Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Governor's Wife Book 2 Complete Hausa Novel

*Part two*   01 *ina godiya ga wanda suka biya kuɗin karanta cigaban wannan labari. Ina fata kuma za a riƙe amana ba za a dinga fitarwa waje ba* *Bama yi...Bama yi....Bama yi. A tsige Saifuddeen Kachallah, a tsige Gwamna Kachallah* " 'Yan Daba kenan da suka wargaza taron buɗe Congo Stadium da aka yi a safiyar yau. Kamar yadda kuka gani jifa kawai suke ta ko'ina amma mun samu labarin cewa Gwamna ya samu ya bar wajen lafiya..." Bilkisu Kachallah ta yi saurin kashe TV ɗin zuciyarta na tiriri. A karo na ba adadi ta sake kiran numbar wayar Gwamna amma taji ta a kashe. Hawaye ne ya shiga sauko mata, bata cika yin kuka ba. Ba za ma ta iya tuna rabon da tayi kuka ba. "Ba wanda ya isa ya tsige ka a kujerar nan, babu wanda ya isa ya tsigeka. Ƙarya su ke, ba macen da ka taɓa ciwa zarafi, i can bet my life for that. Saifuddeen ka buɗe wayarka please?" Za ta yi faɗa da shi, ta yi fushi da shi, amma soyayya ɗaya ce kuma ta bawa Saifuddeentun ba ta da wayo. Ba zata taɓa bari a ci zarafinsa ba matuƙar tana numfashi. Goge hawayenta tayi ta kira wani number. "A nemo min wacece Lami Ninja" Tana faɗin haka ta miƙe ta shige ɗaki, Kachallah House za ta je ƙila chan zai wuce, hankalinta ba zai taɓa kwanciya ba sai ta gan shi...   Tun tuni take tsumayin kiran Gwamna, ya kamata ace ya ga saƙonta. So take ya kira ya mata faɗa, ya kirata munafuka, macuciya, azzaluma kamar yadda ta dinga kiransa a baya. Miyasa bai nemi kariya ba?, miyasa ya tsaya har suka zo? Tana jin ringing wayarta ta ɗauka ba tare ta ga sunan mai kiranba. "Hello Excellency" "Ina fata hankalinki ya kwanta da abinda kika sa aka masa. Ki ji tsoron Allah Asiya, ki ji tsoron Allah" Kiit aka kashe wayar. Ta cire wayar daga kunnenta a hankali ta ce "Ya Ubayd kayi haƙuri, na yadda na tafka kuskure. Amma koda Gwamna zai sake ni ba zan tafi ba sai na wanke sunansa. I promise" Tukunna wacece Lami Ninja? Kiran numbar Fou'ad Salisu tayi bugu biyu kafin aka ɗaga. "Fou'ad wacece Lami Ninja?" "Nima ɗazu da na ga labarin na fara bincike. So far dai abunda na gano shine, cikakken sunanta Lami Haladu. Ta yi Jami'ar Congo lokacin da Gwamna yake koyarwa a chan. Na sa a duba min ina take yanzu da kuma dalilin wannan ƙaran data shigar amma ban samu feedback ba. I'll keep you posted idan na samu labari" "Nagode" Lokacin da ta fito daga banɗaki Sumayya na zaune tana jiranta. "Gwamna ya dawo?" "A'a, yanzu first lady ta fita inaga wajensa za ta je" "Ƙila Kachallah house zai je" Asiya ta furta tareda zama a bakin gado ta kifa fiskarta kan cinyoyinta. "Anty ke kika sa aka jefi Gwamna ko?" "Kar ki dameni Sumy, ki barni na ji da abinda ke raina" Sumayya ta ja baya saboda yadda Asiyar ta hayayyaƙo kamar zata maketa. ***   Gwamna gidansa ya wuce bayan ya kashe duka wayoyinsa, ya kuma bada umurnin duk wanda ya zo kar a bashi damar ƙarisowa wajensa. Yana shiga ɗakinsa ya kwanta kan gado ko takalmi bai cire ba. Bai taɓa tunanin tsanar da ta masa har ya kai haka ba. Ba damuwarsa tsige shi da za ayi ba, ko kuma jifansa da 'yan daba suka yi. Damuwarsa yadda ta saka 'yarsa cikin wannan lamari, she's willing to destroy his daughter's life saboda cimma burinta. *Dan Allah ka yafemin, ka bar wajen taron nan yanzu please, akwai 'yan daba da za su jefeka idan aka tashi* Yana karanta saƙon komai ya dawo masa. Ba yadda za ayi ta san za a jefe shi sai idan tanada hannu a ciki. Dan ya tabbatar da zarginsa sai ya ɗan rankwafar da kansa gefen COS ya raɗa masa magana a kunne "Asya ce 'yar jaridar da ke wa Climax rubutu ko?" "Excellencyyy" COS ya faɗa a hankali, hakan ya tabbatar da zarginsa. Abinda ya ɗaure masa kai shine yadda tayi rubutu tana kiransa *Rapist* idan shi ɗin mai fyaɗe ne zai ƙyaleta wata biyu da kwanaki da suka yi tare bai nemeta ta ƙarfi ba. Tunani ya shiga yi wacece ma Lami Ninja da ake faɗa. Ya kai kusan minti biyar kafin ya iya tuno abinda ya faru shekaru shabiyar da suka wuce. Lokacin da ya ke koyarwa a jami'ar Congo, 'yanmata da dama sun yi ta damunsa, wasu da maganar soyayya wasu kuma da tayin iskanci. Office ɗinsa kullum ba a rasa wasiƙar mace tana masa tayin soyayya. Saboda yadda mata ke masa idan sun zo office ɗinsa shiyasa ma ya hana mata zuwa office ɗinsa, duk wani abun da zai haɗashi da mace ɗaliba to a cikin aji ne ko a wajen aji amma banda office. Shi har staff mata bai tsira daga harinsu ba. Yana ɗaya daga cikin dalilin dayasa yake son Misturah saboda har ta gama ba ruwanta da shigewa Malamai, shima bata sake da shi sosai ba sai da ta gama makaranta. Akwai wata ɗaliba a aji huɗu da take yawan masa kallon karuwai duk lokacin da ya ke koyarwa, da sun haɗa ido da shi sai ta fara tauna cize leɓe tana kashe masa ido. Idan kuwa tambaya za ta yi a aji to sai dai ta tashi tsaye tana magana tana shafa ƙirjinta. Ta taɓa zuwa office ɗinsa ya koreta. Dake 'yar duniya ce ko ya akayi ta sa masu shara suka buɗe mata office ɗinsa oho. Ya dai shigo office watarana ya zauna kenan ta fito daga bayan labule tsirara. Da farko tsorata yai dan ya ɗauka Aljanace ko mahaukaciya. "Ko sau ɗaya ne Dr Saifuddeen ka taɓani, kar kayi komai ma ni kawai ka sa hannunka ka shafa jikina zan haƙura da haka" Banda matarsa Bilkisu a lokacin zai iya rantsewa bai taɓa ganin mace tsirara a gabansa ba sai ranan. "Ki sa kayanki ki fita min daga office" ya daka mata tsawa idonsa a rufe. "Ko kayi abinda nace ko na maka sharri. Ihu zan saka sai an shigo an same mu a haka kuma nace ta ƙarfi ka dannneni" Ƙoƙarin fita daga office ɗin yai ta tareshi. Ya sha ji ana cewa akwai ƙaƙƙarfan mata, amma bai gamsu ba sai ranan. Kokawa suka fara da ita, shi yana son ya kai ƙofa ita kuma tana son danneshi ta ƙarfi... *** "Baba mi yake faruwa? Ina Saifuddeen? Ya ban ganshi a nan ba" Bilkisu ta faɗa tana sheshsheƙar kuka. "Kwantar da hankalinki, yana lafiya" "Ina yake?" "Zauna tukunna" Bilkisu ta zauna gefen mahaifinta. "Yana buƙatar hutu, ki bashi kamar awa biyu kafin ki je ki sameshi a chan gidansa" "A'a Baba, ni yake buƙata. Kai baka San halinsa bane, ba zai taɓa magana ba, komai yake damunsa ba zai yi magana ba. Dole na je wajensa, ba zan iya rayuwa ba idan wani abu ya sameshi" "Shi ya buƙaci hakan, ya yi min text akan yana buƙatar kaɗaici. Ki barshi ya huta" Ta goge fiskarta tace "Baba wace karuwar ce Lami Ninja?" "Lokacin da kika je haihuwa a America akwai wata ɗaliba da ta yiwa Saifu sharri. Ta shiga office ɗinsa ta far masa, it was a scandal saboda yarinyar Karuwar Malamai ce, amma an rufe maganar tun lokacin" "Miyasa ba a gayamin ba, Wallahi dana san da wannan da tuni na sa an ƙona shegiya. Waya gaya mata mijina yana shiga trash can" "Ba wannan ne matsalarmu ba, Umaru Kwom yana so yai amfani da ita wajen ganin an tsige Saifu. Dole ne mu bi komai a hankali" "Baba, Saifuddeen bai mata komai ba. Ƙarya take, i know my husband" "Na sani, amma lokacin da abin ya faru an gansu tare a office ɗinsa. Its something..." "Baba, ba abinda ya shiga tsakaninsu" Bilkisu tayi maganar da yarda na ban mamaki. Ko shi Alhaji Sani yanzu a da yana kokonto ko abin ya faru ko kuma bai faru ba, amma yadda 'yarsa tayi maganar da absolute certainty cewa babu abinda ya faru, sai ya ji ya gastata. Ita take zaune da Saifuddeen shekaru shabakwai, ita ta san mi zai iya yi, mi ba zai iya ba. "Ita kuma karuwar bayan komai ya lafa sai na sa an ƙona mata fiska" Alhaji Sani ya sake baki yana kallon 'yarsa, yadda Bilkisu ta yi maganar nan mai ƙwatan Lami Ninja a hannunta sai Allah.   ***   Lami Ninja a gidan Umaru Kwom aka mata mafaka tun lokacin data shigo jahar. Umaru Kwom tun kafin Fou'ad Salisu ya gano cewa account ɗin Sa'ad Kachallah na Alhaji Sani ne shi ya riga ya sani saboda shi ba yaro bane, mutane irin Saifuddeen Kachallah ba za su iya cin dukiyar talakawa ba. Tarihin Saifuddeen ya shiga dubawa tun sanda aka haifeshi har zuwa yanzu da yake kan kujerar Gwamna. Bai samu komai ba hakan yasa ya tafi jami'ar Congo neman ƙwaƙwaf. A nan ya samu wanda ya gaya mishi shekaru da daɗewa akwai wani abunda ya faru da wata ɗaliba, amma an rufe case ɗin an wanke sunan Saifuddeen saboda matsayin Alhaji Sani. Yai bincike har ya gano inda Lami Ninja take, ta buɗe ƙaton club a Lagos tana kuma sana'ar fitar da 'yanmata waje karuwanci. Tun kafin ta faɗa masa cewa ita ta nemi Saifuddeen ya riga ya sani amma yace ta fito tace Saifuddeen ya ci zarafinta, sannan saboda haka ne ma ya bata carryover a course ɗinsa. Ba dan kuɗin da yace zai bata ta amince da hakan ba sai dan yayi alƙawarin idan har bata yi yadda yace ba zai sa a ɗaureta, yanada shaidu akan mummunan harka da take yi. "Mi zai faru idan aka gano cewa ƙarya nake?" "Ke macece, babu wanda zai ƙaryata ki" Har yanzu da shekaru suka ja mata akwai sauran burbuɗin son Saifuddeen a ranta. Amma ya za tayi aikin gama ya gama...   Asiya data shirya gidan Saifuddeen ta wuce saboda Uwani ta shaida mata Gwamna yana gidan amma yace baya son ganin kowa. Ƙirjinta sai bubuk bubuk yake lokacin da take haurawa matattakala. Ƙofar falonsa a kulle yake da key, ta fito da key ɗin data karɓa a wajen Uwani ta buɗe da shi. Ta ja dogon numfashi sannan ta kutsa kai ciki ta wuce ɗakinsa. Yayi wanka ya chanja kaya zuwa T-shirt ruwan toka da wando ruwan ƙasa, yana zaune kan gado ya jingina bayansa da filo yana rubutu. Ta ji daɗi da ta murɗa ƙofan ta ji ta buɗe. Suna haɗa ido ya sauke idonsa ya cigaba da rubutun da ya ke. Duk wani ƙarfin gwiwar da take da shi sai da ya sace da ta ganshi, gashi nan kamar kullum fiskarsa wasai babu alamun yana cikin tashin hankali. Kamar ba shine Gwamnan da aka jefa ɗazu ba, kamar ba shine Gwamnan da ake shirin tsigewa ba. "Kin zo ki duba ko zuciyata ta buga ko?" Yai maganar ba tareda ya ɗago ba. Gwiwowinta biyu ta sa a ƙasa ta fara magana. " na san ba lallai ka yarda ba, amma wallahi ban san da abinda ake tuhumarka ba kenan, sai yau na gani, ba ni na rubuta ba. Ka yafe min" Ɗagowa yai ya dubeta yace "A matsayina na Uba bana tunanin zan iya yafe miki nan kusa. A matsayina na Gwamna kuma zan barki ki cigaba da zama hajar Kamfen" "Dan Allah ko zaka sake ni ka bari na wanke sunanka tukunna" Dariya ya fara har sai da fararen haƙoransa suka bayyana. "Waya gaya miki zan sake ki?" "Kayi haƙuri" "Haƙuri akan kin ci amanata?, ko haƙuri akan kina so ki tozarta 'yata a idon duniya, ko haƙuri akan da aurena kike mu'amala da Umaru Kwom ba tareda izina ba" "Za ka iya yi min komai amma dan Allah ka bani dama na taimakeka" Shiru yai na tsawon minti uku kafin yace " bana buƙatar taimakon ki, Allah ne shaidata kuma shi zai taimakeni" Ta zauna kusan minti goma amma bai sake magana ba, hakan yasa ta miƙe ta fice daga ɗakin. Tana isowa falo ta haɗu da Bilkisu. "Mi ya kawoki?" Asiya tayi shiru, Bilkisu ta ja tsaki ta mangajeta ta wuce ɗakin Saifuddeen. *** Wasu samari guda biyu ke zaune a majalisa suna jira sauran abokansu su ƙariso. "Wannan lamari akwai ɗaure kai, gaskiya ban yarda Gwamna SSK zai iya cin zarafin mace ba" mai farin jumfa yai magana yana cigaba da latsa waya. "Kai kabar ustazai masu gemun nan, yawancinsu ustazancinsu a baki ne" "Kaiiii! banda Prof S Kachallah, ya koyar damu Shekaru goma da suka wuce, a lokacin mata ke binsa yake gudunsu. In fact, lokacin da muke school in za a kira malaman da basa neman mata to Prof S Kachallah za a fara kira" "Tunda kace haka na yarda" "Lami Ninja fa karuwace, ance a Lagos wani ƙaton gidan karuwai take da shi, shine za'a yarda da magananta" "To Allah ya fitar da shi"...   Lokacin da Asiya ta koma gida numbar MD na Hill TV ta kira, fili take son siya wanda za a rinƙa ɗaura wani shirin da take son farawa gobe. Suna gama waya da shi ta kira CY. Satin CY ɗaya da shigowa ƙasar. "CY akwai aikin da zaka min" "An gama your Excellency" Bayan ta gama waya da CY ta zauna ta kunna laptop ɗinta ta fara rubutu. Fou'ad Salisu ya ce mata Lami Ninja ta taɓa aure, shekara biyu ta rabu da mijin ta koma Lagos da zama sannan kuma ita ce ke da Sunlight Club a Lagos. "Idan har alƙalamin ɗan jarida na iya kawo fitina to lallai ko zai iya kawo gyara. Lami Ninja ko Lami Spider kike, sai kin ƙwammace baki biyewa Umaru Kwom ba"*Part two*   01 *ina godiya ga wanda suka biya kuɗin karanta cigaban wannan labari. Ina fata kuma za a riƙe amana ba za a dinga fitarwa waje ba* *Bama yi...Bama yi....Bama yi. A tsige Saifuddeen Kachallah, a tsige Gwamna Kachallah* " 'Yan Daba kenan da suka wargaza taron buɗe Congo Stadium da aka yi a safiyar yau. Kamar yadda kuka gani jifa kawai suke ta ko'ina amma mun samu labarin cewa Gwamna ya samu ya bar wajen lafiya..." Bilkisu Kachallah ta yi saurin kashe TV ɗin zuciyarta na tiriri. A karo na ba adadi ta sake kiran numbar wayar Gwamna amma taji ta a kashe. Hawaye ne ya shiga sauko mata, bata cika yin kuka ba. Ba za ma ta iya tuna rabon da tayi kuka ba. "Ba wanda ya isa ya tsige ka a kujerar nan, babu wanda ya isa ya tsigeka. Ƙarya su ke, ba macen da ka taɓa ciwa zarafi, i can bet my life for that. Saifuddeen ka buɗe wayarka please?" Za ta yi faɗa da shi, ta yi fushi da shi, amma soyayya ɗaya ce kuma ta bawa Saifuddeentun ba ta da wayo. Ba zata taɓa bari a ci zarafinsa ba matuƙar tana numfashi. Goge hawayenta tayi ta kira wani number. "A nemo min wacece Lami Ninja" Tana faɗin haka ta miƙe ta shige ɗaki, Kachallah House za ta je ƙila chan zai wuce, hankalinta ba zai taɓa kwanciya ba sai ta gan shi...   Tun tuni take tsumayin kiran Gwamna, ya kamata ace ya ga saƙonta. So take ya kira ya mata faɗa, ya kirata munafuka, macuciya, azzaluma kamar yadda ta dinga kiransa a baya. Miyasa bai nemi kariya ba?, miyasa ya tsaya har suka zo? Tana jin ringing wayarta ta ɗauka ba tare ta ga sunan mai kiranba. "Hello Excellency" "Ina fata hankalinki ya kwanta da abinda kika sa aka masa. Ki ji tsoron Allah Asiya, ki ji tsoron Allah" Kiit aka kashe wayar. Ta cire wayar daga kunnenta a hankali ta ce "Ya Ubayd kayi haƙuri, na yadda na tafka kuskure. Amma koda Gwamna zai sake ni ba zan tafi ba sai na wanke sunansa. I promise" Tukunna wacece Lami Ninja? Kiran numbar Fou'ad Salisu tayi bugu biyu kafin aka ɗaga. "Fou'ad wacece Lami Ninja?" "Nima ɗazu da na ga labarin na fara bincike. So far dai abunda na gano shine, cikakken sunanta Lami Haladu. Ta yi Jami'ar Congo lokacin da Gwamna yake koyarwa a chan. Na sa a duba min ina take yanzu da kuma dalilin wannan ƙaran data shigar amma ban samu feedback ba. I'll keep you posted idan na samu labari" "Nagode" Lokacin da ta fito daga banɗaki Sumayya na zaune tana jiranta. "Gwamna ya dawo?" "A'a, yanzu first lady ta fita inaga wajensa za ta je" "Ƙila Kachallah house zai je" Asiya ta furta tareda zama a bakin gado ta kifa fiskarta kan cinyoyinta. "Anty ke kika sa aka jefi Gwamna ko?" "Kar ki dameni Sumy, ki barni na ji da abinda ke raina" Sumayya ta ja baya saboda yadda Asiyar ta hayayyaƙo kamar zata maketa. ***   Gwamna gidansa ya wuce bayan ya kashe duka wayoyinsa, ya kuma bada umurnin duk wanda ya zo kar a bashi damar ƙarisowa wajensa. Yana shiga ɗakinsa ya kwanta kan gado ko takalmi bai cire ba. Bai taɓa tunanin tsanar da ta masa har ya kai haka ba. Ba damuwarsa tsige shi da za ayi ba, ko kuma jifansa da 'yan daba suka yi. Damuwarsa yadda ta saka 'yarsa cikin wannan lamari, she's willing to destroy his daughter's life saboda cimma burinta. *Dan Allah ka yafemin, ka bar wajen taron nan yanzu please, akwai 'yan daba da za su jefeka idan aka tashi* Yana karanta saƙon komai ya dawo masa. Ba yadda za ayi ta san za a jefe shi sai idan tanada hannu a ciki. Dan ya tabbatar da zarginsa sai ya ɗan rankwafar da kansa gefen COS ya raɗa masa magana a kunne "Asya ce 'yar jaridar da ke wa Climax rubutu ko?" "Excellencyyy" COS ya faɗa a hankali, hakan ya tabbatar da zarginsa. Abinda ya ɗaure masa kai shine yadda tayi rubutu tana kiransa *Rapist* idan shi ɗin mai fyaɗe ne zai ƙyaleta wata biyu da kwanaki da suka yi tare bai nemeta ta ƙarfi ba. Tunani ya shiga yi wacece ma Lami Ninja da ake faɗa. Ya kai kusan minti biyar kafin ya iya tuno abinda ya faru shekaru shabiyar da suka wuce. Lokacin da ya ke koyarwa a jami'ar Congo, 'yanmata da dama sun yi ta damunsa, wasu da maganar soyayya wasu kuma da tayin iskanci. Office ɗinsa kullum ba a rasa wasiƙar mace tana masa tayin soyayya. Saboda yadda mata ke masa idan sun zo office ɗinsa shiyasa ma ya hana mata zuwa office ɗinsa, duk wani abun da zai haɗashi da mace ɗaliba to a cikin aji ne ko a wajen aji amma banda office. Shi har staff mata bai tsira daga harinsu ba. Yana ɗaya daga cikin dalilin dayasa yake son Misturah saboda har ta gama ba ruwanta da shigewa Malamai, shima bata sake da shi sosai ba sai da ta gama makaranta. Akwai wata ɗaliba a aji huɗu da take yawan masa kallon karuwai duk lokacin da ya ke koyarwa, da sun haɗa ido da shi sai ta fara tauna cize leɓe tana kashe masa ido. Idan kuwa tambaya za ta yi a aji to sai dai ta tashi tsaye tana magana tana shafa ƙirjinta. Ta taɓa zuwa office ɗinsa ya koreta. Dake 'yar duniya ce ko ya akayi ta sa masu shara suka buɗe mata office ɗinsa oho. Ya dai shigo office watarana ya zauna kenan ta fito daga bayan labule tsirara. Da farko tsorata yai dan ya ɗauka Aljanace ko mahaukaciya. "Ko sau ɗaya ne Dr Saifuddeen ka taɓani, kar kayi komai ma ni kawai ka sa hannunka ka shafa jikina zan haƙura da haka" Banda matarsa Bilkisu a lokacin zai iya rantsewa bai taɓa ganin mace tsirara a gabansa ba sai ranan. "Ki sa kayanki ki fita min daga office" ya daka mata tsawa idonsa a rufe. "Ko kayi abinda nace ko na maka sharri. Ihu zan saka sai an shigo an same mu a haka kuma nace ta ƙarfi ka dannneni" Ƙoƙarin fita daga office ɗin yai ta tareshi. Ya sha ji ana cewa akwai ƙaƙƙarfan mata, amma bai gamsu ba sai ranan. Kokawa suka fara da ita, shi yana son ya kai ƙofa ita kuma tana son danneshi ta ƙarfi... *** "Baba mi yake faruwa? Ina Saifuddeen? Ya ban ganshi a nan ba" Bilkisu ta faɗa tana sheshsheƙar kuka. "Kwantar da hankalinki, yana lafiya" "Ina yake?" "Zauna tukunna" Bilkisu ta zauna gefen mahaifinta. "Yana buƙatar hutu, ki bashi kamar awa biyu kafin ki je ki sameshi a chan gidansa" "A'a Baba, ni yake buƙata. Kai baka San halinsa bane, ba zai taɓa magana ba, komai yake damunsa ba zai yi magana ba. Dole na je wajensa, ba zan iya rayuwa ba idan wani abu ya sameshi" "Shi ya buƙaci hakan, ya yi min text akan yana buƙatar kaɗaici. Ki barshi ya huta" Ta goge fiskarta tace "Baba wace karuwar ce Lami Ninja?" "Lokacin da kika je haihuwa a America akwai wata ɗaliba da ta yiwa Saifu sharri. Ta shiga office ɗinsa ta far masa, it was a scandal saboda yarinyar Karuwar Malamai ce, amma an rufe maganar tun lokacin" "Miyasa ba a gayamin ba, Wallahi dana san da wannan da tuni na sa an ƙona shegiya. Waya gaya mata mijina yana shiga trash can" "Ba wannan ne matsalarmu ba, Umaru Kwom yana so yai amfani da ita wajen ganin an tsige Saifu. Dole ne mu bi komai a hankali" "Baba, Saifuddeen bai mata komai ba. Ƙarya take, i know my husband" "Na sani, amma lokacin da abin ya faru an gansu tare a office ɗinsa. Its something..." "Baba, ba abinda ya shiga tsakaninsu" Bilkisu tayi maganar da yarda na ban mamaki. Ko shi Alhaji Sani yanzu a da yana kokonto ko abin ya faru ko kuma bai faru ba, amma yadda 'yarsa tayi maganar da absolute certainty cewa babu abinda ya faru, sai ya ji ya gastata. Ita take zaune da Saifuddeen shekaru shabakwai, ita ta san mi zai iya yi, mi ba zai iya ba. "Ita kuma karuwar bayan komai ya lafa sai na sa an ƙona mata fiska" Alhaji Sani ya sake baki yana kallon 'yarsa, yadda Bilkisu ta yi maganar nan mai ƙwatan Lami Ninja a hannunta sai Allah.   ***   Lami Ninja a gidan Umaru Kwom aka mata mafaka tun lokacin data shigo jahar. Umaru Kwom tun kafin Fou'ad Salisu ya gano cewa account ɗin Sa'ad Kachallah na Alhaji Sani ne shi ya riga ya sani saboda shi ba yaro bane, mutane irin Saifuddeen Kachallah ba za su iya cin dukiyar talakawa ba. Tarihin Saifuddeen ya shiga dubawa tun sanda aka haifeshi har zuwa yanzu da yake kan kujerar Gwamna. Bai samu komai ba hakan yasa ya tafi jami'ar Congo neman ƙwaƙwaf. A nan ya samu wanda ya gaya mishi shekaru da daɗewa akwai wani abunda ya faru da wata ɗaliba, amma an rufe case ɗin an wanke sunan Saifuddeen saboda matsayin Alhaji Sani. Yai bincike har ya gano inda Lami Ninja take, ta buɗe ƙaton club a Lagos tana kuma sana'ar fitar da 'yanmata waje karuwanci. Tun kafin ta faɗa masa cewa ita ta nemi Saifuddeen ya riga ya sani amma yace ta fito tace Saifuddeen ya ci zarafinta, sannan saboda haka ne ma ya bata carryover a course ɗinsa. Ba dan kuɗin da yace zai bata ta amince da hakan ba sai dan yayi alƙawarin idan har bata yi yadda yace ba zai sa a ɗaureta, yanada shaidu akan mummunan harka da take yi. "Mi zai faru idan aka gano cewa ƙarya nake?" "Ke macece, babu wanda zai ƙaryata ki" Har yanzu da shekaru suka ja mata akwai sauran burbuɗin son Saifuddeen a ranta. Amma ya za tayi aikin gama ya gama...   Asiya data shirya gidan Saifuddeen ta wuce saboda Uwani ta shaida mata Gwamna yana gidan amma yace baya son ganin kowa. Ƙirjinta sai bubuk bubuk yake lokacin da take haurawa matattakala. Ƙofar falonsa a kulle yake da key, ta fito da key ɗin data karɓa a wajen Uwani ta buɗe da shi. Ta ja dogon numfashi sannan ta kutsa kai ciki ta wuce ɗakinsa. Yayi wanka ya chanja kaya zuwa T-shirt ruwan toka da wando ruwan ƙasa, yana zaune kan gado ya jingina bayansa da filo yana rubutu. Ta ji daɗi da ta murɗa ƙofan ta ji ta buɗe. Suna haɗa ido ya sauke idonsa ya cigaba da rubutun da ya ke. Duk wani ƙarfin gwiwar da take da shi sai da ya sace da ta ganshi, gashi nan kamar kullum fiskarsa wasai babu alamun yana cikin tashin hankali. Kamar ba shine Gwamnan da aka jefa ɗazu ba, kamar ba shine Gwamnan da ake shirin tsigewa ba. "Kin zo ki duba ko zuciyata ta buga ko?" Yai maganar ba tareda ya ɗago ba. Gwiwowinta biyu ta sa a ƙasa ta fara magana. " na san ba lallai ka yarda ba, amma wallahi ban san da abinda ake tuhumarka ba kenan, sai yau na gani, ba ni na rubuta ba. Ka yafe min" Ɗagowa yai ya dubeta yace "A matsayina na Uba bana tunanin zan iya yafe miki nan kusa. A matsayina na Gwamna kuma zan barki ki cigaba da zama hajar Kamfen" "Dan Allah ko zaka sake ni ka bari na wanke sunanka tukunna" Dariya ya fara har sai da fararen haƙoransa suka bayyana. "Waya gaya miki zan sake ki?" "Kayi haƙuri" "Haƙuri akan kin ci amanata?, ko haƙuri akan kina so ki tozarta 'yata a idon duniya, ko haƙuri akan da aurena kike mu'amala da Umaru Kwom ba tareda izina ba" "Za ka iya yi min komai amma dan Allah ka bani dama na taimakeka" Shiru yai na tsawon minti uku kafin yace " bana buƙatar taimakon ki, Allah ne shaidata kuma shi zai taimakeni" Ta zauna kusan minti goma amma bai sake magana ba, hakan yasa ta miƙe ta fice daga ɗakin. Tana isowa falo ta haɗu da Bilkisu. "Mi ya kawoki?" Asiya tayi shiru, Bilkisu ta ja tsaki ta mangajeta ta wuce ɗakin Saifuddeen. *** Wasu samari guda biyu ke zaune a majalisa suna jira sauran abokansu su ƙariso. "Wannan lamari akwai ɗaure kai, gaskiya ban yarda Gwamna SSK zai iya cin zarafin mace ba" mai farin jumfa yai magana yana cigaba da latsa waya. "Kai kabar ustazai masu gemun nan, yawancinsu ustazancinsu a baki ne" "Kaiiii! banda Prof S Kachallah, ya koyar damu Shekaru goma da suka wuce, a lokacin mata ke binsa yake gudunsu. In fact, lokacin da muke school in za a kira malaman da basa neman mata to Prof S Kachallah za a fara kira" "Tunda kace haka na yarda" "Lami Ninja fa karuwace, ance a Lagos wani ƙaton gidan karuwai take da shi, shine za'a yarda da magananta" "To Allah ya fitar da shi"...   Lokacin da Asiya ta koma gida numbar MD na Hill TV ta kira, fili take son siya wanda za a rinƙa ɗaura wani shirin da take son farawa gobe. Suna gama waya da shi ta kira CY. Satin CY ɗaya da shigowa ƙasar. "CY akwai aikin da zaka min" "An gama your Excellency" Bayan ta gama waya da CY ta zauna ta kunna laptop ɗinta ta fara rubutu. Fou'ad Salisu ya ce mata Lami Ninja ta taɓa aure, shekara biyu ta rabu da mijin ta koma Lagos da zama sannan kuma ita ce ke da Sunlight Club a Lagos. "Idan har alƙalamin ɗan jarida na iya kawo fitina to lallai ko zai iya kawo gyara. Lami Ninja ko Lami Spider kike, sai kin ƙwammace baki biyewa Umaru Kwom ba" 2 *Afuwan Dan Allah. Wayata ta mutu ina kan editting, sai da aka kawo wuta na ƙarisa. Mu kwana lafiya* *Ilimi, nitsuwa, tausayi, jajircewa, kawaici, kwarjini.Kaɗan kenan daga halayen Prof Saifuddeen Kachallah lokacin da yake koyarwa.# SSK is innocent* *babu salihin malami a Jami'ar Congo sama da Prof S S Kachallah. #the Gov is innocent* *i've never seen a gentleman like him. #Our Gov is innocent* Bilkisu Kachallah ta cigaba da karanta tweets na mutane da ke supporting Gwamna. Wasu ma suka faɗi yadda Gwamna ya biya musu kuɗin Makaranta lokacin da yake koyarwa. "This is good ai, mutane na bayanka Saifuddeen" Ta yi magana tana ajiye wayar a kusa da dressing mirror, ta gyara ɗaurin ɗankwalinta da kyau sannan ta ɗau gyale ta saƙala a kafaɗa, a karo na biyu ta ɗau janbaki ta sake gogawa a leɓenta. Ta saka waya a jaka ta ɗau jakar ta fice daga ɗakin. Asiya na zaune akan kujera ta ƙurawa TVn ɗakinta ido. Lokaci zuwa lokaci tana duba agogon wayanta, jira take ƙarfe tara da rabi ya cika a sako shirin da ta ɗau nauyi. CY ya gaya mata cewa ya yi hira da mutane takwas kuma duka za a saka su a shirin. Tun jiya da dare take ganin tweets na mutane suna bayyana kyawawan halayen Gwamna lokacin yana koyarwa. Ƙofarta da aka fara bugawa da ƙarfi ba kakkautawa yasa ta miƙewa da sauri tana faɗin lafiya? . Ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ne tana tsaye jikinta na rawa "Madam, your brother" "What happened?" "He has run mad" Har ta fito daga ɗaki sai kuma ta koma ciki da sauri ta buɗe closet tana neman hijabi. Ta jawo wani skirt tana ƙoƙarin sakawa kafin ta ankara cewa ba hijabi bane. Ta jefar da skirt ɗin ta ɗauko hijab ta saka ta fice waje. Tunanin Asiya ɗaya, Allah yasa ba wani Yaya Bello ya shaƙe ba, dan Yaya Bello idan ya sha abubuwansa bata gaya masa dai dai. Ba zata taɓa mantawa da lokacin da ya kusa sanadiyar bugawar zuciyar Ale ba. Ma'aikata da security sun yi cirko-cirko, wasu kuma na ƙoƙarin taro Yaya Bello da ke saman mota. Bilkisu Kachallah na wajen ta taɓe baki tana ganin drama. Babban mutum daya kusa cika shekaru arba'in shine ya ke a tuɓe daga shi sai wando three quarter yana tiƙan rawa a saman motan Bilkisu Kachallah. "Miya faru?" Asiya ta tambaya tana kallon Hansa'u dake gefen Bilkisu Kachallah. "kawai na fito raka Hajjajuna bakin mota sai muka ga ya zo da gudu ya hau saman motan yana tiƙan rawa wai shine wannan afton nan Krish" Bilkisu Kachallah ta juyo ta kalli Asiya tace " ƙusumbi, kurmanta, hauka, what else kuke da shi a zuri'arku?" Asiya ta kalleta cike da takaici tace "babu wanda yafi ƙarfin jarrabawar Ubangiji" "Hansa'u kai min jakata ɗaya motar, wannan da mahaukacin ya hau ta riga ta zama condemn" Hansa'u ta kalli Bilkisu sannan ta kalli Yaya Bello da wani security ya damƙo ƙafarshi ya jawoshi da ƙarfi har ya faɗo ƙasa, tim. Illar irin miyagun ƙwayoyin da suke shigowa da shi kenan. Shiyasa ranan data kama Nana da Zunnairah suna shan syrup bata gayawa kowa ba, saboda ta yarda cewa abinda Bilkisu ta shuka ne take girba. Ta wuce gefe tana faɗin "Allah ka bashi lafiya alfarmar Annabin tsira" Bilkisu ta bi bayanta tana murmushi. Sai da aka samu aka ɗaure Yaya Bello, sannan Asiya ta samu bayani akan ainihin abinda ya faru. Wai basu san miyasha ba, mai gyaran flowers bai iso ba sai ya ɗau kayan aiki ya je wai zai gyara flowers, ashe zuwa yai yana ta sare flowers ɗin yana tuɓɓuke jijiyoyinsu. Da aka zo aka hanashi sai yace zai je yai wanka, basu sake ganinsa ba sai da Bilkisu Kachallah ta fito zata shiga mota suka ga ya taho da gudu da shovel a hannunsa ya hau saman motar ya fara tiƙar rawa. Asiya ta kame kai tana salati, yanzu kowa a gidan ya san Yaya Bello na shaye-shaye. Ga damuwar abinda ya faru da Gwamna da ta sa kanta ciki tana fama da shi, ga kuma Yaya Bello anan yana so ya ƙara mata ciwon kai. Sai da ta ga an wuce da shi Quarters na ma'aikata kafin ta juyo ta kalli wani matashi da take ganin yana da matsayi a cikin security ɗin, ta masa kashedi akan idan har ta ga video na abinda ya faru a media sai ta sa an hukuntasu. Lokacin data shiga gida saura minti biyar a kammala shirin da take biɗa. Mutum ɗaya ta gani da yai bayani akan kirkin Gwamna lokacin da ya koyar da su. Ana ƙare shirin ta kira CY tace ya turo mata da interview ɗin ta gani. Tana magana da CY kiran Fou'ad Salisu ya shigo. "Hello akwai labari?" "Na samu labarin inda tsohon mijin Lami Ninja yake" "Ka mishi magana?" "Yana buƙatan kuɗi" "Kanbuuu! Gaskiyar da zai faɗa ma sai an biyashi" "Mutane kenan" "Ok nawa yake buƙata?" "Miliyan biyar amma ya bari a miliyan biyu" "He's crazy, manta da shi Fou'ad"... *** "Ina so a rufe case ɗin nan kafin ayi primary election. Na san kanada hanyar da zaka yiwa House magana su bi umurninka, ina so maganar Lami Ninja ya zama tarihi daga gobe Monday" "kasancewar Lami Ninja ta shigar da ƙara kotu ne, inaga sai kotu ta wanke Gwamna kafin House suyi wani abu akai. Akwai wanda zai binciko sirrinkan Lami Ninja nanda kwana uku, za'a iya amfani da haka wajen kashe maganar" Bayan tafiyar Kachallah. Yallaɓai ya shiga shafa gemu yana murmushi. Lallai Saifuddeen Kachallah ɗan gata ne. Gwamna na office ya kalli program ɗin da Hill TV suka watsa. Duk cikin mutanen da suka yi magana, mutum ɗaya kawai ya iya tunawa, wani mutumi wanda yanzu ya zama babban magidanci, loƙacin da ya koyar masa kusan shekaru goma ko shabiyu baya, sai daya maimaita course ɗinsa sau biyu a na ukun Prof Saifuddeen ya sa shi a gaba kaman ƙaramin yaro yana biya masa karatun da Hausa, a hankali yana masa haka har ya zo ya zamana duk wani darasi da baya ganewa sai ya kawowa Prof SSK ya biya masa koda ba shi ke ɗaukan darasin ba. Abubakar Talle sai daya maimaita shekaru biyu amma ranan da yai presenting project nashi yai bayani da Hausa da kuma Turanci kowa tafa masa yake saboda ya burge kowa, dalilin wannan project ɗin ya samu scholarship a ƙasar waje. Duk da ya jima basu haɗu ba amma ba a wata ɗaya ko biyu Abubakar Talle bai kira sun gaisa ba. Ya sani aikin Asiya ne, amma hakan bai burgeshi ba ko kaɗan. Zai fi so ma ace ta cire kanta daga wannan matsalar. Yana da yaƙinin cewa Allah daya kuɓutar dashi daga sharrin Lami Ninja shekaru shabiyar baya shi zai fitar da shi daga wannan ma. Shi yanzu ko da za'a tsigeshi ba zai damu ba, After all mulkin da komai ya fita a ransa. Sakatare daya shigo ne ya sa shi yin firgigit, ya ajiye jaridar Congo Daily a gabansa "Your Excellency ka duba shafi na uku" "Idan akan maganar nan ne ka ɗauke jaridan" "Sir?" "Ka ɗauke please" Sakatare ya ɗauka ya fita da shi. Ɗazu da Bilkisu ta kira shi ta masa maganar abinda aka rubuta a jaridar. Yana jin brief na abinda aka rubuta ya san Asiya ce. Ta rubuta cewa Lami Ninja karuwa ce Uwar Karuwai da take da gidan karuwai A Lagos.   *** Madam Bintu ta shigo ofishin Bilkisu Kachallah jiki na rawa. "Mi yake faruwa? Ya haka?" "Na ji labarin za ki tona asirin Lami Ninja" "Ofcourse, inada shaidah akan cewar tana fitar da mata yin karuwanci a ƙasar waje" "Hmmm! Bilkisu ki haƙura da batun nan" "Miya sa?" Madam Bintu ta sassauta murya tace " idan kika tona mata asiri, Umaru Kwom zai tona naki" "Ban gane ba?" "Yadda kike da hanyar nemo ɓoyayyun bayanai haka shima Umaru Kwom keda hanyar nemowa. Infact shiya kirani ɗazu yace idan maganar sex trafficking da Lami Ninja takeyi ya fito, zai fitar da namu sirrin" Bilkisu ta buga teburin gabanta tana faɗin "DAMN" Da bata shiga harkan ƙwaya ba shekaru biyar da suka wuce da babu yadda za ai Umaru Kwom yai mata barazana. Yanzu kenan ga samu ga rashi. "Ba zan bari a tsige Saifuddeen ba Bintu" "Bilkisu sai dai ta wani hanyar amma ba wannan ba"... Washegari ma an watsa shirin Asiya inda wasu ɗalibai daban suka sake bayyana kyawawan halayen Gwamna lokacin yana Malami. A kafar sadarwa ta twitter ma sai campaign ake yiwa Gwamna ana faɗin Gwamna bai da laifi. A washegarin ne kuma gidan rediyon 'Yanƙasa ta sako shiri inda mutanen da Umaru Kwom ya biya suka dinga muzanta Gwamna suna ɓata masa suna, akwai wanda yace ma lokacin yana ɗalibi Prof Kachallah ya ƙwace masa budurwa. "Damn it, CY, Umaru Kwom yayi amfani da rediyo saboda ya san zai fi shiga lungu da saƙo" A ɗaya ɓangaren CY yace " munada supporters a twitter" "Ba ka gane ba CY, wannan abin Kamfen ne. Koda ba a tsige Gwamna ba, Umaru Kwom ya riga ya ɓata mishi suna zai affecting zaɓe. Kasan mutane sunfi ɗaukan maganar ƙarya akan na gaskiya" "Zamu iya sa shirin a gidan rediyo muma" "Sai dai haka. Ina fata Fou'ad zai nemo wani abu akan Lami Ninja before it is too late. Sati ɗaya Gwamna keda shi, idan house suka voting ayi trial ka san idan Gwamna bai iya wanke kansa ba cikin watanni uku, automatically ya tafi kenan" "Mi zai hana ki je department ɗin daya koyar kiga ko zaki samu wani abu. Ai tace ya bata carryover ne saboda ya nemeta ta ƙi, if you can prove her wrong then inaga za a zargi maganarta" "CY ashe dai jinya da kayi bai taɓa maka ƙwaƙwalwa ba" CY yai dariya. Ƙarfe biyu na rana ta shirya ta fito. Tsayawa tayi chak lokacin data ganshi yana takowa. Tun ranan da sukayi magana bata sake ganinsa ba sai yanzu. Half jamfa ya saka na baƙin Geztner da baƙar hular Zannah, komai na jikinsa baƙi ne, takalmi, agogo da ma gilashin daya ɓoye idanunsa da shi. Yayi kyau sosai. Sai da ya zo daf da ita ta saka masa murmushi tace "sannu da zuwa Your Excellency" Hannu ya ɗaga mata ya wuce ba tare da ya amsa ba, ta shaƙi ƙanshin turarensa, ƙanshin ya shige har chan ciki ya fara kaɗa mata hanji. Ta rasa kunyarsa da take ji yanzu ne ya kawo wannan baƙon yanayin, ko kuma tun dama tanajin nannaɗewar hanji idan suka haɗu?. Taku biyu ta yi ta juya ta ƙara kallonsa, mutum biyu ne a bayansa wanda zasu rakashi zuwa ƙofa, kanshi zuwa ƙeyarsa kawai ta gani saboda ya kere securities ɗin tsayi. Tana shiga mota ta tambayi Yaya Bello ko ya sha wani abu kafin ya fito. "Yasin ba abinda na sha sai ruwa" "Ni dai kayi tafiya da hankali Yaya, idan kuma kana so a kaiwa Ale gawana ne to" Yaya Bello yasa dariya yace " yanzu kam ai kin zama ta Gwamna, ko mutuwa kikayi shi ke da iko da gangar jikinki" A take maganar Gwamna ya faɗo mata *"Ki faɗi koma minene, hakan ba zai chanja cewa daga yau gangar jikin, zuciyar da ruhin duka Allah ya mallaka min ba"* Da wani ido zata kalli Ubangiji idan ta mutu Gwamna bai yafe mata ba? A dai dai department na Political science Yaya Bello ya ajiyeta. Makarantan ya ƙara yiwa Asiya cika, rabonta da cikin makarantar tun watarana da tazo yin rahoto lokacin da ɗalibai sukayi riot saboda 'yan cult sun kashe wani ɗalibi. Sau ɗaya ta taɓa zuwa department ɗin saboda akwai wani course da sukayi da 'yan Pol Science lokacin tana aji huɗu. Ba ta san Prof SS Kachallah ba a lokacin saboda a shekarar ya ajiye aiki. Ita ɗaya ta fito daga motar ta nufi cikin department ɗin. Ba kamar Bilkisu Kachallah ba, tunda ta zama Matar Gwamna duk fitar da za ta yi ita ɗaya ko kuma ita da Sumayya suke fita. Bilkisu idan zata fita to da motoci biyu ko uku ne, tareda securities da mai ɗauka mata jaka. Wasu ɗalibai da suka fito daga cikin department ɗin suna ganinta suka fara ihu "Wow! First lady ce, Asiya Kachallah" Saboda ma kar a ganeta da wuri yasa ta saka ƙaton glass ta toshe fiskanta, amma duk da haka sai da aka ganeta. Ta tambayi ɗaliban suka nuna mata ofishin HOD. Sakatariyar HOD na ganinta ta miƙe jiki na rawa ta mata iso zuwa ofishin HOD. Matsayi kenan, da ace bata auren Gwamna bata tunanin wannan tsohuwar matar za ta yi rawar jiki dan tana neman ganin HOD. "Sunana Asiya Shahidah Faruƙ Baba, MATAR GWAMNA" Asiya ta faɗa lokacin data zauna. HOD ya gyara zaman gilashinsa daga kan hanci zuwa ido yace " sannu da zuwa Excellency" 3 Kafin Asiya ta fara magana wayarta ya shiga ƙara. Ganin Sumayya ne ke kira ya sa ta katse kiran ta saka wayar a silent. "Dr Nuru ina neman haɗin kanka ne bisa wani bincike da nake yi" "Bismillah Hajiya" HOD ya faɗa yana rarraba ido. "Ina son ganin file ɗin wata ɗaliba mai suna Lami Haladu, ba sai nayi dogon bayani ba kasan wa nake nufi. Sannan ina son ganin exam scripts ɗinta na shekarar 2000, abu na ƙarshe kuma ina son sanin wanene Dean na faculty da kuma HOD na department a shekarar" "To Ranki shi daɗe naji daɗi ƙwarai da zuwanki, abinda zan iya faɗa shine scripts na jarrabawa basa wajenmu a yanzu haka, ana kaiwa exam and record ne, dan haka ba zan iya cewa ga inda za a samu script na Lami Haladu ba amma zan iya sawa aje a duba miki ko akwai ko babu. Abu na gaba kuma ki bani minti ɗaya na duba wani file" Dr Nuru ya miƙe ya je wajen shelf ɗin dake office ɗin ya fara dube-dube. Kusan minti uku bai samu ba, ƙarshe sai ƙwalawa Sakatariyarsa kira yai. Miss Ifunanya na zuwa ko sakan talatin bata yi ba ta fito masa da file ɗin da yake nema. Dr Ɗanladi shine HOD a lokacin kuma ya riga yayi retire sannan shekaru biyu kenan da rasuwarsa. Shima Dean ɗin lokacin ya jima da rasuwa. Asiya ta sauke ajiyar zuciya tana tunanin abinda za tayi. Mutumin da aka aika ya je exam and record ya dubo script shine yanzu kawai zaɓinta. Kusan minti goma shabiyar sai ga shi ya dawo. Ƙasaƙasa yaiwa HOD bayani, bayan ya gama HOD ya gaya mata cewa babu scripts na shekarar 2000 duk an riga an ƙona su wanda suke ƙasa daga shekarar 2007 ne. Gwiwa a sace Asiya ta fito daga department ɗin ta nufi wajen motarta. Bayan ta shiga motar ne ta kira C Y ta faɗa masa cewa bata samu abinda ta je nema ba. *** "Anty lissafin mi kike ne?" Sumayya ta tambaya tana riƙe ƙugu Asiya bata kulata ba, ta cigaba da rubuta ranaku tana lissafin yaushe ne ranakun girkinta. Gwamna bai fito ya raba musu kwana ba amma lokacin tana chan gidansa satinta ɗaya ya koma yana zuwa yai mata kwana biyu duk da ma ba wai ta sa masa ido bane amma lokaci zuwa lokaci Sumayya na faɗa mata cewa Gwamna ya kwana a gida yau. Bayan kusan minti shabiyar sannan ta samu bakin zaren, idan lissafinta ya tafi dai dai to gobe zata karɓi girki. Abu ɗaya take so a wajenta shine ya yafe mata abinda ta aikata. Babu sallama babu komai Bilkisu Kachallah ta shigo ɗauke da jarida a hannunta, tana zuwa ta jefa gaban Asiya da ta bararraje a kan kafet. "Fix this, matsalar Lami Ninja ya ishemu ba sai an haɗa da taki ba" Asiya ta ɗauki jarradar ta kalli hoton da ke gaban jaridar. Hotonta ne ita da Gwamna ranar dinner aurensu daidai wajen da take shirin faɗuwa Gwamna ya tarota. Tana ganin headline ɗin ta ɗago ido ta kalli Bilkisu wacce itama ido ta zuba mata. Asiya ta sake maida dubanta ga jaridar ta buɗo shafin da akayi rubutu ta fara karantawa. Bata san tana hawaye ba sai da Sumayya tace "Anty mi aka rubuta? Anty lafiya?" Asiya ta yi saurin miƙewa ta je ta ɗau wayarta da ke kan gado. Numbar dai da suke communicating da Umaru Kwom ta buga. Ana ɗauka kafin ta yi magana yace " kinga saƙona?" "Ka san zan iya yin ƙarar jaridar Climax. Ka san zan iya ƙaran ƙazafi da kuka mana" "Ahaf na ɗauka ai so kike ki rabu da mijinki" "Babu ruwanka da rayuwata, sannan ka sani Insha Allahu babu wanda zai tsige Mijina" "Bana tunanin kinada ikon yin komai. Fou'ad Salisu kike taƙama da shi kuma na dakatar da shi daga yi miki aiki" "Da Allah na dogara ba da Fou'ad ba kuma Allah yana tareda masu gaskiya" "Idan na hau kujera zan iya shigo dake a ta huɗu" "La'ananne" ta faɗa tana kashe wayar. Sai kuma ta fashe da kuka. Dama wutar fitina kunnata kawai zakayi amma baka isa ka ce ga inda zata je ko kuma ga inda zata tsaya ɗinba. Ga shi dai Jaridar Climax da ta rinƙa yi musu rubutu a ɓoye tana zagin Gwamna tana aibata shi da iyalinsa sai gashi yau itama Jaridar ta kirata Karuwa sannan ta auri Gwamna da ciki. "Anty" Sumayya ta dafa kafaɗanta. "Sumy ya zanyi?, komai ya lalace mini, idan aka tsige Gwamna ban san da wani ido zan kalleshi ba. I'm confused" "Addu'a za ki mishi, In Allah ya yarda gaskiya zata fito" Asiya ta cigaba da sheshsheƙar kuka sai ga wayarta ya sake ƙara. Baƙuwar number ne kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka. "Hello Fou'ad ne" "Fou'ad na ji ka shiru, mi yake faruwa?" "Umaru Kwom yana bibiyata. Numbar ƙanwata ce wannan idan na samu evidence zan kiraki da numbar, but kafin nan kar ki kirani" "Amma...". Kiit aka kace wayar. *** A chan gidansu Asiya. Hankalin Umma ne ya tashi saboda Hindatu ta nuna mata abinda aka rubuta a jaridar Climax. Tunda aka fara maganar Asiya da Gwamna bata iya baccin kirki sai da akayi bikinta, ɗan kwana biyu da ta fara sakewa kuma gashi an sake kawo wani zancen. Ta dai karɓi ƙaddara ne amma zuciyarta bai so auren Asiya da Gwamna ba. Ƙarshe da ta ga damuwa zai jawo mata illa sai ta ɗau ƙur'ani ta fara biyawa... A chan Jami'ar Congo kuwa CY ne da Yaya Bello suke tsaye da wani guntun mutum wanda ke rarraba ido alamar marar gaskiya. "Mr Silas yanzu dai kana nufin akwai script ɗin Lami Ninja a ƙasa" "Na rantse da jinin Yesu yana nan. Lokacin da aka ce mu je mu tattare scripts na shekarar 2000 mu ƙona na san saboda case ɗin Gwamna ne shiyasa na cire nata na ɓoye" "Kenan akwai script na course ɗin da ake magana akai?" "Duka scripts na first and second semester nata na sace" "Ina suke?" "Oga Clement you know nah. 5M to my account zakuga script" Yaya Bello da ba wai ya gama gane maganarsa bane yace " amma kasha giyar wake, akan takarda za a baka miliyan biyar" "Oga Clement, idan ba za ku iya bayarwa ba zan kai wa waɗanda zasu biya" "Za mu tura maka daga nan zuwa dare" "Haba baƙin Inyamuri..." CY ya sa hannunsa na ƙarfe ya dafa kafaɗar Yaya Bello yace " takardun sun fi kuɗin mahimmanci, ka barshi" Bayan Mr Silas ya bada account numbarsa sannan ya bar wajen, yana tafiya yana waige-waige. "Dan kawai dukkanku ba kwa Sallah shine zaku cuci ƙanwata. Kwaranƙwasi babu wanda zai bashi miliyan biyar koda Gwamna ne da kansa kuwa. A barni na buge shege wallahi sai ya fitar da takardun nan" C Y yai dariya duk da maganar Yaya Bello ya ɓata masa rai. Da ya san matsayin Asiya a zuciyarsa da babu abinda zai sa ya ce wai zai cuceta kuɗi. Duk da ya rasata har Abada, duk da ta kasance Mallakin wani hakan ba zai hanashi taimaka mata ba, koda kuwa zai rasa rayuwarsa ne. Lokacin da Asiya ta gayawa CY cewa ta zo makaranta ance an riga an ƙona scripts ɗin shekarar shine ya jarraba tasa basirar. Maimakon ita da taje wajen manyan department shi ya bi ta wajen wanda suke ƙasa ne, mutanen da sune ke sanin duk wani shige da fice na department ɗin. Bai sha wahalar gano cewa Mr Silas shine ya fito ya dinga ihu ya tara mutane lokacin da ya shiga office ɗin Prof SS Kachallah ya ganshi suna kokawa da Lami Ninja ba. Yanzu da suka yi magana da shi ya sake tabbatar da cewa akwai hannun Mr Silas a abinda ya faru tun shekaru shabiyar da suka wuce, idan ba haka ba taya zai san mahimmancin scripts ɗin Lami Ninja har ya ɓoye su kafin a ƙona. Sai da suka shiga mota CY yace da Yaya Bello idan yana son dukan Mr Silas to ya shirya zuwa dare, Yaya Bello yace yanzu na ji magana. CY ya ɓoyewa Asiya komai ne saboda baya son sa mata rai a zo ba a samu komai ba, gara kawai sai komai ya tabbata kafin ya sanar da ita. *** Yau lauyoyin Gwamna dana Lami Ninja zasu gana. Close case za'ayi, dan haka daga Lauyoyi, Alƙali sai shaidun mai ƙara da wanda ake ƙara. Tunda Asiya ta tashi da Asuba bata koma bacci ba, tana gama Azkar ta wuce main kitchen inda ake dafa abincin iyalen gidan, ta taɓa duba wajen sau ɗaya amma wannan karan ba wai ta je dan ta leƙa bane, ta je dan tayi girki ne. Chief cook ɗin namiji ne dan haka ta sallameshi akan ita za tayi abun kari. Daga ita sai Hansa'u da Sumayya da ta biyota suka fara shirya komai. A wajen Hansa'u ta samu bayanin yadda ake tafiyar da girki a gidan. Ba koyaushe Gwamna ke karyawa ba kafin ya fita, musamman ma ranakun Litinin da Alhamis da yake yin Azumi. Sunada menu da suke bi sai dai idan Bilkisu ta bada specific na abinda za a mata. Bayan sun gama komai aka jera abincin a dining room inda suke haɗuwa su ci abinci. Ƙarfe bakwai da rabi ta buga ƙofar ɗakin Gwamna jin ba a amsa ba yasa ta kutsa kai cikin ɗakin. Yana tsaye gaban madubi yana taje gemunsa. Ta madubi suka haɗa ido amma yai kaman bai ganta ba ya cigaba da abinda yake. "Ina kwana" ta yi maganar tana kallon ƙasa dan tun da ta ga idonsa ta madubi ƙirjinta ya shiga taka rawa a cikin ƙirjinta. "An shirya maka abin kari, Junior yana jiranka" "Ba aikin ki ba kenan" "Na sani amma ina so na yi" "Bana buƙata" "Dan Allah ka yi haƙuri, na san abinda aka rubuta a jaridar Climax zai dameka amma..." "Ba yau jaridar Climax ta fara rubutu akan abinda zai dameni ba" Ta yi shiru ganin ya juyo yana fiskantarta. "Matsa min" "Na'am" ta faɗa cikin rashin fahimta. Ta gefenta ya bi zai wuce ta riƙo hannunsa. "Allah ya bada nasara" Cikin zuciyarsa ya furta Amin ya cire hannunsa cikin nata ya fita. "Anya damuwa bai fara taɓa min kwanya ba kuwa?" Asiya ta tambaya bayan fitan Gwamna. Ba ta san dalilin riƙe hannunsa da tayi ba, bata ma san dalilin da ya sa take son faranta masa ba yanzu. Ta ɗauka ba zai tsaya karyawa ba amma sai ta ga ya zauna Hansa'u tana shirin serving ɗinsa. Asiya ta yi saurin ƙarisawa wajen ta ce "Hansa'u jeki kawai" Hansa'u ta ajiye serving spoon ɗin ta bar wajen. Gwamna yana riƙe jarida yana dubawa amma hankalinsa na kansu. Bayan ta gama zuba mishi soyayyen dankali da miyar hanta sannan ta ajiye masa toasted bread da shayi a gefe. Zama ta yi gefen Junior da yake cin noodles da ƙwai ta shafa kansa sannan ta ɗau plate ta fara serving kanta. Krit krit krit krit ƙaran takalmin Bilkisu ya sanar da shigowanta dinning ɗin. Ta kalli Asiya sannan ta zauna gefen Gwamna tana faɗin "ina kuma Hansa'un ta shiga yau" "Hansa'u, Hansa'u" "Hancha'u where are you?" Junior ya taya Bilkisu kira Hansa'u ta fito da gudu kamar dama a ankare take. Asiya ta tsaya kallon mamaki wai ga abinci a gaban Bilkisu amma sai mai aiki ta fito daga wata duniya ta zo ta zuba mata a plate. "Miyasa aka yanka dankalin manya?" Hansa'u ta fara sosa kai tana inda inda. "Wuce ki bani waje" Bayan tafiyar Hansa'u ta kai lomar abinci sai ta tsaya, kaman za ta ce wani abu akan abincin sai kuma ta fasa. "Barrister Waziri is the best, Darling kar ka ji komai, we'll win this case" ta riƙo hannunsa tana murzawa. "Daddy yaushe Nana da Mayrah za su dawo" Junior ya katse kallon-kallon da ake tsakanin Bilkisu da ke riƙe da hannun Gwamna da kuma Asiya da ta kasa sauke idonta daga kallon Bilkisu zuwa hannunta da ke kan na Gwamna. "Daddy zan je wajen Dadda nima" "Ba inda zaka je, suma su Nanan sun kusa dawowa gida" Gwamna bai ƙare cin abincin ba ya miƙe ya ce ya tafi. Bayan tafiyarsa Bilkisu tace "gurin shiga kike nema a wajen Darling" ta ƙyalƙyale da dariya sannan ta cigaba "idan aikin girki kika zo yi, zaki iya komawa Quaters ɗin mai'aikata saboda nan yafi dacewa da ke, " "Indai kullum zai dinga cin girkina zan so komawa Quarters ɗin" Bilkisu ta sake bushewa da dariya wannan karan har sai da ta ƙware... *** Zaman da akayi bai haifar da ɗa mai ido ba saboda Lauyoyin Gwamna ba su iya bada ƙwararren shaida da zai ƙaryata iƙirarin Lami Ninja ba, haka aka sake ɗaga zaman zuwa wata sati. Gwamna yana duba wasu takardu COS ya shigo ya sanar da shi zaman da aka yi bai yi wani tasiri a case ɗin da aka yi ba kuma House gobe za su kada ƙuri'a ko a fara trial ko kar a fara . Gwamna yai kaman bai ji shi ba ta hanyar sako zancen wani project da yake so ya fara. A chan gidan Mr Silas ana jimamin rashin ganinsa sa da ba ayi ba tun daren jiya. A ɓangaren mutanen Umaru Kwom ma sun shiga ruɗu saboda suna tunanin za su sameshi daren jiya akan za a kira shi shaida a kotu sai suka tarar baya nan, kuma ba a san inda ya shiga ba. An riga an biya shi Miliyan biyu saboda aikin da zai yi. Sai gashi kuma ya saɓa alƙawari.   