CANJIN RAYUWA Book 4 Complete Hausa Novel
Chanjin rayuwa book 4
1⃣Saboda ta samu canjin rayuwa, daga jahilci zuwa ilimi, daga rashin tarbiyya zuwa tarbiyya, daga mara mutunci zuwa mai mutunci. Sauda, da farko nayi wa Mimi wannan auren ne don in quntata mata, in qona mata rai, kamar yadda ta qona min. Amma daga baya tunani ya shige ni, nayi nazarin dalilin wannan auren zata iya samun canjin rayuwa. Ismail zai iya bata ilimi na addini wanda ta rasa daga gareni. Sannan, ilimi zaisa ta zama mai tarbiyya ko dan yaya, tunda anbar shiri tun rani. Dalilin da yasa nace kar kuje gurinta, nima nace kar su sake nemana, sbd idn bata tare damu, zata fi samun tarbiyya. Shi ba zaiji shakkar mu ba, ko tsoron mu in tayi abin hukunci. Kuma yanda na lura dashi, bashi da shakka, kinga kenan ba zaiji tsoron duk wata barazanar ta ba. Haka kuma ba zamu taimaka musu da kudi ba, sbd shi kansa banason mu kashe masa zuciya, ya kasa neman na kansa, ko yaushe yana jiranmu. Haka kuma ita kanta rashin taimaka musun zaisa ta saba da Rayuwar babu, wadda bata sani ba ada. Yanke alaqa dasu shine zaisa ita da shi suyi abinda ya kamata.
Hajiya sauda ta sauke ajiyar zuciya, "Na fahimceka sosai Alhaji, saidai nayi wani kuskure daya. "ya kalleta, na tura musu dubu dari. "karki damu, saidai karki sake tura musu kudi. Da zaki iya ma ko wayarsu karki sake kira. Ta danyi shiru tana nazari. Ya katseta, kar kisa ma kanki damuwa, nayi miki alqawarin bibiyar miki labarin duk halin da suke ciki. Ta tsura masa ido, a cikin qwayar idanunsa ta tabbatar da abin da yake fada. Tace, shikenan Alhaji. Allah yasa mu dace. Yace, "Ameen matar qwarai". Ya kama hannunta, "nasan ranki ya nutsu da yaron, kuma nima na fahimci cewa, yaron mai hankali ne. "Sukayi dariya. Yace, kinsan menene sauda? Tace a'a. yace, "Ni kaina ina cikin matsanancin kewar Mimi. Na sani sarai tunaninta ne ya hana ciwwonnan sauka. Tace, nasan za'ayi haka, amma tunda kanada wannan qudurin, wajibinka ne ka daure, ka jure, ka kuma kauda kai, sannan mu hada da Addu'a, Allah ya taya mu. Yace, Ameen ya rabbi. Ynxun kuma na samu natsuwa tunda Allah yasa kin fahimceni. Ranar nan suka yini suna qoqarin kyautata ma juna.
2⃣Haka itama Mimi tayi ta jinya, yaya Amina da Ismail suna matuqar kula da ita. 'yan uwan mamansu na Daura sunzo, sun duna jikin Mimi, sannan sun kawo musu kudin gonarsu da aka saida. Don haka shirye-shiryen tafiyar Ismail ya kankama. Haka nan 6angaren Mimi, zuwa ynxun Ismail yayi nasarar saka Mimi ta fara sallah dole, ba don ta so ba. Yawan nasiha da nacinsa ya sata sauraronsa. Ya nuna mata yadda zatayi sallah, kuma ya dauki nauyin yi mata akwalla. Ranar daya fara tsananta mata tayi sallah da kuka tayi sallar. Da farko ma bata yi ba, sai da yace shikam ba za yayi jinyarta ba, matsawar ba zata yi sallah ba. Ya nuna mata shifa tafiyarsa zaiyi. Yaya Amina ita ma cikin son ta tsorata ta tace, in ko ka tafi, nima zaman me zanyi? Kinga kenan saiki zauna babu mai jinya, ba mai kula dake. Tana kukan nata tace, yayi mata alwalla. Tun daga ranar, duk lokacin sallah in yayi, sai ta yita. Wani abin da yaba Mimi al'ajabi shine tunda ta soma sallah, sai ta samu kanta cikin wata natsuwa, ta kuma qara imanin cewa sallah tana kusanta bawa ga ubangijinsa. Haka kuma lokacin da yace zai dinga koya mata gajerun surori, bata qi ba sbd sallah.
Kwanci tashi har taci wata daya da sati daya a asibiti. Lokacin ne kuma da Doctor din dabyayi mata dori ya dibar mata zaizo ya duba in dori yayi kyau, sai ya kwance. Ranar litinin da misalin qarfe goma na safe, likitan suka shigo shida doctor salis. Kallon qafafun nata kawai yayi, yace inasa ran cewa dorin yayi kyau. Zan kwance shi ynxun sai ku kaita ayi mata hoto, sai ku kawo mu gani. Ismail cikin murna yace, Alhamdulillahi, dama na gaji da zaman asisibitin nan, har ita ma khadijan ta gaji ko?. Ya fada tare da kallonta. Mimi ta kalli likitan, kenan in hoton ya nuna cewa, dorin yayi za'a sallameni ne? Likita yace, eh, to ku daiyi hoton mu gani. Bayan an kwance tana ta shagwa6a, ta qanqame yaya Amina. Likitan yace, a kaita hoto ynxu. Ismail ke tura ta a kujerar tura marasa lfy suka nufi gefen hoto. Yaya tana jere da shi suna magana. Yace, "Yaya Allah yasa hoton babu tsada sbd Kinsan fa babu sauran kudi, gashi kudin dakinmu dana sake biya ya qare. "Wai saura nawa ne ma kudinnan da aka ajiye sbd tafiya? Yace "ta6" ai baifi saura dubu goma ba acikin dubu hamsin din dana ba Mahmud don kar in kashe, amma duk sun qare. Tace, ai dama zara bata barin dami.
Barkanmu da sallah sis
[17/09 1:18 pm] Inna: Canjin rayuwa
5⃣A qofar gidansu yakeyin wankin, amma yanajin nauyin shanya kayan Mimi a igiyar waje, sbd duk qananan kaya ne matsattsu. Sannan har pant din ta yake wankewa, don haka sai ya daura igiya acikin zauren kusa da qofar dakinsa yana shanya kayanta a gurin. Wani lokacin ma sai ya jira sun dan sha kadan ya kwashe, sbd yaran Gidan marasa ji, wani sa'in suna zubo da kayan qasa. Yau ma daya gama wanka, yayi shirinsa zai fita, sai ya kwashe panties din da vests yaje ya shanya su kan akwatunanta, ya kunna musu fanka, sannan ya kulle qofar ya nufi gidansu Mahmud. Hirarsu kullum bata wuce ta tafiya. Mahmud yace, Ismail kasan Rabi'a ta daga hankalinta akan batun tafiyarnan? "saboda me to?" Inji Ismail. Mahmud yayi 'yar dariya, wai tana tsoron kar in hadu da wata acan in manta da ita. Nace ta daina wannan tunani, tana damun kanta bayan anyi mana baiko. Sai tace, to yaushe zan dawo? Nace mata ban san lokacin ba. Shine take fushi dani. Ismail yace, mata kenan 'yan rigima. Ni baga wannan shagwa6a66iyar Yarinyar ba. Lokacin da zan fito fa kuka takeyi, wai bazan fito ba. Mahmud yasa dariya, to ba yaya Amina tananan ba? Yace bata nan, tana gidansu. Tazo dai da safe, amma ta koma sbd batajin dadin jikinta. Kasan Allah, Mahmud na gaji da zaman asibitin nan, ita kuma gata da shegen son jikin tsiya. An ce, ta dan dinga dan takawa, amma taqi. Shiyasa na barta ita kadai don tayi zuciya ta motsa.
Mahmud yace, Ismail saidai fa kayi ta haquri, domin yarinyarnan cikin shagwa6a ta taso, hakan ya zama jinin jikinta. Ai ma kaci nasara tunda tana cin duk abin da aka dafa aka bata, sannan ta amince zata zauna daku. Ismail yace, ni damuwa ta ynxun, inda zan barta in zamu tafi. Mahmud yace, inda lafiyar ta lau ne, da sai mu tafi tare da ita. Ismail yace, kasan Allah, ko lafiyarta lau bazan iya tafiya da ita ba, haka kawai taje ta dameni. Tunanina in barta gurin yaya Amina da mijinta, tunda suna da dakin yara, da kuma dakin da mahaifiyarsa da take ciki kafin ta rasu.
6⃣Mahmud yace, hakane, kai ai yaya Amina tanada zumunci. Nasan ma ba zata qi ba. Ismail yace, ba zata qi ba insha Allah. Yaya Amina, aita zamar min uwa saidai ince Allah ya bani ikon yi mata biyayya. Mahmud yace, Ameen, ai tafiyar tamu ma tazo. Naji yana cewa nan da qarshen wata, sati uku dai a taqaice. Ismail yace, tabbas tafiya tazo, Allah dai yasa a sallamemu kafin ranar. Kai ni gobe ma zan samu likitan ince masa sallama kurum nakeso. Mahmud yace, kafin su sallameku, ya kamata itama ta dan taka su gani. Matsa mata ai zakayi. Sai daf da magriba sannan suka rabu. Gida ya koma ya kwashe kayan shanyarsa, sannan ya daukar mata wasu kayan ya nufi asibitin. Yana sauka ana tada sallah. Don haka sai ya bada ajiyar ledarsa cikin wani shago, ya shiga sallah. Har zai bari sai yayi isha'i, sai kuma ya tuna itama tana buqatar yin sallar. Zaune ya same ta akan gadonta, taci kuka ta gode ma Allah. Tausayinta ya kamashi, amma sai ya dake tamkar baiga fuskarta ba. "Muje kiyi alwalla! " Tayi banza dashi. Yazo zai dauke ta zuwa bandaki, tace, ka barni, ka tafi abinka. Dama nasan dole ka gaji dani, iyayen da suka haifeni ma sun gaji dani, sun gujeni bare kai da suka jona maka ni? Banga laifin ka ba. Amma meyasa kasa nayi maka alqawarin zama tare da ku bisa sharadin cewa zaka kula dani, sai gashi tun kafin mubar asibitin ka gaji? Nasan kaida 'yar uwarka kuna dawainiya dani, amma yadda ka nuna nima 'yar uwarka ce, na zata za'a dan jima kafin in gundureku.
Ismail yadan tausasa murya, cikin sigar lallashi yace, wai waya fada miki cewa, mun gundira dake ne? Ni kin bani haushi ne yadda kk qi kidan taka ko sau daya ne. Kuma khadija wanki naje nayi miki, ya sake matsowa kusa da ita daf, yasa hannu ya dago fuskarta, cikin wani salo ya kira sunanta, khadija! Ta dago jajayen idanunta ta kalleshi. Yace, "Wlh baki gundiremu ba, kuma bamu gaji dake ba, kuma ke 'yar uwarmu ce. Tace, nidai nafiso ka bani saki na, ka tafi abinka. "Ya dora yatsansa akan la66anta, "shhhh, ki daina cewa haka mana qanwatah. Kiyi haquri! In kaiki kiyi alwalla ko? Taqi magana. Da qyar ya lallasheta, sannan ya kaita alwalla. Bayan isha'i ne tana cin cake da fanta, yace, kinji tafiyarmu zuwa qarshen wata ko? Tayi takwa-takwa da fuska "to ni kuma ina zaka barni? Ya kwaikwayi muryarta, shine nakeson muyi shawara dake.
[17/09 1:18 pm] Inna: Canjin rayuwan
3⃣Mimi, wadda ake turawa tana jinsu, duk qarma-qarmar da yakeyi tana jinsu, kuma ta sani. A zaton ta ma da kudinta akeyi mata komai, har suka qare ya shiiga nasa. Tace, to yaya Amina su sallamemu mana tunda dai babu kudi. Yaya ta kalli Ismail, "Nima nawa tunanin kenan, ko ya ka gani? Ismail yace, bari dai ayi hoton mu gani. Allah yasa dai kudin babu yawa. Ynxun ma tunanina ko zan barku anan inje in amso ragowar na hannun Mahmud. Yaya tace, muje dai, in kaji kudin, sai ka tafi. Dubu shida da dari shida ne kudin hoton, don haka dole ne ya tafi ya amso ragowar kudin, kafin ya isa, saida ya kira layin Mahmud din, don haka mai acha6ar da ya kaishi, shine ya dawo dashi. Don haka suka biya akayi musu, sannan suka amshi sakamako suka koma. Sai sha biyu sannan likitan ya dawo ya duba, yace Alhmdlh, kuma tana da jiki mai kyau. Don haka zata iya soma koyon tafiya. Ismail ya kalli doctor. Ismail ya kalli Doctor salis yace, za'a iya Sallamar mu? Sbd gsky duk abinda muke dashi ya qare. Doctor salis yace, karka damu malam Ismail, kayi qoqari sosai. Ba duka namiji za'a samu ya tsaya kan matarsa haka ba. Mimi ta dago, ta kalli Ismail, idanun ta da alamun tambaya. Sai yayi murmushi, ya kalli likitan, ai yaya baya kasa dawainiya da qanwarsa. "Take likitan ya kalli Mimi, sai ya tuna 6aran6aramar da yayi, don haka yace, "oh na manta hakane, yaya ne ashe. "
Yammacin ranar, Ismail babu yadda baiyi ba da Mimi ta dan soma takawa, amma taqi, sai kuka takeyi wai ba zata iya ba. A qarshe haushi ne ya cika Ismail ya fita waje ya zauna akan benci. Tunanunnuka ne kashi-kashi suka addabeshi, yana mamakin yadda yaketa neman layin Hajiya sauda, amma baya samu itama kuma ta daina kiranshi. Sannan yau sati uku kenan da ita hajiyar ta sallami Mahmud daga koyar dasu hasana. Ko yaushe in Ismael yayi ma Mahmud wannan qorafin, sai yace, karka damu ni dama ko basu sallameni ba, dole in barsu tunda kaga karatu zamu tafi. Game da rashin waiwayar 'yarsu kuwa ka qara haquri.
4⃣Gashi yana tunanin ina zai samu kudi, ko ba don ciwonta ba, ko don sbd tafiyarsa. Sannan in an sallamesu, ina zai ajeta? Domin gsky bai kyautu ba yasa ta dakin zaure.Duk bama wannan ba, gurin wa zai barta? Yana jiyo ta daga ciki tana magana cikin shagwa6a, "to kazo mana, ka kamani zan kwanta ne fa kaji! Shiru yayi mata, sai dai zuciyar sa tana tambayarsa meyasa ynxun Mimi bata kiran sunansa? Bata cewa, Ismail, bata cewa, malam. Nauyinsa take ji, ko menene? Oho! Tayi, har ta gaji tayi shiru. Saida yaji kiran sallar la'asar, sannan ya shiga dakin. Har lokacin idanunta da hawaye. Ya kalleta, sai kuma ta bashi tausayi, yace, khadija! Taqi kallonsa. Ya gane alamun tayi fushi kenan. Yace, zan yi miki alwalla ne, nima zan tafi masallaci. Ta kumburo baki, to ka kiramin nurse Ramatu. Inaso inyi fitsari ne. Yace, ba zan kira wata ba. Muje in taimaka miki. Nurse dinnan fa da kkga tana kulaki, ina bata wani abu. Kwanakin nan da bani dashi, ban bata ba, kinga tana shigowa? Mimi tace, to fa, kai namiji ne, shine zaka taimaka min? Banida lokacin 6atawa khadija, sallah zanje. Menene zaki 6oyemin wanda ban gani ba? Kuma tunda ni matsayin wanki nake, ai ba wani damuwa. Ta zaro idanu, me ka gani? Bayan yaya Amina ce takemin komai. Da zaka ce... "kafin ta kai qarshen maganar, har ya dauketa cak ya sakata a toilet din. Ya zaunar da ita a kan kujerar da yaya Amina kan zaunar da ita in zatayi mata wanka. "sai kuma me zan taimaka miki dashi? " ka fita nidai kawai! Zaki iya yin komai harda fitowa? Tace, nidai ka fita! Murmushi yayi sannan ya fice, "to karki dade, kusan mintina hudu tace, "to kazo ka fito dani! Tayi maganar, ranta a 6ace. Ya shiga, inyi miki alwalla? Ta turo baki, "ni nayi abina. "A qasa yayi mata shinfidar sallah, yace, kiyi a qasa, tunda an kwance maki. Yasa mata hijabin sannan ya fita. Bayan ya dawo ya soma hada kayan da yaya Amina ta cire mata da safe. Yace, zanje gida inyi wankinmu, ya dan taru, sai kuma inyi wanka. Ta 6ata rai, cikin shagwa6ar ta tace, ni kuma ka barni da wa? Yace, da Allah mana! Dama shine mai tsarewa. Kinga kuma kinji sauqi babu laifi ko? Ya qarasa cikin sigar lallashi. Ta matse kafada cike da shagwa6a, idanunta suka soma zubo da hawaye, nidai bazan zauna ba. Ya ce, (cikin takaici ) karki zauna, inkin gaji da zaman Asibitin kidan taka mana, ki yarda kidan taka ko a sallamemu, amma kinqi. Ya dauketa cak ya dora ta akan Gado. Sai na dawo. Bata dai ce komai ba, shi kuma yayi tafiyarsa.
[17/09 1:18 pm] Inna: Canjin rayuwa
7⃣Ta aje cake din hannunta akan gado, "Nidai ka tafi dani mana." yace kwantar da hankalinki, wannan ba abin damuwa bane, ga yaya Amina, sai ku tare, inkin sauqi sosai, in nazo sai mu tafi. Tace, to ka fadawa yaya Amina dinne? Yace, ban fada mata ba, amma nasan cewa ita babu matsala. Tace, shikenan yaya jikinta fa? Yace, da sauqi, dukda banbi ta gidanta ba. "Ya ciro wayarsa, bari in kira Abban su saddam ya bata mu gaida ta. "sun gaisa da abban su saddam, sai ya tambayi mai jiki. Abbansu saddam yace, gatanan tanata rawar sanyi, ta qudundune, ta dai sha magani. Ismail yace, to ka gaisheta. Khadija ma tanayi mata sannu. Abbansu saddam yace, zataji. Ya kalli Mimi, kinji har ynxun jikin ko? Tace, Allah warki yaya! Allah ya bata lfy. Washe gari yaya bata samu zuwa ba, sbd jikin nata. Ismail yace, to yau yaya zamuyi da wanka? Ko in miki? Ta zaro idanu, tana kallonsa, a ranta tace, shi wannan nufinsa dole sai yaga tsiraici na ne? A fili tace, na haqura sai taji sauqi. In tazo zatamin, harda gashina zata wankemin, yayi datti, duk ya dameni. Yace, wai meyasa baki yarda dani ba, sai kace zanyi miki wani abu. Ki tsaya ko gashin ba sai in wanke miki ba? Naga yadda tayi miki ranar nan mana. Tace a'a karka samin ruwa a kunne. Ni saloon nakeson zuwa. Yace to yau kidan taka ne mana khadija. Kinga basu so mu tafi da wata matsala ne. Da sunga kindan taka zasu sallamemu, sai in kaiki duk inda kk so. Ranar dai da qyar ya samu ta dan taka, daya biyu yana sagale da ita, sai ko ta fada jikinsa. Wani iri yaji, tsigar jikinsa ta motsa. Yayi mamaki, bai ta6a jin haka ba aduk irin daukanta da yakeyi mata a cikin wannan jinyar. Cikin sauri ya dagota daga jikinsa, muryarsa a sarqe ya dago ta, "kin cika ragwanta, to zauna kidan huta.
8⃣Cikin sati daya, mimi tana dan fita tare da taimakon yaya Amina don taji dan sauqi ta dawo, da kuma taimakon uban gayya, Ismail. Burinsu lokacin a sallamesu, domin basuda kudi a hannunsu. Ranar litinin kuwa Doctor salis da lukman, likitan da yayi mata dori suka tabbatar ma da mimi sallama. Ismail yayi murna tamkar dan kurkuku a ranar daya fito. Duk sunyi murna sosai. Yace, ma yaya Amina ta shirya kayansu, shi kuma zaije ya dan karkade dakinsa. Yaya tace, ina zata? Gidanmu zamu wuce tunda mun riga mun sanar da Abbansu saddam. Yace da inason indan gyara mata dakin na Gidanku, tare da dan sa mata abin kwanciya kafin dai mu wuce. Tace, hakane. Tare da Mahmud suka share ko ina na dakin sannan suka dauki shatar tasi zuwa asibiti. Likitoci da Nurses sunyi masu murna da barin asibitin, nan ne ma Doctor salis ya basu tabbacin cewa, duk lokacin da wata bukatar taimako ta taso, to qofa a bude take su tunkareshi. Yaba Ismail katinsa mai dauke da lambobinsa a jiki. Ismail ma bai qwauron baki ba ya fada masa cewa, shi zai tafi karatu ne a madina, amma duk abinda ya taso ga yaya Amina nan. Doctor salis yayi masa fatan alheri, tare da samun nasara.
Zainabu tana zaune a bakin gadonta da 'yar rediyo a hannunta, tana sauraro. Ta babansu ce ta dauko lokacin da zata dawo gdn Alhajin bayan barowarta daga asibiti, sosai rediyon ke debe mata kewa, da shirye-shiryensu, musamman wanda suke karanta littafin hausa. Da ta qagara taji wani littafi da ake karantawa, sai ta samu bushira tana ce mata ina zata samu littafai? Bushira tace mata, sai dai na haya. Wannan ne mafarin karance-karancen ta. Kuma suna debe mata kewa don tana cin karo da matsalolin da suka zarta nata. Kuma tana qaruwa sosai. Don haka sai tayi haquri ta dangana, ta kuma ci gaba da kai ma Allah kukanta. Shi kuma Alhaji lawal bai canza ba, saima abinda yayi gaba. Hakanan wani abin dake damunta shine tunda ta dawo gidan batayi al'ada ba. Saidai bataji wani canji a jikinta ba. Tsoronta daya, kar dai wani cikin ne ta sake samu, domin gsky ba tada burin hada zuri'a da Alhaji lawal, sai dai masoyinta Ismail. Kullum cikin sa take, duk da wata zuciyar tana fada mata cewa, Ismail yayi mata nisa. Amma bata debe tsammani ba tunda tana Addu'a.
[17/09 1:18 pm] Inna: Canjin rayuwa
9⃣Haka rayuwa take, dama idn kace tukunyar wani bazata tafasa ba, taka ko dumi ta bar yi. Na fadi haka ne sakamakon gani halin da Na'ima take ciki, Ga ta kwance cikin halin laulayin ciki, amma shi ko a jikinsa. Gashi irin crikinnan ne mai aman tsiya. A qarshe ma da yaga ba zata yi masa wani amfani ba, sai ya yaye zaman gdn. In ya fita tun safe sai dare. Bata sanin shigowarsa, sannu bata hada su. Ganin abin yana qara gaba, ta daga waya ta kira momy tace mata, "ki fada masa zanzo in maido ki nan gida gurina, tunda daddyn ku yana katsina ba zaisan kina gidan ba. Washe gari da sassafe kafin ya fita, Na'ima da bin bango takai saman Abbas, ya fito cikin shirin fita ya ganta sharkaf a kwance a falo, cikin tsawa yace, ke! Ki fita a falona banason qazanta, karki sake kiyimin amai anan. Cikin numfarfashi tace, don Allah ka kaini Gida, su kaini asibiti. Yace, ba zaki haumin mota ba, saidai in ki kira su, suzo da tasu, su daukeki, su 'yan gidan naku. "yace ke sauka muje zan rufe gefena. Tace, to don Allah ka kiramin su. Yace, banida lambar kowa a Gidanku. Qiri-qiri yaqi kiran su sam, sannan ya tasa qeyarta har dakinta ya fice abinsa. Ita ce ta sake kiran momy ta fada mata komai. Momy tace, gatanan zuwa.
Gidan aminiyarta Nana ta soma zuwa, ta karanto mata komai. Nana ta sa6i mayafinta tace, muje Gidan uwarsa domin lallai sai tasan halin da ake ciki, in yaso ta jawa danta kunne. Momy Nafisa tace, shiyasa na biyo ta gurinki, don nasan dole zaki kawo shawara mai amfani. Cikin motar Momy Nafisa suka dunguma zuwa gdn minister. Saida masu Gadi sukayi waya cikin gdn bayan sun fadi ko su suwaye, sannan aka basu izinin shiga ciki. A falo aka dauke su. Sunfi qarfin minti sha biyar sannan masu aiki suka kawo musu abinsha. Cikin isa da cin magani, Hajiya Bilkisu ta sauko gurinsu, dai-dai take kallonsu. Hakan yasa su momy Nafisa yin dari-dari.
1⃣0⃣Hajiya Nana ce tayi qarfin halin cewa, Hajiya dama abinda ya kawomu, qara muka kawo miki, qaran Abbas. Sai sukaga tayi wani murmushi, wanda ba zasu iya fassara shi ba. Hajiya Nana taci gaba da cewa, tunda muka kai yarinyarnan banda wulaqanci da cin mutunci babu abinda take fuskanta daga gareshi. Gashi ynxun tana fama da laulayin ciki amma yaqi ya kaita ko asibiti. Momy Nafisa tace, kuma banda diban matan banza babu abinda ya... "Hannuwan da Hajiya Bilkisu ta daga shine ya dakatar da Momy Nafisa. Cikin matsanancin 6acin rai, Hajiya Bilkisu tace, ina zaton kun manta alaqar dake tsakanina dashi ne, kuka zo kuna aibanta shi a gabana. To bari in tuna muku, shine dana na farko, nasan dukkanku kunsan zaqin soyayyar dan fari ko? Ta miqe tsaye, wato ku ga masu 'ya ko? To ni kunsan abinda 'yar taku tayiman da qawayena? Taje daf dasu ta zauna akan hannun kujera, in baku sani ba, inason kuje ku tambayeta.
Hajiya Nana tace, tayi mana bayani, kunzo kun buga qofa bata san cewa ku bane, tayi zaton ko Abbas ne da matan da yake kawowa, tunda yana zuwa dasu harsu kwana. Ranb Hajiya Bilkisu ya sake 6aci, ta nuna Hajiya Nana, "kece lauyar Na'ima? Watau in shine sai taqi bude masa gidan, don tana taqama gidanta ne ko me? Momy Nafisa ta tausasa murya, ba tana nufin wai don Gidanta bane, kinsan dai kishinmu na mata, ko ke da girmanki ba zakiso mijinki ya shigo miki da matar banza cikin gidan aurenki ba ko? Hajiya Bilkisu cikin tsawa tace, don Allah ku saurara min, ya kawo mata dubu ciki gidan, ba Gidansa bane? Ko da kudinta yake bin mata? Ba Kuma sammata zunubin za'a yi ba. In bata iyawa ga hanya nan ta fita. Yarinyar da bakuyi mata tarbiyyar arziki ba sai rowar tsiya. Naje nida qawayena tayi mana rowa. Haka yara da suka je ko dan turare ta gagara basu. Sbd haka shi kansa bakusan abida take masa ba. Don haka ya kamata ya nema, lokacinsa ne. Ku fita a Gidana! Kuje kukai 'yarku asibiti, ko nawa aka caza zamu bada albarkacin danmu da take dauke dashi.
[17/09 1:18 pm] Inna: Canjin rayuwa
1⃣1⃣Momy Nafisa tace, kin bani mamaki, da sunan wasa ban zace ki ahaka ba. Hajiya Bilkisu tace, nafi nan, in dai akan yarana ne. Haka kema ban zaci 'yarki bata samu tarbiyya ba. Hajiya Nana tace, zo muje! Kuskure dai anyi shi tunda aka basu aure. Hajiya Bilkisu tace, Eh kuje, bazan takura ma dana ba, ya mori quruciyar sa da lafiyarsa. Haka dai aka rabu ana fadawa juna magana. Gidan Na'ima suka dire, inda suka dauke ta zuwa asibiti. Kai tsaye Gado aka bata sbd halin da take ciki. Momy Nafisa ta kira Alhaji bashir ta fada masa cewa, an kwantar da Na'ima a asibiti, kuma an tabbatar musu da cewa, tana dauke da juna biyu. Daganan bata fada masa komai ba. Lokacin data yo wayar, Alhaji suna zaune a babban falo, shi da saudar shi da kuma yara. Nan suka shiga murna kamar ance ta haihu. Yace, abata wayar. Momy tace, tana varci. Yace, ko inzo in duba jikinta? Tace, a'a kayi zamanka Alhaji. Jikinta da sauqi. Kasan dama shi ciki, in an dauka, sai an sauke kafin a samu lafiya gar-gar. Yace, haka ne. To, zamu kira in ta farka. Sauda tace, bani mu gaisa, suka gaisa. Tayi mata murna, tare da fatan samun sauqi. Bayan sunyi sallama ne, sauda tace, al'amarin Allah kenan, mai rayuwa cike da canji, da kuma launi kala-kala. Dama rabon a gurin Na'ima yake, shiyasa Mimi ta bijire. Yace, hakane. Allah ya nuna mana daidai ya bamu ikon bi.
Yace, Ameen. Ta danyi jim, ita kuma Mimi ko menene labarin ta? Oho. Alhaji yadan runtse ido, sannan yace, tana samun sauqi insha Allah. Allah yasa, inji Hajiya sauda. Kwanan Na'ima uku a asibiti sannan aka sallameta, suka wuce Gida. Abbas dai baizo ba, amma Hajiya Bilkisu tazo ta kuma biya kudin komai. Shi ko minister baisan komai ba, saida Alhaji bashir ya kira shi yace, kai zanyi wa murna ko juna za ayi wa murna? Minister yace, tame? Na'ima tana dauke da jikanmu. Ba ka samu labari bane? Cikin murna minister yace, bani da labari. Kasan yau kwana na uku bana qasa. Ynxun haka durowa ta kenan, ina filin jirgi. Kaine mutum na farko da na amsa wayarka. Nayi murna sosai, kuma naji dadi qwarai. Amsarka kuma ni za'a yiwa jika. Domin kai ka dauki dan Gidan Abba. Suka sa dariya, sannan sukayi sallama. Cikin murna minister ya isa Gida, sai dai baiji kowa yayi masa batun jikan da zai samu ba. Hajiya Bilkisu tana rawar jikin tarbar sa ta hanyar abinci da sauran kyautatawa.
1⃣2⃣Ya Kalli abicin sannan ya kalleta, "Wai ni banji kunamin batun jikan da zan samu ba. Wani abinda kuka bani haushi, wanda ya kamata ace nina bashi labarin qaruwar, sai shine yake bani" Da sauri ta soma neman yadda zata wanke kanta, sbd tasan shi akwai maida qaramar magana babba. Tace "wai dama Alhaji ban fada maka ba?" kaina bisa wuya. Ya dauki cokali, "ta yaya kk zaton zan manta da wannan babban labarin in har kin fadamin? Ta dora hannunta akan nasa, kayi haquri nayi tsammanin cewa, na fada maka sbd hankalinmu yana tashe, ita Na'imar ce babu lfy. Yace, banji haushi ba Bilkisu. Na dai yi miki takaicin rasa goron albishir daga gareni. Yace, Abbas din fa? Shima bai fadamin ba, kodai wani abu ya faru ne, ko kuma yana shirin faruwa? Tace, babu wani abu, ina zaton dai bai wuce, jikin matarsa ba, kuma ga yanayin aiki. yace tana gida ne ko asibiti? Ta soma in-ina, "eh, a'a tana asibiti, amma munyi shawara in an sallameta su wuce gida, sbd ta dan qara samun qwarin jiki. ya aje cokalin dake hannunsa, "ban amince da wannan Shawarar taku ba! Wai keda wa kuka shawarta? Tace, da Abbas ne da kuma mahaifiyarta. Yace, to nan Gidan ya kamata ta dawo, sbd jikana ya saba da gidansu tun kafin ya iso Duniya. "A ranta tace tirqashi! Wannan wace irin qaunar jika ne haka? Amma a fili sai tace, ai sai a canza shawara, duk ba laifi bane. Yace, shi kuma Abbas yazo, shima jikana a bude masa account din, kamar yadda nake yiwa 'ya'ya na. Sannan jikana na fari, in ya kasance namiji, zanyi masa kyauta mai tsoka. Yayi 'yar dariya, meya kamata in ba jikana? Hajiya Bilkisu, wadda abubuwa uku suka tarun mata a lokaci daya, qaryar da tayi masa, takaicin dawowar Na'ima Gidansu, ga kuma kudin da ta lura za'a 6arnatar ma cikin. Cikin yaqe tace, sai mu jira mu gani me zamu samu? Yayi 'yar dariya, kuma fa Gskyrki ne, qila ma 'yan biyu ne. Ta lumshe ido sbd takaici, sannan ta bude, Allah yasa haka. Yace, Ameen. Yana shiga wanka, ta nufi dakinta. Cikin sauri ta kira Abbas a waya, ta karanto masa duk yadda sukayi. Tace, ynxun yaya kkga za'ayi? Domin dadynku ya zurfafa da qaunar abinda ke cikin matarka. Abbas yace, karki damu, zanje gidan kuma dole ta dawo.
[17/09 1:18 pm] Inna: Canjin rayuwa
1⃣3⃣Na'ima tana zaune a dakin momy tana cin tuwon semo, suhaila ta shigo, tana cewa "sis Na'ima ga Abbas nan yazo da abokansa. Na'ima ta ture tuwon dake gabanta gefe, tare da jan tsaki, tace, ni bazan fito ba harma naji na qoshi. Suhaila tace, suna tare da momy ai. Na'ima ta fito falonta, ta tsaya inda ba zasu ganta ba. Tana iya jiyo muryar Abbas yana cewa, "Ayyuka ne suka sa ni banzo asibitin ba, amma ai momy tazo. Tace, Momyn taka me tazo tayi in ba wulaqanci ba? Don haka inason in fada maka babu inda Na'ima zataje. A Gidanka ma bataji dadi ba bare a gidan iyayenka? Usman yace, ayi haquri dai momy. Nan da can duk daya ne. Momy tace, ba zataje ba. Abbas yace, shikenan zan kira daddyn nan gidan. In ba zata koma ba, saidai mu rabu. Momy tayi shiru, ta kasa magana. Domin tasan Alhaji baisan komai ba a kan matsalar. Da qyar tace, ka fada masa mana! Zai matsa mata dole ne? Abbas ya miqe, ku tashi muje su usman! Zan bada mamaki Gidannan. Suna fita Na'ima ta fito tana kuka tace, Momy ni bazan koma Gidansa ba, bare Gidan iyayensa. Ni tsoron mamansa ma nakeji. Momy tace, qyaleshi yayi ta fadama daddynku din. Ynxun ne suka san ki koma can? Da suna so ki koma da basu kaiki asibiti ba? Na'ima dai sai kuka, ita kuma momy tana lallashi.
Shi kuwa Abbas ya gama tsara ribar da zaici gurin mahaifinsa da wannan cikin. Ynxun burinsa a samu namiji kamar yadda mahaifinsa ke matuqar so. Haka kuma shi da mahaifiyar sa suna ruwan ido akan abinda ya kamata su za6a a matsayin kyautar da kakan zai bawa jikansa. Shi dai yana sha'awar gidan saida motocin Alhajin nasu, yayin da Hajiya Bilkisu ke sha'awar wani kamfanin Alhajin. Ranar asabar, Alhaji Bashir yana zaune a bayan mota tare da 'yan samarin sa guda hudu, malumfashi suka nufa gurin Hajiya Binta. In sun kwana biyu su wuce masari don ganawa da dangi, wato su ziyarce su. Wayarsa ta buga, Ameen ya miqo masa, yana kallo yaga lambar Abbas. Bai ta6a kiransa ba. A fili yace dan nemabbaka ta6a kirana ba, sai yau da aka samu qaruwa. Ya daga suka gaisa, sannan yace, daddy dama inason in fada maka ne an sallami Na'ima daga asibiti, amma momy tace, ba zata dawo gida ba saidai ta zauna Gida gurinta. To kuma daddyn mu daya dawo yace ta koma can gidanmu gurin Hajiyarmu. Da naje don mu taho, sai kuma momy ta hana. Ran Alhaji Bashir ya 6aci matuqa, cikin zafin rai yace, karka damu zansa akawo ta har gurin Hajiyar taku. Abbas yace, nagode daddy. Alhaji yace, babu komai. Suna yin sallama ya kira layin momy Nafisa, tana dagawa, ko amsa Sallamar ta baiyi ba ya soma ruwan bala'i. Nafisa kina hauka ne zaki rabo yarinya da Gidanta? Sbd me? Ba zan amince ki zubarmin da mutunci ba, in har ke baki damu da naki mutuncin ba.1⃣4⃣Tace, tsaya kaji Alhaji! Ba zanji komai ba. Ya katse ta. Zan kira Hamisu ynxun nan yaje ya kai yarinyarnan Gidan minister, kamar yadda suka buqata. Sannan zan gargadeki, kar ki bari inji wata matsala ta fito da sunanki a ciki, ko wani tseguminku na mata. Aure zaki kashe mata ko me? Tace, kasan da Yarin..."ya sake katseta, ba nace kiyimin shiru ba ne? Kinsan Allah kikayi sanadin kashewa yarinyarnan aurenta, ko kuma kika zama silar matsala tsakanina da Abokina, wlh saina baki mamaki, zan yi miki abinda baki zata ba bare tsammani. Ke baki da hankali ne? Baki ganin halin da nake ciki na rashin Mimi da kuma ciwon dake damunap. Shiyasa har in koma ga Allah ba zan daina son Sauda ba da ganin qimarta da girmanta. Kizo katsina ki ganni, kiga yadda na samu lfy da kwanciyr hankali, sbd ina tare da mace ta gari mai tattali. To na fada miki, ki fita idona in rufe. Ya kai qarshen maganar tare da kashe wayarsa
Momy Nafisa, tayi shiru da waya a hannunta, bata ta6a ganin ranar da Alhaji yayi dogon sababi ba kamar na yau. Bata da wani za6i face, yin abin da yace, amma dukda haka saida ta kira layin Hajiya Nana, ta fada mata cewa, Alhaji yace, lallai sai Na'ima ta koma Gidan surukanta. Hajiya Nana tace, ki barta ta koma zamu san yadda zamuyi mu samu mafita. Tana aje wayar, Hamisu yana shigowa. Ya gaida momy, ta amsa rai 6ace. Yace, maigida yace... Ta katseshi, karka cikani da surutunka! Jeka naji, zata zo inta shirya. Ta shiga dakinta inda Na'imar take kwance kan gado, ta zauna a bakin gadon. Na'ima taso kiji! Tace, menene? Bayan ta taso, momy tace, ki tashi ki koma can gidan su Hajiya Bilkisun. Na'ima ta soma kuka, ni ba zanje ba momy. Gsky, na haqura da auren Abbas. Baya sona ko kadan. Momy Nafisa ta riqe kai, cikin damuwa tace, kai ni dai wannan abu ya isheni dai, wannan abu ya isheni. Duk nice na jawoshi. Inda nasan ma haka halin Abbas din yake, wlh da nabar Mimin ta auri Abbas din. Na'ima tace, inda itan ce na tabbata ba zai mata haka ba, don yana mugun sonta. Momy tace, yi mata zaiyi dan bariki, dan bariki ne. Da an gama soyayyar, za'a shiga tsiyar. Ke dai ynxun ki tashi muje can din mu gani. Na'ima tana kuka, tana komai ta kwashi nata ya nata aka nufi Gidan minister da ita.
