Governor's Wife Book 3 Complete Hausa Novel
01
***
"Nana ki fito mu yi breakfast da Daddy" muryan Mahirah ya doki kunnen Nana da ke zaune chan ƙuryan gado tana maƙyarƙyata. Minti biyar da suka wuce ta fito zata je dinning ta yi kiciɓis da macijin mommynsu ta koma ɗaki a guje jikinta na maƙyarƙyata. Ba yau ne hakan ya fara faruwa ba, ranan da ta fara ganin macijin a nannaɗe a hannun mommynsu sai da ta kusa shiɗewa saboda tsoro, a hakan sai Mommyn na su ta shiga yi mata faɗa wai babu abinda macijin zai mata it's just a pet snake. Pet snake kamar wanda suke zaune a daji. Tunda suka zo gidan ko kyanwa babu balle kare amma a rasa pet ɗin da za a kawo gida sai maciji.
Su uku ne zaune a wajen dinning ɗin, yau ne ɗaya daga cikin ranaku biyu da Gwamna ya tilastawa kansa zama yai breakfast da 'ya'yansa. A yanzu kam zama da 'ya'yansa shine kaɗai ke saka masa nitsuwa.
Mahirah ta miƙe ganin har yanzu Nana ta ƙi fitowa, bayan tafiyar Mahirah Gwamna ya zubawa Junior idanu yana kallon yadda yaron ke wasa da abincin da ke gabansa, gani yai yaron ya rame masa kuma babu walwala a tattare da shi kamar da.
"Babana" Gwamna ya kira shi a hankali, amma maimakon da idan ya kirashi da hakan yake cewa shi ba Babansa bane, yau kam ko ɗaga idanunsa bai yi ba balle ya tanka masa.
Gwamna ya riƙo hannun yaron yana faɗin "Sa'ad junior"
Ai kafin ya ƙarisa maganar Junior ya challah ƙara yana faɗin "Mommy no snake, please no snake"
Gwamna ya taso ya rungume Junior tsam a jikinsa yana bubbuga masa baya. Shi kansa wannan maciji da Bilkisu ta kawo gidan ya tsaya masa a rai amma ya kasa yi mata magana a kai.
Mahirah ta fi minti biyu tana buga ƙofar ɗakin Nana kafin da ƙyar Nanan ta ja jiki ta zo ta buɗe mata.
"Miyasa kika kulle ƙofa?... Nana miya sameki?... kuka kika yi?"
Shiru babu amsa sai kuka da Nanan ta sake fashewa da shi.
"Nana minene please?" Mahirah ta faɗa itama kaman zata yi kuka.
"Mom...Mom... Mommy's snake" ta faɗa da ƙyar.
"A ina kika ganshi, Mommy ta fita da shi ɗazu"
Nana ta yi shiru ta kasa magana dan kanta ya ruɗe shin kafin Mommyn ta fita da shine ta ga macijin ko bayan an fita da shi?
"Kar ki damu babu abinda zai miki, ki zo muje mu karya Daddy na ƙasa kin san ba wai koyaushe muke ganinsa ba"
Da ƙyar Nana ta amince suka sauko ƙasa. A nan suka tarar Daddyn nasu na fama da lallashin Junior.
Mahirah tace "Daddy dan Allah ka ce Mommy ta dena yawo da macijin nan. Nima ba wai ina son shi bane, amma Nana da Junior always panic idan suka ganshi. Daddy dan Allah kayi wani abu akai"
"Ku kwantar da hankalinku, zan mata magana"
Safiyar ranan dai sun ci abincin ne a darare dan kowa ba wai ya ci da kwanciyar rai bane.
***
Nana da Mahirah suka shiga haɗa kayansu da sauri-sauri saboda basa so mahaifiyarsu ta dawo ta samesu a gidan. Kwana uku kenan da Daddy yai musu alƙawarin zai yiwa Mommy magana amma babu abinda ya chanja dan ko yau da safe da macijin Mommynsu ta fita. Jiya da yake Mommy ta wuni a gida Nana ko iya fitowa bata yi ba saboda tsoro dan idan Mommy na gida tana barin macijin yai ta shawagi tsakanin ɗakinta da kuma falon ƙasa.
Sai da suka gama haɗa komai sun sauko da akwatunan kawai suka ji ƙaran siren.
"Mommy" Nana ta faɗa a tsorace
"Inaga Daddy ne fa"
"Mommy ce Mahirah" Nana ta faɗa tana shirin kuka.
Mahirah tayi ƙarfin hali tace "koma Mommyn ce mu tsaya mu gaya mata matakin da muka ɗauka"
Suna tsaye riƙe da akwatuna Bilkisu Kachallah ta shigo biye da ita kuma wasu manya-manyan mata ne guda biyu da suke matsayin personal bodyguards ɗinta. Ko a ina ta samo su oho, dan kuwa basu yi kama da 'yan Nigeria ba. Sun fi kama da black Americans da suka ƙware a body building. Da za su cire rigan jikinsu babu tantama sai ka ga 6 abs kaman a jikin shaharraren ɗan damben nan The Rock. Suna sanye da baƙaƙen kaya riga da wando da kuma baƙin gilashi da suka toshe idanunsu da shi, fiskarsu a ɗaure babu alamun fara'a ko kaɗan.
"Ina zuwa?"
Nana ta ɗan matsa bayan Mahirah, duk da babu macijin a hannun Bilkisu amma a karan kanta Mommyn na su yanzu tsoro take bata.
Mahiran ma tsoron ne ya ɗarsu a zuciyarta lokacin da suka haɗa ido da Bilkisu Kachallah.
"Ehen, ina zaku je kuka tattaro kaya kaman masu shirin ƙaura?"
Mahirah ta haɗiye miyau tana karanto addu'a a ranta *Allahumma lah sahla illa ma ja'altahu sahla...*
"Khadijah, Mahirah, baku da baki ne?"
"Mommy.... Kachallah house zamu je. Ba zamu iya zama a nan ba, idan kina so mu zauna ki zaɓi ko mu ko macijin ki"
Bilkisu ta yi mamakin ƙarfin halin Mahirah. Yarinyar da ada bata iya buɗan baki tayi magana idan tana wajen sai gashi ita ce ke ɗaga murya a gabanta. Ita fa yanzu ta kai matsayin da babu wani mahaluki da zai ɗaga mata murya, not her parents, not her husband and especially not 'ya'yan data haifa balle bare.
Hannu ta ɗagawa guards ɗinta masu suna Vayentha da Mistica nan da nan suka sara mata suka bar falon da sauri.
Bayan fitan su Bilkisu ta maida dubanta ga Mahirah tace "ni kike ɗagawa murya Aisha, are you cra...zy" ta wanke Mahirah da mari sai da yarinyar ta faɗi ƙasa.
"Nobody shouts at me. Nobody gives me orders. Kai ku sawa ran ku cewa daga yanzu babu mai fita daga gidan nan sai da izinina. Kachallah house or not babu inda zaku je daya wuce makaranta, Islamiyya ma na soke shi daga yau, zan sa malami ya dinga zuwa gida yana koyar da ku. Now get out of my sight"
Kafin ta ƙarisa maganar Nana ta yi sama a ɗari. Mahirah kuma ta miƙe riƙe da fiskarta tace "Mommy dan Allah ki bari mu tafi ko ba dan ni ba, Nana zata iya suma idan ta sake ganin macijin nan, Junior ma..."
"Oh! Ba za ki dena magana ba kenan. Mahirah ni kam aiko ki aka yi ne?"
Mahirah ta juya zuciyarta cike da ƙunci tana addu'ar Allah ya shiryi mahaifiyar su.
***
*Ya Hayyu Ya Qayyum. Ya Hayyu Ya Qayyum* abinda Asiya ke maimaitawa kenan lokacin da warden Maida ta buɗe ƙofar cell ɗinta.
"Asiya Kachallah ki fito Lawya zata ganki"
Lokacin da suka ƙarisa wajen da Barr. Zaytoonah ke jiranta sai Asiya ta yanki jiki ta faɗi ƙasa. Warden Maida ta daka mata tsawa akan ta tashi, sai dai tana ƙoƙarin tashi ta sake faɗuwa saboda jikinta da babu ƙwari. Warden ta sa kulki ta ɗan shureta hakan yasa Barr Zaytoonah ta daka mata tsawa.
Bayan fitan warden Maida Asiya ta ƙyaftawa Barr Zaytoonah ido, Zaytoonah ta ɗaga mata babbar yatsa alamar jinjina.
Ba wani magana suka yi mai tsawo ba daya wuce ta kwantar da hankalinta komai zai tafi dai dai.
"Barr Zaytoonah jaridar"
Zaytoonah ta fito da jarida daga jaka ta miƙa mata, hoton Gwamna Saifuddeen daya ke shafin farko ne ya ɗauke mata hankali. *Gwamna Saifuddeen Kachallah ya riƙe albashin ma'aikata*
"Wannan watan ma bai biya albashi ba ko?" Asiya ta faɗa a hankali
"ya rage albashin malamai ma ki duba shafi na biyar zaki gani"
Duk da Asiya ta sani shafi na biyar shine shafin da Zaytoonah ta rubuta mata saƙo amma a yanzu ta fi damuwa da chanjawar da Gwamna yai, wai wata biyu kenan bai biya albashin ma'aikata ba.
Ta buɗo shafi na biyar ta fara karanta saƙon da Zaytoonah ta rubuta.
"Zasu kawo Timothy mutumin da BBC eye tayi hira da shi, na san an riga an biya shi akan ya nuna cewa ke ce uwar ɗakinsa, amma kar ki damu na san yadda zan yi na rushe duk wani hadda da aka sa shi yai. There's hope, ki cigaba da addu'a"
Asiya ta rintse ido sai hawaye. Ba komai ke damunta ba fiye da yadda Gwamna ya koma azzalumi.
***
A zaman kotu na gaba, Barr. Zaytoonah ta gabatar da video da ta naɗa lokacin da warden Maida ke ƙoƙarin ture Asiya tana mata tsawa.
Ta yi nuni da cin zarafin client ɗinta da aka yi bayan kotu bata zartar da hukunci akanta ba. Idan Kotu ba ta bada bail ɗin Asiya ba hukumar human right zasu shigar da ƙara saboda an take haƙƙin Asiya.
Da wannan kotu ta bada bail ɗin Asiya, amma zata zauna under house confinement ba me zuwa wajenta kuma ba fita sai idan zata je kotu ko kuma idan akwai emergency.
Bilkisu na jin wannan labari ta dinga ihu dan a yadda ta tsara Asiya ba zata bar kurkuku ba sai ta serving jail sentence na aƙalla shekaru goma.
"Ban gane an bada bail ɗinta ba, yaushe za a gabatar da Timothy ne?"
"Sorry Boss Lady ya kamata Agent Dahlia ta zo da shi kotu wannan zama da aka yi amma bata zo da shi ba, i think... "
" Don't think Lamara, you should act" Bilkisu ta daka masa tsawa.
***
Ranan da aka maida Asiya gida haka ta dinga ƙarewa ɗakinta kallo domin ya mata faɗi, zaman sama da wata ɗaya da tayi a ɗan ƙaramin ɗakinta na kurkuku sai take ganin ɗakinta na gidan Gwamna ya zamo tamkar wani mansion.
Bata yi tunanin ganin kowa ba dan Zaytoonah ta faɗa mata cewa babu wanda zai zo wajenta aside ita da take lawyarta sai kuma masu kawo mata abinci. Ko ina Sumayya da Jummai suka shiga? bata gan su ba har aka shigo da ita cikin falonta. Kuma ya kamata ace suma sun tsaya a ƙofar gida kamar yadda Yaya Bello ya tsaya suka gaisa a tsanake.
Lokacin da ta yi sallar Isha sai ta kwanta dan ta huta amma sai ta kasa bacci, ta takure gefe guda tana maƙyarƙyata. Yadda sauro suka cizeta a kurkuku, ka ɗauka duka sauron cikin kurkukun ne suka tare a ɗakinta.
Washegari da safe kamar Barr. Zaytoonah ta san bata da lafiya, lokacin da ta zo sai ta taho da wata likita mai suna Dr Hoodah. Ko dama zazzaɓin jira yake ta sha magani, tana shan magani ko minti shabiyar bai kai ba ta fara kela amai. Ƙarshe dai allura aka mata aka saka mata ledar ruwa saboda ta samu ƙarfin jiki.
Kwananta na biyu a gidan da ta samu ta ci abinci sai gashi ta ɓarke da gudawa saboda system ɗinta ya fara sabawa da abincin prison.
***
A yau ma Gwamna ya sake yunƙurin zare jiki dan yaje ya duba Asiya amma yana buɗe ƙofar ɗakinsa yai kiciɓis da macijin Bilkisu ya fasa kai yana zaro harshensa. Ƙirjinsa ya buga dam yai saurin rufo ƙofan ya koma ya kwanta.
Tunda aka bada bail ɗin Asiya Bilkisu ta tare a ɗakinsa da kwana, rabon da ta kwana a ɗakin har ya manta, amma tunda aka sako Asiya ta dawo kwana ɗakinsa. Ta riga ta masa kashedin akan bata yarda ya je ya ga Asiya ba amma duk da haka idan ya kwanta sai wani sashe na zuciyarsa ya dinga ingiza shi akan yaje ya dubata musamman da yaga videon da ya watsu a media na yadda ake maltreating matar gwamna a kurkuku.
Gwamna ya dinga juyi ya kasa bacci, Asiya ce a ransa, Asiya yake son gani. Ƙarshe ya miƙe ya je ya ɗauko maganinsa ya sha guda huɗu maimakon ɗaya, duk da haka ya jima kafin bacci ya ɗauke shi...
***
Nana ta shige banɗaki a sulale dan bata so ta tayarda Mahirah. Tunda ta fara shan ƙwaya saboda ta dena jin tsoron macijin Mommy sai kuma muguwar sha'awar shan ƙwayar ya dawo mata fiye ma da da, sai abinma ya zamo kaman bata taɓa dena sha ba.
Ta buɗe wata baƙar leda da Kabir ya bata a school bayan ta bashi dubu goma cash. Jikinta har rawa yake lokacin data fito da ƙaramar takarda da aka nannaɗa ƙwayar a ciki, ta zuba rabin garin da ke cikin takardar akan cover na toilet sit, ta ja layi guda uku da garin cocaine da ta zuba sannan ta toshe hancinta ɗaya ta zuƙi garin da ɗaya hancin, ta girgiza kai sannan ta sake zuƙan sauran layuka biyu data zana sai a sannan ta fara jin kanta dai dai. Ta maida sauran ƙullin garin cikin leda ta cusashi cikin aljihun pyajamas ɗinta sannan ta koma ɗaki ta kwanta, wannan data shaƙa zai kaita har rana sauran na ledan zai kai mata zuwa dare, gobe Kabir zai kawo mata na dubu hamsin.
Bata jima da kwantawa ba Mahirah ta tashi sallar Asuba. Bayan ta yi alwala ta zo ta tashi Nana sallah.
Da alwalan da sallar duka babu wanda Nana tayi cikin nitsuwa dan dai tayi sallah ne amma bata san ma takamaimai mi take faɗa ba a cikin sallar. Tayi sujjada ya yi sau biyar kafin ta sallame. Hankalin Mahirah na kan Qur'ani da ta ke karantawa bata lura da irin shirmen da 'yar uwarta ta dinga yi a sallah ba.
***
Yau aka gurfanar da Timothy Igwe a gaban kotu, mutumin da yai iƙirarin matar Gwamnar jihar Congo yake wa aiki.
Bayan alƙalin Gwamnati yai masa tambayoyi. Tamkar wanda yai hadda haka Timothy ya dinga jero amsoshin tambayoyin babu ko fargaba ko wani gargada.
Bayan an ba wa Barr. Zaytoonah damar yi masa tambaya abinda ta fara yi shine tace a kira mata Asiya Kachallah. Gaba ɗaya sai aka fara kallon kallo saboda ga Asiyar da kowa ya sani tsaye a witness box.
Bayan matar da aka kira ta zo ta tsaya sannan Barr. Zaytoonah ta mayar da dubanta ga alƙali tace " wannan mata da kuke gani sunanta Asiya Kachallah, shekarunta hamsin da biyu a duniya kuma ta kasance cousin ga Alhaji Sani Kachallah"
"Objection my Lord Barr Zaytoonah ta sake layi daga abinda ake magana a kai"
Alƙali yace Barr Zaytoonah ta fito fili ta bayyanawa kotu mi take nufi.
"Ina so kotu ta tuna da bayanin Timothy Igwe a wannan video inda yace matar Gwamnar jahar Congo yake yiwa aiki, sannan ina so kotu ta tuna cewa yanzu kuma Timothy ya bayyanawa kotu cewa Asiya Kachallah yake yiwa aiki. A lokacin da yace matar Gwamnar jahar Congo yake yiwa aiki matan Gwamnan Congo su biyu ne, so Bilkisu Kachallah is also a suspect. Sannan yanzu da ya ce Asiya Kachallah yake yiwa aiki wannan mata mai suna Asiya Kachallah zata iya zama suspect saboda sunan client ɗina *Asiya Shahidah Faruƙ Baba* kafin aure da kuma bayan aurenta. So a nan, ya nuna cewa Timothy ya chanja magana kuma ƙarya yake yi"
"Objection my lord" Lawyan Gwamnati ya faɗa da ƙarfi.
"Objection sustained"
Barr. Zaytoonah ta girgiza kai dan ta san an siye alƙalin, idan ba haka ba abinda take faɗa yana kan hanya bai kamata a dakatar da ita ba.
"My Lord, Mr Timothy ya ƙi bayyana suna ne saboda yarjejeniyar da akayi da BBC eye kenan kafin a saka shi a documentary da aka yi akan safarar miyagun ƙwayoyi. Ina so kotu ta tuna da irin muggan ƙwayoyin da aka samu a ɗakin Asiya Kach... Asiya Faruq Baba"
"Objection my Lord" Barr Zaytoonah ta faɗa a fusace...
***
"Shikenan Mommyn Alinah. Nagode da ƙoƙarin ki akaina"
Abinda Asiya ta faɗa kenan a hankali dai-dai za a fita da ita.
"Asiya, bai ƙare ba, we will appeal, sai mun je har supreme akan gaskiyar mu" Barr. Zaytoonah ta faɗa kamar zata yi kuka.
Lokacin da aka fito da Asiya idan kaga ruwan jama'a a bakin kotun ka ɗauka sarauniyar ingila ce zata fito.
Da ƙyar aka samu aka shigar da ita mota dan mutane dayawa kowa na son ganin Asiya...
Bilkisu Kachallah tayi murmushi ganin yadda ake tura Asiya cikin mota duk dama an rufe fiskarta da gyale amma ba ƙaramin nishaɗi ta ji ba ganin maƙiyiyarta a hanyar zuwa kurkuku.
"Ten years imprisonment, na tabbata wannan lawyar zata ɗaukaka ƙara"
"Sai me idan ta ɗaukaka ƙara, we'll keep bribing the judges, wanda ya ƙi yi mana abunda muke so mu kau da shi"
COS ya ɗan yi shiru sannan yace "what's next? Boss lady"
Bilkisu ta yi murmushi tace "ka aikawa mai martaba da takardar kira"
COS ya kalleta cikin rashin fahimta. Maimakon ta bashi amsa sai tace yai abinda tace kawai...
2
*Congo Prison Female Ward*
Ɓangaren mata na kurkukun yana da hawa har guda huɗu. Wannan hawa-hawa kuwa shi ake kira da iya kuɗinka iya shagalinka. Tun daga lokacin da aka kawo firsuna to ma'aikatan kurkukun za su tsarge maka wannan mataki-mataki da aka tsara wanda kuwa duk dan saboda neman kuɗi, son zuciya da kuma rashin gaskiya ne aka ƙirƙiri hakan.
Idan kai faƙiri ne, yaku bayi, marar gata to chan general cell za a kaika inda zaka zauna da inmates sama da hamsin. A dake ka, a ci zarafin ka babu wanda ya damu da kai, ƙarfin ka da wayonka ya ƙwace ka. General cell wato A-ward ake kira da Ghetto cell.
Idan kana da 'yan chanjin ka za a kaika B- ward inda ake kira Grade-3 a nan kowanni firsina yana biyan dubu biyar a wata, a shekara dubu sittin kenan. Firsina biyar zuwa shida ake zubawa a ciki idan kun yi rabo ku zama ku huɗu amma ba a saka ƙasa da haka. Banbancinsa da Ghetto shine akwai banɗaki da iya 'yan ɗakin zasu dinga amfani da shi sannan akwai fanka a ɗakin.
Hawa na uku shine C-ward da ake kira Sarauniya-Hall, a nan mutum biyu ake sawa a ɗaki, kowannensu yana biyan dubu shabiyu a wata. Banbancinsa da Grade-3 shine banɗakinku standard ne akwai ruwa a famfo, akwai shower, akwai fanka, sannnan idan babu wuta idan aka kunna generator zaku samu wuta. A da Sarauniya Hall shine jin daɗin ƙarshe a kurkukun kafin kuma shekaru kusan bakwai da suka wuce aka gina D-ward..
D-ward shine mataki na ƙarshe wanda shine ƙololuwa, nan ne gidan ajebos wato yaran 'yan siyasa da attajirai dama manyan 'yan kasuwa mata da aka kama da laifi. Yawancin waɗanda ake sawa a ciki ma ba su cika jimawa ba, dan da an kawo mutum yayi ɗan watanni zuwa shekara zaka ga an sake mutum saboda anbi ta ƙarƙashin ƙasa an gyara shari'ar da aka yanke da farko.
Aso rock kaman yadda ake kiran wajen, waje ne na hutu, dan idan kana wajen ba za ma ka ɗauka kana cikin prison ba saboda abubuwan more rayuwa da suke wajen kaman kana gida ne. A wannan waje kowanni ɗaki mutum ɗaya ne a ciki sai wanda ya ɗauko guard daga Ghetto cell wanda duk wannan na cikin kuɗin da zaka biya. Guard firsina ne da zaka ɗauka kana bashi 'yan chanji wani zubin ma baka bada komai just saboda samun wajen kwanciya mai kyau da rashin takura shikesa wasu ke rububin 'yan Aso rock su ɗaukesu a matsayin guard. Guard kaman mai aiki ne, gyara ɗakin VIP dake Aso rock, wanki, wanke-wanke da duk wani aikatau. Saboda yawanci 'yan Aso rock basa cin abincin gidan kurkukun, guard shine zai dinga yin girki.
'Yan Aso rock har alfarmar amfani da waya suke da shi duk da dai ba wai an yarda bane amma iya kuɗinka iya shagalinka dan haka kuɗin da ake biya yana covering duk wani rules da zaka breaking a prison ɗin.
Prison officials su ke karɓan aike su yiwa 'yan Aso rock siyayya saboda 'yan chanjin da za su samu dan ko abun goma ka siya to zaka iya sayar da shi ɗari ko ɗari da hamsin kuma za a biyaka.
Kowanni ɗaki a Aso rock ana biyan dubu arba'in a wata, yana kamawa dubu ɗari huɗu da hamsin idan zaka biya kuɗin shekara lokaci guda.
Idan kana Aso rock ko uniform ɗin firsina sai ka ga dama ka saka. Akwai tsaro a wajen dan ba kowanni firsina ke shiga anyhow ba, idan kai ba guard bane a wajen to sai da izinin warden kafin ka shiga. Yawanci ma abinda zai sa a barka ka shigan sai idan zaka shiga kayi kitso, wanki ga waɗanda basu ɗauki guard ba ko kuma zaka yi tallen hajarka wanda yawanci ƙwaya ne saboda kaso hamsin na 'yan Aso rock ba a rasa su da shaye-shaye duk da kuwa wasun su shaye-shayen ne dalilin kawo su wajen.
Akwai Isolation Hall wanda ba kowa ne ya san da zaman wajen ba. Hall ne daya ƙunshi ɗakuna goma, a nan ake ɓoye mutum idan ba a so a san da zaman shi a cikin kurkukun. Wani lokaci akan kawo mutum ba bisa ƙa'ida ba a rufe shi a wajen a dinga gallaza masa azaba.
Da sashen mata babu Isolation hall sai daga baya aka ware wani tsohon gini aka maida shi isolation lokacin da aka ɓoye wata karuwa data san sirrin wani ɗan siyasa. Karuwar tayi shekara tara a isolation kafin daga baya aka cireta aka maidata cikin sauran firsinoni saboda wanda yasa aka kawota ya riga ya mutu...
Sati biyun farko da Asiya tayi a kurkuku tayi sune cikin kaɗaici dan ɗakin nan dai dake isolation hall da aka rufeta da farko nan aka sake maidata. Sai kuma kwatsam aka zo aka chanja mata ɗaki aka maidata cikin sauran firsinoni a Ghetto cell.
Chief wardress da Bilkisu Kachallah ke bawa kuɗi akan ta rufe Hansa'u sannan ta ware Asiya gefe ta dena bawa sauran officials dake ƙasanta kuɗin toshe baki. Infact kuɗin da ake bata yanzu shaguna biyar ta gina ta zuba kaya ana mata kasuwanci.
Wardens da suka ga an dena basu komai sai duk suka fita harkan Asiya. Shine ma yasa suka fito da ita daga isolation hall suka kaita Ghetto dan babu wanda ya biya mata kuɗin haya balle a sakata a ɗaya daga cikin VIP cells da suke da shi.
Lokacin da aka shigo da Asiya cell 3 a cikin ghetto firsinonin ciki sai ihu suke suna faɗin "ga Excellency, ga Matar Gwamna fah".
Da gangan aka sakata a cell 3 saboda nan ne aka haɗa taron rough firsinoni. Duk wani mugunta a kurkukun to ya ƙare a cell 3. Waje ne da aka haɗa mata 'yan ƙwaya, ɓarayi, 'yan lesbian, da mugayen mata masu take ƙanana.
A da cell ɗin mutum arba'in da biyu ne a ciki amma lokacin da aka kawo Asiya wasu an riga an sallamesu wasu kuma sun zama guards a Aso rock dan haka basa kwana a ghetto. Mutum ashirin da tara ke cell ɗin, Asiya ta zama cikon talatin.
Asiya ta rufe idonta ta buɗe bayan ta ji ƙaran rufe cell ɗin da aka yi. Taron mata ne daban daban, wasu yara da ba za su haura shabakwai, shatakwas ba. Wasu manyan mata 'yan 20's da 30's haka, sai ɗai ɗaiku da za su haura shekaru arba'in.
"Ku turota ta kwashi gaisuwa" Asiya ta jiyo wani kakkausan murya daga chan ƙuryan ɗakin. Wata siririya da ke lashe baki tunda aka shigo da Asiya ta kama hannunta ta jata har gaban wata ɗikekiyar mata da ke zaune akan bokitin ƙarfe ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya, wata firsina na mata fifita.
Siririyar yarinyar tace " ki tsugunna ki gaishe da Maama dan ki samu alfarma a nan"
Asiya ta kalli yarinyar sannan ta maida dubanta ga matar da aka kira Maama wacce da gani girman fuku-fuku ce babu shekaru dan Asiya zata iya rantsewa bata kai shekaru talatin ba.
Wata mata da man bleaching ya gama ƙona mata fiska tace da Asiya "Ekselensiya kiyi abinda aka ce dan shine gatan ki a nan"
Siririyar yarinyar tayi yunƙurin tura Asiya gaban Maama Asiya ta kama hannun yarinyar ta kalleta da rinannun idanunta ta ce "kar ki kuskura ki sake taɓa min jiki"
Yarinyar ta fara ƙyafƙyafta ido jikinta na ɓari dan idanun Asiya sun matuƙar tsorata ta.
Ta ture yarinyar gefe ta kalli Maama dake ta hura hanci ta ce " na yi tunanin mata ake cewa suna da tausayi amma ban ɗauka akwai tausayi ko imani a idanun ki ba. Kina jira na tsugunna na gaishe ki ko? Well kin yi kaɗan domin har yanzu dai ban ji ance Gwamna ya saki Asiya ba ko? Har yanzu Matar Gwamna nake, and i deserve respect"
Ta juya ta fara kallon sauran matan da suka zuba mata idanu kowa da abinda ke ransa, sun san al'amarin 'yan siyasa a ƙasar azimun ne, ba mamaki gobe a cire Asiya daga kurkuku a bata wani matsayi mai girma.
Ganin kalamanta na ƙarshe ya shiga jikinsu sai ta fara naɗe hannun rigan uniform ɗinta tace "kowacce shegiyar data rena kanta ta taƙale ni ta gani. Zata gane cewa ni ba girman indomie bace, da tuwon masara mai ƙarfi na girma. Sannan kafin na zama Matar Gwamna, Asiya-Shahidah nake kuma bana ɗaukan wargi"
Kowa na jiran Maama ta yi magana amma shiru ko uff bata ce ba, infact yadda hanjin cikinta suka kaɗa har wani gudawa-gudawa ta fara ji.
Asiya ta samu chan ƙuryan ɗakin opposite da Maama ta zauna ta miƙe ƙafa ta jinginar da kanta ta rufe ido kamar mai bacci.
"Your Excellency ga bargo ki shimfiɗa a ƙasa" wata guntuwar mata ta faɗa tana miƙa mata bargon hannunta na rawa.
Faali ta azabtu a hannun Maama, ganin Asiya ta taka Maama yasa ta ke son samun madafa a wajen Asiya saboda ta samu nitsuwa.
Ba tareda Asiya ta buɗe ido ba tace "bana buƙata, nagode"
Duk da haka Faali sai da ta ajiye bargon a gefen Asiya ta zauna kusa da ita ƙirjinta na bugawa buk-buk-buk. Watanni shida da tayi a kurkukun sai da ta fara zargin anya halittarta bata koma irin ta jakuna ba kuwa, abubuwan data dinga yi yafi ƙarfin a kirata da mutum. Maama da wata da ake kira Suwaiba sune suka sata a gaba. Bauta, duka, da kuma biyan buƙatarsu saboda dukkansu maneman mata ne.
Har dare kowa kaffa kaffa ya dinga yi da Asiya. Wajen da zata kwanta ma space sosai aka bata wanda ko Maama ba a taɓa bata makamancin space haka ba.
Haka Asiya ta kwanta a ƙasa kamar sauran, duk da cikin masu barguna kusan mutum uku sun mata tayin amfani da bargonsu amma ta ƙi.
Washegari lokacin da aka zo buɗe su warden Bisola ta lura da Asiya a cell 3. Mamaki ya kamata dan bata san ma an ɗauketa daga isolation hall ba.
Wannan yasa bayan ta gama abinda take ta je ta samu Chief Wardress domin ta gwada sa'arta.
Bayan tayi bayani akan rashin dacewar saka Asiya a ghetto, Chief wardress ta ɗan jingina kai tana tunani. Tabbas maganar Bisola akwai ƙanshin gaskiya, what if the table turns aka saketa tunda anyi appealing case ɗinta. What if Gwamna ya maida ta gidansa ya bata matsayi fiye da Bilkisu Kachallah and she choose to revenge.
"Ma, ɗakin Madam Chess akwai vacancy, yarinyar da aka sake a grade-3 sati biyu da suka wuce akwai sauran kuɗin hayarta na wata huɗu. I think a bawa Hajiya Asiya ɗakin ta zauna kafin a samu mai biya mata VIP apartment"
Muryar Bisola ya katse mata tunani.
Ta kalli Bisola tace "Ok, a maida ta chan ɗin"
***
Ɗakin da aka maida Asiya su uku ne a ciki ta zamo ta huɗunsu. Lauratu, Josephine da ake kira JP, dukkansu ba su fi shekara talatin zuwa talatin da biyar ba. Ta ukun su ita ce Madam Chess. A shekaru shabakwai da tayi a kurkukun babu wanda ya san sunanta na ainihi. Farkon kawota wardens ɗin kurkukun suna kiran asalin sunanta da ke jikin register wato Flora amma daga baya da firsinoni suka saka mata Madam Chess sai sunan yabi bakin kowa kusan ma an manta ainihin sunanta yanzu, sai dai ko idan an dubo register. Ba komai yasa ake kiranta haka ba sai dan yawan buga game ɗin chess da ta ke. Tun tana yi da duwatsu har kuma wani warden a lokacin ya siyo mata chess board aka bata. Ba ta cika magana ba sai ta kama, idan bata buga chess to zaka ganta tana karanta littattafai. Kaf cikin firsinoni dake kurkukun itace ake mugun bawa girma, da firsinonin da ma officials na kurkukun.
Kwana biyun da Asiya tayi a ɗakin ba ta kula kowa ba, Lauratu da JP sun yi ƙoƙarin taƙalarta da taɗi amma ta share su, ta lura abin nasu harda iskanci dan har da mata gatse wai excellency zasu kirata ko first lady.
Madam Chess tana lura da yanayin Asiya tunda aka kawota ɗakin, ta ji ana gulmanta tun ranan da aka kawota prison ɗin a karon farko, ta san shekaru goma aka yanke mata amma tana da yaƙinin nan ba da jimawa ba za a saketa.
Yau ce rana ta huɗu da Asiya ta koma ɗakin su Madam Chess. Kamar kullum ta miƙe ta shiga banɗaki ta yo alwala ta zo ta fara sallar nafila. Raka'a shabiyu zata yi amma tana yin huɗu ta zauna ta fashe da kuka. JP da Lauratu sunyi bacci sai Madam Chess kaɗai da ke karanta wani littafi mai suna 48 laws of power na Robert Greene.
Addu'a Asiya ke son yi amma bakinta ya kafe. Gwiwarta yayi sanyi tun lokacin da aka yanke mata hukunci a kotu, zuciyarta ya karaya lokacin da aka dawo da ita Kurkuku a karo na biyu. Sauran burbuɗin yaƙinin fita daga jarrabawar nan yana neman kufce mata. Imaninta ya fara girgiza lokacin data fara tunanin auren Gwamna Saifuddeen shiya kawo mata wannan musibar, da Ubayd ta aura da duk wannan bai faru ba.
Ganin sheɗan na shirin sakata yin saɓo sai ta fara maimaita kalmar shahada a zuciyarta.
Madam Chess na zaune akan katifarta tana lura da yadda Asiya ke ta sheshsheƙar kuka daga inda tayi sallah.
Bata yi niyyar yi mata magana ba amma kuma wani zuciyar na ingizata akan ta faɗa mata wani abu ko za ta dena tunanin ita kaɗai ce ke da matsala a wannan gida.
"Kina kuka saboda kina amsa laifin da ba ki yi ba ko?"
Asiya ta yi shiru dan ƙarshen maganar kawai ta ji.
"At least na ki case ɗin za a iya gano gaskiya nan bada jimawa ba a wanke sunanki"
Wannan karan Asiya miƙewa ta yi ta juya tana kallon Madam Chess duk dama hasken lamp ne a ɗakin dan babu wuta. Ta ɗauka matar kurma ce saboda tunda ta shigo ɗakin ba ta ji ko tari daga gareta ba balle magana.
"Wasu sukan ƙare rayuwarsu a nan gidan ba tare da sun aikata laifi ba, wasu kan mutu a haka, wasu kuma saboda wannan trauma ɗin har su mutu ba za su taɓa zama dai-dai ba.
"Kina ganin zaki shekara goma a kurkuku ne?"
Asiya ta buɗe baki zata yi magana amma ta rasa abin faɗa.
"Ki kwanta kiyi barci, kukan da kike ciwon kai da hawan jini zai sa miki ba zai chanja fate ɗin ki ba"
Daga haka sai ta rufe littafin hannunta ta ajiye a gefe ta kwanta.
Asiya ta jima tana kallon Madam Chess kafin itama ta je ta kwanta a ƙaramar katifar da ke gefen katifar Lauratu...
3
Mai Matarba Sarkin Congo bai samu amsa kiran first lady Bilkisu Kachallah ba, sai ya aika mata da wakilinsa wato Galadiman gari. Wannan abu da yai ya sosa ran Bilkisu dan a ganinta indai Gwamna nada ikon ya kira sarki ya zo to itama tana da wannan damar.
Haushi yasa bata sanar da Galadima ainihin dalilin kiran Sarki da ta yi ba. Ta dinga tufka da warwara kan yadda zata ɓullowa wannan lamari ƙarshe ta yanke hukuncin tana dawowa daga tafiyar da zata yi zata je fadan da kanta ta faɗawa Mai Martaba abinda take so...
Gwamna yana zaune a falonsa yana duba wasu takardu ya ji sallamar mace. Saura kaɗan ya kira Asya saboda ji yai kamar irin sallamarta. Ganin ƙanwar matarsa sai ya sake fuska yana murmushi.
"Yaya fushi sosai nake da kai, shikenan yanzu idan mun kira ka ba zaka ɗauka ba kenan. Da dai na san Yayanmu ba haka yake ba"
"Sadiya kenan, na isa na share kiran ki"
Ya faɗa yana duba wayar sa sai gashi missed calls ɗinta har uku.
"Kiyi haƙuri Wallahi wayar a silent take saboda ina aiki"
"Ba wani, tun kwana huɗu da suka wuce nake kiranka baka ɗauka, yanzu ma Mahira na kira tace min kana gida shiyasa na zo"
Gwamna ya haɗa hannunsa biyu yace "Afuwan ƙanwata, kwana biyun nan aiki ya min yawa be"
Zama ta yi kujerar da ke opposite ɗinsa, ta ajiye jakarta a ƙasa sannan suka fara gaisawa. Duk cikin cousins ɗinta maza kai har matan ma Saifuddeen kaɗai ta yarda da shi kuma ta saba da shi har suke mutunci sosai duk da kuwa basa jituwa da matar sa.
"Yaya ba maganar siyasa ya kawoni ba, dan na san kai kanka ka san people are dissapointed in your Government"
Gwamna ya sauke ajiyar zuciya yana kauda kansa daga kallon Halima Kachallah.
"Maganar Anty Asiya na zo yi. Yaya Saif i've being going to Congo prison tunda aka kaita chan amma duk lokacin da naje sai a hanani ganinta. Mi yake faruwa ne wai?"
"Sadiyyyaah"
"Na san kai Gwamna ne but shikenan idan kai ba zaka je ka dubata ba sai muma ba za a bari mu ganta ba. This is cruel gaskiya. Ni yanzu zuwan da nayi na zo ka rubutamin permission ne a barni na ganta duk lokacin da na je dubata"
Nana ce ta shigo falon da gudu kamar wacce aka korota.
"Daddy Yaya Bello yace na kawo maka key"
Maimakon ta bashi key ɗin a hannu sai ta jefar da shi ya faɗi gefen ƙafarsa.
"Haba Nana, idan kika same shi a ƙafa yanzu mi zaki ce"
"Anty Halima ba ki san ina buga basket ball ba, na san ba zai same shi ba ai"
Halima ta riƙe baki tana mamakin wannan kalar rashin tarbiyyan.
Gwamna ya ɗauke zancen da cewa "Nana kira min shi Bellon"
Har ta fice daga falon Halima bata dena mamakin Nana ba. To dai ita ance mata tunda ta dawo daga Rehab center ta chanja amma gaskiya bata ga chanji ba indai wannan ake kira da chanji.
Minti uku sai ga Yaya Bello ya shigo. Halima na ganinsa ta fara murmushi tana faɗin "Yayanmu"
Yaya Bello ya zauna a ƙasa yana gaisheda Gwamna.
"Bello na ga ka aiko da key ɗin mota na miye kenan?"
"Allah ya ja zamanin ka, zan koma ƙauye ne, dama Asiya ce ta ɗaukeni aiki kuma bata nan"
"Ayi haka kuma. Ya kamata ka zauna ka dinga kai su Sumayya makaranta"
Yaya Bello ya sosa kai yace " Mai girma ai Sumayya ta koma cikin makaranta da zama "
Kunyar kansa ya ji kan rashin sanin halin da ƙannen matarsa suke ciki.
"Ka riƙe key ɗin, akwai aikin da zaka min nan bada jimawa ba"
Gwamna ya sa hannu ya ɗau key ɗin ya miƙawa Yaya Bello.
"Yayanmu idan aiki kake nema zan baka aikin tuƙi, dama kwana biyun nan idan ina tuƙi sai na dinga jin ciwon kai"
Yaya Bello yace "to ai ni Dreba ne ba Likita ba. Dreba na maganin ciwon kai ne?"
Mi Halima zata yi banda dariya. Gwamna ma sai da ya ɗan murmusa.
Lokacin da Yaya Bello ya miƙe zai tafi Halima tace " Dan Allah ka jirani idan na gama da Gwamna zamu kaiwa 'yar uwarka ziyara"
"Da gaske?" Yaya Bello ya faɗa cike da ɗoki. Yayi kewar ƙanwarsa ba kaɗan ba.
"Allah" Halima ta kwaikwayi maganarsa
Bayan tafiyarsa Halima ta kalli Gwamna ta ce " Your excellency ka rubutamin permit ɗin"
Gwamna ya ce ina zuwa.
Shigewarsa ɗaki keda wuya Alhaji Abdullahi ya shigo falon sai wani ƙanshi yake ta zubawa.
"Haly dubu" ya faɗa ganin Halima zaune tana danna waya.
Firgigit Halima ta yi ta miƙe tsaye tana dafe ƙirjinta. Jikinta ya shiga ɓari saboda sunan daya kira ya tada tsohon gembo.
"Manyan mutane kenan, ke ba a ganinki ma yanzu sai an yanki ticket. Miye sirrin ne na ga kin yi wani fresh fa"
Alhaji Abdullahi ya faɗa yana kashe mata ido.
"Haly dubu lafiyanki?"
Ya faɗa yana matsowa kusa da ita.
"Don't touch me, don't touch me, don't touch me" ta fara faɗa da ƙarfi saida Alhaji Abdullahi ya ja baya a tsorace.
"Sadiya? Are you ok" Gwamna ya kira cike da damuwa.
Gyaɗa masa kai ta yi ta zauna tana haɗa hannayenta da suke ɓari.
Jiki a sanyaye Alhaji Abdullahi ya kalli Gwamna yace " it seems na zo a bad time, dama maganar bikin 'yarka ce, na zo na ƙara jaddada maka cewa sati mai zuwa ne, ba zan karɓi uzurinka ba, you have to be there"
"Of course, taya zan missing auren 'yata"
Alhaji Abdullahi ya kalli Halima yace " ni kam Halima yaushe zaki kawo mana angon ne, gashi duk 'ya'yanki suna ta tafiya gidajen mazajensu
Hawayene ya fara silalowa a idanun Halima Kachallah. Taya Abdullahi zai samu nasara a rayuwarsa bayan abubuwan daya aikata. Taya zai samu damar aurar da 'ya'yansa bayan ya ɓata mata rayuwa. Taya nashi 'ya'yan zasu samu miji amma ita ta rasa. Taya zai iya buɗan baki ya mata gori bayan ya barta da gembon da har yau tana jin raɗaɗinsa.
Shekaru ashirin da huɗu da suka wuce ba zata manta ba, koda shi ya manta. She was a kid, she was just 9years.
"Haly dubu" sunan daya ke kiranta kenan a lokacin har ta sake da shi a matsayin babban Yaya. Ba sau ɗaya bane, sau biyar, sau biyar ya mata abinda ko maƙiyinta ba za ta so aiwa 'yarsa haka ba a wannan shekarun.
Aljanu aka ɗauka suka shafeta aka dinga neman magani har Maiduguri kafin daga baya Hajiyan Saudiyya ta tafi da ita wani zuwan da ta yi, lokacin shi Abdullahi baya ƙasar ya tafi masters na shi. Sai da ta shekara biyar a Saudiyya kafin ta fara dawowa dai-dai.
Akwai lokutan da ta tsani maza gaba ɗaya, akwai lokutan da ta ce ba za ta yi aure ba saboda ganin maza take tamkar Abdullahi.
Idan shi ya manta komai ita ba zata manta abinda ta fuskanta tana shekara tara ba.
Jakarta ta ɗauka ta fice daga falon. Gwamna yana kiranta amma bata kulashi ba.
Bayan fitar ta. Gwamna ya harari Alhaji Abdullahi yace "Allah ya shiryeka, ban san yaushe zaka girma ba. Taya zaka faɗa mata irin wannan magana kasan halin da take ciki. Son ranta ne ta ƙi auren?, ko ka taɓa kawo mata miji tace maka bata so?"
Alhaji Abdullahi yai shiru yana jin zafin abinda ya aikata a shekarun ƙuruciyarsa. She was 9 or 10 ba zai iya tunawa ba yanzu, amma ya san laifin daya aikata, he violated her when she was just a child.
Fitowan da Halima Kachallah ta yi cikin kuka zuwa shigewarta mota duk akan idon Yaya Bello ne. Koda ta shiga motar kifa kanta tayi a steering tana kuka. Dadda ta sani kuma ta faɗawa Babansu amma a lokacin sai cewa yai idan Haliman ta ƙara girma zai sa Abdullahi ya aureta. By the time Halima ta gama sakandare matan Abdullahi biyu. Lokacin da Halima ta ƙare degree ɗinta na farko sai Dadda ta sake yiwa Babansu tuni akan alƙawarinsa amma daya tuntuɓi Halima da maganar cewa tayi idan aka aura mata Abdullahi kashe shi zata yi ta kashe kanta shiyasa aka rufe maganar. Har Dadda ta rasu rashin auren Haliman na damunta musamman idan ta tuna abinda Abdullahi ya mata wacce itama bata sani ba sai a lokacin da ake yawon neman magani bayan abin ya faru da kusan satuttuka ma.
Yaya Bello ya fara buga glass ɗin motar Halima hakan yasa ta ɗago a firgice. Ƙoƙarin goge hawayen ta yi sannan ta sauke masa glass ɗin ta ƙaƙaro murmushi tace "Yayanmu"
"Hajiya Halima kina lafiya kuwa?, miya sameki kike kuka?"
"Ba komai, wata ƙawata ce aka ce ta rasu. Zan kiraka gobe idan zan je ganin Asiya"
Daga Haka ta rolling glass ɗin ta kunna motar ta fara reverse. Yaya Bello ya bita da ido yana mamakin wannan lamari dan bai yarda dalilin kukanta ba kenan akwai wani abu a ƙasa...
Ƙarfe taran dare ta kira shi a waya tace ya kawo mata irin abubuwan da yake sha yake manta damuwarsa.
"Hajiya Halima anya lafiyarki kuwa?. Abinda nima ke ƙoƙarin dena sha kike son sha"
"Ya zan yi Yayanmu. Ya zan yi?. Har yana da bakin yi min gori saboda zai aurar da 'yarsa. Ba zan taɓa yafewa ba, ko a lahira ba zan yafe masa ba" ta ƙarisa maganar tana fashewa da kuka.
Yaya Bello yai shiru yana sauraron kukanta. Ya ma rasa mi zai ce, duk da a da haushi take bashi amma yanzu ji yake inama yana da abinda zai share mata hawaye, ya yaye mata matsalarta.
Kusan minti ɗaya kafin aka kashe wayar, ya sake kiran numbar amma ba a amsa ba, ƙarshe kuma daya kira ya ji wayar a kashe.
Hankalinsa ya tashi, tunda ta fara maganar kayan maye kada fa ta je ta aikata abinda bai dace ba.
Isuhun ƙauyensu ya taɓa rataye kansa a jikin bishiya aka dinga cewa hauka ce ta kama shi, wasu kuma suka ce damuwa ce ta mai yawa.
Kasa haƙuri yai ya fita ya ɗau motar Asiya sai Kachallah house.
Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da ake yasa Halima ta sassauta sheshsheƙar kukanta.
"Anty Halima wai Bello na nemanki a waje. Anty Halima kin yi bacci ne?"
Mai aikin nasu Indo ba dai shirme ba kam.
Halima ta goge fiskarta tace "Indo kice masa na yi bacci"
"Anty kika ce me?"
Halima ta ɗan ɗaga murya tace "Kice masa" sai kuma ta chanja tace "ina fitowa"
Minti goma sai gata gaban Yaya Bello da ke tsaye gaban mota.
"Yayanmu zuwan dare haka"
"Yo ai kin tsorata ni, babbar mace da kuka ai akwai damuwa"
"Dama kuka na yara ne kawai?"
"A'a. Sai dai ina tsoron kada ki rataye kan ki irinna Isuhu. Shima lokacin da ya ke kuka kowa ya ɗauka Aljanu suka buge shi"
Halima tayi murmushi mai ciwo sannan tace "ba zan rataye kaina ba Yayanmu"
"Sai yanzu na ji hankalina ya kwanta. To sai da safenmu"
Juyawa yai zai buɗe mota ya ji ta ce "Yayanmu ka aureni dan Allah"
Yaya Bello ya juya kai gefe da gefe dan ya tabbatar da wani tayi maganar ba shi ba, sai ya ga babu kowa su biyu ne kawai a wajen.
"Ko ba ka sona ka aureni, ni ina son ka"...
***
Asiya da Madam Chess sun ɗinke sosai cikin kwanakin nan. Madam Chess ta mata alƙawarin matuƙar ta cita a wasan Chess da suke bugawa zata bata tarihinta da dalilin zamanta a wannan kurkuku. Har yanzu Asiya bata gama gane wasan ba shiyasa ko minti goma ba ayi Madam Chess ke cinta.
Lauratu da JP sun zama 'yan kallo a ɗakin dan walwalar da basu taɓa gani a wajen Madam Chess ba suke gani yanzu tun da Asiya ta zo ɗakinsu.
"Mommy dan Allah ki faɗa min. Ina zan iya karawa da ke bayan kin ɗau shekaru kina bugawa"
Madam Chess ta yi murmushinta na manya tace " ba ki da haƙuri kuma kina da gaggawa. Wannan su suke sawa na cinye ki tun a tashin farko"
Asiya ta zumɓura baki tana jujjuya knight ɗin dake hannunta, ta sake ganin board ɗin da kyau sannan ta maida knight ɗin data ɗauka ta ɗauki queen.
Madam Chess tace "Good move"
Tarayya da wannan mata yasa Asiya ta rage saka damuwa a ranta. Infact itama karatu ta ke yi a duk free time ɗinta tunda ba laifi ba a sakata aiki.
Ranan kwatsam sai aka kirata wai tanada baƙi. Jiya Barr. zaytoonah ta zo mata da albishir akan za a fara sauraron ƙara a court of appeal nan da kwanaki tara masu zuwa. To suwaye kuma suka zo? Ban da Lawyarta babu wanda ya taɓa zuwa dubata.
Lokacin data fita sai ga Halima Kachallah, Sumayya da kuma Jummai. Suka dinga ihun murna lokacin da suka ganta kamar wasu yara ƙanana.
Abinci mai rai da lafiya suka kawo aka haɗu aka ci. Duk yadda Asiya ta daure sai da ta yi hawayen farin ciki ba dan komai ba sai dan 'yanuwa rahama ne.
Labarin 'yan gidan su da ta samu da kuma dawowar Abba da Ale daga Makkah ba ƙaramin daɗi ya sata ba.
"Anty Asiya kar ki damu yanzu kam duk sati sai mun zo miki. Gwamna ya bamu permit babu wanda ya isa ya hanamu ganinki"
Asiya tace " nagode Anty Halima"
"Kiyi haƙuri. Na san kina tunanin bai damu dake ba amma wallahi ya damu. Ban san dai ya zan faɗa miki bane amma kamar Yaya Saif baya hayyacinsa, kowa complain yake"
"Nagode sosai Antyna ta kaina. Ya maganar Albino kuma?"
Asiya ta chanja maganar dan bata son maganar Gwamna dan yana taɓa mata zuciya.
Halima ta yi murmushi ta ce " ni yanzu nema nake a wajen Yayanmu amma na rasa gane kansa. Wai ce min yai nayi haƙuri ba zai iya da ni ba"
"Wani Yayanmun?"
Halima ta ɗan rufe fiskarta tana dariya.
"Dan Allah Yaya Bello kike so?" Sai kuma tayi saurin chanja maganar da cewa "kai nayi murna. Allah ya sanya alkhairi"
"Idan ya amince ba, kin san Yayan naki kaman mai matsa-matsai, inji ki da faɗa"
Asiya ta saka dariya harda tafa hannu. Rabonta da genuine dariya haka har ta manta...
***
Bilkisu Kachallah ta gama tsare-tsarenta, ta je Fada da macijiyarta amma lokacin data yiwa Mai Martaba maganar sarauta sai yai biris da zancen. Duk da ta lallami yai maganar amma hakan ya fusata ta matuƙa. Har take yi masa iƙirarin itama jinin sarauta ce. Mai Martaba tsoho mai dattaku ya maida martani da cewa Uba yake gareta idan har tana tinƙaho da jinin sarauta to dole ne ta yiwa magabatanta biyayya.
Bacci ranan ƙauracewa Bilkisu yai dan kota kwanta maganganun mai martaba ke yawo a kwanyarta. Sarautan Gimbiyar Congo take so kuma ko ana so ko ba a so sai an bata wannan sarauta.
Zuwa safiya wani tunani ya faɗo mata. Idan ta sa aka tsige sarki aka kuma ɗaura mahaifinta babu tantama sarautan da take so automatically ya zama nata. Da wannan tunani ta tunkari ɗakin Gwamna Saifuddeen Kachallah...
4
Lokacin da Bilkisu Kachallah ta shiga ɗakin Gwamna baya nan ya shiga banɗaki. Joter da ta gani akan gadonsa ta ɗauka.
*And then i kissed her* shine taken waƙar da yake rubutawa. Ba sai ta karanta ba ta san waƙar dan wa aka yita. Wani kibiyar kishi ne ya soki zuciyarta lokaci guda ta kama joter ta fara yagawa.
Gaskiyane she wants to outshine him, amma kuma soyayyar da take masa gaskiya ce. Shine namijin da ta fara so kuma take so har yau.
"Bilkisu" ta jiyo muryansa a bayanta. Ta juyo da rinannun idanunta da suka ciko da hawaye ta ce " baka taɓa rubuta waƙa danni ba. But, her"
"Ba abinda kike tunani bane, it's just a poem."
Watsa masa takardun hannunta ta yi tana faɗin " it's just a poem. Ni ba mahaukaciya bace Saifuddeen. Na san komai, na san ita ka ke wa rubutu, na san..."
"Assalamu Alaikum Daddy" muryan Mahirah ya katse ta.
Suna haɗa ido da Bilkisu annurin fiskar Mahirah ya ɓace.
"Ehen, miya kawo ki?"
"Dama...dama za mu je Kachallah house ne da su Nana"
"Ba inda zaku je"
Mahirah ta juya jiki a sanyaye dama ba wai Kachallah house ɗin za su je ba. Sun yi waya ne da Anty Halimah ta ke faɗa mata sun je prison jiya sun dubo Asiya. Shine ta zo tambayar Daddynsu suma ya basu izinin zuwa prison su je su ga Asiya dan ba ƙaramin kewarta suka yi ba.
Bayan fitan Mahirah daga ɗakin Bilkisu kasa ƙarisa maganar ta yi ta watsawa Gwamna mugun kallo sannan ta fice daga ɗakin.
Bayan ta samu zama da Chief of staff ta ke gaya masa buƙatarta na son a tsige Mai martaba. Maganar ta zamo masa banbaraƙwai. A wani dalilin za a tsige mutumin da yai kusan shekaru talatin da bakwai akan kujerar mulki.
"Boss lady idan ban katse miki hanzari ba. Bana tunanin abinda kike nema zai yiwu, babu dalilin da zai sa a ɗaga Mai martaba akan kujerarsa, mutane za su yi magana"
"I don't care!" Ta faɗa tana buga desk ɗinta.
"Ki sake duba maganar nan"
"Lamara Damana ina so ka nemo min dalilin da zai sa a tsige sarki"
Wannan karan COS bai yi magana ba sai miƙewa yai ya bar office ɗin. Bayan tafiyarsa Bilkisu ta kalmashe ƙafa ta sa hannu tana mammatsa kakkauran wuyanta. Yadda take jin kanta a gajiye ma ya kamata ta je spa ne a mata massage. Kiran sakatariyarta tayi ta ce ta haɗa mata appointment da wajen salon da kuma wajen spa treatment.
"Excellency Ma, Halal salon za a booking ko Prime beauty parlour?"
Har ta ce mata Halal salon sai kuma ta tuno cewa Asiya co-owner ce na Halal salon.
"Ki booking prime beauty"
Tana ajiye wayarta ta rufe idonta tana juyi akan kujerar. Ba zata taɓa bari Asiya ta fito a prison ba, duk abinda za ayi sai court appeal ma ta tabbatar da hukuncin farko.
Washegari aka shirya taro a gidan Bilkisu. Bayan kowa ya hallara a wajen sannan ta fito still ɗauke da macijinta. Bayan ta zauna a kujerarta na zinari sannan ta bada damar a fara meeting. Bayan an gama tattauna abinda ya dace sai kuma Bilkisu ta kawo maganar tsige Mai Martaba.
Dukkansu sai suka fara kallon-kallo.
Alhaji Sani Kachallah yace " babu fa'ida a cikin tsige Sarki"
"Exactly" Alhaji Macciɗo ya goyi bayan Alhaji Sani.
Bilkisu ta saukar da macijinta ƙasa ya fara yawo a ƙasa. Tuni Mr Paul ya ɗaga ƙafafuwansa ya aza bisa kujera yana rarraba idanu.
Suma sauran da basu ɗaga ba kowa yana shakkar wannan maciji da ke yawo a tsakaninsu.
Bilkisu sai da ta gama ƙare musu kallo sannan ta ce "lokacin kamfen Mai Martaba ya karɓi kyautar mota daga wajen Umaru Kwom, wannan ya nuna baya tare da mu kenan. Za mu cire shi mu ɗaura wanda ke tareda mu ɗari bisa ɗari"
Alhaji Sani ya buɗe baki zai yi magana amma sai ya kasa. Shi ɗan sarauta ne, idan aka tsige Mai Martaba kaman an ci mutuncin gidansu ne. Ba wannan bama, Mai Martaba tamkar uba yake a gareshi...
Lokacin da aka kawo wa Gwamna takardar ƙorafi akan sarki. Kan sa ne ya kulle, miye haɗin Gwamnatinsa da kuma motar da aka ce Umaru Kwom ya baiwa Sarki. Besides an bayar da motar ne shekara ɗaya da ta wuce, kafin ma a fara maganar zaɓe kenan.
Da Gwamna ya isa gida kuwa tuntuɓar Bilkisu yai akan maganar tsige sarki.
"Yes dole a tsige shi, sarki ya koma ɗan siyasa tunda yana karɓan kyauta a hannun 'yan adawa"
"Bilkisu Mai Martaba is our father. Kin manta cewa a cikin fadarsa aka ɗaura aurenmu"
"And so?"
"Ba zan iya ba, ba zan iya tsige shi ba"
A firgice Bilkisu ta juyo ta kalleshi dan da madubi take kallo tana shafa powder a fiskarta.
"Ba zan tozarta shi ba" Gwamna ya faɗa da kakkausar murya
Yatsun hannunta ta duba ta ga zobenta baya nan. Idan har tana al'ada malaminta yace ta cire zoben. Yanzu data fito daga wanka ta cire shi ta ajiye a kan dresser saboda shigarta banɗaki ta ga jini.
Gwamna ya ajiye mata takardar da aka kawo masa akan dresser ya fice daga ɗakin ya bar Bilkisu tana nishi sama-sama...
***
Yau ta kama ranan Lahdi, ta ko'ina ka duba firsononi ne ke kai kawo a cikin kurkukun. Wasu na wanki wasu na kitso wasu na yin karta wasu kuma suna buga ludo. Wasu taƙadarun ma sigari suke sha.
Asiya ta fito tana zazzagawa, ta rasa dalilin dayasa tun ranan da ta ga Hansa'u bata sake sakata a ido ba.
Tana tafiya tabi ta wani lungu, anan ta hango wata firsina riƙe da wuƙa a hannunta tana sheshsheƙar kuka.
"Dan Allah kar ki aikata, ki yi haƙuri mu yi magana"
Faali ta waiwayo ta kalli Asiya idonta fal da hawaye.
"Ki ajiye wuƙar a ƙasa Dan Allah"
"Ki barni na kashe kaina, bani da wani amfani a duniya"
"Ke ce kika bani bargo ranan ko? Miye sunanki?"
"Faali" ta amsa da muryan kuka
"Faali? Sunan yare ne?"
Faali ta girgiza kai tace "Falila ne ake kirana da Faali"
Asiya ta fara matsowa kusa da ita tana faɗin "Falilan ma kuskuren harshe ne amma Fadila ya kamata ya kasance. Kaman suna Bukhari ne da ake kira da Buhari, kaman sunan Faɗima da ake kira da Fatima"
Faali tayi murmushin yaƙe tace "mu 'yan ƙauye ina muka san wannan"
"A wani ƙauye kike?"
Faali tayi shiru ba ta ce komai ba sai hannunta da ke rawa.
Asiya ta yi saurin riƙo hannunta tace "Fadila ki sake wuƙar kin ji. Ran ki yana da daraja a wajen Allah shiyasa yace kada mutum ya kashe kansa ko ya kashe wani rai ba tareda haƙƙin da ya shar'anta ba"
Faali ta sake wuƙar ta fashe da kuka sosai. Asiya ta rungumeta jikinta tana bata baki, sun jima a haka kafin Faali ta dena kuka.
Bayan sun samu waje sun zauna Asiya ta tambayi labarin Faali. Faali tace auren dole aka mata a ƙauyensu tana shekara shahuɗu, to kuma mijin duka yake ga kuma kishiyoyinta sun sata a gaba shiyasa ta gudu daga gidan ta shigo gari neman aikatau. Ta samu aiki a gidan Alhaji Manniru, shekaru huɗu tana aiki a gidan kwatsam sai wani yaron gidan yai wa Alhaji sata shi kuma ya rantse kowaye sai ya hukunta shi. Matarsa Hajiya Sa'a ta laƙawa Faali sharri akan ita tayi satar duk da ta san ɗanta Hafiz ne yai wa Uban sata.
"So, shekara nawa aka ce za ki yi a nan?"
"Ni ai ban sani ba. Kwanana biyu a police station aka kawo ni nan"
"Ba a ma je kotu ba kenan?"
Faali ta amsa da "ba a je ba"
Bayan Asiya tayi jimamin wannan abu sannan tace " to kinga wannan abunda ya faru jarrabawar Ubangiji ne a kan ki. Kin gudu daga gidan mijinki ba tareda mijinki ya sake ki ba, shekaru huɗu kin yi nisa da iyayenki da 'yan uwanki ba ki sake bi takansu ba. Kina tunanin zaki samu jin daɗi a inda kike bayan kin watsawa iyayenki ƙasa a ido?"
