ni kafa maka hujja".
Ya marairaice ya ce "Harshe da hakori ma ana samun sab'ani. Mun fahimci juna yanzu. Na yi alkawarin bazan kuma yi mata hakan ba. Mu rufe wannan matsalar a tsakaninmu dan Allah".
Ta kalle ni ta ce "Zaki koma, ko sai mun zauna da iyayensa na nan na fada musu BAK'AR TA'ADAR da yake neman tsiro da ita, kada nan gaba su ce na kashe masa aure".
Na kasa magana. Shi kuma fadi yake "Babah mun fa shirya ta fahimce ni, na bata hak'uri."
Ta ce "Kasan Allah sai na ji da kunnena sannan zan bari ku tafi. Ai kai yanzu maganar ka ba abin dubawa ce ba".
Ya rasa inda zai sa ransa. A kidime ya ce "Asiya taimake ni ki fada mata, kin huce, daure ki ce komai ya wuce. Kalli yadda yaran nan suke barcin nutsuwa a jikin ki. Ko baki hakura dan ni ba, huce saboda su".
Dakin ya dauki shiru. Kallon Tijjani kawai za'a yi a gane yana cikin zullimi sosai.
Ta sassauta ta ce "me kika ce, zaki koma, ko kuwa?"
Na yi k'asa da kaina na ce "Tunda ya gane kurensa, ya janye kalamansa, ya kuma bada hakuri, to ba sai an tara masa jama'a ba. Ai mun ba shi assignment ".
Ya yi maza ya ce "Wallahi exam ma kuka ba ni."
81&82
*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633
Ya juya ga Babah ya ce "To ga shi nan ta fada miki ta hak'ura".
Ta fita tana fad'in "Y'aya'nta dai sun raunana ta. Ni kam ban so hakan ba."
Gabadaya ya yi sanyi da kalamanta. Yana ganin zasu sa na sake botsare wa. Da sanyin murya ya ce "Mu tafi yanzu ko sai anjima little?"
Na dauke kai ban amsa ba. Ya diririce. Ya ce "Mun gama magana fa Asiya".
"Sai na shirya kayana". Na fada ba tare da na juyo ba. Ya ce "To bari idan an yi azahar sai mu tafi ko?"
Ya fada da sigar da tambaya. Ni kuma na yi bakam.
Ya yi shiru yana kallona. Ya saki gauron numfashi ya ce "Ina kayan na ki suke na hada miki?"
Ban juyo ba na ce "Suna cikin wadirof din".
Ya bude ya fito da jakar kayan nawa. Ya gyara su. Ya ninke wanda Hamim ya dauko a igiya ya saka, sannan ya zuge.
Ya zauna yana ta yin mini maganganu da nufin mu yi hira. Ni kuwa sai basarwa na ke yi. Amma bai daina ba.
Ya dawo daga masallaci ya tarar yara sun tashi muna falo duka muna cin abinci.
Ya zauna shi ma ya zuba nasa.
Babah ta sake yi masa fada sosai. Sannan ta hadamu gabadaya ta ja kunnenmu akan mu kara hak'uri da junanmu. Sannan ta gode mini da har yau ban canja mata matsayin da na bata ba.
Ta rufe da ce wa "Dama idan kin ga kin gaji to wajena ne mafarki matukar ina raye".
Na amsa mata da ce wa "In sha Allah Babah".
Ya kasa hak'uri ya ce "Kin bata lasisin ta yiwa zaman aure tustu kawai Babah".
Ta girgiza kai ta ce "Matukar za'a tozarta ba. Amma idan akan son zuciya zata yi, ai ba yarda zan yi ba. Kai ba abin kunya ba ne ace anji kanki?"
Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa. Ya ce *Tsautsayi ne. Zan kuma kiyaye.
Muka gama sannan muka yi haramar tafiya.
Har kofar gida ta rako mu tana sake ba ni hakuri.
A hanya kuwa shi da su Hanif suke ta hirarsu, yana ta amsa musu gwarmcin maganarsu.
Muka isa gidan. Kaca-kaca yake tabbacin bai samu nutsuwar da yake gyara shi ba.
Ya tafi masallaci sallar laasar. Ina idarwa na hau aikin gyara gidan. Ya dawo ya shiga taya ni. Cikin lokaci k'ank'ani muka kammala.
Na yi wanka, na shiga kicin na fara hidimar had'a abincin dare.
Ya fito sanye da jallabiya sai kamshi yake yi tabbacin shi ma wankan ya yi . Sannan ya yiwa yaran.
Ya shigo kicin din ya ja turmi ya zauna.
Ya zuba mini ido. Ya ce "Little ba ki huce ba ne?
Ban kalle shi ba. Na ce "Me ka ga ni?"
Murya babu amo ya ce "Ba ki dawo da walwalar ki ".
Na yi k'asa da kaina tare da ce wa "Na huce mana. Kawai zuciyata ce take ta yin wasiwasi mai yawa".
Ya mik'e da azama ya rungume ni ta bayana.
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWIA SAIWOWIN SANYI*
AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU*
*AKWIA SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.
Ya rankwafo sosai in ya dora kansa a wuyana ya sassauta murya ya ce "Bai kamata ki yi wasiwasi a kaina ba Little. Kuskure ne wanda ajizanci yake sababa shi. Ki manta wannan al'amarin. Ina cikin matsanancin damuwa da fishin ki. Pls my little angel double sorry ".
Na saki ajiyar zuciya tare da ce wa "Allah ya kiyaye na gaba"
Ya amsa da "Ameen dear. Allah ya yi miki albarka."
Ya dinga kissing d'in kunnena da wuyana da duk inda ya yi masa.
Tamkar ya jani daki. Amma kusantawor magariba ya sanya ya hakura a dole.
Da daddare yara na yin barci, ya fito da maitarsa a fili. Bai sarara mini ba sai da ya samu nutsuwar da yake so. Kalaman soyayya da na rarrashi ya dinga amayarwa. Wasu ma ni ban tab'a jinsi ba sai a ranar.