[17/09 1:18 pm] Inna: Canjin rayuwa
1⃣5⃣Mimi tana zaune a tsakiyar katifar dakin Ismail na zaure, da idanu take ta bin dakin da kallo tamkar bata ta6a shiga cikinsa ba. Ismail dake qoqarin kunna mata 'yar tsohuwar fankarsa, ya kalleta, "me kk kallo a dakin? Shine dai, ba'a qara komai ba, kuma ba'a rage komai ba. Mimi batasan ma yayi ba, tunaninta yana can gurin sashinta na Abuja, amma dubi inda take ayau. Gsky bata ta6a tsammanin ko a cikin mafarkinta abinda ya faru dinnan zai faru da ita ba. Kuma kowane lokaci tayi dogon tunani don ta gano menene laifinta a cikin duk wadannan abubuwan da suka faru, amma bata gano ba. Kowane lokaci tunaninta yana tsayawa ne akan laifin na mahaifanta ne. Tafi dogara akan cewa, basa sonta ne, ko kuma tace, daddy ya daina sonta, don dama can Hajiya ba wai tana sonta bane. Da wannan ta dogara, takeson nesanta kanta dasu iyayen nata yadda ba zasu sake jin labarinta ba.
Ismail dai tsaye yayi yana kallon yadda hawaye ke kwaranya daga idanunta. Dukda cewa ya saba da ganin kukan mimi, amma daga ganin wannan na musamman ne. Da haka ya nufi gurinta, ya zauna a gefen katifar, cikin sanyin murya ya kira sunanta, "khadija! Kina jina khadija? Kina jina? A firgice ta kalleshi, yace me kk yima kuka? Cikin shasshekar kuka tace, babu komai. Yace, khadija, Kalle ni! Ta dago ta kalli cikin manyan idanunsa. "zuwa ynxun na fahimci halayenki a dan zaman da mukayi, fahimta ta sosai. Inda ni marubuci ne, tsaf zan rubuta halayenki. Duk kalar kukan da zakiyi, ina iya fahimtarsa. Nasan kukanki na shagwa6a, nasan kukan ki na rigima, sannan nasan na takaici da kuma na zallar baqin ciki. Wannan kukan naki na tsantsan baqin ciki ne, hade da takaici. Don Allah ki fadamin menene silar wannan kukan naki?" Ta sunkuyar da kai. Yace, karki manta kin dauki alqawari a asibiti cewa, zaki riqeni tamkar dan uwanki. To, in baki fadamin damuwarki ba, wa zaki fada mawa? Kuma nima ynxun dole ne in inada wata damuwa kece zaki fara sani, kafin kowa tunda kece muke daki daya. Ki kalli cikar Gidanmu, amma babu wanda zan iya kaima kukana cikinsu. Daga yaya Amina, sai Mahmud, sune abokan shawarata. Fadamin abin da yasa ki kuka.
1⃣6⃣Tace (cikin shessheka) Na tuna yadda mahaifana suka watsar dani. Dubi inda na dawo. Ni ko cikin novels din da nake karantawa na turanci, labarai irin na turawa masu yin wata irin rayuwa da tasha bambam ta tamu, amma ban ta6a cin karo da labarin masu hali irin na iyaye na ba. Ismail yace, khadija inkin duba tsaf, zakiga cewa, kema fa baki kyauta musu ba. Yadda na samu labarin gatan da mahaifinki yayi miki, bai dace ki watsa musu qasa a ido ba. Amma shikenan duk abinda zai faru ya riga da ya faru. Bari in miki wani alqawari, na sani cewa arziki na Allah ne, amma inya bani, zan miki duk abinda kkso. In ya kai arzikina kamar na mahaifinki, zanyi miki fiye da abinda mahaifinki yayi miki. Inason ki rubuta wannan ki ajiye ko don sheda. Amma ynxun inason ki daina kukan nan, ki kuma yi haquri da yadda kk sameni. Ta runtse idanunta. Ina matuqar da na sanin dawowa ta hutu daga Dubai, na rantse da na san cewa duk wadannan abubuwa zasu faru dani, da na zauna can nayi hutuna. Daddy ya matsamin wai in dawo, ya kuma sake matsamin inje katsina. Ashe yamin hakane sbd ya daina sona.
Ismail ya sake yin qasa da murya, "ki daina fadin haka khadija. Ki sani bawa baya iya gujema qaddararsa. Sannan bana zaton akwai iyayen da zasu daina son dansu. Kuma na tabbata inda iyayenki suke, ynxun suna tare da takaicin rabuwa dake. Hankalinsu yana kanki. Tace a'a ban yarda da batunka ba. Hankalinsu yana kaina ne zasu watsar dani bayan sun samu labarin halin da nake ciki? A dan qaramin tunani na kome nayi musu bai dace su banzatar dani ba acikin halin ciwo. Shiyasa nima nakeso ka nesantani dasu kamar yadda kayi min alqawari. Ta soma wani irin kuka mai shiga rai. Baisan lokacin da ya rungume taba ajikinsa. Kiyi shiru. Zanyi miki duk yadda kk so khadija. Saidai ina sake neman hadin kanki. Yadda kk sameni talaka, ki qara haquri. Kinji khadija? Kimin alqawarin zama na har abada. Ko na tafi makaranta ki zauna da yaya kinji. Haka dai Ismail yayi ta lallashin Mimi da kalamai. Kasancewarsa mai hikimar magana, har tayi shiru, ta kuma amince, tare da alqawarin ko baya nan kar ya damu babu inda zataje.
[17/09 1:18 pm] Inna: Canjin rayuwa
1⃣7⃣Ismail ne ya girka musu abinci, taliya ce yayi dafa duka, ya zabga kifi. Kuma Mimi taci sosai. Matsalarsa ban daki, amma tunda ga 'FO' din daya siyo mata, sai yace, tayi amfani dashi, zai dinga zubarwa. Cikin kwana ukun da sukayi, Mimi har nauyin Ismail takeji, domin ko cikin dare ta farka fitsari ko ba haya zaisa ta a 'FO' in ta gama, ta wanke sai yazo ya zubar, kuma ta lura yanada matuqar tsafta sosai sbd yadda yake gyaran dakin, ya wanke komai na girki, sannan yayi musu wanki. Wanka ne dai matsalarta ynxun, don acikin kwanaki ukun nan batayi wanka ba, sannan yana sata su danyi tattaki a cikin layin ya sagale ta a kafadarsa don tadan taka qafarsa. Sai dai damuwarta yana matsa mata sai ta saka hijabi, ita kuma bata saba da yawo dashi ba. Da ma shi ya sai mata sbd sallah. Yakan lallasheta da cewa, kinga duk kayanki matsattsu ne, khadija ki saka, in mun dawo daki, sai ki cire. A ranar ne Ismail ya daga katifa yayi share-share, har ya ciro ma Mimi Jakarta. Daya gama share-sharensa, sai ya taimakawa Mimi, ta koma kan katifar dama cikin zaure ya zaunar da ita. Sannan ya dauko Jakarta ya ajiye a gabanta. Har ta dauki littafin daya bata na tarihin Annabi Muhammad (SAW) ta bude tana cewa, ina page na ashirin da uku. Sai yace ga jakarki. Tace jefa ta can kan akwatunan can. "yace da kudinki a ciki fa." Ta dago ta dubeshi, sannan ta kalli jakar, "kudi?" yace duba mana. Ta ajiye littafin, sannan ta dauki jakar, ta zazzago kudin. Cikin mamaki ta kalleshi, "dama ba dasu ka biyamin kudin asibiti ba? Yace a'a. Tayi shiru tana kallonsa, ta sake cewa kodai bakasan dasu bane? Yace na gansu. Sai taga ya qara qima a idonta. Sai tace, nagode sosai, amma ka amshi wannan kudin kayi duk abinda kkso dasu, na baka. Yace, kudin da yawa khadija, ki riqe abinki. Tace babu abinda zanyi dasu. Amfanin dana debo kudin don inyi dasu basu min ba. Komai ya zama tarihi. In ma bakada buqatarsu, to zaka iya ba wasu masu buqata. Kuka ya kufce mata. Ismail yace, shikenan kiyi shiru, na amsa kuma nagode. Ya tattara kudin guri daya, yana tunanin me zaiyi dasu? Cikin baqar leda ya zuba su. A zuciyarsa yana Jindadi, domin ko babu komai, zai samu tarin buqatun dake gabansa.
1⃣8⃣Waje ya fita ya kira Mahmud cikin waya ya sanar dashi komai, Mahmud yace, Ismail ka gode ma Allah. Duk lokacin da wata matsala ta taso maka, sai kuma Allah ya kawo maka mafita. Kaga kana cikin matsalar abinda zaka bar musu in zamu tafi da wanda kai kanka zaka riqe don amfaninka, sai kuma ga wadannan kudin. Ismail yace, Allah shine abin godiya. Ni kaina nayi tunanin sassauci ne Allah ya turomin. Kuma fa kasan harda darajar aure ko? Inji Ismail. Mahmud yace, tabbas! Kasan aure daraja gareshi. Albarkacinsa sai kaga budi ko ta ina. Shiyasa ko yaushe nake baka haquri, ina tausarka a kanta. Kuma duk runtsi kar kace, zaka saketa. Ismail yace, insha Allahu zan kula. Amma fa karka manta ba sona takeyi ba, kuma nima harga Allah banajin sonta a zuciyata, tausayinta kurum nakeyi. Mahmud yace, "Allah yayi mana za6i mafi alkhairi. Ismail yace, Ameen. Sannan sukayi sallama. Ummin yaya Amina ce tazo ta kawoma Mimi faten wake hade da kifi. Sai Ismail yace, ummi zauna da aunty khadija inje gurin mamanki in dawo. Tace, to kawu. Amma ka fada mata inanan. Yace zan fada mata. Ya kalli Mimi, sai na dawo. Kai kurum ta daga masa.
Sun tattauna da yaya Amina, inda sukayi shawarar a gyara ma Mimi dakin kakarsu saddam. Babansu saddam da ma ya Amince ta dawo nan. Yace, ai Ismail dansu ne tunda ance babbar ya uwa. Yaya Amina tace, ka ba Salisu aikin,, qanin babansu saddam. An kira Salisu yaga dakin, kuma Ismail ya fada masa yanason asa masa tayals a qasa, sannan a saka silin na zamani na roba, kuma a yi masu fenti duka Gidan, ya canke kudin da Salisu ya fada ya bashi harda na aiki. Sannan ban dakinsu yasa shima a duba, aka duba, yace abin tsugunno na zamani asa tayals a qasa ayi fenti asa wuta. Dama tsakar gidansu mulmule yake da siminti. Sannan ya ware wasu kudi ya ba baban su saddam yace, su siyo kayan abinci sbd halin yau da gobe. Bayan fitarsa itama yaya Amina ya bata 'yan wasu kudin ahannunta, sbd yasan Mimi ba zata amshi kudi daga wannan kudinba. Yace ta riqe do zuwa asibiti ko wata buqatar. Bayan ya koma ya tarar Mimi tana varci, ummi kuma tana zaune a tsakiyar dakin tana wasa. Yace, a'a varci tayi antin taki? Ummi tace, eh tana cikin karanta littafi, sai naga tayi varci. Ya kalli littafin, sai yaga littafin tarihin nan ne daya bata. Ya dauka ya duba yayi mata alama a inda ta tsaya ta hanyar ldan linke gefen littafin sannan ya ajiye. Ya kalli Ummi, to tashi kije gida ko mamana. Tace, to kawu, sai Anjima. Ta tashi ta fita.
[17/09 1:18 pm] Inna: Canjin rayuwa
1⃣9⃣Daga tsaye yake yana kallon Mimi. Duk runtsi saidai yace, bayason Mimi, amma ba dai yace, ba tada kyau ba, don ma fatarta ta rage haske sakamakon canjin rayuwar data samu. Ga ta da gashi, abinda yake matuqar so ga mace. Ya koma gefen teburin daya dora littafin akai ya zauna yana kallon Mimi sosai. Yaga abubuwa da yawa a tare da ita wadanda suke sawa mace ta amsa sunanta mace. Harma ya jishi cikin wani irin yanayi daya tilasta masa lumshe ido. Muryar Mimi yake tunowa irinta matan da suka amsa sunansu na mata. Domin duk macen data amsa sunanta mace, bata yin magana da qarfi. Mimi ko masifa takeyi ba zakaji muryarta a sama ba. Hakanan in tana waya, qarya ne don kana kusa da ita kaji me take fadi, in dai ba ka saurara sosai ba. Haka zalika in tana magana da kai tamkar bata so. Wadannan dabi'un da kuma shagwa6arta tana matuqar burge Ismail, kuma yana sonta ga matar da zai aura. Qarar wayarsa ya dawo dashi tunaninsa. Ya daga, Mahmud ne yace, ka fito ina waje. Ismail yace, ganinan.
Yayi masa bayanin Yadda sukayi da yaya Amina. Mahmud yace, yayi hakan. Ismail ya ciro dubu biyar yaba Mahmud yace, kaima kadan qara. Mahmud yace, babu matsala ka barsu don Allah. Ismail yace, a'a ka amsa kudinfa sunada dan yawa, dukda ban qirga ba. Ni tunani ma in na cire abinda zanyi amfani dasu, sauran sai in buda account in zuba, ko don buqatar su khadija. Mahmud yace, wannan ma tunani ne mai kyau. Sun jima suna tattaunawa sannan sukayi sallama. Daren ranar, gurin misalin sha daya Mimi ta farka daga varci, sakamakon hasken wutar lantarki da aka kawo, dana rashin wankanta na kusan kwana hudu, ya sata sai juyi takeyi. Ta tashi zaune tana kallon Ismail, wanda babu riga, ta lura sam shi ba mutum bane Maison varci da tufafi. Amma yanason rufa sosai. Ynxun haka rabin jikinsa, ko ince daga qafa zuwa qirjinsa a rufe yake. Sannan fuskarsa tamkar yana murmushi. Ta dauke idanunta tare da lumshe su. Sannan ta sauke ajiyar zuciya. Wannan duk don idanunta sun kalli sumar dake kwance a tsakiyar qirjinsa ne. Hasken wuta ne yasa shi bude ido, yayi miqa tare da salati, yace NEPA sun kawo wuta kenan. Yana tashi zaune yaga Mimi a zaune. "kema hasken wutar ne ya farkar dake? Na manta ban kashe ba. 2⃣0⃣Ta 6ata fuska, cikin shagwa6a tace, jikina yana yimin qaiqayi. Yace khadija kinqi yin wanka dole kiji haka a jikinki. Tace yaya zanyi ynxun to? Yace, bari in kaiki ciki, ki daure kiyi mana. Tace amma zaka tsareni a waje? Yace eh. Riga ya saka, sannan ya nufi cikin Gidan. Saida ya wanke bayin, sannan ya kai mata ruwan wankan. Yace, babu dai na zafi, kuma kinga har ynxu da dan sauran sanyi. Tace, zanyi hakanan. Kujera yasa mata ta zauna sannan ya fita. Data gama saida tasa kayanta data dauko na varci masu dan kauri sannan tace, na gama. Yazo ya kamota suna tafe a hankali. Sunzo daidai qofar dakin fatu, sai ta turo qofa ta fito. Ta kallesu, "ikon Allah, don jaraba ba'a bari a warke ba? Su dai basu tanka ta ba. Sai da Mimi ta zauna akan katifa sannan tace, wai me matarnan take nufi da abinda ta fada? Ismail dukda ya fuskanci inda fatu ta dosa, sai yace, nima ban gane nufinta ba. Daya koma kwaso kayan wankanma, saida tace, ya dai kamata a bari a warke. Ismail yace, ai da ciwon ma ba haramun bane. Tace, eh lallai ka riqa. Shidai ya fice a zuciyarsa yana cewa, sa ido sana'ar banza!
Cikin kwanaki uku zuwa hudu an kammala gyara tsaf. Lallai komai yanason gyara, inji abban su saddam, lokacin daya gama kallon Gidan. Sannan ya juya ya kalli Ismail, qanina muna godia fa. Ismail yace, Ameen. Ismail shida Mahmud sukaje kasuwa, inda suka siyowa Mimi Gado waya goma na kwanciyar mutum daya, saitinsa harda sif. Sai fanka, dan TV dinta madaidaici. Mahmud yace, ga wata shawara, me zai hana kudin da kace kaba yaya Amina, ka amshe su ka cika ka sai musu firji ko dan qarami ne. Kaga ko da ruwan sanyi suke saidawa zasu samu dan na rufin asiri. Ismail yace, haka ne, amma bari mubar musu wancan kudin tunda ga wasu nan, sai mu sai musu dashi. Dogon fridge suka siya, sannan suka nemi shatar a kori-kura suka loda kayan, suka nufi Gidan yaya Amina. Maqota sai leqe sukeyi. Wasu suce 'yan haya suka sa a gida, wasu kuma suce kodai aure abbansu saddam ya sake yi. Suka shiga da kaya suka shirya komai tsaf, firjin kuma suka sashi a dakin yaya Amina. Su Ummi kam murna babu dama. Tana fita wata maqociyarsu, Bakaraba tana ta leqe, dama tanason taga giccin wani dan gidan ta kirashi. Tana hango Ummi, ta kwada mata kira. Ummi tazo, tace kunyi baqi ne a gdn naku, ko ko abbanku ne yayi aure? Ummi tace a'a kawunmu ne zai tafi madina, shine matarsa ta dawo Gidanmu. Tace ohoo, wadda ke asibiti? Ummi tace eh.
[17/09 1:18 pm] Inna: Canjin rayuwa
2⃣1⃣Daga nan fa duk wanda yazo jin meya faru, sai tace, qanin mamansu Ummi ne zaije karatu, ya dawo da matarsa Gida. Dama ita balaraba gun nan duniya ce. Ga duk maison jin wani tsegumi a Unguwar, gurinta yake zuwa don ta shahara. Tunda taga anayin fenti a gidan take shige da fice don jin dalili. Bata samu cikakken bayani ba, sai a bakin Ummi. Saida komai yayi tsaf, sannan suka tafi. Bayan sunyi sallama da Mahmud ya shiga gida, ya zauna. "khadija na barki ke daya ko? Don Allah kiyi haquri. Ta dube shi, sannan ta kwantar da kanta gefe, babu komai, karka damu dani na saba da zama ni kadai. Yace, an gama gyaran dakin naki, na gidan su yaya Amina, yaushe zaki koma? Cikin sauri ta tashi, "ynxun zan koma. Yayi murmushi, meyasa kk gaggawar rabuwa dani? Kin gaji da zama dani ko, bana kula dake yadda ya kamata. Cikin sauri tace, a'a Nayi kewar yaya Amina ne, kuma nan din ina takura maka sosai. Qasa fa kk kwana, amma kana kula dani sosai. Yace nikam inata kewar rabuwa dake, tsawon lokaci muna kwana daki daya, zamu rabu. Ta sunkuyar da kai, "ba zaka rinqa zuwa Gidan ba? Yace, zan dinga zuwa kullum kafin in tafi. Ya kamata in sai miki waya ko? Sai mu dinga gaisawa ko? Tace, ka barni kawai tunda banida wanda zan kira. Yace, ba gani ba? Tace, a'a ka saimin novels na dan dinga karatu. Yace, wadanne iri? Tace, na turanci. Yace zan hada miki dana addini, tarihin Annabawa, da kuma wadanda zasu koyar dake, kisan yadda zaki ibadarki. Suma akwai masu fassarar turanci, akwai na hausa. Tace, to ka saimin. Yace kuma sai gobe zako koma gidan yaya din, sbd yau da dare nida Mahmud mu kwashe kayankin nin, ya nuna akwatunanta da yatsansa. Tace, "to Allah ya kaimu.
Ya shiga cikin Gida ya sanar dasu inna cewa, matarsa zata koma gidansu yaya Amina, sbd zasu tafi makaranta. Tace, "sbd nan din ba za'a kula da ita ba? Yayi murmushi, don dama ya zaci zata fadi haka. Yace a'a saboda bata gama samun sauqi ba. Tace, Allah ya taimaka. Yace, Ameen. Haka kuma da dare ya samu 'yan uwansa mazan ya fada masu. Suma sai suka ce, hakan yanada kyau. A daren suka kwashe kayansa da Mahmud tsaf. Sannan washe gari ya kama ta Suka shiga cikin gidan tayi musu sallama, dukda dai ba kulata suke ba, sai wanda yayi biyya yake leqawa dakin yayi musu sannu. Tayi mamakin ganin dakin haka don gsky bata zaci dakin yayi kyau haka ba. Ta kalli Ismail, nagode da kulawa. Sannan tace ma yaya Amina taba ta Ummi su dinga kwana. Yaya tace gatanan.
[17/09 1:18 pm] Inna: Canjin rayuwa
2⃣2⃣Shi kuwa Ismail daya koma ya kwanta a dakinsa kan katifarsa, sai yakejin dakin yayi masa girma. Zuciyarsa ta cika da kewar Mimi. Itama a nata 6angaren haka ce ta kasance, juyi kurum takeyi tana kallon Ummi wadda keta sheqa varci. Gizo Ismail yakeyi mata, sai taga kamar gashi yana sallah. Koda ta tabbata ba wai tanason Ismail bane, amma yana da dabi'un da take matuqar so, suke kuma burge ta. Yanada tausayi, ga gsky da Amana. Shine mutum na farko wanda ya kasance mai addini kuma yake birgeta. A da in taga ustaz kamarsa, sai ta dinga yi musu kallon 'yan kauye wadanda basu waye ba. Haka kuma yana burgeta Kasancewarsa tsayayyen namiji, wanda baya daukar raini, gwarzo mai tsayawa da safafunsa. Don duk lokacin da ta tuno da yadda suka yita takun saqa dashi, tana jinjina masa, domin ko a gabanta bai ta6a shakkarta ko nuna Tsoronta ba, kamar yadda sauran mazaje da yawa sukayi a baya. Ta tuna irin yadda tayi ta wulaqanta samari 'ya'yan manyan mutane, wadanda suka nuna cewa suna sonta. Kai ko khalil dinta ya wulaqantu kafin ta soma sonshi, kuma har zuwa lokacin da ya rasu, bai daina shakkarta da tsoronta ba. Tasan cewa da ya kasance mijinta, babu shakka za suyi zama ne na sai yadda tayi. Domin ba zai iya juya ta ba. Da wadannan tunanukan varci yayi awon gaba da ita.
Shikam Ismail bayan ya dawo daga masallaci sallar asubahi, saiya nufi gurin malaman da suke daukar karatu. Daga gurin karatun ne ya nufi gidan yaya Amina. Lokacin abbansBBCu saddam shima zai shiga Gida. Suka gaisa, cikin salon tsokana abban saddam yace, kazo duba ajiyarka ne? Ismail cikin dariya yace, kuma fa kamar hakane. Tashin Mimi kenan daga varci, tana tunanin da suna tare da Ismail da ynxun ya kaita ban daki, sai taji Sallamar sa. Da sauri ta koma ta kwanta don taga me zaiyi. Yaya Amina tana kicin tana dora ma yara ruwan wanka, suka gaisa. Yace, 'yar amanata ta tashi kuwa? Yaya Amina tace, leqawata biyu bata farka ba. Yace, kinsanta sarkin varci ce dama, ko gajiya batayi. Yace, bari in tasheta tayi sallah. Yaya tace, "to" amma tasan cewa mimin tana fashin sallah, domin jiya da dare bayan tafiyar Ismail ta tambayi yaya audugar mata. Yaya kuwa da kanta ta fita zuwa shagon Bello ta siyo mata.
[17/09 1:18 pm] Inna: Canjin rayuwa
2⃣3⃣Ya jima tsaye yana kallonta, sannan ya dauko kujerar gaban madubi, yazo bakin gado ya zauna. Babban yatsan safarta ya kama ya dan ja. Dole tayi motsi, domin taji dan zafin qafar. Yace, ki tashi kin makara, kiyi sallah. Ga Ummi har ta tashi tayi nata. Tace, cikin salonta na shagwa6a "nifa ba zanyi ba yau. Ta sake sunne kanta cikin filo don kunya. Ya gane batunta, cikin sigar tsokana yace, wai, wai, wai, shine baki fadamin ba in sai miki biredinku na mata? Koda yake naga ba kiyi ba muna asibiti, sai na zata baki fara bane. Ta dago, tayi masa wani kallo, meke daukeni ne? Ya kashe ido daya, "Baby mana. Ta tashi zaune, me kace? Kada ka manta fa naje jami'a. Yace, haka fa, kinje jami'a, na manta sam, shekarunki nawa ne ma? Ta gano so yake yaji shekarunta, don haka tace, ba zan fada maka shekaruna ba, sai dai ranar zagayowar haihuwata. Tace daya ga watan daya. Yace tabdi! Gsky ke ta musamman ce, to bari in kalleki in fadi 'yan shekarun naki, don basuda yawa. Tace, fadi muji. Yace sha takwas, sha tara, ashirin, in na cika miki kenan. Ta dan zaro ido, alamun aciki ya fadi daidai, amma sai ta wayance da cewa, sam ba haka bane, baka canka ba.
Yaya Amina ta katsesu da sallama suka amsa, tace, khadija ga ruwan wanka can muje in kaiki ko? Ismail ya miqe "to nima bari in tafi dama nazo ne mu gaisa. Yaya Amina tace, kardai ka manta da sandar da za'a sai mata ta tafiya, tunda sunce zai taimaka mata sosai gurin tafiya da sauri. Ismail yace, ai kuwa nagode, shaf na manta. Anjima zamuje asibiti da Mahmud. Haka kuwa sun sai mata sandar. Kwanci tashi, babu wuya har anzo jajibirin tafiyarsu Ismail. Kafin ranar tafiyar dama ya zaga duk 'yan uwansa mata, yayi musu ban kwana, domin shi harga Allah yanason 'yan uwansa mata, yayi musu ban kwana, domin shi harga Allah yanason 'yan uwansa. Kuma yana sha'awar suyi zumunci. Wadanda basuje asibiti duba su ba, sai 'yan kame-kame gami da ban haquri yace, babu damuwa Allah ya bada ladan niyya. Haka nan yaje Daura, yayi bankwana da dangin mahaifiyar sa. Ta kano zasu tashi, don haka tun ranar jajibirin zasu tafi kano din tare da Malam Aminu. Sai yaga tashinsu sannan zai dawo.
2⃣4⃣Sun gama shirinsu tsaf, Ismail ya shiga don yin bankwana da matarsa da kuma yaya Amina. Ya dauko wayarnanda ya ta6a saima Zainabu yazo ya samu tayi aure, ya bawa yaya Amina, yace, ya dinga kira don jin lafiyarsu ba sai ya dami abbansu saddam ba. Mimi tana kwance akan gado Rigingine, ta tasa tulin littafin daya sai mata, sai dai duk na addini ne, bai sai mata novels dinba, waishi baisan ina ake saidawa ba. Yace, ta karanta wadannan don tafi buqatarsu ynxun, kuma kinga duk na turanci ne, tunda kince hausa tana baki wahala. A sanyaye yace khadija! Ta kalleshi, yace munfa shirya zamu wuce. Malam da abokinsa da kuma Mahmud zasu biyo tanan ynxun mu wuce. Ta dubeshi, "tam shikenan sai kun dawo, kamar zuwa yaushe kenan zaku dawo? Yace, sai dai munje muji lokacin da suke samun hutu. Ai zan dinga kiranku muna gaisawa. Tace, am nayi zaton kafin ka wuce zaka sakeni? Gaban Ismail yayi wata muguwar faduwa, har taso ta gane. Amma sai ya wayance tare da yin dan yaqe, "kinada gurin da zakije ne kafin in dawo? Ta kalleshi "a'a" yace to kada kiyi gaggawa, wannan kibar zancen, sai in nazo hutu, sai muga yaya za'ayi ko? Tace shikenan, Allah ya taimaka, ya kaiku lfy. Ta koma ta kwanta. Ya dube ta, "babu rakiya? Tace ka manta banida qafa? Yace, shikenan kiyimin Addu'a sai munyi waya. Su yaya Amina ce da yaranta suka rakashi lokacin da su Mahmud suka iso. Suna tsaye har saida motar ta 6ace, sannan suka koma Gida. Suna idar da sallar asubahi, jirginsu Ismail ya daga, su Malam suka dawo cike da kewarsu.
Zainabu ta gama girki ta raba taba kowa, kusan kwano ashirin da uku. Matuqa ta qosa ta fita a madafin sbd hayaqi da kuma zafi. Ta dauki nata da kuma na mai gidan, duk da baci yake ba, amma qa'ida ce kullum sai an zuba masa. Habu da adamu suna jira ace su dauka, tace, ku dauka, sai ku fadama sauran cewa suzo su dauki nasu. Habu ya dauka tare da fadin, ke kullum abincinki baya dahuwa. Adamu yace, eh mana ke baki iya girki ba. Tace, ku bakuda kunya. Ni sa'arku ce? Maman su Habu ta fito, dama kamar tana jira, "karki takura min yara. Ai ba qarya sukayi ba. Duk ranar girkinki, saidai a zubar ko ko aci da haquri. Jikin zainabu ya soma 6ari don tsoron fada gareta. Tace, ni bazan takura musu ba kuyi haquri, ta nufi samansu.
[17/09 8:49 pm] Inna: Canjin rayuwa
2⃣5⃣Daidai lokacin kuma Alhaji ya shigo, yana jiyo hayaniya, yace, Hama lfy kuke min hayaniya da farar magriba? Tace, Zainabu ce zatayi min rashin kunya, don yara sunce ba zasu iya cin abincinta ba. Alhaji yace, sbd me? Tace, to abincin bai ciyo don bata iyaba. Alhaji mutum ne wanda komai qanqantar magana, sai ya ririta ta. Don haka sai yace, yanason duk 'yan gidan su hallara. Ya tara su har zainabun. Yace, su fada masa da gske ne girkin Zainabu babu dadi? Maman bushira tace, injiwa? To kai da zaka tambayemu baka ta6a ci bane? Yace, to iya magana, jikar zance, ban dake, don na kula kinfi son yarinyarnan da iyalina. Ya dinga bin yaran da sauran matan yana tambayarsu ko ta iya? Suka dinga cewa babu dadi. Sai 'ya'yan Maman bushira ne kurum Sukace sudai suna ci. Alhaji yace, ban ta6a cin abincinta ba amma yau zanci, in har baiyi dadi ba, kamar yadda kuka ce, to zan dauki mataki. Don bazan dinga fita da sassafe neman abinci ba, sannan kizo kina girka shi son ranki, a kasa ci ana zubar dashi. Zainabu dai shiru tayi, sbd ba tada ta cewa, amma fatanta shine Allah yasa ya yanke mata hukuncin saki.
Shi Alhaji ba mutum bane maicin abincin gidansa, yafi zuwa Gidan abinci shagunan masu indomie koko gurin masu tsire. Dakinsa ya kira Zainabu yace, ta bude abincin ya gani. Jikinta sai 6ari yake, ta bude, qauri ya cika dakin. Yace, eh lallai dole yara su kasa cin abinci, tun kafin in kaishi baka ne wannan qaurin yake tashi? Ta kalleshi cikin tsananin tsoro, yace, uwarki bata koya miki girki bane? Tace, ni ban iya yin girki da babbar tukunya ba, kuma gashi a murhu. Yace, da Allah rufe min baki! Nine zaki fadawa baki iya girki a murhu ba. Ubanki baya iya ci da gidanku. Ni nake riqe da gidanku, da har zakice min baki iya girki da murhu ba. Wa zaki gaya ma kokai dan uban waye. Da dai kince sakaryar uwarki bata koya miki ba, sai yawon talla da nafi yarda. Ran Zainabu yakai maqura gurin 6aci, tace nidai gsky duk abinda za'ayi, ayi, amma a daina zagin iyayena. Kuma ai duk yaushe muka hadu da zaka ce kai ne kake ci da gidanmu? Ashe Zainabu ta tafka kuskure daya fada ta fada. Domin ba'a fadi yana fadi. Nan take ya tashi a fusace, ya hau kilarta. Maman bushira tana zaune Zugum tana jiyo ihun Zainabu, baqin ciki fal a zuciyarta, domin tana tsoron kar wannan halin da mijinta keyi ya juye kan 'ya'yanta, sbd in ka cutar da dan wani, sai an cutar da naka don kaima kaji. Haka yayi ta kilarta har ya gaji, yabarta don ba zuwa ceto.
2⃣6⃣Tun Zainabu tana kuka har ta kasa. Yace, tashi ki fitarmin a daki! Kasa tashi tayi, domin data yunqura, sai ta koma ta zube. Sai kuma ga jini ya soma zuba. Idanu ya zaro yana kallonta. Sai kuma ya soma kiran Maman bushira. Ta shigo ranta 6ace, yace, kamata zuwa daki, naga jini yana zuba, ko dai al'ada takeyi? Maman bushira tace, wace al'ada kuma? Yarinyarnan ciki gareta, saidai inka sake doko cikin. Yace, ni ban doketa a ciki ba. Maman bushira ta dago ta tana kiran sunanta "Zainabu! Zainabu! Cikin tsoro tace, Alhaji yarinyarnan tana da rai kuwa? Da sauri yasa takalmi yace dauke ta zuwa dakinta, bari in kira danladi Mai chemist. Tace, ka dauketa dai, ni ai bazan iyaba. Cikin tsawa yace, kama ta muje mana. Kan gadonta suka dora ta, duk jini ya 6ata hanyar da kuma dakinsa da nata. Ya fita da sauri. Maman bushira tace, maganinka kenan! Allah yasa ya zamar maka ishara. Zainabu dai tanaji, ba suma tayi ba, amma tana cikin mawuyacin hali. Sake yin lamo tayi tare da sakin jiki sbd jin rudewar da Alhaji yayi. Ko da danladi mai chemist yazo, dauke Numfashinta tayi. Dama shi ba wai ilimin gareshi ba, ya ta6a yin shara ne a asibitin Gwamnati, shine yazo ya bude chemist mutane suke ta tururuwa. Danladi yana ta6a ta, sai yace wai, wai, Alhaji! Gsky kuje asibiti, don gsky ba zan iya ba. Dubi jinin fa kamar an yanka qaramar dabba. Alhaji ya zaro ido cikin fargaba, to ni yanxu wane asibiti zamuje? Banason zuwa wannan asibitin Gwamnatin. baba yace bari in kwatanta maka wani na kudi ka kaita bakinka alaikum.
Sun kaita, an amsheta, amma yayi kashin kudi masu yawa, sannan kuma cikin yananan bai fita ba. Bayan tafiyarsa Gida, gurin qarfe sha daya Nurse din da ta taya likitan aiki lokacin da ake qoqarin tsaida jinin, ta samu maman bushira a zaune kan kujerar dake kusa da gadon da Zainabu take kai kwance, tace, sannu mama. Maman bushira tace, yauwa 'yan mata sannu da aiki. Mun gode fa. Tace, yauwa dan Allah mama, wannan 'yarki ce? Maman bushira tace, a'a kishiya ta ce. Nurse din ta zaro ido. "Kishiyarki kuma? Kina nufin wancan daya fita mijinku ne?" tace, eh.
[17/09 9:56 pm] Inna: Canjin rayuwa
2⃣7⃣Nurse tayi shiru tana matuqar mamakin lamarin. Can tace, to wai wanene yayi mata dukan jikinta? Tace, shine ya duke ta. Wlh haka yakeyi. Yayita auro 'ya'yan mutane yanacin zalinsu. Nurse din tace, kinga ko Mama da ace Allah zan hadaki da ainihin babbar likitar dake da wannan asibitin. Kiyi mata bayani, wlh zata gyara masa zama. Maman bushira tace, rufamin asiri. In ya sani ai na shiga uku, domin dama inacin darajar manyan 'ya'ya na ne, sai kuma irin wannan ranar in yayi ta'asarsa yazo ya matsamin in tayashi. Nurse tace, inda zaki iya da na hadaki da ita. Allah zatayi muku maganinsa, sai ya daina. Kuma ko daya sunanki ba zai fito ba. Tace, to shikenan ki hadamu don zan mata bayani, amma don Allah kamar yadda kkce, kar sunana ya fito. Tace, ba damuwa. Gobe ai kina nan ko? Tace, eh nizan kwana, amma na san shima zaizo da safe. Alhaji lawal, tunda yaje Gida ya tara sauran matan yasa su suka gyara gurin jinin. Shi dai tunda ya shige dakinsa ya zauna ya zabga Tagumi, ya rasa bakin magana. Da na sani ce cankas a zuciyarsa. Tsoronsa daya kar 'yar mutane ta mutu. Ranar dai bai runtsa ba, sai juyi yake. Washegari tun takwas ya nufi asibitin. Lokacin Zainabu tana varci don ta farka cikin dare har Maman bushira ke bata labarin yadda sukayi da Nurse. Zainabu tayi ta roqon ta akan cewa, ta taimaka mata don Allah don Allah ta fadawa mai asibitin.
