BAKAR TA'ADA BOOK 4 Complete Hausa Novel
*BAKAR TA'ADA BOOK 4 Complete Hausa Novel
*BY*
*SURAYYA DEE*
*Ina da saiwowi marasa illah. Masu matukar amfani da gamsarwa*.
85&86.
Ta fashe da kuka tana fad'in ai bata san haka zamu yi mata ba. Da bata zo gidanmu ba. So muke mu kunyata ta ita da Baban Marina.
Dukkanmu kowa ya shiga tashin hankalin kukan da take yi. Domin kuka ne wanda yake bayyana tsananin bakin cikin da me yinsa yake ciki.
Da k'yar na bude baki na ce "Dan Allah ki yi hakuri Babah".
Bata kula ni ba, ba kuma ta fasa kukan ba.
Da k'yar ta yi shiru. Amma duk juyin da muka yi akan ta yi hak'uri ta tashi ta shiga daki bata ko yi motsi ba bare ta tanka.
A wannan ranar na gane ita ma kafaffiya ce ta gaske. Domin kuwa dukkanmu a falon muka kwana a zaune, don bata yarda ko kishingida ta yi ba.
Tashin hankalin da muke ciki tamkar idan an tsaga jikinmu ba za a ga jini a ciki ba.
Ana idar da sallar asuba kuwa ta fice ko sallama bata yi mini ba. Haka nan Tijjani bai kai ga dawowa ba. Na bita ina fad'in "Dan Allah Babah ki rufa mana asiri ki yi hakuri, ki dawo ki gafarce mu."
Tafiya kawai take yi. Muka yi kicibus da shi ya dawo daga masallaci. Duk kokarinmu akan ta dawo bata yarda ba. Duk rokon da Tijjani ya yi akan ya mayar da ita bata tanka ba, bare ta amince.
Akan dole na dawo gida a dalilin ya ce na taho saboda mun bar yara.
Na zauna ina hawaye domin ban tab'a ganin Babah ta yi fishi irin haka ba tunda na ke.
A sururuce na shirya yara, na basu abinci . Amma ko makaranta na kasa tafiya. Kan dole suma suka zauna. Har azahar babu Tijjani babu labarin sa. Na tabbatar bin ta ya yi dan ya bata hak'uri. Tun fil-azal yana gudun bacin ran ta. Bare kuma yau da ta yi matsanancin fishi.
Sai la'asar ya dawo gabad'aya ya yi zuru zuru, ya hargitse. Kallon sa kawai na yi na gane bai ci komai ba. A sanyaye na masa sannu. Ya zauna a falon ya amsa mini shi ma a raunane. Kaina a kasa na ce "Ya ya Babah?"
Ya ce "Bata huce ba. Ya zuba mini ido ya ce "Asiya taimake ni ki fada mini laifukan da nake yi miki."
Na yi shiru na k'i ce wa komai. Ya numfasa ya ce "Wallahi sai kin fada mini, na gaji da wannan jidalin na ki. Komai na yi miki babu gwangwaninta, kin tada hankalina kin tashi na ki. Mene ne haka. Kowa ya gan ki sai ya ce kina cikin damuwa ko jinya mai tsanani. Me nake yi miki hakan?"
Na dauke kai daga kallonsa. Ya taso daga inda yake a zaune ya gurfana a gabana. Ya ce "Tun ban miki duka ba, ki bude baki ki fada mini musgunawar da nake yi miki"
Na ce "Doke ni kawai, ai ka fi ga hakan ranka ya dade Alhaji".
Ya damke ni ya ce "Tunda kika yi mini sanadin da uwata ta yi mini tofin Allah tsine Bilhillazi komai zai iya faruwa a tsakaninmu ".
Ganin ya rikice da gaske idonsa ya kad'a tamkar wanda ya sha kayan maye.
Yasa na bude baki na ce "Son ka ne bana yi, na gaji, kawai ka sallame ni".
Jikinsa ya saki, damkar da ya yi mini ta yi sanyi a dalilin ya rasa karfinsa.
Ya zuba mini ido tamkar mai son ya fahimci hakikanin abin da yake cikin zuciyata.
Murya babu amo ya ce "mene ne dalilin janye soyayyar da kika yaudare ni da ita, har na yi zaton babu abin da zan yi ki janye ta Asiya?".
Ban amsa masa ba. Ya kasa hak'uri ya ce"Mene ne bana yi miki? Duk abin da na gani burina na siyo na kawo miki, ko na siyo wa y'aya'n ki. Wanne nau'in abinci ne bana ajiye miki duk tsadarsa?
Wanccan watan kina ce mini kayan Oriflame kike son amfani da shi, haka na daure na ce ki fadawa yar lame din da take siyarwa ta aiko miki, kuma tuni na biya. Da me na rage ki da kika janye samar mini da nutsuwa?
Tunda muka dawo gidannan bamu jitu sosai ba, bamu samu nutsuwar da ta dace da mu ba. Na dauka bandakin da na samar miki a cikin daki zai sa ki yi farincikin ki gane komai kike so sannu a hankali zan yi miki shi "
Ido cikin ido na kalle shi duk da bai sake ni ba, na ce "Duk wadananan abubuwan da ka lissafa hakkina ne da ya zama wajibi ka yi mini su, ba wai taimakona ka yi ba. Idan kuma yinsu alfarma ce to ka daina bana so. Daki mai bandaki kuma bana sonsa, nafi son wanccan gidan da yake fallen falle mai bandaki a tsakar gida, domin nafi samun gamsuwa da mutuntawa a cikin sa. Ya sake ni yana fad'in "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Asiya sai yaushe mata zaku gane hidimar da take kan namiji ba zata bar shi kullum ya mu'amalance ku yadda kuke so ba? Da din da kike marari ba ni da abin yi ne, ina rayuwa ne a takure saboda bana iya samar miki abubuwan da suka dace da ke. Yanzu kuma da na samu hanyar daukan nuyinmu sai ya zama tashin hankalin? Shi kenan sai ya zama laifin da zaki janye soyayyar da kike yi mini?"
Na ce ",Eh dama ai ba son ka nake yi ba. Kirki da ririta ni da kake yi ne ya janyo maka soyayyata. Amma tunda ka janye su, nima na fasa son naka sai ya ya kuma? Har kana kumfar bakin ka kai ni Kano ka mini siyayya to ga kayan can bana so. Tunda har zaka yi waya a cikin dakin da kasan ina ciki kana fad'in baka tsorona, zaka bayar da mamaki akan lamarina. To ina ce sai na damu da kai ko kuma idan na zauna da kai? Sannan zaka tozarta ta ni ta hanyar nunawa duniya ni din ba komai ba ce a wajen ka. Ni kuwa me zaka yi mini na ga farin ka Tijjani?"
Ya sake ni a matukar sanyaye. Domin ya gane da dukkan zuciyata na shirya wa ko wacce irin fitina. Ya zauna kawai ya jingina da bango sama da awa bai iya ce wa komai ba.
Sallah ta fitar da shi. Ya dawo ya zauna a inda ya tashi, gabadaya ya zube tamkar mai amai da gudawa. A sanyaye ya kalle ni ya ce "Ba ni shayi na sha. Yau ko ruwa ban kai bakina ba. Ban yi masa musu ba na hado na kawo masa. Yaran namu su kansu sai suka zama babu walwala a dalilin sun ganmu a birkice.
Yana dawowa daga sallar isha ya rufe gida. Da yake da yaran ya je. Suna dawowa Hamim ya yi barci. Hanif ne ya dan jima yana kallon cartoon kafin shi ma barcin ya sure shi bai sani ba.
Har lokacin muna zaune jigum jigum tamkar masu zaman makoki. Ya numfasa ya ce "Asiya mu fahimci juna mana. Ko motsi ban yi ba. Bare na tanka masa. Ya ce "Na rasa gane halin da nake ciki. Gabadaya jina nake yi a juye. Amma mu fahimci juna. Kin ga Babah ta yi fishi da mu mai tsanani. Mu shirya kanmu, gobe sai mu je mu bata hak'uri."
Na ce "To".
Ya ce "Ban gane to ba Asiya".
"Allah wahidun! Me zan ce maka to?
Na ce a,a?"
Ya kalle ni kawai.
Ya mik'e ya sure ni tamkar yar tsana ya yi dakinsa da ni. Yana fad'in "Mu je kan katifa na rarrashe ki, domin na gane rarrashi akan katifa yafi na kan gado ratsa jiki".
Na dinga mutsu mutsu tare da son na kwace amma ina.
Ya mini kamun kazar kuku. Duk fizge fizgen da nake yi bai kula ba. Sai da ya dangana ni da katifar. Ya bini ya mini rumfa da jikinsa. Karshe ma ya sakar mini nauyinsa ta hanyar danne ni. Na daure na ki na nuna na kosa.
Ya bini da kisses da sauran al-amura masu nauyi.
Tun ina dauriyar kin karbar rarrashin nasa har na kasa jure wa na fara karba ta hanyar sakar masa jiki da daina ture shi. Sai da ya gama jagwalgwala ni, sannan ya kankance murya ya ce "Da gaske ba kya sona Asiyaty?"
Na dauke kai ina jin kunya na kama ni. Domin ni kad'ai nasan yadda nake jin sa a zuciyata. Kawai wulakancinsa ne yake neman kwantar da ni.
Sai da yasan yadda ya yi muka shirya, ya zangwanyar da fishin da na yi.
Bayan ya jaddada mini, ba abin da yake so nan duniya sama da ni.
Cikin saa'a bai mini zancen mutuwa ba.
Bamu yi barci ba, a wannan dare, domin ko da muka samu nutsuwa. Maganganu muka cigaba da tattauna wa. Haka ya dinga bani hak'uri tare da rokon na daina yi masa irin wannan fishin mai tsanani. Na daina damun kaina ta hanyar kaurace wa abinci da kuma walwala.
Sai da muka karya, muka shirya sannan muka dauki hanyar Bulkachuwa.
Da k'yar Babah ta sauraremu. Mun shafe fiye da awa ban da sallamarmu bata sake kallon inda muke ba. Harkokokin ta take yi ita da su Hanif. Su kawai ta bawa ruwa da abinci, mu kuwa ko kallon inda muke bata sake yi ba.
Ni na fara yin kundubalar bin ta daki. Yayin da ya biyo bayana, amma ya toge a bakin k'ofar tabbacin jiya bai ji da dad'i a hannunta ba. Na zauna a gefenta. Na lankwasa harshe na ce ",Dan Allah Babah ki yafe mana. Idan ba ki huce ba, ba zamu ga haske ba. Kuma tun jiyan ma mun sasanta kanmu."
Sai lokacin ta bude baki ta ce "To ni kuma ina ruwana da al'amarinku? Ni da kika ganni bana shiga kasafin da babu mutunci a cikinsa. A gabana ki zagi mijin ki Yabi?" A sanyaye na ce "Ban zage shi ba Babah". Ta ce "Kalmar da kika fada masa ai zagi ne
Na yi shiru. Ta dinga yi mini fad'a
tamkar zata doke ni. Ganin ta tsananta ya sanya na ce ",Babah Wallahi ni kad'ai nasan kuttun da yake cusa mini. Yanzu ba dama ya dawo ya zauna mu yi hira, sai dai ya yi da wayarsa, na sani kuma da y'anmata yake yin hirar ni ya bar ni gaho. A Kano kuwa da kunnena na ji yana zancen zai tura gidansu".
Ta ce "Akan me ba zai yi aure ba? Akan ki zata zauna, me ce a cikin kishiya ne da kika tsananta wa kanki k'in ta. Allah ya ce su yi mataye sama da d'aya idan zasu iya adalci. An janye ayar ne, ko kuwa rushe ta zaki yi, ki kafirta?"
Tana rufe baki na rushe da kuka ina fad'in "Kin bi bayansa ya yi mini kishiya ko Babah?"
Ta janyo mafici ta shiga kwada mini tana fad'in "Na bi bayan nasa sakarya. To hakan da kike yi masa ne zai hana shi k'ara auren. Tun yanzu kin tattara kin bar shi, idan ta zo ba sai ta karbe shi gabad'aya ba."
Cikin kuka sosai na ce "Babah na rantse da Nasiba yake soyayya. Ya auro kowa amma ban da ita. Ni Wallahi bazan yi kishi da ita ba. Mutuwa zan yi, idan kuwa ban mutu ba, daga ranar da ya aure ta. Billahi a ranar na haramta gare shi!"
Na fada cikin matsanancin kuka.
Ta saki maficin hannunta ta ruko hannuna ta ce "Ni ma matukar bai nisance ta ba Wallahi sai dai ya nemi wata uwar. Na yafe shi. Share hawayen ki har abada ba zaki yi kishi da ita ba. Na miki wannan alk:awarin".
Ya shigo a sanyaye ya durkusa a gabanta ya ce "Ki tsananta yi mini addu'a. Ban san me yasa nake jin ina zakuwa akan lamarinta ba. Idan na je wajenta kwata kwata bana jin sukuni dan tsananin takurar da nake shiga. Ko ganin ta bana son yi. Amma da zarar na taho kuma sai na ji zuciyata tana azalzalar na koma Toro dan na ganta. Ku mini addu'a, ku mini uzziri dan girman Allah. Wallahi addu'ar da nake yi ne ma take saisaita mini al-amurana, amma abubuwan da suka sha kaina masu tsanani ne. Ku taimake ni, kune mafi kusa da ni a yanzu."
"Tirkashi"
Babah ta furta a fili domin ta fahimci ba haka aka bar shi ba tabbas.
Ta nisa ta ce "Allah mun tuba, Allah kada kasa shaid'an ya yi galabar tsinka siriryar igiyar zumucin gidan marina da ta yi saura."
Kukana ya tsaya cak a dalilin yadda na ga Babah ta tsorata da furucinsa ainun. Yayin da zuciyata ta shiga zullimi sosai. Ke nan Tijjani da gaske yana burin auren Nasiba.
Wani irin k'ullutu mai ciwo ya tokare ni.
A matukar sanyaye take fad'in "Zan dage da addu'a, kai ma ka dage da addu'ar da kuma danne yadda kake ji akan lamarinta. Sannan ka saka a ranka ba matar ka ba ce, domin matukar ina raye ba zaka had'a su ba, kai gabadaya ne ma ba zaka aure ta ba. Dalilin da ya hana a baka ita a farko, shine dalilin da yasa ba zaka zama mijinta ba a yanzu"
Ta juyo gare ni ta tausasa harshe ta ce "ki yi hakuri kin ji Yabi. Yana cikin canka cakare. Ki tallafe shi har ya tsallake wannan siradin. Mutanan yau da yawansu mugaye ne, zuciyarsu cike take da gilli mai yawa."
Na kasa ce wa komai domin na kidime, idan har Tijjani da yake kawaici a gaban Babah zai bude baki ya ce yana zakuwa akan lamarinta a gabanta to lah shakka abin da yake ji babba ne.
Hawaye ya dinga tsere a fuskata. Tabbas ina cikin tashin hankali. Bana jin tsoron karawa kishi da ko wacce mace, domin na yi imani namiji baya zama da wacce baya so. Idan kishiya ta kere ka a wani fanni to kai ma da ikon Ubangiji sai ka samu fannin da zaka kere ta. Abu biyu ya dame ni. Nasiba suntumemiyar halitta ce irin matan da suke birge Bulkachuwa. Sannan mahaifiyarta kowa yasan bata barin mazanta haka, a hannunta suke, ko marigayi mijin Nasiba kullum a yunkurin mallake mata shi ta ke. Na tabbatar Tijjani ma za'a yi komai dan ta sha gabana, tunda a yanzu ma da bai aure ta ba idan ta gan ni kamar ta doke ni haka take ji. Da k'yar Babah ta shawo kaina na samu nutsuwa, na daina kuka.
Sai yamma muka baro Bulkachuwa. Dan haka sai dare muka iso.
Na daure na yi k'arfin zuciya ban cigaba da share shi ba. Na rungume shi da hannu biyu muka cigaba da zama lafiya. Duk dare kuma sai ya fita waje ya yi waya. Idan kuma yana gida baya amsa waya matukar bata shafi kasuwancinsa ba. Asalima kamar ya dakatar da a a kira shi idan yana gida ne. Da kaina na fahimci da gaske ya canja, wulakancin yin waya idan yana gida yanzu ya daina, asalima kaffa kaffa yake kada na tuntsire masa.
Yayin da ni kuma na tsananta addu'ar Ubangiji ya tsaremu akan duk abin da ake nufi da mu na sharri. Sa'a d'aya har yau Tijjani bai bar sallar dare ba. Yana wahalar gaske ya kwanta bai tashi ya yi nafila ba. Kullum kuma a cikin addu'ar duk kaddarar da zata hau kansa ta zama mai sassauci daga Ubangiji.
Na sani asiri zai kama shi, amma na yi imani zai zo da sauki tunda wadatar da ya samu bata sanya ya bar Allah ko ya koma BAK'AR TA'ADAR neman matan da ya yi a baya ba.
Na kira gwaggo na fada mata komai na roki ta tsananta yi mini addu'a.
Cikin rarrashi ta ce "Ina yi miki Yabi. Zan kuma ninka addu'ar da ne yi miki. Abin da zan fad'a miki shine ki barwa Allah ya yi miki zabi, ba wai ke ki yanke hukuncin idan ya aure ta kin bar shi ba. Allah ne ya halasta dan haka akwai bukatar ki nutsu, kada ki bari Ubangiji ya bar ki da dabarar ki."
Da kuka na ce ",To Gwaggo".
Cikin rauni ta ce "Allah ya yi miki albarka ya shiga tsakanin ki da duk abin da zai birkita miki auren ki. Da ikon Allah ba za'a kai ki k'asa ba. Kin yi sa'a kina cikin albarkar uwa da uba. Dan haka ki yi ibada tuk'uru ki kuma yi barci da minshari ba abin da zai same ki sai alheri da ke da dukkan zuriar ki Yabi".
"Na gode Gwaggo". Na furta cikin rawar murya irin ta kuka.
Sannu a hankali na samu sassauci na cire hankalina kan maganar Nasiba da Tijjani. Iyaka dai ban daina addu'a ba, ban daina tofawa Tijjani addu'ar tsari a cikin duk abin da zai ci ko ya sha ba.
Na rungumi zaman lafiya a tsakanina da shi. Na rungumi karatuna da y'aya'na.
Mussaman a yanzu da nake gaf da kammala N.C.E.
Twins sun girma domin suna shirin shiga shekaru shida da haihuwa. A lokacin suna aji daya na firamari. Hanif yafi Hamim kokari domin kullum na daya yake zuwa. Amma kuma ba shi da magana. Yayin da Hamim yake zuwa tsakanin bakwai zuwa goma. Amma kuma ba wanda bai san shi ba, saboda suruntunsa, ya kuma yi sa'a ya iya turanci. Kamar wanda ya girma a cikin masu yi. Surtunsa da fadansa ya sanya a ke fafatawa da shi. Sau tari sai ya yi tsokana ko laifi a hukunta Hanif a madadinsa tunda ba'a gane su. Shi kuma Hanif ba zai ce ba shi ba ne. Ko ni ma yana mini wannan iya shegen. Dan haka na daina binsu a guje. Sai ya manta yana ta surtunsa kamar aku sannan zan rik'e shi.
Duk sadda na je Toro bin mu kawai ake yi da ido ni da y'aya'na a dalilin yadda muke fita daban muke daukar ido.
Wadanda kuma basa iya boye wa hassadarsu a fili sai da kawai na ji suna fad'in iyalin babban direba shugaban masu kayan gwari na Bauchi gabad'aya. Ko yaushe aka nada masa wannan mukamin?
Ni da Nasiba kuwa muna gaisawa, bama gaba sai dai babu doguwar hira. Domin idan ta gan ni sai na ga tana d'ad'are wa bata da katabus duk da bata yi mini kallon raini ko na izgili. Shi yasa nima nake jarumtar mu'amalantar ta da sakakkiyar fuska.
Ina kammala rubuta jarabawar karshe. Na fara hutun zirga zirgar da na shafe shekaru uku ina yi. Hatta lalle sai da na tafi hutun wata guda a kokarina na son na dinga yin barci yana isa ta. Da zarar na sallami twins da babansu sun fita da yake shi yake kai su makaranta, sadda zasu tashi idan ya dawo yana gari sai ya dauko su. Idan kuwa baya gari sai su taho da yaran bayan layinmu.
Suna fita nake rufe gida na gama abin da zan yi na karya na kwanta na yi barci, bana tashi sai azahar.
Daidai wannan lokacin Tijjani ya k'osa na samu ciki. Har ta kai ya fara zargin ni nake yin wani abu dan kada na sake haihuwa.
Haka kawai rannan ya tuntsire akan ba zai yadda ba. Daga haihuwa d'aya zan kulle bakin mahaifa, to shi ba yahudu ba ne, ba kuma ba Caine ba ne da za'a kiddidge masa yawan y'aya'n da zai haifa. Ya riga da ya gano hak'uri kawai yake yi, to yanzu kuma ya gaji.
Na kalle shi a tausashe na ce "Ashe ba Allah ne ke kawo ciki da haihuwa ba Baban 2?"
Da kumfar baki ya ce ",Tun kafin ki zo duniya nasan da hakan Asiya. Akan me duk abokan aurenmu haihuwarsu uku amma ke sau daya tak. Ba dan Allah ya so ya bani biyu tashi guda, da yanzu d'aya ne jallin jal. Gaskiya ni yara da yawa nake so malama."
Na sake daure wa na ce "Allah bana shan komai ka yarda da ni".
"To akan me ina bakin kokarina ba zaki karbi cikin ba?"
Na zuba masa ido cike da fargabar ko dai ya fara afa wani abu ne. Tas
na gan shi babu alamun maye ko rashin lafiya.
Ido cikin ido na ce "Wato ma ni ce na ki karba ko?"
Fuska a daure ya ce "Eh mana. Nima ba haka kika yi ta yi mini sadda baki samu ciki ba, ce wa kike ni ne ban yi miki ba. To nima yanzu kawai ki karba Asiya na gaji, ki yi ciki abin da na sani, na ke kuma son ga ni ke nan".
Na yi dariya na daga hannu sama na ce "Allah kasa na samu ciki ya zauna kada ya zube ".
Ya saki ransa ya ce "Yanzu kika nemi zaman lafiya tunda kin roki mai bayar wa. Kuma na saka miki doka kullum ki dinga wannan addu'ar idan kin yi sallah."
Na gintse dariyar na ce "To mai sunan shehu".
Ya harare ni tare da ce wa "Kin dauki umarnina wasa ko?"
Na girgiza kai da sauri tare da ce wa "Wace ni da wasa da lamarin ka, indai ba so kake Babah ta ce na raina miji ba".
Da haka na lallaba na shiritar da maganar, dan kuwa da na dauka da zafi rikici zamu yi mai yawa. Tunda da gaske ya kosa na haihu kamar bamu da yara kwata kwata.
***
Baba Maryo ta isa gidan yar'uwarta a Bulkachuwa da la'asar lis. Babah ta karbe ta da karamci da walwala. Har dare suna hirarsu da ta shafe su. Sai da daddare sun kwanta. Babah a kasa ta yi shimfida yayin da kanwarta yake kan gadon.
Cikjn hirarsu ta kutso da maganar Nasiba da Tijjani.
Ta ce "Na rasa ga ne inda matsalar take, sai sun shirya ya ce zai tura gidan iyayenta sai kuma magana ta kwanta. Sama da shekara guda yana mata yawo da hankali. Shi bai fito ba, shi kuma ya fantsama mata mane ma".
Da madaukakin mamaki ta ce"Ban fahimce ki ba Maryo!"
Ta kuwa ce "Maganar y'ar ki da Tijjani mana. Ai gara ki yi magana da waliyyinsa a yi komai a gama na gaji da wannan hirar tasu ba tare da an yiwa lamarin kai ba".
Babah ta sandare a zaune, ta cika k'warai da rashin kunyar kanwarta.
Amma sai ta ce "To shi ban da ma rashin tunani me zai sa ya nemi Nasiba da sunan soyayya. Ai ita matar manya ce. Sannan ta ya ya zai hada yan'uwan jini kishi?"
A ladabce Baba Maryo ta ce "Wa ce ce Nasiba da za'a ce tafi k'arfin Tijjani? Bayan haka zumuntar ta da Yabi ba zai hana su zama kishiyoyi ba, tunda Allah bai hana ba."
Ba ja in ja Babah ta ce "Gaskiya ba zai yiwu ya had'a Yabi da Nasiba a matsayin matansa ba".
Haka kawai ta fad'a Baba Maryo ta fashe da kuka tare da ce wa "Ta fifita bare akan Nasiba".
Babah ta ka'du da furucin yar'uwarta. Ta kasa daure wa ta ce "Wacce baren na fifta?" Ta yi tambayar da dukkan zuciyarta.
Da kuka ta ce "Yabi mana. Dama sai da na yi zargin ke ce baki d'aure gindin ya aure ta ba, saboda kina gudun zuciyarta da ta uwatata. To komin abin dai ni ce taki ba Asama'u ba".
A sanyaye Babah ta ce "Ni Yabi d'iyar Asama'u ce da ta zo da ita daga wani gidan ko kuwa tare da Yaya Sani ta same ta?"
Cikin ko in kula ta ce "Shine ubanta amma ai wata ce ta haife ta. Ni kuwa fa? Jikina Nasiba ta tsaga ta fito. Kuma tun lokacin Annabta zumuncin dangin uwa yafi na uba sahihiyar soyayya da tausayi".
87&88.
Babah ta kasa ce wa komai domin ita gabad'aya ma alamarin tsoro ya shiga bata. Tana kuma mamakin rashin kunya da son kai irin na Maryo.
Bata yi zaton son zuciyarta ya kai hakan ba.
Ta kasa ce wa uffan saboda tsananin kaduwa da ta yi.
Ita kuwa ta dinga kuka tana face majina tamkar Dada ce ta kwanta dama.
Washagari ko karyawa bata yi ba ta ce zata juya. Da k'yar Babah ta roke ta akan ta bari ta karya.
Rai a bace suka rabu a dalilin Babah ta tabbatar aure kam babu a tsakanin Nasiba da Tijjani.
Rai a matukar bace ta isa Toro. Ta gurfana gaban Dada tana kuka tana fad'a mata karya da gaskiyar cin mutuncin da Hauwa ta yi mata.
Dada ta taya ta bacin rai tare da rarrashinta tamkar yarinya karama. Tana cin alwashin sai ta ci mutumcinta tunda bata san yakamata ba.
Bijirewar da Babah ta yi akan auren tare da fitowa baro baro da ta yi ta ce alamarin ba zai yiwu ba. Sai ya zama d'an zani. Domin hakan ya fusata Baba Maryo tare da cin alwashin sai Tijjani ya auri Nasiba ko zata yi yawo tsirara, ta ga karshen rashin kara da nuna banbanci.
Takanas ta tafi cikin jeji can kudu da Jos. Ta samo asiri da surkullen da muradinta zai cika.
*Bayan waatanni biyu*
A hankali Tijjani ya fara rikice mini fiye da bara. Sai mu kwana gari ya waye bai ce mini uffan ba. Zan masa magana goma bai fi ya amsa ni sau biyu ba a gajarce.
Ya daina shayin yin waya a gabana. Yanzu har an kai jallin da zai bawa twins waya su gaishe ta. Duk da dai bai tab'a kama suna ba.
Sai ya ga dama yake cin abincina. Jiya ma da na zauna kusa da shi ce mini ya na tashi yana bukatar kad'aici. Murjewar da na yi, nan da nan na fara tsomare wa. Sosai ya murde irin yadda ban taba zaton zai yi ba. Na hakurkurtar da zuciyata na dinga ba shi hak'uri tare da rokon ya fad'a mini laifin da na yi masa.
Yana bude baki sai ce wa ya yi "Haihuwa yake so. Tunda ba zan haihu ba, shi aure zai yi, idan zan zauna na zauna idan kuma bazan zauna ba, to bai rik'e ni ba."
Na zuba masa idona da suka soye. Na ce "Tsakanin ka da Allah kana mini adalci Tijjani?"
Ya hassalo ainun tare da ce wa "Ta ya ya zan yi miki adalci Asiya? To ko kawai zaki yi gaba ko zaki samu adalin?"
Na sake daskare wa. Na yi maza na kame bakina domin na gane komai na iya faruwa a tsakaninmu.
Amma hawaye ke tsere babu jinkiri kuncina.
Ya ja tsaki ya fice ya bar ni. Yana fad'in "Me za'a yi da mace mai rainuwa da azababben kishi. A ce mace ba zata taimake ka ta rufa maka asiri, ta taya ka son abin da kake so ba. Sai sarhutu da mance alheri kawai ta iya ".
Na yini cikin bacin rai. Yayin da shi kuma ya yi tafiyarsa Toro da yara bai damu da halin da ya bar ni a ciki ba.
Ina kuka na d'auki waya na bugawa Baban Marina karon farko da na yi hakan tunda ya aurar da ni. Na kasa magana sai kuka nake yi masa mai tsuma zuciya.
Bai katse ni ba. Sai da na gaji dan kaina na katse wayar.
Baban Marina ya dawo gida cikin sanyin jiki a dalilin yadda kukan Yabi ya buge shi.
Ya leka kofar Dada dan ya bata man zafin da ya siyo mata sai kawai ya ga Tijjani da Nasiba a gefen bisihiyar zogale suna zance. Dada na daki abin ta. Duk da ba yau ya saba ganinsu ba, amma yau din sai da zuciyarsa ta buga da tsananin gaske.
Ya amsa gaisuwarsu cikin k'arfin hali. Ya shiga wajen Dada ya fito, ya fita.
Ya zauna kan tabarma amma zufa ta rufe shi. Ya dinga jin wani iri. Duk yadda ya so jurewa kasa wa ya yi. Yana tambayar kansa yanzu Tijjani yana da rigar da za'a bashi aure ke nan?.
Ya tuna irin kukan da Yabi ta kira ta yi masa dazu, ya san kuka ne na neman agaji, kuka ne mai harshen damo. Daren ranar ya yi masa tsawo ainun.
Washagari ana idar da sallar asuba ya ce Salisu ya raka shi Bauchi.
Tamkar jifa haka Yabi ta gansu. Zuciyarta ta karye. Domin ta hango rauni da wata irin soyayyar ta a kan fuskar mahaifinta.
Tare da Tijjani suka musu iso zuwa falo.
Yana amsa gaisuwarsu ya yi gyaran murya ya ce "Zuwa na yi takanas dan na fad'a miki ce wa ki yi hakuri ki zauna a dakin ki. Ki kuma sauke dukkan hakkina da kika san Ubangiji ya dora miki. Daga nan har zuwa lokacin da Allah ya kaddara muku zaman kada ki yarda ki zalunce shi. Kada kuma ki fito babu izininsa. Aure da kike ga ni darajar sa ta wuce duk zaton mai zato. Sai dai bisa adalcin Ubangiji ya kewaye shi da dokoki da kuma sharudda daban daban. Bai barmu kara zube ba. Ina rokon ki, ki k'ara hak'uri a cikin wannan tsukun da ake son kaimu k'asa da bak'inciki mai tsanani. Idan har kika yarda kika yi hak'uri, ni kuma na miki alkawarin zan jaddada damar da shari'a ta baki na zabin cigaba da zaman ko akasin hakan matukar zalunci da cin fuska ya shigo gidan auren ki".
Cikin kuka da rawar murya na ce "To Babanmu".
Ina fad'in haka ya mik'e tare da ce wa "Allah ya yi miki albarka. Ya fice bai ko bi takan tagwaye da suke ta rige rigen gaishe shi ba. Yaya Salisu ne kawai ya amsa musu tare da ciro ledar alawowi a aljihunsa ya damka kowa tasa ledar.
K'warai Tijjani ya muzanta da yadda suka fice basu bi takansa ba. Ya bi bayansu. Ba jimawa ya shigo ya zauna. Ya ce "Baban Marina ya canja, ya yi bangaranci. To wai a kaina aka fara k'arin aure ne da za'a mini wulakanci irin haka?"
Ban kalle shi bare na ba shi amsa. Maimakon shi ma ya sawa bakinsa linzami tamkar yadda na yi sai ya zarce da ce wa "Baban kasuwa ne kawai mai mace daya, shi ma nasan a dole yake zaune bai k'ara ba. Shi Baban Marina din da yake tunzuri irin haka ai uku ne da shi, shine ni zai nemi hana ni jin yadda a ke ji?"
Na kalle shi da fishi sosai na ce "Ya isa haka! Ina rantse maka da Allah Tijjani zamu kwashi y'an kallo. Komai kake ji da shi na wulakanci ya tsaya iya kaina. Amma ka yi kad'an ka tabo alfarmar ubana. Ya wuce hakan Wallahi".
Bansan ya aka yi ba jikinsa ya mutu. Ya kasa ce wa uffan.
Na ja tsaki mai tsananin gaske na tashi na bar masa wajen.
Muka k'ulla gaba sosai. Domin ya kullaci zuwan Baban Marina da kalamansa, dazu har da shaguben laifinsa ya shafi twins a wajen Baban Marina bai kula su ba. Yana wankin kayansu yana mini azanci. Ya kuma zabe iya nasu ya bar mini nawa. Ko kallo bai ishe ni ba. Domin sosai nake jin zafinsa.
Ranar da aka tabbatar mini su Baban Tsakiya sun kai masa kudin aure gidan iyayen Nasiba kwana na yi ina kuka. Sassafe na yi Bulkachuwa. Ina zuwa na sake tarar da wani abin alajabin. Fad'a kawai Babah take mini wanda babu rarrashi ko nuna soyayya a ciki. Cikin sanyi ainun ta ce "Haba kina da k'warzaba Yabi. A kanki aka fara yin kishiya ne? Tun yaushe kike jidali?. To ni bazan iya hana shi aure ba. Ni nan da kike ganina kan kishiya aka kawo ni. Mahaifiyar ki ma kan kishiyar ta zo, sannan bayan ita ma ya sake yin wata. Ina dalilin wannan kai komon da kike yi na azina?"
Na kafe ta da ido na ce "Har cikin zuciyata nasan ba haka siddan kika mini hakan ba. Allah Ubangiji ya kawo karshen wannanan al'amarin." Na fada ina kuka sosai. Ina kula da yadda kukan nawa ya raunanta amma ta kasa ce wa komai.
Haka na dawo Bauchi da kaina. Tare da hak'urin dole. Amma ni kad'ai nasan me nake ji a zuciyata.
*Toro*
Tunda a kai kudin auren Tijjani gabadaya lafiya ta yiwa Baban Marina karanci. Ba komai ke nukurkisar sa ba illah yadda babu wani mutum d'aya a gidan Marina da ya fito ya nuna rashin dacewar al'amarin. Ya kasa samun Hauwa uwar Tijjani a waya. Kowa murna yake yi da auren.
Tun jinyar na sand'arsa a hankali har ta kai ya kwanta. Ba'a samu wanda ya fito ya soki al'amarin a cikin yan'uwansa ba, balle a farga da yadda bakinciki ke sakatarsa. A wannan karon dukkan juriyarsa ta k'are. Ya yi amannar yan'uwansa basa son sa da gaske. Ban da haka mene ne za'a fifita Nasiba akan Yabi da take yar gidan?