Faali ta sunkuyar da kai tana nadamar abinda ta yi. Koda ace mahaifinta bai da wani tasiri a rayuwarta saboda banzatar da lamarinsu da ya ke yi shi dai kuɗi kawai ya sa a gaba. To amma Innarta fah.
"Dan Allah kada ki sake yunƙurin kashe kan ki. Haramun ne mutum ya kashe kan sa. Allah yana iya jarrabtar imaninmu ta kowanni ɓangare na rayuwarmu. Nima da kika gani a nan kina tunanin na aikata laifin da aka ce nayi?"
Faali ta girgiza kai.
"Ko ban auri Gwamna ba ina da gata a gidanmu. Amma gashi yau kinga inda Allah ya ajiye ni. Nima da kike gani farkon kawoni nan sai dana yi tunanin kashe kaina amma na yaƙi sheɗanin da ke riya min gurguwar shawaran nan.
"Zan miki wani alƙawari, matuƙar ina wannan kurkuku babu wanda zai cutar da ke, kuma zan sa a nema miki lawya da zai bibiyi case ɗinki, Insha Allah za a samu nasara"
Kafin Asiya ta ƙarisa maganar Faali ta rungumeta tana kuka tana godiya...
Asiya ta yiwa Warden Bisola magana nan da nan aka maida Faali ɗakin su. Lokacin da aka kawo Faali ɗakin sai JP da Lauratu suka fara ƙananun maganganu akan an fara yawa a ɗakin zasu takura, sai dai duk ciki babu wanda ya ke da ƙarfin gwiwar tunkaran Asiya da maganar.
Washegari Monday sai ga CY ya zo. Wayar warden Bisola Asiya ta karɓa ta kira shi jiya da yamma.
"Zan tsole maka ido CY, irin wannan kallo kamar ka ga ghost"
CY yai murmushin ƙarfin hali yace " ai ghost ɗin na gani, ni kuma wajen Aseey na zo"
"CY i'll wound you ooo, ka fita a hanci na"
CY ya fara dariya. Rabon da yai dariya haka har ya manta. Jiya bayan sun yi waya da Asiya kamar ya jawo wayewar gari yake saboda yadda ya matsu gari ya waye. Ko bacci bai iya yi ba.
"Aseey i miss you, i really miss you" abinda CY ya furta a zuciyarsa kenan amma a fili sai yace " Aseey are you OK?"
" no, i'm K O" ta yi dariya sannan tace "dan Allah CY ina so ka nema min lawya da yake aiki tsakani da Allah ba lawya mai aiki dan kuɗi ba. Maganar case ɗin Alhaji Manniru Buba da mai aikin gidansa na ke so a kai kotu. This innocent soul tana shan azaba ba tareda laifinta ba, sannan ko kotu bata san da maganar ba balle a yanke hukunci"
"Ok zan yi. Amma naki case ɗin fa"
"Na barwa Allah"
"Aseey lets say yanzu an wanke sunanki, an fitar dake daga gidan nan. Zaki koma gidan Gwamna?"
"Ina zan je CY? he's my husband"
CY ya ɗan yi dariyan yaƙe yace " na ɗauka zaki rabu da shi, tunda bai damu da ke ba"
"Idan na rabu da shi taya zan samu na yi revenge ɗina?. Bilkisu Kachallah will pay for what she did to me"
"That's my Aseey. Oops, Excellency"
Asiya ta harare shi. Shi kuwa sai dariya yake...
Bayan fitan CY daga gidan kurkuku sai ga kira daga mahaifiyarsa Mrs Kimberly inda ta mi shi albishir mai daɗi. Sai ga CY yana tsalle yana ihu a gefen titi kusa da machine ɗinsa. Ganin mutane suna kallonsa ya sa shi kaɗa machine ɗin yai gaba dan wannan good news ɗin yana buƙatar sirri.
***
Game ɗin chess Asiya ke bugawa da zimmar dole sai ta cinye Madam Chess amma abun ya faskara. Move ɗin da take son yi yanzu shine zai nuna ko zata ci ko kuma za a cita.
Tana ajiye knight ɗinta. Madam Chess ta saka Queen ɗinta ta kashe wani knight hakan yasa ta check mating ɗinta.
"Allah Mommy game ɗin nan akwai ruɗarwa. Taya za ace daga nan kuma ki dawo nan?"
"Kina da damar cinyeni amma rashin haƙuri yasa ki ka yi wrong move"
"Kai Mommy"
Madam Chess ta jawo littafin 48 laws of power ta miƙawa Asiya tace "Happy birthday Asiya"
Asiya ta karɓi littafin mamaki shimfiɗe a fiskarta.
"Kina tunanin ya aka yi na sani ko"
Asiya ta girgiza kai.
Madam ta jawo jarida a gefen gado ta bata tace " jaridar data fito yau ne"
Taken jaridar ya nuna *ko ya Matar Gwamna Asiya Kachallah za ta yi bikin birthday ɗinta a kurkuku?*
5
First Lady Bilkisu Kachallah tana zaune a office ɗinta tana kurɓan tea tana duba wani magazine, sai kuma idonta ya hango hoton da ke jaridar da Sakatariyarta ta ajiye mata ɗazu.
Wannan wushirya na Asiya na mugun ɓata mata rai, domin yana ƙarawa murmushinta armashi, idan za ka shagala da kallon murmushinta zaka iya narkewa kaman kitse ba tareda ka ankara ba. Ko ita Bilkisu murmushin Asiya yana tasiri a ranta, murmushi ne da ke yiwa zuciyar ma'abocin kallo albishir ɗin nitsuwa da kwanciyar hankali.
*ko ya Matar Gwamna Asiya Kachallah za ta yi bikin birthday ɗinta a kurkuku?*
Bilkisu ta karanta kanun jaridar. Tabbas 'yan jarida akwai iya tsara zance domin Bilkisu na karanta kanun wani tunani ya zo mata.
"I'll definitely celebrate your birthday Asiya" Bilkisu ta faɗa tana dariya ƙasa-ƙasa. Naɗe jaridar ta yi ba tareda ta karanta ba, ta miƙe tsaye ta ɗau wayarta da jakarta ta fice daga office ɗin. Kai tsaye ofishin Gwamna ta wuce fiskarta ɗauke da fara'a.
Gwamna ya ƙurawa Bilkisu ido har ta gama karanto bayananta. Bai ce komai ba duk da zuciyarsa ta riya masa rashin dacewar haka.
Ya kai ziyara gidan kurkuku, bayan Asiya na wajen? Taya zai fiskanci Asiya a wannan waje?...
***
A chan kurkuku kuwa warden Maida ta fito daga ofishin Chief wardress na su tana murmushi. Tabbas wannan abu zai faranta mata rai. Haka kawai jinin Warden Maida bai haɗu da na Asiya ba. Ganin Asiya na tuna mata da wata ƙanwarta da ƙaddarar rayuwarta ta zo da jin daɗi. Sun taso tare amma kuma ita komai cikin sauƙi ya zo mata, ta gama sakandare da ƙarancin shekaru, ta shiga Jami'a da ƙuruciyarta. Tana aikin bautar ƙasa a wani babban kamfani ta haɗu da wani ɗan siyasa. Mijin da ta aura yayi senator shekara takwas kuma har yanzu ana damawa da shi a gwamnati. Yadda 'yar uwarta ta yi sa'ar rayuwa da miji haka ita kuma ta yi rashin sa'a wanda tata ƙaddarar ne ya zo da haka. Ta tsani mutanen da rayuwa ke zuwa musu da sauƙi. Sai dai ta manta cewa a mahangar da ta ke kallon rayuwar Asiya ba haka Asiya ke gani ba. Ita warden Maida kallon matsayin da Asiya ta samu na matar Gwamna ta ke yi kamar ba ta dace da hakan ba. Ta manta cewa zaman Asiya a kurkuku ya zo ne sanadiyyar wannan matsayi na MATAR GWAMNA.
Tunda aka kawo Asiya kurkuku ba a taɓa fita da ita aiki ba. Wannan yasa lokacin da ta ji an kira sunanta a cikin wanda za su fita aiki mamaki ya kamata.
Tana gani warden Bisola ta ja warden Maida gefe tana mata magana ƙasa-ƙasa amma warden Maida ta yi biris ta fara ɗaga murya tana faɗin "ita ɗin waye da ba za a fita da ita ba?. Ni Sunan da aka bani kenan, idan kina da matsala da wannan to sai ki je ki yi ƙorafi.
Lokacin da Asiya ta haɗa ido da warden Bisola girgiza mata kai ta yi alamar kada ta damu.
Tunda ta ga matan da aka haɗata da su wanda za su je su yi aikin tare ta san shiri ne kawai aka yi dan a walaƙantata.
Su takwas aka fita da su dukkansu cikin uniform na firsinoni riga da wando blue, wasu sun ɗaura ɗankwali blue wasu kuma haka suka bar kan na su babu komai, duk cikinsu Asiya ce ke sanye da baby hijab kalar uniform ɗin na su.
Dukkansu na zaune a bayan motar pick-up Maama da wata da ake kira Molly suka fara waƙar da aka yiwa Asiya lokacin zaɓe.
"Zuciyar Saifuddeen ta ki ce, Hajia Asiya" Maama ta rera waƙar tana ɗaga ƙatuwar muryarta.
Sauran suka fara amsawa da
"Hajia Asiya"
"Hajia Asiya"
Duk yadda Asiya ta so kauda kai daga wannan izgili da cin mutuncin kasawa ta yi, abin ya taɓa zuciyarta matuƙa. Ta kauda kai tana kallon titi tana mai ƙoƙarin danne hawayen da ya taru a idanunta kada su zubo.
Lokacin da motarsu ta tsaya, Asiya ce ƙarshen fitowa. Tana saka ƙafarta ƙasa Molly ta ce "excellency ko na zo na goya ki ne dan na ga akwai kwatami a wajen nan"
Asiya ba ta ce komai ba ta dai-daita tsayuwarta tana ƙarewa wajen da suke kallo. Kwatami ne ya gangaro daga wani layi ya kawo har wajen kwalbatin da su ke tsaye, abin dai ba kyaun gani.
"Officer ta ina za a fara?"
Asiya ta faɗa tana kallon police da ya rako su.
Warden Maida ta hura hanci tace "kun dai ga yadda wajen nan yake. Lambatu ɗin nan ya toshe saboda datti da ake zubawa, ku gyara komai a samu ruwa ya dinga wucewa"
Tun kan ta ƙarisa maganar Asiya ta ɗauki shovel ta nufi wajen da warden Maida ke nuna mu su...
***
A chan gidan Gwamna kuwa first lady Bilkisu Kachallah ce zaune a falonta ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya, ta ɗauki bowl ɗin fruit salad tana sha tana kallon TV.
Kira ne ya shigo wayarta, hakan ya sa ta ɗau wayar ta ƙara a kunne.
"Ya kusa isa wajen?. That's very good. Zan ga komai daga nan"
Tana ajiye wayar ta kai sokalin data haɗo kankana, apple, strawberry da kuma blueberry baki. Ta lumshe ido tana taunawa a hankali tana santin daɗi.
Gwamna da tawagarsa suka nufo titin da ke daura da inda su Asiya ke aikin kwasan kwata. Asiya tana jin siren da ƙaran motoci ta ji ƙirjinta na dokawa da ƙarfi-ƙarfi. Ta dai cigaba da aiki ba tareda ta nuna damuwa a fiskarta ba amma kuma ita kaɗai ta san abinda ta ke ji a ranta.
Asiya ta ji lokacin da officer ke yiwa warden Maida bayani cewa Gwamna ya zo buɗe titin da ya tafi 'yan Aduwa ne...
Bilkisu Kachallah tana kallon yadda Gwamna Saifuddeen ke ta murmushi yana gaisawa da muƙarrabansa bayan ya yanka ribbon da aka sa a wajen, tunda aka fara aiki a wajen aka rufe hanyar ba a wucewa. Yau ne official buɗewa kuma motocin Gwamna ne za su fara bin titin.
"I want you to see her in trash, where she belongs to" Bilkisu ta furta tana dariya.
Kamar daga sama sai ga wasu 'yan jarida guda huɗu sun nufo wajen da su Asiya ke aiki da gudu.
"Kamar Asiya Kachallah"
"Hajiya Asiya Kachallah ko za ki faɗa mana yadda rayuwar ki ta kasance a kurkuku?"
"Shin a matsayin ki na matar Gwamna ana ɗaga miki ƙafa a cikin kurkuku?"
"Asiya Kachallah mun samu labarin yau ne zagayowar ranan haihuwarki, ko mi za ki ce da wannan rana?"
Tambayoyin 'yan jaridar kenan da suke ta zuwa lokaci guda wanda ka iya saukarwa mutum ciwon kai.
Asiya ta cigaba da aikin da ta ke ba tareda ta ɗago fiskarta ba. Amma duk da haka bata tsira ba daga wannan tuggu da aka shirya mata dan kuwa Maama ce ta ɗebo kwatami ta yaɓa mata a kafaɗarta tana faɗin "Happy birthday Excellency"
Asiya ta ɗago a firgice sai dai kuma me wata firsina da bata taɓa ganinta ba sai a lokacin ta shafa mata kwata a gefen kumatu tana faɗin Happy birthday itama.
A chan falon Bilkisu Kachallah kuwa dariya ta ke sosai harda bubbuga cinyoyinta.
"See her face, look at her face. Matar Gwamna indeed"
Duk abinda ake yiwa Asiya life aka dinga nunowa a gidajen talabijin bayan an katse wajen da Gwamna ke ƙoƙarin shiga mota saboda ya gama abinda ya zo yi.
Sabuwar titi motocin Gwamna suka hau dan kai shi ofishinsa wanda dole ne sai an bi ta hanyar da su Asiya ke aiki.
Tun kafin su ƙarisa wajen Halima Kachallah ta kira Gwamna.
"Yaya dan Allah kana ina ake cin zarafin Anty Asiya. Yaya it's embarassing, ka sa a dakatar da wannan haukan Dan Allah" kuka ne ya ƙwace mata hakan yasa ta kashe wayar. Kaman haɗin baki sai ga kiran Hajia Umma, itama dai ƙorafin da Halima tayi ta yi masa.
Wannan ya sa ya fara duba saƙonnin da suke shigowa ɗaya wayarsa da gudu-gudu.
*Big story of the year. Asiya Kachallah celebrates birthday with crazy inmates*
Headline daya fara cin karo da shi kenan, kafin ya ƙare wa hoton da aka turo kallo hayaniyar mutane da ya ji ya sa ya ɗaga ido yana kallon titi, dandazon mutane ya gani a gefen titi ana ihu. Ya saukar da idonsa ya kalli wayar da ke hannunsa hoton Asiya ya gani tsaye looking shocked, ga kuma wani baƙi-baƙin abu a gefen kumatunta.
Bai gama farfaɗowa daga shock ɗin daya shiga ba Bilkisu ta kira shi wayarsa.
"Darling ka ga abinda ake yiwa Asiya kuwa? Its so humialiating, ko zaka kira commisioner of police ne a zo a hana mutane ɗaukan video a wajen?"
Wayar ne ta suɓuce a hannunsa lokacin da ya ke ƙoƙarin dafa ƙirjinsa da ya cunkushe. Numfashinsa ya fara sarƙewa. Da ƙyar ya lalubo inhaler a aljihunsa ya matsa a bakinsa sau biyu, bayan sakwan goma ya fara dawowa hayyacinsa...
Allah sarki Officer Ɗanladi yana ta ƙoƙarin koran 'yan jarida dama mutanen da su ke ɗaukan videon Asiya amma sun fi ƙarfinsa babu ma wanda ke saurarensa. Har ga Allah shi bai san da wannan shirin ba. Ita warden Maida da aka yi shirin da ita kuwa dan tsabar munafurci sai ta riƙe hannun Asiya tana faɗin ta zo su je su shiga mota. Asiya tana tsaye a wajen kaman gunki, idanunta na kallon ƙasa ta kasa haɗa ido da kowa. Duk tambayoyin 'yan jarida, duk hayaniyarsu babu wanda ta tanka wa.
Tausayin Asiya ya shiga ɗaya daga cikin firsinonin da suke wajen. Anita ta karɓi kuɗin da aka basu dubu goma-goma akan su shafawa Asiya kwatami a jiki amma kuma lokacin da Maama da Molly su ka fara shafa kwatar sai ta kasa yi, ba dan komai ba sai dan ganin rashin dacewar abin,duk da kuwa ita ɗin ma ba kanwar lasa ba ce wajen cin zalin firsinoni a chan kurkuku. Anita ta ƙariso wajen da Asiya ke tsaye ta ciro ɗankwalinta ta fara goge mata kwatamin daya ɓata mata jiki.
Warden Maida ta fara shureta alamar ta bari amma ko a jikinta.
Shiru ne ya ratsa wajen na 'yan wasu sakanni, tun kafin Asiya ta ji ana ihun "your Excellency" ƙanshin turarensa ya ratso hancinta duk da warin kwata da ke wajen.
Daga inda Gwamna Saifuddeen Kachallah ya dakatar da drebansa ya fito daga motar cikin sauri ba tareda ya jira an buɗe masa ƙofa ba. Securities ɗinsa ma sai gudu suka yi suka iso shi, kafin ya kai inda dandazon mutanen su ke, wasu securities ɗinsa sun yi gaba sun fara koran mutane da 'yan jarida da ke wajen nan da nan aka buɗewa Gwamna fili, hatta warden da sauran firsinonin kowa baya ya ja ganin mai jihar Congo.
Gwamna Saifuddeen ya ciro farar hankerchief a aljihunsa ya fara goge fiskan Asiya.
"Are you Ok?" Ya tambaya da sansanyar muryarsa.
Hawayen da Asiya ta ke riƙe da su tun daga cikin mota suka samu saukowa dai dai sanda ta ji muryan Gwamna.
Gwamna ya tallafo fiskanta da hannunsa biyu, ya sa babban yatsunsa ya fara goge mata hawaye.
Yana goge hawayen wasu na ƙara zubowa duk da haka ta kasa bari su haɗa ido.
Gwamna bai ji ƙyamar jikinta ba sai kawai ya jawota jikinsa ya rungumeta ƙyam, wannan ya ba wa Asiya damar fashewa da kuka son ranta.
I'm sorry ya furta a dai dai kunnenta saboda ita ce kalmar da zai iya faɗa a wannan hali.
Bowl ɗin da ke gaban Bilkisu Kachallah ta ɗauka ta wurgi TVn da ke manne jikin bango da shi tare da sake ihu.
"Taya za ka je ka rungumeta?, why will you destroy my plan. Why will you show her care?"
"Mommy... Mommy... Nana"
A haukace Bilkisu ta juyo tace " Sa'ad get out of here"
Yaron tsabar tsoro sai da ya saki fitsari, ya shiga zare ido yana ƙoƙarin buɗe baki saboda iskar wajen da ta masa kaɗan. Sai a lokacin Bilkisu ta dawo hayyacinta ta yi kan yaron da gudu saboda asthmatic attack daya same shi.
Babu inhaler a aljihunsa ta shiga kiran masu aiki. Onome, Safiyya, John. Hansa'u Hansa'u" tsabar ruɗewa mantawa ta yi Hansa'u tana prison.
Bayan ta samu Safiyya ta kawo inhaler Junior ya shaƙa sai kuma ta hau Safiyar da faɗa.
"Hajiya Aljanu ne su ka taɓa Nana shine mu ke ƙoƙarin kama ta."
"Aljanu a ina?" Bilkisu ta saɓa Junior a kafaɗa ta yi waje. Safiyya ta bi bayanta a ɗari.
Kallo ɗaya Bilkisu ta yiwa Nana ta san ba Aljanu bane, ƙwaya ce kawai ta ke aiki a jikinta. But yaushe Nana ta koma shan ƙwaya?
Zuciyarta ya motsa da ganin halin da 'yarta ke ciki, amma Shaiɗan ya mantar da ita cewa tana ɗaya daga cikin manyan-manyan ma su shigo da ƙwaya cikin ƙasar.
"Nana"
"Mommy i'm swimming" Nana ta faɗa tana jujjuya hannunta kaman me swimming a cikin ruwa. Daga ita sai bikini. Brazzier ɗin ma a tsinke yake, garin su Safiyya na ƙoƙarin kamota ɗazu da take ta gudu cikin falon wai tana swimming ya tsinke.
Wannan wace irin rana ce?. Ta ya za ta shiryawa Asiya matsala sannan itama ta fuskanci matsala a tata gidan. Dole ta fita da Nana ƙasar waje dan ba za ta jure wannan haukar ba...
***
Ofishin NDLEA Abuja.
Agent Dahlia tana zaune a ofishinta tana sipping tea aka banko ƙofar ofishin.
"Vic!" Ta faɗa a firgice
"Na gaya miki she's innocent, look at this" yai maganar yana miƙa mata wani file.
Agent Dahlia ta karɓi file ɗin ta buɗe, takardar farko data gani ta fara karantawa, details ne na bank statement hakan yasa ta kalli Vic cike da alamar tambaya.
"How did you get this?"
"Someone send it to me this morning. Yace yanada copies a wajensa idan bamu yi abinda ya dace ba zai tura gaba"
Agent Dahlia ta zauna ta cigaba da duba sauran documents ɗin a hankali dan ta tabbatar da ingancinsu.
Tabbas gashi nan maƙudan kuɗi ne ake tura wa account ɗin Timothy Igwe tun shekaru biyu da suka wuce har zuwa ƙarshen kuɗin da aka tura sati uku da suka wuce. Account ne da ke ƙasar Cape Verde amma kuɗin da ake turawa daga Nigeria yake shiga daga wani account name mai suna BILLY SANNY.
"Billy Sanny?" Agent Dahlia ta maimaita sunan
"Two years ago Asiya tana kan yin bautar ƙasa babu yadda za ayi ta samu maƙodan kuɗin nan"
Agent Dahlia ta haɗa da cewa "two years ago ba ta haɗa hanya da Gwamna Saifuddeen ba balle ta aure shi"
"Exactly" Vic ya faɗa yana buga table
"Idan ba Asiya ba ce, then???"
Vic yace "Bilkisu Kachallah"
"Shit!" Dahlia ta faɗa tana kama goshinta
"She played us, babu yadda za ayi a san akwai ƙwayoyi a gidan Gwamna idan ba wai dama planting na shi aka yi a wajen ba. And she got backup shiyasa aka bada warrant a je a chaje gidan Gwamna"
Abu da tashin turai ba abinda Dahlia ke faɗi sai "shit! Bullshit!"
Vic yace "But still with this ba zamu iya kama Bilkisu Kachallah ba"
"But atleast zamu sa a sake Asiya Kachallah right?"
"Yes" Vic ya faɗa confidently...
06
***
Ƙarfe goma na dare Asiya ta farka daga bacci, ɗakin tar yake da haske hakan ya bata damar ganin Faali da ke zaune akan kujera ta ɗan jingina kanta da gini da alama bacci ya ɗauketa.
Asiya ta dubi hannunta da aka sakawa canula ga ledar ruwa saƙale a jikin stand yana gangarowa jikinta a hankali. Ta dafe goshinta da ɗaya hannun tana murzawa a hankali. Ɗakin da suke ciki yayi girma ace a ɗakin prison ta ke.
Kusan sakan goma ta ɗauka kafin abubuwan da suka faru suka fara dawo mata.
Cikin motar Gwamna aka kawota kurkuku, maganganunsa ya fara dawo mata kaman a lokacin ya ke faɗinsu.
"Ban san mi yake damuna ba Asya, i long for you yet i cannot be with you. Duk lokacin da na yi yunƙurin zuwa wajenki sai na ji tsoro ya dabaibayeni, wani lokacin sai na ji kaman ana saka kacha mai wuta ana shaƙe min wuya. I miss you Asya, I miss you so much Love. Ki min addu'a na dawo hayyacina, ban san mi na ke ba, ban san ya aka yi na ke samun jirkicewar tunani ba..."
Sai kuma yai shiru ya sake ƙanƙameta jikinsa yana kissing goshinta.
Tun kafin su iso kurkuku labarin zuwansu ya riski Chief Wardress hakan ya sa ta shiga ruɗani tana dana sanin biyewa Bilkisu Kachallah da ta yi ga shi yanzu aikinta kan ta sani ya bi ruwa kenan.
Madam Chess da Faali ta sa aka kawo ofishinta ta basu umurnin da an kawo Asiya cikin kurkukun su taimaka mata su kaita sabon ɗakin da aka bata a Aso rock.
Duk wani ma'aikaci a prison ɗin sai da ya sha jinin jikinsa lokacin da motocin Gwamna suka shigo kurkukun, hatta ɓangaren maza na prison ɗin sun shiga ruɗani saboda tunanin abinda ya faru su ma zai shafesu.
Sai dai ga mamakinsu bayan an fito da Asiya daga motar motocin Gwamna suka bar cikin haraban kurkukun. Duk da Gwamna bai yi magana ba amma aka ce shiru ma amsa ne.
Lokacin da Asiya ta shiga banɗaki ta yi wanka ta fito ta kwanta kan ƙaton gado da ke ɗakin sai kuma zazzaɓi mai zafi ya rufeta. Lokacin da Faali ta kawo mata abinci ne ta lura da hakan wannan ya sa ta notifying warden Bisola nan da nan aka kira likitan prison ya zo ya dubata, alluran da za ayi mata ma babu shi a clinic ɗin kurkukun sai da aka tura waje aka je aka siyo.
"Fadilah, Fadilah"
Faali ta yi firgigit ta buɗe ido "Excellency kin tashi"
"Dan Allah ki kira a cire min wannan zan shiga banɗaki"
Faali ta ce " an nuna min yadda zan cire miki"
Bayan ta cire mata ta tallafa mata ta shiga banɗakin da ke cikin ɗakin.
Mutane kenan, rana ɗaya an ga Gwamna ya nuna mata kulawa har an chanja mata ɗaki.
Lokacin da ta buɗe ruwa ta fara ƙoƙarin yin alwala saurin rufe tap ɗin ta yi saboda gani ta yi kaman ruwan kwata ke zubowa. Ta ja dogon numfashi, ta yi Isti'aza a zuciyarta sannan ta sake buɗe tap ɗin a karo na biyu.
Lokacin da ta tada kabbara za ta yi sallah sai kuma Shaiɗan ya fara kawo mata wasi-wasi a ranta, sai ta ke gani kaman akwai najasa a jikinta, kaman akwai sauran kwata da bai fita ba, gaba ɗaya ma jikin nata sai ya fara mata wari ta fara ƙyanƙyamin kanta. Ganin ta kasa cigaba da sallar sai kawai ta fashe da kuka. Faali ta yi saurin ƙarasowa wajenta tana tambayar mi ke damunta.
"Your Excellency ki yi haƙuri, suma wanda su ka miki abin nan suna cikin damuwa. Da sannu za su girbi abinda suka shuka"
"Ba za ki gane ba Fadilah. Ba za ki taɓa ganewa ba"
Ta jima tana sheshsheƙar kuka kafin daga baya ta samu ƙarfin gwiwar rama sallolin da suka wuce ta...
Shi kuwa Gwamna kiran Bilkisu ne ya sa bai iya tsayawa a kurkukun ba. Ko babu magani da ke cinsa maganar 'yarsa ya isa ya ɗaga masa hankali har ya koma gida cikin gaggawa.
Lokacin da ya isa Nana ta yi bacci, sai a lokacin ya lura yarinyar ta bushe masa, gaba ɗaya ƙwaya ya figar da ita. Farkon dawowarta gida har ta fara maida ƙibanta amma kuma yanzu ta tsotse kamar me cutar ƙanjamau.
A inda yake zaune gefen gadonta ya lura da wani ƙullin baƙar leda, an cusa jikin gadon amma bai rufu da kyau ba.
Bai yi mamakin ganin garin cocaine da ta wiwi ba nannaɗe a wasu takardu. Kaman an tsikare shi sai ya miƙe ya fara dudduba ɗakin ko zai ga wani abun kuma. Lokacin daya buɗe banɗakinsu warin wiwi ne ya tabbatar masa abunda ta sha kenan ya zautar da ita, da alama ƙila ma farkon shanta ne dan ga sauran ɗaurin a ƙasa ba a ma ƙarisa zuƙeshi ba.
Ya tattare abubuwan daya ɗauke ya fice daga ɗaki ran shi a ɓace...
Bilkisu Kachallah kuwa tunda Gwamna ya shigo ta fice dan ta gyara ɓarnar da aka yi, ta ko wanni hanya so take idon mutane ya dawo kanta. Yadda jama'an ciki da wajen jaha su ke Allah wadarai da abinda aka yiwa Asiya ya fara bata tsoro domin idan aka fara tausayin Asiya za a iya samun matsala nan gaba.
Awa biyu bayan abinda ya faru gidan talabijin su ka yi hira da Bilkisu inda ta yi tur da abinda aka yiwa 'yar uwarta Asiya. Ita a wajenta duk da cewa an kama Asiya da laifi hakan bai chanja matsayinta na ƙanwa a gareta ba. Lokacin da ta ke bayani sai kawai ta fashe da kuka tana yin Allah ya isa ga mutanen da suka walaƙanta Asiya.
Interview ɗin ya ɗan samu karɓuwa a wajen mutane, sai dai duk da haka videon da aka yiwa Asiya yayi yawo cikin duniya tamkar ƙonewar auduga.
Yadda maganar Asiya ya ɗagawa Bilkisu hankali, ko kusa lamarin Nana bai kai haka a ranta ba. Kafin Gwamna ya iso ta dai kira wani na hannun damanta akan ya nema mata rehabilitation home mai kyau a ƙasar America.
Kafin daren ranan har an fara samun different campaign tweets akan a sake Asiya, Asiya is innocent.
Wasu kuma ba abinda ya ke ransu irin labarin soyayyar Gwamna da Asiya. Video da ɗibbin jama'a suka gani ya zama shaida akan irin soyayyar da Gwamna SSK ke yiwa Asiya.
A ɗaya ɓangaren kuwa wasu gani su ke renin hankali ne duk abinda yake faruwa, tun daga kulle Asiya da aka yi har zuwa yanzu da wannan abu ya faru..
***
Washegari dakatar da Chief wardress na kurkukun mata da aka yi ya sake tabbatar da zancen mutane na cewa Gwamna ya fara dawo da hankalinsa kan lamarin Asiya. Yayinda wasu kuma ke ganin cewa duk shirin Bilkisu Kachallah ne saboda a interview ɗinta ta yi maganar za a hukunta waɗanda su ke da hannu akan abinda ya faru.
A ɓangaren Asiya kuwa duk abinda yake faruwa ana sanar da ita. Tsakanin abinda bai cika awa ashirin da huɗu ba Asiya ta zamo tamkar sarauniya a cikin kurkukun. Tunda aka kori Chief wardress kowa sai ya shiga taitayinsa. Hatta warden Maida ta rasa nitsuwarta tun jiya har zuwa wayewar gari, idan ta rasa aikinta ba ƙaramin tashin hankali zata shiga ba saboda aikinta yana mugun rufa musu asiri ita da 'ya'yanta.
Asiya da kanta ta zaɓi a maidata ɗakin Madam Chess saboda ta saba da zaman chan, sabon ɗakin da aka bata ya mata faɗi.
Warden Maida da ta gama tufka da warwara akan lamarin da zai fishsheta sai ta shirya sanar da Asiya duk abubuwan da ta sani.
Warden Bisola ta roƙa ta je ta taho da Asiya office ɗin su. Da farko kame-kame ta fara yi, sai daga baya ta faɗi abubuwan da ta sani tunda ita ɗin ta hannun daman Ogan su ne. Asiya ba ta girgiza da jin cewa Bilkisu Kachallah ce ummul aba'isil komai ba. Abu ɗaya kawai ta nema a wajen warden Maida wato Hansa'u.
Ko minti goma bai cika da fitan warden Maida ba ta shigo da Hansa'u.
Hansa'u da Asiya su ka shiga kallon-kallo sai kuma a tare su ka fashe da dariya...
***
Bilkisu Kachallah na shirin shiga mota wayarta ya shiga ringing, bata ɗauki kiran ba sai da ta shiga ciki ta zauna da kyau sannan ta amsa.
"Yes ina ji"
Daga ɗaya ɓangaren aka faɗa mata saƙo.
"Ina zuwa office yanzu, ka sameni a office"...
Office of the first lady of Congo State babban ofishine mai zaman kansa wanda yake da full staff da officials. Tunda aka sanar da wanda ya ci zaɓe Bilkisu Kachallah ta sa aka fara gyara mata wajen, tsohon state library ne da aka kashe ta siya ta maida shi ofishin first lady. Ta yi alƙawarin bayan sun yi shekaru takwas akan mulki bazata bari wata shegiya ta gaji wajen ba, zata maida shi main office ɗinta ne, amma for now nan ne ofishin first lady Bilkisu Kachallah.
Tana isa office ɗin ta tarar da COS yana jiranta, tun kafin ta zauna a kujera tace " Lamara mi hakan ke nufi?"
"It means akwai yiwuwar fitowar Asiya nan kusa"
"Ban gane ba. An samu ƙwayoyi a cikin kayanta that should count"
Mr Lamara yai dariya yace " kin manta cewa za a fara binciken account ɗin Billy Sanny"
"No way. Ba za su iya linking ɗin account ɗin da ni ba. Inada different account names a ciki da wajen ƙasar nan"
"Boss Lady ina zargin akwai international body da su ka saka hannu a wannan bincike, idan ba haka ba taya za a samo bank details ɗin nan ba tareda kin sani ba"
Bilkisu Kachallah ta dunƙule hannunta tana cizon leɓe. Ba damuwarta asirinta zai tonu ba, dan ta san babu yadda za ayi hakan ya faru saboda back up da take da shi, amma kuma idan aka fito da Asiya kaman aikinta ya dawo baya ne
"I don't want Asiya out. Inaga kawai a kashe Timothy Igwe"
Bilkisu ta faɗa bayan dogon nazari.
Lamara Damana yace "Wrong idea"
"Kaman ya?"
"Idan aka kashe Timothy Igwe zai kawo zargi"
"To ko a kashe Asiyar ne kawai?"
COS ya sheƙe da dariya yace " idan aka kashe Asiya zaki ruguza komai. Ni dai idan zaki karɓi shawarata, inaga ki bari Asiya ta fito, sai mu maida zancen kan 'yan adawa tunda kinga kotu tayi watsi da ƙaran da Umaru Kwom ya shigar na rashin karɓan sakamakon zaɓe..."
"Bana son attention ya koma kanta idan ta fito, she's better off a prison"
"Zaɓi dai ya rage naki"
Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Chief of Staff Lamara Damana, ko da bata yarda da kowa ba za ta iya cewa ta bawa COS yardanta kaso casa'in cikin ɗari. Idan har wani zai cuceta to banda COS saboda manufarsu ɗaya ce...
07
A yau Litinin ne aka yi zama na farko a kotun ɗaukaka ƙara. Yadda aka bijiro da wasu sabbin hujjoji ya bawa ɗaukacin magoya bayan Asiya hope na samun nasara a wannan shari'a.
Kotu ta tashi ne da ɗaga ƙara zuwa wata sati inda za a sake gabatar da Timothy Igwe domin ya amsa wasu tambayoyi.
A ɓangaren Asiya kuwa ta duƙufa ne wajen tsara yadda za ta aiwatar da ɗaukan fansa, bisa shawaran Madam Chess ta yi alƙawarin adana hujjojin da Hansa'u ta bayyana mata zuwa lokacin daya dace a bayyana su.
A bisa gigin son ganin ta samu 'yancinta lokacin da Badawiyya (Hansa'u) ta sanar da ita cewa akwai backup copies na hujjojin da ta tara wanda ta saving a cloud yunƙurin kiran CY Asiya ta yi dan ya retrieving information ɗin ya bawa Barr Zaytoonah a gabatar da su a kotu, amma sai Madam Chess ta nuna mata illar yin hakan.
"Ashe ba ki koyi darasi ba zaman ki a wannan gida Asiya, kina ganin idan an gabatar da hujjojin nan za a kama Bilkisu Kachallah ne?"
Asiya ta ajiye littafin da ke hannunta ta tsurawa Madam Chess ido.
"It seems kin manta mi yake faruwa a jahar nan, Bilkisu Kachallah ke juya jahar nan and there's no way zata bari asirinta ya tonu har ma a ma ta hukuncin daya dace"
"Mommy ya zan yi? Ba zan taɓa yafe mata abubuwan da ta yi min ba"
Madam Chess ta ɗan saki ajiyar zuciya sannan tace " ko dai ki zaɓi tunkaranta gaba da gaba, wanda ina miki albishir da ɗayan biyu. Imma dai a dawo da ke gidan nan ki cigaba da zama ba tareda laifi ba. Ko kuma ki rasa rayuwarki gaba ɗaya. Ko kuma ki zaɓi yafiya, ki haƙura da duk abinda ta miki sannan kina fita daga gidan nan ki nemi Gwamna ya sake ki, idan kika rabu da mijinta za ta bar ki kiyi rayuwarki ba tareda ta takuraki ba"
Dukkan zaɓin da Madam Chess ta kawo babu na ɗauka a ciki, dan kuwa bata ji a ranta koda a mafarki ne zata iya yafewa Bilkisu Kachallah ba.
"to mi zan yi Mommy? Help me please"
Madam Chess ta yi murmushi irin na manya sannan ta ce " wait"
Cikin rashin fahimta Asiya ta ce " wait kuma?"
"Ki jira lokacin ki Asiya, ki jira lokacin da zaki samu abinda ta ke da shi, ki jira zuwa lokacin da sunan ki kaɗai idan ta ji sai hanjinta sun kaɗa saboda tsoro"
"Kada ki taɓa nunawa Bilkisu Kachallah manufarki a kanta. Infact ki nuna mata kinada rauni kuma kina buƙatar tallafi. Idan kika bari ta san fiskarki za ta yaƙe ki duk inda za ki shiga, amma idan kika ɓoye mata fiskarki zata nemeki a ko'ina amma ba za ta same ki ba. For the mean time you have to become blind, deaf and dumb to everything"
Asiya ta sunkuyar da kai tana nazari.
Madam Chess ta ƙara da cewa "If you want to be invincible Asiya, you have to wait for your moment"
Chan Asiya ta nisa ta tambayi Madam Chess akan mi Bilkisu Kachallah ke da shi. Kalma ɗaya tak ta furta mata, wato "mutane"
Ta ina za ta samu mutane ita ba 'yar kowa ba? Tukunna ma wasu irin mutane Madam Chess ke nufi? Tambayoyin da ya zamowa Asiya assignment kenan saboda Madam Chess ta ƙi yi mata ƙarin bayani akan kalmar data faɗa.
***
A ranan uku ga watan Satumba da misalin ƙarfe shaɗaya da rabi na safe kotu ta wanke sunan Asiya Shahida Faruƙ Baba bisa dukkan wani laifi da aka tuhumeta da shi a baya. Yayinda aka yankewa Timothy Igwe hukuncin zama a gidan kaso na shekaru ishirin. Ita kuwa Uwani Maikifi wacce ta amsa laifinta bisa saka ƙwayoyi cikin akwatin kayan Asiya, kotu ta yanke mata hukuncin shekaru uku a kurkuku.
Duk da yanayi na matsi da ake ciki, duk da mutane dayawa na sukar Gwamnatin Saifuddeen Kachallah saboda rashin biyan albashi da kuma tauye hakkin talakawa da ya ke yi hakan bai hana mutane fitowa domin taya Asiya murna ba. Ɗaukacin mutanen da su ka yi cincirindo a bakin kotu suna jiran fitowar Asiya kuwa, kace taron kamfen ne da ake raba buhuhhunan shinkafa.
Tun lokacin da aka watsa videon Asiya ana shafa mata kwata tauraronta ya ƙara haskaka a idon mutane, musamman saboda yadda Bilkisu Kachallah ta-kasa-ta-tsare, ta yi kane-kane a kan mulkin jihar.
Fosta fosta na hotunan Asiya sun zagaye lungu da saƙo na cikin jahar, ko ina ka ga hoton Asiya sai dai kaga ana yabonta.
Ga wanda su ke da burbuɗin jahilci a tunaninsu kuwa ganin Asiya su ke a matsayin wata waliyyiyar Allah ko kuma Shahidiya. Suna kambamata fiye da kima, har abun ya wuce gona-da-iri.
Barrister Zaytoonah ta fito daga cikin kotu da tsohon cikinta da ke nuni da haihuwa ko yau ko gobe, biye da ita kuma Asiya ce wacce watanni uku da sati biyu na zaman gidan kurkuku ya koɗar da farar fatarta, ga wasu ƙananun ƙuraje da suka ɓata mata fiska.
Ihu mutane suka saka, ana kiran sunanta, ba dan Jami'an tsaro da su ka zagaye wajen ba da babu abinda zai hana mutane haurowa saman matattakalar bakin kotun.
Asiya ta ɗaga hannayenta biyu tana waving ɗinsu. Mutane aka saka ihu, wasu kuma suka shiga kabbara.
Duk yadda Asiya ta daure sai da ta fara hawaye. Dole ta yi kuka. Ɗaukacin mutanen nan duk sun fito ne saboda ita, saboda su taya ta murna.
Yaya Bello da wasu ƙannenta biyu wanda rabonta da ganinsu ta jima su suka kewaye ta tareda security aka wuce da ita cikin mota. A hakan mutane sai da suka bi motocinsu da gudu ana yabon Asiya.
A cikin mota da ƙyar Asiya ta iya tsaida kukanta duk da kuwa ta yiwa Madam Chess alƙawarin ba zata sake kuka ba har sai ta samu nasara a shirinta.
"Mommy ki gaya min tarihinki Dan Allah?" Tambayar da Asiya ta yiwa Madam Chess kenan jiya da daddare da su ke tare.
Madam Chess ta girgiza kai ta ce " na yi alƙawari ai Asiya, kuma har yanzu ba ki cinye ni a game ɗin ba"
"Kai Mommy ke fa Pro ce, ni kuma har yanzu koyo na ke"
"Kar ki damu da labarina, ki maida dukkan ƙarfin ki wajen ganin kin chanja wannan mummunan shafi na rayuwarki zuwa makamin da za ƙi yaƙi maƙiyanki da shi.
"Remember, never show your real face to anyone"
Asiya ta yi murmushin jin daɗi, ko ba yanzu ba sai ta samo labarin Madam Chess ta kuma fitar da ita daga gidan kurkuku kaman yadda aka fitar da Faali.
Ganin sun nufi hanyar gidan Gwamnati Asiya ta tambayi Yaya Bello da ke tuƙi akan miyasa za su je chan ba asalin gidan Gwamna ba.
Yaya Bello ya amsa "Gwamna ne ya ce a kawo ki nan"
Asiya ta maida dubanta ga titi har aka iso gidan.
Taron mutane da Asiya ta gani yasa ta fara tunanin akwai wani abu a ƙasa. Motar su na tsayawa Halima Kachallah da Jummai ne suka fara rige-rigen buɗe ƙofar gefenta. Asiya sai murmushi ta ke dan da Jummai da Haliman duk shirmensu ya yi yawa.
Tana fitowa Halima da Jummai suka rungumeta kowa na faɗin shi ya riga ɗanuwansa. Daga su kuma sai Sumayya, Ali da Gwani suka rungumeta suna kuka.
A hankali Asiya ta gaisa da 'yanuwanta da su ka zo dan kuwa kusan duka ƙannenta sun zo har wanda bata san da haihuwarsu bama saboda 'ya'yan Ale ba dai yawa ba.
Ale yana gefe ya sha babban riga fara da farar hula, idanunsa sanye da ƙaton baƙin gilashi daya fi ƙarfin idanunsa. Asiya na ganinsa ta saka dariya. Jummai da ke maƙale da ita ta ce " Adda wai idonsa ke ciwo aka bashi gilashi a Asibiti"
"To Baba baƙin glass sai ka ce makaho"
Ale yai dariya yace "ke dai ba ki so na saka na zama guys 'yanmata su kalleni su ƙyasa?"
"Guys indeed" Asiya ta faɗa tareda rungume Ale. Duk yadda ta ce ba za ta ƙara kuka ba sai da hawaye suka zubo mata yayinda kalaman alƙali su ka dinga dawo mata lokacin daya ke karanto sunanta yana wanke ta daga laifin da aka laƙa mata. Koma minene dalilin Uwani na ƙin faɗan sunan Bilkisu Kachallah ba zai wuce tsoratata aka yi ba.
Ale ya katse tunaninta da cewa " Asiyar Gwani kin ma lura da haƙorina kuwa"
Asiya ta janye jikinta daga nashi ta kalli fiskarsa da ke ɗauke da murmushi yana bayyana haƙorin Makkah daya saka.
"Yanzu kam Alhaji ne ba Ale ba"
Gaba ɗaya aka saka dariya saboda kusan kowa a wajen ya san dalilin da ya sa ake kiransa da Ale. Tsohon labari ne da kowa daya tashi a gidan sai ya sani.
Shekaru kusan talatin da suka wuce lokacin Ale Faruƙ yana ji da kuɗi da ƙuruciya, lokacin bai tara zugar 'ya'ya har haka ba. Wata shekara ya shirya tafiya Hajji, ya gama shela a gari cewa Hajjin bana da shi za a je. Da ya ji kuɗin jirgi sai hankalinsa ya tashi dan bai zata kuɗin zai kai har haka ba. Ya dai tsaya tunani akan ya biya ko kar ya biya, lokacin daya gama saiɓinsa ya je zai biya sai kawai ya tarar babu kujera.
Wani abokinsa da za su je tare yace masa ya je Kano ko Bauchi ya duba ko akwai kujera a ƙasa sai ya tafi ta chan. Ale ya amsa da toh. Mutuminka dama kuɗin nan na cizonsa da ya tafi kano sai ya je ya saro kaya ya fara kasuwanci da su shi bai dawo gida ba shi kuma bai je Makkah ba. Lokacin da ya ji Alhazai sun fara dawowa sai ya dawo gida da tsaraban Kano a matsayin na Makkah. Sai daya gama karɓan gaisuwar ban gajiya sai wani abokinsa daya gan shi a Kano ya tona masa asiri. Daga nan aka fara masa habaici da Ale mutanen Kano. A hankali sunansa ya rikiɗa ya koma Ale Faruƙ...
Asiya ta kalli mahaifinta ta ce " Allah ya taimaki Hajji Faruƙ"
Ale ya ce "Allah ya miki albarka"
Ana tsaye ana dariya ana raha Uwargida First Lady ta fito cikin tafiyar ƙasaita. Duk wanda ya ɗaga ido ya kalleta sai ya sha jinin jikinsa.
Asiya na kallonta ta sake murmushi amma chan ƙasan zuciyarta addu'o'in tsari take karantowa.
Itama Bilkisun murmushin ne manne a fiskarta. Tun kafin ta ƙaraso ta fara faɗin welcome home my sister. Tana zuwa ta rungume Asiya. Nan da nan aka saka tafi 'yan jarida suka fara ɗaukan hotuna.
"Welcome Asiya, ina fata kin gane banbancin Aya da Tsakuwa"
"Your Excellency na san banbancin zuma da maɗaci"
"Good"
Bilkisu Kachallah ta kama hannun Asiya suka wuce cikin gida sauran mutane aka bi bayan su...
08
Mutane da dama sun yi hasashen samun chanji idan Asiya ta dawo rayuwar Gwamna sai dai kuma har gashi an doshi wata guda da fitowarta daga kurkuku amma ba a ga wani chanji na zahiri ba. Abin takaicin ma tunda aka nuna dawowarta a talabijin, irin yadda Bilkisu Kachallah ta mata tarba na musamman ba a sake ganinta ba. It's as if she does not exist.
A hankali burukan mutane a kanta ya dishe tunda ta kasa taɓuka komai.
Asiya tana yin rayuwarta ne cikin kwanciyar hankali. Sau ɗaya su ka yi karon batta da Bilkisu washegarin ranan da ta zo gidan.
Tana zaune kan sallaya tana azkar Bilkisu ta shigo ɗakinta ƙarangatsau babu knocking bare sallama.
"Ina da labarin kin haɗu da Hansa'u a gidan kurkuku"
Ba tareda Asiya ta kalleta ba tace " kina da matsala da hakan ne?"
"Wannan shiru-shirun na ki tun jiya na san kina tunanin gayawa Gwamna abinda ta faɗa miki ne. Sai dai albishirinki, duk abinda za ki faɗa masa ba zai yarda da ke ba, and besides babu wanda zai yadda da maganar baki as evidence"
"Kina so ki san mi Hansa'u ta gaya min ne?"
Bilkisu ta zaro ido waje duk da ta san Hansa'u ta san gaskiyar komai amma kuma ta girgiza da yadda Asiya ta yi maganar.
Asiya ta yi murmushi ta ce " babu amfanin maimaitawa tunda dukkanmu mun san gaskiya. Besides Timothy da Uwani sun karɓi laifinsu, babu amfanin tone-tone kuma"
Bilkisu ta haɗe rai ta ce "i'll be watching you Asiya"
Bayan tafiyar Bilkisu Asiya ta ƙarisa addu'o'inta ta hau gado ta miƙe don jiya ba ta samu ta kwanta da wuri ba saboda jama'a...
Ranan da Asiya ta kalli Gwamna kuka ne kawai ba ta yi ba. Ashe hotunansa da ta ke gani a jarida ma yana rufa masa asiri. Dama tun asali shi ba mutum ne mai ƙiba ba. Amma kuma da ɗan kaurinsa dan ba za ka saka shi a sahun sirarara chan ba. Sai dai yanzu mutumin da ta gani zata iya kiran shi ƙashi da rai. Manyan idanunsa kaɗai su ka cika fiskar sai kuma dogon hanci da ya ɗan baiwa fiskar fasali.
Ranan da su ka haɗu na ƙarshe bata ƙare masa kallo ba, amma ta tabbata daga lokacin zuwa yanzu ya sake bushewa.
Hatta a maganarsa babu nitsuwa ko kaɗan. Yana mata magana ma kamar a firgice ya ke.
A kullum tana saka shi cikin addu'o'inta amma idan shi baya yiwa kansa addu'ar fa?. Bata son nuna manufarta shiyasa bata gwada zaƙewa a kansa ba.
Sai da Asiya ta yi wata ɗaya da dawowa sannan ta fara fita, lokacin har ta maida jikinta. Tana sane da cewa Bilkisu Kachallah na lura da lamurranta shiyasa ma duk wani communication da za ta yi na sirri ta ke amfani da wayar Jummai.
Yau gidansu ta je dan tunda ta fito ba su haɗu da Abba ba, ance mata tun dawowarsa daga aikin Hajji ya ke jinya.
Ta wuni a gida sosai inda a nan ta ke jin labarin wasu abubuwan da su ka faru lokacin tana kurkuku.
Daga gidansu ta wuce gidan Queen Bee wacce watanta biyu kenan da aure. Ta samu ma tana fama da laulayin ciki dan haka ta dinga mata shaƙiyanci irin yadda dai ta ke ma ta. Queen Bee dai babu bakin magana dan ba ƙaramin wahalar da ita cikin yake ba.
Lokacin da za ta tafi ne kuma ta ke faɗa mata cewa Insha Allahu za ta je Umura nan da sati ɗaya. Duk da Queen Bee na jin jiki hakan bai hanata yin ihu ba.
"Allah ya shiryeki Bahijjah, ni dai ki rage wannan ihun kar ki sa Babyn mu ta taso da ciwon kunne"
"Thank God mai sunan ki ce, idan ta taso da ciwon ajiye miki ita zan yi na ƙara gaba"
"Ta Allah ba taki ba, healthy baby za ki haifo mana"
Queen Bee ta amsa da Amin.
***
Bilkisu Kachallah tana zaune a office tana duba wasu takardu waɗanda tsarin ginin Estate ɗin da ta ke so ta gina ne. Sai ga kira daga Sakatariyarta. Bayan ta ajiye wayar ko sakan ishirin bai kai ba baƙon nata ya shigo.
"Lah lah wa na ke gani a nan?"
"Mommy, ko na ce Boss lady"
Bilkisu ta taso ta zo ta rungume shi tana faɗin "Babana ka ganka kuwa? Yaushe a gari?"
"Tun last month" ya faɗa yana zama a kujera.
"Amma Muhammad ka min laifi, kana garin nan tun last month amma ba za ka zo ka gaishe ni ba"
"Your Excellency ai yanzu ganin ki ya fi ganin Gwamna. Kin san sau nawa ina zuwa government house ba kya nan"
"Sorry son, na manta ranan Mahirah ta gaya min ka zo"
"Kin yarda kin fi Gwamna kenan" M Sani yai maganar yana murmushi.
"Duk abunda mu ke ai don Gwamna ɗin ne"
"I see"
Shiru ne ya biyu bayan haka sai takardu da Bilkisu ke ta flipping cikin sauri da alama ba ta ga abinda ta ke nema ba.
"Excellency I want to join politics"
Bilkisu ta dakatar da abin da ta ke ta zuba masa ido.
"Tun Baba na da rai na ke son miki magana amma Mommy ta hana shiyasa na yi shiru da zancen"
"Yanzu Rufaidan ta yarda kenan?"
M Sani ya girgiza kai
"Then?"
"Na riga na deciding zan shiga ko tana so ko bata so"
Bilkisu ta yi murmushi har sai da haƙoranta su ka bayyana. Ta hango dogon buri a idon ɗan 'yaruwarta, kuma lallai idan ta tallafa masa akan burinsa za ta samu mataimaki na jini.
"Babana ka je ka yi tunani ka san ba a jayayya da iyaye"
"Haba Excellency, i'm an adult ina da damar da zan yi duk abinda na ga dama ko iyaye na suna so ko basa so"
"Babana lallai ka girma"
"commisioner M Sani at your service Boss"
Bilkisu Kachallah ta bushe da dariya harda buga table. Tabbas dole ta jawo M Sani jikinta domin irin dakakkiyar zuciyar da ta ke so kenan.
***
Lokacin da Asiya ta shirya tafiya Umurah Bilkisu ba ta ji wani ɗar ba dan ta riga ta sa an mata bincike kuma tabbas babu hannun Gwamna a tafiyar da kuɗinta ta biya kuɗin jirgi.
Abu ɗaya ne ya ke damunta shine shirun da Asiya ta yi ta bibiyi komai na ta amma bata ga alamar tana yin wani abu akan abinda ya faru ba tunda dai yanzu kam kowa ya san kowa.
Lokacin da Asiya ta wuce Saudiyya kuwa sai Bilkisu ta tarkata hankalinta ta maida shi kan batun tsige Mai martaba Sarki sai dai kuma har yanzu dai abun bai yiwu ba. Ta rasa gane kan al'amarin Gwamna, a wasu abubuwan baya mata gardama, amma wani batun idan ta masa sai ta ga ya yi shiru ya ƙi aiwatar da abinda ta ce. Ta sa a ranta da ta samu sarari za ta je India a bibiyi ƙarfin aikin da aka mata.
Ranan da Asiya ta dawo Nigeria ba ta wuce jihar Congo ba sai ta wuce NIPSS da ke Jos. Tun kafin ta tafi Saudiyya CY yai mata maganar makarantar tareda kwaɗaita mata samun nasara akan burinta na yaƙar Bilkisu matuƙar ta samu shiga wannan makaranta. Lokacin da ta yi bincike akan makarantar sai ta ga ba ta da ko ɗaya daga cikin requirement na su, asali ma ita ɗin bata chanchanci ta shiga makarantar ba saboda tsaurinsa. Babu yadda za ayi a nominating ɗinta bata kai shekara arba'in ba sannan bata taka wani matsayi ba a rayuwarta.
Sai dai bata san ya aka yi CY ya samu shigar da ita wannan makaranta ba har ta kai board of governors sun nominating ɗin ta.
Lokacin da ta je gaban board of directors ta sha mamakin ganin mutumin da ba ta taɓa tsammani za ta gani a wajen ba.
Ta tambayi CY kafin ta zo kuma ya tabbatar mata da cewa babu sunan Gwamna Saifuddeen a cikin board of directors na makarantan amma kuma sai ga shi zaune cikin su.
Da ƙyar ta iya saita nitsuwarta lokacin da ta tsaya gaban su tana amsa tambayoyi. Kusan kowa ya mata tambaya a wajen amma banda shi, asalima bai maida hankalinsa kan ta ba sai kawai ya duƙar da kai yana ta rubuce-rubuce.
Minti talatin da takwas ta yi a wajen ta fito daga hall ɗin a ruɗe. Ba dai Gwamna zai hana a bata admission ba.
Bayan ta samu waje ta zauna ta kira CY yana ɗauka ta ce " CY kana son kashe min aure ne?"
Daga ɓangarensa yai shiru saboda maganar ta masa dirar mikiya.
Yana son Asiya, zai iya rantsewa ya fi Gwamna son Asiya. Tsananin soyayyar da ya ke mata ya sa shi nema mata wannan makaranta ta hanyar mahaifiyarsa, don ya tabbata idan Asiya ta yi National Institute for Policy and Strategic Studies (NIPSS) za ta samu makamin ya ƙi da Bilkisu Kachallah. Asiya is far from an eligible candidate a makarantar. Makarantar da sai manyan 'yan siyasa ko 'yan kasuwa ke shigarta, makarantar da ko malami sai ya kai matsayin professor ko associate professor kafin a iya bashi admission. Makarantar da idan ba ka kai shekaru arba'in bama ba za a kalleka ba balle a saurareka. But he boycott all this for her.
"CY kana jina? Ka ce babu sunansa a cikinsu kuma gashi nan na gan shi a wajen"
A ruɗe CY ya shiga ba ta amsa " i'm sorry Asiya. Babu sunansa a cikin sunayen da Mommy ta turo min shiyasa na gaya miki baya ciki"
"Shikenan, inaga tunda ya ganni ba zai yarda ma su bani admission ba"
"I'm truly sorry Asiya"
"Shikenan ya wuce CY"
Asiya ta katse wayar tana sauke ajiyar zuciya.
***
Sati biyu bayan dawowarta daga Saudiyya aka turo mata admission letter ta email. Ta yi murna sosai dan kuwa ta cire rai da samun gurbin karatu saboda Gwamna ya ƙi mata maganar zuwanta Kuru a Jos.
Lokacin da ta fitar da admission letter ɗin har ɗakinsa ta same shi ta masa maganar tafiya makarantar...
Ba su rabu ta daɗi ba shiyasa ko sallama ba ta masa ba ranan da ta tattara kayanta ta tafi.
Shiri ne na musamman ta yi dan haka ta samu Bilkisu a falo ta sanar da ita cewa za ta tafi yin masters ɗinta a Stanford University tana mata albishir da ta ci karanta ba babbaka dan ita kam karatu ne a gabanta.
Bilkisu ta mata fatan nasara. Ta riga ta samu tabbaci daga COS akan da gaske ne Asiya ta samu gurbin karatu a Stanford dan har kwafin admission letter ɗin ya kawo mata. Abinda bata sani ba shine takardar na bogi ne da CY yai ya bawa Asiya a matsayin shaidar tafiyarta Stanford.
Wannan rabuwa yai wa Asiya ciwo domin tafiya ce za ta yi ba tareda ta waiwayi gida ba har na wata goma ba wai dan babu hali ba sai don tana son ta samu nitsuwa wajen yin abinda ya kaita da kuma sauran bincike da ta ke yi ta ƙarƙashin ƙasa.
Ta damƙa amanar ƙannenta a hannun Abba wanda tun dawowarta daga prison ma ba su koma da zama wajenta ba, sun dai zo mata hutu na kusan sati ɗaya daga nan suka koma gidan Abba da zama.
Wani abu daya tsayawa Asiya a rai har ta tafi shine furucin Gwamna a kanta. Zarginta da ya ke da CY kwata-kwata bai kama hankali ba...
09
***
Idan akwai ƙuncin rayuwa, to kuwa ƙofofin ta'addanci da fitintinu suna buɗuwa. Watanni shida kenan da fara shugabancin Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah bayan ya lashe zaɓen jihar Congo. Abubuwan da ake gani za su yi sauƙi sai kuma komai ya fara taɓarɓarewa. Wata uku babu albashi ga shi babu wani major aiki da aka fara. Ba a ɗauki aiki ba sai ma dakatar da ma'aikata da aka dinga yi saboda verification na ma'aikata da Gwamna ya ƙirƙiro .
Da za ayi Verification ɗin tsakani da Allah to akwai macuta dayawa da za a zaƙulo waje, amma su masu cutan sai ka ga an clearing na su, amma masu gaskiyan sai abin yake ta shafansu fiye da ainihin macutan.
Cikin 'yan kwanakin nan anyi fashi a babbar hanyar da ta sada jihar Congo da jihohin Kano da Bauchi kusan sau biyar, kuma duk fashin da aka yi sai an samu salwantar rayuwa. A cikin jaha kuwa yara 'yan shaye-shaye sun addabi mutane da sace-sace na cikin gida. Kowa yanzu yana taka tsantsan ne da gidan sa, wasu har karnuka suka dinga siya suna ajiyewa a gida saboda gadi, dan abin ya kai halin ha'ula'i.
Kaza nan nan bata isa ta yi nisa da ƙofar gida ba, dan tana shiga lungu to babu fitowa kenan.
Ana cikin wannan matsi kuma aka sake shigo da harkan kidnapping. An fara da ɗaukan wani tsohon Kansila ne, wanda bayan an biya kuɗin fansa sai gawar sa aka sako musu.
Cikin watanni biyu an sace magidanta da ma matasa sama da arba'in, wannan abu ya sake tunzura mutane, aka shiga Allah wadai da mulkin SSK. Abinda a ke ji yana faruwa a wasu jahahohi nesa da su sai ga shi an fara a kusa da su.
A 'yan kwanakin nan kuma maganar tsige Sarki da ake son yi ne ya saka wasu mutane yin zanga-zanga a cikin jahar. Maganar bata gama tabbata ba, amma ƙishin-ƙishin da ake ji shine an fara maganar a state house of assembly. Babu makawa idan aka tsige Sarki kowa ya sani cewa Alhaji Sani Kachallah za a ɗaura a kujerar mulki tunda shima sarautar gidan su ce. Wannan son zuciya da ake son yi ya sake ɗarsawa mutane ƙiyayyar Gwamna Saifuddeen.