Ya kalli Maman bushira yace, ya jikin nata? Tace, da sauqi. Yace, ta farka? Cikin son qara tsorata shi, tace eh ta farka, amma bata cikin hayyacinta. Domin bata ganeni ba ma. Alhajin ya sake rudewa. To likitan bai sake dubata bane? Ance asibitin kudi, kuma na bada duk abinda akace, amma ba zasu duba ta yadda ya kamata ba? Zai fara sababinsa tace, Alhaji gara fa kabi ahankali sbd likitan ya fara tambayoyi akan shedar dukan dake jikinta. Sannan zuwan su biyu nemanka. Yace, to ni dai bari ma inzo in tafi kawai. Ya ciro kudi ya qirga dubu goma ya bata, "ga wannan ki riqe a gurinki. In sun tambaye ni kice nayi tafiya. Sannan karki sake aji daga bakinki cewa, ni na duketa." Tace, to shedar dukan fa data fito a jikinta? Yace, kice musu bulala ce ta fito mata. Ba awai ciwon bulala ba? Tamkar Maman bushira ta saki dariya, sbd ganin yadda Alhajin ya birkice. Bayan tafiyarsa tace, ai zaka gane kuranka. Nurse dai tazo kamar yadda tace, kuma ta raka ta har gurin mai Asibitin a cikin ofishinta. Da ma takan zo qarfe goma ta tashi sha biyu. Bayan Maman bushira ta gaisheta ne, sai Nurse din tace, gata nan momy. Doctor din ta kalleta, malama kiyimin bayanin dana samu daga wannan Nurse din. Maman bushira tayi mata bayanin yadda abin ya faru har ya kaiga dukanta. Sannan tace, tashi muje in ganta. Sun samu Zainabu ta farka. Tana ganin likitar ta soma kuka tana cewa, don Allah ta taimake ta. Likitar tace, karki damu, hadin kanki nake buqata. Tayi ma Zainabu tambayoyi, ta amsa. Sannan tace, to babu damuwa qarfe nawa zaizo? Maman bushira tace, ai yazo har ya tafi. Kuma zaiyi wuya ya qara zuwa don a tsorace yake. Likitar tace, qarfe nawa za'a saleshi a Gida? Tace takwas na safe ko tara na dare. Likitar tace, babu komai.
2⃣8⃣Doctor Asma'u Adamu mace ce mai kamar maza. Tana da taimako sosai, musamman akan abinda ya Shafi mata. Duk lokacin data samu matsala makamanciyar wannan, ko ba'a Asibitinta ba ne, takan nemar wa mai haqqi haqqinta. Har ta kai ga kafa qungiya mai qwato wa mata 'yanci. Suna da lauyoyi da mai qwato wa mata 'yanci. Suna da lauyoyi da 'yan sanda da malamai da kuma alqalai a cikin qungiyarsu. Bada 6ata lokaci ba suka rubuta takarda suka aikawa 'yan sanda, inda suka gayyaci Alhaji lawal zuwa ofishinsu. Da yaso yayi gardama, sai suka tura masa 'yan sanda. Dole ya zo suka tasa shi har asibiti. Lokacin Zainabu tana zaune tana shan tea. A cikin kudin daya ba Maman bushira ta fita ta siyo kayan tea din. Sun duba jikinta kuma sunyi mata tambayoyi ta basu bayanin duk avinda kenan tun daga tun daga tursasa mata auren sa da akayi har zuwa yau dinnan. Sun tasashi har Gidansu Zainabu inda aka taso qeyar innar Zainabu. Likita Asma'u ta rufe innarsu Zainabu da fada. Tace, aje a rufesu, sai gobe za'a shiga dasu kotu. Nan fa hankalin Alhaji yayi matuqar tashi. Ya shiga bada baki, tare da roqon don Allah ayi masa afuwa tunda bata sonshi, yaji kuma ya haqura, zai sake ta. Likita tace, ai dama wannan dole ne, sannan kai zaka kula da ita har ta warke, sannan ka dauki nauyin cikinta, har ta haihu ta yaye. Yace, duk na yarda.
Ita kuwa inna, saida aka rubuta takarda dasa hannu kan cewa ba zata sake tursasa ta ba. Cikin su duk wanda ya sake, sai yayi zaman jarum. Bayan gargadi mai tsanani aka sallamesu, bayan Alhaji ya rubuta takardar sakin Zainabu, yayin da maman bushira ta shirya yanata-yanata, ta dauki kudin da Alhajin ya bata, taba Zainabu. Zainabu taba ta dubu uku daga ciki. Har taqi kar6a, Zainabu tace, lallai saita kar6a. Ta qara da cewa, taimakon da kk yi min, Allah ne kawai zai biyaki. Murna gurin Zainabu tamkar sallah, wannan sakin da akayi mata, matsalarta daya, wannan cikin dake jikinta. Kwana uku ta qara aka sallameta. Suka je ta kwashe nata-yanata suka nufi Gida. Kafin su wuce, dama likita ta tabbatar ma da Zainabu duk wata, gurinsu zata dinga zuwa ta amshi duk abinda aka yanke dashi. Shi kuma sun tabbatar masa cewa, sun saka ido akansa, in ya sake yiwa 'yar wasu haka, to ba shakka zai qare rayuwarsa a Gidan kaso.
[18/09 3:31 pm] Inna: Canjin rayuwa
2⃣9⃣Rayuwar Na'ima a Gidan minister dai sai a hankali, don in yana gari ne zaka ga suna kula ta, amma da yayi tafiya ko ya fita, banza ma ta fita. Abbas kuwa ko yazo gidan bata isheshi kallo ba. Haka qannensa batajin dadinsu, har gara Aisha ma data dawo hutu, takan dan kulata. Saima ta gwammace zaman gidan Abbas dana iyayensa. Don haka wata safiyar talata ta samu Hajiya Bilkisu, bayan ta gaisheta, ta amsa cikin jin kai. Na'ima tace mata, momy na samu sauqi inaso in koma gidana. Hajiya Bilkisu tace, ai gara kam ki koma don nima kin takuramin. Ta kira Abbas tace masa, "ka kira daddynku ka fada masa cewa, zaku koma gida. Ko da Abbas ya kira shi, saida ya kira Na'ima ya tambayeta cewa, ko itace ta buqaci komawa gidanta? Tace, eh itace. Ya tambayeta ko akwai wani abu da take buqata? Tace, a'a babu komai. Yace to likitan dake dubata yayi mata? Tace eh yayi yace, to zaici gaba da zuwa duba ta a gidanta. Haka ta tattara ta koma Gidanta wanda bata iya bambantashi da gidan yari, ko da dai bata san gidan yarin ba. Shi kam Abbas dalilin cikinnan ya samu abubuwa da dama a gurin mahaifinsa. Sannan, yasha gargadi cewa, ya lura da jikansa, tare da ba uwar duk abinda take so, don jikansa ya fito duniya da girma.kusan duk sati biyu, sai anyi hoton cikin don tabbatar da lafiyar sa. Namiji ne kamar yadda sukeso. Sai dai fa, har ynxun Abbas bai daina kawo mata gidanba, mata kala-kala wataran a ita yake sawa tayi musu girki, kuma dolenta tayishi tana kuka, tana komai ga ciki. Hakanan kuma duk randa yaji cewa, yana ra'ayinta dolenta ta miqa kanta, sannan kuma ya gargadeta cewa, har dai in ta bari dadynsa yaji wata magana daga gareta, to kuwa nata daddyn sai abinda yafi haka. Babu ranar banza da Na'ima ba zatayi kuka ba, gami da dana sani, ga dinbin nadama data cika zuciya da ga6o6inta. Gani take ko mimi ynxun ta fita kwanciyar hankali. Abin takaicin gashi babu dama ta koma gida sbd in daddy yaji allura ce zata tono garma. Ita kanta Momy Nafisa komai ya kwance mata. A ynxun bata qi ace auren Na'ima ya mutu ba, cikin ma ya 6are. Rayuwa kenan mai canji.
3⃣0⃣Kwancitashi har an cinye wata daya da tafiyar su Ismail. A farkon tafiyarsu, Mimi bata da wata matsala domin yaya Amina tana yi mata komai, sannan ko girki zatayi, saita tambayi Mimi me zata ci, a dafa. Mimi bata komai, sai kwanciya sai sallah, sannan takan dan taka da sandarta a tsakar Gida da cikin daki. Zuwa ynxun ma takan dan taka ba sanda, amma ba sosai ba, din Mimi tana da tsoro. Haka nan Ismail kan kira su a waya yana jin lafiyar su a duk lokacin daya samu sukuni. Sai dai kamar yadda hausawa suke cewa, zara bata barin dami haka yake. Domin kudinda Ismail yabar ma yaya Amina sun qare, sannan abincin ma ya qare, sai dai awo sukeyi in abban saddam ya dan samo. Haka ruwan sanyi in sun saka na saidawa a fridge, sai a yini bai fisu yi Naira hamsin ba, ko kuma maqota su amsa bashi. In kuma da kudi zasu saya su tafi shago. Hakan yasa suka shiga halin matsi, musamman ga Mimi wadda bata saba da irin wannan rayuwar ba. Kafin akai wanu lokaci, Mimi ta qara lalacewa, tayi baqi, ta kode. Ga wasu qurarraji da suka fito mata a fuska. Wata safiya Mimi tana zaune akan tabarma a tsakar dakinta, ruwan Lipton ne a gabanta da yankan biredi. Hawaye suka zubo mata da ta tuna abinda takeyin kari dashi a gidansu. Ta kalli fatar jikinta, a fili tace, dubi yadda fata na mai daukar hankali ta dawo. Ta shafa sassan wuyanta, ga rama wadda ta sani yin muni. Ta kalli dakinta, dole jikina ya zama haka, babu cima mai kyau, ba AC, ba makwanci mai kyau, ga hayaniya. Sai dai duk da haka babu abinda zance ma wadannan mutanen. Saboda sunyi matuqar qoqari daidai qarfinsu kenan. Duk abinda takeci a gurinsu bata saba da cinsu ba koma tace, bata ta6a ci ba. Amman batada za6i, dole taci, domin yunwa ba tada hankali, kamar yadda taji wani almajiri yana fadi in yazo bara. Haka nan ta tsantsoma taci ta tashi. Su kuwa mutan madina suna can karatu yana tafiya yadda ya kamata, musamman dayake sun samu wadansu 'yan Nigeria acan suna gabansu a karatu. Don haka basu sama wata matsala ba, domin har abinci sukan samu gurin 'yan uwa mazauna can wadanda suka je da matansu. Hazaqa da nacin karatu, da nacin halattar majalisin da malaman sukeyi sune suka sa Ismail kar6uwaba gurin malamansu da dama.
[18/09 10:20 pm] Inna: Canjin rayuwa
3⃣1⃣Wata rana suna zaune da Ismail da Mahmud, sai Ismail yace, ko yaushe tunanina in mun gama karatunnan mun koma Gida, wace sana'a mutum zai kama don ya kare mutuncin kansa. Mahmud yace kamar yaya? Ismail yace, banaso in zama daya daga cikin malaman da gwamnati take juyawa ko 'yan siyasa. Inaso in riqe kaina ta hanyar sana'a ta, yadda zanji dadin fadawa mutane gsky. In kirasu zuwa ga addinin Allah, ba tare da na canza maganar Allah da manzonsa zuwa son zuciyata ba. Kwadayin abin hannun mutane shike sa wasu malaman kasa fada masu gsky. Ya dafa Mahmud, ka san Allah, sai ynxun ne ma na dana zo nan na qara sanin darajar ilimi. Na fahimci cewa, babu wani mai kudin daya kamata abi shi Gidansa don koyama 'y'ayansa karatu. Ilimin addinin musulunci ya girmi haka. Kamata yayi duk mai buqata yabishi zuwa makaranta. Mahmud yace, hakane batunka Ismail. Amma in mun yi digiri dinmu, ba koyarwa zamu nema a jami'a ba? Ismail yace, zamu nema, ba don dokar makarantarnan ta hana dalibi yin sana'a ko aiki ba, da munyi aiki ko sana'a. Mahmud yace, da ko littattafai muke siya da irin su jallabiyu muna turasu can Gida. Ismail yace, ko ta gurin Malam ne, da an samu alheri. Amma tunda qa'idarsu ce, sai mu haqura mu bisu yadda sukeso. Mahmud yace, karka damu, zamu yi wannan tunanin in mun kusa hada karatunmu. Ismail yace, inason in gina makaranta, babbar makaranta, amma lamarin babu sauqi. Mahmud yace, inda anan qasar ne, zaka samu masu taimakawa, amma mu masu kudin qasarmu, gsky taimakonsu da sauqi. Masu taimakon basuda yawa, wasu ma in zasu taimaka sai sun debi 'yan jarida. Sukayi dariya, sannan suka tafa.
3⃣2⃣A batun kyau, Ismail yayi kyau. Sun yi kyau na ban mamaki, musamman Ismail, wanda ya kasance fari. Jajir yayi sbd AC, ga cima mai kyau. Yayi 'yar qiba, farinsa yayi tas-tas, gashin kansa da sajen sa zuwa gashin bakinsa, sunyi shar tamkar an shuka su. Idanunsa sunyi tas-tas le6unansa sunyi jajir. Kallo daya daka masa, zaka san ya canza. Kai ko shi da kansa ya kalli kansa yana gode ma Allah daya halitta shi. Ko Mahmud dayake baqi yayi kyau, yayi sumul. Kwanci tashi rayuwa tana tafiya, har azumi ya kawo kai. Su Ismail sukan dan yo aike daga dan abinda sukayi ta ragewa daga dan abinda suke samu na tallafi daga makaranta. Wani dan uwansu dalibi shine ya hadasu da wanda zasu dinga turawa saqon, sai Malam ya amsa sannan ya kira abbansu saddam yaje ya amsa. Farkon azumi sai yaya Amina ta samu ciki, ta kama laulayi, sai aikin gidan ya koma hannun Ummi da saddam. Rashin lafiya yaya Amina takeyi sosai. Hakan shi ya tilasta Mimi fitowa don kamawa su Ummi aiki. Tana taimaka mata da girki, shara da wanke-wanke. Sbd lokacin ta warke sarai, sai dan dingishin da takeyi wanda ba dolene a gane in ba kayi mata kyakkyawan sani ba. Shima dingishin da takeyi saida sukaje asibiti, Doctor salis ya fada musu lokacin da likitan da yai mata aikin zaizo. Ko da lokacin yayi sunje kuma sunyi masa bayani, yace karta damu zata koma rass dinta. Tsoro taji lokacin da zata soma tafiya. Amma tunda batajin ciwo agurin, babu wata matsala. Haka kuwa kafin sallah, tayi sumul a fannin lfy. Saidai fa ga wanda yasan Mimi zaiyi wahala in ya ganta ya ganeta. Hakanan tunda tazo gidan bata ta6a fita ba, ko kanta saidai a wanke a gida. In ya isheta, tasa yaya ta kama mata kalba, domin ko a da bata damu dayin kitso ba. Amma lokacin sallah a ranar idi ta saka Ummi ta rakata saloon ta wanko kanta. CANJI DAI NA RAYUWA gashi nan qarara a gurin Mimi.
[19/09 9:35 am] Inna: Canjin rayuwa
3⃣3⃣Alhaji bashir ya kalli Hajiya sauda, sannan ya 6alli karas din data wanke masa yakeci, sbd likitansa yace, lallai yana da kyau ya dinga cin karas sbd yana qarawa masu ciwon suga qarfin ido. Yace, "kina dai korata ko?" ba haka bane, ta yaya zan gaji dakai? Yace to kince in tafi Abuja. Tace kawai naga ka dade bakaje bane, kusan tunda ka sallamawa yaran nan kasuwancinka, sau daya kaje. Gashi har anyi azumi, an gama, yau kuma sallah. Yace, shikenan zance Nafisa ta tattaro yarannan gaba dayansu, suzo katsina suyi sallah anan katsina. Sam bana jin dadin yin sallah ko ina inba gida ba. Kinsan wannan. Tace, shikenan suzo nan din. Yace, banda Na'ima tanada tsohon ciki, da sun zo da ita nan itama cikin danginta. Sauda tace, zaiyi wuya minister yabarta, yadda naji kana fadin yanaji da jikansa. Yace, hakane kam. Sai kuma Mimi ta fado mata a rai. Ko ynxun ina Mimi take? Ko tana cikin wane hali? Anya kuwa ba zata bi shawarar Hajiya mardiyya bane? A wani zuwa da tayi ne, suna zancen Mimi, tace ynxun ke Hajiya sauda kin biyema zancen mazannan, kinbar 'yarki ba tare da kinsan halin da take ciki ba? Kiyi tunani fa, su maza ba kamar mu bane, zai iya jure rashin ta, kuma koda wane irin hali take ciki. Hajiya sauda tace, ni banason yace, banji maganarsa ba. Tace, a 6oye zakisa a bincika miki inda take, sai kije ki ganta. Sauda ta danyi shiru tana nazari, can tace, yayi min bayani kuma na gamsu, harma nayi masa alqawari. Hajiya mardiyya tace, shikenan tunda kince haka.
Alhajin ne ya katse mata tunani da cewa, kina tunanin Mimi ne ko? Ta kalleshi. Yace, sauda nima tana raina. Hawayen data jima tana tarawa suka zubo mata. Ya zaro idanu, cikin matuqar mamaki. "Sauda keda kk bani haquri, kuma yau kece da hawaye? Lallai haqurinki ya soma gazawa. Tace, Alhaji inason Mimi kamar yadda kowace uwa takeson danta. Kaga kuwa dole in damu da lamarinta. Da ace mutuwa tayi, na tabbata da ynxun na dangana. Amma tunda tana raye dole in zama cikin tunaninta. Kila ma ynxun ta rasu.
3⃣4⃣Ya matsa hannunta, ba ta mutu ba, ta samu sauqi tun watannin baya, an sallameta daga Asibiti, kuma tana zama gidan 'yar uwar mijinta wadda sukayi zaman jinyarta tare, ko da bata fita, ina zaton zuwa ynxu ta saba da irin rayuwarsu. Ta kalleshi da mamaki, "duk ina ka samu wannan labarin? Yayi murmushi, ke kinsan son da nake yiwa Mimi bazan iya yin da nake tayin iqirari ba. Sbd haka nayi bincike akanta. Tun daga kan likitan daya amshesu har zuwa can Unguwar tasu. Kuma an tabbatarmin yaron yana kula dasu sosai. Haka nan tunda ta shiga gidan 'yar uwar tasa bata ta6a fita ba. In ma ta fita, to mai bani labarin yace, shi bai ta6a ganinta ba. Hajiya sauda tace, lokaci yayi daya kamata mu nemeta, tunda ta horu. Yace, a'a lokaci baiyi ba. Ki sake yin haquri kadan, sbd ynxun haka batun da nake miki mijin nata bayanan, yana madina yana karatu. Sannan akwai wata yarjejeniya tsakanin Mimi da mijinta. Likitan ke bani bayani. Bai fadamin yarjejeniyar da sukayi ba, amma ya bani shawara akan kar mu nemeta da wuri, domin akwai yiwuwar ta sake guduwa. Ya tabbatar min cewa zai nememu da kansa in lokaci yayi, don ya kawo mana ita da kansa, a wata fira da sukayi. Don haka inason ki qara haquri.
Ta sauke ajiyar zuciya. Shikenan Allah yasa munada rabon ganawa, ya sada mu da alkhairi. Yace, insha Allahu zamu gana da ita. Tace, to Allah yasa. Mutuwa ce gatanan da take ci kamar rana. Ynxun kuna tare da mutum, Anjima ace maka ya mutu. Yace, hakane, Allah dai ya bamu cikawa da imani. Dubi maqocin nan namu mutuwarsa ta kada ni sosai. Tare fa mukayi sallar isha'i, lafiya mukayi sallama dashi. Amma sai muka wayi gari ya zama gawa. Sauda tace, ikon Allah kenan. Allah yasa mu cika da imani, in tamu tazo. Ameen, inji Alhaji. Sannan ya miqe yana fadin bari indan fita. Itama tashi tayi donyi masa rakiya. Bayan dawowarta ne ta nufi dakin su hasana don tabasu labarin data samu game da Mimi. Domin kullum suma cikin zancenta suke.
[19/09 6:54 pm] Inna: Canjin rayuwa
3⃣5⃣Kwanci tashi mai cinye kwanakin bawa. Yau gashi mun wayi gari su Na'ima anayin naquda. Da qyar ta kira wayar momy Nafisa ta fada lata, sbd azaba. Tace, Momy kizo marata tana yimin wani irin ciwo wanda ban ta6a ji ba, ina zaton ma dai mutuwa zanyi. Momy tace, ganinan haihuwa ce. Saida tabi ta gidan Hajiya Nana ta dauketa suka nufi asibiti. Hajiya Nana tace mata ki kira mara mutuncin ki fada masa mana. Ta kira Abbas har sau biyu bai dauka ba. Don haka sai ta kira uwarsa ta fada musu. Ba'ayi minti talatin ba sai gasu a asibitin. An gaisa sama-sama, sannan suma suka nemi wani mazaunin suka yada nasu zangon. Momy Nafisa tana fatan 'yarta ta sauka lfy, yayin da Hajiya Bilkisu ke fatan jikanta ya iso lfy. Kusan awa biyu a haka sannan wata Nurse ta fito tanayi musu albishir da haihuwar 'yarsu, kuma ta samu da namiji kamar yadda hoto ya nuna. Nan aka kaure da murna. Su Hajiya Bilkisu kam tasu murnar tayi yawa. Nan suka shiga kiraye-kirayen 'yan uwa suna fadawa dangi tare da daukan yaron hotuna kala-kala. Qa'idar asibitin, ko lafiyarki lau kk haihu, sai kinyi kwana biyu kafin a sallameki sbd su tabbatar da babu wata matsala. Hakan ta kasance ga Na'ima. Amma randa aka sallameta, rannan tsiya taso ta kaure a Tsakanin su. Domin Hajiya Bilkisu tace, gidanta za'a je, yayin da mai jego tace, itafa ba zataje can ba, Gidansu zataje. Momy Nafisa tace, tunda bataso abarta. Hajiya Bilkisu tace, sam. Nanma Abbas dinne ya kira Alhaji wanda ke umra, ya fada masa halin da ake ciki. Ransa ne yayi matuqar 6aci, ya kira Momy Nafisa yayi mata tatas. Yace kula ta bar masa mata yayi yadda yakeso da abarsa. Kuma yana mai sake sheda mata kar ta bari tayi sanadiyyar auren yarinyarnan. Ba tada yadda zatayi, cikin takaici ta bari suka tafi.
3⃣6⃣Ranar suna yaron yaci sunan mahaifin Abbas, wato Aqilu. Sam Na'ima bataso wannan sunan ba, domin itama taso ne tasa sunan nata mahaifin. Amma yace, ba tada ikon za6a ma dansa suna. Tace, kai kayimin naqudar yaron? Yace ai ba ruwa kk sha kk samu cikin ba. Haka dai take ganin qarfin hali iri-iri akan san da ta haifa. Sai kace wanine cikinsu yayi mata wahalar cikin. Hajiya sauda da Hajiya Binta, duk sun halarci sunan, amma Gidan Momy Nafisa suka yada Zango. Sai dai 'ya'yansu ne sukaje can gidan sunan, domin harda su usaina akaje. Sai yamma sannan su Hajiya sauda sukaje gidan mai jego. Sai dai Hajiya sauda tayi matuqar mamakin ganin yadda Na'ima take a kode, a rame, Na'ima mai garin jiki, amma harda qashin wuya. Hajiya sauda ta kasa dannewa tace, Na'ima kinyi ciwo ne kafin ki haihu? Kai ta sunkuyar, "nayi ciwo sosai Hajiya. Hajiya Binta kuwa baki ta ta6e, tare da cewa, Ai dama hangen dala ba shiga birni ba. Alhaji Bashir kuwa, ta Abuja ya sauka don yaga sabon jikan nasa tare da 'yar tasa. Duk da yana namiji, yayi matuqar mamakin ganin lalacewar Na'ima. Amma sai yayi shiru sbd ya san cewa haihuwa tayi, kuma baisan irin wuyar da tasha ba.
[19/09 6:54 pm] Inna: Canjin rayuwa
3⃣7⃣Ismail da Mahmud suna zaune a farfajiyar makarantarsu, inda sukan hadu da abokansu don qarama junansu sani, da qaruwa da basirar juna. Yau kam su biyu ne saura basu riga sunzo ba. Mahmud yake cewa, Ismail kasan me nake tunani? Ismail ya dago kansa daga littafin dake hannunsa, yana dubawa yace, sai ka fada. Mahmud yace, wannan hutun da zamu samu tunda na qarshen shekara ne, yanada tsawo, zamuje gida. Ina tunanin da matata zan taho. "wace matar?" Mahmud yace, Rabi'a mana. Aure zansa a daura mana. Dariya sosai Ismail yayi, sannan yace, ba kace ka fasa ba? Mahmud yace, kai malam haqurina ya qare. Kullum cikin mafarkai, gara kai gwanin azumi ne. Ismail yace, in kaga zaka takura kuwa yin hakan shine mafita. To amma ya batun aikin hajinmu? Don gsky koda hutuna zai qare banje gida ba, nayi wa kaina alqawarin aikin hajji. In na samu yadda nakeso la duk shekara sai nayi har in gama karatu. Mahmud yace, munada lokaci ma, tunda sai an yi fiye da sati biyu da gama aikin hajji za'a koma hutu. Ka ga kuwa har zamuje mu dawo. Ismail yace, Allah ya kaimu lokacin, ai hutun ma ya qarato. Su Ismail sun dan tara kudi sakamakon wani aiki da sukayi tare da amincewar hukumar makarantarsu. Wadanasu masu hannu da shuni ne suka nemi makarantar ta taimaka musu da dalibai wadanda zasuyi musu rabon abincin sabil, da yake can qasar kowa so yake yi yaga an cinye nasa. Shine makarantar ta nemi dakiban ta tuntu6e su ko akwai wanda keson yi. Ismail da Mahmud suka shiga cikin sahun wadanda suke son yi. To anan ne suka samu kudi. Kamar yadda suka tsara hakan ce ta kasance, domin sunyi aikin hajji lfy sun gama lfy. sannan suka koma makaranta sukayi shirye-shiryensu suka nufi gida Nigeria. Abuja aka sauke su. Zukatansu fal da farin ciki mara misaltuwa. Ismail yace, gsky Gida daban ne, duk da cewa Abuja ba katsina bace, sai naji wani irin dadi, duk da cewa qasar dana baro tafi tawa komai, amma farin cikin na daban ne. "Ai Gida yayi." inji Mahmud.
[20/09 12:59 pm] Inna: Canjin rayuwa
3⃣8⃣A kaduna sukayi azahar, sannan suka dauki hanyar katsina cikin qosawa. Mahmud yayi murmushi don Jindadi, don cewa zaiga iyaye da kuma Rabi'a. Ya kalli Ismail, na qosa matuqa mukai Gida. Ismail yayi dariya, "wai kai wa kk zumudin gani ne haka?" Mahmud yace, su inna dasu Malam, sai kuma rabi'a. Ismail yayi murmushi. "Gara dai ka fadi gsky. Mahmud yace, gskyr kenan, kai wa ka qosa ka gani? Ismail yace, yaya Amina mana da 'yan yaranta, tunda ni ba uwa gareni ba bare uba. Sai dai 'yan Gidanmu da yayuna, duk da cewa, su ba lallai bane suyi murna da ganina. Amma harga Allah nidai ina sonsu, kuma nayi kewarsu. Haka ina kewar Malam sosai. Mahmud yace, kayi tuya ka mance da albasa, matarka fa khadija? Ismail yayi murmushi, "kasan harga Allah na manta da ita." Mahmud yace, sbd me? Ismail yace, sbd ko waya na kira, ba ko yaushe take amsa ba. Ba ta damu dani ba, shiyasa. Amma duk sadda zan sayi Tsaraba bana mantawa da ita. Mahmud yace, kenan bakayi kewarta ba? Ismail yace, ba sosai ba. Don nasan itama bata damu da ganina ba. Mahmud yace, kamata yayi kawai ka taho da ita in zamu dawo. Ismail yace, banajin hakan a jikina, ni kwanakinnan ma mafarkin Zainabu ke damu na, da kuma yawan tunaninta. Mahmud cikin jin haushi yace, wacece kuma zainabu? Nayi tsammanin ma ka dade da shafe babinta? Gidan wani fa take. Ismail yace, na dade da shafe babinta Allah kuwa. Tunda tayi aure, ka ta6a jin nayi maganarta? Mahmud ya girgiza kai. Ismail yace, ni kaina bansan dalilin dayada ta dawo cikin rayuwata ynxun ba. Mahmud yace, sharrin shaidan da mugayen mafarkai.
3⃣9⃣La'asar sakaliya, guraren qarfe biyar suka sauka garin katsina. Shatar mota sukayi zuwa gida, za'a fara sauke Ismail gidansu yaya Amina, domin suna kan hanya, sannan a wuce da Mahmud. Ta kan layinsu Zainabu zasu wuce, sbd Gidansu yana bakin titi. Tun kafin su qaraso yaketa leqen gidan. Daf da zasu gota gidanne, kamar cikin mafarki, idanunsa suka qyallo masa Zainabu ta fito daga maqotansu dauke da bokiti a hannunta. Da alamu ruwa ta debo. Ismail cikin sauri yace, Kalli Zainabu, Mahmud. Mahmud ya waiwaya ya hangeta. Yace, tabbas itace. Qila tazo ganin gida ne. Ismail dai yana can yanata waiwayen Zainabu har ta shige gidansu. Ya lumshe ido gabansa yana wata irin faduwa. Gida Zainabu tazo kamar yadda Mahmud yace, ko kuwa aurenta ne ya mutu? Mahmud ya lura da yanayin da Ismael ya shiga. Don haka sai ya harareshi, cikin salon son kushe Zainabu yace, duk ma ta tsufa, qila ma ynxun ta haifi yara uku. Da sauri Ismail ya kalleshi, "haba dai Mahmud! Sai kace, akuya, duka yaushe akayi mata auren? Mahmud yayi dariya, tsufan ne naga yayi yawa. Ismail dai bai tanka ba illa dai yanason sanin labarinta. Sadam yana fitowa an aikeshi sai kurum yaga mota ta tsaya. Shima tsayawa yayi, domin ganin ko su kawun nasa ne. Sororo ya tsaya yana kallon kawun nasa tamkar wani sabo fil. Da gudu ya juya cikin gida yana fadin mamanmu! Kizo ga kawunmu nan ya iso! Mimi ta rasa dalilin dayasa taji gabanta yayi wata irin faduwa. Tana daga cikin dakinta, ta sake jiyo saddam yana fadin, kinga kawunmu sai kace wani balarabe. Da sauri su yaya Amina suka fita, ga tsohon ciki, Ummi kam da gudu ta isa ta qanqameshi. Cikin murna suka gaisa da Mahmud, sannan aka kwashe kayan Ismail zuwa cikin gidan, sannan ya rako Mahmud zuwa gurin motar, sukayi musabaha, yace, ka gaidamin Malam. Sai na shigo zuwa dare. Ya koma cikin Gida, ya samu su yaya sunata yi masa shirye-shiryen inda zaici abinci. Ya Kalli yaya, dama ciki ne dake? Shine muna waya baki ta6a fadamin ba, da nayi miki tsarabar kayan jarirai da kuma pampers. Suna arha acan. Ina gani gurin abokan karatunmu masu iyali. Tayi murmushi, cikin kunyar qanin nata. Tace kurum sai ince maka inada ciki? Kafin ya sake magana tace, mu shiga ciki mana ga abinci.
[20/09 12:59 pm] Inna: Canjin rayuwa
4⃣0⃣Ta kalli Ummi, "kira auntynku mana, ko tana varci ne, sarkin varci." Ya kalli dakin, "dama tana ciki ne? Yaya tace, eh, sai dai ynxun haka varci takeyi. Yaya ta soma gabatar masa da abinci dana sha mai sanyi harda kaza aka soya masa. Yace da baku wahalar da kanku ba gurin soya min kaza, ko acan na jima banci ba, sbd ta hau min kai. Yaya tace, ai kuwa gashinan ka zama tamkar balarabe. Ka ganka kuwa? Ismail yayi murmushi, bari inci Alalata dai yaya. Yana ci suna hira. Ummi ta shigo tace, mamanmu aunty khadija tana varci. Tace ki tasheta kawai. Yace a'a ki varta kawai. Bayan ya gama, suka fito, yace, su saddam su kwashe kayansu sukai masa dakin khadija. Tana kwance tamkar mai varci, amma idanunta biyu. Gabanta ke faduwa tanajin jin qamshinsa, lokacin daya shigo dakin, bata ta6a jin irin qamshin ba. Yana tsaye yana kallon ta. Yaya ta shigo tasa hannu ta girgiza ta, "khadija ki tashi mana, magriba tabkawo jiki, ke varci baya yi miki wahala." Miqa tayi sannan tace, yaya kk ce mene? Tace, ki tashi Malam Ismail sun iso dazu. Shikam yana jingine da bango ya harde hannuwansa. Mamakin ramarta yakeyi, ga shi tayi baqi, ga qurarraji a fuskarta. Da ma ita ba qiba ba, sai tyi tamkar wata baby. Mimi kasa dago ido tayi ta kalleshi. Kanta a qasa tace, sannu da zuwa kawun su Ummi. Sunan data kirashi dashi yasa shi murmushi. Yace, yauwa sannunki malama khadija. Muryarsa da taji ta canza ne yasata dago kai. Jin muryar tayi tamkar ta balaraben da ya koyi hausa, ko ko bafillatanin da hausa bata isheshi ba. Mamakin kyawun surarsa ta bayyana a fuskarta, ta kafa masa ido, batasan lokacin da bakinta ya furta cewa, kai! Amma kayi kyau da yawa. Qasar ta canza ka, ta amshe ka. Yayi murmushi, a zuciyarsa yace, ina girman kan? Ya dubeta, nayi kyau? Khadija dama can ni mai kyau ne. Tadan ta6e bakinta tare da yin dana sanin fadar hakan a ranta, ta lumshe ido. Maza sunada kyaune? Kawai dai ka samu hutu. Yayi dariya, ko ma dai yaya ne kin yaba, kuma nagode. Taso kidan taka in gani, tafiyarki ta koma daidai? Yaya dake zaune bakin gado tana jinsu, sai ta tashi, "bari in kira abbansu saddam in fada masa ka iso, ta fice.
[20/09 8:59 pm] Inna: Canjin rayuwa
4⃣1⃣Mimi tace, in kayi haquri, ai zaka gani, ba sai kasa ni yin wata tafiya ba. Yace, amma kin daina dingishin? Harynxu tana tare da jin haushin maganarsa ta dazun, tace, "Qila." ya matso ya zauna a bakin gadon, ya rage muryarsa, "kinyi baqi, kin rame. Amma muryarki dinnan mai sauti can qasa da miskilancinki suna nan." Ta zuro qafafunta ta dayan gefen ta sauka. Sannan tace, bai kamata kaji mamakin ganin na canza ba, domin kafi kowa sanin komai. Ina Mahmud? Shi ma ya miqe, yana gida. Anjima ki shirya muje mu gaida malam. Ta girgiza kai, "ban fita kayi haquri." yayi dan murmushi, hakane, tam bari na dan yi wanka kafin a kira magriba. Ta nufi gurin madubinta tana fadin yanada kyau. Ummi ce tasa ruwan wanka takai masa. Ya bude jakarsa ya dauki kayan wankansa cikin wata jaka ta leda, wadda aka yita don saka kayan wanka. Sannan ya ciro jallabiyarsa, wata mai shegen kyau ruwan hanta, tana da zif daga qirjinta har wuya, sai kuma tsintsiyar hannu da ma6alli. Sai hula mai kalar zaren da akayi dinkin. Mimi tana kallonsa da gefen ido, ya dora kayan saman gadonta, sannan ya fita. Da kallo tabi bayansa. Kyawunsa yana bata mamaki. Bayan ya fito, sai daya shirya tsaf, Mimi tana ta satar kallonsa. In ta ga alamun zaya waiwayo saita sauke kanta. Ya feshe jikinsa da turarukan larabawa, qamshinsa ya gauraye ko'ina, sannan ya kalleta, nayi kyau? Cikin zolaya yayi tambayar. Ta ta6a baki, tare da cewa, ina wani kyau anan? Yace son ranki kk fada. Bari inje gidanmu. Daga can in wuce in gaida malam. Tace ka gaida su. Ya dauki qaramar jaka daga cikin jakunkunan da yazo dasu. Tabi bayansa da kallo har ya saki labulan. Ta jingina da sif dinta tana mamakin yadda ya rikita ta har haka. Yaya tana zaune zatayi alwalla, ya ajiye jakar a gabanta, tsarabar 'yan gidanmu ce, su yaya jallabiyu, matan kuma dabino ne da zam-zam. Inna kuma harda darduma da wata doguwar riga. Yaya tace, yayi, Allah ya bada lada. Yace Ameen. Ya dauka ya fita.4⃣2⃣Duk wanda suka gaisa da Ismail, sai yace, Masha Allahu kayi kyau. Yana shiga gidansu ana kiran magriba, ya Kalli dakinsa yayi murmushi, sannan ya shiga cikin gidan, babu zato suka ganshi. Don haka suka shiga kallon kallo. Sai kuma aka shiga yi masa sannu da zuwa. Yayi musu qwarjini sosai, don haka da 6are-6aren jiki sukayi ta amsa gaisuwarshi. Ya shiga dakin inna sai yaga ta qara masa tsufa. Ya gaida ta sannan ya kawo tsarabarsu ya bata tare da yi mata bayani a gurguje ita kanta duk sai yaga tayi sanyi. Ya nufi masallaci. Bayan sun idar da sallah nan sukayi ta gaisawa da mutane suna tayi masa sannu da zuwa. Yana tare da jama'a har zuwa bayan isha'i, sannan ya nufi Unguwar su Mahmud. Ya shiga cikin gidan suka gaisa da mutan gidan, sannan ya fito ya zauna gaban Malam inda suka gaisa tare da ci gaba da hira. Malam yayi murna da zuwansu, sannan ya saka musu albarka. Sun jima suna hira suna ta bashi labarin makarantar. Daga bisani suka nufi gidansu Rabi'a, shida Mahmud. Yaro ya samu ya tura cewa, ana kiran Rabi'a. Bayan tafiyar yaron ne yace, bari mu gani tana fita da bananan. Ismail yace, kar kayi zargi. Rabi'a ba zata yi maka haka ba. Dan aiken ne ya katse su da cewa, wai ance tayi aure. "Aure?!" Mahmud ya tambaya cikin faduwar gaba. Ismail yace, ba kunyi waya ba? Mahmud cikin tashin hankali yace, ko jiya munyi waya, bazata kawai naso inyi mata, shiyasa bance mata muna hanya ba. Ismail yace kai yaro je kace inji Mahmud. Tare da dan aiken suka fito tayi murna sosai da ganin masoyinta. Tace ina zuwa. Duk da cewa dare ne, saida ta qara hoda a fuskarta sannan ta fesa turare mai madaidaicin qamshi, sannan ta dauki tabarma ta fito. Shikam Ismail, suna gaisawa daya lura masoyan suna dokin juna, sai yaga ya dace ya basu guri. Don haka sai yace, to ni zan tafi. Suka yi musabaha da juna. Ismail yana cewa, sai na shigo da safe. Zan shigo in kawo ma Malam tsarabarsa. Mahmud yace, shikenan Allah ya kaimu. Gidan yaya Amina zaka kwana? Ismail yace, a'a Gidanmu zanje in gyara dakina ynxunnan. sukayi bankwana ya wuce.