A cikin wannan yanayin Babah ta Bulkachuwa ta zo garin.
A dakinsa ta tarar da shi. Kallon sa kawai ta yi hawaye ya tsinke mata. Domin a cikin sati kacal tsufa ya keto masa na ban mamaki. Tausayi ya kamata, ta sani bakin cikin yadda al'amarin ya juye ne yake neman kassara shi. Mussaman yadda kowa ya koma bangaren uwar Nasiba da ta take komai ta runtse idonta. Babban abin da yake damunta bata san me yasa take jin tamkar idan ba a yi auren Nasiba da Tijjani ba zata dauma a cikin kaico. So take ta bude baki ta barranta kanta daga lamarin amma ta kasa.
Murya na rawa ta ce "Sannu Yaya!
Ya kalle ta da idanuwansa da suka kad'a. Murya babu amo ya ce "Hauwa Tijjani zai yi aure nan da kwanaki kad'an. Bana inkarin k'arin aurensa domin kuwa yana da sukunin da zai ajiye mace hudu ma. Amma ki sani Wallahi ba zai had'a mini y'aya'na guda biyu kishi ba. Idan har dukkan ku babu mai fitowa ya yi magana to ni na yi. Bazan yarda na mutu na bar Yabi a cikin wannan taskun ba. Domin na san kafatalin ahalin gidannan ba zata samu wanda zai mata adalci irin na uba ba. Ke nake da garantin zaki tsaya mata. To ga shi ke ma an juya miki tunani. Shin kina ganin ya dace na zuba ido ana jifanmu ni da ahalina da sihiri bayan na jure dukkan k'iyayya da warakin da na shafe lokaci mai yawa ana mini ni da zugata?"
Kamar a tsaorace ta ce "A a Yaya! Ni kaina ina tambayar kaina me yasa na kasa yin magana? Me yasa nake jin tsoron yin magana? Me yasa tashi d'aya na ji soyayyar al'amarin ta shige ni fiye da komai a yanzu?"
Ya jijjiga kai ya ce "Na barwa Allah ya kawo mini dauki. Abin da nake so da ke yanzu. Yau din nan ki shiga mota ki dauko mini Yabi. Saboda ke na bawa Tijjani ita. Kin sani a wanccan lokacin ba shi da rigar da za'a bashi aure, asalima hana shi ake yi gida da dawa. Ke na bawa amanarta, ke na damkawa ita a hannunki. A yau kuma ina son ki dawo mini da ita salin alin yadda na baki ita cikin girma da arziki".
Ta fara kuka mai tsananin gaske. Tana fad'in "kada ka yi hakan Yaya. Daure mu bi al'amarin a nutse. Tunda har ka gano sihiri ne, ka taimake ni mu lalubo bakin zaren mana!"
Ya yi shiru yana sauraren kukanta. Ya numfasa ya ce "Bayan sihiri ai kin san yadda ni da y'aya'na muka zama saniyar ware. Lokacin da Jabir yake hakilon zai had'a Yabi da Maijidda gabad'aya kowa tofin Allah tsine aka yiwa lamarin. Bansan adadin kashedin da Dada ta yi mini akan na jawa Yabi kunne ba. A gabana Badamasi yake fad'in Jabiru ba zai auri Yabi ba. Iliya kuwa shi ma ya sha fad'in "Daga ranar da aka ce Jabiru zai auri Yabi to a lokacin zai sako masa Maijidda. Amma kuma an zuba ido tare da bada goyon baya a kwace wa Yabi mijin da ba'a yarda aka bata shi ba, sai da aka tabbatar ba shi da mamora. Yanzu kuma da ya samu madogara sai aka ga yafi k'arfin ta. Tunda abin hakane sai ta fito ta basu waje. Adalcin Ubangiji ya ishi kowa.
Kuka kawai take yi tana jin yadda tsoro da sanyi yake d'ada girma a zuciyarta.
Murya babu amo ta ce "Dan Allah Yaya ka janye umarnin na dauko maka ita. Kasan dai yadda Ubangiji ya mutunta sha'anin aure. Ka yi hak'uri mana har muga karshen wannan waki'ar".
Ya yi shiru kamar ya yarda sai kawai ta ji ya ce "Wallahi ba zai had'a su ba. P bi mini kadina. Bare ina fatan na yi tsawon rai dan kawai ran Yabi kad'ai ".
Kukanta ya karu. Tana yi tana ce wa "Allah ka warware wannan dambarwar. Ubangiji ka taimaki zumuncin ka fahimtar da ni abin da yake boye. Allah na tuba astagafirillah. Ta mike ta tafi babu waiwaye. Ya bi ta da ido yana gasgata surkullen dabaibaye zuciyarta aka yi.
Hawaye mai ciwo ya dinga gangarowa ta kwarmin idonsa.
Gwaggo ta shiga ta tarar da shi a hakan. Ta zauna ta ce "Alhaji ba zaka karanta wa kanka damuwa ba? Ina jin tsoron kada ka hadu da ciwon nan mai shanye barin jiki".
Murya a karye ya ce "Ban da darajar sallah da salati Asama'u ai da tuni zuciyata ta buga ma gabad'aya. A ce haka zan kare cikin bak'inciki da tashin hankalin cikin yan'uwana? Yanzu na rasa mutum daya da zai yuwa Yabi kara da alkunya duk cikin dangina? Tausayin yarana gabad'aya ne yake neman kassara ni. Idan na mutu haka zasu yi ta tashi fad'i babu mai tsaya musu, yanzu shi ke nan bani da wanda zai kula mini da alamarinsu ko wanda zan damk'asu a hannunsa?"
Idonta ya ciko sosai amma ta sanya jarumta ta hadiye. Ta ce "To Alhaji ban da abin ka, duk wanda ka damkasu gare shi ai shima zai mace wata rana. Kawai yi dabarar damkasu a hannun Ubangiji domin shi ne rayayye wanzazze. Ina kuma son ka yiwa Hauwa adalci. Al'amarin ne yafi k'arfinta. Shi kansa Tijjani ai ba'a hayyacinsa yake ba. Idan muka daure muka yi hakuri. Muka taushi Yabi ta yi hak'uri komai zai wuce. Duk abin da aka gina shi da son zuciya baya k'arko".
Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa. Ya ce "Kina nufin na sake tirsasa Yabi ta zauna da Tijjani ko da bata son hakan?"
Da sauri ta ce "Eh. Domin babu abin da hak'uri ba zai bayar ba idan aka nutsu."
Ido cikin ido ya ce "To a yau kam bazan d'auki shawarar ki ba. Sassauci d'aya zan yi, idan ta ga zata zauna shi ke nan sai na bita da addu'a. Idan kuwa ta ga ba zata zauna ba, to kuwa ko menene zai faru sai dai ya faru amma zan fanshi y'ata."
Ta kasa ce wa komai domin ta san da dukkan zuciyarsa yake magana.
*Bauchi*.
Ina falo kan sallaya na idar da la'asar ina jan tasbaha. Hawaye kuma sai sintiri suke yi. Yayin da Tijjani yake zaune babu sukuni a tare da shi. Yara kuma suna islamiya.
Na daga hannuwana sama a fili na ce "Allah kai ne mai sarrafa zuciya, Ubangiji ka sarrafa mini ita ta zama mai hak'uri, Allah ka mini baiwa da juriyar shanye ko wacce irin damuwa ba tare da hakan ya tab'a imanina da lafiyata ba. Ina rokon a cire mini damuwa akan wannan al'amarin domin na zama cikin masu imani da abin da ka hukunta. Allah ka warware mini dukkan abin da zai tunkare ni na sharri. Allah ka bawa Mijina lafiya, ka k'ara masa arziki, ka kare shi daga dukkan mummunar kaddara. Ina rokon a shirya zuriata, a tsare mini su, a kuma sanya su a cikin bayi na gari. Allah ka jik'an iyayena ka musu tukuici da aljanna."
Na sake yin salatai da istigifati sannan na shafa.
Na jingina da bango ina ta sakin ajiyar zuciya domin gabad'aya ji nake tamkar na ciro ta, ko na huta da azababben ciwon da nake ji.
Ya sassauta murya ya ce "Asiya na gode miki. Ki cigaba da yi mini addu'a dan Allah. Ina ji a jikina bani da lafiya. Na kasa gane kaina, ki yi hakuri da ikon Ubangiji komai zai faru bazan bar ki ba Asiya".
Cikin kuka na ce "Bari na nawa Tijjani? Sau nawa zaka ga ina kuka ka banzantar da ni, sau nawa kake sanadin sa ni kuka? A da na dauka duk lalacewar giwa ta fi k'arfin kiyashi ya ja ta. Ashe sannu a hankali idan suka yi taron dangi sai su jata su kacaccalata. Amma babu komai na barwa Allah ya zame mini garkuwa."
Ya tsugunna a gabana ya ruko hannuna a tausashe ya ce "Ba dan ki gamsu ba, ina rantse miki da Ubangijin Al-arshi bana jin so ko wacce mace da sunan soyayya ko sha'awa a zuciyata sai ke Asiya. Amma bansan me yasa nake jin zuciyata na tafarfasa a dalilin Nasiba ba. Ina jin idan ban aure ta ba bazan samu nutsuwa ba har abada. Ki yi hak'uri kada ki juya mini baya a cikin wannan halin da nake ciki. Masifu sun dabaibaye ni, ikon Allah kad'ai yake rik'e da tunanina. Amma gabadaya bani da sukuni.
A gida babu nutsuwa a tsakaninmu, a wajen sana'a ta jifana ake yi. Ga shi an kulle mini zuciya da tunanina. Babban tashin hankalina yadda Baban Marina ya shirya kwace mini ke. Dan Allah little kada ki barmu ni da twins. Ya ya ake son mu yi, k'arfin hali kawai nake yi, amma ni yanzu har na fara fatan mutuwa ta dauke ni na huta da wannan dambarwar".
Na kasa kwace hannuna. Wani irin abu ya dinga taso mini. Na gasgata ina son Tijjani k'warai da gaske. Domin saukowar da ya yi, ya mini magana ta rarrashi da tausayawa sai na ji k'ullin zuciyata ya fara kunce wa.
Na fara kuka na ce "Ta ya ya zan yarda kana sona Tijjani alhalin kullum sai ka mini abin da zai sa ni kuka? Yaushe rabon da ka zauna ka ji damuwata, hatta yaran nan sun san ka canja mini. A gabansu kake rufe ido ka tsigale ni haka siddan. Kullum a cikin yi musu karyar baka da lafiya na ke dan kada su kullace ka. Yaushe rabon ka da nemi wani abu a tare da ni, me kake so na fahimta tunda nasan baka da hak'uri a wannan fagen?".
Ya tsananta rikon da ya yi mini ya ce Na gode da kike rufa mini asiri a idon y'aya'na. Allah ya yi miki albarka. Sannan Allah ne shaidar furucin Baban Marina da yake nuni zai k'wace mini ke ya sanya na rasa k'arfi a tare da ni. Wallahi bana aikata komai na b'arna Asiya".
Ban ce komai ba ya sake sassauta murya ya ce "Kin tab'a mini alkawarin ba zaki sake fita daga gidan nan ba sai da izinina, ina son ki samar mini da nutsuwa ta hanyar tabbatar mini har yanzu ma ba zaki fita babu yardata ba. Wallahi Asiya ke ce Tijjani. Ke ce nutsuwata, ke ce rufin asirina idan har kika bar ni, ina tabbatar miki komai zai kwace mini. Masu son nawa ma sai sun guje ni, saboda zan rasa abin da suke so a tare da ni."
Na kalle shi hawaye na sintiri akan fuskarsa. Ya jani jikinsa ya rungume yana fad'in "Dan Allah ki yafe mini, ki fahimce ni, ki mini uzziri, ki tsananta yi mini addu'a ".
Muka dinga kuka babu mai rarrashin wani. Dukkan jarumtar Tijjani ta k'are gabad'aya. Na kuma gasgata ba a haiyacinsa yake yi mini wani wulakancin ba. A haka yaran suka dawo suka tarar da mu.
Hamim ya zuba mana ido. A hankali Tijjani ya sake ni tare da dabarar dauke hawayen sa. Yayin da nawa ya kasa tsayuwa.
Hanif ya ce "Ammi Baban 2 yau ma ba shi da lafiyar ne, ya sake yi miki wani abu ne?"
Kafin mu amsa masa Hamim ya ce "Lafiyarsa k'alau fa. Ammi ce take ce mana ba shi da lafiya, marar lafiya yana yin fad'a ne?"
89&90.
Bamu yi mamakin furucinsa ba domin tamkar dan kama haka Hamim ya ke da magana. Ga kafirin wayo tamkar ya shekara goma.
A sanyaye Tijjani ya jasu jikinsa dukkansu. Yana gode wa Yabi a zuciyarsa da ta rufe masa k'ofar da y'aya'nsa zasu tsane shi. Domin ya riga ya gane Hamim, ba abin da yake so a duniya sama da Yabi. Hanif ne ba shi da alkibla, bai san wa ya fi so a tsakaninsa da ita ba.
Sosai ya tisa mu gaba a da tarairaiya. Rabon da ya yi mini hakan na manta. Gara yara yana ta tasu ni ce dai babu dad'i a tsananinmu. Da wuri ya sa suka kwanta. Suna yin barci kuwa ya ja ni dakinsa. Bamu samu kanmu ba sai tsakiyar dare. Mun tabbatar mun yi kewar junanmu. Haduwar kuma ta yi awon gaba da wani kason bacin ran da ke zukatanmu.
Barci na shirin daukemu ya yi azama ya ce "Mu tashi mu kai kukanmu gun Allah. Ya taimake mu ya kawo mana mafita ya kuma yi mana maganin duk abin da zai farrak'amu". Duk yadda na gaji tikis. Haka na daure na yi wanka, na bishi sallar da ya tayar muka dinga yi har sai da lokacin asuba ya yi.
Kwanakin da suka biyo baya na samu sassauci domin ya yi matukar rage kyara ta. Sannan ya daina fita ya shafe lokaci yna waya a waje. Watak'ila yana yi ne kafin ya shigo.
**
Tunda Babah ta koma Bulkachuwa ta shiga damuwar halin da ta baro d'an uwanta, mahaifin Yabi. Sannan ta shiga alhinin yadda ake ta shirin bikin Tijjani da a Nasiba babu nadamar komai a gidan Marina.
Ta kasa gane kanta sai kawai ta durfafi addu'a tare da fatan Ubangiji ya warware dukkan abin da babu alheri.
Kwanaki biyu kullum sai ta yi mafarkin wai randar Dada ta sanyi akwai maciji mai dafi a ciki.
Kwanaki biyu a jere tana wannan farkin babu tsagaitawa. Tun bata tunawa har ya fara shiga ranta mussaman da take ganin macijin na yunkurin fitowa ya hallaka Dada.
Ta kasa katabus ta fara kokwanto akan lamarin.
Yayin da ya rage saura sati uku biki. Baban Marina ya mik'e ya fara samun sauki a dalilin yadda Yabi ta kwantar da hankalinta. Takanas ta zo har Toro ta bashi tabbacin zata jure matukar ba Tijjani ne ya sake ta ba, to zata yi dukkan iyawarta ta tsallake dukkan kalubalen da yake gabanta. Murya na rawa ta ce ",Ya kamata ka huta Baba. Ya kamata ka samu nutsuwa, sannan mune zamu yi gwagwarmaya mu tsaywa kanmu. Ranar da babu kai kuma waye zai tare mini fad'a ko ya tsaya mini? Bini da addu'a kawai, na karbi wannan kaddarar da dukkan zuciyata, Allah yasa abokiyar arziki ce".
Ya d'ora hannunsa a kaina ya ce "Ina alfahari da haihuwar ki Yabi. Ina samun nutsuwa saboda Ubangiji ya azurta ni da haihuwar ki. Da ikon Allah duk abin da kika saka a gaba na alheri sai kin ga fatahi a cikinsa. Allah ya shirya miki yaranki, Allah ya hore miki mijinki. Ya miki shamaki da dukkan abin da zai cutar da ke, ko ya gigita miki kwanciyar hankalinki".
Cikin jarumta na ce "Ameen na gode Baba".
**
Mafarkin maciji a randar Dada sai idan bata kwnata barci ba. Kan dole ta shirya ta tafi Toro, a lokacin sati biyu ya rage daurin aurensu Nasiba.
Sai didima ake yi tare da kambaba lamarin. Masu adawa da Yabi suna fad'in "Duk d'aya ne to wa za'a ki a tsakaninsu? Tare da fake wa da ce wa rabon aure ai kisa yake yi, gara a yi, kowa rabon ta zata samu".
A wannan tsukun na gasgata k'arfin jini domin hatta su Yaya Indo da suke mana yan'ubanci na gaske sun kaurace wa shiga shirgin auren ko taya masu adawa kanzagi da nuna kowa nasa ne a tsakaninmu. Kafatalin y'an k'ofarmu sun kame daga shiga cikin maganar auren gabadaya. Sun janye jikinsu sai isu isu. Ai kuwa mutanan gidan suka yi ca wajen sakin maganganun tare da ce wa "Kamar gaske. Su a tsakaninsu ma suke son ganin wani a uku shine yanzu zasu nuna mana an tab'asu? Suka dinga furzar da maganganun da su Yaya Indo suke fad'a akanmu a baya. Yaya Ummi kuwa ta k'i yarda da yadda ake son a sake gwara kansu. Tunda yawanci a kanta suke gulmar sai kuwa ni da na ke cikin rufin asiri. Suke taya masu yamididin duk abin da aka gani a jikina ni nake yiwa kaina. Da kuma ce wa duk k'afafar da nake yi bana gaban Tijjani domin har yau bai bar iskancin kule kulen mata ba.
Na ka'du k'warai da Nazira take mayar mini wadannan maganganun da ake ta fitowa da su tare da ce wa a bakin su Yaya Indo aka fara ji. Amma yanzu sun fitittke wai suna kishin kanwarsu sai ka ce gaske.
***
Babah sai dube dube take yi a tsakanin randunar Dada amma bata ga komai ba.
Ta kasa samun nutsuwa. Rashin ganin macijin, ga shi bata daina ganisa a mafarkinta ba. A yanzu al'amarin ma yafi ta'azzara ko barcin rana ta yi sai ta ga ni.
Tana zaune a gefen randar Aliyu ya k'ira ta a waya wanda a yanzu likita ne a F.M.C Azare.
Cikin rauni ya ce "Babah kina yawaita addu'a kuwa? Tunda kika fad'a mini auren Yaya Tijjani da yarinyar nan ban sake samun nutsuwa ba. Anya kuwa! Ke ce da kanki kika mara bayan irin wannan kwamacalar a zuria guda? Duk matan duniya a rasa wacce zai aura sai wannan abar da aka tozarta ki saboda ita?"
Ta kasa ce wa komai a dalilin yadda take jin an danne zuciyarta. Ga kuma sanyin da yake bin zuciyarta da gangar jikinta gabad'aya.
Ya numfasa ya ce "Ki tsananta addu'ar tsari. Ina yawan mafarkin wani abu kamar tulu ya danne ki. Sannan a k'ofar Dada nake ganin abun. Na kasa gane mene ne shi."
Jikinta ya sab'e da rawa. A rarrabe ta ce "ko randa ka ke ga ni?"
Kai tsaye ya ce "Abu dai da ake zuba ruwa. Amma ba randa ba ce".
Ta ce "Ai kuwa nima kullum sai na ga ni duk yadda aka yi akwsi wani abu a randar nan."
Ta katse wayar, ta zabura ta mike ta dauko tabarya.
Ta yi a'uziya, tare da ce wa "Innahu Sulaimanu wa Innahu Bismillahir rahamanin Rahim".
Ta kuwa fasa gindimemiyar randar da tashi ta yi ta ganta a wajen.
Dada ta fashe da kuka tana ce wa "Hauwa kika fasa mini randa ta. Kinsan ke ma kanki tare da aba ta kika gan ni. Kwanaki biyu tak a duniya Malam ya siyo mini ita tare da katangar wankan jegon ki. Amma yau kika fasa mini da gangan?".
Ita kuwa tunda ta fasa gumi yake yanko mata. Wani irin abu tamkar kiyashi take jin yana sauka daga kanta. Bakinta ya yi nauyi ainun. Daidai lokacin da Innarsu Ubaida ta shigo yiwa Dada sallama zata gidan suna.
Tana ganin ruwa ya jik'a tsakar gidan ga fasasshiyar randa ta hau jaje tana ce wa "Yanzu randar nan mai kafirin sanyi yau ta hadu da ajalinta?"
Da kuka Dada ta ce "Eh kuma kisan wulakanci da rainin wayo a hadu da shi. Ta ajiye ledar kayanta, ta shiga kwashe rugurguzun randar. A nan ta ga k'atuwar laya.
A tsorace ta ce "Dada a 'kona wannan ko ta tsari ce?"
Murya babu amo ta ce "Jefa ta a wuta bansan ko ta mece ce ba. Gidan nan kam ai tuni Malam ya kafe shi. Ba dai mugu ya ga kofar shigowa ba.
Ai kuwa ana kona layar Baba ta ji nauyin da zuciyarta ta yi ta ware. Sanyin da yake ratsa ta na tsoro da zullimin yin jayayaya ta ji duk ya gudu. Ta dinga Hamdala. A zuciyarta kuwa sai gasgata surkulle a ka yi mata ita kanta.
A haka Tijjani suka shigo tare da Nasiba asibiti suka je yin gwaji.
Bin su kawai take yi da ido. Bak'inta sai ambaton "Hasbunallahu wa ni'imal wakil yake yi.
Zufa kuma bata fasa feso mata ba. Gabadaya ta shiga alhinin BAK'AR TA'ADAR da y'ar uwarta shakikiya ta aikata a dalilin son kai da na zuciya.
Ta zuba ido tana nazarin Tijjani. Gabadaya ya kasa sukuni. Idonsa ya kad'a tamkar gauta. Shima sai zufar yake yi. Ya gaishe ta a sanyaye. Ta amsa masa murya babu amo domin gabad'aya ta duniyata ta yi mata tsanani.
Jira take ta ji ya yi sallama ko ta fita. Amma yana zaune, duk da bai sake Bude baki ya yi magana ba.
Duk takalarsa da magana da Dada take yi.
Ya dai gaishe ta a gajarce.
Tsawon lokaci yana zaune. Rigarsa ta jike ta gaba saboda yadda zurlfa take keto masa tamkar mai hadiyar kunama.
Fiye da shudewar mintina talatin yana zaune ba ya um ba ya um um. Gabadaya Babah ta shafa'a da miyar da take yi wa Dada.
Sai tashin kauri suka ji a hancinansu. Da azama ta yunkura ta sauke. Sannan ta janye wutar ta kashe.
A tausashe ta ce "Dada me za'a d'ora kuma?"
Cikin bagararwa Dadan ta ce "Kashe kawai."
Domin bata sakar mata fuska a dalilin tana taya autarta Maryo fishin cin mutuncin da suke k'irarin ta yi mata da ta je wajenta takanas.
Ta fito da garwashin. Ta kashe sannan ta yayyafa ruwa a murhun ta kashe shi gabad'aya.
Ta dawo ta zauna. Sannu a hankali Tijjani ya fara dawowa cikin nutsuwarsa. Gumin da yake yi, ya fara tsane wa. Mintina kad'an ya mik'e ya ce "Zan tafi. Babah yaushe zaki koma?"
Da mamaki ta ce "Tukunna."
Da hanzari ta fice yana fad'in ",Na tafi Dada".
Bai ko bi takan Nasiba ba, bare ya yi mata sallama.
Babah ta kasa gane al'amarin domin tamkar mai jinnu haka yake canjawa. Ta hakura ta kudiri aniyar tsananta addu'a domin ta yi imanin Ubangiji ba zai juyar da addu'ar ta ba.
Sannu a hankali kwanaki suna ta shude wa har ya zama saura kwanaki goma auren da ake ta cece kuce a kansa.
Lefe ne kawai ba a kai ba, an yanke shawarar idan ta je gidansa ya bata domin zuciyoyi sun kai kololuwa wajen fusata.
*
Da safe bayan ya tafi da yara makaranta, shi kuma ya wuce Dass. Ina zaune a falo ni kad'ai, kuka kawai nake yi, irin kukan nan da yake zuwa ko da baka so ba. Gabad'aya duniyar ta mini zafi. Idan na tuna saura kwanaki 'kalilan na fara raba Bulkachuwa da Nasiba sai na ji ina fatan mutuwa ta dauke ni kawai.
Na kifa kai a hannun kujera ina kuka tamkar mai wake, domin bilhakki na Bude baki nake yi.
Ba zato waya ta hau kuwwa. Na mika hannu a dalilin Gwaggo kawai na saka taken da yake tashi.
Sai da na yi jarumtar shanye kukan sannan na dauka.
Murya ta kawai ta ji. Ta tausasa harshe ta ce "Kuka kike yi ne Yabi?"
Haka kawai ta fad'a na rushe da kuka mai tsananin gaske.
Cikin kuka sosai na ce "Gwoggo ba zan iya ba, zuciyata na mini ciwo, tana zafi mai radadi."
Ta numfasa ta ce ",Zaki iya mana. Ai ba a kanki aka fara yin kishiya ba, ba kuma za'a kare a kanki ba".
Da rawar murya na ce "Amma dai kishiya irin tawa Gwaggo zan zama cikin mutane kad'an da aka yiwa irin ta. Mena yiwa Tijjani da zai mini irin wannan cin mutuncin a rayuwata?"
Da taushi sosai ta ce "Nutsu ki ji ni! Shawara zan ba ki, ba umarni ba, kinsan umarni wajibi ne ki mini biyayya. Ita kuwa shawara sai kin so za ki bi. Amma idan kika bi zai fi miki alheri fiye da barin."
Ta nisa tare da ce wa "Duk runtsi kada ki ce mijinki ya sake ki matukar bai keta haddi da alfarmar shari'a ko ta aure ba. Sannan ki yi dukkan iyawar ki, kada ki nuna damuwa ko gazawarki a gaban mahaifin ki Yabi. Ya damu da halin da kike ciki. Ki daure, ba abin da ba zai wuce ba, sai ikon Allah".
Na yi shiru illah kukan da nake yi mata tamkar zan shid'e. Cikin jarumta ainun ta ce "Allah ya sassauta miki, ba komai kin ji. To ban da ma kin saka damuwa a ranki ai bai kamata al'amarin duniya ya susuta ki irin haka ba Yabi. Kinsan kalubalen da yake gaban ki kuwa?
Kwanciyar kabari kad'ai da muna saka ta a gabanmu da bamu bari kalubalen duniya ya kidima mu ya shagaltar da mu yiwa kanmu tanadin kwanciyar da Ubangiji kad'ai yasan adadin tsayin ta ba.
Me yasa kishi ya ke sawa mu manta Annabi ya ce mu yawaita sadaka, sallah da istigifari. Domin ya hango mataye da yawa yan'wuta ne. Kuma tsananta kishi alamu ne, na mace ta barranta kanta daga ayar da Ubangiji ya saukar. Wacce kuwa ta barranta daga imani da ayar Allah. La budda tana cikin hatsarin kafirta matukar bata gaggauta tuba tare da yin hak'uri cikin hukuncin da Ubangiji ya halasta ba."
Tsikar jikina ta zuba k'warai da gaske. Na sassauta kukan da nake yi. Ta sake sassauta wa ta ce "Ki yawaita karatun kura'ani domin karanta shi kad'ai yana wanke tsatsar zuciya. Ki yawaita sallah. Ki rungumi y'aya'nki da sana'ar ki. Miji kuwa kada ki zalunce shi, kada ki tauye shi, kada ki hana shi samun nutsuwa da ke ko a gidansa. Illah iyaka ki sassauta zazzafar soyayyar da zata saka ki halaka, ki kuma halaka shi".
Na numfasa tare da ajiyar zuciya mai nauyi na ce "To"
Ta shiga jero mini albarka. Ta ce "Idan akwai abin da yafi albarka da yafiyar uwa na roki Ubangiji ya yi miki da ke da zuriarki. Idan har Ubangiji baya juyar da addu'ar uwa akan d'anta , to alafamar ma'aiki ba zaki wulakanta a wannan duniyar ba. Duk inda rayuwa zata kai ki, komin tsanani zaki zama cikin rufin asiri mai yawa. Da ikon Allah wani mahaluki ba zai ga gazawar ki ba Yabi".
Da rawar murya na ce "Na gode Gwaggo! Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana mai albarka".
Na jiyo ajiyar zuciyarra alamun ta samu nutsuwa da yadda na karbi ban hak'uriinta. Ta ce "Ameen, ina tagwaye?"
Na ce "suna makaranta".
"To ke me kike yi yanzu?"
Ta tambayar cike da soyayya mai yawa.
A hankali na ce "A zaune kawai nake Gwaggo ".
"Tashi ki yi nafila, ki daina bari wannan lokacin mai tsada na wuce ki, baki yi salatul duha ba. Kinsan duk abin da Ubangiji ya rantse da shi mai falala ne, mai daraja ne. Allah ya ce "Wad Duha!
Lalle ki yawaita neman gafara da rahamar Allah a wannan lokacin, Ubangiji baya juyar da addu'ar da aka yi ta a wannan sa'ar sai dai jinkiri, ko ya mussnya maka fiye da abin da ka roka alheri".
Na ce "To!Da budaddiyar murya.
Ina jin soyayyar Gwaggo na sake tunbatsa a dukkan sassan jikina. Kwalla ta zubo mini wacce bata ciwo ba ce, ta tausayinta ne, tare da tausayin wacce duk bata girma da uwa mahaifiya ba. Tabbas soyayyar uwa ita ce mafi kololuwa a wannan duniyar. Muka yi sallama na tashi na dauro alwallah, na yi walaha. Akan sallayar barci ya sure ni, irin wanda na jima ban samu yin sa ba.
Akai Babah take yi mini waya, tana tambayar lafiyata da lafiyar yara. Na dinga mamakin yadda ta sauko. Na sani tana sona. Amma a kwanakin baya gabadaya ta canja mini. Yanzu kuma ta dawo mini Babah tawa Mai kaunata. Na dinga mamakin haka, da na ga kaina zai dauki caji Sau kawai nayi Hamdala a raiana tare da rok'on Ubangiji ya sake tsare mu daga sharrin masu tofi a cikin kulle kulle.
Da daddare muna kwance a dakinsa yara suna dakinsu da yake cikin falona sun yi barci.
Dukkanmu kowa tunanin zuci yake yi.
Ba abin da nake so irin na fice na bar gidan Tijjani. Tufka da warwara kawai nake yi. Maganganun Gwaggo sun yi matukar karya lagona. Domin a da na kudire wa raina daga ranar da ya shiga dakin Nasiba ya kwana da ita. Tabbas washegari zan bar shi, bari na har abada tunda nasan Baban Marina zai bani masauki tare da kyakkwar mu'amala a tsakaninmu.
Amma yanzu Gwaggo ta mini tilas din cigaba da zama ta hanyar rarrashi da dabara.
Na nisa na saki ajiyar zuciya.
Daidai lokacin ya ce "Sannu Asiya!
Ban kula shi ba, ya ruko ni, na yi bakam tamkar mai barci.
A sanyaye ya ce "Zullimi ne yake kama ni from no where! Samar mini da nutsuwa pls. Dan Allah bude baki ki fad'a mini wata kalma da zan samu sassauci a zuciyata. Ina daf da tarwatse wa Asiya".
Na ja tsaki mai tsananin gaske tare da ce wa "Tsuntsun da ya ja ruwa".
Ya sake rik'e ni ainun. Ya kasa ce wa kanzil. Ajiyar zuciya kawai yake yi. Murya babu amo ya ce "Idan na mutu Asiya dan Allah kada laifina ya shafi twins. Ni kaina bana gane kaina a wasu lokuta, kin ga da hantsi ko yamma sai na ji tamkar ana hura mini huta a kirjina.
Da zarar wani aka jima kuma sai na ji duk yadda aka azalzale ni na je Toro sai kuma na ji ke nake son na dawo ma ga ni. Ko dai na haukace ne Asiya?"
Da k'arfi sosai na ce "Tunda har kana banbance wasu alamuran da hamkalinka sarai. Kuma ina nan akan bakana, ba zan zauna da kai ba Bulkachuwa. Ana kawo maka Nasiba ka tabbatar na hak'ura da kai".
Jikinsa ya dauki rawa. Ya ce "Bazan iya rabuwa da ke ba. Haka kuma idan ban aure ta ba, bazan tab'a samun nutsuwa ba. Ki taimake ni mana".
Na ce "zaka ga taimako ganin idon ka. Na rantse maka duk wani sababin duniya ka shiryawa ganinsa. Hala dai ka manta Yabin marina ne Tijjani?".
Ga mamakina bai iya taso mini da masifar sa ba. Gabadaya jikinsa ya sake sosai.
Washagari na tashi da bala'i ko kallon inda yake ban yi ba. Na yarda da zancen Gwoggo. Amma bazan iya samar masa da nutsuwar da ake so ba.
Ya je can ya k'arata da dibar albarkar sa, shi da masu goya masa baya.
A wannan safiyar ya mini magana yafi sau goma ban kula shi ba. Na ki yin girki. Shi kuma ba shi da kuzarin da zai yi. Gabadaya ya koma Tijjanin farkon aurenmu. Ba na yanzu da yake masife ni a dalilin ina adawa da k'arin aurensa.
Ya kai ya kawo a tsakanin dakinsa da nawa. Ya kasa fita bare na samu na d'an sarara. Tunda gabadaya haushinnsa nake ji mai kama da tsana.
Sallah kawai yake fita. Da k'yar ya lallaba ya tafi dauko su Hanif.
Da gudu suka shigo. Na yi maza na hadiye damuwar da nake ciki na shiga yi musu oyoyo tare da murmushin yak'e.
Na dora musu indomie, bayan na juye musu ruwan wanka. Na kammala yi musu wanka, suka yi sallah.
Sannan na juyo mana indomie muka fara ci da su.
Hanif ya ce "Baban 2 sauko mu ci".
Hamim ya ce "Ba shi da lafiya ai marar lafiya ba ya cin abinci"
Takaici ya shake Bulkachuwa.
Ya daidai ta zamansa ya ce "Hamim baka tausayina ko kad'an?. Zaka ga tsiya, daga yau Hanif zan dinga siyo wa abina tunda kai uwarka kake so kawai".
Da yake mai kwadayi ne sai ya marairaice ya ce "Na daina Baban 2 sauko mu ci to."
Bai sauko ba, ya koma ya zauna. Ba tare da ya sake ce wa komai ba.
Muka kammala da kansa ya saka musu yunifom din islmamiya ya rakasu waje ya dawo.
Ya zauna daf da ni ya ce "Asiya Tsakanin ki da mai rumfa me ya hana ki daukar ciki?"
Na hassalo na ce "Saboda na gama haihuwar da kai, sai da wani".