***
*National Institute for Policy and Strategic Studies, Kuru*
A wani ɗakin karatu kuwa wata mace ce data amsa suna wayayyiyar mace ta ke dudduba wani littafi da ke gabanta, matar sanye ta ke da baƙar jacket da ya kai mata gwiwa, tana sanye da pencil jeans, sai rigar ciki da ta saka kalar ruwan goro, ta yi rolling da gyale shima ruwan goro. Akwai manya manyan bangles a hannunta ruwan ƙasa sai kuma zobben azurfa guda biyu da ke yatsarta na uku dana huɗu a hannunta na dama . Minti biyar kenan da gama lectures da aka yi mu su yau, kuma Alhamdulillah ta ƙaru da abubuwa sosai a wannan lecture da aka yi akan maudu'i mai taken Shugabanci.
Matar ƙoƙarin ƙarisa haɗa lecture note ɗinta take, daga gefe tana sauraron recording da ta yi na amsoshin tambayoyi da guest lecturer ɗin yai ɗazu a aji. Ba ta da komai yanzu sai ƙarfe biyar na yamma inda su ke da zama a study group na su. Ba sallah ta ke ba shiyasa ba ta damu da tashi daga ɗakin taron ba duk da kuwa ɗazu da ta duba agogon da ke manne a ɗakin taron ya nuna mata ƙarfe biyu ne da minti goma na rana.
"Asiya Kachallah" Asiya ta yi firgigit dan ba ta tsammanci akwai mutum a ɗakin taron ba, a zaton ta kowa ya tafi.
Ta ɗan juyo a hankali ta kalleshi sai kuma ta haɗa rai. Tunda ta fara karatu a wannan waje Colonel Modi ke takura mata, ba shi kaɗai ba ne amma na shi yayi yawa. Wani lokaci ta kan yi tunanin ko dai ta manna tag a goshinta cewa ita matar aure ce ko hakan zai sa su dena yi mata maganar banza. To amma dukkansu ba yara bane sun san mi su ke sun san tanada aure sun kuma san wa ta ke aure.
"Tambayar da kika yi ɗazu was brilliant" Colonel Modi yai maganar yana zama gefenta.
Asiya ta duƙar da kai ta cigaba da rubutu ba tareda ta ce wani abu ba.
" ba za ki haƙura da rubutun nan ki zo mu je ki ci abinci ba?"
Asiya ta ɗago idanunta ta kalli Colonel Modi tace "babu ruwanka da ni Colonel, ka yi harkanka na yi nawa please"
" Asiya kenan. Ki dena ɓatawa kan ki lokaci da auren mutumin da baya ra'ayinki. Ki yarda da ni na nuna miki kulawar da kika dace da shi"
Asiya ta buga littafinta da ƙarfi akan desk ta ce "Colonel wannan ya zamo na ƙarshe da za ka min magana makamancin wannan, idan ba haka ba zan ɗau mataki akan ka"
Bata jira amsar da zai bayar ba ta tattara sauran littattafanta da jaka ta fice daga ɗakin taron...
Yau ta kama monday, kuma rana ce da suka kwana da sanin cewa guest lecturer na su na wannan mako ba kowa bane face matar Shugaban ƙasa, itama Alumna ce ta institute ɗin hakan yasa za su samu insight sosai akan karatun da su ke.
Kamar kullum a gaba-gaba Asiya ta zauna, duk da kuwa idan ka duba kaf ajin ita ce ƙarama a ciki. Ba ƙaramin sa'a ta taka ba wajen samun damar shiga wannan makaranta duk da kuwa bata cika requirements da ake buƙata ba. Babu abinda za ta ce da CY sai dai tace Allah ya datar da shi da gaskiya. Ba ta san ya aka yi ya iya boycotting protocol ba, amma koma ya aka yi ta tsinci kanta a nan, tana alfahari da wannan dama da ta samu.
Minti goma da zamansu matar Shugaban ƙasa ta iso ajin inda ta gabatar da lecture na minti arba'in sannan aka bada damar tambayoyi da kuma ƙarin gudummawa daga participant.
Sau uku Asiya na yiwa matar shugaban ƙasa tambaya wannan ya ja hankalin first lady zuwa kanta. Bayan an gama class ɗin first lady ta buƙaci ganawa da Asiya. Minti ishirin su ka ɗauka suna tattaunawa mai mahimmanci kuma Asiya zata iya cewa bayan Madam Chess hiranta da first lady na ɗaya daga cikin hirarrakin da suka zamo silar gyara mata alƙiblar data dosa na cimma burikanta.
***
Su shida ne zaune a round table suna tattauna wasu batutuwa. Kasancewar su manyan mutane shiyasa Asiya ta ke ba su girma wajen kasancewa ta ƙarshe a wajen magana. Ita kaɗai ce mace a group ɗin kuma ita ɗin ce dai ƙaramar cikinsu. Idan ka cire Colonel Modi dukkansu sun haifeta, kai Alhaji wakili kam yayi jika da ita.
Da gangan Colonel Modi ya kawo case study na Jahar Congo cikin tattaunawar da su ke ya tura tambayarsa ga Asiya bayan ya gama kawo ƙorafin matsalolin da jahar ke ciki na rashin tsaro da kuma faɗuwar tattalin arziƙi.
"Kina ga akwai yadda za ayi a farfaɗo da tattalin arziƙin jahar Congo musamman ƙarƙashin jagorancin Gwamna Saifuddeen Kachallah?"
Asiya ta ɗaura hannunta ɗaya akan table ta ce " Tabbas za a iya farfaɗo da tattalin arziƙin jahar idan aka maida hankali kan harkan noma. A baya Jahar Congo ta kasance ɗaya daga cikin jihohin da ake alfahari da su wajen noman shinkafa, shinkafa kaɗai ya bunƙasa arziƙin jahar har..."
"Hajiya Asiya Kachallah kina maganan kusan shekaru goma baya ne, muna magana ne akan gwamnatin Saifuddeen Kachallah wacce ta gaza biyan albashin wata huɗu na ma'aikatanta. Kina maganar noman shinkafa, nan nan taki na zamani Gwamnati ta gaza sakewa manoma ya kike ga za ayi nomar?"
Asiya ta yi shiru tana nazari.
"Kin yadda kenan shekaru uku da Saifuddeen zai yi gaba za a samu rugujewar tattalin arziƙi a jihar ku fiye da tunani"
"Ko kaɗan Colonel Modi" Asiya ta faɗa da confidence.
"Infact, shekaru uku ma su zuwa zasu zamo abin kwatance a duk faɗin ƙasar nan"
Colonel ya jingina bayansa da kujera ya ce " ba cika baki ba, we need plans"
"Project tomatonion" Asiya ta faɗa tana kallon 'yan group ɗin ɗaya bayan ɗaya.
Kafin ta cigaba. " kafin na zo nan, na jima ina dogon bincike akan tarihin jahar Congo musamman gameda harkan noma. Na san mi ake nomawa shekaru ɗari baya. Na san yanayin ƙasa da yanayin ruwan sama da ake samu a yankunan jihar, na san minene arziƙin kowacce ƙaramar hukuma a cikin ƙananan hukumomi goma shatara da ake da su a jihar. Wannan ya bani damar ƙirƙiro project Tomatonion domin dawo da tattalin jihar nan ba da daɗewa ba Insha Allah"
Dukkansu su ka zuba ido suna kallonta.
"Anyi zamanin da jihar Congo tana fita da Albasa jihohin kudu, dama ƙasashen da ke kusa da mu irinsu Niger, Cameroon da Chad. Har a zamanin mulkin turawa, farar Albasa a jahar Congo daban ta ke da ta ko'ina. Zan farfaɗo da noman tumatir da albasa fiye da shekarun baya"
Asiya ta kalli Colonel Modi ta ce "ina fata ka gane cewa ba noman shinkafa kaɗai ne arziƙin Congo ba"
Alhaji Ɗanfisa da Alhaji Wakili su ka shiga tafa wa Asiya cikin nuna jinjina gareta. Colonel kam bakinsa ne ya kafe ya rasa abin faɗa dan dama so yake ya kushe Gwamna Saifuddeen, ya aibanta shi, sai kuma aka samu akasin haka...
10
"Azzalumi, Macuci, Allah ya tsine maka, Azzalumi, Azzalumi..."
Gwamna Saifuddeen Kachallah ya farka a firgice ya danne kunnensa da ƙarfi yana faɗin "No, No, No i'm not"
Kusan minti biyu ya ɗauka tsaye yana maimaita abu ɗaya, yana cire hannayensa daga kunne yai saurin maida su saboda irin ihun da ake masa a cikin mafarki ya ke ji. Ya dena kwana cikin duhu dan haka ɗakin tar yake da haske, Da gudu ya ƙarisa wajen table ya ɗauki wata ƙaramar roba ya buɗe ya zaro ƙwayoyi huɗu ya jefa a baki ya haɗiye. Tsayawa yai a wajen yana maida numfashi. Cikin 'yan kwanakin nan baya iya bacci, sleeping pills da ya ke sha ya riga ya zama addicted da shi har ta kai baya iya ma baccin ko da ya sha, idan kuwa ya samu yai bacci to ire-iren mugayen mafarki da ya ke yi shi ke hana barcinsa tsawo.
Saifuddeen ya tsaya a tsakiyar ɗakin yana kallon makeken gadon da ke shimfiɗe da duvet na alfarma amma bacci ya gagara a kai. Ina ma zai iya zama kamar Malam Habu mai share masa office, ya sani ba shi da gado kamar wannan amma a duk inda ya ke ya sani yana nan yana bacci hankali kwance.
"Excellency 'yata dana aurar kwanaki Allah ya azurtata da haihuwar ɗa namiji"
"Masha Allah. Ya sunan yaro?"
"Ranka shi daɗe mai sunan ka ne. Saifuddeen amma Ameer ne laƙabinsa" Malam Habu ya faɗa fiskarsa ɗauke da murmushi.
Watanni goma da suka wuce kenan.
"SAIFUDDEEN, SAIFUDDEEN, SAIFUDDEEEEEN" Gwamna ya kira da ƙarfi kamar wani zautacce.
Gaskiya ya kamata a chanjawa jikan Malam Habu suna, kada shima ya zama Azzalumi kamar mai sunansa abinda ƙwaƙwalwarsa ke gaya masa kenan. A take kuma sai ya je ya ɗau wayarsa ya shiga lalubo lambar Malam Habu sai dai kuma idanunsa dishi-dishi ya ke gani dan haka har ya wuce Mal Habu cleaner kamar yadda ya saving numbar bai gane ba. Ya shafe kusan minti goma yana surfing contacts ɗinsa amma bai gani ba. Chan wata zuciyar ta ce masa ya ajiye wayar gobe idan ya je office sai ya masa maganar.
Kamar wani ƙaramin yaro Gwamna SSK ya takure jikinsa a gefen gado yana rawan sanyi. Ya kasa tashi ya kashe AC da ke ɗakin ya ma kasa komawa tsakiyar gado balle ya rufe jikinsa da bargo ko zai ji ɗumi.
A wannan yanayi daya kamata a ce ya kokawa Allah lamarinsa, ya nemi taimakon Ubangiji akan mulkinsa. Gaba ɗaya basirarsa ta tsaya ne a shan anti- depressant saboda ya samu sauƙin damuwarsa.
Bai samu bacci ba sai kusan Asuba. Hakan yasa shi makara sallar Asuba. Infact sai da Bilkisu ta zo ta tashe shi ƙarfe takwas na safe saboda akwai wani taro da za su je tare yau da ƙarfe tara.
A gurguje yai sallah yai wanka ya shirya ya fito yana murmushin da bata wuce fatar baki ba. Babu wanda ya san abunda ya same shi jiya da dare, babu wanda ya san kullum kukan talakawa ke hana shi bacci. Ita matarsa da ya kamata ace ta kwana tare da shi har ma ta lura da damuwarsa ta riga ta saka katanga tsakaninsu. Rayuwar da su ke ta Gwamna ne da Matar Gwamna ba wai mata da miji ko kuma 'yan uwa ba...
***
"Bikin cikar shekara ɗaya da ake son yi, ni ina ga ya kamata a ajiye shi gefe Ranki shi daɗe"
Bilkisu Kachallah ta kalli
M Sani irin kallon kana da hankali kuwa?.
"Seriously Excellency, this is a bad time, idan har aka yi wani abu na taro a critical moment haka duniya za ta zage mu. Already ana kukan babu a jihar nan, ga ɗaliban da aka sace sun doshi wata ɗaya babu labarinsu. Ko da za ayi celebration Boss sai dai ayi shi low key. Kamar a kira taron addu'a haka kin gane ai"
Bilkisu ta yi shiru tana nazarin kalamansa. Tunda Muhammad Sani yai nasaran ture Lamara Damana daga jikinta shine ya zamo na hannun damanta mai bata shawara a kan komai.
"Inaga ki ƙara sunan mutanen da za ki tura Hajji wannan shekaran, saboda a rufe bakin malamai"
"Yawwa M Sani, shi wannan Malam Idris Tukur ɗin ya za ayi da shi ne?"
M Sani ya kwashe da dariya. Sai da ya yi mai isar sa kafin ya kalleta ya ce " Boss kin san bana wasa da assignment ɗina"
Ya ɗauko wasu takardu a cikin folder ya miƙa mata ya ce " Malam Tukur ba zai ba mu matsala ba daga yanzu, he has received 50M fisabilillah. Masallaci da Makarantansa duk za a kammala masa ginin su nan da watanni uku, duka Fisabililahi daga ƙarƙashin jagorancin Hajiya Bilkisu Kachallah"
Bilkisu ta tintsire da dariya tana faɗin "Malam zai ci kaji yai naman wuya kenan"
"Ofcourse My Boss, sauran ƙananun ƙwarin kam miliyan biyar-biyar da kujeran Makkah zai miki maganinsu"
"Amma wannan bagidajen Malamin fa? Tuna min sunan sa"
"Malam Hussaini Zango"
"Yes shi. Na ji labarin shima yana ranting acikin gari"
"Kar ki damu da shi. Na karance shi, gaskiya ba zai sayu da kuɗi ba, amma kuma mabiyansa ai mayunwata ne, da sannu za su tattara su koma ƙarƙasin Malam Tukur" M Sani ya faɗa yana murmushin mugunta.
Bilkisu Kachallah ta ce "weldone my boy"
***
A ofishin Chief of Staff kuwa. Lamara Damana ne ke zaune akan kujera yana jujjuya biro a hannunsa. A koda yaushe shi yana tare ne da mai nasara, yana goyon bayan inda zai samu daraja da kima ne, yana goyon bayan wanda zumar mulki ke hannunsa.
Ba haka ya hango ba lokacin da ya goyawa Bilkisu Kachallah baya. Tunda yaron nan ya zo ta fara rena masa wayo. Ta ya za ta yi amfani da shawaran yaro ƙarami ɗan shekara ashirin da bakwai ta yi watsi da nasa shawaran. Yaushe Muhammad Sani ya zo duniya? Yaushe ma ya shiga harkar siyasa?.
Yai murmushin gefen baki ya ce " idan ƙabilanci da 'yanuwantaka za ki nuna min Bilkisu, ni kuma zan nuna miki cewa ni Lamara Damana ba kanwan lasa ba ne"
Hoton poster na Asiya ya ɗauko daga cikin wani file. Yana sane da cewa Asiya ta je institute ne saboda ta ɗau fansar abinda Bilkisu Kachallah ta mata. Shiyasa ma da Bilkisu ta sa shi bincike a kan makarantar da Asiya ta tafi ya mata ƙarya cewa fa gaske ɗin ta je America yin masters ɗinta ne.
COS yai murmushi ya ce idan kuwa Asiya na son revenge ni kuma zan taimaka mata da duk abinda za ta buƙata. Ya ɗau red marker ya zana ƙaton × akan hoton Bilkisu Kachallah. Sai kuma ya ɗauko green marker ya zana ƙaton good mark a hoton Asiya. Yana ajiye marker ya ce "let the battle begin"
A zuciyarsa ya fara tsara yadda zai koma gefe ya kalli yadda waɗannan mata biyu za su yi yaƙi tsakaninsu. Yayi alƙawarin tsayawa a gefen kowacce ya bata gudummawa gwargwadon ƙoƙarinta. Daga ƙarshe idan ya hango mai nasara a ciki sai yai maza ya koma wajenta gaba ɗaya. Duk da zuciyarsa na riya masa Asiya ce za ta yi nasara amma for now ba zai bar jikin Bilkisu Kachallah ba.
***
Yayinda lamurra su ke ta sake taɓarɓarewa a jahar Congo. Kan Malaman addini ya rabu ne kashi uku. Akwai masu kallo, waɗannan sun zuba ido ne suna kallon yadda ake shugabanci a jihar amma ba su saka baki a kai ba balle har su yiwa Gwamna da muƙarrabansa wa'azi.
Kashi na biyu kuwa su ne su ke ta sukan Gwamna da matarsa wacce yawo da ta ke da maciji a cikin gari yasa su ke kafurtata wasu kuma su ke kiranta da 'yar ƙungiyar asiri. Waɗannan su ne ire-iren tawagar Malam Tukur wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan malamai da ake ji da su a jihar. Lokacin da Malam Tukur ya ga miliyoyi a account ɗinsa ya kuma ga an kama aikin masallacinsa gadan-gadan sai kawai ya fara reversing wa'azinsa yana gayawa Mutane kada a tsinewa shuwagabanni, addu'a za a dinga musu a kuma ci gaba da haƙuri har Allah ya kawo ɗauki, domin Allah Sami'un Basirun ne yana ji kuma yana gani. Da sannu maganganun Malam ya fara shiga zuciyar mutane.
Kashi na uku su ne ire-iren Malam Zango, waɗannan su ke ƙoƙarin yiwa Gwamnati wa'azi, tareda ƙoƙarin kawo kukan talakawa ga kunnunwan gwamnati. Sai dai irin su Malam Zango ba su da Mabiya dayawa, yawancin ma su zuwa ma yunwa da talauci ne ya sa su komawa ga masallaci suna bibiyar wa'azi da karatuttukan sunnah, da zaran an samu sauƙi za su watse...
***
Gwamna SSK ya fara duba visar da ke gabansa. Bai san ya aka yi ya ce a booking masa tafiya wannan ƙasar ba. Yaushe ya bada wannan umurni?
Lokacin da Sakatare ya kawo masa file ɗin ya gani tsoron tambayar sa yai kada yai tunanin ko ya fara zaucewa ne.
Mi zai yi a Gambia?. Ya sake tambayar kansa.
Ya latsa computer da ke gabansa ya duba duka schedules ɗinsa na wannan sati amma bai ga inda aka tsara tafiyarsa wannan ƙasa ba. To ya aka yi aka booking masa tafiya ƙasar Gambia shi ɗaya, kumama tafiyar yau da yamma ne.
Chan dai da ya rasa amsoshin tambayoyinsa sai ya ɗau waya ya kira COS. Ba a jima ba sai ga shi ya shigo office ɗinsa.
Lamara Damana na zama Gwamna ya tura masa visar da ticket na tafiyar.
"Na minene wannan?"
Lamara ya kalli takardun sannan ya dubi Gwamna ya ce "umurnin da ka bani jiya kenan Excellency"
Cikin rashin fahimta yace "umurni? Da yaushe kenan?"
"Your Excellency Sir ba ka tuna ba? Jiya ƙarfe biyun dare ka kirani kace na booking maka jirgi zuwa Gambia za ka je ka duba mahaifiyar ka"
Gwamna ya zaro ido waje lokacin da ya tuno abinda ya faru jiya da dare. Tabbas shi ya kira Lamara, ba ma haka ba har kuka ya fara yi masa lokacin da ya ce masa ba zai iya booking masa yau ba saboda akwai meeting da za su yi da wasu manya.
"Excellency sorry to say, amma mahaifiyarka ta rasu Sir. Ko dai wajen wata 'yar uwarta za ka je?"
Maganan da Lamara ya masa kenan jiya, kuma maimakon ya nitsu ya saurare shi, sai ya daka masa tsawa akan ya nema masa jirgi shi zai tafi ƙasar Gambia wajen mahaifiyarsa.
Gwamna da COS suka fara kallon-kallo. Idan wannan magana ta fita akwai matsala babba. Gwamna ya fara zaucewa.
Gwamna ya buɗe baki a hankali yace " maganar nan ta tsaya a nan"
COS ya ce " an gama Excellency"
Bayan tafiyar Lamara Damana, Gwamna ya dafe kansa da ke mugun sara masa ya fara tunanin taya zai ɓullowa wannan lamari. Anya bai fara zaucewa ba kuwa? Domin ba wannan ne karo na farko da ya ke yin abu kuma ya manta da cewa yayi ba.
Jiya mafarkin mahaifiyarsa ya farkar da shi daga bacci, kewarta ya ke. Yanayin daya ganta a mafarki ya masa kamar tana nan raye kuma tana fushi da shi. Lokacin da ya farka nan da nan ya shiga kiran numbar Sakatarensa amma numbar bata shiga ba shiyasa ma ya kira Chief of Staff ɗinsa...
***
A yau ma Gwamna Saifuddeen Kachallah bai iya rintsawa ba, duk da kuwa cikin dare an yi ta tsala ruwan sama kaman da bakin ƙwarya, ni'ima ta sauka a wannan dare.
Washegari tun kafin Gwamna ya fita office aka kawo mishi labari cewa an samu ambaliyar ruwa a ƙaramar hukumar Boyo da kuma wa su ƙauyuka kusan guda huɗu wannan ya jawo asarar rayuka da dukiya. Saboda ƙarfin ruwan sai da ta yanke Gadar da zai kai ka Boyo daga garin Saje, wannan ya haifar da hatsari har aka rasa rayuka da dama.
Gwamna yana ajiye waya Bilkisu ta kalleshi ta ce "yanzu ya za ayi kenan?"
A handsfree ya saka kiran dan haka ta ji komai, bai san mi zai ce ba dan a mafiya lokuta ya kan rasa abun faɗa idan yana tareda ita.
"Inaga ka je ka sympathising da su,wannan zai ɗaga darajar ka a idon su. Ƙila ma ya kawo ƙarshen ƙananun maganganu da ake yi a kanka a yankin"
Gwamna ya amsa da toh...
11
Gwamna Saifuddeen Kachallah ya miƙe daga kujerarsa ya nufi banɗaki dake cikin makeken ofishinsa. Ya buɗe tap ya wanke hannunsa sannan ya sa hannu ɗaya ya tari ruwa ya wanke fiskarsa da shi, sai da yai haka sau uku kafin ya rufe tap ɗin ya ƙurawa fiskarsa ido ta jikin madubi. Wannan fuska da ya ke gani a jikin madubi ba shine Saifuddeen da ya sani watanni goma shaɗaya da suka wuce ba.
Ba zai iya tuna abinda ya banbanta wancan Saifuddeen da wannan Saifuddeen ɗin ba amma tabbas akwai banbanci mai faɗi tsakaninsu.
Ya kai kusan minti biyar yana kallon kansa a madubi kafin yai saurin ɗauke kai saboda mummunan abinda zuciyarsa ta ayyano masa.
Lokacin daya fito daga banɗakin ya saita kansa kamar babu abinda ke damunsa dan kuwa a kullum abinda ke bayyane wa jama'a kenan wato Gwamna yana nan cikin kwanciyar hankali duk da kuwa ana fama da talauci, tsadar rayuwa, kidnapping dama fashi da makami a Jihar.
Minti biyu yai a office ɗin sannan ya fito inda tawagarsa suka mara masa baya dan kai ziyarar ganin ido garuruwan da ambaliyar ruwa yai wa ta'adi.
***
Yau ta tashi ne da kewar mijinta. Mafarkin da ta yi ya bata tsoro hakan ya sa ta ke kwaɗayin kasancewa da shi ta nuna masa komai ya kusa zuwa ƙarshe.
Saura ƙiris ta dawo gare shi, ta dawo don ta taimaka masa cikin mulkinsa.
Ta yi kewar moments ɗin su tare wanda bai yi tsawo ba saboda yadda abubuwa su ka dinga faruwa tsakaninsu.
Ta yi kewar soyayya, kulawa da kuma kwanciyar hankali da bata samu a wajensa ba...
Kasancewar tana kan aikin project ɗinta ne sai ya zamto kaso hamsin cikin lokacinta ya tafi ne kan bincike musamman da ya ke fannin da ta ɗauka ya kasance tattalin arziƙin Jikar Congo ne.
Sai dai yau kam hankalinta ya kasu ne wajen tunanin aikin da ta ke da kuma mijinta. Ta sani kullum yana nan a ranta da shi ta ke kwana da shi ta ke tashi amma yau tunaninsa ya tsaya mata a rai fiye da kullum. Like, har rubuta sunansa ta yi cikin rubutun da ta ke.
"Kai! Asiya focus" ta faɗi kalmomin nan ya fi sau goma, amma a hakan sai ta tsinci kanta wajen duba hotunansa a wayarta ko kuma ma ta buɗe littafinsa tana karantawa.
Ƙarshe dai sai numbarsa ta lalubo ta tura masa saƙo mai daɗi duk da kuwa ta san ba lalle ne ya dawo da reply ɗin ba...
Ƙarfe uku na yamma Asiya ta farka daga bacci bakinta na furta Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun. Ta dafe ƙirjinta tana haki kamar wadda ta yi tsere. Ta sa hannu ta goge gumin da ya tsatstsafo mata ta miƙe da sauri ta fara neman wayarta, chan ta same shi akan desk kusa da laptop ɗinta.
Numbarsa ta shiga kira tana cigaba da maimaita Innalillahi. Numbobinsa duka biyu bai shiga ba hakan ya sa ta kira numbar Mahira, numbar ta yi ringing amma ba a ɗauka ba.
"Ya Ilahi! Somebody should please pick the call"
Asiya ta yi maganar dai-dai tana kiran numbar Halima Kachallah.
"Thank God. Anty Halimah lafiya kika ƙi ɗaukan wayar ki"
"In-law na bar wayar a falo ne yanzu aka miƙo min ita"
"Kin san inda Excellency ya ke? Duka nambobinsa basa shiga"
"Hmmm somebody is missing the governor"
"Anty Halimah joke aside, ki kira First lady ki tambaya"
"Ok ina zuwa"
Asiya tana tsaye riƙe da waya tana addu'ar Allah ya sa kar mafarkinta ya zamo gaskiya. Idan wani abu ya samu Gwamna ba za ta yafewa kanta ba.
Minti huɗu kafin Halima ta kirata.
"Hello, yana lafiya ko?"
"Yana lafiya In-law, wai ya kai ziyara inda ambaliyar ruwa yai ta'adi ne. Ƙila ba network ne shiyasa numbar ba ta shiga ba"
Asiya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce " Ok, nagode Anty Halimah"
"Yaushe za ki dawo, mun yi missing ɗin ki fa"
"Ni ma nayi missing ɗin ku Anty Halimah. Insha Allah na kusa dawowa"
Sun ɗan jima suna taɗi kafin Asiya ta kashe wayar sai dai kuma har lokacin tana jin raɗaɗi a ranta.
Bayan ta yi sallar la'asar tana kwance akan sallaya tana duba wasu takardu bacci ya sace ta, ko minti goma ba ta yi ba ta farka saboda mafarkin da ta yi. Wannan karan kam ta ɗaura aniyar komawa gida, dole ne ta je ta ga mijinta, wani irin mafarki ne wannan wanda ya maimaitu mata har sau uku.
Ba ta ma gwada kiran numbarsa ba sai da ta haɗa wasu kayanta ta shiga mota sannan ta kira numbarsa. Bai ɗauka ba hakan ya ƙara tsoratata, ta dai daure ta cigaba da tuƙi tana karanto addu'o'i a ranta.
***
Lafiya-Lafiya Gwamna da tawagarsa su ka isa garin Boyo. Sai dai bayan sun gama abunda za su yi Gwamna ya tsaya
zai wa wasu matasa jawabi dai-dai bakin gadar da ta tsinke. Yana cikin magana wani matashi daga nesa ya saita goshinsa da dutse, kafin securities su ankara dutsen ya bugi goshin Gwamna. Kaman an aikosu kuwa sai aka fara jifan Gwamna da tawagarsa ta ko'ina. Duk da securities sun bawa Gwamna kariya hakan bai hana an samu Gwamna ba da ƙyar aka wuce da shi mota saboda inda aka yi parking motocin yana da nisa.
Kafin ka ce me an ɗaura abinda ya faru a yanar gizo. Matasan ƙaramar hukumar Boyo sun jefi Gwamna Saifuddeen Kachallah.
Tunda aka shigar da shi motar ya sunkuyar da kansa yana dafe da goshinsa da ke fitar da jini.
Ba abinda ke yawo a ƙwaƙwalwarsa sai ihun mutane da ya ke jiyowa "bama yi, bama yi, a tsige mana Azzalumi, Allah ya tsinewa Saifuddeen Kachallah".
Bai je da securities dayawa ba saboda babu wanda ya hasaso haka zai faru. Sannan kuma ɗaruruwan mutane ake magana bisa securities 'yan tsiraru da ke tare da shi wanda suma da ƙyar suka sha.
Kafin Gwamna ya shigo gari labari ya baza ko'ina a cikin jahar, kowa na faɗin Allah shi ƙara, Allah yai wa matasan nan albarka saboda sun nuna jarumta.
Straight office ɗinsa ya ce a wuce da shi ba gida ba. Yana zuwa kuwa cikin sauri ya shige katafaren ofishinsa bayan ya bada umurnin kada a bari kowa ya shigo inda ya ke.
Ya taka a hankali har ya kai tsakiyar office ɗin sannan ya durƙusar da gwiwonsa ƙasa ya dafe kansa da hannu biyu ya fashe da kuka. Kuka sosai ya ke yi kamar ƙaramin yaro. Tunda ya mallaki hankalinsa bai taɓa kuka makamancin wannan ba.
A chan gida kuwa Bilkisu sai masifa ta ke tana rantse-rantse cewa sai ƙaramar hukumar Boyo ta ji a jikinta kan abinda su ka aikata. Ta shiga kiraye-kirayen mutanenta dan ganin an dakatar da yawon da videon jifar ke yi. Sai dai kash! a zamanin social media abin da kamar wuya.
"Yana ina ne?. Ok idan ya fito daga office ɗin ka gaya min"
Bilkisu tana ajiye wayar hannunta ta shiga ƙwalawa Safiya kira.
Safiya ta shigo falon a ruɗe dan suma sun ga videon abinda ya faru a TVn da ke falon ƙasa.
"Ina kika shiga ina ta kira tun ɗazu?"
"Ran ki shi daɗe..."
"Ɗauko mun jaka da gyale a ɗaki ki same ni a ƙasa"
"Toh Excellency"
***
"Ba zan iya zama da kai ba, ba zan iya zama na yi shiru kan lamarin mulkin ka ba. Idan ka hana ni tafiya zan iya ja da maganar ka"
"Saboda shi za ki tafi?. Na ji labarin mahaifiyarsa ce ta sama miki gurbin karatu a wajen"
"Babu abinda ke tsakanina da CY. Idan har ba ka so na tafi ne saboda zargina da kake gara ka sawwaƙa min yanzu na san cewa tafiya ce zan yi ba tareda igiyar ka ba. Idan kuma saboda matar ka ce kake son hanani tafiya to ka sani zan tafi koda ba da yardar ka ba"
"Ki yi duk abinda kike so Asya, ki je duk inda za ki je. Ba ki ɗauke ni a matsayin mijin ki ba balle ki nemi shawarata akan rayuwar ki"...
Kuka ne ya kufcewa Asiya lokacin da ta tuno yadda suka rabu da Gwamna dai-dai ta iso hold up na shiga jihar Congo.
"Anya ban cuci kai na ba? Anya ban ci amanar sa ba?, idan ya mutu na shiga uku ni Asiya"
Steering mota ta fara duka a hankali tana faɗin " why did i choose revenge over him, why did i choose to leave him?"
Horn ta shiga dannawa da ƙarfi saboda ta ƙagu ta bar wajen, bata san miyasa hold-up ɗin yai yawa ba kuma kamar ma motocin basa moving.
Wani soja ne ya ƙulu da horn da motar Asiya ke yi. Bai ma lura da numbar motar ba yana zuwa ya ƙwanƙwasa glass ɗin ya fara masifa.
Asiya ta rolling glass ɗin kaɗan ta miƙa masa wata kati. Yana ganin sunan da ke jiki ya ƙame yana faɗin "sorry Ma"
Ya wuce da sauri ya je yai magana wa Ogan su nan da nan aka bada hanya motocin da ke gaban Asiya guda bakwai su ka wuce sannan itama ta wuce da tata motar.
Shigar ta gari sai jikinta yai sanyi, sojoji ta ke gani ta ko'ina hakan yasa bugun ƙirjinta ya tsananta. Ba dai wani abu ya samu Gwamna ba? Ba dai Gwamna ya halbe kan sa ba kamar yadda ta gani a mafarki. Hannunta ya shiga rawa, zufa ya fara keto mata ta ko'ina. Addu'a ta fara jerowa a bakinta dan ta samu nitsuwa.
***
Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah ya fito daga office ɗinsa. Ya riga ya bada umurnin cewa a bar masa mota ɗaya. Har ya fito waje murmushine shimfiɗe a fuskarsa, irin murmushin nan da ya fi kuka ciwo.
Daga shi sai dreban sa su ka wuce gidansa kamar yadda ya buƙata. Har ya shigo gidan gaisawa ya ke da mutane cike da nitsuwa tamkar babu abinda ya ke damunsa, kaman babu abunda ya faru yau.
Yana isa gida aka kira Bilkisu Kachallah aka sanar da ita ya shiga gida. Lokacin tana hanyar zuwa gidan su dan ta gana da mahaifinta. Har ta ce za ta juya sai kuma ta fasa akan idan sun gama magana da Baba za ta wuce chan tunda ba wai wani nisa ne tsakanin gidan Saifuddeen da Kachallah house ɗin ba.
Ɗakinsa na nan tsaf-tsaf kamar ɗakin amarya, ko'ina sai ƙanshi yake. Ya kan shigo gidan a lokutan da ya ke son kaɗaici shiyasa masu aiki basa rabuwa da gyara shi.
"Allah ya tsinewa Saifuddeen Kachallah" kalaman da su ke ta yawo a kansa kenan tun fitowar sa daga office. Yanzu ma jin abin yake yana maimaituwa a kunnensa kamar waƙar da aka sa a repeat mode.
Hannunsa na rawa ya buɗe closet ɗinsa, cikin kayansa ya jawo wata ƙaramar akwati, ya unlocking key da ke jiki sannan ya buɗe akwatin. Ya ƙurawa bindigar da ke cikin akwatin ido. Tunda ya karɓeta ya mata lasisi (license) bai taɓa fito da ita ba sai yau. To babu abunda zai sa ya fito da itan domin kullum yana tare da masu tsaro.
Gwamna ya sa zira-ziran yatsunsa ya fara shafa bindigar har lokacin zuciyarsa na ingiza shi ya aikata abinda yai niyya kawai.
Bayan ya ciro bindigar ya zauna a ƙasa ya saita bindigar dai-dai gefen goshinsa. Ya koyi yadda ake harbi ne a wani zuwansa ziyara ƙasar Mexico kusan shekaru takwas da suka wuce.
A hankali tarihin rayuwarsa ya fara dawo masa daga ƙarshe kuma maganganun Asiya su ka zo masa ranan da su ka yi rabuwa ta ƙarshe da ita.
"Ta ya zan ɗauke ka mijina bayan ba ka taɓa kwatanta adalci a kaina ba. Ta ya zan ba ka matsayin miji bayan kana take hakkin talakawan da ke ƙasan ka. Kana so in zauna da kai fushi da tsinuwar talakawa yana bin ka duk inda ka shiga? Kana tunanin kai kaɗai tsinuwarsu zai shafa? Zai shafeni, zai shafi 'ya'yan ka da duk wani na kusa da kai. Ba zan iya zama da miji kamar ka ba"
Gwamna yai murmushi ganin kyakykyawar fiskarta ya bayyana a idonsa.
"Gara da ki ka tafi Asya, gara da kika rabu da ni. I hope idan bana nan tsinuwar zai tsaya a kaina ni kaɗai"
Hannunsa na rawa ya sake harsashin bindigar...
12
"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun. Dan Allah kar ka harba, Dan Allah miji na kar ka harba"
Asiya tana maganar tana takowa a hankali idanunta na zubda hawaye.
"Kar ki matso inda na ke"
Ta tsaya chak da tafiyar cikin kuka ta ce " idan ka harba ka san mi zai faru?. Nima bindigar zan ɗauka na harbe kaina sai kawai akai mu wutan tare.
"Mijina Idan kana ganin ka ci amanar mutane nima na ci amanar aurena. Idan ka kashe kan ka saboda kana ganin shine mafita to nima zan kashe kaina saboda ba zan iya rayuwa ba tare da kai ba "
"Asya" ya kira sunanta da muryar shi mai rauni. Sai kuma ya ajiye bindigar a ƙasa ya fashe da kuka. Da sauri Asiya ta ƙarisa wajensa ta rungume shi itama ta saka kukan mai tsuma zuciya.
Allah ne ya kawota a dai-dai wannan lokaci, domin ɗazu da Gwamna ya harbi kansa harsashi ne babu a cikin bindigar, lokaci guda ya ji gwiwarsa ta yi sanyi amma shaiɗan ya cigaba da tunzura shi sai ya ji wani ƙarfin gwiwa ya dawo masa nan da nan ya jawo akwatin bindigar ya ciro harsashi guda ya saka cikin bindigar.
"I love you Saifuddeen Sa'ad Kachallah" Asiya ta faɗa dai-dai kunnensa.
"Ni Azzalumi ne Asya"
" shhhhh. Kai mutumin kirki ne, kanada niyya mai kyau a jihar nan. Allah yana tare da kai idan ka nemi taimakonsa, ka yi nisa da shi My love, ka yi nisa da mahaliccinka shiya sa komai ya lalace a ƙarƙashinka.
"Kin guje ni Asya, kin ce ba za ki zauna da ni ki raɓi tsinuwar talakawa ba. Ki bar ni kawai na je na amshi laifina a wajen Allah"
"No my love, ba zan taɓa gudun ka ba, duk abinda na ke ina yi ne dan na taimakeka. I love you Excellency, ba zan taɓa rabuwa da kai ba. Daga yanzu i promised to be honest with you, respect you and always support you. Ba za ka je gaban Allah kana Azzalumi ba ka ji. We can fix this ka ji, akwai sauran shekara uku a gaban ka"
"Shekara biyu da wata tara Asya"
Asiya ta saka dariya tana bubbuga bayansa ta ce " yes Excellency, cikin shekara biyu da wata tara da suka rage zamu gyara komai. Da taimakon Allah za mu yi iya ƙoƙarinmu wajen ganin mun tafiyar da jihar nan bisa gaskiya da adalci"
Gwamna ya ɗago kanshi ya ƙurawa Asiya ido kaman a ranan ya fara kallonta.
"Asya kina nufin..."
"Yes Excellency, ni da kai za mu gyara jihar nan Insha Allah"
Gwamna ya sake jawota jikinsa yana jin wani sabon son ta na shiga jikinsa.
"Hasbiyallaahu Laa'ilaaha Illa Huwa Alaihi Tawakkaltu wa Huwa Rabbul Arshil Azim"
Asiya ta fara maimaitawa da ƙarfi a kunnensa.
Gwamna ya buɗe baki zai maimaita abinda ta ce amma bakinsa yai nauyi.
Asiya ta cigaba da maimaita addu'ar tana yi tana shafa kansa. Ganin ya kasa maimaita addu'ar sai yai shiru yana sauraronta chan kuma sai barci ya ɗauke shi.
Duk da yayi barci Asiya bata dena karanto addu'ar ba.
Banko ƙofar aka yi da ƙarfi wannan yasa hankalin Asiya ya koma kan ƙofar. Ba ta yi mamakin ganin matar da ke tsaye bakin ƙofar ba.
Idanunsu na haɗuwa Bilkisu Kachallah ta ji tsikar jikinta ya tashi. Ta yi saurin janye idonta ta maida shi kan bindigar da ke gefen ƙafar Asiya.
"Mi ya same shi?. Mi kika masa?" Bilkisu ta faɗa a kiɗime tana ƙarasowa wajensu da sauri.
Ta janye Gwamna daga jikin Asiya da ƙarfi sai ta ga ya faɗi yijif.
"What did you do to him?"
"Bacci ya ke"
Asiya ta bata amsa a taƙaice.
"Ki fita ki bamu waje" Bilkisu ta faɗa da muryar umurni.
"Ina ganin ke ce ya dace ki yi hakan"
"What!"
"Yes Bilkisu, ki bamu waje"
Mamakin ƙarfin gwiwar Asiya ta yi a wani ɓangare kuma tunanin yaushe zuwanta gari?, mi ta zo yi? da ma wasu tambayoyin su suka hanata magana.
Bayan fitan Bilkisu daga ɗakin kiran COS ta yi ta ce su haɗu a chan gidan gwamnati.
A falonta ya sameta ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana karkaɗa shi cike da bala'i.
"Boss"
"You are very stupid Lamara. Ni zaka raina wa hankali, dama Asiya tana Nigeria ka ce min ta fita ƙasar waje"
"Boss ban san ya aka yi..."
Bilkisu ta wurgeshi da kofin glass da ke kan centre table, kofin ya samu kafaɗarsa ya faɗi ƙasa ya tarwatse.
"When i give you assignment you execute it perfectly. Taya za ka bani report cewa Asiya ta tafi Stanford yin masters ɗinta bayan tana ƙasar nan. How dare you lie to me"
Idanunta suka kaɗa su ka juya zuwa idon maciji ta fara huci.
Nan da nan Lamara yai ƙasa da gwiwowinsa ya shiga bada haƙuri.
Bayan ta dawo hayyacinta sannan ta umurce shi daya zauna ya gaya mata gaskiyar inda Asiya ta je.
Tana jin sunan makarantar jikinta ya bata akwai abinda Asiya ke shirya mata amma koma minene tana dai-dai da ita.
Abu na farko da za ta yi shine ta sa a revoking sponsorship ɗinta sai ta ji da uban me za ta yi taƙama idan aka koreta.
Waya ta ɗauka ta kira M Sani dan yanzu ta ƙara jin a ranta cewa dole ta jawo shi jikinta fiye da da, idan har Lamara Damana zai ci amanarta to ɗan Rufaidah Kachallah ba zai ci amanarta ba domin abinda yai Rufaidah shi ya yita, shekara biyu da wata biyar ne tsakaninta da yayartata.
Bayan ta tabbatar da cewa M Sani zai tura saƙonta makarantar sannan ta samu nitsuwar shiga ɗaki dan ta kwanta gobe za ta je ta dawo da Gwamna wannan gida. Idan har saboda jifar sa da aka yi ya ke son kashe kan sa to ya sani ita Bilkisu Kachallah bata shirya zama bazawara ba sannan uwa uba bata shirya sauka daga matsayinta na MATAR GWAMNA ba.
***
Da dare zazzaɓi mai ƙarfi ya rufe Gwamna. Yadda jikinsa yai zafi ka ce idan ka fasa ƙwai ka zuba a ƙirjinsa zai soyu tas har ma ya ƙone. Asiya ta shiga banɗaki ta ɗauko bokiti ta saka ruwa sannan ta ɗauko ƙanƙara a chan falonsa ta zo ta jefa a ciki ta dinga tsoma towel a ciki tana matsewa tana shafe ilahirin jikinsa da shi. Lokacin da ta taɓa ƙafarsa saurin ɗauke hannunta ta yi dan tsananin zafi. Tana cikin shafa masa towel ta ji ya fara sunbatu cikin baccinsa.
"Ku yi haƙuri, ni ba Azzalumi bane. Ku yi haƙuri kada ku tsine min, ku yi haƙuri"
Hawaye ya sakko mata dai dai lokacin da ta dafe goshinsa tana karanto masa Ayatul Kursiyyu.
Gaskiya ta so kanta dayawa, tana sane da cewa akwai sihiri a jikinsa amma ta shure ƙafa ta wuce makaranta, ɗaukan fansa kawai ta saka a gaba ta manta cewa yana buƙatar taimakonta. Idan da ace duk watannin da ta ɗauka ta yi su ne cikin nema masa magani ƙila da ya samu waraka tuntuni, ƙila ma ba za a kai matsayin da su ke yanzu ba.
Ba abinda za ta ce sai dai Alhamdulillah kawai tunda Allah bai ba shi damar idda nufinsa na yin kisan kai ba.
Wani abu daya ƙara saka mata zubar hawaye shine tunanin bayan sihiri Gwamna yana fama da ciwon damuwa. He is depressed, akwai yiwuwar zai iya samun matsalar ƙwaƙwalwa duba da irin maganganun da yai ɗazu da kuma magagin bacci da ya ke yi.
Ta cigaba da shafe masa jiki da ruwan sanyi har zuwa Asuba lokacin da zazzaɓin ya sauka.
Da safe Gwamna ya buɗe ido ya kalleshi kwance kan gado gefensa Asiya da kuma likitan da ya ke ƙoƙarin ɗaura masa ruwa.
"Asya" ya kira da dasashshiyar murya.
"Excellency ya jiki?"
Shima Likitan na shi Dr Haruna ya tambayi lafiyarsa.
"Kai na ciwo Asya" ya faɗa yana binta da ido.
Hannunsa ta kamo ta kissing har sau biyu sannan ta ce " Insha Allah zai dena"
Bayan Likita ya gama saka ruwan Asiya ta biyo bayansa dan ta ji ƙarin bayani daga gare shi. Da Asuba Gwamna ya farka ta taimaka masa ya miƙe zai je banɗaki sai kawai ya riƙe kan sa ya yanki jiki ya faɗi ya suma wannan yasa hankalin Asiya ya tashi har ta kira likitan sa.
"Hajiya Asiya gaskiya Gwamna yana buƙatar hutu sosai, sannan ya kamata ya rage tunani, jininsa ya hau sosai kuma gaskiya hakan na barazana ga lafiyar sa. Idan ya cigaba da tafiya a haka zai iya faɗuwa ya shiga coma koma ya faɗi ya..."
"On whose authority kika kira Likita gidan nan?"
Muryan Bilkisu ya katse Dr Haruna
"Good Morning Mrs Kachallah"
"Dr Haruna bana tunanin yau ranan check up na Gwamna ne"
"Gwamna patient ɗina ne, inada damar zuwa duba shi idan ya buƙaci hakan"
Bilkisu ta kalli Asiya ta ce "Leave us"
Asiya ta yi murmushin yaƙe sannan ta koma ɗakin Gwamna, ba wai ta bi umurninta bane dama dai tana son komawa ɗaki dan ta ga Gwamna.
Lokacin da ta shiga ɗakin yana rigingine da filo ya ƙurawa bangon ɗakin ido kaman mai kallon TV.
"My love za ka iya yin sallar Asuba yanzu ko kuwa sai ruwan ya ƙare za ka yi"
"Zan yi yanzu, ban yi sallar Magariba da Isha ba jiya"
Asiya ta shiga banɗaki ta fito masa da buta da kuma empty bucket. Ta gyara masa zama dan ya samu yai alwala da kyau. Yana cikin yin alwalar Bilkisu ta shigo ɗakin. Ta zauna gefen Gwamna tana tattaɓa jikinsa tareda tambayarsa inda ke masa ciwo yanzu.
Asiya ta miƙe ta shumfiɗa sallaya ta ƙariso wajen Gwamna ta fara ƙoƙarin cire masa drip.
"Are you mad! Kina son kashe shi ne?" Bilkisu ta daka mata tsawa
"Ruwa na biyu kenan da aka sa masa, tunda ya samu ƙarfin jiki inaga sallah ya dace yai"
"You must be very stupid. Waye ya baki izinin zaɓa masa abinda ya dace da shi"
Asiya ta harzuƙa amma sai ta tuno karatunta nan da nan ta karya harshe ta ce "Mrs First Lady Gwamna da kansa ya buƙaci na cire masa ruwan zai yi sallah"
Bilkisu ta kalli Gwamna sannan ta kalli Asiya.
"Idan kina ganin ba shi da ƙarfi har yanzu, musulunci ya bashi damar yin sallah a zaune"
A zaunen yai sallah yayinda duka mata biyun suka bishi da ido kowa na kitsa abubuwa a ranta.
A ɓangaren Asiya tana tunanin fitar da Gwamna waje dan a duba lafiyarsa. Ita kuma Bilkisu tana kitsa yadda za ta takawa Asiya birki ta ke.
Wunin ranan Asiya tayi shi ne tareda Gwamna tana nuna masa kulawa da soyayya. Da yamma Bilkisu ta zo wai zata tafi da shi chan gidan Gwamnati. Asiya tace bata san zance ba, Likita yace Gwamna yana buƙatar hutu.
"Kar ki ga kin je National Institute ki nemi nuna min iko a gidana. Only Bilkisu rules here, kuma na ce ba zai zauna a nan ba"
Asiya ta yi murmushi ta ce " na san Likita ya miki bayanin halin da Gwamna yake ciki idan kina son lafiyarsa, the best thing shine ki bar shi a nan ya samu hutu"
"The Governor stays with me" daga haka ta juya ta tafi.
Washegari kuma Asiya ta bita chan gidan Gwamnati dan ta duba lafiyar Gwamna tareda yiwa Bilkisu maganar fita da shi ƙasar waje. Bilkisu ta ƙeƙasa ƙasa tace bata san zance ba infact cewa ta yi bata yarda Asiya ta sake takowa Government house ba ta tsaya a ɗaya gidan. Asiya za ta yi magana Bilkisu ta kira bodyguards ɗinta Vayentha da Mistika ta ce su raka Asiya waje.
"Kada ki taɓa bari maƙiyinki ya san fiskarki balle har ya gane manufar ki a kansa" maganar Madam Chess da ta tuna ya sa ta haƙura ta fice daga gidan ba tareda ta yi gardama ba...
13
"Kina ganin abinda kika shirya shine dai dai?"
"Tabbas kuwa ba zan bari ta tafi da Gwamna ba. She's planning something"
"Amma ba kya ganin Gwamna yana buƙatar ganin Likita"
"Zai ga Likita a nan Nigeria, za mu shigo da ƙwararren Likita idan akwai buƙatar hakan"
"Shikenan Boss, duk abinda kika ce ahi shi za a yi"
Bayan tafiyar M Sani, Bilkisu ta zauna tana juyayin abinda Asiya ta faɗa. Wato so ta ke ta tafi da shi ta nema masa magani. Babu wanda ya isa ya ɗauke mata Saifuddeen, ita kaɗai za ta juya shi, ita kaɗai.
Da wannan ta rufe batun a ranta.
***
A bangaren Asiya kuwa ta fara gabatar da duk wani shiri na tafiyar su, idan yaƙi ma za a yi to sai dai a yi amma dole ne ta je a duba lafiyar Gwamna. Ba asiri ne kawai ke cin sa ba har da damuwar ƙwaƙwalwa, yana buƙatar ganin ƙwararren Likita.
Ta fito kenan daga ɗaki ta samu saƙon Chief of Staff a wayarta.
Dan haka kafin ta fara zuwa chan Kachallah house sai ta wuce inda ya ce su haɗu.
Tana zuwa gidan aka wangale mata gate ta shiga. Bayan ta fito daga motarta wani bodyguard ya mata jagora zuwa inda Lamara Damana ke zaune a wajen gazebo yana hutawa.
"Your excellency" ya faɗa fiskarsa ɗauke da murmushi yana miƙewa tareda nuna mata wajen zama.
Asiya ta zauna ta kalmashe ƙafarta ta haɗe rai ta ce " a wani dalilin kake son mu haɗu?"
"Haba Excellency ko ruwa kya sha ai"
"Ban zo nan dan na sha ruwa ba, ka faɗi maganar ka bana son ɓoye-ɓoye"
COS ya kurɓi giya kaɗan sannan ya ce
"Idan kina son ganin bayan Bilkisu Kachallah za ki buƙaci taimakona"
Asiya ta fashe da dariya mai kama da ta renin hankali.
"Waya gaya maka ina son ganin bayan Bilkisu Kachallah? Gaskiya ka chanja tunani"
"Hajiya Asiya ke kan ki kin san na san mi ya kai ki Kuru"
Ya ɗan yi shiru yana nazarinta sannan ya cigaba "REVENGE, kin tafi chan ne saboda kina son ɗaukan fansa. Wannan ne dalilin da ya sa ban faɗawa Bilkisu ainihin inda kika je ba don na san daga airport na Congo jirgin Jos kika shiga ba ta zuwa Abuja ba balle ki shiga ta tafiya New York"
"You are getting it wrong Mr Lamara, Revenge sai ka ce a film. Abinda ya kaini Kuru shine KARATU"
Ya gane sarai ta fahimce shi, rainin hankali ne kawai da dabara kuma indai wannan za ta nuna masa to shi ya taka ta a irin hakan
"Ina da evidence da za ki yi amfani da shi wajen tura Bilkisu Kachallah kurkuku cikin sauƙi"
Asiya ta juya maganar da cewa " na ɗauka za ka taimaka min ne wajen samun lafiyar Gwamna amma tunda wani tatsuniya kake faɗa gara na tafi dan ina da abinyi"
"Kina so ki ce kin damu da samun lafiyar Gwamna amma ba ki damu da ganin ƙarshen Bilkisu Kachallah ba?"
Asiya ta saka baƙin glass a idonta sannan ta ce " ba abinda zan yi da ƙarshen Bilkisu Kachallah. Abu ɗaya ke dictionary ɗina, samun lafiyar mijina"
Bayan tafiyar Asiya Chief of Staff Lamara Damana ya ɗau champagne cup ya kwankwaɗi sauran giyan da ke cikinsa sannan ya fito da tabar sigari mai kauri irin wanda manyan mutane ke sha ya sa a baki sannan ya saka mata wuta ya shaƙi hayaƙinta ya furzar ta gefen baki. A fili ya furta "so you are playing hard to get huh"
***
A chan Kachallah house kuwa Asiya da Halimah Kachallah ne suka baza koli a ɗakin Haliman. Kayayyaki ne A barbaje akan gado Halima na nunawa Asiya.
"In-law cikin peach gown da pink ɗin nan wanne zai tafi da kalar fatata?"
"Anty Halimah duk biyu babu wanda ba zai je ba"
"Kai In-law ba dan ki tayani zaɓe na kira ki ba. Tun ɗazu sai rawar ido na ke kin ƙi ki sa min baki. Anty Asiya kefa fashion diva ce "
"Kiyi haƙuri Anty Halimah. Gaba ɗaya raina ne a dagule. Bilkisu tana son hana ni fita da Gwamna"
"Ba dole ta hana ba, tana tunanin honeymoon za ku je"
"Kai! Anty Halimah"
Halima ta sa dariya. Itama Asiyar ta yi ƙoƙarin danne damuwarta ta shiga yin dariyar.
Duk da tata matsalar da take ciki hakan bai hanata jin tausayin Halimah Kachallah ba. Finally ta kusa shiga gidan miji. Tunda Asiya ta saita tsakaninsu da Yaya Bello lokacin da aka sakota daga kurkuku Halimah ta saka buri a ranta cewa kafin ta clocking thirty six zata shiga gidan miji to yanzu saura wata huɗu kuma an saka auren na su zuwa wata biyu masu zuwa. Duk bidirin da ake yi Bilkisu bata da sani a kai domin tunda Halimah ta yiwa Alhaji
Sani maganar saurayinta zai turo ya haɗata da Kawunsa akan ta tura su wajensa dan bashi da lokaci. Ta ji zafin abinda ya mata amma ta share dan farin cikinta ya mamaye duk wani kayan haushi da za a yi a gidan, balle ta riga ta kwana da sanin Mahaifinsu ya koma sai abinda mai girma Bilkisu ta faɗa...
Kwana biyu ya rage su tafi Gwamna ya kira Asiya yace mata ta dakatar da duk wani shiri da take don babu inda zai je ya riga ya samu lafiya. Maganarsa ya matuƙar kaɗata dan a iya maganar da su ka yi da shi ba shi da matsala da tafiyar da take shirya musu.
Ta ji a ranta ta je ta samu Bilkisu ta nuna mata ta san mi yake faruwa amma sai wata zuciyar ta gargaɗeta akan hakan domin akwai sauran rina a kaba, sai kawai ta fara tsara yadda za a sato mata Gwamna ranan da za su yi tafiyar.
Ana gobe ne tafiyar da Asiya ta shirya Gwamna da First Lady suka karɓi baƙuncin party chairman wanda ya zo ne takanas saboda abinda ya faru kwanan baya. Jam'iyyarsu tana fushi da ayyukan Gwamna a jihar, kuma sun yi Allah wadarai da abinda ya faru da shi a ƙaramar hukumar Boyo.
Da ke zuwan na bazata ne a tsanake Bilkisu ta shiga ƙoƙarin shiryawa party Chairman liyafar girmamawa.
A wajen liyafar Chairman Alhaji Ado Lawali ya taɓo batun abinda ya faru a Boyo tareda kawo suggestion na yadda za a yi maganin abin musamman saboda an fara zagin jam'iyyarsu gaba ɗaya har matasa suna iƙirarin zaɓe na gaba ba za su dangwalawa duk wani ɗan takara daya fito daga jam'iyyar ba.
Maganar Boyo ya saka Gwamna cikin damuwa, ƙwaƙwalwarsa ta ɗau chaji tana tuno masa duk abinda ya faru a wannan rana. Yana tsaye a wajen suka ga ya dafe kansa yana ƙoƙarin jan numfashi da ƙyar kafin chairman ya ankara Gwamna ya sake jiki ya faɗi ƙasa. Hankalin Bilkisu yai ƙololuwar tashi ta yi kansa da gudu tana kiran sunansa a birkice. Ƙoƙarin neman inhaler ta ke a jikinsa ta rasa lokacin da ta samu kuwa ta kama matsawa da ƙarfi amma inaaa tuni Gwamna ya suma.
"Saifuddeen ka tashi kar ka mutu. Ka tashi please. Look at me, ka tashi, ka tashi na ce"
Da ƙyar aka janyeta daga jikinsa aka fice da shi ruwa ruwa daga ɗakin taro.
Kafin kace me gaba ɗaya gari ya ɗauka cewa Gwamna Saifuddeen yana asibiti rai a hannun Allah. Wasu na yi masa addu'a, wasu na Allah shi ƙara, wasu sun yi shiru suna tunanin mi zai faru idan Gwamna ya mutu.
Asiya na gida tana zoom call da 'yan study group ɗinta na chan Kuru wannan mummunan labari ya risketa. A gaggauce ta shirya ta nufi Asibiti. Bilkisu Kachallah kawai aka bawa damar ganinsa tun fitowar likitoci daga ɗakin da aka kwantar da shi. Asiya na zuwa securities da su ke tsaron ƙofar su ka bata damar shiga duk da kuwa Bilkisu ta bada umurnin kada su bari wani ya shigo ɗakin.
Asiya ta bishi da ido tun daga tafin ƙafarsa da ke lulluɓe har zuwa goshinsa.
Bilkisu na durƙushe da gwiwowinta ƙasa ta riƙe hannunsa ganin an saka masa oxygen dan taimaka masa wajen numfashi ya ƙara birkitata. Ba abinda ya ke zuwa mata irin ace yanzu mi zai faru idan Saifuddeen ya mutu.
Lokacin da ta tuno da yadda aka yi ya hau kan mulki sai ta firgita sosai. Ba dai za a samu maimaita tarihi ba ne a jihar. Gwamna ya mutu mataimakinsa ya hau kan kujera.
"Nooo" ta furta da ƙarfi ba tareda ta lura da Asiya da ta shigo ɗakin ba.
A ɓangaren Asiya kuwa wani tunani ne ya faɗo mata wanda ya sata zubda ƙwalla. Saboda wannan mata ta rabu da mijinta tsawon watanni, yanzu idan ya rasu babu abu ɗaya na shi da ta ke da shi sai dai ta rayu da tarin dana sani. Ko kyakykyawan zama irin ta ma'aurata ba su taɓa yi ba. Idan Bilkisu ta kashe shi ba ta da asara tunda ga 'ya'ya har uku ta haifa masa zata kallesu ta ji daɗi.
"Zan fita da shi gobe" Asiya ta faɗa bayan ta share hawayen da ke fiskarta.
Bilkisu ta juyo ta kalleta amma bata yi magana ba sai kawai ta juyar da kanta ta cigaba da kallon Gwamna da ke kwance.
Sai yamma lis Gwamna ya farfaɗo. Ikon Allah ne kawai ya kiyaye shi bai samu shanyewar ɓarin jiki ba faɗuwar da yai. Likitocin kansu sun yi mamakin farfaɗowansa ba tareda wata babbar matsala ba sai ciwon kai da ciwon ƙirji da ke damunsa.
Bilkisu ta saƙa, ta raya, ta auna komai. Mafita ɗaya ce kawai shine ta bari Asiya ta fitar da Gwamna waje jinya. Abu ɗaya ta sa a ranta shine Asibiti za a kai shi dan duba lafiyar jikinsa ba wai dan ya samu waraka daga ɗaurin da ta masa ba shiyasa ma ta yiwa ɗaya daga cikin bodyguard ɗinta magana akan ta raka Asiya ta tabbatar komai ya tafi dai-dai. Ba dan tana cikin tsaka da wasu ayyuka ba da ita da kanta za ta raka Gwamna. Amma idan ayyukanta su ka yi sauƙi za ta je ta duba shi.
Washegari da safe ƙarfe bakwai ta wuce kaɗan ta yi musu a airport ne, har da Bilkisu aka zo tareda yaransa biyu. Sai a lokacin ne ma Asiya ta ga Junior, yaron kaman ba ɗan shekara bakwai ba gaba ɗaya ya ƙyamushe bashi da walwalar da ta san shi da shi da, yadda ya ke yi ma tamkar bai taɓa sanin Asiya ba a rayuwarsa wannan ya ba Asiya mamaki sosai.
A wheelchair aka tura Gwamna har cikin jirgi saboda ba shi da ƙarfin jiki, tunda ya farfaɗo ɗinma baya magana sai dai ya girgiza kai kawai ko ya zubawa mutum ido.