4⃣3⃣Gidansu ya koma, inda ya bude dakinsa, duk qura da yanar gizo-gizo. Ya kai qarfe goma sha biyu Tsakanin share-share da kuma goge-goge, sannan ya shiga gida yayi wanka. Sai daya kwanta sannan ya tuna cewa yayi masu yaya alqawarin cewa, zai koma. Ya kalli agogon wayarsa, a fili yace dare yayi. Washegari tunda ya dawo daga masallaci ya sake kwanciya bai farka ba sai qarfe takwas. Ya shiga cikin gida suka gaisa da mutan gidan. Sai dai yayi Mamakin ganin yadda suka sakar masa fuska. Amma sai ya tuna cewa fa yayin dawafin sa a dakin ka'aba, yayi ta roqon Allah cewa, Allah yasa shida 'yan uwansa da suke uba daya sun fahimci juna. A fili yace, Allah ya amshi addu'ar sa. Bayan yayo wanka ne, sannan ya ciro jakar kayansa tada, ya cire ma abbansu saddam kala biyu, sannan ya dauki sauran zuwa cikin gida yaba yayyinsa, sannan ya nufi gidan yaya Amina. Mimi ce amsa sallamarsa lokacin da ya isa gidan. Tana zaune akan qaramar kujera, tana wanke-wanke a bakin rijiya. CiKin Mamaki ya kalleta, tare da tausayi, yace, Mimi kece kk wanke-wanke? Ina Ummin? Ta dago ta kalleshi, "sunana khadija ne, ba Mimi ba. Ummi sunje makaranta, yaya kuma taje ganin likita. Ko dama tana nan ka san tana buqatar taimako. Ya tsugunna kusa da ita, qamshinsa ya daki hancinta, gabanta kuma ya shiga wata irin faduwa. Maganarsa tamkar rada yace, in taimaka miki ko? Ta dago ta dubeshi, wata irin kunyarsa ce ta ji ta kamata, sbd cikin idonsa ta kalla, ta sunne kanta cikin cinyarta. Tace, ka barshi kawai, "yaya ma za'ayi kayi aikin mata? Cikin kwaikwayon muryarta yace, ai nima na matanne, kinga kenan babu laifi don nayi aikinsu ko? Yadda yayi din, sai taji ya birgeta sosai. Tace, nikam ka barshi kawai. Ya miqe tare da fadin shikenan tunda bakison taimako. Ya koma kan galan din ruwa ya zauna. "ki gama muyi magana dake. Tace, to. Kallonta kawai yakeyi cikin tausayi da birgewa. Ta gama ta kife, ta kai kwandon mazauninsa, Sannan tasa ruwa ta wanke gurin. Tana sanye ne da doguwar riga, tun irin kayanta ne data zo dasu. A ransa yace, kaya masu tsada sunada qwari, dubi yadda har ynxun kayanta suke da kyansu. Zasu jima basu lalace ba. Ta dubeshi, sannan ta nufi dakinta.
[20/09 9:57 pm] Inna: Canjin rayuwa
4⃣4⃣Da kallo ya bita, yana tuno asalin Mimi 'yar gata, 'yar jin kai, yarinyar da batason talauci balle hulda da talaka. Matuqar tausayinta yakeyi ynxun. Sannan ya jinjina mata sosai, domin bai ta6a zaton zata sauko haka cikin sauri ba. Hakanan ya fahimci cewa halinta ne yin abinda tace zatayi. A fili yace, wannan ya zama dole in cika mata dukkan alqawuran dana daukar mata. Wata zuciyar tace, harda saki? Gabansa ya fadi, amma sai ya miqe ya nufi dakin. Tana kakka6e gado, ya shigo ciki. Yace, ina zan zauna? Ta nuna masa bakin gado, bayan ta gama gyarawa, ka zauna anan. Ya zauna, yana kallonta tare da ci gaba da tuno da gatan ta har ta gama. Aikin dai babu sauri, amma tsaf-tsaf. Ta kalleshi, in nace zanyi wanka zan 6ata maka lokaci ko? Yace, yi wankanki. Ta dauki hijabi ta saka sannan ta fita. Ta dauki ruwan wankanta da Ummi ta zuba mata, sbd bata iya jan ruwa a rijiya, tsoron rijiya gareta. Bayan fitarta ne yaga wani littafi akan Allon gadonta. Ya dauka ya Kalli bangon, INDA RAI, DA RABO. Haka yaga an rubuta ajikin littafin, sunan littafin shine yaja hankalinsa zuwa ga bude shafukan littafin yana dubawa jefi-jefi har ta fito. Lura da tayi baya kallonta, sai ta shafa manta a cikin hijabin, da tazo saka kaya ne ta kalleshi, a tunaninta hankalinsa yana kan littafin ne, sai ta faki idonsa ta saka kayan. Murmushi yayi, a ransa yace, khadija ke nan, domin tunda ta fito hankalinsa yana gurinta. Bayan ta gama tazo ta zauna a daya gefen gadon. Ya dubi littafin, menene ma'anar inda rai, da rabo? Ta danyi murmushi, bansan yaya zance maka ba, sbd ka san bansan kan hausa sosai ba. Kawai dai naji su yaya suna sauraron littafin ne a rediyo, shine nace, a siyomin. "wa ya siyo maki? Tace ban sani ba yaya ce tasa aka siyo. Yace, kin karanta? Ta daga kai, alamun eh. Kin qaru da wani abu? Tace, sosai ma, duk da cewa labarin soyayya ne. Yace, shikenan zaki bani labarin wani lokaci.
[21/09 3:17 pm] Inna: Canjin rayuwa
4⃣5⃣Ya aje littafin ya fuskance ta sosai, "ki bani hankalinki muyi magana mai muhimmanci. Ta sunkuyar da kai, "ina sauraronka" bata iya kallonshi, don sai taga yayi mata wani qwarjini, ya cika dakin, "zan fara da son sanin matsalarki, in kina da wata matsala. "tana wasa da hannunta, tace, ni banida wata matsala, domin duk abinda akaci, shi za'a babi daidai qarfinsu, kuma zuwa ynxun na iya cin komai. Kuma ba'a takura min, komai nakeso nayi, zanyi ba wulaqanci. In babu zan haqura kamar yadda kowa ya haqura, shine kawai. Yace, na fahimta, to kina son siyan wani abu, ko burin yin wani abu, ina nufin na kudi? Ta saci kallonsa, banison komai na kudi, don duk abinda nakeso na kudi, bakada qarfin saimin. Don haka kar ka damu, khadija ba mimin daka sani bace, Nayi haquri da iyayena ma bare wani abin duniya. Babu komai a raina. Babu abinda yake birgeni cikin duniya ynxun. Yace, har nayi zaton zaki koma makaranta, don ki kammala digiri dinki? Tace, baka zaton in na fita iyayena su samu labarina. Yace, har ynxun baki huce da fushi dasu ba? Tace, na huce tun bayan da bakanan yaya Amina tayi ta karantomin kurakuraina ta hanyar nasiha, har na fahimci irin sa6awar da nayiwa iyayena. Ynxun kam ina nesanta kaina dasu ne, sbd ganina kusa dasu zaita sakasu cikin 6acin rai, zasu dinga tuno abinda nayi musu. Shiyasa bana fita. Banida wani buri daya wuce cikawa da imani inje in tarar da khalil. Gaban Ismail yayi matuqar faduwa, domin bai zaci jin haka daga bakinta ba. Baisan lokacin daya ce, dama har ynxun baki manta da khalil ba? Da sauri ta kalleshi, ta yaya kk zaton zan manta da wanda yake matuqar sona? Wanda ke fadamin kalamai masu sani cikin farin ciki, da nishadi. Wanda ke kwadaita min wata irin rayuwa, amma kafin mukai gareta, sai mutuwa ta katse hakan. Ya barni cikin qunci da takaici! Kuka ya kufce mata.
4⃣6⃣Shiru yayi tamkar ruwa ya cinyeshi, nazarin zantukanta yakeyi. ya dan qara matsowa kusa da ita, ya tausasa muryarsa qwarai. "Yi haquri khadija, inda zaki bani labarin soyayyarku da khalil, zanso ji. Ta dubeshi, fuska cike da hawaye, ba zan iya ba. Banason in tuna da komai game da labarin. Abinda kawai ba zan manta ba shine tsananin son da khalil yayi min. Haka kuma ba zan manta da yadda nayi ta wulaqantashi ba. Salon son da khalil yake nunamin ta hanyar chatting dina a facebook, wtsapp, da sauran irin wadannan kafofin, tun bana bashi amsa, har dadin kalamansa suka sa na soma bashi amsa, duk da ni ba amsa mai dadi nake bashi ba. Ranar dana soma son khalil, yawun bakina na watsa masa fa a cikin mutane. Amma kasan me yayi? Ismail yace, a'a tace,, ga mamakina sai naga kurum yasa harshensa ya lashe yawuna daya sauka kan kafadarsa, sannan yayi murmushi, "komai naki inason sa. In na bari yawunki ya sauka a qasa nan, nayi muguwar asara. Ta soma sabon kuka, wannan kadan ne daga irin son da khalil yayi min. Ismail yace, shikenan kiyi haquri. Allah ya yafe masa tace Ameen. Yayi shiru. Yasan ynxun yaya Amina ta rage mashi hanya da tayi wannan jihadin, na yiwa mimi nasiha harta fahimci cewa tayiwa iyayenta laifi, ba zai wahalar shawo kanta don zuwa basu haquri ba. Amman wannan ba ynxun ba. Ya dubeta, har ynxun tana share hawaye. Nace kiyi haquri. Kuma zaki iya samun wanda yafi khalil sonki, kema kuma ki soshi fiye da son da kk yiwa khalil din. Ya girgiza kai, Da wuya hakan ta kasance, nina kulle babin so, koda na samu mai sona, ni kam na tabbata ba zan soshi ba. Ismail yayi murmushin yaqe, to yaya batun islamiyya fa? Mimi tace ina daukan karatuna a gurin yaya Amina. yayi dariya, shikenan Allah ya biyata da aljannarsa.
[21/09 7:46 pm] Inna: Canjin rayuwa
4⃣7⃣Ya miqe ya dauko jakar tsarabarsu, ya dawo ya zauna bakin gado, "zo ki za6i abinda kk so cikin tsarabata. Ta matso. Ya dauko jakar ya dora ta saman Gadon. Ya soma ciro jallabiya, pink mai ratsin baqi, sai jarta, itama mai ratsin baqi, sai takalma da riga da wando kala biyu, duk ire-iren wadanda take sawa. Ta tsaya tana kallonshi, sbd ta san tsadar kayan. Kafin tace wani abu, sai kurum taga ya ciro wani gwangwani a can qarshen jakar, ya miqo mata. Da sauri ta kar6a sbd irin turarenta ne. Ta soma karanta rubutun jiki a fili tace, "tabbas shine" ta dago ta dubeshi, "siyan turarennan kayi? Yace eh, siya miki nayi. Tace ina ka samu kudi haka? Na ga kai din dalibi ne, kuma duk kayan nan suna da tsada, musamman wannan turaren? Yayi murmushi, "munyi aikin raba abinci ne ga mabuqata aka biyamu. Ta soma hawaye, ban ta6a tunanin zan qara amfani da wannan turaren ba. Nagode sosai. Ya tausasa murya don jin dadin sake burgeta. Karki damu khadija, nayi miki alqawarin in Allah ya buda min, zanyi miki gatan da yafi wanda kk ta6a shiga a fannin jin dadi. Ta sa idanunta cikin nasa, "nasan zaka iya, domin duk abinda kayimin alqawari, ka cika. Ina ganin kimar ka sosai, ynxun saura abu daya ya rage. Ya zaro mata manyan idanunsa, me? Tayi shiru, gabanta yana faduwa. Yace karki damu ki fadamin, qila na manta ne. Ta sunkuyar da kai, "maganar rabuwarmu." Gabansa yayi wani mugun faduwa. Dakin yayi tsit na wasu daqiqai kamar hudu. Maimakon yaci gaba da zancen, sai kawai yace, yau yau dale kuka karya ne a gidan nan? Yunwa nakeji. Tace, ruwan Lipton ne da biredi. In zaka ci ina zaton akwai a flask. Yace zansha shayin, kinsan mu shine ma abin shanmu kowane lokaci. Ta miqe ta nufi kicin ya bita da kallo, tafiyarta ta dawo tamkar da, cikin nutsuwa da kamewa. Ta dauko filas din ta hado da kofi da cokali da kuma suga. Sai ledar bread din. Zuciyarta kuwa tambayar kanta takeyi menene dalilinsa na share zancen rabuwarsu? Yace, ba zanci bread ba. Na saba dana can da mukeci bashi da suga.
[9/21, 16:54] A~PROF: 4⃣8⃣Ya miqe ya janyo jakarsa, ya zuba wani ganyen tea, ya zauna yana sha. Duk sukayi shiru, kowa da kalar tunaninsa. Shi ba wai ba zai iya sakinta bane, amma tsoron sa kar ya saketa, ta sake guduwa. Ta katse masa tunani, "Wai meyasa ka share batun da kawo? Ya kalleta, "ba sharewa nayi ba. Khadija muna buqatar qarin lokaci ne. Kiyi haquri har in kammala karatu na." Tace, zuwa yaushe? Ya dubeta da sauri, "kin samu wanda kk so ne? Itama cikin sauri ta kalleshi, "Allah ya kiyaye min, ni kam banason kowa. Nauyin ne nikeson a sauke min. Yayi murmushi baice komaiba. Sati biyun da Ismail sukayi a Nigeria sunyisu ne a cikin hidimar bikin Mahmud. Babu yadda baiyi da Mimi ba akan taje gurin walimar bikin, amma taqi, dolensa ya haqura ya barta. Bayan kwana biyu da kammala bikin, suka soma shirin komawa madina. Ango da Amarya cikin dokin juna a ranar tafiyar, ko cikin jirgi tamkar su hadiye juna suna ta birge Ismail, wanda ya lumshe ido yana tuno hawayen Mimi da suke zuba lokacin da sukeyin sallama. Ya tuna tambayar da yayi mata. Khadija wannan kukan kuma na menene? Ta girgiza kai, "nila ban san ko na menene ba. Ya ciro kyakkyawan hankici daga aljihunsa, sai qamshi yakeyi. "share hawayenki da wannan, sai in munyi waya kenan ko? Ya sauke ajiyar zuciya, tare da furzar da wani huci mai zafi. Yana kewar rabuwa da yarinyar. Yayi ta tuna huldarsuda kuma irin CANJIN RAYUWAR da Allah ya saukar mata. Allah yasa ya zama sanadin shiriyarta kenan. Labarin data bashi na tsohon saurayinta, abinda ya fahimta da Mimi, ita mutum ce maison aso ta, aji da ita, a nuna mata tsantsan so a fili, sannan a fada mata kalaman tada hankali. A fili ya furta cewa ban iya wannan ba. Sai kuma Zainabu ta fado masa, ya tuna da zancan su da yaya Amina bisa ganin da yayi mata. Yaya tace, masa tana gidan mijinta, qila dai tazo duba su ne. Haka yayi ta tunane-tunane har Allah ya kaisu lfy.
[9/21, 17:35] A~PROF: Satin su Ismail daya da tafiya, yaya Amina ta haifi 'yarta mace, aka sa mata Aishatu. Yaya tasha mamakin ganin 'yan uwanta mata yadda suka zo mata barka harda suna, sa6anin da ba kowa ke zuwa mata barka ba bare suna. Inna kuwa zuwanta uku. Mimi kam ta takura sosai ranar suna, domin sam batason jama'a, kamar ta bar gidan amma ba yadda zatayi, dole ta haqura.
[22/09 11:26 am] Inna: Canjin rayuwa
4⃣9⃣Lokaci yana qhudewa kwanaki quna qarewa, yau gashi su Na'ima anyi arba'in. Ta matsu qwarai tabar gidan minister, domin ko abincin da zataci sai taje kicin da kanta ta kar6a. Hatta 'yan aikin gidan sunsan batada wata kima, tunda a gabansu za'a zage ta tass. Don haka ko aiki tasa su basa yi mata. Sannan ga gadara da yaron, kullum akayi masa wankan safe, za'a tafi dashi gefen kakarsa, sai yamma ko in ya buqaci Nono. Da ma mai wanka da shirya shi musamman aka dauko. Shi kuwa Abbas sai dai ta jiyo muryarsa daga can sasan. Bata damu ba don ita ynxun ya gama sire mata. Kwana arba'in da bakwai suka maida ta gidanta bayan an kafa mata dokoki da sharudda akan yaron, sai kace ba itace ta haifeshi ba. Lokacin ne ma ta samu zuwa gidansu yini. Kuka momy Nafisa ta tasa Na'ima tayi tayi, sbd baqi data qara akan nata, gashi duk tayi zuru-zuru, idanu sun shige. Lokacin Alhaji bayanan Abuja, tace, bari dai yau dadynku ya dawo zan fada masa komai game da halin da kk ciki. Na gaji, gara komai zai faru, ya faru. Na'ima tace, yauwa momy don Allah ki taimaka min. In ba haka ba, wata rana zakije ki dauko gawata a gidan Abbas. Har dare Na'ima tananan tana jiran dawowarsa. Sun zauna sun karanto masa komai game da halinda Na'ima take ciki. Yace sam qarya ne, domin ta jima tanason kashema Na'imar aurenta. Su tashi su bashi guri. Ya kalli Na'ima, "karki daka ta mahaifiyarki, ki zauna dakinki shine cikar mutuncinki. Na'ima tace, Allah dady duk abinda kaji dinnan shine yake faruwa, yace kije zan bincika. Fitarta keda wuya, Alhaji Bashir ya kira layin Abbas. A tunanin Alhaji Bashir, Abbas da Na'ima duk daya ne agurinsa. Bayan sun gaisa, sai Alhaji Bashir yace, zantuka nakeji marasa dadi abakin Na'ima, tana fadamin wai bakwa zaman lfy tunda taje gidan. Shine na kira ka inji menene gskyr zancen? Abbas yace e.. to kusan akwai hakan daddy. Alhaji Bashir yace, to menene dalilin hakan Abbas? Abbas babu kunya ko shayi, yace, gsky daddy ina matuqar qoqari gurin zama da Na'ima, sbd gsky ni na wai ina sonta bane sam, Mimi nake so. "kalaman sukazo ma Alhaji Bashir a bazata, ya kuma fassarasu da cin fuska.
5⃣0⃣Amma sai ya danne, yace, in banda abin Abbas abinda yayi Mimi aishi yayi Na'ima, dukkansu 'ya'yana ne. Abbas yace, daddy Mimi fara ce mai aji. Na'ima baqa ce mai naci, amma aka dauki dauki Mimi aka ba wanda baisan darajata ba... "Dakata Abbas! Alhaji ya katseshi, cikin zafin zuciya. Yaya inayi maka magana kanayi min wani shirme? Zancen Mimi ba naka bane, qanwarta ce matarka, kuma a kanta muke yin magana. Bakason ta shine baka fada ba tuntuni, sai ynxun da kuka soma samun qaruwa? Ynxun dai abinda nakeso dakai, in tana yi maka wani laifi ne to sanar dani, sai in tsawata mata ta daina. Abbas yace, nidai son da banayi mata shine kawai matsalarmu. Alhaji Bashir yayi shiru, cikin Mamaki ya rasa me zaice, sai kawai yace, shikenan in ka samu lokaci kazo ina nemanka. Mamakin Abbas ne ya cika Alhajin, yadda yake magana cike da rashin ladabi. Kar dai ace yaronnan bashida tarbiyya. Sai kuma ya canza kiran wayarsa zuwa ga minista. Bayan sun gaisa, sai yace, ashe dama yaran nan zaman rashin jituwa sukeyi tun tuni? Minister yace, kamar yaya? Nan Alhaji ya kwashe komai ya fadawa minister har yadda suka yi ynxunnan. Sai kawai yaji minister yasa dariya, tare da fadin, karka shiga zancen yarannan. Baya sonta, yaya akayi ta haihu? Ya kamata da kayi masa wannan tambayar, lokacin daya ke fada maka cewa baya sonta. Alhaji Bashir yace, neman mata da tace yanayi shine matsalar ai. Minister yasa wata dariyar. "kar ta damu da wannan, in dai ya sauke mata nata haqqin. Kasan yarannan ba'a rabasu da son nishadi. Su kuwa mata, ai sune nishadin rayuwa. Kan Alhaji Bashir ya kulle, kenan ya daure ma dansa gindi yayi duk abinda yakeso, kuma bazai iya hanashi sa6ama Allah ba kenan? Minister ya katseshi da cewa, nayi zaton zakayi min magana akan hauhawar farashin man fetur ne? Alhaji Bashir yace, a'a ba wannan bane. Shi kenen saida safe mayi maganar kasuwanci, in Allah ya tashemu lfy, minister yace, Allah ya kaimu. Kada kasa kanka a damuwa game da batun wadannan yaran.
[22/09 11:55 am] Inna: Canjin rayuwa
5⃣1⃣Kwana Alhaji Bashir yayi da abin a ransa. Washegari ya nufi katsina. Tun saukarsa hajiya sauda ta karanci damuwa can qasa tare dashi. Amma data tuntu6eshi, sai yace, wai babu komai. Ta takura masa da tambaya don ta fada masa cewa, saidai inba zai fada mata ba, to ba zata takura masa ba. Amma batun matsala tabas tasan yana ciki. Sannan ya fede mata komai. Yace, ni damuwata ban san ta ina zan 6ullo ma lamarin ba. Hajiya sauda cikin damuwa tace, dama Alhaji baku binciki halinsa ba? Yace, ni ina na wani bincika. A zatona yayi tarbiyyar 'ya'yansa, nayi hasashen sunada lfy tamkar nawa. Ashe nayi kuskure. Shi kansa ministan, sai ynxun nake sanin nasa halayen, sbd haduwarmu babu dadewa muka qulla wannan auren. Hajiya sauda tace, duk abinda ya faru, da kuma wanda zai faru nan gaba, duk laifinka ne, kai kawai ka duba abinda zaka samu ne kawai, ka dauki 'yarka ka bada. Yace, sauda abinda ya faru, ya riga da ya faru, sai dai a kori gaba. Ni ynxun roqo na a gurinki, ki bani shawara, domin kaina ya riga ya kulle. Hajiya sauda tayi shiru, tana tunanin me zatace. Gashi dai lokacin da za'a qulla abin ba'a nemi shawararta ba, sai ynxun da za'a kwance shi. Tanason ganin mijinta cikin kwanciyar hankali, musamman shida ke fama da ciwon suga. Don haka ba tare da ta tuno masa wani abu da yayi mata abaya ba tace, shawara dai daya ce, tunda shi uban yaqi kuyi batun, ka samu shi abbas din kuyi magana. In har baya sonta, da zaman uquba gara su rabu kawai, Allah ya hada kowa da rabonsa. Yace hakane kawai mafita, ai nayi da na sani babu adadi, har ina tozarta Mimi, ina cin zarafinta, ashe ba dan mutunci bane, kuma bai fito daga cikin mutunci ba. Hajiya sauda tace, kuskure ne dai ya riga ya faru, sai dai muce, Allah ya tsare gaba. Kwanansa uku ya koma Abuja sbd kawai ya gana da Abbas. Da safe Abbas ya sameshi a Gida. Bayan sun gaisa, yace, na kiraka ne don muyi magana ta fahimta, ni da kai. In har kana ganin bakason Na'ima to kawai ku rabu. Allah ya raya muku danku. Abbas yace, daddy ka samu daddy na kuyi magana, kamar yadda kukayi lokacin da zaku qulla auren, in ba haka ba zaice nine na saketa sbd banajin maganarsa. Alhaji yace ni zan masa bayani, abinda nawai nakeso shine ka fadamin abinda ke ranka Abbas yace, daddy nima inason a rabamu. Alhaji u, shikenan jeka zanyi magana da Dadyn naku.
5⃣2⃣Sai dai duk yadda Alhaji Bashir yaso suyi maganar da minister sam yaqi. Ransa ya 6aci sosai. Don haka ya taka har gidan Abbas ya samu Na'ima, ya tambaye ta ko akwai wani canji tsakaninta da mijinta? Tace, babu wani canji, domin ynxu ko wace irin mace kawowa yakeyi, kuma dole inyi musu girki, sannan ya daukarmin yaro ya kai musu shi, kowace jaruwa tayi ra daqunarsa. Yace, dauko mayafinki da kayanki kizo muje gida. Wannan shine mafarin tsiyar data 6arke Tsakanin Alhaji Bashir da minister. Qiriqiri minister yace, shifa bai yadda da wannan hukuncin ba, saidai inta koma can Gidansa da zama har zuwa lokacin da zata yaye jikan nasa, tabashi abinsa. Alhaji Bashir yace, wannan kuma wani abu ne da ba zai yiwu ba ko a cikin mafarki. Buqatarsa kawai Abbas yaba 'yarsa takarda, in ta yaye dansu, suzo su dauka. Wannan rigima itace ta datse kasuwancin da suka qulla suke aiwatarwa. Ikon Allah kenan. Shiyasa akace, komai mutum zaiyi, tofa yayishi don Allah.
Masu son Zainabu sunata fitowa tun daga lokacin da ta haifi danta saurayi, amma kowa fada masa takeyi tanada wanda takeso, duk da cewa ba tada tabbaci akan samun wanda takeson, ko inda yake bata samu labari ba, bare tasan ko zata samu shiga. Amma begensa yananan cikin Zuciyarta, dashi take kwana, tana tashi. Bugu da qari, dole inna ta zuba mata ido, sbd tsoron hukuma, duk da irin son kudinta. Ita fatanta Zainabu tunda ta haufi danta lfy, ta samu miji ta qara gaba, ko bata yaye danta ba. Su kuwa mutan madina suna can suna ta karatu, babu ji babu gani. Ismail ya qware sosai a fannin tafsiri, yana da haddar litattafai da dama a cikin kansa. Malamansu suna jinjina ma Qwaqwalwarsa sosai. Sun sake samun wani hutun, lokacin Rabi'a matar Mahmud tanada tsohon ciki. Wannan hutun sun sameshi daf da azumin watan Ramadan. Sunso tsayawa, amma sai Malam Aminu yace, su dawo sbd shine sukeson ya gabatar da tafsir a sabon masallacin da aka gina nan Unguwar su. Masallacin Juma'a ne katafare. Kuma lokacin azumi za'a budeshi. Don haka suka nufo gida cike da doki, sbd shi Ismail mutum ne maison ganin yana daukaka kalmar Allah, kuma jama'a su qaru da iliminsa.
[22/09 4:38 pm] Inna: Canjin rayuwa
5⃣3⃣Wannan karon sun sauka cikin shirye-shirye sbd karatun azumin da zasuyi. Sam bai zauna dasu Mimi ba. Tun ranar da suka iso suka gaisa, ko kan kayansa bai dawo ta kansu ba, sai dai suyi waya da yaya. Sai ana sauran kwana biyu Azumi, sannan ya samu zuwa gidan yaya Amina, ya kwance kayansa ya basu tsarabarsu. Ranar ma dai bai zauna ba, sbd yana shigowa, Mahmud ya kirashi ya sanar dashi cewa, Rabi'a tana kan gwiwa. Da sauri ya fita ya samu Mahmud din a qofar gidansu Rabi'a. Fada ya rufe Mahmud din dashi kan cewa a fito da ita akaita asibiti. Zasu tafi nemo mota kenan, saiga wan rabi'a ya fito daga cikin gidan, cikin murna ya fada masu cewa, ta sauka, kuma an samu da Namiji. Murna gurin Ismail tamkar tashi matar ce ta haihu. Da dare ya shigo Gidan su yaya Amina, Aishatu ce kadai a tsakar gidan tana ta wasan ruwa, yasa hannu ya dauketa cak. Yayi sallama a qofar dakin yaya, tana sallar isha'i, yace Ummi yaya kk barta ita kadai a tsakar gida tana ta wasan ruwa duk ta jiqa jikinta. Tace, nima ina sallah ne kawu. Ynxun na ida. Ya miqa ta ,amsheta kisa mata kaya. Auntynki tana ciki? Tace, tana cikin tana sallah itama. Mimin batasan dalilin dayasa ta damu da Ismail ba wannan zuwan nasa. Duk da cewa, shi sam bai damu da ita ba wannan karon, tanason yin abinda zai birgeshi. Haka wannan karon yafi wancan zuwan wayewa, da gogewar ilimi, sannan kyawunsa yafi na wancan zuwan. Ko itace ke ganin haka? Oho. Lokacin da ta jiyo muryarsa, saita samu kanta da fesa turare a jikinta da kuma dakinta, ta zauna a bakin gado. Sai Zuciyarta ke tambayarta wai sbd me tayi hakan? Kafin ta lalubo amsa, har yayi sallama, ta amsa. Yace, in shigo? Tace ka shigo mana.
5⃣4⃣Ya shigo, cikin salon zolaya yake cewa, bayi zaton bake daya bace. Tadan ware idanu, da alamun Mamaki, "nida wa kk zaton samu? Yace, qawarki mana. Ta dafa hannunta da saman gadonta, tare da karkata kanta, ta dora kan kafadarta. "Nikam banida qawar data wuce Ummi, sai ko Aishatu. Yace, kardai kicemin har ynxun baki fita? Tace to ina zani kawun su Ummi? Wa na sani? Yayi dariya sbd sunan da ta kirashi dashi. Sunan nan da kk fadamin yana bani dariya khadija. Me zaisa ba zaki kirani da sunana ba Ismail? Tayi murmushi, "to ni bana iya fada ne. Na fa girmama ka ne. Ta fada da sigar shagwa6arta. Nidai gsky a daina fadamin wani kawun su Ummi, a kirani da wani abu kawai. Ta dubeshi, to Malam? Yace a'a ni dalibi ne, koyon karatu nakeyi. Kice min Ismail bin Abdurrahaman, ko kice, Abu Rumaisat. Tace ban gane Abu Rumaisat ba? Yace sunan yarinya ta kenan ta farko in Allah ya so. Rumaisat ko kice ummu suleim, duk sunanta ne. Ba kayi aure ba, amma kana fadin Yarinyar da zaka haifa? To in Maman taqi yarda fa? Maman babyn. Ya rasa dalili, sai yaji gabansa ya fadi, da take Cewa baiyi aure ba. Yace, nasan zata yarda, domin duk matar da zan aura, ba taqi yimin biyayya akan hakaba. Zataso abinda nakeso. Game da batun aure kuwa, zanyi shi da zarar na kammala karatuna. Kafin lokacin na samu mai sona. Mimi ta samu kanta da damuwa, sakamakon amsar daya bata. Tayi shiru. Ya katse ta, bayan ya Kalli agogon hannunsa. Lokaci yana tafiya. Nazo ne muje kiyi ma Rabi'a barka. Karki cemin a'a, duk abinki yaukam sai kinje. Mimi ta 6ata rai. Yace tashi tashi kawai. Ta miqe tana fadin nidai banason fita ne. Yace, kuma saikin fita ba, gashi da nisa kuma a qafa zamuje, dare ne bare kice kar wanda yasanki ya ganki. Tace kai baka gane nufina ba. Ni fa banason inyi hulda da kowa ne, ballantana in saba da kowa. Yaya Amina da kai da yaranta kun isheni. Yace, amma ai kinsan cewa mutum rahama ne ko? Shikenan muje, ba sai kunyi hira ba, bare ku saba. In kinyi mata varka, kiyi shiru.
5⃣5⃣Ta dauki qaramin mayafinta ta yafa. Ya kalleta, kisa hijabi mana khadija. Tace duk fa hijaban da ka kawomin qasa suke ja. Ni ban saba dasu ba, ina yin sallah dasu ne. Yace karki damu kome suke ja, in dai baki sani ba zakiyi sallah da abinki. Bata sake cewa komai ba, ta bude durowar ta ta ciro ta saka, suka leqa tayiwa yaya sai sun dawo, shi kuma tsaya suka gaisa, ya fada mata inda zasu je. A hankali suke tafe iskar damina tana kadasu, zukatansu sun cika da nishadi. Ismail yace, ki tunamin in zamu dawo akwai wani gurin saida kifi, sai mu biya in sai miki. Cikin doki tace, tam, dama nayi kwana biyu banci kifi ba. Nagode. Yayi 'yar dariya, "menene na godiya? Tace, gurinka na koya. Koni ka saima abu in na amsa, sai kace min wai ka gode. Ta dubeshi, kai baka damu da cin kifi ba ko? Yace, aikam bai dameni ba. Amma ynxun na koya a gurinki. Tasa dariya, shikenan mun koya ma juna abu kenan. Yace ai dole kiyi abinda nakeyi. Tace, sbd me? Cikin zolaya yace, kin manta da jinina dake yawo a jikinki, ya gauraye da naki? Tace, daman hakane? To kai ba'a sa maka jinina ba, amma ya ka fara cin kifi? Yayi dariya, sbd ganin yadda ta shiga, ta yarda da abinda ya fada mata. Yace ni ai kara nayi miki. Yadda naga kinata son kifi dinne, shine nima naji ina sonshi. Tayi dariya, "kuna siya a madina ko? Nasan sunada shi, lokacin da mukaje umra da daddy naci sosai, sai dai nasu ba maggi sosai, yace, inaci mana, musamman innaji kewarki, sai in sayi kifi inci. Wani dadi taji a Zuciyarta, Ashe yana tunata. Tace kasan me? Ya dubeta, "a'a. Ban zaci kana tunani ba. Yace, sbd ke ba kya tuna ni, shine kk zaton nima bana tunaki? Ya ce, hakane don yaji ta bakinta. Wa ya fada maka ba na tuna ka? Yace, To in kinyi kewa ta me kkyi? Ta dago ido ta Kalli sararin samaniya babu taurari, sai alamun hadarin dake gudu. Sannan ta dubeshi, "qila zaka manta da wani hankacif daka ta6a bani, in ka tuna, to shine nakan dauko in kalla, wani lokacin ma har in shaqi qamshin turarenka. Dadi yaji matuqa, sannan yace, ashe na kai har haka a gurinki? Kafin tayi magana, yace, gashi har mun iso gidan, sai naga babu nisa ko? Ya fada tare da kallonta. Tace, nima dake fadin nisa, sai naga munyi sauri. Yace, to shiga kimin iso, zan kira angon qarnin ynxun a waya.
[22/09 9:54 pm] Inna: Canjin rayuwa
5⃣6⃣Tana shiga Mahmud din yana fitowa, yace, ga dakinnan, ki shiga. Bari mu shigo, ynxun ya kirani. Ta shiga da sallama dakin mai jego. Tana zama suna shigowa. Suka gaisa, Ismail ya miqa ma mimi yaron, ta amsheshi tare da kallon Ismail, "banfa iya daukar jarirai ba, karka sakemin shi." Hannuwansu suka hadu, dukkansu sun samu kansu cikin wani yanayi sakamakon hakan. Ta kalleshi. "me me ake cewa? Yace, hausawa suna cewa, Allah ya raya ko Allah ya amfanashi da dai sauransu. Ta kalli mai jego, "to Allah ya raya shi, yayi masa albarka. Ta sake kallonshi, haka yayi? Suka sa mata dariya. Mahmud yace, yayi. Nan kuma sai su Ismail suka canza harshe zuwa larabci. Ismail ke tambayar Mahmud "da wa yaron ke kama?" Mahmud yace, da ni mana. Ismail yace, a'a yafi ka kyau. Ismail ya miqa ma Mahmud yaron, tare da qifta masa ido, alamun zai tsokani Mimi, "khadija to in kin haifi naki yaron wa zai daukar miki? Ta harari Ismail, "ni ba zan haifi ko wane yaro ba. Don ko Aishatu ban ta6a daukarta ba saida tayi girma. Rabi'a tace, ba zaki haifi yaro ba. Sai yarinya? Mimi ta zaro ido, ni dai ba ruwana. Suka sa mata dariya sbd yanayin yadda tayi maganar
Ya tsugunna kusa da ita, "yaya kk ga yaron? Cikin harshen turanci tace, yanada kyau sosai. Domingo mimi tafi iya harshen turanci fiye da harshen uwa. Duk lokacin da zatayi magana mai kalma goma, to turanci zai zama guda bakwai. Don haka saddam da Ummi suke qaruwa da ita. Tana taimaka musu da homework. Sun jima a Gidan har goman dare ta gota, sune dai sukeyin Hirarsu, ita dai Mimi jinsu kawai takeyi. Hammar daya lura tanayi ne yasa shi miqewa, "to bari dai mu tafi, yau dai mun hana 'yan barka sakewa. To duk wadda tazo saidai mamansu Rabi'a ta leqo a miqo mata yaron." Mahmud ya miqe shima, "nima wucewa zanyi" sukayi musabaha tare dayin sallama. Mimi ma sukayi sallama da Rabi'a.