Ai kuwa ina rufe baki ya cakume ni yana kokarin murde mini baki.
Na dinga zille wa, ina ture shi. Maimakon ya bar ni tunda ya ga kuka nake yi sosai, duk da bai mini komai ba, kuka nake na takaicinsa da na aurensa.
Amma bawan Allah bai yarda ya kyale ni ba. Ya sure ni ya yi dakina da ni. Sai da ya yi abin da yake so. Ya tara mini gajiya ya ce "Ya kika ji? Kin hana ni abinci, amma kin dafa muku ke da y'aya'n ki, kun ci. Sai kuma na zarta ki k'arfi da kuzari."
Na ja tsaki na juya masa baya, bayan na ja mayafi na lullube jikina.
Da daddare ya fita ya siyo tsire mai yawa. Ya dafa shayi ya kawo falo.
Ya juye naman a plate ya ce mu sauko mu ci.
Shi da yaran suka ci. Ni kuwa ko sha'awar ci ban ji ba, duk da yadda k'amshin ya cika wajen gabad'aya.
Washagari har wajen tara yana gida kamar ba zai fita ba. Kamar zan masa magana a dalilin yadda ya bani tausayi, amma da zarar na tuna ba janye wa zai yi ya fasa auren Nasiba ba, sai na ji tsanarsa na sake darsuwa mini.
Yana zaune sai waya ake yi masa babu kakkautawa. Kan dole ya yi shirin fita. Murya babu amo ya ce "Zan fita Asiya sai na dawo".
Ko motsi ban yi ba bare na masa shi. Ya sa kai ya fice. Sai kuma ya dawo, ya gama kame kame ya fita.
Mintina kusan talatin ya sake dawo wa.
Ya tarar da ni a zaune. Ya ce "Gabad'aya jikina bana jin dad'i. Ga shi fitar ta zame mini dole. Kano zan je na kai kaya. Amma yau zan dawo komin dare in sha Allah ".
Na dauke kai na kasa ce wa A dawo lafiya.
Ya fita. Na ja tsaki tare da ce wa "Ka gama shige da ficen ka ba kula ka zan yi ba.
Azahar ta tayar da ni. Na yi sallah na d'ora abinci saboda yara.
A daddafw na yi shara na gyara dakin.
Na fito wanka su Hamim suka dawo.
Da yake alhamis ne babu islamiya.
Dan haka sai suka debe mini kewa, ban fada nazarin yadda zamana da Nasiba zai kasance ba. Tunda a duniya bani da matsalar da ta wuce hakan.
Ban ankara da rashin dawowarsa ba sai wajen goma na dare. Yana wahalar gaske ya yi dare. Idan kuwa hakan ta kasance sai ya bugo mini waya, ko da ni ban masa wayar ba.
Na fara tsorata da shadaya ta gota. Zuciyata na bugawa na d'auki waya na k'ira shi.
Abin mamaki wayar ta ki shiga, na dage da kira babu kakkautawa.
A karshe a ka ce a kashe take gabad'aya.
Na shiga zullimi sosai. Mussaman da ya tabbatar mini zai dawo komin dare.
Na rasa yadda zan yi. Na Kalli yara na barci. Hamim ya dora kafarsa jikin Hanif.
Hawaye ya tsinke mini domin yadda nake jin jiki da zuciyata suna bari, nasan akwai abin da zai biyo baya marar dad'i.
Duk yadda na so na tashi na yi sallah kasawa na yi. Daren ya mini tsayi ainun. Domin tunda muka dawo Bauchi bai tab'a tafiyar kwana ya barmu ba.
Na dinga kuka ina fad'in "Allah ka taimake ni ka dawo da shi lafiya."
Da asuba na cigaba da kiran wayarsa nan ma shiru.
Ina idar da sallaj na bugawa kaninsa Aliyu waya na sanar masa Tijjani bai dawo ba, kuma wayarsa a kashe. Ya yi yunkurin kwantar mini da hankali. Na katse wayata na kira Yaya Salisu na shaida masa.
Har karfe daya na rana babu labarin sa. Hankali dangi ya fara tashi. Da la'asar sai ga Babah ta Bulkachuwa tare da Aliyu.
Kuka kawai muke yi ni da ita. Aka rasa mai bawa wani hak'uri a tsakaninmu.
Yayin da Yaya Salisu da Yaya Aliyu suka nufi Kano tun hantsi.
Tashin hankalinmu ya sake tsananta da la'asar ta yi babu wani tartibin labari akan Tijjani ko motarsa.
Hatta Toro hankakula ya tashi ainun domin tabbas abu marar dad'i ya same shi, mutuwa ko mummunar hadarin da aka kasa gane shi.
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai muke ta ambata ni da Babah.
Babu abin da yake sake tayar mini da hankali irin idan na kalli twins.. gabadaya sun kasa sukuni. Duk fitinar Hamim ya zauna a gefe ya nutsu tamkar marar lafiya. Maganganunsa da ya dinga yi mini a baya akan mutuwa suka dinga dawo mini. Na fara kuka sosai ina ce wa "Sai da na sakankance ba mutuwa zaka yi ba shine zaka tafi ka bar omu, me yasa zaka tafi yanzu alhalin zukatanmu cike suke da gilli da bacin rai mai tsananin gaske?.".
Babah ta kasa ce wa komai illa hawaye da ita ma yake k'waranya daga fuskarta.
Ina cikin haka sai ga Yaya Ummi da Mama. Baban Marina ya turo su, su zauna da ni. A dalilin bai san Babah tana tare da ni ba. Ganinsu ya sake rikitini ina sake gasgata abu marar dad'i ya same ni. Ina kuka ina fad'in "Ni Yabi yaushe zan tsallake damuwowi ne a rayuwa ta?"
Gabadaya na rikice, sai tausa ta suke yi, duk da Yaya Ummi ma kukan take yi sosai.
Sai dare Aliyu ya k'ira Babah. Murya babu sukuni. Ya ce "Al'amarin dai sai hak'uri."
Abin da na ji ke nan na yanke jiki na fad'i ban sake gane komai ba.
91&92.
Na farfado ne na gan ni ana k'ara mini ruwa sai fifita suke mini tare da kuka dukkansu.
Baki na rawa na ce "Babah ni din musulma ce! Ki fad'a mini Tijjani ya rasu ne?"
Da rawar murya ta ce "Bai ce ya mutu ba Yabi. Amma dai akwai abin da ya same shi marar dad'in ji, tunda har Aliyu ya jinjina lamarin".
Na fizge k'arin ruwan na zabura na ture su na tashi. Hijabi na raruma na yi hanyar waje ba tare ma da na saka ba.
Yaya Ummi ta ruk'o ni tana fad'in "Ina zaki a wannan halin Yabi?"
Da kuka sosai na ce "Kano ba zan tab'a samun nutsuwa ba, matukar ban san halin da yake ciki ba".
Fuskar kowa k'walla ce da tashin hankali. Hatta Mama jikinta a sanyaye yake ainun.
Da k'yar suka tirsasa ni na hak'ura na zauna. Sai ambaton Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai nake yi. A fili nake fad'in Allah ka kaddara mini na ga dawowar Tijjani cikin gidan nan, ko da ba akan kafafunsa ba ne. Fatana ace yana numfashi. Ubangiji ka rufa mini asiri ni da y'aya'na".
Ba abin da yake sake tayar mini da hankali irin yadda Babah ta kasa tsayar da hawayen ta.
Akai akai take share hawaye babu kakkautawa.
Kwanaki biyu muna cikin wani irin zullimi mai tsananin gaske. Domin duk asibiti da yake cikin Kano su Aliyu sun karade a kwanakin nan amma babu Tijjani babu labarin sa. Kowa ya karaya. A ranar Baban Marina ya taho Bauchi tare da Gwaggo. Nasiha kan nasiha suka shafe lokaci suna yi mini akan yarda da kaddara na yi hak'uri mu bishi da addu'ar idan a raye yake Ubangiji ya tsare mana shi, ya kuma bayyana shi. Idan kuwa rai ya yi halinsa to Allah ya sanar da mu, ya kuma jik'an sa.
Na rarrafa na fad'a jikin Baba cikin matsanancin kuka na ce "Sai yaushe zan huta, yaushe ne zan ji dad'in da ake ta fad'in zai same ni? Gabad'aya walagigi yafi yaws a rayuwata Baba! Kalli k'ananun y'aya'n Tijjani wa zai taya ni tarbiyarsu da wahalarsu Baba?"
Muryarsa na rawa ya ce "Ubangiji da ya baki su shine jagoran da zai taya ki kulawa da su. Sannan matukar ina numfashi ko y'aya' nawa kika haifa zan kula da su iyakar yadda zan iya, tamkar y'aya'n da na haifa!
Yadda ya kare maganar da kuka ya sanya Gwaggo fara kuka duk kuwa da yadda take da jarumta mai yawa. Kowa na falo kuka yake, hatta Mama kuka kuma na gaske ba na ganin ido ba.
Tsawon lokaci muna kuka tamkar an tabbatar Tijjani ya k'are.
Hanif ya ce "Ku yi hak'uri" Hamim kuwa ya ce "Baban 2 zai dawo a motarsa bai b'ata ba."
Gabadaya yaran sun rasa kuzari da karsashi a tare da su.
Da yamma mun idar da sallar la'asar Yaya Salisu ya kira Baban Marina da yake zaune a cikinmu tamkar mace.
A sanyaye ya ce "Mun samu labarinsa, mun je mun gan shi".
Gabadaya dakin muka hau fad'in Alhamdulillah Alhamdulillah!
Sai dai Innalillahi wa inna ilaihir rajiun din da Baban Marina yake fad'i ya yi matukar tsorata mu, mussaman ni da zuciyata tamkar ta fad'o k'asa.
Na kasa fahimtar bayanin da ake masa. Nasan dai na ji ya ce mun gan shi.
Gumi ya dinga keto mini. Ina tambayar zuciyata wanne ibtilai ne ya samu Bulkachuwa irin haka?.
Sai da Baban ya ajiye wayar. Tsawon mintina bai iya ce wa komai ba. Gabadaya ya jike da zufa.
A sanyaye Gwaggo ta ce "Alhaji fad'a mana halin da ake ciki kada zullimi ya karasa kassara mu.
Murya babu amo ya ce "Yana hannun jami'an tsaro. Tun shekaranjiya suke tsare da shi. Kuma damln tsabar raina talakan k'asa suka kashe wayarsa bare wani nasa ya ji halin da yake ciki."
Na saki nannuyar ajiyar zuciya, da kuka nake fad'in Allamdulillah!
Domin sai na ji tamkar an dauke mini k'atuwar masifar da ta nannad'e ni.
Tunda yana da ransa komai mai s'auki ne. Domin ban fahimci ana iya yiwa mutum talala ya zama ba shi da yancin yin komai a rayuwarsa ba.
Na kasa yin walwala a dalilin yadda Baban Marina ya yi laushi. Na tabbatar Tijjani na cikin k'ak'ani ka yi.
*Toro*
Baban kasuwa da Baban Tsakiya zaune a gaban Dada da take kuka face face tana fad'in "Ubangiji ka kare mai sunan manya, ka bayyana shi".
Baban Tsakiya ya ce "Ki daina damuwa sai ciwon ya tashi ne? An ce miki a gan shi. Sai dai fitowarsa sai ikon Allah. Tunda laifin da aka kama shi da shi idan a wata k'asar ne take za'a tabbatar masa da haddin kisa."
Hannun biyu ta d'ora aka tana kururuwa tana ce wa "Allah ka yi mini dan ma'aiki. Alfarmar Shehu Amadu Tijjani mai karama ka saukakawa wannan yaro".
Baban kasuwa ya ce "Allah ne ya yi sakayya ya toni asirinsa. Wai Tijjani ya rasa wadanda zai wulakanta sai mu? A fili yake nuna wa Yaya Sani ne kawunsa da zai yiwa hidima. Akan idonmu zai ta d'orawa yara kayan abinci da kayan miya ana kai wa kofarsa amma mu wayam. Wai shi mai suruki. Alhalin ba akan son ramasa ya bashi auren iblishiyar yarinyar nan ba. Mune muka so a bashi"..
Baban Tsakiya ya yi k'uta tare da ce wa "Allah ke nan! Ai duk mai gilli mai son ya wulakanta na gaba da shi ya dinga ganin jarraba ke nan."
Dada dai kuka take bil hakki. Domin tun farko tana son Bulkachuwa. Da ya samu wadata kuma ya jiyar da ita dad'i duk da dai ce wa take yi bashi yake biyan ta. Tunda dukiyarta da ya salwantar mata runduna ce babba.
Washagari muka dunguma Kano tare da Baban Marina. A babbar hedikwatar y'an sanda ta bonfai muka tarar da shi cikin mawuyacin hali. Hawaye ya tsinke mini. Domin gabad'aya ya fita a hayyacinsa. Babu alamun duka a tare da shi. Amma ya jigata k'warai da gaske. Abin mamaki a wajen muka tarar da su Yaya Jabir ya zo daga Kaduna da kuma Yaya Ammar yayan Nasiba. Duk da shi ma a BAUCHI yake aiki a gidan Yari. Tunda su Yaya Salisu suka fada musu, suka bar komai suka biyo su Kano dan sanin halin da Tijjani yake ciki.
Cikin tashin hankali Tijjani ya ke fad'in "Wallahi bana harkar. Ina gida aka mini waya akan na biya na karbi sako a Wunti. Ashe wiwi da koken ce ga shi an kasa samun lambar da aka kira ni da ita. Wallahi ba kayana ba ne, ba ni da alak'a da ita".
Ya fad'a idonsa ya kad'a ainun tamkar na rikakken mashayi.
Na rushe da kuka riris. Domin dai na riga na gane mun fad'a cikin garari mai girma. Kallon sa na yi na gane iyakar gaskiyarsa yake fad'a babu alamun karya ko kwaskwarima domin ya riga ya bani damar da na fahimci gaskiyar sa da kunbiya kunbiyarsa.
Babah ta kasa magana, yayin da Baban Marina ya ce "Tijjani ka fadamana gaskiyar magana, dan musan ta yadda zamu b'ullowa wannan azal d'in. Kasan wahalar da shari'a ma laifi ne babba."
Murya na rawa ya ce "Wallahi gaskiyar magana na fad'a. Bana harkar, ba ni da alak'a da kayan da aka kama ni da shi Baba".
Gauron numfashi Baba ya yi tare da ambaton "Subhanallah!
Baba ta kasa magana duk da idonta a soye yake babu alamun kuka. Na sani kuma tana cikin damuwa ne mai yawa.
Na tsugunna a gabansa ya sassauta murya ya ce "Asiya na rantse miki ba ni da alak'a da wannan al'amarin sharrin magauta na had'u da shi. Kaddarar da azal ce ta hau kaina".
Na zuba masa ido tamkar ba a gaban iyayenmu muke ba. Shi ma ya zuba mini nasa, tsawon lokaci muna kallon juna. A cikin wannan kallon na tabbatar Tijjani bai aikata laifin da aka jingina masa ba. Na kuma gasgata shi akan gaskiya yake amayarwa.
Ni na fara janye idanuwana da hawaye suka cika su taf. Da rawar murya na ce "Na gasgata ka Baban 2! Ina baka tabbas din ko baka samu mutum daya da ya gasgata ka ba. Ni Yabi na yarda bak'in k'azafi aka yi maka, tare da hak'a maka ramin mugunta. Dan haka ina tare da kai cikin ko wanne bigire har mu ga me Ubangiji zai zartar mana".
Daga hakan na fara kuka sosai. Yaranmu da suke jikinsa suka yi tsuru tsuru suna kallon yadda nake kuka sosai, shi kuma ya susuce ido ya kad'a.
Sai lokacin Babah ta ce "Allah ya warware maka, ya bayyana gaskiyar al'amarin".
Yaya Ummi kuwa da Mama kuka suke yi. Gwaggo ce bata um bata um tunda ta yi jaje cikin rauni da kasala bata sake iya magana ba.
Muna kallo da lokacin da suka bamu ya cika suka iza keyarsa hannunsa dauke da ankwa tamkar kasurgumin mai laifi.
Ni dai har muka dawo BAUCHI ban iya daina kuka ba.
Tun ana bani bakin na yi shiru har aka zuba mini ido.
Maimakon mu yada zango a BAUCHI sai Baba ya ce a wuce Toro kawai.
A k'ofar gida muka tarar da su Baban Tsakiya. Na kalle su na gasgata ce wa Baban Marina ne kawai ubanmu. Ba wanda ya bi bayan Tijjani ko na ahalinsa a cikinsu.
Dukkanmu a gaban Dada muka zube tamkar masu neman gafara. Tana kuka, matan cikinmu muna yi, tamkar dai mutuwar fuju'a Tijjani ya yi.
Sai ta dauko salatil fathi sai ta rikice ta dauko ashafa da k'yar dai ta fara karanta casa'a ta sauke ta. Tana yi tana ce wa "Rabbani a saukakawa mai babban suna, a tausayawa wadannan y'aya' nasa".
Da k'yar Baban Marina ya hakurkurtar da mu aka daina kukan.
A dakin Gwaggo na yada zango. Dakin da nake matukar samun nutsuwa a cikinsa. Amma a yau sai na ji ina cikin matsanancin kunci da zullimi domin sai nake ganin tamkar ana shirin raba ni da Tijjani ne. Na ga tsayin wannan dare tamkar dai ace gawa ce a dakin.
Ban yi barci ba. Karfe uku na ga Gwaggo ta fita ta dauro alwallah. Duk yadda na ke cikin zullimi sai da na tuna irin wannan yanayin muka shiga a lokacin da aka zartar mini da hukuncin auren Bulkachuwa. Yau kuma ina kukan bak'in cikin nisanta ni da gidansa da aka yi.
Gwaggo tana shigowa da alwalarta, nima na zabura na mik'e na doro alwalar.
Muka dinga nafila muna shigar da bukatunmu. Ina kuka hannuwana na sama "Tijjani, Tijjani kawai nake iya fad'a gabad'aya kaina ya kulle. Domin dawo da ni gida ya yi matukar sake tsorata ni.
Me yasa za'a raba ni da dakina?
Kwanaki biyu kacal a gidan Marina na gane masu farinciki yadda na shiga cikin garari sun rinjayi masu tausayi da rarrashina.
A k'ofarmu kam babu wanda yake takura mini ko habaici. Amma da zarar na fita da NIYYAR zuwa wajen Dada sai na samu wanda ya yi mini yarfe ana mini habaicin dama karyar arzikin da a muke yi ba mai tsarki ba ne.
Har ta kai bana k'aunar na fita. Amma idan ban je ba sai ta aiko wai na je, a wannan lokacin k'warai Dada take tausayina ni da yara. Kullum a cikin sadaka da addu'a take yiwa Tijjani. Kuka kam bansan wa yafi yi a tsakaninmu ba. Ta damu k'warai har jininta ya hau.
Ban sake samun damar gano Tijjani ba har aka yi sati da zuwanmu. A lokacin kuma na fara gazawa.
Tashin hankalina na sake hauhawa.
Baban Kasuwa da na Tsakiya babu wanda ya tako kafarsa da nufin yi mini jaje.
Ashe wai na yi laifi da ban bisu kofofinsu na gaishe su tare da yi musu jaje tunda ai su d'ansu ne tun kafin ya zama mijina.
Ni luma damuwata ta girmi tunanin zuwa gaishe gaishe. Sannan mafi yawa a wajen Dada nake ganinsu na kuma gaishe su a mutunce.
A lokacin na sake fahimta tare da gasgata idan Baban Marina ya kauce bamu da wanda zai tsaya kai da fata ya tallafemu idan mun shiga cikin kalubalen rayuwa. Tausayin k'ananun y'aya'n Baban Marina ya sake rub'anya tashin hankalina. Gabadaya na zama tamkar wata zararriya, na k'are na fige tamkar kudin guzuri. Bayan addu'ar da nake yi wa Tijjani da y'aya'na, sai na sake tsananta addu'ar Ubangiji ya sanya soyayya da tausayi mai yawa a tsakanin y'aya'n Baban Marina.
Domin kam al'amarin Baffaninmu sai shukuran. Kullum mutuwa na daukarmu daya bayan d'aya amma bata zame musu izna ba.
Abin da na sake fahimta kawai shaidan da son zuciya gami da hassada ne suka yiwa zumuncin yau k'awanya.
Sassaucin rayuwar da Baban Marina ya samu a dalilin y'aya'n sa ya zama wani abin tattaunawa. Kullum a cikin fad'in ai yanzu ya farfado suke.
Na tabbatar ba za'a bar ni na ji da ibtilain da ya fad'o mana ba, sai an tusa ni gaba da muzanci kala kala. Dan haka na kudire da na yi sati biyu zan fad'awa Baban Marina zan koma dakina tunda dai Tijjani bai mutu ba.
Washagari muka tafi Kano da ni da Nazira da Yaya Salisu.
Gabadaya Tijjani ya fita a hayyacinsa. Ina kuka nake fad'in "Basa baka abinci ko?"
Ya girgiza kai ya ce "Abin nan da nake fad'a miki. Da zarar hantsi ko yamma, ta yi sai gabad'aya na rikice, zuciyata kamar ta yi bindiga wajen son na tafi Toro na ga Nasiba. Masifar zafin da nake ji a zuciyata da kirjina ya wuce misali ina fatan na mutu kawai Asiya".
Na kasa ce wa komai. Yaya Salisu ya ce "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun! Allah mun tuba."
Nazira kuwa kuka take yi tana fad'in "Dama nasan ba haka siddan ka runtse ido ka kafe sai ka aure ta ba."
Ni kuwa na zama tamkar mutum mutumi. Domin a yanzu na yarda Tijjani na bukatar na samar masa da nutsuwa. Tunda duk yadda yake cikin wannan tashin hankalin amma yana fad'in yadda yake ji game da al'amarin ta. Na tabbatar ba son zuciya ko tozarci ba ne ya sanya yake fad'a mini yadda yake ji akan Nasiba ba.
Cikin tausayi nake kallon sa gabad'aya ya zube, ya yi duhu. Tausayi, so, kauna suka sake yi mini rubdugu a dukkan zuciyata da gangar jikina.
Murya a tausashe na ce "Ka tsananta addu'a ka kuma yi hak'uri. Da kaina zan kawo ta ka ganta".
Ya zuba mini ya ce "Yaushe?"
Na ce "Gobe ko jibi".
Ya yi k'asa da kansa ya ce "Goben dai."
Da k'arfin hali na ce "To".
Ya kidime ya ce "Wanne irin to kike nufi Asiya?"
Na ce na gaskiya da gaskiyar magana ".
Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa ya ce "Ina twins, me ya hana ki zo da su na gansu?"
Idona cike da k'walla na ce "makaranta suka bi yaran gidan."
Haka muka ba shi abin da zamu ba shi. Aka tafi da shi.
Tuni kuma an saka ranar da za'a gurfanar da shi gaban kotu.
Sai dai Yaya Ammar ya tabbatar mana BAUCHI za'a dawo da shi. Tunda a cikin jahar Bauchi aka kama shi. Ba'a san dalilinsu na kawo shi Kano ba tare da sun sanarwa da kowa nasa ba har tsayin kwanaki biyu.
Da yammaci sosai muka isa Toro. Muka tarar da Nasiba a k'ofar Dada domin mijin babarta aka kwantar a asibitin koyarwa na jamiar Jos. Lokacin da abin ya faru tana can bata dawo ba, sai yau aka sallame su. Babar tata ta wuce gidanta da marar lafiya.
Ni da Nazira muna kallon yadda gabadaya ta takure ta kasa sakat tunda muka shiga. Akwai alamun tasku a tare da ita.
Na yi jarumtar ce wa "Nasiba Bulkachuwa na ta jajen ki. Ya damu da rashin ganinki cikin masu zuwa duba shi tare da jajanta masa. Gobe zan koma, sai mu tafi tare ko ya samu nutsuwa".
Ta kasa amsawa. Hatta Dada ma na kashe ta da kunya gabad'aya sun rasa me zasu ce. Yanayinsu ya sa na gane suma tamkar an tursasu ne akan sha'anin Tijjani.
Washagari kuwa na shirya yara na ce mun tafi Kano. Baba bai so ba, amma saboda lallaba farincikina yake yi bai hana ba. Sai ma ya ce "Ubaidun Inna ya raka ni.
K'ofar Dada na dire. Na tisa Nasiba a gaba muka tafi a kan dole ba yadda zata yi. Domin na lura tsoro nake bata.
Har muka isa Kano ba wata hira a tsakaninmu.
Sai kuma muka hadi da tasgadon y'an sanda. Wai ba zamu gan shi ba, ana yawan yi musu zarya da sunan ganin Tijjani bayan shi mai babban laifi ne.
Hanif ya fashe da kuka yana ce wa "Zamu ga Baban 2 dan Allah ".
Hamim ma ya fara kuka sosai.
Watak'ila tausayi suka bawa wannan babban dansandan sai kawai ya bada umarnin a fito da shi.
Ga mamakina sama da mintina goma da isowar Tijjani bai kalli inda Nasiba take zaune ba. Tunda ta gaishe shi ya amsa hankalinsa na kan su Hanif da suke kan cinyarsa bai sake bi ta kanta ba.
Ni da yara kawai ya ke kulawa.
Na mike na ce "Bari na baku waje tunda idona yasa ka kasa yin hirar".
A zabure ya ce "Zan ci mutuncin ki little! Jiya da yau ban ji azabar da nake ji ba. Akwai abin da ake yi mini wanda zalunci ne da k'eta. Alfarmar Annabi kuma Allah zai kawo mini k'arshen al'amarin tunda kwana nake ina fad'awa Ubangijin al'arshi ya warware mini wannan masifar. Ni ko wannan k'azafin da aka yi mini baya gigita ni, kamar yadda al'amarin ta yake gigita ni. Amma akwai Allah."
Ba Nasiba ba, ni kaina sai da na ji babu dad'i ainun. Na yi tsuru tsuru na kasa ce wa komai. Domin na tabbatar k'arshen muzanci Tijjani ya yi shi. Amma na sake gasgata surkulle ake yi masa. Ban da haka jiya k'iri k'iri ya fad'a mini yau na kawo masa ita. Ko tunanin rikicin da zan yi masa bai yi ba, saboda an ringa an kidima shi a kanta. Na daure na rakito ta, amma bai ko kalli inda take ba, sai ya b'uge da cin mutunci. Jikina ya mutu domin nasan zata zargi na kwaso ta ne dan na saka mijina ya wulakanta ta a gabana. Tunda a hakan kafatalin gidan Marina sun tafi akan na gama da Bulkachuwa tsorona yake ji. Sai abin da na shimfi'da zai bi. Har fad'i suke idan bana son mutum to ko kallon arziki Tijjani baya masa saboda gudun zuciyata.
Ta mike a kasalance ta ce "Bari na jira ku a mota Yabi".
Murya babu amo na ce "To".
Tana tafiya ya saki dogon tsaki mai karfi da na tabbatar zai je kunnuwanta.
Na zuba masa ido ba tare da na iya ce wa komai ba.
Da k'yar na ce "To da sun san zasu mayar da kai Bauchin me yasa suka kawo nan?"
Ya kalle ni ya ce "Akasi aka samu. Sun tsayar da ni a farko ban tsaya ba. Shine suka harbi tayar motar ikon Allah ne yasa motar bata yi bari da ni ba".
Zuciyata ta buga da tsananin gaske na ce "mene ne dalilin ka na k'in tsayawa Baban 2? Ta ya ya kana dan k'asa amma ka ce ba zaka girmama dokar k'asar ba? Ko dai kasan dama baka da gaskiya ne?"
Nan da nan ya kidime ya ce "Wallahi Tallahi ina da gaskiya, bansan an saka mini wannan abin ba. Ban sani ba, ki yarda da ni Asiya!.
Na saki karfaffan numfashi tare da ce wa "Rashin tsayawar ka ba k'aramin hujja zasu kafa da ita ba. Na yarda da kai".
Ya nutsu ya ce "Idan har kin yarda da ni to kowa ma kada ya gasgata ni Asiya! Nasan mahaifuyata zata shaide ni, duk fitina ta bana harkar maye bare kuma a yanzu da na girma. Ba zan shiga safarar abin da nasan illah ce ga al'umma ba. Ina miki ranstuwa da girman Allah ban san mugun abu aka bani ba. Waya kawai aka mini akwai sakon kaya da zan karba a Dutsen tanshi, idan na kai Kano za'a karba a biya ni. Kinsan kuwa ina harkar sakonni(Delivery). Ban tab'a zaton za'a mini kutse a cikin sana'a ta ba. Ni yanzu babban tashin hankalina ke ce. Ban san hukuncin da za'a yanke mini ba little. Kinsan k'asar nan waka sani ne waya sanka."
Idona taf da hawaye na ce "Nasan baka aika ta wannan BAK'AR TA'ADAR ba. Da ikon Allah ina tare da kai, komin tsanani".
Ya murmusa ya ce "Alhamdulillah! Na samu amincin firgicin da nake ciki. Dan Allah Asiya kada ki canja, kada ki juya mini baya a cikin wannan halin canka cakare da nake ciki." Idonsa ya kad'a sosai ya kasa cigaba da magana alamun ya shiga rudani.
Hanif ya ce "Baban 2 kada yi kuka zamu zauna mu taya ka zama. Ammo ta tafi ta barmu tare da kai".
Hamim ya ce "No zamu je mu koyo yadda zamu kwace shi daga hannun yan sandan kawai".
Na yi k'asa da kaina kawai ina hawaye domin tausayin da suka ba ni ba kad'an ba ne.
Ban iya ce musu komai ba. Shine ya yi jarumtar sake rungume su tunda a akan cinyoyinsa suke. Murya na rawa ya ce "Baban 2 baya karya domin wanda ya yi karya ya zagi Allah, Wanda ya zagi Allah kuwa dan wuta ne. Dan haka am innocent, ban yi laifi ba. Sharri aka yi mini. Kowa ya yi sallah ya yi wa Baban 2 addu'ar ya zama free".
Suka had'a baki wurin ce wa zamu yi sosai ".
A sanyaye muka rabu domin gobe za'a dawo da shi BAUCHI dan shiga kotu.
A hanya Nasiba ta sake rasa kuzarin ta, dama kuwa bata iya sake wa a gabana na dade da fahimtar a takure take da ni. Abin da Bulkachuwa ya yi mata kuwa ya sake sanyaya mata jiki. Ina hankalce da ita, ina ganin yadda take son yi mini magana amma ta kasa.
Cikin kundubala ta ce "Yabi!.
Na amsa da "Na'am" murya babu amo.
Ta kalli twins da suke barci a jikina. Ta ce "Idan na ce miki bana son Yaya Bulkachuwa na yi karya domin na girma da son sa, ke ma kin sani. Idan na ce miki a yanzu dole aka mini a kan aurensa zaki yarda?"
Ban ce komai ba. Illah ido da na zuba mata.
Ta numfasa ta zarce da ce wa "Ni da kaina bani da yadda zan yi ne. Domin kuwa mutane da yawa suna haduwa da kalubalen a hadasu da iyaye karkatattu. Sai dai duk da hakan ba zamu ki sonsu ko janye wa daga gare su ba. Na sani tun farko soyayyar sa gare ni ba mai yawa ba ce, bare yanzu da yake auren ki. Dan Allah ki yi hakuri kada ki datse mu'amala da ni Yabi. Al'amarin zumuncin yau ya shiga rudani mai yawa, amma idan aka yi hak'uri aka danne, aka yi sassauci sai a samu masalaha a duniya, a kuma samu rabauta a duniya.
Zan yi iyakar kokarina na fita a harkar mijinki, na yarda Yaya Bulkachuwa ba mijina ba ne, ba kuma zai zama ba. Kada ki ce maganganun da ya yi cin fuska ya yi mini, zahirin gaskiya ya amayar".
Na rik'e hannunta murya na rawa na ce "Ban kullece ki ba. Amma idan na ce ban ji ciwon abin da ya faru ba na yi karya. Har abada ba zan iya auren mijin ki ba Nasiba. Amma na hak'ura na barwa Allah ya yi mini zabi akan lamarinku. Tunda ai ba haramun ba ne. Shi yasa na hak'ura na barwa Allah komai".
Dukkanmu kowa zuciya ta narke, muka dinga kuka.
Ubaid da yake gaban motar ya yi tsaki ya ce "Sai ku yi ai. Amma ai mu kam mun kudire matukar ya aure ta sai ya sako mana ke ko da kuwa a gaban alkali ne".
Na daskare da maganar sa. Na tuna na ba shi watanni shida. Gabadaya ma shekarunsa ashirin da uku ne. Amma ya yi magana kamar wani babban wanmu. Sai kuma hawayena ya sake zuba a dalilin yadda maganar auren Nasiba da Bulkachuwa ta zama silar samar da soyayya a tsakanin ahalin Baban Marina. Yan ubancin da manyanmu suke gwada mana ya yi matukar zangwanye wa.
Na yarda mafi yawan kalubale ya kan zo da wata nasarar komin kankatarta sai dai idan ba a kula ba, ko an bari hankali ya kwace an yi fishin da ya shallake hankali.
93&94.
Washagari duku duku Baba Maryo ta zo.
Domin na je gaida Dada na juyo muryarta tana ce wa "Ai ko baki bijire mini ba gabad'aya ba zai aure ki ba, wane shi. Ashe dama arzikin da ake ga ni a tare da shi kazami ne? To ba zata sabu ba. Aure kam tabbas ya fasu fas. Dama ai ba so kike ba, tunda kin ringa kin tsorata da iblishiyar mata tasa. To ta je ta samu sai ta tabbata a matar d'an safarar kwaya ita kad'ai. Mutane babu Allah a ransu. Ka dinga neman arziki yaki haram yaki halal. Dama so na yi na nuna wa uwarta da ita Yaya Hauwa iyakarsu. To tunda bai shiryu ba, huta toro an bar musu shi. Watak'ila ma daurin rai da rai za'a yi masa. Ai da a sau'udiyya aka kama shi fille wa d'an banza mai yiwa iyayensa kallon raini za'a yi".
A sanyaye Dada ta ce "Ai kuwa mai sunan manya ya yi hankali da girmamawa yake gaida kowa kamar ba shi ba. Kawai dai yana nuna son kai ne, ya fi nan nan da k'ofar Alhaji. To wannan kuma dariyar matarsa yake so, ya za'a yi tunda ya jarabtu akan ta.!"
Baba Maryo ta ce "Ban da ni din, ni ce ai ko gaishe ni ba zai yi ba, ya kullace ni ainun. Tunda ake fad'in labarin wadatar da yake ciki, ashana bata tab'a had'a mu ba. Kai ya taka ya je gidana bai san wannan ba. Idan ya gan ni tamkar zai doke ni. Amma yanzu da yake ba shi da kunya har zarya yake yi mini. To na fasa ba shi Nasibar. Ba zai yiwu ba, ya je dai ya k'arata da afiruwar matarsa mai izgili. Kai ahalin Tijjani da Yabi za'a yi majununai, biyu ta had'u y'aya'n iska marasa albarka".