Gwamna daga office Rehab center ya wuce inda aka kai Nana. Ita Zunnairah ƙasar waje mahaifiyarta ta kaita. Sai yanzu da Nana ta shiga withdrawal stage ya ganta cikin yanayi na hauka ya ji hankalinsa ya tashi fiye da ma lokacin da ya gano tana shaye-shaye. Zuciyarsa a cunkushe ya dawo gida bayan ya mata addu'ar samun lafiya. Yana shiga falonsa ya tarar da Asiya tana zaman jiransa. "Mi kike nema?" "Ina so Dan Allah ka bani dama naje Lagos" "Kin saba yin abinda kike so" "Ka yi haƙuri" ta faɗa tana kallon ƙasa saboda ba za ta iya dubansa ba, tana buƙatar zuwa Lagos ko akwai abinda za ta iya samu akan Lami Ninja. "Akwai abinci a dining ko na kawo nan?" Ta faɗa lokacin da take shirin shigewa. Bai amsa ba ya wuce ya barta tsaye. Bisa mamakinta tana cin abinci da junior ya zo ya zauna ta serving nashi. Har suka gama ci Bilkisu bata ɓullo ba, kamar ma bata gidan. Lokacin da ta shiga ɗaki ta fara haɗa kayanta Sumayya ta tambayeta ina kuma za ta je, tace mata Lagos. "Anty Asiya kinada gajen haƙuri Allah. Yanzu ana cikin matsala za kiyi tafiya, idan wani abu ya sameki fa" "Ba ruwanki da ni, ba zan iya zama komai ya lalace ba" *"Kinada taurin kai Asiya, Ba kya jin shawara a rayuwarki, babban matsalarki kenan"* ta tuno kalaman Ubayd. Ta zauna bakin gado riƙe da gyale a hannunta. Sumayya tayi gaskiya, Fou'ad yace zai nemeta idan ya samu evidence, C Y yace mata ta kwantar da hankalinta akwai abinda ya samu amma sai ya tabbatar da komai zai gaya mata. Miyasa ba za ta iya jira ba? *not edited* 4 Wani ƙyamusasshen mutum ne zaune a kan Buzu yana muimui da baki alamar yana magana da Ruhanai ko Aljanu. Ya kai kusan minti biyar yana buga ƙasa, yai rubutu akan ƙasar da ke kan wani faifai ya share, ya sake wani rubutun nan ma ya share. Bayan ya gama bincikensa sai ya ɗago ya kalli mutumin dake gabansa yace "Akwai wata mace a jikinsa, tana da ƙarfi sosai, tauraronta yana da haske. Matuƙar tana tare da shi sai dai bai nemi abu ba amma yana nema, ya samu. Ita ɗin irin matan nan ne da aka haliccesu da baiwa, duk wanda suka raɓa sai rayuwarsa ta chanja, irinsu da za su auri faƙiri da bashi da anini, to da sannu sai ya samu wadata" "Malam wace macece kenan? Matarsa ce ko 'yarsa, ko kuma wa? Sannan kana nufin Umaru Kwom ba zai samu nasara ba?" Mutumin ya ƙyalƙyale da wata irin dariya marar daɗin ji, idan ka saurari dariyar da kyau ka ɗauka tsuntsuwa ce ke kuka. Bayan ya gama dariyar sai kuma ya haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba. "Kai! Ubangiji kaɗai ke da sanin Gaibu. Wacece ita? kamanninta, ina take? Banida amsar su. Abunda aka faɗa mini shine, ita ɗin kariya ce a gareshi kuma zai ɗaukaka fiye da tsammani matuƙar tana tare da shi. Kabar batun tsige shi, an hasko mini shi akan kujerar mulki" Mutumin da aka faɗawa maganar ya shiga ruɗu yana neman agaji ko akwai abinda za a iya yi. Malam Nawaso ya fatattake shi daga wajen, yana faɗin shi aikinsa yana da iyaka, kuma ya riga ya faɗa masa abinda ya zo tambaya. Tunda ya bar wajen Malam Nawaso, ya shiga jujjuya maganar a ransa, yana neman ta yadda zai faɗi maganar ba tareda ya ɓatawa Umaru Kwom rai ba. Lokacin da ya isa gidan Umaru Kwom, kasancewar akwai kusanci tsakaninsu bai tsaya wata-wata ba aka masa iso a falon Alhaji Umaru Kwom. A ƙasan carpet ya zauna yana jiran fitowar Maigidansa. Minti bakwai sai ga Alhaji Umaru Kwom ya fito sanye da farar riga 'yar shara da wando. Tun kafin ya zauna mutumin ya shiga yi masa kirari yana faɗin sai ka yi Gwamnan Jahar Congo. Umaru Kwom ya zauna akan kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya yace "Bature kai ne da dare haka. Fatan ka taho min da labari mai daɗi" Bature ya haɗiyi yawu maƙwot sannan ya fara washe baki yana zuba bayanin da ya tsara kafin tahowarsa. "Ai Excellency, Malam Nawaso ya kai inda mutane suke maganarsa. Yace akwai nasara a tafiyarka, sai dai kuma..." "Ka faɗi koma minene, ba yau muka fara jin labarai marasa daɗi ba " Bature ya kaɗa baki ya cigaba da bayani " ya faɗamin cewa ɗaya daga cikin matansa tana da asiri mai ƙarfi a tattare da ita, ba zata taɓa bari Saifuddeen Kachallah ya faɗi a zaɓe ba. Yace ba za a tsige Saifuddeen Kachallah ba, sannan idan lokacin zaɓe ya zo za ta yi komai wajen ganin mijinta ya ƙara hawa kujera" Jiki na rawa Umaru Kwom yace " akwai mafita? wani mafita ya bayar? sannan waccece a cikin matan nasa?" Bature ya gyara zamansa, ganin haƙarsa ta soma cimma ruwa. "Ai wato Malam Nawaso bai bayyana wacece a cikin matan ba, amma inaga ba zai wuce Bilkisu Kachallah ba dan matar nan da ka ganta ka ga hatsabibiya" Ya karya murya ya cigaba " Malam ya buƙaci wasu abubuwa da za ayi amfani da su wajen yaƙar wannan Asirin. Yace akwai sadakar da zai sa ayiwa Aljanu kaman miliyan goma, saboda su dinga yi maka addu'a har ranan zaɓe" "Nawa yake buƙata?" "Ranka shi daɗe ya buƙaci kuɗi dayawa fa" Bature yai maganar yana sosa kai. "Na ce nawa ne?" "Miliyan goma cash" "Shine kuɗi dayawa. Zan sa a haɗa maka shi gobe da safe sai ka kai masa. Ka tabbatar yayi duk abinda ya dace" Bayan tafiyar Bature. Umaru Kwom ya zauna yana nazarin waccece a cikin matan Saifuddeen. Wani zuciyar na riya masa cewa Bilkisu Kachallah ce, amma kuma Asiya ma akwai alamar tambaya akanta. Yana da labarin ita ɗin jikar wani babban malami ne maiƙusumbi. Malaman zaure kuma akwai su da sirrika, ƙila kafin Kakanta ya rasu ya bata wasu laƙanin ƙarfi. Bai manta yadda take masa magana babu tsoro bare wani ɗar ba jiya data kira shi. Koma minene dai wannan zaɓen sai ya lashe, ko ta yanene... *** "Baba, mi kake yi akan wannan zancen?. Monday fa House za su voting, kuma kasan saboda wannan abun waɗansu sun fara maganar kar a bari Saifuddeen ya tsaya takara. Primary election is this Saturday amma saboda wannan abin an sake kaishi wata sati. I can't stand this" Bilkisu ta faɗa cike da damuwa a ranta, abu ɗaya da zata yi ta warware wannan maganar kuma zai iya jawo a bankaɗo nata sirrukan, shima kuma scandal ne da zai kawo wa Saifuddeen matsala a kujerarsa. "Kin san dai ba zan zuba ido a tsige Saifu ba ko, dan haka ki kwantar da hankalinki" "Baba there's no time" " na yi waya da shugaban ƙasa, sannan mun zauna da party chairman na ƙasa, sun tabbatar mini House zata dismissing trial ɗin. Matsalar da zamu fiskanta shine, dole kotu ta wanke Saifu kafin zaɓe idan ba hakaba, zamu bar giɓi mai faɗi da Umaru Kwom zai yi amfani da shi wajen Kamfen" "Indai aka warware maganar impeachment shikenan, sauran mai sauƙi ne" Da haka ta ɗau kofin shayi ta kai bakinta ta kurɓi kaɗan, zafin daya ratsa harshenta ko kaɗan bai kai zafin da take ji a zuciyarta ba, saboda fargabar barin kujerar first lady of the state. Zumar da ke ƙunshe cikin kujerar Mulki tanada wuyar sha'ani, saboda zaƙi da daɗinta. Da ka ɗanɗana, ko da ɗan kaɗan ne, to sai kayi da gaske kafin ka iya rabuwa da shi. Alhaji Sani da 'yarsa dukkansu sun ɗanɗani zumar Mulki kuma sun san zaƙinta, ba abinda suka rasa na kuɗi da dukiya amma Mulki...suna son wannan Mulki ya kasance na su, har zuwa lokacin da aka ɗiba. Yayinda ake cikin wannan kuma, an sako Mr Silas ya dawo gida. Mr Silas ya sha bugu a hannun Yaya Bello kafin ya faɗi gaskiyar lamarin abinda ya faru shekaru shabiyar da suka wuce. Lami Ninja ne ta biyashi kuɗi akan ya bar mata ƙofar ofishin Prof Kachallah a buɗe. Sannan shine ya tsaya stand by akan idan Saifuddeen ya fito ya saka masa ihu, ya tara masa mutane. Domin idan ya amince da buƙatarta ita zata fara fitowa daga office ɗin ba shi ba. A ranan da Lami ta far wa Saifuddeen, da ƙyar ya samu ya turata gefe ya buɗe ƙofa ya fita, yana fitowa Mr Silas ya tareshi a bakin ƙofa yana faɗin wai ya ji ihun mace a cikin office ɗinsa. Lami na jin Mr Silas ya iso ta saka ihu tana kuka tana kururuwa, hakan ya sa Mr Silas ya riƙe Saifuddeen yana yekuwa har mutane suka taru. Da ke Saifuddeen bai iya magana cikin hayaniya ba haka aka fara maida zancen ƙarya, ya kasa kare kansa. Lokacin da aka yi case ɗin ya ƙaryata abinda ya faru amma duk da haka an rufe case ɗin ne ba tareda an yi dogon bincike ba saboda akwai masu yiwa Saifuddeen hassada cikin Malaman faculty ɗinsu... Mr Silas na dawowa kuwa wasu mutane suka zo suka tafi da shi gaban Umaru Kwom. Ya sha bugu kam dan ƙafafuwansa da ƙyar yake taka su. Ga bayansa da yake ji kamar an fafe ne aka bar masa ƙashin bayan kawai a waje. "Mi suke buƙata a wajenka?" Ko bai tambaya ba ya san cewa Bilkisu Kachallah ce da wannan aikin. Baki na rawa Mr Silas yace " suna so na faɗa musu gaskiyar abinda ya faru ne 15 years back" "Ka faɗa musu?" "Ranka shi dade ba dan duka na faɗa ba, sun ce za su kashe family ɗina." "Yanzu dai ka faɗa musu komai?" Mr Silas ya karya wuya yace " i'm sorry" Wani da ke gefen Umaru Kwom yace "Ranka shi daɗe ai magana ta tashi kenan, tunda na san zasu naɗi abinda ya faɗa" Umaru Kwom yai murmushi yace " gaba ta kaimu ai, we can still use it against them. Idan suka kawo confession ɗinsa mu kuma sai mu bayyana cewa sace shi aka yi aka gana masa azaba, shiyasa ya faɗa musu abinda suke son ji" Mutumin yai murmushi. Bayan an fita da Mr Silas. Umaru Kwom ya faɗawa muƙarrabinsa cewa aje a ƙara dukan Mr Silas a ɓata masa fuska sannan a kaishi Asibiti sai a ɗauki hotonsa a gadon Asibiti, ya ƙara da cewa "Ku faɗawa Gideon ya rubuta headline mai kyau a jaridar gobe" Lokacin da wani ƙaton bodyguard mai zubin Samudawa ya mari fiskar Mr Silas da kacha, sai da haɗoransa biyu suka zube ya faɗi ƙasa a sume. Da ya farfaɗo a gadon Asibiti ya tsinci kansa an ɗaure masa fiska hannu da ƙafa. Abinda Yaya Bello ya masa ashe ba komai ba ne akan bugun daya sha a gidan Alhaji Umaru Kwom. *** "CY ba ni da bakin yi maka godiya" "Anything for you Aseey. Oops! Excellency" "Kai bana son Excellency ɗin nan. Har yanzu Aseey ɗin da ka sani ce" "A'a rufa min asiri. Ke yanzu tsauni ce ni kuma ɗan ƙaramin dutse" "Thank you my brother from another mother" "Kai! you should thank your brother ooo. Ba dan shi ba inaga Mr Silas ba zai faɗi komai ba" "Ai Yaya Bello. Allah dai ya shirya mana shi"... Bayan sun rabu da CY Asiya ta godewa Allah da bata yi gaggawar tafiya Lagos ba. Shiyasa aka ce gaggawa aikin Shaiɗan, gashi da ta sallamawa Allah komai sai gashi ta hango nasara. Washegari da safe bayan ta bi dare tana addu'ar Allah ya taimaketa ta warware wannan matsalar kafin Gwamna ya saketa sai ga kiran CY yana faɗin ya kamata su haɗu akwai abunda zai nuna mata. Ba shiri ta shirya ta wuce shagonsu tace Yaya Bello ya koma gida zata kira shi idan ta gama. A office ɗin Queen Bee ta saka dogon hijab da niƙaf, ita da Queen Bee suka wuce wajen da CY yace su sameshi. Ganin CY tareda Yaya Bello sai abin ya ɗaure mata kai. "CY mi yake faruwa?" "We've got the script" ya faɗa yana murmushi. "Dan Allah?" "Ashe akan wasu tsohin litattafai har ake ɓatawa Gwamna suna" Yaya Bello ya sa baki. "Yaya Bello ba zaka gane ba" Bayan ta zauna ne suka mata bayanin Mr Silas da kuma sato shi da suka yi har suka samu wasu bayanin ma da basu tsammanta ba. "Mun yi recording confession nasa, za a iya presenting a kotu ai" Asiya tayi shiru. "Ya ba kya murna?" "Umaru Kwom ba wawa bane. Ɗan siyasa ne, he will manipulate the evidence, hakan zai ƙara dagula lamari" "To kawai mu presenting script ɗin ba tareda an bayyana abinda Mr Silas ya faɗa ba" Asiya ta yi shiru na kusan minti huɗu tana nazari, chan kuma tace " i have a plan"... *** Washegari jaridar Climax ta fitar da hoton Mr Silas kwance akan gadon Asibiti cikin mawuyacin hali. Aka rubuta cewa Gwamna ne ya sa aka sace shi saboda kar ya faɗi gaskiya a kotu, domin shekaru kusan goma shabiyar da suka wuce shine ya kama Gwamna yana cin zarafin Lami Ninja. "Your Excellency jaridar Climax tayi sabon rubutu" Gwamna ya kalli COS yace " bayan since na auri Asiya da ciki, me kuma ya rage, sun gano ina da 'ya'yan shegu a waje ne?" Ya ƙarisa maganar yai dariyar takaici. "Ka karanta Sir" Gwamna ya jawo jaridar ya fara karantawa. Cikin ɗayan biyu ne, ko Alhaji Sani ne da wannan aiki ko kuma Asiya. Ya naɗe jaridar ya jefata cikin kwandon shara. "Akwai matsala Excellency, an fara kirana daga Gwamnatin tarayya ana son sanin gaskiyar wannan magana" Gwamna ya ajiye biro ya ɗago ya kalleshi yace "akwai hukumar bincike ai, wannan ba aikin ka bane" COS ya hangame baki yana kallon ikon Allah. Bai san wani irin zuciya ce da Gwamna ba. Ta ya zai iya kwantar da hankalinsa a yanayin da ake ciki. Yana zaune akan kujerar da take gargada tana shirin kifar da shi amma ko ajikinsa... Kiran da Alhaji Sani ya masa yana tambayar ko ya ga abinda aka rubuta ya tabbatar masa babu hannunsa a ciki. Can she be this cruel? Shin a dalilinta na son ganin ta goge laifinta a wajensa, za ta iya yin wannan abu? Da fargabar sanin zai iya yiwuwa ita ta aikata hakan ya je gida. Asiya na waya Hansa'u ta shigo ɗakinta da sallama. Ganin ta shigo ya sa Asiya ta juya harshenta zuwa turanci dan kar Hansa'u ta ji abinda ta ke faɗa. Hansa'u ta yi murmushin gefen baki, Yare biyar ta ke ji: Hausa, Fillanci,. Turanci, Larabci da Faransanci. Da Asiya ta gama wayar ta kalli Hansa'u tace "lafiya?" "Mai Girma yace wai ki sameshi a falonsa" "Gwamna ya dawo?" Ta tambaya dan ba ta taɓa gani ya dawo da wuri haka ba, ƙarfe shabiyu ta ɗan wuce ne yanzu, ko zai dawo da wuri to irin ƙarfe huɗun nan ne. "Na ji". Riga da wandon jeans ne a jikinta dan haka ta ɗauko Abaya ta saka akai. Ba ta sameshi a falonsa ba, dan haka ta wuce ɗakinsa kai tsaye. A tsaye ta sameshi yana kallon bango, ya goya hannunsa baya. "Assalamu Alaikum, Barka da dawowa" Ta yi minti biyu tsaye kafin ya juyo ya kalleta, tayi saurin sauke idonta ƙasa saboda yadda ta ga fararen idanuwansa sun rine sun koma ja. "Ki gaya min gaskiya. Kinada hannu a abinda ya faru da Mr Silas Isege?" "Ehm...Ehm..." "Answer me!" Ta yi saurin matsawa baya saboda firgita da tayi. "Na ce ki cire hannunki, na ce bana buƙatar taimakon ki, miyasa kike da taurin kai ne?" "Ba gaskiya jaridar Climax ta faɗa ba, ba a ji masa rauni har haka ba..." "Ki je gida" "Hahn!" "Ki je gidanku zan nemeki" 'Ka yi haƙuri Dan Allah, zan maka bayanin komai idan aka warware wannan case ɗin' abinda ta ke son faɗa kenan amma kalmomin sun tsaya a maƙoshinta sai ma hawaye da ta ji ya ciko mata yana barazanar saukowa. Tayi saurin ficewa daga ɗakin ba tareda ta furta komai ba. Bayan ta fita Gwamna ya sauke ajiyar zuciya yana tunanin wannene cikin shawaran da zuciyarsa ke bashi zai yi. Ya datse igiyar da ke tsakaninsu ne ko kuma ya cigaba da haƙuri da ita zuwa lokacin da Allah zai gyara tsakaninsu?... Ta san zai iya fushi da ita amma ba ta san irin wannan matakin zai ɗauka ba. Ta san ko ba daɗe ko ba jima zai saketa saboda abinda tayi masa ya kai ya rabu da ita har abada. Sai dai atleast ta ɗauka zai haƙura zuwa a warware matsalar da take ƙasa tukunna. Ta haɗa kayanta dana Sumayya ta kira Hansa'u tace ta fita mata da su waje. "Hajiya ina za ki je?" Hansa'u ta tambaya data ga akwatunan. "Zan koma ɗaya gidan ne" "Ai nan ma gida ne" "Nan gidan Gwamnati ne Hansa'u, ba a zama a cikinsa na din din din" Hansa'u na fita ta kira Sumayya tace idan ta bar makaranta ta wuce gidan Abba. Da ta cewa Yaya Bello ya kaita gidan Abba, tambaya yai ko lafiya? tace masa lafiya. "Ka san saura sati ɗaya bikin Faty, zan je mu fara shirye shirye ne. Nima ta tsaya min lokacin bikina" Da suka isa gida kuwa, aka shigo mata da akwatuna Inna Yaha ce a tsakar gida ta shiga tafa hannu tana salati wai auren da bai kai wata uku ba har an yi saki. Asiya bata kulata ba, ta shige ɗakin mahaifiyarta da ke kwance saboda bata jin daɗi. *** "Na ji ance jikar maiƙusumbi ta tafi. Ka saketa ne?" Gwamna ya juyo ya kalleta sai kuma ya juyar da kai ya cigaba da duba ipad ɗinsa. "Ba wai ina son zamanta bane amma ko zaka saketa, ka bari a gama rikicin zaɓe tukunna. Na gaji da jin ana ɓata maka suna a kanta" Sai a lokacin ya buɗe baki yace " ki dinga sawa ranki ba a tabbata akan mulki. I might not win the election ko da babu maganar Lami" "Tabɗi!" ta saka dariya. "Wallahi shekara takwas ɗin nan sai munyi ko za a mutu. Ai mutanen Congo ba su da wani Gwamna sai kai. Ko suna so ko ba sa so" "Allah ke bada Mulki Bilkisu" "Allah ma ya baka Saifuddeen, rantsarwa ya rage" Gwamna ya miƙe saboda idan ya cigaba da wannan magana ransa zai ɓaci fiye d a yadda yake ji yanzu... Da dare Asiya sai juyi take ta kasa bacci. Ba wai tana son zama da Gwamna bane, ba wai ta fara sonsa bane. Amma tana ganin ba zata samu nitsuwa ba sai an kashe zancen nan gaba ɗaya. Maganganun da suka yi da Ubayd ya sa ta gane cewa akwai 90% cewa abinda ta ji ranan a office ɗin COS rabin hira ne. Ƙila Alhaji Sani Kachallah ne ya kashe tsohon Gwamna dan ɗansa ya hau. After all, idan Saifuddeen ya hau kamar shine akan mulkin. Wani ɓangare na zuciyarta na tunanin ƙila Saifuddeen ya san da maganar za a kashe tsohon Gwamna amma bai iya yin komai ba, saboda ba shi da zaɓi. Koma minene gaskiya, yanzu ta gane cewa al'amarin 'yan siyasa sai su. Idan ta samu ta wanke kanta a wajen Gwamna zata rabu da shi hankalinta kwance. Sai dai kuma akwai wani ƙaramin gurbi a cikin zuciyarta da ya fara kwaɗaito mata rayuwa tareda Saifuddeen Kachallah. Ƙila tunanin da wannan gurbin yake ne ya hanata bacci, amma Asiya ba za ta taɓa yarda da hakan ba... Ta faɗawa Umma da Abba cewa Gwamna da kansa ya ce ta zo gida amma ba ta gaya musu akan wani dalili ba ne. Ga sauran 'yan gidansu cewa ta yi saboda bikin Faty da za ayi ne ta zo. Sumayya ma bata san ainihin dalilin zuwansu gida ba, amma kamar yadda Inna Yaha da Hindatu ba su yarda cewa saboda biki ta zo ba, haka itama ta yarda cewa akwai matsala ne tsakaninta da Gwamna. *** Ranan Monday aka watsa labarai cewa kaso biyu cikin uku na matsalisar jaha sun zaɓi ayi watsi da maganar tsige Gwamna, sun faɗi cewa abubuwan da ake tuhumar Gwamna da shi shati faɗi ne na 'yan adawa. A ɓagaren Umaru Kwom kuma jaridar sa ta Climax ta cigaba da fitar da labarai marassa daɗin ji gameda Gwamna. Alhaji Kwom ya ɗaura aniyar a zama na gaba a kotu zasu kawo Mr Silas ya bada shaidah. Ranan Laraba aka yi Primary election. Gwamna mai ci Saifuddeen Sa'ad Kachallah ya zamo ɗan takarar Gwamna a jihar Congo a zaɓe mai zuwa a ƙarƙashin jam'iyyarsu. Duk wannan bidiri da ake yi tsakanin Bilkisu da Alhaji Sani Kachallah da ma mutanen da ke goya masa baya, shi Uban gayyar hankalinsa ba a kwance yake ba, babu nitsuwa a tattare da shi. Kowacce rana yana wuni ne da abinda ya dace yai wa Asiya. Duk ta inda ya ɓullowa lamarin sai ya ga zuciyarsa ta kasa gamsuwa da shawaran daya yanke. Ya aureta ne da niyyar rabuwa da ita amma yanzu ga dalilin rabuwan yana da shi amma zuciyarsa ta ƙi amincewa da hakan. *** Duk wani hidiman biki da aka yi, Asiya ta yi shine cikin rashin jin daɗi. Ta ɗauka da House suka janye maganar tsige shi Gwamna zai nemeta, amma shiru, yanzu fatanta kawai komai ya tafi dai dai ranan da za ayi zama na gaba a kotu. Ranan ɗaurin auren Faty, Fou'ad Salisu ya kirata, ba yadda za ayi ta fita dan haka sai Queen Bee ta aika ta karɓo saƙon. Ranan Alhamis. Alhaji Umaru Kwom yana zaune a falo ya ƙurawa TV ido jira yake a gama yanke hukunci ya ji sanarwar da za a yi. Yana da mutanensa da za su halarci zaman kotun duk da kuwa zama ne za a yi ba tareda 'yan kallo ba. Duk da ba a tsige Saifuddeen Kachallah ba, yana da dama a kansa idan shari'ar ta tafi yadda ya tsara. Idan kotu bata wanke Saifuddeen Kachallah ba yana da damar da zai soke shi a lokacin yaƙin zaɓe. Sama da awa ɗaya bai samu labari daga muƙarrabansa ba, haka duk tasoshin da yake jira su kawo labari da ɗumi-ɗuminsa, har yanzu ya ji shiru. "Hello Halliru, mi yake faruwa ne? Alƙali bai faɗi hukunci bane har yanzu?" Halliru yace " akwai matsala, Ranka shi daɗe komai ya lalace. Yanzu dai an tafi hutun rabin lokaci idan an dawo Alƙali zai zartar da hukunci" "Wani matsala kuma? Mr Silas yana nan, Lami na nan, wani shaida kuma suke nema?" "Allah ya taimaki Excellency. Ga saƙo nan ance a kawo maka" Alhaji Umaru Kwom ya dakatar da mai maganar yana cigaba da bibiyan bayani daga bakin Halliru. Amma Halliru ya ƙi faɗa masa komai, ƙarshe ma wayar yankewa tayi. Ya duba mai aikinsa da ya kawo saƙon yace " saƙo daga ina?" "Ance daga wajen Matar Gwamna" "Matar Gwamna?" Ya dai karɓi dogon envelop ɗin daga hannunsa. Yana yaga envelop ɗin ya duba abinda ke ciki. Hoton Lami Ninja ce tana zaune akan wani mutumi, shigar da tayi a hoton ya bayyana cewa ita ɗin ba kamilalliyar mace bace. Hoto na gaba kuma ita ce riƙe da sigari a wajen party, wannan tsohon hotone ma, dan zai iya kaiwa shekaru shatakwas baya. Takardun gaba kuma photocopyn script ne na jarrabawar da Lami tayi aka bata carryover take iƙirarin Prof Kachallah bai bata dai dai bane saboda abinda ya faru tsakaninsu. Sai wata takarda kuma da itama photocopy ce wanda rubutu ne da Mr Silas yai ya bayyana duk abinda ya auku shekaru shabiyar da suka wuce, tareda faɗin cewa Lami Ninja ce ta biya shi dan ya aikata komai. Takardar ƙarshe kuma anyi rubutu ne da hannu inda aka rubuta *idan ka ga saƙona ka kira* a ƙasa akayi signing da initial A wanda ke nuna Asiya ce. Cikin kiɗima ya kira numbar Asiya wacce dama kiransa ta ke jira. "Ya ka ga saƙona?" "Kin yi ƙoƙari kam" ya faɗa da ƙarfin hali "Kar ka damu babu wanda zai kira sunanka cikin Mr Silas da Lami Ninja, amma ka shirya, Jaridar Climax za ta biya tara na rubutun bogi da ta buga ta ɓatawa Gwamna suna" "Kina tunanin zan tsorata ne?" "A'ahhh! Alhaji Umaru tsoro kuma. Ni dai ina son tabbatar maka ne kawai kujerar Gwamna ta maka nisa, ka shirya congratulatory speech wa Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah" Kafin ya kashe wayar ta riga ta kashe. Tabbas ita ce Malam Nawaso yake nufi. Ta ya zata shammace shi haka?. She completely make a fool out of him, taya ma haka ta faru?... 5 Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Alkali ya zartar da hukunci. Lami Ninja ta rintse ido lokacin da ta ji hukuncin da Alkali ya karanto. Ita Lami Ninja wacce take cin karanta ba babbaka a chan Lagos shine yanzu ake maganar za ta yi shekaru bakwai a kurkuku, sannan za ta biya tara kuɗi moliyan goma na ɓatawa Gwamna suna da tayi. Tana da sirrikan mutane dayawa a tafin hannunta, mutanen da akwai jarinsu acikin sana'ar da take yi, idan suka juya mata baya za ta tona musu asiri. "Mi zai faru idan mutanen Gwamna suka samu hujja a kaina?, mi zai faru idan Alkali ya turani kurkuku?" "Wannan ba zai faru ba, idan kuma aka samu akasi hakan ya faru to za a nemi ɗaukaka ƙara. At most ki biya tara, ko da za a turaki kurkuku ba zai wuce na wata shida ba" "Ka san akwai abinda zan faɗa ya zamowa wasu mutane matsala" "Ba abinda zaki faɗa Lami. Rayuwarki da ta shegiyar 'yarki yana da mahimmanci a gareki" Hirarta da Umaru Kwom kenan. Ba dan kanta za ta yi shiru ba, sai dai ba za ta so a taɓa lafiyar 'ya ɗaya tal data mallaka ba. Ta san mutane irinsu Umaru Kwom ba wani abu bane a wajensu su sa a kashe rai. Mr Silas zai yi shekaru uku a kurkuku amma shi ba zai biya tara ba. A hakan kotu ta masa sassauci ne saboda halin da ya ke ciki wanda yai iƙirarin wasu 'yan kidnappers ne suka kama shi suka lakaɗa masa duka da suka ga bashi da komai suka sake shi. Dukkansu biyu kowa da nashi dalilin na ƙin ambaton sunan Umaru kwom *** "Gobe za a buɗe Kamfen ɗin Saifuddeen, muna buƙatar goyon bayan ku" Alhaji Sani ya faɗa yana kallon Yallaɓai "Alhaji Sani, jam'iyya tana tareda Saifuddeen ɗari bisa ɗari sai dai dole ne ya ɗau alkawari akan ba zai juyawa Jam'iyya baya ba idan aka rantsar da shi" Alhaji Macciɗo ya faɗa yana kallon Alhaji Sani Kachallah da ke fuskantarsa. "Dole ne ya ɗau alkawari, idan ba haka ba we'll not support his campaign" Mr Paul yai maganar yana jijjiga hannu, jijiyoyin wuyansa har sun fara tashi. "Da mutane nake magana, ban saka dabbobi cikin maganata ba" Alhaji Sani ya faɗa yana watsa masa mugun kallo "Alhaji Sani are you calling me an animal?" "So?" "Enough!" Yallaɓai ya buga sandarsa da ƙarfi. "Muna magana mai mahimmanci kuna mana zancen yara. Wata uku muke da shi wajen tabbatar da cewa Saifuddeen Kachallah ya samu matsuguni a kowanne lungu da saƙo na jihar nan" "Sorry Yallaɓai, Ka san akwai tsohon banza a cikinmu" Mr Paul ya faɗa yana dariya Alhaji Sani ya miƙe tsaye, cikin fushi yace "ba zan zauna yaron bayana yana gaya min magana ba. Yallaɓai za mu haɗu a zama na gaba" "Alhaji Sani, Alhaji Sani..." Alhaji Macciɗo ya shiga kira amma ina, tuni Alhaji Sani ya cikawa babbar rigansa iska. Bayan tafiyarsa Yallaɓai yaiwa Mr Paul faɗa saboda ko ba komai Alhaji Sani Kachallah ya girmeshi nesa ba kusa ba. Damuwar Mr Paul dai shine a san yadda za a yi Saifuddeen ya saka hannu a buƙatun jami'iyya saboda kar ya zo ya hau a samu matsala.     *** Gwamna na tareda COS lokacin da aka bayyana hukuncin kotu a talabijin. "Congratulations your Excellency" "Thank you Mr Lamara" "Yanzu babu wata matsala sai mu fara Kamfen kawai" "Allah ya shige mana gaba" Har ya bar office bai daina mamakin Asiya ba, bai san takamaimai mi tayi ba amma ya san tanada hannu wajen yadda komai ya warware. Lokacin da ya shiga gida yana isa falo Bilkisu ta miƙe da sauri ta zo ta rungumeshi tana faɗin "Congratulations Darling, we won. Yanzu bamuda wata matsala sai ta Kamfen. Ita kuma tsinanniyar nan Lami na so life imprisonment aka rubuta mata" Chan ƙasan ransa yake tunanin babu wacce ta dace da wannan rungumar sai Asiya. Kafin ya bar office yasa an binciko masa duk abinda ya faru kuma ya samu bayanai kan cewa Asiya ce ta aiko da hotunan Lami Ninja wanda ya nuna ita ɗin tun asali 'yar bariki ce, sannan script ɗinta da aka samo an saka wani Professor ya duba marking ɗin kuma ya tabbatar abinda Saifuddeen ya bawa Lami Haladu, shi ta ci. Ko da ita ta sa aka yiwa Mr Silas duka saboda ya faɗi gaskiya, to tayi ne domin shi. She went this far just for him. "Come here Darling, na saka an girka maka favourite food ɗinka" Bilkisu ta katse shi. Da ta yi maganar girki ƙwaƙwalwarsa tuno masa tayi da kwana biyu da ya ɗanɗani girkin Asiya matarsa. Akwai professional Cook da yake musu girki a gidan, amma albarkar dake girkin mata ga mijinta yana da yawa. Bilkisu ta kama hannunsa ta wuce da shi ɗaki dan ta taya shi kimtsawa... Har ƙarfe tara na dare Asiya na jiran kiran Gwamna. Abu biyu take juyawa a ranta. Ko dai idan Gwamna ya kira yace ta dawo gida ko kuma idan ya kira yace ya saketa. Tun tana jiransa har ta fara gyangyaɗi, ƙarshe bacci ya sace ta. Da Asuba da ta tashi wayarta ta fara dubawa, babu missed call sai text message guda ɗaya wanda aka tura ƙarfe shaɗaya da rabi na daren jiya. *Bello zai zo ya ɗauke ki ƙarfe goma na safe* "Shikenan kawai" ta furta ranta a ɓace. Da safe ta shiga banɗaki tana wanka ta jiyo ihun Ali da Gwani. Da sauri ta watsa ruwa ta sanya hijabi a saman zanin wanka ta fito. "Mi ya sameta?, mi kuka mata?" Asiya ta daka musu tsawa. "Ta fito daga kitchen ne zata shiga ɗaki kawai muka ga ta faɗi" Ali ya faɗa kaman zai yi kuka. Abba ne ya nemo mai mota aka saka Umma suka wuce da ita Asibiti. Saura kaɗan Asiya ta fita da zanin wanka Abba ya ce ta koma ta shirya, kafin ta fito sun riga sun wuce dan haka ita da Sumayya suka tsaida Keke suka bi bayansu. Sai da aka basu damar ganin Umma data shiga ɗaki sannan ta cire niƙab da ya zama mata dole yanzu, indai bata son idon mutane akanta. Sai yanzu ta lura da wata rama da Umman tayi. A tunaninta laulayin cikin ne ya figar da ita haka. Bayan Umma ta farfaɗo Asiya take tambayarta miyake damunta?. Umma ta kauda kai gefe. "Dama kin daɗe ba lafiya Umma, amma shine kike ta ɓoyewa. Ranan da kika koma Asibiti mi Likita yace?" "Asiya ki barta ta huta" Asiya ta kalli Abba sannan ta kalli Umma dake kwance. Maganarsa yai mata kamar akwai abinda suke ɓoyewa, da alama wannan jinyar ba baƙonsu bane. "Abba mi yake damunta?" "Zamuyi magana idan mun koma gida"... Ƙarfe goma da 'yan mintuna Yaya Bello ya iso ɗakin da suke, yaje chan gida ance suna Asibiti. Ya gaida Umma sannan yacewa Asiya Gwamna ne ya turoshi ya zo ya ɗauketa. "Yaya Bello ina zan je kana ganin Umma a kwance" Umma dake kwance ta yafito ta tace ta tashi ta tafi tunda Sumayya na wajen. "Sumayya zata tafi makaranta" Ta ɗau wayarta ta danna numbar Gwamna wanda ta rasa dalili amma da *His Excellency* ta saving numbarsa. Bayan ta amsa sallamarsa tace "Umma tana Asibiti, kayi haƙuri ba zan iya zuwa ba" "Allah ya bata lafiya, a isar min da gaisuwa" Ganin idon kowa akanta yake yasa tace "za ta ji, mungode" Zuwa dare aka sallamesu saboda Umma ta takura akan zata tafi wai ta samu lafiya. Lokacin da suka koma gida Abba ya samu daman yiwa Umma bayanin ciwon Umma. Haka Asiya ta tsaya galala tana kallon Abba cikin rashin fahimta. Umma na da ovarian cancer sai kace shirin film. Tukunna ma yaushe suka sani amma suka sakata a duhu babu wanda ya gaya mata?. Kusan watanni biyar kenan da suka san da zaman ciwon a jikinta, tana shan magani amma yanzu cikin daya shiga jikinta ba zata shi yake galabaitar da ita. Asiya haushin kanta ta fara ji sannan ta maida haushin kan ciwon Umma, kan Abba da Ubayd da suka ɓoye mata ciwon, kan jaririn da bai tashi zuwa ba sai yanzu, bayan kusan shekaru goma da suka wuce tana cikin ƙoshin lafiya. "Tana zuwa check-up amma yanzu suna maganar kaman ya shiga stage IV, amma basu tabbatar ba sai sake yi mata wasu gwaje gwaje" Ba ta ce masa komai ba ta miƙe ta wuce ɗaki, gefen Umma ta kwanta ta ƙanƙameta ta fashe da kuka... Sai da Asiya ta ƙara kwana uku kafin ta koma gida, asalin gidan Gwamna. Bataso tafiya ba, Umman ce ta tursasata akan matuƙar bata tafi ba sai ta saɓa mata, akwai aure akanta ba zata zo ta tare mata a gida ba. Ganin ta samu ƙwarin jiki Asiya ta tafi da niyyar kullum za ta zo ta dubata kafin su sake komawa Asibiti. Ranan data koma gidanta Gwamna bai leƙota ba, bata damuba saboda yanzu lafiyar Umma ne a gabanta. Wasu mata da suka zo dubata ma ƙin fita tayi. An fara Kamfen suna neman matsuguni a jikinta, bata da ƙarfin yin hayaniya yanzu. Ta godewa Allah data samu ta yanke alaƙa da Umaru Kwom sannan aka wanke sunan Gwamna. Ita yanzu koda zai saketa bata da matsala saboda burinta yanzu shine ta kasance kusa da Umma. Washegari Gwamna ya shigo da safe misalin ƙarfe takwas saura kwata. Asiya na ɗaki Sumayya ta shigo tace mata Gwamna ya zo yana jiranta a sama. Rigar bacci ne a jikinta dan haka ta ɗaura hijab ta fita. Lokacin data gaisheshi, fiskarta daya kumbura ya fara lura da shi, sannan idanunta da suka ƙanƙance. "Ya jikin Umma?" "Alhamdulillah" ta amsa tana jujjuya wayar hannunta. "Ina so a fita da ita waje, akwai wanda zai zo gobe saboda passport ɗinki ke da ita da kuma mutum biyu maza da za su iya binku" Da ba Umma bace ƙila zaginsa za ta yi akan yadda suka maida fita Asibitin ƙasar waje kamar tafiya anguwa, ƙila tace masa bata son sadaka da kuɗin talakawa, ƙila kuma tace masa bata son burga da nuna isa. Amma lafiyar Ummanta ake magana ba zai tayi wasa da wannan dama ba. Asiya ta ɗaga ido ta kalleshi, shima ita ɗin yake kallo, ta rasa dalilin dayasa kaifin idanunsa ke tsoratar da ita take kasa jure kallon cikin fararen idanunsa. Ta maida dubanta ga wayanta tace "mun gode, Allah ya saka da alkhairi" Shiru ne ya biyo bayan haka kusan minti uku kafin tace " ina so naje na shirya ƙarfe tara zamuje ganin Likita" "Bismillah" ya faɗa yana mata nuni da hannu alamar zata iya tafiya. Akwai maganar da ya ke so suyi, akwai tambayoyi daya ke son yi mata amma a yanayinta baya tunanin zata fahimci koma minene yake son faɗa dan haka zai bari zuwa lokacin da take cikin kwanciyar hankali. A ranan da Gwamna yazo gidan Asiya, a ranan aka sace wasu ɗalibai 'yan Sakandare su goma shaɗaya daga wata makarantar gwamnati dake cikin jahar Congo. Irin haka ya faru farkon hawan marigayi Gwamna Saminu Bacchi inda aka sace wasu ɗalibai huɗu a hanyarsu ta zuwa Makaranta, an samu an karɓo yaran kuma daga nan ba a sake sace ɗalibai ba. Maganar satan ɗalibai ya karaɗe jaha ya karaɗe ƙasa baki ɗaya. Ko'ina sai maganar satan ake. Kwana ɗaya kwana biyu shiru babu labarin za a sako ɗaliban sannan kidnappers ɗin basu fito sin bayyana mi suke buƙata ba.   *** Bilkisu Kachallah ta dawo daga taron mata da aka yi ta tsaya a tsakiyar falonta tana kallon TV saboda kanun labaran da ta ji ya ja hankalinta. Umaru Kwom ne a wajen Kamfen ya jefi Gwamna da rashin bawa rayukan al'umma mahimmanci, taya za ayi a sace raya ƙanana 'yan ƙasa da shekaru shabiyar kusan kwana biyar amma babu abinda Gwamna ya iya yi akai?. Ba a ji daga jami'an tsaro ba balle 'Yan kidnappers da suka sace yaran, mi hakan ke nufi? "He's behind this. Shine da wannan aikin, Umaru Kwom yanzu kuma dirty tricks ka fara? Mu zuba mu gani" ta snapping hannunta, daga haka ta ɗau gyelenta ta wuce ɗaki. A ɓangaren Gwamna kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda wannan lamari. Ya dakatar da fita Kamfen saboda ya bada hankalinsa ga case ɗin sace yaran nan. Daga wajen Alhaji Sani ya fara fuskantar matsin lamba saboda ajiye fita kamfen da yai a gefe, yayinda Umaru Kwom na chan yana fita Kamfen yana kururuta maganar satan ɗaliban da aka yi. Ya yi meeting da Commisioner of police ya fi sau ba adadi amma duka shiru ne domin kwana bakwai kenan babu labarin yaran da aka sace.   *** A kwana na goma shaɗaya da ɓatan ɗalibai jikin Umma ya tashi, cikin dare aka wuce da ita Asibiti. Ba a sanar da Asiya bama sai washegari... "Umma ya jikin?. Umma an kusa gama haɗa takardun, naki ne ma ya bada matsala, Insha Allah da zaran an gama harhaɗa takardunki zamu fita" Tana yiwa Umma bayani ne da hannu, Umma da ke rigingine a kan gado ta kalli Asiya ta mata murmushi. Duk da bata da ƙarfin jiki haka ta fara mata bayani da yaren Kurame. "Ki kwantar da hankalinki Asiya, sauƙi na Allah ne. Idan da yiwuwar na samu waraka to ko a nan ɗinma zan samu, dan haka babu inda zan je, idan Allah zai ɗau raina ina son kasancewa kusa da iyalina" "Babu abinda zai sameki Umma, ba abinda zai sameki, zaki warke, cancer ba mutuwa ba ce, ki dena faɗin haka" "Allah ya miki albarka Asiya. Ina alfahari da ke, ko ba na nan na san za ki zama uwa ta gari wa ƙannenki." "Umma ya isa haka, dan Allah ya isa" Asiya ta faɗa tana goge hawaye. "Ki bari na yi magana Asiya Shahidan Gwani. Kinada kyakyawan zuciya amma kina da taurin kai, kinada riƙo. Ki yi ƙoƙari ki yaƙi Shaiɗan akan wannan" ta ja dogon numfashi sannan tace " Na yiwa Ubaydullah mata" Asiya ta zaro ido waje, baki na rawa tace "Um...ma" "Ki haƙura da mijin da Allah ya baki, ki masa biyayya, ki riƙe aurenki da kyau. Nan da wata ɗaya Ubaydullah zai auri 'yaruwarsa Salma" Ta san Salma. 'Yar Umma Hussaina ce matar da ta raini Ubayd, matar da saboda shaƙuwa bai taɓa kukan rashin uwa ba, saboda ita ne koda yai wayo bai dawo wajen Abba da zama ba, sai dai ya dinga zuwa yana komawa. Ba za ta manta Salma ba, ita ce ta rubuto mata wasiƙa kusan shekaru biyar da suka wuce take roƙonta wai Dan Allah ta bar mata Ya Ubayd. Ita ce lokacin da aka saka aurensu ta shiga damuwa tayi ta rashin lafiya kamar ba zata tashi ba. "Ummaaa" ta kira da ƙarfi duk da ta san mahaifiyartan ba ji za tayi ba. "Idan kika kashe aurenki dan ki auri Ubaydullah, ban yafe ba. Idan aurenki ya mutu saboda Allah bai yi zaku jima tare da Gwamna ba, wannan kuma Allah ne masani. Amma ki manta da Ubaydullah, ki rungumi auren ki bilhaƙƙi. Sannan ki rage dogon buri, wani kwanciyar hankalin, wani jin daɗi da soyayyar sai a Aljannah. Idan kuma Allah ya rubuta za ki samu a duniya to ki godewa Allah da ni'imar da yai miki amma ba yin ki bane. Ki dai cigaba da ƙoƙari kina addu'a idan Allah ya baki kwanciyar hankali ta jikin mijinki wannan ni'ima ne da zaki gode masa. Idan kuma ya jarrabce ki da mijinki kuma kiyi iya naki ƙoƙarin ki barwa Allah sauran, idan kuma zaman ya kai akwai cutarwa har kina ganin zai jawo ki dinga aikata zunubi to inaga rabuwa shine mafi Alkhairi. Ina miki addu'ar Allah ya baki kwanciyar hankali a gidanki. Abu na gaba shine, abinda haƙuri bai bayar ba inaga faɗa ba zai ba da shi ba, idan baki so kanki ba, idan baki samarwa kanki zaman lafiya ba komai mijinki zai miki ba zaki taɓa godewa Allah ba. Na yadda, gidan da kika taso yanada nasaba da yawan zafin ranki amma kuma ya kamata ki daure ki cire komai a ranki, ki ɗauki rayuwa da sauƙi. Allah ya miki albarka ya kuma baki 'ya'ya na gari Amin" Zuwa lokacin Asiya kuka kawai take yi. Zuciyarta ya karaya da maganar Umma, sai yai mata kamar wasiyyar ƙarshe Umma ke yi. Kusan ƙarfe biyu na rana wasu securities biyu suka yi sallama a ɗakin da aka kwantar da Umma. Umma tayi bacci, Asiya na danna waya, ƙaninta Gwani kuma na cin abinci. "Hajiya, Excellency yace mu taho da ke" "Ni kuma?" "Yes Ma, in fact emergency ne" "Barin kira nayi confirm" kafin ta danna wayar message ya shigo wayarta *ki biyosu Asya, Bello ba lafiya* "Yaya Bello, mi kuma ya sameshi?" Ta dai san lafiya lafiya ya kawota Asibiti da safe. To ko wani abin yaje ya sha ya fara haukan daya saba. "Gwani, idan Umma ta tashi kace Gwamna ne ya kirani, ba zan jimaba zan dawo" "To" Lokacin da ta miƙe securities ɗin suka sara mata yayinda ɗaya ya shige gaba ɗayan kuma ya tsaya a bayanta. Haka suka ƙarisa wajen wasu motoci guda biyu. Yanayin motocin bai sawa Asiya wani shakka ba. Aka buɗe mata ƙofa ta shiga tana addu'ar Allah yasa Yaya Bello na lafiya. Suna fita daga Asibitin aka kunna wani turare daga ɓangaren Dreba. Asiya ta riƙe kai saboda wani ciwon kai data fara ji, ta fara ƙoƙarin toshe hancinta amma ina ta riga ta shaƙi abin, idanunta suka fara rufuwa a hankali, tana ƙoƙarin magana ta faɗa ɗaya gefen sai bacci...   *Afuwan Dan Allah. Still kuna bina bashin shafi biyu. Insha Allah gobe zaku samu* 6   Gwamna Saifuddeen Kachallah yana zaune a dinning room yayi tagumi Bilkisu ta shigo sanye da wata doguwar riga na material kalar abin cikin ƙwai. "Darling ka manta wayarka a ɗaki" tayi maganar tana ajiye wayar a gefensa. Ta maida dubanta ga Junior da ke wasa da abinci, sai ya ɗebo shinkafa a cokali ya zuba a kan dinning table ɗin yana barbazasu ɗai ɗai "Junior eat your food, ko na saɓa maka" "I'm not hungry" "Mi kake son ci?" "Ice cream" "Ice cream fa ka sha shekaranjiya ya saka gudawa. Eat, gobe sai a siyo maka ice cream ɗin" Ta kalli Gwamna da har yanzu ko taɓa abincin bai yi ba, tace "Darling Dan Allah ka ci abinci, jiya kayi Azumi, yau baka karya ba ka fita and now..." Gwamna ya kalleta yace " Bana tunanin iyayen yaran nan suna cin abinci. Bana tunanin suna samun bacci" "To Saifuddeen ya zamu yi musu? You are doing your best, wanɗannan kidnappers ɗin suna yiwa 'yan adawa aiki ne, da sannu za a kama su" "Ni ake kallo Bilkisu, nine Shugaba" "Ka yi iya naka ai, tunda ka saka jami'an tsaro su nemo su, ko so kake ka ɗau bindiga ka shiga daji farautar Kidnappers?. Please, akwai abubuwa dayawa a gabanmu, za mu fita campaign gobe ka kwantar da hankalinka, za a samesu" Ta ƙarisa maganar tana riƙo hannunsa tareda ɗaura murmushi a fiskarta. *** Ubayd ne ya kawo Habibu da Ali a motarsa, suna shiga ɗakin Umma suka samu ta tashi tana yiwa Gwani magana. Abu na farko da ta tambaya shine ina Asiya? Daga gida suka taho sun san Asiya bata nan, shiyasa sukayi tunanin ko tana chan gidanta ne. Wasa wasa ana jiran shigowar Asiya har aka yi sallar la'asar amma shiru, numbarta kuma a kashe. Lokacin da Sumayya tazo Asibitin tayi ta ƙoƙarin kiran numbar Asiya amma still a kashe, ƙarshe ta kira Yaya Bello ta tambayeshi ko Asiya tana gidan Gwamna ne ko gidan Gwamnati. "To ai ni tuntuni nake jiran kiranta" "Yaya Bello aka ce Gwamna ne ya aiko aka ɗauketa da rana, kuma har yanzu numbarta baya shiga. Umma ce take nemanta tun ɗazu" "To ni dai ban sani ba, amma zan sa a duba mini cikin gidan" Kusan minti goma sai ga kiran Yaya Bello inda yace Hansa'u tace Asiya bata zo gidan ba. Sumayya ta kira Uwani ta tambaya ko Asiya ta zo gida amma zancen ɗaya ne, tunda Asiya ta fita da sassafe bata dawo ba. Jikin Sumayya yai sanyi, amma tunda akace Gwamna ne ya aiko taje, ƙila tana Kachallah House ne ko kuma wani wajen daban. Babu wanda ya kawo komai a ransa sai da aka ga har anyi sallar Magariba Asiya bata dawo ba sannan bata kira ta faɗi rashin zuwanta ba ga kuma numbarta har lokacin a kashe. Kusan ƙarfe takwas na dare, Sumayya ta shimfiɗa sallaya ta fara sallar Isha. Mazan tun da suka fita sallar magariba babu wanda ya dawo cikinsu. Sumayya na sallah Umma ta fara wani irin nishi, daga ƙarshe kuma sai shiru. Da Sumayya ta idar da sallah sai ta kwanta akan sallayar, ta buɗe wayarta ta cigaba da chatting, da sabon saurayinta take chatting kafin ta fara sallan kuma yana har yanzu yana online shiyasa ko azkar bata yiba ta ɗau wayar dan ta maida masa reply ɗin chat daya turo. Minti shabiyar bayan haka Abba ya shigo ɗakin da sallama. "Har yanzu ba a ji daga Asiya ba?" ya tambaya bayan Sumayya ta masa sannu da zuwa. "Har yanzu Abba, Abba nace ko zaka kira Gwamna ka tambaye shi ne?" "Sumayya mutum ya kira matarsa sai mu fara bibiyarsa ko lafiya, ƙila wani wajen suka je kin san ana kan kamfen" Ya ɗan matsa kusa da gadon Umma dan ya tambayeta ya jiki amma yana ganinta zuciyarsa ta harba. Sumayya tana cikin chatting ta ji Abba ya furta Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun. "Abba miya faru ?" Ta furta a firgice. "Kira min likita" ya furta a hankali yana faman gyara kwanciyar Umma. Lokacin da Sumayya ta dawo da likita samun Abba tayi zaune gefe yana waya, kaman da Ubayd yake magana dan taji yace "ka kira Yahanasu ka faɗa mata sannan ku taho da Habibu" Ba abinda likita ya iya yi sai dai kawai jaddada rasuwar Umma da yai. Sumayya ta fashe da kuka mai shiga rai. Kusan ƙarfe tara da rabi na dare aka kawo gawar Umma gida. Inda Inna Yaha da wasu mata ke zaune jugum suna jiran dawowarsu Abba. Tunda Ubayd ya sanar da Inna Yaha mutuwar Umma, ta fashe da kuka tana sunbace sunbace, kuka da kururuwarta ne ma ya ja hankalin maƙota. Tun a Asibiti Abba ya kira Gwamna amma numbarsa a kashe. Ƙarshe dai Yaya Bello aka kira akace ya gayawa Gwamna saƙon mutuwar saboda numbarsa bata shiga. Yayinda ake wannan, Gwamna yana meeting ne da jami'an tsaro kan ɗaliban da aka sace. Rikiɗe musu yai a wajen yana faɗa akan ya basu awa arba'in da takwas su gano inda yaran suke, ko gano su waye kidnappers ɗin, sannan mi suke so. Idan babu wani labari mai ma'ana, zai sauke dukkansu daga muƙamansu. Commisioner of Police yana shiga mota ya kira wani number yace "Gwamna yayi fushi sosai fa, ya bamu 48hrs mu nemo yaran nan, kasan abinda zaka yi ko kuma na bawa yarana daman kama su" yai shiru yana sauraran bayani daga ɗaya ɓangaren. Ƙarshe ya amsa da "To, to na ji"... Lokacin da Gwamna ya isa gida, ana buɗe masa ƙofa Yaya Bello ya iso ya sara masa yana yi masa sannu da zuwa. "Ranka shi daɗe ina da saƙo daga wajen Abban Asiya" Gwamna ya kama hannunsa suka wuce cikin gida. Falon farko suka zauna. Gwamna yaiyai Yaya Bello ya zauna akan kujera amma ya ƙi wai ba girmansa bane Gwamna ya zauna a kujera shima ya zauna. "Lafiya dai ko?" Gwamna ya tambaya bayan sun ɗan nitsu. "Ranka shi daɗe. Ɗazu Malam Nuhu ya kirani ya sanar dani an masa rasuwa" "Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun, wa ya rasu?" "Allah yai wa Umman Asiya rasuwa" Gwamna ya dafe kansa yana addu'ar Allah ya jiƙanta, ya gafarta mta. Lokaci guda kuma ya ɗago kansa jin abinda Yaya Bellon ya faɗa. "Yace a faɗawa Asiya rasuwan, idan da hali kuma ta zo ta ga mahaifiyarta kafin a mata sutura" As far as he know, Asiya tana Asibiti tun safe. "Ban gane ba. Asiya bata Asibitin ne?" Yaya Bello ya ɗago ya kalli Gwamna cikin rashin fahimta yace "ai tunda ka aiko aka ɗauketa bata sake dawowa ba, kuma nambarta a kashe tun lokacin" "Na aiko aka ɗauketa? Yaushe? Wa zan sa ya ɗaukota idan ba kai ba. Su waye suka zo suka ɗauketa? Bata chan gidana kuma?" Yai maganar duka lokaci guda. "Ance bata koma gida ba tun lokacin data fita da safe. Ƙaninta yace mutane biyu ne suka zo sanye da baƙaƙen kaya suka ce ka ce su ɗaukota" Gwamna ya miƙe tsaye yana faɗin "kana so kace ba a san inda Asya ta shiga ba tun da rana?" "Ranka shi daɗe ayi haƙuri" Gwamna ya fito da waya ya kira wata numba. Daga yadda yake faɗa ka san ransa ya ɓaci matuƙa. Bayan tafiyar Yaya Bello, Gwamna kiran Abba yai ya masa ta'aziyya tareda neman ƙarin bayani gameda waɗanda suka zo ɗaukan Asiya, tsabar ruɗewa ya ma manta cewa Gwani Mahaifiyarsa ya rasa amma haka aka bashi waya bisa umurnin Gwamna, Gwamna ya shiga jera masa tambayoyi kamar ɗan jarida. "Ya abin ya faru? Wani kaya suka sa? Ya kamanninsu yake? Mi suka cewa Asiya da suka zo? Mi Asiya tace kafin ta tafi?" Abu ɗaya ne Gwani bai faɗa ba saboda lokacin hankalinsa baya wajen, wato batun text da Asiya ta gani daga numbar Gwamna.   "Darling calm down, kanata ihu tun ɗazu, zaka sawa kanka ciwon kai fa" "Someone kidnapped Asya kina cewa ina ihu, Bilkisu ina mulkin garin nan amma aka sace min mata, kin san mi za a faɗa gobe kuwa?" "To naga dai Asiya ba ƙaramar yarinya bace. Besides, zai iya zama 'yan adawa ne..." Wani irin kallo ya mata wanda yasa ta haɗiye sauran maganan da tayi niyya. Ta tsani irin wannan lokuta da kaifin idanun Saifuddeen ke tasiri akanta. Ba abinda ta iya cewa har ya fice daga falon sai huci da take akai akai. *** Asiya sai da tayi awa shida tana barci kafin ta farka. Lokacin data farka akan gado ta tsinci kanta, ta buɗe ido tana ɗan danna goshinta saboda nauyi da takeji a kan. Kusan sakan biyar kafin hankalinta ya dawo jikinta har ta hankalta da inda take da kuma abinda ya faru. Ɗakine madaidaici, yana da komai na amfani a ciki, akwai: TV, fridge, AC, fanka, da kujeru guda biyu, table da kuma gado. Kai tsaye ƙofar ɗakin ta nufa ta shiga bugawa da ƙarfi, bayan ta murɗa hannun ƙofar ya ƙi buɗuwa. Ta dinga bugawa har sai da hannunta ya fara zafi. Ta je ta buɗe banɗakin dake cikin ɗakin amma shima babu hanyar fita aciki, dan ko window ɗin wajen ɗan ƙarami ne, kuma kaman ta baya aka kulle dan yaƙi buɗuwa ma. Duk wani ƙoƙarinta na ganin ta fita daga ɗakin ya faskara. Ta tsugunna a tsakiyar ɗakin ta fashe da kuka tana kiran Umma Umma... Tafi awa biyu tana kuka kafin ta ankara ko sallah bata yi ba. Ta duba agogon dake manne a bangon ɗakin, ƙarfe tara da rabi na dare. Ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala abin mamaki data fito ne kuma ta lura da wata akwati da aka jingine a gefen gado. Tayi saurin buɗewa dan ganin mi ke ciki. Kaya ne a ciki duka jallabiya, hijabi guda biyu da kuma underwear na mata. Da alama wanda ya kawota ɗakin bai shirya saketa da wuri ba. "Ya Allah albarkacin mahaifiyata ka fitar dani daga wannan wajen. Ya Allah mahaifiyata bata da lafiya tana buƙatata kusa da ita Ya Allah ka fitar dani daga wajen nan. Ya Allah na roƙe ka da girman zatinka da girman ƙudirarka, na roƙeƙa da ƙuwwa da ke jikin kalmar La'ilaha Illallah, na roƙeƙa da ƙarfin ayatul Kursiyyu, na roƙeƙa da girman Al'arshinka, Ya Allah na roƙeƙa da jinƙai da kake yiwa dukkan bayinka, ya Allah ka kuɓutar dani daga hannun koma wanene ya ke son cutar dani, Ya Allah Ya Hayyu Ya Ƙayyum ka kaini wajen mahaifiyata a daren nan, Ya Allah kai kaɗai kake baka da abokin tarayya. Mala'iku, Manzo, Annabawa, Aljanu da sauran Mutane dukkanmu muna ƙarƙashin rahamarka ne Ya Allah, sai abinda ka ce Rabbul Izza, kaine Kun Fa Ya Kun Ya Allah. Kai ne Ar-Rahman, kaine Jalla Jalal. Ya Allah kowanne ganye yana faɗuwa ne da saninka, Ya Allah kowanni numfashi na halittun dake duniyar nan yana fita ne da iliminka, Ya Allah ka fitar dani daga wajen nan naje na ga Umma ta" Addu'o'in da Asiya ta dinga yi kenan bayan tayi sallah har baccin da ba ta shiryawa ba ya ɗauketa. *"Asiya-Shahidah"* wata murya mai sanyi ya tashi Asiya daga baccin da take yi mai daɗi. Umma ta gani a gefenta tana mata murmushi. Ta tashi zaune da sauri tana faɗin "Umma ke kika kira sunana? Kin fara magana ne?" *"Asiya-Shahidah"* Umma ta sake faɗa da murya mai sanyi fiskarta ɗauke da murmushi. Asiya ta rungume Umma tana hamdala, tana faɗin ta ƙara kiran sunanta. For the first time a rayuwarta ta ji maganan mahaifiyarta. "Kiyi ta kiran sunana kawai Umma, ba zan gaji da ji ba" *"Allah ya miki albarka Asiya-Shahidah"* Farkawa da tayi daga mafarkin da ta ke yi, yai dai dai lokacin da aka buɗe kofan ɗakin. Ta miƙe da sauri tana faɗin "mi kuke so a wajena? Wa ya sa ku kawo ni nan?" Bindigar dake hannun mutane biyu da suka shigo ya hanata yunƙurin ficewa daga ɗakin da ta yi. "Umurni aka bamu akan mu kawoki nan har zuwa lokacin da za a sakeki" "Wa?, Gwamna?, Umaru Kwom?" "Ba mu da ikon bayyana miki komai, amma an bamu saƙo ɗaya mu gaya miki" "Kun san ko ni wacece kuwa? Kun san matsayina a jahar nan kuwa?" Wata mata sanye da uniform ta shigo ɗauke da tray ɗin abinci, ta ajiye akan table sannan ta fita. "Ance mu faɗa miki cewa ki kunna TV da ƙarfe tara na safiyar yau saboda za a nuna jana'izar mahaifiyarki live" "Jana'iza?, Mahaifiyata?, mi ya sameta?, me kuka mata?" "Ance mu faɗa miki cewa idan kika zauna babu taurin kai har zuwa lokacin da za a sakeki, babu abinda zai samu 'yan uwanki" Bata ma gama jin mi mutanen ke faɗa ba ta zauna daɓas a ƙasa hawaye na zubo mata. Har suka fita ba tayi ƙwaƙwƙwaran motsi ba. Kasa yarda tayi da abinda suka faɗa. "Umma is fine, ba abinda ya samu Umma, Umma tana Asibiti tana bacci, ba abinda ya sameta, babu abinda ya samu Ummata" ta dinga maimaitawa kamar mai taɓin hankali. 7 Misalin ƙarfe bakwai na safe Alhaji Umaru Kwom yana karyawa aka kira shi aka sanar da shi rasuwan sirikar Gwamna, da farko ma mahaifiyar Bilkisu Kachallah ya ɗauka sai da wanda ya kira ɗin ya jaddada masa cewa matar Malam Nuhu Principal ce. Bayan ya ajiye wayar yai murmushi. Matarsa da ke gefe tace "Alhaji lafiya naga kana murmushi, ba maganar rasuwa aka maka ba?" "Rasuwa ce da ta buɗe min wata dama" "Wa ya rasu?" "Mahaifiyar Asiya Kachallah" ya amsa mata har lokacin bai bar murmushi ba. Hajiya Mariya ta yiwa Umma addu'ar samun rahama yayinda mijinta ya cigaba da cin abinci ba tareda ya amsa addu'ar da Amin ba. *** Jiya yadda Gwamna ya ga rana haka yaga dare, bai rintsa ba ko kaɗan. Lokacin daya je Kachallah House tambayar Alhaji Sani yai ko yana da hannu wajen sace Asiya amma yace masa bai da masaniya akan haka. "Baba dan Allah kayi haƙuri idan ma ..." "Saifu baka yarda dani bane? Kana ga zan maka ƙarya ne?" "Ka yi haƙuri, ba haka nake nufi ba" "Ba zan yi wasa da rayuwar iyalinka ba Saifu. Ina zargin Umaru Kwom da hannu akan wannan, amma zan sa a bincika mani komai" To mi Umaru Kwom yake nufi da sace Asiya? Da wannan tambayar ya raya darensa, yayinda wani ɓangare na zuciyarsa ya ke zargin kansa da sakaci da yai da rayuwar Asiya. Idan da ya haɗata da masu tsaro ƙila haka ba zai faru ba. Ahalin gidan Malam Nuhu Principal kuwa sun kwana sun tashi ne da juyayin mutuwar Umma da kuma rashin sanin inda Asiya take. Tun dare aka yiwa Umma sutura ana jiran gari ya waye a kaita makwancinta. Washegari da safe gidan ya cika sosai, 'yanuwa da abokan arziƙi da ke kusa duk sunzo. Tun safe aka fitar da labari cewa Allah ya yiwa mahaifiyar Matar Gwamna rasuwa. Abin mamaki tawagar Alhaji Umaru Kwom ce ta fara isowa kafin ta Gwamna ta iso minti shaɗaya tsakani. Gwamna rufe idonsa yai da baƙin gilashi saboda kar a ga kumburarrun idanuwansa. Gwamna yana isowa ƙarfe tara da minti biyar aka yiwa Umma Sallah sannan aka wuce da ita maƙabarta. Gwamna Saifuddeen bai yi niyyar wucewa maƙabarta ba amma yana shiga mota Alhaji Sani ya kirashi yace ya wuce maƙabarta saboda Alhaji Umaru Kwom nan zai je. Innalillahi akan aikin ladan ma sai an saka siyasa a ciki. Haka dai aka wuce da Gwamna maƙabarta. Asiya bata kunna TV ba. Tsoro take ji, gani take idan ta kunna ne abinda aka faɗa zai tabbata, amma idan bata kunna ba Ummanta za ta kasance kwance a Asibiti ba abunda ya sameta. Sai kusan ƙarfe goma da rabi saura ta samu ƙarfin gwiwar kunna TV ɗin. Kamar yarinya haka ta zauna a gaban TV ta naɗe kafafuwanta ta riƙe fiskanta da hannayenta biyu. Hill TV ta kunna, ta san suna ƙoƙarin fitar da labarun gaskiya ba kamar Congo News ba. Ƙarfe goma da rabi suka sako maimaicin labaren safe. Labarin farko a kanun labaren shine rasuwan mahaifiyar matar Gwamna wato Asiya Kachallah. Haka Asiya ta baza ido tana kallon labaran. Aka nuna wajen da Alhaji Umaru Kwom yazo yana gaisawa da su Abba, aka nuna wajen da Gwamna shima ya iso, sannan aka ɗan nuna wajen da ake yiwa gawar Umma sallah, aka nuno wajen da ake saka gawar Umma a cikin ƙabari. Daga ƙarshe aka nuna Gwamna yana yiwa iyalen Malam Nuhu Gidaɗo ta'aziyya sannan aka nuna Alhaji Umaru Kwom shima yana yiwa Gwamna da iyalinsa ta'aziyya. Da gangan ɗan jarida ya tambayeshi ko miye dalilin daya sa ya halarci sallan sirikar Gwamna sannan har ya zo maƙabarta akayi biso da shi. Umaru Kwom ya karkata kai yace *"watoo, ita siyasa ba gaba bace"* kafin ka ce me a duniyar yanar gizo mutane sun ɗauki kalmomin Umaru Kwom suna masa kamfen da shi *#Siyasa ba gaba bace* Ta ko'ina a faɗin jihar sai maganan ƙarfin hali, jajircewa da kuma imani irin na Umaru Kwom ake. Hatta wasu masu faɗa aji a ƙasar sai da suka yaba da Umaru Kwom. Asiya tana ganin rahoton amma hawaye ko ɗaya bai fito ba, zuciyarta ya yi mata nauyi. Tana ji kamar kumbura zuciyar take, nan da anjima kaɗan zata fashe, idan ta fashe kuma sai itama a kaita inda aka kai Umma. Sai dai haka ta zauna a wajen tana jiran zuciyar ta fashe amma taƙi fashewa, bata ma da alamar zata yi komai saboda duk yadda take dokawa cikin ƙirjinta babu abinda ya faru. Kamar wata zararriya ta tashi tsaye tana safa da marwa a ɗakin tana faɗin "sun kashe Umma, sun kashe min mahaifiya, ba abinda ta musu suka kashe min ita, bata magana ma amma basu barta ba, tana fama da cancer amma basu barta ba, ɗan albarka da take sa min kullum ma sun katse" ta dinga safa da marwa ƙarshe ta faɗi ƙasa tim saboda hajijiya... Ba a gama juyayin rasuwar sirikar Gwamna ba, special adviser na Gwamna ya fito ya bayyana cewa an sace matar Gwamna Asiya Kachallah. Umaru Kwom yana gidansa yana sauraren masu kawo masa gulmar yadda mutanen gari ke yabonsa aka fito da labarin da ya girgiza shi. "An sace Asiya Kachallah?. This is a set up" ya faɗa cike da damuwa domin ya hango ma'anar hakan. Saifuddeen Kachallah ba zai iya amfani da iyalinsa wajen Kamfen ba amma akwai wanda zai iya...Alhaji Sani Kachallah. Kafin dare maganar Siyasa ba gaba bace ta rikiɗe ta koma *#Save Asiya Kachallah?* Ale Faruƙ ya zo ta'aziya dan bai samu sallar jana'iza ba. Daya zo ne kuma ya samu labarin sace Asiya da akayi. Abin ya ɗaure masa kai, taya za a sace Matar Gwamna guda?. A matsayinsa na Uba ya ji ba daɗi, ya shiga ruɗu, dan har gwada kiran numbar Asiya yai ko za a dace ta ɗauka, ƙila wani wajen ta shiga ba a sani ba. Bai bar cikin jaha ba sai chan yammaci, ya tafi da niyyar idan anji wani labari akan Asiya zai dawo. Ga sauran ahalin Malam Nuhu kuma, kowa ka gani ciki kasan baya cikin kwanciyar hankali. Abba dannewa kawai yake amma kusan shi yafi kowa damuwa a gidan, shi daya rasa matarsa uwar 'ya'yansa uku, biyar idan ka haɗa da wanda ya rasu kafin a haifi Ali da kuma wanda ta tafi da shi a cikinta. Tun bayan rasuwan Hassana mahaifiyar Ubayd sai daya auri Zainabu Kurma ne ya samu nitsuwa. Kai, zai iya cewa Zainabu tafi Hassana kodan zaman da yai da Hassana shekaru biyune da burbuɗi, ita kuma Zainabu shekaru goma shatara ba wata biyu. *** "Saifuddeen...Saifuddeen...Darling. idan baka ci abinci ba taya zaka samu ƙarfin yiwa Jahar nan aiki?" Gwamna Saifuddeen ya ɗago rinannun idanunsa ya kalli Bilkisu. Abinci ne ƙarshen abinda zai sa a ransa yanzu. "We can fix this amma sai ka kwantar da hankalinka. Without food, ƙwaƙwalwarka ba zata iya aikin komai ba" "Azumi nake Bilkisu" "Idan anyi Azumi ai ana shan ruwa, rabonka da abinci tun jiya fa Saifuddeen" "Kawo min Apple" "Apple kaɗai za ka ci?" "Ki haɗo da ruwa mai sanyi"... A ɓangaren Asiya bata farfaɗo ba sai lokacin da aka kawo mata abincin dare. Suna ganinta haka hankalinsu ya tashi suka shiga yayyafa mata ruwa har sai da suka ga ta jaa dogon numfashi kafin suka daina yayyafa ruwan. Babu yadda ba suyi ba akan ta ci abinci amma ta ƙi, dan su tunaninsu abincin da bata ci bane tunda aka kawota ya sata suma. Sai da ta shammacesu sun sake jiki suna mata magana tayi wuf, ta nufi hanyar ƙofa da gudu amma bata kaiba aka sake mata bindiga a baya. Harsashin dake cikin bindigar wata allura ce dake saka mutum bacci dan haka allurar na cakarta ko sakan biyu bai cika ba, ta faɗi a wajen. Bilkisu Kachallah tana zaune kusa da Gwamna tana yanka masa Apple wayarta ya shiga ƙara. "Ki ɗauka mana" Gwamna ya faɗa ganin ta share wayar duk da kuwa ta gama yanka Apple ɗin. "Ƙila masu neman kuɗi ne" Gwamna bai ce komai ba ya dai cigaba da cin Apple a hankali, ba dan daɗi ba sai dan dole ne ya sa wani abu a ciki duk da ya ɗau alkawarin yin Azumi har ranan da za'a ga Asiya... "Nace ban yarda ta fita ba, idan taƙi cin abinci ruwanta ne. Idan kuka ga ta galabaita ku mata ɗure, ban damu da lafiyarta ba but keep her alive" "Waye a nan?" ta faɗa lokacin data juyo tana sauke waya daga kunnenta. "Lah! Hajjajuna dama ina so na nemi wata alfarma ne" Bilkisu Kachallah ta harari Hansa'u tace "shine zaki shigomin ɗaki ba sallama" "Kwarankwatsi tun ɗazu nake ta sallama a bakin ƙofa ba ki amsa ba, shine na shigo" "Minene?" Bilkisu ta faɗa da kakkausar murya. Hansa'u ta tsugunna tace "An bugo wai Gyatumata bata da lafiya" Ba zata taɓa manta farkon zuwanta gidan ba. Watarana Bilkisu ta kirata ɗaki, tana shigowa sai ta tsaya a tsaye. Kafin ta farga har ta kai ƙasa saboda wani maka da Bilkisun ta kai mata tana faɗin "ina tsaye kina tsaye" Bilkisu tayi tsaki tace "Bakin kine gyatumar ai. Mi kike so?" "Hajjaju ina so Dan Allah ki bani kwana biyu na je na gaisheta" "Kwana biyu? Are you mad, wa zai kula da Junior?" "Ranki shi daɗe akwai su Onome, su Safiya su..." "Duk ciki waya saba da su idan ba ke ba. Ba inda zaki je, zan baki kuɗi ki aika mata, Allah ya bada lafiya" Hansa'u ta langwaɓa kai. Idan kaji Bilkisu tana maganar kula da Junior, zaka ɗauka jariri ne. Yaro ɗan shekara shida amma yadda ake nuna masa gata sai ka ɗauka ɗan goye ne. "Hajjaju a taimaka ko kwana ɗaya ne naje na dawo. Ban sani ba ko jinyar mutuwa ne, ina so mu gana kafin rai yai halinsa" "Idan mutum yai abu sai ku ce shi mugu ne. Kin san dai tunda aka fara Kamfen ba zama nake ba, sannan Junior yana buƙatar kulawa ta musamman" "A taimaka dai, a duba Dan Allah" "Fine. ki je ki dawo a goben" "Nagode Hajjaju" ta faɗa tana riƙe ƙafar Bilkisu. Bilkisu ta yarfe ƙafarta tareda jan tsaki ta fice daga ɗakin. Tana fita Hansa'u tayi murmushi. Washegari Hansa'u data fito daga gidan Gwamnati Keke ta nema ya kaita wani madaidaicin gida. Tana shiga suka gaisa da matar dake kula mata da gidan sanan ta wuce banɗaki tayi wanka. Tana fitowa sanye da towel ta kalli kanta a madubi, shekaru sun ja amma har yanzu tana da kyau. Ba zata taɓa manta ranan da aka kawota gidan Alhaji Rufa'i ba, 'yar ƙauye da ita. A shekaru shashida ba abinda ta sani na uƙubar rayuwa sai data shigo gidan. Ita 'yar ƙauye ce amma a ƙauyensu ita ɗin 'yar babbar mutum ce saboda Baffanta yafi kowa Shanu a ƙauyen dan haka ba cikin wahala ta fito ba. "Aaah, kai Masha Allah! Ashe kyakykyawar Bafulatana aka samo maka Alhaji" maganar Madam Bintu ya sake maimaituwa a ƙwaƙwalwarta. "Wannan ai dana haihu da wuri ai sai dai nayi jika da ita, ba kishin da zan yi da ita Alhaji, ai ni 'ya ka kawo min" Munafukin mutum akwai shi da iya daɗin baki. Ranan da Alhaji Rufa'i ya haɗasu yana musu nasiha Madam Bintu yadda ka san matar Aljannah haka ta dinga maganganu masu daɗi tana nunawa mijinta babu komai. Ita ɗin kamar sadaka ce aka yiwa Alhaji Rufa'i. Tana shekara shauku aka mata baiko da ɗan uwanta Siddiƙu. Watanni uku da baikon aka fara shirye-shiryen biki. Ranan da za a ɗaura aurensu Allah ya masa rasuwa. Daga nan aka yaɓa mata baƙin jini akan tana da farar ƙafa idan ba haka ba taya za ayi mutum lafiyarsa ƙalau ace ranan aurensa ya rasu. Duk wanda aka yiwa tayi a ƙauyensu sai yace a'a yana tsoro, wasu ma har maita suka laƙa mata. A wani zuwan da Alhaji Rufa'i yai ne Baffanta ya masa maganar ko zai sama masa miji a birni dan 'yarsa tayi kwantai. Mamaki ya kama Alhaji Rufa'i lokacin da ya ji shekarun yarinyar shashida amma har ana faɗin tayi kwantai. Duk bayanin da Baffa Kabiru ya masa gani yai kawai jahilci ne irin na 'yan ƙauye. Daga ƙarshe dai da Baffa Kabiru ya masa tayin Rabi'atul Badawiyya sai ya amince, a tunaninsa ƙila za a dace ya samu haihuwa tunda matarsa Bintu shekaru ashirin da ɗaya da aure amma shiru babu haihuwa. Alhaji Rufa'i yana shekara hamsin da biyar ya auri Rabi'atul Badawiyya. Shi ba mazaunin ƙasar bane amma saboda auren sai da ya zauna a gida na watanni uku ko za a dace. Farko farkon aurensu yayi ta yawoce yawocen Asibitoci ciki da wajen ƙasa amma duk zancen ɗaya ne, ba shi da matsala. Bai san dalilin dayasa ya kasa ƙara aure ba tun lokacin, duk da irin matsin lamba da ya ke fuskanta daga 'yanuwansa. Kafin rasuwar mahaifiyarsa sai da aka aura masa mata amma zamansu bai jima ba ta gudu, tace dole sai dai ya saketa har yau bai san dalili ba kuma bai nemi sanin ba. Ƙaddarar aure ne ya shiga tsakaninsa da Badawiyya shiyasa har ya ji sha'warta bayan Baffanta ya masa tayinta. Watanni uku yai bai fita ko'ina ba yana addu'ar Allah yasa a dace. Shiru kuwa har ya tafi ƙasar Germany duba wani kamfaninsa dake chan. Satinsa biyu a chan Likitansa ya kira shi yana masa barka domin Amaryarsa tana ɗauke da cikin sati biyar. Kaman Alhaji Rufa'i yai tsalle ya ganshi a Nigeria haka ya dinga ji, murna a gunsa ba a magana. Jirgin washegari ya booking zai dawo amma ɓarayi suka shiga gidansa suka harbeshi har lahira. Tunda Madam Bintu ta ji bayanin Likita lokacin da ta kai Badawiyya Asibiti bayan ta suma, hankalinta yai mugun tashi. Ƙarshe ta tura kuɗi chan Germany wani Assassin ya je ya kashe Alhaji Rufa'i har gidansa. Lokacin da aka zo maganar rabon gado haka Madam Bintu ta ƙeƙasa kasa akan sai dai a bari Badawiyya ta haihu tukunna wai ai ba sauri suke ba. Ita ta hana 'yanuwan Badawiyya su tafi da ita tace zata kula da ita sosai. Tayi duk abinda za tayi cikin ya zube amma bai zube ba. Ƙarshe ta haƙura zuwa lokacin da za a haifeshi ta kashe jinjirin tace bai zo da rai ba. Ta hana Badawiyya fita, ta dinga gana mata azaba, huron yunwa, aiki kamar jaka da tsoratarwa. Kafin ranan haihuwan gaba ɗaya Badawiyya ta fice daga kamanninta, in fact, ƙwaƙwalwarta ya taɓu. Madam Bintu ce da wata tsohuwar ma'aikaciyarta mai suna Gamboji a cikin gidan, sai kuma maigadi da Dreba. Ranan da Badawiyya ta fara naƙuda Gamboji ce ta kira Madam Bintu akan ko za a kai Badawiyya Asibiti amma Madam Bintu tace fir haihuwan gida zata yi. Gamboji tana tunanin ita zata karɓi haihuwan tunda ba laifi ta manyanta kuma ta taɓa karɓan haihuwan shekarun baya a ƙauyensu amma sai Madam Bintu tace ita zata karɓi haihuwan wai Gamboji ta je Dreba ya kaita kasuwa ta siyo kayan jarirai saboda ba abinda aka tanada. Gamboji ta fita zuciyarta na wasu-wasi. Badawiyya na cikin ƙunci amma Madam Bintu ko kaɗan bata tausaya mata ba, lokacin da kan yaron ya fara fitowa haka ta dinga turashi ciki da ƙarfi dan kar ya fito, so take ya mutu a ciki kar ma ya fito duniya. Badawiyya tun tana kuka har wahala yasa tayi dogon suma. Ganin kan yaron ya koma ta ƙarfi sai ta fara duba alamun numfashi a tattare da Badawiyya amma bata gani ba. "Sa'a biyu kenan, shegiyar itama ta koma" Madam Bintu ta yarfe gumi ta fice daga ɗakin tana jiran dawowar Gamboji. Da Gamboji ta dawo kuwa samun Madam Bintu tayi a falo tana kuka. "Madam miya faru?" "Badawiyya ta mutu Gamboji" Gamboji ta wuce ɗakin da gudu tana salati. "Madam ya aka yi? Lafiya na tafi na barta fa" Ba ta iya yin musu ba lokacin da Madam Bintu ta ce tayiwa Badawiyya wanka ta mata sutura kafin ta dawo, idan ta dawo zata kira mutane ta faɗa musu cewa Badawiyya ta rasu wajen haihuwa, sannan babu mahalukin da zai san ita ce ta karɓi haihuwan Badawiyya. Tana da 'ya'ya biyu a ƙauye, kowacce da iyalinta. Madam Bintu tayi alƙawarin kashe mata 'ya'ya da jikoki idan ta buɗe bakinta ta faɗi abinda ya faru. Fitar Madam Bintu daga gidan, Gamboji ta kasa zaune ta kasa tsaye, jikinta sai ƙyarma yake. Ba wai bata taɓa yiwa gawa wanka bane amma wannan gawar daban ce. Ta sani Madam Bintu ce ta kashe Badawiyya. Sanda ta fara yiwa Badawiyya wanka ne kuma baiwar Allah ta farfaɗo, da ke Allah yayi da sauran numfashinta a duniya. Gamboji ta tsorata ta fice daga gidan da gudu tana ihu. Maigadi ne ya kamota ya fara tambayar lafiya. Da ƙyar Gamboji ta iya yi masa bayanin komai. Maigadi ya shawo kanta da ƙyar suka koma cikin gidan. Sai da Maigadi ya shiga ya tabbatar Badawiyya da ranta kafin ya fito ya sanar da Gamboji da ke zaune a falo tana rawan jiki. Bayan ta shiga ta tabbatar Badawiyya ba mutuwa tayi ba sannan suka shiga shawaran ya za ayi, idan suka bari Madam Bintu ta dawo to ba makawa sun kaɗe sannan Badawiyyar ba zata tsira ba tunda sun ga manufar Madam Bintu akanta. Ƙarshe Maigadi ya kawo wata shawara. Dake maiɗakinsa itama a gidan take sai kawai suka nemo taxi suka saka Badawiyya a ciki Kande matar Maigadi ta wuce da ita Asibitin Dr Mustafah wanda ya kasance likitan Alhaji Rufa'i kuma aboki gareshi. Da Madam Bintu ta dawo Gamboji ta faɗa mata cewa 'yanuwan Badawiyya ne suka zo suka ɗauketa wai zasu binneta a chan ƙauyensu. Tunda Malaminta ya faɗa mata babu mai sake ɗago maganar gado ta sawa kanta salama ko ma ya akayi da gawar Badawiyya bai dameta ba. Ba dan an kaita wajen Dr Mustafah da wuri ba da mutuwa za ta yi na gaskiya saboda jini da taketa zubarwa. Hansa'u ta shafa cikinta. Shekaru sun ja amma ba zata manta cewa akwai ɗan daya taɓa zama a ciki ba, ba zata manta cewa saboda Madam Bintu Likitoci sun tabbatar mata ba zata sake haihuwa ba. Bilkisu Kachallah ɗaya take da Madam Bintu, shiyasa zata iya sawa a sace matar mijinta har ma tayi iƙirarin bata damu da lafiyarta ba. Koma minene ta kusa ƙarisa aikinta tunda taga inda Bilkisu Kachallah take ajiye mahimman takardunta. Da zaran ta samu Engineer ɗinsu ya gano mata yadda ake buɗe akwatin shikenan komai ya ƙare. Game over. Ita kuma Madam Bintu Chadi sai ta karɓi komai da ta tara da gumin Alhaji Rufa'i ta kuma turata kurkuku.. Sai da Rabi'atul Badawiyya Kabir ta sarawa Oganta kafin ta zauna tana murmushi lokacin da ya ce Barka da zuwa Hansa'u. Sai da ya sa aka kawo mata coffee kafin ya fara bayani. "Badawiyya na san yadda wannan aiki yake da mahimmanci a gareki. Kin sadaukar da komai naki akan wannan case ɗin but unfortunately ƙasarmu bata buƙatar masu jajircewa irinki. Bilkisu Kachallah tanada protection daga sama" "Ban gane ba" Ya ja dogon numfashi yace "an rufe case ɗin, in fact yanzu ba a zargin Bilkisu Kachallah da Bintu Chadi da safarar miyagun ƙwayoyi" "Impossible Sir, akwai audio proof na hirarsu, written document kawai nake jira kuma shima na kusa samu. Sir Bilkisu Kachallah da Madam Bintu suna shigo da ƙwaya ƙasar nan" " na yadda Badawiyya, sai dai abinda zaki fahimta shine ba su kaɗai bane masu wannan harka kuma an gano cewa ana bincike akansu shiyasa aka ce a rufe file ɗin case ɗin" "Sir tayaya za a rufe? This people import things that kill our youths. Matasanmu sun lalace da shaye-shaye alot of criminal activities yana faruwa ne saboda shaye-shaye" "I know. Amma daga sama ne Rabi'ah. Sunce a terminating assignment ɗinki dan haka dole ki bar wannan case ɗin ki dawo office" "Ba zan iya ba Sir, i need this case, ka san case ɗin nan is personal to me" "I'm sorry, amma dole ki haƙura da aikin" Badawiyya ta rintse ido tana jin wani ƙunci a ranta. Tayi tunanin zata samu abinda take so shiyasa ta jona aikin force tun lokacin data dawo ƙasar. Case ɗin Bintu take nema aka bata harda na Bilkisu, ba zata iya zama wajen Bintu ba saboda zata iya kasheta abinda therapist ɗinta ya faɗa kenan shiyasa ta zaɓi zama gidan Bilkisu Kachallah dan tayi bincike. "Ki yi haƙuri Badawiyya" Oganta ya sake maimaitawa. "Ka bani lokaci dan Allah na ƙarisa aikin nan, just small time, dana samu papers ɗin ba zan turawa kowa ba sai DEA na America, they will intervane" "Badawiyya it's risky" "Sati biyu Dan Allah" Oga yai shiru yana nazari sannan yace "sati biyu Badawiyya, idan ya wuce haka i can't cover for you, kuma zaki sa kanki cikin hatsari ne" "Nagode Sir"   ***   Wanda suka sace ɗalibai sun fito sun bayyana cewa suna buƙatar miliyan ɗari kafin su sake ɗaliban, amma basu yi maganar Asiya Kachallah ba. A ɓangaren Gwamna Saifuddeen Kachallah kuwa ikon Allah ne yasa bai haukace ba, abubuwa sun masa yawa, ga yaran da ake nema ga kuma Asiya da kullum yake kwana da ita ya tashi. Ina take? Tana lafiya? Wani hali take ciki? Rashin samun amsoshin nan ya birkita masa tunani. A wani gefen kuma ga ayyukan Jaha sannan kamfen da ya zame masa dole. Umaru Kwom ma yana taka tsantsan da wannan sabon yanayi. Maganar sace Asiya Kachallah ya ɓata masa shiri domin yanzu tausayin Gwamna ake maimakon zaginsa da ake a da saboda gazawarsa. Ba abinda ya ƙara ɗaga masa hankali sai da ya ga Bilkisu Kachallah ta zargi 'yan adawa akan cewa sune da hannu a wannan sace-sacen da ake kuma da sannu komai zai warware. Daga wannan maganar rating ɗinsa ya fara sauka yayinda na Gwamna S S Kachallah ya ke ɗaguwa. Yayinda ake wasa da rayukan yara ƙanana saboda siyasa, su iyayen yara suna cikin tashin hankali marar misaltuwa. Akwai wata uwa wacce aka sacewa ɗa ɗaya da Allah ya bata sai da shock ya sata faɗuwa ɓarin jikinta ya shanye. Su ma iyayen Asiya da basu san a wani hali 'yarsu take ba suna cikin jimami da addu'ar Allah ya bayyanata. A inda aka ɓoye Asiya kuwa ta ƙi cin komai sai kuka, kullum saƙa yadda zata ɗau fansar duk wanda ya mata wannan abu take. Har lokacin ta ƙi cin abinci, ruwa kawai ta ke ɗan sha a famfo idan za ta yi alwala a banɗaki. A kwana na huɗu da ɓatan Asiya aka sake sace wasu 'yan Islamiyya yara ƙanana irin 'yan rabin ajin nan su guda bakwai. A ɓangaren Umaru Kwom ya ɗaura aniyar har a zo zaɓe ba zai bari Jahar Congo ta samu lafiya ba. Idan an ɓoye Asiya Kachallah ne saboda a ɓata masa shiri to zai ga yadda za su yi idan aka cigaba da sace ɗaliban makaranta, lokacin babu wanda zai tuna da wata Asiya Kachallah da aka sace. A ranan da aka sace 'yan Islamiyya Gwamna ya sauke wasu Kwamishinoni da wasu special advisers guda biyar daga kan muƙamansu, ya naɗa wasu tareda faɗin suma zasu tafi idan ba a samo ɗaliban da aka sace da matarsa ba. Asiya bata ga wannan news ɗin ba. Lokacin data kunna TV tun bayan ganin rahoton mutuwar mahaifiyarta da tayi, taron addu'a da first lady Bilkisu Kachallah ta haɗa ake nunawa. Taron mata ne kowa a wajen ya sha anko, wasu sun saka farin leshi da head gear orange, wasu kuma sun saka atampa blue. Bilkisu Kachallah ta hau podium ta fara bayani kan yadda 'yan adawa suke ɓatawa Gwamnatin Saifuddeen Kachallah suna. Ta buge da karanta suratul Quraishi, ta karantata gayau babu tajweed ba komai, cike da kura kurai. Ta haɗa da addu'ar Allah ya bayyana yaran da aka sace da kuma ƙanwarta Asiya. Daga ƙarshe ta buge da kuka. Aka kira wata Malama tayi karatun ƙur'ani kafin aka bawa wata Evangelist dama ta zo tayi addu'a. Wasu Mata Yarabawa suka fito suna addu'a da waƙa suna rawa, da suka gama aka kira wasu mata da suka yi shigar fararen kaya, basu sa takalmi ba, sannan ba ɗankunne a kunnensu. Suka dinga tsalle suna sumbatu duk dai da sunar addu'a. Asiya na zaune tana kallo yayinda ƙwaƙwalwarta ke lissafin abinda yake faruwa. Ita ɗin hajar Kafen ce, ita ɗin decoy ce, ita ɗin bata da matsayi a wajen Gwamna Kachallah sai dai yai amfani da ita ya yar. Bata san ina ta samu ƙarfi ba, lokacin da aka nuno Gwamna Saifuddeen Kachallah yana magana table ɗin dake ɗakin ta ɗauka ta bugawa TVn tana faɗin *I hate you Saifuddeen Kachallah* *ba ruwana na yi nan* 7 Misalin ƙarfe bakwai na safe Alhaji Umaru Kwom yana karyawa aka kira shi aka sanar da shi rasuwan sirikar Gwamna, da farko ma mahaifiyar Bilkisu Kachallah ya ɗauka sai da wanda ya kira ɗin ya jaddada masa cewa matar Malam Nuhu Principal ce. Bayan ya ajiye wayar yai murmushi. Matarsa da ke gefe tace "Alhaji lafiya naga kana murmushi, ba maganar rasuwa aka maka ba?" "Rasuwa ce da ta buɗe min wata dama" "Wa ya rasu?" "Mahaifiyar Asiya Kachallah" ya amsa mata har lokacin bai bar murmushi ba. Hajiya Mariya ta yiwa Umma addu'ar samun rahama yayinda mijinta ya cigaba da cin abinci ba tareda ya amsa addu'ar da Amin ba. *** Jiya yadda Gwamna ya ga rana haka yaga dare, bai rintsa ba ko kaɗan. Lokacin daya je Kachallah House tambayar Alhaji Sani yai ko yana da hannu wajen sace Asiya amma yace masa bai da masaniya akan haka. "Baba dan Allah kayi haƙuri idan ma ..." "Saifu baka yarda dani bane? Kana ga zan maka ƙarya ne?" "Ka yi haƙuri, ba haka nake nufi ba" "Ba zan yi wasa da rayuwar iyalinka ba Saifu. Ina zargin Umaru Kwom da hannu akan wannan, amma zan sa a bincika mani komai" To mi Umaru Kwom yake nufi da sace Asiya? Da wannan tambayar ya raya darensa, yayinda wani ɓangare na zuciyarsa ya ke zargin kansa da sakaci da yai da rayuwar Asiya. Idan da ya haɗata da masu tsaro ƙila haka ba zai faru ba. Ahalin gidan Malam Nuhu Principal kuwa sun kwana sun tashi ne da juyayin mutuwar Umma da kuma rashin sanin inda Asiya take. Tun dare aka yiwa Umma sutura ana jiran gari ya waye a kaita makwancinta. Washegari da safe gidan ya cika sosai, 'yanuwa da abokan arziƙi da ke kusa duk sunzo. Tun safe aka fitar da labari cewa Allah ya yiwa mahaifiyar Matar Gwamna rasuwa. Abin mamaki tawagar Alhaji Umaru Kwom ce ta fara isowa kafin ta Gwamna ta iso minti shaɗaya tsakani. Gwamna rufe idonsa yai da baƙin gilashi saboda kar a ga kumburarrun idanuwansa. Gwamna yana isowa ƙarfe tara da minti biyar aka yiwa Umma Sallah sannan aka wuce da ita maƙabarta. Gwamna Saifuddeen bai yi niyyar wucewa maƙabarta ba amma yana shiga mota Alhaji Sani ya kirashi yace ya wuce maƙabarta saboda Alhaji Umaru Kwom nan zai je. Innalillahi akan aikin ladan ma sai an saka siyasa a ciki. Haka dai aka wuce da Gwamna maƙabarta. Asiya bata kunna TV ba. Tsoro take ji, gani take idan ta kunna ne abinda aka faɗa zai tabbata, amma idan bata kunna ba Ummanta za ta kasance kwance a Asibiti ba abunda ya sameta. Sai kusan ƙarfe goma da rabi saura ta samu ƙarfin gwiwar kunna TV ɗin. Kamar yarinya haka ta zauna a gaban TV ta naɗe kafafuwanta ta riƙe fiskanta da hannayenta biyu. Hill TV ta kunna, ta san suna ƙoƙarin fitar da labarun gaskiya ba kamar Congo News ba. Ƙarfe goma da rabi suka sako maimaicin labaren safe. Labarin farko a kanun labaren shine rasuwan mahaifiyar matar Gwamna wato Asiya Kachallah. Haka Asiya ta baza ido tana kallon labaran. Aka nuna wajen da Alhaji Umaru Kwom yazo yana gaisawa da su Abba, aka nuna wajen da Gwamna shima ya iso, sannan aka ɗan nuna wajen da ake yiwa gawar Umma sallah, aka nuno wajen da ake saka gawar Umma a cikin ƙabari. Daga ƙarshe aka nuna Gwamna yana yiwa iyalen Malam Nuhu Gidaɗo ta'aziyya sannan aka nuna Alhaji Umaru Kwom shima yana yiwa Gwamna da iyalinsa ta'aziyya. Da gangan ɗan jarida ya tambayeshi ko miye dalilin daya sa ya halarci sallan sirikar Gwamna sannan har ya zo maƙabarta akayi biso da shi. Umaru Kwom ya karkata kai yace *"watoo, ita siyasa ba gaba bace"* kafin ka ce me a duniyar yanar gizo mutane sun ɗauki kalmomin Umaru Kwom suna masa kamfen da shi *#Siyasa ba gaba bace* Ta ko'ina a faɗin jihar sai maganan ƙarfin hali, jajircewa da kuma imani irin na Umaru Kwom ake. Hatta wasu masu faɗa aji a ƙasar sai da suka yaba da Umaru Kwom. Asiya tana ganin rahoton amma hawaye ko ɗaya bai fito ba, zuciyarta ya yi mata nauyi. Tana ji kamar kumbura zuciyar take, nan da anjima kaɗan zata fashe, idan ta fashe kuma sai itama a kaita inda aka kai Umma. Sai dai haka ta zauna a wajen tana jiran zuciyar ta fashe amma taƙi fashewa, bata ma da alamar zata yi komai saboda duk yadda take dokawa cikin ƙirjinta babu abinda ya faru. Kamar wata zararriya ta tashi tsaye tana safa da marwa a ɗakin tana faɗin "sun kashe Umma, sun kashe min mahaifiya, ba abinda ta musu suka kashe min ita, bata magana ma amma basu barta ba, tana fama da cancer amma basu barta ba, ɗan albarka da take sa min kullum ma sun katse" ta dinga safa da marwa ƙarshe ta faɗi ƙasa tim saboda hajijiya... Ba a gama juyayin rasuwar sirikar Gwamna ba, special adviser na Gwamna ya fito ya bayyana cewa an sace matar Gwamna Asiya Kachallah. Umaru Kwom yana gidansa yana sauraren masu kawo masa gulmar yadda mutanen gari ke yabonsa aka fito da labarin da ya girgiza shi. "An sace Asiya Kachallah?. This is a set up" ya faɗa cike da damuwa domin ya hango ma'anar hakan. Saifuddeen Kachallah ba zai iya amfani da iyalinsa wajen Kamfen ba amma akwai wanda zai iya...Alhaji Sani Kachallah. Kafin dare maganar Siyasa ba gaba bace ta rikiɗe ta koma *#Save Asiya Kachallah?* Ale Faruƙ ya zo ta'aziya dan bai samu sallar jana'iza ba. Daya zo ne kuma ya samu labarin sace Asiya da akayi. Abin ya ɗaure masa kai, taya za a sace Matar Gwamna guda?. A matsayinsa na Uba ya ji ba daɗi, ya shiga ruɗu, dan har gwada kiran numbar Asiya yai ko za a dace ta ɗauka, ƙila wani wajen ta shiga ba a sani ba. Bai bar cikin jaha ba sai chan yammaci, ya tafi da niyyar idan anji wani labari akan Asiya zai dawo. Ga sauran ahalin Malam Nuhu kuma, kowa ka gani ciki kasan baya cikin kwanciyar hankali. Abba dannewa kawai yake amma kusan shi yafi kowa damuwa a gidan, shi daya rasa matarsa uwar 'ya'yansa uku, biyar idan ka haɗa da wanda ya rasu kafin a haifi Ali da kuma wanda ta tafi da shi a cikinta. Tun bayan rasuwan Hassana mahaifiyar Ubayd sai daya auri Zainabu Kurma ne ya samu nitsuwa. Kai, zai iya cewa Zainabu tafi Hassana kodan zaman da yai da Hassana shekaru biyune da burbuɗi, ita kuma Zainabu shekaru goma shatara ba wata biyu. *** "Saifuddeen...Saifuddeen...Darling. idan baka ci abinci ba taya zaka samu ƙarfin yiwa Jahar nan aiki?" Gwamna Saifuddeen ya ɗago rinannun idanunsa ya kalli Bilkisu. Abinci ne ƙarshen abinda zai sa a ransa yanzu. "We can fix this amma sai ka kwantar da hankalinka. Without food, ƙwaƙwalwarka ba zata iya aikin komai ba" "Azumi nake Bilkisu" "Idan anyi Azumi ai ana shan ruwa, rabonka da abinci tun jiya fa Saifuddeen" "Kawo min Apple" "Apple kaɗai za ka ci?" "Ki haɗo da ruwa mai sanyi"... A ɓangaren Asiya bata farfaɗo ba sai lokacin da aka kawo mata abincin dare. Suna ganinta haka hankalinsu ya tashi suka shiga yayyafa mata ruwa har sai da suka ga ta jaa dogon numfashi kafin suka daina yayyafa ruwan. Babu yadda ba suyi ba akan ta ci abinci amma ta ƙi, dan su tunaninsu abincin da bata ci bane tunda aka kawota ya sata suma. Sai da ta shammacesu sun sake jiki suna mata magana tayi wuf, ta nufi hanyar ƙofa da gudu amma bata kaiba aka sake mata bindiga a baya. Harsashin dake cikin bindigar wata allura ce dake saka mutum bacci dan haka allurar na cakarta ko sakan biyu bai cika ba, ta faɗi a wajen. Bilkisu Kachallah tana zaune kusa da Gwamna tana yanka masa Apple wayarta ya shiga ƙara. "Ki ɗauka mana" Gwamna ya faɗa ganin ta share wayar duk da kuwa ta gama yanka Apple ɗin. "Ƙila masu neman kuɗi ne" Gwamna bai ce komai ba ya dai cigaba da cin Apple a hankali, ba dan daɗi ba sai dan dole ne ya sa wani abu a ciki duk da ya ɗau alkawarin yin Azumi har ranan da za'a ga Asiya... "Nace ban yarda ta fita ba, idan taƙi cin abinci ruwanta ne. Idan kuka ga ta galabaita ku mata ɗure, ban damu da lafiyarta ba but keep her alive" "Waye a nan?" ta faɗa lokacin data juyo tana sauke waya daga kunnenta. "Lah! Hajjajuna dama ina so na nemi wata alfarma ne" Bilkisu Kachallah ta harari Hansa'u tace "shine zaki shigomin ɗaki ba sallama" "Kwarankwatsi tun ɗazu nake ta sallama a bakin ƙofa ba ki amsa ba, shine na shigo" "Minene?" Bilkisu ta faɗa da kakkausar murya. Hansa'u ta tsugunna tace "An bugo wai Gyatumata bata da lafiya" Ba zata taɓa manta farkon zuwanta gidan ba. Watarana Bilkisu ta kirata ɗaki, tana shigowa sai ta tsaya a tsaye. Kafin ta farga har ta kai ƙasa saboda wani maka da Bilkisun ta kai mata tana faɗin "ina tsaye kina tsaye" Bilkisu tayi tsaki tace "Bakin kine gyatumar ai. Mi kike so?" "Hajjaju ina so Dan Allah ki bani kwana biyu na je na gaisheta" "Kwana biyu? Are you mad, wa zai kula da Junior?" "Ranki shi daɗe akwai su Onome, su Safiya su..." "Duk ciki waya saba da su idan ba ke ba. Ba inda zaki je, zan baki kuɗi ki aika mata, Allah ya bada lafiya" Hansa'u ta langwaɓa kai. Idan kaji Bilkisu tana maganar kula da Junior, zaka ɗauka jariri ne. Yaro ɗan shekara shida amma yadda ake nuna masa gata sai ka ɗauka ɗan goye ne. "Hajjaju a taimaka ko kwana ɗaya ne naje na dawo. Ban sani ba ko jinyar mutuwa ne, ina so mu gana kafin rai yai halinsa" "Idan mutum yai abu sai ku ce shi mugu ne. Kin san dai tunda aka fara Kamfen ba zama nake ba, sannan Junior yana buƙatar kulawa ta musamman" "A taimaka dai, a duba Dan Allah" "Fine. ki je ki dawo a goben" "Nagode Hajjaju" ta faɗa tana riƙe ƙafar Bilkisu. Bilkisu ta yarfe ƙafarta tareda jan tsaki ta fice daga ɗakin. Tana fita Hansa'u tayi murmushi. Washegari Hansa'u data fito daga gidan Gwamnati Keke ta nema ya kaita wani madaidaicin gida. Tana shiga suka gaisa da matar dake kula mata da gidan sanan ta wuce banɗaki tayi wanka. Tana fitowa sanye da towel ta kalli kanta a madubi, shekaru sun ja amma har yanzu tana da kyau. Ba zata taɓa manta ranan da aka kawota gidan Alhaji Rufa'i ba, 'yar ƙauye da ita. A shekaru shashida ba abinda ta sani na uƙubar rayuwa sai data shigo gidan. Ita 'yar ƙauye ce amma a ƙauyensu ita ɗin 'yar babbar mutum ce saboda Baffanta yafi kowa Shanu a ƙauyen dan haka ba cikin wahala ta fito ba. "Aaah, kai Masha Allah! Ashe kyakykyawar Bafulatana aka samo maka Alhaji" maganar Madam Bintu ya sake maimaituwa a ƙwaƙwalwarta. "Wannan ai dana haihu da wuri ai sai dai nayi jika da ita, ba kishin da zan yi da ita Alhaji, ai ni 'ya ka kawo min" Munafukin mutum akwai shi da iya daɗin baki. Ranan da Alhaji Rufa'i ya haɗasu yana musu nasiha Madam Bintu yadda ka san matar Aljannah haka ta dinga maganganu masu daɗi tana nunawa mijinta babu komai. Ita ɗin kamar sadaka ce aka yiwa Alhaji Rufa'i. Tana shekara shauku aka mata baiko da ɗan uwanta Siddiƙu. Watanni uku da baikon aka fara shirye-shiryen biki. Ranan da za a ɗaura aurensu Allah ya masa rasuwa. Daga nan aka yaɓa mata baƙin jini akan tana da farar ƙafa idan ba haka ba taya za ayi mutum lafiyarsa ƙalau ace ranan aurensa ya rasu. Duk wanda aka yiwa tayi a ƙauyensu sai yace a'a yana tsoro, wasu ma har maita suka laƙa mata. A wani zuwan da Alhaji Rufa'i yai ne Baffanta ya masa maganar ko zai sama masa miji a birni dan 'yarsa tayi kwantai. Mamaki ya kama Alhaji Rufa'i lokacin da ya ji shekarun yarinyar shashida amma har ana faɗin tayi kwantai. Duk bayanin da Baffa Kabiru ya masa gani yai kawai jahilci ne irin na 'yan ƙauye. Daga ƙarshe dai da Baffa Kabiru ya masa tayin Rabi'atul Badawiyya sai ya amince, a tunaninsa ƙila za a dace ya samu haihuwa tunda matarsa Bintu shekaru ashirin da ɗaya da aure amma shiru babu haihuwa. Alhaji Rufa'i yana shekara hamsin da biyar ya auri Rabi'atul Badawiyya. Shi ba mazaunin ƙasar bane amma saboda auren sai da ya zauna a gida na watanni uku ko za a dace. Farko farkon aurensu yayi ta yawoce yawocen Asibitoci ciki da wajen ƙasa amma duk zancen ɗaya ne, ba shi da matsala. Bai san dalilin dayasa ya kasa ƙara aure ba tun lokacin, duk da irin matsin lamba da ya ke fuskanta daga 'yanuwansa. Kafin rasuwar mahaifiyarsa sai da aka aura masa mata amma zamansu bai jima ba ta gudu, tace dole sai dai ya saketa har yau bai san dalili ba kuma bai nemi sanin ba. Ƙaddarar aure ne ya shiga tsakaninsa da Badawiyya shiyasa har ya ji sha'warta bayan Baffanta ya masa tayinta. Watanni uku yai bai fita ko'ina ba yana addu'ar Allah yasa a dace. Shiru kuwa har ya tafi ƙasar Germany duba wani kamfaninsa dake chan. Satinsa biyu a chan Likitansa ya kira shi yana masa barka domin Amaryarsa tana ɗauke da cikin sati biyar. Kaman Alhaji Rufa'i yai tsalle ya ganshi a Nigeria haka ya dinga ji, murna a gunsa ba a magana. Jirgin washegari ya booking zai dawo amma ɓarayi suka shiga gidansa suka harbeshi har lahira. Tunda Madam Bintu ta ji bayanin Likita lokacin da ta kai Badawiyya Asibiti bayan ta suma, hankalinta yai mugun tashi. Ƙarshe ta tura kuɗi chan Germany wani Assassin ya je ya kashe Alhaji Rufa'i har gidansa. Lokacin da aka zo maganar rabon gado haka Madam Bintu ta ƙeƙasa kasa akan sai dai a bari Badawiyya ta haihu tukunna wai ai ba sauri suke ba. Ita ta hana 'yanuwan Badawiyya su tafi da ita tace zata kula da ita sosai. Tayi duk abinda za tayi cikin ya zube amma bai zube ba. Ƙarshe ta haƙura zuwa lokacin da za a haifeshi ta kashe jinjirin tace bai zo da rai ba. Ta hana Badawiyya fita, ta dinga gana mata azaba, huron yunwa, aiki kamar jaka da tsoratarwa. Kafin ranan haihuwan gaba ɗaya Badawiyya ta fice daga kamanninta, in fact, ƙwaƙwalwarta ya taɓu. Madam Bintu ce da wata tsohuwar ma'aikaciyarta mai suna Gamboji a cikin gidan, sai kuma maigadi da Dreba. Ranan da Badawiyya ta fara naƙuda Gamboji ce ta kira Madam Bintu akan ko za a kai Badawiyya Asibiti amma Madam Bintu tace fir haihuwan gida zata yi. Gamboji tana tunanin ita zata karɓi haihuwan tunda ba laifi ta manyanta kuma ta taɓa karɓan haihuwan shekarun baya a ƙauyensu amma sai Madam Bintu tace ita zata karɓi haihuwan wai Gamboji ta je Dreba ya kaita kasuwa ta siyo kayan jarirai saboda ba abinda aka tanada. Gamboji ta fita zuciyarta na wasu-wasi. Badawiyya na cikin ƙunci amma Madam Bintu ko kaɗan bata tausaya mata ba, lokacin da kan yaron ya fara fitowa haka ta dinga turashi ciki da ƙarfi dan kar ya fito, so take ya mutu a ciki kar ma ya fito duniya. Badawiyya tun tana kuka har wahala yasa tayi dogon suma. Ganin kan yaron ya koma ta ƙarfi sai ta fara duba alamun numfashi a tattare da Badawiyya amma bata gani ba. "Sa'a biyu kenan, shegiyar itama ta koma" Madam Bintu ta yarfe gumi ta fice daga ɗakin tana jiran dawowar Gamboji. Da Gamboji ta dawo kuwa samun Madam Bintu tayi a falo tana kuka. "Madam miya faru?" "Badawiyya ta mutu Gamboji" Gamboji ta wuce ɗakin da gudu tana salati. "Madam ya aka yi? Lafiya na tafi na barta fa" Ba ta iya yin musu ba lokacin da Madam Bintu ta ce tayiwa Badawiyya wanka ta mata sutura kafin ta dawo, idan ta dawo zata kira mutane ta faɗa musu cewa Badawiyya ta rasu wajen haihuwa, sannan babu mahalukin da zai san ita ce ta karɓi haihuwan Badawiyya. Tana da 'ya'ya biyu a ƙauye, kowacce da iyalinta. Madam Bintu tayi alƙawarin kashe mata 'ya'ya da jikoki idan ta buɗe bakinta ta faɗi abinda ya faru. Fitar Madam Bintu daga gidan, Gamboji ta kasa zaune ta kasa tsaye, jikinta sai ƙyarma yake. Ba wai bata taɓa yiwa gawa wanka bane amma wannan gawar daban ce. Ta sani Madam Bintu ce ta kashe Badawiyya. Sanda ta fara yiwa Badawiyya wanka ne kuma baiwar Allah ta farfaɗo, da ke Allah yayi da sauran numfashinta a duniya. Gamboji ta tsorata ta fice daga gidan da gudu tana ihu. Maigadi ne ya kamota ya fara tambayar lafiya. Da ƙyar Gamboji ta iya yi masa bayanin komai. Maigadi ya shawo kanta da ƙyar suka koma cikin gidan. Sai da Maigadi ya shiga ya tabbatar Badawiyya da ranta kafin ya fito ya sanar da Gamboji da ke zaune a falo tana rawan jiki. Bayan ta shiga ta tabbatar Badawiyya ba mutuwa tayi ba sannan suka shiga shawaran ya za ayi, idan suka bari Madam Bintu ta dawo to ba makawa sun kaɗe sannan Badawiyyar ba zata tsira ba tunda sun ga manufar Madam Bintu akanta. Ƙarshe Maigadi ya kawo wata shawara. Dake maiɗakinsa itama a gidan take sai kawai suka nemo taxi suka saka Badawiyya a ciki Kande matar Maigadi ta wuce da ita Asibitin Dr Mustafah wanda ya kasance likitan Alhaji Rufa'i kuma aboki gareshi. Da Madam Bintu ta dawo Gamboji ta faɗa mata cewa 'yanuwan Badawiyya ne suka zo suka ɗauketa wai zasu binneta a chan ƙauyensu. Tunda Malaminta ya faɗa mata babu mai sake ɗago maganar gado ta sawa kanta salama ko ma ya akayi da gawar Badawiyya bai dameta ba. Ba dan an kaita wajen Dr Mustafah da wuri ba da mutuwa za ta yi na gaskiya saboda jini da taketa zubarwa. Hansa'u ta shafa cikinta. Shekaru sun ja amma ba zata manta cewa akwai ɗan daya taɓa zama a ciki ba, ba zata manta cewa saboda Madam Bintu Likitoci sun tabbatar mata ba zata sake haihuwa ba. Bilkisu Kachallah ɗaya take da Madam Bintu, shiyasa zata iya sawa a sace matar mijinta har ma tayi iƙirarin bata damu da lafiyarta ba. Koma minene ta kusa ƙarisa aikinta tunda taga inda Bilkisu Kachallah take ajiye mahimman takardunta. Da zaran ta samu Engineer ɗinsu ya gano mata yadda ake buɗe akwatin shikenan komai ya ƙare. Game over. Ita kuma Madam Bintu Chadi sai ta karɓi komai da ta tara da gumin Alhaji Rufa'i ta kuma turata kurkuku.. Sai da Rabi'atul Badawiyya Kabir ta sarawa Oganta kafin ta zauna tana murmushi lokacin da ya ce Barka da zuwa Hansa'u. Sai da ya sa aka kawo mata coffee kafin ya fara bayani. "Badawiyya na san yadda wannan aiki yake da mahimmanci a gareki. Kin sadaukar da komai naki akan wannan case ɗin but unfortunately ƙasarmu bata buƙatar masu jajircewa irinki. Bilkisu Kachallah tanada protection daga sama" "Ban gane ba" Ya ja dogon numfashi yace "an rufe case ɗin, in fact yanzu ba a zargin Bilkisu Kachallah da Bintu Chadi da safarar miyagun ƙwayoyi" "Impossible Sir, akwai audio proof na hirarsu, written document kawai nake jira kuma shima na kusa samu. Sir Bilkisu Kachallah da Madam Bintu suna shigo da ƙwaya ƙasar nan" " na yadda Badawiyya, sai dai abinda zaki fahimta shine ba su kaɗai bane masu wannan harka kuma an gano cewa ana bincike akansu shiyasa aka ce a rufe file ɗin case ɗin" "Sir tayaya za a rufe? This people import things that kill our youths. Matasanmu sun lalace da shaye-shaye alot of criminal activities yana faruwa ne saboda shaye-shaye" "I know. Amma daga sama ne Rabi'ah. Sunce a terminating assignment ɗinki dan haka dole ki bar wannan case ɗin ki dawo office" "Ba zan iya ba Sir, i need this case, ka san case ɗin nan is personal to me" "I'm sorry, amma dole ki haƙura da aikin" Badawiyya ta rintse ido tana jin wani ƙunci a ranta. Tayi tunanin zata samu abinda take so shiyasa ta jona aikin force tun lokacin data dawo ƙasar. Case ɗin Bintu take nema aka bata harda na Bilkisu, ba zata iya zama wajen Bintu ba saboda zata iya kasheta abinda therapist ɗinta ya faɗa kenan shiyasa ta zaɓi zama gidan Bilkisu Kachallah dan tayi bincike. "Ki yi haƙuri Badawiyya" Oganta ya sake maimaitawa. "Ka bani lokaci dan Allah na ƙarisa aikin nan, just small time, dana samu papers ɗin ba zan turawa kowa ba sai DEA na America, they will intervane" "Badawiyya it's risky" "Sati biyu Dan Allah" Oga yai shiru yana nazari sannan yace "sati biyu Badawiyya, idan ya wuce haka i can't cover for you, kuma zaki sa kanki cikin hatsari ne" "Nagode Sir"   ***   Wanda suka sace ɗalibai sun fito sun bayyana cewa suna buƙatar miliyan ɗari kafin su sake ɗaliban, amma basu yi maganar Asiya Kachallah ba. A ɓangaren Gwamna Saifuddeen Kachallah kuwa ikon Allah ne yasa bai haukace ba, abubuwa sun masa yawa, ga yaran da ake nema ga kuma Asiya da kullum yake kwana da ita ya tashi. Ina take? Tana lafiya? Wani hali take ciki? Rashin samun amsoshin nan ya birkita masa tunani. A wani gefen kuma ga ayyukan Jaha sannan kamfen da ya zame masa dole. Umaru Kwom ma yana taka tsantsan da wannan sabon yanayi. Maganar sace Asiya Kachallah ya ɓata masa shiri domin yanzu tausayin Gwamna ake maimakon zaginsa da ake a da saboda gazawarsa. Ba abinda ya ƙara ɗaga masa hankali sai da ya ga Bilkisu Kachallah ta zargi 'yan adawa akan cewa sune da hannu a wannan sace-sacen da ake kuma da sannu komai zai warware. Daga wannan maganar rating ɗinsa ya fara sauka yayinda na Gwamna S S Kachallah ya ke ɗaguwa. Yayinda ake wasa da rayukan yara ƙanana saboda siyasa, su iyayen yara suna cikin tashin hankali marar misaltuwa. Akwai wata uwa wacce aka sacewa ɗa ɗaya da Allah ya bata sai da shock ya sata faɗuwa ɓarin jikinta ya shanye. Su ma iyayen Asiya da basu san a wani hali 'yarsu take ba suna cikin jimami da addu'ar Allah ya bayyanata. A inda aka ɓoye Asiya kuwa ta ƙi cin komai sai kuka, kullum saƙa yadda zata ɗau fansar duk wanda ya mata wannan abu take. Har lokacin ta ƙi cin abinci, ruwa kawai ta ke ɗan sha a famfo idan za ta yi alwala a banɗaki. A kwana na huɗu da ɓatan Asiya aka sake sace wasu 'yan Islamiyya yara ƙanana irin 'yan rabin ajin nan su guda bakwai. A ɓangaren Umaru Kwom ya ɗaura aniyar har a zo zaɓe ba zai bari Jahar Congo ta samu lafiya ba. Idan an ɓoye Asiya Kachallah ne saboda a ɓata masa shiri to zai ga yadda za su yi idan aka cigaba da sace ɗaliban makaranta, lokacin babu wanda zai tuna da wata Asiya Kachallah da aka sace. A ranan da aka sace 'yan Islamiyya Gwamna ya sauke wasu Kwamishinoni da wasu special advisers guda biyar daga kan muƙamansu, ya naɗa wasu tareda faɗin suma zasu tafi idan ba a samo ɗaliban da aka sace da matarsa ba. Asiya bata ga wannan news ɗin ba. Lokacin data kunna TV tun bayan ganin rahoton mutuwar mahaifiyarta da tayi, taron addu'a da first lady Bilkisu Kachallah ta haɗa ake nunawa. Taron mata ne kowa a wajen ya sha anko, wasu sun saka farin leshi da head gear orange, wasu kuma sun saka atampa blue. Bilkisu Kachallah ta hau podium ta fara bayani kan yadda 'yan adawa suke ɓatawa Gwamnatin Saifuddeen Kachallah suna. Ta buge da karanta suratul Quraishi, ta karantata gayau babu tajweed ba komai, cike da kura kurai. Ta haɗa da addu'ar Allah ya bayyana yaran da aka sace da kuma ƙanwarta Asiya. Daga ƙarshe ta buge da kuka. Aka kira wata Malama tayi karatun ƙur'ani kafin aka bawa wata Evangelist dama ta zo tayi addu'a. Wasu Mata Yarabawa suka fito suna addu'a da waƙa suna rawa, da suka gama aka kira wasu mata da suka yi shigar fararen kaya, basu sa takalmi ba, sannan ba ɗankunne a kunnensu. Suka dinga tsalle suna sumbatu duk dai da sunar addu'a. Asiya na zaune tana kallo yayinda ƙwaƙwalwarta ke lissafin abinda yake faruwa. Ita ɗin hajar Kafen ce, ita ɗin decoy ce, ita ɗin bata da matsayi a wajen Gwamna Kachallah sai dai yai amfani da ita ya yar. Bata san ina ta samu ƙarfi ba, lokacin da aka nuno Gwamna Saifuddeen Kachallah yana magana table ɗin dake ɗakin ta ɗauka ta bugawa TVn tana faɗin *I hate you Saifuddeen Kachallah* *ba ruwana na yi nan* 8 *not edited* "Kana da ƙarfi a wannan jaha Yallaɓai. Taya za ka bari Umaru Kwom ya juya garin nan. Jahar nan gaba ɗayanta a ƙarƙashin ikonka take, ko dai tsufa ya sa ka yi sanyi?" Yallaɓai ya fara murmushi yana shafa gemunsa. Ya kai minti ɗaya yana haka kafin yace "Zan kira Commisioner of police, za a nemo yaran cikin awa arba'in da takwas amma ina da sharaɗi?" "Ka san babu abinda zai gagareni" "Saifuddeen zai sa hannu a takardar yarjejeniya" "Idan wannan ne an gama"...   *** Gwamna Saifuddeen Kachallah bai bar Office ba sai ƙarfe shabiyu saura na dare. Yana isa gida ya tarar da Bilkisu ta kalmashe ƙafa akan kujera tana jiransa. Daga yanayin kayan jikinta ya san akwai abinda take buƙata. "I'm tired Bilkisu" "Na sani Baby na. Na san yadda abubuwan da suka faru suke damunka" Ta riƙe hannunsa suka ƙarisa ɗakinsa. Suna shiga ta shiga taya shi cire kayan jikinsa. "Akwai yadda za a yi a ƙwato yaran nan" Gwamna yai saurin ɗago ido ya kalli Bilkisu, tayi saurin kauda kai tareda jawo ƙaton towel ta fara ɗaura masa a ƙugu. "Bilkisu talk to me" yai maganar kamar ya shiga zuciyar Bilkisu ya ga mi take shirin faɗa. Sai da ta ƙarisa ɗaura towel ɗin ta kamo hannunsa suka fito daga banɗaki, ta zaunar da shi a bakin gado. Kamar wani ƙaramin yaro haka yai galala yana binta da ido. "Ba yaran kaɗai za a sako ba har da Asiya " "Go straight to the point please" Bilkisu ta ƙarisa wajen bedside drawer ta ɗauko wani file ta zo ta ajiye a kan cinyar Gwamna Saifuddeen. "Darling sign the agreement" Ba sai ya buɗe file ɗin ba ya san wani agreement take magana akai domin kafin a fara wannan hatsaniyar Alhaji Sani ya kawo masa ita kuma ya rantse ba zai sa hannu ba. "Bilkisu kin san mi aka rubuta a ciki kuwa? Baba ne ya saki ko?" "Darling this people are powerful, ba za su bari ka hau kujeran nan ba sai kayi abinda suke so, idan kuma har ka hau to ba za su bari ka aiwatar da komai ba har sai kayi yadda suka ce" "Two years na farkon tenure ba zan ɗau ma'aikata ba, babu ƙarin albashi, zan yanke wasu benefit da allowance na ƙananun ma'aikata, zan yi titi a iya wajen da aka shata min, 80% na cabinets nawa zaɓa min su za a yi... This is absurd Bilkisu, miye amfanin mulkin idan ba zan iya aiwatar da komai da kaina ba" "Its just two years, daga nan sai ka yi duk yadda kake so" "No Bilkisu, ki cewa Baba yai haƙuri but i still can't" "Idan yaran nan suka mutu, ba lallai ka iya samun nasara a zaɓen nan ba. Idan Asiya ta mutu bana tunanin zaka yafewa kanka Saifuddeen" "Ba zan yi ba, idan na yi wannan zan siyawa kaina tsinuwa ne daga wajen waɗanda suka zaɓeni. Ba wannan bama. Allah zai tambayeni Bilkisu, Allah zai tambayeni" Bilkisu ta kamo hannunsa da suke rawa ta riƙe gam cikin nata. " a duniya babu wanda zai soka sama dani Saifuddeen. Ba wai ina so ka amince saboda kada ka yiwa talakawa aiki bane, ina so ka kuɓutar da yaran nan da ma matarka saboda rayuwarsu tana cikin haɗari. Umaru Kwom is a monster, ba damuwarsa bane idan Asiya ta mutu ko kuma duka ɗaliban nan sun mutu. Shi dai burinsa ya ɓata sunanka saboda ya ɗaukaka nasa sunan. Ka ga dai how desperate he was a kan case ɗin Lami Ninja. Kaine Gwamna amma sune da ƙarfin iko, idan ka amince da sharaɗinsu zasu sa a nemo yaran nan, because they know the right button to press" "Miyasa ba za a nuna min right button ɗin ba?, miyasa ba za a barni na danna button ɗin ba" "Come here Darling, idan baka so shikenan, we'll find another way" ta rungumeshi tana ɗan shafa kansa fiskarta ɗauke da murmushin mugunta. Gwamna yai lamo jikin Bilkisu saboda ba abinda yake buƙata sai hakan. A zuciyarsa addu'a kawai yake yi domin ita kaɗai ke kawowa zuciyarsa sanyi. Ashe lokacin da yake mataimakin Gwamna bai san komai ba gameda siyar Jahar nan. Tun ranan farko da Alhaji Sani ya kaishi gaban Yallaɓai a matsayin Ubangidansa, mutumin kwata-kwata bai masa ba, yana da nuna gadara kaman yafi ƙarfin kowa. *** "Ina zaku kai ni?, ina zaku kaini?" Asiya ta faɗa tana ƙoƙarin tirjewa. Daga bayanta aka kwaɗa mata bakin bindiga a ka, hakan ya sa ta faɗi ƙasa a sume. Gwamna na zaune a office COS ya shigo. "Ranka shi daɗe kana da saƙo" Gwamna ya buɗe envelop ɗin da aka miƙa masa. Kafin ya fito da abinda ke ciki COS yace "Your Excellency demands na kidnappers ɗin kenan" Hoton da Gwamna ya gani ya sa shi miƙewa tsaye ba shiri. "Mi suke so? Mi suke buƙata?" Babu komai a cikin envelope ɗin sai hoton nan hakan ya sa ya juya bayan hoton inda aka rubuta MILIYAN ƊARI BIYAR NAN DA KWANA BIYU. Ba shiri Gwamna ya zauna akan kujera. Ba wai kuɗin ne ya ɗaga masa hankali ba. Kwana biyu da suka rubuta na nufin za su iya yiwa Asiya komai idan ba a kawo kuɗin ba nan da kwanaki biyu. Ya rintse idonsa amma hoton Asiya yake gani zaune akan kujera an ɗaure mata hannu, ƙafa da baki. Yanayinta na nuni da tana cikin wahala. "Mi za mu yi ranka shi daɗe?" Gwamna bai yi magana ba sai kawai ya ɗaga masa hannu. Bayan COS ya fita. Gwamna Saifuddeen ya shiga tunani. Umaru Kwom, Yallaɓai, Alhaji Sani duk wasa suke da hankalinsa. Amma ba abinda zai iya a halin yanzu sai dai yai abinda zai ceci rayuwar ɗaliban da aka sace da kuma matarsa. Asiya bata cancanci hakan ba. Bai sani ba ko tama san mahaifiyarta ta rasu. Ko ya zata ji idan ta dawo ta tarar da rasuwan?. Yana fita daga office kai tsaye gida ya wuce. File ɗin nan yana nan a saman drawer har yanzu. Ya ɗauki file ɗin ya fice daga ɗakin cikin sauri... "Your Excellency, kaine da kanka a gidana" Yallaɓai ya faɗa yana saukowa daga matattakala. "Bismillah, ka zauna" ya faɗa yana murmushi. Gwamna ya ajiye takarda akan center table yace " 50% na cabinets nawa ne, na yarda ba za a ɗau sabbin ma'aikata ba, amma ba za a rage albashin ƙananun ma'aikata ba" Gwamna da Yallaɓai suka tsaya kallon kallo, kowa da abinda ke ransa. Gwamna ji yake kamar ya shaƙe tsohon nan kowa ya huta. Shi kuma Yallaɓai yana hasaso wani abu gameda Gwamna Saifuddeen ɗin. "Shikenan, na yarda da gyaran da kayi" "Idan wani abu ya samu matata ko kuma ɗaliban da aka sace yarjejeniyarmu ta tashi" "Ba abinda zai same su" Gwamna ya duƙa ya saka hannu a takardar. Yana ɗagowa Yallaɓai yace "seal" Gwamna bai yi magana ba, ya ciro seal ya manna akan takardar. Lokacin da Gwamna ya tafi, Yallaɓai ya shafa gemunsa yace "Aff! tanada tasiri a rayuwarka" *** A kwana na uku da Gwamna Saifuddeen Kachallah ya sanya hannu a yarjejeniyar Yallaɓai, 'yan Sanda suka gano maɓuyar kidnappers suka far musu. An kashe kidnappers biyu yayinda sauran suka tsere. An kuɓutar da ɗaliban nan duka, inda aka wuce da su Asibiti saboda a tabbatar da lafiyarsu. Gwamna na samun wannan labari ya fara murmushi yana hamdala. Ya damu da ɗaliban kamar yadda ya damu da matarsa amma jin cewa ba a samu Asiya ba sai hankalinsa ya tashi. Ya dai yi ƙoƙarin danne zuciyarsa. Sawa yai a shirya masa tafiya Asibitin da aka kai yaran yaje ya dubasu... A ɓangaren Umaru Kwom Kuma tamkar ya haɗiyi ransa saboda baƙin ciki. Bai san miyasa Commisioner of Police ya shammace shiba bayan irin maƙudan kuɗin daya bashi. Lokacin daya kira shi ya tambayi bahasi cewa yai Yallaɓai ne ya basu umurnin su nemo yaran kota halin ƙaƙa. "Yallaɓai" ya furta sunan da ƙarfi. Tabbas Yallaɓai ya fi shi ƙarfi, ya yi zama ƙarƙashinsa kuma ya san tasirinsa a jahar da ma ƙasa baki ɗaya. Ba a jimaba ya ɗau waya ya kira Yallaɓai. Ya jima da rabuwa daga jikin Yallaɓai amma har yanzu akwai shakkar Yallaɓai a ransa. Yana riƙe da wayar amma zuciyarsa na bugawa da ƙarfi ƙarfi. "Umaru Inuwa Kwom" "Yallaɓai" Umaru Kwom ya kira da tausasashshiyar murya kaman ba shi ke ta zagin Yallaɓai ɗazu ba. "Yau ka tuna dani kenan" "Yallaɓai ban san miyasa ka bawa Saifuddeen dama ba tun a wancan tafiyar. Saifuddeen ba zai taɓa baku abinda kuke so ba, he's incompetent. Ba shi da ƙarfin zuciyar yin siyasa" "Kayi Kamfen ɗinka ta hanyar da ta dace Umaru. Maganar sace yara ba inda zai kaika" "Yallaɓai..." Kafin yai wata maganar aka katse kiran. Idan har wannan ba zai yiwuba. Zai yi amfani da kuɗi ya sayi ƙuri'u.   *** *"Idan kika buɗe baki kika faɗi abinda ya faru tamkar kin kashe Iyalen Malam Nuhu Principal ne..."* Asiya ta buɗe ƙofar gidan su ta shiga, kashedin da aka mata na yawo a kanta. Tunda akayi sadakan uku gida ya watse. Musa ta gani yana cin abinci a ƙofar ɗakin Inna Yaha. Yana ganinta ya miƙe zumɓur yana kiran mahaifiyarsa. "Inna ga Anty Asiya, Inna..." Inna Yaha tana sallar magariba ta katse sallar ta fito da gudu. Tun rasuwan Umma jikinta yake a sanyaye. Abinda bai taɓa faruwa ba sai ga Inna Yaha ta rungume Asiya. "Inna Yaha ya naga ɗakin Umma a rufe da kwaɗo?" Maimakon Inna Yaha ta bata amsa sai kawai ta fashe da kuka. "Ina Umma? Ta je anguwane?" " Ummanki bata nan Asiya. Ki shigo ciki" ta kamo hannunta zata kaita ɗaki. Asiya ta tirje tace "ki gayamin inda taje"... Asiya ta zauna a ƙofar ɗakin Umma tana jiran dawowar Abba. Ita dai ƙarya Inna Yaha ta mata da ta ce Umma ta rasu. Sharrin Inna Yaha ne kawai zata ce Umma ta rasu. Umma na nan. Gajiya, Yunwa, ciwon jiki duk ba sune damuwar Asiya ba. Ita dai tana so ace mata Ummanta na nan da ranta, abinda ta gani a TV ba gaskiya bane film ne. Inna Yaha tace Musa ya je ya kirawo Abba a masallaci. A hanya suka haɗu dan ko minti ɗaya bai cika da fitansa ba ya shigo biye da Abba. "Asiya, Asiya kina lafiya? Kema 'yan sanda ne suka kuɓutar da ke?" Abba ya tambaya yana riƙe hannun Asiya. Tun da la'asar da suka ji labarin an samu ɗaliban nan suke sa ran su ji an samu Asiya amma shiru. Yama kira Gwamna dan ya tambayi labarin Asiya amma Gwamna bai ɗauka ba. Bayan sun ɗan nitsu Abba ya fara yiwa Asiya nasiha akan mutuwa daga ƙarshe ya sanar da ita rasuwan Ummanta. Mutumin da take tunanin zai ƙaryata labarin da ta ji sai gashi ya sake tabbatar mata da mugun labari. "Abba da gaske sun kashe min Umma?" "Kul Asiya. Kul kika sake magana irin wannan, sai kace jahila" "Abba..." "Addu'a zaki mata ba ƙorafi ba Asiya. Addu'arki take buƙata yanzu". Asiya ta sunkuyar da kai sai hawaye. "Asiya na kai miki ruwan wanka. Kije kiyi wanka, sai ki zo ki ci abinci" Inna Yaha ta faɗa lokacin data shigo falon. Ba Asiya ba, shi kansa Abba ya yi mamakin kalaman Inna Yaha... Gwamna na hanyar zuwa gidan Yallaɓai bayan ya bar Asibiti Abba ya kira shi. "Da kanta ta dawo? Ba abinda ya sameta ko?" Gwamna ya faɗa cike da farin ciki yama manta da sirikinsa yake magana. Yana gama wayar yasa aka juya da shi. Da farko gidan zai wuce direct sai ya ga idan yaje haka zai ja hankalin jama'a shiyasa ya fara zuwa chan tsohon gidansa. Ya ce Dreban Gwamnati da excort su wuce chan Government house yayinda shi kuma ya shige motarsa drebansa ya fice da shi. Asiya ta jima a banɗaki tana kuka kafin tayi wanka ta fito. Lokacin da ta fito an buɗe ɗakin Umma, ta tsaya bakin ƙofa tana jiran ta ga ko za ta hango Umma kwance akan sallaya ko akan gado amma bata gani ba. Gwani da Habibu ne a ɗakin suna magana. "Anty, Yaya Ubaydu yace a gaisheki" Ba ta yi magana ba sai ta gyaɗa masa kai... Abba na cewa Ubayd Gwamna na hanya ya miƙe yai wa Abba sallama. Dama yana jira Asiya ta fito su gaisa ne, amma tunda mai guri ya zo sai mai tabarma ya naɗe.   *ku yi haƙuri banida lafiya ne. Amma Insha Allah gobe zan typing* 9 *Assalamu Alaikum. Da fatan kowa yana lafiya, na san an samu jinkirin update da kuma shiru daga gareni. To amma muna namu ne Allah kuma ya tsara nasa. Simple ciwon kai dana raina sai ya zamo min zazzaɓi mai tsanani, amma Alhamdulillah naji sauƙi. Nagode da addu'o'inku. Allah ya ƙara mana lafiya baki ɗaya Amin* *wanda suka min magana ban reply ba ina bawa kowa haƙuri. Wanda suka kira suka gaisheni da wanda suka gaisheni ta chat da kuma text duk ina godiya Allah ya saka da alkhairi. Wanda suka turomin da saƙo marar daɗinji suma nagode*   "Ina Sumayya?" Asiya ta tambayi Ali daya shigo gaisheta. "Yau ta koma hostel" "Har yanzu kana yawon dare ko?" "A'a na dena... yeeh Gwamna yazo" ya miƙe ya fice da gudu jin ƙaran tsayuwar mota a gidansu. Lallai yaro yaro ne. Ko sati bai cika ba da rasuwar Mahaifiyarsa, amma damuwarsa Gwamna ya zo gidansu. Asiya ta sauke ajiyar zuciya ta zubawa abincin da aka kawo mata ido. Tuwon masara ne da miyar kuka, da alama cikin wanda aka rage na ɗumamen gobe aka ɗebo mata dan babu nama a ciki sai ƙullin balangu a leda da ke gefe. Sai kuma lipton da madara guda biyu na leda da aka ajiye a gefe. Ta ɗeba sugar ta saka a lipton ɗin ta raugaya ta fara kurɓa kaɗan kaɗan. Duk da yunwar dake cinta hakan bai hanata jin haushin Gwamna ba. Da zata ga fiskarsa ruwan shayin nan zata watsa masa saboda yadda ta tsani fiskarsa... Abba yai ta zarewa su Habibu ido amma yaran suka dake suka ƙi tashi, suka maƙalewa Gwamna suna cewa sai yayi hoto da su. Gwani ne mai hankalin cikinsu dan haka Abba yace "Lukman ka je ka kira min yayarka" "Abba abinci take ci" Ali yai saurin faɗa saboda matuƙar Gwani ya tashi suma ɗin aikansu za ayi. Abba ya haɗe rai yace " Aliyu kayi tilawar yau ne?" Ali yai saurin miƙewa dan yanzu idan yai ƙarya Abba zai sa shi karatun dole. Ganin Ali da Gwani sun fita ya kalli Habibu yace " kaje ka duba min lafiyar mashin" Habibu ya miƙe yana ƙunƙuni. Bayan yaran sun watse Abba da Gwamna suka sake gaisawa sannan suka yiwa juna jajen abinda ya faru. Gwamna ya nisa yace " Sumayya bata nan ne? " "Yau ta wuce hostel" Ganin shirun yayi yawa Asiya bata shigo ba Abba ya miƙe yace yana zuwa. Asiya ta ƙarisa shan shayi amma bata taɓa tuwon ba, bata da appetite na cin komai. Abba yai sallama ya shigo ɗakin. "Ki je ku gaisa, idan kika dawo sai ki faɗi abinda zaki ci" babu wasa a yanayinsa hakan yasa Asiya ta miƙe ta shiga neman hijabi. Lokacin data fito daga wanka jallabiya sabuwa Inna Yaha ta kawo mata, tana tunanin ma ba zai wuce cikin kayan Faty bane data bar wa Hindatu. Bata san miyasa aka tattara kayan Umma ba, bata san miyasa aka ma rufe wardrobe dake ɗakin ba. Sai kuma ta tuna cewa yanzu fa kayan Umma sun zama na gado. "Asiya ba zaki wuce bane" "Abba hijab nake nema" "Ke da mijinki sai kin wani tsaya neman hijabi" Da a lafiyarta take, da cikin nitsuwa take, cewa za tai "Lah! Abba da kanka" sannan tayi dariya. Yanzu kam ba abinda tace, sai ta ɗau gyalen kayan wanda har lokacin yana cikin ledar jallabiyar, ta yafa akanta ta fita. Lokacin data shigo waya yake yi. "Eh nina ce su wuce gida, ina tareda Asya, an sakota...Amin" Ya ajiye wayar gefe ya kalli Asiya da ke tsaye ta riƙe ƙugu. Abinka da farar mace har wahala tasa ta fara dishewa. Duk da haka tayi masa kyau, baƙar jallabiya mai duwatsu blue ya amshi jikinta duk da ramar da ta yi. "Asya" ya furta cike da shauƙi. "Ka zo ka gani ko sun karya min ƙafa ne? Ko kuma sun datse harshena?" "Ki zauna mu yi magana Dan Allah" hajijiya ta fara ji hakan yasa ta bi umurninsa ta zauna suna fuskantar juna. "Ina miki ta'azziyar rasuwar Umma, Allah ya gafarta mata" "Kanada bakin ta'aziyya dama. Ai na ɗauka abinda kake so kenan" Ya ɗan zaro ido cikin rashin fahimta "Asya bana so ki ɓoye min komai. Ki faɗamin yadda komai ya faru, ina suka kaiki? Mi suka ce miki?. Ina ganin kamar..." "Kamar me? Har kana da bakin magana. You are a fraud Gwamna Saifuddeen, kai munafukine kuma Azzalumi. Har na fara tunanin tayaka Kamfen ashe kai ka riga ka shirya naka Kamfen ɗin. You said it yourself ni hajar Kamfen ce, i mean nothing to you. Taya zaka sa a sace ni a ranan da mahaifiyata take kwance a gadon Asibiti. Taya zaka sa a hanani yiwa mahaifiyata addu'a?" Gwamna ya miƙe tsaye ya tako zuwa gabanta hakan yasa ta yi shiru sai nishi da take sama sama. Ya sa hannu biyu ya miƙar da ita tsaye. Sai da idonsu ya haɗu kafin tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa. "Asya kina tunanin zan sa a sace ki saboda Kamfen? Abinda suka faɗa miki kenan?" Tayi shiru ta kasa magana saboda kusancinsu da yai yawa, turarensa da take shaƙa ma kaman jawota jikinsa yake. "Wani irin ƙiyayya kike min Asya?, miyasa akoda yaushe ba kya min zaton alkhairi sai na sharri?. Aurenmu zai iya kasancewa ƙaddara amma ko a hakan, matar mutum matar mutum ne, no matter what. Idan zaki min adalci Asya, a iya zaman da muka yi ya kamata ki gane cewa bana wasa da iyalina, and you are my family" "Kai kace su ɗauko ni. Kai ka tura min text kace na bisu. Akwai wanda ke da numba irin naka ne?. Ni ba yarinya bace, Excellency na san yadda 'yan siyasa suke zama a lokacin yaƙin neman zaɓe. Ka yi amfani da ni ne saboda ka samu mutane" Ya san tana cikin raɗaɗin rashin uwa, ya san abinda ya faru dole ne ya taɓa tunaninta, amma idan da zata iya duban ƙwayan idanunsa da zata ga tsananin so a cikinsu. Da ta san abinda yai saboda ita, da bazata ƙara tunanin zai iya cutar da ita ba. "Ina son ki Asya" Asiya-Shahidah ta yi saurin ɗago ido ta kalleshi. Shima ita yake kallo hakan ya bashi daman ƙarisa maganar "Ba zan taɓa cutar da ke ba, ba zan taɓa amfani da ke wajen neman duniya ba. Ina fatan watarana za ki fahimci hakan" Bai jira mi zata ce ba, bai yi ƙoƙarin goge hawayen da ya gangaro mata ba. Bai yi ƙoƙarin ƙara wasu kalaman ba saboda babu amfanin yin hakan. Har Gwamna ya fice daga falon Asiya tana tsaye tana rawar jiki yayinda hawaye ya cigaba da zubo mata. Ƙarshe tsayuwar ya gagareta, ta tsugunna a ƙasa jikinta ya cigaba da rawa. Kalaman Gwamna sun ratsa kowanni lungu da saƙo na jikinta. *"ina son ki Asya"* ya fara maimaituwa a kunnenta, hakan yasa ta toshe kunnen da hannu biyu jikinta ya cigaba da rawa... *** Lokacin da Gwamna ya isa gida kai tsaye ɗakinsa ya wuce ya zauna yana tunanin kalaman Asiya. Wani irin tsana ta masa ne? A iya saninsa da ita, shi bai taɓa yi mata komai ba. Daya fito daga banɗaki ya ga Bilkisu zaune a bakin gado tana jiransa. "Na ɗauka gida zaka kawota ai?" "Tana buƙatar kasancewa da 'yanuwanta" "Hakane, fatan tana lafiya?" "Ba kya ganin Baba ne ya sa aka ɗauke Asiya?" "Baba kuma!" Bilkisu ta faɗa tana kama baki. "Anya Baba zai iya haka?, ni gaskiya ban yarda ba" ta faɗa ganin Gwamna bai yi magana ba. "Junior yayi bacci ne?" Ya kauda maganar...   *** Lokacin da Asiya ta farka a gadon Asibiti ta ganta, kusa da ita Sumayya ce da kuma Bilkisu Kachallah. Jiya da dare da Abba ya shiga falo ya sameta bata cikin hayyacinta. Har aka kawota Asibiti bata san inda kanta yake ba. Da sassafe Gwamna ya zo ya dubata lokacin tana bacci. "Anty Asiya ya jikin?" Sumayya ta tambaya murya ƙasa-ƙasa saboda tsoron Bilkisu Kachallah da take. Asiya tace "Sumy zan sha ruwa" Sumy ta miƙe ta wuce wajen ƙaramin fridge dake ɗakin. Sai da Bilkisu Kachallah ta gama waya kafin tace "sannu fa, ya jikin?" Asiya ta kauda kai gefe. "Ɗarling ya zo kina bacci, yace a isar masa da gaisuwa" Asiya ta miƙe zaune tace "tunda ke da minjinki kun samu abunda kuke so, sai ku barni ai, ku bar ni na ji da damuwata" Bilkisu tayi murmushi tace " mijinmu dai ko ? Don't pretend cewa ba kya jin daɗin kasancewarki matar Gwamna." "Allah ya sawwaƙa" Bilkisu ta miƙe tace " zan wuce, Allah ya kawo sauƙi" Daga Asibiti, Bilkisu gidansu ta wuce saboda Hajiyarsu data kira meeting. Sai da ta isa gidan ta samu meeting ɗin su uku aka kira. Ita, Saudah da kuma autarsu Halima. Hajiya tayi musu bayani akan bata ji daɗin yadda aka watse family meeting da suka yi kwanan baya ba, an rabu ranan ba da daɗi ba. Dama tsakanin Bilkisu da Halima babu jituwa to amma bata san miya haɗa Bilkisun da Saudah ba, kasancewa a baya sun fi kusa da junansu. "Hajiya yanzu har na gayyaci Halima da Saudah wajen Kamfen ɗina su ƙi zuwa" Bilkisu ta faɗa tana kallon Hajiya. "Ni na je Kamfen ɗinki Bilkisu. Allah ya tsare" Saudah ta faɗa tana tafa hannu Hajiyarsu tace " Saudah wani irin magana ne wannan?" "Hajiya taya zan amsa gayyatarta bayan abinda ta yiwa 'yata" "Oh! Saboda shegiyar 'yarki kike fushi. Chan ta matse miki dan ko yau na ganta a gidana sai na cire mata ƙafa" "Hajiya kinji mi take kiran Zunnairah ko?" "To ba 'yar shegiyar bace. You are 6 weeks pregnant lokacin da aka ɗaura miki aure kuma..." "Bilkisu" Hajiya ta daka mata tsawa. "Oh Lalala! Aikin ya fara warwarewa kenan" Halima ta faɗa tana miƙe ƙafa akan kujera tareda fashewa da dariya. Saudah ta miƙe a fusace tana faɗin "Bilkisu kar ki manta akwai sirrinki a tafin hannuna. Zan ga da wani ido zaki kalli Yaya Saifuddeen idan ya san kin je an cire miki mahaifa" "Subhanallahi!. Wai lafiyarku kuwa?. Ke Bilkisu da gaske ne abinda Saudah ta faɗa?" Bilkisu ta miƙe tsaye ta ɗau jakarta tace " cire mahaifa ba abin kunya bane Hajiya, saboda lafiyata na cire. Amma ki jawa Saudah kunne idan bata kama kanta ba, ni da kaina zan faɗawa duniya cewa Zunnairah 'yar wani Bamaguje ne a jahar Benue" "Yau ana drama a gidan nan" Halima ta faɗa tana kwashewa da dariya. "Halima!" Bilkisu ta faɗa da ƙarfi "Allah ya huci ranki excellency" Halima ta faɗa tana haɗa hannu biyu. Bilkisu ta fice daga falon ranta a ɓace. Bayan fitan Bilkisu Hajiya ta kalli Saudah tana neman ƙarin bayani gameda abinda Bilkisun ta faɗa, amma Saudah tayi shiru itama nadama ya damaimayeta. Hajiya ta san da batun cikin shegen da Saudah tayi, kuma ƙaryar da tayi cewa cikin na Usman ne shiyasa ta bari aka yi auren cikin gaggawa. Ƙuruciya a lokacin da kake ji da kuɗi, jin daɗi da kuma 'yanci irin na turawa yana iya sakawa ka shagala da biyewa son zuciya. A wajen party ta haɗu da mutumin da har yau ba za ta iya tuna sunanshi ba. Sau ɗaya da suka kasance tare cikin maye ya zamo ciki. An riga an saka bikinta da Usman kuma shima sun taɓa sanin juna shiyasa ta jona masa cikin. Yanzu shekaru sun ja, amma har yau bata dena nadamar ƙuruciyar da ta yi ba. *** Da safe bayan fitar Bilkisu Kachallah, Hansa'u ta shiga ɗakinta ta ɗauko akwatin sirrin Bilkisu, ta saka password da aka aiko mata da shi nan da nan akwatin ya buɗe. Zaro ido tayi ganin dami damin kuɗi na dollars. Sai data ɗebe kuɗin ta zuba a kan gado sannan ta ci karo da wasu takardu, takardun duk wani business da take ne. Takardan ƙarshe wanda yake cikin wata jar file shine wanda take nema. Kwanan wata da saka hannu da duk wani bayanai gameda harkan safarar ƙwayoyi da suke yi tsakanin ƙasar Mexico, America da kuma Columbia yana ciki. Ta zaro wayarta ta fara ɗaukan takardun a hoto, da ta gama ta maida takardun cikin akwatin tareda jera kuɗi a samansu kamar yadda ta samesu. Ta maida akwatin inda ta ɗauko shi, kafin ta fice daga ɗakin. Ta riga ta samu abinda take so dan haka a yau zata bar gidan. Kayan aikinta kawai ta ɗauka ta saka a jaka ta rufe da wasu tsummokara ta fito, ta yiwa masu aiki sallama akan za ta je ta dubo mahaifiyarta a ƙauye. Ita ɗin ta hannun damar Bilkisu ce dan haka ba su zargi komai ba. Tana fita daga gidan Gwamnati kai tsaye gidanta ta wuce. Tayi wanka ta chanja kaya sannan ta fito, har zata fita sai kuma ta tuna cewa ya kamata ta gayawa Asiya wacece Bilkisu Kachallah. Ta ga rahoton da aka yi da safe, inda aka nuna Bilkisu Kachallah tana matse ƙwalla a gefen gadon da aka kwantar da Asiya, tana faɗin ba za su yafewa wanda yai wa Asiya wannan ba. Idan ka san waye maƙiyin ka zaka iya yaƙarsa, amma maƙiyin ɓoye da wuya ake cin galaba a kansa. Saboda ba a san fiskarsa ba, ba a san ya yake ba sannan ba a san ta ina zai ɓullo ba. Ta nemi takarda ta yi gajeren rubutu sannan ta naɗe ta saka a envelop. Dogon hijabi ta saka a kan kayanta ta fice daga gidan, ta nemi Keke ya kaita gidan Gwamna. Tana shiga gidan ta tambayi masu gadi ina Yaya Bello aka ce mata ya tafi Asibiti. Ba lallai ta sake dawowa gidan ba sannan kuma tana tsoron bawa wani takardar. Sai kawai ta shige cikin gidan. Suka gaisa da Uwani tace mata an aikota ne ta ɗauki abu a sashen Asiya. Tana shiga ɗakin Asiya ta fara neman inda zata ajiye mata wasiƙar da wani ba zai gani ba, sannan Asiya zata gani da wuri. Ƙarshe ta saka wasiƙar a tsakiyar ƙur'ani data gani a kan wardrobe na gefen gado tana addu'ar Allah ya sa Asiyar da ta ajiyewa ce kawai za ta gani. Daga gidan Gwamna kai tsaye office ɗinsu ta wuce. Ofishin Oga ta shiga fiskarta ɗauke da murmushi, ko da hukumomin Nigeria ba su kama Bilkisu Kachallah ba akwai hukumomi na ƙasar waje da za su shigo cikin lamarin, kuma za su iya sawa a hukunta Bilkisu Kachallah da Madam Bintu Chadi. Oga na ganinta hankalinsa ya tashi suna gaisawa zata fara magana yace "Badawiyya ba ki duba wayarki bane?" Wayarta yana silent a koda yaushe saboda aikinta shiyasa ba ta ji ƙaran shigowar saƙonsa ba. Ta ɗauko wayar a jaka ta karanta saƙon da ya turo mata kusan minti goma da suka wuce. *Badawiy ki bar gidan Gwamna, an aika wasu suje su kama ki. Ki ɓuya a inda kika san ba za a sameki ba* Badawiyya ta ɗago kai cikin rashin fahimta. Oga ya miƙa mata wayarsa yana ɗaura yatsa ɗaya akan bakinsa alamar tayi shiru. Ta karɓi wayar ta karanta abinda ya rubuta. * ki tafi daga nan, ance a arresting ɗinki. Idan kika yi gardama an bada umurnin a halbe ki* Badawiyya ta ɗago ido da sauri cikin kaɗuwa. Mi tayi? Tana yiwa Gwamnatin Nigeria aiki sama da shekaru takwas kenan. Oga ya mata nuni data ƙarisa karantawa. *ance ke ɗin 'yar ta'adda ce da kika shiga aikin nan dan ki samu bayanan sirri. Ance kina shirin tada Bomb a gidan Gwamna. Na gaya miki dama Bilkisu Kachallah tanada protection daga sama* Badawiyya ta fara maimaita Innalillahi... a ranta. Ta miƙe da sauri ta fice daga office ɗin Oga. Tana kaiwa bakin ƙofar da zai fitar da ita daga building ɗin aka ɗaura bindiga a ƙeyarta aka ce " Agent Rabi'atul Badawiyya Kabir, you are under arrest"... 10 Bilkisu Kachallah na isa gida kai tsaye ɗakinta ta nufa ta je ta ɗauko akwatin sirrinta. An gaya mata duk abinda ya faru kuma da izininta aka rufe Agent Badawiyya a kurkuku. Bilkisu ta fito da damin kuɗaɗenta ta gansu yadda ta barsu sai kuma ta duba takardunta duka sun cika. An riga an karɓe wayar Agent Badawiyya dan haka bata da wata matsala. Tabbas ta ji zafin yadda aka yi tayi sake irin haka, bata jan mutane jikinta amma kuma Hansa'u ta daban ce. She carried her disguise so perfectly, ta yadda tsawon wannan lokaci bata taɓa zarginta ba. Ta jinjinawa Agent Badawiyya saboda a rayuwarta tana son mata masu jajircewa akan aikin da suka sa a gaba. A tsarinta, mace is very powerful...   *** Bayan Azahar ɗakin Asiya ya cika da 'yan dubiya. Motoci uku suka biyo bayan ta Ale Faruƙ cike da 'yan gidansu Asiya. Fulani da Tabawa ne suka zo a manyan mata, a maza kuma Ale da Baffa Malam. Sauran kuma yayyu da ƙannenta ne da kuma jikokin gidansu. Ran Asiya a ɓace yake tun tafiyar Bilkisu Kachallah saboda Sumayya ta faɗa mata cewa wasu 'yan jarida sun zo sun yi hira da Bilkisu lokacin da take bacci. Bata da lafiya ma ba za a ƙyaleta ba. Ta sake tabbatarwa kanta cewa ita ɗin bata da wani matsayi a rayuwar Gwamna da Bilkisu Kachallah. Sai dai zuwan 'yan gidansu ya washe duk wani baƙinciki da kaɗaici da take ciki. Ta yi kewansu sosai. Kaka Tabawa da ta fara ɓaran-ɓarama a ɗakin haka Asiya ta ɓigire da dariya har da ƙwallah. Yau ne rana na farko da tayi dariya tun rasuwan Umma. Tabawa ta dage wai sai ta ga Gwamna kafin ta tafi hakan ya sa Asiya ta tsuke fiska. Tabawa ta shiga tsokalarta wai kota ɓata rai ba za ta janye batunta ba, ai Gwamna mijinsu ne duka. Ba su bar Asibitin ba sai yamma liƙis, sun so kwana amma Baffa Malam ya hana. Da dare Bayan Isha Ubayd ya zo dubiya. Ganinsa da Asiya tayi ya tuno mata da wasiyyar Umma. Shikenan ta rasa Ubayd har abada kenan? Shima Ubayd ɗin a daddare ya gaisheta ya fita, tsoron kasancewa da ita yake saboda abubuwan da zuciyarsa ke ayyana masa. Asiya Shahidah ce first love ɗinsa, kuma har yanzu daya amince zai auri Salma bai ji ko kaɗan wani abu ya ragu na soyayyar da yake mata ba, sai dai kawai zai cigaba da danne zuciyarsa har lokacin da Allah zai yaye masa soyayyarta gaba ɗaya, duk da kuwa hakan ba lallai ya faru nan kusa ba. CY ne ya zo na ƙarshe kafin Asiya ta yi bacci. Ya zo da yamma ya samu ƙofar ɗakin cike da mutane sai ya juya bai ƙariso ba. Yana sane cewa zuwansa dubiyan zai iya zama wani abu amma bai damu ba saboda zuciyarsa ba za ta taɓa samun sukuni ba har sai ya ganta. Tunda aka nunota kwance akan gadon Asibiti ya ji tsananin tausayinta ya kamashi. Ita ɗin wata ɓangare na zuciyarsa ne da ba zai iya yakicewa ba. "CY the CY, mi ka kawo min ne?" CY ya miƙa mata ɗan ƙaramin box ɗin daya shigo da shi. Asiya ta karɓi box ɗin hannunta ya shafi hannun CY. Duk da hannun na roba ne hakan bai hana CY jin wani abu ya ratsa jikinsa ba. Asiya ta buɗe box ɗin cike da farinciki. "Chocolate?. Shine ka kawo guda ɗaya, marowaci kawai" ta cire chocolate ɗin ta ɓare ta fara ci "Allah ya shiryeka CY, harda wani yi mata karama ka saka a box kamar abin kirki" CY yai murmushi itama Asiyar murmushi tayi sannan ta cigaba da cin chocolate ɗin. Sallamar Abba ya saka CY da Asiya ɗagowa suka dubi Abba da yake bin Asiya da wani irin kallo. CY ya gaishe shi sannan yai wa Asiya sallama ya tafi. Su biyu ne a ɗakin saboda shigowar CY ɗakin yayi dai-dai da ficewar Sumayya data je kiran nurse da zata zo ta cirewa Asiya ruwan da aka ɗaura mata saboda ya kusa ƙarewa. Abba yace "Asiya!" sai yai shiru saboda Sumayya data shigo tareda wata nurse. Bayan an cire ruwan Abba yai musu sallama ya tafi. Asiya ta san akwai magana a bakin Abba kuma koma minene abu ne da ba zai mata daɗi ba saboda yanayin fiskarsa tunda ya shigo babu walwala a tattare da shi. Ƙarfe shaɗaya da rabi na dare Sumayya na kwance a kan ƙaramin katifa a ƙasa tasa earpiece a kunne tana kallo aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin. Ba ta ji da farko ba sai a na uku ta miƙe ta kunna wutan ɗakin sannan ta je ta buɗe ƙofa, ganin Gwamna tsaye a bakin ƙofa tayi saurin matsawa gefe tana faɗin "sannu da zuwa" "Ya mai jiki?" ya tambaya lokacin daya shigo ɗakin. Ta amsa da sauƙi ance ma gobe za a sallamesu. "Ta yi bacci ne?" "Tun ɗazu" Sumayya ta faɗa tana komawa gefe. Gwamna ya matsa kusa da gadon Asiya ya zuba mata manyan idanunsa. Bacci take hankalinta kwance dan har hulan kanta ya zame gefe. Murmushi Gwamna yai ganin wani baƙi-baƙin abu a gefen bakin Asiya. Hannu ya kai zai goge mata, Asiya ta ɗan juya gefe ta kwantar da fiskarta akan hannunta. Maimakon ya sa hannu a wajen sai ya sa hannu a kanta ya fara shafa lallausan gashinta, ya warware bun ɗin da tayi saboda ya ga tsayin gashin. Ya kai hancinsa yana shinshinar gashin wanda ke ƙanshin coconut da jasmine oil. Ya kai bakinsa ya sumbaci gashinta, goshinta da kuma saman hancinta. Ya kai harshensa ya lashe baƙin abinda ya gani wanda yake tunanin ragowar abinda ta ci ne. Ɗan zaƙin daya ratsa harshensa ya tabbatar masa da chocolate ne. Ya kissing lips ɗinta a hankali sannan ya miƙe sai ya ji tace "i love you Asya, mtsww... munafuki, what did he think of himself mtsww ... Sumy kina jina ko?..." ta yi maganar tana nuna yatsa, sai kuma ta juya ɗaya gefen ta cigaba da bacci. Gwamna yai murmushi, Junior da Nana ne masu magana cikin bacci. Bai san manya ma suna iya magana cikin bacci ba sai yanzu. Ya ji daɗi daya fahimci abinda ke ranta shine sirrin daya bayyana mata jiya. Yai wa Sumayya sai da safe sannan ya fita. Bayan tafiyarsa Sumayya ta fito da dariyar da take ta gimtsewa tuntuni... Washegari da safe Sumayya ta shiga tsokanar Asiya akan jiya Gwamna yazo ta faɗa masa tana son shi cikin bacci. "Sumy bana son maganar banza" "Inada shaidah fa Anty" "Maƙaryaciya" Sumayya ta fito da wayarta ta nuna mata hoton da ta yi musu jiya dai dai lokacin da Gwamna ya kissing goshinta da kuma lips ɗinta. Asiya ta zaro ido tana faɗin "na shiga uku. Sumy hoton nan gaskiya ne kuwa?" Sumayya ta haɗe rai tace " ke da bakinki kika ce masa i love you, please kiss me. Shi kuwa yai kissing ɗinki" "Zan ci ƙaniyarki Sumayya" "Ni ƙarshe dana ga kin kanainayeshi ma bar muku ɗakin na yi" "Asiya ta yi saurin ɗaura yatsarta a baki tana tantamar maganar Sumayya. Ta sani tana da magagin bacci musamman lokacin da take yarinya, dan har cewa ake tana taɗi har ma tayi faɗa cikin baccinta. Amma anya za ta iya faɗin abinda Sumayya tace ta faɗa? Wani dalilin ne zai sa ma ta faɗi haka? "Kai Nooo!" Ta furta a fili tana goge bakinta da bayan hannunta da babu canula. Sumayya ta fashe da dariya. Duk yadda ta nace akan Sumayya ta faɗa mata gaskiyar abinda ta faɗa cikin bacci ƙi tayi, sai maimaita mata maganarta na farko ta ke yi. Hakan ya sa wani ɓangare na zuciyarta ya fara yarda da maganar yayinda ɗaya ɓangaren yake ƙaryata haka. Ko a mafarki Allah ya sawwaƙa ta cewa Saifuddeen I love you balle har ta roƙe shi ya kissing ɗinta. Ƙarfe shabiyu na rana aka sallameta. Ba su san ya akayi 'yan jarida suka san da sallamar ba. Suna fitowa daga cikin Asibitin 'yan jarida suka musu chaa suna neman ƙarin bayanin sace ta da aka yi da kuma jinyarta, ko kidnappers ɗin sun mata wani abu?, sannan su wa ta ke zarga da wannan aikin?. Idan ba ta yi magana ba matsala ne, idan tayi ma matsala ne, dan ko mi ta faɗa ma sai an fassara shi zuwa wani abun daban. Shirun dai shi yafi dacewa tayi. Yaya Bello da Habibu ne su suka sata a tsakiyarsu suka ratsa 'yan jarida suka wuce da ita har wajen mota... ***   Asiya ba ta samu zama da Abba ba sai dare bayan sallar Isha. "Ya jikin naki?" "Da sauƙi Abba" "Alhamdulillah" Shiru ne ya biyo bayan abinda ya faɗa. Sai chan kuma ya ɗago maganar rabon gadon Umma da za ayi. Miyasa da wurwuri haka? Miyasa kayan Umma zai kasance na magada? "Mutuwa" zuciyar Asiya ya bata amsa. "Ban ji daɗin yadda na sameki da wannan yaron ba. Asiya ki riƙe aurenki da daraja dan Allah" "Abba gaisheni fa ya zo yi" "Shine kike mishi tarban da ba ki yiwa mijin ki ba?" Asiya ta ɗago da sauri ta kalli Abba cike da rashin fahimta. "Ban san mi kuka tattauna ba amma na wuce naji kina ɗagawa mijinki murya. Kina ganin hakan ya dace Shahidah?" "Allah ya gafarta wa Ummanki, har na koma ga Allah addu'a zan dinga yi mata, saboda ita ɗin macen da ta dace da a kira da suna mar'atul saliha ce. Mahaifinki da ya zo ta'aziyya a nan ya zauna yana zubda hawaye yana bayyana mini kyawawan halayenta a iya zaman da suka yi. A lokacin tanada ƙarancin shekaru ma kenan. Asiya ba ki ɗauki aurenki da mahimmanci ba, ba ki ɗauki mijinki da daraja ba. Idan har saboda mun raba ki da Ubaydullah ne kika yi watsi da aurenki to ki sani abinda kike ba abinda zai haifar miki sai baƙin ciki. Ban ji daɗi ba Asiya. Shikenan ba zaki saki ranki ki rungumi aurenki a matsayin ibada ba" "Abba shine bai ɗaukeni da daraja ba. He's using me for his campaign" "Sai me?" "Abba!" "Sai me idan yayi amfani dake wajen kamfen ɗinsa, ba mijin ki bane?" Asiya ta saka hannu ta fara goge hawayenta. Ita kam akan Gwamna Abba kamar baya sonta. Sauran nasihar Abba ma dai Asiya ba ji tayi ba, dan rabi kuka rabi saƙe-saƙe ta ke yi a zuciyarta. A rana ta uku da dawowarta sai ga Mahirah da Junior sun zo gaisheta. Lokacin tana Asibiti Hajia Umma da wasu 'yan tsiraru cikin 'yan uwan Gwamna sun zo sun gaisheta. Sai yau ne Asiya ta zauna da Mahirah saboda duk zaman da tayi a gidan Gwamna Mahira tana Kachallah house. Yarinyar kam ba laifi akwai hankali ba kamar Nana ba. Maganarta sanyi, kominta a sanyaye. Ta yi tunanin Bilkisu Kachallah ce ta turosu amma ga mamakinta sai Mahira tace mata Gwamna ne ya ce su zo su gaisheta. Junior ya sake jiki da su Ali da Gwani suka tafi da shi yawo. "Ya jikin Nana?" Asiya ta tambaya ganin shirun yayi yawa dan Mahira bata da yawar magana kamar 'yar uwarta. "Da sauƙi" "Har yanzu ba a dawo da ita gida ba?" "Sun ce sai ta cika wata shida a wajen" "Amma kuna zuwa dubata ko?" "E muna zuwa duk weekend" Asiya tana ƙoƙarin updating wayarta saboda lokacin da aka bata wayar kafin a sakota sun share kusan komai na kan wayar. "Anty Shahidah dan Allah ki kula da Daddy, wallahi bashida lafiya" Asiya ta kalleta da mamaki. Kanta a ƙasa ta cigaba da bayani "tunda aka ɗauke ki bashida lafiya. Akwai ranan da ya zo gaishe da Dadda da zai tafi sai kawai gani muka yi ya faɗi. Ya cewa Dadda kar ta faɗawa kowa, kuma har yanzu ya ƙi yaje a duba shi. He was busy, Mommy ma kuma kamfen ne a gabanta yanzu" "Miyasa kike gaya min wannan?" "Because...because you are a good person" Asiya ta kauda kanta kamar bata damu da abinda Mahira ta faɗa ba. Sai yamma kafin suka tafi, lokacin da aka dawo da Junior yayi futu-futu da shi wai ball ya buga. Da ke yaron kullum a takure yake, yanzu da ya zaga anguwa yai wasa da sa'anninsa da kuma wanda suka girmeshi sai ya langwaɓe jikin Ali yace ba zai tafi ba. Da ƙyar Asiya ta lallashe shi akan za a kawo shi gobe. Bayan tafiyar su Mahira, Asiya ta shiga tattauna maganarta dama maganar Abba daya tsaya mata a rai tun jiya. Ta kasa yarda cewa Gwamna ba shi da hannu a saceta da aka yi saboda alamu sun nuna shi munafukine. Amma yanzu kuma maganar Mahirah ya sa ta fara tantama da abinda ta sawa ranta. A wani gefe kuma kalaman Gwamna na ranan suna kashe mata jiki, suna tunkuɗe duk wani haushinsa da take ji. 'Ina son ki Asya' duk lokacin da ta tuno waɗannan kalamai sai ta dinga ji tsikar jikinta na tashi. Sannan ƙwaƙwalwarta na ƙoƙarin gano mata a wani siga za ta fayyace kalaman. Shin Gwamna yana sonta a matsayin matarsa ne, ko kuma a matsayin wacce ya kamu da soyayyarta?... Kwananta biyar a gida ta warware kamar ba ita ba. Ranan ne kuma aka raba musu gadon Umma wanda Abba ko tsinke bai ɗauka ba, dan cewa yai ya yafe nashi kason. Washegari Abba yace ta tattara ta koma gidanta. Tun maganar da Abba ya mata take shakkarsa dan haka da yai maganar ko musu ba ta yi ba ta kira Yaya Bello tace ya zo ya ɗaukesu bayan sallar magariba. Abin mamaki gidan Gwamna ta ɗauka za su wuce sai ta ga yayi hanyar gidan Gwamnati. "Yaya Bello ka kaini gidansa bana son hayaniyar wanchan gidan" "Mai girma ne yace nan gidan za a kawoki" Tayi shiru ba dan ranta ya so ba, sai dan tana ƙoƙarin bin nasihar Abba. Shine da ikon sakata a duk inda ya ga dama, tunda sunan matarsa take amsawa. "Mommy where is Hancha'u?" Junior yayi wa Bilkisu tambayar nan yafi a irga. Yanzun ma Safiyya ce ke zuba masa abinci shiyasa ya tambaya saboda tunowa da yai da ita. "Na gayama kar ka sake tambayar Hansa'u a gidan nan. She's gone" "Mommy why?" "Ni kam ko yarinyar nan mayya ce, kullum minti ɗaya biyu sai ka tambayi Hansa'u. Eat your food ko kuma na hanaka zuwa Kachallah house gobe" "gidansu Ali zan je gobe" "Waye kuma Ali?" "Alin gidansu Asiya. Oops Anty Asiya" Dai dai lokacin Asiya ta shigo dinning room ɗin da sallama. "Speaking of the devil" Bilkisu ta faɗa a ranta. Ɗakin da Asiya ta zauna kwanan baya an rufe shi. Ta tambayi wata mai aiki tace Bilkisu ce ta rufe. "Ina buƙatar key ɗin ɗakina" "Wani ɗaki fa?" Asiya ta haɗe gira tace "ɗakin da ya dace da matar Gwamna" Bilkisu Kachallah ta saka dariya, dariya sosai har da buga table. Asiya da Junior suka zuba mata ido... 11 Gwamna yana zaune a falo yana karanta jarida lokaci zuwa lokaci yana ɗan kurɓan tea. Safiyar Lahdi ne kuma ya yi niyyar babu inda zai je da safe sai yamma idan ya fita duba 'yarsa Nana. She's improving sosai, ba kamar farkon kaita ba, dan har kaman zarewa ta yi saboda ƙwayar data dena sha. Kwanan Asiya ɗaya kenan da dawowa gidan kuma tun dawowanta bata haɗu da Gwamna ba, sai yanzu da ta zo falonsa. "Barka da safiya" Tun da ta buɗe ƙofa yake binta da wutsiyar ido amma ba zaka gane hakan ba saboda gilashin da ke idonsa akwai ɗan duhu. Idonsa da kullum suke a kumbure saboda rashin isashshen barci da hutu ya saka shi sanya gilashi a koda yaushe. "An tashi lafiya?" "Lafiya" Shiru ne ya biyo bayan hakan na wasu mintina da za su iya haura biyu. "Ranan a Asibiti..." sai tayi shiru saboda nauyin maganan. Har yanzu ta kasa yarda da maganar Sumayya amma kuma hoton data gani yana yawan yi mata shawagi a idanunta musamman idan ta rufe ido. Wani lokaci tana duba hoton a wayarta saboda ta ƙara fassara hoton da Sumayya ta ɗauka. Ta saka Sumayya goge hoton a wayarta, amma kafin nan sai da ta tura hoton zuwa nata wayar ba tareda sanin Sumayya ba. "Ina jin ki?" "Abinda na faɗa cikin bacci duka ka manta dashi, saboda shirmen bacci ne" Gwamna ya ajiye jarida akan cinyarsa ya kalleta yace "ni kuma sai nake ganin kamar kin faɗi abinda ke ranki ne, dan abinda ka kwanta da shi da shi kake tashi" "A'uzubillahi. Ni wallahi ba abinda zai sa na yi irin wannan tunanin. Balle na furta munanan kalmomi haka" ta rage muryarta ƙasa ƙasa tace "sai kace wata karuwa" Gwamna bai gane inda ta dosa ba amma yace "shikenan in kince a rufe maganar za a rufeta. Amma..." "Allah shirmen bacci ne ba komai ba. Ka manta da duk abinda na faɗa" ta faɗa da sauri Sai daya kalleta kamar mai nazari sai yace "shikenan zan manta da komai" "Ina so na je garinmu. Mama bata da lafiya" "Ki yi haƙuri zuwa wani lokaci sai kije amma ba yanzu ba" Har ga Allah bata ji daɗi ba, sai dai kuma yanzu ta yi alƙawarin yi masa biyayya gwargwadon iyawarta tun lokacin da Abba ya mata faɗa... *** Sati ɗaya Asiya ta lura Hansa'u bata gidan. Da ta tambayi masu aiki sai aka ce mata tunda ta tafi ƙauye bata dawo ba. Ta ja bakinta tayi shiru, dama saboda ta saba da ita a gidan ne yasa ta tambaya da bata ganta ba. Asiya bata taɓa ganin Alhaji Abdullahi ba sai a lokacin bikinsu da Gwamna. Kafin nan kam tana jin sunansa amma ba za ta iya tuna takamaimai kamanninsa ba. Sai ga hotonsa a wayar Sumayya daga shi sai towel daya ɗaura a ƙugu. Ga tunbinsa ya fito kaman mai cikin wata takwas. Abin haushi harda riƙe ƙugu kamar wata mace. Kanta ya ɗau zafi saboda hoton da kuma inda ta samu hoton yana nuni da cewa shi ya turo hoton ta whatsapp. A ina Sumayya ta san Alhaji Abdullahi? Garin sauri saboda makara yasa Sumayya ta manta wayarta a gida. Asiya hotunan ta na biki da akayi a gidansu take son turawa taci karo da wannan hoton. Ta san password ɗin Sumayya dan haka kai tsaye ta buɗe whatsapp ɗinta ta fara neman tushen wannan hoto. Sunan da aka yi saving da My Abdul ta shiga, kuma a nan ta tarar da hoton da aka tura, a ƙasan an rubuta "yanzu na fito daga wanka" Ɗan saman chat ɗin kaɗan ta ga hoton da Sumayya ta tura masa wanda yake dishi-dishi saboda an riga an goge hoton akan wayar. Hoton ƙirjinta ne zuwa cikinta wanda babu riga babu komai. Hannu na rawa ta fara bibiyar chats ɗin wanda ya tsaya kusan sati biyu baya. Da alama an goge sauran ne saboda daga inda maganar ta fara ya nuna anyi wani a baya gogewa akayi. Idan bata manta ba Alhaji Abdullahi cousin ɗin Gwamna ne kuma abokinsa. Ba ta da masaniya akan iyalinsa amma ta san yanada mata da 'ya'ya. Nawa Sumayya take? Ko shatakwas idan ta cika to kwanan nan ne. Ta ina ma suka haɗu? Ta sake tambayar kanta. Haka ta riƙe wayar tana sintiri a ɗaki, zuciyarta na ayyano mata abubuwa dayawa. Kafin ta taho ranan kaman ta ji warin sigari tattare da Habibu amma bata sa hankali ba saboda ba a nitse take ba. Wace irin 'yaruwa ce ita da tayi watsi da lamarin ƙannenta haka? Kullum tana cikin jin haushin Gwamna ta ina zata lura da abubuwan da suke wakana a kusa da ita. Lokacin da Sumayya ta dawo, ɗakin Asiya ta fara shiga saboda ta gaisheta kamar yadda ta saba. Asiya na zaune akan sallaya lokacin da ta shigo, da alama ta idar da sallah kenan. "Wash! Anty Shahidah yau na zaunu, lectures tun safe har ƙarfe huɗu ko sallah ba a bari mun fita ba" Sumayya ta faɗa tana zama kan gado. Asiya ta juyo ta kalleta da rinannun idanunta tace " Sumayya waye My Abdul?" Sumayya ta fara wuri-wuri da ido. "Baki da bakine?" "Wani ɗan makarantanmu ne, na manta ban gaya miki bane" "Yaushe Alhaji Abdullahi ya zama ɗan makarantanku?" Sumayya tayi shiru. Asiya ta jawo wayar Sumayya a ƙasan sallaya ta buɗe ta nuna mata hoton tsoho mai tumbi. "Ki faɗa min gaskiya ko na ci uban ki a gidan nan" "Cewa yai..cewa yai yana sona" "A ina kika san shi" Asiya ta daka mata tsawa. "Tun muna wancan gidan ne, ranan ya zo neman Gwamna shine ya sameni a falo muka gaisa" "Sai kika bashi numbarki kina tura masa hoton nonuwanki ko?" Cikin Sumayya ya juya saboda bata yi tsammanin Asiya ta ga komai ba. Ta ɗauka hoton data nuna mata ne kawai. "Cewa yai zai aureni" "Zai aureki a whatsapp? Yaushe wuyanki yai ƙwari Sumayya. Har kin iya soyayya da babban mutum" "Kema ai babban mutum ɗin kika aura" Asiya ta buɗe baki ta kulle, ta kasa magana saboda tsananin mamaki. Duk da ƙirjin Sumayya na lugude saboda abinda ta faɗa hakan bai hanata jin haushin Asiya ba. Taya zata cewa My Abdul ɗinta babban mutum. "Gaskiya ne Sumayya, na auri babban mutum kam. Sai dai ni ba a titi ya sameni ba, iyayena ne suka damƙa mishi ni" ta faɗa lokacin da ta iya danne zuciyarta daga abinda take shirin aikatawa na rufe Sumayyan da duka. "Ba za ki zo ki fantsare a gidana ba, idan aure kike so zan kira Ale na faɗa mishi, dama shi ba son karatun yake ba. Daga yanzu na siezing wayarki" Sumayya ta miƙe fuuu tayi hanyar ƙofa tana faɗin " sai ki faɗawa Ale ɗin ai, ki faɗa masa. Idan an tashi ki rinƙa nuna kin fi kowa a hakan ba abinda kike tarawa kanki sai zunubi, mijinki bashida daraja a gunki" Asiya ta zauna daɓas a ƙasa lokacin da taji ƙarshen maganar Sumayya. Salati ta fara tana tantamar lafiyar Sumayya ko kuma dai Aljanu gareta?. Har dare bata sake jin ɗuriyar Sumayya ba. Tunaninta Sumayya zata gane nauyin furucinta ta dawo ta bata haƙuri amma hakan bai faru ba. Kanta bugawa ne bai yi ba saboda yawan tunani. Ƙarshe da ta ga ba sarki sai Allah ta turawa Gwamna text akan tana son magana da shi idan ya dawo. Mi tsohon nan yai wa Sumayya har ta ke iya maida mata magana?. Sumayyan da take tsananin tausayinta saboda ta rasa uwarta tun tana 'yar shekara shida. Lokacin tana gidan Ale ita ce gatan yarinyar nan saboda ba uwarta a gidan kuma babu wanda ya jata jiki. Tun tana jami'a take turawa Sumayya kuɗi saboda kada ta rasa abin buƙata. Kuɗin jarrabawarta na WAEC, JAMB dama registration da tayi da ta shiga Jami'a duk cikin aljihun Asiya ne. Yarinyar da take ganin bayan Ummanta babu wanda take kusa da ita sama da ita. Gwamna bai dawo ba sai ƙarfe goma saura na dare. Lokacin da Asiya ta ji shigowarsa gidan da sauri ta miƙe ta wuce sashensa. Baya falonsa dan haka ta wuce ɗaki dan maganar dake cinta bazata iya jiransa ba. Rage kayan jikinsa yake lokacin data shigo, daga shi sai singlet da kuma wandon da yake shirin zugewa lokacin da Asiya ta shigo ɗakin. "Afuwan. Barin jira a falo" Tayi saurin komawa da baya tana rufe ido kamar ta ga abinda bai dace ba. Minti shashida sai ga Gwamna ya fito sanye da jallabiya ruwan ƙasa. "Barka da dare" ya faɗa lokacin daya zauna. "Ina so ka jawa Alhaji Abdullahi kunne ya fita harkan Sumayya. Mutumin nan ya haura hamsin amma ƙwaƙwalwar kifi gareshi. Can you imagine yana koyawa Sumayya iskanci? Ya manta yanada nashi 'ya'yan ne? Ɗan iskan mutum kawai, Wawa, Dabba, Bunsuru, Mahaukaci. Wallahi sai na sa an ɗaure shege idan bai fita harkan ƙanwata ba, Alade kawai, mtssw" ta ƙarisa maganar tana sauke numfashi. Gwamna ya zuba mata ido, yadda ta harzuƙa tana faɗa kaman shine Alhaji Abdullahin. "Miya faru?" Ya tambaya daya ga Asiya ta ɗan nitsu. " wai soyayya su ke da Sumayya. And there exchanging nude pics" Gwamna ya zaro ido waje. Ya san halin abokinsa da shegen neman mata wanda hakanne ma ya sa ba sa taɓa zama ba su yi faɗa ba. Sai dai bai ɗauka abin yayi ƙamari har haka ba. "Mi Abdullahi yake nema ne?" Gwamna ya faɗa a ransa. Matansa uku, ta huɗun sun rabu shekara ɗaya da rabi daya wuce. Mata shida ya aura a rayuwarsa, ya rabu da uku yana tareda uku yanzu. "Ka san saboda na yiwa Sumayya faɗa yarinyar nan ta shiga gayamin maganganu marasa daɗin ji. Ka faɗa masa ya fita harkanta ko kuma na yi maganin Shege" Bai ji haushin zagin Alhaji Abdullahi da take ba saboda shi ya jawa kansa. In