Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Daudar Gora Book 2 Page 49

DAUDAR GORA....!! Chapter: 49 Kyakykyawan bowl din data dauro saman tray mai kyau shima da tambulan din madara yabi da kallo. Ta ajiye a saman dan table din data janyo kusa da gadon kasancewar a baki- baki ya ke zaune shi ta daura. Bowl din ta bude tana dan kallonsa kasa-kasa kamar yanda yake binta da shegen kallon nan nasa. A saman lips ta furta "Kana son shi?". Gasashen naman da ke ta tashin kamshi mai tada kwadayi ya dan kalla. Batare da yace komai ba ya kamo hanunta da ke rike da murfin ya zaresa ya ajiye. Rikota yay ya zaunar a kusa da shi. "Sai dai in zaki bani da kanki. Hannuna ciwo suke min". Yanda yay maganar acan kasan makoshi matuka ya sata kallonsa da sauri, ido daya ya kashe mata da sakar mata wani lalataccen murmushi daya nema raba jikinta na numfashinta. Da sauri ta maida kan ta risinar zuciyarta na wani masifar harbawa da sauri-sauri. Hannunta ya riko cikin nasa ya dan murza yana kara narkar da idanunsa kan fuskarta Cikin sake tausasa harshe da cigaba da murza hannun ya ce, "A duk lokacin da kike tare da15:37 hannun ya ce, "A duk lokacin da kike tare da < an ki kallesa abokin ki, amininki, yaya A kal harma kaninki idan ya kama, sannan farin cikin ki. Ina son gidana da iyalina su kasance aljannar duniyata da duk inda naje na dawo da damuwa za'a goge min shi da farin ciki, duk sanda kaina ya dauka zafi za'a sanyaya min shi da nishadi. Duk sanda na shigo da farin ciki za'a tayani yi har ma a ninka min shi da wani da yafi wanda nake tare da shi. Anan Eshaan sunansa Eshaan Ion Haysam Abdul-majeed MIJIN Fhareedah (Iffah) bint Zayyan ba Tajwar Eshaan ko Shahan-shan ba. Ki raineni kamar jariri a fadarki, Ni kuma mai sallamawa ne gareki duk rintsi TAURARUWA TA". Wata irin nutsuwa ce ke ratsa mata zuciya, tabbas tana jin dadin kasancewa da shi, amma har yanzu bata san mi takeji game da shi ba. Ita dai kawai yana burgeta, a cikin ado ko sabanin hakan. Sannan duk da taji ciwo da a jikinta da jigatuwa a jiya batajin haushinsa ko jin bai kyauta ba, dan koba komai tayi ilimin addini, tasan hakkokin mace aka mijinta, tasan hakkokin miji akan matarsa, tasan muhimmancin aure da fa'idarsa. Ta kuma san Shahan-shan bazai taba sakinta ba koda ace zata bukaci haka. Mammy ta sake tisa mata fiye da abinda ta sani, har ma da wanda zatayi domin tabbatar da kanta a matsayin diya MACE a gabansa ko gaban wanin sa "Wayyo!". A ada yana matse ciki, da sauri ta kalles yamutse fuska kamar gaske shi adole yunwa yake ji. Cike da nuna damuwa ta ce, "Sorry". Sai kuma ta dakko tray din saman cinyarta. Cokali ta dauka zata diba naman ya rike hannun. Kallonsa ta sakeyi da mamaki. Cikin dan dage gira ya ce, "Nikam da hannu nake so". Komai batace ba ta ajiye cokalin kawai, tare da ajiye trayn ta mike, bai ta nufa bata wani jima ba ta dawo da alama hannu ta wanko. Tray din ta sake maidawa saman kafarta bayan ta koma inda ta tashi ta zauna ta debo naman ta kai bakinsa. Hannun ya riko da kyau ya karasa da naman bakinsa yana lumshe idanunsa, harda sakin siririyar ajiyar zuciya. Ita sai ma abin ya bata dariya harda murmusawa. Wani irin sanyi da nutsuwa yaji har cikin