Na sake jin cikin rauni Dada ta ce "Yanzu fa sun yi hankali suna girmama kowa. Yabi da kanta jiya ta zo har nan ta tafi da Nasiba wajen mai sunan manya. Kin san idan Yabin da ce ba za'a yi hakan da ita ba".
Ta saki tsaki ta ce "Yo tunda ya rikice mata ai dole ta kai ta. Amma daga yau zan yanke komai."
Dada ta kame bakin ta. Ita kuwa ta ci gaba da sakin maganganu masu nuni da dama ba Tijjanin take so ya zama surikinta ba. Wadatar da ake kallon ya samu ne ake son su lasa. A yanzu da ya hadu da ibtila'i kuma an janye saboda dama ba da zuciya d'aya aka yi abin da aka yi ba.
Na shiga daga bakin kofa na gaida Dada, duk da tana ce wa "iso mana, ina tagwaye ko basu farka ba?"
"Eh suna barci Dada".
Na gaida Baba Maryo a gajarce. Ta amsa fuska babu walwala. Har na juya sai ce wa ta yi "Yabi ashe haka ya faru da Tijjani?"
Na ce "Eh!
Sai ji na yi ta ce "To wadannan kadarorin da suke yatsun ki da kunnawan ki sai ki hanzarta kad'ar da su dan ki dauka masa lauya domin dai a gindinki da na iyayen ki ya k'are. Gyatumar sa ma yar amshin shata aka mayar da ita. Watak'ila hakkin ta ne ya sanya yake gani a k'waryarsa.
Na juya da nufin bata amsa sai na tuna kanwar mahaifina ce. Ba zai yiwu na yi fad'a da ita a yanzu da hankali ya ratsa ni ba. Nasan kuma dole ni ce a ciki tunda shi da kansa Baban Marina zai ce ai kanwarsa ce ta shiga rigarsa mana.
Dan haka sai na hadiye na ce "To Baba Maryo zan yi hakan".
Ta tunbatsa domin ta washi mu fad'i sunan ta.
***
*BAUCHI*
Kotun ta cika makil domin sharioi za'a yi masu daukar hankali.
A kuma wannan ranar za'a yanke wa Tijjani hukunci.
Da wuri muka iso. Da ni, da Yaya Salisu da Baban Marina da kuma Yaya Salamatu.
Sai ko Yaya Ammar da yake Bauchi.
Karfe shadaya aka fara shari'arsa. Babu wata hujja da zata wanke Tijjani. Domin lambar da ya ce an k'ira shi da ita kwata kwata bata shiga. Sannan an tambaye shi me yasa da aka ba shi kaya bai bude ya duba ba? Tunda ya dauki delivery a matsayin sana'a. Me yasa ba ya nazarin kauce wa dukkan wata matsala da zata taso. Wajibi ne idan zaka karbi sako, ka duba ka ga mene ne a ciki tunda idan aka kama ka ai kai ne a ciki.
Sannan me yasa bai binciki ainihin inda mutumin yake ba?"
Lauyan da k'aninsa Aliyu ya daukar masa, ya kasa inkarin hujjojin lauyoyin gwamnati tunda tabbas Tijjani bai yi bincike ba ya karbi kaya. Bai kuma bude ya duba ba. An ba shi abu a d'aure cikin buhu kawai ya danna a mota. Sannan bai san mutum ba. Kawai ance idan ya je Kano za'a karba a biya shi.
Sannan lauyan gwamnati ya k'ara kafa hujja da ce wa "saboda Tijjani yasan ba shi da gaskiya ya dauko wiwi da koken mai nauyin tam goma shi yasa ya ki tsayawa da jami'an tsaro suka tsayar da shi wanda hakan rashin da'a ne da raina jami'an tsaron da k'asa ta wakilta su duba shige da ficen al'umma."
Na zuba wa Tijjani ido da yana tsaye jikin kantar da ake tsayar da wadanda ake tuhuma. Ya zube aiun, ya sake yin duhu.
Zuciyata ta karaya, na hangi rashin sassauci a shari'ar. Ta zo fiye da yadda muka tsammace ta.
Domin maganarsa d'aya ce ba shi kayan aka yi, bai san kuma san mutanan ba. Lambar wayar da ya gabatar a matsayin wacce aka kira shi da ita bata yi.
Jikin kowa ya yi sanyi. Bayan dogon rubutu da alkalin ya yi.
Ya yi gyaran murya ya ce "Duba da hujjojin da lauyan gwamnati da kuna jami'an tsaro suka gabatar kotu ta yanke wa Tijjani hukuncin shekaru biyar a gidan yari babu tara. Bisa kama shi da safarar kwaya wanda hakan ya saba kashi na goma sha takwas b cikin baka. Bayan haka kotu ta sake d'aure shi shekara d'aya bisa cin zarafim jami'an tsaro da ya yi ta hanyar yi musu gaddama. Har ila yau kotu ta daure Tijjani na watanni uku ko tarar dubu ashirin saboda rashin kiyaye kaidojin kasuwanci. Ba zai yiwu mutum yana hulda da jama'a ba amma babu taka tsantsan da sanin me mutum ya dauko ko mai zai kai. Yana cikin dab'iun d'an kasa na gari ya zama yana duba komai yana kuma kiyaye dukkan doka."
Ya rattaba hannu akan takardun tare da buga stamfi.
Gabadaya ahalinmu hankaliinmu ya yi mummunan tashi. Ni kam kuka na ke yi mai gunza. An daure shi shekaru bakwai babu tara?
Wacce irin bak'ar kaddara ce wannan?
A harabar kotun muka tsaya da shi tunda Yaya Ammar na cikin ma'aikatam gidan yarin. Na kalle shi sai kawai na fashe da kuka a dalilin raunin da na ga ni ya bayyana masa a dukkan jikinsa da zuciyarsa.
Muka zubawa juna ido ba tare da mun tuna daruruwan mutanen da suke wajen ba .
A sanyaye ya ce "Asiya shekaru bakwai da yawa. Tashin hankalina bai wuce ke ba. Ba zaki iya ba. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun "
Sai kawai hawaye ya ya k'wace masa shabe shabe".
Na rik'e hannunsa na ce "Ko shekaru sha bakwai ne zan jira ka Baban 2. Idan har rayuwarmu ta kai zaka fito ka tarar da ni a dakin ka. Zan kiyaye maka amana, zan yi aiki tuk'uru na kular maka da y'aya'n ka. Jarumtar nan da ka ke fad'in na dinga yi, zan nin ka ta daga yau".
Baban Marina ya dauke idonsa amma bai iya tsayar da hawayensa ba. Tijjani ya matsa kusa da shi ya ce "Wallahi ban aikata laifin da aka jingina mini ba, rami aka haka mini na fad'a. Ka taimake ni, ba zullimin hukuncin ne ya zautar da ni ba. Fargabar yadda zan iya rasa Asiya ne. Shekaru hudu ne gejin da shari'a ta dibawa mace akan dakon mijinta. Ni kuwa shekaru bakwai aka zarge ni".
Hawaye ya cigaba da tsere babu kakkautawa.
Baba ya kasa ce wa komai. Su Yaya Salisu kowa hawaye. Cikin k'arfin zuciya na ce "Idan ni ce matsalar ka, to ka kaddara baka da damuwa. Zan jira ka. Ba ka ce ko ka mutu na zama jaruma dan na tallafi y'aya'n ka ba? Zan kiyaye mutuncin ka, zan kuma maye wa y'aya'n ka gurbin ka har zuwa lokacin da zaka dawo ka cigaba da kulawa da mu gabadaya. Ka sa a ranka ban yi kokwanto akan ka ba Tijjani. Na gasgata ka, na yarda da kai."
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Allah ya k'ara lafiya Baba. A sanya ni cikin addu'a. Ni kuma ya mini murmushi kad'an ya ce "Na gode".
Daga haka suka tafi da shi.
Fir na k'i yarda na koma Toro. Domin idan ina gida tashin hankalina yafi yawa a dalilin ina ganin tamkar Tijjani ya rasu ko mun rabu. Bayan haka karatun yara ya dakata.
Baban Marina bai matsa mini ba, jikinsa ya yi laushi ya kamu da mugun tausayinmu.
Yaya Indo ta zauna da ni na kwanaki biyu. Komai ita take yi, ta ji da hidimar yara ta kuma yi girki da kwantar mini da hankali. Tun sanadin auren Nasiba muka hade da su. Gabadaya yan k'ofarmu muka dinke, muka dunkule, duk wani tsegmi ya yi s'auki tunda dama manyan namu ne karkatattu.
Sai da Babah ta Bulkachuwa ta zo sannan ta tafi. Dada ce ta zartar da umarnin Babah ta zo ta zauna da ni. Cikin alhinin rashin Tijjani da kuma tausayi da kyautatawa muke zaune. Nasirun ta wanda shi Ihisan take bi a kai a kai yake zuwa mana domin dalibi ne a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da take cikjn Bauchi.
*Toro*.
Anas da yake bin Yabi. Yana bandakin k'ofar Dada yana simince shi a dalilin wanda aka yi mata da ta rubza ya farfashe, ba'a yi aikin aminci ba.
Gabadaya Baba Maryo ta shafa'a shaf yana k'ofar, kuma kusa da kicin din da take zaune ne.
Ta hau tonon murhun tana ce wa "Allah suturi buk'i da auren mazinaci kuma mai dilar k'waya. Wane mutum na had'a iri da shi cikin sanina?"
Kalaman ta suka ja hankalinsa ya ajiye abin aikin ya leko tunda bayin ba me k'yaure ne ba.
Ganin da ya yi tana tono ya sake jan hankalinsa k'warai da gaske, ya matso sosai. Yana kallonta k'yar. Ya jima yana zargin Yaya Bulkachuwa ba a bar shi haka siddan akan al'amarin Nasiba ba. Ashe kuwa hakane. Ya sandare cikin tu'aajjibi a lokacin da ya ga ta fito da laya a k'asan murhun ta kyasta mata ashana ta k'one.
Ta ja tsaki mai tsananin gaske tare da ce wa "Allah na gode da baka k'addara mini ganin auren ta da mai arzikin bogi ba. Ban da ma dai batan basira me za'a yi ne da wanda aka yiwa bulalar zina a bainar nasi? Lallai na yi mantuwa mai yawa. To na tone ramin da na hak'a tun ban rufta ba. Dama Yabi ce ta dace da shi a wannan duniyar."
Daidai lokacin Anas ya kasa jure wa ya yi gyaran murya. Ta waiwaya a ankare. Idanuwansu suka hadu, ta yi wura wura. Ta rasa inda zata tsoma ranta. Shi kuwa sai ya ce "A dinga yin sara ana duban bakin gatari Baba! Da Yaya Bulkachuwa, da Adda Yabi, da kuma Adda Nasiba kamata ya yi ki dauke su abu guda. Ba wai ki nemi rugurguza zaman lafiyarsu dan bukatar kan ki ba. Kin cutar da su duka. Ita kanta Adda Nasibar ai dan ba yadda zata yi ne, akan dole ta bi ra'ayin ki domin tana da darhamin imani a zuciyarta. Ya fara hawaye ya ce "Duk duniya ki rasa wanda zaki yiwa kulunboto ya so diyar ki sai mijin d'iyar Baban Marina! Kaico da
Bakar hassada, kaico da mutanan da suke da son zuciya, wacce irin BAK'AR TA'ADA ce haka? Asiri kika yi wa Yaya Bulkachuwa! Innalillahi wa inna ilaihir rajiun " Sai kawai ya fito daga bayin a gigice ya zunduma ihu da dukkan muryarsa tamkar mace ba jarumin namiji ba. Domin ya riga ya gigita da abin da ya ga ni k'warai da gaske.
Ta hau tafa hannu tana ce wa "Ashe a maza ma akwai makirai majununai? Zaka ga tsiya da tuggu kuwa! Zan nuna maka uban ka ma ya wuce ya tozarta ni, ya kwaye mini asirina. Zaka gasgata makircin mace aziman ne yau din nan".
Sai kawai ta takarkare ta zunduma ihu mai tsananin gaske. Da yake Dada barci take, a firgice ta farka tana fad'in "Waye ya mutu Maryamu? Jin shiru sai kukan Anas da na autarta ya cika mata kunnawan, ita ma sai kawai ta fashe da kukan daga dakinta. Tana fad'in "Allah kasa basu harbe mini "Mai sunan manya ba. Lah ha ilah ha ilallahu!
Mintina kalilan jama'a suka taru a k'ofar ta da Dada.
Baban Kasuwa da na Tsakiya suna gidan yayin da Baban Marina baya nan. Dan haka a sukwane suka bu sahun ahalin gidan da suke ta shigowa a gigice.
Kowa sai tambayar ba'asin kukansu yake yi. Anas sai hadiyar zuciya yake yi ya kasa bude baki ya yi magana.
Jikin kowa ya yi sanyi tare da sake shiga rudani mai yawa. Domin kowa yasan Anas ba mai hayaniya ba ne sannan yaro ne mai juriya da hak'uri na gaske. Sun tabbatar ba zai yi kuka irin haka ba tare da ya ga wata masifar, domin a lokacin da yake yaro ma ba mai fitina ko koke koken banza ba ne, bare kuma yanzu da yake da shekara ashirin da biyu, ya zama saurayi na sosai.
Baban Kasuwa ya ce "Maryo mene ne haka? Me ya faru ya tambaya zuciyarsa na rawa irin ta zullimi.
Ta kuwa karkace ta kara k'arfin kukanta ta ce "Ban san yana makewayi ba. Sai na afka bayin ba tare da na tambaya ko akwai mutum a ciki ba. Babu zato na ga Anas ya gogawa al'aurarsa sabulu yana wasa da ita! Na zauce na fito a sukwane ina hirji. Kunya tasa ya kasa fitowa. Sai yanzu ya yi jihadi ya fito, wai dan na yi masa matashiya akan haramcin hakan shine ya fasa mini ihu yana neman k'ulla mini sharri tunda dama dukkansu y'aya'n Alhaji sun tsananta mini akan Tijjani, mussaman y'aya'n Asma'u da ko gaisuwa sun yanke yi mini dan su nuna mini Yabi ta fini a wajensu. Amma ni ban ga laifinsu ba. Ubansu ne ya yarda
ta ni irin haka." Sai ta zarce da sabo n kuka.
Su Baban Kasuwa suka d'auki salati tare da ce wa "Muminin kare ne ashe kai. Kullum da kai ake kwatance a gidan nan da ma unguwar baki daya saboda nutsuwar ka da hamlnkalin ka ashe BAK'AR TA'ADAR da kake tafi ta yaranmu da ake yi musu kallon fitinannu ne! Duk yadda aka yi kai ne ka yiwa y'ar wajen Malam Kabiru fyade satin da ya wuce. Yarinya karama da ko magana bata iya ba, aka kasa gano mugun da ya aikata mata aika aikar ashe kai ne".
Kuka ya tsayawa Anas cak. Ya Kalli Baba Maryo ya kalli Baban Kasuwa. Yana ta kissima sune k'ananu a cikin iyayensu amma sune suke kan gaba wajen ruguza gidan Marina. Bai gama nazarinsu ba sai ya jiyo Baban Tsakiya ya ce "A a tunda ba mu ga ya haike mata ba, bai kamata mu jingina masa ba, shaidar zina babban al'amari ne. Sannan idan aka ji maganar a bakinmu ai muma mun kunyata domin baza mu ce ba daga gidan nan ya fito ba. Kawai shata masa layi zamu yi da y'aya'nmu kada ya dinga b'ata manaa su bamu ankare ba tunda ya jefa kansa a wannan BAK'AR TA'ADAR ta istimina'i".
Yara da manya kowa yabi Anas da kallon tsana da tuhuma. Duk Mama da kanta ta ce "Anas ba lallatacce ba ne. Na tabbatar bai aikata hakan ba Maryo".
Sai lokacin ya samu kuzarin Budeibaki ya ce "A a Mama kada ki ce mata komai. Na riga na kai alkalanci gaban Ubangiji. Idan ya tabbata na yi abin d at fada to ku nema mini gafarar Allah. Na kuma yafe mata tozarta ni da ta yi, tunda ai ba hakan ya kamata ta yi mini ba.
Idan kuwa ban aikata ba ta mini hakan to da ikon Allah ba zaki mutu da ido ba Baba Maryo ".
Ta zunduma ihu tana d'ura masa ashariya.
Bai rufe baki ba ya ce "Ganinta na yi ta tono mugun k'ullin da ta yiwa Yaya Bulkachuwa akan ya rikice akan Adda Nasiba. Tana fad'in ta fasa auren tunda dan k'waya ne kuma mazinaci. Ganin na ganta ta k'ona layar shine ta mini hakan. Ba zan zage ki ba, ko a lahira wani kan ci arzikin wani. Ban ci arzikin ubana a wajenki ba. Nima ba zaki ci nasa ba. Kin ci arzikin kasancewar ki uwar Yaya Ammar. Ba dan shi ba, ina rantse miki da girman Ubangiji sai na miki dukan da ko Dada sai ta yi gaske da ta shaida ki. Amma babu komai na barwa Allah komai."
Ya mik'e yana tangadi yayin da kowa ya yi tsit. Ya kalli Baban Kasuwa ya ce "D'a na kowa ne Baba".
Baban Kasuwa ya ce "Ni kad'ai zaka fad'awa hakan, shima Baban Tsakiya ai ya tofa nasa"
Anas ya ce "Ko ya tofa dai bai mini k'azafi ba, gaskiyar fahimtarsa ya fad'a.
Dada tana bakin k'ofarta tana kurshegen kuka tana fad'in "Dambarwa ta tsananta a cikin ahalina. Ubangiji na ci albarkacin sallah da salati, ka sassauta, yafe mini, ka shirya mini zuria gabadaya".
Har aka gama wannan cecekucen Baban Marina da Gwaggo basu tofa ba. Mama ce ta shiga lamarin ta yi kane kane tunda yanzu yar tsama ce mai tsananin gaske a tsakaninta da Maryo.
Baya ga hakan kowa yasan Anas ba zai yi abin da ta fad'a ba. An kuma gasgata shi,asirin da yaga ta tone.ne ya ya sanya ta yi wannan dibar albarkar.
Nasiba kuka ba wanda bata yi shi ba. Ammar da yake BAUCHI da ya ji labarin bai dauke shi da muhimmanci ba. Murnar yadda ta kunce k'ullin da ta yi yake yi. Domin yana matukar tausayin yadda Bulkachuwa yake damunsa ya kawo masa Nasiba ya ganta. Yanzu kuwa tunda an warware zai daina, zai samu nutsuwa, tunda wani lokacin har susuce wa yake zufa na karyo masa.
Da labari ya zo mana Babah ta ce mini "Tare ta hada ta mana ai, ni tun kwanaki na kubuta. Nawa a kasan randa aka yi mini ta yadda zan zama mai sanyi akan sha'anin. Sannan aka danne mini zuciyata.
Shi kuwa a k'asan murhun. Matukar aka hura wuta a murhun ba shi ba sukuni idan bai ganta ba. Kai wacce irin BAK'AR TA'ADA ce haka?
Ta fara hawaye. Na taya ta muka yi kukanmu sosai domin ta ba ni tausayi. Da ciwo kwarai ace d'an-uwanka ne zai musguna maka irin haka.
A raina kuwa na yafe dukkan musgunawar da Tijjani ya yi mini akan Nasiba. Na sake gasgata ba yin kansa ba ne. Na kuma sake kudire a raina matukar ba Babah ba, wani mahaluki ba zai ji halin da nake ciki da shi ba.
Zan jira shi har ya kammala WA'ADIN da zai yi, zan kuma yi gwagwarmaya har komai ya daidaita mana.
Karshe na yi jarumtar ce wa "Mu yi hak'uri Babah ai ba kuka zamu yi ba. Alhamdulillah zamu tsananta fad'a, mu kuma sake dage wa da addu'a."
Murya babu amo ta ce "Allh ya yi miki albarka, ya kara miki hak'uri, da ikon Allah Ubangiji zai miki sakamakklon alheri na gode sosai"
Nafi wata biyu ban warware na fara sabgogina ba. Duk karshen wata zamu je mu gano shi. Aliyu kuwa daidai gwargwado idan karshen wata ya zo zai siyo mana kayan abinci, ya kawo da kansa ya kuma damkawa Babah kudin da zamu rik'e. Ya tisa yara a gaba su fita, ya yo musu siyayya sai ya dawo da su. Shirin aurensa ake yi wannan al'amarin ne ya dakatar da komai.
Haka su Yaya Salisu akai akai suke mana aika. Yaya Ammar kuwa duk sadda muka je prison sai ya bawa Yara kudi masu auki, kuma babu jami'in da yake tsaya mana a kai saboda Yaya Ammar.
Ba laifi kuma yana leko mu jifa, jifa shi da iyalinsa.
Yaya J ma duk watan duniya yana aikowa yara kudi amma bata hannuna ba, ta hannun Yaya Rabiu. Shi kuwa yana turo mini ta asusuna. Idan na yi masa text din godiya sai ya ce ba sai an ji ba. Bamu da wata matsala gagaruma. Amma da tafiya ta fara nisa sai na fahimci dukkan masu tallafa mini kama daga kan mahaifana, Aliyu kanin Tijjani, su Yaya Salisu da J hadi da tsirarrarun dangi masu bamu sabulai kowa yana da nauyi a kansa baza su tabbata suna mana hidima ba . Mussaman da kullum rayuwar take sake tsefe wa. Ina kwnace ni kad'ai a daki yara sun tafi makaranta yayin da Baba take dakinta tana lazimi. Tunani nake yi tare da nazarin kaalaman da Tijjani ya yi ta yi mini a lokacin da nake bacin ran shiga makaranta. Ba abin da yafi tsaya mini a rai fiye da yadda yake ta nanata ni kad'ai ce yake da tabbacin bazan gaza da hidimar y'aya'nsa ba.
A lissafi watanninsa tara a tsare. Har lokacin kuma bana aikin komai, ban dogara da komai ba sai wanda dangi suke mana. Tunda na riga na gajiya na kasa yin kitso bare lalle.
Na numfasa a fili na furta "Ya kamata na yi hobbasa na taimaki kaina.
Na hakurkurtar da zuciyata na fita na siyo kayan kunshi. Na fara posting na fara lalle.
Ba'a dauki lokaci ba mutane suka fara dawo mini.
Da yake bamu da wasu matsalar sosia, sai na ninka aiken da nake yiwa Babanmu. Tunda aka rufe Tijjani ahalin Baban Marina suka gane Tijjani ke hidimar k'ofar da kaso bakwai cikin goma. Wanda ko ni ban gane hakan ba sai yanzu.
Dan haka na dage nake tallafawa Yaya Salisu da Yaya Rabiu rik'e gidan.
Gefe ina ajiye dan ajiye wani abu a banki, dan tsaron lalurar da zata zo mini b'akatatan. Na shafe tunanin siyan gidan da nake burin yi. Domin tunda muka yi fad'an da Baban 2 ya ce mini gidansa ne ba nawa ba nake tunanin ya kamata na siyi gidan kaina. Idan na had'a zobuna na da dankunne na na sani ciko zan yi tunda manya ne sosai kowa yasan yadda gold ya tsefe. Zan siya zuwa gaba idan na warware matsalar Tijjani.
Sannu a hankali nake samun k'arfin zuciyar rungumar kaddarar da afko mana bakatatan. Mussaman da Baban 2 ya kwantar da hankalinsa ya yi imani da kaddarar da ta same shi.
95&96.
Auren Aliyu ya samu tasgado. Ba akan komai ba sai akan an kai suka gidansu amaryar cewar d'an-uwansa dan safarar kwaya me gwamnati ta rufe shi Shima ana kyautara zaton yana da BAK'AR TA'ADA. Muna ji muna ga ni aka hana Yaya Aliyu aure ba a akan laifinsa ba. Dama Kuma Babaiba son inda ya dauko auren ba, yar babban attajirice. A raina na Jin ciwon yadda mutanan yau suke yiwa mutane hukunci da laifin yan'uwansu ko na dangunsu alhalin Allah da kansa baya bawa da laifin mahaifansa bare kuma laifin d'an-uwansa. A zuciyata tamkar na ce masa ya nemi Iklima da a yanzu take kwalejin koyon aikin jinya da ke Azare, tana shekarar karshe. A kansu a aka zurfafa karatu ba tare da aure ba a gidanmu. Sun kammala sakandire babu samarin aure. Hakan ya sanya Jabir samowa kannensa gurbin karatu a inda yake koyarwa. Gabadaya mun tafi a cewa iyayensa suka hana ya had'a da ita. Hakan da muka gani ya sanya ni da su Yaya Salisu muka yi kundubalar saka Iklima a Health Technology Azare.
A tsaye take cak, doguwa mai cukar halitta kuma fara tas. Na tabbatar ba zai tankwabe ta ba, amma ina jin tsoron na furta.
Dan haka sai na tsiri gayyato ta hutu a karshen watan da na tabbatar yana yi mana jele. Akai akai suke haduwa kuwa. Su yi ta cakar juna tunda shi ma mai zolaya ne. Ni kuwa na dinga fad'in "um um fa Yaya Aliyu kada fa reshe ya juye da mujiya."
Wani lokacin ya yi dariya ya waske, wani lokacin kuma ya ce "Ba Wani reshe da zai juye, yarinya kankanuwa, raini dai nake son jawo masa.
Baba kuwa idan ta ji ya ce haka sai ta ce "Saboda ka kallafawa ranka son ka auri sa'aninka. Ban da haka ai itacw daidai da kai ".
A duk sadda Babah ta fad'i hakan dad'i ne yake matukar kama ni. Ina ganin nasara a kudirina.
Matukar yana gidan ita zan saka ta yi masa girki, ta dafa masa zobo. Wani lokacin ya yi godiya ya kwashi girki. Wani lokacin ya ce "Tunda na zama matar yayansa na ture girme mini da ya yi, nake mu'amalantarsa a matsayin k'anina. Ban da haka me yake hana ni na yi masa hidima da kaina sai na saka yarinya ta yi masa."
Na yi dariya na ce "Yaya Aliyu ko a lahira wani na cin arzkin wani ai"
Ba'a d'auki lokaci mai yawa ba ya fara fad'awa tarkonmu. Domin idan ya zo bai ganta ba, ya dinga tambayar me ya hana ta zuwa. Ko ba hutu suke yi ba, da sauran tambayoyi. Da na fahimci hakan kuwa sai na dakatar da zuwan nata. Domin so nake ya taka ya neme ta a inda take ba wai sai ya ganta dan ya zo ba.
Ilai kuwa wanne tudu wanne gangare ya silala yake zuwa daga haka har suka had'a kansu.
Tunda aka garkame Tijjani ban yi farin ciki har zuciyata ba sai akan wannan al'amarin. Domin dai Na tabbatar Aliyu mutumin kirki ne. Sannan Babah uwace ta gari bayan haka Ikilima zata auri mai rufin asiri. Zamu sake zargowa k'ofarmu wani hasken.
Bugu da kari y'aya'nmu zasu kasance cikinsu guda. Tunda shi da Tijjani daya ne, haka ni da ita.
Da maganar ta fasu a gidan Marina a lokacin da iyayensa suka je nema amsa aurenta. Ba abin da ba'a ce ba. Bak'in ciki muraran har ce wa aka yi ai k'aramin likita ne, wasu kuwa cewa suka yi ba ma likita ba ne. Malamin tsafta ne. Shi dai Baban Marina ya ce ya basu. Mu kuma dukkanin y'aya'n sa muka goyi bayan al'amarin. Aka saka aure idan ta kammala makaratan da wata daya, watanni biyar masu zuwa.
**
Alhaji Auta yana zaune al'amarin duniya ya sake damalmale masa. Gabadaya kasuwa ta juya masa baya fiye da bara. Fatan da yake yi akan kamfani ya kyamaci filin Tijjani saboda an kama shi da laifi bai ci ba. Har asiri yake nema akan su saki filin amma shiru. Su kuwa kamfani sunce riba suke nema. A wajen suke samun gamsuwa, babu ruwansu da laifin Tijjani. Idna lokacin da zasu biya ya yi, zasu tuntubi iyalinsa.
Ya rasa inda zai saka ransa. Jiya aoa kama babban dansa a cikin sahun y'an kidnaffing.
Dazu kuma k'aramin dansa aka kama shi da yana yuwa yarinya yar shekaru uku lalata a cikin gidansa. Gabadaya kwanciyar hankali da nutsuwa ta yi masa tutsu. Ya rame, ya zama tamkar mai ciwon sida, tsufa ya keto masa na ban mamaki.
Yana kishingide amma damuwa ta yi masa k'awanya. Wai shine naira dubu take yi masa wahalar rik'e wa?. Zullimi ya kama shi, idan akwai Bakar Taadar da ya yi ta dame shi bata wuce had'a kai da aka yi da shi wajen yiwa dan amininsa kazafin da yake kulle tsawon shekara guda ba. Ya yi shiru yana tuna irin yadda Tijjani yake zuwa yana gaishe shi cikin girmamawa. Akai akai yake yi masa alheri a matsayinsa na aminin ubansa kuma ubangidansa a kasuwa. Amma shaid'an da hassada suka saka ya jagoranci zaluncin da aka yi masa.
Kuka shabe shabe da hawaye. Ya rasa ta inda zai warware wannan k'ullin da suka yi.
Kan dole ya kira diaya abokin sharrin nasa, wanda yaro ne a kansa dan ba zai girme wa Bulkachuwa ba. Ya dauka murya a shak'e ya ce "Alhaji kana mini waya da ta wuce kaidar hankali gaskiyar magana na ke fad'a maka. Nima nema nake idan zan samu, ka fitine ni da bani bani gaskiya".
Da zullimi ya ce "Ba rokon zan yi ba Haladu! Maganar Tijjani zan yi maka. Gaskiya na yi abin da ya sha mini kai. A harzuke ya ce "To ni me zan yi maka? Ina ce Kai ka kawo shawarar, Kai ka kitsa yadda za'a yi? Ni kawai na karba a hannunsa tare da bawa haro ya ba shi. Hatta lambar wayar da aka kira shi, kai ka siya tun kuma a ranar ka taune shi. Kai ka yiwa Yan sandar hanya shunensa tare da bada lambar motarsa. Kaine zaka yi dakon zunubin ka. Idan ka yi kuskuren saka ni a ciki kuwa Wallahi sai na bata maka suna a idon duniya. Sannan sai na lahanta ka."
Kuka wiwi ta k'wace wa Alhaji Auta tamkar mace.
Ta ya ya zai kubutar da Tijjani?
***
Yini na yi ina yiwa wata hamshakiyar Hajiya kunshi ita da mukarrabanta. Da zata tafi ta ajiye mini kudi a envelope. Ga mamakina da na bude dubu hamsin na gani a ciki. Duk da sunzo da yawa sosai. Amma tabbas kudina bai kai haka ba. Rub'anya mini ta yi. Ban sani ba ko dan na yi jarumtar yi musu jollof din taliya mai dad'i ne. Na kuma baibaye su da pure water mai sayi tunda Ina siyarwa.
Na lura ta ji dad'in yadda na yi musu, sannan ta yaba da kunshin da na yarfawa kakkaurar k'afarta fara tas.
Cikin hira nake fad'a mata na iya kwalliya ma sai dai nafi bada k'arfi a lalle da kitso.
Kwanaki biyu da tafiyar ta sai ga waya ta k'ira ni akan wani satin zan je gidan gwamnati na yiwa mai dakin gwamna kunshi zata je bikin d'iyar gwamnan Jigawa.
Jikina ya sab'e da rawa. Ni Yabi zan je government house a sanadin sana'a ta?
A fili na ce "Alhamdulillah! Ubangiji ka bani damar da zan yi amafani da ita na fito da Baban 2. Allah ka yi alkawarin taimakon wanda aka zalunce shi. Ubangiji ka shiga lamarin Tijjani."
Na zauna kusa da Babah ina fad'a mata. Ta yi farinciki sosai.
Na ce "Idan mun je ganinsa zan fad'a masa, idan bai amince ba zan hak'ura, tunda nasan baya son na dinga zuwa gidajen mutane".
Ta zuba mini ido ta ce "Allah ya yi miki albarka, Ubangiji ya kawo mana karshen ibtilain nan. Allah ya dawo da mijin ki, zaman zai yi miki yawa babu miji a tare da ke."
Sai kawai ta fashe da kuka sosai. Da rawar murya nake bata hak'uri. Ina ce wa "Zan iya Babah! Zan jira shi, da ikon Allah zai dawo a kusa ma".
**
Muna ta shirin tafiya dubo Baban 2 a dalilin a irin wannan ranar ta asabar din k'arshen ko wanne wata muke zuwa duba shi, tare da kai masa kayan shopping tamkar na dan makarantar kwana.
Ni nake had'a masa wannan kayan. Kudin lallena da kitso suna tafiya ne a hidimarsa da ta gidanmu domin Yaya Aliyu ne yake rik'e da mu. Daidai da pencir ban san na siyawa su Hanif ba. A yadda na taso a irin gidanmu da babu tausayi da tallafawa na k'asa ban yi zaton Aliyu zai yiwa Bulkachuwa irin wannan zumuncin ba. Na sani hidimar kayan abincinmu da baya mantawa akwai alfarmar mahaifiyarsu a tare da mu. Amma yadda baya mance wa da y'aya'n Tijjani na gamsu ko Babah bata tare da mu zai yi iyakacin kokarinsa.
Da na fahimci basu mayar da hankali wajen kai wa Tijjani kayan ciye ciye ba. Ni kuwa sai na mayar da hankali, domin shopping nake yi masa mai sunan shopping. Hatta kifin gwangwani ina siya masa fiye da dozin guda duk wata. Kayan shayi da su conflakes kam ba'a maganarsu. Babah har fad'i take wai kayan suna yin yawa. Biskit irin masu dadin nan kullum na yi lalle sai na siya, kafin lokacin da zamu je, sai na yara masu yawan gaske. Sannan bana raba shi da cincin da cake. Kullum fes muke ganinsa. Illa duhu da ya yi. Amma da dukkan zuciyarsa ya karbi kaddarar da ta fad'o masa. Da wuri muke tafiya, da k'atuwar tabarmarmu. Tunda Yaya Ammar yana cikin manyan gandorurobobin kurkun bamu da matsalar komai. Domin yini muke sai yamma lis muke dawowa.
Muna zaune mun gama cin abinci. Ya kalle ni ya ce "Baba lafiya bata zo ba yau?"
Na yi murmushi na ce "Ta ce wai takuramu take yi, ba zata zo ba sai wani zuwan".
Murya babu amo ya ce "Da ta zo abin ta."
"Ni ma hakan na ce mata Wallahi".
Ya kalli yaran suna can nesa damu suna kallon bishiyar mangwaro da y'aya'n suka sauko kasa kasa ana iya mika hannu a tsinko.
Ya kankance murya ya ce "Little kina kewata ko?"