fact ya ji daɗin yadda ta same shi da maganar kai tsaye ba tareda tayi wani abu a bayan idonsa ba. "Ki bita a hankali Asya" "Da ɗin da zafi nake binta?" Ta faɗa tana kumbura baki. "Ina nufin idan kina so ta fahimce ki sai kin bita a hankali. She's in a phase da take jin kanta dai dai da ke, idan kika bita da faɗa ba zata taɓa ganewa ba sai dai ma ta fara gaba da ke. Zan mata magana amma zai kai gobe saboda a gajiye nake yanzu" Asiya ta sassauta murya tace " ya jiki? Kwanaki Mahirah tace baka da lafiya" "Kin damu da ni ne?" Ya tambaya yana tsura mata idanu. Asiya tayi narai narai da ido kaman za ta yi kuka. Ba dai shima gaya mata magana zai yi ba kamar yadda Sumayya ta chaka mata magana ɗazu da rana. "Ba ruwanki da Abdullahi, zan masa magana da kaina. Akwai wani abu ko na shiga ciki?" "Babu komai" Sai da ta miƙe ta fara tafiya sai kuma ta dawo tace " a kawo maka abinci ne?" "Kin damu dani ne?" Ya maimaita tambayarsa ta ɗazu. "To... to sai da safe" "Allah ya baki haƙuri Asya. A taimaka min da ruwan shayi Dan Allah" Asiya ta fita da sauri ba tareda ta sake cewa komai ba. Ita da kanta ta shiga kitchen ta haɗo masa shayin ta kawo. Tana ajiye masa ta juya da sauri ta bar falon saboda yadda ƙirjinta ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi. Gwamna yai murmushi. Yau ɗaya dai sun yi magana ta nitsuwa tsakaninsu... *** Washegari Sumayya ko leƙa Asiya ba ta yi ba ta kaɗa kai ta wuce makaranta. Cikin ranta Asiya kishi take da ita dan tana tarayya da Alhaji Abdullahi wanda shima wani hamshaƙin ne a jahar Congo kuma jinin Kachallah duk da ma ta ɓangaren mace ya zo. Asiya ta haɗa breakfast na musamman ta kai falon Gwamna ta jera komai a ƙaramin dining area dake haɗe da falon. Bata san ina Bilkisu ta je ba, amma ta lura kaman tunda ta fita jiya da safe bata dawo gidan ba. Lokacin da Gwamna ya fito. Asiya ta zubawa Junior abinci yana ci ita kuma tana zaune tana danna waya. Bai yi niyyar tsayawa ya karyawa ba, amma ba zai bari wannan damar ta wuce shi ba. Ɗan chanjin daya gani tattare da Asiya jiya ya bashi ƙwarin gwiwa. Yana zama Asiya ta shiga serving ɗinsa. Data gama ya mata godiya. "Ina Sumayya?" "Ban ma san lokacin da ta fita ba" Asiya ta faɗa cike da mamakin wannan chanji na bai ɗaya da Sumayya tayi duk saboda namiji. "Kar ki damu a hankali za ta gane gaskiya. Ki dinga mata addu'a" Asiya ta gyaɗa kai sannan ta fara cin abimci duk ranta babu daɗi... Ƙarfe shaɗaya na safe Asiya ta wuce chan gidan Gwamna, wasu kayanta zata ɗauko tunda dama bata zo da kaya dayawa nan gidan Gwamnati ba. Da ace ba abinda ya haɗata da Sumayya da ita zata aika ta ɗauko mata kayan idan ta taso daga school to amma... Sun gaisa da Uwani sannan ta wuce sashenta dan ta haɗa kayan. Minti arba'in da biyar ta ɗauka tana zaɓan kayan da zata ɗauka da wanda zata bari. Ƙarshe akwatuna huɗu ta cika da kaya. Ta kira Uwani tace ta kai mata su mota. Har zata fita ta lura da Qur'aninta da ke kan dressing mirror. Tanada wani a chan gidan, amma kuma tafi jin daɗin karatu da wannan saboda da shi ta ƙarisa haddarta, ta saba da shi, dan sama da shekaru goma kenan tana amfani da shi. Cikin handbag ɗinta ta saka Qur'anin sannan ta fita. Lokacin da Asiya ta isa gida ta samu Bilkisu ta dawo tana meeting da wasu mata. Sama sama ta amsa gaisuwan matan ta wuce ɗakinta. Wasa wasa bata ga Sumayya ba har aka yi Isha hakan ya sa ta kira Gwamna. Lokacin data kira yana tareda Alhaji Abdullahi yana masa faɗa. "Wacece kuma Attaruhu?" Alhaji Abdullahi ya tambaya da shaƙiyanci. Gwamna bai kulashi ba sai ya swiping ya amsa kiran da sallama. "Sumayya bata dawo gida ba. Ka kira Aladen nan ka tambayeshi ina ya kai min ƙanwata" "Ki kwantar da hankalinki, za ta dawo" Yana kashe wayar ya dubi Alhaji Abdullahi fiska a murtuke... Sumayya bata shigo gidan ba sai ƙarfe tara da rabi na dare, dake Asiya tace idan ta shigo a mata magana tana shigowa Safiyya ta zo ta sanar da ita. "Ina kika je?" "Lectures" Sumayya ta faɗa ko kallon Asiya ba ta yi ba. "Lectures har ƙarfe goma na dare?" "Na tsaya a hostel nayi assignment ne" Asiya ta kai mata mari tace " kar ki raina min hankali. Yaushe kika fara assignment a hostel" "Idan gorin gida zaki min sai na koma inda na fito" "Kafin ki koma kuwa sai na gyara miki zama a gidan nan..." 12 "Subhanallah!" Gwamna Saifuddeen ya furta ganin Asiya na kaiwa Sumayya duka. Hannu ya sa ya jawota yana faɗin "haba Asya, miye hakan?" Kirjinta na bugawa da ƙarfi ta fara magana "har zata ce min ina mata gorin gida, how dare she talk to me that way. Ka barni na cire mata duk wani matsamatsen dake kanta saboda nawa jujun yafi nata" ta ƙarisa maganar tana shirin kaiwa Sumayya wani dukan. Gwamna ya jawota jikinsa yana faɗin "ya isa haka, mu je ɗaki" akwai wani sinadari na saka nitsuwa a maganarsa dan kuwa yana maganar wani sanyi ya ratsata ta kasa yi masa musu haka kuma bata janye jikinta daga nasa ba har ya mata jagora suka koma nata ɗakin. Zaunar da ita yai akan gado yace " ba kya jin magana Asya. Nace miki zan mata magana" "Ina na san taje. Mi na san tsinannan tsohon nan yake mata. Idan wani abu ya sameta ni za a zaga. I've being taking care of her since she was a baby. Mahaifiyarta bata da dangi saboda cirani sukazo da iyayenta Ale ya aurota. After her death babu wanda ya san danginta saboda sun bar gari. Bata da dangin Uwa sai mu, kuma gidan mu anyi yawar da sai dai ka ci kanka. I took care of her, na zama mata uwa, na jawota jikina amma yanzu har tana da bakin gaya min maganar banza saboda wani Bunsuru" "Idan kin daketa hakan zai sa ta gane abinda kike faɗa mata ne?" "I will beat the hell out of her, har sai ta fara gudun maza" "Learn to control your anger Asya. Learn to listen and use your brain instead of your heart. Sumayya bata haɗu da Abdullahi ba yau, he was out of town, yana shigowa gari na je na sameshi a gida. Ƙila hostel ta je ko kuma ta je chan gidan ku" " Ko hostel zata je ba zata kirani ta sanar dani yau ba zata dawo da wuri ba, ta faɗi dalili" "Asya!" Yadda ya kira sunan da kuma hannunta daya riƙe yai daidai da wani halbawa da zuciyarta yai wanda sai da cikinta ya amsa. "Ki rage fushi Dan Allah" Asiya tayi shiru tana jan hanci tana ƙoƙarin danne kukanta amma ina abin ya gagara. Kukan dake cikinta yana dayawa. Kukan gazawarta, kukan yawan fushinta da kowa ke mata faɗa akai, kukan maganganun Sumayya, kukan yanzu bata da mahaifiyar da zata samu ta yiwa ƙorafin matsalarta, kukan ta kasa fuskantar rayuwan aurenta ta karɓi ƙaddararta, kukan kukan... Gwamna ya sa hannu ya jawota jikinsa ya fara bubbuga bayanta a hankali. Kamar shiga jikinsa da tayi ya ƙara mata ƙwarin gwiwa ne na yin kuka, dan buɗe baki tayi da kyau ta fara kuka kamar ƙaramar yarinya. Bai hanata ba har sai da ta gaji da kanta tayi shiru tana ajiyar zuciya akai-akai. Wannan ne karo na farko da suka kasance cikin irin wannan yanayi na kusanci. Da ta daina kukan sai ta maida hankalinta kan bugun ƙirjinsa da take ji. Ya kamata ta tashi daga jikinsa amma ta rasa taya zata fara, kunyarsa take ji da kuma kunyar yadda gangan jikinta ke jin daɗin kwanciyar da tayi a jikinsa. A ɓangaren Gwamna shima wannan kusancin yayi tasiri a jikinsa. Ji yake kamar su dawwama a haka. Babu wanda yayi yunkurin sake wani sai da wayar Gwamna tayi ƙara, hakan yasa Asiya tayi saurin barin jikinsa ta miƙe da sauri sai taji an riƙo hannunta. "Ina zaki je?" "Ban banɗaki" ta faɗa ba tareda ta juyo ta kalleshi ba. Ƙin fitowa tayi daga banɗakin har sai da ta ji alamar ya fita daga ɗakin sannan ta fito. Ta tsaya gaban madubi tana kallon fiskarta da ke jiƙe saboda alwala da ta yo. *"a duk lokacin da kike cikin tsananin fushi to ki yawaita yin Isti'aza. Idan kin samu dama ki yi alwala ki yi sallah raka'a biyu ki nemi tsari daga Shaiɗan, idan kina da lokaci ki buɗe Alƙur'ani ki karanta saboda samun nitsuwa"* Nasihar Gwani kenan, wani lokaci da daɗewa da take gidan Ale, wata Amaryar Ale da suke kusan sa'anni ta cire mata kayanta daga igiyar shanya ta zubasu a ƙofar ɗakin Tabawa bayan akwai kashin Awaki a wajen. Da ta zo ta ga kayan aka ce mata Basira Amarya ce sai kawai taje ta ɗau jarkan manjan Fulani ta shiga ɗakin Basira ta buɗe akwatunanta guda uku kowanne ta zuba manjar a ciki ta ɓata mata duka kayanta. Data gama ta wuce gidan Gwani Fulani ta dawo ta dinga bala'i a gidan sai an biyata kuɗin manjarta. Itama Basira data gani ta fara masifa ƙarshe sai da Aljanunta suka tashi. Ale ya dawo gida ya samu gidan a rikice, aka gaya mishi abinda Asiya ta aikata. Ala tilas ya biya Fulani kuɗin manja, ita kuma Basira dama da Aljanun suka lafa sai ta wuce gidansu. Bayan Isha yaje ya samu Gwani ya faɗa masa abinda Asiya tayi. Gwani bai mata magana a ranan ba sai washegari data dawo daga makaranta ya kirata ɗakinsa ya fara mata nasiha akan yawan fushi. *"Ki daina saurin aikata duk abinda zuciyarki ya haska miki Asiya Shahidah. Saboda yin hakan zai saka miki rashin nitsuwa, zai sa ki cikin ƙunci"* "Allah ya ƙara maka rahama Gwani" Ta furta a fili sannan ta wuce closet ta ɗauko hijabi ta tada sallah. Data gama tayi addu'ar Allah ya sanyaya mata zuciya ya kuma bata ikon kula da tarbiyyan 'yaruwarta dama sauran ƙannenta. Shigowar Gwamna ɗakin ya sa ta fasa buɗe Ƙur'anin da ke gabanta. "Asya a mana addu'a zan wuce Abuja" "Yanzu?" "Flight ɗin ƙarfe shaɗaya na dare ne" "Allah ya kiyaye hanya" ta faɗa tana sunkuyar da kanta ƙasa saboda idonta daya faɗa nashi. Murmushi yai ya ƙaraso wajen da take zaune. Ganin ya zo daf da ita sai ta fara ƙyafƙyafta ido tana tambayar kanta mi zai yi kuma?. Ba dai abinda ya faru ɗazu ya buɗe mishi wata dama bane. Hannunta ɗaya ya kamo yace " kwana biyu zan yi na dawo. Ina neman alfarma Dan Allah. Za ki min?" Ba tareda ta ɗago ta kalleshi ba tace "minene?" "Kada ki yiwa Sumayya faɗa. Na yiwa Abdullahi magana kuma zan tabbatar cewa ya rabu da ita completely. Andddd..." "And?" Ta maimaita ganin bai ce komai ba. "Ki rage zafi kin ji" Za ta yi magana ya manna mata peck a goshi yace na tafi. Bai jira farfaɗowanta daga ɗaukewan numfashin hucin gadin da tayi ba, ya miƙe ya bar ɗakin. Like mentally gani take har lokacin yana ɗakin, har lokacin laɓɓansa na dai-dai tsakiyar goshinta, hakan ya sa ta kasa buɗe idanunta. Ba zata iya fassara yadda hanjin cikinta ya taƙune ba. Ko butterflies ne ko ma wani abun ne daban, ta dai ji wani abu ya fara mata yawo a ciki hakan ya sa ta sa hannu ta riƙe cikin. "Anty Asiya" muryar Junior ya fargar da ita daga yanayin data shiga. Bata san iya tsawon lokacin data zauna a wajen ba bayan tafiyar Gwamna. "Junior baka yi bacci ba?" Ƙarfe tara ne dokar baccinsa ko yana so ko baya so. Ɗan kwanakin nan data dawo ta ke ɗan kula da yaron yasa ta san kusan komai nasa. Yana sanye da Pyjamas kalar sky blue ganin fiskarsa sai ta hango fiskar Gwamna Saifuddeen. "Tell me a story" ya faɗa yana zama gefenta. Tunda ta bashi labarin CY da Biri kullum sai yace ta sake bashi labarin baya gajiya da jin shi. "Wani labari?" "CY and the Monkey" "Kaga dare yayi, idan Mommy ta san baka yi bacci ba zata yi faɗa" "Mommy bata nan" Ta jawo shi jikinta sosai tace "barin koya maka addu'ar bacci, gobe sai ayi labarin"... A ɓangaren Gwamna Saifuddeen kuwa, yana fita daga gida ya dinga murmushi. A cikin mota kafin su kai airport kasa haƙuri yai ya fito da wayarsa ya fara duba hotunan Asiya ciki harda wanda ba zata taɓa tunanin yana da su ba. Yana fata wannan chanjin ya zamo mai ɗaurewa. Bayan Asiya ta kai Junior ɗakinsa sai ta dawo ta naɗe sallaya ta kwanta. Maimakon bacci ya zo sai bacci ya ƙaurace mata, ta dinga juyi akan gado tana ƙoƙarin hana ƙwaƙwalwarta tunanin mutumin da a da ko sunansa bata son ji. Sai chan tsakar dare bacci ya saceta. *** Washegari tana idar da sallar Asuba ta yi Azkar ta fara tilawa. Wanda zata yi karambanin yi masa breakfast baya nan, dan haka ba zata wahalar da kanta ba. Bata ma jin ƙarfin fita waje. Kamar jiya haka yau ma Sumayya ta fice daga gidan ko leƙa Asiya ba ta yi ba. Asiya tana cikin karatu ta lura da wata takarda acikin Ƙur'anin. Da da chan tana da yawan ajiye kuɗi acikin ƙur'ani, amma rabonta da yin hakan har ta manta. Ta jawo takardar tana son ganin ko na minene, ƙila ma irin ayoyin addu'a da take rubutawa Umma ne. *Dear Asiya...* *zan so ki yarda da mijinki, ki taimaka masa saboda shi ba maƙiyin ki bane. Ki yi hankali da Bilkisu Kachallah, ita ta sa aka sace ki, kuma zata iya yin fiye da haka. Shawarata gareki shine "don't act stupid, act smart"* *Agent R.B.K (Hansa'u)* "Hansa'u?" Asiya ta furta cikin kaɗuwa. 13 Tabbas Biri yai kama da Mutum. Abinda Asiya ta faɗa kenan a ranta. "What should i do?. Idan na tunkari Bilkisu Kachallah haka, zata iya ƙaryata komai. Tukunna ma ina Hansa'u ta shiga?". Tun kafin wannan rana bata taɓa ganin Bilkisu Kachallah a matsayin matar da zata sota har ta karɓeta hannu bibbiyu ba. Yanzu kuma ta ƙara fahimtar manufar wannan mata akanta. "Think Asiya, Think Shahidah" Asiya ta faɗa tana bubbuga kanta da yatsun hannunta biyu. Ta jima tana saƙa da warwara, kafin ta tsaida mafita ɗaya. Dole ta nemo Agent RBK ɗin nan, ita ne zata mata ƙarin bayani. "Excellency yace na dinga amfani da ƙwaƙwalwata. Letting my emotions get over me shiyasa na haɗa hannu da Umaru Kwom kwanan baya" Ta saka kanta a tsakiyar cinyoyinta tana huci. "Rashin tunani yasa nake zargin Gwamna da sawa a sace ni while he's innocent. He's always innocent, ni ce na tsane shi" Ta ɗago kanta tana faɗin "miyasa ma na tsane shi?" Ta gama tunanin duniyan nan bata gano ƙwaƙwƙwaran dalilin da yasa ta tsani Saifuddeen Sa'ad Kachallah ba, domin tun kafin ta aure shi ta tsane shi balle tace aurenta da yai shine dalilin. Ƙarshe wani tunani ne ya zo mata hakan yasa tayi saurin janyeshi daga ranta dan ba tunani ne mai kyau ba. Ta ɗau wayarta ta kira numbar Fou'ad Salisu amma bai ɗauka ba dan haka ta tura masa text. *** Asiya ta sauko ƙasa kenan suka yi kichiɓis da mai girma Bilkisu Kachallah da ke shirin haurowa. Kallon-kallo suka fara yi dan kuwa babu wanda yake da niyyar matsawa ɗan uwansa. Bilkisu daga wajen rabon kayan Kamfen take. Ba ita tayi rabon ba amma jimawa da ta yi a tsaye tana karɓan gaisuwa da jinjina daga waɗanda suka karɓi kayan da aka basu ya gajiyar da ita. An raba kwalin sabulai, kwalin spaghetti mudun sugar da shinkafa sai kuma turmin zani mai hoton Bilkisu da Saifuddeen. Kanta kamar zai tsage saboda hayaniya da kuma ihu da ta dinga yi a mic lokacin da take ihun 'Jama'a, Congo sai waaa?' Matan talakawa da miskinai suka dinga wage baki suma suna ihun 'Congo sai Saifuddeen Kachallah' ko kuma suce 'Congo sai SSK' A zuciyar Asiya ji take kamar taje ta shaƙe wuyar wannan munafukar mata amma ta dinga bawa zuciyarta haƙuri da cewa ba yanzu ba, akwai lokaci. A ɓangaren Bilkisu kuma tunanin yadda za ayi ta fitar da Asiya daga gidan Gwamnati take. Indai aka ci zaɓe to dole ne ta koma chan gidan, saboda ba za ayi Matan Gwamna biyu a gidan Gwamnati ba. A nan gidan there will be only one Governor's wife, Bilkisu Kachallah. Ganin Asiya bata da niyyar matsawa yasa Bilkisu ta ƙariso ta bangajeta ta wuce. Asiya tayi saurin riƙe kafaɗanta saboda ba ƙaramin bugu Bilkisun ta mata ba. Magana take so ta faɗa amma sai ta lura da Safiyya dake wajen riƙe da jakar Bilkisu Kachallah tana wiki-wiki da ido. Bata son ma'aikatan gidan su fara gulman matan Gwamna suna faɗa, shi yasa ta kauda kai ta sauko. Safiyya ta ɗan duƙar da kai tana faɗin "ranki shi daɗe" Asiya ta haɗe rai ta wuce ta Tana fita Motarta ta shiga Yaya Bello ya wuce da ita Kachallah house. Rabonta da gidan tun ranan da za a kawota gidan miji. Sashen Hajiya Dadda ta wuce. Ta samu tsohuwar a falo tana karanta jarida. Sallamar Asiya yasa ta ɗan tura gilashinta sama sannan ta ɗago tana kallon ƙofa dan bata gane muryar ba. "Lah lah. Amarya ce da kanta?. Marhaban Marhaban" Asiya zata zauna Dadda ta ce ta matso ta raɓeta. Asiya ta ƙarisa ta rungumi tsohuwar. "Kinsan mu da muke kan gangara muna son jin ɗumin mutane kusa da mu" tayi maganar tana dariya tareda zare gilashin idonta ta maida shi gidansa. "Haba dai. Hajiya ai har yanzu da sauran ƙarfin ki, ai sai kin cika ɗari har da ɗaya tukunna" "Ko shekaru nawa kayi a doron ƙasa ƙarshe dai sai ka ɗanɗani mutuwa, ko yaushe dai ta taho muna addu'ar ta same mu masu imani, kar ta ɗaukemu muna cikin shashanci da gafala" ta nisa tace "Ya aka ji da haƙuri kuma, kiyi haƙuri ciwon ƙafa bai barni na je gaisuwa ba?" Jiki a sanyaye Asiya ta amsa da cewa " Alhamdulillah Hajiya. Allah ya ƙara lafiya" "Allah ya gafarta mata Amin" "Amin" Shiru ne ya ɗan biyo bayan haka kafin Dadda tace " ya aka ji da hayaniyar Kamfen kuma. Ita 'yar uwarki kullum sai an nunota a tv ko jarida tana yawon kamfen, bana tunanin tana kula da lamarin Saifu ko 'ya'yanta. Ita Aisha tana cewa tunda aka kai mai suna gidan 'yan ƙwaya sau ɗaya mahaifiyarsu ta ziyarceta. Kar ki manta fa ita ce sanadin lalacewar 'yar, yo ina ta zauna da su ta fuskanci matsalarsu ma, yau tana wannan ƙasa gobe tana wancan gari. Haka take tun tana ƙarama ƙafarta baya zama waje ɗaya" Asiya bata yi mamakin wannan zance da Dadda keta sakewa ba. Dama idan mutum ya tsufa ba abinda yake so irin a saurareshi. Ba zata manta lokacin da cikin matan Ale suke zagin Tabawa ba wai tana haɗa guri. Ta sani dama tun kafin tsufan Tabawa akwaita da gutsiri tsome to amma shekaru yasa abin ya ƙara gaba. Sai dai baka zauna da ita ba amma haka zata kawo zancen wannan ta kawo na wancan, wani ma ya sake zuwa haka zata kwashe naka ta gaya mishi. Dadda ta cigaba " kwanaki ma haka suka yi faɗa da ƙannenta. Saudah a gaban Uban ta rantse babu ruwanta da Bilkisu har abada. Halima kam tun ranan da ta kira Bilkisu da Boka suka raba gari. Yo idan ba Bilkisu ba, Haliman nan fa abar tausayi ce, ta kusa shekara talatin da biyar amma babu mashinshini, wannan ai ya isa ya taɓa mata lafiyar ƙwaƙwalwa." Asiya tace " ina Anty Halima ita ce autar Alhaji ko?, lokacin biki kaman ita da Hajiya Umma suke ta shige da fice" " itace Auta. Daga Rufaida sai Bilkisu, sai Saudah, mai suna, sai kuma ita Halima" Asiya ta dinga gyaɗa kai tana sauraron tarihin 'ya'ya da kuma jikokin Hajiya Dadda. Ba wannan ne ya kawota ba amma kuma wannan ɗinma ba a banza ya tafi ba dan ta ƙara tsintar wasu halayen Bilkisu Kachallah. "Ai Bilkisu a rayuwarta ita kaɗai kawai ta sani. Har yau tana juya kaf yayye da ƙannenta. Na yi mamaki da bata tada fitina ba lokacin da Saifu yace zai aure ki" A zuciyar Asiya tace "saboda ta san abinda ta shirya min idan na shigo ba" Labarin Saifuddeen data fara ne ya jawo ta tuna da ɗanta Sa'ad. "Saifu kaf halin ubansa ya ɗauko. Dai dai da magana da tafiya duk irin tasa ce. Harta murmushi idan yai sai naga kamar Sa'ad ne a gabana" sai kuma ta fara goge hawayen daya fara zubo mata. Mutuwa sama da shekaru arba'in amma har yanzu idan ta tuno sai ta ji ɗaci aranta kamar yau aka yita. "Hajiya Allah ya gafarta masa" "Amin, Amin fa. Ai Sa'ad ya tafi a sa'a, gashi ya bar baya da kyau. Allah ya ƙarawa ɗansa lafiya da nisan kwana" Asiya ta amsa da Amin. Chan cikin zuciyarta kuwa tana tunawa da sati ɗaya zuwa biyu baya babu wanda ta tsana a duniya sama da Saifuddeen Kachallah har take ganin da zai mutu ma da zata fi kowa jin daɗi. Dadda ta miƙe ta shiga ɗaki ta kawowa Asiya hotunan tarihi. A nan ta ga hotonan bikin Dr Sa'ad Habu Kachallah da Aicha Ali Jallow. Ashe Saifuddeen gadon kyau yayi. Duk da hoton black and white ne hakan bai ɓoye kyawun iyayensa ba musamman mahaifiyarsa wacce daga wajenta ya ɗauki manyan idanu da kuma dimple sai dai bai ɗauko farinta ba sai ya ɗau baƙi da tsawon Uban shi. Yana daga cikin dalilan da zata iya cewa sun haddasa mata ƙiyayyar Saifuddeen a baya, irin yadda mutane suke kururuta shi. Kyaunsa, iya wankansa, tafiyarsa dama maganarsa. A baya ta tsani muryarsa saboda sanyin muryar yayi yawa kamar na mace. Amma yanzu koyaushe ta tuna maganarsa "ina son ki Asya" sai ta ji tsikar jikinta ya tashi. Lokacin da Dadda ta faɗa mata Saifuddeen bai taɓa ganin iyayensa ba sai a hoto, wani tausayinsa ne ya ratsa ta. Ashe gara ita ta rayu da tata mahaifiyar har zuwa lokacin data mallaki hankalin kanta. Amma shi... Sai yamma liƙis Mahirah ta dawo daga Islamiyya. Lokacin Asiya da Dadda sun wuni hira, a nan tayi sallar Azahar da La'asar kuma suka ci abinci tare. Ta taso da tsofi kusa da ita dan haka duk tsawon zaman da suka yi bata gaji da ita ba, ta ƙaru sosai kuma ta sake samun darasin rayuwa. Duk da ahalin Habu Kachallah suna cikin arziƙi amma suma suna fuskantar jarabawa iri-iri, daga kan 'ya'ya, jikoki da ma 'ya'yan jikoki. Dama haka rayuwar take babu wanda zai tsira daga jarrabawar Allah, sai dai na wani ya banbanta da na wani. Bayan sun keɓe da Mahirah ne ta tambayeta ko tanada hoton Hansa'u a wayarta. Mahirah tace baza a rasa ba cikin hotunan da ta ɗauke su ita da Junior lokacin tana gidan. Ta jima tana duba wayarta kafin ta samo hoto ɗaya da Junior ya musu selfie. Fiskar Hansa'u na karkace amma dai duk wanda ya santa zai iya ganeta. Asiya ta tura hoton a wayarta sannan ta musu sallama ta tafi. A cikin mota ta turawa Fou'ad hoton tana addu'ar Allah yasa ya binciko mata agent RBK da gaggawa. Lokacin data isa gida ɗakin Sumayya ta fara wucewa, ta samu Summayar ta dawo tana sallah. Ta wuce nata ɗakin dan a gajiye take. Bayan ta gama sallar Isha ta kwanta tana tunanin abinda ya dace ta yi a wannan lokaci. Idan ta yi gaggawan yanke hukunci akan Bilkisu zata iya rasa bakin zaren da take son warwarewa, dan haka dole tabi komai a nitse sannan tayi shiru da bakinta har zuwa lokacin da zata san duka gaskiyar. *** Cikin kwana biyun da Asiya tayi kafin Gwamna ya dawo ta yi su ne cikin takatsantsan da kuma shirye-shiryen wani ƙudurinta da take son aiwatarwa idan Gwamna ya dawo. A rana ta uku da take tunanin dawowan Gwamna har dare shiru babu ɗuriyarsa. Tsoron zaƙewa take shiyasa ta kasa kira ko ta masa text ta ji ko lafiya bai dawo ba. Besides da yamma ta shiga kitchen ta ga ana ta kan shirye-shirye wai Bilkisu ce ta bada umurnin girkin da za ayi saboda Gwamna na hanya. Haushi ya sa ta koma ba tareda ta yi abinda tayi niyya ba. Kenan bai damu da ita ba, har zai sanar da Bilkisu dawowarsa amma bai tuntuɓeta ya gaya mata ba. Haushi ya cika mata ciki ta kasa cin abincin dare. Tana kwance kan gado duk bata jin daɗi, ga haushin Gwamna ga baƙon wata da ke yi mata sallama. Junior ya shigo wai ta masa labari. "Junior bana jin daɗi ka bari gobe zan maka" "No, jiya ma baki min ba" Ganin ba haƙura zai yi ba yasa ta miƙe tace su je ɗakinsa. "Wani labari zan yi" "CY and the monkey" "Ikon Allah. Idan CY ya kamaka kana masa dariya zaka gayawa 'yan garinku" Junior ya fara dariya tun ma bata faɗi labarin ba. Tun ranan da ta bashi labarin indai ya tuno sai yayi dariya, kuma kowanni lokaci zata bada labarin sai ya ji kaman yanzu ne farkon jin labarin a bakinta. Da ke a gajiye take, a gurguje zata bashi labarin ta huta da rigimarsa. "Akwai wani abokina ana ce masa CY amma asalin sunansa Clement Yohannah. Watarana ni da shi muka je gidan zoo ɗaukan rahoto saboda tsohon Zakin gidan zoo ɗin ya mutu. Da muka gama naɗan rahoto sai muka fara yawon buɗe ido a cikin zoo ɗin. Muka haɗu da wasu 'ya'yan birrai suna wasa. CY ya ɗau camera yaje wajensu ya fara ɗaukansu a hoto. Da ya matsa kusa da su sai suka watse sai guda ɗaya. CY ya shiga ɗaukanta tana rawa, ƙarshe data gudu sai ya bita. Ina kiran CY akan ya haƙura da Birran nan ya zo mu tafi amma yai kunnen ƙashi. CY ya bi Birrai har wajen duwatsu. Yana saƙale da camera a wuyansa ya riƙeta yana shirin ɗaukan wani Biri sai wancan Biri mai rawan nan ta zo bayan CY ta zabga masa bulala a wuya. CY ya riƙe kunne ya juyo da sauri ya ga daga ina aka dake shi, bai gama juyawa ba aka sake zuba masa bulala a tsakiyar kai. CY ya saka ihu ya fara gudu yana kiran 'Jesus my head ooo. I don die ooo' ai kuwa Birrai kusan biyar suka biyo CY da gudu dukkansu da bulala a hannunsu. CY ya yar da camera, ya yar da takalmi ya cigaba da ihu yana kiran 'i don die oo' Har muka koma gida CY bai san inda kansa yake ba, da an taɓa shi zai fara 'i don die oo' kafin a kai gida kan CY ya kumbura suntun" Tun kafin ta kawo nan Junior ya ke dariya. Itama dariyan ta fara, saboda tunowa da tayi wannan ne silar shaƙuwarsu da CY dan lokacin bata jima da fara bautar ƙasa a tashar Hill TV ba. Gwamna da ke tsaye bakin ƙofa ya tako har bakin gadon. Ƙanshin turarensa da Asiya ta ji yasa ta tsaida dariyan, bugun zuciyarta ya ƙaru. "Daddy" Junior ya faɗa yai tsalle ya faɗa jikin Gwamna. "My boy ya kake?" "I'm fine Daddy" Asiya bata ɗaga ido ta kalleshi ba saboda tsoron haɗa ido take da shi. Dai dai kunnenta ta ji yace " ki faɗawa Junior gaskiya, ba CY kaɗai aka zane ba, mai bada labarin ma an taɓa lafiyarta" A fusace ta juyo tace "waya gaya ma..." bakinta ya kafe lokacin da ya kissing goshinta. "Anty Asiya da gaske kema Monkey ya dake ki?" Junior ya faɗa dan ya ji abinda Gwamna ya faɗa. Da ƙyar Asiya ta iya haɗa kalmomin bakinta tace " a'a Junior, CY kaɗai aka zane" Miƙewa ta yi ta yiwa Junior good night sannan tayi hanyar ƙofa da sauri, bata kai ƙofar ba aka riƙo hannunta. Zuciyarta yai wani tsalle lokacin da Gwamna Saifuddeen ya mannata da ƙirjinsa ya rungumeta da kyau yana faɗin "Asya ko sannu da zuwa ba zan samu ba" Duk ƙoƙarinta na son yin magana ta kasa saboda duk abinda ya taho a maƙoƙoro yake tsayawa. "Fatan na same ku lafiya?" ya faɗa bayan ya rabata da jikinsa amma bai sake mata hannu ba. "Wanda kake son samun su lafiya suna nan lafiya, sun ma shirya maka liyafar dawowa" Tayi ƙoƙarin raba hannunsu amma ta kasa. "Nan da kwana biyu zaki iya shirya mini taki liyafar saboda kema na same ki lafiya" ya ƙarisa maganar yana murmushi. Ganin ya sake mata hannu yasa ta tura baki ta fice daga ɗakin tareda banko musu ƙofa. Har ga Allah ta ɗauka zai biyota ɗaki amma har bacci ya ɗauketa bata ji ɗuriyarsa ba. Bayan Gwamna ya bar ɗakin Junior kuma, sashensa ya wuce inda Bilkisu ke jiransa. "Darling akwai improvement sosai a Kamfen namu. Duk anguwar daka shiga posters ɗinmu suka fi yawa and..." "Tun ban zauna ba Bilkisu" "Sorry Darling, kayi wanka ka fito, na shirya maka special dishes" "Cook ya shirya special dishes" "Da izini na ba, kaga kaman ni na yi kenan" Ya girgiza kai ya wuce ɗaki bayan ya manna mata kiss a kumatu. A gajiye yake dan haka baya son dogon musu... *Afuwan Dan Allah. School activities ne ya riƙe ni* 13 Tabbas Biri yai kama da Mutum. Abinda Asiya ta faɗa kenan a ranta. "What should i do?. Idan na tunkari Bilkisu Kachallah haka, zata iya ƙaryata komai. Tukunna ma ina Hansa'u ta shiga?". Tun kafin wannan rana bata taɓa ganin Bilkisu Kachallah a matsayin matar da zata sota har ta karɓeta hannu bibbiyu ba. Yanzu kuma ta ƙara fahimtar manufar wannan mata akanta. "Think Asiya, Think Shahidah" Asiya ta faɗa tana bubbuga kanta da yatsun hannunta biyu. Ta jima tana saƙa da warwara, kafin ta tsaida mafita ɗaya. Dole ta nemo Agent RBK ɗin nan, ita ne zata mata ƙarin bayani. "Excellency yace na dinga amfani da ƙwaƙwalwata. Letting my emotions get over me shiyasa na haɗa hannu da Umaru Kwom kwanan baya" Ta saka kanta a tsakiyar cinyoyinta tana huci. "Rashin tunani yasa nake zargin Gwamna da sawa a sace ni while he's innocent. He's always innocent, ni ce na tsane shi" Ta ɗago kanta tana faɗin "miyasa ma na tsane shi?" Ta gama tunanin duniyan nan bata gano ƙwaƙwƙwaran dalilin da yasa ta tsani Saifuddeen Sa'ad Kachallah ba, domin tun kafin ta aure shi ta tsane shi balle tace aurenta da yai shine dalilin. Ƙarshe wani tunani ne ya zo mata hakan yasa tayi saurin janyeshi daga ranta dan ba tunani ne mai kyau ba. Ta ɗau wayarta ta kira numbar Fou'ad Salisu amma bai ɗauka ba dan haka ta tura masa text. *** Asiya ta sauko ƙasa kenan suka yi kichiɓis da mai girma Bilkisu Kachallah da ke shirin haurowa. Kallon-kallo suka fara yi dan kuwa babu wanda yake da niyyar matsawa ɗan uwansa. Bilkisu daga wajen rabon kayan Kamfen take. Ba ita tayi rabon ba amma jimawa da ta yi a tsaye tana karɓan gaisuwa da jinjina daga waɗanda suka karɓi kayan da aka basu ya gajiyar da ita. An raba kwalin sabulai, kwalin spaghetti mudun sugar da shinkafa sai kuma turmin zani mai hoton Bilkisu da Saifuddeen. Kanta kamar zai tsage saboda hayaniya da kuma ihu da ta dinga yi a mic lokacin da take ihun 'Jama'a, Congo sai waaa?' Matan talakawa da miskinai suka dinga wage baki suma suna ihun 'Congo sai Saifuddeen Kachallah' ko kuma suce 'Congo sai SSK' A zuciyar Asiya ji take kamar taje ta shaƙe wuyar wannan munafukar mata amma ta dinga bawa zuciyarta haƙuri da cewa ba yanzu ba, akwai lokaci. A ɓangaren Bilkisu kuma tunanin yadda za ayi ta fitar da Asiya daga gidan Gwamnati take. Indai aka ci zaɓe to dole ne ta koma chan gidan, saboda ba za ayi Matan Gwamna biyu a gidan Gwamnati ba. A nan gidan there will be only one Governor's wife, Bilkisu Kachallah. Ganin Asiya bata da niyyar matsawa yasa Bilkisu ta ƙariso ta bangajeta ta wuce. Asiya tayi saurin riƙe kafaɗanta saboda ba ƙaramin bugu Bilkisun ta mata ba. Magana take so ta faɗa amma sai ta lura da Safiyya dake wajen riƙe da jakar Bilkisu Kachallah tana wiki-wiki da ido. Bata son ma'aikatan gidan su fara gulman matan Gwamna suna faɗa, shi yasa ta kauda kai ta sauko. Safiyya ta ɗan duƙar da kai tana faɗin "ranki shi daɗe" Asiya ta haɗe rai ta wuce ta Tana fita Motarta ta shiga Yaya Bello ya wuce da ita Kachallah house. Rabonta da gidan tun ranan da za a kawota gidan miji. Sashen Hajiya Dadda ta wuce. Ta samu tsohuwar a falo tana karanta jarida. Sallamar Asiya yasa ta ɗan tura gilashinta sama sannan ta ɗago tana kallon ƙofa dan bata gane muryar ba. "Lah lah. Amarya ce da kanta?. Marhaban Marhaban" Asiya zata zauna Dadda ta ce ta matso ta raɓeta. Asiya ta ƙarisa ta rungumi tsohuwar. "Kinsan mu da muke kan gangara muna son jin ɗumin mutane kusa da mu" tayi maganar tana dariya tareda zare gilashin idonta ta maida shi gidansa. "Haba dai. Hajiya ai har yanzu da sauran ƙarfin ki, ai sai kin cika ɗari har da ɗaya tukunna" "Ko shekaru nawa kayi a doron ƙasa ƙarshe dai sai ka ɗanɗani mutuwa, ko yaushe dai ta taho muna addu'ar ta same mu masu imani, kar ta ɗaukemu muna cikin shashanci da gafala" ta nisa tace "Ya aka ji da haƙuri kuma, kiyi haƙuri ciwon ƙafa bai barni na je gaisuwa ba?" Jiki a sanyaye Asiya ta amsa da cewa " Alhamdulillah Hajiya. Allah ya ƙara lafiya" "Allah ya gafarta mata Amin" "Amin" Shiru ne ya ɗan biyo bayan haka kafin Dadda tace " ya aka ji da hayaniyar Kamfen kuma. Ita 'yar uwarki kullum sai an nunota a tv ko jarida tana yawon kamfen, bana tunanin tana kula da lamarin Saifu ko 'ya'yanta. Ita Aisha tana cewa tunda aka kai mai suna gidan 'yan ƙwaya sau ɗaya mahaifiyarsu ta ziyarceta. Kar ki manta fa ita ce sanadin lalacewar 'yar, yo ina ta zauna da su ta fuskanci matsalarsu ma, yau tana wannan ƙasa gobe tana wancan gari. Haka take tun tana ƙarama ƙafarta baya zama waje ɗaya" Asiya bata yi mamakin wannan zance da Dadda keta sakewa ba. Dama idan mutum ya tsufa ba abinda yake so irin a saurareshi. Ba zata manta lokacin da cikin matan Ale suke zagin Tabawa ba wai tana haɗa guri. Ta sani dama tun kafin tsufan Tabawa akwaita da gutsiri tsome to amma shekaru yasa abin ya ƙara gaba. Sai dai baka zauna da ita ba amma haka zata kawo zancen wannan ta kawo na wancan, wani ma ya sake zuwa haka zata kwashe naka ta gaya mishi. Dadda ta cigaba " kwanaki ma haka suka yi faɗa da ƙannenta. Saudah a gaban Uban ta rantse babu ruwanta da Bilkisu har abada. Halima kam tun ranan da ta kira Bilkisu da Boka suka raba gari. Yo idan ba Bilkisu ba, Haliman nan fa abar tausayi ce, ta kusa shekara talatin da biyar amma babu mashinshini, wannan ai ya isa ya taɓa mata lafiyar ƙwaƙwalwa." Asiya tace " ina Anty Halima ita ce autar Alhaji ko?, lokacin biki kaman ita da Hajiya Umma suke ta shige da fice" " itace Auta. Daga Rufaida sai Bilkisu, sai Saudah, mai suna, sai kuma ita Halima" Asiya ta dinga gyaɗa kai tana sauraron tarihin 'ya'ya da kuma jikokin Hajiya Dadda. Ba wannan ne ya kawota ba amma kuma wannan ɗinma ba a banza ya tafi ba dan ta ƙara tsintar wasu halayen Bilkisu Kachallah. "Ai Bilkisu a rayuwarta ita kaɗai kawai ta sani. Har yau tana juya kaf yayye da ƙannenta. Na yi mamaki da bata tada fitina ba lokacin da Saifu yace zai aure ki" A zuciyar Asiya tace "saboda ta san abinda ta shirya min idan na shigo ba" Labarin Saifuddeen data fara ne ya jawo ta tuna da ɗanta Sa'ad. "Saifu kaf halin ubansa ya ɗauko. Dai dai da magana da tafiya duk irin tasa ce. Harta murmushi idan yai sai naga kamar Sa'ad ne a gabana" sai kuma ta fara goge hawayen daya fara zubo mata. Mutuwa sama da shekaru arba'in amma har yanzu idan ta tuno sai ta ji ɗaci aranta kamar yau aka yita. "Hajiya Allah ya gafarta masa" "Amin, Amin fa. Ai Sa'ad ya tafi a sa'a, gashi ya bar baya da kyau. Allah ya ƙarawa ɗansa lafiya da nisan kwana" Asiya ta amsa da Amin. Chan cikin zuciyarta kuwa tana tunawa da sati ɗaya zuwa biyu baya babu wanda ta tsana a duniya sama da Saifuddeen Kachallah har take ganin da zai mutu ma da zata fi kowa jin daɗi. Dadda ta miƙe ta shiga ɗaki ta kawowa Asiya hotunan tarihi. A nan ta ga hotonan bikin Dr Sa'ad Habu Kachallah da Aicha Ali Jallow. Ashe Saifuddeen gadon kyau yayi. Duk da hoton black and white ne hakan bai ɓoye kyawun iyayensa ba musamman mahaifiyarsa wacce daga wajenta ya ɗauki manyan idanu da kuma dimple sai dai bai ɗauko farinta ba sai ya ɗau baƙi da tsawon Uban shi. Yana daga cikin dalilan da zata iya cewa sun haddasa mata ƙiyayyar Saifuddeen a baya, irin yadda mutane suke kururuta shi. Kyaunsa, iya wankansa, tafiyarsa dama maganarsa. A baya ta tsani muryarsa saboda sanyin muryar yayi yawa kamar na mace. Amma yanzu koyaushe ta tuna maganarsa "ina son ki Asya" sai ta ji tsikar jikinta ya tashi. Lokacin da Dadda ta faɗa mata Saifuddeen bai taɓa ganin iyayensa ba sai a hoto, wani tausayinsa ne ya ratsa ta. Ashe gara ita ta rayu da tata mahaifiyar har zuwa lokacin data mallaki hankalin kanta. Amma shi... Sai yamma liƙis Mahirah ta dawo daga Islamiyya. Lokacin Asiya da Dadda sun wuni hira, a nan tayi sallar Azahar da La'asar kuma suka ci abinci tare. Ta taso da tsofi kusa da ita dan haka duk tsawon zaman da suka yi bata gaji da ita ba, ta ƙaru sosai kuma ta sake samun darasin rayuwa. Duk da ahalin Habu Kachallah suna cikin arziƙi amma suma suna fuskantar jarabawa iri-iri, daga kan 'ya'ya, jikoki da ma 'ya'yan jikoki. Dama haka rayuwar take babu wanda zai tsira daga jarrabawar Allah, sai dai na wani ya banbanta da na wani. Bayan sun keɓe da Mahirah ne ta tambayeta ko tanada hoton Hansa'u a wayarta. Mahirah tace baza a rasa ba cikin hotunan da ta ɗauke su ita da Junior lokacin tana gidan. Ta jima tana duba wayarta kafin ta samo hoto ɗaya da Junior ya musu selfie. Fiskar Hansa'u na karkace amma dai duk wanda ya santa zai iya ganeta. Asiya ta tura hoton a wayarta sannan ta musu sallama ta tafi. A cikin mota ta turawa Fou'ad hoton tana addu'ar Allah yasa ya binciko mata agent RBK da gaggawa. Lokacin data isa gida ɗakin Sumayya ta fara wucewa, ta samu Summayar ta dawo tana sallah. Ta wuce nata ɗakin dan a gajiye take. Bayan ta gama sallar Isha ta kwanta tana tunanin abinda ya dace ta yi a wannan lokaci. Idan ta yi gaggawan yanke hukunci akan Bilkisu zata iya rasa bakin zaren da take son warwarewa, dan haka dole tabi komai a nitse sannan tayi shiru da bakinta har zuwa lokacin da zata san duka gaskiyar. *** Cikin kwana biyun da Asiya tayi kafin Gwamna ya dawo ta yi su ne cikin takatsantsan da kuma shirye-shiryen wani ƙudurinta da take son aiwatarwa idan Gwamna ya dawo. A rana ta uku da take tunanin dawowan Gwamna har dare shiru babu ɗuriyarsa. Tsoron zaƙewa take shiyasa ta kasa kira ko ta masa text ta ji ko lafiya bai dawo ba. Besides da yamma ta shiga kitchen ta ga ana ta kan shirye-shirye wai Bilkisu ce ta bada umurnin girkin da za ayi saboda Gwamna na hanya. Haushi ya sa ta koma ba tareda ta yi abinda tayi niyya ba. Kenan bai damu da ita ba, har zai sanar da Bilkisu dawowarsa amma bai tuntuɓeta ya gaya mata ba. Haushi ya cika mata ciki ta kasa cin abincin dare. Tana kwance kan gado duk bata jin daɗi, ga haushin Gwamna ga baƙon wata da ke yi mata sallama. Junior ya shigo wai ta masa labari. "Junior bana jin daɗi ka bari gobe zan maka" "No, jiya ma baki min ba" Ganin ba haƙura zai yi ba yasa ta miƙe tace su je ɗakinsa. "Wani labari zan yi" "CY and the monkey" "Ikon Allah. Idan CY ya kamaka kana masa dariya zaka gayawa 'yan garinku" Junior ya fara dariya tun ma bata faɗi labarin ba. Tun ranan da ta bashi labarin indai ya tuno sai yayi dariya, kuma kowanni lokaci zata bada labarin sai ya ji kaman yanzu ne farkon jin labarin a bakinta. Da ke a gajiye take, a gurguje zata bashi labarin ta huta da rigimarsa. "Akwai wani abokina ana ce masa CY amma asalin sunansa Clement Yohannah. Watarana ni da shi muka je gidan zoo ɗaukan rahoto saboda tsohon Zakin gidan zoo ɗin ya mutu. Da muka gama naɗan rahoto sai muka fara yawon buɗe ido a cikin zoo ɗin. Muka haɗu da wasu 'ya'yan birrai suna wasa. CY ya ɗau camera yaje wajensu ya fara ɗaukansu a hoto. Da ya matsa kusa da su sai suka watse sai guda ɗaya. CY ya shiga ɗaukanta tana rawa, ƙarshe data gudu sai ya bita. Ina kiran CY akan ya haƙura da Birran nan ya zo mu tafi amma yai kunnen ƙashi. CY ya bi Birrai har wajen duwatsu. Yana saƙale da camera a wuyansa ya riƙeta yana shirin ɗaukan wani Biri sai wancan Biri mai rawan nan ta zo bayan CY ta zabga masa bulala a wuya. CY ya riƙe kunne ya juyo da sauri ya ga daga ina aka dake shi, bai gama juyawa ba aka sake zuba masa bulala a tsakiyar kai. CY ya saka ihu ya fara gudu yana kiran 'Jesus my head ooo. I don die ooo' ai kuwa Birrai kusan biyar suka biyo CY da gudu dukkansu da bulala a hannunsu. CY ya yar da camera, ya yar da takalmi ya cigaba da ihu yana kiran 'i don die oo' Har muka koma gida CY bai san inda kansa yake ba, da an taɓa shi zai fara 'i don die oo' kafin a kai gida kan CY ya kumbura suntun" Tun kafin ta kawo nan Junior ya ke dariya. Itama dariyan ta fara, saboda tunowa da tayi wannan ne silar shaƙuwarsu da CY dan lokacin bata jima da fara bautar ƙasa a tashar Hill TV ba. Gwamna da ke tsaye bakin ƙofa ya tako har bakin gadon. Ƙanshin turarensa da Asiya ta ji yasa ta tsaida dariyan, bugun zuciyarta ya ƙaru. "Daddy" Junior ya faɗa yai tsalle ya faɗa jikin Gwamna. "My boy ya kake?" "I'm fine Daddy" Asiya bata ɗaga ido ta kalleshi ba saboda tsoron haɗa ido take da shi. Dai dai kunnenta ta ji yace " ki faɗawa Junior gaskiya, ba CY kaɗai aka zane ba, mai bada labarin ma an taɓa lafiyarta" A fusace ta juyo tace "waya gaya ma..." bakinta ya kafe lokacin da ya kissing goshinta. "Anty Asiya da gaske kema Monkey ya dake ki?" Junior ya faɗa dan ya ji abinda Gwamna ya faɗa. Da ƙyar Asiya ta iya haɗa kalmomin bakinta tace " a'a Junior, CY kaɗai aka zane" Miƙewa ta yi ta yiwa Junior good night sannan tayi hanyar ƙofa da sauri, bata kai ƙofar ba aka riƙo hannunta. Zuciyarta yai wani tsalle lokacin da Gwamna Saifuddeen ya mannata da ƙirjinsa ya rungumeta da kyau yana faɗin "Asya ko sannu da zuwa ba zan samu ba" Duk ƙoƙarinta na son yin magana ta kasa saboda duk abinda ya taho a maƙoƙoro yake tsayawa. "Fatan na same ku lafiya?" ya faɗa bayan ya rabata da jikinsa amma bai sake mata hannu ba. "Wanda kake son samun su lafiya suna nan lafiya, sun ma shirya maka liyafar dawowa" Tayi ƙoƙarin raba hannunsu amma ta kasa. "Nan da kwana biyu zaki iya shirya mini taki liyafar saboda kema na same ki lafiya" ya ƙarisa maganar yana murmushi. Ganin ya sake mata hannu yasa ta tura baki ta fice daga ɗakin tareda banko musu ƙofa. Har ga Allah ta ɗauka zai biyota ɗaki amma har bacci ya ɗauketa bata ji ɗuriyarsa ba. Bayan Gwamna ya bar ɗakin Junior kuma, sashensa ya wuce inda Bilkisu ke jiransa. "Darling akwai improvement sosai a Kamfen namu. Duk anguwar daka shiga posters ɗinmu suka fi yawa and..." "Tun ban zauna ba Bilkisu" "Sorry Darling, kayi wanka ka fito, na shirya maka special dishes" "Cook ya shirya special dishes" "Da izini na ba, kaga kaman ni na yi kenan" Ya girgiza kai ya wuce ɗaki bayan ya manna mata kiss a kumatu. A gajiye yake dan haka baya son dogon musu... *Afuwan Dan Allah. School activities ne ya riƙe ni* 14 Washegari ya kama Asabat dan haka Gwamna ba zai fita da wuri ba saboda yana son hutawa. Ƙarfe tara na safe ya kira numbar Sumayya yace ta same shi a falonsa, tun ranan ya sa Asiya ta mayar mata da wayarta. A ƙasa ta zauna tana duƙunƙune kai dan tun ranan da ya ƙwaceta a hannun Asiya take fargaban haɗuwarsu, saboda bata san mi zai ce mata ba. "Ya karatu" ya tambaya saboda ta sake jiki da shi. "Alhamdulillah" ta amsa murya ƙasa-ƙasa. Tambayoyi ya fara mata gameda karatunta da kuma burinta idan ta ƙare karatun. Wannan yasa ta ɗan saki jiki da shi. Chan sai ya sako mata tambayar da take tsoro "Alhaji Abdullahi ya tura wajen Baba ne?" Ta yi shiru tana rarraba idanu. "Sumayyah?" "Na'am" ta faɗa ciki ciki. "Alhaji Abdullahi ya nemi izini a wajen Baban ki ne? Ko dai a Bello yai wa magana?" Ta girgiza kai tana ji kaman ta nitse cikin rug saboda kunya. "A bisa yadda na sani dai da ke da 'yaruwarki amana kuke a hannuna, kuma ni Abdullahi bai sameni akan maganar ki ba, shiyasa na tambaya ko ya wuce wajen Baba ne kai tsaye" Ya ɗan yi shiru yana nazarinta saboda ya lura maganganunsa ya fara tasiri akanta. "Idan Alhaji Abdullahi yana sonki Sumayya, wajena zai zo ya nemi izinin magana da ke, wannan shi zai tabbatar da cewa da gaske ne yana son ki, ba wai ya dinga bin ki a waya yana cewa ki turo masa hotunan ki ba" Maganarsa ta karshe tai wa Sumayya ba zata, har take ganin inama tana da layar ɓata ta ɓace ɓat a wajen. Ya shiga mata nasiha kan rashin dacewar abinda ta aikata, daga ƙarshe yace "Daga yanzu duk lokacin daya kira ki. Kice masa ya nemi izinin magana da iyayenki kin ji" Sumayya ta gyaɗa kai idanunta cike da ƙwalla. *** Asiya tana zaune gaban mirror tana shafa powder Gwamna ya shigo ɗakin da sallama. Ba tareda ta san dalili ba sai kawai ta haɗe rai. Ta yi kaman bata ganshi ba, nan kuwa har zuciyarta ya fara bugawa da ƙarfi-ƙarfi. " Madam barka da safiya" ta haɗe rai ta cize leɓe tana jin haushin kiranta Madam da yai. Madam kuma? Wa yaga irin tsohuwar nan. Ya ɗan rankwafo daidai kunnenta yace "Jiya kika gudu ba tareda mun yi sallama ba" Dama a cike take da shi, sai ta juyo a fusace tace " ina ruw..." komai ya tsaya chak saboda haɗe bakinsu da yai, koma minene take son faɗa ya ƙare, dan har lokacin da ya raba bakinsu bata dawo dai-dai ba. Idonta a rufe, hannunta na rawa, hanjin cikinta sun cunkushe, ƙirjinta na bugawa kaman tayi gasan tsere, sannan ba zata iya cewa ga inda kanta yake ba dan kamar a kan iska ma take yawo. Gwamna ya shafa kumatunta yace "zan fita. Na yiwa Sumayyah magana kuma nace ta baki haƙuri. Dan Allah banda duka banda tsawa, ki mata nasiha a hankali, hakan zai sa ta gane da wuri" Ya sa hannu ya riƙo hannunta biyu da suke kan cinyarta, ya lura da yadda hannunta ke rawa, hakan yasa shi kissing kowanni hannu yace "lallen hannunki yayi kyau" Asiya ta haɗiyi yawu maƙwot, tana jin wani abu na yawo a duk ilahirin jikinta. "Zan je Kachallah House. Dadda tace kin kai mata ziyara, nagode da kulawa" Ya sake kissing hannun yace "gobe ina jiran taki liyafar" Ya hura mata iska akunne saura kaɗan Asiya ta shiɗe dan abin ya zo mata bazata. "Na tafi" Sai da ta ji ƙaran rufe ƙofa kafin ta sauke nannauyan ajiyar zuciya ta dafe ƙirjinta dan ta tabbatar zuciyarta bai bulloƙo waje ba. "Na shiga uku ni Asiya" ta yi maganar tana hura iska waje saboda ta samu sauƙin cunkushewar da ƙirjinta yai. Ba ta gane wannan sabon salo na Gwamna ba. Bata ma gane ya aka yi duk wani abu da ya mata yake tasiri akanta ba. Da ta ɗan samu nitsuwa sai ta kalli kanta a madubi. Ta yi saurin sa hannu ta taɓa laɓɓanta saboda ta tabbatar suna nan lafiya lau. "Na shiga uku, ko dai wani abu ya saka min ne?" Ji tayi lips ɗin na mata daɗi domin har lokacin akwai sanyin lips ɗinsa akan nata. It was a brief kiss amma har yanzu effect ɗin na jikinta... Bayan awa ɗaya da tafiyar Gwamna Sumayya ta shigo ɗakin Asiya. Ƙasan idanunta sun kumbura, farin idon kuma yayi ja. Asiya na aiki da laptop ɗinta amma gaba ɗaya hankalinta ya kasu kashi biyu. Ɗaya yana ga aikin da take tsarawa, ɗayan kuma yana ga abinda ya faru awa ɗaya daya wuce. "Anty Asiya kiyi haƙuri Dan Allah" Ta sake maimaita maganar ganin Asiya bata juyo ba, balle ta amsa mata. "Allah ba zan sake ba, kiyi haƙuri. Allah ban san ya akayi na tura masa hoton ba" Sai a lokacin Asiya ta juyo tace " ni nasan ya akayi ai. Ya ce miki yana son nono irin naki 'yan ƙanana masu daɗin taɓawa, ki tura masa ya gani ga rage zafi tunda kince ba za ki bar shi ya taɓa ba" Ta sani Asiya akwai saurin riƙe abu, amma bata yi tunanin har ta haddace chats ɗinsu data karanta ba. "Da kika ce ba za ki barshi ya taɓa ba, mi ya hana kice masa ba zaki tura ba saboda da taɓawan da turawan duk sammakal. Miyasa kika ji tausayinsa da ya ce miki 'plz my Sumy, ki taimakawa Bawan Allah' ke daƙiƙiyace za ki tausaya masa bayan yana da mata uku a gida kuma kowacce tana da nonon daya halatta masa ya gani ya taɓa?. I'm dissappointed in you Sumayya, har anyi namijin da zai haɗani da ke." Jin ta fara ɗaga muryarta yasa ta tuna maganar Gwamna sai ta sassauta murya tace " to yanzu dai ɗaya daga cikin matansa ta ga hoton a wayarsa kuma tace za ta wallafa hoton da chats ɗinku a duniya kowa ya gani" "Na shiga uku Dan Allah Anty ki bata haƙuri. Wallahi ba zan sake ba" "Ina ruwana, yanzu ma data min maganar cewa nayi ta yi duk abinda ta ga ya dace ƙanwata tace babban mutum take so" Da gaske Sumayya ta tsorata ta riƙe ƙafar Asiya tana kuka tana bata haƙuri. Asiya ta haɗe rai kamar abinda ta faɗa gaskiya ne. "Ki shirya auren Alhaji Abdullahi dan na yiwa Ale magana, kin san dama Ale da ya ga mai kuɗi jikinsa ke rawa. Idan kin je kuma ku fafata da matan gidansa" Da ta ga kukan nata yayi yawa sai ta yi gyaran murya tace " Zan ce kada ta yaɗa hoton. Idan kika cigaba da mu'amala da mijinsu kuma ruwanki. Tashi ki bani waje" Sumayya ta miƙe sumi sumi ta bar ɗakin. Asiya ta jinjina kai, rayuwa kenan. Ko a mafarki bata taɓa tunanin akwai ranan da zasu zauna suyi irin wannan magana ba. Lokacin da ta ke kamarta ina ma take da lokacin tunanin irin waɗannan abubuwa. She's so occupied da karatu da kuma sana'a, bata da lokacin mummunan tunani irin wannan, sannan soyayyarsu da Ubayd tsabtacacciya ce. They were so sure za su yi aure shiyasa suka nisanci duk wani abinda zai jawo su aikata wani abu da bai dace ba. Ta sake taɓa leɓenta tana tuna lokacin da take gayawa Gwamna cewa gangan jikinta da ruhinta duk na Ubayd ne. Lokaci guda kuma ta tuno amsar daya bata. *"Ki faɗi koma minene, hakan ba zai chanja cewa daga yau gangar jikin, zuciyar da ruhin duka Allah ya mallaka min ba"* *** Bayan Gwamna ya bar wajen Alhaji Sani Office ya wuce saboda suna da wani meeting ƙarfe huɗu na yamma da za ayi da wasu Dakacin wasu ƙauyuka biyu da suke rikicin fili tsakaninsu. Da ke yana cikin farin ciki, kafin ya shiga meeting ɗin ya rubuta ƙaramar poem ya tura a blog na shi. Ya san zata gani, dan ranan da tayi comment akan waƙarsa ta Attaruhu , ranan ne ya gane ko wacece fan ɗinsa mai amfani da suna *SeeyaShahidah* ta sha tura masa message ta email tana son haɗuwa da shi, dan a tunaninta kamar kowa macece marubuciyar. Ai kuwa yana ɗaurawa ko minti biyar bai kai ba Asiya ta gani, dama ta jona wifi na gidan tana aiki da wayarta dan haka tana ganin notification daga www.kasasapoems.com ta yi saurin buɗewa. Sai da ta karanta waƙar sau uku tana nazarin ma'anar waƙar wanda yai kama da yanayin da ta shiga lokacin da Gwamna ya kissing ɗinta. "Allah kaɗai ya san wacece KaSaSan nan. She's a good poet amma ko mi yasa take ɓoye kanta oho" Asiya ta furta a fili. Gaba ɗaya ranan wasan ɓuya Asiya ta yi da Gwamna dan bata bari sun haɗu ba kwata-kwata, ɗakinta ma kullewa tayi saboda kar ya mata shigowar bazata irin wadda yai da safe. Washegari Sunday bata san da yaushe ya fita ba, hakanan kamar tare suka fita da Bilkisu. Sai da ta karya, kusan ƙarfe shabiyu na rana ya turo mata saƙo. "Na fita bamu gaisa ba, mijin Rufaidah ne Allah ya masa rasuwa yau da Asuba. Ba zan dawo ba sai dare" Rufaidah dai yayar Bilkisu Kachallah ce, idan haka ne ai dole ta je musu ta'aziyya, sai dai bata san ina ne gidan ta ba. Tura masa saƙo tayi masa ta'aziyya tareda tambayarsa tana son zuwa gaisuwa. Ya mata reply da cewa zai turawa Bello address ɗin sai ya kaita gidan da yamma dan a gidan iyayensa ake karɓar gaisuwa. Ƙarfe biyar Asiya ta shirya ta kira Sumayya da ke ƙunshe a ɗaki tun safe, tace ta zo ta rakata gidan rasuwa. Lokacin da suka je gidan ta ci sa'a ta ƙofar baya mata ke shiga dan maza sun cika gaban gidan. Niƙab ta sauke ta fito daga mota suka shige gidan. An cika gidan maƙil saboda mamacin shima wani ƙusan Jaha ne, ɗan babban gida ne kuma ta wajen Uwa yanada haɗi da familyn Kachallah. Asiya ta isar da ta'aziyyarta ga iyalen mamaci, ta ɗan zauna kaman na minti goma shabiyar sannan ta tafi. Ta haɗu da yayye da ƙannen Bilkisu a wajen amma bata ga Bilkisun ba... *** *"mace bata juya mace. Musamman wanda taurarinsu ke da ƙarfi. Dan haka dole maza uku kawai za ki iya juyawa. Idan mace ta taɓa zoben gaba ɗaya aikin zai warware"* Matar da aka yiwa kashedin nan ta tuno da kashedin da aka mata lokacin da aka bata zoben nan. Gashi mutum biyu da take son juyawa sun taɓa zoben amma zuwanta gidan rasuwa ya sa aikin da aka mata a zoben ya warware. Da ta sani da bata je gidan rasuwan nan ba sai data cika dukka sharuɗɗan Shri Hari Bansari. Kafin zoben nan ya isota daga ƙasar India kusan sati shida kenan. Ta kira wanda ya haɗata da Shri amma yace ana cikin ranaku masu mahimmanci a lissafin taurari dan haka Shri baya magana da kowa yanzu har sai kwanakin nan sun wuce tukunna. Tanada tabbacin zata samu cikar burinta da zaran ta iya juya waɗannan mutane uku. Ta furzar da iska mai zafi tana tunanin sai yaushe ne zata samu cikar burinta?... *** Da dare Asiya ta jira isowar Gwamna amma shiru har shaɗaya hakan ya sa ta kwanta duk da kuwa akwai maganar da take so suyi koda kuwa tana kunyar haɗuwar ta su. Washegari da sassafe ta shiga sashen Gwamna ta wuce ɗakinsa saboda ta ji fitarsa sallar Asuba. Gyara masa ɗakinsa ta yi sannan ta fito, ganin Safiyya ta fara gyara falon na shi sai ta haƙura ta sauka ƙasa dan ta je ta haɗa masa abin karyawa. Cook ɗin gidan ta lura kaman ma kishi yake da ita, dan duk lokacin da tace za ta yiwa Gwamna girki sai ta ga yana tsumewa. Lokacin da ta gama komai Safiyya ta tayata ɗaukowa, suka shirya komai a dining ɗin falonsa. Daga inda take shirya plate ta jiyo muryan Bilkisu tana magana sama-sama. "Ban gane daga yanzu kwana bibbiyu zaka dinga yiwa kowa ba. Don't tell me ka fara kwana da ita. Magana nake maka Saifuddeen, did you sleep with her?" Bata jin maganar Saifuddeen saboda a hankali yake tasa maganar. "You told me you married her for political reason. Kace da zaran komai ya lafa zaka rabu da ita. Miya kawo maganar haƙƙi kuma yanzu?, answer me... answer me" Kaman zata bar wajen jin an buɗe ƙofa sai kuma ta tsaya dan dole ne ayita da wajewa. Kalaman Bilkisu sun kaɗata amma yanzu ba da bane, dole ne ta ji daga bakin shi kansa Saifuddeen ɗin kafin ta zartar da hukunci. "Asya" Ya kira da sigar mamaki dan bai tsammanci ganinta a wajen ba. "Saifud..." Bilkisu ta yi shiru ganin Asiya a wajen. Wani abu ne ya ɗarsu mata a zuciya lokacin da suka haɗa ido da Asiya. Kamar yadda Tsu Zhang ya faɗa, Shri Hari Bansari ma ya sake jaddada mata cewa matuƙar Asiya ta rabu da Saifuddeen to ba zai ci zaɓe ba, sannan ba zai sake yin kowanni irin mulki ba. Dan wannan ne kaɗai ta ke daurewa da kasancewar Asiya a matsayin Matar Saifuddeen, koma minene yarinyar ke da shi ba zata taɓa bari yai tasiri a jikin Saifuddeen ba, saboda kar a samu matsala idan ya shimfiɗa sabon Gwamnatinsa. Ganin irin kallon da Bilkisu ke mata yasa Asiya ta matsa gefen Gwamna ta sa hannunta cikin nashi tace "Maman Nana an tashi lafiya?" "Maman Nana?. How dare you insult me" "Insult you? How? baki da 'ya mai suna Nana ne?" A wajen Dadda ta ji gulman wai Bilkisu bata so a kirata da Maman wane ko Maman wace saboda hakan na nuna tsufan mutum. Bilkisu ta kalli Asiya sannan ta maida dubanta ga Gwamna tace " ina nan ina jiranka" Bayan fitar Bilkisu Asiya tayi ƙoƙarin cire hannunta cikin na Gwamna amma sai ya riƙe gamgam yana faɗin " not so fast" Ta sunkuyar da kai tana jin kunyar abinda ta aikata. Bai sake hannunta ba har sai da ya zauna a kan kujera yace "na makara, amma zan ci koda kaɗan ne" A gurguje ta zuba masa farar shinkafa da kuma farfesun kaza ta haɗa masa da fresh apple and pineapple juice data haɗa. Yana cikin ci ya riƙo hannunta yace "naga saƙon ki jiya, kiyi haƙuri meeting ne ya riƙe ni shiyasa ban dawo da wuri ba. Mi kike buƙata?" "Kana sauri ai, zamu yi maganar idan ka dawo?" Ya ajiye sokali yace "ba abinda ya fi sauraron buƙatar ki mahimmanci yanzu, anything else can wait" Wani murmushin jin daɗi ne ya kuɓuce mata. Saboda bata tsammanci zai saurareta ba. Da ƙyar ta iya haɗa kalmomin bakinta saboda har lokacin hannunta ɗaya na cikin nashi. Sannan bata san mi zai ce ba idan ya ji buƙatar tata. "Minene?" Asiya ta ja dogon numfashi sannan tace " ina so na maka kamfen" Cike da mamaki yace "miyasa?, besides saura sati huɗu a rufe Kamfen ma" "Idan Bilkisu zata maka kamfen miyasa ni ba zan maka ba? Ko dai maganarta gaskiya ne, you married me ONLY for political reason?" Ta ƙarfafa kalmar only ɗin saboda da gaske tana son sanin ko shi kaɗai ne dalilin. Maimakon ya bata amsa sai yace "zan yi magana da Bello, za a haɗaki da securities naki sannan Dan Allah ki kula da kanki" Miƙewa yai zai tafi tace "Dan Allah ka ƙarasa abincin" Juice ɗin kawai ya kurɓa ya wuce ya barta a wajen... 