5⃣7⃣Suna fitowa shagwa6a66iya Mimi tace, Ni kam na gaji kawun su Ummi, bazan iya tafiya da qafa ba. Yace, ba don kince min kawun su Ummi ba, da na goya ki hai gida. Cikin hamma hade da shagwa6a, ta ce, don Allah kawun su Ummi, ka mu hau abi hawa. Kaga inajin varci kaji? Yace kin cika langa6ewa khadija. Tace ni ba kaga qoqarina ba, don Allah ban ta6a yin tafiya kamar ta yau ba fa. Nayi qoqari mana. Yace, ba zamu samu mota ynxun ba, kuma ko da mun hau mota, inda za'a sauke mu da nisa, tafiya sosai kafin aje gidanku, sai dai in aca6a. Tace eh naji mu hau aca6a din. Yace, ni banason mata suna hawa aca6a. To ka siya mana mota mana. Yace lokaci ne, insha Allah. Mahmud ya fito, "har ynxun baku tafi ba? Ismail yace, tana nan tana shagwa6ar ta, ba za ta iya zuwa gida a qafa ba. Mahmud ya miqo ma Ismael makullin mashin dinsa, tare da cewa, kuyi amfani da mashin dina tunda ban kaiku nisa ba. Kuma ga hadari yana haduwa. Ismail yace, to kar ruwa ya sameka fa. Mahmud yace, ko ya sameni kaga ni daya ne. Ismail ya amsa, tare da fadin shikenan muje ko? Tace, yaya zan hau? Ka san fa sau daya na ta6a hawa mashin, lokacin zanje in samu khalil a gareji. Saboda sauri ban san ta yaya na hau aca6ar ba, na dai ganni akai. Ina tsoron mashin da yawa. Yace ki dafa ni ki hau. Ta dafa shi ta hau suka soma tafiya. Don ya tsorata ta, sai ya taka birki, a tsorace ta qanqame Ismail, tana salati. Ya sa dariya. "Ya kamata ki rage tsoro. Ita kam batasan ma yana yi ba. Illa hannuwanta da tasa ta zagaye cikinsa ta riqe gam. Sannan ta kwantar da kanta a Gadon bayansa. Wani irin nishadi Ismail ya tsinci kansa aciki mara misaltuwa. Don haka maimakon ya nufi Gida kai tsaye, sai ya dinga shawagi ta layuka, sannan ya sassauta gudu, iga iskar hadarin tana ta kadawa, sai Ismail ke ganin kamar su kadai ne a garin katsina da kewayenta. Ita kuwa Mimi wani daddadan varci ne taji yana fizgarta, iskar tana ratsa ta ko ta ina. Ga kuma qamshin turaren Ismail dake saka Zuciyarta shiga cikin wani yanayi mai wuyar fassara.
[23/09 5:32 pm] Inna: Canjin rayuwa
5⃣8⃣Can yace, zamuje siyen kifin ne, ko muje gida? Ji tayi tamkar suyi ta yawon su a haka har abada. Don batason abinda zai tashe ta daga yadda suke. Amma kifi fa? Sai tace zanci kifi mana. Ya karkata kan mashin zuwa Gidan suya. Gurin ya burge Mimi musamman tunda taji qamshi yana dukan hancinta. Ya kalleta, zamu ci anan ne? Tace, amma zamu yi ma su yaya Amina tsaraba in munci bamu ko? Yace, yadda kika so, tace, in ba mutane muci, sai mu sai musu nasu. Babba daya ya sai musu, sai tataccen 'ya'yan itace mai sanyi, wanda za'a taceshi a juye maka cikin kofi a gabanka. Sunaci, Ismail yana kallon Mimi, wadda ke ta yin hannu baka, hannu qwarya. Yayi murmushi, "ci sannu Dija! In bai usheki ba zan qara miki." Ya shiga salo mata tsokar kifin sala-sala, yana ajiye mata a gabanta. Ta lumshe ido, "kar kaga laifina, inason abin nan. Ta salo tsokar ita ma ta aje a gabansa, "In baka ci, nima sai ya ginsheni. Ya dauka ya saka a bakinsa. Haka sukayi ta salo ma juna tsokar kifin, suna turawa a gaban juna, har suka cinye. Suka sha abin shansu. Yace, zaki qara? Ta girgiza kai, "cikin yayi dam. Dama banci abincin dare na ba." Yace, kunyi tuwo kenan? Tayi 'yar dariya, "shine kam. Na kasa sabawa da tuwo. Shi kadai ne har ynxun bai min ba, duk a abincin mu na Hausawa. Yace yaya ta fadamin, kin kasa sabo da tuwo. Amma kikanci kadan. Kafin tayi magana, sai sukaji iska mai qarfi alamun tasowar hadarin. A tare suka miqe, da sauri, ya biya sannan suka dauki nasu yaya Amina suka dane mashin. Fatansa tayi irin zaman dazun wanda itama hakane muradinta. Tana lafe a bayansa suna keta gudu, sai ko ga ruwa mai qarfi ya sauka. Sake qanqameshi tayi. Yayin da shi kuma ya rage gudun sbd ya Kalli gaban shi da kyau. Sha biyu da wasu abubuwa suka tsaya a qofar Gidan su yaya, sun jiqe sharkaf. Ya sauka ya buga gidan sosai, kafin suka ji takun Abban su saddam. Sai da ya tambaya wanene? Ismail yace, mune. Sannan ya bude. Mimi ta kalleshi, "kazo ciki mana ruwa yayi sauqi! Yace karki damu, gara in tafi sbd dare zai qara yi. Abban saddam yace, to ka kwana mana anan? Yace, a'a duk na jiqe kayana suna gidanmu. Saida safenku. Ta daga masa hannu tare da fadin bye! Sai da yaga abban saddam ya rufo qofa, sannan ya wuce. Ita kuma tana shiga taba abban saddam ledar tsarabarsu. Yace, bari in taso miki Ummi, don irinki ce, sarkin tsoro taqi varci a dakinku, wai ita kadai.
5⃣9⃣Bayan ta kunna tocila, sannan ta rufe qifar, ta cire kayanta ta maida na varci. Tayi lamo akan Gado, sam varcin yaqi zuwa mara. Sai tuno yadda suka kasance da Malam takeyi. Bata ta6a jin a kafatanin rayuwarta irin na yau ba, domin batasan ya zata fasalta yadda taji ba har a fahimce ta. Saidai a can qasan Zuciyarta tana tambayar kanta shin yadda ta ta6a jikin Malam ya dace, su da zasu rabu? Ta sake yin juyi akan gadon tare da maqale filo, sbd sanyin da taji yana ratsata. A fili tace, kai gsky bayansa yafi katifar nan dadin varci. Wata zuciyar tace, ba wani laifi domin har ynxun mijinki ne, tunda baku rabu ba ai. Haka tayi ta tunani tare da surutai barkatai har varci gwanin iya sata yayi gaba da ita. Washegari yaya tayi ta ma Mimi tsiya, tana cewa, mun zaci ko kun kama daki ne, mu biyo ku da kayanku? Mimi tace, munje siyan kifi ne ruwa ya tare mu. Tace, muma munci kifi, gsky sun iya gashi. Dariya kurum Mimi tayi.
Tun kwanakin baya Mimi tana yawan tuno mahaifanta, haka kuma har abada ba zata manta da gatan da dadynta yayi mata ba. Kewar ganinsu takeyi. Sau da dama takan zauna daki taci kukanta ma'ishi, ta share hawaye, saidai tanajin kunyar tunkarar mahaifinta sbd ta kasa yi masa abinda ya dace, a lokacin daya dace. Duk da cewa ya nuna wa momy Nafisa cewa zai haqura in taqi yarda kamar yadda Momyn tace mata. Amma ita ta yarda cewa tafi kowa laifi don me yasa ba tabi abinda yace ba tun farko? Don haka ta tattara duk wasu laifuka ta dora a kanta. Sannan zata jira lokacin da Allah zai sake hadasu don ta roqesu gafara. Kwanaki biyu da fara azumi, Mimi tana zaune a saman gadonta tana karatun littafin tahzib mai fassara da hausa, duk lokacin da take karanta littafin dashi da Al'adab, sai ta dinga tunanin cewa gsky rayuwar da tayi ada, rayuwa ce irin ta dabbobi, tunda batasan komai game da addininta ba. Abinda ya kamata ace ta sani tun tana ajin rauda shine take karantawa ynxun. Bokon da dauka a matsayin wayewa, ashe qauyanci ce ga wanda baida ilimin addini. Duk ilimin Bokon da take taqama dashi, wani lokacin Ummi ke cinta gyara a fannin addini. Kai ta fahimci ko maganar fatar baki ta mai ilimin addini ta bambanta da ta mai taqama da boko.
[23/09 5:37 pm] Inna: Canjin rayuwa
6⃣0⃣Ummi ta katse mata tunani da cewa, kunna TV dinki kiga kawunmu yana yin tafsir. Sai tsalle Ummi keyi. Ita kanta Mimi batasan meyasa ta sauri ba don ganin ta kunna TV. Dirshan ta zauna a gaban TV din tana kallon Ismail cikin qaton masallaci, mai cike da jama'a sunyi tsit suna sauraron daddadar muryarsa. Ta qaro sautin TV din ta koma saman gado tana kallonsa. Tsawon awa daya daya dauka yana yin wa'azin, haqiqa ya ratsata. Bata ta6a zama ta saurari wa'azi ba kamar yau tunda take. Yaya ta shigo tana cewa, kinfa kawunsu Ummi ko? Mimi tace, gsky yanada basira sosai, ya iya tafsir. Yaya tayi dariya, ji tayi tana alfahari dashi. Mimi kuwa, qosawa ma tayi ta ganshi. Inda ya sake burgeta, yadda ya yita amsa tambayoyin mutane da sukayi ta rubutowa bayan an gama wa'azin. Haka ya yita basu amsa cikin ilimi da hikima tare da kawo hujjoji cikin Qur'ani da Hadisai, ko kuma ittifaqin malamai. Mimi dai Ismail ya burgeta har qarshe. Don haka yau da sukayi qosai da kunun gyada, da kanta ta debi nasa ta shirya masa, ta shinfida darduma tana jiran zuwansa. Amma har kusan tara baizo ba. Bata ta6a damuwa don Ismail baizo ba irin yau. Jiya ma da yazo Ummi ce ta kawo masa abin buda baki, amma yau wata kimarsa ce ta qaru a idon Mimi. Tayi ta kai kawo a cikin daki, ta qosa sosai ta ganshi. Agogon dakin ya buga qarfe tara da kwata, ta miqe da nufin ta tambayi yaya, wai yau Kawunsu Ummi ba zaizo ba? Sai kawai taji muryarsa yayi sallama ya shigo gidan. Ta koma baya ta zauna a bakin Gado. Qosawa tayi su gama gaisawa da yaya Amina ko ya shigo, amma ya jima can kafin ya shigo. Da farko ta tsara zata tareshi cikin murna, amma yana shigowa sai taji wani jinkai ya taso mata, ta kishingida tare da fadin sannu da zuwa. Ya zauna bakin gado, sannunki da hutawa. Tace, kaine da sannu. Yau kam bakazo shan ruwa ba? Yace, eh wani bawan Allah ne ya gayyace mu shan ruwa. Can mukaje. Tace ok.
6⃣1⃣Sun danyi shiru na wasu 'yan daqiqoqi, kafin Mimi ta kori Shirun da cewa, mun kalli tafsir dinka, yau kayi qoqari. Yace, to nagode. Wayarsa ta soma ringing. Ya dauka tare da sallama. Ta amsa, macece. Yana qoqarin tambayar wacece, sai ta katseshi da cewa Malam mun yini lfy? Yace lfy Qlw. Tace dama Malam ba kira ne in gaisheka. Wani haushi ne ya tirniqe shi a zuciya. "Amma don Allah kaiki sake kirana." ya kashe ba tare da ya jira jin amsarta ba. Mimi ta kalleshi, "wacece?" shima ya dubeta, "Nima bansan ko wacece ba. Tace, ina ta samu number dinka? Yace ina zan sani? Kinsan Allah, khadija abinnan yana bani haushi da Mamaki. Wai mata masu daraja da aka sansu da kima shine suke tallar kansu ga mazaje. Kafin tace wani abu, sai daya wayar ta soma ruri. Tamkar kada ya dauka, amma saibya daga, kamar yadda yayi zato itama macece. Kamar ya kashe, saidai ya fasa, ya amsa gaisuwar da takeyi masa a qagare. Tace, din Allah Malam zanyi talbaya ne akan bashin azumi da nasha, gashi har wani azumin yazo. Jin cewa ita neman fatawa takeyi, sai ya saurareta, yayi mata kuma cikakken bayani yadda zata gamsu. Mimi dai tana kallon Ismail cike da birgewa. Duk abinda yayi sai taga yayi masa kyau. Ya kalleta. Bari inzo in tafi. Tace da wuri haka? Yace dama nazo ne in duba ku. Akwai wasu litattafai da zanyi nazari, sannan zan qara karatu a gurin Malam, duk a daren nan. Tace ok. Yace, babu wani abu ko? Ta girgiza kai, tare da fadin babu jolai. Yace shikenan in tafi sai gobe kenan? Ta daga kai.
Ismail ya soma karatun nan da qafar dama inji hausawa. Domin kafin azumi ya raba, saida labarin basirarsa da hikimar wa'azinsa ya watsu cikin birni da qauyukan katsina. Faya-fayan karatunsa da kasina naji dana gani, sun fantsama a kasuwa. Su kuwa wasu shaidanun matan, labarin kyawunsa sukeyi, da yadda yake shigarsa ta manyan kaya da kuma jallabiyu 'yan gske. Wasu kuma yadda yake fitar da larabci da turanci tamkar yarensa shi ke burgesu. Kai ko hausa Ismail keyi zakaji hausarsa mai burgewa. Wasu kuma suce, iyayi da salo.
[25/09 9:26 am] Inna: Canjin rayuwa
6⃣2⃣Masallacinsu kam yana cika tantsam har ta harabar makarantar. Ganin haka sai Ismail ya kawo ma manyan malamai dasu Malam Aminu shawarar cewa, me zai hana su kafa asusun marayu don taimakon marayun dake unguwarsu da maqotan Unguwar. Suka amince. Shida Mahmud suka soma bada tasu gudunmuwar har yace ga ta yayarsa da kuma matarsa. Shi kuwa Mahmud harda ta dansa mus'ab ya saka. Daganan sai Ismail yace yanason kowa ya saka tashi sadakar a ranar na duk abinda Allah ya hore masa. Ranar dai yayi wa'azi ne akan falalar dake cikin taimakon marayu da tsabar ladar da hakan ke dashi. Kafin wani lokaci mutane sukayi ta zuba kudi, wadanda kuwa basuda shi sukayi alwashin kawowa gobe. Kafin sati daya saida takaisu ga bude asusu a Banki. Sbd, wadanda suke kallon wa'azin a TV kuma suna son su bada tasu sadakar. Wannan al'amari ya haskaka Ismail, amma dukda haka bai kasance daga cikin malaman da in daukaka tazo musu, zakaga sunayin girman kai ba. Yana bin duk malamin daya san zai samu qaruwa dashi, ko da kuwa ya girmi malamin. Hakanan ko qaramin yaro ya nuna masa kurensa a harkar karatu yana kar6a. Sannan ko yau yayi tafsir, bayan ya tashi wani yace masa, jiya fa kaza ba daidai bane, in ya dawo gobe zaiyi bayani cewa jiya nace kaza, ba daidai bane, wani dan uwa yayi min gyara. Haka nan shi yayi imani cewa, daukaka ta Allah ce, ba wai iliminsa ne ya kaishi ba. Daukaka daban, ilimi da hikimar wa'azi daban. Ismail ya zama cikin uzurin da sai yayi kwanaki baije gidansu Mimi ba. Ita kuwa Mimi sai take zargin ko don yaga ya soma zama wani abu shine zaija baya dasu. Yau kwana uku tanason ganinsa don taji wacece matarsa din daya bada sadaka harda ita. Amma baizo ba, saidai su ganshi a TV in yana tafsir ko lacca, wadda aketa faman gayyatarsa. Yana yiwa maza ko mata, wata lacca da aka nuna yayi wa mata mai taken Ramadan lacca. Tasha mamakin yadda yake fadawa mata su riqe mazajensu, da hanyoyin kula da miji. Ya kuma kwadaita musu irin romon ladan da zasu samu a gurin mahaliccinsu. Sai taga duk ta zama wata sokuwa, domin ita kanta da take macen bata san abubuwan dashi ya sani ba, na game da yadda ita kanta mace zata kula da kanta. Ta jima tana Mamaki, kuma ta sake yarda Ismail ya dara kallon da takeyi masa.6⃣3⃣Shikam Ismail yakan kira yaya Amina su gaisa, yaji lafiyar Mimi a gurinta, kuma tana sanar da Mimin, domin bashida lokacin kansa. Ba su suka ga Ismail ba, sai azumi yana ashirin, misalin qarfe uku, lokacin Ummi tana daga citta zata kai niqan geron kunun tsamiya, ta gai dashi. Ya amsa tare da cewa, ina mamanki? Mimi qin dago kai tayi. Ummi tace, tana ciki. Yaya ce ta fito tana fadin dan gyangyadi ne ya soma dauka ta, sai kuma naji muryarka sama-sama. Yace, nine kun ganni sai yau. Ya saci kallon Mimi, cikin zolaya yace, 'yar amanata ma na lura fushi takeyi dani. Ko kallo ban isheta ba. Mimi ta dago ta dubeshi, ya dan rame, hakan sai ya qara masa kyau. Shaddar jikinsa mai tsada ce sosai, mai ruwan siminti, hular kansa ta dace sosai. Ta maida kanta taci gaba da firar dankalin da dama shi takeyi tun kafin ya shigo. Ta kammala ta kwashe 6awon sannan ta kai kicin ta wanke hannunta, duk yana kallonta, suna 'yar hira da yaya. Ta zo ta shige dakinta. Ya bita tare da cema yaya, bari inyi lallashi. Can saman Gadonta ta harde qafafun ta. Ya shigo da sallama,a ciki ta amsa. Ya tsaya a gaban gadon, "yau fushi kkyi dani? To, kiyi haquri. Ya ranqwafo tare da sa hannuwansa duka biyu ya dafa gadon. Kinji. Sam ta kasa fada masa cewa, rashin ganinsa ne ya bata haushi. Sai ta kauda kai. Yace, kullum ina fada ma yaya ta gaisheki, sannan ina fada mata uzururruka na, ko bata fada miki? Ta turo baki, ni fa rashin zuwanka bai dameni ba. Cewa din dakai ni matarka ce. Ya zauna, na fada a ina? Cikin salon shagwa6arta ta nuna TV, "anan mana, daka bada sadaka, harma kace, da na yaya. Yayi murmushi, yana son salon shagwa6arta. Yace amma nace matata khadija? Ni fa nufina wadda zan aura. Ta ware idanunta ta kalleshi, zakayi aure ne? Yace eh mana insha Allah. Ta ta6a baki tare da cewa, Hu'um! Zuciyarta fal da takaici. Ta dubeshi, "to ni yaushe zamu rabu? Tayi tambayar cikin daurewar fuska yace, kinsan dai ko ba lokacin azumi ba, laifi ne mace ta nemi a sake ta, babban laifi ne ko!? Ta sake turo baki, ai shi ma alqawari cikashi abu ne mai kyau ko? Yayi murmushi, "haka ne, amma banda haramtaccen alqawari. Ina nufin kayi alqawarin laifi. Misali mutum ne yayi alqawarin aikata wani laifi da Allah baya so, to ba'ason ya cika. Tace, jiya fa naji kana cewa saki halasne, a cikin tafsirinka. Yace, sai kuma nace me? Allah baya sonshi, dukda halas ne. Na lura in kinyi ilimi nan gaba za'ayi fama dake kema.6⃣4⃣Yasa hannu cikin aljihu ya ciro kudi 'yan dari biyar-biyar. Yace zan sallameku sbd batun sallah dake gabatowa. Tace, ai yaya zaka bawa kudi. Ni ina zuwa kasuwa? Yace, nima bance kije kasuwa ba ai. Tace, to naga zaka bani kudi ne. Yace na fasa baki ki shirya gobe muje tare. Tace, kana son sole sai wanda ya sanni ya ganni kai kam. To shikenan, ki rubuta min abinda kk so. Ya miqe ya shiga dakin yaya ya qirga dubu goma ya bata, yace ta saima yara kayan sallah. Tayi godiya tare da cewa, kaima da kk fama da kanka. Kaima fa dalibi ne har ynxu. Yace wani bawan Allah ne ya sameni nayi masa bayanin yadda zai fidda zakkarsa, shine da ya cire ya bani. Yaya tace, Allah ya taimaka. Ai ranar da kayi wa'azin zakkarnan, dole zukatan mutane su raunana, indai da sauran imani, su fito da zakkar su ba da. Yace kinsan kudi shiga zuci ne dasu. Sai su dinga ganin kamar in sun bada zakka kudin zai qare. Ba su san in sun cire haqqin Allah daga cikin dukiyarsu ba, Allah zaisa musu albarka, qila ma tafi ta da. Tace, rannan ma munji ka bada sadaka harda mu. Allah ya saka da alheri. Yace, Amin. Tare da miqewa. Ya koma dakin Mimi, "bani in kin rubuta. Ta miqa masa 'yar guntuwar takarda. Ya amsa, ya bude. Sai yaga ta rubuta cewa, duk abinda ya sauwaqa. Ya kalleta, zuciyarsa dajin dadin hakan da tayi. Yace nasan ba zan iya sai miki abinda kk so ba, amma zanyi iyakacin qoqarina. Ya juya ya fita. Kwana uku bayan nan, Ismail yazo Gidan da safe, misalin qarfe takwas, Mimi tana varcin safe. Ya gaisa da yaya sannan ya shiga dakinta. Bai mata dogon kallo ba, ya aje ledar hannunsa ya duba durowar gefen gadonta ya dauko takarda da biro ya rubuta cewa, ga kayan nan, in kin farka ya ke mai yin kyau a varci. Ya dora takardar a tafin hannunta. Sannan ya fice, yayi sallama da yaya ya wuce.
[25/09 9:28 am] Inna: Canjin rayuwa
6⃣5⃣Mimi kuwa tana farkawa taji da abu a hannunta, sai ta duba, taga abinda ya rubuta. Sai tayi murmushi tace, waton in idanuna biyu banida kyau, amma a varci inada kyau. Ta dauki ledar ta bude, wani tsadadden leshi ne mai kalar 6awon dorawa, sai Atamfa 'yar England sai takalma masu kyau da tsada. Ba anan tasha mamaki ba, saida taga irin man shafawarta da hodarta, sai kuma jan bakin da take shafawa. A fili tace, "ina Ismail yasan wadannan? Lallai zan tambaye shi inji. Ta ciro hijabai dogaye guda uku, sai niqabi guda daya. Tace, wai harda wannan yakeson in sa, ta6! Na dai saka hijabin in zanyi sallah. Ta kaima yaya ta gani. Suka tayata murna. Tace, in yazo anjima sai ince yakai dinki ko? Yaya tace, eh kam ya kai don inda na kai nasu Ummi macece, kuma ba wani qwarewa tayi ba. Dama su Ismail sun kafa kwamiti qarqashin jagorancin Mahmud inda za'a dauki sunayen marayun Unguwar, da na kusa dasu. Don haka sai suka sai kayan abinci dana sallah na yara, maza da mata. Sannan sukaje suka kai ziyara gidan yari, inda yayi musu wa'azi tare da basu taimako. Ana saura kwana biyu sallah, ya kawo masu Mimi cefane jibgi guda, da kuma kaji, sannan Washegari ranar jajibiri masu hali sukayi ta aiko masa da nama cikin manyan ledoji. Yaba Malam Aminu, harda Mahmud, sannan ya miqa cikin gidansu. Irin wadannan abubuwan suna burge Mimi.6⃣6⃣Hasana da usaina suna zaune suna kallon rufe tafsir din Ismail, Hasana tace, kai Malam yayi wlh! Na qosa daddy yayi mana izinin zuwa muga sis Mimi. Itama nasan ynxun ta hadu. Usaina tace, ai na dauki number din da ya bada wadda yace mutane suyi message kawai banda kira in sunada tambaya, so muyi masa text cewa, mune. Sainya fada mana gidansu, sai muje muga sis Mimi. Muryar Hajiya sauda ta katsesu da cewa, Allah yasa in samu labari. Wai ba ku nace ma tana lfy bane. Kuma fa na fada muku cewa, akwai matsala in munyi yunqurin zuwa gurinta zata sake guduwa. Karku damu tunda muna samun labarinta. Muyi ta Addu'a komai zai wuce. Hasana tace, Hajiya shi Malam a matsayinsa na Malami ba sai ya nemi lambarki ba kiji komai daga bakinsa? Usaina tace, ya fa san nan gidan meyasa ma ba zaizo ba? Hajiya sauda tace, Nice da laifi, don na tura masa saqo cewa, naji dalilan mahaifin Mimi, kuma na gamsu dashi. Don haka nima zaka jini shiru. Kaima kayi haquri karka sake nemana ko a waya. Ina mai sake baka amanarta. Lokaci yana zuwa da zamu nemeka da kanmu. Kunji tun daga lokacin ban sake nemanshi ba, shima bai sake ji daga gareni ba. Hasana tace, to sai zuwa yaushe ne sannan za'aje gurinta? Usaina tace, ke kam kamar bada hausa Hajiya tayi magana ba? Hajiya sauda tace, zaku soma musunku ko? To ni nayi nan! Ta nufi kicin. Ranar sallah, Ismail ya matsawa Mimi wai ta shirya suje masallaci. Da ma tun ranar jajibiri yake fada mata lokacin da yazo ya kawo mata dinkinta. Tace, ba zataje ba, qila 'yan gidansu zasuje. Yace, ba ga niqabinki ba, sai ki 6oye fuskarki, dama amfaninsa kenan. Zama haka ba ya yiwuwa Mimi, dole sai da dan fita ana dan motsa jiki. Balle sallar idi wadda daga shekara sai shekara. Ba tada za6i dole ta shirya cikin leshinta, yayi mata kyau matuqa, tayi alwalla, sannan ta shafa hodarta da jan baki, ta saka hijabin da niqabi. Suka fito tace, yiwa yaya sallama. Ummi ma da take ta rabon abinci gidajen maqota tayi kyau cikin kayan sallarta. Su kuwa su saddam dama sun tafi da abbansu a mashin.6⃣7⃣Ismail yayi kyau cikin wani tsadadden yadi, mai ruwan madara, malum-malum ce ta dauki aiki. Hularsa da takalminsa sun dace da kayansa. Yayi kyau matuqa. Ita kanta Mimi lokacin da ya shigo Gidan, sai da Zuciyarta ta buga. Daga lokacin da Ismail ya soma tafsir zuwa ranar sallah, yayi abokai kala-kala, kowa yanason ace suna hulda, masu da kuma talakawa. Daga cikinsu ne wani yazo har gida ya daukeshi, shine yace, su biyo ya dauki matarsa. Mutane sukanyi mamakin ganin Ismail a wani guri daban. Duk wanda ya tambayeshi yakan ce masa, shi ba lazauni bane. Matarsa kuma ba tada isasshiyar lfy, shiyasa ya barta gidan yayarsa. Bayan sun dawo sallah ne Ismail yaci abinci anan gidan, sannan ya miqe zai fita. Sai Mimi taji sam batason ya fita. Amma ba tada ikon hanashi, wani sonshi ne taji a cikin Zuciyarta. Tana kallonshi ya fice. Bayan sallah da kwana tara Ismail suka shirya nasu-yanasu sai makaranta. A ranar ne Mimi taji inama itace, Rabi'a. Ranar ce, tayi kuka sosai, wanda batasan ko na menene ba. Ismail yayi zaton ko tana yi ne don bai saketa ba. Sai yace, karki damu khadija, shekara kamar kwana ce, in na dawo komai zaizo qarshe, kinji? Bayan tafiyarsu tayi ta dana sanin qin yarda da tayi ya sai mata waya. Amma tace, bataso. A fili tace, kashh! Menene ma zai sa ince ban son waya? Tsaki taja, tare dayin tagumi. Ynxun kam ta gama fahimtar cewa, Zuciyarta tana matuqar son Ismail, sai dai tsoronta daya shine, shi baya sonta. In ba zata manta ba ya sha fadin cewa, shi mace mai kyau yakeso ya aura. Tuna hakan sai taji jikinta ya mutu. Ta kalli kudin daya bata kafin ya tafi. A fili tace, dole ne in nemi wanda zai siyomin waya ko don in hada hulda dashi. Tsaki taja, a ranta tace, ta yarda jama'a rahama ne, inda tana hulda dasu da ynxun ta samu mai siyo mata. Dakin yaya Amina taje, tace yaya inason a siyomin waya ne. Yaya Amina tasha mamaki, "ke kuwa meya hanaki yarda Ismail ya siya miki? Don nasan babba zai sai miki. Tace, lokacin banason wayarne, amma inasonta ko don inji Rediyo. Amma fa karki fadama kawun su Ummi. Tace, shikenan ki kawo sai qanin abban su saddam ya siyo miki. Ta dauko dubu bakwai, cikin dubu ashirin din da Ismail ya bata kafin ya tafi.
[25/09 9:30 am] Inna: Canjin rayuwa
6⃣8⃣Zainabu kuwa tunda taga Ismail a TV, hankalinta yayi matuqar tashi. A fili tace, Ismail yafi qarfi na ynxun. Ta saka kukan takaici, tayi har ta gode ma Allah. Innarta cikin tsantan nadama tace, zainabu kiyi haquri, qila zaku hadu ne ko anan gaba. Tunda yana sonki, na san ma zai dawo gareki. Zainabu dai bata tanka ba. Innar ce da kanta ta fita neman labarin Ismail, har gidan mahaifinsa gurin su fatu. Anan ne fatu take fada mata cewa, Ismail yana madina garin manzo, dama zuwa yayi don can yake karatu. Ta qara da cewa, Ismail fa ya wuce da tunaninki, mu kanmu mun dangana bare ke. Dole mu dangana ko don alherin da yakeyi mana. Azumin nan shine geron kununmu, shine waken qosanmu. Da sallah tazo kuwa, zo kiyi kallon hidimar, dinkunanmu da yara, ke har cefanen sallah. Innar zainabu tace nima ai nadamar ta kawoni, ban san yaya zanyi da zainabu ba, taqi sauraron kowa. Fatu tace, dama ta saurari kowa, sbd Ismail da ya yafe tunaninta. jiki babu qarfi ta koma Gida.6⃣9⃣Ya zuwa wannan lokacin, rikicin su Na'ima ya kai su ga zuwa kotu, inda shi Abbas ke qarar Na'ima, akan ta bashi dansa. Ita kuma Na'ima tace, ba zata bada shi ba. Duka 6angaren guda biyu sun dauki lauyoyi. Inda ake fafatawa tare da dage zaman sauraron shari'ar. Nadama kuwa, Momy Nafisa tayi akan auren nan yafi cikin buhu. Ita kuwa Na'ima nata ganin alhakin Mimi ne. Duk lokacin da tace haka, sai momy Nafisa tace, ki daina wannan maganar, ai komai muqaddari ne. Na'ima tace, qaddarar da mutum yake qadddara ma kansa ba. Da mun bar Mimi ta aure shi, na tabbata hakan ba zai faru ba. Haka Allah yake ikonsa, sau da yawa sai mutum yayi ha'inci, sai kuma kaga ya dawo yana nadama. Kukan Na'ima da yawa, ita ba a karatunba, ita ba ga auren ba. Ynxun ne take burin in ya saketa, ta koma makaranta. Shi kuma yace, tana bashi dansa zai sake ta. Lauyoyinta suna ta zuba hujjojinsu kan cewa, dole ne ya saketa tare kuma da bar mata danta don itace tafi dacewa ta kula dashi. Su ma nasa lauyoyin hujjojinsu suke bajewa akan cewa shine yafi dacewa ya riqe dansa a matsayin sa na uba. Nidai nace, ku kuka sani, mu dai 'yan kallo ne.
Lokacin da aka kawo wa Mimi wayarta, ta hada ta tasa aka sai mata layi ta saka aciki. Number Ismail kawai ta dauka a cikin wayar yaya Amina. Wtsapp Mimi ta bude, cikin sa'a kuwa da lambar yakeyi, hotonsa ne ma yasa a D.P dinsa,yana sanye da farar jallabiya. A saudiyya ya dauki hoton daga gani. Wannan lokacin ma yana online. Mimi tayi murmushi sannan tayi masa sallama. Sam bai kula sallamarta ba, duk da tayi ta kusan sau goma. Tace, nasan yaya zanyi. Ta sauka daga kan wtsapp din ta tura masa message, da cewa. Dama haka malaman suke basa son sauraron al'ummarsu, balle su basu fatawa akan matsalolinsu? To, ka sani bin Abdurrahaman, in har na mutu ban samu mafita a matsalar da nake ciki ba, to ka sani har da kai zunubin, domin na kira baka daga ba. Kuma nayi maka magana ta wtsapp baka kula ni ba. To ynxun ga message dina nan. Tana turawa tayi murmushi, sai ta kashe wayar ta aje.7⃣0⃣Bata sake kunnawa ba sai bayan kwana uku. Tana kunnawa saqonni guda uku suka shigo, data duba daya na MTN, biyu na Ismail dama da Malam tayi saving. Murmushi tayi, sannan ta bude saqon. Gajerrn saqo ne, kawai cewa yayi, ki fadi matsalarki. 'yar dariya tayi don ganin cewa zatayi wasa da hankalinsa. Ta hau wtsapp nan ma saqon iri daya ne. Ta soma tunanin me zata rubuta masa, wanda zaija hankalinsa, ya saurareta? Sai ta soma rubuta cewa, Malam Allah ya sani tunda nake ban ta6a ji ko ganin matsala irin tawa ba, ko da a film ko kuma labarin qirqira. Sai ta tura masa. Daga nan sai ta kashe wayar. Washegari data hau wtsapp sai taga yace, ki fadi matsalarki kai tsaye ba tare da kin gutsutsura batun ba. Ke nake sauraro. Dariya tayi, sosai sannan ta tura masa cewa, roqo na da kai, shine in kaji wannan matsalar tawa ka taimakamin, kuma ko da kisan kai ne ya kasance hukunci na to zan dauka. Ta tura masa. Haka tayi ta tura masa wadannan saqonni na wasa da hankali, tun yana nuna mata yanason jin ko wace matsala ce, ta daina jin tsoronsa ta fada masa, har ya gaji yayi banza da ita. Tare da haka, in ya kira yaya Amina yakance, a bashi Mimi su gaisa. Cikin ja masa ajin data saba yi take amsa su gaisa. Inya tambayi matsala, sai tace babu. Kwancitashi su Ismail sun kammala karatu na digiri, tare da sakamako mai kyau. Hukumar qasar ta tuntu6i daliban da aka yaye a wannan shekarar, ko akwai wanda yakeson yin aiki tare da su bisa ga albashi mai tsoka? Su Ismail kam cewa sukayi sunfi son suzo su amfanar da ilimin da suka samo ga al'ummar qasarsu. Sannan Ismail yanason samun nasa iyalin, ya gaji haka.
Mimi bata ta6a yin murnar dawowar Ismail ba kamar wannan karon. Domin gsky tayi kewarsa, tanason ganinsa, sosai matuqa. Wani abu da ya sake burge ta shine tasha gwada Ismail da sim kala-kala, don taga ko yana hulda da mata, amma sai ta sameshi a natsattse wanda bashi da lokacin shashanci. Sun iso gida cike da murna da doki. saidai Ismail ya baro madina cike da burin komawa don samun digirinsa na biyu, in komai ya tafi masa daidai. Dakinsa ya sauka, wannan karon zai kama masauki amma sai ya saita lamuransa.7⃣1⃣Shi mahmud bashi da wannan matsalar ta gurin zama, domin suna da mazauninsu, daya daga cikin gidajen mahaifinsa. Sunyi isowar dare ne wannan dawowar. Kusan qarfe biyun dare suka shigo katsina. Kai tsaye gidansu ya wuce, ya sauna da kayansa. Su kuma su Mahmud da Rabi'a da dansu mus'ab yayi wayo sosai, suka wuce nasu gidan. Ismail ya buga gidan. Yayyinsa maza guda biyu sukazo sun a tambayar ko wanene? Ismail yace nine Ismail. Da sukazo suka buds mass, suna yi masa sannu da zuwa. Sun yi sallama Sai da safe, suka nufi ciki. Shikam bai kwanta back Sai daya share dakin. Want Abu daya bawa Ismail mamaki, bayan yay sallar asubahi ya dawo, ya kwanta don ya huta, bai yi niyyar fita ba don yana tsammanin babu Wanda yasan ya dawo, gurin qarfe goma yaji sallama a qofarsa. Barcin nasa sama-sama ne. Don haka Sai ya tashi ya suka jallabiyarsa ya fito, ya baqon nasa, Sam bai sanshi ba, amma ya miqa masa hannu, suka gaisa. Mutumin ya Ciro wasu takardu ya miqa masa, game saqo daga wani bawan Allah, yace in Baka tun kusan wata uku da suka wuce. Ismail ya kalleshi cikin rashin fahimta, saqon menene? Yace mai gidana be, inayi masa aikin sama. Ni kafintan same ne. Duk wani aikin gidajensa ni keyi masa daya shafi Sana. To shine ya tambayeni ko ma sanka? Nace unguwarmu daya. Ta yiwu Baka sanni ba, ina can bayan mayo be, gidan malam kadi. Ismail ya kalleshi. Gidan su hashimu? Baqon yace, yauwa, to ni wansu hashimu be. Zakkar gida be, ko ince kyautar gida yace in Baka. Wadannan takardun gidan be. A can unguwar GRA be gidan take. in ka shirya Sai mine in Nina mama.
[25/09 3:10 pm] Inna: Canjin rayuwa
7⃣2⃣Cikin mamaki, Ismael yace a ina wannan mai gidan naka yake, kuma yaya sunansa? Baqo yace nidai sunana Nasiru amma shi mai gidana ya hana ni in fadi sunansa ko unguwarsa. Yace, shi yayi ne don Allah, kuma malam ya sakashi a cikin addu'ar Allah ya biya masa buqatunsa na alheri. Ismail yace jirani ina zuwa. Ya koma daki ya canza kaya, ya fito yace, zo muje gurin malam. Sun samu malam Aminu, inda dan aike yayi masa bayanin kimai. Bada 6ata lokaci ba, suka nufi gidan, harda mahmud, wanda ismail yayi masa waya, shima yazo ya samesu. Sun samu mai gadin gidan ya bude musu suka shiga. Mai gadi yazo ya gaishesu tare da tambayar su ko wanene mai gidan cikinsu? Mahmud yace, wa yasa ka gadin gidan? Yace 'yalla6ai ne. Yace min duk randa wanda yaba gidan yazo, shi aikinsa ya qare. Mahmud yace, to ya sunan shi 'yalla6ai din? Tsoho maigadi yace, ya hanani in fadi sunansa.