Na yi k'asa da kai, idona ya cicciko domin babu yadda za'a yi mu zo bai mini wannan tambayar ba. Na fahimci ita ce tafi damunsa. Na kalle shi na ce "Ina kewar ka sosai Baban 2. Kullum dare idan na kalli inda kake kwanciya sai na jika filo da hawaye! Amma ina karfafa kaina guiwar cewa tunda muna shakar numfashi daya a wannan duniyar akwai lokacin da zai zo da zaka dawo cikinmu mu cigaba da rayuwa. Ina kuma da tabbacin rayuwar da zamu yi zata Fi wacce muka yi a baya nutsuwa da kwanciyar hankali. Yaya Aliyu yana matukar kokari akan gidanka. Su Yaya Salisu da su Ammar suna taimaka, bamu da matsalar komai sai rashin ka."
Ya ce "Ke Baki fad'o naki k'ok'arin ba little ".
Na ce "Ka sha fad'a mini, ni kake da tabbacin ba zan gaji da hidimar y'aya'nka ba. So nake ka gane ba y'aya'nka ba kawai kai kanka da mahaifiyarka ba zan gaji da hidimar ku ba, muddin ina numfashi."
Ya kasa magana. Sai can ya nisa ya ce "Ina son ki sosai little. Ina rok'on Ubangiji ya taya ni son ki, ya k'ara miki hak'uri da jarumta".
Cikin rauni na ce "Ameen" domin ya yi matukar ba ni tausayi.
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "jiya shekara ta d'aya a nan. Tunanin ki kad'ai yasa nake ganin na dade. Amma ban da hakan ba k'aramin gata aka yi mini ba. Domin tunda nake ban tab'a samun damar da nake yin ibada nake ambaton Ubangiji irin a wannan lokacin ba. Na gamsu akwia hikimar Ubangiji ta sakaye ni a nan. Ba ni kaina ba, ko ke addu'ar da nake yi miki little ta ishe ki, bare kuma y'aya'n ki. Shi yasa ban damu sosai ba, da aka kasa fitar da ni".
Na ce "Allah ya karba. Ina kuma ganin tasirin addu'ar ka garemu domin bamu tozarta ba Baban 2."
Ya ce "Ki tsananta addu'ar nan ta*RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN.* Kullum ina fad'a miki tasirinta mai yawa ne".
Na zuba masa ido, shi ma ya zuba mini tsawon lokaci muna kallon juna, idanuwanmu cike da k'walla.
Ya yi k'arfin halin danne nasa hawayen ya hadiye. Ya ce "So nake na gan ki da ciki Little"
Nasan yadda kike son haihuwa. Na kuma tabbatar renon ciki da hidimar bebi zaisa ba zaki ga nisan zaman da zan yi ba".
Na ce "Ta ya ya hakan zata kasance Baban 2?"
Domin ni kaina idan har zan samu cikin zan yi matukar farinciki mai yawa.
Ya ce "Kina so?"
Na daga kaina da sauri amma ban yarda na d'ago kaina ba. Domin haka kawai na ji kunya ta rufe ni.
Ya ce "Shike nan zan roki arzikin Ammar ko zai mini alfarma".
Na ce "Me zaka ce masa?"
Ya ce "Zaki ji daga baya."
Na d'ago na ce "Amma Baban 2 idan na samu ya bare kada ka ce na zubar maka fa, nasan halin ka".
Ya dan murmusa ya ce "Ai ina fad'a miki ne dan na rama rikici da tashin hankalin da kika dinga yi mini kafin ki samu cikin twins".
Na rufe idanuwana ina dariya sosai".
Na ce "wanccan satin dai aka daura auren Nasiba".
Ya ja tsaki ya ce "Ammar ya fad'a mini. Ya isa haka kuma".
Na yi maza na sauya maganar da ce wa "Ka saurare ni da kyau Baban 2 ".
Ya ce "Ina jin ki".
Na ce "Jiya wata baiwar Allah ta mini waya akan gobe suna son na je gidan gwamnati na yiwa mai dakin gwamna kunshi. Na ce su saurare ni kad'an. So nake mu tattauna me zaka ce game da hakan. Na fi son na yi komai da yardar ka".
Ya yi shiru. Sai kuma ya ce "Kuna da matsalar Wani ma abinci ko ma bukata ne?"
Da azama na ce "Wallahi bamu da ita. Kuma Ubangiji yana kawo mini mutane har gida babu yanke wa."
Ya ce "To bana son zuwan ki gidan mutane Asiya"
Na zuba masa ido na ce "Bajq zuwa, ba Kuma zan je ba. Amma sai nake ganin da ka yi hak'uri na je wannan din. Domin ina son a shiga jikin matar gwamna. Watak'ila ta sanadin ta sai Ubangiji ya fito mini da kai, tunda ka hana ni dauko maka lauyoyi, ka hana ni neman taimakon manyan mutane. Ka bani dama yanzu,tunda ita mace ce kuma komai sai da sabab"
Ya yi shiru. Kafin ya nisa ya ce "Tsoro nake ji Asiya. Ina jin tsoro kada ki samu dama mai yawa ki fi k'arfina ki k'asa yi mini hak'uri da kike yi yanzu"
Ya fada hankalinsa a tashe ainun. Na ce "Haba mana Baban 2! Me yasa kake wasiwasi a kaina? Har duniya ta nade ni taka ce. Ina fad'a maka idan shekaru hamsin aka daure ka Wallahi zan jure na jira ka. Da bakinka ka fad'a mini akwai iyaye mata da suke sadaukar da kuruciyarsu saboda y'aya'nsu. Ashe ni baka gamsu zan yi irin wannan sadaukarwar idan kasa ta rufe maka ido ba. Tunda ga shi da ranka ma kana kallon ba zan iya sadaukar da komai saboda na reni yayanka ba."
Ya girgiza kai ya ce "Ba hakan ba ne Asiya. Na sani zaki yi mini komai. Sannan ke yaranki basi yawa".
Na ce "Ba yanzu ka gama mini albishir din zaka samo hanyar da zamu bi mu samo wasu yaran ba? Har na fara tunanin zan ga likita dan a d'ora ni a maganganun da zan zasu taimake ni wajen samun ciki da wuri.
Ashe da wasa kake yi, ni kuma have nasa rai".
Ya ce "Ba wasa nake yi ba. Na ce "To ka ba ni wannan damar. Bana son na yi abu ba tare da ka sani ba, bana son na bata maka rai Baban 2 ".
Ya saki ajiyar zuciya ya ce"Shike nan. Amma tare da yara da Babah za'a dauke ku".
Da sauri na ce "Dama tare da su zamu je. Na gode, Allah yasa hakan ya zame mana sanadin alheri".
Ya ce "Ameen.
Daga haka na shiga ba shi labarin Aliyu da Iklima. Ya murmusa farincikin zuciyarsa ya bayyana akan fuskar sa.
Haka muka dinga hira. Har lokacin tafiyarmu ya yi. Hanif ya ce "Baban 2 sai mun sake dawowa. Hamim kuwa ya ce "To bude ka bamu biscuit din naka"
Ya kuwa bude ya bawa kowa a hannunsa.
Suka had'a baki suna fad'in"Mun gode, Allah ya fito mana da kai!
Ya ce "Oya ku je office din Uncle ku ce masa zaku tafi ".
Suka ruga a guje, suka nufi office din Yaya Ammar.
Ba jimawa ya fito rik'e da hannuwansu. Ya kalle ni ya ce "Zaku tafi Yabi?"
Na ce "Eh Yaya mun gode sosai."
Ya ce "Dafatan dai kin fad'a masa ya dinga cin abinci. Ba kasafai yake cin abinci ba. Kullum sai na taho masa da abinci daga gida. Amma baya wani cin na kirki."
Na yi murmushin kunya na ce "Ina ce wa "Na yi masa".
Daga hakan muka taho ya bude mana k'ofa, har titi ya kawomu. Ya tarar mana Napep ya biya sai da ya ga mun tafi sannan ya koma.
Muka isa gida na fad'awa Babah ya amince amma ya ce mu je tare. Ta ce "To sai mu je taren. Allah ya tabbatar mana da alheri.
Ai kuwa har kofar gida Hajiyar nan ta zo ta kwashe mu ni da zugata. Tunda yara na hutu.
Sai gamu daredare cikin fadar gwamnati. Aka baibaye mu da abubuwan motsa baki. Ashe Hajiyar nan mai magana da yawun matar gwamnace. Ba'a bata mana lokaci ba aka yi mana iso zuwa dakin da zamu yi kunshin.
Zuciyata tana harbawa na fara yi mata. Sai addu'a nake Ubangiji ya ba ni sa'a na yi wadda zai yi kyau ta kuma yaba.
Cikin nutsuwa nake yi. Tana yi tana kallona. Na kammala kunshi. Na fara yarfa mata kitso akan dogin gashinta da ya sha gyara na garari.
Na kammala. Ta ce hadinaeta ya dauko matso mata dogon console mirror din da yake gefe. Ta ga yadda na yarfa mata kitso. Ta murmusa alamun ta gansu da abin da ta ga ni. Ta kalle ni ta ce "Kin kammala sakandire ne?"
Na kasa amsawa domin na tabbatar k'ank'anta ta ya sanya ta yi zaton ko ban yi Kandi ba. Ta lalli Babah ta ce "Hajiya kar dai bata zuwa makaranta?"
A tausashe ta ce "Ta kammala tuntuni. Ta nuna su Hamim da suka lafe a jikinta ta ce "wadannan ai y'aya'nta ne ba kanne ba."
Ta dauki salati tare da fad'in "Wonderful. Yanzu ke ce uwar wadannan samarin?"
Babah ta ce "Ita ce kinga Kuma sai da shekara biyu a daki sannan ta haife su. Tana shatakwaas ta haife su".
First lady ta sake tsananta mamakinta ta ce "Yanzu shekarun yaran nawa tunda masu garin jiki ne ba irin ba ne tsaba"
Babah cikin dariya ta ce "Shekarunsu bakwai."
Ta sakki ajiyar zuciya tana kallona ta ce "Shekaru ashirin da biyar a wannan yarinyar. Ikon Allah. Tunda na ganta na ce kyakkwar yarinya Allah dai yasa tana zuwa makaranta ba iya sana'a take yi ba. Ashe ba yarinyace ainun yadda na zata ba, ban zaci ta cika sha biyar ba ma."
Ta ce kin yi karatu ne bayan na sakandire?"
A hankali na daga kaina na ce "Na yi N.C.E a nan college of education. Na karanta Home economics "
Ta fadada murmushin ta ta ce "Da kyau! Kina aiki ne?"
Na ce "A a takarda ta ta yi kyau amma Ubangiji bai kawo mini sababin samun aikin ba".
Ta ce "Ai kuwa kin samu yarinya".
Ta Kalli Hajiyar da ta kawo mu ta ce "A buga mata upper. A kai ta women center mafi kusa da ita ta dinga koyawa yaranmu sana'ar kitso da kunshi, hadi da tattalin gida."
Daga yau kuma na bata mukamin costume din first lady".
Cikin farin ciki Hajiyar take godiya a madadinmu. Ni kuma mamakin murnar da take yi ne ya sandarar da ni domin dai na jima ban ga mutanan da basu da Bakar Taadar kyashi da hassada kamar Hajiya mai magana da yawun matar gwamna ba.
Baba ta shiga godiya ita ma. Haka nima na shiga godiya mai yawa, kna hawayen farinciki. Na samu daukaka ta sanadin sana'a. Hatta aikin da na samu arzikin sana'a ne ya janyo mini. Alhamdulillah na dinga ambato babu sassautawa.
97&98
Da zamu tafi aka zuba mana leshina da atamfofi da kayan yara fall leda. Ga Kuma kayan ciye ciye da soyayyun nama. Sai da na nutsu sai na gane har da material din Malaysian Fabrics na umm Nihla.
Ta ce kuma Hajiyar ta sallame ni. Murya na rawa Babah ta ce "Baby wata sallama Kuma. Ai kin nuna mana ke din uwar kowa ce a wannan jahar. Allah ya kare ki, ya dora mijin ki akan magauta. Ya dauwamar da arziki ya shirya muku zuria "
Cikin Jin dad'i take fad'in Ameen amen".
Har gida Hajiyar ta kawo mu . Ta shigo ta huta. Kafin ta bar gidan Baba ta zayyane mata matsalar da mkue ciki akan lamarin Tijjani.
Ta ka'du k'warai da gaske. Sannan ta ce zata shigar da maganar gaban first lady da IZININ UBANGIJI.
Ta ajiye envelope tana ce wa "Ga albashin ki na farko costumes din matar gwamna. Kafin kuma ki fara karboa na gwamnati. Cikin satin nan zan kawo miki upper din ki har gida "
Na dinga yi mata addu'ar fatan alheri da godiya mai yawa. Ta karbi takarduna ta tafi da su.
Kwanaki uku ta dawo mini da upper kamar yadda ta yi alkawarin kawo mini har gida. Sannan women center din unguwarmu aka tura ni. Wnai abin burgewa a weekend ne aikin nawa. Ga albashina da tsoka babu laifi.
Sati na zagowa muka tafi wajen Tijjani muka yi masa bayanin halin da ake ciki. Ya yi murna, ya yi fatan alheri.
Ya sake jaddada mini bai yarda na dinga zuwa gidajen mutane ba. Gidan gwamnati ya amice Slshima sai tare da Babah zamu je. Da girmamawa nake ce wa to, domin ya samu nutsuwa. Nima kuma bana k'aunar abin da zai bata masa rai. Domin a yanzu na gasgata bayan iyayena ba abin da nake so a duniya irin Tijjani da y'aya'nsa. Hatta uwarsa da y'an uwansa ina jinsu daban a duniyata.
Ganin ya amince na ce wa Babah zamu je Toro na KAIWA su Baban Marina su ga upper ta."
Ta ce "hakan ya yi. Washagari kuwa muka tafi Toro.
Murna kan murna Baban Marina ya yi. Ya dafa kaina ya ce "Nasan zaki yi albarka Yabi. Na sani akwai babban al'amari a tare da ke. Na sani zaki daukaka. Alhamdulillah! Ubangiji ya fito mana da Tijjani. Allah ya shirya miki zuria. Allah yasa albarka a cikin komai na ki. Yadda kike tsaye a kaina da iyalina Ubangiji ya tsaya miki ke da ahalin ki fiye da haka. Asiya ke kad'ai gayya ce a gidan Marina".
Na yi k'asa da kaina ina hawaye. Ina Jin rashin Tijjani ne cikas dina.
Amma babu abinda ban samu ba na rufin asiri a duniyar nan ba.
Kafin ka ce miye wannan sai na fara Tara kudade masu nauyi. Domin dai ban fasa yin lalle a gida ba. Duk wata albashi biyu nake ja. Ga wanda gwamnati zata ba ni. Ga wanda ake ba ni a envelope idan na je gidan gwamnati na yiwa Madam da iyalin ta kunshi da kitso.
Bana tab'a su tunda har yau Yaya Aliyu bai tab'a yin lako lako da abincinmu da kuma kula da yara ba. Iya na lalle dai da shi nake hidimar da nake yi. Domin so nake na yiwa Baban Marina ba zata ta ban mamaki.
A hankali alherin da ya same ni ya fara shiga kunnuwan mutanan gidan Marina.
Nan da nan aka fara cece kuce. Ko a biki aka taru saa'anninmu da na yi musu zarrra zasu yi ta sakin baki a gaban Nazira suna ce wa "Ai yanzu na zama y'ar siyasa ba kuma siyasar ce abin kaico ba. Manyan mata ne suke dauka ta muke sheke ayarmu. Ta ya ya za'a ce wai matar gwamna nake yiwa kunshi. Wace ce ni? A wanne karatun da bai fi cikin cokali ba. Tun Nazira na hak'uri, tana tankawa cikin dad'in rai tana fahimtar da su, har ta shiga yin tashin hankali da duk wanda zai soke ni. Hatta yaran dakin inna k'ananunmu ke nan da a yanzu suke y'anmata matukar suka ji wani ya soke ni sai dai aji na gwabza fad'a. Tunda ce wa suke hi karuwanci nake yi. Gabadaya y'an k'ofarmu ba yadda za'a yi a tab'asu su kyale a yanzu. Ganin hakan sai aka koma fad'in ni ce nake musu huduba tunda nima hakan na yi , sannan na mayar da dukkan ahalin Babanmu agwagi sai abin da na ce tunda na fisu kudi. Dan ma sunsan kudin nawa da ake famkama na kazanta ne. Sannan mugun k'ullin da yake raina ne ya sanya aka gane mijina dilar k'waya ne.
Dana zauna na nutsu sai na gane tabbas wata k'iyayyar bata da dalilin yin ta. Mafi yawa hassada ne da kyashi. Ba kuma zai yiwu kowa ya so ka ba. Babbar godiyar da nake tsananta yi ban tab'a zuwa gidan Marina na tsugunna a gaban wani na ce a taimake ni ba. Duk yadda aka yi mini aure dan a kassara ni, sai Ubangiji ya yi kishina. Wahala kam na sha ta, amma ba mai yawa ba ce. Sannan Ubangiji ya yi mini rufin asiri irin wanda ko y'aya' mazan gidanmu basu same shi ba.
Mafi girman Niimar da Ubangiji ya yi mini, itace ta lafiya da kuma sana'ar hannu, ya kuma ba ni haihuwa, ya sake ba ni mijin da yake tsananin sona. Bugu da kari ina cikin wadanda Ubangiji ya yi musu gata irin na gam da katar na girma da iyayena guda biyu. Wannan kad'ai babbar niimace a wajen bawa. Domin ko da ban san zafin rashin iyaye ba. Allah ya sani ina matukar tausayin wanda iyayen sa suka rasu domin al'amarin da suke fuskanta mai tsananin gaske ne. Ka ga masu iyaye suna samun TAGOMASHIN addu'a, suna samun tallafi, suna zuwa su yi hira da su, domin sun san zasu boye damuwarsu, sabanin wadanda basu dasu a raye sun dinga tiri tiri da matsalar da ta dame su saboda gudun za'a fantsama matsalarsu a duniya.
Da na tattara wadannan ni'imomin sai na ga ba zai yiwu kuma a ce kowa ya so ni ba. Ba zai yiwa kuma na ga yadda nake so ba. Tunda sunnar rayuwa ce kowa da irin k'alubalen da zai fuskanta a duniyarsa. Sai na gamsu kalubalena rufe Tijjani da aka yi. Ina rayuwa babu miji tsawon shekara guda. Sai kuma rashin soyayya daga dangi, da rashin hadin kai a tsakaninmu.
Na numfasa na ce Alhamdulillah. Ubangiji ka yi mini komai. Allah ka fito mini da Mijina. Ubangiji a sanya soyayya da tausayi a zukatan ahalin gidan Marina gabad'aya. Domin na riga da na gaji da gutsiri tsoma Wallahi.
A haka bikin su Ikilima ya matso. Ta ko ina ba ni da sukuni. Domin da na fad'awa mai dakin gwamna za'a yi auren kanwata. Tana bude baki sai ce wa ta yi mu je da Hajiya na zaba gado da kujeru da kayan dakin koami da koami zata yi.
Allah ya dora mata sona da tausayina, mussaman yadda na bata labarin tabbas Tijjani sharri aka yi masa ba halinsa ba ne. Ta yi mini alkawarin za'a fito da shi amma ba tashi guda ba. Na saurare ta.
Dan haka komai na garari aka siyawa Iklima. Har Toro kuma ta tura Hajiya ta kai kayan abinci gidanmu ta ce a yi hidimar biki.
Ganin yanayin gidan namu ya sanya Hajiya ta sake buda mini a dalilin ta yadda gidan yake na masu k'aramim k'arfi ne ainun.
Idan na zauna sai na yi ta ambton Ubangiji domin ya yi mini komai. Mafi Jin dad'i ta yadda ni ce sanadin hadin kan y'an k'ofarmu.
A haka aka yi bikin cikin rufin asiri. A cikin BAUCHI ya yi gidansa ba nisa da ganeral hospital din da yake aiki.
Ba'a jima ba aka kawo Baban 2 asibiti ba shi da lafiya. Kwanaki biyu na fahimci dan yana da hanya ne har aka fito da shi, ban da hakan ai za'a ba shi magani a sickbay din kurkun. Yaya Aliyu kuwa ya saka aka bashi daki a aminity. Yayin da Yaya Ammar ya yi kane kane shine jami'in da zai zauna da shi a madadin ma'aikatan gidan yarin. Dan haka da rana anan muke yini. Da yamma mu tafi da su Babah. Da daddare kuwa Yaya Aliyu zai zo da kansa ya dauke ni da abinci mu tafi. Ba zan dawo ba sai da safe. Tun ina jin kunyarta har na matse na cigaba da harkar gabana tunda bata taba ce mini komai ko bin ba'asin kwanan da nake yi a asibiti ba.
Ragowar saiwowin da aka yiwa Iklima da garin daka na yi ta sha. A gefe kuma Ina hadiyar zabbabun supplement na GHT da FASEELAT ta zaba mini su.
Muna kwance akan bargon da na shimfi'da akan tabarma tunda gadon ya yi mana kad'an.
Ya ce "Kina shan maganin kuwa?"
Na ce "Na kai wata ina sha, da yake an dora ni kan maganin da zai taimaka mini wajen conceiving. Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Allah yasa satin da na yi addu'armu ta cika. Gobe zan koma kin sani. Wato albarkacin Ammar na yafe wa Baba Maryo! Asiya Ammar mutum ne. Kullum sai ya kai mini abinci. Wanccan satin na nuna masa ina son ya mini alfarmar ganin iyalina na kwana d'aya. Ina rufe baki ya ce "Na fara zazzabi, zai yi kokarin a kai ni asibitin waje daga nan sai ki zo."
Ki ga irin hadarin da ya runguma saboda ya faranta mini. Tunda idan aka gane shi za'a iya sallamarsa daga aikin ace ya ci Amanar aikinsa. Ki ga yadda ya bamu sati a maimakon kwana d'aya ko biyu."
Na numfasa na ce "Ni ma na yafe mata Allah ya shirye mu gabadaya."
Ya ce "Ameen! Allah yasa kin harbu little."
Na rufe fuskata a kirijinsa.
Ya dinga Shafa fatar jikina ya ce man nan na Oriflame ya karbe ki. Jikar Dada dai ta iya zabarwa mutum man da ya dace da shi."
Na murmusa cikin jin dadin yabawarsa na ce Aisha lame ai ta k'ware, wajen mayar da mace zama y'ar gayu ta gaske".
Ya ce "Na gasgata ki".
Washa gari kuwa aka sallame shi. Ina kallon yadda aka tafi da shi. Sai kawia kuka ya kwace mini a dalilin Babah tana gida saboda yara.
Aliyu ya dinga ba ni hakuri yana ce wa "To da ba ki samu damar ganinsa ba fa?
Sati guda fa ya zo ya yi miki haba dai Yabi. Ki yi hak'uri komai zai wuce.
***
*Watanni biyu*
Ana cikin haka kwatsam gwamnatin tarayya ta rage lakcarori cikin ikon Ubangiji har da Yaya Jabir aka sallama.
Gabadaya mun ji ba dad'i mussaman da yake ya tara iyali. Tunda amaryarsa ma yaranta biyu, Maijidda na da biyar domin haihuwa take akai akai tamkar da gayya.
Zaman Kaduna ya gagara tunda dama a quayers yake. Kan dole ya tattaro ya dawo Toro.
Na tausaya, na ji babu dad'i dole a aka hak'ura tare da fatan Allah ya kawo wata damar.
Baban Tsakiya ya dinga fad'in sa hannu ne. Kuma a cikin wadanda yake zargi har da Baban Kasuwa. Domin ya ce ai tunda Jabir ya kara aure yake ta tsiyace wa. Tabbas hannu aka saka masa. Yayin da Baban Kasuwa da ahalinsa suke murnanr hakan da ya samu Yaya J. Tunda sun tafi a cewar Jabir yana fifita amaryarsa akan Maijidda da take yar'uwasa kuma uwar y'aya'nsa. To yanzu sai ya yi rashin mutuncin su ga ni.
Daga Baban Tsakiya har Baban Kasuwa kowa so yake a ce Baban Marina a bayansa yake. Har yau din nan sun fishi kudi. Amma ya fisu gata da rufin asiri . Domin a yanzu yana fita wajen sana'arsa saboda sabo da kuma mike kafa. Amma duk watan duniya sai mun ajiye abincin da za'a ci a kofarsa da kudin cefane. Hatta sabulun wanki da na wanka da zai bawa iyalinsa mun dauke shi. Hadawa muke yi gwagwadon k'arfin mutum. Ni ce sha kundum.
Hakan da suke gani kuma sai kowa a cikinsu yake son ya shige masa, ya soki d'an-uwansa a gabansa. Shi kuwa baya biye wani a cikinsu suyi hirar wani. Amma ya karbe su da fuskar afuwa da sassauci yake mauaamala da su. Tunda ba abin da Ubangiji bai masa ba. Jahilci ne ka ce zaka rama sharri da sharri. Bakar Taada ce ka ce zaka maimaitawa wani irin kuskuren da aka yi maka. Mussaman akan zumunci, matukar ana son gyara, matukar ana son cigaba. To a bar BAK'AR TA'ADAR riko da kullaci. Afuwa da yafiya yana kawo soyayya da masalaha a tsakanin jini guda. Tashin tashina kuwa yana dawo da gaba da k'iyayyar juna. Allah ya yafe mu gabadaya.
Zaune nake kusa da Babah yayin da Anas yake kan kujera su Hanif suna ta dabdala a jikinsa. Babah ta kalle shi ta ce "Kai bana son iskanci ka ji. Da wasa kake ko kuwa da gaske kake wannan maganar?"
Da murmushi ya ce "Wallahi ta makance Babah!
Ga mamakinmu sai Babah ta fashe da kuka tana fad'in"Allah mun tuba. Allah ka yafe mana. Ni dai ka shaida na yafe mata.
Anas ina rokon arzikin ka, ka yafe mata. Addu'ar da ka yi mata cikin fishi ne Ubangiji ya karba. Ka yi hak'uri. Yau na sake gasgata A guji addu'ar wanda aka zalunta, mussaman idan ya yi ta cikin fishi da neman agajin Allah".
Nan da nan ya ce "Na yafe mata. Ko yanzu idonta ya bude zan yi murna, idan bai bude ba kuwa Allah yasa ya zame mata kaffara. Amma ai ko yanzu ta ga karshen sharri. Tsofe tsofe da ita ta yi mini bakin sharri irin wannn. Haba wannan duniyar cike take da rudani. Ace wai jinin ka bai k'i ka tozarta ka yi bak'in ciki ba?"
Ta share hawaye tana fad'in "Babu wanda zai mori zumunci sai wanda ya yi hak'uri ya hadiye komai, ya yi sassauci ya kuma yi afuwa. Zumunci da kansa ya roki Zati ya ce "Ubangiji ka jefa wanda ya yanke ni cikin wuta. Ubangiji ka tsananta wa wanda ya tsananta mini. Allah kuma take ya karbi addu'ar zumuncin. Shi yasa Annabi ya yi ta jan kunnenmu akan zumunci. Hatta makoci da aminin iyaye sai da Annabi ya yi ta jan kunnenmu a kansu bare kuma wadda nasabarku guda. Akwai bukatar mu ninka hak'uri da kawaici, hadi da yafiya idan kuwa ba hakan ba, gaisuwa ma sai ta gagara a tsakanin jini guda."
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Da dukkan zuciyata na yafe mata. Na yafe wa kowa. Allah ya cigaba da dafa mana."
Ta ce "Ameen na gode Anas. Na gode da ka yarda da maganata Ubangiji ya yi maka albarka".
*Ya ce "Ameem Hajiya Babah tamu".
**
Jumaa da yamma muka yi Toro. Muka tarar da baba Maryo a zaune a dakinta jikinta ras. Ido kuma gwaragwara amma bata ga ni. Fadi take yi "Na rantse bakin Anas ne ya kama ni. A yiwa ma'aiki a kira mini shi. Wallahi ya fini gaskiya. Hauwa ki yafe mini. Ki roka mini afuwa a wajen Yabi da Tijjani."
Ta kece da kuka. Na matsa kusa da ita na ce "Baba ki yi hakuri. Ban kullace ki ba. Na kuma yafe miki. Na Ari bakin Tijjani shi ma ya yafe miki. Allah ha baki lafiya."
Babah ma tana kuka ta rik'e hannunta ta ce "Sannu da ibada Maryo! Tuni na yafe miki babu komai a zuciyata game da sha'anin ki. Sai alheri. Allah ya yafe mu gabadaya ya kuma gajarta miki wahala. Sannan Anas ya yafe miki tuni, zan kuma k'ira miki shi ki ji da kunnen ki.
A take Babah ta kira Yaya Aliyu ta ce ya bar komai gobe ya zo ya dauke su zuwa asibiti a duba ta da kyau.
A Toro Babah ta barmu suka nufi asibitin Jos tare da Yaya Aliyu da kuma Yaya Ammar. Dama Nasiba a can take aure dan haka babu matsalar abinci.
Kamar jira jikina yake na zo Toro ai sai kawai na hau wani irin zazzafan zazzabi. Hak'ora na har kad'uwa suke yi. Ga azabar ciwon k'asusuwa. Sai na ji tamkar ana kwankwatsa mini jikina. Kullum jiki sai dada rikice wa yake yi. Amai ya tisa ni a gaba. Ba dama a d'ora tukunya yanzu zan fara amaye amaye.
Hankali iyayena ya tashi. Da yake yanzu mamam ta hakurkurtar da zuciyarta ta daina tsiyataku, aka rasa me za'a ce mini. Tunda alamu k'arara na mai shigar ciki sun bayyana mini. Gwaggo ta rasa me zata ce mini. Sai da dare ya yi dare. Ta yi gyaran murya bayan ta gama danna mini jiki ta ce "Yabi alamun shigar ciki nake ga ni a tare da ke"
Sanin a cikin zullimi take ya sanya ban tsaya noke noke ba na ce "Ni ma ina kyauta zaton shine Gwaggo".
Ta hau salati ta ce "Cikin haihuwa Yabi?"
Na ce "Shi fa Gwaggo".
Ta dauki sabon salati ta ce "Ta ina kika samu ciki Yabi? Nasan dai da ikon Ubangiji ba zaki yi ashararanci ba, ina kyautata miki zato."
Na saki ajiyar zuciya. Ga shi ina jin jiki. Ina nishi na ce "Na gode da kyakkwar shaida Gwaggo".
Daga haka na kulle bakina a dalilin yadda nake jin tsananin kwankwatsa a duka jikina.
Kan dole ta tashi doro alwallah ta tada sallah. Ganin bata samu nutsuwa ainun ba. Ya sanya bayan ta yi sallama na ce "Gwaggo
Zaton da kike kyautata mini tabbas hakane. Kuma hakkun ciki ne. Idan Babah ta zo ki tuntube ta ki ji me zata ce akan hakan".
Ta zuba mini ido ta ce "Yabi a gidan kurkun kuka yi cikin ko a ina?"
Na fara nishi ina fad'in "Ki bari ta zo, ni ba iya bayanin nan zan yi ba. Dan Allah ki zo ki cigaba da matsa mini kafafuwana".
Ta sake daukan salati tare da tafa hannu. Sai nanata iko sai lillahi take yi. Sai ta yi shiru sai ta sake zabura ta d'auki salati tana ce wa "K'warzaba da jarabar yaran yau ta kai kure wa. Ni Asma'u ina kallon zamani".
A kan dole ta cigaba da yi mini tausa. Tana yi, tana hirji domin ta shiga mamaki mai yawa.
Da safe da Baban Marina ya shigo duba ni. A sanyaye ta ce "cikine da Yabi Alhaji".
Babu dar ya ce "Ma sha Allah! Ai rabo ba k'aramin al'amari ba ne. Allah ya raba lafiya".
Ta yi galala ta ce "Alhaji na ga baka ka'du ba!
Ya murmusa ya ce "kad'uwar me zan yi bayan na gasgata Yabi tamkar yadda na gasgata yunwar cikina. Ita tasan yadda ta had'u da mijinta. Tana da miji kuma dan na ganta da ciki sai na bi ba'asi, akan me?"
Ta ce "To ai kowa yasan baya nan, sai kuma a ganta da ciki, kana jin yadda ake daura mata magana haka siddan. Ina kuma a ganta da ciki".
Ya ja tsaki ya ce "Idan har kika daka bak'ak'en taadodin jama'a babu abin da zaki yi. Ya mik'e yana ce wa "Sannu Allah ya raba ku lafiya."
Ya saka kai ya fice.
Satin su baba biyu sannan suka dawo, cikin sa'a ido daya ya budu. Daya ya mutu. Aka yi murna da yi mata barka da arzikin da ta auna.
Babah tana zaune a dakin Gwaggo. Yayin da nake kwance akan k'aramin gadon. Na samu sauki, amma jikin babu k'warai.
Gwaggo ta ce "ikon Allah Yabi dai ciki ne da ita."
Ta dauke kai ta ce "Ho ke kam yanzu kina neman baci da magana. Ina dalilin wannan tuyar da kike yi ne. Nasan da shi tun kafin mu zo."
Gwaggo ta sake ce wa "ikon Allah sai kallo. Abin ne yake dafa ni. Wato kinsan komai ke, shi yasa ta ce idan kin zo, na ji a bakin ki".
Babah ta mik'e ta ce "Sai ki yi ke kad'ai ina dalilin bin wannan diddigine haka? Mace da mijinta".
Da mamaki Gwaggo ta sake ce wa "To wai a kurkun, a ina suke haduwa ni Ma'u!
Babah ta fice ta ce "A a nima ban sani ba. Sai ki tambayi mijin nata tunda ita kin saka duk ta sururuce da kunya. Domin ke sai akan girman ki zaki baci da magana, sai ki je ki gano shi, ki tambaye shi yadda aka haihu a ragaya ".
Ta fice da sauri.
A haka muka sake shafe sati biyu. Yaya Aliyu ya zo ya kwashi yara ya ce tunda ba tafiya zamu yi ba, to ba zasu yi asarar karatunsu ba.
Na kuma gane Babah tana son ta zauna da Dada a dalilin ta damu da lalurar da ta sami autarta.
Sannu a hankali na fara warware wa. Matan gidanmu sai nan ake yi da ni. Mama da kanta sai ta tambayi abin da zan ci. Na tabbatar ta dad'e da ajiye makamanta. Amma yadda nake tiritiri da rik'e musu gidan ya kara mini kima k'warai da gaske.
Ahalin gidanne dai idan muka had'u ko idan na fita da nufin zagaye ake bina da kallon k'urillah da tuhuma.
Yara basa iya ce mini komai ba. Amma da kunnena na jiyo matansu Baban Kasuwa da na Tsakiya suna gulmar cikin jikina suna fad'in "iyalin Tijjani bata yi shashanci ba, ai a yi mamaki, irin fasadin da ya yi a doron kasa, sai kurum."
Na yi kamar ban ji ba. Domin a yanzu da nake fama da rashin Baban 2 mene ne bazan yi hak'uri a kansa ba?
Baban Tsakiya kuwa fama yake da ciwon hawan jini. A dalilin mafi yawan y'aya'nsa sun kangare. Dama dai Jabir ne mai dama, to a lokacin da yake da dama bai bari ya taimaki kowa ba. Domin ko ni a farkon farkon rufe Baban 2 idan ya tura mini kudi sai ya ce "Ba sai an ji ba".