15   Not edited. Ƙarfe biyu na rana Queen Bee ta shigo wajen Asiya. "Kai! ƙawalli irin wannan tsaro. Kin san sai dana nuna musu hoton da muka ɗauka dake ranan dinner. God! Mulki akwai daɗi, yanzu ni da bestie ɗina sai an yi bincike kafin a barni na shigo na ganki" "Yi haƙuri, ban san zaki zo ba dana sa an musu magana" Asiya ta faɗa tana miƙa saboda bacci take aka kirata wai tayi baƙuwa. Queen Bee ta tsaya kallonta har da taɓe baki. "What!" Asiya ta faɗa tana riƙe ƙugu. "Shahidah tell me the truth ciki gareki ko?" "Ungo naki Bahijjah, ke kika min cikin ai" "Seriously bestie kin yi ƙiba. Yaushe ne n aganki a Asibiti kaman skeleton amma gashi yanzu kin cicciko ta ko'ina. Kin ga wuyar ki kuwa?" Asiya ta sa hannu ta fara shafa wuya tana faɗin Allah bata yi ƙiba ba. Bayan sun nitsu, aka kawowa Queen Bee abin taɓawa ta buɗe ciki ta fara cin pepper chicken da aka kawo mata da kuma cupcake sai Berryblast 5alive. "Zan shirya kamfen wannan saturday, ina buƙatar taimakon ki" Queen Bee ta fara gyaran murya tana tarin shaƙiyanci. "Bana son iyashege. Faɗi son ranki bana son kame kame" "Allah! Allah!. Bari dai nayi shiru. Kai wannan abu da mamaki yake. From --- ni ban san mi kuka gani ajikin wannan tsohon ba. Allah ya sawwaƙa na crushing ɗinsa. Uban wa ya isa ya haɗa shi da My Ubayd..." Asiya ta wurga mata filo tana faɗin "Bahijja kinci gidanku" Queen Bee ta fara dariya tana faɗin "ina son irin wannan soyayya" Sai da ta ga Asiya ta ɓata rai kafin ta dena tsokalarta. Suna zaune Sumayya ta zo ta wuce su bayan ta gaishe da Queen Bee a tsaitsaye. "Yaushe Sumayya ta dawo haka?" "Mi kika gani?" "Mi na gani? Da haka take yi idan ta shigo? Tukunna ma shiga jami'ar ne ya sata chanja shiga, baki ganin a kafaɗa ta lanƙaya gyalenta ne?" "Hmmm. Kin san dai ko kai ka haifi ɗa sai dai ka tsawatar masa sannan ka masa addu'a ko?. To ni dai yanzu sai addu'a dan idan nace zan yi magana raina ne kawai zai ɓaci" A hankali ta warware mata yadda komai ya faro da kuma matsayin da suke yanzu. Queen Bee ta taɓe baki tana jimamin wannan batu, daga ƙarshe itama ta bata labarin wata 'yar yayarta da ta falle kwanan baya, ƙarshe ma taje haɗuwa da wani saurayinta ne babban yayansu ya hangota ta shige gidan ya bi bayanta, ya mata shegen duka ya tiso ta gida. "Ban faɗawa Yaya Bello ba saboda na san dukan kawo wuƙa zai mata. Kuma Excellency yace na bita a hankali" "Ehm ehm, Excellency manya" Asiya ta watsa mata harara... Da dare Asiya ta shiga ɗakin Gwamna ta tabbatar komai tsaf-tsaf kafin ta fito ta zauna a falonsa tana jiran dawowar sa. Ƙarshe da ya zo ma falon baƙi ya wuce bai ƙaraso personal sitting room nashi ba saboda yana tareda wasu manyan mutane da zasu yi meeting na gaggawa tareda su. Lokacin da ya gama da su ƙarfe ɗayan dare har ta gota. Ransa na matuƙar ɓace saboda duk zaman da suka yi jayyaya ne kan wasu 'yan china dake son buɗe kamfanin ƙere-ƙere a jahar. Tun yana mataimakin Gwamna ya kawo shawaran kada a bari baƙi daga wata ƙasa su sake buɗe babban kamfani a jahar. Yana so ya haɗa hannu da wasu manya su buɗe kamfanin ƙere-ƙere saboda mutanen jahar Congo zasu fi amfanuwa da shi. Kamfanin da ke titi ya kamata ya zamo mallakin jahar Congo ba na wasu bare ba. Yayi mamaki da ya ga Asiya kwance kan gadonsa tana barci. Like, bai tsammanci hakan ba. Ganinta da yai sai ya sassauta masa zuciya. Ya cire kayansa ya shiga banɗaki yai wanka tareda alwala ya fito ya shirya cikin kayan bacci sannan ya kwanta ɗaya gefen. Chan kuma ya kasa haƙuri ya gangaro inda take kwance ya rungumota jikinsa tareda kissing kanta da kuma wuyanta. Yai addu'a ya kwanta. Asiya ce ta fara tashi saboda alarm ɗinta na ƙarfe huɗu da rabi da yai ƙara. hannunsa ɗaya yana ƙirjinta, ɗayan kuma yana kanta. Anya shawaran da ta ɗaukawa kanta shi zai fishsheta kuwa? Ta fara ƙoƙarin cire hannunsa a ƙirjinta dan ta samu ta bar gadon amma sai ta ji ya sake mannata jikinsa yana faɗin "sleep" Ta yi shiru tana ƙyafƙyafta ido a cikin duhu ƙirjinta yana bugawa da ƙarfi ƙarfi. Kusan minti biyar ta sake yunƙurin barin gadon nan ma aka sake jawota baya. "Sal Sallah zan yi" ta faɗa da dasashahiyar muryar bacci. "Please stay a few minutes" Ta yi shiru tana sauraron bugun zuciyoyinsu da kusan a tare yake bugawa. Kusan minti uku suna haka sai ta ji yace "kada ki tursasawa kanki abinda ba kya so. Kada kiyi abinda zai jawo miki baƙin jini a gurin jama'a. Bilkisu a gidan da ake siyasa ta taso, she has it in her. Duk abinda take yi tana yi ne saboda tana son yi, she's inlove with politics tun kafin muyi aure. Background ɗin ki aikin jarida ne, kada ki sa kanki cikin abinda baki da masaniya akai" Asiya tayi shiru tana nazarin kalamansa. "Asya siyasa akwai ruɗu acikinta" "Ba ka so na shiga harkar siyasa saboda inada ƙayyadadden lokaci a wajenka?" "I want to protect you" "Allah protects me. Duk abinda zai same ni yana cikin ƙaddarata ne" "Akwai abubuwa dayawa da baki sani ba Asya. Zai fi kuma idan baki san su ba" Ta jaa dogon numfashi saboda abinda take son faɗa yana da nauyi. "Kafin Umma ta rasu tace bata yafe ba idan na kashe aure na" Ta yi shiru tana tunanin yadda zata faɗi sauran maganar ba tareda ya mata wani fahimta ba. "Zaki zauna dani ne saboda Ummanki?" Ya katse shirun na su. Ƙila da suna fuskantar juna da bazata iya faɗin abinda tayi niyya ba, amma akwai duhu, sannan ta bashi baya ne. "I want to help my husband... zan zauna da kai saboda na samu albarkar aure" Ya gane sarai mi take nufi amma sai yace "albarkar aure fa haihuwa kenan" Da sauri ta tureshi ta bar gadon saboda ya sassauta riƙon da ya mata. Kunna wutan ɗakin yai, hakan ya sa ta gane hanyar banɗaki tayi ba ƙofar fita ba. "A banɗaki za a fara neman albarkar ne?" Ta sa hannu biyu ta toshe kunnenta sannan ta fice daga ɗakin da sauri. Gwamna Saifuddeen yai murmushi mai sauti. Soyayya takan iya shiga mutum sannu a hankali, kamar soyayyar sa da Misturah. Akwai kuma soyayyar da take iya shigar mutum farat ɗaya, sannan ta dabaibaye zuciyar mutum ta hana shi sakat. Soyayyar Asiya ta masa shigar kwab ɗaya ne. Kamar da wasa ya dinga tunaninta a lokutan da bai shirya ba. Kafin wannan rana da murmushinsa ya zamo silar buɗewar wani babi daya jima da rufewa a zuciyarsa. Ya san 'yar jarida Asiya Shahidah Faruƙ Baba saboda muryarta da ya zamo shaidarta a duk lokacin da take bada rahoto. Bai taɓa ƙare mata kallo ba, sai wannan rana mai tarihi. A wani ɗakin taro yake zaune shi ɗaya yana huci saboda shirmen da aka gabatar masa ya sa shi koran duk wanda yake zaune a ɗakin taron. Tunanin mi ya kai shi harkan siyasa yake bayan mutanen da suke zagaye da shi kusan kaf ɗinsu Aljihunsu suka sani ba wai yadda za a inganta rayuwar talaka ba balle har a kawo cigaba mai amfani wa Jahar ta su. Gilashin daya zagaye ɗakin taron mai duhu ne, na ciki zai iya kallon na waje amma kuma na waje ba zai iya kallon na waje ba. Tafiya take ita da wani saurayi wanda yanzu ne ya fahimci saurayin lokacin CY ne. *"Yanzu sai ace dan ganin Gwamna na yi kwalliya. Mima ya kaini saka jambaki... mtsww"* Ta ciro hankerchief a jakarta ta shiga goge bakinta, sai data gama gogewa ta shiga tura baki, ta turoshi gaba, ta baje shi, ta ƙumbushe shi, duk dan ta saita bakin nata. Ganinta a wajen ya sashi yin murmushi, ƙila da ta san ana kallonta da baza ta yi wannan shirmen ba. *"Aseey lets go now"* CY ya faɗa da ɗan ƙarfi. Ranan suka fara zuwa neman izinin interview da Gwamna. Wannan murmushi shine mafarin komai. A rannan haka ya wuni da nishaɗi, duk lokacin daya tuno da 'yar jarida Asiya sai ya ɗan murmusa. *** Kwanaki biyun Asiya tayi su ne cikin sassauta zuciyarta ga mijinta. Ba za ta ce tana son shi ba, amma tunda ta shirya gyara aurenta dole ta yi duk abinda ya dace dan ganin bata yi wasa da damar ta ba. A rana ta biyu da ta saka filo a tsakiyar gadonsu Gwamna ya faɗa mata maganar da ya sata kunya sannan ya sata tunanin anya bata ƙwaran wannan bawan Allah. "Ki kwantar da hankalinki, ba gangan jikin nake so ba. Duk lokacin da zuciyar ki ta buga saboda Saifuddeen ke da kanki zaki cire waɗannan" ya ƙarisa maganar yana nuna pillow data jera... Duk shirye-shiryen da ake Bilkisu Kachallah bata san Asiya zata yi Kamfen ba. In fact ranan Asabat da sassafe ta fita saboda akwai wani sabon kayansu da aka shigo da shi saboda zaɓe. Ƙarfe takwas Asiya da tawagarta suka fita zuwa wajen taron da suka shirya. Queen Bee, Halima Kachallah, Mahirah SSK, Sa'ad SSK, Nawwarah Isa Kachallah sune suka takawa Asiya baya. Yayinda Yaya Bello ya zamo Chief security na Asiya, yayinda CY ya zamo Campaign Director. Taro ne na manyan mata, matan talakawa har ma da nakasassu. *** "Wannan da kike gani, idan mutum ya sha ɗayan sa zata kai shi awa ashirin da huɗu bai nemi komai ba. Wannan na wanda zasu kasa su tsare akwatunan zaɓe kenan" "Ya za ayi a raba musu kenan? Ba tareda sun san cewa da wannan manufar za a basu ba?" "Inaga a fara saida shi a farashi mai rahusa. Idan lokacin ya zo sai a basu shi kyauta, bayan zaɓe komai ya lafa sai a siyar da shi a farashi mai tsada saboda lokacin jininsu ya saba da shi, idan ba su samu ba ba za su taɓa jin daɗi ba" "Ka tabbata kuɗinmu zai fito?" "Sosai ma Excellency" "Shikenan" Wayar Bilkisu yai ƙara. Ganin Madam Bintu ya sa ta sallami manager ɗinta. "Hello" "Bilkisu kina ina, Asiya ta fara kamfen?" "Kamfen kuma?" "Ki kunna TV ki ganta da idon ki" Bilkisu hannu na rawa ta chanja tashar tv dake ofishinta zuwa tashar Congo News. Asiya na tsaye jikin podium ta yafa gyalen tutar jam'iyya, tana sanye da dogon riga shadda da ya sha aikin hannu kalalolin tutar jam'iyya. Babu kwalliya na azo a gani a fiskarta amma tayi kyau na ɗaukan hankali. "Ba za mu yi alkawarin kawo chanji ba, saboda ba abinda zamu iya chanjawa a wannan jaha. Ni da ku dama waɗanda suke gida mun san mi ya kamata mu yi jahar Congo ta samu cigaba, ta samu haɓakar arziƙi. Dan haka muna muku alƙawarin Insha Allahu Gwamnatin Saifuddeen Kachallah zata haɗa hannu da ku saboda mu taru mu gyara jahar mu mai albarka..." Idon Bilkisu ya hango Junior da ke tsaye gefen Asiya yana wasa da bindiga. Kamar haɗin baki kuma sai aka hasko matan dake zaune gaba gaba inda ta ga ƙanwarta da kuma 'yarta Mahirah. Ta taɓa zuwa Kamfen da Mahirah amma Halima Kachallah cin amanar da zata mata kenan. Ganin an hasko mutane suna ihu kiran sunan Asiya ya sa Bilkisu Kachallah ta buga teburin gabanta da ƙarfi. Wani zuciyarta na faɗin "ba zan taɓa bari ta fini haske ba" A ɓangaren Yallaɓai da Alhaji Sani Kachallah duk sun saurari speech ɗin Asiya. "She's a very good political orator" Yallaɓai ya faɗa yana shafa gemu. "She's eloquent" Alhaji Sani ya faɗa bayan ya gama ganin speech ɗin. A ɓangaren Umaru Kwom ma ya ga speech ɗin hakan kuma ga sanyaya masa jiki, musamman daya tuno kalaman Asiya a waya. Ubayd da ke zaune a office kuwa ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin gaskiya ne da aka ce tsakanin miji da mata sai Allah. Kwanan baya a wannan office ɗin ta ke iƙirarin zata tarwatsa shi, yanzu kima gata tana faɗin tana tareda mijinta ɗari bisa ɗari. It hurts, amma ya zai yi tunda Allah ya riga ya rubuta Asiya ta Saifuddeen ce... 16 Gwamna na office ɗinsa yana kallon talabijin wayarsa ta hau ƙara. Ya ɗau wayar. Daga ɓangaren Yallaɓai yace "da tun farko ita ka bari ta jagoranci tafiyarka. Mun samu ƙarin sponsors biyu dalilinta" "Don't bring her into this" Gwamna ya daka masa tsawa. "Don't underestimate her. Ka bata dama, zaka sha mamaki" "Kar ka..." Yallaɓai ya kashe waya ya bar Gwamna da baki buɗe. A dai dai lokacin kuma Bilkisu Kachallah ta shigo office ɗin kamar walƙiya. Kamfen ɗin Asiya ya girgizata matuƙa, sai da take tahowa ne a cikin mota sun zo dai dai wani round about ta lura da ƙaton bill board da ke ɗauke da hoton Asiga inda aka rubuta suna *first lady Asiya F B Kachallah* Tun da aka fara Kamfen bata taɓa ganin an saka poster na Asiya ba. Duk wani souvenirs da aka raba tun daga riguna, zannuwa, littattafai, memos, key holders, calenders, jakukkuna da sauransu. Hoton Saifuddeen ne ko na Bilkisu ko kuma nasu su biyu. Kafin a ƙaraso da ita sai da ta ga posters na Asiya guda shiga kuma kowanne an saka first lady kafin sunan. "I am the first lady. The only first lady" ta furta a fili. Irin kallon da take binsa da shi tun kafin ta ƙariso ya san babu lafiya ba. Miƙewa yai daga kan kujerarsa ya nufota. "Don't touch me" Tsabar sauri a office ɗinta ta bar gyalenta, ɗaurin ɗankwalin ma dai ya karkace kusan reto ma yake, ikon Allah ne yasa bai kai ƙasa ba har ta iso da shi a haka. "Let's sit please" ya faɗa yana nuna mata kujerun da ya ke zama ya karɓi baƙi. "Ban zo dan na zauna ba. Why did you allow her to campaign?. Miyasa baka gaya min ba?" "Ki zauna tukunna" yai maganar yana kamo hannunta. Bilkisu ta wafce hannun tace "ka amsa min tambayata" " Just like you, Asya is my wife. Ban ce ki min Campaign ba, kin yi ne a karan kan ki, itama kuma ban sata ba, ita da kanta ta zaɓi yi. Don't give me that face Bilkisu, kin sani sarai bana sa ido a harkan mutane" "I accepted your marriage to her only...only" sai ta yi shiru tana huci. Dole ne ta ƙara haƙuri na ɗan lokaci kaɗan. Abinda ya ke mai mahimmanci shine Saifuddeen ya ci zaɓe, it doesn't matter who campaigned. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kalleshi ido cikin ido tace "idan ka ci amanata ba zan yafe ba" Daga haka ta juya ta fice daga office ɗin fuuu kamar yadda ta taho. Gwamna Saifuddeen ya rakata da ido har sai da ta fice. Bai gane matsalar Bilkisu da Kamfen ɗin Asiya ba. Sai kuma ya tuna da abinda ake kira kishi... *** "Nagode Anty Halima. Allah ya saka da Alkhairi" Asiya ta faɗa tana murmushi. "Amin ba komai, yiwa kai ne. Bari mu wuce" Asiya har bakin mota ta raka Halima Kachallah kafin ta koma cikin gida. Tana fitowa daga wanka aka gaya mata akwai wasu mata dake son ganinta. A gurguje ta shirya ta fita. Wasu matan manya ne guda uku wanda suka halarci Kamfen ɗinta. Biyu daga ciki a da suna tare da Bilkisu Kachallah ne amma sun raba gari tun kafin Saifuddeen ya hau kujerar Gwamna. Yabo da jinjina ne ya kawosu tareda neman matsugunni a wajen Asiya. Suna zaune da Asiya, Bilkisu Kachallah ta dawo. Sai da ta bi su da kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ta bar wajen bayan ta ja dogon tsaki. Washegari gidan talabijin na Hill TV suka nemi hira da Asiya. MD da kansa ya bugo yana neman wannan alfarma hakan yasa Asiya ta amsa gayyatarsu. Da yamma ta je studio ɗinsu. Kowa jikinsa rawa yake ana ƙoƙarin burge matar Gwamna, musamman wanda a da basa shiri da Asiyar. Yadda sukeyi sai ya bawa Asiya dariya, watanni kaɗan baya ita ɗin ƙaramar ma'aikaciya ce a tashar amma auren Gwamna ya bata wani matsayi mai daraja cikin al'umma, Allah ya ɗaga ta, ta yiwa tsohin ma'aikatan fintinkau. Daren ranan, interview ɗin da aka yi da Asiya ya zamo abin kallo ga miliyoyin jama'a, a ciki da wajen jaha. Yayinda hankalin mutane ya karkata ga yadda ta iya sarrafa harshe, ta iya haɗa kalmomi su bada ma'ana sannan ka ji maganar na taɓa maka zuciya. A wani ɓangare kuma wasu suna yabon kyaun surar ta ne da kuma iya wankanta. Kan kace kwabo, posters na Asiya sun zagaye gari har ma yafi na Bilkisu Kachallah zagawa. Cikin abinda bai fi sati ɗaya ba sunan Asiya ya koma *Hasken Talakawa* is like mutane na ƙara son SSK ne saboda Asiya Kachallah. Duk inda ta je tana nuna cewa Talaka yana da mahimmanci kuma sai ya bada haɗin kai za a samu cigaba mai amfani. Yadda mutane ke ƙaunarta lokacin da take aikin jarida yanzu abin ya ninka haka. An manta da duk wani ƙarairayi da aka yi tayi a baya kafin aurenta da Gwamna. Abinda ake gani shine in har mace kamar Asiya na tareda Gwamna Saifuddeen to za a samu cigaba sosai a jahar. Asiya tana bayyana matsalolin da ake fuskanta a jahar da kuma yadda Gwamnatin Saifuddeen ta shirya magancesu bisa tsari, hakan ya sawa talakawa hope. Gwamna yayi mamakin yadda Asiya ta ke iya composing kanta ta bada speech mai ma'ana da kuma ɗaukan hankali. Bai sani ba ko dan ya mata gorin cewa ba a haifeta a gidan da ake siyasa bane, amma cikin kwanakin nan ta nuna masa cewa ta fi ma wacce ta taso tsundum a gidan siyasa iya siyasar. Ranan Kamfen ɗinta na ƙarshe a wata ƙaramar hukuma tayi. Mutane kaman ruwa haka aka cika stadium na wajen don ganin Asiya Kachallah, wannan ya ƙona ran Bilkisu Kachallah matuƙa saboda clearly mutane sun fara nuna musu banbanci, mutane sun fi ƙaunar Asiya a kanta. Na lokaci kaɗan ne, sunan Asiya zai shafe a bakunan mutane, da sannu sunan Bilkisu Kachallah sai ya zamo national anthem na jahar. Ranan da Bilkisu Kachallah ta rufe nata kamfen ɗin, kwana huɗu bayan na Asiya bata samu rabin mutanen da suka zo wajen na Asiya ba duk da kuwa ita ɗin tayi a cikin Congo ne yayinda Asiya tayi nata a ƙaramar hukuma. Duk yadda taso ɓoye ɓacin ranta hakan ya faskara dan kuwa fiskarta babu walwala kwata kwata har aka gama taro. Ihu da ta dinga yi ma ba kamar na kullum ba domin gwiwarta ya sake babu ƙarfin gwiwar ɗaga murya. Ta yi ƙoƙarin danne ɓacin ranta da tunanin zobenta zai isota nan bada jimawa ba. Shri Hari Bansari ya gama bautan ranaku masu alfarma a gareshi. Idan zobe ya zo, ba Gwamna Saifuddeen ba, gaba ɗaya jahar za su dawo ƙarƙashin ikonta. Sai da Umaru Kwom ya rufe kamfen ɗinsa kafin Gwamna Saifuddeen ya rufe nashi. A bayyane take mutane na tareda SSK sama da Umaru Kwom. Hatta waƙoƙin zaɓe na SSK yafi na Umaru Kwom daɗi musamman wanda wani haziƙin mawaƙi ya rera yana yabon Gwamna da amaryarsa Asiya Shahidah. *** Asiya na zaune gefen Junior Gwamna ya shigo. Asthma ɗinsa ce ta tashi ɗazu bayan ya gama tsalle-tsallensa a waje shi da wasu yaran ma'aikata na gidan., ba inhaler kusa da shi shine ya shiga mawuyacin hali kamar zai shiɗe yaran suka gudu, sai da wani security ya ganshi ya kawo shi cikin gida wurjanjan. Aka ci sa'a Gwamna na kusa ya fito da inhaler ɗinsa ya matsa masa, still ya jima kafin yaron ya dawo dai dai "Ya jikin na shi?" Gwamna ya zauna gefen Asiya bayan ya kissing goshin Junior "Da sauƙi" Bata ankara ba taji ya kamo hannunta, yanzu kam har ta saba da irin haka dan indai suna tare baya rabo da riƙe hannunta ko kuma ya kissing goshinta ko kumatunta. "Zan fita, zan je wajen Baba" "Allah ya kiyaye hanya" "Amin" ya kissing goshinta sannan ya miƙe ya fita. Ta cigaba da kallon Junior tana tuno yadda kwanaki suka dinga tafiya da sauri har haka. Gobe Jummu'a za'a ɗaura auren Ubayd da Salma, jibi Asabat za a yi zaɓen shugaban ƙasa yayinda sati biyu na gaba kuma za ayi zaɓen Gwamnoni. Tunda ta gama kamfen ɗinta bata sake fita daga gidan ba. Duk wani shirye shiryen biki da ake yi ta ƙi zuwa gidan. Ta dai aikawa Inna Yaha kuɗi, sannan ta turawa Faty ma kuɗin gudummawa saboda hidimar bikin da za a yi. Ba zai kyautu ba idan bata halarci ko ɗaya daga cikin hidimar bikin ba, idan tayi haka zata zama butulu. Ko babu komai, Yaya Ubayd Yaya ne a gareta, sannan ko dan darajan Abba dole ta je. Ba wai tana jin haushin auren bane amma ta rasa ya akayi zuciyarta ya rasa samun sukuni tunda satin bikin ya shigo. Ta miƙe ta koma ɗakinta saboda ta fara shiryawa domin shaiɗan ke jefa mata wannan wasu-wasi. Matuƙar tana auren Saifuddeen, Ubayd ya haramta mata har abada. Soyayyarsa ta fara gushewa a zuciyarta sai dai abinda ba za a rasa ba daga shaiɗan wanda ke motso mata rayuwar soyayyarsu ta baya a wasu lokutan. Ta kan tsinci kanta da damuwa idan Gwamna bai kirata ko ya mata text ba a kwanakin da ba nata ba. A ranakun da ya kasance nata, idan har tafiya ta kamashi ba zai kwana a gari ba gadonta na mata faɗi. Duk da idan yana nan ɗin, filo take jerawa tsakaninsu ko kuma lokutan da ta manta bata yi hakanba, kasancewar su kwance a gado ɗaya yana sa mata nitsuwa. Duk ranan da ba su kwanta tare ba, tana yin kewar numfashinsa, ƙanshinsa, tusarsa idan ya shiga banɗaki da Asuba zai yi fitsari, abin mamaki har ƙwaƙwalwarta ya haddace sautin tusar ta yadda a ko'ina ta ji zata ce tasa ce. Ta kan yi kewar wata rana da take al'ada suna kwance tayi tusar gaba ba su jima da bacci ba dan haka sarai ta san ya ji tusar amma ta kafse ta rintse idonta tana Allah yasa kada yai magana. Ko sakan arba'in bai cika ba ta sake wata tusar mai ƙara, wannan karan ta fita ta baya ne dan haka bayan ƙaran da tayi har da wari. Asiya ta ji kaman ta nitse cikin gadon saboda kunya. "Gaskiya za a ciki tara. Domin daga yanzu Gwamna ya saka dokar hana tu..." Asiya ta sa hannu ta toshe masa baki, tana ji a ranta kaman ta fasa ihu. Ƙoƙarin cire hannun yai amma ta hana sai ma ƙara matsowa da tayi tana faɗin "ai kaima kullum kana yi idan ka shiga banɗaki, nima idan ka sake zan ci tarar ka ehe" Ganin ta dage da danne masa baki dan kada yai magana hakan yasa ya fara mata cakulkuli, nan da nan ta sake mai baki tana ƙoƙarin riƙe hannunsa tareda faɗin ya dena, bai denan ba kuwa har sai da ta birkice tana dariya sosai tama manta cewa dare suke. Tuni ya samu daman haɗe bakinsu ya shiga kissing ɗinta passionately. Jikinta ya riga yayi laƙwas dan haka ta kwanta shiru tana karɓan zazzafan saƙo daga Gwamna. A hankali kuma ba tareda ta shirya ba ta shiga maida masa da martani tana kwaikwayon yadda yake mata. Sun jima suna kissing junansu, sun manta da duniyar da suke ciki dama wani damuwar dake cikinta, sun manta ƙiyayya ko soyayya domin all that matters a lokacin shine wannan kiss ɗin, wanda shaƙar numfashine kaɗai ke raba bakunan su. Kusan minti takwas suka ɗauka a haka kafin Asiya ta yi saurin juyar da kai gefe tana fitar da numfashi da sauri sauri saboda hankalinta ya fara dawowa jikinta. Ganin haka yasa Gwamna ya janye jikinsa yana faɗin "sai da safe" Dukkansu sun tsinci kansu cikin wani sabon yanayi. Gwamna ya shiga jin wani matsananciyar buƙatarta, ya dinga sauke ajiyar zuciya yana ƙoƙarin saito nitsuwarsa, ƙarshe ya miƙe ya shige banɗaki ya sakewa kansa ruwan sanyi. Sai da ya shige banɗaki Asiya ta samu damar motsawa, ta mirgina gefenta ta lulluɓe duk jikinta da duvet sannan ta sa yatsu uku ta danne lips ɗinta tana ajiyar zuciya akai akai. Ba zata iya fassara yanayin da ta shiga ba, duk da tana jin kunyarsa amma yadda jikinta da ruhinta ya amsa wannan saƙo, ji take kamar ta miƙe ta bishi banɗaki ta haɗe bakinsu su dawwama a wannan yanayi har abada. Haushin kanta ma ta fara ji data katse wannan daɗin, at least da ta bari sun ƙara koda minti ɗaya ne, kai koda sakan talatin ne. Zuciyarta ya shiga ƙiyasta mata abubuwa dayawa har Gwamna ya dawo ya kwanta. Deep down tana fata ya sake yi mata chakulkuli, ya sake kissing ɗinta ya sake faɗin "i didn't know you are a good kisser" wanda sai yanzu ta tuno in between kissing ɗinne ya faɗi hakan. Ko mi itama ta faɗa masa cikin yanayin nan oho. Haka ta dinga tariyo komai a zuciyarta, tun daga cin abinsu tare zuwa kwanciyar da ta yi, zuwa shima shigowar sa ɗaki, wanka da yai da kuma kwanciya da yai yana mata addu'ar Allah ya tashe su lafiya bayan tace masa sai da safe, zuwa tusar da ta yi, chakulkuli and then...kiss. Washegari ita ta fara tashi ta bar ɗakin da wurwuri tun kafin ma alarm ɗinta ya buga dan ba wani baccin kirki ta yi ba. *** Ƙarfe biyu da rabi ta isa gidansu. Gidan ya cika da 'yan biki, ana ganinta aka shiga ihu ana mata kirari. Inna Yaha ta shiga nan nan da ita, yadda Asiya take bata girma bayan ta san irin zaman da suka yi da Ummanta, hakan yasa ta ke jin kunyan abubuwan da ta aikata a baya. Yarinyar da ta ke wa gori da Agola itace ta ke da matsayin da ya ɗaukaka darajan gidansu a anguwa. Gidansu ya koma abun kwatance. Muna layin gidan su matar Gwamna. Gidanmu na daura da gidansu matar Gwamna. Gidan da zanje da ka wuce layinsu matar Gwamna kaɗan sai ga layinmu. Wasu masu abin hawar ma kana cewa gidansu Asiya Kachallah to a ƙofar gidan Abba za a saukeka. Asiya ta halarci walimar Amarya amma bata jima a wajen ba. Haka kawai kuma data ga Amarya sai ta ji zuciyarta yayi sanyi. Ta sani Salma na son Ubayd kuma zata kula da shi. Nan da lokaci kaɗan tsakaninsu zai daidaita, Ubayd zai manta da cewa sun taɓa soyayya. Asiya bata koma gida ba sai ƙarfe tara na dare. Ba ita ke da kwana ba shiyasa kawai ta wuce ɗakinta ta murɗa key ta kwanta bayan tayi wanka. Sumayya bata nan anyi hutun zaɓe ta koma gida. Koda tana nan ma tsakaninsu har yanzu basu daidaita ba. Suna dai magana kam, amma babu wannan walwala kamar da, ko ɗakin Sumayya bata shiga sai da dalili itama kuma Sumayyar hakane. Yanzu a gidan Junior ne ya maye mata gurbin Sumayya domin indai yana gidan to yana maƙale da ita, wannan nema yasa ta jajirce wajen koya masa karatu na addini saboda ta nan ne yake da naƙasu. Malamin dake zuwa koyar da shi ba kullum yake zuwa ba, kuma kaman yana koyarwar ne da tsoro tunda baya iya tsawatar masa saboda Bilkisu Kachallah ta gindaya masa sharuɗɗa lokacin da aka kawo shi. Dalilinta ne yaron ya fara sake jiki da yaran ma'aikatan dake gidan duk da yasan idan Mommynsa ta sani ya kaɗe dan faɗa zata masa sannan tasa a zane yaran(Allah Sarki basu da gata)a ganinta sune zasu ɓata mata yaro, sannan a dalilin yaran ne ma har Junior ya fara magana da Hausa sosai. Bilkisu ta yiwa Asiya magana akan ta dena shiga harkan 'ya'yanta tun ranan da ta gansu a wajen kamfen ɗinta. Asiya ta yi banza da maganar. Bilkisun bata zama a gidan balle ta sanya musu ido, shima yaron da ya gane mahaifiyarsa bata so ya dinga zuwa jikin Asiya sai ya dena faɗa mata abinda suka yi da Asiya, ko wani abu ta siya masa baya faɗa mata sai dai ya faɗawa Daddynsa... A ɗan tsurkukin kwanakin daya rage ayi zaɓe aka fara yaɗa jita-jita wai Gwamna Saifuddeen bare ne ba ɗan asalin jahar Congo ba. Iyayensa 'yan ƙasar Gambia ne, Alhaji Sani Kachallah ne ya adopting ɗinsa saboda ba shi da ɗa namiji. Yayinda wasu ma suka sheganta Gwamna Saifuddeen, suka ce Dr Sa'ad Kachallah bai haihu ba har ya rasu. Alhaji Sani kwarton Aicha Jallow ne wanda baƙin cikin hakan ne ya kashe Sa'ad Kachallah. Maganganu dai marassa kan gado da ake yi duk dan a ruɗar da mutane a karkatar da hankalinsu daga zaɓan Gwamna Saifuddeen... "This is rubbish. Dole ne mu maka jaridar Climax a kotu. Sai sun nemo mana hujjojin da suke iƙirarin suna da shi" Ta ɗago ido ta kalli Saifuddeen ta ga idanunsa sun kaɗa sun yi ja, har lokacin kuma idonsa na kan jaridar hannunsa. Ta dafa hannunsa tace "kar ka bari wannan ya girgiza ka. Duk sharrin Umaru Kwom ne, we will win this election ko sun ƙi ko sun so" Ta karɓe jaridar hannunsa ta zauna a cinyarsa ta tallafo fiskarsa tana masa magana. Asiya ta shigo falon saboda ta tambayeshi ko zai ɗauko Nana saboda zaɓe na matsowa, amma ta tsaya chak saboda ganin su tare cikin wani yanayi da ya motsa mata kishin da bata san tana da shi ba. Ya za tayi tunda ita ta kawo kanta wajen, dama saboda zata je gida ne take son yi masa maganar yanzu, jiya data dawo basu haɗu ba balle ta masa maganar. Har ta shiga mota hoton Bilkisu zaune akan cinyar Gwamna take gani. Yadda take taɓa masa fiska ma waya sani ko sun... tayi saurin shafa laɓɓanta tana tuno zazzaƙar kiss ɗin Gwamna. A wajen biki ma kasa walwala tayi, Inna Yaha harda mata guntun nasiha wai Allah bai haɗata da Ubaydullah bane saboda Gwamna Saifuddeen yafi dacewa da ita. Ta dinga nuna mata karamcin Gwamna gareta. A tunaninta dalilin yau aka ɗaura auren Ubayd da Salma shi ya dameta har ta kasa sakewa, bata san cewa Gwamna shine silar ɓacin ran Asiya ba. A ɓangaren Gwamna kuwa duk yadda yai ƙoƙarin danne zuciyarsa daga ƙarairayin daya karanta a jaridar Climax ya kasa, mutuncin iyayensa aka taɓo, iyayensa da suka jima a cikin ƙasa. Da farko ya ji a ransa zai bi shawarar Bilkisu, amma daga baya ya gane ɓata lokacine saboda biyewa wannan jita jitar ma kaman buɗe ƙofa ne na sawa mutane su yarda da maganganun, gara kawai ya share. Duk abinda zai faru gameda makomar kujerar Gwamna a jahar Congo, Allah ne masani. Bai samu halartar ɗaurin auren Ubayd ba duk da Abba har office ya kawo masa katin gayyata. Ya dai kira Abban ya bashi haƙuri tareda yiwa Amarya da Ango addu'a. Asiya da wuri ta dawo gida amma bata bi ta kan Gwamna ba duk da kuwa kwananta ya fara yau ne. A ɗaki wani zazzaɓi ne ya rufeta har lokacin zuciyarta ya kasa samun sauƙi. Miyasa Bilkisu zata zauna a cinyarsa bayan ya san daga karyawar safiya lokacinta ya shiga. Idan ma karyawar suke miyasa zata zauna a cinyarsa?, shin shi yace ta zauna ko kuma ita ta ga dama ta zauna saboda duk abinda suka yi daren jiya bai isheta ba. "Bilkisu zauna a cinyata na ji ɗuminki" ta yi maganar tana kwaikwayon muryarsa. "Mtswww" ta yi tsaki a karo na ba adadi tun safiyar yau. Yunwa take ji dan ko a gidan biki bata sa abu a bakinta ba, kamar mai azumi haka ta wuni da yunwa. Yanzun ma yunwar ne ya fara murɗa mata ciki amma taƙi tashi ta nemi abinci ko ta kira a kawo mata ɗaki. Ƙarshe ta gama juye-juye ta tashi ta sa ƙaramin hijab akan riga da wando na bacci ta wuce sashen Gwamna. Idan ta tarar da Bilkisu a wajen sai dai ayita da wajewa tunda dai lokacin ta ne. "Lokacina" ta faɗa a hankali tana tabbatarwa kanta cewa ba zaƙewa take son yi ba, hakkinta zata bibiya. Bawan Allah na zaune akan kujera a falo yana kallon tsohon ajiya. Saboda abinda ya karanta gaba ɗaya wunin ranan yayi shi ne babu walwala da kuma tsananin ciwon kai. Saboda ta nuna masa ranta a ɓace yake, sai ta wuce cikin ɗaki ba tareda tayi masa magana ba. Kusan minti ashirin tana ɗaki amma bai yi niyyar shigowa ba balle har ta ganshi a ɗakin. Da video da yake kallo ya kai ƙarshe yake maida shi farko ya sake maimaita kallon. Yana bin kowanni movement na iyayensa a cikin videon, musamman mahaifiyarsa, wacce ita ce bai san kowa nata ba, akwai iyayenta a video ɗin suna yi mata kari da kuɗi amma su kaɗai ya sani daga danginta. Ya sha jin Dadda na cewa mahaifiyarsa 'yar babban gida ce amma kuma gashi har yau babu wani nata da ya taɓa nemansa, hakanan shima ya kasa zuwa nemo su. A mafiya lokuta ya kan sa a ransa zai je Gambia ya nemo dangin mahaifiyarsa amma sai wani abu ya sha gabansa. Asiya ta zauna gefensa ganin hankalinsa ya tafi kan screen ɗin TV dake falon. Ta ɗaura hannunta akan hannunsa ɗaya tace "Excellency" "They were in love. Very much in love. Ki kalli nan, baki ga irin murmushin da suke yiwa junansu ba? My father is shy, but my mother is witty. Kiga yadda take bashi cake a baki tana dariya har da ja masa hanci" ya ƙarisa maganar yana dariya. Sai yanzu ta fahimci mai yake faruwa. Lokacin da take tafiya gidan biki Yaya Bello ya faɗa mata gulmar abinda ake cewa a gari amma hankalinta baya wajen. "Ka yi haƙuri. Jita jitar mutane ne kawai saboda a hana jama'a zaɓenka" "Na sani" "Kada ka bari wannan ya taɓa ka. There are more important things..." "Than my parents honour?" "Kayi haƙuri, ba haka nake nufi ba?" "Ko da sau ɗaya ne zan iya bada duk abinda na mallaka dan na gansu, na taɓa su, na ji ɗuminsu, na yi hira da su. Ko da..." Asiya ta rufe masa baki da nata. Da farko bai responding ba, hakan yasa ta janye bakinta tana shirin miƙewa daga wajen amma ya riƙota ya jawota jikinsa da kyau ya shiga kissing ɗinta a hankali. Chan bayan ya saketa sai yace " you are right, there are more important things to do" Asiya ta zaro ido tace "like what?" Kumatunta ya ja ya miƙe yace "like zamu shiga ɗaki ki sake min abinda kika min yanzu" Asiya ta shiga wiki-wiki da ido tana faɗin "ni ni fa ban yi komai ba" Yadda tayi maganar sai ya bashi dariya. Yace " kwantar da hankalinki, Sallar Isha zan yi" Har ya shige ɗaki Asiya bata bar jin fargaba ba dan tunaninta wani abin daban yake nufi. Tunda yace bai yi sallar Isha ba ta san kenan ko abinci bai ci ba, hakan yasa ta kira a kawo musu abinci dan yadda jikinta yai lakwas ba iya shiga kitchen zata yi ba. Har suka gama cin abinci suka kwanta bata daina jin tsoro ba sai da ta ji fitar numfashinsa ya chanja alamar bacci ya ɗauke shi...   *MATAR GWAMNA* 17 *MATAR GWAMNA* Washegari Asabat aka fita zaɓen shugaban ƙasa. Gwamna da Bilkisu sun je sun jefa ƙuri'ar su amma Asiya bata bisu ba, duk da itama an chanja mata katinta zuwa polling unit ɗaya dana Gwamna, wanda ke kusa da ƙofar Kachallah House. Tun daga zaɓen shugaban ƙasa count down ya fara, saboda zaɓe na gaba shine na Gwamnoni. A ɓangaren Gwamna Saifuddeen ya fawwalawa Allah lamarinsa, ya sani yana da goyon baya na manyan manyan jahar amma duk da haka mulki na Allah ne. Bilkisu Kachallah ta shirya 'yan shaye-shaye domin duk inda aka ga wani ya samu ƙuri'u fiye da Gwamna Saifuddeen to a sace akwatin zaɓen. Duk da ta sani cewa akwai ƙanshin Gwamna Saifuddeen ne zai lashe zaɓe, amma ba zata bar wata ƙofa da za a ɓata mata duk wani shiri da tayi ba. Ta sani Umaru Kwom zai yi ƙoƙarin dagula zaɓe idan bai ci ba amma kuma duk ta inda ya ɓullo zai samu babu hanya. Shima Umaru Kwom ya shirya nashi jama'ar da zasu sace akwatunan zaɓe, ya fitar da kuɗi na fitar hankali wanda in har bai ci zaɓe ba kafin ya farfaɗo daga ɓarnar kuɗin da yai sai an ɗau shekaru sama da biyu. Masu faɗa aji a jahar kowa ya baza ido yana jiran sakamakon zaɓe. Daga ƙarshe dai ƙuri'ar ɗan talaka shi zai bada kujerar Gwamna. Cikin satin biyun da ake zaman jiran ikon Rabbana, kowa ya duƙufa da abinda suka yarda da shi. Masu addu'a na yi, ma su bin duhun dare na bi, masu tura 'yan aike a musu duba duk sun bazama yi. Bilkisu Kachallah bata da kwanciyar hankalin da Gwamna Saifuddeen ke da shi. Ita da Alhaji Sani babu wanda yake iya bacci da kyau, kowa da fargaban da yake. A wannan lokacin ne ma Saifuddeen ya tattara nitsuwarsa kan iyalinsa musamman 'ya'yansa da suke hutu, da kansa ya je ya ɗauko Mahirah daga wajen Dadda yace sai an koma makaranta zata koma mata. Nana ma dai saboda yana son ta warke sarai ne shiyasa bai ɗaukota ba, duk da kuwa Asiya ta nuna masa ya kawota gida, zuwa a gama zaɓe sai ya mayar da ita amma ya ƙi, sai dai duk bayan kwana bibbiyu yana zuwa ya Nana a Rehab. *Ranar zaɓe* Duk son Asiya ranan zaɓe bai faɗa kwananta ba. Amma duk da haka ta yi tsayuwar dare akan Saifuddeen, inda tai masa addu'ar samun nasara idan hakan shine mafi alkhairi a gareshi. Idan kuma babu alkhairi to Allah ya bashi ikon karɓar ƙaddararsa hannu bibbiyu. Da Asuba ta tura masa text tana masa fatan samun nasara, ko minti ɗaya bai cika ba ya turo mata da saƙon godiya. Ta yi niyyar zuwa zaɓe wannan karan saboda kar ace bata bawa mijinta support ba. Dama ita bata taɓa yin zaɓe ba, tana dai da katin saboda mahimmancinsa. Mahirah ta nuna mata kayan da zasu saka, wai anko Mommy ta musu har da Daddynsu. Tunda shigar fari za su yi itama zata sa fari, sai kuma ta chanja ra'ayi ta ce ba zata saka pure white ba. Ta jima tana neman takamaimai kayan da zata saka, daga baya ta fito da wani Bangladeshi Abaya gown. Fari ne fat amma zanen flowers na jikinsa kalar royal blue ne, ta yi rolling da gyalensa kalar royal blue sannan ta saka wani high heel da ya zo da purse ɗinsa dukka kalar royal blue. Ta ɗan kalli fiskarta a madubi ta furta Masha Allah, domin ko bata saka komai ba a yadda take ta yi kyau babu ƙarya. Ta ɗan bi idonta da kwalli saboda su sake fitowa, kaman wanda ta sa da farko bai yi raɗau yadda take so ba. Junior ne ya shigo ɗakinta da gudu yana faɗin "Anty Asiya, i'm ready" "Zo nan handsome ɗina" Turare ta fesa masa kaɗan duk da akwai turaren a jikinsa. Ta karanto addu'a ta shafa masa a kai tana neman tsari daga duk wani sharri da kuma kanbun baka. Ta ƙara kallon kanta a madubi sannan ta fita hannunta riƙe dana Junior. A bakin ƙofa ta tsaya chak tana binsu da kallo zuciyarta na wani tafarfasowa. "You look handsome my Governor" Bilkisu ta faɗa bayan ta gyara masa zaman hularsa. "Daddy, Anty Asiya is here" Junior ya faɗa da ƙarfi. Hakan ya sa dukkansu biyu suka juyo suka kalleta. Lokacin data haɗa ido da Gwamna idonta ne ya ciko da hawaye, tayi saurin komawa da baya tun kafin tayi abin kunya, tayi kuka a gaban Bilkisu. Miyasa ma ta damu da shi? miyasa take jin haushi idan ta ganshi da Bilkisu? Tambayar data kasa bawa kanta amsa kenan. Hawayen dai data ke ɓoyewa sai da suka zubo. "Asiya kina son Gwamna Saifuddeen" abinda wani ɓangare na zuciyarta ke faɗi kenan, amma ta shiga ƙaryata hakan. Kusan minti huɗu sai ga Gwamna ya shigo ɗakin. "Lafiya?" Ya tambaya ganin tana faman goge fiska tareda jan hanci. Magana take son yi amma kuka ne ya ƙwace mata. "Asya minene? Miya faru?" yana ƙoƙarin riƙeta ta wafce jikinta ta koma gefe tana sauke ajiyar zuciya. "Kina kuka saboda kina ganin zan faɗi zaɓe ne?" Wani kallo ta wurga masa. Ɗan rainin hankali kawai, saboda rashin cin zaɓe za ta yi kuka? "Ki fito mu tafi, ke ake jira" "Ba zan je ba" "Miyasa?" Ya tambaya yana tsareta da idanu. "Zaɓen shugaban ƙasa ma ban biku ba, wannan ma na fasa zuwa" Ya ɗan yi shiru kafin yace " shikenan, ayi zaman gida lafiya" Ganin da gaske yayi hanyar ƙofa sai tayi saurin cewa "shine ko ka bani haƙuri" Murmushine ya suɓuce masa saboda ya riga ya sani kishi takeyi. Ya haɗa hannu yace "Ranki shi daɗe, ayi haƙuri" Bayan minti uku ta fito idonta sanye da baƙin glass. Tana ganin Bilkisu tana yiwa Mahirah faɗa wai gyalen data saka yayi girma amma bata ce komai ba ta samu kujera ta zauna, ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya. "Kwata-kwata baki da fashion taste Mahirah. Miye wannan dan Allah? Inaga zaki dawo zama a nan permanently, ya isa haka zama da tsohuwan nan" Mahirah ta zumɓura baki tana magana ƙasa-ƙasa Bilkisu ta gama mita ta haƙura dan Mahirah bata da niyyar chanja mayafin data saka wanda Asiya bata ga wani aibu a jikin gyalen ba. Zaman minti biyar suka yi a babban falo, har Bilkisu ta miƙe zata je ta dubo Gwamna sai kuma gashi yana saukowa, fiskarsa ɗauke da murmushi amma deep down yana jin tsoro. All this while, bai saka damuwar zaɓe a ransa ba, yau da za ayi zaɓen sai ya fara jin duk wani ƙwarin gwiwarsa na ƙoƙarin sacewa. Shine a gaba iyalinsa na baya har suka kai wajen da motoci ke jiransu. Gidajen talabijin na jahar duk sun nuna jefa ƙuri'ar da Gwamna da iyalinsa suka yi, hakanan an nuna na babban abokin adawa ma, wato Alhaji Umaru Kwom. Daga polling unit Gwamna da iyalinsa suka koma gida dan su saurari abinda Allah zai yi. *** Zaɓe ya fara tafiya lafiya-lafiya sai daga baya kuma a wasu rumfunan zaɓe aka tada tarzoma. 