Ya jadda mini ce wa "Dukkan nasarar da ya samu tana d'amfare da irin gudunmawar da na ba shi a zamanmu. Ya sani bai manta ba, ba kuma zai mance ba.
Ni kuma na yi lamo a jikinsa na shige ya rufe ni ruf. Ina jin kalamansa suna warware dukkan damuwata.
Ina sake gasgata yana sona, so na hakika. Domin ya shayar da ni kalolin kauna masu tsayawa a rai da gangar jiki gabadaya.
Ya kaurara murya ya ce "Ki mini alkawarin baza ki sake barin gidan nan babu izinina ba. Ki mini alkawarin komin runtsi ba zaki juya mini baya, Asiya ki mini alkawarin zaki gasgata ni ko da kowa bai yarda da ni ba. Idan har kin tsaya mini zan yi ta samun cigaba a rayuwata. Amma idan kika juya mini baya ina tabbatar miki komai zai lalace mini ya cakalkale watak'ila ma na shiga rayuwar da tafi wanda na yi a baya muni!"
Ya karasa cikin matsanancin damuwa da karaya.
Tausayin sa ya baibaye ni. Na nisa na ce "Idan har ka mini alkawarin zaka kame daga kule kulen mata, zaka kiyaye dukkan iyakokin shari'a to mene ne ba zan yi maka ba Baban 2?"
Ya sake tsanta rungumar da ya yi mini.
Yana fad'in "Na gode sosai Asiyata".
Sai kawai na ji hawayensa na sauka a kan goshina.
Na shiga rudani mai yawa domin a tsawon lokacin da na shafe tare da shi ban tab'a ganin kukansa ba hana rantsuwa lokacin rikicin Rafi'a. Na ga k'walla a idonsa amma hawaye bai zuba ba . Murya na rawa na ce "mene ne?"
Shi ma da rawar murya ya ce "Haka kawai nake ganin kamar duniyata ta zo karshe. Karbar filina da kamfani ya yi, yana neman zame mini fitina. To idan ke ma zaki dinga yi mini irin wannan fishin akan sabanin ra'ayi, ki dinga zargina akan abin da baki ga ni ba. Na tabbatar wata rana za'a wayi gari ne bakin cikin duniya ya mayar da ni gawa".
Murya babu amo na ce "Da ikon Ubangiji hakan ba zata faru ba. Ba zan sake yi maka irin haka ba. Ka yi hakuri ".
Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa, domin shi din mai son na ba shi hak'uri ne ainun.
Ya sake ce wa "na sake rokon ki?"
Zuciyata na bugawa ainun na ce "Ina jin ka."
Ya ce "Dan Allah ki yi dukkan iyawar ki, kada ki bari yaran nan su tagayyara idan har mutuwa ta yi gaggawa ta sure ni".
Ai bansan yadda aka yi ba, kuka ya goce mini mai tayar da hankali domin k'warai ya gigita ni.
Maimakon ya kwantar mini da hankali sai ya sake ce wa "Na sani idan na mutu dole zaki yi aure Asiya. Domin a yanzu ne ma kika yi shekaru ashirin. Amma dan Allah, dan darajar ma'aiki ban da Jabir, ban da shi little!".
Ya fada da wani irin yanayi na tashin hankali sosai.
Kukan da na ke yi ya tsaya cak a dalilin tashin hankalin da ya jefa ni ya wuce kukan hawaye ko na baki. Sai kukan zuci da na gangar jiki. Zufa ta dinga yanko mini tamkar na yi tsere.
Na kasa ko da motsi. Tsawon lokaci muna ta fama da sake saken zuciya da fargaba.
Murya babu amo na ce "wannan ne tukuicin dawowar da na yi ko Baban 2? Haka kawai ka tayar mini da hankali. Kana nufin mutuwa zaka yi ka bar ni da k'ananun y'aya'n ka Tijjani?"
Ya ce "Jikina da zuciyata ke raya mini hakan, amma ai bani da tabbacin hakan domin gaibu ne. Fatana dai ki cigaba da zama jajirtacciya ko bayan babu ni. Akwai mata da yawa da suka sadaukar da kuruciyarsu da jin dadinsu dan inganta goben y'aya'nsu. Ki kula da su, ki saka idon a kan tarbiyarsu, idan Ubangiji ya baki tsawon rai sai suma su raine ki, su ji kan ki".
Na sake kece wa da kuka tare da ce wa "Kada ka mini haka Baban 2. Dan Allah ina son na rayu da kai. Ina son twins su girma a tsakanin uwa da uba, bana son na rasa ka. Kai nake fatan ya zame mini miji har a aljanna. Idan mutuwar zata dauke ni, to kawai ta hada ta dauke mu tare."
Da sauri ya ce "A a In sha Allah ke zaki rayu, ki zame wa y'aya'nmu bangon jingina. Me yasa ba ki gano girman kalubalen da zasu fuskanta a dalilin rashin uwa da uba ba?."
Cikin kuka sosai na ce "Allah ka jinkirta mana rayuwarmu gabadaya".
Ganin hankalina ya tashi ainun, sai ya kawar da maganar ya shiga rarrashina da tarairaya ta. Amma gabadaya hankalina bai kwanta ba. Na riga da na ankara matuka da gaske.
Washagari haka na tashi sukuku babu kuzari bare walwala. Ya yi shirin tafiya kasuwar Ilela. Zuciyata ta dinga ayyana mini na hana shi fita domin sai nake ganin tamkar ba zai dawo ba.
Ai kuwa na fasa masa kukan ba zai fita ba. Duk yadda dinga rarrashina amma ban yarda na amince zai fita ba. Kan dole ya zauna ya fasa fitar.
Ya sassauta murya ya ce "Idan Ubangiji ya so ikon sa sai na mutu a kan katifata lafiya lau ba tare da ciwon komai ba."