Asiya tana riƙe da hannun Gwamna jirginsu ya lula sararin samaniya. Fiye da rabin tafiyar su ma Gwamna yayi shi cikin bacci ne.
Tun da Bilkisu ta gaya mata za su tafi tare ne da Mistika sai kawai ta kira Colonel Modi ta roƙe shi alfarma.
Suna sauka a filin jirgin NewYork aka kama Mistika aka tafi da ita bincike sai sunbatu ta ke tana faɗin tare ta ke da tawagar Governor Kachallah amma babu wanda ya saurareta. Tun shirinsu na farko dama mutum huɗu Asiya ta booking mu su, ƙaninta Ɗayyibu da ya samu scholarship karatu a ƙasar Morocco shekaran da ta wuce sai kuma Al'amin ɗan Fatima Kachallah babbar 'yar Alhaji Sani Kachallah...
Bilkisu na zaune a office M Sani ya shigo cikin wata Shaddah blue mai yauƙi. Tunda Bilkisu ta sa aka bashi Commisioner of Youths and Sports yake tsula tsiyarsa a jihar Congo. Dududu shekarunsa ashirin da bakwai ne amma kuma abinda ya ke idan mutum ya ji sai ya tsorata da duniya.
"Boss ya naga kin yanƙwane ne. Ko tun yanzu kin fara kewar Gwamna ne?"
"Muhammad ba za ka gane ba, idan Saifuddeen ya mutu asirina zai tonu a jihar nan"
M Sani ya bushe da dariya yace " shine kike son bawa kan ki hawan jini"
Bilkisu ta jefe shi da mugun kallo
"Think of it this way, idan Uncle ya mutu wa kike ganin zai zama Gwamna a jihar nan?"
Bilkisu ta zaro ido waje.
M Sani yai murmushi sannan yace "idan ya mutu you can easily become the governor of the state"
Ganin bata fahimci maganarsa ba ya sa shi faɗin " idan Aka rantsar da mataimakin Gwamna akan kujera kina ganin wa zai ɗauko a matsayin deputy ɗin sa?. Ba kya ganin kina zama mataimakiyar Gwamna za ki iya hallaka shi ki haye kujerar ko kuma ki sa yai resign na dole. Ya kike gani idan aka kira ki da GOVERNOR BILKISU SANI KACHALLAH?"
Wani murmushi ne ya suɓucewa Bilkisu dan har ta hasko kanta zaune a ofishin Gwamna zaune akan kujerar da ke da daraja ta farko a gaba ɗaya jihar wato first citizen of the state.
"You can make things easy tun yanzu, za ki iya sawa Mistika ta kashe shi a chan kinga waccar yarinyar dole ta dawo ta yi takaba"
"Muhammad Sani!" Bilkisu ta faɗa tana miƙewa tsaye, idonta ya fara rikiɗewa yana komawa na maciji wanda hakan ke faruwa a duk lokacin da ta ke cikin tsananin ɓacin rai.
M Sani ya sha jinin jikinsa dan har sai da ya saki fitsari kaɗan.
Ta fi minti biyu kafin ta iya dawowa dai-dai.
"Zan iya yin komai akan mulki amma banda taɓa lafiyar mijina da 'ya'yana. Idan lokacin Saifuddeen ya cika i will mourn him amma ba zan taɓa kashe shi ba, duk wanda ya taɓa lafiyarsa ma sai na ga ƙarshen sa a doron ƙasa"
"Tuba na ke Boss. Ki gafarta min" M Sani ya faɗa a tsorace.
"Leave!" Bilkisu ta faɗa da kakkausar murya.
14
Sati guda Gwamna yai a Asibiti ya fara samun sauƙi, kullum Asiya tana cikin tofe shi da addu'o'i bayan magungunan da ya ke sha. Tabbas hasashenta yayi gaskiya dan kuwa Gwamna yana fama da depression, jifan da aka mishi ya taɓa shi sosai. Duk lokacin da aka masa maganar abin sai hankalinsa ya tashi.
Therapist ɗinsa musulmi ne mai suna Dr Ayyub Khan dan haka bayan taimako na fannin kimiyya yana bashi shawarwari da kuma amfani da magungunan musulunci, dan tun zuwansu ya tuntuɓi wani abokinsa mutumin Egypt wanda ke da sani akan Ɗibbun Nabawiy (medicine of the prophet) su ke aiki tare wajen ganin Saifuddeen Kachallah ya samu lafiya.
A hankali Gwamna ya fara dawo da walwalarsa har ta kai yana ɗan magana har ya sa baki idan Asiya da su Al'amin suna hira. Sakewa da ya ke ya ƙara saurin samun sauƙinsa.
Satin su huɗu cur a ƙasar Gwamna har ƙiba ya ɗan yi saboda yana samun bacci da kwanciyar hankali yadda ya dace.
Wasu lokaci Asiya ta kan shirya mu su fita strolling da yamma ko kuma da sassafe.
Yau ma fitar su ka yi da dare bayan sun yi sallar Isha, kasancewa ana yanayi na sanyi dukkan su sun yiwa jikinsu tanadin sanyi. Gwamna na sanye da wandon jeans baƙi, black turtle neck shirt da kuma navy blue jacket, hannayensa sanye da baƙin safa. Itama Asiya irin shigar ta sa ta yi banbancin nata jacket ɗin dogo ne sannan ita ta ɗaura brown scarf a wuyanta kanta kuma sanye da baƙar turban. Hannunsu sarƙe cikin na juna su ke tafiya, labarin zuwanta Saudiyya ta ke bashi wannan yasa ya maida hankalinsa kan ta sosai bai ma lura da ya hau hanya ba sai da ya ji ihunta ta jawoshi da ƙarfi.
"Ya Allah!" Ta faɗa tana dafe ƙirjinsa. Shi kuma mai motar da ya kusa buge Saifuddeen bai tsaya ba sai ma ihunsa da suka ji yana faɗin "fuck off man"
Asiya ta bishi da daƙuwa tana faɗin "Ashole"
Kafin ta juyo Gwamna ya jawota jikinsa ya rungumeta tsam a ƙirjinsa. Turawa babu ruwansu dan haka kowa harkan gabansa ya ke babu wanda ya kula da su.
"Excellency abakin titi fa mu ke" ta faɗa da wata ƙaramar murya wanda rabon da ta masa irin wannan har ta manta. Bai saketa ba sai da suka yi kusan minti biyar a gefen titi rungume da juna and all that matters a lokacin shine zuciyoyinsu na bugawa ne da soyayyar junansu.
Lokacin da suka koma hotel suite ɗinsu kusan dare ya raba, su kan mazan tuni sun yi bacci, ba kamar Ɗayyibu ma wanda sanyin garin ke damunsa baya ma wani fita sosai.
Ba su fi minti biyar da kwanciya ba ta ji hannunsa a cikinta. Shafa mata ciki ya fara a hankali hakan ya sa tsikar jikinta ya fara tashi. Ya matso da ita jikinsa yana shafa cikinta zuwa chan ƙasan maranta. A hankali kuma ya sa bakinsa a wuyanta yana kissing ɗinta a hankali chan kuma ya juyo da fiskarta ya haɗe bakinsu. Ta yi kewarsa sosai shiyasa jikinta ya shiga mazari lokacin da ya fara yawo da hannayensa a saman ƙirjinta. Kafin ta ankara ya rabata da wandon pyjamas ɗinta ya fara wasa da cinyoyinta.
Ganin wasan na su ya fara wuce gona da iri yasa ta fara ƙoƙarin janye jikinta amma yai mata kane-kane bai bata dama ba. A hankali ya fara shigarta wannan ya sa Asiya ta furta addu'ar saduwa a fili "Bismillah, Allahumma Jannibnash-shayɗaana, wa jannibish shayɗaana ma razaqtanaa"
Shima sai ya faɗi "Bismillah" a fili sannan ya tura ciki da ɗan ƙarfi wannan yasa Asiya ta ƙanƙameshi tana cize leɓe...
A dai-dai wannan gaɓa zoben hannun Bilkisu ya kawo wani jan haske kamar wuta sai kuma ya disashe hasken ya ɓace ɓat. Da ke bacci ta ke bata ga abinda zoben yai ba.
Lokacin da Asiya ta zare jikinta ta tashi Gwamna yana kwance yana bacci mai daɗi.
Ji take kamar an zuba mata yaji a gaba saboda zafi amma haka ta daure ta ƙarisa cikin banɗaki, sai da ta dafe bango ta ɗan huta kafin ta samu ƙarfin haɗa ruwan zafi ta shiga ciki. Bata kawo wannan abu zai faru da wurwuri haka ba, ta sa a ranta sai ya warke sarai ƙila ma sai sun komai Nigeria. Sai dai Alhamdulillah yanzu kam ta zama cikakkiyar matar aure. Bayan ta yi wanka ta ɗauro alwala ta fito. Tana tunanin za ta iya ko sallah raka'ah biyu ne amma sai ta ji ta kasa saboda zogi da ta ke ji a gabanta duk da yanzu da ɗan sauƙi. Da ƙyar ta iya daddafawa ta kai jakar kayan kwalliyar ta ta ɗauko da robar zuma da ta taho da shi wanda take haɗawa da mayukanta tana shafawa sannan kuma tana sha ita da Gwamna duk safiya.
Ta tsiyayi zumar a hannunta ta shafe gabanta da shi. Bayan ta gama ta rufe goran zumar ko iya maida shi inda ta ɗauko bata yi ba ta koma gado ta kwanta ta ƙudundunu cikin bargo.
Washegari da safe Gwamna ne ya fara tashi sannan ya tasheta. Tana haɗa ido da shi ta ji wani kunyarsa ya rufeta ta yi saurin rufe idonta da tafukan hannunta.
"Alhamdulillah! Yanzu kam gangan jikin da ruhin duk mallakin Saifuddeen Sa'ad Kachallah ne ko?"
Asiya ta juyar da kai gefe tana murmushi. Lokacin da ta tashi daga gadon ta ji sauƙin zogin da take ji ba kamar jiya da dare ba. Da ke ta yi wanka jiya alwala kawai ta ɗauro ta fito ta tada sallar Asuba lokacin Gwamna ya idar da tasa sallar.
Kwanakin da suka biyo baya sun kasance ranakun farinciki a tarihin rayuwar Asiya domin kullum cikin samun kulawa da soyayyar Gwamna Saifuddeen ta ke ciki. Abun daya ƙara faranta mata rai shine yadda yanzu Gwamna ya dage da sallar nafila da kuma azkar ba kaman farkon zuwansu garin ba. Ganin ya samu lafiya kawai Gwamna ya sallami Al'amin da Ɗayyibu akan su wuce Nigeria su zasu iso daga baya. Samarin biyu sun gane manufar Gwamna don haka ko da Asiya ta nemi dalilin tafiyar ta su kowa ya kawo dalilinsa na ƙarya. Ranan litinin Gwamna da Asiya suka raka su airport suna dawowa kuwa Gwamna ya buɗe babin honeymoon ɗinsa dan kuwa Asiya ta yi jinyar jikinta na kwana biyu. Sati ɗaya suka yi suna honeymoon Asiya ta tada zancen komawarsu Nigeria, na farko saboda research project ɗinta da take son submitting na biyu kuma saboda bikin Halimah Kachallah da Yaya Bello.
Gwamna bai musa ba amma yace su fara zuwa su gabatar da godiya a ɗakin Allah sannan su kai gaisuwa kabarin fiyayyen halitta.
Ranan da suka dira a garin Madina ranan Yallaɓai ya rasu a chan ƙasar Germany inda yake jinya. Dai dai lokacin kuma zoben hannun Bilkisu yai wani haske sai kuma zoben ya ɓace ɓat.
Faɗa ta ke yiwa M Sani akan ya kasa sawa a withdrawing Asiya daga National institute. Masifa take masa amma babu laifinsa aciki saboda duk inda ya je da sunanta ya ke zuwa kuma an ƙi karɓan duk ƙorafin da ta kawo. Infact Asiya na ɗaya daga cikin ɗalibai masu tsananin ƙwazo a gaba ɗaya tarihin kafa makarantar dan haka ba za su koreta tana daf da ƙarɓan certificate ɗinta ba.
Ɓacewar zoben Bilkisu ya sa ta danna wani ƙara. Jikinta ɓari yake lokacin da ta ɗau waya ta fara neman numbar Malaminta.
"Boss lafiya?" M Sani ya tambaya a firgice
"Get out!" Ta daka masa tsawa
"Alkadarin jiki ya karye har sau biyu dan haka mai yiwa zoben hidima ya gudu kar a hallakashi gaba ɗaya"
Abinda Shri ya faɗa mata kenan lokacin da ta kawo masa ƙorafinta. Mi zai sa alkadarin ya karye bayan mutum uku da aka haɗa zoben dan su suna raye?
Tana gama waya da Shri Chief of Staff ya kirata ta sanar da ita mutuwar Yallaɓai. Mutuwar zaune ta yi akan kujerarta tana tunanin mafita idan har aikin da aka yiwa Saifuddeen ya warware.
***
A chan Kachallah House kuwa Halimah da mahaifiyarta da kuma Hajiya Ummah sun duƙufa wajen shirye-shiryen biki tunda yanzu sauran kwanaki goma sha uku a ɗaura auren. A da Mommyn su ta ƙi haɗin kasancewa duk 'ya'yanta sun yi aure ne a babban gida ita kuma Halimah wanda za ta aura ba ɗan kowa bane sannan ba abinda yake da shi, abin takaicin ma wai dreban taxi ne kuma tsohon ɗan shaye-shaye. Babu yadda ta iya tunda babu wani da ya zo neman Halimar kuma gashi ta doshi shekaru arba'in.
Tun lokacin da Yaya Bello ya amince zai auri Halimah yai wa kansa karatun ta nitsu ya ce zai fara sana'a tunda Asiya tace zai daina tuƙata dan itama zata koyi tuƙi. Shi ya zaɓi aikin taxi dan ya fi gane harkan mota fiye da kasuwanci.
Allah Sarki Alhaji Sani sai da Baffansa ya sake masa maganar cire hannunsa da yai a hidimar bikin Halimah bai kyauta ba sannan hankalinsa ya karkato kan autar sa. Ya rasa gane dalilin hukuncin da ya zartar, lokacin da matarsa ta faɗa masa shi da kansa ya ce Halimah ta nemi wani waliyyin da zai mata jagora ba shi ba, abin ya girgiza shi matuƙa domin ya sha buri sosai akan bikinta.
A hankali kuma ya fara tuno wasu abubuwan da ya aikata a lokacin daya ke ƙarƙashin ɗaurin 'yarsa Bilkisu.
Bilkisu ta shiga ruɗu sosai har wani rashin lafiya ne ya sameta ta dinga jin jikinta na ɓari tana jin sanyi sosai na shigarta.
Da dare da ta samu nitsuwa ta wuce chan gidansu dan ta tabbatar ko akwai sauran hope ta wajen mahaifinta sai dai kash aikin gama ya gama. Lokacin da ta je ma ƙaramin meeting ake yi kan yadda bikin Halimah zai kasance.
Lokacin da ta shigo falon Babansu duk cikin 'yanuwanta babu wanda ya kulata. Saudah kan ma tsaki ta ja yayinda Rufaidah ta bita da harara.
Wannan chanjin fuska da ta gani kaɗai ya sanyaya mata jiki. Ta dai zauna dan ta saurari abinda ake tattaunawa. Wai abin mamaki har za a haɗa meeting a gida bata da labari.
"To yanzu dai Anty Batulah za ta haɗa kuɗin gudummawa sai kowa ya buɗe aljihunsa ayiwa Auta kara"
Saudah ta yi magana tana hararan Bilkisu.
Cikin rashin fahimta Bilkisu tace " Halimah ce za ta yi aure?"
"Eh Allah yayi, Allah gatan bawa"
Saudah ta amsa tana gyatsina fuska.
Bilkisu ta shanye ɓacin ran da ya taso mata tace " wa za ta aura?"
Kaman jira dama Saudah take ta tambaya sai ta amsa da cewa " za ta zama Amaryar Muhammad Bello Faruƙ Baba"
Kusan sakan biyar Bilkisu ta ɗauka tana processing sunan kafin ta gano alaƙar sunan da matar da ta fi tsana a duniya.
"Baba kana zaune ana maganar haɗa maka zuri'a da useless family"
Alhaji Sani yai murmushi mai ciwo yace
"Kina baƙin ciki da zaɓinta ne?"
Bilkisu ta buɗe baki ta rufe ta rasa abun faɗa...
*THE RETURN*
15
Murna da farin ciki ne ya shiga zuciyoyin jama'a lokacin da suka ji cewa Gwamna yana tafe ranan jummu'a. Yawanci jama'a sun yi ittifaƙi ne akan cewa jinya ce ta saka Gwamna Saifuddeen ya ke yin halin ko in kula da talakawansa.
Lokacin da Asiya ta sake selfie ɗinta da Gwamna a shafinta na twitter ta kuma yi gajeren rubutu a ƙasan hoton kan kace kwabo hoton ya zaga ko'ina a cikin jahar, kowa na faɗin albarkacin bakinsa kan cewa akwai ƙanshin alkhairi a dawowar Gwamna. Sai dai duk da haka an samu wasu da suke ganin wannnan dawowar ne ma zai zamo mafi muni a tafiyar mulkin Gwamna SSK, sun yi amanna da cewa Gwamna ba jinya ya tafi ba, honeymoon ce irin ta turawa dan gashi yayi ɓulɓul ya ciko kamar ba shi da damuwar talakawa a ransa.
***
Hajiya Bilkisu Kachallah ta cigaba da kai kawo a ƙaton ɗakin cin abinci na manyan baƙi da ke cikin gidan Gwamnati, yadda ta ke tafiyar da komai zaka ce babu wani abu da ke damunta. Liyafa ce ta ke shiryawa saboda zuwan Gwamna, 'yanuwa mafi kusa kaɗai ta gayyata zuwa wannan liyafa.
Tana tsaye jikin kujera tana nunawa wani staff inda zai ajiye wani dessert da ta san Gwamna yana mugun so kunnenta ya jiyo abinda wani reporter ya faɗa. A fusace ta juya ta kalli TVn da ke manne da bango idonta yai tozali da hoton da ɗan jarida yake magana a kai. Hoton selfie ne na Asiya da Gwamna a cikin jirgi, "THE RETURN" Bilkisu ta karanta rubutun da ke ƙasan hoton.
"Excellency Ma, your Excellency Ma"
Bilkisu ta yi firgigit ta juyo ta kalli staff ɗin da ke mata magana. Lokaci guda wasu abubuwa suka fara dawo mata ta yi saurin girgiza kai tare da barin dinning hall ɗin.
Kafin ƙarfe uku na rana an kammala komai na shirye-shiryen liyafa har wasu ma daga cikin wanda aka gayyata sun fara isowa.
Tun ƙarfe uku saura mutane suka cika bakin airport ɗin riƙe da poster-poster na Gwamna da Amaryarsa Asiya.
Gidajen talabijin da na radio suma sun aiko wakilan su dan live ake so a kawo rahoton wa mutane.
Ƙarfe uku da minti biyar jirginsu Gwamna ya iso.
Gwamna da Asiya suka sauko daga cikin jirgi hannunsu sarƙe cikin na juna sai murmushi suke da ka gansu kasan akwai farinciki da soyayya mai ƙarfi dunƙule a zuciyar su. Haka suka dinga ɗagawa mutane hannu suna murmushi yayinda ake ta watsa musu ruwan hotuna.
A cikin mota Asiya ta lura hannun Gwamna yana ɓari hakan yasa ta ɗaura ɗaya hannunta akan nasa tace "ka kwantar da hankalinka Excellency, talakawa na tare da kai har yanzu, kuma da yardar Allah za ka sauke musu hakkinsu"
Ta ranƙwafo dai dai kumatunsa ta manna masa kiss tace "ina tare da kai Mijina"
Gwamna ya gyaɗa mata kai yana murmushi.
Lokacin da suka iso gidan Gwamnati tarba na musamman uwargida Bilkisu Kachallah ta musu sannan kuma ta musu jagora har zuwa wajen taron liyafa.
Gwamna ya ji daɗin ganin 'yan uwansa da suka zo dan rabon da ya ga wasun su ma tun kafin rashin lafiyar sa.
Haka aka zauna ana cin abinci ana raha ana dariya, duk wani abu dake ran Bilkisu shanye shi tayi ta dinga fara'a tana nuna cewa tafi kowa murna da dawowar Gwamna.
Bayan an gama cin abinci Asiya ta wuce ɗakinta dan ta watsa ruwa ta chanja kaya amma me, ɗakinta na nan yadda ta tafi ta barshi babu gyara babu komai duk yayi ƙura. Ta san aikin Bilkisu ne dan haka maimakon ta fara tada zance cikin baƙi sai kawai ta hau gyaran ɗakin da kanta, da alamu dai har yanzu Bilkisu na tunanin zata bar mata gidan ne kamar da.
Sai kusan bayan Isha kafin gaba ɗaya baƙin suka gama tafiya idan ka cire Alhaji Sani Kachallah dake ganawa da Gwamna kan tattaunawa ta musamman.
Wajen ƙarfe goma da rabi Gwamna ya shigo ɗakin Asiya, a tunaninsa zai samu tayi bacci amma idonta biyu sai faman duba takardu take.
"Baby kina buƙatar hutu fa" yai maganar yana kissing goshinta.
Asiya tayi murmushin yaƙe tace " na ma gama, yanzu zan kwanta"
Ya ɗan ja kumatunta yace " sleep well kin ji"
Ji ta yi kamar ta kwaɗe shi saboda tsananin kishi amma ta danne ta ce "Insha Allah"
Yana fita daga ɗakin kiran Halima ya shigo wayarta, sun jima suna waya kafin ta tattara komai ta ɗauro alwala ta zo ta kwanta.
Bayan fitar Gwamna daga ɗakin Asiya ɗakin yaransa ya wuce ya duba lafiyar su kafin ya wuce ɗakin Bilkisu.
Tana nan tsaye gaban madubi tana shafa mai daga ita sai bathrobe fari a jikinta.
"Sannu da ƙoƙari Uwargida. Nagode da liyafar da kika shirya min"
"Uwargidaaa?" Bilkisu ta faɗa tana jan ƙarshen.
"Lallai" ta cigaba " ko kusa ban sa a raina zaka zama butulu ba, amma mu je zuwa, da kai da itan duk zaku kwashi kashinku a hannu"
"I come in peace Bilkisu" Gwamna ya faɗa a sanyaye daga haka bai jira mi za ta ce ba yai waje. Bai tsammanci zata biyo shi ɗakinsa ba dan haka yana gama duba wasu saƙonni a wayarsa ya shirya ya kwanta, ba a jima ba bacci ɓarawo ya sace shi.
***
*Office Of the Governor*
Monday 8:30am.
Tun shigowar Gwamna ilahirin staffs da ke aiki ƙarƙashin ofishin Gwamna su ke takatsantsan da abinda zai je ya dawo. Yau ne officially Gwamna Saifuddeeqn ya resuming aiki, kuma akwai labarai da ke ta yawo kan dawowar Gwamna fa zai haifar da ɗa mai ido.
Meeting na farko da Gwamna yai tareda mataimakinsa ne bayan nan kuma aka yi board meeting daga nan kuma ya haɗa meeting da Chief of Staff da kuma Commisioner of finance.
COS yana jin buƙatun Gwamna ya san cewa akwai matsala a ƙasa kuma yanzu ne mafari.
Mr Paul ya dubi COS sannan ya dubi Gwamna yace " Your excellency ba zai yiwu a biya albashin wata uku lokaci guda ba"
"Ba shawara na ke nema ba Mr Commisioner"
"Sorry your Excellency, i'm just saying..."
Gwamna ya dakatar da shi ta hanyar ɗaukan wayar office ya kira Sakatarensa.
"Ka kawo min takardar korar Commisioner of Finance"
Yana ajiye wayar Mr Paul ya shiga bashi haƙuri amma Gwamna ko gizau bai yi ba. Minti uku sai ga Sakatare ya shigo ya miƙawa Gwamna takardar kora.
Mr Paul ya dubi COS ya roƙe shi akan ya sa baki kan wannan lamari. Sai da Gwamna ya ɗaga seal zai liƙa a jikin takardar bayan yayi signing sannan COS ya ce " your excellency ina ga a bawa Finance Commisioner dama na biyu ya gyara kura-kurensa. Yau za a biya albashin wata biyu kafin ranan talatin ga wata za a biya na uku"
Gwamna ya ɗaga ido ya kalli COS sannan ya kalli Mr Paul yace " idan ka saɓa bisa yadda Mr Lamara yace ranan talatin ga wata za a naɗa sabon chief of staff"
Mr Lamara ya cize leɓensa na ƙasa. Wato Gwamna ya ɗaure su ne duka biyu saboda duk yadda za ayi sai sun yi yadda yake so.
suna barin office ɗin Gwamna Mr Paul ya fara masifa nan COS ya dakatar da shi yace yai yadda Gwamna yace. Daga nan ya ƙarisa office ɗinsa dan ya kira Bilkisu Kachallah.
Kafin ƙarfe shabiyun rana ma'aikata suka fara samun alert na albashin wata biyu, ya zamana saura bashin albashin wata biyu suke bin Gwamnati. Wannan ya faranta ran mutane har suke saka ran cewa da gaske dai za a iya samun chanji na alkhairi a mulkin Gwamna Saifuddeen Kachallah.
***
Ranan Alhamis aka yi waliman aure a Kachallah house, Asiya ce ta shirya dan Ango yace ba za ayi wani hidima ba itama kuma Amarya ta yarda da hakan.
Ranan Jummu'ah da safe Asiya tana taya Gwamna shiryawa sai ɓaɓɓata rai yake dan jiya gaba ɗaya ta wuni ne a Kachallah House bai ganta ba sai dare haka nan ta dawo da mugun gajiya ko hiran kirki ba su yi ba ta kwanta bacci.
Sai da ta gama fesa masa turare sannan tace " a dawo lafiya Excellency" za ta juya ya jawota jikinsa yace "ni fa wannan sauri-sauri da ake sai na hana fitan yau"
"Tuba nake ranka shi daɗe" ta faɗa tana ɗaga hannayenta sama alamar ta sallama masa.
Ya shinshina wuyanta yace " ki min addu'a"
"Insha Allahu"
Light kiss ta masa sannan ta raka shi bakin ƙofa.
Tun da Asuba Halima ta kirata a waya tana mata tuni akan ta zo da wuri.
Allah Sarki Halima, yadda ta ke tun jiya kenan, sam hankalinta baya jikinta, a tsorace take sosai, gani take kamar ba za a kai ga ɗaura auren ba. Dauriya ce kawai ke sa ta du wani fara'a da take yi.
**
Gwamna yana gama gabatar da ƙudirinsa na ranan ya wuce sallar Jumu'ah saboda daga nan za a ɗaura auren Halima Kachallah. Kan kace kwabo umurnin Gwamna ya karaɗe ko'ina.
Bilkisu Kachallah na zaune a office ɗinta tana duba wasu takardu aka bugo mata waya, tunda Gwamna yasa aka biya albashi take ƙoƙarin gyara asarar da hakan ya jawo musu da ita da sauran masu amfani da albashin jama'a wajen yin kasuwanci.
"Calm down Babana, ka gaya min miya faru?"
Tana ajiye wayar COS ya shigo office ɗinta. Da gani abinda Gwamnan yayi ya taɓa shi matuƙa dan bai tsaya neman izini ba ya kutso cikin office ɗin
" Kwamishinoni shabiyu ya sauke, Yayi hauka ne?"
COS ya ce " Mr Paul yana cikin wanda aka cire, kin san zamu samu babbar matsala idan Kwamishinan kuɗi ya zamo daga wani ɓangare ba namu ba.
"Duk wanda aka sauke yana da haɗi da ke. Idan ba ki yi wani abu akai ba, nima ba lallai na tsira da kujerata ba "
"Ba abinda zai faru, zan shawo kan matsalar" Bilkisu ta yi maganar dan ta tabbatar masa da cewa har yanzu tana da iko da Gwamna sai dai da ita da ta yi maganar da shi COS ɗin duk sun sani cewa lamurra sun sauya daga ranan da Gwamna ya dira a garin.
....
Ƙarfe biyu da rabi na ranan Jummu'ah aka ɗaura auren Halima Sani Kachallah da angonta Muhammadu Bello Faruq Baba.
"An ɗaura" Asiya ta faɗa bayan ta gama waya da ƙaninta daya sanar da ita an ɗaura auren. Halima ta rufe fiska tana murmushi, Jummai da ke gefenta ta kama hanci ta saka guɗa. Asiya ta kwaɗe kanta tana faɗin " sa'arki ce ita"
Kafin Jummai ta bata amsa wasu mata suka shigo ɗakin suna guɗa.
Yadda mutane ke ta shigowa suna jaddada tabbacin an riga an ɗaura auren yasa Halima fashewa da kuka, Asiya ta rungumeta tana bata baki...
16
Gwamna bai samu dawowa gida ba sai kusan ƙarfe goma na dare. Tun kafin ya shigo gidan ya tanadi abinda zai yi idan suka haɗu da Bilkisu, yau kwananta ne kuma tunda ta samu labarin sauke commissioners da kuma special advisers da yai take ta faman kira da aika masa saƙonni amma bai amsa ba.
Ai kuwa a falonsa ya sameta ta cika fam tana jiransa.
Cikin takun ƙasaita ya ƙarisa kujerar da ke kallonta ya zauna dai-dai yana faɗin " ban ji daɗi ba da aka ce baki halarci bikin 'yaruwar ki ba. Haba Bilkisu, Halima ƙanwar ki ce, koma minene..."
"Babu ruwanka da abinda ke tsakanina da Halima. Besides ba matar ka ta zame mata uwa da uba a wajen ba"
"you should be happy for her, babu kyau"
"Ban zo dan mu yi maganar auren Halima ba. Idan ma kuturu ta aura wannan rayuwarta ce, bai shafi Bilkisu ba"
Shiru ya biyo bayan hakan na kusan sakan talatin kafin ta ce "Ina so ka maida duka kwamishinonin da ka sauke" Bilkisu ta yi maganar tana tura baki.
"Inada damar reshuffling cabinet ɗina, wannan bai shafi Bilkisu Kachallah ba"
"How dare you Saifuddeen!" ta miƙe tsaye a fusace.
"How dare you humiliate me. Kama san irin asarar daka jawo min cikin 'yan kwanakin nan kuwa. Kai yanzu ba ka ji kunyar cire sunan ɗan Rufaidah a matsayin Kwamishina ba?"
Gwamna Saifuddeen ya dunƙule hannunsa kamar mai shirin kai duka a filin dambe. Maganganun Bilkisu sun tunzura shi. Har tana da damar magana akan asara. Sai dai dole ne ya shanye ɓacin ransa ya bi komai a hankali wannan yasa ya miƙe tsaye ya tako har gabanta yace "kamar yadda na faɗa da farko, babu ruwan Bilkisu Kachallah cikin harkokin ofishin Gwamna Saifuddeen"
"Saifuddeen...Saifuddeen...Saifuddeen" haka ta bi shi da kira amma bai kulata ba ya shige ɗaki abinsa ya barta tanata ɓaɓatu.
*
Washegari tun kafin ta kai office COS ya kirata ya sanar da ita Gwamna ya miƙa sunayen sabbin kwamishinoni da special advisers zuwa majalisan jaha. Abinda su ke tsoron ne kuwa ya faru domin kuwa an maida Mr Paul zuwa kwamishinan wasanni, wato muƙamin M. Sani na da.
"Mi ya bawa Muhammad Sani?" Bilkisu ta tambaya tana sa ran shi za a bawa commissioner of finance. COS yace "bai bashi komai ba"
"Waye finance commisioner ɗin?" Bilkisu ta tambaya a kiɗime
" Tijjani Bukar"
Shiru Bilkisu ta yi na sakan biyar tana nazarin waye ma Tijjani Bukar a jahar, kafin ta tuno waye COS ya cigaba da bayanin sa " bana tunanin Gwamna zai chanja sunayen da ya bayar, abu ɗaya zamu iya yi yanzu"
"Mi kenan?" Bilkisu ta tambaya a zaƙale
"mu yiwa speaker na House magana akan ya rejecting nominees ɗin da Gwamna ya bayar "
"Zan same shi anjima"
COS na gama waya da Bilkisu Mr Paul ya shigo ofishinsa ya jefa masa wata takarda.
"Commissioner of youths and sports, is this some kind of a joke?"
"Mr Paul calm down. Boss lady ta san da maganar zata yi wani abu a kai"
"Ka gaya mata tayi duk abinda ya dace, idan ba haka ba bakina ba zai yi shiru ba"
Daga haka ya juya ya fice. COS ya furzar da iska ta baki yana tunanin mafita idan har Speaker bai amince da maganar su ba.
***
A yau ne ranan da majalisa suka yi zama kan amincewa ko rashin amincewa da sunayen sabbin Kwamishinoni da Mai girma Gwamna ya kawo.
Cikin 'yan kwanaki biyu kacal Hajiya Bilkisu Kachallah ta yi sintirin zuwa wajen speaker da deputy speaker na House of assembly yafi sau uku. Wasu mahaukatan kuɗi ta fitar dan a rabawa members na House ɗin saboda su ƙi yarda da sunayen da aka turo. Sai dai abin mamaki tun kafin a gama zaman COS ya kirata ya faɗa mata mummunan labari kan cewa Speaker ya amince da duka sunayen kamar yadda Gwamna ya turo. Bilkisu suman tsaye ta yi ta kasa koda jan numfashi ne na wasu daƙiƙu.
Mi yake faruwa? macijinta yanzu ba kowa yake tsoratarwa ba shi yasa ta yi ƙoƙarin toshe bakin speaker da kuɗi amma duk a banza.
"Kana nufin Tijjani Bukar shine Kwamishinan kuɗi?"
"Yes"
"Ba zai yiwu ba Lamara. Tijjani Bukar da Saifuddeen ra'ayinsu ɗaya ne, yama fi Saifuddeen bahagon aƙida"
"Akwai ƙaramar matsala fah"
"Miye kuma!"
"Mr Paul ya resign"
"Ya yi me ?"...
*
Asiya Kachallah tana zaune kan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana karanta wani littafi Bilkisu ta shigo falon fuuu kaman wata iska.
" Ki cire hannun ki a Gwamnatin Saifuddeen. Babu ruwanki da mulkinsa"
Asiya bata ɗago ba ta cigaba da karatun da take dan tana jin daɗin littafin dake hannunta. Bata ankara ba ta ji an wafce littafin hannunta anyi jifa da shi, sai a lokacin ta ɗago ido ta kalli Bilkisu da ke tsaye kanta tana surfa masifa.
"Ki tattara ki koma Kachallah House kafin yamma,"
Maimakon Asiya ta yi magana sai ta saka murmushi, irin murmushin rainin hankali ɗin nan.
Har Bilkisu ta bar falon bata dena murmushin ba domin tun ba a fara komai ba har Bilkisu ta fara karaya. Lallai idan haka ne kuwa komai zai zo musu da sauƙi.
Bilkisu na barin falon Asiya ta yi kiciɓus da M Sani dai dai zata je ta shiga mota.
"Boss kin ga rashin mutuncin da Uncle yayi min ko. Shiyasa nace mu kawar da shi lokacin da yake jinya, you should be the governor"
"Ya isa!" Ta daka masa tsawa. Ta ya zai mata magana irin wannnan a gaban excorts ɗinta. Mota ta shige ta barshi tsaye a wajen baki buɗe.
Duk wani shige da fice Bilkisu ta yi dan ganin an sauke Kwamishinan kuɗi amma abin ya faskara. Dr Tijjani Bukar malamin jami'a ne da yai suna sosai a jihar, abokin Gwamna Saifuddeen ne ƙut-da-ƙut tun lokacin yana koyarwa a jami'ar Congo.
***
A yau safiyar Asabat Gwamna Saifuddeen yana karyawa tareda iyalinsa aka bugo masa waya daga Fada.
Yana ajiye wayar Asiya ta zuba masa ido tana jiran ƙarin bayani dan ta ji yana ta'aziyya a wayar.
Gwamna yace "Allah ya yiwa Mai Martaba rasuwa"
Asiya da Mahira suka haɗa baki wajen faɗin Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun.
Tea kawai ya kurɓa ya fita saboda Alhaji Sani na jiransa za su wuce chan Fada.
Bayan fitarsa Asiya da Mahira suma abincin fita yai musu akai dan haka sai kira suka yi aka tattara abincin...
Rasuwan Sarkin Congo ya zo da alhini dayawa. Jama'a da dama sun ji mutuwar sarkin a jikinsu saboda Sarki ne adali kuma uban ƙasa da kowa ke alfahari da shi.
Bilkisu Kachallah na jin rasuwan ta ji ƙishirwan sarauta ya tasan mata. Idan har aka naɗa mahaifinta sarki zata ƙara samun wani daraja a idon mutane musaman wanda suke gani kaman tauraron Asiya ke haskawa a wajen Gwamna Saifuddeen.
Bata jira anyi kwana uku ba ta tuntuɓi Gwamna da maganar naɗa mahaifinta wato Alhaji Sani Kachallah.
"Bilkisu idan Allah yayi Baba zai yi sarautan garin nan babu makawa sai yayi, idan kuma har Allah bai rubuta ba then babu yadda zamu yi domin babu alkhairi a cikinsa"
"What do you mean Saifuddeen!. Yes ka gaya min mi kake nufi da wa'azin da ka fara kaman an naɗa ka limamim masallacin anguwa"
"Ina nufin ki sa a ranki cewa Allah ke bada sarauta, idan bai bawa Baba ba ban isa na bashi ba"
"Oh please cut this bullshit. You are the governor of this state, kai ne ke da damar naɗa sarki a jihar nan. Yanzu butulcin da za ka yiwa Baba kenan bayan duk irin gatan daya maka a duniyar nan"
Gwamna Saifuddeen ya dafa kafaɗar Bilkisu cikin sigar lallashi yace " i'm sorry my dear, ba zan zaɓi Baba a matsayin Sarki ba har sai idan ya chanchanci hakan"
Wafce hannunta tayi da ƙarfi tana faɗin " i will fight you with everything i have Saifuddeen, ko ka naɗa Baba Sarki ko kuma jahar nan ta maka zafi"
daga haka ta fice daga ɗakin yana jin yadda tsinin takalminta ke buga tiles kaman zai tsaga shi.
Bai yi mamakin maganganun Bilkisu ba tunda a baya tayi yunƙurin saka shi tsige Sarki lokacin yana raye.
Asiya ce da kwana dan haka ya wuce ɗakinta ko zai samu nitsuwa. Ganin bata ɗakin yasa shi zama kan gadonta yana jiranta. Kusan minti huɗu sai ya ji ƙaran buɗe ƙofar banɗaki, sanye take da bathrobe kalar ruwan ƙwai, gashinta ƙunshe cikin towel data ɗaura kamar turban.
Gwamna ya ƙura mata ido cike da kewarta, tunda aka yi rasuwan nan ba su yi ƙwaƙƙwaran zama na minti goma ba.
Da hannu ya mata alamar ta zo ta zauna a cinyarsa, tana zama ya kwantar da kansa akan ƙirjinta, a hankali ta sa hannu ta fara shafa gashin kansa tana ɗan hura masa iska a kunne.
Kusan minti biyu suka yi a haka kafin yace " Bilkisu na so na zaɓi Baba a matsayin sarki, Baba baya cikin candidate ɗin da mutane suka fi so"
Asiya ta ja numfashi sannan tace "ka yi istikhara, sannan ka nemi shawaran mutanen da kake tunanin za su baka shawara ba tareda son zuciya ba, ina ga idan ka yi wannan Allah zai shige maka gaba akan zaɓin da za ka yi".
Gwamna ya ɗago fiskarsa ya ƙurawa Asiya idanu tabbas yanzu ne ya san yayi sa'ar mata ta gari.
"Wannan kallon fa?" Asiya ta faɗa tana ɗaga masa gira.
"I love you"
Ba tareda ta shirya ba, wani ƙasaitaccen murmushi ya kuɓuce mata. Tana jin daɗin kalaman nan musamman a lokutan da take ganin zahiri a idanunsa cewa sonta yake bilhaƙƙi.
"I love you nace fah! Ba zaki amsa min ba"
'Yar dariya tayi sannan tace " kai Gwamna ne ni kuma Saifuddeen nake so"
Hannunta ya riƙe dai-dai tana ƙoƙarin tashi.
"A gida da waje Saifuddeen naki ne"
Asiya ta shige jikinsa tana murmushin jin daɗi...
***
"Banyi mamaki ba da aka ce Gwamna ya kori kwamishinoni da kika kawo, amma kuma hana mahaifinki sarautar Sarki wannan ya wuce tunanina. Gaskiya ki tashi tsaye akan yarinyar nan idan ba haka ba kan ku ƙarisa tenure ɗin nan za ta sa shi yai waje da ke" Madam Bintu ta ƙarisa maganar tareda kurɓan juice dake hannunta.
"Yanzu miye abinyi Bintu?"
"Ke kin fi yarda da mutanen India ni kuma malamai na baƙaƙen fata ne, idan za ki gwada aikinsu to sai na raka ki"
"As long as zan samu biyan buƙata ban ƙi muje ko'ina ba. Duk aikin da aka min ya dena yiwa Saifuddeen tasiri, ita kuma shegiyar tun asali ma maciji na tsoronta yake.
"Yanzu yaushe zamu je?"
"Duk sanda kika shirya First lady"
"A matse nake Bintu, ba zan yarda a naɗa wani Sarki ba matuƙar Baba na raye a doron ƙasa"
"Gimbiya Bilkisu!" Madam Bintu ta faɗa da shewa. Bilkisu tayi murmushin jin daɗi.
***
Bilkisu Kachallah ba ta yi tunanin akwai irin wannan ƙauye ba a jahar Congo, kafin su isa ƙauyen ba ƙaramin jigata suka yi ba. Tafiya ce suka yi a machine na kusan awa biyu sannan daga ƙarshe da zasu je jejin da bokan yake sai da suka yi tafiyar ƙafa itama ta kusan awa ɗaya.
Shiga ce suka yi ta ɓadda kama kamar yadda Madam Bintu ta bada shawara, da wuya ka kallesu a yadda su ke ka gane cewa Hajiya Bilkisu Kachallah ce uwargidan Gwamna da kuma babbar aminiyarta fitacciyar 'yar kasuwa wato Madam Bintu Chadi.
Rashin kwalliya dama zafin rana sun saka fiskar Bilkisu ta jeme ta kuma ƙara tsufa. Saboda akwai ƙura a hanyar babu wanda ya san cewa ɓoye matsayinsu shine dalilin daya sa ko sau ɗaya basu cire nose mask da suka rufe fiskar su da shi ba.
Babu abinda ya fi ƙona ran Bilkisu cikin tafiyar da suka yi irin rashin samun abinda suka je nema. Bokan kamar yadda Madam Bintu ta faɗa hatsabibine sosai domin kuwa suna zuwa ya sanar da su abinda ya ke tafe da su sannan ya bayyana dalilin da ya sa ba zai iya yiwa Bilkisu kowanni irin aiki ba, ya ƙara da cewa koda ta je wani wajen daban baya tantama cewa ba za a iya yi mata kowanni irin aiki ba.
A cikin mota suna hanyar su ta dawowa Madam Bintu ta fara rarrashin aminiyarta tareda yi mata alƙawarin za su keta chan kudancin ƙasar domin su samu wani bokan daban.
Tunda suka baro wajen boka Bilkisu ta kasa magana. Na farko saboda ta san abinda Bokan ya faɗa gaskiya ne dan an mata kashedi akan cewa baƙin aljani da ke yiwa macijinta hidima baya son kishiya. Na biyu kuma haka kawai bayan sun fito daga jejin ta ji ƙirjinta na mata wani irin nauyi kamar wanda aka ɗauki ƙaton dutsi aka ɗaura a kai.
A wannan yanayi suka ƙarisa cikin gari, sai dai tun a hanya suka lura cewa akwai wani abu da ke faruwa a garin musamman da suka isa dai dai anguwar Gwamna.
Motocin da suka yi tozali da shi a gidan shi ya tabbatar wa Bilkisu cewa akwai matsala...
Suman zaune Bilkisu ta yi lokacin da mahaifiyarta da Hajiya Umma suka sanar da ita rasuwan da aka yi. Ƙauyen da suka je babu network shiyasa duk kiran da ake mata tun faruwan abin baya shiga.
"Wasa kuke min right?" Bilkisu ta faɗa bayan ta iya buɗe bakinta.
Jagora suka mata har inda aka shimfiɗa gawar mamacin wanda kallo ɗaya zaka yi kasan cewa gawar yaro ce. Addu'a aka ce ta yi masa amma sai ta kama ƙoƙarin buɗe likkafanin tana faɗin ba abinda ya samu babyn ta, wai bacci yake yi, nan da nan aka fara ƙoƙarin riƙeta, Hajiya Umma kuwa abin ya zo mata har wuya ta kama Bilkisu ta tsinke ta da mari tana faɗin
"Ki nitsu ki masa addu'a dan Allah, wannan abinda kike ba dawo da shi zai yi ba"
Jikin Bilkisu ya shiga ɓari saboda ta gani, tabbas ta ga tabon saran da ke goshin gawar ɗanta Sa'ad Junior.
17
Tunda aka fita da gawar Junior Bilkisu ta rufe kanta a ɗakin yaron ta ƙi fitowa, anyi bugun duniyar nan, an mata magana amma ta ƙi buɗe ɗakin. Ƙarshe sai barinta aka yi kamar yadda Hajiya Umma ta faɗa. Har ga Allah mutuwa da ciwo amma kuma sanin cewa macijin Bilkisu ne ya kashe mata ɗa yasa ko kaɗan Hajiya Umma bata tausaya mata ba, idan da hali ma titsiyeta zata yi da duka har sai ta huce baƙin cikin dake ranta, sai dai kuma Junior ya tafi kenan babu abinda za ayi ya dawo duniyar, sai dai haƙuri kawai.
Asiya ce ke karɓan gaisuwa a madadin Bilkisu. Itama ɗin da ka kalleta kasan tana cikin tashin hankali saboda ita ce ta fara ganin gawar Junior.
Ta tsorata matuƙa lokacin da ta shiga ɗakin yaron dan ta masa wanka ta same shi ƙwance a ƙasa baya motsi. Kumburin goshinsa da tabon cizo guda biyu a goshin ya sa Asiya tayi zargin saran maciji ne, koda aka kai shi asibiti report ɗin da suka bayar ya nuna cewa gubar maciji ce ta kashe shi. Babu wanda ya san lokacin da abin ya faru kuma tunda abin ya faru Gwamna yasa a dubo masa macijin Bilkisu ya kashe amma babu ita babu dalilinta. Abin haushin ma kuma ita kanta Bilkisun anyi ta kiranta amma duka nambobinta basa shiga, ba a san inda taje ba balle yaushe za ta dawo. Anyi jinkirin jana'izar saboda ita ne, wanda Asiya da mahaifiyar Bilkisun ne suka nemi hakan a wajen Gwamna, awa biyu daya bayar akan idan Bilkisu bata zo ba za a kai yaron sai gata nan a sama.
Bilkisu ta rungume hoton Junior tana sheshsheƙar kuka haɗe da sunbatu. Rabon da ta yi wani magana mai tsayi da yaron ta manta, tun kafin dawowar Gwamna. Shine magajin Saifuddeen shine magajinta abinda ta sakawa ranta kenan tun ranan data haife shi, kai tunma da aka yi scanning aka ce mata namiji zata haifa. Yanzu gashi nan ya tafi ya barta, bata da magaji...
*
Mutuwar Junior ya kawo wani sauyi a tattare da Gwamna dama iyalinsa gaba ɗaya. A ɓangaren Bilkisu tunda aka yi rasuwan ta tare a ɗaki, har aka gama gaisuwan uku bata fita daga ɗakin ta ba, a daren ranan rasuwan ne ta fito daga ɗakin Junior idanunta a kumbure ta wuce nata ɗakin ba tareda ta amsa gaisuwar kowa ba. Hatta manyan mata ire-iren matan Gwamnoni dana senatoci da suka zo yi mata gaisuwa babu wanda ta sakewa fiska wannan yasa mutane ke tunanin mutuwar yaron ya taɓa mata ƙwaƙwalwa.
Shi kan shi Gwamna dauriya yake amma zuciyarsa tana cikin ƙuna. Maganar sanadin mutuwar yaron ya tsaya ne iya cikin gida, duk dama akwai wata ƙaramar gidan jarida da suka wallafa cewa Sa'ad Junior ya rasu ne sakamakon harbin maciji. Hakan yasa Mai magana da yawun Gwamna ya fito ya ƙaryata jaridar wannan yasa maganar bata yi tsayi ba aka tsaida tasirinta a cikin mutane...
Yanzu hankalin kowa ya karkata ne kan naɗin sabon sarki. Kowa ya baza ido yaga wa za a naɗa. Wasu ɓangare na matasa har sun shirya zanga-zanga da tarzoma da za su yi idan har aka naɗa Alhaji Sani Kachallah a matsayin sarki.
Alhaji Sani Kachallah bai da sha'awar neman takarar sarautar gidansu. Amma kuma a ɗan tsurkukin kwanakin rasuwan sarki munafukan mutane suka cusa masa wannan ra'ayi, tun yana kauda kai har ta kai shaiɗan ya samu galaba a kansa. Chan cikin zuciyarsa ya sani cewa Saifuddeen ba zai taɓa naɗa shi sarki ba, amma wannan sabon buri dake cinsa ya raya masa cewa babu wanda ya kamata Saifuddeen ya naɗa sarki sai shi!.
*
Kwanaki shauku da rasuwan Junior aka naɗa sabon sarkin garin Congo. Sarki Ya'aqub shine zaɓin gama-garin talakawa dama mutanen da su ke son zaman lafiya da cigaban gari. Duk da cewa shi ɗin ɗa ne ga ƙanin Sarki mai rasuwa amma hakan bai hana shi samun sarautan gidan su ba, abu uku su suka saka mutane suka yi ra'ayinsa sama da asalin ɗan sarki mai rasuwa wato Yarima Isma'il. Na farko an masa shaidar baya shan giya tun daga samartakarsa har zuwa yanzu da yake shekaru arba'in da bakwai a duniya. Babu wani daya taɓa yi masa shaidar shan giya a bayyane ko a ɓoye cikin abinda ya bayyana wa makusantansa, sai dai Allah ne kaɗai masanin gaibu.
Na biyu ya kasance masanin addini kuma kyawawan halayensa su suka fi bayyana wa mutane. Na uku shine yana da yawan kyauta, tun yana saurayi wannan shaida ya ke binsa. Ba kamar Yarima Isma'il ba wanda a ɗan shekaru biyun ƙarshe na mahaifinsa ya fara ƙoƙarin jawo mutane jikinsa tareda ƙoƙarin sake aljihunsa wa talakawa...
Tun da aka bada sanarwar naɗin sabon sarki gari ya kaure da murna da farin cikin matasa, ta ko'ina sai shagulgula ake domin bayyana farin cikin da ake ciki. A yayin da wasu magoya bayan Yarima Isma'il suka yi yunƙurin tada husuma, sai dai abin bai kai ko'ina ba jami'an tsaro suka tare abin.
Yayinda wannan naɗi ya kawo farin ciki a zukatan mutane shi Gwamna Saifuddeen Kachallah ya wuni ne cikin ƙunci da kuma tsoron abinda zai biyo bayan abinda ya aikata. Kafin wannan rana sun yi magana mai tsayi tareda Alhaji Sani wanda ta kowanni fiska uba yake a gareshi. Cikin maganganunsa ya karkatar da hirar ne zuwa shekaru da dama da suka shige irin yadda shi Alhaji Sani ya nunawa Saifuddeen so da ƙauna sama da 'ya'yansa na cikinsa daga ƙarshe ya sake tunasar da shi cewa wannan kujera da yake kai ta zo gareshi ne bisa shiri da kuma taimako da yai masa.
"Ina fata bazaka watsa min ƙasa a ido ba" maganar ƙarshe da Alhaji Sani yai kenan kafin rabuwar su.
Ashe kwaɗayi da ya gani muraratan a idon matarsa Bilkisu wasu daga cikin makusantansa suma sun fara irin wannan kwaɗayi.
Kwana ɗaya bayan maganarsa da Alhaji Sani sai mahaifiyar Bilkisu ta nemi ganawa da shi kuma bil-haƙƙi ta fito fili ta bayyana manufarta wato idan har ya cika ɗan halak to kujerar sarki ta mijinta ne. Bayan nan ya samu 'yanuwa na kusa da na nesa da suka dinga zuwa suna bashi shawaran naɗa mahaifinsa a matsayin sarki, wasu na ganin wannan zai kawo masa kwarjini da cigaba a harkar siyasar jihar. Sai dai kuma duk ta inda ya duba duk addu'a da istikhara da yai tun kafin rasuwan ɗansa dama bayan nan zuciyarsa bai amince da naɗa Alhaji Sani sarki ba.
A cikin kwanakin da aka ɗauka kafin a bayyana sunan wanda Gwamna ya zaɓa ko sau ɗaya Bilkisu ba ta yi magana da Gwamna ba. Tana nan tana fama da raɗaɗin rashin ƙaramin ɗanta kuma ɗa namiji ɗaya tal data haifa. Sai dai tun kafin a fitar da sanarwar wanda aka naɗa ta riga ta samu labari, sai dai babu wani abu da zata iya yi akai illa ta bi shawaran da wani ɓangare na zuciyarta yake bata.
Cikin dare da Gwamna ya dawo gida a karo na farko cikin sati biyu Bilkisu ta shirya tsaf ta wuce ɗakin mijinta. Sai dai ba wai ta je ne domin ta amsa sunan matarsa ba, taje ne domin ta bayyana masa abinda ke ranta.
Gwamna sai daya tsorata da ganinta kwatsam a ɗakinsa, ta sameshi yana ƙoƙarin cire kayan jikinsa domin yai wanka ko zai rage jin nauyi da ciwo da ilahirin jikinsa ke yi. Yadda ya ganta fiska ɗauke da kwalliya da kuma shiga ta alfarma kamar mai shirin zuwa bikin 'yar shugaban ƙasa yasa shi tunanin lallai ba lafiya ba. Yaushe rabon ya ganta da kwalliya?.
"Kayi mamakin ganina ko?"
"Bilkisu it's 1:00 am, a gajiye nake please, koma minene ki bari gobe zamu yi magana"
"Baka ma damu da mutuwar ɗana ba. Kai damuwar ka shine kayi abinda ranka yake so, oh! Na manta. Abinda tsinanniyar nan ke so.
"Well let me tell you this Saifuddeen. Ba zaka tozartani ba, sannan ka tozarta mahaifina daya buɗe maka ƙofar shiga siyasa. Idan kana tunanin zaka samu zaman lafiya a kujerar ka to ka sake tunani"
Matsowa tayi daf da shi ta sa yatsarta manuniya dai-dai ƙirjinsa tace "Na rantse maka Saifuddeen sai kayi dana sanin zama Gwamna a jihar nan, na rantse sai ka ƙwammace baka taɓa amsa sunan Gwamna ba. Na rantse maka ni Bilkisu Sani Kachallah sai na maida ka ba kowa ba a wannan jaha, duk abubuwan da ka ƙwacemin tun ina ƙarama sai na ƙwace su a hannunka"
"Mi kike nufi Bilkisu?"
"Kar ka damu Mr Governor, da sannu zaka fahimci komai"
Juyawa ta yi zata bar ɗakin ya kira sunanta "Bilkisu!"
A ƙasaice ta juyar da wuyanta ba tare da ta amsa ba.
" Idan kina tunanin na manta da cewa macijin ki ne ya kashe min ɗa, to ki sani ina sane da komai, kuma ba zan taɓa yafe miki ba"
"Wannan kuma kai ta shafa"
Bilkisu ta fice daga ɗakin ta bar Gwamna tsaye yana huci, ƙarshe kuma numfashinsa ya fara ƙoƙarin sarƙewa da ƙyar ya lalumo inhaler ya shaƙa.
Wannan dare ya buɗe wani sabon babi a rayuwar auren Saifuddeen da Bilkisu. Kowannensu ya kwana ne da yaƙinin ba zai taɓa bari abinda ɗanuwansa ke iƙirari ya faru ba...
***
Meeting na gaggawa Bilkisu Kachallah ta shirya a gidanta. Wannan ne zama na farko da za ta yi tun bayan rasuwan Junior. Tun da aka yi rasuwan babu wanda ta gana da shi cikin muƙarrabenta, hatta COS ma waya kawai suka yi sau biyu.
An buɗe meeting ɗin ne da maganar sauke kwamishinoni da aka yi da kuma resigning da Mr Paul yai. Duk wani muƙami da yake da daraja an cike ne da mutanen Gwamna wanda hakan bai yiwa kowa daɗi ba.
"Ina shi Mr Paul ɗin?" Bilkisu ta tambaya bayan COS ya gama bayaninsa.
"Yace zai zo" M Sani ya amsa mata.
Bayan ta gama jin duk wani ƙorafi da shawarwari sannan ta fara magana, dai-dai nan ne kuma Mr Paul ya shigo falon.
Mr Paul yana zama yace " gentlemen, ban ga dalilin da zai sa a kira ni wannan zaman ba. I am no longer the commissioner of finance. Lokacin dana dage akan incompetency na Saifuddeen babu wanda ya goyi bayana, yanzu ga irinta nan"
Ya duba ilahirin falon bai ga Alhaji Sani Kachallah ba yace "yau ina Alhaji Sani da ke kukan ana so a hana ɗansa zama Gwamna shekaru biyu baya"
Ya kalli Bilkisu ido cikin ido yace " na ji ance hana shi sarautar sarki da Gwamna yai ya sa mishi ciwon damuwa. Ku yi saurin kai shi psychiatric fa, depression is real you know"
"Mr Paul! " COS ya daka tsawa
"Mafita muke nema anan ba izgili ko cin mutunci ba"
"Oh really! To ai babu amfanin zama na a nan domin na riga na nemawa kaina mafita. Zaɓe mai zuwa ina tareda Umaru Kwom, untill then na barku lafiya"
Yana miƙewa Bilkisu tace " ka cewa iyalinka su tanadi akwatin gawa kafin kwana bakwai"
Mr Paul ya juyo a firgice
"Mi hakan ke nufi?"
Wata ƙaramar dariya Bilkisu tayi sannan ta miƙe tsaye tace " duk wanda yai ƙoƙarin cin amanata ba zai wuce kwana bakwai a doron ƙasa ba. Wannan shine hukuncin mai cin amanar alƙawarin jini"
Ɗaga wata takarda da ta yi sama yasa kowa a wajen ya waro ido waje daga nan kuma aka fara kallon-kallo. Tabbas takardar yarjejeniya ce da aka rubuta kuma kowa ya sanya hannu da jininsa kusan shekara ɗaya daya wuce. A ranan da suka yi abin Bilkisu ce ta basu wata ƙaramar allura kowa ya chaki babbar yatsarsa da shi sai da jini ya fito.
"Idan kun ga dama ku chanja jam'iyya idan kun ga dama ku gudu ku bar ƙasar, amma ku sani duk wanda ya ci amanata ni Bilkisu Sani Kachallah to ya sani ya shirya sallama ne da duniya"
Tsit falon yai na kusan minti ɗaya kafin Bilkisu ta kalli COS tace "ina so a kashe Project tomatonion, ya za ayi?"...
18
***
Wani shiri aka fitar daga ofishin Kwamishinan noma da raya karkara, wato PROJECT TOMATONION kamar yadda aka saka wa shirin. Kowa a cikin jahar ya baza ido don ganin yadda wannan shiri zai kawo cigaba wa jihar kamar yadda Kwamishinan da matar Gwamna Asiya Kachallah suka yi iƙirari. Ganin cewa shirin ya maida hankali kan ƙananan manoma dake ƙauyuka da karkara sai ya zamto mutane da dama na zuwa ƙauyukansu dan su yi rajista su amshi tallafi na kuɗi da taki da gwamnati ke son bayarwa. Aksarin mutane dake shirin karɓan tallafin dan aljihunsu suke yi amma ba wai dan farfaɗo da arziƙin noma ba. Sai dai daf da za a fara raba tallafin aka kawo wani tsari wanda zai tantance masu gaskiya da kuma manoman bogi.
Wasu saboda tsaurin tsarin yasa dole suka yi amanna da cewa zasu gwada sa'arsu wajen noman da gwamnati ke son ayi.
Yiyuwar wannan shiri ya rataya ne kwacokam a wuyan Asiya shiyasa ta duƙufa sosai wajen ganin cewa ba a yi magu-magu a shirin ba.
Alhamdulillahi kuma har aka gama raba tallafin kuɗi da taki dama iri ba a samu wata babbar matsala da zata jawo wani cikas a shirin ba.
Kusan sati uku Asiya ta ɗauka tana zirga -zirgan yawo garuruwa da ƙauyuka abin sai ya dawo kamar wani sabon kamfen. Mutane da dama sun gano manufarta amma sai suke ganin kamar ba zai yiwu ba musamman daya ke har yanzu akwai ɗan matsalolin tsaro dake kutsowa jahar kaɗan-kaɗan. Bayan duk wasu shirye-shirye Asiya ta ƙaddamar da shirin PROJECT-TOMATONION ranan wata Asabat da safiya a ranan ne kuma ta buɗe wani sabon babi a tarihinta na matar Gwamna Saifuddeen Kachallah...
***
Kwanaki biyar kenan da lauching wannan program ɗin. A yau ne kuma Asiya ta shirya zuwa manyar makarantu dake jahar dan gani da ido cewa suma ɗin sun fara wannan Project kaman yadda ya kamata. Sai data gama shiryawa zata fita taji hajijiya na neman kada ita da ƙyar ta samu ta dafa bango, duk da haka sai data kai ƙasa ta zauna kafin ta ji dai-dai. Ta kai minti uku tana riƙe da goshinta.
"Ranki shi daɗe" Badawiyya ta faɗa tareda ƙarasowa wajen da sauri. Taimaka mata tayi ta miƙe tana tambayarta ko lafiya?.
"Hajijiya ne kawai, inaga dan ban karya bane"
"Amma..."
" zan sha magani kafin mu tafi"
Basu tafin ba sai da Badawiyya ta tabbatar ta sha tea da slize biyu na bread sannan ta sha maganin ciwon kai.