'Yan bangar siyasa suka dinga sace akwatunan zaɓe. A wasu wajen kuma jayayya tsakanin mutanen da Bilkisu Kachallah ta baza ne da kuma na Umaru Kwom shi ya tada fitinar. Duk abinda yai farko dai zai yi ƙarshe. Duk wani ƙoƙari na ganin an wargaza zaɓe a mafiya yawancin rumfunan zaɓe hakan ya faskara, saboda jami'an tsaro sun yi maganin abun da wuri. A chan ƙauyuka da ba a samu jami'an tsaro ba ma suma sun yi zaɓe lafiya, duk wanda yazo da niyyar tada husuma, tuni zaratan sammari ke yin waje da mutum. Rumfunan da aka tada husuma wanda hukumar zaɓe ta tabbatar an kashe zaɓukan wajen, yawansu bai kai har ace za a sake zaɓe ba. A ɗan wannan tsurkuki da ake jiran sakamakon zaɓe 'yan siyasa da dama kan rasa imaninsu. A ɓangaren Bilkisu Kachallah tayi imanin idan har mijinta bai lashe zaɓe ba to kuwa babu abinda zai hana a tada yaƙi a jahar. Shima Umaru Kwom yana da shirin kota kwana. "Mune muke gaba a ƙaramar hukumar Layyat. Darling we are winning" Gwamna yace "Hmmm" ya cigaba da rubutun da yake saboda ya kau da hankalinsa akan sakamakon zaɓe. An riga an gama jefa ƙuri'u, babu abinda ya rage sai dai su zubawa sarautar Allah ido. Da yaga Bilkisu ta dame shi da maganar wanda ke gaba akan irga ƙuri'u da ake, sai ya miƙe ya wuce cikin ɗaki... Ranan Litinin da ƙarfe goma na safe Gwamna da iyalinsa suna zaune a falonsa sun ƙurawa tv ido, a yau ɗinne za a sanar da wanda ya lashe zaɓe, duk da kuwa sun san a bisa ƙuri'u da aka irga Saifuddeen Kachallah ne a gaba. A ɓangaren Umaru Kwom shi ɗaya ya kulle kansa a ɗaki yana kallon talabijin duk da kuwa zuciyarsa ta karye saboda ƙuri'un Saifuddeen sun fi nashi yawa, amma duk da haka he's holding up to last minute miracle. Ƙarfe goma da minti talatin da uku aka sanar da wanda ya lashe kujerar Gwamna a jahar Congo. Shugaban zaɓe na jaha yana kiran sunan Saifuddeen Sa'ad Kachallah a matsayin wanda ya lashe zaɓe Bilkisu Kachallah ta daka tsalle tareda yin ihu ta faɗa jikin Gwamna. Asiya kam sujudush shukri ta yi ita da Mahirah, shima Junior ganin sun yi sujjada sai ya yi. Gwamna ya tura Bilkisu gefe dake ta ihun we won, shima ya kai goshinsa ƙasa yana yiwa Allah godiya... Umaru Kwom na jin sunan Saifuddeen sai da ya samu temporary shock na wasu sakanni. Chan ya ɗau kwalbar giyarsa ya kwankwaɗa daya ajiyeta sai ya ɗau waya ya kira wata numba yace "a hargitsa gari" Nan da nan mutanen da aka biya suka shiga ihun "bama yi, Umaru Kwom ne ya ci zaɓe" kafin kace me aka shiga ƙone-ƙone a wasu gurare. Gwamna yana magana da Alhaji Sani Kachallah a waya Asiya ta taɓa shi tana nuna masa wayarta. Sallama yai da Alhajin sannan ya maida hankalinsa ga Asiya. "Wasu matasa sun fara riot. Dan Allah ka sa a ɗauko Nana daga Rehab. Hankalina bai kwanta ba" Kafin ya bata amsa COS ya kira shi. Ya ɗauki wayar hannu na rawa. Asiya tace "zan ɗaukota" Ta fita ba tareda ta jira amsarsa ba. Ikon Allah suna barin Rehabilitation centre ɗin ko minti takwas bai cika ba 'yan banga suka iso wajen suna neman 'yar Gwamna amma babu ita a ciki. Hakan yasa suka cillawa wajen wuta, marasa lafiya da likitoci kowa ya fara ta kansa. "Hello, nace a tura fire service Rehab centre dake layin Kura" Daga ɓangaren data kira aka ce " babu fire service a ƙasa, motar ƙarshe tana Kachallah Mall da aka sawa wuta" "Da mall da Asibiti wanne yafi mahimmanci? Yanzu yanzu a tura mota wajen" Asiya ta kashe wayar tana faɗin Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun. Hanya ta uku kenan da Yaya Bello ke chanjawa saboda samun tsira, ana ganin plate number mai ɗauke da Kachallah to sai ta Allah. Nana ta ƙanƙame Asiya tana kuka. "Yaya Bello ka tsaida motar nan, gari ya hargitse zamu iya shiga matsala" "Ina zamu je idan na tsaya?" "Daga nan babu nisa zuwa gidan Abba, zamu ƙarisa gidan da ƙafa" "Da ƙafa kuma?" "Shine mafita" Tsabar ruɗewa Yaya Bellon kawai ta tiso gaba babu security ɗinta. Hijab ne a jikin Asiya dan haka ta ciro ɗankwalin atamfar data saka ta rufe baki da hancinta, yai kamar face mask ta saka. Ta kama hannun Nana suka fita daga motar, bayan sun fita ta gyara mata ɗan ƙaramin gyalenta ya rufe mata rabin fiska. "Yaya Bello ka cire plate number ɗin nan Dan Allah" "Kar ki damu ba abinda zai faru" "Ban yarda ba, ka cire" Sai data tabbatar da ya cire numbar kafin ta ja hannun Nana suka fara bin lungu lungu, tafiyar minti shida ta kaisu gidan Abba. Gwamna tun da aka kira aka ce masa an cinnawa rehabilition centre wuta ya shiga tashin hankali. Bai san halin da Nana ko Asiya suke ciki ba, gashi numbar Asiyar ta ƙi shiga. Itama Bilkisu Kachallah jin an ƙona rehab sai hankalinta ya tashi, duk wani murnan lashe zaɓe da Saifuddeen yai sai ya ɓace, ta shiga kiraye kirayen waya dan ta tabbatar da lafiyar 'yarta. Kusan awa uku akayi ana ƙone-ƙone kafin sojoji da aka baza suka ci ƙarfin abun, dan wannan faɗa yafi ƙarfin 'yan sanda. Tuni aka shiga yin kamen samari bayan ƙura ta lafa. Da wanda ya ji da wanda bai ji ba idan hau ta hau ka sai kawai a rafkeka a je a kulle. Curfew aka saka na ƙarfe biyar na yamma. Zuwa ƙarfe huɗu ma gari yayi tsit, sojoji na ta shawagi a ko'ina. Asiya tana gidansu tanata ƙoƙarin kiran numbar Gwamna dan ta sanar da shi suna lafiya amma ta ƙi shiga. Sai ƙarfe shida da kusan rabi na yamma Gwamna ya ga saƙon Asiya wanda ta tura tun da rana. "Alhamdulillah! Alhamdulillah!" Ya faɗi yai sujudush shukri. Ikon Allah ne ya kaishi wannan lokaci ba tareda wani abu ya same shi ba saboda rashin sanin halin da matarsa da 'yarsa su ke ciki. Ɗakin Bilkisu ya shiga ya sanar da ita Nana da Asiya na lafiya. Damuwarta Nana ce ba Asiya ba amma koba komai tunda ta taimakawa 'yarta she's grateful. Ƙarfe takwas na dare Gwamna da kansa ya je gidansu Asiya dan ba zai iya samun nitsuwa ba sai yasa su a idonsa. Yai wa Abba godiya sannan ya masa sallama ya ɗau matarsa da 'yarsa suka tafi. Asiya da Nana suka shiga baya saboda mota ɗaya ya zo da shi, daga shi sai Dreba. A ɓangaren Umaru Kwom rashin sace Nana Kachallah ya fi komai dagula masa lissafi. Dan yasa a ransa zai yi amfani da ita wajen samun wani abu a wajen Saifuddeen. Suna shigowa falo Bilkisu ta zo da gudu ta rungume 'yarta. She might be a bad mother amma kamar kowacce uwa, tana son 'ya'yanta. Sauran yaran ma suka zo suka rungumi yayarsu suna kuka... "An ce mutane shatakwas suka mutu, anyi asaran dukiyoyi dayawa. Excellency shin wannan ne siyasar?" Asiya tayi tambayar idonta cike da hawaye. "Asya" "Mun tsira, amma sauran al'umma fa?. Duk wani ɗan siyasa akan talakawa zai sauke takaicinsa, Miyasa? Miyasa?" Wannan karan sai ta fashe da kuka. Ya jawota jikinsa ya shiga bubbuga bayanta a hankali. Chan sai yace " Insha Allahu zan yi ƙoƙari naga irin haka bata sake faruwa ba. I'll try my best Insha Allah" Ya kwantar da kansa a kafaɗarta... Cikin sati guda komai ya lafa. Dama abinda ya faru ɓata gari ne 'yan shaye-shaye da aka biya suka tada husuma. Umaru Kwom ya fito ƙarara ya nuna rashin gamsuwa da sakamakon wannan zaɓe tareda iƙirarin cewa zai shigar da ƙara kotu, wai dole wajajen da aka soke zaɓensu a sake yi musu sabon zaɓe. Ya manta cewa ratan da Gwamna Saifuddeen ya bashi ko da ya samu ƙuri'un duka wajajen da aka soke to ƙuri'unsa ba za su zo kusa da na SSK ba balle har ya wuce shi. *** "We need to celebrate this victory Yallaɓai" "Kachallah" Yallaɓai ya faɗa yana murmushin nasara. Kaman yau ne Chief of Staff ya kawo Kachallah wajen Yallaɓai. *"Ina so a kashe Gwamna Saminu Bacchi, ina so mijina ya hau kujerar Gwamna"* kalaman Kachallah kenan a wannan lokacin. Bayan fitan Kachallah daga falon Yallaɓai. Ta kalli zoben dake hannunta wanda dutsen dake saman zoben daga fari ya koma ja. Ta yi murmushi saboda maganar Shri Hari Bansari ta tabbata, idan zoben ya koma ja to ya fara aiki kenan. "The whole state is now mine. Saifuddeen, Yallaɓai, Baba" ta yi murmushi sannan ta dunƙule hannunta gam alamar ta musu kamun talala. A cikin mota ta fara tuno yadda komai ya samo asali. Watanni kusan bakwai da suka wuce matar Gwamna Saminu Bacchi ta ci mata mutunci, ta mata walaƙancin da tunda aka haifeta ba a taɓa yi mata ba. Ta tuno hirarta da Babanta lokacin da ta kai masa ƙorafi "Baba yaushe Saifuddeen zai zama Gwamna?" Alhaji Kachallah ya saka bredi ya dangwali romo zai kai baki ya ji maganar Bilkisu ta ma sa dirar bazata. "Wace tambaya ce kuma wannan?" "Baba dan Allah ka amsa min tambayata" Alhaji Sani Kachallah ya kalli idon 'yarsa da kyau ko zai gano wani abu amma bai karanci komai a fiskarta ba sai tsananin ɓacin rai, ya ce " idan Saminu Bacchi ya ƙarisa tenure ɗin sa guda biyu Jaha za ta koma ta Saifu dan shi za mu tsayar a zaɓe na gaba" "A taƙaice kusan shekaru biyar kenan?" Alhaji Kachallah ya ture kwanon gaban sa gefe, ya ɗaura hannu akan table yana zubawa Bilkisu ido. "Babu yadda za'ayi Saifuddeen ya zama Gwamna kafin lokacin?. Baba ku ne da gwamnati, ku kuke juya jahar nan, mi zai hana ka ɗaura Saifuddeen a kujerar Gwamna, shekaru biyar masu zuwa sun yi nisa sosai" "Bilkisu!" "Baba break the rules, boycott the protocols make Saifuddeen the governor and own the state" Idan da bai yi tunanin hakan ba to yanzu Bilkisu ta ankarar da shi. Mr Paul da ya ke son haɗa ma sa manaƙisa a wajen Yallaɓai dole ne ya nuna ma sa cewa kafin mutum ya ga biri to biri ya gan shi. To sai dai wani hanzari ba gudu ba, idan ba mutuwa ko kuma an tsige Saminu Bacchi ba, babu yadda za ayi Saifuddeen ya zama Gwamna. "Ki je zan yi tunani akai" Da wannan Bilkisu ta bar falon mahaifinta amma babu gamsuwa a tareda ita saboda bata ga alamar Baban nata is desperate kamar yadda take ciki ba. A hanyar komawarta gida ne Chief of Staff Lamara Damana ya kirata. Munafukai dama basa rasa gulma. Daga barinta gidan Gwamnati har an kai masa gulmar abinda Sha'awanatu Bacchi ta yi mata. "Ina so mu haɗu mu tattauna wani batu, ni dake zamu benefitting da wannan shawara" Lokacin da Bilkisu Kachallah ta haɗu da COS. Dama zani ne ta tadda muje, dan haka yana faɗa mata interest ɗinsa akan ɗaura Saifuddeen kujerar Gwamna tace tana tareda shi ɗari bisa ɗari. COS shi ya kawo mata Medical report ɗin Saminu Bacchi ita kuma tasa aka kawo mata wani ƙwaya mai ƙarfi. Mai hawan jini idan ya sha ƙwayar sama da 2gram a lokaci guda sai ta saka shi cikin temporary shock, idan ba ai taimakon gaggawa ba sai mutuwa saboda ƙwayar tana ƙara gudun bugawar zuciyar mutum ne. COS ya san ciki da wajen gidan Gwamnati kuma ya san yadda Saminu Bacchi yai amanna da shan giya. Shi ya saka aka zuba masa ƙwayan a kwalbar giyansa saboda nan ne hanyar da Saminu Bacchi zai sha ƙwayar cikin sauri ba tareda kuma an zargi komai ba... Saminu Bacchi ya mutu, Saifuddeen ya hau kujerar Gwamna, yanzu kuma zai fara sabon tenure na shi. *"Baba zaka gani, Bilkisu Kachallah ce zata mulki jahar nan. Sai na nuna maka cewa muma mata munada damar yin duk abinda muka ga dama. All of you will answer to me, only me"* Ta sake duban zoben dake yatsarta tayi murmushi. Ba zata taɓa manta yadda Baba ya fifita Saifuddeen akansu ba, saboda kawai shi namiji ne su kuma mata. Lokacin da ta gayawa Alhaji Sani cewa political science zata karanta saboda tana son yin siyasa abinda yace bai bar ranta ba har yau *"ke macece Bilkisu, ki karanta economics ko wani course ɗin daban. Ko kin karanta political science ba za ki shiga siyasa ba, ki bar mu maza muyita fama da wannan. Ga yayanki Saifu, shi nake tunanin zai gaje ni. In fact sai ya zama Gwamnan jahar nan"* "Ke macece" Bilkisu ta maimaita kalmomin data fi tsana a rayuwarta. Daga yanzu sai da bazarta za su yi rawa. "From now on, I make the rules" Ta furta dai dai an buɗe musu gate ɗin gidan Gwamnati... *ku ƙaramin afuwa Dan Allah. Insha Allah komai zai daidaita daga wannan satin. Dana gama test na gobe sai next week, so zan yi typing dayawa Insha Allah* 18     "Excellency ina neman alfarma" "Minene?" "Ina so nayi amfani da email ɗinka wajen tura wani saƙo" "Ok" Gwamna ya miƙawa Asiya wayarsa yana faɗin "hope i'm safe dai ko?" "Akwai abinda kake ɓoyewa ne?" Tayi maganar tana kama ƙugu "Kin san 'yan jarida akwai su da juya magana" Asiya ta haɗe rai ta tura baki tace " su kuma 'yan siyasan fa, Ka manta cewa duk bayan minti biyu suke juya maganarsu" ta juya zata bar wajen, ya sa hannu a ƙugunta ya jawota jikinsa. "Not so fast, ai bamu gama magana ba. Tawa 'yar jaridar ba irin sauran bane, gaskiya take nema ido rufe and sometimes she missed it" "Eh ɗin, ai idan idonka a buɗe yake tsole maka shi za ayi" Yai dariya ya sake ƙanƙameta saboda ƙoƙarin ƙwace kanta da take. "Ina tunanin maida CY ɗaya daga cikin special adviser ɗina. Or what do you think?" Juyowa tayi tana kallonsa, har lokacin hannunsa na ƙugunta. "Kana ganin CY ya chanchanci matsayin?" "Miyasa kika ce haka?" "Bana so ka bawa wani matsayi saboda ni, that's very bad. Idan ka fara da haka ba inda zamu kai. Ko waye kake son bawa matsayi should earn it, ba wai dan yana haɗi da kai ko da matarka ba" "Na ji Matata" Yai maganar tareda tallafo fiskarta ya manna mata light kiss a baki. Asiya ta rufe ido tana jin kanta na yawo a iska. Ganin ta rufe ido sai yai kissing saman idanunta, ya sake kissing hancinta wannan yasa Asiya ta shige jikinsa tana dariya dan ta san ina ne next bayan hanci. Ya sa hannu ya rungumeta sosai yana faɗin " gashi har kin fassarani, ni dama daga nan zan tsaya" Ta cigaba da dariya jikinsa tana jin daɗin yanayin da suke ciki. Yanzu ta dena tsoron taɓata da yake yi, in fact she longs for it, har idan bai taɓata ba takan ji haushi a ranta. Bayan fitan Gwamna Asiya tayi amfani da wayarsa wajen tura wa KaSaSa saƙo ta email ɗinsa. Deep down tana fata mawaƙiyar ta amince da buƙatarta na rubutawa Gwamna Saifuddeen waƙa, tana son ta karanta waƙar ranan inauguration ɗin shi. She loved poetry amma har yau bata iya rubutawa ba... Da dare Gwamna ya duba wayarsa ya kalli saƙon da Asiya ta tura sai yai murmushi. Ta riga ta goge saƙon data tura da email ɗinsa dan haka a wayarsa da yake amfani da shi wajen hidimar rubutunsa ya ga saƙon da ta rubuta. *Dear KaSaSa...Na jima ina bibiyar rubutunki bana gajiya da karanta waƙoƙinki. A matsayina na matar Gwamnar Jahar Congo ina neman alfarma, ki rubuta min waƙa na yabo da jinjina ga mijina Gwamna Saifuddeen. I want it to be a surprise, so ki tura min reply ta email ɗina mai suna seeyashahidah@gmail.com* Ba kalmar data ɗau hankalinsa sai kalmar MIJINA data rubuta. Kenan... sai kawai yai murmushi. *** "Ina ga waɗannan su zasu kasance candidate namu. Ku duba ku gani" Yallaɓai ya miƙawa Mr Paul wasu takardu. Mr Paul ya karɓa ya rarraba takardun dan kowa ya gani. Bayan sun gama gani suka yi na'am da list ɗin sai mutum biyu da Alhaji Sani Kachallah yai ƙorafi akansu amma ganin cewa shi kaɗai yai ƙorafin sai kawai aka buga stamp akan cewa list ɗin za a ba wa Gwamna Saifuddeen. Da yammacin ranan kuwa Bilkisu ta samu Yallaɓai ta tambayeshi mutanen da aka saka a list. Yana miƙa mata list ɗin ta karɓa ta kekketa shi ko karantawa ba ta yi ba. Yallaɓai ya zaro ido da mamaki amma ya kasa cewa komai. "Zan duba mutanen da suka dace, ko suna cikin list ɗinku ko basa cikin su wanda na zaɓa za a saka" Yallaɓai ya gyaɗa kai. Tana isa gida ta samu Asiya na zanawa Nana lalle. "Mommy ki ga hannuna yayi kyau" "Wani irin ɓata guri ne wannan? Za a iya yin baƙi a kowanni lokaci amma kun zauna anan kuna ɓata waje" Asiya ta kalli Bilkisu sai kuma ta sunkuyar da kanta ta cigaba da sakawa Nana lalle a ƙafa. Tun jiya da Nana ta ga lalle a hannunta ta dinga damunta akan tana so ta mata irinsa. Bata ga aibun zamansu a nan ba, ba falon da ake karɓan baƙi bane, zamansu a wajen ma saboda Queen Bee data zo ne Nana ta fito wai a mata lalle shine kawai suka fara a wajen. Bilkisu ta tauna leɓenta na ƙasa tana ƙoƙarin shanye rashin mutuncin Asiya. Bilkisu Kachallah tana tsaye amma ta yi kaman bata ganta ba. Wannan iyayi da Asiya ta ke ya isheta. Yau yau zata sa Saifuddeen ya mayar da ita gidansa, idan aka rantsar da shi kuma guguwar zaɓe ya lafa sai ta sa ayi waje da ita. Ta riga ta gama amfani, ba abinda zamanta zai ƙara musu yanzu. Ta wuce fuuu ta ba tare da ta sake cewa komai ba. Da dare da suka kwanta Bilkisu ta riƙo hannun Gwamna Saifuddeen, lokacin da hannunsu ya haɗu zoben hannunta yai wani ƙyalli na sakan da bai wuce ɗaya ba. "Darling, ina so ka maida Asiya gidanka" "Asiya?" "Yes" ta faɗa tana shafa ƙirjinsa. Yana son tambayar dalili amma kuma ya kasa. Ganin yayi shiru sai ta cigaba "Ina so ka hanata fita hidima kowanni iri. Kuma bana so ka bata haƙƙin matarka" Ta yiwa Yallaɓai haka kuma ya ci shi, dan haka shirun Gwamna akan zancenta bai zo da mamaki ba. Dan ma ta ƙara tabbatarda ƙarfinta sai tace "Ina so kace mata ta bar gidan nan a daren yau" Gwamna Saifuddeen ya kalleta a firgice amma kuma hakan bai hanashi miƙewa ba, ko takalmi bai sa ba ya fice daga ɗakin ya nufi ɗakin Asiya. "Excellency ka bari gobe sai na tattara na koma chan ɗin tunda baka son zamana a nan" Asiya ta faɗa bayan Gwamna ya tasheta daga bacci ya mata maganar barin gida. "Ba zaɓi nake baki ba, umurni ne" "Allah ya baka haƙuri" Asiya ta faɗa a tunzure dan taga abin nasa ma rainin hankali ne. Taya zai zo ƙarfe goman dare yace ta tattara ta koma ɗaya gidan. Babu wanda ta kira cikin masu aikin gidan, da kanta ta shiga haɗa kayanta. Tana yi zuciyarta na ƙuna, yadda take jefa kayan cikin akwati kaɗai zai tabbatar maka ɓacin ran da take ciki. A cikin zuciyarta tayi alƙawarin ba zata sake zama a wannan gidan ba, na ƙarshe kenan da zata zo, idan ya ga dama chan gidansa ma zai iya ɗauketa ya kaita duk inda ya ga dama. Ƙarfe shabiyu da rabi saura na dare Asiya ta shiga ɓangarenta na gidan Saifuddeen. Wajen yayi shiru kuma da ɗan ƙura dan da alama an kwana biyu ba a gyara ba. Haushi da ke cinta ya ɗauke duk wani bacci da take ji. Ta cire hijabi ta shiga gyara ɗakinta, data gama ta koma falo shima ta fara gyarawa. A ƙalla ta yi kusan awa uku kafin ta gama komai ta zo ta yi wanka sannan ta faɗa gado sai baccin gajiya. Bata tashi bama sai ƙarfe bakwai na safe. Ta miƙe da sauri tana hailala sannan ta shige banɗaki ta ɗauro Alwala, data idar da sallah sai ga kiran Hajiya Umma. Walima ce aka shirya a Kachallah House saboda taya Saifuddeen murnan cin zaɓe. Ƙarfe huɗu na yamma za ayi walimar iya matan family. Dake maganar walimar cikin kwana biyu aka tsarata shiyasa ba a gaya mata ba sai yau ɗin. Asiya ta amsa da zata je, ba dan tana son zuwan ba sai dan kawai bata son musawa Hajiya Umma dan tana ganin girmanta. Ta fi minti goma tana kallon numbar Gwamna ta kasa kira. Yadda suka rabu jiya ke dawo mata, miye matsalarsa da zamanta a gidan Gwamnati, minene dalilinsa na fitar da ita a gidan cikin dare? Ganin Shaiɗan ya fara tunzura mata zuciya sai kawai ta dinga Istigafari a zuciyarta, ƙarshe ta tura masa text akan zata je Kachallah House. Bata samu reply ɗinsa ba sai kusan ƙarfe biyu na rana, har ta fitar da rai ma akan zai reply sai kuma ta ga sunansa lokacin da text ya shigo wayarta tana game. *ban amince ba* Ga saƙon gajeriya amma abinda ta haifar a zuciyar Asiya yayi girma matuƙa. Saƙonsa ya ƙara tabbatar mata akwai wani abu a ƙasa. Ko lokacin da suke zaman shiru ma bai taɓa hanata fita ba balle yanzu kuma da ya kasance akwai fahimta mai ƙarfi tsakaninsu. Duk yadda ta yi ƙoƙarin hana kanta shiga damuwa saboda saƙonsa sai da hakan ta faru. Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Mi yake faruwa? shine abinda take tambayar kanta. Rashin samun amsar yasa tayi ƙarfin gwiwa ta danna masa kira. Kira har sau biyu amma bai ɗauka ba. Ta riƙe wayar a hannu kamar abin sadaka, ta tisawa fiskar wayar ido. Tun tana jiran ganin haske har ta karaya da shigowar kiransa. Ganin ƙarfe huɗu saura sai ta kira Hajiya Umma tace mata ba zata samu zuwa ba ƙaninta ba lafiya ta je gidansu. Har dare bata sake jin ɗuriyar Gwamna ba. She was totally confused. Kwana biyu suna tare lafiya lafiya amma cikin yini ɗaya komai ya chanja mata. Bata gane wannan chanji ba, bata kuma san mi ya kawo wannan chanjin ba. Ta gama tunanin duniyan nan amma duk abinda ta kamo sai ta ga bai kai dalilin da zai sa Gwamna ya mata haka ba... 19   Asiya tana kishingiɗe akan kujera hannunta riƙe da littafin Jojo Moyes mai suna Me Before You, a zahiri karatu take amma ranta baya ga labarin, kewar mutumin da yanzu ganinsa a TV yafi ganinsa a zahiri take. Ba za ta iya tantance irin damuwa da take ciki akan shi ba. Yana cin abinci? Yana bacci? sau nawa yake murmushi a rana, har yanzu yana tusar Asuba? Mi yake a kwanakin da ba na uwargidansa ba. "Ranki shi daɗe, Ranki shi daɗe" Asiya tayi firgigit ta kalli Uwani da ke risine a gabanta. "Uwani lafiya?" Asiya ta faɗa tana saukar da ƙafafuwanta ƙasa. "Yanzu aka kira daga gate wai wata yarinya tana iƙirarin ita ƙanwarki ce" "Ƙanwata?. Yaya Bello baya nan ne?" "Ina ga, dan Badamasi yace yarinyar duk tsoratar da ita da akayi taƙi tafiya sai rantse rantse take wai ƙanwar Sumayya ce" "Mi tace sunanta?" "Jummala Ale Faruƙ" Asiya ta yi shiru tana tuno waye cikin ƙannenta ake kira da Jummala. Babu wacce ta faɗo mata a rai amma sai ta cewa Uwani a shigo da yarinyar. Da Sumayya na nan ma da ita zata tura ta dubo waye tunda babu wacce bata sani ba cikin 'ya'yan Ale, to bata nan ta tafi makaranta. Asiya ta jingine kai tana ƙoƙarin saita tunaninta wanda har yanzu tafiya yake ga mutumin da ƙarfi da yaji ya mata kane-kane a cikin zuciyarta. Yarinyar da Uwani ta shigo da ita falon Asiya tun daga babban falo taketa ihu da shirirtar ƙauyenci irin ta 'yan ƙauye. Tana sanye da riga da zani na Atampa da suka yanƙwane saboda rashin guga da kuma zaman cikin babban mota. Hijabinta yellow shar dashi har wani wawal wawal yake a ido. Ta rungume jan jakar Ghana-must-go wadda tsabar tsofewa ya fara zare zare, ba wasu kayan azo a gani bane hakan yasa ta cukwuikwuye jakar a ƙirjinta kaman za a ƙwace mata. "Adda Shahidah" hakan data faɗa ya bayyana haƙwaranta da suka dafe da datti har da wani green green ta saman haƙoran wanda yai kama da daɗaɗɗen kuka ne daya samu gindin zama a wajen. "Adda Shahidah Jummala ce, aaf! Jummai, Jumman Delu" Kafin ta gama lissafinta Asiya ta riga taga kamannin 'yan gidansu a jikin yarinyar, datti ne ya maida ta haka amma idan ta sha wanka zata iya fin Asiya ma farar fata. Akwai wata Delu mai Daddawa da Ale ya aura kusan shekaru shabiyar da suka wuce alokacin Asiya ba zata wuce shekara tara zuwa goma ba amma akwai abinda zata iya tunawa game da Delu. Ƙazantar matar ya kai na misƙala zarratin ga sana'ar Daddawa da take babu tsafta sai ya zamana koyaushe gidan yana nan gum idan baka ɗauke kai bama ba zaka iya cikakken minti shabiyar a gidan ba koda kuwa kana sashen Ale ne wanda yake ɗan nesa da nasu ɓangaren. Kwashe kwashen Ale ba irin macen da ba su gani ba a gidan. Delu ga ƙazanta ga kuma masifa. Sau uku tana aure tana fitowa kuma dukkansu babu rabo ciki, sai dai shigarta gidan Ale da watanni uku rabo ya ratsa tsakaninsu. Ta zauna ta haifi Aisha wacce suke kira Jummai saboda sunan mahaifiyar Delu ce. Jummai na da watanni biyar auren Delu ya mutu, sai data tafi ne ma suka san cewa saki na uku kenan aka yi dan haka babu kome. Jummai bata tashi a gidan Ale ba amma takan zo lokaci zuwa lokaci musamman a lokutan Sallah ko kuma idan tayi faɗa da Delu. Abinda Asiya zata iya tunawa akan Jummai shine kusan shekaru uku da suka wuce taje gida ta samu yarinyar ta zo gida. Fulani na mata magana tana mata tsiwa hakan yasa Asiya ta zo ta ɗauketa da mari. Yarinya sai ta kwanta ƙasa tana shure shure wai Aljanunta sun tashi. Asiya ta sa aka ɗauko mata bulala ta shiga zane Jummai ta ko ina, da ta ji wuya ta miƙe garau wai sun tafi. "Waya kawo ki?" Asiya ta faɗa bayan ta ƙarewa Jummai kallo. "motar Ubale na biyo" "Mi kika zo yi? Waya nuna miki nan? An san da zuwanki a gida?" "Kwarankwatsi ko kin koreni ba zan tafi ba. Nima ina son zama 'yar birni irin Sumayye. Ha'an ai ba Sumayye bace kawai ƙanwar matar Gamna" "Bakin ki ne Gamna ai. Ba zaki jawo min masifar Delu ba, gobe zaki koma gidanku" "Delu ta rasu, a gidan Ale nake yanzu" Jikin Asiya yai sanyi. Ba zata iya tuna yaushe rabon da ta saka Delu a idonta ba tun bayan barinta gidansu. Ance ta sake aure a wani ƙauye bayan ta rabu da Ale iyaka abinda Asiya ta sani kenan. "Yaushe Delu ta rasu?" "Cikin Azumin bara" Asiya tayi mata ta'aziyya sannan tace Uwani ta kai Jummai ɗakin Sumayya tayi wanka ta chanja kaya. Bayan tafiyarsu Asiya ta kira Ale dan ta tambayeshi ko yasan da zuwan Jummai. Dama ta addabi 'yan gidan da fitina shiyasa babu wanda ma ya lura ta gudu daga gida idan ba yanzu da Asiyar ke magana ba. Ale dai ya nuna Asiya ta bar Jummai a wajenta tayi kwana biyu ko zata nitsu. "Baba idan na karɓi Jummai gaba sauran 'yan uwanta ma zasu iya cewa zasu bar gida" "Kiyi haƙuri ta zauna a wajenki kafin na sama mata miji" Bata da ƙarfin yin ƙorafi dan haka ta ce masa zata faɗawa Gwamna, idan ya amince shikenan. Bayan wayarta da Ale sai ta gwada kiran numbar Gwamna ko wannan karan zai ɗauka, amma kamar koyaushe har wayar ta gama ringing ba a ɗauka ba. Bata tsaya ɓatawa kanta lokaci ba sai kawai ta tura masa text akan ƙanwarta Jummai ta zo zata zauna da su. Ba a jima ba kuwa ya mata reply da cewa babu matsala. Lokacin da Sumayya ta dawo ta ga Jummai a ɗakinta ihu ne kawai bata kurma ba musamman data ga kayanta ajikin Jumman sannan ga yagaggiyar jakarta akan gadonta. Jummai ta sake tunzurata da cewa "nima na zo cin arziƙi, ai dukkanmu ƙannen matar Gamna ne" Asiya na kitchen tana haɗa abincin dare Sumayya ta shigo fiskarta a haɗe kamar zata yi kuka. "Anty Asiya, wai Jummai ta zo zama damu kenan?" Ko kallon inda ta tsaya Asiya bata yi ba tace "kema ba kina zama dani ba" "Anty Jummai fa na da Aljanu, Wallahi zuwan da nayi hutu kusan kullum sai ta tada iskoki" "Idan sun tashi akwai ayoyin ruqya zan karanta mata su" Sumayya ta ƙara taƙune fiskarta tana hura hanci. "Ki duba cikin kayan da ta zo da shi idan babu na arziƙi ki bawa Uwani taje ta ƙona su. Ki bata kaya guda biyu, zuwa gobe ko jibi zan mata siyayya. Kin san daga inda ta fito dan haka ki koya mata brush da duk abinda ya dace" "Ni kam..." "Zaki wuce ki bani waje ko sai na make ki a wajen" Sumayya ta fice tana ƙunƙuni. Asiya ta yi tsaki. Halayen da Sumayya ta tsiro da su yana bata mamaki, tamkar shigarta Jami'a ya chanja mata tarbiyya. Da yamma lis Queen Bee ta kawo wa Asiya ziyara. Kallo ɗaya ta mata ta shiga ƙorafin ko lafiya?. Asiya ta kauda tambayar da cewa yanayin sanyin garin ne ya sa mata zazzaɓi. Bayan sun gama lissafin kuɗi da kuma wasu chanje-chanje da suke son yiwa shagon Queen Bee ta kawo shawaran chanja sunan shagon daga Halaal salon zuwa sunan Asiya Kachallah. Asiya ta ɓata rai tace " sunana Asiya Faruƙ ki daina jingina min Kachallah domin bada shi za a tasheni ba ranan gobe. I'll always be Asiya Faruƙ Baba aurena bai chanja komai ba" "Na sani Bestie, wai kinga dai tunda kika samu wannan matsayi shagonmu ya ƙara samun ɗaukaka. Kuma a matsayinmu na 'yan boko dan kin amsa sunan Kachallah ai ba komai bane" Kamar dama jira take tayi wannan magana Asiya ta fusata "zai iya saki na any moment from now, idan hakan ta faru zaku maida sunan shagon Asiya Faruƙ ne? Bamu buɗe shagon saboda zan zama matar Gwamna ba. Da matsayina ko babu our business is doing fine, kuma da yardar Allah zamu cigaba da samun alkhairi a cikin sana'ar mu. Bama buƙatar chanja sunan shago, bama buƙatar sunan Kachallah kafin mu samu ɗaukaka. Allah ke ɗaukaka mutum ba..." "Shahidah?" Queen Bee ta kira a ɗan tsorace saboda tsananin ɓacin ran data gani a tattare da Asiya ga kuma kukan da ya ci ƙarfinta har ta kasa ƙarisa kalamanta. "Mi yake faruwa? Kina da matsala da Gwamna ne?" Tayi tambayar tana rungumo Asiya jikinta. "Ya dena kula ni Bahijjah, ya dena shiga harkata, tunda yace na dawo wannan gidan sau ɗaya na sashi a ido, bai iya min magana sai dai yai text. Ban san matsayina a gidan nan ba, ban san mi yake nufi dani ba" Queen Bee ta shiga bata haƙuri har ta samu ta nitsu ta dena kuka. Tana shirin bata shawara. Jummai ta fito da gudu tana ihu. "Lafiya?" Asiya ta daka mata tsawa. Jummai ta miƙa mata hannunta na hagu tana faɗin "Sumayya ta ƙona min hannu" Asiya da Queen Bee suka zaro ido cike da mamaki dan ba ƙaramin ƙonewa yatsunta huɗu suka yi ba. "Mi ta saka miki a hannu?" "Wani abu ne kamar almakashi tace min wai yana miƙar da yatsun mutum shine tace na gwada na gani" "Shahidah ina jin flat iron ne" Queen Bee ta faɗa tana ƙara duba hannun Jummai. "Idan ban sa Yaya Bello ya min maganin Sumayya a gidan nan ba zata samin hawan jini" Queen Bee ne ta shiga ƙwalawa Sumayya kira yayinda Asiya ta wuce da Jummala ɗaki dan ta mata first aid. A tsorace Sumayya ta fito dan bata ɗauka wautan Jummai ya kai harta manna flat iron a hannunta ba bayan taga irin tiririn da yake fitarwa. Lokacin da Sumayyar ke straightening gashinta da flat iron ɗinne Jummai ta shiga yi mata tambayar ƙauyenci, ƙarshe tace mata yana miƙar da hannu ma ta gwada ta gani. Kamar da wasa Sumayyan ta ajiye flat iron tana amsa waya Jummai ta ɗauki flat iron ɗin ta sa yatsunta ciki ta matse kamar yadda taga Sumayya na yiwa gashinta, sai kuma zafin ƙuna yasa ta yarda abin tana ihun zafi. Duk da an cire flat iron ɗin a wuta amma dake be huce ba shiyasa ya ƙonata sosai. Queen Bee ta shiga yiwa Sumayya faɗa kamar zata cinyeta duk dama bata san matsayin Jummai a wajen Asiya ba amma ta ga kammannin jini a tsakaninsu. Lokacin da Asiya ta fito da Jummai Sumayya ta tsugunna ta bawa Asiya haƙuri bisa umurnin Queen Bee sannan ta cewa Jummai tayi haƙuri. "Idan kin yi na gari dan kanki Sumayya. Ke da Jummai matsayi ɗaya kuke a wajena, kuma yadda kike zaune dani babu takuri ba zan yarda ki takura mata ba. Ku wuce ku bani waje" Bayan tafiyarsu Asiya ta riƙe kai tana faɗin wannan kaɗai ya isa ramar dani ba sai matsalar Excellency ba" "Jummai ma 'yar Ale ce?" "Ya zamu yi da Uban da Allah ya haɗamu da shi. Ba dan ta zo gidan bama na manta da ina da ƙanwa Jummai" "Daɗin abin ma dai dukkanku kyaunsa kuke ɗaukowa" "Ni dai Umma na ɗauko" "Wallahi ana ganinki an ga Ale, ke da kin ɗauko gaba ɗaya kyaunsa ma da baturiya zaki zama sak" Asiya tayi shiru saboda Ummanta data tuno. Rashin Uwa babu daɗi. Da Umma na nan da ko zuwa gida tayi ta kalleta za ta samu sassauci cikin lamurranta. Maganar Gwamna da Queen Bee ta sako ne ya kauda hankalin Asiya daga tunanin Umma... *** Mutane da dama su kan ɗauka cewa ƙarfin iko ko mulki kaman kuɗi yake. Idan kana da shi ƙaruwa zai yi ta yi domin kuwa zuciyarka ba zata taɓa nitsuwa da kaɗan ba kullum cikin nema zaka kasanca. Bilkisu Kachallah ta fara ganin tasirin zobenta sai dai juya mutum uku kacal bai isheta ba, chan cikin zuciyarta tana neman iko akan duk wanda ta ga dama. Hakan ne ya sa ta matsawa Malamanta na ƙasar India dana ƙasar china akan a ƙara mata ƙarfin mulki, tana so duk wanda zai yi jayyaya da ita daya tunkareta to tsoro da firgici ya hana shi magana. Shirye shiryen bikin naɗin Gwamna Bilkisu ta saka gaba, bata da lokacin 'ya'yanta kona mijinta, so take ta haɗa inauguration party da babu wanda ya taɓa yi a ƙasar. Ba tada matsalar kuɗi dan haka komai da take shirin yi sai ya fito da sunanta a tarihin jahar dama ƙasar gaba ɗaya. Abun daya sake ɗauke mata hankali shine batun wani kasuwanci da take son farawa. Dake yanzu babu wani sirri na Yallaɓai da bata sani ba shiyasa data fahimci yana cinikin makamai ana kaiwa ƙasashen maƙota da suke yaƙi hakan yasa itama tayi shawaran zuba jari a ciki. Babu tunanin illar hakan a ranta sai dai kawai miliyoyin daloli da ta ke hangowa idan komai ya tafi dai dai. Sannu a hankali wanda suke kusa da Gwamna suka fara fahimtar akwai lauje cikin naɗi domin, mafiya lokuta yana sako zancen zai yi shawara da mai ɗakinsa wanda kuma sun fahimci Bilkisu Kachallah yake nufi. *Assalamu Alaikum. Bani da bakin bada haƙuri amma duk da haka Dan Allah ku yafe min. Na so ƙarisa part two ranan sallah ko washegarin Sallah amma Allah bai bani iko ba. Yanzu ma zan nemi afuwarku domin update zai zo jifa-jifa ne har sai na gama exams ranan 14 August Insha Allah. Final exams ɗina ne dan Allah ku yi haƙuri i have to concentrate* Ban yi editting ko ɗaya cikin pages ɗin ba so za a iya ganin kura-kurai na rubutu.   20 Not edited.   Yau safiyar Litinin an tashi da ruwa tun Asuba hakan yasa garin ya ɗau sanyi. A irin wannan lokuta mutum kan so ya kasance cikin bargo dan yaji ɗumi yai barci mai daɗe. A ɓangaren Gwamna Saifuddeen Kachallah yana tsaye a bakin window na ɗakinsa, ta jikin gilashin windon yake ganin yadda ruwan sama ke cigaba da tsalawa kaman da bakin ƙwarya. Tun Asuba ake ruwan kuma har yanzu babu alamar zai tsaya nan kusa. Tsawa da walƙiya aka tsala wanda ya dawo da hankalin Gwamna daga nisan kiwo da yai. Zuciyarsa ta tafi ne ga kyakykyawar surar daya gani a jikin gilashin tana masa murmushi, cikin kwanakin nan yana kewarta irin kewa na fitar hankali amma ya rasa dalilin da yasa zuciyarsa ta kasa yunƙurin zuwa gareta. a ranakun da ya je chan gidansa baya nemanta, sau ɗaya da ta je gareshi kuma bai bata fiska ba, bai saurareta ba ƙarshe ma sai ya sakata hawaye domin tsawa ya daka mata akan ta fita daga ɗakinsa. Taya mutum zai yi kewar abar sonsa sannan ya kasa isa gareta. Taya zuciya da gangan jiki zasu so kasancewa da masoyiya amma idan hakan ta faru sai zuciya ta shiga ƙunci? Ya furzar da iska yana mai sake kallon gilashin dake gabanshi, sai dai wannan karan saukan ruwan sama yake gani ba wai fiskar Asiya ba. Yau Asiya ta tashi ne da matsananciyar zazzaɓi. Tun ranan da Gwamna Saifuddeen ya daka mata tsawa ya koreta a ɗakinsa ta kamu da wannan zazzaɓi, maimakon yadda kwanaki suke tafiya jikinta yai sauƙi sai ma komai ya sake lalacewa, ga kuma matsalar Sumayya da Jummai kullum cikin faɗa suke, tayi alƙawarin ba zata raba musu ɗaki ba, idan ma zasu ci kansu ne to sai dai su ci. Tunda tayi sallar Asuba ta duƙunƙunu cikin bargo tana rawan ɗari. Kusan ƙarfe goma na safe Jummai ta shigo ɗakinta. Bata ji shigowarta ba har sai da ta hawo gadon ta fara taɓata. "Adda Shahidah Gamna ya zo, Gamna ya zo" "Miye haka zaki cika min kunne da ihu" "Wallahi na ganshi, dogo ne kaman Dogo mai nama na ƙasan layinmu. Ya min wani turanci ban gane ba nace masa Yas Yas Jummala Ale Faruƙ" "Bakinki ne Jummalan ai. Matsa ki bani waje" Miƙewa tayi ta wuce banɗaki. Shawaran Queen Bee take son gwadawa. Duk abinda yake faruwa harda laifinta a ciki. Data bashi haƙƙinsa ƙila wannan ba zai faru ba. Wanke fiskarta tayi ta fito saboda ta san bai daɗewa a gidan, kar ta tsaya wanka ya tafi. Hangame baki tayi ganinsa tsaye a ɗakinta. Shi ɗin ne dai da take mararin gani iya tsawon lokacin nan. Shima ƙura mata ido yai yana bin ilahirin jikinta da kallo. Rigar barcinta mai laushi ne daya tsaya mata dai dai gwiwa, rigar kalar ƙwai da aka kaɗa wannan yasa ya dace da fatar jikinta. "Ex Excellency" "Dadda bata da lafiya, kije ki gaisheta" Ya faɗa a hankali. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta matso inda yake ta kamo hannunsa tace " tana Asibiti ne?" Haɗuwar hannunsu ya motsar da zukatansu duka. Bai iya taɓuka komai ba har ta saita fiskarsu sannan ta fara kissing ɗinsa a hankali, a nashi ɓangaren wani kewarta ne ya ziyarce shi hakan yasa shi jawota jikinsa sosai ya shiga shafa ko'ina na jikinta. Bata san ya aka yi suka kai gadonta ba har ma ya shiga ƙoƙarin rabata da rigan jikinta sai kuma komai ya tsaya chak. Kaman wanda aka tsikara ya tashi a kanta ya fice daga ɗakin, tsabar sauri har sai daya buge kansa da gini dan ƙofar ɗakinma bibbiyu yake gani. "Ya Salam! Minene a jikina ne?" Asiya ta faɗa tana shinshina jikinta. Ƙarfe biyar na yamma ta kira Halima Kachallah ta tambayeta wani Asibiti aka kai Hajiya Dadda. Zuwa ƙarfe shida ta isa ɗakin da aka kwantar da tsohuwar. Dake ɗakin a cike yake da 'yan dubiya bata wani jima ba ta tafi. Washegari da safe sai ga kiran Abba wai ta yiwa Gwamna godiya ya biya masa Hajji na wannan shekaran. Kaman haɗin baki ko awa ɗaya ba ayi ba Ale ya kirata wai yana hanya zai zo godiya Gwamna ya biya masa kujerar Makkah. Da Ale kaɗai ya biyawa sai ta yi tunanin ko roƙonsa yai amma kuma wannan ya nuna ra'ayin kansa ne ya biya musu. Abin ya ɗaure mata kai dan bata san ma'anar hakan ba. Yana gudunta amma kuma yana ƙoƙarin yiwa iyayenta irin wannan Alkhairi. "Anty Asiya ki yiwa Jummai magana, sau biyu ina saka sabon MaClean a banɗaki tana shanyewa" "Ki gaya mata abin wanke baki ne ba na sha ba" "Wallahi na gaya mata amma ta ƙi denawa" "Kira min ita" Bayan fitan Sumayya daga ɗaki Asiya ta maida hankalinta ga zane da take yi a jikin baƙin masking tape wanda za a ɗaurawa wata Amarya gobe. Idan har babu aikin da za ta yi a gidan gara ta koma sana'arta na da. Akwai ma wani offer da aka bata na aiki wanda article ne zata dinga rubutawa amma bata karɓa ba saboda wanda ya ajiyeta a gidan bai saurareta ba balle ta masa maganar. Kaman daga sama ta ji muryan Junior yana ƙwala mata kira, tana miƙewa ya shigo ɗakin da gudu yana dariya. "Juni Juni kai ne ka girma haka?" "I miss you Anty" ya faɗa yana ƙara shigewa jikinta. Sallamar Mahira da Nana yasa ta ɗaga kai da sauri har lokacin fiskarta ɗauke da murmushi. Ba ƙaramin daɗin ganinsu ta yi ba. Haka suka wuni tare suna hira, ƙarshe dukkansu suka shiga kitchen suka tayata girki. Ma'aikatan gidan suka ja gefe suna mamakin yadda yaran suka sake da Asiya. Lokacin da Bilkisu Kachallah ke zaune a gidan bata taɓa shigowa kitchen dan ta dafa wani abu ba balle har ta shigo da yaran su tayata aiki. Abin gwanin sha'awa dan har Junior sai da aka bashi aikin mummula meatballs kafin aka zo aka soya su. Lokacin da aka haɗu ana cin abinci suka dinga dariyan shiriritan Jummai, magana ɗaya tayi sai kaga sun kwashe da dariya wai hausanta abin dariya. Zuwan yaran yasa Asiya ta samu walwala ta sake sosai kamar bata da wata damuwa a ranta. Basu bar gidan ba sai dare bayan sun yi sallar Isha. Shi Junior ya so su kwana ne ma amma sanin halin Mommynsu yasa dole suka tafi.   *** Washegari da safe misalin ƙarfe tara sai ga wasu mata biyu sun zo wajen Asiya. Bata san su ba amma yanayin shigarsu ya nuna mata cewa su ɗin manyan mata ne. Bayan sun gaisa sai suka fara wani batu daya ɗaurewa Asiya kai. Wai su daga ƙungiyan mata suke, suna so ta shiga ƙungiyarsu saboda su bata kariya daga Bilkisu Kachallah dama duk wani wanda zai so takata. "Ban gane zaku bani kariya ba?" Baƙar cikinsu ta sassauta murya tace "wai baki da masaniyar cewa an ajiye ki a nan ne saboda baki da wani amfani? Ko ba kya jin abinda ake faɗi a gari" Ganin idon Asiya ya buɗe na mamaki sai ta cigaba " Bilkisu Kachallah ke juya Gwamna" Da ta lura maganar yai wa Asiya shigar ba zata sai ta cigaba. "Mun san ba haka ta zauna ba shiyasa muke so ki shigo cikinmu mu baki kariya. Idan kina tare da mu babu abinda zai gagareki a jahar nan domin..." "Idan har na fahimce ku so kike na shiga ƙungiyar ku ku bani kariya daga Bilkisu Kachallah ko?" Ɗaya matar, fara 'yar duma-duma ta ce "bayan kariya, zaki samu ki juya mijinki yadda kike so. Muna tareda matan Gwamnoni da kuma..." "Ban katse ki ba Hajiya, amma a iya karatuna Allah kaɗai ke kare mutum. Bana tunanin akwai waninsa da zai iya kareni daga wani abu ko da kuwa tuntuɓene. Sannan ni ban san mi ake nufi da juya miji ba, shin maida muciyar tuwo za a yi ne ata juya shi ko ya abin yake?" Matan suka kalli juna. Sun lura raina musu hankali Asiya ke son yi. Sai kuma farar matar tace "ki zauna kiyi shawara da zuciyarki kafin zaman gidan nan yafi ƙarfin ki" Sai da suka miƙe sannan suka ajiye mata card ɗinsu wai ta kira su idan tayi shawara. Asiya ta bi bayansu da kallo, yadda suke iya juya bayansu ma sai Allah dan ba ƙaramin mazauna garesu ba, irin matannane da zaka gani a bikin yarabawa suna chanja ɗaurin zani duk bayan minti ɗaya. "Allah ka raba ni da sharrin mutanen nan" Asiya ta faɗa bayan sun fice daga falon. Ta jima tana alhinin wanɗannan baƙi wanda ko sunansu basu faɗa mata ba har suka tafi, duk dama dai wani abu da suka faɗa ya tsaya mata a rai wato batun Bilkisu da aka ce tana juya Gwamna. Queen Bee ta mata maganar amma ta shashantar da batun saboda ba ta son zargin abinda bata da tabbas a kai. Sai dai kuma a yanzu da waɗannan mata suka yi maganar sai take ganin ƙila akwai ƙanshin gaskiya a batunsu idan ba haka ba taya Gwamna zai juya mata baya lokaci guda haka, miyasa zai guje ta?. Anya kuwa babu wani abu a ƙasa? Tana cikin wannan saƙa da warwara Halima Kachallah ta yi sallama a falonta. Sai data ganta ma ta tuna da cewa ashe yau suka yi zata mata ƙunshi. "Kin san Allah Anty Halima ko yanka cellotape ɗin ki banyi ba" "Ai kuwa yau za a yi ta a gidan nan. Ko sama da ƙasa zasu haɗu ba zan bar gidan nan ba sai an mini lalle, kuma irin design ɗin dana zaɓa za ayi" "Ai kuwa sai dai ki kwana dan maigidan ya hana" "Taɓ! Ai ko Anty Bilkisu ce ta hana sai anyi, balle kuma na san Yayana ba shi da matsala" Asiya tayi dariya sannan kuma suka shiga gaisawa. Bayan sun gaisa ta tambayi jikin Dadda. Minti shabiyar da zuwan Halima Asiya ta kira Jummai ta bata saƙo ta kaiwa Yaya Bello ya kaiwa Queen Bee chan shagonsu. Minti biyu da fitar ta ta dawo da gudu tana haki wai Aljanu sun taɓa Yaya Bello. Asiya na jin haka ta san ya sha wani abu kenan. "Da gaske Anty Shahidah Aljanu sun sace masa ƙafa, ga ƙafa a jikinsa amma sai neman ƙafafunsa yake, inaga sun tafi da nashi ne sun saka masa nasu" Takaici ya kama Asiya, yau gashi ƙanwar bayansu ce take tsokalar Yaya Bello wanda da ya yi aure da wuri kaman sauran 'yanuwansa da zai haifi 'ya kamar Jummai. "Anty Shahidah ba za ki je ki masa addu'a ba?" "Ki bawa Inuwa Driver saƙon zai kai min" "Anty Asiya dama maza na samun Aljanu ne?" Halima ta faɗa bayan tayi dariyar abinda Jummai ta faɗa. "Ba wani Aljanu fa, he's jus high ne" "Dan Allah? Barin je na gan shi" Halima da Jummai suka fice daga falon da sauri. Asiya kan ta san ranta ne kawai zai ɓaci idan ta fita shiyasa tayi zamanta. Ai kuwa sun fi minti goma kafin suka dawo, Halima Kachallah har da ƙwalla a ido tsabar dariya. "Kai Anty Asiya kin missing show Wallahi. Kinga yadda yake kuka wai an sace masa ƙafa?" "Sai dai Allah ya shirya min shi. Yaya Bello case ne ai. Akwai wani lokaci shekarun baya tun ina gida Ale ya tara buhuhhunan wake da masara a store zuwa lokacin da zai yi tsada sai ya fitar, kawai sai Yaya Bello ya je ya buɗe store ya kira mutane yana raba musu wake da masara wai an masa wahayi ya fitar da zakkah. Ale baya nan ya tafi kasuwar ƙauye aka kira aka sanar da shi, tsabar ruɗewa gudawa ya fara har suka shigo gari, kafin ya iso an riga an gama raba kaya, store ya koma wayam babu komai. Da Ale ya fara rashin lafiya saboda asaran da yai an ɗauka ba zai yi rai ba" Halima tsabar dariya zama ta yi daɓas a ƙasa tana riƙe ciki tana dariya, tsabar dariya sai da wuyanta ya riƙe. Halima Kachallah bata bar gidan ba sai ƙarfe tara na dare, kafin lokacin Yaya Bello ya warwarewa sarai kaman ba shi yake ta hauka da rana ba. Tsabar rigima Halima ta ga ce ta gaji wai Asiya ta sa Yaya Bello ya kaita gida ba zata iya tuƙi ba. A cikin motar kuwa ta dinga tsokalar Yaya Bello tana masa dariya tun yana sharewa har abin ya fara bashi haushi, dariya ya ƙi ci ya ƙi cinyewa akan abu ɗaya. Lokacin daya sauketa a ƙofar sashensu ta kalleshi tace " idan gobe an sace maka ƙafa ko hannu ka kira ni zan haɗaka da cousin ɗina lawyer ne zai ƙwato maka haƙƙinka" Ya bi wayar da ta miƙa masa da kallo. Ya sani so ta ke ya sa mata numbarsa amma abu biyu ya ɗaure masa kai. Na farko tunanin matar aure ya ke mata, na biyu kuma shi bai iya amfani da babbar waya ba. Ganin ya ƙi amsar wayar sai ta ce " ka bani wayarka na sa maka number na" Ganin ta dage sai ya fito da ƙaramar wayarsa daga aljihu ya miƙa mata ta amsa ta sa numbarta ta flashing numbar. Da ya isa gida ko fitowa daga mota bai yi ba ya ga shigowar kira. Yana ɗauka ya ji ance " ka taɓa ƙafafuwanka suna nan ko an sace?" Ya ɗan haɗe rai kamar tana ganinsa yace " suna nan" Halima ta kwashe da dariya, sai da ta yi mai isarta kafin tace "Sai da safe Yayanmu" Ƙarfe huɗun Asuba Halima Kachallah ta kira Asiya ta sanar da ita rasuwan Dadda. Duk da tsohuwar ta ja miya amma hakan bai hana Asiya jin mutuwar a jikinta ba. Da safe ƙarfe shida da rabi a Kachallah house ya mata. Ƙarfe tara na safe za ayi jana'izarta amma tun ƙarfe bakwai gidan ya fara cika. Mutuwar Dadda ya girgiza Gwamna Saifuddeen Kachallah. Dadda ita Kaka ce sannan Uwa a gareshi, duk wani tarbiyyan da zai tinƙaho da shi to kaso saba'in ciki ya samo daga Hajiya Dadda ne. *** Ranan da Dadda ta rasu mashahurin marubucin nan KaSaSa ya rubuta waƙoƙi guda bakwai saboda tunawa da Hajiya Khadijah Kachallah. Asiya bata samu karanta waƙoƙin ba sai bayan kwanaki huɗu da rasuwan. Wani abu ne ya ɗaure mata kai bayan ta karanta waƙoƙin, kamar akwai alaƙar jini tsakanin marubucin da kuma Hajiya Dadda. Idan har haka ne to KaSaSa zai iya zamowa ɗaya daga cikin jikokin Dadda. Ba daɗi ta kira Halima Kachallah ta shiga yi mata tambayar ƙwaƙwafi kwanaki kaɗan bayan rasuwan kakarta da take matuƙar so. Dan haka sai ta bar zancen a ranta zuwa wani lokaci... 21 Not edited.   A ofishin NDLEA na Abuja kuwa Agent Maryam Dahlia Aliyu ce ke ta tiriri saboda wani batu daya taso ake son rufewa. "Ban gane za a dakatar da binciken nan ba. DEA suna da interest akan wannan case, miyasa za a ce a rufe shi. Ina buƙatar mutumin da BBC eye ta yiwa interview" Kallonta kawai suke yi saboda abu ne da ba zai yiwu ba domin kuwa daga sama aka aiko akan a rufe file ɗin. "Ba kallona zaku yi ba, i need answers" Wani dogo a cikinsu ya sassauta murya yace "Gwamnati ba zata saka hannu a binciki Matar Gwamnan jahar Congo ba" Agent Dahlia ta ƙura masa jajayen idonta tana mamakin kalamansa, chan kuma ta furzar da iska sannan tace " inaga ka manta cewa ni ɗin Gwamnatin America nake yiwa aiki ba taku Gwamnatin ba. My country does not take shit" Ta kalli sauran jami'an dake wajen ɗaya bayan ɗaya sannan tace " mark my words, sai na kai matar Gwamnan jahar Congo kurkuku" Daga fitanta daga ɗakin taron aka shiga tattauna yadda wannan iƙirari nata ba zai zamo gaskiya ba, a wani ɓangare kuma suna tsoron fushin Gwamnatin America idan wani abu ya samu jami'arsu.   *** Bilkisu Kachallah ta sake kallon documentary na BBC eye a karo na uku, chan cikin zuciyarta tana ayyana wani abu mai girma wanda zai iya girgiza jahar Congo sannan ya ƙarawa Gwamna Saifuddeen Kachallah farin jini. "What if she goes to jail?. Wannan zai zama sakamakon amsa sunan matar Gwamna da tayi iya tsawon waɗannan watanni" Da tayi maganar kuma sai ta fashe da dariya musamman da idonta ya hasko mata Asiya cikin kayan firsina. "And the uniform will suit her, hahahaha" ta cigaba da dariya har sai da Junior ya farka daga bacci a firgice. Ganin mahaifiyarsa na irin wannan dariyan sai abin ya bashi tsoro, dama tunda tace idan ya sake zuwa wajen Asiya zata bari macijinta ya sare shi yake matuƙar tsoronta. *** Wannan ne karo na farko da zata je gidan Ubayd tunda yai aure. Ba zai kyautu taji Salma tayi ɓari har an mata wankin ciki sannan ta ƙi zuwa dubiya ba. Tareda 'yanmatanta ta tafi wanda har a cikin mota sai da suka yi faɗa saboda kowa na son zaman window ƙarshe dai Jummai ce ta zauna a tsakiya bayan Asiya ta daka musu tsawa. Sun samu Inna Yaha a wajen dan dama ita da Umma Hussaina suke karɓa karɓa wajen kwana da Salma a Asibiti kafin a sallamota. Sun samu Salmar na barci dan haka basu jima ba suka fito. A dai-dai bakin ƙofa suka haɗu dUbayd yana ɗauke da wasu manyan ledoji. Da ganinsa kaga magidanci dake cikin kwanciyar hankali, ta jima bata ga Ubayd ba amma duk da haka zata iya rantsewa cewa ya chanja sosai a yadda ta san shi, yayi naman wuya, ga kumatunsa da suka cicciko suka yi ɓulɓul da su. "Asiya" "Ina wuni Ya Ubayd" Asiya ta faɗa tana ƙoƙarin tare wani abu daya taso mata daga ƙasan zuciyarta wanda ta san Shaiɗan ne ke ƙoƙarin kitsa mata wani abu daban. Gashi dai tana auren Gwamna amma bata da ko kwatan kwanciyar hankalin da Salma ta samu a tattare da Ubayd. "This was suppose to be my house" ta faɗa a zuciyarta dai dai ta matsa masa dan ya shigo falon. Ta bi bayansa da kallo lokacin da yake amsa gaisuwan Sumayya da Jummai. Kafin yanzu, ta taɓa shigowa cikin gidansa lokacin ana kan aikin gini. Tsarin gidan gaba ɗaya ya tafi ne da ra'ayinta. Saboda tun daga planning Ubayd yake tambayarta wani irin gini za a yi? Mi za a sa mi za a cire? Daga ƙarshe gida ya zama na Salma. "Har za ku tafi Asiya?" "Mun daɗe da zuwa ai, akwai inda zamuje daga nan" "Shikenan, mun gode. A gaishe min da Excellency Dan Allah" Wani kallo Asiya ta masa wanda yasa shi fahimtar maganar da yai bai mata daɗi ba. Kafin yai wata maganar ta fice daga falon. Gidansu Queen Bee da take son zuwa ma fasawa tayi saboda ranta babu daɗi. Da suka je gida ɗaki ta shiga ta kulle ƙofa ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta. Ita ne ya kamata tayi irin wannan chanjawar da Ya Ubayd yai, ita ne ya kamata tace "Excellency yace na isar masa da gaisuwa. Allah ya kawo wani rabo mai albarka" Ta kalli fiskarta da kyau ta ga yadda idanuwanta suka yi wuri-wuri da su kaman an kama yaro a kitchen hannu nasha-nasha da miya da kuma naman daya ɗauka a tukunyar miya da dare bayan koya yayi bacci. Fiskarta ya koɗe, hatta foundation data shafa bai iya ɓoye koɗewar da fiskarta yai ba. Rashin bacci ya haifar da ƙaton jaka mai tudu a ƙasan idanunta. Asiya ta cire mayafin dake kanta gashinta ya bayyana. Gashin yai buzu-buzu da shi irin yadda masu kinky hair ke tashi daga bacci idan sun kwana da tsefaffen kai babu hula ko ɗankwali. Kenan wannan Ya Ubayd ya gani? Ta faɗa bayan ta gama nazartar fiskarta. Dole ne ma yace ta gaida masa Excellency ai. Asiya-Shahidar da ya sani watanni takwas da suka wuce ba itace wannan ta jikin madubin ba. 