Sun zaga gidan qato ne sosai. Ginin na gefe hawa daya. Mai gadin ne yabasu makullan ciki tare da nuna musu ko ina na gidan. Shikam ismail filin gidan ne yafi burgeshi, domin har ya hango yadda zaiyi makaranta a gurin, harda masallaci. Take ya sanar da su malam Aminu sha'awarsa da gurin, suka ce tabbas bakan yayi. Sun yi bankwana da maigadi bayan ismail ya bashi dan abinda ke hannunsa tare da bashi baquri kan cewa bai fito da kudi ba. Suka fito suka kulle gidan suka tafi da makulli. Babu abinda gidan ke buqata saidai kayan da za'a zuba na amfani. Sun koma gida, inda Ismail ya kawo dubu biyar tare da sabbin jallabiyu a cikin kayansa yaba dan aike tare da bashi haquri, kan cewa dawowarsa kenan daga karatu bashida kudi. shi kuwa dan aike godia yayi, tare da cewa, ni ai babu abinda yafi faranta mun rai kamar sada ka da saqonka da nayi. Domin tun shekaran jiya yake cemin cikin satinnan zaku dawo. Ismail yace, wato harma ya san lokacin da zan dawo. Dan aike yace gsky ya sanin kenan. Sukayi bankwana, ismail ya rakashi tare da yi masa godiya mai yawa. Ko daya dawo daki, yayi iyakacin qoqarinsa don ya gane ko wanene. Amma hakan yaci tura. Sai kurum yayi masa addu'ar Allah ya cika masa burinsa, duniya da lahira.
7⃣3⃣Mimi suna da labarin dawowar ismail amma basu ganshi ba. Mimi bataji dadin hakan ba, domin sai taga kamar bai damu da ita ba. Sai washe gari bayan la'asar, yinin ranar Mimi tayishi ne cikin qunci da rashin walwala. Har yaya ta nemi dalili, amma sai Mimi tace, kanta keyi mata ciwo. Tana zaune a tsakar dakinta tana yanke qumba, kanta babu dankwali ta kama gashinta a tsakiya, kamar yadda ta saba tun tana 'yar gayunta, muryarsa ta jiyo yayi sallama, sai sowar yara ta jiyo suna yi masa sannu da zuwa. kamar ta tashi ta fita sai kuma ta fasa, ta kalli jikinta, riga da wando ne wadanda shine ya sai mata su. Taje madubi ta kalli fuskarta. Sai ta samu kanta da zazzaga hoda a tafin hannunta ta hure, sannan ta shafa ta hau tsakiyar gadonta ta zauna, ta kunna TV. Catoon sukeyi. Kusan minti ashirin da tara, sannan ya kalli dakinta, ita wannan bata nan ne? Yaya tace, tananan. Dazun dai tayi fama da ciwon kai, amma yayi sauqi. Da sallama ya shigo. Ta dago tamkar lokacin taji shigowarsa. Qwarjinin dake kan fuskarsa ya doketa, tayi saurin sunkuyar da kai, sannu da zuwa. Yace, sannunki, in zauna bakin gado? Ta dago ta dubeshi, yaune zaka nemi izinina? Yayi murmushi, ai na qara wayau ne ynxun. Da kinsan yaro ne. Tayi dariya, to ka zauna. Ya tsura mata ido, "kinci naman hawainiya ne? Yayi tambayar cikin tsokana. Ta zaro ido, meka gani? Duk lokacin da na tafi na dawo, sai inga kin canza kala. Gabanta ga fadi, tsoronta kar ya kusheta, ta kalleshi, duk nayi muni ko? Yayi dan murmushi, nidai ban fada ba. Tace to fadamin me nayi? Da ya fahimci tanason jin ta bakinsa game da yabon da yayi niyyar yi mata, sai ya canza da cewa, wai don Allah meyasa in na dawo baki doki na? Tayi masa kallon gefen ido, injiwa? Yace injini mana. In ana dokin mutum ai anayi masa tarba ta musamman da girke-girke. Ta ta6a baki, ai muma bakayi dokin ganinmu ba. Sai fa da kayi kwanaki, mutane suka gama ganinka, sannan kake zuwa mana nan. Yayi murmushi, amma zuwana na farko nan na fara sauka. Mimi tace, wannan ne kawai. Ta sake maido da wancan zancen. Baka fa bani a msa ba. Tame? Ya fada tare da kanne mata idonsa daya. Canzawar daka ce inayi. Shine nace muni na qara ko? Yayi 'yar dariya nidai bance ba. Ki kawomin ruwa mai sanyi insha, ya sake kauda zancen.
7⃣4⃣Ta sauka sannan ta dauki qaramin hijabi tasa. Yasan sbd kayan jikinta ne don sun kama fa tsam, duk motsin da tayi jikinta yana rawa. A zuciyarsa yace, lallai! Yau Mimi ce da rufe tsiraici? A fili yace Albmdlh. Ta kawo masa ruwa da kofi, ya kalli goran ruwan, lallai 'yan gayu, swan kuke sha? Tayi masa hararar wasa, wa zai bamu ruwan swan? Na fanfo ne muke sawa yayi sanyi. Ya tsiyaya ya sha. Cikin son jin me yayi niyyar cewa yaqi fada, tace ai kaima ka canza. Ya dubeta don ya riga ya dago ta. Yace, eh nima nasan na canza, na qara kyau sosai haka? Ta harareshi, ka cika son kanka da yawa. Yace inba gaky na fada ba sanar dani kawai. Tayi shiru. Yace shiru yana nufin eh ne. Ni nasan inada kyau. Ta 6ata rai, kai kyau ya dama. Ni ynxu nafison kyan hali. da ne nake kallon kyau wata tsiya. Yayi dariya shima inada shi, don naji mutane suna fada. Ranta ya sake 6aci. Da gske batasan shi zolayarta yake ba tace, ka cika wasa kanka. Kuma ance duk wanda yace shine, to ba shi bane. Yace nidai nine ismail bin Abdurrahaman. A ranta tace, karma yaga cewa na wani damu dashi ne ma, bari in masa zancen rabuwarmu. Tace gashi dai karatu ya qare, yaushe zamu warware maganarmu? Gabansa ya fadi. Nasa zaton ta dangana da wannan maganar. Maimakon yabata amsa, sai yace, ni na manta ma munyi gida fa. Ya miqe bari in sanar da yaya Amina. Itama ta miqe ta biyoshi. Nan ya labarta musu komai. Suka yi murna sosai. Yaya tace, kuma takardun da sunanka da komai? Yace cikakken sunana kuwa. Tace ko wanene wannan, Allah ya saka masa da alheri. Yace Ameen, gurina da akwai wasu kudi, zan gani ko zasu sai mana kayan gado dana girki. Ba sune dai akafi buqata ba? Yaya tace sune mana. In ma na gado ko katifa ce zatayi muku. Kayan kicin shine yafi zama dole. Yace hakane mu shirya gobe zanzo in kaiku gidan.
Haka kuwa washegari yazo ya kwashesu. Gidan ya burgesu sosai. Mimi ta shiga fargaba, tana tambayar kanta wa zaisa a gidan? Bata san lokacin da tace to kawunsu ummi yaushe zaka dawo nan gidan? Ya kalli cikin idonta, ya karanci wani abu. Don haka sai yace, bari mu koma gida, zaki bani shawara ko? Ta daga gira, alamun eh. Yayi murmushi.
[26/09 8:41 am] Inna: Canjin rayuwa
7⃣5⃣Ismail tunda ya dawo bai zauna ba, abubuwa zunyi masa yawa. Sun raba takardun neman aiki a jami'o'i kamar su A.B.U da B.U.K, har Abuja. Sannan qungiyarsu ta da'awa, suna ta gudanar da aikace-aikace, musamman na gidan marayun da suke ginawa. Sannan ga gayyata da yake samu gidajen rediyo, da talabijin da gabatar da filaye na addini irinsu tambayoyin addinin musulunci, Filin fatawa, da dai sauransu. Haka sauran jihohi irinsu kaduna, kano, sakoto, suna gayyatarsa don yin majalisi dashi. Hakan yasa ismail ya zama kullum yi nan, yi can. Ga shi har ynxun bai daina zama gaban malamai ba don neman qarin ilimi. Daukaka ta Allah, lokaci qanqani sunansa ya karade jihohin Arewa. Wannan yasa mahmud ya matsa masa. Wai ya tare a gidansa. Yaso su tare da mahmud din tunda sama ne da qasa, amma sai mahmud yace, in har ya sake ya tare a gidan ismail din, ba zai maida hankali a nasa ginin ba, wanda yayi nisa da farawa. Ranar wata lahadi misalin qarfe takwas da wani abu na dare, ismail ya shigo gurin su mimi, lokacin babu wutar NEPA ta kwanta a tsakar daki akan tabarma, tana dannan wayarta. Sallamarsa ta jiyo yasa ta kashe tocilar wayar, sannan ta kashe ta gaba daya, ta tura a qasan gado. Lokacin daya iso dakin da sallama, ta amsa. Yace farko dana shigo, sai naga kamar dakinnan da haske. Tace, idonka ne yaga haka. Ya ciro qaramar wayarsa daga aljihu, ya haska dakin. Kafin ya zauna yace, me kuke dashi na ci? Tace shinkafa mukayi da wake, sai mai da yaji. Jiya ne yaya tace, muyi alala, qila kozo, tunda ka kwana biyu baka zo ba. Amma sai kaqi zuwa.
Yace ba zaki gane bane khadija. In a lissafa maki lamurran dake gabana, zaki sha mamaki. Karku damu da yin abinci dani. In nazo kamar haka in na samu zanci. Ban cika son cin yaji ba, shirya ki rakani muci abinci. Ko kuma ke kici kifinki. Tace kana son jana yawo, ni kuma banason fita. Yace shikenan ba zan matsa miki ba. Tace to bari in shirya muje. Ya ciro wayoyinsa banda wadda ya haska. Kamar ana jira sai ga kira, tamkar kar ya daga, sai kuma ya daga don ya lura da lambar anata kiransa da ita bai ta6a dagawa ba.
7⃣6⃣Kamar yadda ya zata kuwa mace ce, ya amsa suka gaisa. Yanason tuna inda yasan mai muryar.Ta katse masa tunani da cewa, baka ganeni ba ko? Yace cikin qosawa eh. Tace zainabu ce. Sai kuwa Mimi taga ya miqe da sauri tare da fadin zainabu?! Tace eh nice, malam. Zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri. Yayi ta maza , yaya gida da mai gida da kuma yara? Tayi 'yar dariya, gida dai lfy mai gida kuwa bama tare. Munfi shekara biyu da rabuwa. Da kuwa qwara daya ne, ya dauki kayansa. Yace, subhanallahi, to Allah yayi miki za6i na alheri. Tace Ameen nagode, na gaisheka. Wannan kuma number ta ce. In ba laifi adan ajeta, don nayi ga kira baka daga ba, qila don bakasan lambar bane. Ban sani ba ko zan kira neman fatawa. Cikin wani shirinka na samu number lokacin daka bada. Yayi 'yar dariya, karki damu zanyi saving dinta, nagode. Kasa kashe wayar yayi, sai itace, ta kashe. Ya zauna bakin gado tare da cewa, auren zainabu ya mutu tun shekara biyu? Kenan ma tun ganin da nayi mata. Yaya tace min tanada aurenta, ashe ba tada shi. Sam ya manta da wata Mimi tana dakin. Ita kam tana zaune hankalinta tashe. Tambayar kanta kawai takeyi wacece kuma Zainabu? Batasan tambayar ta fito fili ba, saida taga ya tsaya cak, daga rawar jikin saving din lambar Zainabu wanda yakeyi. Shi sam ya manta a ina yake ma. Yace, am.. Wata yarinya ce. Ya miqe, ba zaki santa ba. Ya kalleta, ni bari in tafi. Tace zuwa gurin cin abincin fa? Yace mu barshi sai zuwa wani lokaci, zan sha tea in naje gida.
Hankalin Mimi yayi qololuwar tashi, tace, ynxun fa kazo amma har zaka tafi? Yace inada wani uzuri ne, karki damu zan dawo da safe. Bata iya amsa shi ba ya fice. Kai kawo ta dinga yi a dakin. Ta gama yarda cewa tanayi ma ismail wani mugun so, shi yanason wata kenan. Ta fita zuwa dakin yaya Amina ta zauna. Yaya tace yau naga malam ya fita da wuri. Mimi tace, yaya in tambayeki mana? Yaya tace ina jinki. Mimi ta tsura ma yaya ido, wai wacece Zainabu? Yaya tace Zainabu? Kinsan tane? Mimi ta sake tambaya. Tace umm, wata yarinya ce da ismail yayi mata wani mahaukacin So, shine iyayenta suka yaudareshi, suka bada ta ga wani mai kudi. Zufa ta karyo wa Mimi, ta miqe. Yaya tace, yayi miki zancenta ne? Mimi tace kawunsu ummi ne naji suna waya, ta fada masa aurenta ya mutu shine fa ya fita jiki yana 6ari.
7⃣7⃣Yaya Amina ta miqe tsaye tabdi! Ai ko duk nacinsa ba zai aureta ba! Shegiya, ko wa ya bata lambarsa? Tuni nasan aurenta ga mutu, amma na share ban fada masa ba. Saboda kar ya koma mata. Mimi cikin fargaba ta miqe tare da fadin saida safe. Yadda yaya taga hankalin Mimi ya tashi ne ya bata mamaki. Har ta miqe da nufin zuwa ta bawa Mimi shawara, sai kuma ta fasa, tace bari in barta ta fara yin shawara da kanta tukunna. Yarinya kinada miji tun tsawon lokaci, amma me kin dage sai an rabu dake. Daga ganin ta kasan kishi ne can qasan ranga. Ta koma ta zauna. Mimi kuwa tana shiga dakinta ana kawo wuta. Sam bata damu da wutarba, duk da cewa fankar data soma kadawa tana kai mata iska. Sitiri kawai takeyi tsakar daki. Ta rasa wane irin tunani zatayi, ta rasa wa zai bata shawara. Ta zauna bakin gado. Na shiga uku na, ni khadija wa zai bani shawara ynxun? Kalaman yaya Amina ke mata yawo cikin kai, "wata yarinya ce da ismail yayi wa mahaukacin so. Ta maimaita sunan wai Zainabu. Ta tuna yadda ya miqe zumbur lokacin da ta ambaci sunanta. Ta tuna yadda ya manta da ita a dakin sbd zainabu. A fili tace, lallai za'ayi tan kuwa. Wani tuquqi ne ke taso mata daga qirji, tace, qila ma suna can tare. Ranar dai su Mimi ba'a runtsa ba, sannan bata qulla ma kanta mafita ba. Barci sama-sama tayi shi har asubahi. Sai da tayi sallah sannan varci ya dauketa.
Ta kai kusan tara na safe sannan ta farka. Ta fito da nufin gaida yaya, sannan tayi wanka, sai kuma taga yayar sanye da hijabi zata fita. Tace ina kuma zakije yaya? Tace nan maqota zan shiga aikin biki, wannan gidan da sukace muje muga lefe. Kinsan yau ne daurin auren. Mimi tace, wai dole ne jn mutum yananan garin sai ya shiga aiki kenan? Ban saba ganin haka ba. Mu in zamuyi biki, ko suna sai akai gurin yin abincj ayi a kawo. Yaya tace, sha'anin masu kudi kenan. Mu nan in baka zuwa, wa zaizo maka? Bakiga sunan Aishatu ba, gidannan cika yayi? Kinsan dai in bana zuwa ba za'a zomin don tsorona ba. Mimi tace, sai kin dawo. Ni dai bana ra'ayin haka. Tayi 'yar dariya. Aishatu tananan tana varci a uwar daki. Mimi tace to. Ta dauki ruwan wankanta wanda ummi ta zuba mata, kamar kullum tunda bata iya jan ruwa.
7⃣8⃣Tana wanka taji shigowar ismail, yana ta sallama ba a amsa. Tana jinshi yana cewa, inma dai yaya Amina batanan, yasan babu inda Mimi zataje, qila tana bandaki. Saida Mimi ta gama ta fito, sannan ta dauki Hijabin Ummi dake kan igiya ta saka. Ta shiga dakin. Yi tayi tamkar bata ganshi ba. Ta wuce, kan madubi ta zauna tana shafa mai. Ta zame hijabin, ya sauka a wuyanta, dogon gashinta ya bayyana. Ta dauki mataji tana tajeshi. Baqi sidik. Ta lakuto manta na gashi tana kallon gashin cikin madubi. A ranta tana cewa, inda nagode ma Allah, duk lalacewar da nayi gashina bai zube ba. Ta kalli fuskarta a madubin, tace wai wane irin kyau mutuminnan yake buqata wanda yafi nawa? Sai dai ko in balarabiya yake son ya aura. A fili tace, zan so ni kuwa inga zainabun nan wace iri ce ita? Kyanta yaya yake? Yace me kk ce? Cikin sauri ta waiwaya, ta dubesbi. Yace yau 'yan miskilancin ne ko? Kin shigo kinyi kamar baki ganni ba. Shiru tayi, sam ta manta yana dakin, tayi zancen zucinta a fili, fatanta Allah yasa baiji taba. Tace kaji abinda nace ne? Yace a'a me kk ce? Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta maida hankali gurin abinda takeyi. Yace, ki fada min me kk ce mana? Sai naji kamar dai kin ambaci zainabu. Ta danyi dim, sannan tace, wai kai ka damu da wata zainabu, tunda ta kiraka jiya, ka fita hankalinka, harma takai ynxun kunnenka yanayi maka gizo ko? Magana mutane sukayi, sai ka zata sunce zainabu ko? Yace ni bance ba ranki ya dade. Ta zauna tana shafa hoda. Ta gama, taja durowar madubi, ta ciro abin daure gashin ta kamashi a tsakiya. Ta fesa turare sanna ta ciro daguwar rigarta leshi ta saka. Ba tare da ta daura dankwali ba ta nufi kicin. Shi dai yana binta da kallo. Tayi masa kyau a idanunsa. Ta dauko biredinta da ruwan shayi mara madara ta zauna, amma sai damuwa ta hanata cin biredin, sai ruwan shayin take kur6a. Yace nima zansha. Ta miqa masa na hannunta, kar6a. Yace, ki hadamin wani mana. Ta kalleshi, munin nawa har ya kai cikin kofin shayin ne, shiyasa ba zaka iya sha ba? Yace bance ba naga kamar baki qoshi bane, tunda ko biredin bakici ba. Ta daure fuska, nina qoshi. Yace shikenan bani. Ta miqa masa. Kan gado ta koma ta kwanta, fuskarta tana kallon gefe, tana tunanin nafita. Ya kalleta, baisan me take yiwa fushi ba. Sai ya samu kansa da shiga damuwa.
[26/09 9:16 am] Inna: Canjin rayuwa
7⃣9⃣Yace ki tashi khadija, magana zamuyi, duk da naga yau kina fushi dani.Ta tashi amma taqi kallonsa, kanta yana qasa, tana wasa da yatsun hannunta, fuskarta a daure tam. Yace, to inason zan tare a gidana. Kina ganin ya kamata mu koma tare ne ko kuwa zaki zauna anan? Mimi tayi shiru cikin nazari, sai taga ya kamata ta gwadashi. Tace, kai me ka gani yafi? Ni ko ina daya ne a gurina. Ya dago yana kallonta cikin ido, sannan yace, banason in takura miki ne, kamar yadda nayi fa fada miki a tun baya. Abin da kikeso shi zan miki. Ta tura baki cikin jin haushi tace ni banida za6i. Ranshi ya sosu, cikin fushi ya miqe, shikenan, ni zan tafi. Duk lokacin da kk za6a, saiki fada min. Ni dai zan tare, kuma zanyi aure. Batasan lokacin da ta miqe tsaye a tsakiyar gadonba. Me kk fada? Yace nasan kinji. Tace ka auri dubu, amma kafin nan ka warware nawa auren dake kanka. Yace, nufina kenan don nasan bakida burin daya wuce wannan. Amma sai kina ta shirmenki.
A sanyaye tace, dama kazo ka sakeni ne? Kafin ya amsa, qaramar wayarsa ta soma ruri. Ya daga ya fita a dakin yana amsawa. Mimi ta zauna tasa kanta cikin gwiwarta tana kuka. Batasan dalilin kukan ba bare asalinsa. Wata zuciyar ta ingizo ta tare da rada mata cewa, tayi tafiyarta. Ta sauka ta dauko akwatunanta, ta dauki daya, ta soma kwaso kayanta tana zubawa a ciki. Shikuwa yana gama waya ya dawo, da bango ya jingina yana kallonta. Bai hanata ba kuma bai tambayeta dalili ba, har ta gama ta dauki mayafinta tasa takalmi, sannan taja jakar, dariya ce taso ta su6uce masa, amma sai ya fasa. Ya tare qofar dakin. Tace, ka bani hanya zan wuce! Yace zuwa ina? Tace ina ruwanka dani? In tafi ko ina ma, mun hada zuri'a ne? Kawai ynxun ka bani saki na. Kai ko baka sakeni ba ma tafiya zanyi. Ya girgiza kai, bamu bada zuri'a ba, sai dai bansan gaba ba. Amma ynxun kafin ki tafi tsaya mu gama magana, in yasa sai ki tafi, ba zan hanaki ba. Ya nuna mata bakin gado, ki zauna anan! Fuskarta a daure ta zauna. Shima ya zauna.
[26/09 4:09 pm] Inna: Canjin rayuwa
8⃣0⃣Fadamin mecece damuwarki wadda tasa har zaki tafi ki barmu? Shiru tayi, domin ta rasa me zata ce. In zata fadi gsky, to kishi ne kawai ke cinye ta a zuciya. Amma sai tace, na gaji da kushe ni da kkyi. Duk lokacin da ka tashi, sai kace min mummuna. Sannan kaqi ka cika min alqawari na. Yayi murmushi, ni ban ta6a ce miki mummuna ba. Ta kalleshi, ba girmanka bane yin qarya. Domin kune masu fadin illarta. Jiyan nan kace min ko yaushe ina canzawa. Yace, canzawa nace ko muni nace? Tayi shiru. yace, banda jiya sai kuma yaushe nace miki? Cikin qarfin gwiwa tace, da muke asibiti, lokacin da nace, bana sonka me kacemin? Inka manta in tuna maka. Cewa fa kayi kaima kafison mace mai kyau. Ya sake yin wani murmushin, tabbas nace haka, amma nace bakida kyau? Tace kusan haka ne? Yace ba dai hakan bane tunda kusan ne. To naji wannan sai kuma batun alqawari, duk alqawurran dana daukar miki a gaban Doctor salis wanne ne ban cika ba? Tayi shiru, tabbas yace zai nesanta ta da iyayenta kuma yayi. Yace zai kula da ita daidai qarfinsa, kuma yayi, in zata duba tsawon lokacin da ta dauka tana jinya, sun yi ta dawainiya da ita. Ta dubeshi, sai na rabuwa, shine baka cika ba. Yace banda shi na cika sauran? Ta daga kai, alamun eh. Yace to bari in tuna miki. Kinsan na jima ina yi miki alqawarin cewa zan yi miki fiye da kk taso anayi miki na gata ko? Tayi shiru tana kallonsa. Ya tausasa murya, inason ki jira ni in cika wannan alqawarin, ko zamu rabu, ki bari in gama yi miki gatan dana tsara ma kaina, inji dake wani irin dadin da baki sanshi ba. In yasa nan, sai inyi miki abinda kk so. Tayi wani dan tunani. Sannan tace, zan yarda ne kawai in kaima ka yarda da abinda zan fada ynxun. Yace inajinki. tace zaka daura aure ne lokacin da ka warware nawa auren. Yace ban fahimta ba? Tace, ina nufin ba zaka ki aure ba, sai lokacin daka warware nawa auren. Yayi shiru don shi tun jiya ya gama tsarinsa. Ya tsara zai auri zainabu don ya gaji da zama haka, ita kuma lokacin data gama shirmenta sai su shirya don babu saki acikin zuciyarsa a ynxun. Daga nan sai ya kaita gaban iyayenta ta nemi gafararsu, duk da Hajiya tace zasu nemeshi in lokaci yayi. Amma dubi yadda ita kuma ta 6ullo masa da wata magana.
8⃣1⃣Ta katse masa tunani da cewa, kayi shiru? Yace, kina ganin zamana babu aure ba ragewar mutunci na bane a matsayina na mai fadakarwa? Ta miqe tsaye, tayi dan taku daya zuwa uku, sannan ta kalleshi, ni da kaine kawai muka san cewa ba kada mata, amma Duniya ta jima da sanin cewa kanada aure. Yace naji saidai karki manta ni fa mutum ne, kuma ba yaro ba, wanda yakai. Kinsan dole ina buqatar abokiyar halittata. Kinsan shekaruna nawa ynxun? Tace ban sani ba, qila zaka gota talatin. Yace yauwa, to in na rantse miki ba zanyi kaffara ba, a takure nake, sannan inason yara. Ynzun dubi mahmud, matarsa tanada ciki na biyu. Ya numfasa, khadija saka idonki cikin nawa, ta kalleshi. Yace ina buqatar abokiyar rayuwa. Ta sunkuyar da kai, wannan ai zancenka ne da kuma wadda zaka aura. Kukan Aishatu ta jiyo, ta miqe da sauri, har tana tuntu6e da qafarsa zata fadi. Ya sa hannuwansa ya tare ta. Sai tsintar kanta tayi a jikinsa.Duk zun jisu cikin wani yanayi. Shine yayi ta maza. Yace ina zakije haka? Kike sauri zaki fadi kije ki karye, dama gaki nan kamar 'yar tsinke. Ta tashi da sauri, bakaji kukan Aishatu ba? Da sauri ta nufi gurin Aishatu. Ta shigo riqe da hannunta, sai lallashinta takeyi. "Yarinya tana kuka kin firgice, ranar da kk haifi naki, sai yaya? Ta harareshi cikin wasa, me zai hadani da haihuwa? Yayi qasa da murya, "wai ba kyajin komai game dani? Tace Aishatu dai tana kallonka. Ya miqe, bari dai in gafi tunda kin fasa yajin. In yaya ta dawo ki fada mata cewa nazo, kuma batun tarewa ya kawoni. Ynxu zance in samu mahmud ne muje kasuwa mj sayi abinda ya sauwaqa, mu zuba a gidan, to shikenan.
8⃣2⃣A zaure zuka hadu da yaya. Nan suka gaisa yayi mata bayanin dalilin zuwansa har yadda sukayi da mimi. Dariya yaya tayi, domin ta gama gano mimi tsabar son mijinta takeyi, amma sai bata nuna ma Ismail din ba. Tace khadija kenan 'yar daru, 'yar shagwa6a. Zamuyi magana da ita. Amma ni shawarata karka tsaya bata wani za6in ko nan ko can. Kawai kace mata ku koma, ko don sbd kauda hankalin mazu zaton bakada aure. Yace nima haka nekeso, amma kinsan rigimarta. Gashi zai da'awar in saketa takeyi. Ni kuma gsky sai inga in nayi haka ban kyauta wa mahaifiyarta ba. Yaya tace wannan ma bata taso ba. Kudai koma din, qila ma ku sasanta. Ismail yace, Allah yayi mana jagora. Yaya tace Ameen. Sukayj sallama tayi ciki shi kuma yayi waje. Kafin sati daya, ismail ya sayi abinda ya sauwaqa, sun kai sjn shisshirya. Sannan sun shirya walima, inda su yaya da maqotanta sukayi musu girki, shinkafa ce da waina, sai kaji. Girkin yayi kyau sosai, ga kuma abin sha. Bayan sun tashi daga walimar ne, sannan sukazo suka kwashe kayan sawar mimi, shi da mahmud. Kayan Gado dai tabarma su Ummi. Duk da haka basu koma ba, sbd ismail zasuje kaduna da kuma Abuja, don gabatar da wasu muhadarori, da kuma lakcoci. Haka kuma suna durowa katsina, ya tarar da takardar gayyata daga gwamnatin jihar katsina. A hannun Malam Aminu ya samu saqon. Yace wannan taro ne na manyan malamai, to ni meya kaini gurin? Malam yace daukaka ce daga Allah, ismail. Shawarar da zan baka kayi taka tsan tsan, domin Malamai ma wasu basa tsoron Allab, musamman in sunga Allah ya baka nasibi. Sannan kar kayi sanyi gurin fadar gsky, komai dacinta. Ismail yace shikenan zan kula insha Allah, nagode. Gidasa ya wuce, sai da yayi wanka ya huta, sannan ya fita zuwa gidan yaya Amina. Yayi matuqar qosawa Mimi ta dawo, ko don Abinci. Gashi a gida mai kyau, amma abinci sai ya siya. Can yaci abinci, sannan yace, yaushe zaku raka mimi can gidan? Tace sai jibi.
[26/09 10:32 pm] Inna: Canjin rayuwa
Washegari ya samu halartar gayyatar da akai masu. Maqasudin zaman dai, sbd tafsir ne na Azumin dake gabatowa. An yi musu jan hankalin hadin kai, su daina zagin juna, da kafirta juna. Sannan kowa yayi wa'azinsa ba tare da izgilanci ba, ko cin mutunci. Ka abinda Allah da manzan sa sukace, a tsage gsky komai dacinta. Malamai sunyi bayani, inda shima ismail yayi nasa bayanin, wanda ya gamsar da dukkan mahalarta taron. Sbd ismail, Allah ya hore masa hikimar iya magana. Shi mutum ne wanda zaiyi wahala yayi maka bayani baka gamsu ba.
Bayan an fito ne, ismail ya miqa hanya da nufin neman dan aca6an da zai kaishi gida, sa6anin sauran malaman da suka zo da motocinsu. Wannan dalilin shine ya kawo inda aka bincika cikin malaman da suka halarci taro, aka fidda guda hudu wadanda basuda abin hawa. Washegari saiga mota sabuwa dal, babu ko lamba an kawowa ismail. Lokacin da Malam Aminu ya kirashi yazo, shiru yayi ya kasa magana, lokacin daya gabatar masa da motar. Bai san da wace kalma zai fara magana ba, duk wani alheri da zaizo masa ta gurin Malam Aminu yake tahowa. Yace Malam, Allah ya saka maka da aljanna. Sunyi ta murna. Ya kira mahmud. Dama mahmud ya iya mota. Nan suka shiga suka zagaya gari, tare da zuwa gurin abokan arziki. Sunje gidansu, inda 'yan gidan suka fito suka ga mota sunata murna. Ta fito wanka , tana shafa, ummi ta shigo da gudu. "Aunty zo kiga motar kawunmu, sabuwa dal, baqa kuma qatuwa. Mimi tayi dariya sbd yadda Ummi ta jero maganar, tare da cewa, Allah yasa alheri. Sai gashi da kansa, khadija kizo ki gani mana, munyi mota. Mimi ta miqe taje taga mota, kuma tayi murna. Yace ki shiga mana ko kin manta da yadda akeyin tuqi? Murmushi tayi, sannan ta amshi makulli, su Ummi suka shiga, ta tashi motar ta tuqa zuwa cikin layi, suka dawo. Ummi sai mamaki takeyi, tana cewa, anty yaushe kk koyi tuqa mota? Ismail ma cewa yayi ashe baki manta tuqin ba. Tace in manta tuqi? Ashe zan manta da yadda zanyi tafiya da qafata. Suka sa dariya.
8⃣3⃣Washegari Ismail da mahmud suka soma fita don koyo ma ismail tuqi. A yammacin ranar ismail, ya kira yaya Amina yace, su shirya zasuyi tasu walimar a gidansa. Bayan la'asar suka zo kwashi su yaya Amina, suka biya suka dauko Rabi'a da innarsu mahmud. Bayan sun kaisu ne, sai suka koma suka dauko su inna, dasu fatu. Dukda ba wani alatu. Ismail ya zuba a gidanba, gidan yayi kyau sosai. Katifu ne a dakunan da sabbin zannuwan gado da fuloli, sai labulaye masu tsada. Sai falon ne ma ya gyarashi sosai, don tsadaddun kujeru ya zuba da kafet din tsakiyar, shi ma mai tsada ne, TV da sauran kayan kallon zamani. Sai dai falon saman bai saka komai ba. Yace sai ahankali zai saka komai. Mimi taga qorarinsa sosai, tunda tasan shi talaka ne. Sun je sun kawo musu abin sha na gora. Daf da magriba suka koma kai su innarsa, sannan su yaya Amina. Mimi harda kuka wai abar mata Ummi. Yaya tace a'a za dai tazo miki hutu, kuma kinsan zata tayani aiki, ga makaranta. Mimi tace yaya baga saddam ba. Kuma indai makaranta ce ai zan kaita tunda ga mota a hannun kawunsu. Tace kiyi haquri har suyi hutu. Ismail dake kallonta burgeshi takeyi, don yanason shagwa6arnan tata. Shiyasa ma yaqi sa musu baki, don yanason kallonta a haka. Ita kuwa yaya Amina, taqi barin Ummi ne don zamansu, su biyun wata hikima ce, tana sa ran su shirya kansu. Sun barta da Rabi'a in sun dawo kaisu yaya, sai mahmud ya tafi da matarsa. Bayan tafiyar su ne, sai kuma suka shiga kicin don ganinsa. Freezer ce, sai tukwane da kuloli, plates da cokula, amma babu risho ko wani gas. Rabi'a tayi dariya, tace to da me zakuyi girki? Mimi tace oho masa. Suka koma sama sukayi sallah, sannan suka dawo qasa suna 'yar hira.
8⃣4⃣Ranar Mimi harta dan saki jiki da Rabi'a, don ta lura Rabi'ar ta san me takeyi. Rabi'a tace, niko da ace zaki yarda da na baki shawara. Mimi tace, me zai hana? Rabi'a tace kar kibar wata mace ta shigo gidannan a matsayin matar malam ismail. Mimi ta tattaro hankalinta gurin Rabi'a. Ta yaya zanyi hakan? Nasan dai kinsan komai dake tsakaninmu da malam din, tunda Aminin mijinki ne. Bafa son juna mukeyi ba. Rabi'a tace ni kuwa sai ina kallon so acan cikin qwayar idanunku. Na farko da baya sonki, da tuni ya sakeki. Rashin sakin jikinki shine ya hanashi nuna miki. Mimi tayi murmushi, ya fada miki ne? Rabi'a tace a'a nice nayi hasashen hakan. Mimi tace bana zaton zai soni, sbd na samu labarin yadda yakeson wata Zainabu. Rabi'a tace, tabbas yanason zainabu, amma da kinso, da tuni kin mantar dashi ita. Kiyi tunani. Mimi ta sauke ajiyar zuciya, ni damuwa ta ma ko auren namu yananan daram ko ya lalace? Oho. Kafin Rabi'a tayi magana, sai gasu sunyi sallama. Don haka, sai suka rufe bakin hirar. Tare suka tafi dukkansu, aka kulle gidan. Mahmud ne ya jasu zuwa gidansu. Sun danyi hira, sannan Mimi ta jawosu zuwa gida. Ismail yaji dadin yadda Mimi ta saki jiki da Rabi'a. Bayan tayi wanka tayi isha'i, ta saka kayan varci, ya buga qofarta, taja hijabi ta saka, sannan tace, shigo mana. Bakin katifa ya zauna, sannan yace kinga dan kayan dake kicin din ko? Sai a hankali zamu qara abinda bamuda shi. Tace maimakon kabar wani abin ka siyo gas ko risho, to dame zamuyi girkin? Ya zaro idanu, alamun sam ya manta da Risho. Sannan yayi dariya, lallai yau akeyinta. Sam na manta fa. Kinsan abubuwan da yawa, gashi ba wai inada kudin bane. Amma karki damu zuwa gobe ko risho dinne, sai in samo. Gas daga baya zamu samu. Ina son ma ki zauna ki rubuta abinda muka fi buqata, sai muyi ta siya a hankali. Ki fara da wanda muka fi buqata. Tace mu bari saida safe. Yace rubuta dai ynxun. Ta dauko takarda da biro, shi kenan dame zamu fara? Yace kayan gado, sai falon sama, abubuwan cikin ban daki, sai me? Tayi dariya sannan ta soma tuno wasu tana fada, suna rubutawa. Sun kai kusan sha daya, kafin yace mata bari ya tafi saida safe.
[27/09 7:59 am] Inna: Canjin rayuwa
8⃣5⃣Ya jima kafin yayi varci, sbd gsky haqurinsa zai gaza. Ko da bayason Mimi, to yasan yana muradinta a gefensa. Ballantana yana da tabbacin cewa wani sashe na zuciyarsa yanason Mimi. Duk lokacinda yazo da niyyar sanar da ita hakan, sauta 6ullo masa da zancen saki, sai dai wasu abubuwan da takeyi, sai yana zargin cewa tana sonshi. Washegari da safe, yana zaune a falon qasa, yana duba wani littafi, ta sauko tayi wanka tasa daguwar riga ruwan qasa, mara nauyi, bata daura dankwali ba, ta kama gashin kanta a gefe. Tunda ta nufo shi ya kasa daina kallonta har tazo ta zauna akan kafet kusa dashi. Tace ina kwana? Yayi murmushi, "lafiya lau" kefa kina lfy? Tayi dan fari da ido " qalau" ta gyara zama tace ynxun yaya zamuyi, tunda bamuda abinda zamu hura wuta? Yayi murmushi. Fita zanyi in siyo mana abinda zamuci. Tace a'a kawai muje gdn yaya Amina muci. Yace kinsan yau dai ba zasuyi damu ba, amma bana siyo butar dafa ruwan zafi ba? Tace haba? Ni banganta ba. Ta miqe zamu dafa ruwan tea. Yace muje in gani, amma tabbas na siyo Butar ruwan zafi. Sun dafa ruwan zafinsu, suna sha, suna labari kadan-kadan. Daga bisani yayi wanka ya fita.