Ina hawaye na ce "Masifa da jafa'in kake jawo mini Tijjani Allah ya yafe maka kawai. Allah yasa kai ne zaka ga gawa ta. In kuwa ba haka ba tabbas sai ka yi mini sababin hawan jinin da zai nannad'e ni na kasa moruwa".
Ya numfasa bai ce komai ba, fitar da bai yi ba ke nan. Yaranmu suna ta kai komon farincikin ganina a tare da su. Mu kuma muna cikin wani irin yanayi mai wahalar wa.
Kwanaki biyu na rik'e Tijjani a gida. Masallaci kawai nake barinsa ya je. Mukullin motar na boye na hana shi. Na kafe sai ya canja sana'a. Da wa'azi da nasiha da lallashi ya shawo kaina ta hanyar cusa mini tauhidi tare da gasgata hukuncin Ubangiji baya sauyawa. Kawai na dinga fahimtar maganganunsa tare da zama jaruma, mai fuskantar dukkan kalubalen rayuwa da k'arfin zuciya, sai kuma na dage da addu'ar duk runtsi Ubangiji ya tsare mini imani ya kuma shirya mini zuria.
Na yarda da nasiharsa. Na ba shi mukullin motar sa.
Ranar da ya fara fita, na k'ira wayarsa tafi sau goma, ina tambayar sa inda yake.
Kwanaki suka yi ta shud'e wa ba abin da ya samu Tijjani. Sai na fara warware wa. Zullimin da nake ciki ya yi sauki. Yayin da shi kuma yake ta samun nasibi. Domin a yanzu ya bar kasuwa. Amma yana sarar kayan miya ya kai kasuwannin k'auyuka. Idan zai juyo sai ya saro abin da yake sauki a garin ya zo ya siyar a cikin gari. Kafin azahar ya dawo gida. Sai ya sake fito da dabarar kai da karbo sako(Delivery). Sosai yake samun alheri da harkar.
Ya fara tafiya Jos ya kai kayan miya da sakonnin jama'a, idan zai dawo ya sake karbo sakonni ya kuma saro dankalin turawa da su atile. Nan da nan sai al'amarin ya karbe shi. Muka canja mu da y'aya'nmu a dalilin wadatar da yake samu. Na fara murje wa, ina haske, suturu suka yawaita mini. Mussaman material din Umm Nihla mazauniyar Malaysia. Bana gajiya da siyan yadinka ta. Saboda rashin nauyinsu da kuma yadda suke shan ruwa babu kode wa. Shi kansa Tijjani yana matukar son na yi masa kwalliya da su....
Yawan fataucin da yake yi tsakanin Bauchi zuwa Jos ya sanya akai akai yake zuwa Toro. Ganin wadatar da yake ciki sai aka fara yi mana sintiri da sunan ziyara ko hutu. Wanda kafin ya shiga wannan rufin asirin ba'a cika tunawa da shi ba. Bare a taimake shi.
Nasiba ce dai bai sake yarda ta zo ba, ya yanke dukkan hulda da ita.
A wannan tsukun na fahimci al'amarin da yake zuciyar Tijjani, domin yadda yake yiwa Baban Marina hidima ko su Yaya Salisu basa yi masa hakan. Yanzu a gidanmu ana iya soya dankali ko doya. Shi da su Yaya Salisu da Yaya Rabiu suka kwaskware kofar tamu ta farfado. Baban Marina da kansa ya fada mini a waya ce wa Duk satin duniya sai Tijjani ya tura masa kudi. Ban da kayan miya da su dankali da yake kai masa babu gajiya.
Haka kuma yake yiwa mahaifiyarsa. Dada kuwa kayan shayi ne da sabulai da turare baya rabata da su.
Maimakon a yaba masa sai gabadaya gidan aka hau cece kucen ni na hana shi ya kyautata wa su Baban Tsakiyar da Baban kasuwa sosai. Tunda ai duk daya suke da Baban Marina a wajen sa. Amma suna gani za'a yi ta shiga da kayayyaki kofarsa akai akai. Amma su a leda ne kuma sai jifa jifa. Shin dan yana surukinsa ne, ko kuwa akwai wata alak'a ce da tafi tasu?"
Nazira ke tsegunta mini. Tare da bani labarin yadda Baba Maryo take cusa masa Nasiba da fad'in ai ba komai ba ne dan ya hadamu ya aura. Rabon y'aya'n da ta haifa ne ya sanya ba a yi da shi ba. Haka kuma ga rabon y'an biyu a jikin Yabi.
Dada dai bata ce wa komai a dalilin tana gudun bacin ran autarta. Yayin da Nasiba bata zafafa ba. Tabbas tana son Bulkachuwa. Idan ya nuna yana sonta a radin kansa zata amince domin ba zata zalunci kanta saboda Yabi ba. Amma ta karaya a dalilin ta fahimci shi kansa a hannun Yabin ya ke. Tunda ta dawo daga gidansa ta zauna ta yi nazari da kyau ta fahimci Yabi ta bar masa gidan ne saboda ya kai ta. Tun daga lokacin kuma bata sake ganin walwalarsa ba. Idan ta gaishe shi zai amsa. Amma ko kallon inda take baya yi, bare ya fahimci me take ciki. Ta kuma tabbatar fishin Yabi yake gudu na gaske. Ita da kanta mamakin yadda yake shiga nutsuwar sa yake idan yana gabanta. Idan kuwa ya zo Toro ta bugo masa waya gabadaya nutsuwa wa yake tamkar uwarsa ce ta masa waya. Ya dinga b'are b'are yana tambayar lafiyarta da ta tagwaye. Sannan ya bawa Dada wayar dan ya tabbatar mata a inda yake.
A kasan ranta bata ganin aibun matsananciyar soyayya da gudun zuciyar Yabi da yake yi. Domin ta tabbatar Yabi ta cancanci ya mata irin wannan soyayyar domin ta sadaukar da abubuwa da yawa saboda shi. Ta jure a lokacin da kowa yake gudunsa duk da tirsasata aka yi. Ta rufa masa asiri da sana'arta. Kenan a yanzu da ya fara samun dama, dan ya kyautata mata ba abin birge wa ya yi ba. Abin da ya kamata yake yi.