Dan haka mafi yawa yanzu ba'a taimakonsa ko tausayinsa domin a lokacin da ya samu ba wanda ya more shi. Sai aka yi mutuwar kasko.
Shi kuwa Baban Kasuwa manyan y'aya'nsa guda biyu na farkon mata ne. Amina sai Maijidda. Kuma dukkansu a yanzu kowa fama take a gidanta bare ta taimake shi. Gara ma Maijidda yanzu ne babu ta same su. Aminu na ukun sa'an Anas ne, yanzu suke tasowa.
Gabadaya rayuwa ta yi juyin waina. Baban Marina da ake ganin babunsa a yanzu yafi su rufin asiri. Abincinmu yafi na kofofinsu. Ba kuma kudi ya yi ba. A a Y'aya' ne suka taso, muka hutar da shi fafutukar rayuwa.
Har yau kuma idan Baban Marina ya samu damar da zai yi mana wasiyya sai ya ce "mu zama masu afuwa da manta sharri, mu kuma rik'e alheri komin kankatarsa. Ko waya ka yi masa sai ya ce "Ba jarumta ba ne fad'a a tsakanin yan'uwan juna. Ba kuma tsoro ba ne idan kai mai gaskiya ka janye ka barwa wanda ya karkace, masalaha ne da takaita rikici.
Har ilah yau ba imani ba ne ka yi fatan ganin wani ya shiga mummunan yanayi duk yadda ya zalunce kuwa. Mafi yawan sakayya yanzu tun a duniya Ubangiji yake fara yinta. Matukar kana da gaskiya baka nufi kowa da sharri ba, to sai ka ga alheri komin dade wa.
Iri iren wadannan nasihohin ne suka dagargaza mini tunanim son ganin su Baban Tsakiya a halin tagayyara, na huce da su nake nema masu gafarar Ubangiji. Na gamsu idan suna cikin tozarci dole dai jininmu ne kuma gidanmu daya.
Nazira akai akai take ziyarta ta. Mu yi hira, ta daho mini abinci, ko ba zata zo ba sai ta aiko mini duk da gidan namu da abinci amma kullum sai ta ciko cooler ta kawo mini.
Muna hira na ce "Adda Nazi wai ya ya Saiwowin dahuwar tattabaru din nan kuwa?
Ni dai na ga kyaunsu. Ya sabunta ni a wajen Baban 2 sosai".
Ta ce "hm kayya bari ke dai suna da kyau. Amma maigidan ne kuzarinsa ba mai yawa ba ne. Na yi dariya na ce ke kuma babu s'auki."
Ta ce ba haka ba ne".
Na ce To zan karbo miki moringa tea ya dinga sha a shayi ko a lemo, zai sha?"
Ta ce "zai sha ba shi da matsa akan hakan. Amma dai Yabi kada ki saka na ba shi abin da zai cutu ko ya hallaka ni"
Ta ba ni dariya ainun na ce "Kai Adda Nazi. Garin zogale ne fa sai sai saiwowi marasa illah. Yana da d'an kudi amma yana da kyau ainun".
Ta ce shima a kano ne?"
Na ce "eh a wajen mai saiwowin ne duka daga Chad take kawosu. *08032773332*.
Ta ce "Tom shi ke nan. Na gode."
Sai da muka yi wata biyu. Muka koma BAUCHI. A lokacin cikin ya shiga wata na hudu.
Tun ina jin kunyar Babah har na hak'ura na ware a dalilin itama mita take yi. Wai a sadda muka yi abin da muka yi, ban yi zaton zan ji kunya ba, sai yanzu?
Ranar da muka je Tijjani ya fahimci ciki ne da ni har ya yi k'wari ya kasa magana ya tafi ya yi sujjud shukur. Babah ta koma gefe ta yi kamar bata wajen.
Ya dinga murna da yi mini addu'a. Gabadaya na danyace. Na ciko sosai. Duk wata ko ban je gidan gwamnati ba, sai Hajiya ta kawo mini kudin envelope tare da nanata basu manta maganar maigidan ba. Karamci kad'an na yiwa Hajiya, sai ya janyo mini sanadin alheri mai yawa. Na kuma fahimci tausayina take ji da gaske. A haduwarmu Allah kad'ai yasan adadin alherin da nake samu. Su Hamim ta mayar da su tamkar jikokinta. Suna bata sha'awa. Kullum a cikin kawo musu suturu masu kyau take, ga kayan wasa kala kala.
A haka rayuwar ta cigaba da garawa har na shiga watan haihuwa. A lokacin kamfani ya sake biyan kudin filin Tijjani. Na yi siyyya mai rai da lafiya amma na kudire ba zan yi Taron suna ba. Ya fad'awa Aliyu yadda za'a yi masa da kudinsa. Yaya Aliyu Kuma Bai fad'a mini yadda za'a ba, Nima ban tambaye shi ba. Bayan ya ce a ware wanda za'a yiwa Baban Marina da mahaifiyarsa hidima. Da ragowar yan'uwan. Ya ce Aliyu ya dauko 250 ya yi wani abin.
Cikin ikon Allah watan Muharram da kwana bakwai na haifo yarinya sankaceciya. Jawur da ita tamkar tsada. Wanda ya yi daidai da 1 ga watan goma miladiyya.
Babah ce ta karbi haihuwar domin cikin dare ciwon ya tashi. Kafin Aliyu ya zo da mota tuni na haihu ta gyara wajen. Kawai mun je asibitin ne an duba ni. A daren muka dawo gida.
Babah ta zuba yarinya ido ta ce "Ke kuma Aliyu kika debo?"
Na kalle ta. Domin ni fa bana gane kamar yara. Aliyu ba sosai suke kama da Bulkachuwa ba, sai dai suna yanayi saboda jini d'aya. Ihisan ce suke kama da Tijjani kwabo da kwabo shi yasa su Hanif suke matukar kama da ita. Dan idan muka hadu kowa ita yake zaton ta haife su ba ni ba.
Washagari Babah ta d'auki jinjira ta kai wa Tijjani da kanta. Aliyu ne ya kaisu. Tare da su Hamin da suke murnar sun yi KANWA tamkar su mayar da ita ciki.
Ya karbe ta cikin kunyar uwarsu. Ya zuba mata ido yana jin sonta da tausayinta na tsaga shi. Zata girma babu soyayyar uba alhalin ba mutuwa ya yi ba. Ya tsinci kansa da ce wa "Allah ka mini sakayya da duk wanda ya k'ulla mini sharrin da aka nesanta ni da iyalina, na kuma rasa y'ancina.
Aliyu ya juya domin idonsa ya ciko da k'walla. Babah kuwa tuni take sharbe.
Domin ya bata tausayi k'warai da gaske.
Murya na rawa ta ce "yi mata addu'a ka kuma yi mata huduba.
Ya shiga jero mata addu'oin tsari da albarkar rayuwa. Ya Kalli Aliyu ya ce dauke ta ka yi mata huduba da duk sunan da kake so."
Ya saka hannu biyu ya dauke ta ya yi mata kalmar shahada ya lakaba mata Hauwa.
Ya mikawa Babah ita yana fad'in sunan ki na zaba mata ".
Da sauri ta ce "Ba kuwa sunana zata ci ba. A saka mata Asama'u. Don Yabi tasan mun san alheri, muna kuma gode mata.".
Aliyu ya ce "Hakane Babah. Ya sake sabuwar huduba ya rad'a mata Asama'u.
Maimakon ya bawa Gwaggo sai ta mika mawa Tijjani domin ta ga bai gaji da kallon ta ba.
Ya ce "Aliyu rago nawa zaka yanka mata? Domin gabadaya kai ta kwaso, kamar da ta yi da kai ta shahara."
Ya ce "Haka na ga ni, Babah ma ta ce ni ta kwaso. Biyu za'a yanks mata. Ana yaye ta kuwa zan dauke ta".
Tijjani ya ce "Yabi kuka zata yi Aliyu. Twins ne naka. Kai na haifawa su, ga shi nan kana ta tiri tiri da su babu gajiyawa. Ko yanzu idan kana so ka wuce da su, amma wannan barta, ita ce zata debe wa Yabi kewar zaman jirana".
Babah ta ce "Uhum! Nan da nan ya kame bakinsa domin ya shafa'a da ita."
Sun jima kafin su tafi su bar shi cikin alhini. Yarinyar ta shiga ransa fiye da twins.
Suna isa suka tarar da mutanan Toro. Gabadaya ahalin Baban Marina ne sai Dada.
Da murna ta fad'i sunan jaririyaya. Kowa ya yi murna take Yaya Salamatu ta ce sai a kirata Husna. Na ce "To". Farincikin sunan Gwaggo ya zangwanyar da alhinin da nake ciki.
**
Na Dade da gane Dada ba k'aramin son Bulkachuwa take yi ba. Domin sai yanzu na fahimci kafatalin jikokinta tafi sonsa. Tunda bata iya boye son tagwaye. Ni kaina na sake samun daraja ne a wajen ta saboda Tijjani. Kullum ta gan ni sai ta yi kuka. Y'aya'nsa kuwa komai hannunta ya taba sai ta basu. Tana yi tana fad'in "Allah ka yiwa mai babban suna abin da zato bai yi zatonsa ba. Wanda duk ya k'ulla masa wannan salalar tsiyar Allahu ka dabaibaye duniyarsa da firgici da tashin hankali."
Kaitsaye Babah ta bawa Dada jinjira. Ta zuba mata ido tana kuka ta ce "Mai sunan manya ya haifi Aliyu. Sai na tuna ranar da aka haife shi. Haka yake sak."
Aliyu da yake tsaye a bakin k'ofar ya ce "Dada ikon Allah! A gaban y'aya'na da kannena kike maganar haihuwa ta?"
Ta ce "To uwaka ma bana yi zancen haihuwar ta bare kai".
Ya ce "Ai shike nan, dama ni ba wai kina sona ba ne . Yaya Tijjani ne na ki. Kin ga da kin bini a hankali gobe dia na zo na kai ki wajensa."
Ta marairaice ta ce "A sannu ma zan bika Ali gadanga angon kilima".
Ya ce "Assha kin batawa amarya ta sunanta. Amma dai zan zo, ya hau gaishe ta. Sannan suka gaisa da su Mama.
Ya ce "Ummi ni da ke waye babba ne?"
Ta ce "Mama fad'a masa".
Mama ta ce "Ita ce babba ranar sunanta aka haife ka".
Ta nuna shi da yatsa ta ce "To ka ji Wallahi ka kiyaye ni"
Ya rik'e kiirji ya ce "oh saboda Ikilima zaki dinga zare mini ido? Sannu gyambo uwar son girma! Haka kike yiwa Yaya Tijjani?"
Ta ce "Ai shi yayana ne kuma duk da hakan girmama ni yake kamar me saboda ya yarda surkuta gaskiya ne. Sai kawai kukan da take danne wa tunda ta ga jaririyaya ya kwace mata duk da dai wasa suke yi.
Kowa ya yi k'asa da kansa ana taya ta kukan da take yi. Domin tun fil-azal idan akwai amintattun da ba cikinsu daya ba a gidan Marina to Yaya Ummi da Bulkachuwa ne. Akwai shakuwa da kauna a tsakaninsu mai yawa.
A sanyaye ya ce "Ki yi hak'uri ummilolo! Ai yana fad'in hakan sai kuwa ta sake rushe wa da kuka na sosai. Don kuwa Bulkachuwa kad'ai yake ce mata ummilolo.
Daada ma ta bare baki ta shiga taya ta suka dinga yin sa kamar me. Da k'yar suka yi shiru.
Aliyu ya tafi jiki a sanyaye. Yana fad'in ba zan sake zolayar ki ba Ummi har sai d'an-uwan ki ya fito.
Har dare babu nishadi a tare da mu.
99&100.
Sai washagari aka hak'ura da juyayyin rashin Bulkachuwa. Dada tun asuba ta yi wankan tafiya gano shi. Tana yi tana fad'in "Allah a saukakawa wannan yaro. A jibanci lamarinsa.
Ya ci arzikin ma'aiki. Ya ci albarkacim Shehu mai karama".
Da wuri ya kawo Iklima. Ya ce "Dada zan dawo idan an yi azahr zan kai ki gano mai sunan manya."
Ta ce "Ina ce yanzu zamu tafi Ali?"
Ya ce "Ai yanzu baza su bari ma a gan shi ba."
Ta kyabe baki ta ce "Ina ce Ammar yana wajen? Ni da nake da kafa har a mini iyaka?"
Ya ce "Yi hak'uri, ki bari na dawo, tiyatar haihuwa zan yiwa wata mata karfe tara zan shiga."
Ta rausayar da kai ta ce "Shike nan sai ka dawo, ya zan yi?"
Da ga dawo kuwa gabadaya suka rankaya ganin Tijjani. Ni da Babah kawai aka bari a gida. Da ga can zasu biya gidan Iklima su bar ta a can.
Dada ta kalle shi ta ce "Mai sunan manya kana wuridin *RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN kuwa?"
Ya ce "Ina yi sosai, ina kuma ganin tasirin ta Dada. Komai ya saukaka mini, na samu k'arfin zuciya da tawakkali, iyalina kuma suna cikin rufin asiri mai yawa ".
Ta ce "Hakane, Hakane! Cikin tausayawa.
Sun jima sosai suna shirin tafiya ta cewa su Yaya Ummi su yi gaba tana zuwa.
Yaya Ummi ta kalle shi da idonta da suka yi ja. Da rawar murya ta ce "Yaya Bulkachuwa sai mun sake zuwa".
Ya yi mata murmushi ya ce "Ummilolona kullum sai kin yi kuka? Kamata ya yi ki gode Allah ina rayuwa. Ban rasa komai ba sai y'ancina. Wanda duk ya zo kurku bisa zalunci sai ya samu daukaka, so ku tsananta yi mini addu'a ba kuka ba".
Ta share hawaye ta ce "Allah ya nuna mini ranar da zaka fito Yaya Bulkachuwa sai na yi azumi uku da ikon Allah".
Haka kawai ya ji ta bashi tausayi. Tun tana k'arama ta damu da shi ainun. Shima kuwa idan aka dauke Ihisan da su Aliyu ba shi da wata yar'uwar da ta wuce ta. Ya tabbatar ko bai auri Yabi ba, amincinsa da ita mai yawa ne. Sai aurensa da Yabi ya sake girmama amincin nasu domin ya sani, tana son Yabi fiye da komai. Shiyasa ta sake kaunarsa, ta kuma bada gudunmawar shawo masa kan Yabi matuka gaya.
Suka tafi, su mama duk jiki ya mutu, tausayi ya ratsa jikin kowa.
Sai da suka yi nisa Dada ta sassauta murya ta ce "Mai sunan manya wai anan din akwai d'akin sirri ne, ko kuwa a ina kuke haduwa da Yabi?"
Kunya ta kama shi. Ya kasa ce mata komai. Ta ce "A a ba kunya zaka ji ba. Kawai ka fad'a mini domin idan cikin jejin can kuke shiga a samowa jinjirar taimako domin idan aka samu ciki da ranar Allah, kuma a fili irin haka aka yi tarayyar da ciki ya shiga to fa wannan yaron ko yarinyar rashin kunyar da zasu yi sai ya gigita kowa".
Dariya ta k'wace masa. Ya yi kad'an ya gintse tare da ce wa "Ki yiwa Allah ki bar maganar nan haka. Ki nemo mata taimakon ki kuma tsananta yi mata addu'oi kawai".
Ta saki ajiyar zuciya ta ce"Mai sunan manya abin ne yake ta bani mamaki to ta ina kuke kebe wa ne? Ga yarinya nan ta kwaso Aliyu amma cikin ikon Ubangiji doguwa ce sambal. Dazu ana mata wanka da na zuba mata ido gabobinta irin naka ne sak, haka gashin kanta. Oh ni Binta. Kullum ina kuka da zullimin rashin ka ashe kai baka fasa komai ba?"
Ya murmusa ya ce "Kina sauke mini dala'ilalul khairati kuwa?"
Da hanzari ta ce "Duk satin duniya kuwa. Ko wacce juma'a nake sauke wa. Kuma hadiyya ce a kanka. Mai sunan manya na ga gurbinka! Dakina a bushe, babu kayan shayi irin naka. Babu sabulai da turaruka irin naka. Ta hau kuka sosai. Jikinsa ya yi sanyi. Ya ce su Baban Kasuwa basa siya miki ne?"
Ta ce "suna siya amma har sai sun k'are, kai kuwa kafin su k'are ka kawo wasu. Sabulai da turare masu kyau ba masu s'aukin kudi ba. Amma yanzu fa?"
Ya ce "Ammar da Jabir basa yi miki ne Dada?"
Ta kyabe baki ta ce "Jabiru kam ai yanzu fama yake yi da kansa. Har ya gama samun damarsa kuwa ban wani more shi ba. Kasan sun k'ullace ni akan ku. Wai nafi sonku. Iyayensa kawai yake yiwa. To yanzu an yi mutuwar kasko, kowa ma ya rasa.
Shi kuwa Ammar yana yi mini bazan masa k'aharu ba".
Amma sai ta waiwaya ta sassauta murya ta ce "Da uwarsa muke raba daidai. Idan ba'a hannuna ya bani kudi ba kuwa, basa zuwa mini".
Ya yi shiru, tausayinta ya kama shi ainun. Abin da ya fahimta Baban Marina da mahaifiyarsa sun fi dukkan y'aya'nta yi mata biyayya da kyautatawa a gareta. Sune kuma wadanda ta rayu tana nuna musu rashin soyayya. Komai sune a baya. Amma kuma shi da kansa ya tabbatar Dada tafi sonsa akan kowa cikin jikokinta. Domin Ammar bai samu sukunin yi mata raddi da fito na fito da ita ba. Da ace shine yake da nutsuwarsa da bai san yadda zata ririta shi ba. Ya tuna sadda zai sadada ya kwashe mata yan kobbonta da kayan amafaninta ya siyar. Bata yi masa fada a gaban jama'a. Bari take sai dare ya raba kowa ya kwanta sannan ta shiga dakinsa su yi sababi, tana yi kuma tana ce wa murya kasa k'asa mai sunan manya kada a gane halin da muke ciki.
Shi kuwa sai ya bude muryarsa ya ce "Aji mana tunda sharri zaki k'ala mini saboda kin washe ni. Duk yawan jama'ar gidan nan m, babu mai yi miki sata sai Tijjani!
Nan da nan zata bar maganar ta ce "Alfarmar shehu zaka bari. Darajar sunan da ka ambata na yafe maka, Allah ya shirya mini kai, ya tsare ka daga hau da sharrin zamani".
Ya nisa ya sake murmusawa ya ce "Ki yi hakuri zan fad'awa Aliyu ya dinga yi miki. Ki kuma cigaba da yi mini addu'a Dada. Sannan ki yafe mini ta'adin da na yi miki a shekarun baya.
Da azama ta ce "Wallahi na manta komai. Kuma menene baka yi mini ba da ka samu dama? Aliyu kuwa ai shima a k'ullace yake da ni. Ya sha fad'a mini ina nunawa uwarku butanci. Wanda sharri ne kawai, to wa zai haifi d'a ya ce baya sonsa saboda Allah? Jiya kuwa a gidanka ya ce "Yasan nafi sonka a kansa. Sannan kasan matarsa d'iyar Alhaji ce, su kuwa gabadayansu sun kwashe kayansu a gaban ma'aiki akan sha'anina. Yabi ce kawai take mini sassauci, itama dan tasan ni da kai ba dai mutum ba. Duk tsiyatakunta, duk yadda ka jarabtu a kanta, ba zaka k'i jin kaina ba, ba zaka k'i ni ba!
Ta fad'a cikin sigar tausayi.
Ya saki gauron numfashi ya ce "Ki yi hakuri Dada. Za'a gyara. Yanzu ki daina damuwa. Sannan kada ki koma Toro. Ki zauna anan BAUCHI ki dan huta. Idan jama'a sun tafi zansa a kawo miki kaji Babah ta gyara miki ki dinga cin abin ki. Idan sun kusa karewa za'a sake soya miki wasu. Sannan yanzu a hanya za'a siya miki kayan shayin ki, ki ajiye a wajen ki. Naki ne ke kad'ai kada Yabi ta yi miki k'auron nata".
Ta yi maza ta ce "A a itama tana yi mini alheri, sannan tunda aka sakaye ka soyayya ta sake kulluwa a tsakaninmu, kullum muka hadu sai mun yi kuka. Kasan yanzu ta yi hankali. Gara na fad'i gaskiya ko ba haka ba".
Ya yi dariya ya ce "Ho Dada ta Yabi. Tsoron ta kike ji ne yanzu?"
Ta rausayar da kai ta ce "Uum kaidin mata mai yawa ne. Yanzun nan idan ta murde kai ma sai ka juya mini baya a kanta. Barta dai tunda ta nutsu, kuma tana mini ya kamata. A lallaba a tafi a haka, domin na riga na yi imani da kiararin da na ji ubanta yana yi mata. Na ce wa ita kad'ai gayya ce a gidan Marina. Ko kasan kaf zuri'ata babu mai ruwan kudi a hannunsa irin Yabi? Yadda na gasgata karamar Shehu haka na gasgata kudinta na halali ne. Ka ga yadda ta mayar da dakin uwarta ne? To ragowar matan uban ma duk ta yiwa dakunansu kwaskwarima lokacin auren Ubaida. Idan ka ga bajintar da ta yi a auren kuwa sai ka rik'e baki. Matar gwamna har tawaga ta turo su wakilce ta bikin.
Kofarsu tafi ko ina haske da kyawu yanzu, kuma duk ita ce. Ko kai ma irin yadda kake yiwa ubanta ai saboda ita ne. Yabi, Yabi duniya ce? K'aramar halitta sai babban al'amari".
Ya kwashe da dariya ainun.
Ta ce "Allah kuwa. Mata ai yanzu sun ri'ka. Idan basa yin ka to mijinsu ma ba zai maka kallon rahama ba".
Ya sake yin dariya ya ce "Duk zan fad'a mata ne".
Ta kyabe baki tare da ce wa "To hudawa cikinka wuka da kanka.
Ta jima kafin ta dingisa ta tarar da su a mota suka tafi.
**
*Watanni uku a gaba*
Zuwa lokacin Husna ta yi gubibi da ita. Shayarwa na matukar ciko da Yabi . Saboda kirjinta suna cika, ita kam tana cikin mata kad'an da goyo yake karbarsu.
Bata da matsalar komai sai ta rashin miji.
Har zuwa lokacin Dada na tare da su.
Ba zato ba tsammani Aliyu ya zo ya kwashe su aka yi musu passport.
Sai da passport ya fito yake fad'a musu kudin hayar filling Tijjani ne. Shine Kuma ya ce Yabi da Dada su tafi su yi Umrah su yi masa addu'a."
Ai kafin ya rufe baki Dada ta zabge da kuka tare da ce wa "Ashe zan koma gabar ni Binta? Hauwa kin iya haihuwa! Shehu ya haifu. Allah ka yiwa Shehu abin da mai zato bai yi zatonsa ba ". Sai kuma ta rushe da kuka wurjajan.
Ya ce "Ganin hakan ya sanya na biyawa tawa uwar sai ku tafi tare"
Nan ma Dada ce ta yi fit ta ce "Wayyo Ali Allah ya yi albarka, yasa kai ma ayi maka tagwaye."
Ya ce "Ai tuni ya bani Dada. Wadannan da suke gittawa ta gabanki ba nawa ba ne? Ko kuwa dan a gidan Marina kowa d'an da ya haifa ne nasa shiyasa kike ganin sai na haifi wasu tagwayen?"
Da yake babu wata shak'uwa a tsakaninsu, asalima tsoro tsoronsa take ji. A sanyaye ta ce "A a kuskure ne, da mantuwa Ali. Yanzu dai ba zamu yi fad'a bayan ka zo mana da babban albishirin da babu irinsa. Allah ya saka da alheri, ya yi muku albarka gabad'aya".
Ya ce "Ameen".
Babah itama ta yi masa godiya da fatan alheri da bunk'asar arziki. Yabi tana bude baki ta ce "Na dad'e ina son na tura Baban Marina Umrah. Na dad'e ina fatan na yi masa ba zata. Ta ce zan tattara abin da nake da shi a yi tafiyar nan da shi".
Idon ta ya ciko da k'walla tana ayyana yadda Baban 2 yake fatan ya kai ta Makkah. Ashe abin na ransa, ashe itace zata riga shi zuwa Sau'udiyya?
Hawaye ya tsinke mata. Babah ma ta shiga taya ta. Aliyu ya ce "Maimakon ku yi masa addu'a sai kuma ku yi masa tukuicin kuka?".
Cikin kuka sosai Dada ta ce "Kai ku yi kukanku da kyau kun ji ai! Ali ai dole mu yi kuka. Yau sama da shekara Shehu na garkame a haka aka samu rabon Asma'u. Kai rabon haihuwa zazzafa ne".
Aliyu ya ce "Kai Dada da fitina kike. Me ya kawo wannan maganar a yanzu kuma? Sannan kuma Yaya Tijjani ne ya koma shehun ko kuwa?"
Ta ce "Eh shi fa. Tunda ga y'aya'nsa na girma ai gara na tsayar masa da suna d'aya. To na zabi Alhaji Shehu kawai domin Sha Allahu wataran zai zama Alhaji da ikon Ubangiji kuwa".
Ya gintse dariyasa ya ce "Ni na tafi, tunda Yabi ta had'a ni da aikin dauko Baban Marina gobe".
Sai lokacin na ce "Tare zamu je, zan duba yaron Anzira da ya yi targade."
Ya ce "Tom in sha Allah".
Babah ta ce "To kuma ya zaka yi da wannan kilifar ne tunda bata isa yaye ba. Watanta uku kacal" Ya ce da ita zaku tafi mana".
Dada ta ce "Allahu akabar! Yabi ta haifo Yabi."
Ya kwashe da dariya ya ce "A a Dada. Ai Yabi wadda aka haifa a hanyar sau'udiyya dan aikin Hajj ne ko aka je da cikinta. Ita kuwa wannan ai ana riga an haife ta, sannan Umrah zaku ce ba tawwali ba".
Ta ce Hakane, sai ace mata Ummara Husna. Domin na tabbatar sai ta yi jidalin Asiya idan ba'a ce mata Ummarah ba. Oh ashe dai da rabon burin Yabi na zama Hajiya a kusa zai tabbata. Nasan Shehu ya biya mini ne dan na kula da ita, na jagorance ta a wajen sa'ayi da safa da Marwa".
Ta bawa Aliyu dariya ainun ya ce "A Ina zaki jagorance ta din? Ai ko ke yanzu kika je d'aya zaku zama, ko wanda ya je bara idan ya koma bana sai ya ga abubuwan da bai san da su ba. Saboda yadda gwamnatin Sau'udiyya ta mayar da hankalinta akan Makkah da Madina gabad'aya. Bare ke mai shekaru ashirin da biyar da zuwa, ina ce da kika je ma ba'a haifi Anas ba?"
Ta rausayar da kai ta ce"Ko Yabi yayarsa ma ba'a haife ta ba. Kasan ana daf da aihuwatata Alhaji ya hadu da sharrin masu zamba cikin aminci, haihuwarta ta zo cikin wani irin yanayi mai tsananin gaske ".
Na hauro na ce "Dada kina son fad'an wannan labarin. Nasan idan tafiya ta mika zaki k'arasa abin da kuke fad'a cewar ni na kore masa arzikinsa".
Ta kama baki da azama ta ce "Yabi ki yiwa darajar Alhaji da Asma'u kada ki birkice mini. Ko mahaukaci ya ji labarin ki da irin bajintar da kike yiwa uwa da uba ai yasan ke din arzika ce ba wai Yabi ba. Yo duk gidan Marina akwai wanda bai ci arzikinki ba ne? Babu shi Wallahi. Allahu ya huci zuciyar ki. Bazan sake ba. Kai Ali tashi ka yi tafiyar ka, nima alwallah zan yi na yi munajiti da Ubangiji. Kai ma ka yawaita zikirrn ambaton Ubangiji ko na istigifari, ko da kuwa tukin mota kake yi ".
Ya yi dariya ya ce "Wayo da Yaya Tijjani da Nasiba da Yabi sune maganin Dada."
Na dauke kai na ce "Kada ka sani Yaya Aliyu! Baban 2 da Nasiba dai. Tun fil-azal sune zasu yi sa insa da ita ta yi mukus. Amma ni kam menene bata yi mini ba?"
Ta yi shiru ya kasa ce wa komai. Sai Babah ce ta fanshe ta da ce wa "To marasa kunya ta yi din. Suma wadancan din waye su da zasu yi maganin uwarmu? Ai tunda aka yi sa'a tana tsananta ibada komai zai daidaita mata."
Da haka aka bar maganar domin jikin Dada ya yi sanyi.
Da kaina na je Toro na sanar da Baban Marina cewar Tijjani ya biya mana Umrah ni da Dada Aliyu kuwa ya biyawa Babah. Ni kuma na biya masa.
Ya yi k'asa kansa tsawon lokaci bai yi ko da motsi ba bare ya yi magana. Ya jima kafin ya d'ago. Na ga hawaye jagejage a fuskar sa.
Nima nawa hawayen ya kwace mini amma ni kam na farincikin yadda Ubangiji ya yiwa fafutukar sana'ata albarka nake yi. Domin bani da burin da ya wuce na sanya Baban Marina farinciki tun ina mitsitsiya ta. Gorin da ake mini, haihuwa ta ce ta tsiyata shi. Da kuma bak'in cikin yadda ya zama koma baya a cikin gidanmu na matuka mintsinin zuciyata.
Da k'yar ya yi jarumtar ce wa "Na sha fad'a miki ke kad'ai gayya ce Asiya. Na fad'a miki zaki yi albarka. Na dad'e ina fad'a miki akwai lokacin da zai zo da kowa sai ya so ki har makiyan na ki. Ga shi na fara ganin sakamakon alherin da Ubangiji zai yiwa hak'uri da juriyar da kika yi a rayuwar ki. Allah ya yi miki albarka. Daga nan har kasa ta rufe mini ido na yafe miki, kina cikin farar addu'a ta. Allah yasa y'aya'n ki su yi fiye da ke. Allah ya miki tukuici da alheri. Kin yi hak'urin aure, kin yi juriya. Da ikon Allah ba zaki sake fuskantar tsanani a gaba ba."
Ina kuka na ce "Allah ya amsa Babanmu! Na gode Allah ya k'ara lafiya.
Ya ce "Ku tafi da gyatumar ki Yabi. Kin ga dukkanku mata ne. Da ikon Allah zaki kai ni."
Na girgiza kai na ce "Zata je Baba! Amma wannan kudin na tara kaso uku cikin hudu da sana'ar da na rayu ina yin ta. Kai nake son ka je, dan kanji dad'i ka kuma godewa Ubangiji da ya jarrabe ka da fitinar yan'uwa. Sai kuma ya baka y'aya'n da zasu sadaukar da komai dan ka yi murmushi. Ka je ka yi mana addu'a. Ka tayamu addu'ar Ubangiji ya kubuto mana da Tijjani ".
Sai kuka na sosai ya k'wace mini. Abin mamaki sai shima ya taya ni kukan muka dinga yinsa a hankali.
Da yake a dakin Gwaggo yake. Ta shigo da Husna a hannunta da ta fara kukan neman nono. Ta tsaya cak bata miko mini ita ba. Ta sassauta murya ta ce "Ayyah Yabi baki ga kullum girma sake kama shi yake ba? Me yasa kike kasa hak'uri a idan kina gabansa? Kinsan yadda kukan ki yake rikita shi kuwa? Kalli irin kukan da yake yi mana. Me yasa kike rasa dukkan jarumtar ki a gabansa?"
Na kasa magana. Sai shine ya ce "Ni ne nake rasa dukkan jarumtata akan lamarin Yabi. Tana matukar bani tausayi, kuma dama ita ce raunina a cikin dukkan y'aya'na. Shiyasa Ubangiji yake ta jarabtata akan sha'anin ta. Tafi kowa shiga garari da kalubalen rayuwa. Asma'u! Ki ji tausayin ta. Ki sake ninka addu'ar da kike yi mata. Zauna a zaune ki ji al'amarin da ta zo da shi."
Yana hawaye ya fad'a mata zuwn nawa albishir na yi masa zai tafi gabas. Yana rufe baki itama ta fara hawaye tana fad'in Allah mun gode. Ina taya Yabi godiyar yadda ka cika mata burin ta, na mayar da Alhaji dakin ka. Allah ka k'ara yaukaka mata arziki, ka shirya mata zuria. Ka mata tsari da dukkan abin da zai cutar da ita ko iyalinta".
Ya k'ira Mama da Inna ya fad'a musu alherin da ya same su ya rufe da ce wa kada su fad'awa kowa sai abu ya kankama. Domin tafiya gabar kiran Allah ne.
A gurgurje na je gidan Nazira na dubo yaronmu.
Da yamma muka juyo da Yaya Aliyu akan gobe Baban zai zo BAUCHI don ayi masa passport.
Ba a fito da maganar tafiyarmu ba sai da komai ya kammala ya rage saura kwanaki hudu.
Baban Marina da kansa ya fad'awa y'an uwansa cewar zasu tafi Saudiya. Da Yabi da diyarta da Dada Tijjani ya biya musu. Aliyu ya biyawa Hauwa. Shi kuwa Yabi ce ta biya masa. Suka ka'du k'warai. Amma da yake dangantarsu ta yi tsami ainun kowa ya hadiye a ransa tunda yanzu so suke ace kowa yafi kusa da Baban Marina a tsakaninsu. Sannan basu gamsu Yabi ce ta biya ba. Duk da dai sun yi matukar sikewa da lamarinta tun auren Iklima. Zuwan tawagar matar gwamna Toro gidan Marina ba k'aramin cece kuce da girmama lamarin Yabi ya janyo ba.
Ranar talata da asuba muka nufi Kano tunda an ce shabiyun rana zamu tashi.
Karfe tara a airport din ta yi mana. Aliyu bai tafi ba sai da ya ga tashinmu. Sannan ya juya da twins da Ikilima da suka yo mana rakiya. Hamim sai kukan sharbe yake yi. Hanif sai hak'uri yake ba shi yana ce wa "Mun girma fa Hamim. Ammi ba dadewa zasu yi ba. Ba ta ce addu'a zasu je su yiwa Baban 2 ba? Husna zata raina ka fa". Suka bawa Aliyu tausayi. Haka kawai yaran suke ba shi tausayi ainun.
Bai bar Kano ba sai da ya siya musu kayayyakin wasa da na ciye ciye dan su warware gabadaya.
Kai tsaye a Madina muka sauka. Mun gaji likis. Dole muka kwanta. Dada sai addu'a take yi tana fad'in "Allah k'amshi ya cika hancina, haske ya cika idona, k'arfi ya yiwa gangar jikina k'awanya, farinciki da imani sun cika zuciyata. Allah ka karawa Annabi daraja. Allah ka karbi addu'ar da zamu yi, ka bamu k'arfin da zamu yi ibada ta gaskiya."