'Yar gata 'yar ƙwalisa mai faran-fatan da jama'a, wannan kuma fayau kamar fatalwan cikin film. Minene aure idan babu kwanciyar hankali? Minene aure idan za ayi dare har gari ya waye ba ka ji ɗumin mijinka ba? Minene aure idan mijinka ya zamo tamkar wata a sararin samaniya, sai dai ka kalleshi daga nesa amma ba zaka iya isa gareshi ba?. Minene aure idan ba zaka iya kiran mijinka ka ji muryansa ba balle kuyi taɗi ko ku tsokani juna ayi wasa a dara? "Anty Asiya. Anty Asiya" Muryan Halima Kachallah ya dawo da Asiya daga tunanin da take. "Anty Halima ke ce agidan namu?" Asiya ta faɗa tana murmushi bayan ta buɗe mata ƙofa. "Ba dole ba, yaushe rabonki da hawa online? Na tura miki saƙo sun fi arba'in amma ba ki duba ba" "Yi haƙuri Antyna ni ɗin ce yanzu sai a hankali" Bayan sun zauna Halima ta kalli Asiya tace "ni kam lafiyar ki kuwa? Ko dai za a yiwa Junior ƙani ne?" Asiya Shahidah tayi murmushin yaƙe wanda sai da ƙwalla ya zubo mata a ido ɗaya. Ina dai sai an taɓaka za ka samu ciki? Tayi saurin shafe fiskarta da hannu biyu kafin Halima ta lura da hawayen daya zubo mata. "Wani zance ne latest?" Asiya ta faɗa tana buga kafaɗar Halima. "Ina addu'ar da kika bani lokacin da zan tafi seminar ɗin nan?" "Uhm?" "Akwai wani mentor ɗinmu daya min magana" "Alhamdulillah! Kice Anty Halima mun kusa cin shinkafa" "Idan Hajiya ta bari ba" "Miya faru?" Halima ta sauke ajiyar zuciya sannan tace " Albino ne, na yiwa Hajiya maganar tace sam bata yarda ba. Inaga Anty Bilkisu ce ta zugata dan da farko ta min fatan alkhairi daga baya kuma tace wai ba ta yarda da haɗa zuri'a da Albino ba. Tell me Asiya su ɗin ba mutane bane?" "Sosai Halima. Suma mutane ne" Sun jima suna taɗi kafin Halima ta tafi bayan Asiya tace ta cigaba da addu'a. Tun lokacin kamfen suka ɗinke da Halima Kachallah, ƙaunar da babu tsakaninta da 'yar uwarta Bilkisu shine ya shiga tsakaninta da Asiya. A ɓangaren Asiya tausayin Halima take saboda a rayuwarmu ta yau ba abu ne mai sauƙi ba ga mace ta kai shekara talatin da biyar a gidansu babu aure. Dole ne ta fuskanci tsangwama da zunɗe a wajen mutane. *** "Sadaka maganin musiba da bala'i, Sadaka yana kauda fitina, Sadaka yana kawo alkhairi" Jummai ta maimaita kalaman da taji a cikin mafarkinta. Bata fiye mafarki ba amma idan tayin kaso saba'in cikin ɗari yana zama gaskiya. Sati uku kafin rasuwar mahaifiyarta Delu sai da ta jera kwanaki uku tana mafarkin rasuwan. Da farko bata gayawa Delun ba sai da ta yi na biyu sannan ta sanar da ita. Dariya Delu tayi ta banzatar da zancen da cewa Aljanunta ke son ɗaga mata hankali, ita kam tana nan da ƙarfinta sai ta tsufa kamar Ayya ta ƙauyen mahaifinta wanda ake cewa sai da ta shekara ɗari da talatin kafin ta rasu. A madaidaicin dinning set na falon Asiya Sumayya ce da Jummai ke faman karyawa. Masu aiki ne suka yi girkin hakan yasa aka jera abinci har kala uku a gabansu duk da kuwa Asiya ta hana almabazzaranci. Shayi da biredi, dankali da soyayyan ƙwai sai kuma pepper soup noodles wanda Sumayya ce ta shiga kitchen ta bada umurnin a dafa mata shi. Kota ina toothpaste ya zo dinning ɗin?. Sumayya ta ɗago kai sai ta ga Jummai na matsa MaClean akan biredi, ta zuba mata ido tana kallon ikon Allah. Jummai ta haɗe biredi ta fara turawa baki tana ci tana korawa da shayin dake gabanta. Allah kaɗai ya san inda Ale ya samo tsatson su Delu. Sumayya ta faɗa a ranta ganin 'yar uwartata har yanzu da ta shafe sati biyu a gidan bata fara nuna alamun zata waye ba. "Dama da Maclean kike cin bread?" Ta tambaya dai dai lokacin da Jummai ta sake matsawa akan sabon slize na bread data ɗauka tana baza maclean ɗin akan bread ɗin da yatsarta manuniya. "Yo kince na goge baki da shi. Alƙur'an zaƙi gareshi har da ƙanshin citta da yaji-yaji a ciki, shine nake cin biredi da shi, ai kema kina saka wani jan abu akan naki biredin wani lokaci" " 'yar ƙauye, jam nake sawa ba toothpaste ba, jam Jummai." Tayi maganar da ƙarfi kaman zata bugeta. "Ki mata a hankali mana 'yar Birni. Daɗin abinma dai dukkanmu daga ƙauyen muka fito" Asiya ta faɗa tana zama a kujerar dake fuskantar ta Sumayya. Ganin bowl ɗin dake gaban Sumayya da kuma sauran abincin dake kan table ɗin sai ta ƙwalawa Uwani kira, duk da chan ƙasan ranta bata son yi mata irin wannan kira saboda Uwani ta girmeta. "Ranki shi daɗe an fito" "Uwani ba nace kada a dinga girki ya wuce biyu a gidan nan ba sai dai idan da baƙi? " "Na riga nayi wannan ɗin kafin Sumayya tace zata ci indomie peppersoup shine na ɗibi peppersoup ɗin da kika yi jiya na mata da shi" Asiya ta kalli Sumayya sannan ta kalli Uwani ta ce "banda Man shanu babu abinda Sumayya bata ci, daga yau idan kin yi girki kada ki sake karɓan order ɗinta. Idan tana son cin wani abu ta gaya miki kafin ki fara girki, idan ba zata iya cin abin da aka girka ba ta haƙura da cin abincin" Sumayya ta tura bowl ɗin gabanta gefe tana tura baki ta miƙe zata bar wajen Asiya ta daka mata tsawa "zauna!" Bayan Uwani ta bar wajen Asiya ta kalli Sumayya rai a ɓace tace "dan kina zaune a gidan nan ba zaki dinga min iskancin da kika ga dama kuma na zuba miki ido ba. Ko ni da nake matar gidan kin ga ina wannan almabazzaranccin? Bana son rashin godiyar Allah Sumayya" "Ni dai kawai kice kin gaji dani a gidan nan. Dan nace kawai a dafa min indomie shine sai kin min gori" "Ungo naki dake da indomie. Uwani sa'ar ki ce da zaki shiga kitchen kina bata umurni? Ko kuma munyi da ke zata dinga yi miki bauta?" Ta kalli Jummai dake zazzare ido tace " idan na sake gani kin sha Maclean sai na sa Yaya Bello ya zubar miki da haƙora. Tukunna ma kin aske hammatarki?" Jummai ta maƙe kafaɗa tana wiki-wiki da ido. Tun kwananta uku a gidan da Asiya ta lura da hammatarta ta bata shaving stick ta mata bayanin yadda zata yi amfani da shi. "Kin aske?" "Kwaranƙwasi tsoron askar nake, ji nake zata kwashe min fatar hammata" Takaici yasa Asiya ta hangame baki, chan ta girgiza kai tace " idan kin gama cin abinci ki sameni a ɗaki" "Now, ku saurareni da kyau domin sau ɗaya zan faɗa ba zan maimaita ba. Daga yau babu mai aiki da zata sake gyara muku ɗaki, ku dinga karɓa-karɓa kuna gyarawa tsakaninku, sannan na yiwa Queen Bee magana zaku fara aiki a salon ɗinmu. Ke Jummai tunda kin iya kitso zaki dinga yi a chan, idan kin fita da safe sai ƙarfe uku ki dawo ki wuce Islamiyya. Idan za a shiga sabon term sai na saki a makaranta" Ta maida dubanta ga Sumayya tace "inada timetable na classes naki dan haka bana son ƙarya. Duk lokacin da baki da lectures ki wuce Halal Salon kije su koya miki aiki idan anyi hutu kuma ɗinki zaki fara koya" "Anty Asiya ɗinki kuma?" "Yes ɗinki" Har aka ƙare cin abinci babu wanda ya sake magana. Sumayya ce ta fara miƙewa ta bar wajen dan dama abincin ya riga ya fita a kanta tunda Asiya ta dizgata a gaban Uwani, ta ƙarisa ci ne kawai saboda Asiya tana wajen. Tana kwance kan gado Asiya ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da sabon shaving stick. "Ina Jummai?" Sumayya tayi banza da ita kaman bata jita ba "Ba tambaya nake miki ba?" "Bata shigo ba" Asiya ta ja tsaki ta fice daga ɗakin. A falo ta samu Jummai ta zauna gaban TV tana kallo. Zuwa tayi ta kashe TVn sannan tace "muje" babu musu Jummai ta bita jiki a sanyaye dan har ga Allah tsoron shaving stick ɗin take. Lokacin da suka shiga banɗaki kallo ɗaya Asiya ta yiwa gashin daya cika hammatar Jummai tana mamakin yawansa kaman cikin sati biyu data yi dasu ya ƙara cika kaman an cukwuikwuye baƙar leda an manna a wajen, idan ta sauke hammatar kana iya ganin gashin ya firfito har ta gefe gefe. Allah ne masani, amma tana tunanin a tarihin rayuwar Jummai bata taɓa cire gashin hammatarta ba. Ba tareda ƙyanƙyami ba ta aske mata gashin tas sannan ta ce ɗauko shaving cream a banɗakin ta matsa tace ta ɗaga mata rigarta. Bata amfani da shaving stick a ƙasanta saboda yana sa mata ƙuraje. "Wayyo na shiga uku! Adda Shahida mi zaki sa min a..." "Ungo naki" Asiya ta mata daƙuwa. Bayan ta gama gyara mata wajen ta barta a banɗakin akan tayi wanka. Still sai da Jumman tayi ƙunƙuni wai ai tayi wanka da sassafe. Lokacin da Asiya ta fito waya Sumayya take, yadda take murya ƙasa-ƙasa babu tantama da namiji take magana. Asiya ta girgiza kai ta fice daga ɗakin, ita yanzu fargabanta ma Jummai ce kar zamanta da Sumayya ya sa ta kwaikwayi halinta, ga ita nan ko shekara shabiyar bata kai ba. Allah dai ya bata ikon kula da amanar su Amin, da wannan ta shige ɗakinta. Da yamma lis Asiya ta kira Jummai akan ta mata kitso. Yadda gashin baya samun gyara gara kawai ta kitsa shi ta huta. Da aka fara kitson ne kuma Jummai ta faɗa mata mafarkin da ta yi jiya da dare tareda cewa shi mahaukacin data gani yace Asiya tayi sadakan kaji. "Ba sadakan kaji ba sadakan giwaye zan yi" "Allah mahaukacin cewa yai kiyi sadaka har waƙa ya dinga yi yana cewa..." ta karkata baki zata rera waƙa Asiya ta katseta "Kar ki yadda ki kawo min zancen Aljanunki na ƙarya dan duka zaki sha a wajena" Duk da Jummai ta sa wasa a abinda ta faɗa amma tabbas mahaukacin data gani yace tayi sadaka amma bai faɗi da minene ba ita ce ta ƙara nata gishirin. "Adda Shahidah Wallahi yace ayi sadaka amma nina ce ayi da kaji tunda kullum sai an yanka a gidan nan" "Jummai ƙarisa min kitson nan inada abin yi" Jummai tayi shiru da maganar amma gaskiya mafarkin ya tsaya mata a rai. Da farko ma bata yi niyyar faɗawa Asiya ba amma baccin da ta yi da rana sai ta sake wannan mafarki sai dai wannan karan ba a ce ayi sadaka ba sai dai yadda aka sakawa Asiya ankwa aka shigar da ita gidan yari a mafarkinta na jiya haka ta sake gani a mafarkin da ta yi da rana. Koma minene gaskiya tana fata babu wanda zai zo ya kai Adda Shahidarta gidan yari... 22 Not edited.     Matar dake gaban wani ƙaramin maciji mesa ta ajiye wata ƙaramar ƙwarya a gabansa, mesar wanda yake baƙi ƙirin da shi ya kafa kai ya shanye ruwan nonon da ke cikin ƙwaryan tas. Sai ta yi kwana ashirin da ɗaya tana bashi ruwan nono kafin ta fara bashi irin abincin daya dace da halittar shi. Ta shafa kan mesar a hankali tace "well done baby" *** Plan na yadda komai zai kasance ranan inauguration tun daga safe har dare Bilkisu Kachallah ta nunawa mahaifinta. Sai dai ransa ya matuƙar sosu da abinda ya gani. Na farko ba a jima da yi musu rasuwa ba, sannan idan har aka yi yadda Bilkisu ta tsara to duniya zata zage su da yin almabazzaranci ba zai so Saifuddeen ya buɗe tenure ɗinsa da irin wannan ɓarnar kuɗin ba. "Bilkisu ya kamata ki adjusting event ɗin nan, mutane za su yi magana" "I don't care, abinda na ke so kenan kuma shi za a yi" Kamar wanda aka ɗaure harshensa haka ya haɗiye duk wani ƙorafin daya taso daga cikinsa bai iya furta mata komai ba sai gyaɗa kai kawai da yai. Daga wajen mahaifinta gidan Yallaɓai ta wuce domin ya aiko mata da saƙo akan yana son ganinta. "Ban gane na dakatar da abinda nayi niyya ba. This is what i want and nobody can change that" Bilkisu ta faɗa a fusace, cikin 'yan kwanakin nan Yallaɓai yana mata taurin kai kafin ya amince da buƙatarta sai ya kawo ƙorafi wanda Saifuddeen da mahaifinta basa iya yi. Anya kuwa Yallaɓai ya zauna haka? "Tura matar Gwamna kurkuku ba abunda zai kawo sai rikici da tashin hankali. Nothing good will come out of this" "Babu rikici a cikin wannan lamari sai ɗaukaka. Idan Gwamna ya tura matarsa kurkuku zai amsa sunan adali, duk wani abu da zai yi musu na zalunci the fools will still praise him" "Ba zan bari ki aikata wannan ba, ba zan bari ba. You will ruin him" Ƙirjin Bilkisu ya buga da ƙarfi saboda jin kalaman Yallaɓai, anya kuwa zoben hannunta na tasiri a kansa? Ta dai san babu wani doka data taka cikin dokokin da aka bata to mi yasa haka? Ta dai ƙara gwada sa'arta dan ta tabbatar Yallaɓai bai kufce daga ɗairinta ba, idan ya kufce ta nemi abin yi kafin ya ɓata mata shiri. "Yallaɓai ka kira ka sanar da su su zo su binciki matar Gwamnan Congo Asiya Kachallah sati ɗaya bayan inauguration. She will go to jail Yallaɓai" Yallaɓai yai shiru yana ƙoƙarin yaƙar zuciyarsa daga faɗawa tarkon Bilkisu amma ya kasa. Tun da ya ankara da cewa ya fara bin umurnin Bilkisu Kachallah ya shiga neman mafita sa dai babban malaminsa baya ƙasar kuma shi ɗin ne ya tabbatar masa da zarginsa cewa Bilkisu ce ta ɗaure shi sai dai wanda yai wannan aiki ba ƙaramin babban malamin tsubbu bane dan a tunaninsa idan ba a je an ciro abinda aka jefa cikin teku ba da wuya ya samu mafita. Bai iya sarrafa kansa ba dan ji yake idan bai aikata abinda Bilkisu ta ce ba mutuwa zai yi. Daga ƙarshe dai wayar tasa ya ɗauko ya danna wasu lambobi ya ƙara a kunnensa.   *** Tun saura kwana biyu ayi bikin rantsarwa, manya manyan hotels da gidajen sauƙe baƙi suka fara cika. Baƙi ne ke ta shigowa cikin jahar Congo daga kowanni lungu da saƙo na ƙasar dama ƙasashen ketare. Duk wani artist da ke ji da kansa ya samu halartar wannan biki domin Bilkisu Kachallah ta shirya girgiza kowa da shirin da ta yi. Asiya bata ma yi yunƙurin zuwa wajen inauguration ɗin ba tunda taga duk abinda ake uban gayyar bai sakota ciki ba. Ranan da ta kira dan ta masa godiyar biyawa Ale da Abba kujerar hajji da yai ƙin ɗaukar wayarta yai. Ta yi kwanaki tana nemansa ya ƙi ɗaga wayarta, ko ta'aziyyar Dadda sai text ta masa. She yearns for him, she longs for him, she misses him. Daga ƙarshe zuciyarta, gangan jikinta da ruhinta duka sun zama mallakinsa yanzu kam babu tantama ta san wannan shine gaskiyarta. Ta dage da addu'a sosai musamman da zuciyarta ya fara bata cewa ƙila da gaske ne akwai hannun Bilkisu Kachallah a chanjawar Gwamna Saifuddeen. Sai dai kuma Allah yana amsa addu'ar bayinsa a duk lokacin da suka roƙe shi, zai iya yiwuwa a jinkinta amsar saboda wani dalili mai girma da kai baka sani ba, Allah shine masanin gaibu. Shi ya halicceka shine kuma ya tsara rayuwarka ya kuma san mi ya dace da kai yaushe kuma ya dace ka samu. Asiya ta banzatar da shawaran Jummai na yin sadaka. Mafarkin da ta gaya mata tayi ba yadda da shi tayi ba balle kuma har abin ya dameta... A falo Asiya, Jummai da kuma Sumayya suka zauna suna kallon rantsarwar da ake yiwa Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah. Duk wani motsawar laɓɓansa lokacin da yake rantsuwar yana kan idon Asiya ko ƙyaftawa na dole take saboda tana son ganin duk wani motsinsa. Bayan an gama rantsuwar suka wuce wajen da za ayi inauguration party ɗin wanda tun da sassafe ake ta nuna highlight na yadda aka shirya wajen. Asiya miƙewa ta yi da sauri saboda ganin Bilkisu Kachallah ta riƙe hannun Gwamna tana dariya, shima yana ɗan murmusawa. Kusan ƙarfe goma shabiyu na rana Queen Bee ta kira wayar Asiya. "Bestie ashe Gwamna shine KaSaSa" ta faɗa da muryan da yafi kama da ihu. "Ban gane ba?" "Ba kya kallon TV ne, yanzu Bilkisu Kachallah tace Gwamna ɗan baiwa ne cikin baiwar da Allah ya bashi akwai rubuta waƙa, wai yafi shekara ishirin yana rubutu... yawwa ki kalli tv Dan Allah ya fito zai karanta ɗaya daga cikin waƙoƙinsa" Kafin Queen Bee ta gama maganar ma ta riga ta isa gaban TV da ke falonta inda dama a nan tayi kallo da safe lokacin da ake rantsar da shi. *"Attaruhu"* Gwamna ya faɗi sunan waƙan da zai gabatar, hakan yasa mutane dayawa darawa wanda basa jin Hausa kuwa suka shiga tambayar ma'anar abinda ya faɗa. Sau biyu ya taɓa performing poem a gaban mutane lokacin da yake degree ɗinsa na farko a ƙasar waje. Ɗimbin jama'ar da ke wajen suka zuba masa ido suna sauraron waƙar da zai yi amma sai da yai tsayuwar kusan minti ɗaya bayan ya ce Attaruhu kafin ya fara karanta waƙar. Zuciyar Bilkisu Kachallah ya kai ƙololowar baƙin ciki saboda ba abinda ta shirya ba kenan. Ta bayyana cewa shine KaSaSa saboda abu ɗaya ne kawai, wato ya mata waƙa ya yabeta a idon mutane amma sai ya karanto waƙar da ta sani dan Asiya Shahidah yai. Ta sani harta nambarta a wayarsa ya saving ne da Attaruhu. A da bata ɗauka komai ba amma yanzu kam ko sunan sai ta saka ya chanza a wayarsa. Da ta san waƙar da zai yi kenan da bata bayyana baiwarsa ta rubuta waƙa ba. Gwamna sai da ya ƙara stanza biyu akan asalin waƙar da ya taɓa rubutawa watannin baya, a ƙarshe ya bayyana zuciyarsa tana dokawa ne ga Attaruhu. Yana gamawa aka masa standing ovation aka saka rinƙa tafi raf raf raf saboda ya burge kowa a wajen duk da ma mutanen wajen sun ɗauka waƙa ce kawai yai cikin waƙoƙin daya taɓa rubutawa, amma shi da yai waƙar, Bilkisu Kachallah da kuma Asiya Kachallah sun san wacece Attaruhu. Hawaye fal a idon Asiya har bata ganin TVn sosai ta sa bayan hannunta ta shiga gogewa, amma tana gogewa wani na sake gangarowa. Ta wuce ɗakinta da gudu, tana faɗawa kan gado ta furta kalmomi ma su tsada gareta wanda ko Yaya Ubayd zata iya tuna sau nawa ta furta masa su. *"I love you Excellency. I love you Saifuddeen Sa'ad Kachallah"* Bayan tafiyar Asiya Jummai ta kalli Sumayya tace "ni kan Gamna rawa yai ne naga Adda Shahidah na kuka?" "Ki ji min sharri, rawa kika ga yayi?" "Yo naga sai jujjuya hannu yake yana ta girgiza kai, kuma sai naga Adda ta fara kuka" "Allah ya yaye miki Jummai" Sumayya ta faɗa bayan ta ja tsaki. *** Bikin inauguration ya zama abun faɗa a gari domin kuwa ko'ina ka shiga sai Allah wadarai ake da irin almabazzaranci da aka yi a wajen. Kwana biyu aka yi ana shagalin bikin, kuma duk ciki babu wanda ba ayi baɗala a wajen ba. Ga Asiya, wannan sabon yanayi ya sakata cikin nishaɗi, bata damu da yadda aka yi biki ko aka ƙare ba, all that matters shine Gwamna Saifuddeen shine KaSaSa sannan har yanzu yana sonta. Ta maimaita kallon wajen da yai waƙar Attaruhu ya fi sau ɗari cikin kwanaki biyun nan. A kwana na uku ne kuma CY ya kira Asiya, ya mata wani zance mai tada hankali. BBC eye sun fitar da documentary na masu ciniki da kuma safaran miyagun ƙwayoyi, inda wani mutum da ba a bayyana asalin sunansa ba da kuma fiskarsa ya bayyana cewa yana yiwa matar Gwamnan jahar Congo aiki. Shine agent ɗinta mai shigo mata da miyagun ƙwayoyi ta ɓoyayyiyar hanya. "I know it's not you Asiya, amma kina ganin Bilkisu Kachallah tana irin wannan harka? Could it be saboda Agent ɗin nan tana bincike akanta yasa aka ɓoyeta" "Ban sani ba CY, ina ka samu bidiyon?" "Sun riga sun cire shi a yanar gizo amma na riga na samu videon kafin a sauke shi daga net. I'm having a bad feeling about this, kina ga Gwamna ya sani?" "Ban sani ba CY, amma zan tuntuɓe shi na ji". Bayan yaƙi ɗaga wayarta, office ɗinsa ta kira, Sakatarensa ya ce mata ai ɗazu Gwamna ya wuce Abuja. Asiya ta shiga ruɗu tana tunanin wa kuma zata tuntuɓa da wannan zance. Ƙarshe ta ce bari dai ta bari Gwamna ya dawo. Ko bai zo inda take ba ita zata je inda ya ke. *** "Ina son kujerar Yallaɓai" Lamara Damana ya zaro ido waje da mamaki. "I need it fast, saboda tsohon nan yana so ya bani ciwon kai" "Boss, idan babu Yallaɓai mahaifinki shi zai gaji matsayinsa haka dokan gidan ya faɗa" "Lamara babu ruwana da dokarsu, abinda na sani shine zan zama shugaban ƙingiyar dattawan Congo, akwai kaso mai tsoka Mr Damana. Mi zai faru idan ka amsa sunan Senator Lamara Damana, kafin nan idan na samu kujerar Yallaɓai zan sa shugaban ƙasa ya baka minister shekaru huɗu masu zuwa ka amsa sunan Senator" Lamara Damana ya motsa baki yai maganar da ta saka Bilkisu Kachallah kwashewa da wata shegiyar dariya.     *** Daga bakin gate aka fara hayaniya da jami'an NDLEA da kuma securities masu tsaron gidan Gwamna. Sun nuna za su yi bincike su kuma sun ce sai Gwamna ya bada izini Gwamna kuma baya gari. Fitowar Jami'a Dahlia daga cikin motar ya kawo sulhu domin tana ɗaga badge ɗinta na DEA ta ƙasar America securities ɗin suka shiga rarraba ido. Asiya na ɗaki aka Uwani da Sumayya suka shigo ɗakinta da gudu dan sun tsorata da ganin jami'ai kusan takwas da ke bin urmurnin wata baturiya wacce suke tunanin ita ce Ogan su. Asiya ta fito jiki a sanyaye dan yanzu ta gama waya da Fou'ad Salisu kuma duk akan labarin da CY ya gaya mata ne. "DEA, Maryam Dahlia Aliyu" baturiyar ta faɗa tana yiwa Asiya kallon tsana. Bayan Asiya ta nemi dalilin zuwansu sai jami'ar ta shiga yi mata bayani " mun samu labarin an kawo wasu miyagun ƙwayoyi gidan ki, munada search warrant dan haka ki bamu haɗin kai" Ta sani babu komai a gidan amma kuma haka kawai sai jikinta ya ɗau rawa, musamman da ƙwaƙwalwarta ya fara hasaso mata possibiloties na samun miyagun ƙwayoyi a gidan indai da gaske Bilkisu Kachallah tana safaransu. Dukkan jami'ai takwas suka saka hand gloves a hannunsu sannan suka bazama gidan neman muggan ƙwayoyi. "Ina so ki sani cewa babu abunda zai hana zuwanki kurkuku matuƙar aka samu hujja akan ki. Ban damu da matsayinki ko ina kika fito ba" Minti shabiyu sai ga wasu jami'ai biyu sun fitoda sauri ɗaya daga cikinsu yana riƙe da farar leda ɗauke da farar powder. "We found something" Da Asiya da Agent Dahlia suka shiga rige-rigen zuwa ɗakin Asiyar bayan jami'in ya ce a ɗakin ƙasa aka samu. Cikin akwatunan kayanta guda uku aka dinga ciro wasu lejoji ɗauke da farin powder da wasu abu ƙanana kamar duwatsu. Kallo ɗaya Agent Dahlia ta yi tace "cocaine, meth, fentanyl" sai kuma ta ɗago ido tace " you are under arrest Asiya Kachallah" "Ban san ya aka yi wannan ya shigo nan ba. Ban san wa ya saka a nan ba, ba ni Matar Gwamnar ake nufi ba Bilkisu Kachallah, Bilkisu..." ta haɗiye maganar ganin Agent Dahlia ta saka mata ankwa a hannu. Koma mi zata faɗa a nan kam bashi da amfani. Taya aka shigo da waɗannan kayan aka saka a ɗakinta cikin akwatinta amma bata sani ba? Jiya ta wuni a gidansu ne, yau Abba za su wuce Saudiyya shiyasa ta je masa sallama, komai zai iya faruwa a tsawon awanni biyar zuwa shida da tayi bata gida. Jami'an suka shiga ɗaukan hotunan abinda aka gani da kuma yadda aka same su kafin daga nan suka shiga kwashe kayan suna sawa cikin akwati guda ɗaya. Lokacin da Agent Dahlia ta fito riƙe da Asiya. Sumayya da Jummai sai suka fashe da kuka musamman Jummai da take tunanin mafarkinta ya tabbata Adda Shahidarta zata yi zaman kurkuku. Kafin kace me gaba ɗaya gari ya ɗauka. Matar Gwamna Asiya Kachallah tana safaran miyagun ƙwayoyi. An kama Asiya Kachallah da buhuhunan kayan maye da miyagun ƙwayoyi irinsu cocaine, codien, har da masu cewa buhun marijuana sun fi hamsin aka gani a gidan...   *** "No no no no nooooo" CY ya fasa ihu a ƙaramin office ɗinsa bayan ya karanta hot news daya gani a waya. Bai yi tsammanin haka ba, bai hasaso haka ba. This is bad, it's going to be very bad. A ɓangaren Alhaji Sani ma hankalinsa ba ƙaramin tashi yai ba da wannan batu. Ya shiga kiraye-kirayen mutane. Babu abinda zai shigo jahar ba tareda jzininsu ba taya za a bawa jami'an NDLEA damar bincikan gidan Gwamna? balle har a arressting Matar Gwamna. Yallaɓai na gama waya da Alhaji Sani Kachallah ya baro ɗakinsa a fusace dan tabbas abinda Bilkisu Kachallah ta ɓaro abu ne mai girma, it can backfired. Matattakala uku ya taka ya dafe ƙirjinsa yana ƙoƙarin shaƙar numfashi da ƙyar, yana ƙara taku ɗaya ya suɓuto daga benin ya faɗo ƙasa tim, sandar hannunsa tayi tsalle ta faɗo gefensa. Yallaɓai shi kaɗai ke zama a gida sai masu aiki, dan iyalensa kaf a ƙasar waje suke rayuwarsu, sai ƙarshen shekara suke kawo masa ziyara. Sai da yai kusan minti goma a wajen kafin wani mai aikinsa ya shigo ya ganshi a wajen... 23 *Barkanmu da dawowa. Nagode da addu'o'in ku da kuma haƙurinku*   Kwalaben giya da ke gaban Clement Yohanna sun yi biyar kuma duka sai da ya shanye giyan dake cikinsu tas. Shi ba ma'abocin shan giya bane, ko a baya yakan sha ne a lokutan da ake hidima balle yanzu ya kai kusan shekara ɗaya da rabi bai sa giya a baki ba tunda suka yi wani jayayya da Asiya akan shan giya illarsa da kuma rashin dacewarsa ga shi ma dake bin addinin kristanci. A yau kam dole ne ya sha giya saboda ya samu ya kauda damuwarsa koda na lokaci kaɗan ne. Sai dai, the more yake sha the more yake sake jin zafin kama Asiya da aka yi. Idan da zai iya bada rayuwarsa domin a saketa to zai bayar. Idan da zai iya zama a kurkuku a madadinta to da zai iya ƙarisa rayuwarsa a kurkuku just so that she could be free. Yau kwana na uku kenan da aka garƙame Asiya Kachallah a kurkuku. Ranan litinin za'a fara sauraran ƙara amma har zuwa lokacin Asiya Kachallah remains in prison. Abinda ake tuhumarta da shi ya fi ƙarfin a bada bail ɗinta, infact a yadda ake ganin abinma koda an je gaban Alkali ba lalle ne ya granting bail ba har sai an gama binciken da ake yi. CY ya mirgina gefe yana so ya jawo kwalbar giya ta shida wanda yake tunanin akwai saura aciki, sai dai yana taɓata da hannunsa na roba kwalbar ta gangara chan nesa da shi alamun kwankwataran babu komai acikinta. Ya rufe idanunsa sannan ya buɗesu yana tunanin mace ɗaya ce ya sani da zata iya taimakon Asiya. Ya riga ya yanke alaƙa da ita kuma baya fatan neman taimako a wajenta har abada amma Asiya means everything to him ba zai bari damar da yake da shi na taimakonta ya kuɓuce masa ba. Idan mijinta Gwamna ya cire hannunsa akan lamarin yayi iƙirarin ba zai sa hannu a binciken da ake ba to shi zai yi koma minene dan ganin Asiya ta samu nasara. CY ya tashi da ƙyar yana tangal-tangal har ya kai tsakiyar falonsa ya shiga neman wayarsa, ya shafe minti ishirin yana laluben wayar da ke maƙale a Aljihun wandonsa kafin ringing ɗin wayar ya ankarar da shi inda wayar take. GrandMa ne a screen ɗin amma saboda ba a hayyacinsa yake ba sai idanunsa suka nuna masa sunan Aseey kamar yadda ya saving lambar Asiya. "Aseey are you ok?" "Clement" Kakarsa ta kira sunansa da ɗan ƙarfi. Maimakon ya amsa sai ya fashe mata da kuka. Kakarsa ta san yana son Asiya shiyasa ma yake ƙin maganar aure, shiyasa duk yarinyar da yai tarayya da ita basa jimawa saboda zuciyarsa tanaga Asiya. Abinda ya faru ya sa ta kirashi, da ke ta je ƙauye bata ji labarin da wuri ba sai yau. Sai da ta tabbatar ya dena kuka kafin ta kashe wayar tareda alƙawarin gobe zata dawo. Tsoronta ma kar wani abu ya sameshi kafin goben dan a maganar da suka yi ta fahimci cewa ba a hayyacinsa yake ba. Bayan ya gama waya da Kakarsa sai ya danna wasu lambobi, bai saving lambar a wayarsa ba amma ya haddacesu ta yadda ko a mafarki aka tashe shi zai karanto su tsaf. Dr Kimberly Yohannah Anderson ya kira, matar Secretary General na United Nations (UN) mahaifiya a gareshi, duk dama alaƙarsu ta ƙare tun ranan data haifeshi ta ajiyeshi ga iyayenta sannan ta gudu. Mahaifiyar CY mai suna Godiya Kimberly Yohanna tanada shekara shabakwai ta yi cikin shege, lokacin tana aji shida a sakandare. Saurayin daya mata ciki ɗan ajinsu ne wanda ko a haife ta bashi watanni bakwai. Abin kunya ne gareta da kuma iyayenta, musamman da Daniel ya ƙaryata cikin lokacin da mahaifin Godiya Kimberly ya je gidansu da maganar. Cikin na wata uku Godiya tayi ƙoƙarin zubar da shi amma hakan bai yiwu ba. Iyayenta musamman mahaifiyarta wacce take strong catholic ta nuna tsananin ɓacin ranta akan haka. Dan a wajenta da a kashe rai gara an haifi cikin, tunda dai ba laifin yaron bane, laifin iyayensa ne. A haka Kimberly ta raini cikin har ta zana jarrabawarta na WAEC. Watanni biyu bayan ta zana jarrabawar ta haifi ɗanta namiji wanda ya ɗauko kamanninta. Ashe tun kafin ta haihu ta riga ta yankewa kanta abinda za ta yi. Dan haka kwana goma shauku da haihuwar ta gudu daga gida, ta bar yaron a wajen iyayenta. Ba a san inda ta shiga ba, haka kuma iyayenta basu nemeta ba tunda sun fahimci guduwa tayi. Godiya Kimberly ƙasar Ghana ta je wajen wata distant cousin na mahaifinta da ke zama a chan. A nan ta samu scholarship na karatu a ƙasar America. Ta yi karatu tun daga digiri na farko har na uku. Sai data zauna da ƙafafuwanta kafin ta waiwayi iyayenta da ɗanta, lokacin shekarunta biyar da auren wani baAmurke amma babu haihuwa kuma likitoci sun tabbatar mata da cewa da wuya idan ta sake haihuwa. Ga mijinta Mark Anderson, rashin haihuwa ba matsala bace a wajensa dan bai damuba, ya taɓa haihuwa da matarsa ta farko amma yarinyar ta mutu tun bata fi shekara shida ba. A yanzu karensa Jerry yafi masa mahimmanci sama da samun ɗa ko 'ya ta cikinsa. A wajen Kimberly wacce ta kasance 'yar Nigeria, 'yar Africa. Rashin haihuwa matsala ce a gareta musamman idan ta tuno ɗan data haifa a lokacin ƙuruciyarta tayi watsi da lamarinsa ko ya rayu ko bai rayu ba batada masaniya saboda shekaru ishirin cur bata waiwayi gida Nigeria ba, bata waiwayi iyaye ko 'yanuwanta ba. Lokacin da ta zo Nigeria ta samu mahaifinta ya mutu, ƙaninta yayi aure da yaransa biyu sannan Clement ya zama saurayi, yana aji uku a Jami'a. Ɗan da ta yi yunƙurin kashe shi lokacin yana cikinta, ɗan da tunda ta tafi bata damu ta san wani hali yake ciki ba balle ta waiwayeshi... fff Shekaru goma da suka biyo bayan zuwanta Nigeria ko kaɗan babu wani jituwa tsakaninta da Clement. Mahaifiyarta da ƙaninta sun yafe mata kuma sukan gaisa a waya lokaci zuwa lokaci amma banda Clement. Zuciyarsa, zurfin cikinsa da riƙo sun hanashi yafe mata balle har ya kirata Uwa. Har yau babu wannan mu'amala ta uwa da ɗa tsakaninsu. Kimberly ta yi kukan tayi magiyar amma Clement ya tsaya kan bakarsa cewa uwarsa ta mutu tun yana jinjiri bai da alaƙa da ita ko kaɗan. A koyaushe tana saka tsammanin Clement zai yafe mata har kuma ya dawo gareta sai dai kuma yana ƙara girma yana ƙara tsanarta ne, but she's ever hopeful zuwa lokacin da zuciyar ɗanta zai karkato gareta. A yanzu data ɗauki kiran Clement kuma ta ji muryansa farin ciki ne ya mamayeta, in dai har saboda matar nan Asiya Clement zai kirata ya roƙeta alfarma to ba ƙaramin mahimmanci take da shi a rayuwarsa ba dan haka zata gayawa mijinta ayi duk abinda za ayi akan wannan maganar.   *** Babban ofishin NDLEA na Abuja cecekuce ne ya kaure tsakanin Agent Vic da kuma Agent Dahlia. Kowannensu gani yake abinda yake akan gaskiyarsa ce shiyasa babu wanda yaiwa waninsa uzuri. "It could be a set-up, she's innocent" "Oh please Vic! Kar ka kawo min maganar banza. Ba a rubuta criminal a goshin mutane balle ka ganesu. I will lead this investigation to the end and i will make sure she rots in jail" Daga haka Agent Dahlia ta juya ta bar ofishin Vic a fusace. Agent Vic ya sauke ajiyar zuciya, tabbas babu mai iya dakatar da Dahlia saboda ta kowanni fanni tana da kariya. Mahaifinta babban mutum ne a ƙasar sannan ita ɗin American citizen ce kuma babbar jami'a a hukumar DEA. Bai san dalilinta ba amma tunda ta zo she's being obsessed with tracking drug traffickers. Amma a wannan case ɗin gaskiya yana ganin akwai lauje cikin naɗi saboda a iya tunaninsa Asiya seems innocent.   *** Gwamna Saifuddeen Kachallah ya ƙurawa agogon da ke manne a bangon ɗakinsa ido yana bin kowanni tik tik tik da agogon ke yi. Cikin kwanakin nan yadda yake ganin rana haka yake ganin dare. Maganin baccin daya ke sha ma duk a banza ne, dan sai dai jikinsa ya mutu amma baya iya yin barci. Bai san dalilin daya sa yai wannan ɓaran-ɓaramar ba ranan da ya fito yai jawabi wa duniya gameda case ɗin Asiya ba. *"Banida hannu cikin binciken NDLEA. Hukumar NDLEA tanada damar kama duk wanda ta samu da laifi, ko wanni irin matsayi gareshi. Ina tabbarwa jama'a cewa Gwamnatinmu ba zata yiwa kotu katsalandan ba, zamu bata goyon baya tayi duk wani bincike daya dace"* Ba abinda yake son faɗa ba kenan, it was what Bilkisu wanted. Saboda haka ne ma tace lawyansa ba zai wakilci Asiya ba. Wani ɓangare na zuciyarsa na gaya masa cewa cire hannunsa a case ɗin Asiya was a betrayal amma kuma ya rasa ƙarfin aiwatar da wanni abu a kai. *** Barrister Zaytoonah Tijjani Abubakar ta ja dogon numfashi sannan ta sake gwada sa'arta a wajen maigidanta wanda ya kasa-ya-tsare tun ɗazu. "Daddyn Alinah ka sake duba batun nan dan Allah. I want to help..." "Adaeze ki haƙura da wannan case ɗin Dan Allah, for my sake. Ki duba condition ɗinki, this is not an ordinary case da zaki je sau ɗaya sau biyu, this can take a long while" "Zunnoon, please!" Ta faɗa tana marairaice murya tareda riƙo hannunsa ɗaya Justice ya sauke ajiyar zuciya yace "Adaeze da condition ɗin ki zaki dinga jeka ka dawo tsakanin Congo da Abuja? Idan baki damu da lafiyarki ba think about our baby" "We'll be fine my love" ta ƙarisa maganar tana kwantar da kanta a ƙirjinsa. Jin bai sake cewa komai ba Zaytoonah ta sani yanzu kam ya haƙura.   *** "Hajiya Bilkisu Kachallah ta gyara zamanta da kyau sannan ta dubi Madam Bintu ta ce "kina tunanin zan bari a bata special treatment ne? No no no, you know me ai" "Shegiya Bilkisu kenan yadda kowa yake rayuwa a kurkuku haka zata yi?" "Of course, ita wacece da za a ɗagawa ƙafa" Madam Bintu da gatse tace "Matar Gwamna ce" Bilkisu Kachallah ta fashe da dariya har da tafa hannu. "Idan akwai Gwamna a cikin prison to Asiya zata amsa sunan matarsa, otherwise, ni kaɗai zan amsa sunan har ya gama tenure ɗinsa biyu" Madam Bintu ta saka ihu "ina yinki tawan" Suna cikin ƙyaƙyatawa da dariya wata mai aiki ta shigo ta rusuna gabansu tareda faɗawa first lady cewa Uwani staff ɗinta na chan gidan Gwamna tana son ganinta. "Uwani?" Bilkisu ta maimaita da mamaki. "Ok ki shigo da ita" "Lafiya dai ko?" Madam Bintu ta tambaya tana kurɓan juice "Bari ta zo mu gani" Minti biyu sai ga Uwani ta shigo jiki a sanyaye. Bayan ta gaishe da matan biyu sannan ta duƙar da kai ƙasa tana tunanin ta ina zata fara bayani musamman gashi ba Bilkisu kaɗai bace a falon. "Miya kawo ki?" "Dama dama..." Uwani ta fara inda-inda "Banida lokacin wasa, ki faɗi abinda ya kawoki ko kuma ki bamu waje" Uwani ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "ina son komawa garinmu" "A wani dalili?" Bilkisu ta tambaya fiskarta ɗaure. "Hankalina zai fi kwanciya idan nayi nisa da nan garin" "Babu inda zakije. Ke Uwani!" Uwani sai da ta ji hanjin cikinta sun kaɗa dan ba ƙaramin firgita tayi da tsawar da Bilkisu ta mata ba. "Babu inda zaki je"... Har Uwani ta koma chan gidan Gwamna bata daina rawar jiki ba. Babu yadda za ayi ta kuɓuta daga hannun Bilkisu. Lokacin da Bilkisu ta tunkareta da maganar saka ƙwayoyi cikin akwatunan Asiya ba ta bata damar cewa e ko a'a ba. Umurni ta bata kuma ta san rashin bin umurnin akwai matsalar da zai jawo tunda babu abinda Bilkisun bata sani ba gameda ita. Tun da aka kama Asiya ta kasa yin bacci, duk da umurnin Bilkisu ta bi, randa gaskiya ta bayyana itama za a iya turata kurkuku. Wani mafita gareta daya wuce ta yi shiru da bakinta ta zubawa sarautar Allah ido.   *Congo state Prison*   Ko a mafarki Asiya bata taɓa tunanin zaman kurkuku ba, kafin a kawota nan ta taɓa zuwa gidan kurkuku na Congo lokacin tana Jami'a ta zo ɗaukan rahoto na wani assignment da aka basu. A rahoton data kawo tayi nuni da yadda gidan kurkukun ke cikin yanayi na neman agaji. Ƙazanta, rashin ruwa mai kyau da kuma abinci wadatacce, ga kuma uwa uba cikowa da wajen yai. Sai gashi wai an wayi gari ita Asiya Shahida Faruƙ Baba ta fara irga kwanaki a gidan yari, yau kwana na shida kenan. Kwana shida tana kulle kamar wacce tayi kisan kai, kwana shida babu wani daya zo dubata koda kuwa lawya ne, kwana shida bata san miyake faruwa a wajen dogon katangar daya zagaye kurkukun ba. Hakanan kwana shida na wani sabon babi a cikin rubutacciyar ƙaddara wacce tun kafin zuwanta duniya an riga an rubuta. Kwanaki biyun farko, ɗakinta ita kaɗai ne kuma abinci mai kyau ake kawo mata duk dama ba wai ci take ba dan azumin dole ta ɗaurawa kanta. Sai kuma a kwana na ukun aka zo aka chanja mata ɗaki, a hasashenta ɗakin da aka ajiyeta shine mafi muni a cikin kurkukun. Tana cikin ɗaki wata warden ta zo ta buɗe ƙofa tace " Hajiya Asiya akwai wata lawya dake son ganinki" warden ɗin mai suna Bisola ita kaɗaice ke yi mata magana cikin girmamawa da kuma tausasa harshe, amma sauran kaman wanda aka musu karatun rashin mutunci musamman kwanki ukun nan. Lokacin da aka fito da Asiya tana cikin tafiya ita da warden Bisola ta ji an kira sunanta. "Asiya Kachallah" Kaman ta wayi mai muryan hakan yasa ta juya ai kuwa sai idonta ya gane mata Hansa'u cikin kayan firsina riƙe da fartanya a hannu. "Hansa'u" Asiya ta faɗa da ɗan ƙarfi. "Anty Bisola barin yi magana da waccar dan Allah" "Hajiya Asiya da ƙyar aka bawa Lawyar data zo wajenji minti goma kuma ya fara reading tun lokacin da aka ce na kawoki" Asiya ta yi murmushin takaici tace "muje" Ta ɗagawa Hansa'u hannu sannan suka tafi... 24   Asiya ta kalli Lawyar da aka ce ta zo ganinta da kyau tana mamakin a ina ta santa. Matar wacce ta kira kanta da suna Barrister Zaytoonah ba zata wuce shekaru ashirin da tara zuwa talatin ba, sannan ga mamakinta ciki ne gareta da zai iya kaiwa wata bakwai zuwa takwas, dake tanada ƙiba ba zaka iya fidda ainihin adadin watannin ba musamman ga wanda bai da masaniya sosai akan ɗaukan ciki da kuma girmansa. "Na san kin yi mamakin ganina. Mun haɗu sau ɗaya a wajen dinner ɗinku da Gwamna amma bana tunanin zaki iya tunawa. Mijina abokin Gwamna ne sosai" Barrister Zaytoonah ta yi shiru tana nazarin Asiya sannan ta cigaba "ina so ki faɗamin duk abinda kika sani musamman gameda ƙwayoyin da aka samu a cikin ɗakin ki" "Ban san komai akan ƙwayoyin ba, ban san ya akayi aka samesu a cikin akwatunan kayana ba" Barrister Zaytoonah ta fito da tab ɗinta daga jaka ta kunna wani video ta miƙawa Asiya wayar tace kin taɓa kallon wannan video? Asiya ta gyaɗa kai tace " inaga bai fi kwana biyu ko uku dana gani ba wannan abin ya faru" "Lokacin da kika gani kuma kika ji da kanki an ambaci sunan matar Gwamnar Congo a matsayin uwarɗakinsu, miyasa baki fito kin ƙaryata ba? ko kuma ki nemi a ƙara bincike a tabbatar da ƙaryar abinda mutumin ya faɗa ba?" Asiya ta haɗe rai ta ƙi magana domin gani take tambayar rainin hankali Barr. Zaytoonah ke yi mata. "Asiya ina jin ki" "Asiya?" "Times up Barrister" wata warden ta faɗa da ƙarfi. "Zan tafi Asiya amma zan dawo gobe" Barr Zaytoonah ta faɗa. Har zata fita sai ta juyo ta faɗi wani magana da ya ƙara tunzura Asiya... Duk yadda Asiya ta so a kaita wajen Hansa'u babu wanda ya saurareta. Warden Bisola ce ta fito ta gaya mata gaskiya cewa umurni ne daga sama akan kada a bari Hansa'u wacce suke kira da Badawiyya tayi mu'amala da kowa. Lokacin da aka kawota kurkukun sai da aka yi kusan wata uku ba a barinta ta fita yin aiki ko wani abu, daga ɗaki sai ɗaki. Ta haɗa da cewa da alama wani yaga lokacin da Badawiyya ta kira sunan Asiya dan ko aikin da take ba a bari ta gama ba aka maidata ɗaki aka kulle. Asiya ta girgiza kai cikin takaici. Hansa'u itace fitilar da zata haska mata sirrin Bilkisu Kachallah. Duk abinda ya faru idan ta fito sai ta ga bayan matar nan. Wani abu daya tsayawa Asiya rai shine bayanin da Barr. Zaytoonah ta mata cewa Gwamna ya fito duniya yace ya cire hannunsa a case ɗinta, dan haka kada ta yi tunanin zata samu alfarma a kotu, gaskiyarta da kuma addu'a ne zasu kuɓutar da ita. Washegari da Barr. Zaytoonah ta zo Asiya ta bata haɗin kai wajen amsa tambayoyinta koda tambayar da ta sani ta rainin hankali ne. Ranan Monday kuwa aka gurfanar da Asiya a gaban kotu. Abu na farko da Barr Zaytoonah tayita fafutuka akai shine akan a bada bail ɗin Asiya. Idan ya so a cigaba da bincike tana gida. Sai dai faufau Alkali ya ƙi bada haɗin kai, kotu ta tashi ba tareda an cimma wani abin kirki ba, aka ɗaga sauraron ƙara zuwa sati biyu masu zuwa, zuwa lokacin ana sa ran hukumar NDLEA zata gama binciken data fara. A ɓangaren CY kuwa, yana nan lokacin da aka yi zaman kotu, haka ya zubawa Asiya ido kamar mai kallon TV. Mahaifiyarsa Mrs Kimberly ta faɗa masa cewa ita da mijinta za su yi iya ƙoƙarinsu akan case ɗin Asiya amma gani yake kaman ba abinda suka yi tunda gashi anƙi ma a bada bail ɗinta. He wished he could protect her lokacin da aka fito da ita daga kotu 'yan jarida suka mata chaa, duk da kuwa akwai securities masu hana su amma kowa ya san 'yan jarida da naci. Haka ya bi bayanta da kallo har aka sakata cikin mota suka bar haraban kotun. Dole ne ya binciko gaskiya cikin sati biyun nan kafin zaman kotu na gaba. *** Rikici ne ya ɓarke tsakanin dattawan Congo tun lokacin da Mr Lamara Damana ya sanar da wasiyyar Yallaɓai ta ƙarshe kafin 'ya'yansa su tafi da shi ƙasar waje. Kowa yana ganin rashin dacewar chanja tsari da aka yi. Taya Yallaɓai zai naɗa wani shugaban daban ba ɗaya daga ciki manya uku da suke da damar maye gurbin muƙaminsa ba, abin takaicinma wai, wanda aka naɗa baya cikin ƙungiyarsu ta dattawa. Anya ma ba ƙarya Mr Lamara ya sharara ba duk da ma dai sun gani a rubuce kuma da saka hannun Yallaɓai cewa Boss Lady ce zata maye gurbinsa. Wasu kuma kalmar Boss Lady na nufin mace ce zata shugabance su, MACE fah!wannan abin ya fi tsaya musu a rai fiye da ma chanja tsari da aka yi. Koma wacece Boss Lady ba za su mara mata baya ba. Duk cikinsu babu mai shekara ƙasa da hamsin amma ace sai wata ƙaramar alhaki mace ta zo ta jagorance su sai kace wasan yara. Dan me ake kiransu Dattawa?. COS ya cigaba da shirye-shiryen naɗa sabon shugaba duk da ya san an shirya yin bore ranan naɗin, amma ya sani duk wanda ya ga Boss Lady to ba zai iya jayayya ba koda kuwa Alhaji Sani Kachallah ne da suke ta kumbar baki a kansa. Saɓanin da da ake yin zama a gidan Yallaɓai wannan karan taron da za ayi an saka cewa za ayi shine a gidan Boss Lady. Ba su san gidan ba amma address da aka turo musu ya basu mamaki, domin gida ne da ya ja hankalin jama'ar gari lokacin da ake ginashi, babu wanda ga san takamaimai mai gidan amma girman gidan da kuma tsarin ginin ya nuna cewa mai gidan wani ƙutsar Gwamnati ne. Abin mamakin ma cikin wata uku da sati biyu aka kammala ginin da ka iya zama gida mafi kyau a duk faɗin cikin jahar. Ƙarfe goma shaɗaya na safe aka shirya taro, kafin goma da rabi mutane suka fara isowa, ba don sun bawa lokaci mahimmanci ba sai dan curiosity da ke cinsu na son sanin wacece Boss Lady sannan koma wacece ba zasu karɓeta ba, Alhaji Sani Kachallah shi zai jagorance su dan yanzu Yallaɓai kam da shi da samun lafiya sun yi hannun riga domin duk wanda ya je ya kalleshi a asibiti kafin 'ya'yansa su ɗauke shi daga ƙasar sun san Yallaɓai yana daf da gangara, mutumin da dukkan jikinsa ya shanye ina yaga tashi balle yai mulki, ko magana baya iya yi sai idanunsa kaɗai yake iya juyawa. Su takwas suka hallara a ƙaton falo mai kama da fada wanda Mr Lamara ne ya musu iso zuwa wajen. Wani abu mai ɗaukan hankali a falon shine wata kujerar zinari da aka ajiye a wajen wacce ke nuni da koma wacece shugabarsu a nan tayi niyyar zama. Zinari ba baƙonsu bane kuma idon su ya shaida cewa zinarin da aka haɗa kujeran da shi ainihin zinari ne mai kyau. Wace mace ce take da wannan ɓatan basirar zata sa a mata kujerar zinari? Koda yake dama mata da ƙyale-ƙyale sai a hankali. To amma wannan hauka ne ai... Lokacin da agogon falon ya buga ƙarfe shaɗaya dai dai aka buɗe ƙofar shiga falon. Dukkanninsu suka ƙurawa ƙofar ido musamman Alhaji Sani Kachallah da yake cike fam da wannan mata da yake tunanin karuwar Yallaɓai ce da ke son karɓe matsayin da kowa ya sani nashi ne. Daga zare ido sai suka koma buɗe baki ganin matar da ke nufo su. Babu wani a wajen da bai san wannan mata ba abinda ya ƙara ɗaure musu kai kenan. Bilkisu Kachallah ta cigaba da shafa kan macijin da ke nannaɗe a hannunta na hagu, fiskarta ɗauke da murmushi har ta iso tsakiyar falon ta je ta zauna a kujerar da dama saboda wannan zama tasa aka ƙera mata shi. Bayan ta zauna sai ta ɗaura ƙafarta ɗaya akan ƙaramin stool na zinari dake gabanta yayinda hannunta na dama ke kan hannun kujera tana ɗan bubbuga yatsunta kaɗan-kaɗan, ta ɗan karkatar da kanta gefe tace "akwai mai jayayya?" Kallon kallo suka fara yi, kowa na tsoron magana. Mr Paul da yafi kowa tsorata a cikinsu musamman ganin macijin da ke hannun Bilkisu yace "babu mai jayayya" Bilkisu tayi murmushin gefen baki sannan tace "A fara Agendar yau" "Yes Boss Lady" Mr Paul ya faɗa yana duba takardar dake gabansa, lokacin da ya ɗau takardar hannunsa rawa ya fara har sai daya sa ɗaya hannun ya supporting takardar dan kar ta faɗo. Duk wani shiri da suka zo da shi na yiwa Boss Lady tawaye ya bi ruwa, domin kowa yayi gum da bakinsa an rasa mai cewa alif a wajen. *"Sai na fi Gwamna ƙarfi Baba, sai na fi kowa iko a jahar nan. Sai na juya jahar nan a tafin hannuna, sai na nuna maka cewa mace tana da daraja, namiji bai fi mace ba, sannan Ubangiji daya sakawa mace mahaifa dan ta ɗau ɗa namiji a cikinta ba ƙaramin baiwa da ƙarfi ya bata ba. Ka zuba ido kawai Baba, that teenage girl daka faɗawa cewa ba zata iya siyasa ba saboda ita macece ta zama matar dake juya 'yan siyasa yanzu"* Abinda Bilkisu ke faɗi a zuciyarta kenan. Alhaji Sani ya ɗaga ido ya kalli 'yarsa Bilkisu, idonsa ya ciko da ƙwalla. Mi Bilkisu tayi?, ina ta shiga?, taya ta iya juya dukkan mutanen nan? Anya Bilkisun daya sani ce kuwa? Tunanin da ya ke yi kenan lokacin da Bilkisu ta kira sunansa "Alhaji Sani Kachallah" *"Yes Boss Lady"* ko ya akayi ya faɗi hakan Allahu a'alam, sai bayan ya faɗa ya ankara da abinda ya fito daga bakinsa. 'Yarsa ya kira Boss Lady, 'yar da shekaru arba'in da ɗaya da suka wuce tana cikin mahaifa yana ta addu'ar Allah yasa a haifa masa ɗa namiji. Har wajen malamai ya shiga yana fata wannan karan ya samu ɗa namiji. 'Yar da a lokacin da aka haifeta nurse ta fito ta gaya masa cewa mace aka haifa masa yaji kamar yaje ya shaƙeta kawai ta koma inda ta fito. 'Yar da ko suna ba shi ya zaɓa mata ba saboda yadda zuciyarsa ta cunkushe da kasancewarta mace. Mahaifiyarta ce ta zaɓa mata suna Bilkisu ana saura kwana ɗaya ayi suna, saboda har lokacin bai zaɓa mata suna ba, kuma bashida niyyar zaɓa. Gashi dai yanzu 'yar da ya raina a lokacin ta haye kujerar da yake nema shekara da shekaru, ta samu matsayin da yake nema shekara da shekaru, wato Mulkin jahar Congo. Ba komai bane idan ka mulki talakawa saboda shi talaka ko Akuya aka ɗaura akan ƙaragar mulki zai masa biyayya. Mulkin daya ke nema shine mulkin dake juya Gwamna ya tanƙwasa attajirai, ya juya Sarakuna sannan mulkin dake haɗa ko ya wargaza komai a faɗin jahar, mulkin da kowanni ƙorafi za a kawo idan bai amince da shi ba to banza ne. Yau dai ga 'yarsa da wannan Mulkin... Bilkisu Kachallah ta yi murmushin nasara ganin tsantsan ruɗani dake shimfiɗe a fiskar mahaifinta. She has long for a day like this, a day da zata nunawa mahaifinta cewa is not all about haihuwar ɗa namiji. Itama mace abun alfahari ne. Ta sani, she went extra length to get this, amma its all worth it ai. Zama a kujeran nan, jin dattawan nan suna kiranta Boss Lady, its worth all the sacrifices da ta yi. Daga yanzu da bazar Bilkisu Kachallah zasu taka a jahar nan. Abu ɗaya ta sani duk wanda ya goya mata baya ya tsira wanda yai jayayya da ita zai bi sahun su Yallaɓai...   *A nan na kawo ƙarshen matar Gwamna Part two. Sai mun haɗu a part three gobe Insha Allah* ***   *tam tam tam....Jama'a tsugunne bata ƙare ba a Matar Gwamna, domin yanzu za a shiga wani sabon batu* *Ga dai Bilkisu Kachallah a kan kujerar zinari, ga Kuma Asiya chan garƙame a gidan yari. Ko ya abin zai kasance a wannan tafiyar?* *shin tukunna idan MACE ta juya NAMIJI ita macen wa zai juyata?.... i guess MACE 'yar uwarta ko?* *ina godiya da haƙuri dani da kukayi iya tsawon waɗannan lokaci da nake kawo update ba akan lokaci ba. Ina kuma godiya saboda supporting ɗina da kukayi ta hanyar biyan kuɗi dan ku karanta labarin nan, wanda suka biya kuma suka haɗa da wani ihsanin a kai duk ina godiya, waɗanda suka biya suka ji dama basu biya ba saboda banida cika alkawari, da kuma wanda suka biya without complains saboda sun min uzuri, duka ina baku haƙuri. Ina godiya kuma ina ƙara bawa kowa da kowa haƙuri tareda neman yafiya a wajenku. Jazakumullahu Khairan* *kafin nan zan so jin ra'ayoyinku akan wannan labari in general, aside Of course rashin update da wuri * *Abu na ƙarshe, Jahar Congo ƙirƙirarre ne, duk da a cikin Nigeria na ƙirƙireta hakan ba zai hana ku ga wasu abubuwan sun faru wanda ba za su faru ba a normal Jaha a Nigeria. After all duka labarin ƙirƙirarre ne, so a ɗauki komai yadda ya zo kawai*   *Nagode sosai* *Ma'assalam*

Post a Comment for "Governor's Wife Book 2 Complete Hausa Novel"