ranta ganin tayi murmushin. Dan gaba daya yau bakin ya mutu kamar ba ita ba, shi kuma yafi son yaga ta saki jiki da shi tana kiriniyarta da surutu kamar da. Sosai yaci naman har hakan ya bata mamaki, hakama madaran. A hankali ta rumtse idanunta sanda yake tsotse yatsun hannun abin kamar da gayya. Da gayyar kuwa yake yi, dan yana kallon yanda take faman matse ido yana murmushi a zuciyarsa Bai bar dakin ba sai da ana kiran sallar magariba < . Yace ta shirya kafin ya dawo zata rakasa wani waje. Da to ta amsa masa kanta a kasa, dan duk wannan abun da ake bata yarda su hada ido sai da kuskure. Bayan fitowarsa alwala a bathroom har ya wuceta ya dawo da baya, kama ta yay ya mikar tsaye da ga zaunen da take. Fuskarta ya dago dan taki yarda ta kallesa, shima bai matsa da sai ta kallesan ba ya manna ma goshinta sumba mai lafiyar da har sai da ta sanya jikinta motsawa. Idanunta a rufe har sai da ya fice sannan ta bude tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, ita har yanzu ta kasa sabawa da salon nasa sam. Sai da ta dan kara gasa kanta kamar yanda Mammy tace ta dinga yi akai-akai sannan tayo alwala ta fito gabatar da sallar magriba. Bayan ta idar zama tai tunani mai zurfi akan Tajwar Eshaan, mutum nan nada abubuwan ban mamaki boyayyu, tabbas ta yarda hatsabibin kansa ne kamar yanda su Miran Arshaan ke fada. Gaskiya tana bukatar sanin yanda akai su Baby suka kasance a wata kasa bayan su Miran Jasim sun mata karyar ya kashesu. Kenan video din data gani jabu ne ko mi?. Rashin amsa da bukatar samunta ya sata mikewa ta gabatar da sallar isha'i da ake kira. Bayan ta idar ta shiga gyara jikinta dan haka kawai take dokin fitar duk da bata san ina suka nufa ba. Tsaf take cikin bakar doguwar rigar abayar datai mata kyau,sai Ver din nan da in aka nada yake yi kamar baoy hijab fari. Fitowa tai tsabar zumudin son fitar ta su. Dakin da suka kwana ta nufa duk da bata zaton ya isa dawowa salla. Kusan a tare suka aura hannayensu kan handle din kofar, ita ta tura shi kuma ya ja batare da kowanne yasan da dan uwansa ba. Cak ta tsaya kanta a kasa tana mai rumtse idanunta dan wata irin kunyarsa takeji har cikin kashinta. Ga kwarjini mai irin mamaye waje din nan da ya kara mata. Kusan minti daya suka kwashe a wajen ita bata tanka ba shima bai ce ba. Tasan in zasu kwana ma zai iya, dan haka ta dan saci kallonsa ta gefen ido. A hankali ta janye idanun nata gain yanda ya kafeta da shegen kallon nan nasa mai hanata sukuni. Sai ta samu kanta da in inar fadin, "Barka da dawowa". Karamar ajiyar zuciyar da bata ji ba ya yayi a ciki, batare da ya amsa gaisuwar tata ba ya karasa fitowa, fuskar babu fara'a sam kamar ko yau she, sai wani irin kwarjini mai cika idon mai kallo, a fisge ya furta, "Muje" yana rabata ya wuce cike da takun nan nasa daddaya. A hankali ta dan sauke numfashi dan jinta take kamar an daureta a wajen, sai kuma ta bisa da kallo kasa-kasa tana mai tsarkake sunan UBANGIJI mahaliccin wannan kyakykyawar halitta. (Kyau dai kam ALLAH ya bashi, sai dai miskilancin nan da jin nan da ke zagaye da shi) ta dan nal fuska kamar zatai magana, sai kuma ta fasa ranta fal tunanin ina ma zasu je a daren nan? rashin mai bata amsa ya sata dan zabura