Jami'a suka fara zuwa kafin suka wuce kwalejin noma da kuma polytechnic. Manufar ita ce a farfaɗo da harkan noma a makarantu. Taya ɗalibi zai yi shekara uku zuwa huɗu yana karantar harkar noma amma idan ya gama aka bashi gona ba zai iya yin komai ba.
An shigo da Project Tomatonion makarantun ne dan a horar da ɗalibai kan harkan noma, ba wai a iya takarda ba har a aikace. Yawanci makarantun sun yi ƙorafin rashin kayan aiki da kuma lalacewar wasu daga cikin kayan aiki da suke da shi. Kafin a ƙaddamar da shirin duk wasu kayan aiki da suka lalace an gyara sannan akwai magana mai ƙarfi daga ofishin Gwamna kan cewa za a fidda kuɗi domin a siyo sabbin kayan aiki da babu.
"Ina so harkan noma ya samarwa manyan makarantu kuɗin shigowa ta inda zasu iya riƙe kansu koda babu tallafin Gwamnati" abinda Asiya ta gayawa kwamishinan noma da kwamishinan ilimi kenan lokacin da ta nemi sa hannunsu kan tallafawa shirin nata ya kai ga manyan makarantu.
A hanyarsu ta dawowa ne Badawiyya ta taɓo batun kama Madam Bintu da take son yi.
Asiya ta riƙo hannun Badawiyya tace "Idan muka ce zamu kama Madam Bintu yanzu, tafiyar mu ba za ta yi dai-dai ba. Na san a matse kike ki ɗau fansa but trust me Badawiyya, Madam Bintu za ta shiga hannun ki, very soon"
"Shikenan zan yi haƙuri kamar yadda kika ce"
"Nagode da kika fahimceni Badawiyya. Da yardar Allah komai zai tafi kamar yadda muka tsara "...
*
Asiya tana shiga babban falon gidan ta tarar da Bilkisu tana surfawa Mahirah masifa hannunta riƙe da wasu takardu.
"I'm very disappointed in you Mahirah. Malamar Islamiyya kike son zama?. Listen to me young lady ba a gidan nan zaki je Sudan ki karanto shirme ba. Ki gyara shirin ki da kyau yarinya you are going to Harvard ko kuma Yale"
"Mommy dan Allah ki saurareni, course ɗin da nake son karantawa kenan..."
"Idan kika sake magana zan mare ki. Bari ma ki ga" ta kama takardan admission letter ɗin ta yaga shi gida huɗu sannan ta watsar da shi. Ko kallon Mahirah bata sake yi ba ta haura sama.
A hankali Asiya ta ƙaraso gaban Mahirah ta riƙeta.
"Anty dan Allah ki saka baki, Daddy yace bazan yi karatu a ƙasar waje ba Mommy kuma tace bazan je Sudan ba dan kawai zan karanta Islamic Jurisprudence"
"Yaushe Excellency yace ba zaki tafi Sudan ba?"
"Bayan rasuwan Junior dana mishi magana akan na samu admission a Sudan shine yace wai a nan Congo zan yi karatu" ta ƙarisa maganar tana sheshsheƙan kuka.
"Ki dena kuka zan gwada yi masa magana. Sai ki dage da addu'a kinji"
Mahirah ta gyaɗa kai tana faman goge hawaye.
Asiya na shiga ɗaki ta rage kayan jikinta ta wuce banɗaki ta ɗauro alwala, tayi mamakin ganin har yanzu jini bai zo mata ba. Tun jiya take tsammanin ganin jini amma har yanzu shiru. Kwana biyar baya ta ɗan ga spotting na jini a underwear ɗinta, da farko ma tayi tunanin ko period ɗin ne yazo da wuri sai daga baya kuma taji shiru ba komai.
Bayan ta idar da sallah tana zaune tana azkar wani tunanin ya faɗo mata. Ko dai ciki gareta ne?...
A gaban madubi dake jikin bangon banɗaki Asiya ta tsaya tana duba fuskarta da kyau. Strips uku tayi amfani dasu dan samun chanji bisa sakamakon data gani jiya bayan Badawiyya ta kawo mata pregnancy test trips data buƙata. Ance fitsarin sassafiya yafi nunawa shiyasa tana tashi ta shiga banɗaki da niyyar yin gwajin ciki. Duka strips biyar da ta yi amfani da su tsakanin jiya da yau sun tabbatar da reading ɗaya ne wato NEGATIVE.
Asiya ta shafa cikinta tana tunanin kodai yayi ƙaranci ya nuna a jikin strip ɗinne?. Sati huɗu da kwana biyu kenan rabon da Gwamna ya taɓa ta.
"Ƙila wata ɗaya yai kaɗan ya nuna ta fitsari, ya kamata naje Asibiti amin gwajin jini dan a tabbatar. Kai scanning ma za ayi"
Ta yi maganar a fili dukkan ilahirin jikinta yana amsawa da tsananin farinciki. Ba ƙaramin daɗi Gwamna zai ji ba idan ya samu labarin wannan alkhairi.
Tun gari bai gama wayewa ba Asiya ta kira Badawiyya akan tazo ta rakata Asibiti.
"Kice nazo na karɓi tukwuici a wajen Gwamna tunda ni na siyo strips ɗin"
"Ban gama tabbatarwa ba Badaweey shiyasa nake son zuwa Asibiti dan ayi scanning"
"Gani nan zuwa maman 'yan biyu"
Murmushi Asiya tayi sannan ta wuce closet ɗinta dan ta zaɓi kayan daya dace da wannan rana.
Gwamna baya gari dan haka bata bi ta kan kowa ba a gidan suka wuce Asibiti ita da Badawiyya.
Likitan Gwamna ta gani. Bayan duk wasu bayanai sannan ya kira daga lab aka zo aka ɗauki jininta daga baya kuma ya turata wajen scanning. Kusan minti hamsin kafin aka samu aka kawo sakamakon gwajin da aka yi...
Badawiyya na tareda ita lokacin da Likita yai bayanan sa kuma taji daɗin cewa bata hanata tsayawa jin sakamakon ba.
Kalamai masu sanyaya rai Badawiyya take gayamata musamman data nuna mata cewa ita ɗin tanada damar da zata iya samun rabo a kowanne lokaci ba kamar ita da Madam Bintu tai mata damejin da baza a iya yiwa gyara ba.
"Kar kisha mamaki kafin shekaran nan ya ƙare kiga Allah ya turo miki rabon ki, ba abinda Allah ba zai iya yi ba"
Har suka iso gida Badawiyya bata daina yiwa Asiya kalamai masu sanyaya zuciya ba.
Lokacin data zauna gefen gado bata san tana hawaye ba sai da ta ji saukansu a kumatunta.
"Yana iya faruwa hakan, stress ne ya miki yawa a jiki shiyasa ya jirkita miki yanayin al'adarki. Kar ki damu bincike ya nuna lafiyar ki ƙalau koda yaushe zaki iya samun rabo"
Kaman dai abinda Likita yace kenan bayan ya tabbatar mata bata ɗauke da juna biyu.
Ta sa bayan hannunta ta goge hawayen dake shimfiɗe a fiskarta tace " ba rabon ki bane samun ciki yanzu Asiya Shahidah"
...
Washegari kuwa kiran Inna Yaha ne ya tasheta, wai Salma matar Yaya Ubayd ta haihu. Asiya ta mata barka tareda kiran Abba shima ta gaishe shi. Taso kiran Yaya Ubayd ɗin amma sai ta fasa ta tura masa saƙƙon taya murna ta waya ko minti ɗaya bai cika ba ya turo reply da cewa 'nagode Hajiya Asiya, nai mata huɗuba da sunan Umma, Zainab (Amirah)'
Har ranta taji daɗin wannan kara da yai na yiwa Ummanta mai suna.
Wannan karan kafin ta shiga banɗaki ma ta riga ta gane cewa period ɗinta yazo. Da gaske dai bata samu rabo ba har yanzu.
***
A ranan da Gwamna ya dawo Asiya ta nemi yi mishi magana akan batun makarantar Mahirah. Abun data ɗauka ƙarami sai gashi har Gwamna yana ɗaga mata murya.
"Dan Allah ka fahimceni, ba wai..."
"Babu 'yata da zata yi karatu a wajen jahar nan, itama Nana tana samun lafiya zan dawo da ita gida. Ki bar maganar nan a haka"
"Your excellency wannan hukunci daka yanke ba lallai ya zama shine zaɓi mafi alkhairi ba. A ko'ina Mahirah take addu'a zaka mata..."
"I'm not loosing any child again Asya. 'ya'yana ba zasu fita ko'ina karatu ba"
Ta gane minene tsoronsa amma kuma wannan tsoro na wanda bai yadda da ƙaddara bane.
Ƙoƙarin fita taga yana yi dan haka ta tausasa muryarta wajen faɗin " a duk inda 'ya'yanka suke Allah shi zai karesu. Idan kayi imani da Allah da kuma ƙaddara dake bin kowanni ɗan Adam zaka gane cewa Sa'ad Junior ya rasu ne saboda lokacinsa yayi, kai da ni dama sauran 'ya'yan naka lokaci kawai muke jira da zai bayyana sababin mutuwarmu"
Ƙura mata ido yai ya rasa bakin magana. Bata jira mi zai ce bama ta fice daga ɗakin ta barshi da tunani a zuci.
Bata yi tunanin zai sakko ba sai dai kuma ko sati ba ayi ba Mahirah ta sameta akan Gwamna ya amince da batun tafiyarta Sudan.
Kusan kwana huɗu akayi ana ja'inja tsakanin Gwamna da Bilkisu kan tafiyar Mahirah kafin daga baya Bilkisu ta amince, ko wani alƙawarin Gwamna yai mata har ta amince oho, amma dai tabbas akwai wani abu a ƙasa.
A cikin satin ne kuma Asiya ta lura cewa Gwamna ya chanja Chief Security Officer (CSO) ɗinsa daga captain Bature zuwa wani wai shi El-Sadiq da ake wa laƙabi da El-Sad.
Ganin bata ji ƙarin bayani gameda chanjin da aka yi ba daga bakin Gwamna yasa tayi shiru ta ɗauke kai daga zancen duk da kuwa Badawiyya ta sanar da ita cewa El-Sad yana yiwa Bilkisu aiki ne.
*
Safiyar wata ranan Asabat Gwamna da iyalinsa na karyawa COS ya shigo dinning area ɗin yanayinsa a hargitse. Tunda COS ya iya ƙarasowa wannan waje ba tareda ya nemi izini ba gaskiya akwai matsala.
Neman magana yai da Gwamna ɗin a keɓe amma sai Gwamna ya bashi damar yin magana a wajen, afterall matansa ne duka biyu a wajen da kuma 'yarsa.
COS ya ciro Tab ɗinsa ya nunawa Gwamna wani video. " jiya da dare 'yan bindiga suka kaiwa wasu manoma hari a ƙauyukan Kwom, Tabu da kuma Jabbuwa"
Gwamna ya sake cokalin hannunsa ta faɗo ƙasa tana ƙara, maida hankalinsa yai kan bidiyon da ake nuna masa yana mamakin wannan abin al'ajabi, kusan gaba ɗaya manyan gonakin ƙauyukan aka cillawa wuta.
Kafin ya gama kallon bidiyon ma wayarsa ta shiga ƙara. Mai magana da yawunsa ne yake kira.
Shima dai maganan harin yai masa tareda faɗa masa cewa Alhaji Umaru Kwom zai yi hira da 'yan jarida da ƙarfe takwas na safe dan ƙauyen iyayensa na ɗaya daga cikin ƙauyukan da aka kai hari. Ya ƙarisa bayaninsa da cewa "your excellency dole ka ce wani abu kafin ya juya maganar kan ka"
Ko kallon iyalinsa bai yi ba balle ya amsa tambayoyin da Asiya ta jero masa haka ya miƙe yabi bayan COS suka bar dinning room ɗin. Bilkisu ta cigaba da cin abinci hankalinta kwance kamar bata ji labarin da COS ya faɗa ba yayinda Asiya ta ɗau wayarta ta wuce ɗaki.
Washe garin ranan da abin ya faru Asiya ta raka Mahirah zuwa ƙasar Sudan tunda Gwamna ba zai samu damar yin hakan ba kamar yadda ya tsara...
19
"YAWAN HARE-HARE DA AKE KAIWA ƘAUYUKA CIKIN KWANAKIN NAN YA SANYA MANOMA DA DAMA YIN WATSI DA HARKAR NOMA"
Gwamna ya ajiye jaridar dake hannunsa bayan ya karanta kanun labarin. Jarida na gaba kuma ƙaton hoton Alhaji Umaru Kwom ne a jiki riƙe da mic, a gefen hoton an rubuta "AL'UMMAR KWOM BA ZASU YARDA DA KISAN GILLA DA AKE MUSU BA"
Gwamna Saifuddeen yai jifa da jaridar yana faɗin "Mr Lamara mi yake faruwa ne? This is getting too much"
"Your Excellency statistics ya nuna cewa tunda aka launching Project Tomatonion hare-haren da ake kaiwa ya ƙaru"
"Mi kake nufi?" Gwamna ya faɗa yana ƙura masa idanu.
"Sir na sani cewa wannan Project an kawo shi ne dan amfanin jahar nan amma kuma kamar ya buɗe ƙofa ne na bawa 'yan adawa yunƙurin hamɓarar da gwamnatin ka. Miyasa aka attacking ƙauyen Kwom da maƙwabtanta, saboda Alhaji Umaru zai yi amfani da hakan wajen kamfen ɗinsa a zaɓe mai zuwa"
"Mi kake ga ya kamata nayi?"
COS ya ɗan ja numfashi kafin yace " abu biyu kawai za ayi kuma dukkansu akwai wahala"
"Ina jin ka"
"Ka sa a rushe shirin Project Tomatonion" wani kallo Gwamna ya watsa masa wanda ke nuni da hakan ba zai yiwu ba.
COS ya cigaba da magana "idan kuma aka cigaba da shirin to dole ne a tsara yadda za a kare rayukan manoma da gonakinsu, idan ba haka ba za ayi biyu babu. Shirin ba zai haifar da ɗa mai ido ba sannan za a yi asarar rayuka da dama."
Gwamna ya sauke ajiyar zuciya yana cigaba da kallon COS domin maganarsa akwai ƙanshin gaskiya.
Mr Lamara ya ɗan matso da kansa yace " har yanzu baka sanya hannu a kuɗin da za a siyo manyan injina da Kwamishinan noma ya buƙata ba. Inaga da wannan kuɗi da za a fitar za a iya amfani da shi wajen daƙile matsalar wannan hare-hare kafin ya fi ƙarfin Gwamnatinka. Idan kuma kana so jahar Congo ta faɗa cikin jerin jahohin dake fama da rashin tsaro a wannan ƙasa toh!"
Gwamna ya sa hannu ya cire hular dake kansa ya ajiye akan table kafin ya sa hannu biyu yai tagumi.
Tabbas duka zaɓi biyu babu sauƙi a gareshi. Tun kafin su dawo ƙasar nan Asiya ke masa waƙar shirin Project Tomatonion da yadda shirin zai kawo cigaba da alfanu da dama a jihar. Ba abu ne mai sauƙi ba cikin ƙasa da makonni uku da ƙaddamar da shirin ace kuma ya dakatar da shirin ko kuma ya cire tallafin da yake ƙoƙarin bawa shirin.
A ɗaya ɓangaren kuma idan babu zaman lafiya babu yadda za ayi ma a ɗabbaka shirin balle har aci gajiyarsa.
"Yanzu babu yadda za a yi muyi zaman sulhu da su 'yan ta'addan?" Gwamna ya faɗa bayan dogon shiru da yai.
" Your excellency banga yiwuwar hakan ba gaskiya"...
***
Alhaji Abdullahi na tsugunne gaban gawar 'yarsa da bazata wuce shekara shaɗaya ba. Ya sa hannun rigan sa ya fara goge mata kumfan da ke bakinta, yana yi yana zubda hawaye.
Yana jin mai aikin gidan tana sake yiwa babban ɗansa bayanin yadda ta shiga ɗakin yarinyar ta tarar da gawarta kusa da roban maganin ƙwari na snipper.
"Abba ya kamata mu je asibiti a tabbatar da sanadin mutuwar nan" babban ɗan Alhaji Abdullahin ya faɗa yana dafa hannun mahaifinshi.
"Yaushe har Abida ta yi wayon da za ta kashe kanta. This is murder" yai maganar ƙarshen cike da tsananin ɓacin rai.
Alhaji Abdullahi ya sake ƙanƙame gawar tareda faɗin "i'm sorry Abida, ki yafe min, ki yafe min kin ji". Haka ya cigaba da sunbatu yana rungume da gawar yaƙi sakewa.
Da ƙyar aka ɓanɓare Alhaji daga jikin gawar lokacin da ƙannensa da 'yanuwansa suka shigo.
Wannan abu ya faru ne lokacin 'yan gidan sun je biki a Lagos. Da alama yarinyar ta zaɓi kashe kanta ne a dai-dai lokacin da gidan yake babu kowa sai ma'aikata da kuma yayyunta maza biyu. Ita ɗin ma da ƙyar ta sha kafin mahaifiyarta ta yarda akan ba za ta je bikin ba. Kasancewar kusan wata guda kafin mutuwar yarinyar ta chanja gaba ɗaya ,shiyasa babu wanda ya kawo komai lokacin da ta nace akan ba za ta je biki ba duk da kuwa bikin na gida ne.
Alhaji Abdullahi bai tsananta bincike ba dan ya riga ya samu suicide note ɗin da Abidar ta bari kafin mutuwarta. Abinda ya ƙara gigita shi kenan saboda sanadin mutuwartata yai kama da abinda ya aikata kusan shekaru ashirin da takwas da suka wuce. Bai taɓa dana sanin abinda yaiwa Halima Kachallah ba sai yau. Ashe da ciwo aiwa 'yar cikin ka fyaɗe. Ashe da ciwo na kusa da kai yai wa 'yar cikin ka fyaɗe.
Mu'azu tamkar ɗan cikinsa yake, tun yaron yana rarrafe aka bashi riƙonsa. Har iyau kuwa yaron bashi da uban daya fi shi, amma...
**
Gwamna yana tareda Asiya suna tattauna batu mai mahimmanci kiran Alhaji Sani Kachallah ya shigo wayar sa. A rikice ya miƙe tsaye jin batun da Alhajin ke masa.
A take ya buga wayar Alhaji Abdullahi dan gaba ɗaya kan sa ya kulle da maganar da aka faɗa masa. Sai yau yake jin maganar fyaɗe da abokinsa yai wa Halima tun tana ƙarama, kafin nan ko a taɗi bai taɓa jin zance makamancin hakan ba.
"Excellency lafiya kuwa?" Asiya ta faɗa a ruɗe
Ba tareda Gwamna ya ajiye wayar ba ya fara gaya mata abinda Alhaji Sani ya faɗa masa. "Abida 'yar Alhaji Abdullahi ce ta kashe kanta yau da safe, suicide note data bari ya nuna cousin ɗinta ne yai mata fyaɗe har sau uku kafin tafiyarsa ƙasar waje. Wai kuma shigen abinda Abdullahin ya aikata kenan shekarun baya lokacin yana zaune a Kachallah House"
"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun! sakayya fa kenan tun daga duniya"
Da mamaki Gwamna ya kalli Asiya yace "kema kin san abinda ya faru da Halima ne?"
"Kwana biyu kafin aurenta take faɗa min, abin ya girgiza ni matuƙa. Na so na faɗa maka amma abubuwan da suka yi ta faruwa bayan bikin shi yasa na manta"
"Ban san mi zan ce ba Asya. Wannan abu da me yai kama"
"Allah dai ya raba mu da sharrin shaiɗan"
Gwamna ya amsa da Amin sannan ya ɗau wayoyinsa ya fice daga falon...
Ko minti uku ba ai ba da ficewar Gwamna kiran Halima Kachallah ya shigo wayar Asiya.
"Anty Asiya na shiga uku, na shiga uku ni Halima" tayi maganar cikin kuka.
"Ki dena faɗin haka, miya faru?"
" nina masa baki, nina sa Abida ta kashe kanta" ta ƙarisa maganar tana sake fashewa da kuka
"Innalillahi! wani irin magana ne wannan, dan Allah ki dena kuka. Ki dena irin wannan mugun tunani, abinda ya faru na daga cikin ƙaddarar yarinyar shiyasa hakan ya faru"
"Na sha yiwa Yaya Abdullahi muguwar addu'a da mummunan fata amma ba irin wannan ba. She's so innocent"
"Ya Allah! Ba laifin ki bane Anty Halimah"
Yadda Haliman ta dage tana kuka sai ga hawaye suna shirin wankewa Asiya fiska. Ƙarshe kashe wayar tayi ta dafe kanta tana jimamin wannan al'amari. Sai data samu nitsuwa sannan ta kira numbar Yaya Bello tace dan Allah yaje gida ya lallashi matarsa. Bata gaya masa dalili ba amma tasan idan yaje chan zai ji da bakinsa.
**
Lokacin da Gwamna ya dawo gida kusan ƙarfe shaɗaya na dare gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi. Abubuwa sun taru sun masa yawa. Batun mutuwar Abida dama bayyanar ainihin halin abokin nasa ya firgita shi sosai. Bai taɓa kawo cewa son matan Abdullahi har ya kai yai wa yarinya 'yar shekara tara fyaɗe ba. Eh aje lokacin yana saurayi ne, to amma ko a lokacin ai ya bawa Halima shekara kusan goma koma fiye da haka.
Bayan wannan kuma yanayin kallon da Alhaji Sani yai masa ya birkita shi matuƙa, kallone da babu ƙyallin soyayya ko farin ciki a cikinsa. Dama ya fara zargin ja baya da Alhajin ke yi dashi 'yan kwanan nan amma kuma yau ya tabbatar.
Ko dai da gaskene maganar da M Sani ya faɗa masa ranan a office cewa ya tozarta Baban sa.
"Uncle Saifuddeen yau na tabbatar cewa akwai ayar tambaya a kasancewarka jinin Kachallah. Ta ya za ka tozarta Grandpa a idon duniya. Baka ma ɗaura wanda darajarsa yazo kusan ɗaya da tashi ba sai ka ɗaura ɗan cikinsa, ɗan cikinsa fah. Wato don yaje fada ya tsugunna yana yiwa yaron bayansa ranka shi daɗe ko."
"Get out!" Gwamna ya daka masa tsawa. Sai dai hakan bai hana M Sani cigaba da magana ba.
"Uncle Sakayyar da zaka yiwa Uban daya raineka kenan, Uban daya sadaukar da komai dan ya ɗaura ka a wannan kujera. Inaga ka koma Gambia ka nemo iyayenka amma kai kam ba jinin Kachallah bane"...
Shigowar Asiya ɗakin ya sa shi yin firgigit daga tunanin daya ke yi.
"My love ya haƙuri" ta faɗa tana rungumeshi ta baya.
"Baba yana fushi dani Asya. I can feel it"
"Ka dena irin wannan magana, kai kan ka kasan yadda Baba ke son ka ko 'ya'yan daya haifa albarka"
"Da kenan Asya, a da kenan"
Bai sake magana ba sai ya miƙe zai wuce banɗaki, bin shi ta yi dan ta taimaka masa yai wanka amma sai ya dakatar da ita...
***
Hare-hare da ake kaiwa a ƙauyuka ya fara yin yawa domin mutane da dama sun sadaukar da gonakin su sun fara baro ƙauyukansu suna neman mafaka a cikin gari. Wannan dalili yasa Gwamna ya dakatar da shirin Project Tomatonion ba tareda shawara da kowa ba.
Asiya na gida itada Badawiyya suna bibiyar wani report da aka basu kiran Kwamishinan noma ya shigo wayarta.
Tana ɗaga wayar Kwamishinan ya sanar da ita hukuncin da Gwamna ya zartar.
"Mr Comissioner Sir, ban gane Gwamna ya ƙi saka hannu a kuɗin da muka nema ba"
Miƙewa tayi zumbur har sai da laptop dake kan cinyarta ya faɗo Badawiyya tayi ƙoƙarin tarewa amma sai daya kai ƙasa.
"Ban gane an terminating project ɗin ba, ban gane komai ba Sir. Ina zuwa zan zo office ɗin" ta ƙarisa maganar muryarta na rawa kaman za tayi kuka.
"Ranki shi daɗe miya faru?"
"Ki kira direba yanzu zamu je ofishin Gwamna"
Daga haka ta wuce wajen closet dan ta chanja kayan jikinta.
*
Lokacin da Asiya ta iso office ɗin Gwamna baya nan ya shiga wani meeting dan haka ta zauna jiransa.
Tana zaune hankalinta ya kai ga wani hoto dake kan table ɗinsa. Hoto ne na Gwamna da iyalinsa. Lokacin kamfen aka ɗauki hoton, sun yi matuƙar kyau sosai kowanne a cikinsu murmushi ne shimfiɗe a fiskarsa. Ta ƙurawa fiskar Junior ido chan sai ta fara ganin yaron a idonta dai-dai lokacin da ta zo ta tarar da gawansa. Hannunta ne ya ɗau rawa hakan yasa hoton ya faɗo daga hannunta kafin ta ankara har ya kai ƙasa glass frame ɗin ya tarwatse.
"Ya Subhanallah!" Asiya ta faɗa tana ƙoƙarin ɗauko hoton sai dai kafin hannunta ya kai an riga anyi sama da hoton. Bata ji shigowarsa ba, ko dan tayi nisa cikin tunani.
"Your Excellency yaushe ka shigo?"
Maimakon ya amsa mata sai yace " miya kawo ki Asya?, i'm very busy today"
Buɗe baki tayi zata yi magana sai ta kasa dan bata san taya zata fara ba.
Kusan sakan biyar kafin ta saita nitsuwarta sannan tace "maganar project tomatonion ne. Kwamishina yace ka ƙi saka hannu akan kuɗaɗen da aka buƙata"
"Ba wai naƙi saka hannu bane, na kashe project ɗin ne gaba ɗaya"
"You can't do this Excellency"
Hannunta ɗaya ya riƙo yace "duk abinda kika ga nayi to nayi ne dan al'ummar jahar nan. Hare-haren da ake kaiwa manoma yayi yawa..."
"Bilkisu ce ta gaya maka haka? ko kuma Chief of staff ɗinka?"
"Asya kina ganin jaridun da ake bugawa kullum kuwa? Kin ma ji hiran da Umaru Kwom yai jiya kuwa?"
"Your excellency na ƙaurace maka na kusan shekara guda duk dan na samawa gwamnatinka mafita amma abinda ke gabanka shine rubutun 'yan jarida!"
"Mutane biyu aka kashe jiya, rayuka biyu Asya, and many more will die idan aka cigaba da wannan project"
"Abinda suka faɗa maka kenan, abinda suka ce kayi kenan?" Asiya ta faɗa jikinta na rawa
"Asya na san yadda wannan shiri yake da mahimmanci a wajenki but you have to know that ina da hakkin kare kowanni mutum da dukiyarsa a jihar nan. Wannan shine sama da komai"
Hawaye ne ya taru a idanun Asiya, ƙoƙarin tare su take sai gashi sun fara zubowa.
"I'm sorry Asiya, i'm really sorry" ya faɗa yana ƙoƙarin rungumeta
Ɗago rinannun idanunta tayi ta kalleshi da kyau. So take tace masa shi rago ne kuma matsoraci amma sai kalaman suka mata nauyi a baki ta kasa faɗin komai. Duk yadda tayi yunƙurin magana sai hawaye ya zubo wannan ya bashi damar rungumeta jikinsa sosai yana bubbuga bayanta.
Kusan minti biyu suka yi a haka kafin Asiya ta zare jikinta ta goge fiskarta da kyau sannan tace
"Alfarma ɗaya nake nema a wajen ka" Gwamna ya zuba ido yana kallonta
"Dan Allah ka bari na gudanar da shirin nan koda ba da tallafinka bane"...
20
***
"Asiya"
"Asiya"
Badawiyya ta sa hannu ta dafa kafaɗar Asiya wacce tunda ta dawo daga ofishin Gwamna bata yi magana ba.
"Kin san kusan awa ɗaya kenan kina zaune a wajen nan baki ce komai ba. Ban damu da abinda Gwamna yace miki ba, ban damu da Project Tomatonion ba"
Wannan furucin yasa Asiya ta juyo a fusace, idan har Badawiyya bata yarda da shirin da take yi ba kenan aikin banza take.
"Kema baki yarda wannan shiri zai kawo cigaba wa jahar nan ba?"
Badawiyya ta zauna gefen gadon tana fuskantar Asiya da kyau.
"Na yarda da alfanun dake shirin ɗari bisa ɗari. Sai dai abinda na fi damuwa dashi shine lafiyar ki. A gabana likita yace akwai stress a jikin ki, na yi wani course a fannin ƙwaƙwalwa kuma bisa hasashena kina fama da both emotional and physical stress. Tun rasuwan Junior nake lura dake, kaman kin sawa kan ki cewa idan kika samu ciki kika haihu hakan zai sharewa Gwamna rashin Junior
"Ina so ki sani cewa ko 'ya'ya goma zaki haifa ba zai cire raɗaɗin mutuwar Junior a zuciyar Gwamna ba domin ba mutuwar kaɗe yake ji a jikinsa ba har da kasancewar hannun matarsa a wajen mutuwar yaron. Dan haka ki cire wannan tunani a ranki, zaki samu haihuwa a lokacin da Allah ya rubuta miki. Amma idan har kika cigaba da tafiya a haka to kwannan zaki yanki jiki ki faɗi ki mutu"
"Badawiyyah!" Asiya ta zaro ido waje
"Gaskiya nake faɗa miki. Lafiyarki ta fi komai mahimmanci domin idan babu lafiya babu wani buri naki da zaki cimma a karan kan ki ko a jahar nan"
Asiya ta sunkuyar da kanta tana sauke wani nannauyan ajiyar zuciya. Chan kuma ta ɗago tace
"Nagode Badawiyya, haƙiƙa ke ɗin 'yaruwa ce ta ƙwarai. Nagode sosai" ta faɗa a hankali, kamar kuma an tsikareta ta fara magana cikin fushi
"A zahiri na ɗauka Gwamna yana da ƙarfin zuciyar da zai iya juran kowanni yanayi domin a samu cimma nasara mai ɗaurewa, ban san cewa zuciyarsa tana da rauni ba. Ban san cewa zai bari Bilkisu ta dinga juya tunaninsa a kowanni lokaci ba"
"Kar ki ce na katse ki amma ranki shi daɗe Gwamna bashi da laifi, ko ince laifinsa ɗaya ne da bai iya siyasa ba"
"Amma Badawiyya..."
"Babu komai idan kika yi haƙuri zaki iya zama sandar jagoransa"
"Sandar jagora sai kace shi makaho ne" Asiya ta faɗa tana dariya
Badawiyya tace " a harkar siyasa shi makahone kece idanunsa"
"To ai gashi yana saka idanun nashi kuka"
Badawiyya ta ce "Shima zai ji a jikinsa ai"
Gabaɗaya sai suka saka dariya...
***
A chan ofishin Bilkisu Kachallah kuwa Chief of Staff Mr Lamara Damana ne ke zaune yana jiran isowar Bilkisu office ɗin domin lokacin da yazo ance masa ta fita. Dake sun yi waya yace yana hanya shiyasa ya zauna zaman jiranta.
"Boss akwai labari mai daɗi" abinda COS ya faɗa kenan dai dai lokacin da ta shigo office ɗin.
"Labari me daɗi shine kace min 'yar matsiyatan nan ta mutu" Bilkisu ta faɗa tana zama akan kujerarta.
"Gwamna ya kashe Project Tomatonion, inaga a dena bawa Tanko Janwuya makamai for now kafin lokacin kamfen"
Wata shegiyar dariya Bilkisu ta fashe dashi.
"Wait a minute, Lamara Damana i highly respect you saboda basirar ka, amma ban san cewa ƙwaƙwalwarka ta mutu ba"
Daga yadda COS ya ɗaure fiska zaka fahimci ransa ya ɓaci da maganar Bilkisu Kachallah.
"Kana tunanin na ciro Tanko Janwuya ne daga kurkuku dan yazo yai barazana na kwana biyu yai shiru. We'll continue the supply kamar yadda muka tsara domin yanzu aka fara zubda jini a wannan jaha"
Cikin rashin fahimta COS yace " me kike nufi?"
Bilkisu ta kalleshi ido cikin ido tace "zan maida gwamnatin Gwamna Saifuddeen Kachallah gwamnatin mutuwa, gwamnatin talauci, gwamnatin Allah ya isa"
"Kina ganin Asiya zata zauna shiru idan kika yi ƙoƙarin yin hakan?"
"Asiya bata san Saifuddeen ba. Ni na san waye Saifuddeen. Saifuddeen cannot stand people dying under his government... because he's a coward"
" kar kiyi gaggawar faɗin haka. Saifuddeen ya chanja fiye da yadda kika san shi..."
"kwanan nan Saifuddeen zai yi murabus daga kan kujerar sa"
COS yai ƙaramar dariya yace "mi zai faru idan yaƙi yin murabus?"
Shiru Bilkisu tayi na tsawon mintuna har sai da COS yai tunanin bata da abin faɗa. Sai kuma ta miƙe daga kujerarta ta ƙariso gabansa ta matso daf da fiskarsa tace " Saifuddeen Kachallah zai ƙarisa rayuwarsa da shanyewar duka jikinsa"
COS ya zaro ido waje.
"Mr Lamara Damana na san baka taɓa jin labarin anyi paralysed Gwamna ba ko?"
Kan Lamara Damana ya kulle da wannan batu. Wani alfanu Bilkisu zata samu idan Saifuddeen ya bar kujerar Gwamna. Matar tsohon Gwamna ai bata da wani daraja.
Kamar ta karanta abinda ke ransa sai tace " ina son rubuta tarihi a jihar nan. Ina son zama Deputy Governor na wannan jaha. Na san kasan mi zai biyo baya idan hakan ya faru"
"Boss Lady ba lallai..."
"Ni Bilkisu Kachallah zan zamo Gwamna a jahar Congo. Ni Bilkisu Kachallah zan zamo mace ta farko da zata zama Gwamna a jahar Congo"
Kamar COS bai ji mi tace ba ta ƙara ɗaga muryarta tana faɗin " I am going to be the governor of this state Mr Damana, just wait and see"...
***
A dai-dai gidan kurkuku dreban Asiya yai parking mota. Asiya ta fito daga motar fiskarta sanye da baƙin nose mask, shigar baƙar jallabiya tayi da gyale kalar ruwan ƙasa ba abin da kake gani sai kyawawan idanunta wanda suka ƙanƙance saboda rashin bacci.
Babu abinda ya chanja a gidan kurkukun, yadda ta san shi haka nan yake. Warden Bisola ce ta raka ta ɗakin Madam Chess a nan dai ɗakin da suka zauna lokacin da tayi zaman kurkuku.
"Ke da zaki sa a kirani mu gaisa"
"Mommy ban isa na sa a kira ki ba, nan ma ai gida ne"
"Inaaa! Ke yanzu kina da 'yanci ba abinda zai haɗa ki da gidan nan"
Bayan sun gaisa Asiya ta ce " Mommy kai na ya kulle, ina buƙatar shawaran ki"
Madam Chess ce tace " let's play a game"
Asiya tayi murmushi tace " yanzu kam zaki sha mamaki Mommy dan nima na zama pro"
"Bari dai mu ga"
Sun kai kusan minti shabiyar suna game ɗin amma kuma babu wanda yaci wani.
A minti ashirin da uku Madam Chess ta cinye Asiya a wasan.
"Checkmate your Excellency"
Asiya ta kama kai tana duba board ɗin da kyau, tabbas an cinyeta a wasan
Madam Chess tayi murmushi tace "kin yi ƙoƙari ai, sai dai ki sani ba a sarki biyu a fada ɗaya"
"Mommy dan Allah ki min bayani na fahimta"
"Ki tashi mata daga fadar ta. Build your own palace, build your own empire. Ki gina tsauni tsananin ku wanda ko ta hau gajimare ba zata iya tsallakawa fadar ki ba."
"Na bar mata gidan Gwamnati kenan?"
Madam Chess ta ɗau kofin dake gefenta ta kurɓi maltina da aka kawo musu...
Asiya bata gama fahimtar maganganun Madam Chess ba sai da ta je gida suka tattauna maganar da Badawiyya. Inda suka yanke shawaran barin gidan Gwamnati su koma chan gidan Saifuddeen.
Koda ta yiwa Gwamna magana bai musa mata ba musamman data nuna masa tana so tayi amfani da filin dake bayan gidan ne wajen yin wani aiki.
Bai san wani irin aiki bane amma dai ya bata goyon baya ɗari-bisa-ɗari.
Tun kafin a gama kwashe kayan Asiya Bilkisu ta samu labarin Asiya zata koma ɗaya gidan. Wannan yasa ta fara tunanin dalilin da zai sa Asiya ta bar gidan Gwamnati rana tsaka haka.
**
"My Governor lafiya?" M Sani ya tambaya ganin tunda Bilkisu ta gama amsa waya ta shiga tunani.
"Nothing, na ga kamar akwai nasara ne a shirin mu, yanzu aka ce min 'yar matsiyatan nan zata koma chan gidan Saifuddeen"
"Dole mu sa'ido akanta sosai dan dole akwai dalilin da zai sata barin gidan Gwamnati bayan a da ƙoƙarin fitar dake take daga gidan"
"Ba abinda zata iya yi a bayan idona, duka ma'aikatan gidan ni suke yiwa aiki"
*
A natse Asiya take yiwa Badawiyya bayani kan yadda tsarinsu zai kasance daga yanzu.
"Badawiyya yanzu ne za a fara yaƙi, yanzu ne za ki ɗau fansar abinda Madam Bintu ta miki, yanzu ne rayuwar mu zata shiga haɗari saboda idan muka fara wannan yaƙi babu gudu ba ja da baya"
"Na sani"
Asiya ta ɗauko ƙaton kwalban turarenta ta ajiye a tsakiyar table tace wannan itace Bilkisu Kachallah.
Ta ɗauko janbaki, eye pencil da wasu brushes tace "waɗannan sune muƙarrabanta da kuma ƙarfinta.
" Mr Lamara Damana shine na hannun damanta shine ke kawo mata duk wani information daga ofishin Gwamna. Tana amfani da kamfanin Madam Bintu wajen shigo da muggwan ƙwayoyi and ina zargin harda makamai ma. Wannan shine Alhaji Sani Kachallah shine mahaifinta kuma da sunan sa take tinƙaho. Wannan kuma Muhammad Sani ɗan yayarta wanda yake mata duk wani dirty work ɗinta"
"Who do we strike first?" Badawiyya ta tambaya idanunta cike da ɗoki
Asiya ta kalli Badawiyya tace " idan aka kama Madam Bintu da evidence dake hannunmu Bilkisu Kachallah zata yi watsi da ita zata ma yi ƙoƙarin kasheta saboda kada ta tona mata asiri. Zamu yi amfani da wannan dama wajen samun wasu shaidu na Bilkisu daga bakin Madam Bintu"
"Amma ya zamu yi da Muhammad Sani? yaron fa yana Asibiti har yanzu"
" kar ki damu ai gobara biyu zamu kunna"
Badawiyya tayi murmushin jinjinawa...
***
Yayinda shirin Project Tomatonion ta sukurkurce cikin ƙanƙanin lokaci tun ma ba a mori shirin ba. Mutane nata Allah wadai da Gwamnatin Saifuddeen Kachallah saboda ta kasa cika alƙawari, ga uwa uba rikici da ke ƙoƙarin cinye kudancin jahar.
A cikin wannan yanayi ne kuma Asiya ta fara gudanar da shiri a gidan talabijin mai suna ASIYA'S GARDEN. Da farko youtube channel ta buɗe take ɗaura shirin a kai sai daga baya ta nemi a saka shirin a TV. Shiri ne da take yi dan encouraging urban farming. Ta nuna cewa ko a gidan haya kake zaune zaka iya fara shuka wasu abubuwa masu sauƙi kamar su timatir, Albasa, Alayyaho, dankali da sauransu. Ta nuna yadda za ayi amfani da bokiti, tayar mota da kuma buhu wajen fara yin shuka.
Mutane da dama musamman mata a cikin gida sun yi ƙoƙarin gwada abinda tace amma basu ɗauke shi da wani mahimmanci ba sai dai bayan wasu kwanaki abinda suka shuka ya fara fitowa wannan ya basu ƙwarin gwiwar cigaba da kula da shukokinsu.
A ɓangare guda kuma kasancewar Project Tomatonion ya bi ruwa sai ya zamana jikin mutane yayi laƙwas da harkar noma. Sai dai kuma ba a jima ba aka fitar da wani tsari daga gidauniyar LIGHT FOUNDATION, gidauniya ce ta wani tsohon Reverend mai retire mai suna Reverend Buba John. Gidauniyar ta haɗa hannu da wasu NGO daga ƙasashen turai tareda amincewar Gwamnatin jiha wajen kawowa manoma wani tsari da zai basu damar samun bashin gona, taki, iri, dabbobi, da ma wasu kayan aiki da ake buƙata a harkar noma.
Da farko wannan shiri bai samu karɓuwa ba saboda wasu malamai masu tsatstsauran ra'ayi dama bagidadan mutane dake iƙirarin wannan shiri da gidauniyar ta kawo ba komai bane sai wata hanya ce ta yaɗa ɓoyayyiyar manufar Reverend Buba John. Maganganu dai kala-kala dake kushe ainihin manufa da alfanun shirin...
*
"Ranki shi daɗe haɗa hannu da Light Foundation ba zai ba da abinda ake buƙata ba. Mutanen da suka bada sunan su basu kai 5% na manoma ba fa."
Badawiyya ta faɗa tana nunawa Asiya Laptop da ta riƙe
"Relax, na san za ayi hakan"
"Kin sani kuma kika yi shiru"
"Reverend Buba ne kaɗai a faɗin jihar nan a binciken da nayi na gano cewa gidauniyarsa akwai gaskiya da amana. Ke da kan ki kika ce min gidauniyar Senator Mubarak ta kamfen ce ba dan al'umma aka kafata ba"
"To yanzu ya za ayi kenan tunda mutane sun ƙi ƙarɓan abin?"
"Na gaya miki zamu je fada gaisuwa ko?"
"Za ki yi amfani da Mai Martaba?"
Asiya tayi murmushi tace "Gaisuwa kawai zamu yi Badawiyya"...
**
"Something is fishy Mr Lamara, taya za ayi ace kwana biyu da zuwanta fada Sarki ya fito ya ƙaddamar da shirin Reverend Buba"
Mr Lamara ya ƙara duba jaridan hannunsa da kyau inda Mai Martaba Sarkin Congo da Reverend Buba suka haɗa hannu suna murmushi.
"Ba zan ce akwai hannun Asiya a ciki ba dan babu ta inda zata samu kuɗin da za ta sayi abubuwan nan"
"To ina Reverend ya samu uban kuɗin nan?"
"NGO mana"
"Oh please! Kai kan ka kasan ba duka kuɗaɗen da ake turowa ke shiga hannun Reverend ba.
"Wai ko dai Saifuddeen yabi ta baya ya bata kuɗaɗen nan ne?"
"No, da an fitar da kuɗin dole zan sani, beside kuɗin dayawa sosai Gwamna ba zai iya biya lokaci guda ba"
Bilkisu ta tura jaridar gefe tace " koma minene dai babu yadda za ayi shirin nan ya karɓu a wajen mutane"
"Mi kike so ayi?"
"Ka ɓatawa Mai martaba suna, ka chanja labarin..."
Sakatariyar Bilkisu ta banko ƙofar office da ƙarfi tana faɗin " sorry your excellency amma ban sani ba ko kin kalli news da ake yi yanzu?"
Bata jira Bilkisun ta amsa mata ba ta ɗau remote na tv ta chanja zuwa tashar Hill TV.
"Bayan wannan video ya fito hukumar NDLEA ta bayyana Madam Bintu Chadi a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da take nema ido rufe. Yanzu haka bincike da ake yi a cikin gidan Madam Bintu ya daɗa tabbatar da cewa ita ɗin ficacciyar mai fataucin miyagun ƙwayoyi ce"
Bilkisu Kachallah ta miƙe zumbur ganin an nuno gidan Madam Bintu inda ake fito da tsagoron bandir-bandir na kuɗi kama daga kuɗaɗen Nigeria har na ƙasashen waje.
Mai karanto labarin ya cigaba " ba iya nan ya tsaya ba. 'Yar sanda mai retire wato Rabi'atul Badawiyya Kabir tana iƙirarin Madam Bintu da kashe mata jariri da yunƙurin kasheta shekaru kusan goma shabakwai da suka wuce, sannan ta sake tuhumarta da cinye dukiyar mijinsu wato marigayi Alhaji Rufa'i"
"Oh my God!" Bilkisu ta faɗa tana dafe ƙirji...
21
***
Kwana biyu ana neman Madam Bintu amma babu dalilinta. Ita kanta Bilkisu Kachallah bata san ina matar ta shiga ba balle ta san yadda za ayi ta taimaketa. Ta dai baza mutane ko'ina akan a nemo mata Madam Bintu kota halin ƙaƙa.
A ɓangaren Asiya kuwa ta samu labarin Madam Bintu shigar maza tayi ta bi motar akori-kura aka fice da ita daga cikin gari. Bata san takamaimai wani ƙauye ta ɓoye ba amma tasa a binciko maɓoyarta kafin Bilkisu ta gano inda take...
***
Sumayya da Jummai suna zaune a falo suna faɗa akan remote ɗin TV Badawiyya ta shigo falon da sallama.
"Anty Badawiyya" suka faɗa a tare suna rige-rigen rungumarta.
"Duk ranan dana shigo gidan nan na same ku a nutse zan muku kyauta"
"Anty Wallahi ita ce ta raina ni"
Sumayya ta faɗa tana hararan Jummai
Jummai tayi caraf ta amsa "Wallahi Anty ni nayi resfek ɗinta sosai, ita ce take da kishin tsiya"
Badawiyya tayi murmushi tace " to ki cigaba da resfek ɗinta dan ta girmeki kin ji"
Sumayya ta tintsire da dariya ganin Badawiyya ta biyema Jummai.
Tunda Jummai taji kalmar (respect) a bakin Asiya watarana da take musu faɗa shikenan ta kama, magana ɗaya biyu sai ta nemi dalilin da zata jefa kalmar ciki.
Ita Sumayya tunda ta nemi gyara mata kalmar akan ba dai-dai take faɗa ba Jummai ta hayayyyaƙo mata sai ta haƙura ta barta.
A kitchen Badawiyya ta samu Asiya tana sauke wannan ɗaura wannan. Dan abin ya bada armashi ma har apron ta saka da doguwar hular nan irin ta masu dafa abinci.
"Gaskiya ne tawan, girki sai kace ana competition"
"Dan Allah duba min oven ina jin kazar nan ta gasu" Asiya ta faɗa tana kwashe dankali daga cikin mai.
Bayan Badawiyya ta fito da kazar ta kalli Asiya cikin zolaya tace " Excellency kaza kam ta ƙone fa"
"Haba" Asiya ta juyo a firgice
Ganin yadda Asiya ta ƙwalalo ido waje sai Badawiyya ta sa dariya tana turo mata tray ɗin gabanta.
"Amma Rabi'atu zan..."
Badawiyya ta haɗa hannu biyu tana faɗin " sorry ma"
Tare suka ƙarisa girkin suka kai falon Gwamna suka jera. sai da suka gama komai sannan Asiya ta samu daman sauraron abinda ke tafe da Badawiyya.
"Mun samu abinda muke nema akan Alhaji Sani Kachallah. Har abinda bamu yi tunani ba mun samu"
"Mi kike nufi?"
Badawiyya ta miƙa mata wasu takardu tace " Alhaji Sani Kachallah ya jima yana badaƙala da dukiyar jama'a. Wannan da kike gani list ne na duk wasu kwangila da aka karɓa a hannun Gwamnati amma ba a ƙarasa ba wasu kuma ba a ma fara ba kuma an cinye kuɗin"
"A ina aka samu waɗannan takardu haka. Waɗannan kwangilar ai akwai na shekaru ishirin baya ma, tun 90's fa. Wa yake bamu waɗannan confidential information haka?"
"Wanda ya bamu shaida akan M Sani shine ya bada wannan" Badawiyya ta amsa mata
Asiya ta zaro ido waje dan mutum ɗaya take tunanin ya aiko musu da Shaidar da zai tarwatsa M Sani, kuma yanzun ma shi take tunanin ya aiko wannan to amma miyasa zai yi hakan?
Badawiyya ta ce "yes shi ɗin ne dai da kike zargi tun tuni. Na sa an bincika min numbar motar mutumin da ya kawo takardun nan kuma an faɗa min sunan sa ne akan rajistar motar"
"Akwai wani abu a ƙasa Badawiyya, ba yadda za ayi ya bamu evidence irin wannan sai dai idan wani abu yake nema"
"Nima abinda nake tunani kenan, ni a tunanina ina ga so yake yai amfani dake ya kawar da Bilkisu"
"He's dangerous Badawiyya, ba wannnan kaɗai ne a ransa ba, ni nafi tunanin so yake ya kawar da Gwamna dan ya cimma burinsa"
"Kina nufin irin abinda aka yiwa Saminu Bacchi?"
"Eh mana" Asiya ta amsa cike da damuwa a ranta.
Itama Badawiyyan shiru tayi tana nazarin wannan batu tabbas biri yai kama da mutum, idan ba haka ba taya Mr Lamara Damana zai so taimaka musu ba tareda sun buƙaci taimakonsa ba...
***
Mr Lamara Damana yana zaune a office ɗinsa aka kira shi aka sanar dashi Gwamna ya shigo gari wani ƙayataccen murmushi yai domin ya hango nasara a tarkon daya haɗa.
A hankali ya fara juyi da kujerarsa, tabbas nan bada jimawa ba wannan kujera da ya ke kai zata koma kujerar Gwamna.
Kalaman Yallaɓai ya tuna lokacin daya je masa da buƙatar Bilkisu Kachallah.
"Lamara Damana na jima ina karantar ka, na san mi kake so, na san kuma minene burin ka. Shawara ɗaya zan baka kuma ko bana nan ita ce zata taimaka maka"
A lokacin da Yallaɓai yai wannan magana ko kaɗan bai ɗauki maganar da mahimmanci ba amma kuma bai manta da maganar ba tana nan a ƙasan zuciyarsa.
"Dama ta kan zo wa mutum lokaci guda ne a rayuwa, idan ta wuce ta tafi kenan har abada, abinda ya rage shine mutum ya cigaba da bincike yana neman wata damar daban amma ba wancan data wuce ba. Wannan kuma ya rage ga ƙaddararsa, walau ya samo wata damar mai kamar waccan ko wadda bata kaita ba, walau kuma ya cigaba da nema har ƙarshen rayuwarsa ba tareda ya samu ba.
"Mr Damana kana da dama ɗaya na zama Gwamna a jihar nan, idan ka bari ta suɓuce maka zaka ƙare rayuwar ka cikin nemar wata damar amma kuma ba zaka taɓa samu ba"
Kusan shekaru uku kenan da Yallaɓai ya masa wannan magana amma kuma sai yanzu ne ya fahimceta da kyau.
Yanzu ne yake da damar zama Gwamnan jihar Congo kuma ba zai taɓa bari wannan dama ta kufce masa ba.
Daɗin abinma yana zaune ba tare da wahala ba dukkan wani shiri da ya tsara zai cimma nasara.
Bilkisu tana son ture Gwamna daga kujerarsa. Ita kuma Asiya tana son ture Bilkisu daga jikin Gwamna.
Babu abinda zai yi illah yai amfani da Asiya ya kawar da duk wani wanda zai kawo masa cikas wajen cikar burinsa.
Asiya ita ce maganin matsalarsa
Da wannan tunani ya yai amfani wajen tsara duk wani tarko daya ɗana, kuma yau ɗin nan ɗaya daga cikin tarkon daya kafa zai kama zomo.
Mr Lamara Damana yai murmushin gefen baki haɗe da jijjiga kansa a hankali cike da farin ciki...
***
Asiya da Badawiyya na tsaka da magana suka jiyo ƙaran siren daya karaɗe gidan.
Wannan yasa Asiya ta bircike ta rasa ma mi zata yi. Wanka zata yi a'a a haka zata fita ta tari Gwamna ko kuma dai ta chanja kaya kawai tunda tayi wanka da safe.
"To ni dai barin tafi dan na san tunda His Excellency ya dawo na tashi a aiki"
ba ta jira amsar da Asiya zata bayar ba ta miƙe ta bar ɗakin.
Jin tsayuwar motoci yasa Asiya ta yi haramar shiga banɗaki kawai tayi wanka kar ya shigo ya sameta a haka.
Ba ƙaramin kewarsa tayi ba shiyasa ta masa tanadi na musamman...
Tun da su Jummai suka jiyo jiniya suka fito harabar gidan da gudu. Dukkansu sun jima basu ga Gwamna ba.
Ita Sumayya a hostel take kwana sai dai ba a sati biyu bata leƙo gidan yayarta ba, ita kuma Jummai boarding school na Federal Government Girls College Congo aka sakata, tana JSS two dan kafin a kaitan sai da Asiya ta sa aka mata lesson na kusan wata huɗu.
Wannan karan dukkansu biyun suna hutu shiyasa suka zo yiwa Asiya hutun sati biyu kafin su wuce ƙauye.
Tun kafin Gwamna ya fito daga mota Jummai ke ta waƙar gaisuwar da zata masa a ranta.
Tunda Gwamna ya fito yake ta sake murmushi har ya iso inda suke tsaye.
Sumayya ta risina tace " Uncle Barka da dawowa"
"Good afternoon Eselensy Gomna Sir, how yuwa joney"
Sumayya ta tintsire da dariya.
Ba Sumayya kaɗai ba su kansu escort ɗin Gwamna sai da suka ɗan dara.
Gwamna yai murmushi tareda shafa kanta yace "kin yi ƙoƙari Nana, ki cigaba da ƙoƙari kin ji"
" Insha Allah Uncle Gomna" Jummai tayi maganar tana hararan Sumayya
Chan ƙasan ransa wani kewa da shauƙin 'ya'yansa ya kama shi. Yaso ace yaje ya duba Mahirah da Nana tun waccan watan amma bai samu dama ba.
In dai har gyaran da yai alƙawarin yiwa jiharsa yake son yi to tabbas dole ne ya rage tafiye-tafiye. To amma kuma 'ya'yansa ma suna da hakki akan sa.
Dole ya ware sati guda ya je ya duba Mahirah a Sudan sannan yaje ya duba Nana a US.
Da wannan tunanin Gwamna Saifuddeen ya shiga gida.
Ɗakinsa ya fara shiga wanda ƙanshin da yai arba dashi a falo ya tabbatar masa ba ƙaramin tanadi aka masa ba.
Ganin bata ɗakinsa ya sa shi cire babban rigar sa ya ajiye akan gado, ya cire takalminsa ya saka room slippers ya fito daga ɗakin ya nufi ɗakin Asiya.
Ƙoƙarin fitowa daga banɗaki Asiya take taji ƙaran buɗe ƙofan ɗakinta.
Shikenan har ya iso bata shirya ba, ta furzar da iska ta baki sannan ta buɗe ƙofar banɗakin.
Kallon-kallon suka tsaya yiwa junan su kowa da abinda ke ransa, amma abu ɗaya suka haɗu akai wato kewa.
Gwamna ya sake mata wani murmushi wanda ya fidda fararen haƙoransa.
Yadda yai murmushin ya ƙara bayyana tsananin gajiyar dake tattare da shi.
Ware mata hannayensa yayi yana cigaba da yi mata murmushi.
Itama murmushin ta sake masa sannan ta ƙarisa ta shige jikinsa ta ƙanƙame ƙugunsa da kyau.
"I miss you" ya faɗa yana kissing wuyanta, kafin ta bashi amsa ya lalumo bakinta ya haɗe da nasa. Kaman jira take yi ta ƙara shiga jikinsa sosai tareda tallafo kansa tana kissing ɗinsa sosai...
Rabon da su kasance da juna wane sati uku. Wannan ya haifar da wani kewa da shauƙi na musamman a tarayyarsu ta yau. Tanadin da ta masa yayi aiki domin in between kisses yake ta maimaita kalmar 'I Love You Asya'
Tare suka yi wanka amma shi ya rigata fitowa saboda wankan tsarki da tayi yasa take ta busar da gashin kanta da blow dryer.
Towel ne kawai a ƙugunsa lokacin daya zauna bakin gado yana ƙara goge kansa da ƙaramin towel. Idonsa ne ya faɗa kan wani ƙaton brown envelope dake kan side drawer, bai san ya aka yi zuciyarsa ta ingiza shi da buɗe envelop ɗin ba, dan a tunaninsa a ciki ne surprise ɗin da ta ce zata bashi yake. Idan kuwa ya kasance ticket ne na jirgi zuwa Sudan zai fi kowa farin ciki da hakan.
Sai dai kuma yana ɗaga envelope ɗin ya ji ta da nauyi sosai, kamar ba zai buɗe ba sai kuma wata zuciyar tace ya buɗe.
Takardar farko daya ci karo dashi ya sa shi miƙewa tsaye zumbur. Hannunsa yana rawa ya fara bin takardun da kallo a tsanake.
Jin alamar ana shirin buɗe ƙofa yai saurin maida takardun ya ajiye envelop ɗin.
Yi yai kamar bai ga komai ba ya dai-dai ta fiskarsa.
A haka ya daure har ta gama shafa masa mai ya miƙe yace zai je chan ɗakinsa ya sanya kaya.
Itama ɗin kaya kawai ta saka ta ɗan gyara fiskarta kaɗan tunda abinci zasu ci. Floral Abaya da ta saka kalar ruwan goro ya mata kyau sosai. Ta feshe jikinta da turaruka sannan ta fita.
A falonsa ta same shi yayi tagumi, duk wani walwala data saka shi mintina kaɗan da suka wuce babu shi a fiskarsa.
"My love lafiya kayi tagumi" tayi maganar tana cire hannunsa
Maimakon ya bata amsa sai kawai ya miƙe ya wuce ɗan ƙaramin dinning dake haɗe da falon.
Jikinta yai sanyi laƙwas, ɗazu-ɗazun nan yake maƙale da ita kamar zai cinyeta amma yanzu kuma ya sauya.
"Mijina akwai abinda ke damunka ne? Maganar ma'aikata da za a ɗauka ne?"
Bai amsa mata ba ya fara ƙoƙarin serving abinci da kansa tayi saurin karɓe serving spoon ɗin ta fara ɗiba masa jikinta a sanyaye.
Sai data gama zuba masa abincin ta tausasa muryarta tace " Dan Allah kayi haƙuri da koma minene ke damunka, idan ma nice na ɓata maka rai ka yafe min. Na sani ba ka ji daɗin yadda na cire ka daga project da nake yi ba, na yi hakan ne domin na san akwai ayyuka a gabanka sannan baka yadda cewa project ɗin zai kawo alkhairi a jihar nan ba. Kuɗin dana samu na endorsing foundation na Reverend Buba kuma Wallahi grant (tallafi) ne na samu daga turai, dama na jima ina nema in case babu kuɗin da za a funding project ɗin sai Allah yasa kuma suka bani a dai-dai lokacin da kace a katse project ɗin gaba ɗaya"
Hawaye suka taru a idonta dan har ga Allah taimako take son yi ba wai bijire masa ba.
Yana sauraron bayanan ta amma abinda yake son ji ɗin bata faɗa ba. Shi maganar project ɗinta bai dame shi ba musamman daya kasance mutane sun rungumi loan daga hannun Reverend tun lokacin da Mai Martaba ya fito yace shima ya karɓi bashin iri da takin zamani daga hannun Reverend.
Abinda ya gani a ɗakinta yake so tayi magana a kai, dalilinta na son kashe masa mahaifi yake son ji, dalilinta na son tozarta danginsa yake son ji.
"My love please forgive me" Asiya ta faɗa tana ɗaura hannunta akan nasa
Ajiye cokalin hannunsa yai ya kalleta da kyau sannan yace " yaushe kike da niyyar faɗa min? Ko so kike sai kin kai shi kurkuku zaki fito ki faɗa min komai?"
Ta ɗan zaro ido waje cikin rashin fahimta.
"Ko kuma dai so kike baƙin ciki ya kashe min shi"
"Your Excellency ban gane maganar ka ba"
"Na ga takardun da ke ɗakin ki. Na san abinda kike shiryawa a bayan idona"
"Ya Subhanallah! Ba abinda kake tunani bane"
"Mi nake tunani Asya? Minene dalilin da zai sa ki nemo shaidu akan abubuwan da Baba ya aikata shekaru kusan ishirin da suka wuce. Tell me Asya, mi kike shirin yi?"
Asiya ta haɗiye yawu da ƙyar tana tunanin ta ina zata fara masa bayani. Shaɗaf ta manta bata ɓoye takardun ba lokacin da Badawiyya ta fita
"Ina jin ki" ya katse mata tunani
"Wallahi ba abinda kake tunani bane. Yes na jima ina tara shaidu akan mutanen da suka saci kuɗin jiha, ina so ne nayi amfani da shaidar wajen yi musu barazana da hukumar EFCC dan su fito da wasu kuɗaɗen da suke dannewa sannan su barka ka yiwa jihar nan aiki"
"You are very stupid Asya. Mahaifina kike iƙirarin zaki turawa EFCC, it seems kin manta cewa duk abinda na zama a rayuwa to dalilin Baba ne. How could you"
"Sai me idan mahaifinka ne. Alƙawari ka ɗauka akan zaka yi shugabanci da gaskiya, amanan talakawa ka ɗauka Saifuddeen Sa'ad Kachallah kuma dole ne ka sauke da daɗi ko ba daɗi idan har kana son gamawa da duniya lafiya"
"Ba ni ke Gwamnati ba lokacin da Baba ya aikata laifukan nan, that was in the 90's Asya"
"Alhaji Sani Kachallah ya cinye kuɗin kwangilar da aka bashi na yin tituna a ƙaramar hukumar Gandu da Taƙal da wasu ƙauyukan da ban ma san sunansu ba. And we are talking about millions of nairas your Excellency. Sannan ko shekara biyu ba ayi da bashi wannan kuɗin ba. Gaya min a Gwamnatin ka ne ko ba a Gwamnatin ka bane?"