Ta sake yarda ko ya aure ta, ba zata iya da jidalin Yabi ba. Tunda a bayyane yake a hannunta yake. Kawai zaman hak'uri zata yi.
Abin da ya dame ta daya ne. Yadda mahaifiyarta ta fantsama nemo mata maganin da za'a karkato da hankalinsa kanta. Kullum a cikin bata rubutu take wanda ta tabbatar sunansa ake rubuce wa.
Tana kwance ita kad'ai a daki tana ta nazari tare da alkalancin bai kamata ta aure shi ba. Mafi muni ma ta hanyar asiri. Ta tabbatar mahaifiyarta ce ta yi sanadin raba ta da shi a dalilin ba shi da komai, kuma ba a kintse yake ba. "Yanzu kuma da ya zama mai daraja sai ki cusa masa ni a kan dole?"
Ta furta a fili ba tare da ta shirya yin hakan ba.
Kunya ta kama Nasiba. Ta ya ya mahaifiyarta zata runtse ido daga yin alkunya ga d'iyar wanta uwa daya uba daya? Ta san zumuncin zamani ya shiga tasgado mai yawa, mussaman na gidansu. Amma tana matukar kaduwa da son kai irin na gyatumarta. Har kunya ta taya ta ji a sadda ta karbo mata taimakon da aka rubuce sunan Tijjani da na uwarsa. Alhalin a sadda yake son ta akan idon uwar tasa ta wulakantasu ta hanyar ce wa d'anta bai kai a ba shi aurenta ba. Amma yanzu wai ba wanda take so ya zama surikinta sai Tijjani, mijin Yabin Baban Marina. Ta sake ce wa "wacce irin BAK'AR TA'ADA ce wannan? Wanne irin son zuciya ne ya yiwa mutanan yau katutu a zuciya?"
*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Saiwowin maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
83&84.
Zaune nake ina duba kayan gyara da na siya a wajen Surayya Halin yau. Domin lokacin haihuwar twins a wajen ta Yaya Ummi ta siya mini kayan da suka gyara ni matuka da gaske har Baban 2 ya dinga tambabar ni na haife su kuwa?.
Tsumin kwakwa ya tayar mini da kwadayinsa da na jima ina yi. Domin dad'i gare shi. Na dauka na sha. Na tashi na je kicin na dauko gwangwanin Madara ta ruwa na fasa. Domin tunda Tijjani ya fara samun sukuni kullum sai na sha gwangwanin Madara. Ban da sauran abubuwan da suke inganta lafiyar jiki.
Na fasa na juye a kofi. Na dawo falo na bude robar koren maganin da na tabbatar da kyaunsa. Na zuba na juya na shanye. Ina hasasho subadin da zan sha yau a wajensa.
Na tattara sauran na kulle dan kada na yi over dose.
Na dauki waya na k'ira shi. Ya amsa na ce "ka taho ne?"
"Eh kina son wani abu ne?"
"Ka taho mini da dabino ko kwakwa ".
Da azama ya ce "Done my little, ban ji hayaniyar 2 ba". Na ce "gasu nan barci suka yi".
Ya ce "Da yammacin nan? Tashe su dan Allah. Bazan yarda da daddare su tisamu a gaba su hana ni hutawa ba".
Na kyalkyale da dariya. Domin nasan nufinsa.
Na mayar da robar y'aya'n gadali domin sai gobe zan ci tunda bani da kwakwa ko dabino a hannuna.
*Akwai kayan Chad masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*.
Sosai muke zamana lafiya da taka tsantsan kan abin da zai janyo mana rikici. Na fahimci yajin da na yi, ya sake sawa Tijjani tsoron mu yi fada. Duk da hakan kuma wani loakcin zai fitittke ya yi mini sababin na raina shi, ko akan abu kad'an sai ya tsiri fishi yana fad'in "Tunda Babah ta bani lasisin na dinga yi masa yaji shi ke nan nake yi masa abin da nake so. Dan na ga ba shi da yadda zai yi. Idan yana irin wannan fishin, wani zubin ya bani dariya. Wani lokacin ya bani mamaki. Idan na so sai na rarrashe shi tunda shi haka yake kamar su Hanif wajen son a ritata shi, a tarairaye shi. Wanii lokacin kuwa na share shi, na fi shi fishi. Idan ya lura da hakan sai ya yi maza ya hadiye nasa fishin ya hau lallaba ni.
*Shekara daya a gaba*
Kwanci tashi tagwaye suka yi shekaru uku. Haka muke gurgura rayuwa yadda ta zo. Wataran fari, wataran baki. Zuwa lokacin sosai harkokokin Bulkachuwa suka sake mike wa. Ni kaina ina siyar da dankalin turawa da su karas da atile a cikin gida. Ba kuma k'aramin alheri nake samu ba. Tunda shine yake siyo mini babu maganar kudin kawowa. Idan na siyar na cire riba na ba shi kudin sai ya sake siyo mini wasu. A hakan har na tara jarina ba tare da na zuba wani kudin ba. Dan haka na ware kudinsa na ba shi, tare da yi masa bayanin yadda kudaden suka haihu dan haka zan cigaba da yi da nawa. Yana bude baki sai ce wa ya yi wadananan din ma naki ne. Kin tuna bashin da kika yi ta ranta mini a lokacin da bani da shi?". Na girgiza lai na ce " A a tsakanina da kai babu bashi Baban 2. Ba ka dauke ni yadda na dauke ba Wallahi." Da azama ya ce "Na gode, na yarda babu bashi. To na ba ki kyauta.
Na murmusa na ce "Ka dai biya ni kawai. Shike nan na gode, Allah ya kara budi da lafiya." Ya amsa da "Ameen maman 2."
Ya kanne mini ido tare da ce wa "Na kosa a yiwa su twins Gambo fa".
Na yi dariya na mike na bar shi dan yanzu sai ya fara tsokana ta akan abubuwan da na yi ta yi masa a baya.