[27/09 3:47 pm] Inna: Canjin rayuwa
8⃣6⃣Ranar da suka cika kwana uku, Ismail yaji haqurinsa zai kasa. Don haka yaga babu abinda yafi illa ya ziyarci zainabu. Koda ya shawarci mahmud sai yace masa kar ya soma, ya dai yi qoqari ya sasanta da matarsa. Sam ismail zancen bai shigeshi ba, domin yasan tun filazal ba sonshi da Zainabun sukeyi ba. Don haka ya yanke shawarar kiranta a waya don ya fada mata cewa zai kawo mata ziyara. Misalin qarfe hudu bayan sun fito la'asar ya ciro wayarsa ya soma neman lambar zainabu. Koda yazo kan lambar saida yadan jima yana tunani kafin ya danna kira ya tafi, lokacin zainabu tana kwance a qofar dakin innarta tana buga game din maciji, sai kawai taga kira ya shigo. Ganin sunan dake rawa akan fuskar wayar, saita zaro ido tare da murza idon, sannan ta dauka cikin sauri tare dayin sallama. Sun gaisa sannan yana ganin saqonta na gaisuwar juma'a kuma yana godia, tace ashe kana gani, nayi zaton ma baka gani tunda kuna hulda da jama'a sosai. Yace ina gani, ko zan sameki anjima? Cikin sauri tace, inanan Malam. Yace, qila in shigo anjima. Tace to Malam, Allah ya kawoka. Duk mahmud yana jinshi.Misalin takwas da mintuna mimi tana daki tana danna wayarta, so take ta tsokani ismail tana kiranshi amma yaqi dagawa, sai kawai Mimi taga ya fito cikin shadda wagambari sai maiqo takeyi. Mai kalar blue, haka hularsa. Ta wundo ta hangoshi. Cikin sauri ta 6oye wayar sannan ta fito, ina kuma zakaje da darennan? Yace wata 'yar unguwa zanje bazan jima ba. Tace inzo in raka ka? Ta fadi haka ne don ranta ya raya mata ko gurin wata zashi. Yace a'a ki barshi ba ni kadai bane nida mahmud ne. Tace kasan dai inajin tsoro, don Allah karka zauna. Yace ynxun zan dawo. Tace amma bada mota zakaje ba? Yace da ita zanje mana. Nifa na tuqo motar daga unguwar su mahmud dazu, bare ynxun da babu cunkoso. Ta windon su na sama take leqensa ya fita da motar, sannan ya dawo ya rufe gidan, ta saki labule, ta koma ta zauna tana ta karanta wasiqar jaki. Yana isa gidansu zainabu, ya kira ta cikin waya ya fada mata ya iso. Cikin soron gidansu suka zauna. Sun gaisa sannan ismail yace, gani nazo a karo na biyu, banda zuciya ko? Cikin sauri tace, malam kayi haquri, ko da ba laifina bane. Wlh ina sonka, shine ma dalilin da ban iya zama gidan Alhaji ba. Yayi murmushi, to ina fatan ba zan sake samun matsala ba, don wannan karon banason aja lokaci. Tace ni ko gobe ka turo, don dama zaman jiranka nikeyi. 'yar dariya yayi, sannan yace shikenan ko ban sake zuwa akan lokaci ba zamu dinga waya.
8⃣7⃣Wasegari ya samu gayyata daga abuja, jami'ar da ya nemi koyarwa. Yaje kuma sun daukeshi, yayi murna sosai. Haka ma dangi sunyi murna, illa mimi kadai da take ganin cewa za suyi nisa da juna. Yayi mata tayin ziuwa abuja tace, ko sha'awar zuwa bataso. Yace, nasan ba zaki iya zama ke daya ba, yaya kk son ayi? Tace zan koma gidan su yaya Amina, in ka dawo sai in dawo. Da kanta tace, ya sakata islamiyya a unguwar su yaya. Sam in kaga Mimi ba zakace ita bace. Sbd dogon hijabi da niqabi. Lecturing daya soma sai ya dauke hankalinsa daga kan batun auren daya so yi cikin gaggawa. Amma dai suna waya da zainabu. Duk sati yake zuwa, wani lokacin sati biyu. Shi mahmud ABU zaria ya samu. Ismai ya kira masu aiki sun duba filin dake gidansa sun tabbatar masa zai iya yin makaranta harda madaidaicin masallaci. Bayan sun bashi tsarin ginin, sai ya soma tunanin yadda zai samu kudin ginin don kudin da aka qiyasta makarantar zataci ba qanana bane. Harkoki sun bude ma ismail, ga alherai da yake ta samu daga jama'a, domin ranar da akayi wata hira dashi a gidan TV na Africa, lokacin gidan TVn yana sabon budewa, har ya sako bayani akan makarantar da yakeson ginawa, ko sati ba'ayi ba, saiga shi mutane sun fara kiransa don son bashi gudunmuwa. Kafin wani lokaci tuni an soma gini. Babban qalubalenshi mata. Ko a makaranta, mata ne keta kawo mashi hari. To don yana malami, shi kam ba waliyyi bane, da yawa ana jarabtar Malamai da son mata da kuma kudi, in bakayi taka tsantsan ba, sai ka fada halaka. Shi yasa ya gama yanke hukunci. Yana samun hutun qarshen zango yazo, to kuwa aure zaiyi, ko ma da wacece. Wata asabar ya dauki takardar da Mimi ta rubuta duk abinda suke buqata, ya shiga kasuwa, sai da yayi rabi, tun daga kan gado zuwa saurensu. Dakin mimi kuwa saida ya tsara mata shi fiye da nasa, sannan yayi mata sayayyar kayan sawa, sannan ga sabuwar waya da kuma layi, tsohon nasa ne ma ya bata. Don har ynxun baisan tanada waya ba.zainabu ma yayi mata 'yar sayayya.
Bayan sunyi hutu, dukda cewa sati biyu ne hutun nasu, amma cikin sati biyun zai yaye ma kansa damuwa. Shiyasa ma washegari da safe yana zaune falon qasa yanashan tea, saida yaga itama tazo ta zauna , sai ya dauki wayarshi yana kiran layin zainabu, da farko hankalinta baya kansa, saida taji yace zainabu, cak ta tsaya ta kada hadiye tea din data kur6a. Yaci gaba ina gari zan shigo anjima yaudai zamu gama magana. Inason kafin hutunnan ya qare zaki zama a gidana. Cikin murna take fadin sai kazo. Yana kashe waya mimi ta maida tea din dake bakinta cikin kofin, sannan cikin wata irin murya tace magana zaku gama? Ya dubeta fuska daure, "khadija aure zanyi" ji tayi tamkar ya soki zuciyarta da qaho. A hankali ta jingina da kujera, sannan ta lumshe ido, ta rasa me ma zatace. Sai kawai ta tashi ta nufi dakinta. Bakin gado ta zauna, rashin wanda zai baka shawara matsalane. Tasan tunda yace mata aure zaiyi, to kuwa yana nufin rabuwarsu tazo kenan. Wata zuciyar tace, lokaci yayi da zaki koma gidan iyayenki. A fili tace, kai da saura. Haka zan koma musu bayan shekara uku, babu wani ci gaba, ba kuma auren da suka daura min, bayan tsohon laifina na baya? Ta girgiza kai, lokaci baiyi ba. Mafita ya kamata in nema. Ya turo qofarta ya shigo. Jikin sif dinta ya jingina. Khadija ban zaci zakiyi fushi ba, Nafi zaton zakiyi murna, don lokaci yayi da zan warware aurenmu.
[27/09 3:48 pm] Inna: Canjin rayuwa
8⃣8⃣Ta daga masa hannu. Don Allah ka fita! Inason inyi tunani. Yace inace kin gama tunani daga yau? Ta miqe, ta ra6a ta gefensa ta fita, qasa ta koma ta kwanta kan doguwar kujera. Murmushi yayi, sannan ya shiga dakinsa. Wayarshi ta gani da sauri ta dauka ta shiga kicin. Bata sha wahala gurin ganin sunan zainabu ba. Ta dauki lambarta. Sannan ta dawo da wayr inda ta dauka. Bayan ta shiga dakinta ma harda shiga bandaki. Layin zainabu ta kira, bayan ta daga mimi ta soma magana da kakkausar murya, "kece zainabu?" tace eh nice. Dama na kiraki ne in fada miki cewa ki fita harkar mijina, in har kinason zaman lfy. Zainabu tace wai waye mijin naki? Mimi taja tsaki, "kinsanshi tunda har kina shirin aurensa. Zainabu tace, oh wai kina nufin malam? In shine sai ince kinyi kuskure. Domin aurensa shine abinda nake buri koda zaki zama ajalina. Ki sani kafin ya soki, ni ya soma so. Kuma ina sonshi, aure babu fashi! Mimi tace, mu zuba! Ni dake zanga wanda keda nasara! Ta kashe wayar, sannan ta fito daga ban dakin, ta jefa wayarta akan gado. Ta shiga yin kai kawo a tsakar dakin. A fili take fadin, wai meyasa ni bana burgeshi ne? Dame zainabu ta fini ne? Ta janyo hijabinta da niqabi ta saka, sannan taja durowa ta dauki kudi ta nufi qasa. Bata zaci yana qasan ba. Saida taji yace, ina zaki? Ba tare da ta tsaya ba, tace gidan yana Amina. Ya daga murya. Ba zaki je ba. Ga waiwaya ta dubeshi, fuskarsa murtuk, sama ta koma fuuuu. A zuciyarta da qudirin cewa shima kuwa sai tayi masa abinda ba zai fita anjima ba. Haka suka yini kowanne zuciya babu dadi. Da dare tanata fakonsa , ya shiga dakinsa yana tashi, sai kuwa ta sauka qasa , ta dauke masa makullin mota, ga jefa qasan kujera. Sannan ta kulle qofar falon ta saka makullin cikin rigar mamanta, sannan ta koma dakinta. Tana kwance, rigingine kusan minti shabiyar, sai kurum taji turo qofarsa. Tashin da tayi da sauri shine ya kawo har yaji qaran makullin. Yace bani makullin mota dana qofar fita. Tace ajiya ka bani? Inama zakaje? Ni gsky tsoro nakeji, ba zaka fita ba. Yace, tadi zanje ki bani, karki 6atamin lokaci. Cikin 6acin rai tace, nifa bazan zauna ni daya ba. Yace to kizo muje tare. Da qarfi tace, Allah ya tsare ni.
8⃣9⃣Har inda take ya tako, daf da ita ya tsaya, ya sa hannu ya dafa kafadarta, girgiza ta yayi don yaji daga ina yaji qaran makullin. Amma sai baiji qaranba, sbd sun samu mazauni mai kyau a tsakiyar qirjinta, makari guda biyu sun taresu. Sai ya soma yi mata wani irin lalube tun daga qugunta yake shafawa da hannuwa guda biyu gaba da baya. Hakan ya kashe mata jiki, har ya tilasta mata lumshe ido, daga ita harshi. Haka nan yanajin makullin, sai ya zura hannunsa ta saman rigarta don ciro makullin. Ya ciro, amma yanayinsa gaba daya ya raunana, kamar yadda itama ta sukurkuce. Ta bude idanu ta kalleshi, shima fuskarta yake kallo. Cikin ido suka kalli juna, sannan a hankali yace, saina dawo. Ta fahimci muryarsa ta canza. Kan gado ta fada ta soma kuka. Kusan minti biyar ta tashi ta rufe qofarta. Shi kansa baisan meya hanashi yin wani zance mai muhimmanci ba, aun daiyi 'yar hira yace, zai dawo kan batun aurensu, yana sauri ne don matarsa ba tada lfy. Ta so ta fada masa kiran da matar tasa tayi mata, sai kuma ta fasa. Lokacin da ya dawo, ya hau sama, kai tsaye qofar Mimi ya murda, amma sai ya jita gam. Don haka sai ya wuce zuwa nasa dakin, bayan yayi duk abubuwan da yakanyi kafin ya kwanta, sai ya kwanta. Juyi kurum yakeyi tare da tuno yadda ya caje matar tasa. Ya gama yarda itama ko bata sonshi, to kuwa tana buqatarsa, don ya lura da halin data shiga a lokacin. Yanke shawara yayi ya tuntu6eta da batun, amma sai ta huce daga wanna fushin da tayi. Da asubahi, kamar kullum saida ya qwanqwasa mata qofa kafin ya wuce masallaci. Ita kam tuni idanunta biyu, domin dai yau duk satar varci, saida yayi mata haquri. Ta amince, baya sonta tunda har ta zubarda kimarta ta 6oye makulli, amma saida ya dauka kuma ya tafi. Zucigarta dai tanata bata shawara akan ta fito fili ta fada masa abinda ke ranta. Sai dai ita tsoronta kar sai yaji sirrin zuciyarta, sannan yace, ba irinta yakeso ba, kamar yadda yayi ta fadi a baya. Takaici ne ya hanata fitowa daga daki. Koda gari ya waye, shi kuwa shareta yayi, har ya gama komai ya fita, sai dai alamu sun nuna bata bude qofar ba, har ynxun qarfe hudun yamma. Yaje ya daga labulen windonta, tana kwance akan sallaya, da alamu tayi la'asar ne. Yace khadija, ki tashi ki bude qofa mana! Tana jinsa tayi shiru, daman so takeyi ya lallasheta, amma ko zata bude ba ynxu ba. Yace kinci wani abu ne? Bata tanka ba. Ya sauka qasa. Baisan me yarinyarnan keso dashi ba. Yau duk ta hana rayuwarsa sukuni, don koda ya fita, hankalinsa yana gida. Baisan mimi da gske takeyi ba saida yaga anyi sallar isha'i ya dawo bata fito ba. Da ya leqa ya ganta kwance rub da ciki akan gado.
[27/09 9:54 pm] Inna: Canjin rayuwa
9⃣0⃣Yace kadija ki dubi girman Allah ki bude, muyi magana. Nifa bansan dalilinki ba. Hava khadija ya kk so inyi da rayuwa ta. Ganin bata tanka shi ba, sai ya yanke shawarar kiran mahmud. Kafin isowar mahmud din, ismail yaci gaba da lallashinta, amma ko motsi batayi ba. Bataji takun shigowar mahmud ba, sai dai muryarsa taji yana cewa, don Allah khadija ki bude qofar nan, muyi magana. Don Allah zaki bude ba don ni ba. Kuma ina bayanki akan kowane dalili ne yasa kika rufe qofar. Sunfi minti biyar kafin ta taso ta bude, tana layi. Cikin hanzari ismail ya shiga ya kama hannunta. Dukda qaton hijabin sallar data saka ya hada, ya dauke ta zuwa falon qasa. Yunwa da damuwa sun hadu sun ramar da ita. Ya zaunar da ita akan kujera. Yace haba khadija kowane irin laifi nayi miki, ya dace ki yanke ma kanki irin wannan hukuncin? Cikin raunanniyar murya tace, ku barni don Allah. Mahmud yace, ka kawo mata ruwan zafi, tunda bataci komai ba, hanjinta zai warware. Ya nufi kicin ya hado mata ruwan zafi. Saida yayi ta lallashinta, sannan ta amsa tanasha. Kafin tayi rabin kofi, zufa ta rufe ta. Sannan taji qarfi a jikinta. Ta kama gefen hijabinta tana sharewa. Mahmud ya dubeta khadija bai dace kiyi irin wannan ba. Horon kanki da yunwa, wannan ba dabi'ar musulmi na gari bane. Ismail yace mema akayi mata ne? Taqi bani dama in nuna mata muhimmancinta. Kullum zancenta daya ne in saketa. Nace mata in nayi aure zanyi mata abinda takeso, kuma ynxu na soma neman aure. Sai tazo tanayin irin wannan? Sai kawai sukaji muryarta tace, duk wadda zaka aura, ka aura amma banda zainabu. Cikin sauri ya miqe, sbd me zakice haka? To ai wannan ba huruminki bane. Wadda zan aura sai kin za6a min, sai kace uwata? Ok, na gane nufinki, wato tunda baki sona kar wadda ta soni ko? To na gaji da wannan mulkin naki. Kuka ta soma, tare da fadin dole ka barta, kamar yadda dole tasa na haqura da khalil. Yace in ba haka ba fa? Tace za kayi da ka sani. Mahmud dake kallonsj, bai katsesu ba, sai yayi murmushi. "Da ace zaku fito da abinda ke zukatanku, wlh da kun huta. Sukayi shiru. Yace shikenan zainabu an bar maganarta. Zai canza wata. Haka yayi miki? Tace eh.
9⃣1⃣Ismail zaiyi wata magana mahmud ya daga masa hannu, tare da fadin an wuce wannan. Ka samu Malam, akwai wani sanata faruk da ya samu malam da maganar 'yarsa. Banji dai kan zancen ba, amma tabbas naji malam yace mutumin ya baka 'yarsa. Ismail yace, Hanan umar faruk kenan. Nasan yarinyar daliba ta ce a Abuja. Tanan kuma ta biyo? Mahmud yace bakamin zancenta ba. ismail yace banida ra'ayin auren yaran masu kudinnan, amma tana da hankali. To in anyi haka ya zanyi da zainabu? Banyi mata adalci ba. Duk zantukan da zukeyi, mimi mutuwar zaune tayi. Sai alokacin ta gane ba wai zainabu kawai take kishi ba. Duk matan duniya takeyin kishi dasu akan mijinta. Saidai ba tada ikon cewa komai akan wannan. Sun juya harshensu zuwa larabci, inda ismail ke qorafin ba'ayi ma zainabu adalci ba. Mahmud yace kafin kayi masu, sune suka fara yi maka. Sannan yarinyarnan tana matuqar sonka. Ina mamaki da kullum kuna tare, amma ni na gane hakan, kai ka kasa. Ismail yace nima inaso in fahimci hakan, sai tayi ta maganar saki, saki. Shiyasa naga kawai in haqura. Yace to ka gwada mana, zaka iya ganewa ta hanyar ta6a jikinta. Mahmud kaqi yarda cewa kana sonta. Alhalin shine dalilin daya hana ka daketa. In kaqi yarda dani ynxun, zaka yarda dani a gaba.
Mahmud ya miqe, tare da cewa, bari inje gida nima, kar Rabi'a ta kullemin qofa. Ismail ya kalli mimi, ya tausasa murya, ina makullin motar in saukeshi a gida? Ta kalli kujerar da suke kai, tana qasan nan. Suka ciro suna dariya. Ismail yace babu irin leqen qasan kujerar nan da banyi ba, ashe yana ciki. Sai daya miqe mahmud yace, dama saboda ta nuna makullin nayi shiru, amma da mashin nazo.
[27/09 9:55 pm] Inna: Canjin rayuwa
9⃣2⃣Bayan ya rakashi ya tafi, shi kuma ya kulle gida, ya kulle qofa. Har lokacin mimi tana zaune anan, amma ta zurfafa a tunani. Wacece Hanan? Ya zauna kusa da ita, "khadija hakan yayi miki ko? Ta kalleshi firgigit, batasan ma yazo kusa da ita ba, ta sauke ajiyar zuciya, "wai itama Hanan din kana sonta? Yace ban sani ba, sai naje na ganta sosai. Ya kalli cikin idanunta data tsareshi dasu. Kishi ya gani qarara a ciki. Tace, itafa tana sknka? Yace gsky tana sona, domin ta nuna min alamu. Tace, dama kana iya gane alamun mace, tana sonka? Yace, sosai kuwa. A ranta tace, to baka qware a wannan fannin ba, tunda ka kasa gane irin wanda nakeyi maka. A fili sai tace, tanada irin kyawun da kake so kenan? Yace banyi mata kallon qurilla ba. Ya rufe wannan da cewa, yau kin tsorata ni. Don Allah karki sake yi min haka kinji? Kallonsa kawai Mimi keyi, amma ita tamaicinta yafi tunaninsa. Ta miqe, bari inje in kwanta. Yace duk yinin da kikayi a gado a kwance baki gaji ba? Tace, karka damu bana gajiya da varci kai ka sani. Ya bita da kallo, damuwarta tana matuqar damunsa. Ya miqe shima yabi bayanta. Tana fitowa ban daki ta ganshi zaune a bakin gadonta. "Lafiya?" ta jefo masa tambaya. Yace, babu inda yake miki ciwo? Ta girgiza kai, a'a yace naga kina cikin damuwa ne har ynxun. In dai maganar zainabu ne ki dauka ya zama tarihi. Tace kaje ka kwanta kawai, ya wuce nima. Ya miqe ya nufi fita, sai kuma idanunsa suka hango wayarta dake kan madubi. Yace waccan wayarfa? Tare suka isa gurin, ya rigata dauka. Cikin sa'a ta amshe, tare da cewa, wayata ce bani. Yace shine baki ta6a kirana ba? Tace, ni bana kira da ita, sai dai inajin rediyo. Yace shikena saida safe.
9⃣3⃣Ya jima yana kai-kawo a dakinsa, zai tattara alamomin so da mimi take nuna masa, to me zai hana ta fada masa? Kuma meya kawo ta dinga batun saki? Wata zuciyar tace kaima ya kamata ka tantance kanka, shin kana sonta ne? Ko tausayinta kk ji? Ko ko sbaquwa ce? Can qasan zjciyarsa sai yaji an amsa da cewa duka ka hada. A fili yace, khadija! Babu batun saki. Ko da baki sona, balle zan gwada ki in gani. Washegari da safe, tana kicin tana hada masu abin karyawa, ya shigo cikin rashin walwala, ta kalleshi, "barka da safiya? Yace barkanmu. Ya kusanto ta, "bar ynxun baki huce ba Dija? Ko itama Hanan din baki sonta ne? Ta kalleshi, sannan ta ta6a baki. "in kai kana sonta, me ya shafi khadija? Yace Allah in bata miki ba, sai in fasa. Ta zaro ido, ni asuwa dan wake a hotel? Yace da gske nakeyi, amma in zaki yarda da wani sharadi guda daya. Tayi 'yar dariya, "inji sharadin. Yace zan turo miki a message. Sai ki bani amsa. Tace, sbikenan ina jira. Ta dauki tiren da abicin karin su, muje mu karya. Ya lura da yadda ta saki ranta daga yin wannan 'yar maganar. Suna karyawa, kowa da tunaninsa. Bayan sun gama ya miqe bari in fita. Tace Allah ya tsare. In ka shigo anjima zanje na wanke gashi na. Yace ki bari na kaiki da dare. Da mimi taji alamun shigar saqo a wayarta, sai ta duba, sai taga MTN ne. Kusan biyar na yamma ya dawo. Tayi kwalliya cikin riga da siket na atamfa. Ta yi masa sannu da zuwa. Ledojin daya shigo dasu ta amsa ta nufi kicin. Ya biyo ta a baya, kin jini shiru ban dawo ba? Tace nasanka da uzuri ai. Daidai lokacin ta bude ledar, kaji ne guda hudu, sai dayar kuma danyen kifi. Ta soma zubawa a freezer, tana cewa farfesun kifi zamu sha anjima kenan? Yace naje sai miki kifin, sai ga wani bawan Allah. Sai kawai ya biya, Kuma yasa asa min kaji. Shiyasa kk ga bana son yin siyayya a unguwar da aka sanni. Sai kawai wani yace zai biya. Tace, arziki ne hakan ma.
[28/09 3:34 pm] Inna: Canjin rayuwa
9⃣4⃣Yace bari inje inyi wanka, zamu fita da ismail. Gabanta ya fadi. Ina kuma zaku je malam? Ya dubeta, gidansu Hanan. Ta rufe freezer, sannan ta biyoshi, to ba ka fadi sharadinka ba. Ko dama kana yi min wasa ne? Yace oh na manta. Ina zuwa. Ya shiga dakinsa, bakin gado ya zauna. Ya rubuta cewa, "in kin yarda in sumbaci bakinki sau daya kullum, to zan haqura da Hanan. Idanu ta zaro, tana qara maimaita abin da ta karanta. Sai taji tanajin kunyar bashi amsa, amma tunda ya ta6a bata amsa da cewa shiru alamu ne, to tayi shiru. Baiga amsa ba. Don haka yayi shirinsa na fita. Ba wani gidansu Hanan zasu ba, don dai ya gwada tane. Rashin ganin amsarta, sai ya zata ko batayi na'am ba, don haka, sai ya shareta. Ita kuwa tanajin fitarsa, amma kunya ta hanata fitowa. Har washegari ba suyi batun ba, duk da sunci abincin dare tare, daren ranar qananan kaya yasa, abinda bata ta6a ganinsa da su ba. Ta kasa daina kallonsa don burgeta da yayi. Sam baiyi niyyar fita ba, kuma dama ya siyo qananan kaya ne don ya burgeta. Amma sai yayi nufin gwada ta. Ya dauki makullin mota zai fita, da sauri tace, ina zaka? Yace, khadija ya kamata ki daina tambayata in zan fita kamar wannan lokacin tunda kinsan komai. Ya kusa kai bakin qofa ta rasa me zatayi, sai kawai ta riqe ciki, "wash Allah na cikin! Ya waiwayo da sauri, yasan cewa qarya tayi, amma sai ya biye mata. Ya riqeta, ya kwantar da ita a cinyarsa, yaja rigarta sama kadan, ya soma yi mata addu'a yana shafa mata a cikin. Lamo tayi cike da burin dama su kwana a haka. Can yace, kinji sauqi? Tace eh, amma kar ka fita. Yace shikenan na bari sai gobe. Tuni Hajiya taba Alhaji shawara akan su miqa ma minista jikansa, sbd dalilinta data fada masa cewa, mutuncinka zai zube a idon jama'a, in kayi la'akari da cewa Abbas shine ubansa. Gashi 'yan jarida sunata bin shari'ar, ana ta yada ku a media. Yace shikenan. Da kansa yaje Abuja, ya kira Abbas yace ya zo ya dauki dansa. Sai dai sati biyu da daukar yaron ya farka da ciwan kunne. Sun kaishi Asibiti sun dubashi, sun basu gado. Kafin yamma ashe ciwon ajali ne, sai kuwa yace ga garinku nan. Hankalin ko wane 6angare ya tasbi. Na'ima kuwa kamar zatayi hauka. Amma dole suka dangana. Allah ya raba musu gardama. Abbas ya tura ma Na'ima saqon sakinta. Bayan watanni kuma sai ta nemi jami'a anan Abuja ta samu ta shiga, amma duk ta rame. Yanxun burinta taga mimi ta nemi gafara. Momy Nafisa kuwa tafi Na'ima da na sani. Hasana da Husaina sun sama mazaje, suna shekararsu ta biyu a jami'ar 'yar adua. Usaina, Abokin yaya mukhtar, kaduna yake. Ita kuma Hasana, Lecturer ne na makarantarsu, amma dan Gusau ne. An basu, amma sai sun qare karatu sannan za'ayi bikin. Shi yasa suka matsawa Hajiya sauda kan don Allah suna son abarsu suje gurin Sis mimi tunda an fada musu unguwar da take. Sun san Gidan ma. Hajiya sauda tace, susa ransu a inuwa daddyn sh ma yace, in ya dawo daga ganin likita a England zamuje gidan gaba dayanmu. Suka dauki murna. Burinsu dai ynxun daddy ya dawo.
9⃣5⃣Mimi kuwa tunda malam ya fita da safe take tunanin wane irin lambon da zatayi in dare yayi don kar ismail ya fita zuwa gidansu Hanan. Wanka tayi, taci kwalliya sosai, da riga da wando masu dame jiki. Ya shigo bayan la'asar. Tana kallonsa yayi ta satar kallonta, lokacin da yakecin abinci. Bayan ya dawo sallar isha'i, yayi kwalliya da qananan kaya, jeans ne baqi sai farar T-shirt mai gajeran hannu. Gaban rigar an rubuta, da harshen turanci cewa ina Alfahari kasancewa ta musulmi. Lokacin itama ta canza kayanta zuwa doguwar riga irin mai rawa dinnan ta kama gashin kanta a tsakiya. Da makullinsa a hannu ya fito, ta dubeshi, "sai ina kuma yau? Jiya ban samu zuwa gurin hanan ba, kuma na fada mata, kinga ai ya dace yau inje ko? Tayi shiru tana kallonshi. Yace sai na dawo, har ya fita daga falon, sai ta bishi, "Malam! Ya tsaya. Sannan ya waiwayo, menene kuma? Tace kalli garinnan hadari ne, kasan kuma ana fara ruwa Nefa zasu dauke wu, kuma inajin tsoro. Ya kalli sararin samaniya, tabbas hadari ne. Yace, zan dawo kafin ruwa ya sakko, wadannan qananan kayan na siyosu ne don ita. Biyu ne kacal, jiya nasa daya, yau ma gashi nasa dayan. In na bari sai gobe me zan sa? Kuma in banje ba, na zama qaramin mutum. Jiya nace, ganinan banzo ba, yauma haka? Ko zamu tare? Shiru tayi masa. Har ya kai gurin motar, guguwar hadarin ta taso. Da sassarfa ta nufeshi, "kazo ka koyamin karatu mana, wai ba ka bani sharadi ba, kuma na Amince? Ya lumshe ido don dadi. Ya juyo, "amma baki fadamin ba, kuma baki turamin message ba. Tace, to ba kace min shiru alamun eh bane? Ya kai hannu ya kamo tafin hannunta, ni kuma sai nayi zaton baki harda bane. Ya fizgo ta da qarfi ta fado qirjinsa, a kunne ya rada mata, tunda kin amince, bari in fara ynxu. Dumin sautin muryarsa a kunnenta, yasa tsigar jikinta tashi. Tafin hannunsa guda biyu yasa, ya lalubo fuskarta. Ya sa bakinsa ya sumbaci le6unanta. Ta zata shi kenan, sai kawai taga ya saka harshensa ya bude mata le6e. Wata kalar sumba yake mata. Kafin minti biyu, ta rasa duk wani kuzarinta. Jin cewa zata zube ne, sai ya jingina ta jikin motar. Saukar ruwan saman bai sashi barinta ba, sai da tace, Ma..lam ru..wa! Cak ya dauketa zuwa cikin falonsu, duk sun jiqe.
9⃣6⃣Kan kujera ya shinfide ta. Sannan yaje ya rufe falon. Har lokacin tananan lamo babu kuzari. Ya dubeta, muryarsa a dushe, "tashi muje ki kwanta. Sai kuma na gobe ko? Ya lura ba zata iya hanzari ba. Don haka ya riqe mata hannu, har bakin qofa ya kaita yace, saida safe. "Lamo tayi akan gado tare da maqale filo, idanunta rufe tana tuna abinda ya faru. Ta kasa tashi ta cire rigarta data soma jiqewa. Shi kansa Malam din juyi kurum yakeyi akan gado. Qarshe dai ya gano mafitarsa daya ce, ya watsa ruwa. Yafi minti biyar ruwan sanyi yana sauka daga tsakiyar kansa zuwa tafin kafarsa. Tsigar jikinsa data tashi ce yasa yasan cewa da akwai matsala. Ya fito kafin yayi wani yunquri har zazza6i ya rufeshi. Singileti da gajeran wando ya saka, sannan ya qudundune da zanin gado. Haka ya kwana. Lura da Mimi tayi yau Malam bai buga mata qofa ba shine yasa data idar da sallah ta nufi dakinsa. Tana turawa ta sameshi yana kakkarwa. Cikin sauri tace, malam lfy? Ta zauna a bakin gadon. Tanason takai hannu ta ta6a wuyansa kuma ta kasa. "In kawo maka magani? Bai iya amsawa ba. Da sauri ta sauka ta dauko panadol da ruwa. Da qyar ya tashi zaune, ya amsa ya sha, sannan yace, "rufamin bargo." ta janyo bargo ta rufa masa, sannan ta zabga tagumi tana yi masa sannu. Kusan minti shabiyar sannan ya ture bargon, zufa ta soma zubo masa. Tace mura ce ko? In dafo maka ruwan zafi? Tea yace eh, bari inyi sallah. Ya shiga bandaki ita kuma ta sauka kicin. Kan sallaya ta sameshi, ta zauna itama ta aje tiren a gabansa, sannan ta tambayeshi, tun yaushe ne bashida lfy? Ya kalli cikin idonta, kece kika zama silar ciwo na. Ta zaro ido, cikin shagwa6a tace, da nayi me? Ya kusanto kunnenta sosai yayi mata rada. Ni dai banji me yace ba, naga dai ta sunne kai a cinya, tare da fadin "kai Malam!" shi kuma yasa dariya. Murmushi nayi don salon soyayyarsu yayi matuqar burgeni. Ranar haka ya yini bai fita ba, wai yana jinya. Ko sallah shine yayi ta musu jam'i. Yayin da mimi tayi ta JI dashi.
[29/09 7:22 am] Inna: Canjin rayuwa
9⃣7⃣Bayan sallar isha'i ne ta leqo don yi masa sai da safe, "yau baki amshi karatun ba" Tace wane karatu? Yace, kin manta ne? Jiya fa kk ce in dinga koya miki karatu. Tace ai jiya ne kawai nace. Yace, naga alamun kin manta da karatun da nike nufi. Zokiji, ta zauna a gabansa yana kan sallaya. Jallabiya ce, a jikinsa mai ruwan qasa, kuma mai gajeran hannu. Ta lura yayi wanka ne bayan fitarta. Ya matso da bakinsa kunnenta, abinda ta zata shine ya fada mata. Ta zata ya manta, domin tana sane ita, kuma tana ra'ayi. Don haka zama ta gyara. Ya tallafe fuskarta suka kalli juna a cikin ido. A hankali yake magana. "INA SONKI KHADIJA..." Wani dadi taji ya rufeta. Har ma ta lumshe ido, lokacin ne ya saukar da la66ansa akan nata. Sai da ta koma tamkar ba tada rai sannan ya barta, don in yace, zai wuce gona da iri ma ya lura ba zata hana ba. Amma yanason koya mata komai daki-daki. Don sai ya raina wayewar da take iqirarin tayi. Domin ya lura batasan komai ba a wannan karatun.
Rana ta uku ne ta soma biya karatun daya koya mata. Don haka a dare na hudu, sai yace, suyi wata sallah raka'a biyu. Bayan sun idar ne, ya dubeta, "kin san sallar nan da mukayi ta mecece?" ta girgiza kai, yace ta ma'aurata ce. Yau karatunmu zai canza salo. Kije kisa turare a duk ga6o6in jikinki kizo. Sam bata iya yi masa gardama ynxun, ko menene dalili? Oho! Tabbas yau sabon darasi ne, sai da karatun yayi nisa, sannan ya rada mata a kunne, "in barki haka ko? Tace, da wuya? Yace ba zan bari kisha wuya ba, sbd naga ke budurwa ce har ynxu. Idanuna ba zasu iya kallonsu ba. Don haka na tura qofa a hankali na fita don barin ma'aurata da sirrinsu. Saidai daga bakin qofa nake jiyo ismail yana karanta addu'ar da mazaje na qwarai sukeyi lokacin kusantar iyalinsu. A fili nace, "an kashe Boss kenan." ban koma dakin ba saida na kusan awa biyu. Lokacin dana leqa ban gansu ba . A raina nace, suna bandaki. Ina nan la6e suka fito. Ya kwantar da ita, shi kuma ya shimfida sallaya. Nace su mimi Amaren asali, kin kai masa mutunci. Shi kuwa sallar godia ce ga Allah yayi. Da asubahi mimi batayi ragwanta ba, tashi tayi ta nufi dakinta don yin sallah. Bayan ta idar, ta kwanta a gadonta, tana tuna abinda ya faru jiya. Gsky Malam ya wuce da tunaninta. Mamakin sa kawai takeyi, dama zata iya tambayarsa, da tace, ina ya koyi salon sa mace ta manta da duniyar da take? Sai dai kashh, tanajin kunyarsa. Barci yayi gaba da ita.
9⃣8⃣Ismail daga masallaci dakinta ya nufa ya kwanta bayanta ya rufesu. Barci sukeyi tamkar wasu taurari. Naso in musu hoto. Sai tara saura ya tashi. Shine ya hada musu abin kari. Lokacin daya dawo saman tana wanka. Ya tsaya jikin bayin, "inzo in taya ki? Tace na gama. Ta fito ta kasa kallonsa. Yana zaune ta gama shiri, harda taya ta gyara gashin kanta. Suka nufi qasa don yin karin kumallo. Cikin sati dai ismail baya nisa, launukan karatun da yake koya ma amaryar tashi kam babu dama. Itama batason yayi nisa, shiyasa ma ta yanke a ranta in zai koma Abuja ba zai barta ba. Haka kuwa hutunsa yana qarewa, tace, Malami na zaka dani? Yace dama izininki zan nema. In kinji zuwa daya kenan. Da ma kema ki soma karatunki. Tace amma zan canza layi. Islamic zan karanta, don sai ynxu na fahimci Musulunci yazo da komai na wayewa.
Sam ismail ya manta da wata zainabu, khadija ce a gabansa, wadda yake kira my Dija. Kafin wani lokaci, mimi tayi kyau, ta goge. Da kanta tace, ismail ashe na jima ina cutarmu. Kuma ka san na dade ina sonka? Yace, na gano haka tun ranar dana saci wayarki na bincika sai naga ashe kece matar dake ta damuna a wtsapp. Tayi dariya, shine baka fadamin ba? Yace gashi ynxun na fada. Yaya Amina kuwa tunda taga Mimi, tasan an kashe boss, domin ta ciko masha Allahu. Sam Na'ima basu ta6a haduwa da mimi ba, ko don ba department daya suke ba, oho. Lokacin da Alhaji ya dawo daga ingila, sai ya samu labarin Mimi suna Abuja kuma tana karatu. Yaji dadin haka, kuma ya jinjina wa malam ismail. Shima ismail ynxun abu daya ya rage masa, shine ya sada Mimi da iyayenta. Amma ya bari sai sunje katsina. Cikin haka, Mimi ta soma laulayi. Ta ga gata ganin idonta. Har da kanta ta darsa a ranta cewa data bar ismail, da ta tafka asarar da ba zata iya maida ta ba. Kullum tayi sallah, sai ta godewa Allah, ta kuma godewa mahaifinta daya za6a mata ismail, ta samu CANJIN RAYUWA.