Tabbas ya bada kwangilar kuma tabbas ba ayi aikin ba, kuma har yau bai bi ta kai ba. Ya bada kwangilar ne lokacin da baya cikin hayyacinsa, ya bada kwangilar ne lokacin da ba zai iya banbance gaskiya da rashin gaskiya ba.
"Why are you doing this Asya, ki bari na gama Gwamnatin nan lafiya. Kin sani dana tona asirin Baba gara na ajiye kujerata"
Hawaye ne suka fara zubo mata dan yau kan ta gama tabbatarwa kanta cewa ita kaɗai ce ke kiɗa da rawanta Gwamna Saifuddeen baya biye da ita a tsarin data shirya na yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma ɗaukaka darajar jahar su.
Abu ɗaya ne bata sani ba, shin dama tun asali bashi da niyyar yiwa jihar nan hidima ne ko kuma dai har yanzu influence na Bilkisu ne ke jikinsa?...
22
A wannan rana Asiya ta kasance cikin fargaba da tsoro. Bayan tafiyar Gwamna ta jima tsaye tana hawaye kafin daga baya ta koma ɗaki ta kwanta.
Haka ta wuni bata ci komai ba.
Kusan ƙarfe bakwai na dare Agent Dahlia ta kirata tana yi mata albishir akan an samu nasarar cafke Madam Bintu a filin jirgin ƙasa tana shirin barin gari bayan tayi shigar tsohuwa. Ko kaɗan labarin bai faranta mata rai ba ta dai amsa da to sannan ta kashe wayoyinta gaba ɗaya.
Har dare Gwamna bai dawo ba kuma alamu sun nuna bashi da niyyar dawowan domin agogon ɗakin Asiya ya doka ƙarfe shabiyun dare kusan mintuna takwas da suka wuce.
Kusan ƙarfe ɗaya saura motocinsa suka shigo gidan, bata yi wani harama dan ta tarbeshi ba dan tasan ɗayan biyu ne. Ko dai ya zo ya sameta a ɗakinta ko kuma ya wuce nashi ɗakin.
Duk da bata saka ran cewa ɗakinta zai zo ba sai ga shi yana ƙwanƙwasa mata ƙofar ɗaki.
A matse take taji mi zai zo da shi dan haka a bugu na uku ta buɗe masa ƙofar ta matsa masa ya shigo ba tareda ta iya kallon fuskarsa ba.
"Na zo ne na faɗa miki hukuncin dana yanke"
Da sauri ta ɗago ido ta kalleshi, duk da faɗuwar gaba da take ji hakan bai hanata tunowa da tarayyarsu ɗazu da rana ba.
"Za ki ajiye duk wani abu da kike da shi akan Baba. Idan kika yi haka zan yi resigning a kan kujerar Gwamna.
"Asirin Baba ba zai tonu akan idona ba Asya"
Wata dariyar rainin hankali ta yi sannan ta zauna bakin gado tana kallonsa ido cikin ido.
"Wannan umurni ne a matsayina na Miji ba a matsayina na Gwamna ba"
"Idan na ƙi fa?" Ta faɗa kai tsaye dan yanzu haushi ya fara bata daya fito da tsantsan son ransa a fili.
Ƙarisowa yai ya zauna kusa da ita tareda kamo hannunta biyu ya riƙe su gam sannan ya fara magana
" kina tunanin na faɗi wannan ne saboda son zuciya? Asya idan aka fitar da waɗannan takardu ba Baba kawai maganar zai shafa ba. Zai shafi wasu makusantan Baba kuma hakan zai iya jawo asarar rayuka. Ban shirya rasa ki ba, ban shirya rasa wani nawa ba. Zan yi resigning, zan ajiye kujerar nan, we can forget about all this. Na yiwa Baba magana kuma na san zai ƙarisa ayyukan kwangilar da aka bashi sannan zai dinga maida kuɗin a hankali har ya gama maida duka kuɗaɗen"
Tayi saurin katse shi da cewa
"Na yadda ba zan miƙa takardun ba. Amma kada ka manta alƙawarin da ka ɗauka ranan da aka rantsar da kai. Ka tuna cewa duk abinda ka aikata zaka yi bayani a gaban Allah"
Maganarta ta shige shi sosai dan har hannunsa ya fara rawa.
Ta zare hannunta daga nashi ta ɗago kumburarrun idanunta ta kalli cikin idanunsa tace " zaka yi resigning saboda tsoron Allah ko dan gudun maganar mutane?.
"Hmmm! kana tunanin ni kaɗai ce ke son ganin bayan Alhaji Sani Kachallah?. Akwai abubuwa dayawa da baka sani ba your Excellency ko kuma nace kake tsoron sani"
"Asya..."
"Zan cire hannuna akan case ɗin Madam Bintu Chadi amma ka sani dole ne Badawiyya ta ƙwaci haƙƙinta.
Zan cire hannuna a duk wani abu daya shafi ahalin Kachallah. Sai dai akwai ɗaya wanda na riga na miƙa shi hannun Human Rights kuma kwanan nan za a shigar da ƙara"
Da sauri ya zaro ido waje dan a gurguwar tunaninsa ya ɗauka maganar mutuwar Junior ta kai Human Rights.
Miƙewa ta yi ta je ta ɗauko wani file cikin drawer dake gefen gado ta kawo masa.
"Ka buɗe" ta faɗa tana masa wani irin kallo mai ɗauke da tuhuma.
Yana buɗe file ɗin yaci karo da wani hoto. Abinda ya gani a hoton ne ya sa shi kallonta a firgice.
"Ka karanta takardun ciki zaka fahimci abinda hoton ke nufi"
"Dan Allah ki gaya min abinda ke ciki Asya"
Murmushin gefen baki tayi sannan tace " Sa'idu Musa ɗan shekara shahuɗu kenan, wanda aka yiwa fyaɗe. Ko ince anyi wata biyar ana luwaɗi da shi. Kamar yadda ka gani a hoton aiki ake masa a bayansa saboda infection daya ruɓar da takashinsa"
Hawayen da suka zubo mata tayi saurin gogewa sannan tace "Sa'idu Almajiri ne da ya gudu daga makarantar su a chan wani ƙauye wai Kantu. Aikin wanki da guga aka ɗauke shi amma aka dinga luwaɗi da shi, da aka ga ya fara ciwo aka bashi dubu hamsin aka kore shi tareda gargaɗi mai tsanani. An samu yaron ne dai-dai yana ƙoƙarin rataye kansa"
Baki na rawa Gwamna yace "wa?... waye ya aikata haka? Waye wannan? "
"Ka duba sauran hotunan"
Gwamna ya maida dubansa ga file ɗin sannan kaman wanda aka zarewa laka haka ya buɗe file ɗin a hankali ya fara duba hotuna da kuma takardun dake ciki, sunan daya gani bai firgita shi ba domin suna ne gama gari sai dai cak ya tsaya lokacin daya ci karo da wani hoto daya sa numfashinsa ɗaukewa na 'yan daƙiƙai.
"Ɗan...ɗan Rufaidah!" ya faɗa yana kallon Asiya kamar dai yana jira ta tabbatar masa abinda ya gani.
"Ya Subahannallah!" Yai saurin riƙe goshin sa dake wani mugun sara masa.
"shima a dakatar da shari'ar ne har sai ka sauka daga kujerar Gwamna?"
Shiru yai yana jin wani raɗaɗi na mamaye ilahirin jikinsa, lokaci guda kuma numfashinsa ya fara sarƙewa.
"Your Excellency" Asiya ta faɗa tana ƙoƙarin riƙe shi. Da ƙyar ta iya zaro inhaler daga aljihunsa ta bashi ya shaƙa sannan ta tallafa masa ya kwanta akan gado.
Kusan minti goma yana kwance abubuwa da dama na yi masa yawo a ka . Chan kuma kamar wanda aka tsikare shi ya miƙe ya ɗau file ɗin ya fice daga ɗaki ko sauraron Asiya dake masa magana bai yi ba.
Tunda ta ji ƙaran fitan mota ta san ba zai kwana gida ba. Addu'arta ɗaya Allah ya tsare shi.
***
Washegari labarin kama Madam Bintu ya baza gari. Duk wanɗanda ke da alaƙa da harkokinta sun fara barin gari, wasu kuwa duk sun ƙona takardun da suke ganin zai iya zama shaidar harkokin kasuwancin su.
Bilkisu Kachallah ta shiga wani hali tun jiya da dare zuwa yau da safen nan da take ganin yadda ake tisa ƙeyar Madam Bintu cikin motar 'yan sanda. Kwanaki kusan takwas da Madam Bintu tayi a ɓoye sun bayyanar da ainihin tsufarta wanda zallar mai da kwalliya ke ɓoyewa a baya. Yadda cinyayyen gashinta yai buzu-buzu kace mahaukaciya ce sabuwar kamu.
Ta kira duk wani contact nata cikin kwanakin nan amma duk abu ɗaya ake gaya mata abinda aka samu game da Madam Bintu zai iya shafarta madamar Madam Bintu ta buɗi baki ta ambaceta cikin shari'ar da za a fara.
Ba wannan bama bata gama gane mi Gwamna ke nufi da hotunan daya nuna mata jiya ba. Duk da kuwa ta ƙaryata komai amma kuma yanzu da komai ke dawo mata dalla-dalla sai ta fara tunanin matsalar da zata shiga idan maganar nan ta fito waje. Ita ce ke ƙoƙarin maye gurbin Saifuddeen kuma tabbas idan aka jonata da Bintu ko M Sani mutane zasu zargeta su yi kokonto akan shugabancinta.
Wai taya ma M Sani zai mata haka ne?
Mi ya rasa a rayuwar nan da zai fara bin maza. Ƙarin abin takaicin ma wai ya auri namiji a US shekaru biyu da suka wuce kuma wai har sun rabu bayan matar (namiji) tayi ƙaransa bisa cin zarafinsa daya ke yi.
Takardun saki da Saifuddeen ya nuna mata jiya ya tabbatar mata da cewa M Sani ya dawo Nigeria ne bayan ya rasa fiye da rabin dukiyarsa ga matarsa mai suna Scott Green.
Bilkisu ta zauna akan kujera tana ƙara gwada numbar M Sani wanda tun jiya take a kashe.
Tana cikin juyayin wannan abu wayar COS ta shigo, da sauri ta amsa dan kuwa dama tana son magana da shi.
"Mr Lamara mi yake faruwa?"
"As you suspect Asiya ce ta bada lead aka kama Bintu. Har yanzu ban samu damar ganawa da ita ko lauyanta ba amma..."
"Ina so shari'ar ta tsaya iya kanta, kayi duk abinda zaka yi ganin bata ambaci sunana ba" Bilkisu ta katse shi
"Matsalar shine bamu san mi Asiya ke da shi game da ke ba, in dai Bintu ce na tabbata zata riƙe amanar ki"
"I'm counting on you Mr Lamara akwai wani abu a ƙasa bayan na Madam Bintu"
"Your Excellency mi kenan?"
Shiru tayi na 'yan daƙiƙai tana nazari kafin tace "ina ga zamu matso da plans namu gaba"
"Ba kya ganin ya kamata ki bari abubuwa su lafa tukunna"
"Yanzu ne nake da dama, this is the best chance i've got. Idan Gwamna ya kwanta ciwo zan samu soyayya da tausayi daga wajen mutane"
Daga inda COS ke zaune ya ɗan sassauta murya yace "ba kya ganin mutane zasu fi tausaya wa Asiya, ba kya ganin ita kanta Asiya zata so kujerar da kike so?"
Maganar da yai ta dake ta, dan take taji tana tunanin yiwuwar abinda ya faɗa. Fiye da rabin cabinet na Gwamna mutanen Asiya ne yanzu sannan sunanta ya kama bakin mutane tunda ta fara program ɗinta.
Mr Lamara yayi gaskiya, ko dan ta cigaba da legacy na Saifuddeen zata so kujerar sa.
"Hakan ba zai yiwu ba" ta ɗan shaƙi numfashi sannan ta cigaba
"Domin mutuwar ta shine dalilin rashin lafiyar Saifuddeen"
Ajiye wayar tayi sannan ta miƙe ta wuce ɗakinta da sauri...
Daga ɓangaren Mr Lamara kuwa murmushin farin ciki yai domin yana jiyo ƙamshin nasara a kusa da shi.
Har ma Bilkisu zata ambaci wannan lokaci da damar ta. Wannan damar sa ce, kuma tsaf zai yi amfani da ita yadda ya kamata.
Ya fara yiwa Bilkisu saran ɓoye ne tun lokacin da ta fara fifita M Sani akan sa.
Tuni ya baza mutanensa dan ganin an nemo masa tarihin M Sani na baya da kuma a yanzu. Ya sani saurayi kaman M Sani ba zai taɓa rasa dirty past ba.
Cikin sati uku aka gama tattara masa duk wani bayani daya ke so, bai yi mamaki ba da ya ga labarin aure da saki tsakanin M Sani da Scott Green.
Sai dai abinda ya bashi mamaki kuma ya ja hankalinsa shine maganar luwaɗi da ƙananan yara da aka ce yana yi. A kan wannan maganar ne ya fitar da maƙudan kuɗi dan ganin an kawo masa sahihin labari da shaida akan fyaɗe da yake wa ƙananan yara maza.
Lokacin da aka kawo masa labarin Almajiri Sa'idu ya so ya shigar da ƙara amma daga baya wata zuciyar tace ya tura bayanan daya tattaro ga Asiya.
Hakan da yai kuwa ya zamo masa alkhairi dan Asiya na samun tabbaci akan labarin ta tura zuwa ga hukumar Human rights.
Mr Lamara ya ɗau waya ya danna wasu nambobi sannan ya ƙara wayar a kunne.
"Begin the process"
Kaɗai abinda ya faɗa kenan kafin ya ajiye wayar, can ƙasan ran sa yana ayyana yadda ahalin Kachallah zai tarwatse kwanan nan.
***
Alhaji Sani Kachallah ya zubawa abincin dake gabansa ido. Tun jiya da Gwamna ya bar wajensa ko ruwa bai sake haɗiya ba.
Matar sa dake gefe ta ajiye cokalin dake hannunta tace " Alhaji wai mi yake damun ka ne? Tun jiya na lura baka cikin hayyacin ka. Ka san dai gargaɗin da likita yai maka akan yawan tunani"
Ta ƙara da cewa "akwai abinda Saifuddeen ya maka ne? dan na san a duniya maganar sa ce kaɗai ke ɗaga maka hankali" ta ƙarisa maganar da muryar da ke nuna takaici.
Maganar Saifuddeen ta jiya ta faɗo masa.
"Baba na juma ina zargin waɗannan abubuwa amma na kan tirsasa zuciyata hana irin waɗannan zargi. Zan dakatar da Asiya daga fitar da waɗannan takardu amma ina so kamin abu ɗaya"
Cikin karyayyiyar murya wacce ta fitar da ainihin rauninsa ya ƙarisa maganar
"Baba ka ƙarasa aikin daka karɓa sannan duk wata ka dinga kwatanta wani kaso na kuɗi kana mayarwa cikin asusun jiha"
Har Gwamna ya fita daga ɗakin bai iya motsin kirki ba.
Tun jiyan kuwa har yanzu bai san mi zai yi ba.
***
Sai da Bilkisu ta gama shiryawa tsaf zata wuce Abuja gameda maganar Madam Bintu aka kira wayan ta. Ganin wacce ke kiran ne ya bata mamaki, tun maganar bikin Halima ba ta mu'amala da kowa cikin 'yan uwanta idan ka cire mahaifiyarta sai kuma wasu cousins nata da suka raɓeta saboda kwaɗayi.
"Rufaidah" ta kira a hankali kamar dai ta san mi za ta faɗa ɗin.
Raunanniyar muryar da tayi magana da shi ya bata tabbacin Rufaidah ta ga hotunan da Saifuddeen ya nuna mata jiya.
"Ina so...ina roƙon ki da Allah"
Muryarta ya sarƙe saboda kuka daya fizgeta.
"Rufaidah kina jina? Zan yi komai don ganin..."
"Dan Allah ki bari a hukunta Muhammad. Idan kika saka hannu aka lalata shari'ar nan zan tsinewa Muhammad kuma ba zan taɓa yafe miki ba"
"Rufaidah tsaya ki ji..."
Katse wayar da Rufaidan ta yi yasa ta ajiye wayarta ta miƙe ta isa wajen tv ta ɗau remote ta ƙara volume sannan ta shiga chanja tasha. Babu tashar da ta kawo rahoto akan M Sani shiyasa tayi tunanin ko dai Rufaidar ce take tunanin kai ƙaran M Sani.
Ba ta bar wajen TVn ba kiran Mr Lamara ya shigo wayarta.
Ta kira duka nambobin M Sani da take da shi amma har yanzu babu wanda ya shiga.
Ashe ma an jima da shigar da ƙaran M Sani ashe dama bibiyarsa ake yi dan ai mishi kamun talala.
Bata gama farfaɗowa daga shock ɗin abinda Mr Lamara ya faɗa ba tashar Congo News suka nuno hoton M Sani hannunsa cikin ankwa daga shi sai gajeran wando da singlet fari, fiskarsa tayi ja, gefen kumatunsa ya kumbura suntum kaman an saka ƙaramin ball, ga uwa uba jini dake fita daga hancinsa.
"An ce yaran boarding school yake ɗaukowa ya biya su kuɗi yai luwaɗi da su. An ce an kama shi ne yana yiwa wani yaro ɗan shekara shabiyu fyaɗe. Boss Lady ina ga kada ki saka hannun ki a wannan shari'ar domin zata goga miki baƙin fenti"
Maganar Mr Lamara ya dawo mata. Ta sa hannu biyu ta riƙe goshinta tana sauke ajiyar zuciya, ta sani yanzu kam babu maganar zuwa Abuja...
*
Gaba ɗaya zuri'ar Alhaji Sani Kachallah sun jijjiga da wannan batu na kama M Sani.
Rufaidah kam tun da ta gama waya da Bilkisu hankalinta ya ƙara tashi, ƙarshe aka wuce da ita Asibiti saboda suma da ta yi. Likita yace jininta ne ya hau sosai.
Sun mata duk wani taimako na gaggawa amma duk da haka da ta farfaɗo ta tuno abinda ta gani a talabijin sai hankalinta ya tashi ta sake suma.
Gwamna da kansa ya je duba Rufaidah a Asibiti dan shima sai a TV ya samu labarin an kama M Sani. Ban da Bilkisu da yai wa maganar M Sani saboda yana zargin ko tana da masaniya akan abinda yaron ke aikatawa ko Baba bai faɗawa ba, ya yi tunanin gayawa Baba amma sai ya fasa saboda irin tashin hankalin da Baba zai shiga idan ya ji labarin abinda jikansa ke yi.
Zuwan Saifuddeen ya yiwa Rufaidah daɗi musamman da ya ɗau mata alƙawarin cewa zai bari hukuma tayi aikinta akan shari'ar M Sani. Sai dai duk da haka uwa uwa ce, abinda ɗan nata ya aikata ya raunana mata zuciya ikon Allah ne kawai yasa baƙin ciki bai kashe ta ba.
Dai dai Gwamna zai tafi Alhaji Sani, Halima da kuma Yazid ƙanin M Sanin suka nufo ɗakin.
Gwamna ya gaida Alhaji yana masa sannu da zuwa. Bai iya karanto komai a fiskar Baba ba hakanan ba zai iya fassara kallon da Baba ya mi shi ba.
Ya so tsayawa su gana da Baba amma kiransa da aka yi a waya yasa shi barin Asibitin cikin gaggawa.
Minti huɗu da tafiyarsa shima Alhaji Sani aka kira wayar sa ana faɗa masa wani zance da ya firgita shi fiye ma da labarin kama jikansa da aka yi.
Ya san wacece Bilkisu, ya san mi zata iya aikatawa, kuma babu shakka ya gane sarai ma'anar furucin da ta yi. Sai dai har ga Allah yana fatan abinda yake tunani ba gaskiya bane.
*
Daga inda Asiya ke kwance saboda zazzaɓi da ke damunta tun jiya ta ɗan sa hannu ta lalubo wayarta dake ringing tun ɗazu wanda shi ya tada ta daga baccin da take.
Kafin ta ɗauko wayar har ta yanke, ganin numbar Badawiyya yasa ta danna kira ta ɗara wayar a kunne.
"Ban gani ba, yanzu...to barin duba"
Tana faɗin haka ta katse kiran ta duba bidiyon da Badawiyya ta turo mata.
Bata yi mamakin ganin Bilkisu tana press conference ba infact bata yi mamakin jin kalaman Bilkisun ba inda take Allah wadai da abinda M Sani ya aikata tareda alƙawarin ɗaukarwa yaran da aka ciwa zarafi lawyer.
Lokacin da wani ɗan jarida ya mata tambaya akan ko tanada masaniya akan halin M Sani duba da cewa shine na hannun damanta tun daya dawo ƙasar bayan karatunsa a ƙasar waje, sai kawai Bilkisu ta fashe da kuka, ƙarshe ta zaro hankici ta fara goge hawaye tana faɗin Allah ya isa idan har tana da masaniya akan abinda M Sani ke aikatawa. Ta haɗa da cewa M Sani ya cuceta, ya cuci zuri'ar Kachallah gaba ɗayan su.
Asiya ta ajiye waya ta tashi zaune dan ta gano lauje cikin naɗi a maganganun Bilkisu...
23
***
Kamar Gwamna zai tashi sama haka ya fice daga cikin asibitin da sauri, hatta securities na shi da gudu-gudu suka dinga binshi a baya dan saurin da ya ke yayi yawa.
Mr Lamara ne ya kira shi ya sanar da shi Bilkisu ta shirya hira da 'yan jarida a gidan Gwamnati kan maganar kama M Sani da aka yi.
A cikin mota ya buɗe waya yana kallon maganganun da Bilkisu ke yi.
Wacce irin zuciya ce da Bilkisu? Ya tambayi kansa yafi a irga.
Ya samu labarin bata je ta duba Rufaidah ba balle ta mata jaje.
Da tunani kaca-kaca ya isa gida wanda kafin ya isa an riga an gama brief press conference ɗin da aka shirya na minti talatin.
Bilkisu na magana da wasu maza biyu Gwamna ya shigo falon.
"In my room now" ya faɗa cikin fushi sannan ya bar falon ƙirjinsa na bugawa da ƙarfi.
Ba ta bi ta kansa ba sai da ta gama bawa assistant ɗinta umurni sannan ta wuce ɗakinta ta shige banɗaki. Ta riga ta ɗauki alƙawarin yin watsi da duk wani umurnin Saifuddeen, daga yanzu za ta yi abinda ta ga dama ne a lokacin da ta ga dama.
Wasa-wasa kafin Bilkisu ta amsa kiran Saifuddeen sai da ta ɗau kusan minti hamsin, ta shirya cikin wani kayan bacci riga da wando mai tsantsi kalar baƙi.
A tsaye ta same shi yana waya har lokacin kayan daya shigo da su ne a jikinsa. Ta zauna akan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya.
Kusan minti shida yana waya kafin ya kashe ya juyo ya kalleta.
"Bilkisu" ya kira sunan ta da murya daya ke nuna tsantsan damuwa.
"Mr Governor" ta amsa kamar yadda yanzu ta ke kiransa.
"Kin ko san implications na abubuwan da kika faɗa kuwa?"
"Mi na faɗa daya wuce gaskiya, ko kana tunanin ina sane da abinda ɗan Rufaidah ke aikatawa ne"
"Ɗan Rufaidah!... Bilkisu yau Muhammad kike kira da ɗan Rufaidah. Kin manta cewa tunda ya dawo ƙasar nan ke ce uwar da ke goya shi"
"Bacci nake ji Mr Governor idan kana da abu mai mahimmanci da zaka faɗa to, idan kuma babu zan wuce ɗaki"
" Bilkisu Rufaidah yayar ki ce, kuma duk rashin jituwar dake tsananinku bata chanchanci wannan rashin mutuncin ba"
"Shikenan dama?" Bilkisu ta faɗa da sigar ko oho da abinda ya faɗa
"Daga yau na hana ki yin hira da 'yan jarida directly or indirectly"
Miƙewa tayi tana dariya ƙasa-ƙasa, tana mamakin ƙarfin gwiwa irin ta Saifuddeen.
"Ba ka isa ka hana ni komai ba Mr Governor"
Ta faɗa cikin ɗaga murya.
Abinda ya karanto a idanun Bilkisu ya tabbatar masa cewa akwai babbar matsala anan gaba, mamaki da fargaba suka mamaye shi lokaci guda...
***
Alhaji Sani Kachallah ya kasa zaune ya kasa tsaye tunda ya gama waya da Bilkisu tace masa tana hanya.
Jiya da dare ya wuni ne yana ta saƙa da warwara kan kalaman Bilkisu, a matsayin sa na tsohon ɗan siyasa ya fahimci kalaman Bilkisu sarai, kalaman na nuni ne da shimfiɗar Kamfen, duka kalamanta babu inda tayi izina da sunan Saifuddeen komai ta faɗa tana alaƙantawa ne da kanta. Idan kuwa haka ne tana nufin ita zata fito takara a zaɓe mai zuwa kenan.
Yana tsaye yana kaikawo cikin zuciyarsa aka buɗe ƙofar ɗakinsa. Yabi ƙofar da kallo har Bilkisu ta ƙaraso kusa da shi tana murmushi.
"Baba irin wannan kira da sassafe haka, hope all is well?"
Nuni ya mata da hannu akan ta zauna akan kujera, shima ya zauna suna fuskantar juna. Ita kanta sai da jikinta yai sanyi da irin kallon tuhuma da Baban nata ke binta da shi.
"Bilkisu kin san dai na san wacece ke kuma na san duk abinda zaki iya yi"
Ya ɗan yi shiru dan maganar daya ke son yi tana da matuƙar nauyi a baki
"Kina tunanin kashe Saifuddeen ne ko kuma zaki sa shi yai resigning da kan shi?"
"Baba mi ya kawo wannan maganar kuma?"
"Gaskiya zaki faɗa min Bilkisu, gaskiya nake son ji daga bakin ki. I know you, i know you can do anything just to get what you want.
"Kin jima kina sha'awar kujerar Saifuddeen, kin jima kina son yin abinda zaki fi Saifuddeen. Na roƙe ki Bilkisu don't walk this part. Saifu mijin ki ne, ɗanuwanki kuma uban 'ya'yan ki"
"And so what Baba, so fucking what dan na so Saifuddeen a baya har na haifa masa yara uku. Kai da shi duka babu wanda ya damu da abinda ni nake so"
"Baba baka taɓa ganina a macen da take da hazaƙa da basirar da zata shiga siyasa ba. A kullum Saifuddeen shine ɗan gaban goshinka shine zai gaji harkokin ka na siyasa kuma ka sani cewa Saifuddeen is a coward, bai da jarumta ko kaɗan"
"Mi kike shirin yi Bilkisu?"
Alhaji Sani ya tambaya a firgice
"Yanzu lokaci na ne, zan yi amfani da baiwa da hazaƙar da Allah ya bani wajen gina ambition ɗina na zama fitacciyar 'yar siyasa a ƙasar nan. I will be the next governor of this state Baba. Zan yi abinda Saifuddeen ba zai taɓa yi ba har ya ƙare rayuwarsa"
"Bilkisu kin haukace ne. Kashe min Saifu za ki yi?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye
"Kisa? Baba ka kwantar da hankalin ka, Saifuddeen na raye a doron ƙasa za a rantsar dani gwamnan jihar Congo"
"Ba zan yafe miki ba idan wani abu ya samu Saifu, kuma ki sani ba zan taɓa bari ki hau kujerar nan ba"
Bilkisu ta miƙe tsaye ta ɗau jakan ta tace "Baba Allah ya bawa kowa sa'a"
Bayan tafiyar Bilkisu Alhaji Sani ya shiga tashin hankali mai tsanani, ya rasa ma ina zai sa kansa.
*
Asiya tana karyawa ita da ƙannenta wayarta ya fara ƙara. Tana ɗaukar wayar ta ga sunan Alhaji S Kachallah, tun wani lokaci da ta kira shi ta masa ya jiki lokacin daya dawo daga Germany bayan yaje an duba lafiyarsa ta saving numbarsa a wayarta.
Ba ta yi mamakin ganin kiransa ba kasancewar yana da masaniyar tana shirin maka shi kotu.
Bayan sun gaisa ya nemi ganinta a Kachallah house nan da awa ɗaya, ta amsa da toh.
Asibiti take son zuwa dan taje ta gaida Rufaidah Kachallah sannan su wuce gidan Halima dan tunda yaran suka yi hutu basu je gidan Yaya Bello ba. Itama Asiyar rabon ta da gidan Haliman ta manta.
Bayan sun gama karyawa tace da su Sumayya Direba zai kaisu gidan Halima ita zata wuce Kachallah house idan ta gama zata same su a chan.
Ta riga su Sumayyan ma fita daga gida dan har lokacin data ɗauko key ɗin mota ta fito basu gama shiryawa ba.
Har falon Alhaji Sani mai aikin matarsa ta mata jagora sannan ta kawo mata kayan marmari da tarkacen ciye-ciye.
Kusan minti biyar da zuwanta Alhajin ya shigo falon.
Asiya ta yi saurin risinawa tana gaishe shi.
Bayan ya gyara zamansa yace da ita "ya kike jin labarin iyayen ki?"
"Suna lafiya Baba"
"To Allah ya ƙara musu nisan kwana"
Ta amsa da Amin. Shiru ne ya biyo bayan hakan gaba ɗaya Asiya ta ƙagu ta ji dalilin kiranta da yai. Kafin tazo ba abinda bata saƙa a ranta ba, har tunani tayi ko cewa zai yi ya saka Saifuddeen ya rabu da ita.
Gyaran murya yai sannan ya katse shirun da cewa "Miyasa kike son turani kurkuku?"
Asiya ta ɗago ido ta kalleshi da sauri dan tambayar ta mata bazata.
"Ki saki ranki ki faɗa min gaskiya, idan hujjojin ki suna da ƙarfi zan miƙa kaina gaban alƙali ba sai kin sha wahala ba"
Bata gama gane zancen sa ba amma idan gaskiya yake nema zata faɗa masa ko da ba zai yiwa kunnuwansa daɗi ba
"Baba ka gafarceni idan akwai rashin kunya a maganganun da zan yi"
"Kar ki damu, dama ina neman wanda zai gayamin gaskiya ba tareda ya ji kunyata ba"
Asiya ta ɗan gyara zamanta sannan ta fara bayani
"Baba ban fara bincike a kan ka saboda ina so na kawar da kai daga jikin mijina ba sai dan ina so na taimaka masa wajen yin jagoranci na gaskiya. Akwai abubuwa dayawa daya kamata ayi a jihar nan amma budget yana kasawa saboda mutane dake cinye kuɗin tun kafin a gudanar da komai. Kuɗin nan kuɗin talakawan jihar nan ne kuma duk wanda ya cinyesu ya ci haram, na fara da kai ne saboda in har Gwamna zai yi gaskiya to daga jikinsa zai fara yaƙi da masu cin hanci da rashawa. Kaine na farko a list ɗina kuma indai aka yi nasara akan ka to babu wanda ba zai shiga hannu ba.
"Ni ina ganin taimakon ka ma za ayi a yi maka hukunci daga nan duniya a rage maka zunuban mutane da kake ta tarawa kanka sama da shekaru ishirin. A ƙalla Baba zaka kai shekara saba'in da biyar koma fiye a duniya kana tunanin nan gaba zaka ƙara shekaru kamar su ne? Mutuwa rigar kowa ce kuma tabbas zata riske ka ko ba daɗe ko ba jimawa. Akwai kwanciyar ƙabari akwai tsayuwa a gaban Allah, shin kana so ka mutu da hakkin dubban mutanene? Shin Baba kana tunanin duk wannan matsayi da kake da shi a nan gida duniya zai ƙwaceka daga azabar Allah. Ko asirin ka bai tonu anan duniya ba akwai ranan da duk wani sirri zai fito fili."
Hawaye ne suka fara zubowa a idanun Alhaji Sani hakan yasa Asiya ta dakatar da maganganunta.
Kusan minti uku babu wanda yace komai. Chan kuma Asiya ta motsa baki a hankali ta furta " ka ji tsoron Allah ka taimakawa Saifuddeen ya gudanar da mulkinsa bisa adalci"...
***
Bilkisu kam ko kaɗan bata damu da halin da mahaifinta zai shiga ba bayan ta fitar masa da maitanta fili. Abinda ta sa a ranta shine idan komai ya tafi dai-dai har ta hau kujerar Gwamna zata damƙa masa sarautar Congo wannan kuma ta sani zai zamo masa compensation bisa abinda zata yiwa Saifuddeen.
Bayan ta samu zama a office ɗinta ta tambayi Sakatariyarta ko an aiko mata saƙo daga ofishin matar shugaban ƙasa amma tace ba abinda aka turo.
Auren 'yar shugaban ƙasa nan da sati mai zuwa, kuma ta ci burin amfani da wannan dama wajen samun wani kusanci na musamman da matar Shugaban ƙasa. Tana buƙatan support na manyan mutane musamman yanzu da abubuwa ke shirin kwaɓe mata.
Ta ɗau waya ta danna numbar first lady ɗin dan ta tayata murnan bikin da za ayi amma har ta tsinke ba a ɗauka ba. Ta ajiye wayar a ranta tana faɗin da zaran anyi kwana biyu maganar M Sani ta lafa zata je har Abujan ta yiwa first lady barka.
*
A ɓangaren Gwamna kuwa ya cigaba da gudanar da harkokinsa cikin ɗarɗar domin bai gama yarda cewa Asiya ta haƙura da case ɗin Baban sa ba. Gani yake ko da wani lokaci zai ga hoton Babansa a talabijin ana saka masa ankwa a hannu.
Da wannan tunanin ya wuce gaisuwa ƙauyukan da aka kai hari kwanan baya.
**
Ita kuwa Asiya jiki a sanyaye ta dawo gida ko gidan Halima bata wuce ba. Maganganun Alhaji Sani sun saka jikinta sanyi.
"Ina so ki ɗauka min alƙawurra guda uku Asiya Shahidah, idan kika yi wannan nayi alƙawari ni da kaina zan kai kaina kotu"
Sosai ta ɗauko nitsuwarta ta ɗaura akan shi yayinda zuciyarta ke fargaban abinda Alhajin zai faɗa
"Na farko ina so ki kare kujerar Saifuddeen, akwai masu harin kujerarsa cikin makusantar sa na jini. Ki taimaka masa ya ƙarisa wa'adinsa bisa adalci.
"Alƙawari na biyu shine ina so ki saka Gwamna ya cire Mr Lamara a matsayin Chief of Staff nasa sannan duk abinda zaki yi ki tabbatar an kama Mr Lamara nan bada jimawa ba domin na tabbata shine ya nemo takardun da kike da shi. Matuƙar Mr Lamara yana nan ba lallai ke ko Saifuddeen ku cimma wani buri naku ba"
"Na uku" ya tsaya da maganan saboda wani abu daya toshe masa maƙoshi. Kusan minti biyu ya ɗauka kafin ya cigaba
"Ina so ki je Gambia ki sada Saifuddeen da 'yanuwan mahaifiyarsa. Na jima ina son yin hakan amma sai wani abu ya zo ya tare, a yanzu babu gatan da zan iya yi masa daya wuce wannan"...
Asiya ta riƙe kai tana furzar da iska saboda ƙirjinta daya cunkushe. Babu ko ɗaya cikin alƙawurran da ta ɗauka daya ke da sauƙi. Haka nan maganganan Alhaji Sani kusan yana mata ishara ne da Bilkisu Kachallah, tabbas hiran da Bilkisu ta yi jiya da 'yan jarida kamfen take a fakaice.
Gaba ɗaya ta rasa walwalarta dan har yamma da su Sumayya suka dawo suna mata hiran wai Halima na da ciki bata sake jikin ta ba.
Yamma lis kusan gab Magariba Badawiyya ta iso gidan zuwan Badawiyyan ne ma ya sanyaya mata rai dan ta san ko da shawara ɗaya ce zata samu a wajenta.
Bayan ta sanar da ita kaɗan daga cikin abubuwan da suka tattauna da Alhaji Sani itama ɗin ta yarda cewa Bilkisu da Mr Lamara suna shirin kawar da Saifuddeen ne daga kujerar sa sai dai abinda ya basu mamaki cikin nazarin da suka yi shine kasancewar Mr Lamara mai fuska biyu.
Shawara ɗaya suka yanke shine zasu bi salon Mr Lamara su rushe duk wani shirin su...
24
"Hajiya Asiya Kachallah" Mr Lamara ya faɗa yana miƙewa tsaye fiskarsa ɗauke da murmushi.
"Your Excellency what a surprise"
"Na zo duba His Excellency ne shine nace barin shigo mu gaisa kuma na yi maka godiya"
"Kai amma nagode sosai, barin sa a kawo miki ruwa"
"No kar ka damu, i'm ok"
"Sure?" Ya tambaya yana murmushin munafurci.
"Mr Lamara inaga tsakaninmu babu wani ɓoye-ɓoye dan haka ka zauna mu yi wata 'yar magana"
Chief of Staff ya zauna yana cigaba da murmushin yaƙe.
"Na ga saƙon ka har guda biyu, kuma sun zo a dai-dai lokacin da nake buƙatar su"
" ban gane wani saƙo kike magana a kai ba?"
Asiya ta ɗan yi jim tana kallon shi kafin tace "aff na ɗauka abu ɗaya muka sa a gaba ai, kwanaki da kace mu haɗa hannu nayi wauta da nace maka a'a, kasan har yanzu ni yarinyace a harkar siyasa. Idan har yanzu ƙofan ka na buɗe ina so mu haɗa hannu mu yaƙi Bilkisu Kachallah"
"Ban san mi kike magana a kai ba Hajiya Asiya amma koma minene bana son saka hannuna a ciki"
"Gwamna ba shi da ra'ayin sake takara a zaɓe mai zuwa, abinda yake buƙata shine ya gama wannan wa'adinsa lafiya"
"Miyasa kike faɗa mini wannan magana?"
"Saboda ni da kai mun san Bilkisu tana son kujerar Saifuddeen"
" idan tana so shi baya so ai baki da matsala da hakan, ko kina kishi da cewa za ta fiki matsayi idan ta ci zaɓe?"
"Ofcourse ba haka ba, ni damuwata lafiyar miji na, na tabbata Bilkisu zata iya hallaka mijina akan kujerar Gwamna. I'm still young Mr Lamara and i love my husband"
"Mi kike nema a wajena?"
"Ko da an kama Alhaji Sani Kachallah ba zai shafi Bilkisu ba, ina so ka bani evidence da za'a iya kama Bilkisu kai tsaye. Ba zan bari ta kashe min miji ba"
"Ki yi haƙuri ba abinda zan iya baki"
" ƙarshen amsar ka kenan?"
Shiru yai na kusan minti ɗaya kafin yace
"Sorry Hajiya Asiya"...
Bayan fitan Asiya daga office Mr Lamara ya kama girgiza kai yana jaddadawa ransa cewa Asiya ta gano ɗaya fiskar daya ke ɓoyewa Bilkisu, dan haka dole yayi takatsantsan sannan ya taka mata birki kafin tayi wani abu da zai ɓata masa shiri.
*
Duk wani tsari da shirye-shirye da Asiya ke yi babu wanda ta sanar sai Allah, so take ta samu nitsuwar da zata iya tunkaran wannan lamari daya kutso kai gadan-gadan.
Gwamna ya ɗauke mata wuta sosai, itama kuma tata matsalolin sun hanata samun damar zama ta sake fahimtar da shi illar rashin sauke amana. Tana fushi da shi, amma bayan maganarsu da Alhaji Sani sai tausayinsa ya shigeta.
A wannan yanayi ne kuma aka kawowa Asiya invitation na musamman daga wajen matar shugaban ƙasa.
Babu yadda za'ayi ta ƙaurace zuwa bikin nan sai dai idan Saifuddeen ne ya hanata. Bayan an kawo mata invitation ɗin ma wanda yazo da kayan anko na musamman da manyan baƙi zasu saka sai da first lady da kanta ta kira Asiya ta jaddada mata akan dole ne ta halarci wannan biki.
Daren yau take da niyyar sanar da Gwamna batun tafiyarta Abuja duk da ma dai ba a gidan ta zai kwana ba.
Fitowarta kenan daga ɗaki zata sauƙa ƙasa wayarta ya shiga ringing. A hankali ta zaro wayar daga cikin purse ɗinta ta ɗau kiran.
"Yes Badawiyya" .
Gyaɗa kai tayi bayan Badawiyyar ta mata wani bayani daya mata daɗi.
"Ok gani nan zuwa"
Da sauri-sauri ta ƙarisa ficewa daga gidan...
***
Alhaji Sani Kachallah yana tsaye a saman balcony na ɓangarensa yana kallon kai kawon da akeyi a farfajiyan gidansa. Lokaci zuwa lokaci yakan sauke ajiyar zuciya ko kuma ya yi tagumi.
Jiya da dare ɗaya daga cikin masu gadin gidansa ya rasu. Malam Jatau ya fara gadin gidan tun mahaifinsu na raye, zai iya cewa ya kai shekara hamsin yana musu gadi, an jima da sallamarsa daga aiki amma saboda sabo da gidan yasa bai tafi ba, a gidan yai aure, kaf 'ya'yansa uku mata da Allah ya bashi a gidan ya aurar da su. Bashi da wani gida daya ke da shi sama da Kachallah house wannan yasa Alhaji Sani yace ayi zaman makoki a cikin gidan..
Da shi aka je maƙabarta kuma tabbas wani ɓangare nashi ya motsa da ganin yadda ake shigar da mamaci cikin ƙasa, ga nan tsofin kabarurruka kuma waɗanda duniya ta manta da su.
Alƙawari ya ɗauka ba zai ci amanar jam'iyyar ba sai dai a wannan lokaci dole ne ya yiwa kan sa zaɓi da zai tsaida musiba dake shirin kunno kai ga ahalinsa dama jahar sa gabaɗaya. Dole ne ya ceci Saifuddeen daga tarkon Bilkisu dole ne ya dakatar da Bilkisu daga abinda take shirin aikatawa.
Idan bai yi wani abu ba abinda Bilkisu zata aikata ka iya zama abun da zai rusa ahalin Kachallah gaba ɗaya.
A hankali ya sa hannu cikin aljihunsa ya zaro waya ya dannawa Asiya kira.
***
Bilkisu Kachallah tana zaune kan wata kujerarar roba sai kaɗa ƙafa take, lokaci zuwa lokaci tana jan tsaki. Ta tsani jira kuma abinda take kenan tun kusan minti goma da suka wuce. A karo na uku ta sake ɗaura ƙafarta na hagu akan na dama. Buɗe ƙofar da aka yi yasa ta ɗaga ido ta maida dubanta ga ƙofan.
Zata iya rantsewa cewa bata taɓa ganin matar da aka turo cikin ɗakin ba, har aka cirewa matar ankwa a hannu Bilkisu bata ɗauke ido akanta ba. Tabbas Madam Bintu ce a gabanta, amma wannan tasha banban da wacce ta sani a baya, idan ba idanunta da kuma yanayin dogon goshi da take da shi ba babu abinda Bilkisu zata iya cewa ya kamantata da waccar Bintun da ta sani shekara da shekaru.
"Bilkisu Sani Kachallah" Madam Bintu ta kira bayan ta ɗingisa ta zauna a wani dogon benchi dake ɗakin.
"Bintu ke ce haka! " Bilkisu tayi maganar da sigar mamaki ba tambaya ba.
Jiya dai-dai wannan lokaci ta gama karanto sirrikan Bilkisu da ta sani. Ta damƙa sirrikan ne a hannun matar da Bilkisun ta tsana. Ko kaɗan bata yi dana sanin abinda ta yi ba domin ba za ta yarda ita kaɗai ta kai ƙasa ba, idan ka cire laifukkan data yiwa Badawiyya duk wani laifi da ta aikata ba komai ba ne idan aka haɗa da tarin laifuffukan Bilkisu.
Da wannan tunanin Madam Bintu ta buɗi baki a hankali tace "sai yau kika damar zuwa duba ni?"
"Wallahi ina zuwa amma basa barina na ganki, wai an basu umurni kada a bari kiga kowa"
"Hmmm Bilkisu kenan, ba sai kin yi min ƙarya ba, na riga na san bani da wani amfani a gareki yanzu"
"Wani irin magana ne wannan, kinada mahimmanci a rayuwata Bintu. Ke kanki kin sani"
Madam Bintu ta sa hannu ta fara sosa kanta a hankali chan kuma ta sa ƙarfi tana sosawa kamar zata ƙwarzane duka fatan kan.
Bilkisu ta bita da kallon ƙyama har da tura kujerarta baya dan kar Bintu ta raɓa mata ƙwarƙwatan dake cin kanta.
Kusan minti biyu Bintu ta ɗauka tana sosa kan, har lokacin bata samu sauƙi gaba ɗaya ba amma ya fara lafawa. Tun ranan da ta fito daga bukkar boka Kalingana take jin wani abu na yawo a kanta, lokaci-lokaci idan abin ya motsa ta fara sosa kai sai ka ga kaman zata cire ilahirin fatan kan ne, wannan yasa duk gashin kanta suka kaɗe sai ɗan abinda baza a rasa ba.
Bilkisu ta yi saurin katse shirun dake tsakaninsu
"Kin tuntuɓi boka Kalingana kuwa tunda wannan abin ya faru?"
"Mi kike buƙata Bilkisu? Dan na san kin zo ne dan kan ki ba dan ki duba lafiyata ba"
"Bintu akwai sirrikana a hannunki kuma kin sani rufin asirina shine kwanciyar hankalinki. Zan fitar dake daga wannan waje idan na zama Gwamna, kafin nan ki kame bakin ki"
Kafin ta bata amsa aka buɗe ƙofa warden ta shigo da ankwa a hannu. Madam Bintu ta miƙe tsaye tareda miƙa hannunta aka saka mata ankwa.
Bilkisu ta miƙe itama da sauri, ta matso kusa da Bintu tace " ki riƙe bakin ki shine kawai gatan ki"
Bintu tayi murmushin nasara dan aikin gama ya gama.
Bayan an fitar da Madam Bintu daga ɗakin, Bilkisu ta yi kusan minti uku tana nazarin murmushin da Bintu ta mata wanda ke mata nuni da cewa Bintu ba zata riƙe amanarta ba.
Koma mi zai faru ba zata bari Bintu ta jata cikin ƙasa ba. Ta wuce wannan...
***
A chan falon Alhaji Sani kuwa Asiya ce durƙushe gaban sirikin nata tana roƙon shi akan ya janye maganarsa. Amma ko kaɗan bai da niyyar yin hakan da alama ya riga ya yankewa kansa hukunci.
"Baba na riga na booking jirgin Gambia gobe, dan Allah ka bar komai sai bayan ka sada Gwamna da kakanninsa"
Bai ce komai ba har sai da Asiya ta kuma cewa " na kira Hajiya Umma kuma ta ce zata yiwa Gwamna bayani"
"Kina nufin Saifu ya san da tafiyar?"
"E Baba, ya amince zai biku"
Ta yi maganar tana addu'ar Allah ya ɗaurata akan Gwamna da kuma Hajiya Umma.
Babu yadda ya iya dole ya amince da tafiyar da Asiya ta tsara.
Tana fitowa daga gidan ta kira Secretary na Gwamna ta tambayeshi schedules ɗin Gwamna na gobe da jibi. Ta ɗan samu sassauci a ranta kasancewar babu wata tafiya da Gwamna zai yi a kwanakin.
Har ta iso gidan Hajiya Umma bata dena addu'ar Allah ya ɗaurata akan matar ba.
Tarba na musamman Hajiya Umma ta mata har da mata gori akan rabon ta da zuwa gaisheta tun tana Amarya ta ƙare da cewa "ko Bilkisu ta gutsira miki ƙafar karen ne? Sai shegen yawo amma ba ziyara"
Asiya tayi dariya tana girgiza kai.
Bayan sun nitsu Asiya ta zayyana mata abinda ke tafe da ita da kuma ƙaryar da ta yiwa Alhaji Sani.
Hajiya Umma ta yi wata 'yar dariya irin tasu ta manya sannan tace "Shahidah kenan, ai sam Alhaji bai yarda da batun ki ba, ya kira ni ya shaida min komai kuma na gaya masa ba muyi zancen zuwa Gambia da ke ba"
Asiya ta rufe fiska cike da kunya.
"Kwantar da hankalinki, kafin ki zo na kira shi Saifuddeen ɗin kuma ya amince zai bimu zuwa Gambia goben sai dai ban gaya masa dalilin tafiyar tamu ba"
"Kiyi haƙuri Hajiya kawai dai..."
"Miye na ban haƙuri kuma, ai abun a miki godiya ne, ni rabon na tuna da cewa iyayen mahaifiyar Saifuddeen mutanen Gambia ne ai na manta"
Haka Hajiya Umma tayi ta saka wa Asiya albarka da addu'ar samun zuri'a masu albarka
*
Ƙaran shigowan text yasa Asiya ta sake towel ɗin da take goge kanta da shi ta ɗauki wayar tana karanta amsar saƙon da ta tura, saƙon bai mata daɗi ba dan zama tayi dirshen kan kujera tana sauke ajiyar zuciya. Wai yanzu tsakaninta da Saifuddeen ne ya dawo haka.
Tunda dai ya bata izinin tafiya ai shikenan. Ta sake karanta text ɗin a karo na biyu nan da nan ta ji hawaye ya zubo mata. Anya kuwa zata iya wannan abin.
"Ki je duk inda kike so ni Saifuddeen ba zan iya hana ki ba"
Ko dai ta fasa zuwa bikin nan ne, ko dai ta amince tabi su zuwa Gambia ne goben. Tambayoyin da ta ke yiwa kanta kenan har sai da kiran Agent Dahlia ya katseta.
*
Tunda aka yi masa maganar tafiya Gambia jikinsa ya bashi akwai alaƙar tafiyar da 'yanuwan mahaifiyarsa sai dai bai nuna wa Hajiya Umma hakan ba.
Da dare bayan ya gama duk wani abinda zai yi ya je gaishe da Alhaji Sani ko zai samu wani batu gameda tafiyar tasu amma har ya masa sallama ya tafi Alhaji Sani bai gaya masa dalilin tafiyar su ba. Abin ma ya bashi dariya wai da girmansa ana ɓoye masa inda zasu je kamar wani ƙaramin yaro.
Lokacin daya shiga gida a falo ya tarar da Bilkisu tana waya tana zuba masifa kaman zata tashi sama. Haka ya ɗauke ido ya wuce sashinsa kaman bai ganta ba duk da kuwa yaji maganar da take yi.
A wani ɓangare kuma yana tunanin dalilin daya sa matar shugaban ƙasa ta gayyaci Asiya bikin 'yarta ba Bilkisu ba. A iya saninsa Asiya bata da haɗi da first lady. Daga baya kuma sai ya tuna cewa ai First lady ta koyar da ita lokacin da taje course a National Institute of Policy and Strategic Studies Kuru.
Bai gama kimtsawa ba Bilkisu ta shigo ɗakinsa.
"Wani munafurcin ne yasa aka inviting Asiya zuwa bikin 'yar shugaban ƙasa. That invitation was mine"
Murmushin takaici yai dan duk cikin abubuwan da ke faruwa babu wanda ya ci mata tuwo a ƙwarya sai maganar bikin 'yar shugaban ƙasa. Lallai a gaishe da Bilkisu.
"Saifuddeen magana nake fa, na san kai ne ka ƙisa wannan munafurcin"
"Idan kina da matsayi a wajen first lady bana tunanin zata hana ki katin gayyata"
"Ya isa!" Ta ja tsaki ta fice daga ɗakin
Wannan shine abinda suka zamo, wannan shine abinda kasancewarsa Gwamna ya haifar. Kafin ya zama Gwamna rayuwar aurensu akwai tarin matsaloli amma ya ƙwammaci rayuwar aurensu kafin ya zama Gwamna da yanzu. Wannan mata data daka masa tsawa, ta ja masa tsaki itace matar da yai rayuwar aure da ita na shekaru shatara.
Abin mamaki da takaici shine bayan shekaru shatara da aure har yanzu babu fahimta mai tsabta tsakaninsu.
Gwamna ya girgiza kai kawai ya maida hankalinsa ga kayan bacci daya ke shirin sakawa yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa.
***
Lokacin da suka sauka a babban filin jirgin ƙasar Gambia wato Banjul international Airport tuni akwai mototoci biyu dake jiransu.
Alhaji Malick Burama shine ya jagoranci tafiyar ta su. Shi ɗin wani tsohon abokin kasuwancin Alhaji Sani ne dake Gambia. Alhaji Malick ɗin ne ma ya shirya zama tsakanin Alhaji Sani Kachallah da iyalen marigayi Ousmana Jallow.
Cikin shekaru kusan hamsin Ahalin marigayi Ousmana Jallow sun kasance daga cikin masu faɗa a ji a cikin ƙasar, saboda kasancewarsu manyan 'yan kasuwa da kuma 'yan siyasa.
An haɗa zaman ne a katafaren gidan marigayi Alhaji Ousmana wanda yanzu an maida shi kamar gidan gona da ahalinsa ke ziyarta idan sun zo hutu.
Tunda suka iso gidan suka ci karo da dandazon motoci. Sanarwa ce aka yi cikin ƙanƙanin lokaci amma duk wani mai alaƙa da Alhaji Ousmana Jallow sai daya halarci wannan zama wanda yafi kama da taron biki.
A cikin mota dai dai zasu fita Alhaji Sani ya riƙo hannun Gwamna Saifuddeen yace " nan ne gidan kakanninka Saifu, nan ne tushen mahaifiyarka. Ka yafe min bisa tsawon lokaci da muka ɗauka ba tareda na kawo ka ba, ni kaina ba zan iya faɗin dalilin da ya sa na gagara yin haka ba duk da kuwa na jima ina son yin hakan"
Hawaye suka cika fal a idanunsa take yaji wani sabon shauƙi da soyayyar Babansa yana ƙara shigarsa. Ya san abinda ya kawosu kenan amma jin hakan daga bakin Alhaji Sani ya ƙara daɗaɗa masa rai.
Wasu mutane biyu ne suka zo suka shiga da su wani falo inda aka shirya za a gana da manyan gidan kafin a yiwa sauran 'yanuwa dake ta baya wajen wani hall da aka shirya taron bayani.
Tun kafin a fara bayani wani tsoho wanda a ƙalla zai yi shekara casa'in ya zo ya rungume Saifuddeen yana kuka, da yaren Fulatanci yake faɗin da gaske wannan ne jikan ɗanuwansa Ali Jallow. Da ƙyar aka samu aka raba su dan kusan kowa a wajen hawaye ya fara.
Bayan an nitsun ne kuma aka buɗe zaman da addu'a sannan aka fara gabatar da kai. Alhaji Sani ya gabatar da kansa da kuma Hajiya Umma a matsayin yayyen mahaifin Saifuddeen wato Sa'ad Kachallah wanda ya auri 'yarsu Aisha Ali Jallow kusan shekaru hamsin da suka wuce.
Tsohon nan da ya ke kuka ya saka kabbara yana ɗaga hannu tareda godiya ga Allah.
Bayan an nitsu tsohon ya gabatar da kan sa a matsayin Alhaji Muhammadou Jallow yaya ga Ali Jallow, ya nuna ɗanuwansa wanda ke zaune gefensa shima yana hawayen yace "wannan shine Yayanmu gaba ɗaya sunansa Audoulaye Jallow" ya cigaba da nuna wasu 'yan uwan na su na kusa da su.
Basu san da haihuwar Saifuddeen ba, su abinda aka gaya musu shine Aisha da ɗan data haifa sun mutu. Wannan shine gaskiyar da suka riƙe shekara da shekaru.
Shekaru ishirin da biyar da rasuwan Ali mahaifinsu ya fara jinya, a lokacin ne kuma yake yawan sunbatu da cewa a nemo masa jinin Ali, a nemo masa 'ya'yan Ali. Basu fahimci mi yake nufi ba sai suka ɗauki hakan a matsayin tsufa ne kawai da kewar Alin daya dawo masa sabo. Duk da ya jaddada musu lallai a nemo masa ɗan Ali basu wani ɗau abin da mahimmanci ba a haka har Allah ya ɗau ransa. Sun ma manta da zancen shaɗaf sai da Boubacar Jallow zai rasu yake faɗin abinda ya aikata tareda nuna musu wasiƙar da aka turo lokacin haihuwar Saifuddeen. Boubacar shi yai wa Aisha sammu sannan shi ya sa aka kashe Sa'ad Kachallah.
Alhaji Sani ya zaro ido waje dan ya san ƙaninsa a hatsarin mota ya mutu. Alhaji Muhammadou bai tsaya da maganar sa ba ya cigaba da faɗin Boubacar ya kashe Sa'ad ne dan ya auri Aisha, sannan ya mata asiri ne dan ta dawo gida amma hakan bai yiwu ba.
Tunda mahaifinsa Alhaji Aoudulaye ya ji wannan zance ya fara jinya. Mun sa a ranmu da zaran ya samu lafiya zamu zo Nigeria mu nemi ɗan Aisha Allah mai ikonsa kwana uku da aka dawo da shi daga ƙasar Jamus muka samu kiran Alhaji Burama akan sirikin Aisha na son zama da mu akan ɗan da ta bari.
Alhaji Aoudulaye ya sake fashewa da kuka tunowa da yai da yadda Boubacar ya ƙare rayuwarsa cikin garari da son zuciya saboda abinda ya aikata. Ko kusa bai yi ƙarshe mai kyau ba. Ta inda Allah ya kama shi yadda ya zo haka ya tafi bai taɓa haihuwa ba, to inama zai haihun tunda ba auren yai ba.
Saifuddeen ya tashi ya matsa jikin Alhaji Aoudulaye ya rungumeshi yana kuka.
Cikin kuka Alhaji Aoudulaye yake faɗin Saifuddeen ya yafe musu.
Haka nan aka dinga jajantawa juna ana kuma taya juna murna.
A wajen liyafa da aka shirya kuwa 'yanuwa kaman zasu cinye Saifuddeen musamman ma 'yanuwan mahaifiyarsa mata (cousins) wanda suka taso tare.
Mutane dayawa na faɗin irin tsananin kamannin Saifuddeen da mahaifiyarsa wanda suka santa da kyau har cewa suke hatta murmushinsa irin nata ne.
Faɗin irin farin cikin da Gwamna Saifuddeen ya tsinci kansa a ciki ma ɓata lokaci ne. Wani ƙishirwa ne da ya ke fama da shi shekara da shekaru Allah ya kora masa ƙishin a rana guda ba tareda ya shirya ba. Duk da mahaifiyarsa da kakanninsa basa raye amma ya ga yayye da ƙannen kakanninsa tareda tarin 'yanuwan mahaifiyarsa wannan kaɗai ya wadatar da shi.
He was so happy da har ya manta duk wani fushi daya ke da matan na sa biyu dukkansu ya tura musu hotunan da ya yai da 'yanuwan mahaifiyarsa tareda tura gajeran saƙo a ƙasa.
Daga wajen Asiya ya samu reply mai daɗi inda ta masa fatan alkhairi da addu'o'i. Ita kuwa uwargida yi tayi kamar bata ga mi ya turo ba balle har ma ta maida masa wani martani gameda abinda ya turo. Bai yi mamaki ba duba da irin rabuwar da suka yi jiya.
***
Babu yadda za ayi ta bari a tozarta Alhaji Sani a wannan yanayi. Yace mata zai gabatar da kansa ga hukuma idan yai hakan zai samu sassauci a idon mutane da kuma ɓangaren shari'a.
"Wannan cin zarafi ne ai?" Asiya ta faɗa tana sake duba jaridar dake hannunta da kyau.
"Samfurin jaridar da za a fitar gobe kenan"
"CY? " ta kira sunansa da sigar tambaya, mamaki da damuwa duka lokaci guda.
"Bisa duka bincike da nayi Mr Lamara ne ya bada duk wasu bayanai da aka saka a ciki"
Asiya ta rintse idonta tana cigaba da sauraron bayanin da CY yake mata.
Bayan ya gama ta ja wani dogon numfashi sannan shiru ya biyo bayan hakan.
"your Excellency kina jina? Hello, Hello"
"Ina jin ka CY kawai dai ina neman mafita ne kan abinda ka faɗa"
"Duk abinda za ayi iya yau ne kawai, zuwa gobe da safe jaridar zai shiga hannun kowa babu wani abu da Alhaji Sani zai iya yi a kai"
"CY Alhaji Sani yana ƙasar Gambia yanzu haka, yau ya tafi babu yadda za ayi ya dawo a yau ɗin nan"
"Kina ga za ki haƙura Mr Lamara ya ɓata miki shiri kenan?"
Ko kaɗan ba za ta taɓa bari wannan baƙin mugun ya ci galaba a kanta ba, da shi da Bilkisu duk ɗaukan kwab ɗaya take son yi musu. Tunanin ta gayawa Bilkisu wannan batu ne ya faɗo ranta, tayi saurin kau da shi ta hanyar faɗin ba za ta taɓa bari Bilkisu ta san makamin da ta ke da shi a kanta ba. Sannan wannan ba zai chanja mutuncin Alhaji Sani da yake shirin zubewa ƙasa ba.
Sai da ta gama tufka da warwara sannan ta dannawa Alhaji Sani Kachallah kira.
*
"Wani batu ne na gaggawa ya taso, dole na juya a yau ɗin"
Abinda Alhaji Sani Kachallah ya faɗawa Saifuddeen kenan.
Ya sani sarai Saifuddeen ba wai ya yarda da maganar bane sai dai kawai ya haƙura ne dan baya son yin sa'insa da shi a cikin 'yanuwansa.
Ba wai cikakken lafiya bane gare shi taya ko hutawa bai yi ba zai sake hawa jirgin awa huɗu zuwa Nigeria.
Ko shi da yake da tarin ayyuka a gabansa ya sa a ransa cewa kwana biyu zai yi a Gambia kafin ya koma. To minene yake da mahimmanci haka da Baba ba zai iya haƙura da shi zuwa gobe ba.