Muna cikin haka babu zato sai ga shi ya zo mini da takardar da take nuni na samu gurbin karatu a kwalejin ilimi ta jihar Bauchi.
Ban yi murna ba, domin tun filazal na fi son na yi kasuwanci. Na kuma fahimci Ubangiji ya sanya mini nasibi a cikin juya kudi. To akan me zan damu kaina sai na yi karatun da babu garantin zan ci moriyarsa tunda kullum kasar sake lalace wa take yi. Aikin gwamnati siyar da shi ake yi da makuden kudade, sai kana da hanya ma da ka samu a siyar maka d'in.
Bai yi fishi ba, ya zauna ya dinga zayyano mini tasirin ilimi a wajen mace ba dan ta yi aiki ta samu kudi ba ne kawai. Ilimin mace da gogewarta na taimaka mata k'warai wajen bawa yara tarbiya da sanin yadda zata yi cudanya da mutane daban daban. Ya sanyaya murya ya ce "Ki daure ki sawa zuciyar ki soyayyar karatun nan Asiya dan sai kin yi shi. Fata na ke yi ko na mutu a ce ke din kina da wata madagora da zaki rik'e mini y'aya'na. Duk duniya ke nake da tabbacin ba zaki gaza da hidimarsu ba. Daure ki bani hadin kai mana".
Na dinga kuka domin idan yana irin wannan maganganun gabadaya kidime wa nake yi. Shi kuma baya fasa fada mini lokaci zuwa lokaci, tamkar mai son na yi haddarsu. Tare muka fara makaranta da su Hanif. Domin Nursery da take cikin college din ya snaya su. Da kansa yake kai mu. Sai ya wuce garin da zai je. Bama koma wa gida sai na gama daukar darussa.
Komawa ta makaranta sai ta jawo takaddama mai yawa a cikin gidan Marina. Domin a tarihin gidan ni ce na kammala sakandire har na fara ta gaba da ita da kuma aurena. Dada ta dinga sababin ya rungumi BAK'AR TA'ADAR arna masu barin matansu suna cud'anya da mazaje kullum da sunan neman ilimi. Babu kishi babu komai. Alhalin ma'aiki ya ce wanda baya kishin iyalin sa babu shi babu jin kamshin aljanna.
Yanzu gabadaya gidan Marina ni na tsole ido. Rufin asirin da muke ciki ya na matukar mintsinin ahalin gidan.
Bana damuwa tunda ba a garin nake ba. Wani abin ma har a yi yamididinsa a gama bana ji bare raina ya baci a banza.
Kwatsam sai ga Maijidda a gida, wai ta yi yaji. Al'amarin bai yiwa iyayenta dadi ba. Domin ni da ake son ganina ina cikin tasku da jele da sunan bacin rai ba a tab'a ganin na yi hakan ba. Kuma abin mamaki Jabir din ne ya kawota gidan da kansa. Domin ta k'ure hak'urinsa a yadda ya fada.
Ya murje idonsa ya juya ya barta. Hakan ya kawo cece kuce da rashin jituwa a tsakanin Baban Tsakiya da na Kasuwa. Duk yadda suka so boye maganar kada mu ji. Sai da maganar ta fantsama domin aure zai k'ara ita kuwa ta ce bai isa ba, sai dai ya zaba ko ita ko amaryar. Ya so su fahimci juna amma ta tada balli domin da ta ga yarinyar da zai aura tunda dalibar kwalejin da yake koyarwa ce. Ai sai ta gigice domin haka take yar tsurut fara kal tamkar dai abokiyar tagwaitakar Yabi ce. Hankalinta ya rubanya tashi domin ta tabbatar ya sota ne a dalilin yadda suke yanayi da ex love dinsa. Ta kuwa ce ba dai ita ba. Shi kuwa ya ce bata da hurumin zaba masa wacce zai yi zaman aure da ita.
Watanni biyu basa cikin zaman lafiya, gabadaya ya murde mata fiye da yadda ta murde. A karshe ya kawo ta gida ya ce ta zauna ta huta tukun.
Da ya tafi ya kashe wayarsa da dukkan hanyar da za'a same shi. Baban Kasuwa ya dinga fad'a tare da fad'in tozarcin da Jabir ya yi, da shi yake. Kuma ubansa ya kasa tsawatar masa. Saboda yana jin tsoron sa. Rikici ya kaure a tsakaninsu Dada ta kasa shawo kan matsalar domin Baban kasuwa ya dauka da zafi, kuma dama tafi gudun zuciyarsa. Baban marinar da ba'a saka shi ba, shine ya tuntunbesu bayan Dada ta fad'a masa a dunkule ba a bude ba.
Abin mamaki kowa ya ce masa babu komai, duk da Dada ta fad'a masa. Shi kuwa sai ya hak'ura ya zuba musu ido.
Bai gane kan al'amarin ba sai da ta yi sati biyu. Da kanta ta je ta durkusa tana kuka ta fad'a masa yadda abubuwan suka kasance, sannan ta roki Baban Marina akan ya bawa Jabir hak'uri. Gabadaya ta shiga damuwa da tunani domin dukkan y'aya'nta uku suna can tare da shi. Mai shan nono kawai ya bar mata. Bata tab'a zaton zai yi mata hakan ba.
Duk kokarin Baban Marina ya amsa samun Jabir. Washagari ya tisa ta a gaba ya nufi Kaduna da ita. A ransa ya tabbatar dan tana son komawa dakinta ne. Ba dan hakan ba da bai isa ya yi irin wannan ikon ba.
Jabir na ganin sa ya ware fuska ya marce shi da girmamawa. Baban ya dinga yi masa fada tare da tabbatar masa ya yi tsaurin ido.