9⃣9⃣Cikinta wata bakwai sukazo katsina, domin za'a bude makarantarsa, kuma zaya kai Mimi gidansu. Bayan an gama kai kawon bude makaranta, da sati daya, tuni ma an soma karantarwa. Ya danqa komai gurin wani bawan Allah dake nan unguwarsu malam Aminu. Shine ma ya kawo shi, yace tunda Ismail baya zama. Sai ismail ya amince, don yasan malam ba zai kawo musu bara gurbi ba. Kuma ya zuba qwararrun malamai a makarantar. Safiyar juma'a, Mimi tana kwance kan cinyar ismail, yace muje in taimaka miki kiyi wanka , zamu fita. Tace zuwa ina malamina? Yace inda muka kwana biyu bamuje ba. Kinsan falalar zumunci. Gashi ke nake jira ki haihu, zamu tafi Madina don neman digiri dina na biyu. Bayan ta fito tana zaune, ya shafa mata mai, sannan yace, wane kaya zamu sa? Tace ka san dai yau juma'a, kuma kamar yadda muka tsara ma kanmu rana ce ta saka kayanmu na al'ada. Dubamin shadda ko atamfa. Sabbin riga da zani ya fito mata dasu na super mai kalar popple, sai ratsin baqi, har da sarqa da dan kunne masu kyau yasa mata. Shima ya shirya tsaf, cikin shadda sabuwa. Tasha hijabi da niqabi, suka shiga sabuwar motar da yayi kakara, ya canza. Saida sukayi tsarabar kayan sha, dana zaqi, sannan ya tuqa su zuwa unguwar. Sam Mimi bata fahimci inda suka dosa ba, sakamakon an samu canje-canjen gine-gine. Wani gurin ma babu gini da. Ko gidansu, saida suka shiga ta ganeshi, sakamakon an canza gaban. Ta kalli ismail, "yaya zaka yi min haka? Gsky mu juya, tunda ba wanda ya ganmu. Yace ni ba wannan ya dameni ba. Baki lura da yawan motocin da ke harabar gidannan ba? Sannan ga mutane can ansa rumfa. Da alamun anayin wani abu agidannan. Kai tsaye tace, Allah dai yasa ba daddynh bane ya rasu. Sai kuma ta bude qofar da sauri, ta fito. Shima ya fito, ya riqeta. Yi sannu My Dija. Babu abinda ya faru, sai alheri. Alhajin ne suka fito daga falonsa tare da qaninsa kawu shafi'u da kuma su Alh kabiru, da Alh isah.
[29/09 8:26 am] Inna: Canjin rayuwa
1⃣0⃣0⃣Ismail yace, to ga Alhajin nan ma. Da sauri ta nufesu tana fadin daddynah! Cak ya tsaya domin ko cikin mjrya dubu zai fidda ta Miminsa, ko da zai shekara dubu bai ganta ba. Cikin sauri yaje ya daga niqaabinta. Kamar yadda ya zata Miminsa ce. Yace, uwata. Idanunta suka kawo hawaye, na'am daddy. Sai ya rungume ta, idanunsa suna masu kawo hawayen farin ciki. Ya kalli Alhaji kabiru. "yanxun fa mukeyin maganarta. Ance min kunzo gari. Ina jira a gama hayaniyar biki, muje gidan. Tace daddy wa ke aure? Yace 'yan biyu, sai mukhtar. Tace nazo a sa'a. Ta kalli mijinta wanda ke kallonsu cikin tausayi, tace Malam baka gaida su daddy ba. Ya qaraso tare da cewa, na jira ne ku numfasa. Nan suka gaisa suka nufi ciki. Shi dai Alhaji nan ya juya shima yabar abokansa da qaninsa. Falonsa ya yace ismail ya shiga. Ita kuma ta rufe niqabinta. Alhajin ya tasa ta suka nufi ciki. Hajiya sauda tana gaisawa da wasu baqi da suka shigo, Alhajin ga shigo yana kwada mata kira, tace Alhajina ho! Yau dai gidanmu da jama'a... Ya katseta, baquwa kikayi. Ta kalli Mimi fuska rufe, tace to ta shigo daga ina? Mimi taje ta rungume mahaiyarta. Sannan ta daga niqabi. Da sauri tace, Mimi ce! Nan dai akayi ta murnar ganin Mimi. Amare suna gidan mai musu gyaran jiki. Da yake sai washegari Asabar ne za'a daura auren. Hajiya da kanta ta kirasu ta fada musu, sai gasu. Murna tamkar zu cinye ta. An kawo mata wannan da wancan duk an jibge mata, sai dai hankalinta yana can gurin mijinta. Hajiya sauda tasa ta gaba, tana cewa, in bakison wannan me zakici? Saboda kowa yaga tsohon cikinta. Ta kalli Hasana, "wai ina Malam ne, ko suna gare da daddy? Hajiya sauda tayi murmushi, yana tare dasu daddynku, harda sy yayanku. Sannan Mimi ta soma tsakurar abincin don batajin yunwa, kuma ta saba ci da Mijinta.
1⃣0⃣1⃣Su Hajiya Binta suka iso da yaranta. Ita ma rungume Mimi tayi don murna. Kowa sai mamakin ganinta yakeyi. 'yan uwan hajiya sauda da dama basu san Mimi ba , sunanta sukeji, yau sai gata gasu. Hatta kakarta saida aka nuna mata. Yau dai ta gane 'yan uwa dadi garesu. Ashe ita 'yar dangi ce, gaba da baya haka? Daddy ma sai kiranta yakeyi yana tambayarta ana bata duk abinda takeso ko? Dariya takeyi, sannan tace, ana bani daddy. Suna dakin daddy ita da Amaren, sbd ko ina mutane sun cika. Ta ce ku tashi muje gurin gyaran jikin, nima za ayi min. Ta ciro waya, "bari in fadama Malam zamu fita.Ta kira wayarsa, dai dai lokacin da ya daga Hajiya sauda ta shigo, tace, musu su koma gurin gyaran jikin. Sai taji mimi tace, Malamina, na zata zanga Miss call dinka? Ka shareni ko? Cikin sigar shagwa6a ta fada. Yace kinsan dai ko a mafarki My Dija ba zan shareki ba. Na barki ne ku walwala da 'gan uwanki. Tace kana inane ynxun? Yace inason zan tafi masallaci, amma sai na koma gida na dauki takardar budubar dana rubuta. In zan dawo zan biya in dauko yaya Amina. Tace da ka kyauta min. Ta zo dasu Ummi, kaji My Malam? Yace zan fada mata. Kina son wani abu ne daga gida? Tace, illa mai da hoda na, sai turare. Yace shikenan. Tace zamu fita da Amare. Yace zuwa ina? Tace inda za'a yi musu kwalliya. Take yaji bari ya gwada ta. Sai yace, a'a ki zauna ki huta abinki. Bata zata ba. Don haka ta danyi dim, sannan tace, shikenan Malam, sai kunzo din. Sosai ta burgeshi, ya san ko ina zatayi masa biyayya. Sai yace, Dijana kuje kawai, sai kun dawo. Tace Allah Malam in baka so, ba zanje ba. Yace, na tsokane ki ne kawai. Basu Hasana ba, hatta mahaifiyarta saida Mimi ta burgeta. Lallai Malam ismail ya ciri tuta. Hajiya sauda ta dauko zanin anko, da wasu sufofi guda uku, da lesuka masu tsada, ta kira telan su, ta bashi tare da cewa gobe takeson su, amma anko yau za'a dinka. Tela yace, an gama! Don yasan Hajiya akwai sauke kudin dinki. Haka bayan sun dawo gyaran jikin ne Hajiya sauda ta zube Hijabai kan gado sabbi sun kai kala goma, tace, Mimi ta za6a in ma tana sonsu duka ta kwashe, ga takalma da jakarsu. Mimi tace, Hajiya kin siyane dama kin ajiye? Tace a'a saida sj mukeyi. Su Hasana suke kaiwa makaranta. Daga baya kuma sai muka kama shago. Odarsu ma mukeyi yanxun daga dubai da china. Mimi ta za6a, ta kuma za6arma yaya Amina, itama harda jaka da takalmi.
1⃣0⃣2⃣Qarfe uku akayi kamun Amare, lokacin ne kuma za'a saka anko. Mimi tayi kyau matuqa, duk da cikinta yasa tayi qiba. Kwalliyarta tasa ta saje da amare, duk da itama har ynxun da 6ur6ushin amarci, tunda bata dade da fara amarcin ba. Jeren kumbo ne akayi. Wannan karon ne na farko da Mimi taga irin bikin nan, kuma yayi matuqar burgeta. Yaya Amina sun iso da yaranta sunga tarba gurin Hajiya da ita kanta Hajiyar. Sunci, sunsha, sannan aka kwashe su a mota zuwa gidansu yaya Abba inda acan ake kamu din. Sai dare sannan Ismail ya kira Mimi yace, su yaya Amina su fito ya maida su gida. Tace abar Ummi, tunda zasu dawo gobe, sbd gobe ne daurin aure. Hajiya ta had musu kayan biki. Mimi ce ta raka su har gurin mijinta. Sun shiga mota, shi kuma ya fito, suka ke6e da Mimi. Yace, ke kam nasan sai an gama biki ko? Tace, sai yadda kace. In kuma kafison na koma, sai mu tafi, ka kawoni da safe. Ya kai hannu ya kama nata, ki zauna kuyi bikinku. Daddy ma dazu yace min, wai inyi haquri sai an gama biki, in barki. Tace ai yadda kasan yana tsoron kar in gudu, ba ayin awa daga bai kira layina ba. Ismail yayi dariya, gurina ya amshi lambar. Ya murza hannunta, yau zanyi kewarku, da dana. Tace mu ma haka. Har ya kai mota zai shiga, ta ce Malam! Ya dawo, tayi qasa da murya saitin kunnensa, "don Allah kar kayi tunanin kowa sai nawa. Ya shafi kumatunta. Yace ai kinyi kane-kane a zuciyar nan. Baki bar gurin da zata tuna wata ba. Zan kiraki an jima, in bakiyi barci ba. Ta shafi kumatunsa, zan jira ka. Saida motarsa ta fice, sannan Mimi ta juya zata koma cikin gida. Ashe duk daddy yana kallonsu daga inda yake zaune. Sai ya fito ya kira Mimi, Uwata! Da sauri ta nufeshi tace, ina ka 6oye daddynh, tun dazu banganka ba, sai dai waya. Yace muna ta fama da jama'a Uwata. Naga mijinki ya tafi. Tace yayarsa ce da yaranta. Yace naji dadin ganin yadda kuke da mijinki, kina sonshi, kuma naji dadin ganin yadda kk samu canjin rayuwa. Tace daddy kullum ina saka cikin addu'a Allahvya saka maka da Aljannarsa, sbd kalar mijin daka za6amin. Yana sona sosai daddy. Kuma shine ya nuna min hanyar wuta data aljanna. Daddy ka yafemin laifukan dan yi mak.
[29/09 2:42 pm] Inna: Canjin rayuwa
1⃣0⃣3⃣Yace, Mimi ba kiyi laifi ba, daidai kk yi da kk gudu. Kinga momynki a bikin nan? Mimi tace, Inason in tambaya, amma sai abin ya shigemin. Ya bata labarin komai. Yace, ynxun haka Na'ima tananan gida. Momyn ku suna bikin qaninta shiyasa bata zo ba, amma Na'ima kunyar fita takeyi. Ko makaranta sai dai tasa hijabi. Mimi tayi ta mamakin Abbas, tace ban zaci zaiyi haka ba daddy. Shima yace, nima ban zaci basuda tarbiyya ba, har na takura rayuwarki. Ai nine silan komai. Kije ki kwanta. Zamuyi magana, sai an watse biki. Gado daya suka kwanta da Hajiya sauda. Mimi tasha labarinsu Na'ima. Hajiya sauda tace, ai gara wahalar da kk sha, da ace ke kk auri Abbas. Daddynku fa har cewa yai gara da Allah yada kk bijire masa. Mimi tace, ni ko inacan ina dana sanin bijire masa. Kuma lokacin don dai Nomy Nafisa tace min duk abinda Za'ayi kar in yarda, wai daddy yace in naqi yarda zaya haqura. Sai daga baya na gane kamar da makirci. Nan dai Mimi taba Hajiya sauda labarin komai. Hajiya tace, saida Hajiya Binta tayi zancen nan, amma nace kar a zargeta, dama 'yarta take son takai gidan. To ai in baka da haqqin mutum, gashinan yadda suka kwashe. Sun raba dare, suna hira kafin sukayi varci. Washe gari daurin aure, ansha sha'ani. Tela ya kawo dinkunan Mimi, sai shiga takeyi tana fita. Yaya Amina sunzo harda Rabi'a. Mahmud ya kawota don shima yayi mota. Sun ga kula, kuma sun kwashi kayan walima. Shi dai Ismail sai kallon Mimi yake, sbd kyawun data qara. Ta jashi ciki, wai ya gaida su kakarta, da kuma dangin mamanta. Inna sa'ade tace wannan Malamin nan bane shaikh Ismail bin Abdurrahman? Mimi tace, shine. "Dama shine mai gidanki? Mimi cike da alfahari tace shine. Sukayi ta sa masa albarka. Suna fadin shirye-shiryensa da suke kallo, da kuma irin qaruwar da sukeyi.
1⃣0⃣4⃣Haka da suka ratso ta falon mata, sai gaida shi akeyi irin gaisjwar ban girma, wadda mazoya suke yiwa wanda suke so. Haka biki ya tashi, sbd Amare sunada nisa. Mimi taso zuwa kai Amare. Daddy yace, ki bari ki sauka lfy, sai kije ma kowa. Tace to shikenan, ba don ranta yaso ba. Ta haqura don dan zaman nan ta san dadin 'yan uwa. Washegari duk mutane 'yan biki suna ta tafiya, don haka Mimi sake kwana tayi. Hajiya Binta da zasu wuce tace ma Mimi, sai kin haihu kuma zamu zo. Har mota mimi ta rakasu.
Yau dai Alhaji da Hajiya da kuma Mimi sun zauna sun sha labari, inda Mimi ta basu labarin bayan rabuwa, suma suka bata. Kuma taji mamakin yadda Alhaji yabi diddigin inda suke. Ashe shine ma ya ba ismail gidannan. Kuma sai yau Alhaji ya gano Nafisa ta hada komai, don mimi ta fada masa har yadda tasa ta ta turo masa text. Ransa ya 6aci, kuma yace, sai yaci mata mutunci. Hajiya sauda tace, a'a karka yi mata komai. Banqi ka fada mata ba, don tasan ka sani. Amma ai Allah ya gama nuna mata sakamakon maci amana. Mimi tace, hakane daddy. Take ta kira ismail, ta fada masa yazo, shima yasha labari. Kuma sai ranar yaji dalilin daddy na sharesu, kuma ya gamsu. Domin in har Mimi tana cikin gatanta ba zata juyu agareshi ba. Sun bar gidan goman dare. Bayan motar su shaqe da abubuwan biki. Suna kwance sunyi kewar juna tace, Malamina yaushe zamu koma Abuja? Yace sauran kwana uku, kin manta ko? Tace na manta sosai kuwa. Ai naji dadin zuwa gida lokacin bakinnan . Naga 'yan uwa, sun ganni. Ta rungumo shi, Allah barni da kai har abada. Yace, Amin tace, kayimin alqawarin cewa ba zakayi min kishiya ba. Yace, Dija banida ra'ayi, amma bansan qaddarata ba. Ina son kema kimin alqawari, in qara aure yana cikin qaddarata ba zaki juyamin baya ba. Ta qanqameshi, "nayi maka, amma zan shiga wani mawuyacin hali, sbd ina tsananin sonka.
[30/09 6:43 am] Inna: Canjin rayuwa
1⃣0⃣5⃣Washegari sunyi girke-girke sbd ziyarar dasu daddy zasu kawo musu, da su yaya Abba da sauran qannenta. Yaya Amina da Rabi'a sune suka taya su. Gidan tamkar biki, haka ya cika. Daddy yaba Mimi kyaututtuka sannan kuma ya fada musu yaba sauran 'ya'yansa irinsu, sakamakon wa'azin da yaji a wani kaset daya kalla na Ismail, mai taken yin adalci ga iyali. Sannan yayi wa ismail kyautar qaton fili, yace ya gina irin makarantar da yakeso. Take ya yanke shawarar zai gina jami'a ta musulunci, duk da ya san ba abune mai sauqi ba, amma zaiyi hakan. Su Malam Aminu sun samu kyaututtuka. Shi kujerar makka, mahmud gida. Sunkai har dare a gidan, sannan suka tafi. Ranar da zasu koma Abuja, sunzo sallama daddy yaba su makullin wani gidansa dake Asokoro, yace su zauna har sai ranar da suka gaji suka tashi don kansu. Ranar wata talata, Mimi ta tashi da naquda, ismail bai fadama kowa ba, saida ta haihu. Kuma abin da ya burge malaman asibitin mai zaman kansa, yadda ismail ya shiga har cikin dakin haihuwar yana shafa kan matarsa tare da lallashi da addu'o'i har ta haifi santalelen yaron su mai kama da su. Hajiya sauda ya soma fadawa, sai daddy da kuma su yaya Amina. Duk da sun yanke cewa gida zata dawo, saida su Hajiya sauda sukaje Asibitin da take a Abuja. Shi kansa Alhajin saida yazo. Momy Nafisa tazo asibitin, sai kunyar Mimi takeji, sbd Alhaji yazo ya warwareta, kuma ya fada mata cewa taci darajar sauda, sbd itace tace, in barki da ishararki. Ranar ta kira sauda tana bata haquri. To yau kam ta yarda cewa, duk wanda yace, tukunyar wani ba zata tafasa ba, tashi ko dumi tabar yi. Yadda taga Mimi, Mijinta yana ji da ita, ga daukaka, ga kuma soyayyar da take yiwa mahaifinta ta dawo sabuwa.
A katsina gidan suna ya cika. Dan yaci suna Aminullah, sunan Malam Aminu, Ismail yasa, domin ya nuna masa qauna. Hasana da Usaina sunzo. Abin sha'awa suke ta kula da 'yan suna. Gurin bada abin tsaraba in mutane zasu tafi, sun samu alheri. Malam Aminu kuwa yaji dadi sosai, wannan kara da ismail yayi masa. 'yan gidan su ma sunzo. Zo kaga idanu gurin fatu, sun ga abin duniya, abinci kuwa sunci sun diba a leda, duk da Mimi tasa anyi musu kyaututtuka na musamman matsayin dangin masoyin mijinta.
1⃣0⃣6⃣Kwanaki arba'in sukayi, duk sati Malam ke zuwa duba su. Abin da yaba Mimi mamaki ta kuma qara miqa masa wuya, yadda shine ya kawo mata abubuwan da zata yi amfani dasu don gyaran jikinta, sannan ya fada mata abubuwan da zata yawaita ci. Yaso sunayin arba'in su dawo, amma tace yayi haquri sudan zaga suga 'yan uwa. Da gusau suka soma (har naji kamar in bisu inje gurin tawa Baida'u Gada) sannan kaduna, duk kwana dai-dai sukayi, sannan suka dawo, sukaje Dangin Hajiya sauda. Sun zaga acan kwanansu biyu. Duk da ba masu kudi bane , taga soyayya irin na dangin uwa. Sannan sukaje masari suka kwana daya, daga nan sai Malumfashi gurin Hajiya Binta. Bayan sun dawo ne kuma suka soma shirin komawa gida Abuja. Har da Hajiya sauda da yaya Amina a 'yan rakiya. Qannenta kuwa su Hasina dasu husna, harda kuka don sun saba da Al'amin. Shi kansa Alhaji yayi keawar dan jikan nasa. Ranar 'yan rakiya suka dawo suka barsu da kayan arzikin da suka rakasu da shi.
Qarfe taran dare, Mimi cikin kayan varci, tana ta lila Al'amin a gadonsa ya soma varci, sai taji qamshin turaren masoyinta, kafin ta waigo sai taji hannuwansa a jafadarta. Cikin murmushi ta juyo, "Malamina ka shigo tun yaushe? Yace baki ganni cikin shirin varci ba? Tun lokacin da kk wanka, na san ni ake yiwa wankan. Don haka nace, kema bari inje in miki. Suka sa dariya. Ya tsugunna ya sumbaci goshin dan nasu, sannan yayi masa addu'a. "Muje ki amshi darasin da kk tara ma kanki." Cikin shagwa6a tace, Malam mu bar karatunnan sai gobe. Ya dora yatsansa akan le6unanta, tare da fadin "shhhhh, wannan ba halinki bane. Na shaide ki baki cikin mata masu juya baya. Ya kai bakinsa kunnenta yayi mata rada, suka tallafe juna zuwa gadon aurensu. Na juya zugum-zugum don in anyi radan nan inajin haushi banjin me suke fadi.
[01/10 8:04 am] Inna: Canjin rayuwa
1⃣0⃣7⃣Watan Al'amin uku, yaro mai cike da kuzari da lfy. Sukazo katsina suka sallami dangi suka wuce Madina don yin digiri dinsa na biyu. Yaso Mahmud ya taho, amma shi yace sai nan gaba. Don haka komai na game da makarantarsa ya barma Mahmud. Watansu uku da zuwa, Azumi gazo, don haka suka dawo gida sukayi Azumi, sbd tafsir din da ismail keyi. Bayan sallah suka koma. Lokacin aikin Hajji sukayi shiri da dansu don yin aikin Hajji. Mimi ta zazzo umura, amma bata ta6a aikin Hajji ba. Koda yake umura dinma, lokacin zuwa kawai take, amma batasan me zatayi ba sai siyayya. Rayuwarsu irin ta larabawa suke kwaikwayo gurin soyayya. Don haka ko yaushe suna nane da juna. A makka ne sun fito harami zasu je masaukinsu, Ismail dauke da Al'amin a kafada sanye cikin jallabiyya fara sol, Mimi cikin baqar doguwar riga ta rufe fuskarta da niqabi tana rataye da jakar tarkacen Al'amin, tana kuma maqale da hannun mijinta suna tafe kamar taurari. Sai kawai ta hango Na'ima. Tace, Malam ga Na'ima suka tsaya a gabanta. Zata kauce, Mimi ta daga niqabinta, tace Na'ima. Wata kunya ce ta rufeta, sai kuma ta rungume Mimi. Mimi tace keda wa kuka zo? Tace nida Momy. Masaukinmu zan koma wancan Hotel din. Mimi tace, muma nan muka sauka. Ta kalli Malam ta gaida shi, sannan suka wuce zuwa masaukin.
Momy Nafisa taji kunyar ganinsu, nan suka gaisa ta dauki Al'amin tana fadin yaro yayi girma. Na'ima bata tsaya 6ata lokaci ba ta shiga neman gafarar Mimi cikin kuka. Itama Momy sai tayi narai-narai tana roqon gafara. Mimi ta rungume Na'ima, tace babu komai, komai ya wuce, nima ku ya feni. Ismail yayi musu nasiha tare da nuna musu illar hakan. Sukayi godiya. Anan ne ma Na'ima tace, ai Malam ina ganinka a makarantarmu, 6oyewa nakeyi. Bayan ya dauki Al'amin ne yace bari suyi gaba kafin ta shigo. Na'ima tace, sis Mimi sai kin qara riqe wuta, sbd 'yan Makarantarmu suna bala'in son Mijinki, don dai dai ne yarinyar da bata labarinsa. Mimi tace, sunyi au gama. Momy tace ke Na'ima karki tada mata hankali, gashi kun saje da larabawa. Mimi tace hakane momy, gsky ta fada, kiran wayarshi da mata keyi ma kadai in nace zan damu, sai jini na ya hau. Sauqi na basa gabansa. Ta jima sannan ta koma dakinsu.
1⃣0⃣8⃣Duk lokacin da suka samu wani dan hutu ko na sati daya ne sai sunje Nigeria. Hakanan daddy yakan nuqo gari yazo ya gansu. Bayan sun shiga shekara ta biyu, lokacin Al'amin yana da wata takwas yana gudunsa ko ina, sunzo. Da zasu koma, Ismail yace, Dija ina ganin ya kamata mubar Al'amin gurin su Hajiya, don mu samo Rumaisarmu ko? Ta kalli dan nata dake varci tace Allah sarki Aminullah, har ya bani tausayi. Zanyi kewarsa. Yace ko yaya kk gani? Tace duk yadda kace babban Malami. Alhaji Bashir tamkar ya goya su Mimi don murna sun bar masa jikan daya shiga ransa. Saidai bai nuna ba don tsoron kar yayi masa irin na Uwarsa. Shekara kwana ce inda rayuwa, domin su Mimi sun dawo gida bayan Ismail ya samu shaidarsa mai kyau, ta samun digirinsa na biyu. Ya iso cike da burika, musamman gina jami'ar Musulunci a katsina. Sun gyara gidansu sosai. Da yake Mimi ma bata zauna ba, a Nadina taci gaba da neman ilimin addini, sai Makarantar nan tasu ta koma qarqashin kulawarta. Zumunci kuwa ita da Rabi'a, tamkar 'yan uwa. Ta sa Ismail ya gyarawa su yaya Amina gida. Ita kuma ta bata jari. Suna yin taimako sosai, duk na kusa da maqota sun shaida haka. Rashin samun cikinta yana damunta, da tace suje Asibiti yace a'a su sake jira, tunda wancan babu inda sukaje. Kwana biyu da yin haka ta soma mura. Yace shikenan gashinan Allah ya bamu. Tace ba ciki bane. Yace na Al'amin daga irin murannan ne. Haka kuwa da suka je asibiti sati shida. Wata Alhamis mimi ta gama hada masa kayan buda baki, sai ta nufi dakinta tace kaci zan dan watsa ruwa Malam, banason ina kusa da kai bana qamshi. Yace sai kin dawo dalibar Malam. Tana barin gurin message na shigowa, kamar yadda ya zata zainabu ce. Ya bude ya karanta. Tunda suka dawo, kullum sai samun saqonta tana fada masa halin da take ciki na sonshi. Kuma in zata mutu babu aure, to kuwa zata jirashi. Yayi shiru yana tunani. Shi gsky ynxu babu ko 6ur6ushin son Zainabu a ransa. Sai dai tausayinta. A fili yace bari dai mai ni din tazo muji ko zata lallasu.
[01/10 8:05 am] Inna: Canjin rayuwa
1⃣0⃣9⃣Bai munafunceta ba ya nuna mata komai. Shiru tayi ta rasa me zata ce. Yace, me kk gani? Ta ban tausayi ne. Sai kurum Mimi ta miqe zata wuce, ya janyo ta jikinsa. "Wlh ba sonta nakeyi ba kinsan dai baki bina bashin rantsuwa. Tace shikenan duk wadda ta baka tausayi sai ka aureta har mu zama mu hudu? Yace shikenan batun ya wuce. Sun zanta da Mahmud akan batun zainabu, Mahmud yace, inda hali a duba yarinyarnan. Tazo gurina yafi sau talatin. Ismail yace to nidai kasan mijin tace ne, sbd banason damuwar matata, kamar yadda batason tawa. Mahmud yace nidai naga wata nan kusa dasu yaya Amina. Kuma dama inason fada maka ne, sai in yiwa su Malam magana suje su nemo min izini. Ai kaima Ismail kayi kuskure yaya zaka nemi shawarar mace, akan zakayi mata kishiya? Ai bari zakayi sai zance yayi nisa sannan ka fada mata. Shiyasa dana fada ma Rabi'a naga wadda nakeso, tayi fushinta ta gama. Ismail ya samu yaya Amina da batun, tace duk da batason ayiwa Mimi kishiya , tana tausayin zainabu. Wani dare ya yanke shawarar ziyartar Zainabu don bata shawarar ta nemi miji tayi aure. Sai dai ya kasa fada mata hakan lokacin da ta fito ta ganshi ta kuma saki kuka. Duk ta rame, tace Malam na sani ko yaushe Allah zai turomin kai. Domin a bakinka naji addu'ar daya kamata bawa yayi in yana neman buqata gurin Allah, litinin da Alhamis in nakai azumi, kafin nasha ruwa, ina fada ma Allah kaine nakeson Allah ya bani. Duk tsawon shekarunnan ban cirema raina ba. Ismail ya kasa magana, sai dai sun rabu da alqawarin zai dawo, don jikinsa ya mutu da kalaman zainabu. Shawarar mahmud itace abinyi. Ya koma gida ya kasa sukuni. Mimi kuma ta tsareshi don son jin dalili. Yace in kinji ma bashida amfani, don haushi zakiji. Ta nace, shi kuma ya fada mata komai. Ranar ce ta farko da suka raba daki tunda suka hada, saidai in daya baya gidan. Cijewa Ismail yayi baije lallashi ba don yasan ba zata saurareshi ba. Ita kam hakan ya sata zaton ko ismail ya daina yayinta. Kwana tayi kuka, sannan tunda duku-duku taja motarta ta nufi gidan Ubanta. Yaji fitarta daya duba sai yaga tabar Al'amin. Shine yayi masa shirin makaranta, ya kaishi. Daga can ya samu malam Aminu suka zanta akan batun zainabu, shima Malam ya amince da Ismail ya auri zainabu, sbd ubanta yazo gurinsa kusan sau biyar. Yace, suje aji sadaki, ya bada, a daura kawai ta tare. Daganan sai ya wuce gidansu gimbiyar sa.
1⃣1⃣0⃣Sun gaisa da Alhaji bayn sun shiga falon baqi. Alhaji yace, saiga mutuniyar fuska kumbure kuma har ynxun sai kuka taqi cewa komai. Ismail ya koro ma Alhaji komai. Alhaji yayi murmushi, "Ni dama nasan tatsuniyar gizo bata wuce ta qoqi. Mata sun tsani kishiya, kuma bayan da biyu ma akace mu fara, sannan uku ko hudu. Ita dama tana auren Malami zata ce ita daya zata zauna? Ismail yace nida banida ra'ayin sake aurema daddy, amma in yana cikin qaddara ta dole nayi. Yace karka damu, kaidai kayi qoqarin adalci, Mahaifiyarta tanada abin ce mata, kuma zata dawo anjima. Ko da Alhaji ya fadama Hajiya sauda maqasudin zuwan Mimi gida, a gaban Mimin Hajiya sauda tace haka ne? Mimi tace hakane. Ran Hajiya sauda ya 6aci, tace dama kina zaton mijinki ya zauna dake daya ne har abada? Ta dago ido ta kalli Hajiyar, "ya fa yi alqawarin ba zaimin kishiya ba, Hajiya sauda tace ga mahaifinki nan zaune, ni ma yayi min alqawarin ba zai min kishiya ba, amma yau kishiyoyi nawa gareni? Mimi tayi shiru. Hajiya ta sake cewa, inace harda ke kun hada baki aka auro miki Momynki Nafisa? Kin manta duk da wannan? To inaso ki sani, mata da yawa suna hana mazajensu aure, a qarshe sai mazajen suje suna bin matan banza. Sannan wasu suna hana mazan su aure a qarshe sai kuma su mutu ayi auren. Banda ma wannan qannai nawa gareki mata? Ce miki akayi ko wacce an bugo mata mijinta ne? In kin hana a auri qanwar wasu waccan ta hana a auri qanwarki, shikenan sai su tabbata babu aure? Inaso ki koma gidanki, ki nutsu ki ba mijinki qwarin gwiwa yayi muku adalci. Karki canza daga son da kk masa. Ki qara gurin kyautata masa. Ki riqe amanarsa, ki zama mai haquri da kuma ki hada da addu'a. In dai ni na haifeki, to karki kuma zuwa gidannan da sunan yaji. Ku kashe, ku rufe keda mijinki. Alhaji ya dubeta, "Mahaifiyarki ta gama fada miki komai. Ni dai zan qara miki da cewa kiyi haquri. Haka mimi ta koma gidanta cikin damuwa, sai dai zantukan mahaifiyarta sun isheta tunani. Ko da ya dawo lallashin ta yayi, tare da nuna mata cewa ba don bai sonta bane. Har zuwa ranar asabar din da aka daura auren, sama-sama suke, sai dai Mimi tace ya nemi gurin da zai saka matarsa, ba zata zauna tare da ita ba. Baiji komai ba, dama ya kama gida, unguwarsu Mahmud, can ya sata. Ranar farkonsu ya tausaya ma Zainabu sbd irin son da take masa. Ita kuwa Mimi kwana tayi kuka, ta san cewa ynxu sun zama su biyu masu shi. Daga masallanci, gidan ya wuto. Tana varci shima ya kwanta kusa da ita. Data farka ta ganshi, sai kawai ta fita ta koma kicin tana hada abin kari. Sai da ta gama soya dankali, da qwai da sauransu, sai taga ya dauki kwando ya jera, yace kiyi wani, wannan zan tafi dashi. Ta daga murya sbd me? Yace sbd Allah da kuma cewa kin isa. Ya debo dankali, muyi in tayaki. Banason ki zubar da kanki gurin zainabu, don a komai bata kaiki ba. Inason kiyi zama da ita na adalci, ki nuna mata girma. Kar kiyi wasa da muqaminki na Uwar gida.
[01/10 8:09 am] Inna: Canjin rayuwa
1⃣1⃣1⃣Zantukansa ta hada dana Mahaifiyarta data sake kiranta a waya ta nana ta mata. Dole ta haqura, kuma ta yarda cewa, mijinta fa ba laifi yayi ba don ya qara aure. Sunna ya raya. Ba taji haushin kanta ba, sai ranar daya kawo mata zainabu, gaba daya sai taji ba taga abin kishi ba. Ita kuwa Zainabu sai taji tana shakkar Mimi. Ga wani qwarjini da Mimin tayi mata, har ita kanta Mimin ta lurabda haka. Don haka sai ita Mimin tace, kar fa kiji komai, nan gidan mijinki ne. Zainabu ta yarda Allah ne kawai ya bata Malam, domin mai kamar Mimi ba zai kalleta ba.
Mimi ta sauka, wannan ma Namiji ne, sai yaci sunan Alhaji. An sha suna, sannan itama zainabu ta kama nata laulayin. Lokacin Ismail baya qasa. Sun tafi Africa ta kudu. Shine ya kira Mimi ya fada mata cewa Zainabu babu lafiya, don Allah ta dubata. Mimi ta tausaya mata halin da ta sameta. Ita ce takai ta Asibiti. Bayan gwaje-gwaje an gano ciki wata biyu. Mimi ta wuce da ita Gidanta kafin mijin ya dawo. Dakin su Al'amin ta sauketa. Da yake ynxu tanada masu aiki, yarinya da tsohuwa, sannan sunada Mai gadi. Mimi tsakani da Allah take kula da Zainabu, kwana biyar ya dawo, samun Zainabu danyayi gurin Mimi tana samun kula, sai ya sake daga darajar Mimi. Harma ya fada mata cewa, My Dija, na jima da yarda cewa ko dabba na daure zaki kula da ita, bare Mutum. Hakan ya qara mata qaimi gurin zama zama da kishiyarta lfy. Zainabu ta haihu ta samu 'ya mace. Ga mamakin Mimi sai Zainabu tace ya sama 'yar sunan Mimi wato Khadija. 'ya kuwa taga kaya gurin Mimi.
1⃣1⃣2⃣Mimi cikin motarta tare da yaranta, a Abuja sunje bikin Na'ima ne ta auri wani maqwafcinsu da matarsa ta rasu gurin haihuwar danta na biyu. Bayan biki ya watse da ranar da zata tafi tace, bata barin Abuja, saita nemo mina qawarta. Gidan iyayen mina taje neman labarin. Har gidanta qanin mina ya raka Mimi anan cikin Abuja. Sun rungume juna sunata murna, kafin suka 6arke da labari. Mina tasha mamakin jin cewa, sheikh Ismail Abdurrahman shine Malaminta da mahaifinta ya bata. Tace, ta san shi domin yana daya daga cikin malaman da take nutsuwa da wa'azin su. Sai mallon mimi takeyi tana Mamakin ta. Tace dubeki kamar matar shugaban qasa, wai matar Malami. Mimi tayi dariya, tace kinsan Allah duk wadda mijinta ba Malami bane, ina mai jajanta mata, domin ta rasa abubuwa da dama. Me zanyi da wani shugaban qasa da ba zai samu lokacina ba sai na mutan qasa? Barni da mijina mai kasheni da kalolin soyayyarsa. Mina tace, qwarai na yarda dake, domin wata lakcarsa da naji yana yiwa mata da maza, saida nace, Allah yasa haka yakewa iyalinsa. Mimi tana dariya, tace yana min. Suna cikin haka saiga wayarsa. Mina kallon mimi takeyi tanata zuba shagwa6a a waya. Wai gobe zata dawo, shi kuma yace idanunsa aun qosa su ganta. Ta bashi mina sun gaisa, suka yi bankwana tare da amsar lambar juna. Rayuwar su mimi abin koyi ce ga mutane na qwarai.
Bayan shekara uku Ginin Ismail yayi nisa, na jami'a, lokacin Mimi tana goyon Abdurrahman sunan mahaifin ismail. Sannan sun tare a sabon gidan su dake nan layin, ita kuma Zainabu ya gyara mata inda suka tashi. Kwanciyar hankali da qaruwar arziki kullum suna cikinta. Yaran ta uku duk maza, Hajiya sauda tace, qila irin tawa zakiyi, sai na hudu ki samu mace. Ta dauko Ummi tana zama gurinta, kuma ta saka ta makaranta mai kyau. Ita ma kuma ta koma makaranta don ta samu digiri dinta ko ba za tayi aiki ba, ta aje kwalinta don wata rana. Mimi ta fito wanka tana zaune a gaban madubi tana ta shafe-shafen jiki da turarruka masu qamshi. Yau Malaminta ya dawo daga tafiyar da sukayi ta sati biyu qasashe biyar, suka zagaya shi da manyan Malamai don yin da'awa. Dakinsa ta nufa don daukar darasi. Fatanta Allah yasa ta samu rumaisa a yau. Yana cikin bandaki, sai ta shige. Ni kuma sai na dawo baya tare da fadin Allah ya qara danqon soyayya. QARSHE.......
Mu hadu a sabbin littafai na, SANADIN FURUCI...da RUDI KO BURI....Taku a kullum Halimarku K/Mashi. Sai na jiku a 08081165107 don jin ta bakinku.
Nima Abdu pro mlf (Abdurrahman) da na rubuta muku, ina yima kowa fatan alkhairi, da fatan Allah ya amfanar damu darussan dake cikin labarin Ameen.
Ma'assalam
sai inna Habiba wace take muku post a whatsapp nace mu
Ma'assalam
Post a Comment for "CANJIN RAYUWA Book 4 Complete Hausa Novel"