Allah ya nufa ma akwai jirgin da zai je Nigeria dan haka ko minti talatin bai cika afilin jirgi ba Alhaji Sani ya shiga jirgi ya juyo gida zuciyarsa cike da raɗaɗi. Raɗaɗin mutuwar ɗanuwansa wanda a yau yake jin asalin sababin mutuwarsa, raɗaɗin rabuwa da Saifu a wannan lokaci mai mahimmanci a gareshi, raɗaɗin sanin gaskiya mai ɗaci wanda ke shirin tarwatsa masa duk wani tsari da yai wa kansa a baya.
Labarin son zuciya irin na Boubacar Jallow wanda ya kaishi ga kashe masa ɗanuwa ya tuno masa da tasa 'yar wadda a yanzu ta saka wani buri a ranta, samun cikan wannan buri kuwa sai dai idan har kawar da Saifuddeen za ta yi. Saifuddeen fa, Saifuddeen ɗan sa, farin cikin sa...
Babu wanda ya san da dawowar Alhaji Sani Kachallah sai Asiya, ita ce ta aika aka je aka ɗauko shi daga airport kusan ƙarfe takwas na dare. Ta so haɗuwar su kafin ya wuce gidan talabijin ɗin amma kamar yadda ya faɗa dole ne ta ɓoye kanta daga wannan batu saboda gudun abinda zai je ya dawo. Gobe zata wuce Abuja bikin 'yar shugaban ƙasa, dole ta rufe ido daga duk wani abu da zai faru daren yau zuwa gobe.
***
"A daren yau ne dai fitaccen tsohon ɗan siyasar nan wato Alhaji Sani Abubakar Kachallah ya fito gidan talabijin na Hill TV ya bayyana ire-iren laifuka da ya aikata wanda ya haɗa da cin hanci da rashawa, sannan ya tabbatar da cewa zai miƙa kan sa ga hukuma tareda duk wani shaida da za a buƙata na laifukan da ya aikata. Har yanzu kuma yana mai roƙon al'ummar jahar Congo da su yafe masa bisa laifukan daya aikata"
Mai karanto labarai yana kaiwa nan aka nuno Alhaji Sani a shiri na kai tsaye da ake hira da shi yana bayani.
Fitsari ne kawai Gwamna bai yi ba daga inda yake zaune jikinsa na ɓari. Ba zai iya cigaba da kallon videon ba dan haka ya ajiye wayar kawai yana huci wata zuciyar na riya masa cewa Asiya ce.
Ashe ba zata daddara ba, ashe ƙarya take da ta yi masa alkawarin ba za ta tona asirin Baban sa ba. Baban sa fa, Baban sa a gidan talabijin yana fallasa munanan laifuka daya aikata tun shekaru ishirin da suka wuce.
"Na maka alƙawarin indai ina tareda kai, zan taimaka maka wajen ganin ka wanzar da adalci a mulkinka"
Wannan kalamanta ne a ɗaya daga cikin dararen da suka kasance manne da juna cike da soyayya da shauƙi.
"Asya Adalcin kenan? Tozarta Baba na shine adalcin na ki" ya faɗa tamkar Asiyar na gaban sa.
Babu jirgin da zai tashi a wannan dare amma tabbas gobe da safe dole ya koma ƙasarsa.
Bai taɓa tunanin ranan daya kasance mafi soyuwa a gareshi zai iya juyawa ya koma baƙin ciki ba. Well thanks to Asiya.
ASYA! ya furta da kakkausan harshe...
25
A hankali Asiya ta maida wayarta cikin jaka ta ƙanƙame jakar kamar wanda 'yan dabaa ke shirin ƙwacewa. Dole ne first lady ta ji haushin rashin zuwan Asiya bikin 'yarta amma kuma dole ta mata uzuri duba da yadda aka wayi gari a jihar ta su.
Sau biyu tana yunƙurin ficewa daga ɗakinta amma ta kasa yin hakan.
Matasa sun je sun yi ƙone-ƙone a Kachallah house, duk da abun bai yi yawa ba amma ta sashen matar Alhaji Sani Kachallah an yi ta'adi sosai.
Ba zata bawa matasa laifi ba duba da irin cin amanar jiha da Alhaji Sani Kachallah yai shekara da shekaru. Idan har aka zauna aka yi lissafin kuɗaɗen daya danne sai an kame baki.
Har yanzu so take ta ji daga Gwamna amma ta kasa yunƙurin kiran numbar sa. Ta sani dole ne ya shigo gari yau duk da kuwa aikin gama ya gama dan Alhaji Sani ya miƙa kansa ga hukuma saura kawai a fara shari'a.
Ta sani wannan ne dama da take da shi akan Bilkisu amma kuma dole ne ta karya Chief of staff tukunna dan shine ƙashin bayan Bilkisu yanzu.
Bata san ya aka yi maganar Alhaji Sani ya tsaya mata a rai ba maimakon ya sakata farin ciki. Ko dan shi ɗin UBA ne?. Ba abu ne mai daɗi ba ace dattijo kamar sa wanda ya bawa shekara saba'in baya ya rasa daraja da martabarsa rana guda. Idan ta tuna yadda Halima da sauran 'ya'yansa zasu ɗauki wannan batu sai ta ji jikinta yayi sanyi.
Amma ta wani ɓangaren idan ta tuna sai ta ƙwammaci gara tonon asirin duniya da ta lahira.
Wani dogon numfashi ta sauke sannam ta miƙe ta ɗau wayarta da ƙaramin purse ɗinta ta fice daga ɗakin.
***
Tun daren jiya Chief of Staff ya kasa zaune ya kasa tsaye. Wannan ya biyo bayan rugujewar shirinsa lokaci guda. Babu yadda za ayi Alhaji Sani ya tafi Gambia sannan ya dawo a ranar haka kawai, sai dai idan ya san da maganar jaridar da za a fitar.
Asara sosai ya tafka saboda dole sai da ya biya kuɗin dameji saboda ba a isa a fitar da shafin farko na jaridar ba tunda abinda ya faru ya sha saɓanin abinda aka rubuta a jaridar.
Lokashi ɗaya yake son hamɓarar da Alhaji Sani sannan ya samu goyon baya daga shugaban Jam'iyya dan ya aiwatar da shirinsa na gaba.
Babu wanda ya zo masa rai gameda rugujewar shirinsa sai Asiya dan haka mafita ɗaya ya nema dan ya samu ya huce haushin asarar da yai a kanta. Shima wannan ɗin zai sake ruguza ahalin Kachallah ne...
Kamar yadda yai hasashe abinda ya faru ya dagulawa Bilkisu Kachallah lissafi, sannan a ɓangare ɗaya kuma ita ɗinma Asiya take zargi da wannan batu dan haka samfurin jaridar da COS ya bata shaida ce na cewa zarginta yana kan dai dai.
"She's trying to send my father to jail Mr Lamara. Ba zan taɓa bari hakan ya faru ba. Ba zan bari ta ci nasara akan Saifuddeen sannan ta ci nasara akan Babana ba"
Sun rabu ne da alwashin sai inda ƙarfinta ya ƙare akan Asiya amma sai ta hanata jin daɗin duniya.
***
Goshinta ne ya tattare ya cure waje guda yayinda idanunta suka Ƙwalalo waje. Lokaci guda ta bi jaridar da Gwamna ya wurga mata da kallo. Sample ɗin jaridar da CY ya aiko mata jiya kenan, jaridar da ta saka Alhaji Sani Kachallah ya fito ya bayyana laifukansa.
"Asya ta wannan hanya kika ɓullo. Kin blackmailing ɗinsa dan kawai ki tona masa asiri. Why Asya? Why kike son zubarwa mahaifina mutuncinsa. What else do you want bayan wannan?.
Tsillin Hawaye ɗaya ne ya samu damar saukowa daga cikin idonta ba tareda ta yi niyya ba.
"I'm dissapointed in you"
Kalamansa na ƙarshe suka kunce duk wani sauran kunya da take da shi.
"Saifuddeen!"
Yadda ta kira sunansa da tsawa ya sa shi kallonta cike da mamaki
"minene aure idan babu yarda?" Ta tambaya, ba tareda ta jira amsa ba ta ci gaba.
"Minene so idan babu gaskiya da amana? Wai ma minene aure idan babu magana ta fahimtar juna? Wai minene alaƙan da ke tsakaninmu idan har akwai zargi?. Minene banbancin farkon aurenmu da kuma abinda muka zamo yau. Wani irin mata da miji ne mu idan ba za mu iya gayawa junanmu gaskiya ba."
Wannan karan hawaye ne suke zubowa sosai babu ko tsayawa
"Kana tunanin zan maka ƙarya ne a bayan idon ka?. Saifuddeen da na sani alƙawari ya ɗauka akan idan ya tako Nigeria zai rufe ido yai mulkinsa bisa adalci da gaskiya. Amma Saifuddeen da nake gani yanzu, he's a coward.
"Shin kama taɓa tunanin yin amfani da damar ka wajen yiwa talakawa aiki? Kama taɓa yin wani huɓɓasa a karan kan ka wajen yiwa talakawa aiki?
"Ba zan bayyana maka gaskiyar jaridar nan ba amma ina so ka sani ko igiyar auren mu ka datse ba zan daina bibiyar mutanen da suka ci amanar jihar nan ba koda kuwa kai ne Saifuddeen"
Har ta bar falon bai iya rufe bakinsa ba. Wancan karan da ta gaggaya masa maganganu bai ji zafin su ba kamar yadda maganganunta na yau suka dake shi.
Ba abinda ya ƙara rikita shi irin kalamanta na ƙarshe.
Shi bai ma san mi zai yadda da shi ba. Ga jarida nan Bilkisu ta bashi amma maganganun Asiya sun sake dulmiyar da shi kan sanin gaskiya. Shin waye ya sa aka buga jaridar nan wanda tabbas ita ake shirin fitarwa kafin Alhaji Sani yai bayani a gidan talabijin.
***
Asiya Shahidah na ɗaukan sabon zango a shirinta na Asiya's Garden Badawiyya ta katse camerar lokacin da suka ji shigowar motoci cikin gidan.
Badawiyya tace "Ina ga kamar first lady ce ta shigo, da fatan kin tanadi bayani"
"Bismillah, tazo ina jiranta. Maganar ƙawarta Bintu zata yi ko kuma na ɗan yayarta ko ta mahaifinta?"
Ko minti uku bai cika ba sai ga Bilkisu ta doso inda suke, dake an kewaye wajen dole sai ta ƙofa ɗaya zaka shigo. Tana cikin tafiya takalminta mai tsini ya maƙale cikin ƙasa.
"Welcome to Asiya's garden, ki tsaya daga wajen a kawo miki takalmin gona" Asiya ta faɗa da ƙarfi muryarta cike da dariyar shaƙiyanci.
Bilkisu ta turo baki ta cigaba da tafiya tana yi tana tattaka albasar da Asiya ta shuka wanda sun fara fitowa sun yi tsayi.
Tana zuwa gaban Asiya ta ɗaga hannu zata kwaɗa mata mari Asiya ta riƙe hannun.
"Kar ki kuskura"
"Dani kike faɗa Asiya, leave my father out of this"
"Ni kuma? Mi ya ke faruwa? Ko dai dama da gaske ne Alhaji Sani ya sace miliyoyin kuɗaɗe?"
"How dare you say that! "
Bilkisu ta nuna ta da yatsa tace "wannan ce dama ta ƙarshe da zan baki Asiya, abinda zai biyo bayan wannan rana ba zai miki daɗi ba domin wutar da kika kunna a gida zai ƙona gari"
"I know how the game works Bilkisu Kachallah"
"Then be ready for a deadly game Asiya"
Daga faɗin haka Bilkisu ta juya ta tafi.
Badawiyya dake gefe ta riƙe baki tana faɗin "amma wannan mata akwai ƙarfin gwiwa, yanzu ko tsoron nata asirin ya tonu bata yi"
"Ƙyaleta. Ta ɗauka har yanzu ni Asiyar data tura kurkuku ce"
Badawiyya ta amsa da cewa " duk da haka ki bi a hankali bata da imani zata iya yin komai"
Da wannan suka cigaba da ɗaukan shirin nasu...
***
Koda Bilkisu ta koma gida kiran Tanko Janwuya tayi ta bashi wani sabon Umarni duk da de yanzu a hannun Alhaji Umaru Kwom yake karɓan kwangila amma ai ba zai manta da Uwarɗakinsa ba.
Bayan ta gama bashi umurni ya kece da dariya yace mata a shirye yake yai duk abinda take so matuƙar zai samu kayan aiki da kuma alkhairin da ta saba yi masa.
Bata da lokaci, yanzu ne dai-dai lokacin daya dace ta yi amfani da damarta kafin ya suɓuce mata.
Saura kwana biyar saƙonta ya iso. Ance mata wannan sinadarin is untraceable, ba za a taɓa iya gano asalin sa ba. Duk wani likita duk wani bincike da za ayi zai tsaya ne akan cewa damuwa da gajiya su suka haifar da shanyewar jikin Gwamna Saifuddeen.
Wani abu ya tsartu mata a zuciya mai kama da soyayya.
A hankali rana ta farko da zata iya alaƙantawa da ranan ne ta fara yiwa Saifuddeen soyayya data wuce ta 'yanuwantaka ya dawo mata.
Duk da tana shekarun da za a iya cewa bata mallaki hankalin kanta ba amma har wa yau ta sani ranan birthday ɗinta na cika shekara shabiyu a duniya da Saifuddeen ya bata kyautar rose flower ta ji a ranta idan ba Saifuddeen ba baza ta iya rayuwa da kowa ba har abada.
Zata iya rantsewa cewa har yanzu furen nan na cikin wani box da take saka jewelries ɗinta a chan gidan Saifuddeen.
A hankali kuma Shaiɗan ya ingizo mata wani tunani wanda akoda yaushe shi ke rinjayanta take aikata duk abinda ta sa a gaba.
Ta miƙe tsaye tana jaddadawa kanta ba zata bari wani abu wai shi SO ya rufe mata ido ba.
"Soyayyata gare ka Saifuddeen ya ƙare ranan da ka shigo da waccar matsiyaciyar rayuwar ka. Na tsani zama a ƙarƙashin ikon ka, ba dan kai ba da Baba ya bani dama na zauna a kujerar da kake zaune. I should be the Governor. I am the Governor"
Kamar kullum da wannan sunbatun Shaiɗan ya ribaci zuciyarta, ko kaɗan bata birkita da umurnin data bawa Tanko Janwuya ba.
**
Zuwa yanzu Gwamna ya fara fiskantar matsin lamba daga 'ya'yan jam'iyya dama shugaban jam'iyya na jiha wanda ke barazanar kai ƙaran sa zuwa ga shugaban Jam'iyya ta ƙasa.
Idan har aka kama Alhaji Sani Kachallah ba ƙaramin tozarci bane ga jam'iyyar su, Alhaji Sani Uba ne a cikin jam'iyya, Uba ne ma a ƙasar gaba ɗaya.
So ake yai duk abinda zai yi domin kashe wannan gobara data kunno kai. Hakan na nufin bayarda cin hanci dama yin abubuwan da suka kasance abin ƙyama a tsarin mulkinsa.
Bai san inda zai sa kansa ba, idan ya tsoma hannunsa cikin wannan shari'a duniya zata zarge shi sannan idan ya bari aka tura Alhaji Sani kurkuku to kamar ya tozarta mahaifinsa ne da hannunsa.
A wani ɓangaren kuma dukka matan nasa biyu babu wanda zai iya tunkara da neman shawara dan dukkansu ya san manufarsu daban ne.
**
A wani makeken falo kuwa Chief of staff na Gwamna wato Mr Lamara Damana ke zaune da wasu mutane guda huɗu. Dukkan su kuwa ana damawa da su a cikin gwamnati.
Cikon na biyar ɗin su ya zo ne minti goma shabiyu da fara tattaunawar su.
Mr Lamara yana ganinsa ya sake fiska domin shine mutum na ƙarshe da yake buƙata idan har kuwa ya zo tabbas ya nuna yana tare da shi kenan.
"Barka da zuwa Mr chairman Sir" Mr Lamara ya faɗa yana faɗaɗa murmushinsa.
"Just get straight to the point ka san akwai meeting gobe da safe"
Chairman ya faɗa yana duba agogonsa
Mr Lamara ya miƙe tsaye hannunsa ɗauke da wine glass dake ɗauke da wani sabon samfurin giya da aka kawo masa daga ƙasar Faransa.
"Mr Chairman na nemi kazo nan ne saboda mu nuna maka manufar mu akan wannan batu daya tada hankalin kowa"
Ya ɗan kurɓi giyan kaɗan sannan ya cigaba.
"kowa a nan ya sani Gwamna Saifuddeen Kachallah ba shi da ra'ayi irin namu kuma iya tsawon wannan lokaci Alhaji Sani da matarsa Bilkisu ke sa shi yin wasu ayyuka da mu 'ya'yan jam'iyya ke buƙata. To yanzu zance ya chanja, abubuwa da dama sun faru wanda yasa ahalin Gwamna Kachallah ke gab da rushewa."
Dukkan su suka bishi da kallo mai alamar tambaya idan ka cire Mr Paul wanda ya san kaso hamsin cikin tsare-tsaren da Mr Lamara yake yi.
"Mr Chairman ina so ka ɗauke ido akan maganar Alhaji Sani Kachallah"
Chairman ya bishi da kallon tuhuma
"Ina nufin ka bari a karya ƙashin bayan Gwamna Saifuddeen"
Kallon-kallon aka fara yi wasu kuma na magana ƙasa-ƙasa, har lokacin kuma Chairman ɗin bai yi magana ba.
Wannan ya bawa Mr Lamara damar jefowa Chairman ɗin wata maganar
"Mr Chairman Sir, ka dafa hannuna na zama Gwamnan jihar Congo"
Kowa a wajen ya zubawa Chairman ido ana sauraron mi zai faɗa.
Chairman dai bai bada gamsashshiyar amsa ba dan cewa yai amsar sa zata fito a meeting ɗin da za a yi gobe.
***
Bacci take amma bai yi nisa ba dan har lokacin tana iya jiyo karatun suratul baƙara ƙasa-ƙasa da ta kunna kafin ta yi bacci.
Wayarta ya ɗau ƙara bayan karatun ya tsaya chak. Ta sa hannu ta laluma wayartata dake kan side drawer ta manna wayar a kunne ba tareda ta buɗe ido ba saboda bacci dake cinta.
"Hello Adda, Adda Shahidah Mansur ne, an sace Ale, Wallahi ɗazu-ɗazun nan aka shigo gida aka sace Ale"
Zumɓur ta miƙe dan kalaman da take ji sun mata wani iri a kunne. Tukunna ma waye Mansur?
"Hello waye wannan? Ka san mi kake faɗa kuwa?"
"Adda Mansur ne, Mansur ƙanin Ɗahiru da Asabe ya kira mata sunayen 'yan ɗakinsu. Ɗazu ɗazun nan wasu 'yan bindiga suka shigo suka sace Ale..." bai ƙarisa maganar ba taji ana faɗin
"Kai Mansur wa kake kira, ba ance kar ku kira kowa ba..."
Sai kuma wayar ta yanke.
Cikin kaɗuwa Asiya ta shiga kiran numbar amma bai shiga ba, nan ta shiga kiran nambobin matan Ale amma duka babu wacce ta ɗauka hakan ya ƙara tada mata hankali ta shiga neman nambobin ƙannen mahaifinta dan numbar Ale kam a kashe take tun gwadawar farko.
Sai bayan kusan minti takwas da jin mummunan labarin daga wajen Mansur sannan Baffa Malam ya ɗaga kiranta ya sanar da ita abinda ya faru. Da gaske ne 'yan bindiga sun zo garin na su kuma sun ɗauke Ale da wani maƙocinsa.
Batun birkicewa kam ba a magana dan a ruɗe Asiya ta kira numbar Commissioner of Police tana masa tsawa akan a nemo mata mahaifi. Bayan ta yi wayar ne kuma hankalinta ya dawo akan ko Gwamna bata gayawa ba. Haka ta fito daga ɗakinta ta nufi ɗakin Gwamna waya a hannu tana zubda hawaye.
Duk wani fushi dake tsakaninsu ya gushe a zuciyar Gwamna lokacin da Asiya ta kwanta jikinsa ta fashe da kuka.
Ƙoƙarin rarrashinta ya fara duk da bai san mi ya faru ba, kukanta na raunata masa zuciya. Sai da ta samu ta ɗan nitsu kafin ta sanar da shi abinda ya faru.
Bacci ranan gaba ɗaya ƙaurace musu yai ba dan ya hanata fita waje bama da bazata kwana a gidan ba. Duk wani bayani na kwantar da hankali ya mata amma taƙi sauraronsa musamman ma data dinga masa izgili da cewa a Gwamnatinsa ne mutum yana kwance da iyalinsa za a shiga gida a sace shi.
Babu abinda zai iya yi mata, duk wasu jami'an tsaro da zai kira ya kira ya sanar da su halin da ake ciki amma a haka gani take bai yi komai ba.
Washegari da safe labari ya baza gari cewa an sace mahaifin matar Gwamna sannan a lokaci guda kuma labarin zama da Gwamna zai yi da shugaban jam'iyya na ƙasa ya fi komai ɗauke hankalin mutane saboda sun sani wannan zama ba komai bane sai wani yunƙuri da ake son yi dan ganin an wanke sunan Alhaji Sani Kachallah daga laifukkan daya aikata...
*Meeting ɗin ka yafi mahaifina kenan?* saƙon da Asiya ta tura masa kenan dai dai zai shiga mota.
Basar da saƙon yai dan bai san mi zai faɗa mata ba abinda ke gabansa ya fi ƙarfin fushinta. Bai san ya zai yi da zaɓin da Chairman ya bashi ba.
"Ka sadaukar da kujerar ka wa Alhaji Sani ko kuma ka sadaukar da adalcinka ka kuɓutar da shi"
Zaɓin da aka bashi kenan kuma kowanne aciki babu sauƙi. Wato idan har zai bari a cigaba da ƙaran Alhaji Sani to dole ne fa yai murabus daga kujerar sa. Idan kuma ya ce zai riƙe kujerar sa to tabbas dole ne yai duk abinda aka buƙata wajen ganin an wanke Alhaji Sani daga tarin laifuffukan daya aikata.
Kaman haɗin baki sai ga saƙon Bilkisu mintuna kaɗan bayan ya karanta na Asiya.
"Ina son mu yi magana, mu haɗu a gida in 10 minutes"
Ya ajiye wayar gefe ya maida kallonsa ga titi. Wannan abu da mi yai kama, idan da zai iya maida hannun agogo baya to da tabbas bai zama Gwamna ba.
Daga office Kachallah house ya wuce yai watsi da saƙon Bilkisu.
A ladabce ya gaishe da Baban nasa bayan ya samu waje ya zauna. Shi da jikokin sa biyu ne a falon suna wasa yana biyewa shirmensu.
"Idan aka kaini kurkuku ba zan samu wannan dama ba" Alhaji Sani ya faɗa fiskarsa ɗauke da murmushi
"Baba ba za je kurkuku ba" Gwamna ya faɗa a raunane.
"Ammar, Farhan ku wuce wajen GrandMa ɗinku"
Yaran suka fice da gudu bayan sun tattara kayan wasan su daga wajen.
Farar Jallabiya ce a jikinsa hakan ya bayyana faɗawar da yai domin hatta tumbinsa ya ɗan sake.
"Ka je ka yiwa iyayen Asiya jaje kuwa?"
"Na kira Baffanta a waya"
"Mi kake yi gameda lamarin?"
Ya sani sarai yana son ɗauke hankalinsa ne daga kan maganar kurkuku amma ba zai bari ba.
"Baba zan wanke sunan ka daga dukkan wani laifuka"
"Idan kayi hakan Allah ya isa tsakanina da kai"
A firgice Saifuddeen ya kalli Alhaji Sani wanda ko kaɗan bai ga alamar wasa a tattare da shi ba.
"Shi Chairman ɗin abinda ya ce maka kenan?"
"Baba..."
Alhaji Sani ya ɗaga masa hannu
"Ka maida hankalinka kan harkan tsaro babu ruwanka da wannan shari'a. Kar kayi ko ɗaya cikin abinda suka faɗa maka, duk wanda yai yunƙurin ɗagaka daga kujeran ka ni Alhaji Sani Kachallah zan ja dashi koda kuwa a kurkuku nake. Kar ka ɗaga hankalinka Saifu, babu wanda ya isa ya ja da kai"
Wannan magana dai kwantar masa da hankali ya kamata ace tayi amma sai ya zamana maganar ta ƙara ɗaga masa hankali ne dan ta fuskar da ya kalli maganar daban. Da Alhaji Sani da Party Chairman ɗin dukkansu na nufin kodai yai abinda suka ce ne ko kuma wani abu da ba a so ya faru a jihar ya faru.
Haƙarsa dai bata cimma ruwa ba dan ba haka ya so tattaunawarsu ta kasance ba. Amma tunda magana ta ƙare da Allah ya isa dole ne ya bi zaɓin mahaifinsa.
Yana fitowa daga Kachallah House Chief security na shi ya faɗa masa cewa akwai ziyarar da zai kai Asibiti dan haka chan ɗin suka nufa.
26
***
"Saƙo aka kawo wai a bawa Matar Gwamna"
Asiya ta tsinci muryar Almajirin dake magana a tsakar gida. Tana jin muryan Adda Yelwa na tambayar yaron wa ya aiko saƙon, yaron yace wani ne akan machine.
Asiya ta miƙe da ƙyar ta fito, tana riƙe da ƙofa ta amshi saƙon daga hannun Adda Yelwa. Yadda aka wrapping saƙon da wrapping sheet mai kyau harda ribbon a jiki yasa Asiya tunanin ko dai saƙon daga Gwamna ne?
Wani irin saƙo zai aiko mata haka kai tsaye.
Ta samu bakin gado ta zauna ta fara ƙoƙarin buɗe saƙon, tana buɗewa zuciyarta na fargabar abinda za ta tarar.
"Barka da shanruwa kenan daga Mai girma Gwamna?" Abida wata jikar Ale dake kwance a ɗakin ta faɗa.
Asiya ta yi murmushin yaƙe. Ba ta yi tunanin Gwamna ya damu da halin da ta ke Azumi ba, balle ya take shan ruwa. Kwana goma shauku kenan da sace Ale, kwana biyu kuma da aka yankewa Alhaji Sani Kachallah hukuncin zaman gidan yari na shekara shahuɗu.
Ta ya mutumin da yake cikin Alhinin zaman Babansa a gidan yari zai damu da matar da ta yi sanadin tura mahaifinsa gidan yarin.
Yau ana Azumi na huɗu kenan. A kowani rana tana ɗaukar Azumin ne da fatan kafin a sha ruwa Ale zai dawo gida. Daga irin adadin kuɗin da aka buƙata wanda kwata-kwata bai kama hankali ba yasa ta ƙara yadda da cewa an kama Ale ne da wata manufa ba domin kuɗi ba. Biliyan goma sai kace hauka.
"Anty Asiya ki buɗe mana mu ga ko sarƙan diamond Gwamna ya sai miki"
Abida ta faɗa cike da ɗoki, idonta ƙyam akan ƙaramin akwatin da ya bayyana bayan Asiya ta buɗe wrapping sheet ɗin.
Tun kafin Asiya ta buɗe ta fara jin tashin zuciya. Koma minene a cikin akwatin nan ba alkhairi bane, zuciyarta ya bata.
"Innalillahi!" Ihun Abida ya karaɗe ko'ina a ɗakin yayinda Asiya ta yi suman zaune.
Adda Yelwa dake shirin fita daga ɗakin ta juyo a fusace dan a tunaninta irin shirmen nan ne na 'yanmata idan sun ga wani abin ƙawa daya burge su.
Sai dai abinda ta gani yasa ta yi kan Asiya da sauri. A jikinta Asiya ta ƙarisa sumewa yayinda ƙaramin akwatin ya suɓuce ƙasa ya gangara hakan yasa idanuwa biyu dake cikin akwatin suka gangara ɓangare mabanbanta. Ɗaya ya tsaya a daidai tsakiyar ɗakin kusa da sallayar da Asiya ta bari ɗazu da ta yi sallar la'asar, ɗaya idon kuma yaje ya tokare dai-dai ƙasan ƙaramin fridge dake ɗakin...
***
Cikin hanzari ta shige office ɗinta ta banko ƙofa da ƙarfi. Ko kaɗan sawa da ta yi aka ƙwaƙule idanun Ale Faruƙ bai dameta ba, abinda ya dameta shine rasa inda ta saka saƙon da aka kawo mata kwana uku da suka wuce.
Shari'ar mahaifinta ne yasa ta bircike a 'yan kwanakin nan. Ta duba ɗakinta a chan gida sama da ƙasa amma bata ga inda ta adana saƙon ba, hatta akwatin sirri data ke ɓoye mahimman abubuwanta ta duba amma baya ciki, wannan yasa ta nufo office ɗinta rana tsaka dan ta duba ko anan ta bari tunda anan aka kawo mata saƙon.
Maƙudan kuɗin da ta bayar aka haɗa mata wannan gubar a Lab ba shine damuwarta ba. Abinda ya dameta shine yadda za ta aiwatar da plan ɗinta idan ta rasa wannan guba. Ba ta son wani abu da zai jawo a zargeta shiyasa ta yarda da wannan guban, a hankali zai ci jikin Saifuddeen ya kwantar da shi ya kuma shanye masa jiki gaba ɗaya.
"It is Untraceable" shine tabbacin da Baturen farfesan da ya jagoranci aikin ya faɗa mata.
Ta gama dube-dubenta amma babu pakitin saƙon balle abinda ke ciki.
"Why is luck not on my side?" Ta furta cikin ɓacin rai...
Lokacin da ta koma gida kusan ta cire rai da samun abin nan, tunaninta ya karkata wajen abinda zai faru idan guban ya faɗa mummunan hannu.
Tana shiga gida Safiya mai aiki ta tareta da wani abu a cikin leda wai John mai wanke mota ne ya kawo ya tsinta a cikin motar da ta fita dashi shekaranjiya. Yadda Bilkisu ta wafce ledar a hannun Safiyya kaɗai ya isa ya nuna maka abinda ke cikin ledan na da matuƙar mahimmanci.
Hannu na rawa ta buɗe box ɗin amma kash! Kwalbar dake cikin box ɗin ya ɗan fashe sannan gubar mai kalar omo ya malale a cikin akwatin.
In har akwatin nan zai zo Nigeria daga America ba tareda kwalbar cikin ya fashe ba tabbas wani ne ya buɗe akwatin ya fasa kwalbar.
Bilkisu ta shiga jijjiga sauran kwalbar ko zata samu sauran guban koda kaɗan ne, amma babu komai ciki.
"Lafiya ƙalau na bar akwatin nan ranan dana buɗe" ta faɗa kamar mai yiwa Alkali bayani.
Lokaci guda kuma ta tuno abinda ya faru ranan data buɗe akwatin bayan ta karɓa daga wajen ɗan saƙon daya kawo mata. Allah Sarki wanda baya ƙaunar zalunci.
Akwatin ya zo da ɗan key wanda da shi kaɗai ake iya buɗewa bayan an saka lambobin sirri akai (password). Ranan data buɗe akwatin ta duba guban dake ciki mantawa ta yi bata rufe akwatin da key ba balle har ta danna lambobin sirrin da ita kaɗai da Farfesan daya haɗo gubar kawai suka sani.
Sai yanzu ta tuna cewa akwatin ya buɗe da kansa ne ba tareda key ba. Kwalba ya fashe, guba ya tsiyaye, miliyoyin kuɗaɗenta sun tafi a banza, plan ɗinta ya dawo zero.
Ta saki wani dariya wanda yafi kama da ta masu taɓin hankali...
***
Sau uku kenan tana kela amai a cikin mota tun tasowar su minti talatin da suka wuce. Tun ma kafin ta ga wannan mummunan abu tana yawan jin tashin zuciya balle yanzu da ko ruwa ta kasa haɗiya ta daɗin rai. Tun jiya allurai da ruwa ake ta yi mata dan duk abinda ta ci sai ya dawo. Babu wanda zai ga ƙwayan idanun mahaifinsa cikin jini sannan ya iya haɗiyar ruwa.
"Anya ba za ki haƙura da tafiyar nan ba. Likita yace kina buƙatan hutu"
Adda Murja da ke riƙe da ita ta faɗa bayan ta goge mata baki da tissue paper.
"Kar ki damu tafiyar tawa tafi zamana mahimmanci"
Duk wanda ya ga Asiya a wannan yanayi sai ya tausaya mata.
Ita kanta Badawiyya sai da ta tsorata da ganin Asiya a bushe haka bata tunanin ko wanka ta yi dan fiskarta a bushe fayau kamar wacce ta yi kwana uku ba ta ga ruwa ba.
"Badawiyya ga 'yaruwata, Adda Murja " abinda Asiya ta faɗa kenan kafin ta wuce cikin gida.
"Yanzu mi kike shirin yi?"
Badawiyya ta tambaya tana tsare Asiya da ido
"Ki bani duk wani abunda na buƙata dan Allah, ba ni da ƙarfin yin dogon magana"
"Kar ki yi komai cikin fushi. A hankali zamu cimma burinmu kuma Insha Allah babu abinda zai samu Ale Faruƙ"
Wani kallo Asiya tai mata wanda ya sa ta haɗiyi sauran maganarta.
Shirun kusan minti biyu ne ya biyo bayan haka. Ganin shirun yai yawa yasa Badawiyya buɗe baki dan ta yi magana amma kuma muryan Asiya ya katse ta.
"What!" Ta faɗa a kiɗime cikin rashin gaskata abinda kunnenta ya ji
"Sun ƙwaƙule idanun Mahaifina Badawiyya" Asiya ta faɗa tareda fashewa da kuka.
"Subhanallah!" Badawiyya ta kama baki cikin kaɗuwa...
***
Meeting ne na gaggawa aka kira, domin duk wanda ya samu saƙon Asiya ba shi da sukuni a wannan rana. Ita kanta Bilkisu abinda ta ji ɗin shi ya sa ta kiran wannan meeting na gaggawa haka.
Kusan kowa ya halarta lokacin da Bilkisu ta iso ɗakin taron na su.
"This is a serious threat, idan waɗannan takardu suka fita waje sunan mu ya kaɗe" Mr Paul ya faɗa fiskarsa cike da bayyananniyar tsoro.
"Ya kamata a gano su waye suke blackmailing ɗinmu, idan kuɗi suke buƙata a basu "
Wani tsohon Kwamishina ya faɗa yana sake kallon takardar hannunsa.
Duk cikin waɗanda suka halarci meeting ɗin mutane biyu ne suka san inda takardun nan suka fito.
Magana Bilkisu ta fara, a hankali domin dawo da hankulansu zuwa ga matsaya guda. Wannan ne damar da za ta fito musu da maitarta fili. Tunda kowa yana da takardar da ke da shaidar cin hanci da rashawa da suka aikata ita babu wanda yake da shaidar laifukan ta.
"Ina so ku kwantar da hankalinku domin matuƙar ina nan babu wanda zai tona asirin ku"
"Anya ba Alhaji Sani Kachallah bane ya aiko mana wanɗannan takardu?" Mai tambayar bai sauke numfashi ba suka ji ance
"Ni ce nan na aiko muku su"
Gaba ɗaya suka maida duban su ga bakin ƙofa.
Riga da wando baƙaƙe ta saka sai baƙar blazer jacket da ya kai mata kusan cinya, kanta na sanye da baƙin ɗankwali ɗaurin turban, tana rataye da wani jakar goyo a kafaɗarta.
Bilkisu ta miƙe tsaye ganin wacce ta shigo ɗakin taron ba tareda gayyata ba.
"Na ga saƙon ku kuma nima zan miƙa saƙonninku ga hukumar EFCC da kuma 'yan sanda nan da awa ishirin da huɗu idan ba a fito min da mahaifi ba"
"What are you talking about?" Mr Paul ya faɗa dan yafi kowa tsorata. Shi da ya riƙe muƙamin Commissioner of finance kusan shekaru bakwai ba ƙaramin almundahana yai da kuɗin jahar ba.
"Ina ganin mutane biyu ne ba su samu saƙo na ba, wait a minute"
Ta sa hannu ta buɗe jakarta ta fiddo da wasu takardu ta ajiye su akan table dake wajen.
"Kashe tsohon Gwamna Saminu Bacchi, ɗaya. Safarar miyagun ƙwayoyi, biyu. Kasuwancin muggan makamai, uku. Cin hanci da rashawa, huɗu.
"Na cigaba da karanto su ko kuma na tsaya"
Wani dariyar takaici ta yi sannan ta ce "ga shaidu akan biyun farko sauran laifukan idan na ga Mahaifina zan iya cigaba da adana su, idan kuma kun hanani ganinsa to tabbas da wannan dake ƙasa da wanda ke hannuna duka za su kai ga hukumar EFCC sannan kowanni talaka zai gansu a gidajen talabijin"
"How dare you Asiya! Waya baki izinin shiga gonata balle har ki zo ki dinga gindaya mana sharaɗi"
"Kin yi mamaki ne, cewa na san komai amma ban tura ki kurkuku ba. Lokaci nake jira Bilkisu, idan lokacin ya zo wanda zai turaki kurkuku zai yi hakan ba tareda ya duba alaƙar da ke tsakanin ku ba.
Awa ishirin da huɗu kacal na bayar. Make your choice"
Tunda Mr Lamara ya fara duba takardun da Asiya ta ajiye gumi ya fara tsatstsafo masa shi da yake da burin zama Gwamna wannan takardun zasu iya tarwatsa duk wani abinda ya tsara. To ma wai ya hakan ta faru?
Written statement na Abdul Tsangaya. Waye ma Abdul Tsangaya?
A take da yai tambayar a ransa a take ƙwaƙwalwarsa ta bashi amsa ta hanyar tariyo masa abinda ya faru sama da shekara uku da suka wuce.
Shi da hannunsa ya bawa Abdul Tsangaya gubar da aka sakawa tsohon Gwamna Saminu Bacchi. Abdul Tsangaya kukun tsohon Gwamna ne.
Amma ta ina aka samo wannan? maƙudan kuɗi ya bashi na sallama kuma tunda suka rabu bai sake ganinsa ba, baima san inda yake ba. Kasancewar idan anyi sabon Gwamna akan chanja ma'aikata Abdul Tsangaya na cikin ma'aikatan da ba a sabunta contract ɗin su ba lokacin da Gwamna Saifuddeen ya koma gidan Gwamnati.
Shi bai damu da takardun safarar miyagun ƙwayoyin bama domin Bilkisu ya shafa kuma zai iya yiwuwa ta hannun Madam Bintu aka samo takardun amma wannan?
Takardar ya yi nuni da cewa akwai hiransu da Abdul ɗin ya naɗa lokacin da shi Chief of Staff Lamara Damana ya bashi umurnin sakawa tsohon Gwamna guba a cikin kwalbar giyarsa.
Itama Bilkisu lokacin data zauna ta fara duba takardun bayan fitan Asiya sai jikinta yai sanyi laƙwas.
Gaba ɗaya mambobin dake wajen sai suka zuba musu ido dan maganar kashe tsohon Gwamna baƙuwa ce a garesu...
***
"Shegu 'yan iska sun ga uwar bari" inji Badawiyya lokacin da ta saurari kanun labaran da aka karanto yanzu. An sako Alhaji Faruƙ Lukman Baba mahaifin Matar Gwamna Asiya Kachallah bayan an ƙwaƙwale idanunsa biyu.
"Da sannu dukkan ku zaku shiga hannu" ta faɗa tunowa da ta yi an yankewa Madam Bintu Chadi hukuncin kisa. Duk da Lawyoyinta sun ɗaukaka ƙara amma da alama akwai nasara idan an je kotun ƙoli ma tabbatar da hukuncin za su yi.
"Assalamu Alaikum" muryan wani namiji ya katse mata tunani
Da sauri ta maida dubanta ga bakin ƙofar dan ko ɗankwali babu a kanta.
A ɗan tsorace ta ce masa sannu yayinda ta fara neme-nemen inda ta saka ɗankwalin na ta.
"Illar zama mutum shi kaɗai kenan" ya faɗa yana murmushi.
Sai da ta samu ɗankwali ta rufe kanta sannan ta samu nutsuwar gaishe shi da kyau.
"Yanzu da kina da abokin hira ai ba za ki zauna cikin kaɗai ci ba ko"
"Lah Uncle Mustafah bafa ni ɗaya nake zama ba yanzu, akwai 'ya'yan yayyena Yusrah da Maimunah sun tafi makaranta ne"
Murmushi yai wanda yasa gefen idanunsa suka sake yanƙwanewa dan tanan kaɗai ake iya gane ainihin tsufansa.
Sai da ta kawo masa ruwa da vanilla cupcakes sannan ya fara bayanin abinda ya kawo shi.
"Na sake kawo ƙoƙon barata ne Rabi'ah. Ki taimaka min kafin na gama tsofewa kice ba zaki iya auren tsoho ba"
Dariya ya suɓuce mata amma ta gimtse ta maida dubanta ga 'yan yatsunta.
"Rabi'ah yanzu kam wacce kika ƙare ƙuruciyarki kina bibiya tana daf da samun hukuncin da ya dace da ita mi kuma ya rage miki banda ki tallafi wannan marayan dake gaban ki. Har gobe ina son ki Rabi'ah"
Hawaye ne ya ciko mata, ba dan taimakon Allah da kuma ƙwarewar Dr Mustafah ba da ta jima da mutuwa lokacin da Madam Bintu ta yi yunurin kasheta shekaru da dama da suka wuce.
Da taimakon Dr Mustafah ta kai matsayin da take kai yanzu, haka nan wannan shari'ar ta zo da sauƙi ne saboda shaidar daya bayar na yadda aka kawota rai a hannun Allah a lokacin.
Taya za ta ƙi tayin Dr Mustafah, idan bata amince da shi ba waye zai yarda ya aureta bayan babban illa da Madam Bintu ta mata a rayuwarta.
Itama ɗin iyayenta musamman mahaifinta sun sa mata ido akan ta yi aure. Mahaifinta kam har cewa yai indai ba miji ta kawo ba kada ta sake gaishe shi tunda ɗaukar fansa ta saka a gaba. To yau gashi ta samu abinda take so, kotu ta maida mata haƙƙinta na gado da kuma gadon ɗanta da Madam Bintu ta kashe yana ƙoƙarin leƙowa duniya.
"Rabi'ah har yanzu fa ban kai sittin ba, saura shekaru biyu sukutum a ƙasa" Dr Mustafah ya katse mata tunani.
"Idan ma aikin spy ('yar leƙen asiri) ɗin kike so idan kin shigo zan amince kiyi ɓadda kama son ranki a cikin gidana"
"Kai Uncle" ta yi murmushi mai faɗi
"Na ɗauki murmushin ki a matsayin amincewar ki?"
"Uncle Mustafah" ta sassauta murya"Maman Fadilah"
"Kar ki damu, da amincewarta na zo nan"
Badawiyya ta yi murmushi. Shima Dr Mustafan murmushi yai sannan ya tura lomar cupcake bakinsa...
27
Taron walima aka shirya dan nuna farincikin sako Ale da aka yi. Duk cikin mutanen gidan babu wanda ya san dalilin Asiya aka sako shi, sun ma fi tunanin ko Gwamna ne ya biya kuɗin fansar a fakaice ba tareda sun sani ba.
Duk da dai ana murnan dawowarsa, a ɓangare guda kuma ana alhinin abinda suka yi masa. Rashin idanu a shekarun tsufanka ba abu ne mai ɗaɗi ba.
Kusan tun da aka sha ruwa gidan ya cika babu masaka tsinke dan yadda ake ta raba abincin sadaka wanda duk da ana yi kullum tun sanda aka shiga Azumi amma na yau ɗin daban ne, hakan ya sa aka samu cincirindon mutane a gidan.
'Ya'ya da jikoki aka kewaye Ale ana jin labarin abubuwan da suka faru. Kafin a watse taro sai da aka kusan kai ƙarfe ɗayan dare.
" 'Yar lelena miya same ki na ga kin rame haka" Ale ya faɗa bayan ya shafa Asiya dake zaune gabansa.
Hawaye take ya sani, dan ya ji saukansu a hannunsa lokacin daya ke shafa ta.
"Haba Asiyar Gwani yanzu ba za ki godewa Allah ba. Mutane nawa aka kama ba su dawo da rai ba, murna za ki yi ba kuka ba Shahidah"
So take ta ce masa tana kuka ne saboda dalilinta ne aka kama shi, dalilinta ne kuma aka ƙwaƙule masa idanu.
Ta faɗa jikinsa kawai ta fara kuka a bayyane dan idan ta cigaba da riƙewa zuciyarta zai iya bugawa.
Shima bai hanata kukan ba dan ya sani hakan ne zai zama mata sauƙi. Ai akwai daɗi ka kwanta jikin mahaifinka ka yi kukan daɗi na cewa Alhamdulillahi yana raye kuma yana da lafiya...
Washegari Gwamna ya zo gaishe da Ale Faruƙ tareda yi masa jaje. Bai samu ganin Asiyar ba sai da zai tafi ita kuma ta shigo ɗakin Ale da alama bata san har lokacin yana nan ba ko kuma dai ta shigo ɗin ne dan su haɗu.
Kallon-kallon suke domin ta ido suke aikawa junansu saƙonni
"I'm sorry Asya" ya furta a hankali lokacin da ya matso kusa da ita.
Yana shirin taɓata ta wafce hannun tareda watsa masa harara.
"Baba ya ce in miki gaisuwa"
Tana da labarin shi ne ya matsawa Lawyoyin Alhaji Sani Kachallah dan a ɗaukaka ƙara kan hukuncin da aka yanke masa.
Sun jima suna aikawa junansu kallon tuhuma kafin Gwamna ya samu ƙarfin ficewa daga ɗakin.
Abin baƙin ciki abinda masoyan suka zamo kenan. Har ya fice daga ɗakin ba ta iya yin kyakykyawan numfashi ba saboda yadda ƙanshinsa ya gauraye ɗakin Ale. Wani ɓangare nata yana kewar kasancewa a ƙirjin shi tana jin bugawar zuciyar shi. Wani ɓangare nata yana kewar dogayen hannunsa da idan ya zagayeta da su take ganin tana cikin ni'ima da kwanciyar hankali.
Ba irin wannan rayuwar ta hasaso ba lokacin da suke chan America. This is not the return she planned for.
"Asiya kina ina?" Muryan Ale ya katseta
"Gani Baba"
Sai da ta zauna gefensa ya riƙo hannunta yace "Mijin ki ya fita ko?"
Gyaɗa kai ta yi kamar yana iya kallonta.
"Ki yi masa haƙuri kin ji, koma minene ya faru ba laifinsa bane. Gwamna yana iya ƙoƙarinsa Abin ne yafi ƙarfinsa. Na sani kina ɗaura masa laifin abinda ya same ni, amma idan kika duba da kyau zaki ga abinda ya faru yana daga cikin ƙaddarata babu yadda za ai na iya tsallakewa"
"Baba ƙaddara ne amma da sakaci. Akwai sakacin shugaba Baba, Gwamna mijina ne, ni na san baya ƙoƙartawa yadda ya kamata. He's a coward, he's just a coward" ta ƙarisa maganar kaman zata yi kuka.
"To ki yi ta masa addu'a mana, sannan ki taimaka masa da shawarwari ki kuma dinga tunasar da shi kowanni lokaci, kada ki taɓa gajiya da hakan kin ji shalelelen Gwani"
Ba dan abinda ya faru ba da sai tace ta yi mamakin kalaman Ale, wai shine ke yi mata nasiha mai taɓa zuciya haka...
***
Har aka ƙare Azumi aka yi sallah Asiya ba ta saka ranan komawa gidan ta ba. Ta bada mahimmanci wajen kula da mahaifinta. Ba dan ma albishir da Badawiyya ta mata ba na cewa Dr Mustafah ya kai kuɗin aurenta da ba za ta saka ranan komawa garin Congo ba.
Badawiyya tamkar 'yaruwa ce a gareta dan haka dole ta je ta tsaya a kan maganar bikinta.
Sallah da kwana takwas Asiya ta shirya komawa Congo.
*
Gwamna Saifuddeen Kachallah yana office ɗinsa wayoyinsa biyu suka hau ringing lokaci guda. Wayar farko numbar Asiya ke kira ɗayan kuma baƙon numba ne, truecaller ya kawo masa sunan Bashir Faruƙ Baba. Yayi mamakin ganin kiranta dan a lokuta biyu daya gwada kiran numbarta a lokacin Sallah da kuma bayan Sallah bata amsa kiran ba.
Har ɗan sandan ya gama bayani Gwamna Saifuddeen bai san inda kansa yake ba. Cikin gaggawa ya fice daga office ɗinsa yana maimaita Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun a bayyane.
Zama yai a kujeran dake gefen gadonta ya ƙura mata idanu. Ta yi fayau da ita abin har ya bashi tsoro, ko dan ya jima bai mata kyakykyawan gani bane.
A hankali ya fara bin zanen lallen da ke yatsunta wanda yadda suka yi ja zur da su suka ƙarawa yatsunta kyau.
Jini leda uku za a ƙara mata dan tana buƙatar jini sosai. Wanda aka saka mata na ƙaninta ne Bashir wanda yake aiki a Asibitin, shine kuma ya kira Gwamna lokacin da aka kawo Asiya jina-jina. Allah ma ya taimaka inda hatsarin ya faru kusa da gari ne da a haka jinin Asiya zai ƙare har ta mace babu taimakon gaggawa.
Ita da dreban ne kawai suka samu rauni mai tsanani amma Jummai dake bayan motar tareda Asiya ba ta wani ji ciwo na a zo a gani ba dan cikin hayyacinta polisawa suka kawo su Asibitin. Ita ne ma ta ƙwalawa Bashir kira lokacin da suka shigo Asibitin ta ganshi yana gaisawa da wani likita.
Asibitin General Hospital dake ƙaramar hukumar Giwo na ɗaya daga cikin Asibitocin ƙananan hukumomi da Gwamna ya gyara kwanan nan. Dan haka kusan duk wasu kayan aiki da ake buƙata akwaisu a Asibitin.
"Your Excellency gaskiya ba zamu iya cewa akwai abinda ya taɓa kanta ba har sai anyi CT scan" babban Likitan Asibitin Dr Muhammad ya bayyanawa Gwamna.
"Akwai abinda ya kamata ka sani Ranka shi daɗe"
Sai daya ja numfashi sannan ya cigaba "Hajiya Asiya ta yi ɓari, inaga ba zai wuce sati biyar zuwa shida ba, wannan nema ya sa ta zubar da jini sosai"
Har ya gama maganar sa Gwamna Saifuddeen bai ko ƙyafta ba daga irin kallon daya ke masa na rashin fahimta.
"Ban gane ba?" yai tambayar cike da fatan abinda Likitan ya faɗa kuskurene.
"I'm sorry your Excellency. Cikin dake jikinta ya zube" yai maganar da yaƙinin cewa Gwamna ya san da zaman cikin a jikin Asiya.
Gwamna ya sa hannu biyu ya riƙe kansa yayinda idanunsa suka ciko da hawaye...
*
Farkawar Asiya na farko a cikin motar ambulance ne, dishi-dishi ta dinga ganin mutanen ciki, ba ta iya ganin fuskar mutumin daya riƙe mata hannu ba dan ya mata tsayi dayawa kusan sakan biyar ta ɗauka kafin ta sake rufe idonta, tana jin wani murya sama-sama yana faɗin "I love you Asya, i really..." shikenan bacci ya sake ɗauketa.
Lokacin da Asiya ta farka na biyu da ƙarfin jikinta ta buɗe ido dan alluran da aka mata ya fara saketa. Babu kowa a ɗakin sai ƙaran na'orori da kuma ƙaramin fridge dake ɗakin.
Sai da ta kusa minti biyar a farke kafin aka turo ƙofar ɗakin aka shigo.
Kallo ɗaya ta masa ta gane cewa Likitan Gwamna ne.
"Your Excellency kin tashi, akwai inda ke miki ciwo?"
Asiya ta nuna kanta wanda har yanzu yana naɗe da bandeji.
"Bayan kan babu inda yake miki ciwo?"
Likitan ya sake tambaya. Asiya ta girgiza masa kai.
"Jummai, Jummai da Direba fa?"
"Suna nan"
"Babu abinda ya same su?"
"Ba sosai ba. Akwai allurar da zan miki yanzu"
Ta ɗan gyaɗa kai amma chan cikin ranta tana ganin kamar akwai wani abinda Likitan yake ɓoye mata.
Gwamna ne ya shigo ɗakin bayan fitan likita, suna haɗa ido ta kauda kai gefe.
Hannunta ɗaya ya riƙe ya kissing yatsunta.
"Yaya jikin ki?" Ya tambaya yana kissing tafin hannunta.
Akwai abubuwan da take son faɗa masa amma bata da ƙarfin dogon magana da shi. Ƙoƙarin janye hannunta tayi yai saurin riƙe hannun gam, ta bi hannunsu da kallo ba tareda tayi magana ba.
"Asya ki yi haƙuri dan Allah. Na sani ban kasance dake ba a lokacin da kika fi buƙatana, i'm sorry. Ki manta da komai mu dawo da farin cikin dake aurenmu"
Buɗe baki tayi kamar za ta yi doguwar magana amma abinda ya fito daga bakinta shine " ka sake min hannu"
"Shahidah please"
Ta so ace abinda ya faɗa mai sauƙi ne amma babu sauƙi ko kaɗan. Matuƙar yana Gwamna ba za ta iya rufe ido ta ɗauke shi matsayin mijinta ba, yes mijinta ne babu shakka amma a lokaci guda kuma shi ɗin shugaba ne wannan kuma yafi komai mahimmanci. Idan har zai zame mata miji nagari a cikin gida amma a wajen talakawa zai zamo azzalumin shugaba, minene ribarta.
Babu ta yadda zata manta da abubuwan da suka faru domin ko ta manta irin haka ba zai daina maimaituwa a rayuwarsu ba matuƙar dukkansu biyun basu fiskanci alƙibla ɗaya ba.
Ganin ta ƙi kula shi sai ya miƙe tsaye ya kissing kumatunta yana mata addu'ar samun lafiya.
Bayan fitansa ta maida dubanta ga ƙofar tana jiran ya sake buɗe ƙofar ya shigo wannan karan ya rungumeta jikinsa yace ya yadda da ita ɗari bisa ɗari ba zai sake zarginta ba.
***
Bilkisu Kachallah ta kasa zaune ta kasa tsaye. Agogon office ɗinta ya nuna ƙarfe huɗu da rabi na yamma. Tunda aka gaya mata Asiya na nan da rai hankalinta ya tashi, ƙarin baƙin cikin shine babu wani ciwo da ta ji na a zo a gani . Labarin daya ɗan daɗaɗa mata rai shine ce mata da aka yi Asiya ta yi ɓari. Wato dama ashe ciki gareta, cikin Saifuddeen.
Ta riga ta ɗau alƙawari a wajen meeting ɗinsu kan cewa za ta kawo ƙarshen matsalar Asiya. Waɗannan mutane suna tsoron hukumar EFCC kamar yadda su ke tsoron mutuwarsu. Ita kam ba damuwarta ba kenan, ta fi damuwa da ƙuri'un da talakawa zasu jefa mata idan lokaci ya zo, hukumar EFCC ba za su iya taɓata ba.
Dole ta yi wani yunƙuri akan Asiya amma kafin nan bari ta samu ganawa da mataimakin Gwamna tukunna.
***
"Your Excellency shugaban gidan jaridar The Daily Breeze yana jiranka"
Gwamna Saifuddeen ya amshi takarda daga wajen Sakatarensa sannan yace "kace ya shigo"
Bayan ya saka hannu a takardun ya miƙa wa Sakatare su dan a miƙa su ofishin da suka dace.
"Your Excellency"
"Mr Odu"
Gwamna ya kira sunan mutumin yana faɗaɗa murmushinsa.
Sai da Gwamna ya mai nuni da kujera sannan Mr Odu ya zauna har lokacin bai bar yin murmushi ba.
Gwamna ya buɗe drawer dake manne da table ɗinsa ya ɗauko wani jarida ya ajiye gaban Mr Odu.
Ko da Gwamna bai ce komai ba, Mr Odu ya riga ya san mi Gwamnan ke nufi da jaridar. Cikin biyu ne yai ɗaya, ko ya faɗi gaskiya ya samu dama a wajen Gwamna ko kuma yai ƙarya ya sake matse Mr Lamara Damana akan ya ƙara wasu maƙudan kuɗaɗe dan ya rufa masa asiri...
***
Ƙarfe uku da minti hamsin da tara na yammacin ranan Alhamis Asiya ta idar da sallan la'asar, sati ɗaya kenan da sallamarta daga Asibiti. Ita da Gwamna babu wani maganar kirki da ke shiga tsakaninsu dan gani take indai bai dena zargin da ya ke mata ba babu yadda za ayi su fahimci juna.
Banbancin wancan zamansu da wannan shine wannan karan a ta ɓangarensa yana ƙoƙarin tuntuɓarta a duk lokacin daya shigo gida. Duk da haka sam ta ƙi sake masa fiska sai dai idan a gaban 'yanuwanta ne dan tunda aka sallamota gidan nasu baya rasa 'yan ziyara.
Har yanzu tana mamakin wannan hatsari, duk da ta yarda ƙaddara ne kuma Alhamdulillahi babu wanda ya rasa rai cikin su ukun amma duk da haka hatsarin na su akwai ayar tambaya a ciki. Babbar motar da ta far musu an nemeta an rasa. Ta yi ƙoƙarin kauda tunanin a ranta kar ya jawo mata damuwa.
Wayarta ta ɗauka ta danna nambar Badawiyya, ta zo ta gaisheta sau ɗaya a Asibiti daga nan ko waya ba su sake yi ba, ba ta ga laifinta ba tunda aurenta da Dr Mustafah dududu yanzu bai wuce saura kwana takwas ba.
"Amarya" ta faɗa tareda ƙyalƙyalewa da dariya
Tana cikin waya aka turo ƙofar ɗakin. Ganin wanda ya shigo yasa ta fara ƙoƙarin yiwa Badawiyya sallama.
Jingina bayansa yai da jikin bango ya harɗe hannayensa a ƙirji ya zuba mata manyan idanunsa. Har ta cire wayan daga kunne kana iya ganin burbuɗin murmushin dake maƙale a fiskarta.
Suna haɗa ido ta ɗan haɗe rai, ta sa hannu ta fara wasa da duvet da aka shimfiɗa akan gado.
"Miyasa ba ki faɗa min ba?"
Ta ɗan ɗaga gira sama alamar rashin fahimta.
"Baba yace ke kika shirya mana tafiya Gambia kwanan baya"
To mi sanin na shi zai mata tunda dalilin tafiyar ne yake ganin ta shirya tozarta mahaifinsa a bayan idon sa.
"Ba wannan kaɗai ya faɗa ba"
Jin shi ta yi tsugunne a gabanta yana ƙoƙarin riƙe hannunta.
"Ya ce min ke kika sanar da shi maganar jaridar da aka shirya wallafawa a bayan idonsa"
Wato ya je duba Alhaji Sani a gidan yari kenan. Allah Sarki! lokacin da aka kaita chan ai bata samu wannan gatan ba.
"Ya faɗa min Mr Lamara Damana ne da wannan aiki amma duk da haka sai da nayi bincike na tabbatar"
Kallon cikin idanunsa tayi wanda dama shi tuni ita yake kallo. Wato ma bai yarda da mahaifinsa ba kenan ko kuma dai bai yarda a zuciyarsa cewa ba ita bace ta yi wannan aikin.
"Asya ina son ki sani cewa na yarda dake"
"Hmm daga baya kenan" ta faɗa da muryan shaƙiyanci
"Ka riga ka nuna min babu yarda tsakaninmu"
Ya ji daɗin da ta tanka masa wannan ya bashi damar cigaba da maganarsa bayan ya samu guri ya zauna gefenta.
"Ki yafe min idan abinda kika fahimta kenan. A mafiya lokuta taƙaitacciyar amsa za ta gamsar dani wani abun amma..."
"Amma tambayoyinka sun fi kama da tuhuma, sun fi kama da tabbacin zarginka kake buƙata ba bayanin gaskiya ba. Your Excellency na dawo daga rakiyar irin wannan..."
"I'm sorry" ya riƙo hannunta na hagu ya manna a ƙirjinsa hakan ya sanya mata wani shock ya hanata ƙarisa maganar da take.
"Na amince da duk abinda zaki faɗa koda zaki dinga kirana da kalmar dana fi tsana"
"Mi kenan?"
"You called me a coward, kin tuna?"
Ta sauke idanunta ƙasa tana tunanin rashin kyautuwar kalmar duk da dai abinda ta faɗa ɗin gaskiya ne.
"Idan ba ka so na kiraka hakan sai ka chanja halayenka"
"Na sauke Lamara Damana"
Ta kalle shi cikin sauri.
"Abinda ya kamata na yi kenan tun jimawa amma na kasa"
"Ki yafe min kin ji. I really need you, idan babu ke a tare da ni ba zan iya aiwatar da abinda ya dace ba"
Anya zai iya abinda za ta ce kuwa? Anya zai iya bata yarda da amincewarsa ba tareda zargi ba?
Anya zai yarda idan ta faɗa masa babbar matsalarsa a wannan jiha ba Chief of Staff bane, babbar matsalarsa matarsa Bilkisu Kachallah ce.
"Can i hug you? " ya dakatar da tunaninta lokaci guda kuma ya haɗata da jikinsa, a tare suka sauke ajiyar zuciya kowanne da tunanin dake ransa amma sun haɗe a abu guda, kewa.
28
Mataimakin Gwamna ya sake gyara zamansa saboda abinda Asiya ta faɗa masa kwanan baya yana faruwa. Ta gaya masa Lamara Damana zai zo wajensa sannan Bilkisu Kachallah ma za ta zo, kuma dukkansu buƙata ɗaya za su kawo masa amma manufarsu daban ne. Kwana biyu kenan da zuwan chief of staff gidansa yau kuma ga Bilkisu Kachallah zaune a gabansa tana masa makamanciyar maganar da suka yi da Lamara Damana.