Cikin jin nauyi ya ce "Ka yi hak'uri Baba! Ta kai ni bango ne da yawa. Ni fa dama hak'uri nake yi domin ba hakan nake so ba, amma tunda kaddara da rabo ya ba ni ita, ban zalunce ta ba. Ga ta nan ta fada maka inda na kuskure domin nasan iyakar adalci ina yi mata. Aure kuwa bata isa hana ni yi ba, bata kuma da hurumin zaba mini wacce zan aura domin ni din ba makaho ba ba ne, bare ta ce zata zaba mini wacce zan aura".
Baba dai ya yi masa fada tare ce wa "Ka dauke ta ka kai mana ita, ka yi tafiyar ka ai rainamu ka yi Jabiru. Duk cikinmu ka rasa wanda zai maka maganin matsalar sai ta hanyar mayar mana da ita? Ko a lahira wani na cin arzkin wani. Kada ka sake irin haka. Kishi kuma ai dole ta yi, ka rarrashe ta, ka kwantar mata da hankali ba wai ka ankara ta ba."
Ya juya ga Maijidda take kuka sosai ya ce "Ke kuma ba ruwan ki da auren sa, matukar yana yi miki adalci, kawai ki yi hakuri ki yi addu'a. Ai kishiya yar uwa ce, ina ruwan ki da ita. Ban da ma sakarci me ya ka ki yin fitina akan wacce ma bata zo hannunsa ba? Kina ahalin gidan Marina ki ce ba kya son kishiya? To ko da kika ga gyatumar ki ita kad'ai ai mu kina ganin kofofinmu mata ne da yawa ba kuma wacce ta kori wata, ko ta hana ta samun arzikin ta."
A ranar ya juyo ya dawo.
Ba jimawa kuwa Jabir ya yi aurensa. Hakan ba k'aramin tasgado ya janyo a taskanin Baban kasuwa da na Tsakiya ba. Da k'yar aka samu suka fara gaisawa. Kunyar mutane da yadda aka san kansu a hade yake ya sanya suke gaisawa. Da kuma yadda Dada ta yi kuka sosai akan gabar da suke yi da juna.
A zahiri sun shirya amma kasan zuciyoyi babu dad'i. Ba yadda zasu yi ne kowa yana ganin shine akan dai dai.
Baban Marina dai bai ce kala ba. Domin yanzu da abubuwa suka fara warware masa a dalilin mafi yawa y'aya'nsa muna cikin rufin asiri. Muna had'a abin da za'a ci a k'ofarmu. Tijjani kuwa ya dauke masa cefanen kayan miya da kudin k'ananun bukatu.
Hakan ya sake janyo masa bakin jinin da babu yadda za'a yi sai zunde a bayan ido.
***
A hakan na cinye shekara d'aya da fara karatun. Na fara nisa a cikin ta biyu. Tun bai shiga jikina ba, har na sanya shi a raina na mayar da hankali, hakan ya faranta ran Tijjani tunda ban sami carry over a shekarar farko ba.
A hankali sai nake ganin Tijjani na d'an sauyawa. Sauyin bai shafi mu'amalata da shi ba. Amma yana yawan zuwa Toro. Kusan kullum sai ya je ko da ba zai je Jos ba.
Ina ta jin rade radin yadda yanzu yake zama ya yi hira da Nasiba da har yanzu bata yi aure ba. Sai ma kasuwanci da take yi sosai. Kayan gwanjo take siyowa a Jos masu kyau. Har ce mini aka yi yana karbo mata sakon kayan.
Tun ina daure wa ina dauke kai daga abubuwan da nake ji har na fara sike wa.
A dalilin kullum dare sai ya fita k'ofar gida ya shafe lokaci mai yawa yana waya. Haka nan kaffa kaffa yake da wayarsa abin da baya yi a da. Da na yi masa magana sai ya balbale ni da fad'an na saka masa ido ne. Ban da hakan me yake yi mini? Dan ya yi wayar da bata shafe ni ba a waje shine laifi?
Na kasa bude baki na ce komai domin ba ni da hujja.
A hankali muka fara samun tazara a tsakaninmu. Na sani bai canja daga kawo mini abubuwan abincin ko na bukata ba. Bai canja a hidimar makaranta ta ko hidimar y'aya'nsa ba. Sannan bai canja mini a mu'amalarmu ta auratayya ba. Har yau din nan a cikin mararina ya ke. Duk da ni din ma kullum a cikin gyara kaina nake da ingantattun kayan Surayya da basu da illah ga lafiya. Sannan ina amfani da kayan g.h.t na FASEELAT.
Amma yawan wayar da yake yi da sintirin zuwa Toro, da sabunta mu'amalarsa da Nasiba da nake ta jin rade radinta, tana matukar ci mini tuwo a k'warya. Na rasa wa zan fad'awa ya fahimce ni. Domin da na fadawa Gwaggo ce wa ta yi "Ina ruwan ki da jita jita? Sannan ai bai zai yi aure bai fada ba. Ki rage kishi mussaman kan abin da baki gani ba, zato ne da shati fadi kawai.
Haka na hak'ura na cigaba da zuba ido tare da hak'uri. Amma sai nake ta d'ad'are wa da shi. Ko a shimfida bana wani katabus shi zai yi kidansa da rawar sa. Wani lokacin ya tambayi dalilin sauyin nawa cikin kwanciyar hankali. Bana iya ce masa komai sai dai na ce "Ban canja ba, babu komai".
Wani lokacin ya ce "Allah ya sauwake. Wani lokacin ya yi tsuka ya juya mini baya tare da fad'in "Zan yi maganin wulakanta ni da kike haka siddan Asiya."
Gabadaya mun koma muna ganin laifin junanmu a dalilin kowa bai gamsu da kokarin d'an-uwansa ba.
A haka na kammala aji biyu. Twins sun yi wayo sosai tunda sun shiga shekaru biyar. Wani irin wayo da fikira a cikinsu tamkar wanda suke siyo dabara a kasuwa. Gabadaya sun juye ubansu sak. Ga shi suna girma suna sake zama iri d'aya. Ni da kaina ina gane su ne ta halayyarsu. Domin har yau din nan Hanif mai hakuri ne, magana bata dame shi ba. Sabanin Hamim d'an hayaniya kuma mafadaci irina. Har yanzu bai bar kuka ba.