tabi bayansan. Ganin ya nufi lift.. taji duk ta tsure. Ita dai harga ALLAH abin nan baya wani birgeta. Dan indai ta shiga sai tayi hajijiya. Shiyyasa ya zamto sai ta rike wani dan batama taba gigin shiga ita kadai ba. Jiki a sabule ta shiga, jin kofar ta rufe kanta ta rumtse idanu da sauri, sai kuma ta bude akan yatsansa da ke kokarin danna inda yake bukatar suje. "ALLAH ina jin toro" ta fada kamar zatai kuka. Sarai ya jita, amma sai bai nuna yaji ba ya gyara tsaiwarsa bayan ya danna 2 floor. Iffah da ke jin kamar ta fasa kuka a hankali tai yunkurin zamewa dan gara ta zauna zai fi mata sauki. Babu zato taji an riko mata hannu, kafin ta iya ko bude idanunta tajita cikin jikinsa da ke fidda wani irin sirrintaccen kamshi mai ratsa zuciya da bargo da bazata taba iya mantawa ba. Da sauri ta bude idanunta sai ko cikin nasa da ke kallonta, dole ta maida nata ta rufe da sauri zuciyarta na wani irin bugawa da sauri-sauri, tabbas bazata mance wannan turaren ba, dan turarene da ta dinga fafitikar nema a washe grin da aka dakkota da ga sashenta cikin dare aka maidata nashi. Kenan da gaske shi dinne ya je ya dakkota kokuwa yaya akai? Dan wannan Kamshin dai shine. Tsaf ya fahimci inda ta nura, kuma a randa ta dinga neman turaren ya sani sarai, abinda bata sani ba ya ajiye abinsa ne kawai inda bataima zaton ganinsa ba o kawowa a ranta zai ajiye din. "Zamu kwana anan ne?". Ya fada a kasan makoshi yana kallon kyakykyawar fuskarta da ke kwance a kan kirjinsa. Idanun ta bude, sai kuma taja jikinta baya kunya na wani mamayeta. Dauke idanunsa yay da ga kallonta ya fice, itama sai ta bisa tana sauke ajiyar zuciya a jajere, sai kuma ta saki murmushi dan ita da kanta kunyar kanta taji. Wata hanyar da batama san da ita a wajen ba suka nufa, koda yake bawai ta taba shiga wani waje a floor 2 din nan bane bayan falo, shima a randa Malikat Haseenat ce ta kawota da suka biyo komai daki- daki ba kamar yanda yay ba yanzu Inda suka shigo dinne ya sakata tsayawa turus tana kallonsa. Sai kuma ta dan waiga ta kalli hanyar da suka fito, ita fa gaba daya notikan kanta sun kwace, ta ma rasa ta yanda zata misalta ta inda wannan hanyar take a zahirin cikin gidan, dan ita shaidace tsakanin sashensa da na Malikat Bushirat akwai nisa. Duk da sunyi yar tafiya suma amma sai gasu cikin sauki. Kallonsa tai fuska a marairaice kamar ba Iffah'r nan matsiwaciya ba da ya sani ta ce, "ALLAH toro nake ji". Kallonta yake da shanyayyun idanun nan nasa masu kaifi kamar bazaice komai ba, sai kuma jitai a hankali kamar mai rada ya furta, "Nima tsoron nake ji ai". Idanu ta dan waro alamar mamaki tace, "Kai din?". Kansa ya dan kada mata da lumshe idanunsa ya bude duk a lokaci daya. Sai kuma ya kai hannunsa kan nata ya matsota jikinsa. "Ki karamin karfi". Ya fada yana rungumeta cikin jikin nasa. Daburcewa tai ma ita gaba daya. Tai kokarin dagowa ya hana hakan. Dole ta hakura tai luff tana mai shakar kamshin da jikinsa ke fitarwa mai azabar dadi. Kusan minti biyu suka kwashe a wajen kafin ya dagota a hankali, kin yarda tai su hada ido sam, shima sai bai matsa ba ya ja hanunta kawai yana dan murmushin da iyakarsa makoshi suka shige.

Post a Comment for "Daudar Gora Book 2 Page 49"