Sai ta zauna. Sai ta zabura ta je jikin windo tana leken asumayar masallaci ma'aiki. Tana kuka tana fad'in "Rabbani yadda ka sake yi mini gatan ganin koriyar gubba ta d'an Amina mai wuyar ga ni. Allah kasa zan gan shi da idona. Allah ka bani ikon rokon gafararka idan na shiga rauda. Allah ka shirya mini zuria, ka jefa soyayyya a tsakanin ahalina. Alla na yi tuba. Allah mai babban suna aiko ni ya yi takanas, Ubangiji a karba a sassauta a kubuto da shi albarkacin masoyinka Baban Nana".
Duk juyin da zan yi zan ga idonta biyu. Babah kuwa barci ta yi sosai domin bata runtsa ba a jirgi, ita take ta fama da Husna.
Daf da asuba muka tashi, muka yi alwallah muka nufi masallaci. A harabar hotel din muka had'u da Baban Marina shima ya fito zai tafi. Na kalle shi cikin sabuwar jallabiyar da na siya masa guda uku a Kano. Ya yi fes da shi. Garin Madina rahama ne.
Gabadaya zukatanmu cike suke da shauki da rauni. Duk juyin da muka yi da Dada ta saka silifas din ta. Ce wa ta yi "Wane mutum ta taka k'asar Madina da takalmi? Mu dai da muka ga zamu taka ba zata ce komai ba. Allah ya yafe mu kawai"
Kan dole muka k'yale ta. Domin har muka yi kwanaki biyar a a Madina bata yarda ta saka ba. Duk ranar da aka yi ranar juma'a ma haka ta tako. Sai da muka shiga motar tafiya Makkah sannan ta saka takalmi, tana hawaye tana fad'in "Allah ina son na sake dawowa. Idna ban samu damar ba, na yi godiya. Allah karbi addu'ar da muka yi."
A Makkah kuwa har tausayi suke bani tunda muka je dukkanmu a masallaci muke kwana. Mu yi sallah, mu yi dawafi. Duk shekarun Dada bata zama. Ko dan yar firit ce irina? Ban sake gasgata komai na Dada na kwaso a halitta ba. Sai a tafiyar nan da muka yi. Kamar da muke yi ta baci. Na tsinci kaina da addu'ar kada Allah yasa na yi halinta idan shekarun girma suka cimma ni. Tunda ta sha fad'ar hatta fad'an da na yi ina karama itama haka ta yi a lokacin kuruciyarta.
Baban Marina kullum sai ya ce "Dada yau ki kwanta ki huta, Hauwa ke ma ki huta, Ubangiji ya ji addu'ar mu da ikon Allah Tijjani zai fito. Idan kuwa har muka ga bai fito ba, to tabbas zamansa a can yafi alheri. Ku duba shekarun da Annabin Allah Yusuf. Da'n Annabin Allah Yakub, d'an Annabin Allah Ishaq, d'an Annabin Allah Ibrahim A.s. ya yi a kurkuku. An tambayi Annabin Rahma wanne mutum ne yafi kololuwar daraja da nasaba, sai ya ce D'an uwana Yusuf A.s. Amma ya yi shekaru masu nauyi a sijin. Hakan bai zame masa tawaya ba, sai ma k'ara masa kusanci da Ubangiji ya yi. Bayan ya fito kuma Ubangiji ya karrama shi daga bawa ya koma shugaban kasa, kuma babban d'an majalisar sarki."
Dada tana kuka ta ce "Hakane Alhaji amma tunda zan iya bari kawai na yi ibada tuk'uru. Na nemi gafarar Allah, na nemi soyayya da tausayi da afuwa ta wanzu a gidan Marina. Bar ni na yiwa Shehu addu'ar ya fito ya cigaba da walwala cikin iyalinsa. Yabi kad'ai idan na kalla sai na ji kuka, bare y'aya'nsa. Ni dai na yafe maka Alhaji. Kaima ka yafe mini". Sai ta kece da kuka. Ya rik'e ta a jikinsa ya ce "Sha'anin uwa ai mai girma ne Dada. Hakkin haihuwa kad'ai ya isa ayi mata biyayya, a girmama sha'anin ta. A kuma dauwama ana rokar mata alherin duniya da na kiyama. Ban kullaci kowa ba bare ke da aljannata take damafare da sawunki."
Cikin kuka ta ce "Albarkar d'aki ka rabauta duniya da lahira Alhaji".
**
Kwanakinmu goma a Saudiya. Saura kwanaki biyar mu koma gida. Addu'a kam mun yi ta sai fatan alheri ya biyo baya.
Imani ya sake cika mini zuciyata. Na ji sassauci mai yawa akan kullatar da na yiwa mutanan da suke gwada mana rashin kirki. Sai na fahimci afuwa da yafiya suna warkar da zuciya, suna sake girmama mutum a wajen jama'a da wajen Ubangiji.
Kwatsam na kunna wayata sai ganin status din danginmu nake babu kakkautawa dauke da hotunan Baban 2 babu kakkautawa
Jikina ya sab'e da rawa na kasa gane me suke rubutawa domin gabad'aya na rikice!
*Dukan books din Haj Saliha Abubakar Abdullah Zaria akwia su availabale insoft copies*
*Haka ma Hajiya Hafsata Sodangi*
99&100.
Sai washagari aka hak'ura da juyayyin rashin Bulkachuwa. Dada tun asuba ta yi wankan tafiya gano shi. Tana yi tana fad'in "Allah a saukakawa wannan yaro. A jibanci lamarinsa.
Ya ci arzikin ma'aiki. Ya ci albarkacim Shehu mai karama".
Da wuri ya kawo Iklima. Ya ce "Dada zan dawo idan an yi azahr zan kai ki gano mai sunan manya."
Ta ce "Ina ce yanzu zamu tafi Ali?"
Ya ce "Ai yanzu baza su bari ma a gan shi ba."
Ta kyabe baki ta ce "Ina ce Ammar yana wajen? Ni da nake da kafa har a mini iyaka?"
Ya ce "Yi hak'uri, ki bari na dawo, tiyatar haihuwa zan yiwa wata mata karfe tara zan shiga."
Ta rausayar da kai ta ce "Shike nan sai ka dawo, ya zan yi?"
Da ga dawo kuwa gabadaya suka rankaya ganin Tijjani. Ni da Babah kawai aka bari a gida. Da ga can zasu biya gidan Iklima su bar ta a can.
Dada ta kalle shi ta ce "Mai sunan manya kana wuridin *RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN kuwa?"
Ya ce "Ina yi sosai, ina kuma ganin tasirin ta Dada. Komai ya saukaka mini, na samu k'arfin zuciya da tawakkali, iyalina kuma suna cikin rufin asiri mai yawa ".
Ta ce "Hakane, Hakane! Cikin tausayawa.
Sun jima sosai suna shirin tafiya ta cewa su Yaya Ummi su yi gaba tana zuwa.
Yaya Ummi ta kalle shi da idonta da suka yi ja. Da rawar murya ta ce "Yaya Bulkachuwa sai mun sake zuwa".
Ya yi mata murmushi ya ce "Ummilolona kullum sai kin yi kuka? Kamata ya yi ki gode Allah ina rayuwa. Ban rasa komai ba sai y'ancina. Wanda duk ya zo kurku bisa zalunci sai ya samu daukaka, so ku tsananta yi mini addu'a ba kuka ba".
Ta share hawaye ta ce "Allah ya nuna mini ranar da zaka fito Yaya Bulkachuwa sai na yi azumi uku da ikon Allah".
Haka kawai ya ji ta bashi tausayi. Tun tana k'arama ta damu da shi ainun. Shima kuwa idan aka dauke Ihisan da su Aliyu ba shi da wata yar'uwar da ta wuce ta. Ya tabbatar ko bai auri Yabi ba, amincinsa da ita mai yawa ne. Sai aurensa da Yabi ya sake girmama amincin nasu domin ya sani, tana son Yabi fiye da komai. Shiyasa ta sake kaunarsa, ta kuma bada gudunmawar shawo masa kan Yabi matuka gaya.
Suka tafi, su mama duk jiki ya mutu, tausayi ya ratsa jikin kowa.
Sai da suka yi nisa Dada ta sassauta murya ta ce "Mai sunan manya wai anan din akwai d'akin sirri ne, ko kuwa a ina kuke haduwa da Yabi?"
Kunya ta kama shi. Ya kasa ce mata komai. Ta ce "A a ba kunya zaka ji ba. Kawai ka fad'a mini domin idan cikin jejin can kuke shiga a samowa jinjirar taimako domin idan aka samu ciki da ranar Allah, kuma a fili irin haka aka yi tarayyar da ciki ya shiga to fa wannan yaron ko yarinyar rashin kunyar da zasu yi sai ya gigita kowa".
Dariya ta k'wace masa. Ya yi kad'an ya gintse tare da ce wa "Ki yiwa Allah ki bar maganar nan haka. Ki nemo mata taimakon ki kuma tsananta yi mata addu'oi kawai".
Ta saki ajiyar zuciya ta ce"Mai sunan manya abin ne yake ta bani mamaki to ta ina kuke kebe wa ne? Ga yarinya nan ta kwaso Aliyu amma cikin ikon Ubangiji doguwa ce sambal. Dazu ana mata wanka da na zuba mata ido gabobinta irin naka ne sak, haka gashin kanta. Oh ni Binta. Kullum ina kuka da zullimin rashin ka ashe kai baka fasa komai ba?"
Ya murmusa ya ce "Kina sauke mini dala'ilalul khairati kuwa?"
Da hanzari ta ce "Duk satin duniya kuwa. Ko wacce juma'a nake sauke wa. Kuma hadiyya ce a kanka. Mai sunan manya na ga gurbinka! Dakina a bushe, babu kayan shayi irin naka. Babu sabulai da turaruka irin naka. Ta hau kuka sosai. Jikinsa ya yi sanyi. Ya ce su Baban Kasuwa basa siya miki ne?"
Ta ce "suna siya amma har sai sun k'are, kai kuwa kafin su k'are ka kawo wasu. Sabulai da turare masu kyau ba masu s'aukin kudi ba. Amma yanzu fa?"
Ya ce "Ammar da Jabir basa yi miki ne Dada?"
Ta kyabe baki ta ce "Jabiru kam ai yanzu fama yake yi da kansa. Har ya gama samun damarsa kuwa ban wani more shi ba. Kasan sun k'ullace ni akan ku. Wai nafi sonku. Iyayensa kawai yake yiwa. To yanzu an yi mutuwar kasko, kowa ma ya rasa.
Shi kuwa Ammar yana yi mini bazan masa k'aharu ba".
Amma sai ta waiwaya ta sassauta murya ta ce "Da uwarsa muke raba daidai. Idan ba'a hannuna ya bani kudi ba kuwa, basa zuwa mini".
Ya yi shiru, tausayinta ya kama shi ainun. Abin da ya fahimta Baban Marina da mahaifiyarsa sun fi dukkan y'aya'nta yi mata biyayya da kyautatawa a gareta. Sune kuma wadanda ta rayu tana nuna musu rashin soyayya. Komai sune a baya. Amma kuma shi da kansa ya tabbatar Dada tafi sonsa akan kowa cikin jikokinta. Domin Ammar bai samu sukunin yi mata raddi da fito na fito da ita ba. Da ace shine yake da nutsuwarsa da bai san yadda zata ririta shi ba. Ya tuna sadda zai sadada ya kwashe mata yan kobbonta da kayan amafaninta ya siyar. Bata yi masa fada a gaban jama'a. Bari take sai dare ya raba kowa ya kwanta sannan ta shiga dakinsa su yi sababi, tana yi kuma tana ce wa murya kasa k'asa mai sunan manya kada a gane halin da muke ciki.
Shi kuwa sai ya bude muryarsa ya ce "Aji mana tunda sharri zaki k'ala mini saboda kin washe ni. Duk yawan jama'ar gidan nan m, babu mai yi miki sata sai Tijjani!
Nan da nan zata bar maganar ta ce "Alfarmar shehu zaka bari. Darajar sunan da ka ambata na yafe maka, Allah ya shirya mini kai, ya tsare ka daga hau da sharrin zamani".
Ya nisa ya sake murmusawa ya ce "Ki yi hakuri zan fad'awa Aliyu ya dinga yi miki. Ki kuma cigaba da yi mini addu'a Dada. Sannan ki yafe mini ta'adin da na yi miki a shekarun baya.
Da azama ta ce "Wallahi na manta komai. Kuma menene baka yi mini ba da ka samu dama? Aliyu kuwa ai shima a k'ullace yake da ni. Ya sha fad'a mini ina nunawa uwarku butanci. Wanda sharri ne kawai, to wa zai haifi d'a ya ce baya sonsa saboda Allah? Jiya kuwa a gidanka ya ce "Yasan nafi sonka a kansa. Sannan kasan matarsa d'iyar Alhaji ce, su kuwa gabadayansu sun kwashe kayansu a gaban ma'aiki akan sha'anina. Yabi ce kawai take mini sassauci, itama dan tasan ni da kai ba dai mutum ba. Duk tsiyatakunta, duk yadda ka jarabtu a kanta, ba zaka k'i jin kaina ba, ba zaka k'i ni ba!
Ta fad'a cikin sigar tausayi.
Ya saki gauron numfashi ya ce "Ki yi hakuri Dada. Za'a gyara. Yanzu ki daina damuwa. Sannan kada ki koma Toro. Ki zauna anan BAUCHI ki dan huta. Idan jama'a sun tafi zansa a kawo miki kaji Babah ta gyara miki ki dinga cin abin ki. Idan sun kusa karewa za'a sake soya miki wasu. Sannan yanzu a hanya za'a siya miki kayan shayin ki, ki ajiye a wajen ki. Naki ne ke kad'ai kada Yabi ta yi miki k'auron nata".
Ta yi maza ta ce "A a itama tana yi mini alheri, sannan tunda aka sakaye ka soyayya ta sake kulluwa a tsakaninmu, kullum muka hadu sai mun yi kuka. Kasan yanzu ta yi hankali. Gara na fad'i gaskiya ko ba haka ba".
Ya yi dariya ya ce "Ho Dada ta Yabi. Tsoron ta kike ji ne yanzu?"
Ta rausayar da kai ta ce "Uum kaidin mata mai yawa ne. Yanzun nan idan ta murde kai ma sai ka juya mini baya a kanta. Barta dai tunda ta nutsu, kuma tana mini ya kamata. A lallaba a tafi a haka, domin na riga na yi imani da kiararin da na ji ubanta yana yi mata. Na ce wa ita kad'ai gayya ce a gidan Marina. Ko kasan kaf zuri'ata babu mai ruwan kudi a hannunsa irin Yabi? Yadda na gasgata karamar Shehu haka na gasgata kudinta na halali ne. Ka ga yadda ta mayar da dakin uwarta ne? To ragowar matan uban ma duk ta yiwa dakunansu kwaskwarima lokacin auren Ubaida. Idan ka ga bajintar da ta yi a auren kuwa sai ka rik'e baki. Matar gwamna har tawaga ta turo su wakilce ta bikin.
Kofarsu tafi ko ina haske da kyawu yanzu, kuma duk ita ce. Ko kai ma irin yadda kake yiwa ubanta ai saboda ita ne. Yabi, Yabi duniya ce? K'aramar halitta sai babban al'amari".
Ya kwashe da dariya ainun.
Ta ce "Allah kuwa. Mata ai yanzu sun ri'ka. Idan basa yin ka to mijinsu ma ba zai maka kallon rahama ba".
Ya sake yin dariya ya ce "Duk zan fad'a mata ne".
Ta kyabe baki tare da ce wa "To hudawa cikinka wuka da kanka.
Ta jima kafin ta dingisa ta tarar da su a mota suka tafi.
**
*Watanni uku a gaba*
Zuwa lokacin Husna ta yi gubibi da ita. Shayarwa na matukar ciko da Yabi . Saboda kirjinta suna cika, ita kam tana cikin mata kad'an da goyo yake karbarsu.
Bata da matsalar komai sai ta rashin miji.
Har zuwa lokacin Dada na tare da su.
Ba zato ba tsammani Aliyu ya zo ya kwashe su aka yi musu passport.
Sai da passport ya fito yake fad'a musu kudin hayar filling Tijjani ne. Shine Kuma ya ce Yabi da Dada su tafi su yi Umrah su yi masa addu'a."
Ai kafin ya rufe baki Dada ta zabge da kuka tare da ce wa "Ashe zan koma gabar ni Binta? Hauwa kin iya haihuwa! Shehu ya haifu. Allah ka yiwa Shehu abin da mai zato bai yi zatonsa ba ". Sai kuma ta rushe da kuka wurjajan.
Ya ce "Ganin hakan ya sanya na biyawa tawa uwar sai ku tafi tare"
Nan ma Dada ce ta yi fit ta ce "Wayyo Ali Allah ya yi albarka, yasa kai ma ayi maka tagwaye."
Ya ce "Ai tuni ya bani Dada. Wadannan da suke gittawa ta gabanki ba nawa ba ne? Ko kuwa dan a gidan Marina kowa d'an da ya haifa ne nasa shiyasa kike ganin sai na haifi wasu tagwayen?"
Da yake babu wata shak'uwa a tsakaninsu, asalima tsoro tsoronsa take ji. A sanyaye ta ce "A a kuskure ne, da mantuwa Ali. Yanzu dai ba zamu yi fad'a bayan ka zo mana da babban albishirin da babu irinsa. Allah ya saka da alheri, ya yi muku albarka gabad'aya".
Ya ce "Ameen".
Babah itama ta yi masa godiya da fatan alheri da bunk'asar arziki. Yabi tana bude baki ta ce "Na dad'e ina son na tura Baban Marina Umrah. Na dad'e ina fatan na yi masa ba zata. Ta ce zan tattara abin da nake da shi a yi tafiyar nan da shi".
Idon ta ya ciko da k'walla tana ayyana yadda Baban 2 yake fatan ya kai ta Makkah. Ashe abin na ransa, ashe itace zata riga shi zuwa Sau'udiyya?
Hawaye ya tsinke mata. Babah ma ta shiga taya ta. Aliyu ya ce "Maimakon ku yi masa addu'a sai kuma ku yi masa tukuicin kuka?".
Cikin kuka sosai Dada ta ce "Kai ku yi kukanku da kyau kun ji ai! Ali ai dole mu yi kuka. Yau sama da shekara Shehu na garkame a haka aka samu rabon Asma'u. Kai rabon haihuwa zazzafa ne".
Aliyu ya ce "Kai Dada da fitina kike. Me ya kawo wannan maganar a yanzu kuma? Sannan kuma Yaya Tijjani ne ya koma shehun ko kuwa?"
Ta ce "Eh shi fa. Tunda ga y'aya'nsa na girma ai gara na tsayar masa da suna d'aya. To na zabi Alhaji Shehu kawai domin Sha Allahu wataran zai zama Alhaji da ikon Ubangiji kuwa".
Ya gintse dariyasa ya ce "Ni na tafi, tunda Yabi ta had'a ni da aikin dauko Baban Marina gobe".
Sai lokacin na ce "Tare zamu je, zan duba yaron Anzira da ya yi targade."
Ya ce "Tom in sha Allah".
Babah ta ce "To kuma ya zaka yi da wannan kilifar ne tunda bata isa yaye ba. Watanta uku kacal" Ya ce da ita zaku tafi mana".
Dada ta ce "Allahu akabar! Yabi ta haifo Yabi."
Ya kwashe da dariya ya ce "A a Dada. Ai Yabi wadda aka haifa a hanyar sau'udiyya dan aikin Hajj ne ko aka je da cikinta. Ita kuwa wannan ai ana riga an haife ta, sannan Umrah zaku ce ba tawwali ba".
Ta ce Hakane, sai ace mata Ummara Husna. Domin na tabbatar sai ta yi jidalin Asiya idan ba'a ce mata Ummarah ba. Oh ashe dai da rabon burin Yabi na zama Hajiya a kusa zai tabbata. Nasan Shehu ya biya mini ne dan na kula da ita, na jagorance ta a wajen sa'ayi da safa da Marwa".
Ta bawa Aliyu dariya ainun ya ce "A Ina zaki jagorance ta din? Ai ko ke yanzu kika je d'aya zaku zama, ko wanda ya je bara idan ya koma bana sai ya ga abubuwan da bai san da su ba. Saboda yadda gwamnatin Sau'udiyya ta mayar da hankalinta akan Makkah da Madina gabad'aya. Bare ke mai shekaru ashirin da biyar da zuwa, ina ce da kika je ma ba'a haifi Anas ba?"
Ta rausayar da kai ta ce"Ko Yabi yayarsa ma ba'a haife ta ba. Kasan ana daf da aihuwatata Alhaji ya hadu da sharrin masu zamba cikin aminci, haihuwarta ta zo cikin wani irin yanayi mai tsananin gaske ".
Na hauro na ce "Dada kina son fad'an wannan labarin. Nasan idan tafiya ta mika zaki k'arasa abin da kuke fad'a cewar ni na kore masa arzikinsa".
Ta kama baki da azama ta ce "Yabi ki yiwa darajar Alhaji da Asma'u kada ki birkice mini. Ko mahaukaci ya ji labarin ki da irin bajintar da kike yiwa uwa da uba ai yasan ke din arzika ce ba wai Yabi ba. Yo duk gidan Marina akwai wanda bai ci arzikinki ba ne? Babu shi Wallahi. Allahu ya huci zuciyar ki. Bazan sake ba. Kai Ali tashi ka yi tafiyar ka, nima alwallah zan yi na yi munajiti da Ubangiji. Kai ma ka yawaita zikirrn ambaton Ubangiji ko na istigifari, ko da kuwa tukin mota kake yi ".
Ya yi dariya ya ce "Wayo da Yaya Tijjani da Nasiba da Yabi sune maganin Dada."
Na dauke kai na ce "Kada ka sani Yaya Aliyu! Baban 2 da Nasiba dai. Tun fil-azal sune zasu yi sa insa da ita ta yi mukus. Amma ni kam menene bata yi mini ba?"
Ta yi shiru ya kasa ce wa komai. Sai Babah ce ta fanshe ta da ce wa "To marasa kunya ta yi din. Suma wadancan din waye su da zasu yi maganin uwarmu? Ai tunda aka yi sa'a tana tsananta ibada komai zai daidaita mata."
Da haka aka bar maganar domin jikin Dada ya yi sanyi.
Da kaina na je Toro na sanar da Baban Marina cewar Tijjani ya biya mana Umrah ni da Dada Aliyu kuwa ya biyawa Babah. Ni kuma na biya masa.
Ya yi k'asa kansa tsawon lokaci bai yi ko da motsi ba bare ya yi magana. Ya jima kafin ya d'ago. Na ga hawaye jagejage a fuskar sa.
Nima nawa hawayen ya kwace mini amma ni kam na farincikin yadda Ubangiji ya yiwa fafutukar sana'ata albarka nake yi. Domin bani da burin da ya wuce na sanya Baban Marina farinciki tun ina mitsitsiya ta. Gorin da ake mini, haihuwa ta ce ta tsiyata shi. Da kuma bak'in cikin yadda ya zama koma baya a cikin gidanmu na matuka mintsinin zuciyata.
Da k'yar ya yi jarumtar ce wa "Na sha fad'a miki ke kad'ai gayya ce Asiya. Na fad'a miki zaki yi albarka. Na dad'e ina fad'a miki akwai lokacin da zai zo da kowa sai ya so ki har makiyan na ki. Ga shi na fara ganin sakamakon alherin da Ubangiji zai yiwa hak'uri da juriyar da kika yi a rayuwar ki. Allah ya yi miki albarka. Daga nan har kasa ta rufe mini ido na yafe miki, kina cikin farar addu'a ta. Allah yasa y'aya'n ki su yi fiye da ke. Allah ya miki tukuici da alheri. Kin yi hak'urin aure, kin yi juriya. Da ikon Allah ba zaki sake fuskantar tsanani a gaba ba."
Ina kuka na ce "Allah ya amsa Babanmu! Na gode Allah ya k'ara lafiya.
Ya ce "Ku tafi da gyatumar ki Yabi. Kin ga dukkanku mata ne. Da ikon Allah zaki kai ni."
Na girgiza kai na ce "Zata je Baba! Amma wannan kudin na tara kaso uku cikin hudu da sana'ar da na rayu ina yin ta. Kai nake son ka je, dan kanji dad'i ka kuma godewa Ubangiji da ya jarrabe ka da fitinar yan'uwa. Sai kuma ya baka y'aya'n da zasu sadaukar da komai dan ka yi murmushi. Ka je ka yi mana addu'a. Ka tayamu addu'ar Ubangiji ya kubuto mana da Tijjani ".
Sai kuka na sosai ya k'wace mini. Abin mamaki sai shima ya taya ni kukan muka dinga yinsa a hankali.
Da yake a dakin Gwaggo yake. Ta shigo da Husna a hannunta da ta fara kukan neman nono. Ta tsaya cak bata miko mini ita ba. Ta sassauta murya ta ce "Ayyah Yabi baki ga kullum girma sake kama shi yake ba? Me yasa kike kasa hak'uri a idan kina gabansa? Kinsan yadda kukan ki yake rikita shi kuwa? Kalli irin kukan da yake yi mana. Me yasa kike rasa dukkan jarumtar ki a gabansa?"
Na kasa magana. Sai shine ya ce "Ni ne nake rasa dukkan jarumtata akan lamarin Yabi. Tana matukar bani tausayi, kuma dama ita ce raunina a cikin dukkan y'aya'na. Shiyasa Ubangiji yake ta jarabtata akan sha'anin ta. Tafi kowa shiga garari da kalubalen rayuwa. Asma'u! Ki ji tausayin ta. Ki sake ninka addu'ar da kike yi mata. Zauna a zaune ki ji al'amarin da ta zo da shi."
Yana hawaye ya fad'a mata zuwn nawa albishir na yi masa zai tafi gabas. Yana rufe baki itama ta fara hawaye tana fad'in Allah mun gode. Ina taya Yabi godiyar yadda ka cika mata burin ta, na mayar da Alhaji dakin ka. Allah ka k'ara yaukaka mata arziki, ka shirya mata zuria. Ka mata tsari da dukkan abin da zai cutar da ita ko iyalinta".
Ya k'ira Mama da Inna ya fad'a musu alherin da ya same su ya rufe da ce wa kada su fad'awa kowa sai abu ya kankama. Domin tafiya gabar kiran Allah ne.
A gurgurje na je gidan Nazira na dubo yaronmu.
Da yamma muka juyo da Yaya Aliyu akan gobe Baban zai zo BAUCHI don ayi masa passport.
Ba a fito da maganar tafiyarmu ba sai da komai ya kammala ya rage saura kwanaki hudu.
Baban Marina da kansa ya fad'awa y'an uwansa cewar zasu tafi Saudiya. Da Yabi da diyarta da Dada Tijjani ya biya musu. Aliyu ya biyawa Hauwa. Shi kuwa Yabi ce ta biya masa. Suka ka'du k'warai. Amma da yake dangantarsu ta yi tsami ainun kowa ya hadiye a ransa tunda yanzu so suke ace kowa yafi kusa da Baban Marina a tsakaninsu. Sannan basu gamsu Yabi ce ta biya ba. Duk da dai sun yi matukar sikewa da lamarinta tun auren Iklima. Zuwan tawagar matar gwamna Toro gidan Marina ba k'aramin cece kuce da girmama lamarin Yabi ya janyo ba.
Ranar talata da asuba muka nufi Kano tunda an ce shabiyun rana zamu tashi.
Karfe tara a airport din ta yi mana. Aliyu bai tafi ba sai da ya ga tashinmu. Sannan ya juya da twins da Ikilima da suka yo mana rakiya. Hamim sai kukan sharbe yake yi. Hanif sai hak'uri yake ba shi yana ce wa "Mun girma fa Hamim. Ammi ba dadewa zasu yi ba. Ba ta ce addu'a zasu je su yiwa Baban 2 ba? Husna zata raina ka fa". Suka bawa Aliyu tausayi. Haka kawai yaran suke ba shi tausayi ainun.
Bai bar Kano ba sai da ya siya musu kayayyakin wasa da na ciye ciye dan su warware gabadaya.
Kai tsaye a Madina muka sauka. Mun gaji likis. Dole muka kwanta. Dada sai addu'a take yi tana fad'in "Allah k'amshi ya cika hancina, haske ya cika idona, k'arfi ya yiwa gangar jikina k'awanya, farinciki da imani sun cika zuciyata. Allah ka karawa Annabi daraja. Allah ka karbi addu'ar da zamu yi, ka bamu k'arfin da zamu yi ibada ta gaskiya."
Sai ta zauna. Sai ta zabura ta je jikin windo tana leken asumayar masallaci ma'aiki. Tana kuka tana fad'in "Rabbani yadda ka sake yi mini gatan ganin koriyar gubba ta d'an Amina mai wuyar ga ni. Allah kasa zan gan shi da idona. Allah ka bani ikon rokon gafararka idan na shiga rauda. Allah ka shirya mini zuria, ka jefa soyayyya a tsakanin ahalina. Alla na yi tuba. Allah mai babban suna aiko ni ya yi takanas, Ubangiji a karba a sassauta a kubuto da shi albarkacin masoyinka Baban Nana".
Duk juyin da zan yi zan ga idonta biyu. Babah kuwa barci ta yi sosai domin bata runtsa ba a jirgi, ita take ta fama da Husna.
Daf da asuba muka tashi, muka yi alwallah muka nufi masallaci. A harabar hotel din muka had'u da Baban Marina shima ya fito zai tafi. Na kalle shi cikin sabuwar jallabiyar da na siya masa guda uku a Kano. Ya yi fes da shi. Garin Madina rahama ne.
Gabadaya zukatanmu cike suke da shauki da rauni. Duk juyin da muka yi da Dada ta saka silifas din ta. Ce wa ta yi "Wane mutum ta taka k'asar Madina da takalmi? Mu dai da muka ga zamu taka ba zata ce komai ba. Allah ya yafe mu kawai"
Kan dole muka k'yale ta. Domin har muka yi kwanaki biyar a a Madina bata yarda ta saka ba. Duk ranar da aka yi ranar juma'a ma haka ta tako. Sai da muka shiga motar tafiya Makkah sannan ta saka takalmi, tana hawaye tana fad'in "Allah ina son na sake dawowa. Idna ban samu damar ba, na yi godiya. Allah karbi addu'ar da muka yi."
A Makkah kuwa har tausayi suke bani tunda muka je dukkanmu a masallaci muke kwana. Mu yi sallah, mu yi dawafi. Duk shekarun Dada bata zama. Ko dan yar firit ce irina? Ban sake gasgata komai na Dada na kwaso a halitta ba. Sai a tafiyar nan da muka yi. Kamar da muke yi ta baci. Na tsinci kaina da addu'ar kada Allah yasa na yi halinta idan shekarun girma suka cimma ni. Tunda ta sha fad'ar hatta fad'an da na yi ina karama itama haka ta yi a lokacin kuruciyarta.
Baban Marina kullum sai ya ce "Dada yau ki kwanta ki huta, Hauwa ke ma ki huta, Ubangiji ya ji addu'ar mu da ikon Allah Tijjani zai fito. Idan kuwa har muka ga bai fito ba, to tabbas zamansa a can yafi alheri. Ku duba shekarun da Annabin Allah Yusuf. Da'n Annabin Allah Yakub, d'an Annabin Allah Ishaq, d'an Annabin Allah Ibrahim A.s. ya yi a kurkuku. An tambayi Annabin Rahma wanne mutum ne yafi kololuwar daraja da nasaba, sai ya ce D'an uwana Yusuf A.s. Amma ya yi shekaru masu nauyi a sijin. Hakan bai zame masa tawaya ba, sai ma k'ara masa kusanci da Ubangiji ya yi. Bayan ya fito kuma Ubangiji ya karrama shi daga bawa ya koma shugaban kasa, kuma babban d'an majalisar sarki."
Dada tana kuka ta ce "Hakane Alhaji amma tunda zan iya bari kawai na yi ibada tuk'uru. Na nemi gafarar Allah, na nemi soyayya da tausayi da afuwa ta wanzu a gidan Marina. Bar ni na yiwa Shehu addu'ar ya fito ya cigaba da walwala cikin iyalinsa. Yabi kad'ai idan na kalla sai na ji kuka, bare y'aya'nsa. Ni dai na yafe maka Alhaji. Kaima ka yafe mini". Sai ta kece da kuka. Ya rik'e ta a jikinsa ya ce "Sha'anin uwa ai mai girma ne Dada. Hakkin haihuwa kad'ai ya isa ayi mata biyayya, a girmama sha'anin ta. A kuma dauwama ana rokar mata alherin duniya da na kiyama. Ban kullaci kowa ba bare ke da aljannata take damafare da sawunki."
Cikin kuka ta ce "Albarkar d'aki ka rabauta duniya da lahira Alhaji".
**
Kwanakinmu goma a Saudiya. Saura kwanaki biyar mu koma gida. Addu'a kam mun yi ta sai fatan alheri ya biyo baya.
Imani ya sake cika mini zuciyata. Na ji sassauci mai yawa akan kullatar da na yiwa mutanan da suke gwada mana rashin kirki. Sai na fahimci afuwa da yafiya suna warkar da zuciya, suna sake girmama mutum a wajen jama'a da wajen Ubangiji.
Kwatsam na kunna wayata sai ganin status din danginmu nake babu kakkautawa dauke da hotunan Baban 2 babu kakkautawa
Jikina ya sab'e da rawa na kasa gane me suke rubutawa domin gabad'aya na rikice!
101-102.
Na nutsu na lalubo na Aliyu sai na ga hoton Bulkachuwa sannan ya rubuta Barka da samun yanci Yaya. Allah yasa wannan al'amarin ya zame maka tsanin shahararka a duniya."
Na bude murya sosai na ce "jama'a Tijjani ya fito, an sake shi. Gabadaya na rikice, na rikita su. Da k'yar na nutsu na musu bayani. Dada aka fad'i aka yi sujjuda. Ni da Baba muka yi maza muka but bayanta muma muka yagi sukjadar. Ta zabura ta ce "Haramin zan koma. Duk da dare ne bamu hanata ba, muma muka bi bayan ta. Bayan mun je dakin Baba baya nan tabbacin yana masallaci a can zai kwana.
Duk son mun gan shi bamu samu zarafin hakan ba. Sai da gari ya waye muka dawo masauki. Ai kuwa gabadaya muka kutsa dakin da yake ciki. Muka hau rigen yi masa albishir. Muna tare a dakin Aliyu ya kira ni vedio call. Aka gaisa aka yi murna, ya nuno mana fuskar Tijjani da ya kare da hannu. Da k'yar ya ce "Ina gaishe ku gabadaya. Na gode sosai. A kuma sake yiwa Ubangiji godiya.
Duk yadda nake jin dad'i a Makkah amma sai na ji kwnanaki hudun da suka rage gabad'aya sun mini tsauri. Ji nake tamkar na bude ido na gan ni a BAUCHI.