Sau biyu ina yin bari. A yanzu haka ina zuwa ganin likita a dalilin hakan. Na karshen nan da na yi Bulkachuwa ce mini ya yi "Ina sane nake bararwa tunda na saka masifa a raina. Ya rasa me yake mini da nake gana masa azaba haka.
Kallon sa na yi kawai. Ba tare da na tanka masa ba. Domin na riga da na saka a raina ce wa hakurin da aka yi ta jaddada mini na yi a lokacin aurena. Yanzu ne zan fara shi. Dan haka na rungumi addu'a, y'aya'na da karatuna hadi da sana'ata. Na tattara shi na zuba masa ido yana yin almuransa yadda yake so.
Muna cikin wannan zaman na fallasa tafi yabon yawa. Kamfani suka sake biyansa kudin hayar filinsa tunda shekaru uku ta cika. A wannan karon har da kari akan wanccan. Duk yadda muke jin haushin juna sai da ya zauna ya mini bayanin komai. Ya kwashe mu ni da yara zuwa Kano. Ya yi mana siyayya. Muka kwana biyu, muka juyo da kaya niki-niki.
Yara na baya duk barci ya sure su. Ya sassauta murya ya ce "Zan canja motar nan. Zan siyo wacce ta fita."
A takaice na ce "Allah ya kara budi".
Ya zarce da fad'in "Ana mini cinikin wani gida mai kyau a Toro zan siya".
Nan ma a gajarce na ce "Allah ya sanya alheri."
Daga haka bamu sake magana ba har muka iso Bauchi. A dalilin ya fusata duk yadda ya kwashe ni ya mini hidima bai sa na saki raina ba. Ni kuma ina masa kallon a yanzu yana ganin yafi karfina tunda yana samun duk abin da yake so. Kasuwa tana gara masa ainun. Shi yasa gabadaya yake neman bijire mini. Duk abin da yasan bana so a yanzu baya jin komai ya yi a gabana. Jiya da daddare ina jin sa a waya yana ce wa "Ga ni kike ba zan iya bata wayar ba? Wai me kika dauke ni ne? Bari ki ga na sayi gidan da zan saka.ki a ciki, ki ga yadda zan fito da maganar gabadaya. Namiji dan zai k'ara aure sai a ce ba zai iya ba? Mata nawa ne a gidansu? Nima kuma mahaifina biyu gare shi. Da ba'a karin aure da ba'a haife ni ba, tunda tawa gyatumar ce amarya a gidanmu ".
Dai dai nan na fito a bandakin. Nan da nan ya katse wayar tare da ce wa "Zamu cigaba da tattauna wa da safe". Ya katse wayar tare da kashe ta gabadaya.
Tun lokacin na sake karaya da shi. Tabbas aure yake nema kuma a Toro tunda har zai sayi gidan da zai saka ta a can.
Sannan tun yanzu na dame ta tunda har tana masa shaguben tsorona yake ji ba zai iya aure ba. A raina na shiga yiwa mutanan da suke ganin Bulkachuwa tsorona yake ji Allah ya isa ta fi goma. Domin a yanzu da kowa yake mini kallon ina cikin rufin asiri da jin dad'i a gidansa. Ni kad'ai nasan me nake fuskanta. Nafi samun nutsuwa a lokacin da ba shi da ko sisi. A yanzu ba abin da bani da shi a gidan na cima, tunda ga kan nama, kifi, madara, dankali, doya, bare kuma kayan miya, da duk nau'in kayan abincin. Ruwa da lemo basa yanke wa. Komai baja baja yake ajiye mana. Haka sutura ta wadace ni ainun. Amma kuma bani da nutsuwar da nake da ita a da. Ba ya shiririce mini kamar lokacin baya. Dan haka sai na fi son waccar rayuwar da kowa yake mini kallon tausayi.
Babah ta kawo mana ziyara. Ta dinga rarrashi tare da shan cikina akan matsalar da ta sanya bana girma, da na fara murmure wa zan sake tsomare wa. Ban yarda na ce komai ba, saboda nasan ba zata yi masa ta dad'i ba, idan ta tafi kuma ya hau sababin ina had'a shi da uwarsa duk da ba komai yake mini ba, ni ce nake zaluntarsa.
Da kanta ta fahimci a yanzu ni da shi kowa harkar gabansa yake yi. Gamu nan ne dai, babu warkajabi irin na da, babu nishadi a tare da mu duk da ba gaba muke yi ba.
Da daddare bayan yara sun yi barci ta zaunar da mu tana bincikar matsalarmu a kokarin ta na son ta sulhunta mu ta dinke barakar da kullum take sake bunk'asa a zukatanmu ba tare da mun ankara ba.
Tsawon lokaci ban iya bude baki na ce uffan ba. Ta hakura ta koma kansa. Cikin kwanciyar hankali ta tambaye shi me yake faruwa. Ai tamkar gudawa haka ya b'arke da zano laifukana. Ya kaurara murya ya ce "Gata nan gabadaya ta ki sarrafuwa mini. Ko dariya take yi da y'aya'nta idan na zauna a cikinsu ta gintse dariyar ke nan. Idan tana zaune a falo na zauna sai ta san abin da zata kirkiro da zai sa ta tashi ta bar mini wajen. Ba zan mata abu ta nuna ta ji dad'i ba, zata dai ta ce ta gode a takaice. Gabadaya ta fitini kanta ta kuma fitine ni. Gara ma da Allah yasa kika fahimci masifar da d'orawa ranta. Gata nan ta fada miki mene ne bana yi a gidan nan da zata kwarzabe mu irin haka. Yanzu idan na fita har fargabar dawo wa nake yi tsabar yadda take shagulatin bangaro da ni, da dukkan al'amarina. Ban sani ba ko miyagun kawaye suke hure mata kunne. Na tabbatar cikin da baya zama idan ta samu ma akwai dalili, idan an tsananta bincike, tunda ta riga ta taurare mini, ita tasan me take nufi da zaman".