**
*Yadda al'amarin ya kasance*
Rundunar ta gurfanar da Alhaji Auta a gaban kotu domin da kansa ya kai karar kansa ofishin y'an sanda ya tabbatar musu laifinsa akan abin da ya yiwa Tijjani. Cikin kuka ya ce "Na aikata BAK'AR TA'ADA, na bari sharrin zuciya da shaidan sun janyo mini wahala. Tunda aka rufe yaron nan. Al'amarina ya sake kacame mini, kullum masifu sake yi mini k'awanya suke yi. Dan haka na zabi na kubuta daga azabar lahira. Tiryan tiryan ya yiwa y'an sanda bayani yadda ya shirya komai.
Take aka k'ira yan jaridu na radio da talabijin ya maimata a gabansu.
Nan da nan abu ya watsu a
BAUCHI da kewaye ko ina maganar ake yi. Sai Allah wadai ake yi da halin Alh Auta. Wasu kuwa su ce ya yi sa'a ma da ya zabi ya fadi gaskiya ya samu sassaucin kwanciyar kabari. Wasu kuwa su ce Yasin aka yi ta buga masa da alkunut shiyasa ya kasa gaba ya kasa baya har sai da ya fito ya lashe amansa.
Mai dakin gwamna na zaune a katafaren falonta tare da mai girma gwamana suna kallon N.T.A BAUCHI. Suna kallon yadda kae nuna Alh Auta kai tsaye (live) yana bayanin tuggun da ya had'a. Take ta tuna labarin da Yabi mai lalle ta yi mata. Nan da nan ta ce "Yallabai ka yi magana a gaggauta sako yaron d aka yiwa kaAmzfin nan babu dogon turanci. Ina sake rokon gwamyta bashi Wani abu na diyya bisa samaye shi da aka yi babu laifinsa. Sannan a gaggauta gurfanar da wannan tsohon banzan a gaban kuliya. Idan ka gaggauta sakinsa tare da yi masa wani alheri jama'a zasu sake son ka su tabbatar adali ne. Tunda a yanzu babu abin da zai dauki hankalin al'ummar BAUCHI irin wannan al'amarin ".
Take kuwa ya dauki waya ya yi magana da mahukunta. Kasa da awa daya aka.gata ganin Tijjani a talabijin, tare da jajanta masa. Gwamnati kuma ya bashi kyautar milyan ashirin bisa bata masa lokaci da suna da aka yi. Bayan haka take gwamna ya bashi S.A. wato mai bashi shawara akan gidajen gyaran hali.
Ba a jima ba sai ga hukumar kare hakkin dan Adam sun dauke shi aiki. Haka ta costom da kuma hukumar kula da kiyaye safarar k'waya da tu'ammali da ita. N.D.LA.
Cikin yini daya tak sai da aka yiwa Tijjani aiki tayin aiki a ma'aikatu biyar.
Ganin hakan gwamna ya sake ce wa ya bashi aiki a a ma'aikaar aikin Hajj. Da albashi mai tsoka. Wajen da aka bawa Tijjani duk shekara sai ya samu gurbin kujerar aikin hajji d'aya ko biyu. Ga shi babban mai bawa gwamna shawara.
Ga milyoyin kudi. An sha wahala, an yi bak'in ciki, amma a karshe sai alheri da daukaka ya biyo ba.
Yanzu da aka gurfanar da Alhaji Auta a gaban shari'a sai aka yanke masa kwantankwacin shekarun da Tijjani zai yi. Bisa kama shi da zambo cikin aminci, da kuma yiwa k'asa da jihar BAUCHI zagon kasa. Ga mamakin alkali sai Tijjani ya mike ya ce "Ni dai laifin ya yi mini na yafe masa. Allah shine shaida na yafe masa, ubana ne, sharrin zuciya ne d azal ya hau kansa. Tare suka yi gwagwarmaya da mahaifunay. A saddna naje gabansa da nufin ya taimake ni ya bani sana'a bai ki, ba asalima ya daukake ni a cikin yaransa. Maganar filina d aka karaba ba nasa ba , shaidan ne ya shafi kirijinsa. Da yawa mutane basa iya tsallake tarkon kyashi da hassada. Dan haka na yafe masa. Allah ne shaidar hakan".
Mafi yawan mutanan sai da suka yi kuka. Suna ayyana da ace mutane irin su Tijjani ne suka fi yawa a duniyar da ba a shiga tsananin da ake ciki ba. Abin da ya yi ya sake zaburar da jama'a girman afuwa da sassauci. Take kotu ta zabtare shekaru biyar a cikin bakwai aka mayar masa shekaru biyu, wanda wannan hakkin cin amanar gwamnati ne bata yafe ba. Sannan ya zama gargadi ga masu son k'ulla sharri haka siddan.
Gabadaya kafafen sadarwa labarin da ake tattunawa akai.
Cikin rakiyar jami'an tsaro aka ki shi gidansa.
Aliyu ne da su Yaya Salisu da Yaya Ammar suka tarbe shi. A ransa kuwa so ya yi ace ya tarar da Babah da Yabi da kuma Dada. Ya tabbatar ukun nan suna gaba da komai a rayuwarsa. Domin ya sani Dada ta so shi hakikanin soyayya.
A daddafe kwanakin suka cika muka tattaro muka dawo cikin tsananin farinciki da murna.
Aliyu bai samu sukunin zuwa daukarmu ba. Muna dira ya kira Baban Marina tamkar mai auna lokaci. Ya ce mu dauko shatar mota ta kawomu. Da yake karfe takwas muka sauka a Kano na safiya. Hakan kuwa muka yi. Ban tab'a ganin nisan tazarar Kano zuwa BAUCHI na sai yaiy. Jin na yi gabad'aya na kosa.
Haka muka isa Lafiya muka tarar da gida cike da mutanan Toro da na Bulkachuwa. Ana murna tare da dawowa lafiya. Na kalle shi yana kan kujera ya yi wanka yana sanye da k'ananun kayansa. Ya rame kam. Amma ya yi kyau. Ya yi aski saisaye. Ya yi fes, twins suna gefen hagu da damansa ma'ana sum sanya shi a tsakiya. Sai satar kallon juna muke muna murmusshi. Gabadaya mutanan da suka cika gidan sun gundure ni. So nake kawai su kauce su bamu waje.
Sai la'asar suka dunguma suka tafi Toro tare da Dada da Baban Marina.
Yayin da Aliyu ya tafi da Baba da twins gidansa. Kafin ta koma Bulkachuwa tunda Tijjani ya fito.
Bamu samu sararin marabtar juna ba sai da ya dawo daga sallar Isha, ya rufe gidan. Ko da mutanan Toro suka tafi, jama'ar unguwar sai shige dagice suke mana da sunan murna da kuma yi mini sannu da dawowa.
Da kansa ya yiwa Husna wanka yana ta tsala kukan kiwa. Daga karshe sai na fahimci da ruwan zafi sosao ya yi mata. Dan haka kukan har da dalili. Ya shafe ya da mantaleta, ya Sha nono. Ba'a jima da yin wankan ba kuwa barci ya sure ta irin mai nauyin nan.
Daga haka ya tisa ni a gaba da rawar jiki. Bamu iya ce wa komai ba illa barin da jikinmu yake yi. A matukar matse muke da juna. Abubuwan da suka biyo baya masu nauyi ne.
Sai dai bai yarda min yi barci ba, wanka muka yi muka dinga sallar godiya. Dukkanmu kuka muke yi. Domin al'amuran da muka tsallake taimakonsa ne kawai. Ba dan ikon Allah ba da tuni aurenmu ya dad'e da daidaicewa. Muna cikin bala'in asiri sai kuma k'azafi da hassada ya sake gigitamu. Amma cikin hucewar Ubangiji komai ya wuce.
Da asuba ma da ya dawo rufe gidan ya sake yi. Dai-dai loakcin Husna ta farka. Na canja mata pampers da ta cika shi da fitsari. Na d'ora ta kan fo. Na gyata ta sha nono sai ta sake komawa barcinta. Na kwantar da ita a gadonta tunda Hajiya mai magana da yawun first lady har gado ta kawo mata na garari lokacin haihuwar ta. Na lallaba na shige jikin Tijjani domin barci da gajiya ne a jikina ainun. Tara muka tashi shima kukan Husna ya tayar da mu.
Ya bude ido ya ga na yi mata wanka na ina shirya ta.
Ya mik'e ya ce "Asiya rabon da na yi barci haka da safe har na manta. Wato mutum baya gane darajar y'anci sai ya rasa y'ancinsa. Gidan gyaran hali babu dad'i! Masifar da na gani ko makiyina bana fatan ya shiga wajen nan. Sannan babu abin da yake sake rikita ni irin Barnar da ta yi katutu a wannan wajen. A had'a masu k'ananun laifuka da manya. Sannan gwamnati bata yi tsarin yiwa masu laifin allurar kashe sha'awa na wani lokaci ba. Ko kinsan luwadi ya yi yawa a gudajen kurkuku?"
Cikin gigita na ce "Subhanallah! Ya rausayar da kai ya ce "Barna kan b'arna sai dai kawai Ubangiji ya yafe mana.
Abin tausayi wani abin da ya sata bai fi dubu biyar ba, amma rashin gata ya sanya an daure shi sherkaru sama da goma. Wani sharri ne irin nawa, wanni sawun barawo ya taka. Wani bisa kuskure ya aikata laifin. Amma duk an runtse ido an ki yiusu sassauci ta ya ya rayuwa ba zata tsananta mana ba? Addu'ar wadanda aka zalunce su babu hijabi. Sannan yanke hukunci babu hujja yana janyowa al'umma fishin Ubangiji.
Bakar Taada ta shiga ko ina a wannan duniyar Asiya."
A raunane na ce "ALLAH ya shiryemu ya kuma kawo mana fita.
Na yi matukar tsorata da yadda ake b'arna a gidan da ake masa lakabi da gidan gyaran hali.
Kwnanaki biyu da fitowarsa muka sami saukin zaryar jama'a. Takanas aka turo mota daga gidan gwamnati. Domin na yi waya da Hajiya akan ina son zu je mu yiwa first lady godiya. Domin na sani abubuwan da aka yiwa Tijjani na alheri har da arzikina da ya ci. Muna zube a gabanta, muna ta godiya. Mai girma gwamana ya ce "Tijjani kana ta sun gurbin aiki a ma'aikatu daban daban saboda a tayaka alhinin halin da ka shiga. Amma Hajiya ta ce "Wanda muka baka zaka yi. Domin ta dad'e da yiwa matarka al'kawarin zata fito da kai, bisa adalcinmu muka jinkirta sai azumi sai ka shiga sahun wadanda gwamnati zata yafe musu, duk da laifin ka mai girmane. Sai kuma gaskiya ta yi halinta. Hajiya ta roki arzikin na rik'e mata kai da kai da kyau dan matarka ta huce wahalar da ta sha ta rashinka. Dan haka zaka zauna a jihar me dan al'ummarka su amafana da kai."
Tijjani ya hau godiya da murna, yayin da kaina ke kasa nake taya shi godiya.
Cikin kasaita first lady ta ce "Sai a kula, a kuma rik'e mini diyata da kyau domin samun yarinya jaruma ikarama kamar Asiya za'a dad'e . Mace ce mai kamar maza. Na shiga zullimi akan sha'anin ka. Saboda soyayya da sadaukarwa da na ga ni a wajenta. Tana son ka. Ka rik'e a ranka ba zan laminci ka juya mata baya ba".
Ga mamakin Tijjani sai ya ji gwamna ya ce "Hajiya yo me yi miki shara ma ai ta wuce ta yi boranci bare y'ar boko irin wannan mai cike da kuruciya."
Tijjani ya ka'du k'warai da gaske. Domin ya fahimci tasirin da uwar dakin Yabi yake da shi a wajen mijinta. Sannan ya gane dukkan alfarmomim da gwamnati ta yi masa da iznin Hajiya ne. Ita kuwa saboda Yabi ta yi hakan. Da gaske nasararorin rayuwarsa na d'amfare da Yabi ne.
Ya sake yin kasa da kai ya shiga yi mata godiya tare da ce wa ", Za'a kiyaye Hajiya!.
Ni kuwa murya na rawa na ce "Na gode mamana. Na sani mahaifiya daya ce, amma idan mutum ya girmama mutane, ya sanyawa harshensa linzami akan sha'anin da ba nasa ba, sannan ya yi gaskiya da juriya sannu a hankali sai Ubangiji ya bashi uwaye masu yawa. Tabbas ina da mahaifiya. Amma ke din uwa ce a waje na. Allah ya kara miki lafiya. Ina fatan idan kin kammala shekarun biyar din data yi muku saura ki zama first lady din Nigerita ba iya ta jihar Bauchi ba."
Dad'i ya kama su daga ita har mijinta. Da barin baki ya ce "Ameen yarinya. Hajiya me za'a bata tukuicin wannan farin fatan da yi mana gabadaya?"
Da murmushin kasaita ta ce "A maye mijinta da gurbin Kwamishinan ma'aikatu da ya rasu satin da ya wuce mutane suke ta zawarcin kujerar."
Ya ce "Angama ranki ya dad'e Tijjani ka zama kwamsinan ma'aikatu na jaha gabadaya. Zan mika sunanka majalisar zartawa ka zama cikin shirin zasu gayyace ka domin tantace ka".
Gabadaya muka rikice da murna da godiya. Yayin da ta ce "Ita kuma a mayar mini da ita wata ma'aikata haka mai dama".
Take ya buga waya akan a kai ni college of education a matsayin non academic staff.".
Ta sake ce wa idan har na zama first lady din k'asa Asiya ki dinga jin ke ce magajiyata."
Na ce "Ina godiya k'warai mamana, alherinki mai yawa ne, ba kya fad'ar magana da zummar wake. Allah ya kai fata mizani".
Muka taho cikin rakiyar jami'an ican tsaro. Kafin kace miye har an sanar gwamna ya nada Tijjani Yusuf Bulkachuwa a matsayin kwaishinan aiyukan jihar.
Ta ko ina murna ake yi. Da kansa Tijjani ya sake gane al'amarin Yabi babba ne. Tabbas ita ce sababin arzikinsa. Sana'ar lallen dai da aka ce zata rike su itace sanadin zargo musu hamshakan matan da suka sada ta da mai dakin gwamna. Babu abin da zai ce da Yabi da sana'arta sai Hamdala. Zai cigaba da girmamata tare da kauce wa dukkan abin da zai had'a su. Domin ya ga ta k'ra wayo. Ta hadu da manyan mata da zasu yi masa fatafata idan ya ce zai taka ta. A ransa sai fad'i yake gwamna na tattala bacin ran Hajiya, bare ni?. Shi kad'ai ya yi dariya tare da kame bakinsa domin ya fahimci sha'anin babbane. Bayan haka Yabi ta yi hak'uri, ta yi juriya, ta yi masa komai. Shi ma zai yi dukkan iyawarsa ya saka mata da alheri kan alheri.
Kwa aki uku kacal aka ba shi ya huta.
Gidan Marina ya kacame da murna kowa ya boye aibu da gilli aka dinga tseren yi mana murna. Baban Tsakiya da na Kasuwa washagari suka zo sai dai tafiyar kowa daban.
Dukansu maganganunsu suna nuni.tare da tuni sune suka had'a auremmu dan mu gane oron alherin da suka yi mana. Baban Tsakiya cikin rauni ya ce "Tijjani danuwanka dai yana zaune babu aiki. Jabiru naka. A duba, ga yaranmu nan ka yiwa Allah ka dubasu. Ka rage banbanci Tijjani. Allah ya shirya zuria."
Da zai tafi ya bude murya ya ce "Ina Hajiya Yabin?"
Gabana ya Fadi ni ce Hajiya Kuma?"
Na saka hijabi na fito na tsugunna na ce ga ni Baba".
Ya ce "To ku kula. Ki kuma dage da yiwa mijiki addu'a kinga dai fad'i tashin da muka yi har asirin da aka ta jifanku ya karye. Kada na ji, kada na ga ni. Ki dinga tunawa mijinki game da rashin aikin yayanki Jabiru. Ki kuma cigaba da hak'urin aure nasara tana gaba. Alhaji Babba mura yake shiyasa bamu taho tare ba".
Da mamaki na ce"wanene ke nan?"
Ya ce "Baban Marina mana"
A sanyaye na ce "Ai to, Allah ya bashi lafiya."
Ya ce "Ameen."
Yafi away da tafiya minda Tijjani bamu iya cewa komai ba. Domin ni tunanin fad'i tashin d Aya ambata sun yi nake yi. A hakan Baban Kasuwa ya iso shima ya gama kamun kafarsa da borin kunyarsa. Abin da yake bani mamaki yadda suka fi karkata akan ni naga farinsu fiye da Tijjani ya ga ni. Na fahimci sun riga sun yi nisa a wajen imani da ce wa sai ina son mutum da Tijjani ya taimake shi.
A wannan loakcin mun barji soyayya. Kusan salon gwamna Tijjani ya dauka na wajen ririta ni da mutunta lamarina.
Tuni ya canja wa twins makaranta ya kai su wacce ta amsa sunanta. Aikina kuwa bai hana ni ba. Haka nan na kan yi kunshi amma ba irin na da ba. Domin a yanzu mai kololuwar daraja nake yi. First lady da mukarrabanta kad'ai sai ko Hajiyar da ta yi mini sanadin zuwana gidan gwamnati.
Watanni uku kafin Tijjani ya gane kan ma'aikatar. Cikin sa'a ya samarwa Yaya J da Yaya Rabiu aiki. Ya daga darajar aikin Yaya Salisu. Hatta Yaya Musa da ya zama shasha ya samo masa aikin security a babban asibitin Bauchi. Ya biyawa Anas da k'aninsa Nasiru karatu suka tafi Sweden karatu. Anas digiri zai yi, Nasiru kuwa PhD.
Ba jimawa azumi ya zo, ya tisa ni a gaba da yara muka tafi Umrah da kuma Babah da abokiyar zamanta hadi da Aliyu da matarsa.
Fad'in irin jin dad'in da muka yi ma bata lokaci ne.
Babah Maryo ce ta kasa zuwa inda muke har yau. Hatta Nasiba ta zo yi mana murna. Ta Kuma ro'ke shi ya sama mata aiki duk da a Jos take. Ya mata alkawri zai saka a bata rubuta kati a asibiti.
Domin mijin nata babu. Na kuma san Tijjani zai yi mata wannan kokarin. Domin ma riga da na fahimci shi mutum ne mai saurin afuwa da sassauci. A yanzu haka ya yi amfani da kujerarsa ya fito da Alhji Auta. Ya gyara masa gidansa. Ya mayar da y'ayamsa makaranta. Ya kuma saka masa albashi duk wata.
Ya yiwa babbar y:arsa da take da hankali hanyar samun aiki in tunda ta yi karatu. Kuka ba irin wadda Alhaji Auta bai yi ba.
Lokacin aikin hajji na zuwa ya biya mini ni da shi, da Aliyu da Yaya Ummi. Da Kuma babbar yarsa da suke uba d'aya. Na so ace Ya biyawa Inna tunda itace babanmu bai samu sukunin kai ta ba.
Ya ce zata je amma sai ya kai Gwaggo Umrah ta dawo. Domin ya sani ta taka muhimmiyar rawa wajen dannata a loakcin da shaid'anu da mugaye suka so yin tasiri a rayuwar aurenmu.
Ummi kuwa mutumiyarsa ce. Kafin ya kai kowa Hajj sai ya kai ta a gidan Marina.
Haka muka dunguma ni da Yaya Ummi muka tafi tare da shi.
Duk da yanzu ba a iya cewa komai akanmu akan gidan Marina sai da aka yi yamididin yan dakinmu na ware masa ta kai. Da azumi ya kai Iklma an kasa gane ba dan ni ya kai ta ba,dabida Aliyu ne. Ko wata ce matar.kuwa zata je. Yaya Ummi kuwa ko ba ni ce matarsa ba zai kai ta. Cikin kankanin lokaci sunan Baban Marina ya koma Alhaji babba a wajen yan'uwansa. Ko yaransu ne zasu yi abu zasu ce basu da ta ce wa sai abin da Alhaji Babba ya zartar. Tun ana ganin abin daban har aka saba. Shekarar Bulkachuwa d'aya a matsayin kwaishina ya rushe gidan Marina. Ya yi gini na alfarma na zamani. Kowa part dinsa aka kawata shi, aka zamantar da shi. Kowa anmasa bene. Gefen Dada ne babu bene, gini mai suna hini aka yi. Hatta can ciki inda akace ya zauna da Yabi loakcin auren sai da ka rushe shi aka tamfatsa gini. Gidan Marina ya sake yin fice a Toro. Shi kuwa Juwad g.r.a yake nasa ginin na alfarma. Wanda ha siya da nufin ya saka Nasiba a ciki ya ce ya bawa Yabi halak malak.
Gidansu na Bulkachuwa ma ya sha gyara tunda gini ne mai kyau mai aminci. Gata na ban mamaki yake yiwa magaitda abokiyar zamanta. Koami tare yake kai musu sai abin da baaytasa ba. Haka nan sisters dinsa mata ko wacce ya sama mata abin yi,.ya dauki yaransu ya kaisu makarantu daban daban.
Ta bangarena hankalina ya kwnata domin na daina zullimi akan sha'anin Tijjani. Hatta saka masa idon da na yi akan sha'anin mata yanzu na janye domin aiyukan da suke gabansa bashi da sukunin wannan lamarin. Na murje na ciko. Na mallaki dukkan abubuwan k'awa na ado da kwalliya. Gwala gwalai manya suturu. Malaysia fabrics na Umm Nihla. Mota. Ga yarana suna karatunsu cikin nutsuwa. A yanzu haka cikine da ni na watanni biyar. Husna ta yi shekaru uka.
Ya dankara mana gida mun tare tun bara. Tun lokacin kuma ya dawo da Dada kusa da mu. Part dinta daban. Idan ta gaji sai ta tafi Toro. Haka ifan ta gaimji da Toro sai ta taho wajenmu.
A yanzu kowa Hajiya yake ce mini. Burina ya cika. Na kai Gwaggo Umrah, na kaita hajji. Nazira ta je, su Yaya Salamatu. Mama ta je Umrah. Inna kuwa aikin hajji ta je bara.
Baban Kasuwa da na Tsakiya suma sun je Umrah da azumi. Shi kuwa Alhaji babba ta bakinsu duk azumin duniya tunda muka samu dama a can yake. Sau kuku Ke nan. Duk shekara idan zai tafi zai tafi da matarsa daya. Haka Baabh da abokiyar zamanta.
Kowa ya hakuri da zuciyarsa ya yarda da hukuncin Allah baya canjawa zai ga alheri mai yawa. Babah Maryo da kanmu muka kai mata ziyara bisa umarnin Babah. Ta saka ya gyara mata gidanta. Aka sanya y'aya'n ta a makaranta. Tunda Yaya Ammar ne kawai ya yi karatun mai zurfi. Nasiba kuwa tuni ta samu aikinta tana cikin rufin asiri. Haka nan Tijjani ya yi k'ok'ari an daga darajar Ammar a wajen aiki.
Amma kunya gabad'aya ta hana Baba Maryo sakewa. Umrar bana ma tare Babah ta ce zasu tafi. Hakan kuwa aka yi.
Babah da Bulkachuwa da Baban Marina sun fahimtar da ni yadda saka alheri idan an yi maka sharri na matukar tasiri a dukkan mu'amala mussaman ma a harkar zuminci.
Duk yadda lokaci ya yiwa Tijjani karanci, ina da lokaci na mussaman a wajensa. Da zarar ya shigo gidan zai kashe wayoyinsa ya tisa ni a gaba da y'aya'nsa. Soyayyar nan da nake so bai fasa shayar da ni ba. Haka nan a shimfi'da sai ya tsiyayar mini da ruwan kai tas. Da kaina nasan an yiwa Baban 2 baiwar lafiya da kuzari.
**
Zaune muke a babban falona ni da dukkan yan'uwana da muka taso tare domin a yanzu kowa so yake ace yana kusa da ni. Hatta Maijidda da Nasiba kuwa. A dalilin na haihu sati hudu baya, sai yau na shirya walima tunda c.s aka yi mini. Na Kalli Nazira na ce Adda Nazira dan Allah ki sam mini kiba. Kin ga yadda kika tara teba kuwa?"
Ta ce baki ga Maijidda da Nasiba ba sai ni? Ni maganin rabge tumbi ma nake nema. Na ce "zansa a kawo miki daga Kano."
Maijidda ta ce ni kuma na sanyi".
Na ce "Tom gangariya ne kuwa maganin sanyin".
Iklima da Ubaida suka ce mu dai a kawo mana na gyara kawai".
Na ce "kowa zan siya masa wadda yake so. Kayan surayya masu kyau ne na yarda da su. Sannan albarkacin Anti Kulsum free delivery ne ga duk wcce ta ta siya take zaune a jihar Bauchi. Suka ce Hajiya kina da yawan jama'a".
Na yi murmushi na ce sana'ata ta had'a ni da mutane masu karamci da kyautatawa dan adam. Ba abin da zance da Allah sai godiya."
Daidai lokacin jariri ya tashi wanda ya ci sunan gwamna. Muke kiransa da Halifa.
Na Kalli kaina a cikin yan'uwana na ga nice zarra. Mafi yawansu kuma sun sake samun rufin asiri ne ta sanadina. Mahaifiinmu da mahaifiyata sun sake samun daukaka ta sanadina. Matan gidan da ada suka hade mata kai, aka mayar da ita banza yanzu kowa so yake ya hlga dariyarta. Ko wacce so take ta samu shiga a wajenta.
A sanadina da Tijjani an samu s'aukiin bak'ak'en taadodin da suka yiwa gidan Marina katutu.
Ba'a dinke an zama abu d'aya ba. Amma hassada da jahilci da suka samu gindin zama a gidan yanzu ya yi k'aura.
Dada tana nan gar da ita. Umrah duk shekara. Tijjani ya tsaya mata. Ta kuma rungumi istigifari. Komai na ce mata na gyara zata karba babu inkari. Idan na so nishadi ma a wajen ta nake yini tana d'ora mini karatukan ta masu sanya ni dariya da tuna baya.
Hatta kangire alherina na isarsu. Har yau din nan da Tijjani ya zama attajiri Ina matukar Jin dadin aikina da kuma sana'a ta domin idan a na je na yiwa first lady kunshi makuden kudade take zuba mini a jaka. Idan zan yiwa dangin uwata alheri bana jiran Tijjani. Duk da shima yana iyakacin kokarinsa. Haka nan yadda nake son ganin dakin Gwaggo da kayan ciye ciye haka nake gani, domin bayan siyayyar kayan abinci na duka gida da Tijjani yake yi. Ina warewa na yiwa uwata hidimar da dace da ita. Suma matan gidan na kan yi musu amma ba kamar ita ba. Tunda dukkan y'aya'n k'ofarmu sai da nasan yadda aka yi aka bawa kowa upper aiki. Duk dai k'ananun ma'aikata ne . Amma dai duk wata zasu ji albashinsu. Hatta Yaya Ummi ta samu aiki a woman center tana koyawa dinki tunda ta iya. Sannan Tijjani ya dauki nauyin karatun y'ayanta biyu maza da suka kammala sakandire a jami'ar Ahamadu Bello da take Zaria. Suna Karantar manyan kwasa kwasai domin sosai suke da hazaka.
Har su Maijidda da su Saratu.
Nazira kuwa koyarwa take yi tunda ta cigaba da karatunta tunda mijinta dan boko ne.
Amaryar Yaya J a gidan radiom Toro ta samu aiki.
Tuni ya farfado. Maijidda ce a BAUCHI a amaryar na Toro saboda aikinta.
***
Waya muke da Nazira akan maganin rage tumbin ya ya isa gareta. Maimakon ta yi mini godiya sai sababi take yi mini tana ce wa "Yabi ban ga Malaysian Fabrics a ciki ba. Ban ga mayukan Oriflame da maclen da kika mini alkawari ba. Ban ga supplement din GHT na FASEELAT ba. Haka nan babu yajin Annur".
Na yi dariya na ce "Adda Nazi ke ce kadai kike gatsa Yabi! Ina ce ke shaidace bayan hajjin da na yi ina ciki, na yi a yanzu kan girmana ma?
Ta ja tsaki ta ce "Ba zance Hajiyan ba. Yar mitsitsiya da ke sai son girman tsiya.".
Na yi dariya na ce "To kwantar da hankalinki gobe Aish lame zata zo garin zata tsaya ta gaida Dada zata taho miki da su. Kinsan wannan Yaya Ummi aka aikowa ta Jos." Ko ma na baki lambarta sai ki zabi duka abin da kike so yayata".
Ta yi dariya ta ce "Yanzu na ji magana. To sai anjima hakima ta Yaya Bulkachuwa ".
Na yi dariya na cigaba da karatun littafim *Ya za'a yi?* da nake yi a waya na marubuciya Binta Abbale. Labarin ya ja hankalina. Tuni na tura kudina ina paid group din ta dan na ji yadda za'a warware wannan dambarwar.
Ina kwance kan gado ya shigo yana sab'e da Halifa. Na kalle shi ya zama CIKAKKEN mutum mai cike da Kamala. Tuni na fara hango shi a matsayin gwamnan gobe. Wato jihar BAUCHI ta jima tana yin zatan gwamnoni dogaye farare masu farar aniya. A fili na ce "Allah ga Baban 2 a cigaba da yi masa afuwa da rahama. A Buda masa kirijinsa a bashi ikon sauken nauyin jama'a babu gajiyawa. A cika zuciyarsa da son Hajiya Yabi da tausayinta da mararinta babu gundaura."
Ya kwashe da dariya sosai ya ce "Ubangijinma sai kin ce masa ke Hajiya ce?"
Na ce "To ai tunda zuwa gabar ne sharadin zama Hajiya ai tuni ita ce tun banzo duniya ba"
Ya rungume ni ya ce "Hakane Hajiya little. Ina matukar farinciki da ya burina ya cika na kai ki gabas Hajiya. Dukkan burikan sun cika fatana Allah ya cigaba da bani lafiyar da zan ciyar da ku halali na jiyar da ke dad'in duniya dan ki gane ba komai a gabana da ya wuce ki idan kika cire Babah".
Na langabar da kaina a jikknsa na ce "Ina godiya. Ubangiji ka so Tijjani, ka karba daga gare shi. Ina godiya bisa kaddara mini ya zama mijina, ina fatan ka tabbatar mini da shi har a aljanna."
Ya dinga Ameen dear Hajiya. Allah ya cigaba da iya miki, ya mayar da makiyanki fadawanki, ya shirya mana zuriarmu. Muddin rai ke ce tauraruwar zuciyata."
Daidai lokacin naji dirin mota tabbacin Yara sun dawo, daga school na yi maza na zame nasan Hamim idan bai ganni a falo ba sai ya biyo ni daki.
Ilah kuwa ya murda kofa ya shigo. Ya ce "Baban 2 Sannu da gida".
"Sannu dai Baban Marina. Tijjani ya fad'a da murmushi.
Ya iso gare ni ya rik'e hannuna ya ce "Ammi mun dawo".
Na ce "To sannu a je a cire uniform a yi wanka tunda kun yi sallah a school".
Ya ce "To ya juya zuwa dakinsu."
Yana fita Hanif ya shigo. Ya bude baki ya ce "Baban 2 yau baka je ofis ba?"
Ya ce "Hutawa nake yi Baban Bulkachuwa".
Ya rik'e baki ya ce "Gaskiya Baban 2 ba'a haka. Babu kyau fashi tamkar tauye mudu ne. Mai tauye mudu kuwa d'an wuta ne".
Ya janyo yaron jikinsa ya ce "Na gode da tunasarwa Babana. Zan kiyaye".
Ya sake shi ya matso gare ni ya dafa ni ya ce "Ammi sannu da gida ina Husna my dear?"
Da murmushi na ce "Tana wajen Dada! Ka je ka yi wanka sai ka je ka ganta."
Ya ce "Tom". Ya ja hannun Halifa da yake zaune a k'asa yana wasa da kayan wasan da Tijjani ya ajiye masa. Ya juya ya tafi amma Halifa ya saka kukan sai ya dauke shi. Haka ya dawo ya dauke shi ya tafi da shi. Ni mamakin yadda Halifa yake banbance shi da Hamim nake yi.
Kafin na yi magana Bulkachuwa ya ce "Wato Hamim ba k'aramin miskili ba ne. Ke ce kad'ai idan bai ganki ba zai damu.
Amma daga ni har yan'uwansa baya damuwa da rashinmu. Gara ma ya damu da Hanif".
Na ce "Ai Hamim danja ne, ance ni ya gado, ni kuwa ai mai son jama'a ce. Mussaman yan'uwana ".
Ya ce "Hakane shima zai warware. Allah ya shirya mana su gabad'aya.
Na ce "Ameen dear".
Da daddare daga ni har yara muna wajen Dada ana ga sharholiya cikin farin ciki ya shigo ya gaishe ta a tsaitsaye.
Ta ce "Alhaji Shehu daga tsaye yau?"
Ya ce na gaji ne Dada. Ina son na kwanta.
Ta ce "To babu laifi. Mu kwana lafiya."
Ya tafi Yara suka bi bayansa a guje. Ta kalle ni ta ce "Haba Hajiya tashi mana ki bi bayansa. Kya bar shi da yara?"
Na ce "Rabu da shi Dada ai yaji na yi masa. Yau tun safe bai kira ya ji lafiyata ba. Na k'ira bai d'aga ba".
Ta dauki salati ta ce "Haba Hajiya kinsan hidimarsa mai yawa ne.
Ban da abin ki irinsu Shehu ai ba'a samunsu da sakwa sakwa. Tashi ki je ai ki fahimtar da shi cikin hikima kin ji Hajiya Yabi"
Na yi dariya na ce "Tom".
Na isa falon na tarar da shi da yara akan dining suna cin abincinsu.
*
Muka kwanta ya ja ni jikinsa yana.ce wa "Sarka mai rikicin gangan Hajiya little".
Na share ya ce "wai ke ba zaki girma ba. Kullum sai kin samo laifin da zaki jingina mini? To ki huce komai na yi ma, ba da gangan ba ne. Ki yi hakuri kin ji My Hajiya love?"
Dariya ta k'wace mini na ce "Na lura dai yadda kake nacin ce mini Hajiya har da gayya"
Shima cikin walwala ya ce "To ba burinki ke nan ba? Zan ta ce miki Hajiya. Kuma duk shekara sai na raka ki umrar azumi tunda Annabi ya ce tamkar aikin hajji ce. Kin ga sai ki ta sabunta Hajiyar ta ki".
Muka yi dariyar Jin dad'i Muna fad'in Allah mun gode maka ka cika ni'imarka a garemu".
*Akwai garin (moringa) zogale ma mussaman dan masu gidaje*
*Akwai maganin sanyi sadidan*
*Akwia kayan gyara na mussaman daga Chad da sudan*.
Alhamdulillah!
Post a Comment for "BAKAR TA'ADA BOOK 4 Complete Hausa Novel"