Na yi k'asa da kaina ina hawaye mai cin rai. Zuciyata tamkar ta fad'o k'asa idan yana danganta b'arin da nake yi ni ce da alhakin hakan.
Babah ta dawo kaina cikin tausasa harshe ta ce "Haba Yabi me zai sa ki abin da baki yi a da ba, sai yanzu da kike girma, kuma Ubangiji yake ta yi muku Alam nasharaha. Me zai sa ki yi haka?"
Na fashe da kuka mai ciwo na kasa ce wa koma a dalilin yadda nake gunji da shessheka mai nauyi.
Baba ta yi zuru tana kallon yadda nake kukan.
Ta koma kansa ta ce "Kai ne kake musguna mata, kai ne ka janye dukkan rarrashi da tarairaiya a tsakaninku saboda kana ganin kana ajiye mata komai na bukata."
Ya yi shiru. Ta sake juyo wa gare ni ta ja ni zuwa jikinta tana bubbuga bayana cikin rarrashi. Tsawon lokaci ina kuka su kuma ba wanda ya iya ce wa komai. Sai da na yi kuka sosai, domin tsawon lokaci ina ta son na yi ban samu inda zan yi ba. Shi yasa yanzu na yi shi son raina. Sai da na nutsu sannan ta d'ago ni ta ce ",Fada mini damuwowinki Yabi". Na ce "Babu komai Babah". Na saci kallonsa na ga ya kidime sosai domin ya sani idan har na ce babu komai to kuwa abin da yake raina mai nauyi ne. Irin kukan da na yi kuma ya saka shi zullimi.
Babah ta hau fad'in "Wato ban isa ba ko Yabi? Na zaunar da ku dan na ji matsalalolinku amma kin ce babu komai alhalin ko makaho idan ya ji irin kukan da kike yi yasan kina cikin bacin rai."
Idona ya sake cika da hawaye na ce "Wallahi Babah ba isa ne baki yi ba, ke ma kin san yadda na dauke ki. Kawai ban san me zan ce ba ne. Abin da na fahimta kawai yanzu ya fi k'arfina ne. A yanzu ya samu damar da zai auro daidai da ra'ayinsa, irin wacce ta dace da shi. Ai dole na ga komai! Dole komai zan yi masa ya zama laifi, dole ya janye dukkan tausayi da sassauci a tsakaninmu, Tunda bana birge shi. Yana zaune da ni ne a kan dole, gane hakan da na yi ya sanya na koma gefe dan na ba shi dama ya yi komai tunda Allah ya ara masa damar."
Na goge hawayen da ya zubo mini da hijabin jikina.
Babah ta yi shiru tana kallonmu tare da nazari sosai.
Ta kasa gane waye yafi gaskiya a tsakaninmu. Amma kalamaina sun yi matukar dukansu gabadaya, shi kansa kallona yake yi ya kasa ce wa uffan.
Karshe dai Babah ta rinjayar da gaskiya a tare da ni.
A sanyaye ta ce "Ban yi mamaki ba. Domin mafi yawa maza haka suke yi. Da sun samu wadata kuma sai wulakanci ya biyo kan wacce aka sha gwagwarmaya da ita. Ba ko wanne namiji yake yin hakan ba, amma dai masu yin sun zarta marasa yin yawa. Sannu Yabi!"
Ta fada cikin wani irin yanayi, mai wuyar fasaltawa.
Kalaman Babah suka sake fadada zullimiin da yake ciki.
Murya babu amo ya ce "Babah kada kalamanta su rude ki, ki bata lasisin cigaba da gasa ni da ruwan sanyi da take yi. Ubangiji ya bata iya sarrafa harshe. Wallahi ita take k'warata. Satin da ya wuce muka dawo daga Kano. Na kuma shirya mana tafiyar ne dan mu samu sauyin muhalli watak'ila hakan zai sa ta huce daga murdewar da ta yi. Jikina na rawa na dinga siya mata komai na ga ni. Amma Wallahi yadda kika san mugun abu na yi mata haka ta sake botsare wa. Tunda muka dawo ta sake taurare wa. Wai a ce yarinyar mace kankanuwa kamar wannan ta iya BAK'AR TA'ADAR gaba da miji haka siddan?"
Na kalle shi na ce "TA'ADAR da baka yi ta sharri a baya, yanzu so kake ka k'ware a kanta. Bana gaishe ka? Masharranci kawai!
Babah ta ce ",Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ashe kina iya zagin miji Yabi? A gabana kika ce masa masharranci? Ta jijjiga kai tare da ce wa "Tun baku je ko ina da zaman auren ba kun fara zaman da babu mutunci a ciki?"
Ta dinga sababi ta inda ta shiga bata nan take fita ba. Gabadaya ta hadamu ta ki yarda da gaskiyar kowa.
Ta kalle ni ta ce "Da kam ni kad'ai nasan wulakancin da zan yi masa a kan abubuwan da yake yi miki. Amma tunda na gane ba ki d'auki tarbiyar gidanmu ta barranta daga zagin mijin aure ba. To ai bani da ta ce wa. Domin na gane dukkanku ne baku da mutunci, dukkanku ne kuke son yiwa auren tawili".
Ni da d'an-uwana kuke son ku tozarta, ku kunyata, ku jefamu cikin bak'in ciki da zunden jama'a ".
*Saiwowin dahuwar tattabaru da na kaza masu kyune matuka d agaske Hajiya. Daga chadi suke. Ki jarraba ki ga yadda Zaki dawo da kuruciyarki, idan kuwa zaku aurar da y'a ko kanwa ki mata amfani da su. *
*Saiwowin maganin sanyi kuwa sun Fi kowanne tafiya sabida kyaunsu*.
*Akwai kayayyaki.masu kyau*
*Tuntube ni a wannan lambar*
*08032773332*.
*Mu hadu a Kashi na uku*
✍️
Post a Comment for "BAKAR TA'ADA BOOK 3 Complete Hausa Novel"