"Saifuddeen ba zai iya ci gaba da mulkan jahar nan ba. Ka sani sarai lokacin da Yallaɓai ya jawoka wannan Gwamnati ba haka jam'iyyarmu take ba, amma ka dubi yadda Saifuddeen ya ɓata lamurra. Idan har zai iya kauda kai ya bari a tura Uban daya masa duk wani gata da yake taƙama da shi kurkuku, ai ni da kai da sauran 'yan jam'iyya ba zamu tsira ba.
"Saifuddeen dana aura kusan shekara ishirin da suka wuce ba shine na ke aure yanzu ba, gaba ɗaya ya chanja ya zama wani mutum daban. Dan haka inaga wannan ne damar ka wajen samun kujerar da ta fi kowanne daraja a jihar nan"
"Hajiya Bilkisu idan na fahimce ki da kyau, so kike a kauda MIJIN ki daga kujerar sa"
"Exactly"
"Ta yaya hakan zai faru? Gwamna Saifuddeen yanada sauran shekara guda a gaba"
"Ka yarda da buƙatata sauran ka bar min komai a hannuna"
*"zasu zo maka da batun ɗaga darajar ka. Kowannensu zai maka alƙawarin zama Gwamna nan da lokaci ƙanƙani, amma ina so ka tuna yadda suka kashe tsohon Gwamna kuma suke ƙoƙarin kauda Gwamna Saifuddeen kaima idan ka faɗa tarkonsu ba tsira zaka yi ba. Zaɓin ka ne ka biye musu ko kuma ka aikata abinda ya dace, amma ina so ka sani cewa ina gab da tona asirinsu a idon duniya, idan ka bi sahunsu kaima ba za ka tsira ba"*
Mataimakin Gwamna Alhaji Bala Yamai ya tuno maganganun Asiya Kachallah.
Ya ɗan gyara zaman shi sannan ya sassauta muryarsa yace " minene buƙatar ki?"...
***
Cikin sauri Mr Lamara Damana ya fito daga mota zuciyarsa fal da farinciki saboda nasara da ya samu a gurin mataimakin Gwamna, yanzu ne zai ji daɗin kassara Gwamna Saifuddeen da uwargidansa Bilkisu Kachallah.
Dukkansu babu wanda zai samu damar siyan form na jam'iyyarsu balle har su yi tunanin fitowa takara a zaɓe mai zuwa. Party Chairman yana tareda shi dan haka komai zai zo da sauƙi.
Hannunsa ɗauke da ƙatuwar envelope ya shigo katafaren office ɗin Gwamna. Sai dai yana ƙoƙarin wucewa ciki Sakataren Gwamna ya dakatar da shi.
Tunaninsa ko Gwamna baya ciki ne amma sai ya tsinkayi Sakataren yana faɗin "His Excellency ya bada umurnin kada a bari ka shiga"
"Mi hakan ke nufi?" Ba tareda ya sauke numfashi ba ma'anar hakan ya dira masa a ƙwaƙwalwa kamar dirar mikiya.
"Akwai saƙon Gwamna a wajen Sakatariyarka"
Bai yi wata-wata ba ya juya zuwa nashi office ɗin
Takardar daya tsammanta ɗin Sakatariyarsa ta damƙa masa.
Ba zai karɓi wannan ba. Ya zo ne domin ya bada takardar ajiye aikinsa ba wai dan ya karɓi takardar kora daga aiki ba. Saifuddeen bai isa ya masa haka ba, bai isa ya walaƙanta shi haka ba.
Ya koma office ɗin Gwamna da sauri...
*
"Mr Chairman" Bilkisu ta kira da sigar jan hankali.
"Idan aka fara wannan case zamu samu matsala da manyan mambobin mu"
"Shhhhh" Bilkisu Kachallah ta ɗaura yatsarta akan ƙaton leɓensa. Ta kashe masa ido lokaci guda kuma ta jawo kansa ta manna da ƙirjinta. Babu namiji lafiyyayye da zai ji ƙanshin turarenta ba tareda ya motsa ba balle kuma mutum kaman party Chairman wanda baya kwana biyu bai nemi mace ba.
Lokacin da ta shiga banɗakin hotel ɗin ta sakewa kanta ruwa ji take jikinta na mata wani irin zafi duk da sanyin ruwan dake dukan jikinta.
Bata taɓa yi ba.
"Saifuddeen" sunan ya fito daga bakinta amma saboda ƙaran ruwan ba za ka iya banbance amon sautinta da kuma saukan ruwan ba.
Ko suna daɗi ko basa daɗi. Duk lokacin da Saifuddeen zai kusanceta yana binta ne a hankali, yana ɗaukan lokaci ya faranta mata rai kafin ya bada mahimmanci wa nashi buƙatar. Bai taɓa mata zuwan dabbobi ba, bai taɓa ɗaura mata jikinshi ba tareda ya tabbatar tana da buƙatarsa ba. A lokuta guda biyu da hakan ya taɓa faruwa tana ce masa " i don't feel like it " ya ɗaga jikinsa ya koma gefe yana furta kalmar "i'm sorry" duk da ya kasance cikin buƙata
Saifuddeen bai taɓa shigarta ta inda Allah ya haramta ba.
"Saifuddeen" ta sake kiran sunan, wannan karan da tsananin kewa. Rabon da ya taɓata, rabon da ta bashi damar taɓata, rabon da ta saurara mishi a lokacin da ya nuna alamun yana son taɓata. Yau shekara guda kenan. Shekara ɗaya da adadin kwanakin da baza ta iya tunawa ba.
Yau ga shi Party Chairman ya mata abinda ko a mafarki bata taɓa tunani ba. Saboda me?. Saboda tana so ya ingiza 'yan majalisa su tsige Saifuddeen.
Saifuddeen mutumin da duk yadda ta kai ga tsanarsa hakan bai goge soyayyarsa dake maƙale a zuciyarta ba, duk da a kullum tana yaƙi da ɓangare na zuciyarta dake jin son sa.
Ta sa hannu ta shafa manyan mazaunanta wanda haihuwa da girma suka ƙara buɗa mata su. Ta sa hannun a takashinta tana jin wani irin zogi na ratsata har tsakan kanta.
Wani ɓangare na zuciyarta, wannan ɓangare da a kullum ke cin galaba gameda tunaninta ya hasko mata kanta zaune a kujerar Gwamna.
"Idan an sha wuya ake jin daɗi Bilkisu, kin jure fiye da wannan ma. Ki bari idan kin zama Gwamna sai ki ɗau mataki akan Party Chairman"
Da wannan nasihar ta ɗan samu nitsuwa kaɗan a ranta...
*
"Bilkisu"
"Na'am" ta faɗa a ɗan tsorace dan bata yi tunanin akwai mutum a wajen ba.
"Are you Ok?"
Tayi saurin kauda idonta daga yadda ya riƙe mata su da nashi idanun. Kallon tuhuma yake mata ta sani. Ko dai ya ga tabo a jikinta ne wanda ya nuna masa irin yadda Party Chairman ya dinga shigarta kamar wata karya.
So take ta tambayeshi mi yake a falonta ƙarfe goma shaɗaya na dare amma tambayar da ya fito daga bakinta daban.
"Mi kake yi baka yi bacci ba?"
Shima ɗin so yake ya tambayeta ina ta je amma ya musanya tambayar da cewa "Gobe za'a sallami Nana daga Rehab ina so na je na ɗaukota, zamu biya Sudan wajen Mahira daga nan sai na kawota gida"
Nana, Mahira. 'Ya'yanta fa kenan. Ita ɗin fa uwa ce.
*"I Bilkisu Sani Kachallah. Do solemnly swear"*
Ta hango kanta a gaban Alkali ana rantsar da ita.
"Sai da safe" ya faɗa tareda wucewa ta gefenta ya buɗe ƙofa ya fice daga falon. So take ta riƙe shi, tace masa yai haƙuri ta ci amanarsa, amma ta kasa yunƙurin yin komai har ya fita.
Ko jakarta bata ɗauka ba daga inda ta ajiye shi bakin ƙofa haka ta wuce cikin bedroom ɗinta dan ta kwanta ko hakan zai sa ta samu nitsuwa...
Ƙarfe tara na safe ta tashi da bugun ƙofar mai aikinta.
"Waye?" Ta faɗa da muryan bacci.
"Safiyya ce Your Excellency"
"Minene?"
"Akwai wasu manyan baƙi suna jiran ki a babban falo"
Bata amsa mata ba ta dafe kanta dake mata ciwo.
Kusan minti arba'in ta ɗauka sannan ta fito shirye cikin wata rantsatstsiyar leshi ja mai duwatsu baƙaƙe.
Ba ta ɗauka baƙin zasu jirata ba amma sai gashi sun zauna jiranta kamar wasu 'yan maula.
" wannan walaƙanci ne Boss, kin san tun yaushe muke jira kuwa" mutumin da ta shaida shi da Alhaji Baffale ya faɗa cikin ɓacin rai.
Da a da ne ko kusa ba zai iya ɗaga mata murya ba balle har ya mata tsawa.
Ta samu kujera opposite da su ta zauna.
"Dole ne ku fito mana da matsaya ɗaya, mun gaji da raba mana alƙibla da kuke yi"
"Alhaji Baffale calm down. Idan baka yi magana a nitse ba taya zan fahimce ka"
Sai a sannan ɗayan wanda shima tsohon Kwamishina ne ya fara magana.
"Jiya ba kya gari Lamara Damana yai meeting yana neman mu mara masa baya a zaɓe mai zuwa, yana so jam'iyya ta bashi tiketin zama ɗan takara a Primary election da za a yi nan bada daɗewa ba. Kema kin yi irin wannan magana a ranan da kika yi alƙawarin zaki yi maganin Asiya Kachallah. Wai wanne a cikin ku zamu bi ne?"
Dariya mai ƙarfi Bilkisu ta sake tareda tafa hannu. Lallai kam! dama ance makashinka yana tareda kai.
Lamara Damana yana so ya ci amanarta, ko kuma ma ya riga ya ci amanarta. Sai kuma ta tuna cewa yasan kusan duk wani sirri nata, hakan yasa ta daka tsalle kamar wata zararriya ta wuce cikin ɗaki da sauri.
Ko mi ta ɗauko oho, dan bata yiwa baƙin nata magana ba ta fice daga falon. Masu tsaronta dake bakin ƙofa suka bi bayanta cikin sauri.
Kai tsaye gidansa ta wuce dan tanada labari daga wajen Party Chairman cewa mijinta ya sauke chief of staff ɗinsa.
Kusan babu shamaki tsakaninsu dan haka har ta kai falonsa babu wanda ya hanata shiga. Tana shiga falon ta same shi yana sipping giya a hankali yayinda yake duba wasu takardu.
Wata ƙaramar bindiga ta fito dashi daga cikin jakarta, ta nuna shi da bindigar, zuciyarta cike yake da tsanar Baƙin guntun mutumin dake zaune gabanta.
"Yau zan kashe ka na kashe banza"
"Shin za ki so ki ji batun sirrikanki dana sanar da Asiya ko?"
"Kai baƙin Arne!" ta daka masa tsawa tareda saka hannu biyu ta riƙe bindigar da kyau tana daf da sake harsashin.
Wata mahaukaciyar dariya Lamara Damana ya fara.
"Na yarda ni baƙin Arne ne, ke kuma fah?"
Ya sake fashewa da dariya yace " gara ni mahaifina Bamaguje ne, mahaifiyata kuma a sama ta tsinci addinin Kiristanci, ban taɓa iƙirarin ina bin wani addini ba dan haka abinda kika faɗa yana kan dai-dai"
"Shut up! ko na bindige mummunan bakinka"
"Idan kina so zamu iya haɗa hannu ki zama mataimakiyata, at least idan ba ki yi amfani a office ba za ki min amfani a cikin ɗaki"
Yawu ta furza masa har lokacin bata sauke bindigar ba, tace " Allah ya kiyaye na zauna a ƙarƙashinka. Ba zaka taɓa samun abinda kake so ba, ni da kaina zan kashe ka"
"Bilkisu kenan, na jima da sanin cewa maganinki ya karye dan haka babu abinda zai sa naji tsoron ki. Ko da yake ya kamata na ji tsoron matar da take ƙoƙarin kashe mijinta saboda kujerarsa"
"Ba kashe Saifuddeen zan yi ba, i will never kill him"
Mr Lamara Damana ya sake bushewa da dariya harda buga ƙafa.
"Hakane. Ba kashe shi zaki yi ba, so kike ya ƙarisa rayuwarsa a kwance. Wannan ma abin dubawa ne"
"Mi ka gayawa Asiya?, mi ka bata?"
"Kiyi tunanin matakin da zata ɗauka idan ta san kina ƙoƙarin kashe mata miji. Af. Na manta ita ɗinma kin yi yunƙurin kasheta ai"
Hannunta ne ya shiga rawa dan lokaci guda wani tsoron Asiya ya shigeta.
Lamara Damana ya cigaba da dariya ko ba komai yau ɗaya yaga tsananin tsoro da damuwa a tattare da Bilkisu Kachallah.
29
Tunda Asiya ta ji bayanan Mr Lamara Damana a waya ta rasa sukuni. Duk da ta sani Saifuddeen ya tafi ƙasar America ɗauko 'yarsa amma hakan bai hanata tsorata ba.
Ashe Bilkisu za ta iya tunanin kashe Saifuddeen balle ma har ta yi yunƙurin yin hakan? Lallai kam ta raina hatsabibancin matar nan. Ce mata da ya yi wai hatsarin da ta yi Bilkisu ce ta sa a kasheta bai ɗaga mata hankali ba, amma Saifuddeen. Mijinta ne fa, uban 'ya'yanta. Kai Bilkisu hatsabibiyace.
Sai da ta yi waya da Gwamna kafin hankalinta ya ɗan kwanta ta samu damar cigaba da shiga shagalin bikin Badawiyya.
Wani abu daya mata daɗi shine tunda Mr Lamara ya iya gaya mata waɗannan sirrikan kenan abubuwa sun ɓaci tsakaninsu. Dama kuma hakan take so.
Idan Gwamna ya dawo zata gwada masa maganar Bilkisu ko zai amince yai takatsantsan da lamurranta.
***
A ɓangaren Bilkisu kuwa ta rasa ina zata saka ranta ya mata daɗi, duk wasu abubuwanta na shirin kwaɓewa lokaci guda. Idan ta bari aka tsige Saifuddeen kamar yadda ta gayawa Party Chairman, Mr Lamara zai yi amfani da wannan damar ya hanata samun damar zama mataimakiyar Gwamna.
"Ke wawiya ce Bilkisu. Ba kya ganin mi yake son yi ne. So yake a tsige Gwamna shi kuma ya kayar da mataimakin Gwamna a lokacin zaɓen Primary elections sai ya zama shi kaɗai ne ɗan takara mai ƙarfi a jam'iyya"
Ta riƙe kai tana furzar da iska lokaci guda kuma jikinta ya shiga ɓari. Tayi saurin jawo wasu ƙwayoyi dake cikin purse ɗinta ta watsa bakinta.
Duk wani namiji ta tsane shi. Su maza basu da amana ko kaɗan. "Mi zan yi? mi zan yi?" Ta fara tambayar kanta kamar wata zararriya.
"Ki zama Asiya" wani ɓangare na zuciyarta ya bata amsa.
Ta miƙe daga kan gado tana neman abinda Asiya zata yi idan ta shiga irin wannan yanayi.
Gaba ɗaya wunin ranan ya tafi ne wajen tunani. Sai da ta fidda rai da samun mafita sannan wani shawara ya faɗo mata wanda take tunanin da shi zata yi maganin Mr Lamara da kuma Asiya.
***
Asiya tana karatun Qur'ani bayan ta idar da sallar Magariba ta ji sallama.
Maimuna ce sabuwar ma'aikaciyarta da ta ɗauko daga garinsu.
"Anty kina da baƙuwa"
Sai da Asiya ta kai ayar da take karantawa sannan ta amsa mata
"Kice ina zuwa"
Bayan ta ƙare shafin da ta ke ciki sannan ta rufe Qur'anin ta fito ko hijabin da tai sallah da shi bata cire ba.
Wa za ta gani a falon banda matar da basa ga maciji da ita.
"Labule kika chanja a falon?. Wannan painting ma baya falon nan da" ta yi maganar tana nuna wani wall paint na furanni dake manne jikin bango.
"Na san ba maganar chanja labule ne ya kawo ki ba"
"Tabbas" idanunta ya sauka akan na Asiya dai-dai ta zauna kujerar dake kallon nata. Wani kishi ne ya motso mata yadda 'yar wannan yarinyar ta shigo gidanta ta mamaye komai. Hankalinta kwance babu wani alamun damuwa a tareda ita.
Wai 'yar wannan yarinyar, jikar maiƙusumbi ta fi ta gata da kwanciyar hankali a jihar nan.
Asiya ta maida kallonta ga tasbahar da take ja dan wannan ya fi mata mahimmanci akan shirun da suka yi dukkannsu biyu.
"Idan kika tona min asiri, asirin Saifuddeen zaki tona"
Asiya ta ɗago ido ta kalleta a fusace.
"Mi kike nufi?"
Bilkisu ta tura mata wasu takardu kan wani glass table dake tsakiyarsu.
Asiya ta ɗauki takardun ta fara karantawa.
Tana gamawa ta kalli Bilkisu cike da ɓacin rai
"Shi kansa Saifuddeen ba zai iya tuna lokacin daya cire waɗannan kuɗaɗen ba amma saboda shi ya cire su inaga hukumar EFCC ba za su zurfafa bincike ba idan suka samu waɗannan takardu"
Ta ɗan matso da kanta ta ce " na sani ba a kama Gwamna idan yana kan kujerarsa amma kinaga 'yan majalisa zasu yi shiru idan suka ga wannan? To ace ma ba a tsige shi ba kina ga bayan ya ajiye mulki ba zai ƙarisa rayuwarsa a kurkuku ba? Bana tunanin da ƙuruciyarki za ki zauna zaman jiran mijin da zai yi zaman shekaru shabiyar ko ashirin a kurkuku"
Ta sani wannan kuɗin an cinyesu ne a lokacin da Gwamna yake ƙarƙashin ikon Bilkisu, a lokacin da baya cikin hayyacinsa.
Sai dai gaskiyar Bilkisu ne da ta ce babu wanda zai damu ya zurfafa bincike, abinda za a ɗauka shine Gwamna Saifuddeen Kachallah ya lashe Biliyan goma shabiyu cikin kuɗin asusun jiha.
Ta cize leɓe tana neman mafita duk da za ta iya rantsewa ko naira ɗaya Saifuddeen bai yi amfani da shi a kuɗin nan ba.
"Idan har kina son mijinki na tabbata duk abinda kike da shi a kaina zaki yi gaggawar ƙona su"
"Idan ban yi hakan ba kashe shi zaki yi?" Asiya ta yi tambayar fiskarta a ɗaure.
"Ya dangana da irin zaɓin ki"
Lokacin da Bilkisu ta miƙe zata tafi Asiya tace " shine fa Uban 'ya'yanki"
Bilkisu ta ƙara taku biyu sannan tace "ba laifi bane idan sun zama marayu, shima Ubansu a maraya ya taso"
"Subhanallah!" Asiya ta furta tana riƙe baki...
***
"Baka da ikon kai min 'yata wajen Asiya. She's my daughter and she stays here with me"
"Kin saurari kan ki kuwa? Ina kike lokacin da na kawo Nana gidan nan?. She waited for you for five hours babu ke babu dalilinki"
"Ban san yau zaka dawo ba, baka gaya min zaka dawo yau ba"
Ya girgiza kai kawai dan duk wani bayani da zai yi ɓata lokaci ne. Inama ta ɗau kiransa balle har yai mata bayani. Ko da suka je Sudan ma ƙorafin da Mahirah ta masa kenan akan Bilkisu bata kiranta, idan kuma ta kira sai ta ga dama take ɗauka.
"Ka je ka dawo min da 'yata"
"Khadijah ba 'yar goyo bace, idan kina son ganinta kin san inda zaki sameta"
Ta so yin jayayya da shi amma akwai inda za ta je yanzu.
Ko ta halin ƙaƙa sai ta siyi award ɗin nan, wannan award shine zai ƙara mata daraja a idon mutane. Mutane biyar za'a nominating kuma dole ta kasance cikinsu.
Da wannan tunani ta fita daga gidan.
*
"Mr Chairman ban gane kana son janye endorsement ɗinka ba. Wa kake da shi daya fini, kana tunanin Saifuddeen zai iya taɓuka abin kirki ne a wa'adinsa na gaba. This man is coming after us, ya bari Asiya matarsa tana yi mana ɗauki ɗai-ɗai tana kaimu kurkuku. Kar ka manta matarsa Asiya ce ta tura Sani Kachallah prison fa"
Party Chairman yai gyaran murya yana ƙara tuno alƙawurran Bilkisu Kachallah. Kaso sittin na duka kasuwancinta nasa ne, daga yanzu har ta yi shekara huɗu akan kujerar Gwamna. Shi kansa ya so sanin sirrin kasuwancin muggan ƙwayoyi da na makamai amma har yanzu bai sani ba, dan yana tsoron kar ta ɓaci.
"Mr Lamara ka ƙara bani lokaci nayi tunani, ka san jama'ar Congo ba za su so zaɓan wanda ba musul..."
"Dakata! Na gane matsayarka"
Ya miƙe tsaye rai a ɓace yace " da kai da ita ɗin dukkanku zaku rasa kujerar Congo"
"Lamara, Mr Lamara" Chairman ya bi shi da kira amma ko juyowa bai yi ba.
Bayan ya koma Congo ko hutawa bai yi ba ya nufi gidan Alhaji Umaru Kwom amma rashin sa'a ya tarar ya tafi jinya ƙasar waje.
Zai koma jam'iyyar su Umaru Kwom sannan ya fito a mataimakin Gwamna, in har komai ya tabbata suka ci zaɓe zai san yadda zai yi ya ɗauke Umaru Kwom a hanya amma kafin nan zai yi maganin Bilkisu Kachallah.
Barin gidan Alhaji Umaru Kwom keda wuya lauyansa ya kira shi. Ba maganar waya bace abinda Lauyan ya faɗa masa kenan.
Gidan shaƙatawarsa yace su haɗu dan asalin gidansa akwai hayaniya, 'ya'yansa sun zo hutu daga ƙasar waje.
Gaba ɗaya notinan kansa sai da suka kunce lokacin da ya karanta takardar gayyata da Lawyansa ya miƙa masa.
"Barrister mi yake faruwa?"
Gashi nan a rubuce amma bai gane inda rubutun ya dosa ba.
"Matar tsohon Gwamna tana tuhumata da kashe mijinta, HOW? Ba tana ƙasar waje ba?"
"Sir, it seems baka san miyake faruwa a gari ba. Kusan wata shida kenan da dawowar Hajiya Sha'awanatu Bacchi garin nan"
A da dai babu abinda zai shiga ko kuma ya fita daga jihar nan matuƙar yana da mahimmanci ba tareda shi Lamara Damana ya sani ba. To mi ya faru? Ko dan ya karkatar da hankalinsa kan batun samun kujerar Gwamna ne, ko kuma dai cire shi daga muƙamin Chief of Staff ne ya rage masa ƙarfi.
Ina munafukai masu kawo masa labarin abubuwan dake wanzuwa a jihar ?
"Da gaske ne Abdul Tsangaya yana da recording na maganarmu?"
"Waye Abdul Tsangaya?" Lawyer ya tambaya cikin rashin fahimta.
Ba zai karaya ba. Wannan ba komai bane, babu wanda ya isa ya gano abinda ya aikata shekaru kusan huɗu, kai biyar ma za ace yanzu kam.
Babu wanda ya isa ya tura shi kurkuku, zai amsa kiransu kuma zai ci nasara.
***
"Wai da gaske ne akwai recording ko kuma dai?"
"Kin ga Badawiyya ki kwantar da hankalinki ki cigaba da cin amarci, wannan case ba naki bane"
"Dole ki ce haka ai, kaman yau ne na fara shiga case ɗin da ba nawa ba"
"Allah ya huci zuciyarki ba haka nake nufi ba. Kin san dai yanzu ke matar mutum ne"
"Ke kuma matar Aljani ko?"
Asiya ta saka dariya ta gyara zamanta sannan tace " Abdul Tsangaya yace ya naɗi hiransu amma gaskiya an sace wayar da daɗewa kuma babu back-up"
"Kina tunanin shi kuma Lamara Damana zai saki baki ya tonawa kansa asiri saboda an masa barazana"
"Ba zai tonawa kansa asiri ba, amma yana fama da wannan case ɗin Bilkisu zata bankaɗo dukkan sirrikansa dan damarta kenan. Idan ba a kamashi ta kisan tsohon Gwamna ba za a kama shi ta cin hanci da rashawa"
"Ita kuma Bilkisu fah?"
Asiya ta yi shiru, dan bata faɗawa Badawiyya kashedin da Bilkisu ta mata ba.
Duk da bata faɗa ɗinba Badawiyya ta gano hakan daga shirun da ta yi.
"Kina tsoron kada ta yiwa Gwamna wani abu?"
"Ban san mi zan yi ba Badawiyya. Wani lokaci na kanji a raina cewa na bar wannan binciken na rufe ido kawai na bar Gwamna ya ƙare wa'adinsa mu bar musu Gwamnatin su cigaba da abinda suka ga dama"
"Kina sauraren radio kuwa?"
Asiya ta girgiza kai "A'a"
"Idan kika cire hannunki zaki katse ladan da kike samu Asiya. Lokacin dana je ƙauye bakina ba zai iya faɗa miki irin addu'o'in da na ji ana yi miki ba. This Projec Tomatonion kaɗai da kika assasa baki san yadda mutane da dama suka amfana da shi ba. Infact saboda shine ma aka nominating ɗinki for the best governor's wife award"
"Kai Badawiyya ina kika ji wannan kuma, yaushe ma aka fara bada award ɗin"
"Matar Shugaban ƙasa ce da wasu tsofin matan Gwamnoni suka ƙirƙiro award ɗin, wannan ne shekara na huɗu da za a sake bayarda award ɗin. Abin alfahari ne a gareki Asiya, kuma ina addu'ar Allah yasa ki ci award ɗin nan"
"kinga bar maganan award ɗin nan. Za ayi wani seminar a College of Agric Congo ina so ki wakilce ni idan Maigida ya amince"
"Chabɗi jam! Ban gama honeymoon ba"
"Honeymoon ko. Za ki gane kuran ki idan kika shiga labour room kina zazzare ido ai" ta ƙarisa maganar tana dariya. Sai dai shirun da ta ji daga ɓangaren Badawiyya yasa ta katse dariyar, murya a sassauce tace "Badawiyya?"
"Ba zan taɓa shiga labour room ba Asiya, Madam Bintu ta ɗauke min wannan damar" Badawiyya ta kufce da kuka. Kukan kenan Asiya ta ji kafin katse kiran da Badawiyya tayi tun kafin ta samu damar yi mata bayani.
Ta manta shaɗaf. Ta ya zata manta da irin wannan tabo mai girma na rayuwar Badawiyya.
*"An cire mahaifar gaba ɗaya, shi da kan shi ya cire mahaifar Asiya"*
Ta tuno kukan Badawiyya ranan da aka kaita ɗakinta.
Ba zata manta ba, addu'ar samun ƙazantar ɗaki ta mata shine ta bata amsa da wannan ɗin.
Ta san labarinta lokacin da suke bibiyar case ɗin Madam Bintu amma bata ɗauka abinda Madam Bintu ta mata har ya kai wannan ba, ta ɗauka kawai jaririn kawai aka kashe.
"I was only seventeen. Ban san anyi komai ba sai bayan kusan wata biyu da yin aikin, lokacin na samu lafiya har ana shirin sallamata. Ina tsaka da baƙin cikin kashe mini jariri da aka yi, then Dr Mustafah ya sake kawo min mummunan labari. Cewa yai anyi hakan ne dan a ceci rayuwata. Ko mi za a yiwa Madam Bintu yau ba zai taɓa dawo min da abinda na rasa ba"
Asiya ta riƙe baki tareda fashewa da kuka kamar wata ƙaramar yarinya. Taya za ta manta da wannan abu Dan Allah. Yanzu Badawiyya sai ta ga kamar gori take mata. To wani gori? Ita dake da mahaifar ma mi ta tsinana ne, har yanzu dai ko ɓatan wata bata taɓa yi ba. Sai... sai...alokacin Azumi. Ta girgiza kai stress ne yasa bata ga jini ba a lokacin, kamar yadda Likita yace wancan karan wai stress na iya jirkita yanayin al'adar mace.
Sake kiran Badawiyya ta yi dan ta bata haƙuri amma sai ta ji numbar a kashe. Idanunta cike da ƙwalla ta tura mata dogon text na ban haƙuri tareda jaddada mata cewa mantuwa ce ta yi ba wai tayi maganar da wani niyya ba.
***
"Mommy, Mommy, Mom"
"What!"
Bilkisu ta juyo a fusace. Tsoro ƙarara ta gani a idon 'yarta dan haka ta ɗan sassauta murya tace "waya nake yi Nana, Please"
Ta maida wayar kunnenta ta cigaba da ihun da take wanda shine ya tada Nanan ma daga bacci.
"So, Rector na College of Agric ya bata award kuma an yi nominating ɗinta a matsayin the best governor's wife. Kuɗaɗena dana baka fa?"
"I should calm down. Ok indai ba a nominating ɗina ba to lallai ba ta isa taci award ɗin nan ba. Wani stupid Project ta aiwatar a jihar nan, eh?. Ni kuma da nake taimakawa marayu sannan na tura mutane Makkah da gumi na fa?. Don't tell me nonsense. Mtsw" ta katse kiran.
Zama tayi gefen kujera tana riƙe kanta da hannu biyu, yayinda dukkan jikinta ya ɗau zafi. Wannan cin mutunci ne a nominating Matar Gwamnar jihar Congo sannan a ɗaura sunan Asiya a kai. Yaushe ma ta aure shi? Three, no four years. Har ta cancanci a dangantata da Saifuddeen.
"She has no right to that award"
"Mommy" Nana ta sa hannu ta dafa kafaɗarta
Bilkisu ta juyo a wahalce ta fuskanci 'yarta, tunda Nana ta dawo gidan yau ne ta tsaya ta mata kallon ƙurilla.
16 year old addict daughter da ta sani ba ita ce ke durƙushe gabanta ba. Wannan kamilalliyar fuska gareta, ga maganarta nan mai sanyi.
"Mommy Dan Allah ki dena ɗagawa kan ki hankali. Rayuwar nan fa tanada ƙaranci. Ki yi haƙuri ki rungumi duk wata ƙaddarar da ta zo miki. Na sani kina son zama fitacciyar mace a rayuwarki but then not at the expense of your family da kuma imaninki"
Da farko kalamanta sun fara tasiri a ranta amma da ta zo wannan gaba sai muryar 'yarta ya rikiɗa ya koma mata na Asiya.
Tura Nana tayi da ƙarfi tana faɗin "abinda ta kitsa miki kenan a kwana biyun da kika yi da ita. To ahir ɗinki da yi mini irin wannan magana"
"Mommy Dan Allah ki fahimceni. I miss you, I miss us. Ya kamata ki dawo mana da farinciki gidanmu kamar yadda muke da"
"Ikon Allah. Yanzu kuma nice sheɗaniyar da na tarwatsa familyn mu. Dole ki faɗi haka tunda ke jinin Saifuddeen ce"
Ta miƙe tsaye tana huci.
"Idan kina so ki ga farin ciki a gidan nan to tabbas Saifuddeen ne ya bani kujerar sa"
Ta bankaɗe Nana dake tsugunne ta wuce ɗakinta bayan ta ja doguwar tsaki.
Nana ta bi mahaifiyarta da kallo.
Gaskiya ba zata zauna a gidan nan ba idan tana jin irin waɗannan maganganu za ta iya komawa ruwa.
***
Ɗakin taron ya cika maƙil da manyan mutane. Ilahirin jama'ar wajen mata ne dan su suka ɗau kaso tamanin cikin ɗari.
A nan tsakiyar ɗakin taro table ɗin da Asiya ke zaune yake. Tana nan zaune da Badawiyya gefensu kuma matar tsohon Gwamnan Congo ne mai rasuwa wato Hajiya Sha'awanatu Bacchi, sai kuma wata tsohuwar minister wacce itama 'yar asalin jihar su ce.
Duk da Asiya bata bawa award ɗin mahimmanci ba amma tabbas lokacin da suka shigo hall ɗin da ake gudanar da taron wani fargaba ne ya shigeta.
Cikin matayen Gwamnoni da ake da shi a ƙasar aka zaƙulo guda biyar wanda sunanta ya faɗa ciki, wannan ma abin godiya ne koda bata ci kyautar ba.
Bayan an buɗe taro da addu'a tareda kaɗe-kaɗe da raye-raye da ake yi a lokutan taro, sai aka shiga gabatar da jadawalin shirin. Wata minister ta fito ta bada taƙaitaccen tarihin kowacce cikin mata biyar da aka zaɓo. Dukka huɗun sun yiwa Asiya fintinkau wajen shekaru da gwagwgwarmaya na rayuwa amma duk da haka itama ba baya ba wajen jajircewa a lamurran jiharta.
Duk da kwaɗayin award ɗin da ta ji a ranta Asiya ta sawa ranta salama da cewa cikin matar Gwamnar Lagos da na Maiduguri ɗayarsu ce za ta lashe kyautar. Sai dai kuma Alƙalami ya bushe dan kuwa tana tsaka da tafawa First lady matar Shugaban ƙasa da ta gama jawabi ta ji ana shirin kiran wadda ta lashe award ɗin.
"And the award goes to.....The youngest wife, the journalist, entrepreneur, beautiful Hajiya Asiya Faruƙ Kachallah. Wife to the governor of Congo state"
Asiya tasa hannu biyu ta rufe fiskarta. Badawiyya dake gefe ta miƙe tsaye tana ihu tana tafi.
"Asiya ki tashi"
Tafin da ake ya ƙaru yayinda idanuwan mutane suka zame mata torchlight har ta kai stage inda First lady ke tsaye. Suka yi musabaha da ita sannan ta damƙa mata award ɗin.
Asiya ta ɗaga award ɗin sama tana murmushi. Masu Camera suka shiga ɗaukan hotuna...
30
Saifuddeen ya ɗauko remote ya kashe TVn da ke office ɗinsa. Wani shauƙi da kuma kunya ya shige shi. Adadin mutanen da Project Tomatonion ya amfanar ba za su irgu ba. Rector na Kwalejin Agric takanas ya zo ofishinsa yana yi mishi godiya. Ashe suna zaune ne akan dukiya basu sani ba. Ada sun bar gonakin makarantar da kayan aiki sun lalace ba tareda ana amfani da su wajen samun kuɗin shiga ba amma just tunatarwa da kuma tallafi da Asiya ta basu ya basu damar yin amfani da makarantar wajen samun kuɗin shiga. Duk wani ɗalibi yana ɗaukan karatun theory na awa huɗu ne a rana yayinda sauran lokacin yake ƙaresu tsakanin gonan makaranta ko Lab. Su kansu ɗaliban daga baya shiga gona su yi aiki ya fi musu zaman aji ɗaukan darasi.
Shi baima san Asiya ta commissioning Congo Yogho ba sai da Director na gidan gonar jihar ya kira shi yana sanya masa albarka. Har ofishinsa aka kawo masa samfurin yoghurt da ma'aikatar gidan gona ta fitar a ƙarƙashin ƙaramin kamfani da ta buɗe na Congo Yogho.
Ya sake Hamdala a ransa da Asiya bata dakatar da project ɗin gaba ɗaya saboda shi ba. Dalilin project ɗinta hanyoyin samun kuɗin shiga a jihar sun ƙaru, yanayin kasuwanci ya sake bunƙasa. Jiya kafin ta tafi Abuja take masa maganar ƙaddamar da gonan zuma da take so a fara a jihar. Dan ta haɗa hannu da ƙwararru da zasu koyawa matasa yadda ake kiwon zuma a kuma sarrafa shi cikin sauƙi.
Yai wani murmushin shauƙi yana fatan Allah ya dawo masa da ita lafiya...
*
"A shirye nake na ɓata komai idan har ba zan samu abinda nake so ba. Sai muga ya za ta yi da ɓangaren tsaro kuma, tunda ance ta kawo abinci jihar Congo, bari muga ko zata iya kawo zaman lafiya"
Kalaman Bilkisu kenan bayan ta gama kallon award ɗin da aka bawa Asiya.
Ta jawo waya ta kira numbar mutumim da ya ƙwaƙule mata idon mahaifin Asiya...
***
Kwanaki biyar suka ƙara a kan yadda suka shirya dawowa jihar su sai dai dole ce ta sa suka ƙara kwanakin dan hanyoyin shiga jihar Congo babu kwanciyar hankali. Fashi da makami da kuma kidnapping sun dawo tamkar sabon yayi a wajen.
Batun murnan samun award na Asiya ya juye ya koma kuka da baƙin cikin kashe-kashe da ake yi babu gaira babu dalili.
Hakanan kawai Tanko Janwuya ya samu sabon ƙarfi da ƙarin makamai. A ɓangare ɗaya Bilkisu Kachallah na bashi tallafi, a ɗaya ɓangaren Alhaji Umaru Kwom yana bada na shi.
Ranan da Asiya za ta dawo dole sai jirgin sama ta hawo dan babu halin ta biyo mota hanyoyin duka babu kyau infact curfew aka saka a jihar na 6am to 6pm.
Ko hutawa ba ta yi ba Asiya ta fara aiwatar da abinda ta shirya. Wannan ya ƙara rura wutan fitinan da ake ciki.
Duk inda ka leƙa sai dai kaga ana tattaunawa kan batun sunayen manyan mutane da aka fitar wanda keda hannu wajen cin hanci da rashawa sannan kuma wasunsu suke da hulɗa da safarar muggan makamai.
Ba ta ga ta zama ba dan tun da aka saki takardun take samun kiraye-kirayen waya.
Dai-dai zata fita daga gidan motar Mr Lamara Damana ta shigo.
"Miyasa kika fidda takardun nan, you are destroying this state. Idan ta wannan ɓangaren kika fito kusan sai an kama kowanni ɗan siyasa a jihar nan. Dukkanmu muna cikin harkan nan"
"You left me no choice. Mutane nawa aka kashe cikin kwana biyar? Ka san adadin mutanen da aka kidnapping?"
" ba ni da hannu a wannan, wannan aikin Bilkisu ne and you know it"
"Idan baka so ka faɗi kai kaɗai, kana da damar jan ƙafarta ku faɗo tare"
"Zan yi biyayya. Zan taimakawa Saifuddeen ya sake zama Gwamna. Zamu miƙa kaso sittin na kuɗaɗen jiha da muka sace"
"Mr Lamara Damana, ka gayawa Alƙali wannan ba ni ba"
Ja baya yayi taga-taga kamar zai faɗi. Yana iya yin komai dan ya samu duniya shiyasa ya zo neman mafaka a wajen Asiya. Duk da yana ƙoƙarin cin nasara a shari'ar da ake da shi da matar tsohon Gwamna amma wannan shari'a idan aka farata baya tunanin zai samu nasara.
"Ka ga yarinyar nan da kake gani, tafi Bilkisu hatsari, be careful with her"
Ya tuno gargaɗin Yallaɓai akan Asiya.
Idan komai ya lafa zai ɗau mataki akan Asiya, zai walaƙantata, zai kowa mata darasin da har ta mutu ba zata manta da shi ba. Saifuddeen shine tinƙahonta, zai kassara Saifuddeen fiye da tunaninta. Amma yanzu...amma yanzu.
Gwiwowi biyu ya zube ƙasa, Asiya ta ɗan ja baya da sauri dan kamar ma shirin riƙe mata ƙafa yake.
"Ki taimakeni" ya faɗa da muryar ƙasƙanci
Asiya ta rintse ido tareda sauke ajiyar zuciya...
***
"Hukumar EFCC dai ta kama tsohon Chief of staff na Gwamna wato Mr Lamara Damana ne a yayin da yake son fecewa daga jihar bayan wata majiya ta bankaɗo manya-manyan laifukansa. Ko tsohon chief of staff ɗin zai amince da kashe tsohon Gwamna marigayi Alhaji Saminu Bacchi?"
Da ita da Gwamna babu wanda ya motsa daga inda suke zaune suna ganin labarun da ake gabatarwa.
Asiya ce ta katse shirun da cewa " Idan aka fara shari'ar nan sunan Bilkisu zai fito"
Ta jima tana kallonsa kafin ta ɗauke kai ganin ba shi da alamar cewa komai, kamar ma maganarta bai masa tasiri ba.
Miƙewa ta yi za ta tashi ta ɗauke kofin shayi da ta gama sha ya dakatar da ita da cewa "Har yanzu babu abinda ya tsaya na abinda Tanko Janwuya yake yi. People are dying"
"Idan na ce maka Bilkisu nada hannu akan abinda Tanko janwuya yake zaka yarda?"
Zaro ido yai waje yana kallonta cikin rashin gaskatawa.
"Idan kana so ka kashe matsalar Tanko Janwuya ka fara kama Bilkisu"
Ta yi ƙwafa ta ɗau kofi ta bar masa falon.
Ta tsani halin ko in kula da yake idan aka zo maganar Bilkisu. Kamar shi fa bai yadda Bilkisu za ta yi abubuwan da take yi ba...
Maganar rashin tsaro ya ɗagawa mutane hankali sama da bankaɗe-bankaɗe da aka yi na manyan mutane da suka saci kuɗin jiha.
Kasuwanci da dama sun tsaya chak saboda matsalar tsaro. Wannan karan yafi kowanni lokaci muni.
Ita kanta Asiya ta ɗauka kama ire-irensu Mr Lamara da Mr Paul zai tsayar da komai amma gaskiyar Mr Lamara da yace mata Bilkisu Kachallah ce matsalar tsaron jihar. Duk wani tunani tayi na yadda za ta kawo maslaha a matsalar amma ta kasa.
Wata Safiya bayan ta idar da sallar walaha ta ɗan kwanta tayi wani mafarki akan Alhaji Sani Kachallah. Mutuwarsa a cikin mafarkin ya firgitata matuƙa wannan ne ma yasa ta shirya tafiya zuwa gidan kurkuku.
Yadda babu tsaro a jihar ƙarfi da yaji ta koma tafiya da masu tsaronta, Gwamna yace bai yadda ta fita ita ɗaya kamar yadda take a da ba.
Minti biyar da zuwanta gidan kurkukun aka turo mata Alhaji Sani Kachallah, gashi cikin kayan fursuna abin tausayi.
Ta ƙura masa ido babu ko ƙyaftawa. Ya yi baƙi da shi, timbinsa ya motse ya koma ciki. Idanuwansa sun yi wani rami kamar a saka ƙwandala ya zauna a ciki. Duk wani alamu na tsufa da ada jin daɗi da kwanciyar hankali suka ɓoye yanzu sun bayyana.
Kunya ya kamata lokacin da ya ce " ni kam ko zana ni zaki yi ne?. Sai dai kuma ban gan ki da kayan zane ba"
A ladafce ta gaida shi tana tambayar shi ya jiki.
Bayan wani dogon shiru Alhaji Sani ya fara bayani " ina sane da duk abinda yake faruwa, kuma na sa a raina ko ke ko Saifuddeen ɗayan ku zai zo. Ashe kin fishi hankali ma"
"Lah Baba"
"Gaskiya ne ai, ba dan ke ba da tuni sun kashe min shi. Allah ya ƙara miki juriya"
"Amin Baba"
Kafin yai magana tari ya kufce masa, ya jima yana tarin kafin ya samu nitsuwa.
"Sannu Baba. Kana buƙatar likita ne?"
"Hmm kada ki damu Likitan da muke da shi a nan ya duba ni"
"Allah ya ƙara lafiya"
Alhaji Sani ya amsa da Amin.
"Baba maganar tsaro yafi ƙarfin mu fa. Ko dai mu nemi taimakon Gwamnatin tarayya ne?"
"Ina da shawara. Ina da yaƙinin za a iya samun mafita"
Wani tarin ne ya sake kufce masa, wannan karan bai yi dayawa ba tarin ya lafa masa.
Asiya ta dinga yi masa sannu, a lokaci guda kuma tana tuno mafarkin da ta yi...
***
"Mommy ki zo ki ga. Mommy come please"
Bilkisu da ke gaban madubi tana gyara ɗaurin ɗankwalinta ta fito daga ɗaki da sauri. Yau take so ta samu party Chairman batun form na takarar Gwamnan da za ta siya da zarar an sake shi ranan Monday. Ita take son riga Saifuddeen siya saboda ta samu damar hana Saifuddeen siyan nashi form ɗin.
A tsaye ta samu Nana gaban TV ta riƙe baki tana kallon mutumin dake jawabi a gaban 'yan jaridu.
Tun daga kanun labaran da aka karanto Nana ta ƙwalawa mahaifiyarta kira dan sunan mahaifiyarta da ta ji an ambata.
"Minene? Mi munafukin uban naki ke faɗi?" Ta faɗa tana cire ɗankwalin kanta tunda yaƙi ɗauruwa.
"za'a bawa duk wanda ya kama taƙadarin ɗan ta'addar nan Tanko Janwuya naira miliyan ɗari. Wanda ya kawo mana gawarsa kuwa za a bashi kyautar naira miliyan ɗari da hamsin. Haƙiƙa Tanko janwuya ɗan ta'adda ne da Gwamatinmu ta bada damar a nemo shi ko a mace ko a raye.
"Hakanan muna jinjina ga ilahirin hukumomin tsaro da suke aiki dare da rana wajen ganin an kawo zaman lafiya a wannan jiha tamu mai albarka. Ina yiwa jami'an tsaro albishir da cewa duk wanda ya ji rauni ko aka rasa rai a wajen kare rayukan 'yan ƙasa Gwamnatinmu ta ware wani kaso mai tsoka na shi da iyalen shi. Akwai ƙarin alawus mai tsoka ga duk wani jami'in tsaro dake cikin jihar nan. Suma 'yan vigilante ba a barsu a baya ba a wannan alawus da Gwamnati za ta bayar"
Dogon numfashi ya ja wanda ya ratsa microphones dake gabansa ya fito ta talabijin ya daki kunnen Bilkisu kafin kuma maganganunsa na gaba su zamtowa Bilkisu tashin bam da ya tafi da jinta da ganinta na gajeran lokaci.
"Daga yau, shahuɗu ga watan July, ni Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah na sauke matata Bilkisu Sani Kachallah daga duk wani muƙami da take da kai, na ɗauke duk wani walwala da jin daɗi da take samu sakamakon kasancewarta tsohuwar first lady na jihar nan. Ni Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah na hanata fita daga cikin jihar nan har sai Kotu ta wanketa daga zargin da tsohon Chief of Staff na jiha wato Mr Lamara Damana ya jefeta da shi. Za ta zauna a gidansu ta jira sammaci daga Kotu. Daga yau, duk wani ayyuka da ya danganci ofishin Matar Gwamna zai dawo ƙarƙashin iko da kulawar matata Asya Shahidah Faruƙ Kachallah."
Ɗankwalin hannun Bilkisu ya faɗo ƙasa biyo bayan sa hannu da tayi a kai ta kwarma ihu Noooo...
"Ba ka isa ka min haka ba. Ba ka isa ba Saifuddeen, Babu wanda ya isa ya fitar dani daga gidan nan"
Samun waje ta yi ta zauna tana ƙara maimaitawa kanta babu wanda ya isa ya fitar da ita daga gidan Gwamnati.
Ko minti talatin ba ayi ba wasu jami'ai mata suka shigo gidan biye da su kuma Asiya ce da ta sha baƙin gilashi.
Nana ta gaji da roƙon mahaifiyarta akan ta tashi ta shirya su bar gidan amma ta ƙi, dan haka ta wuce ɗaki ta shiga fidda kayanta a closet tana zuba mata su cikin akwati.
Bilkisu na ganin Asiya tayi kanta kamar za ta shaƙeta securities da suka biyo Asiya suka riƙe ta.
"I'm going to kill you, da hannuna zan kashe ki. Ku sakeni babu inda zan je. Ku sakeni na ce"
Asiya ce ta ɗaga musu hannu suka sake Bilkisu. Kallon-kallo suka tsaya yi kowannensu yana kissima abubuwan da zai yi wa ɗanuwanshi.
Kamar an tsikareta Bilkisu ta haura sama da gudu.
Nana na tsaka da haɗa kayan mahaifiyarta ta ji tsigowarta ɗakin. A fusace ta shiga duban wani abu daga cikin kayan nata.
"Mommy" Nana ta faɗa a ɗimauce ganin abinda mahaifiyarta ta ɗauko cikin wani baƙin akwati.
Bilkisu na fita daga ɗakin Nana na bin bayanta tana ƙwala mata kira tareda faɗin kada ta yi abinda za ta yi nadama.
Asiya na nan tsaye a inda ta barta.
"Ba zaki taɓa cin nasara a kaina ba. Ni Bilkisu Kachallah na fi ƙarfin ki"
Ta saita bindiga dai dai goshin Asiya. Suma securities ɗin suka saita mata bindiga suna faɗin ta ajiye nata bindigar. Wani takaici ya rufeta, waɗannan yaran chief securityn Gwamna ne kuma itace ta kawo su wannan gida.
Asiya kam rufe ido tayi tana jiran saukan harsashi dan ko yunƙurin guduwa bata yi ba.
Ƙaran fashewar glass yasa Asiya ta buɗe ido dan ƙaran da ta ji bai yi kama da ta bindiga ba.
Nana ta riƙe kai ta fashe da kuka ganin mahaifiyarta ta faɗi ƙasa jini na zuba.
Wani verse ta ɗauka ta rutsawa Bilkisu a ka lokacin da suke sa'insa da securities akan ta ajiye bindigarta.
***
"Yanzu laifina kake gani kenan?"
"I just said it was unnecessary. Kin riga kin san halinta miyasa zaki je inda take a lokacin da take cikin ɓacin rai"
Asiya ta buɗe baki ta rufe dan gaba ɗaya maganarta ya toƙare ne a maƙoshi. Yau da mutuwa Bilkisu ta yi kenan cewa zai yi ita ta kasheta.
"Allah ya baka haƙuri"
Ta faɗa da ɗan ƙarfin daya rage mata.
Bai ce komai ba ya wuce ya barta tsaye cike da tunani...
Kwana ɗaya Bilkisu tayi a asibiti aka sallamota ko kuma ace ta sallami kanta. Duk yadda ta yi dan ta koma gidan Gwamnati hakan bai yiwu ba dan Mahaifiyarta sam ta ƙi yarje mata, dole ta huci zuciyarta suka koma Kachallah house wanda shima gidan ya rasa fasalinsa tun lokacin da aka kama Alhaji Sani.
Ta ci duk wani buri na ɗaukan fansa da kuma lalata lamurran Gwamnatin Saifuddeen sai dai kash, ta kasa samun wayar Tanko Janwuya, shima yanzu ta kansa yake dan jami'an tsaro sun tasanmai haiƙan, kutsa kai kawai suke yi cikin ƙauyukan daya mamaye suna kashe muƙarrabansa.
Party Chairman ma ya dena ɗaukar wayarta tayi kiran, tayi text amma duka babu amsa. Duk lokacin da ta yi yunƙurin fita daga gidansu sai jami'an tsaro dake tsare da gidan su hanata.
Faɗa take da kowa a gidan, ta zama tamkar wata zararriya sabon kamu. Mahaifiyarta kaɗai ke iya yi mata magana wani lokaci ta ji wani lokaci kuwa ta daka mata tsawa.
Duk wasu sources ɗinta ta kira amma kowannensu ta kansa yake. Babu wanda zai so a haɗa shi da tuhumar da ake mata.
*
A yau Asabat ne kuma aka wayi gari da labarin heart attack da Alhaji Sani ya samu a gidan yari. Daga Asibitin gidan kurkuku aka wuce da shi Teaching Hospital.
Kan Gwamna Saifuddeen ya ɗau zafi, musamman daya je ya ga halinda Baban nasa ya shiga.
Tabbas yana buƙatar kulawa ta musamman kuma indai za a sake mayar da shi gidan kurkuku ne to bare taɓa samun sauƙi ba.
Matsawa masu kula da shari'ar ɗaukaka ƙarar Alhaji Sani yai dan shi hankalinsa ya bar kan maganar Bilkisu ya koma ta samun lafiya da kuma 'yancin Baban sa.
Ba zai yafewa kansa ba idan Alhaji Sani ya mutu a kurkuku. Idan har shari'ar ba za tayi daɗi ba gara kawai yai amfani da damarsa yai wa Alhaji Sani afuwa ya granting na shi state pardon.
A wani zuwa da ya yi gaishe da Alhaji Sani sai da ya zubda hawaye, ya dinga kuka kamar ƙaramin yaro.
"Ka yafe min Saifu. Duk abinda ya faru, duk abinda Bilkisu ta aikata akwai hannuna a ciki. Na gagara yi mata tarbiyyan da ya dace, sannan nayi sakaci da lamurranta har suka lalace haka. Ka yafe min Saifu domin a lokacin dana haɗa ku na sani biyayya ka min ba wai kana sonta ba. Ba dan arziƙin 'ya'ya ba da sai nace nayi dana sanin haɗa ku aure da na yi"
"Baba please"
"Ka bari na faɗi abinda ke zuciyata domin ba lallai nayi nisan kwana ba"
"Insha Allahu zaka samu lafiya, sannan za ka samu 'yancinka"
"Na roƙe ka kada ka riƙe auren Bilkisu saboda ni. Idan har ka ji a ranka rabuwarku yafi alkhairi Dan Allah ka sawwaƙa mata. Zan so kayi hakan tun yanzu amma ba zan tursasa maka ba. Ina fata ko bayan raina zaka samu damar yafe mini. Ba zan yiwa Bilkisu baki ba, Ina mata addu'ar shiriya kafin lokaci ya ƙure mata"
Daga haka yai shiru. Sai da Saifuddeen ya miƙe zai tafi sannan yace " ka turo min Asiya"
31
Kwanan Alhaji Sani Kachallah takwas a Asibiti aka yi zaman kotu na ƙarshe akansa. A wheel chair aka turo shi kotun dan bai gama warkewa ba. Duba da yadda rashin lafiyarsa take buƙatar a fitar da shi waje yasa Lawyoyinsa suka roƙi alfarmar kotu bisa sassauci ga hukuncin da aka yanke masa.
Kotu ta 'yanta shi bisa sharaɗin zai sawwaƙar da dukiyansa ga batulmalin jiha. Babu abinda Alhaji Sani ya ja da shi sai dukiyar ƙaninsa wanda yanzu ya zamo na Saifuddeen akan dukiya ce ta gado kuma ko kaɗan bata harmtacciyar hanya aka sameta ba.
Babu abinda Alhaji Sani Kachallah ya tsira da shi sai gidansa wanda ya kasance cikin gidan mahaifinsa ne na gado da ya gyara shi tsarin zamani. Sai wata tsohuwar gona da yama manta da shi wanda itama ta gado ce.
Lokacin daya damƙa ragamar komai a kotu sai ya ji zuciyarsa yayi saƙayau tamkar an sauke masa wani ƙaton dutse a kansa.
*
Duk wani shirye-shiryen tafiya ƙasar waje an kammala amma Alhaji Sani Kachallah ya ƙeƙasa ƙasa yace ba zai yi jinya a ƙasar waje ba. Yace da Saifuddeen ya ajiye kuɗinsa zasu masa amfani ranan da ya bar kujeransa.
Saifuddeen kamar zai yi kuka haka ya shiga roƙonsa akan ya haƙura a fita da shi amma sam ya ƙi. Yace a barshi ya mutu cikin 'ya'ya da jikoki.
Kullum cikin nasiha yake yiwa Bilkisu akan ta tuba ta ajiye makaman yaƙi ta bada kanta wa hukuma. Ba abinda ke raba su sai faɗin " ba zan ƙare kamar kai ba. Babu wanda ya isa ya kaini kurkuku"
Cikin kwanaki ƙalilan da ta fara jelan zuwa kotu sai gashi ta zabge, ta fita hayyacinta. Duk wani boka ko malami da ta ji labari sai ta nemi yadda ta yi ta aika masa da kuɗi akan a rufe kan shari'ar nan amma ba abinda 'yan tsubbu ke yi da kuɗinta sai cin kaji. Wanda suke da duba ma sun riga sun san cewa babu nasara a tattare da ita dan haka babu wanda ya damu ya gayyato Iskokai balle ya ɓata musu lokaci.
Al'amarinta Maktub ne, rubutacce ne, ta riga ta gama samun nasara a rayuwa.
A zaman kotu na uku aka tsare Bilkisu saboda sabbin shaidu da aka samu a kanta wanda ya sanya babu damar ayi bail ɗinta, dole ne ta kasance a tsare har sai kotu ta gama bincike ta yanke hukunci. Zargin kisa, safarar muggan makamai da kuma miyagun ƙwayoyi ba wasa bane.
***
Shiryawa ta yi cikin wata leshi mai kyau, turquoise color daya ƙara haskata.
Sai da ta gama shiryawan kuma wani abu ya daki zuciyarta mai kama da kishi. Ta yi saurin yin isti'aza dan kar ta saɓawa Allah. Idan bata gode na ɗibbin ni'imomi da Ubangiji ya mata ba mi za ta yi.
Duk da abubuwan da suke faruwa a gidan su bai hana Halima Kachallah ta haɗa taron suna ba. Infact a yadda ta faɗa mata ma Babansu ne ya encouraging ɗinta akan tayi taron suna.
Tun kafin yau ta sani yaron ya ci sunan mahaifin Halima ne wato Muhammad Sani amma Halima tace da Muhammad za a dinga kiransa saboda a duk lokacin da ta ji an kira sunan tana so ta dinga tunawa da Fiyayayyen halitta, kuma tana so yaronta ya samu albarkar mai ainihin sunan wato Manzon tsira, Manzo mai daraja, gatan kowa, Habibullahi.
Tuni Asiya ta chanja sunan Halima Kachallah a wayarta zuwa sunan Umm Muhammad.
Ta nufi gidan sunan tana addu'a a ranta, albarkacin wannan yaro itama ta samu rabo.
Ba wani taro ne na ɗaga hankali ba amma duk da haka 'yanuwa sun yiwa Halima kara musamman ma saboda suna mata kallon wacce ta auri talaka wanda ko albashin da ta ke samu ya ninka abinda yake samu a sana'arsa. Sai dai wani abu daya bayyana musu yasa kuma wasun su ke envying Halima shine kwanciyar hankali da soyayyar miji, abinda da yawansu suka rasa kenan a gidan mazajensu.
Taro ya tafi lafiya sai dai Asiya bata jima a wajen ba dan yadda 'yanuwan Halima ke mata kallon wacce ta tarwatsa ahalinsu ya hanata sukuni, musamman mahaifiyar su Haliman wacce ta kasa ɓoye abinda ke ranta sai da ta amayar...
Sunan ɗan Halima da kwana uku Allah yai wa Alhaji Sani Kachallah rasuwa, a gidansa a cikin barcinsa.
Labarin mutuwar ya zo wa Gwamna ne a dai dai lokacin daya dawo daga sallar Asuba. Fiskarsa cike da hawaye ya zo ya sanar da Asiya da ke ƙoƙarin tada sallah saboda bata tashi da wuri ba.
Ya amsa ta'aziyyarta sannan ya fice daga ɗakin.
Mutuwar Alhaji Sani Kachallah ya girgiza mutane da dama bama Gwamna kaɗai ba. Ita kanta Bilkisu da ta ji labarin mutuwar sai da jikinta yai sanyi, sai dai babu nadama ko ɗis na abubuwan da ta aikata, da kuma irin rabuwar da suka yi da mahaifinta.
Ta yi imanin muddin ta samu ta fito to tabbas Saifuddeen da Asiya sai sun je inda mahaifinta ya je dan su suka kashe mata mahaifi.
*
Bayan rasuwan Alhaji Sani Gwamna ya ji gabaɗaya Gwamnatin ta fita masa a kai. Jam'iyyarsu ta buɗe saida form na 'yan takara amma a ɓangarensa bai yi wani huɓɓasa na siyan form ɗin ba. A yadda yake jin kansa ma kamar zai haƙura ne yai wa'adi ɗaya ya sauka. Wannan kujerar itane silar rugujewar farin cikin ahalinsa.
Shawarar marigayi Alhaji Sani Kachallah ta haifar da ɗa mai ido dan kuwa ba ayi sati uku da karon batta tsakanin jami'an tsaro da kuma Tanko Janwuya ba, jami'an tsaro suka samu galaba a kansa. Tuni aka fille kan taƙadari. Sauran muƙarrabansa suka yadda makamansu suka miƙa wuya.
Abubuwa sun fara lafawa yayinda farin ciki da walwala ya wanzu cikin mutane. Magana ɗaya ke yawo yanzu, yadda za a ƙarisa shari'ar su Mr Lamara Damana da kuma Bilkisu Kachallah duk da dai abubuwan da aka gabatar na shaidu akan Bilkisun basu da ƙarfi amma ko a haka ta chanchanci hukunci.
Sai dai kamar yadda aka sani shari'a da manyan mutane akwai ta da jan lokaci. Wannan ma dai kullum aka yi zaman kotu ana faman ɗaga shari'ar zuwa wani lokaci daban ne.
***
Asiya ta ajiye ƙaton brown envelope a kan table tace " wannan shine shaida na duk wani laifi da Bilkisu Kachallah ta aikata, tun daga safarar miyagun ƙwayoyi, kasuwancin muggan makamai, cin hanci da rashawa, alaƙarta da Tanko Janwuya, komai yana nan"
"She's the mother of my kids Asya" Gwamna ya faɗa murya a raunane.
Tabbas maganar ya mata zafi, cikin kwanakin nan ba abinda ta tsani ji irin a kira Bilkisu Kachallah da uwar 'ya'yansa. Abinda mahaifiyar Bilkisu ta faɗa kenan ranan da suka haɗu a taron sunan ɗan Halima.
"Na san kina bibiyar Bilkisu kuma duk wani na kusa da ita kin tura shi kurkuku. Sai dai ka da ki manta cewa Bilkisu uwar 'ya'yan Saifuddeen ce, ko dan wannan ya kamata ki rufa mata asiri, tonuwar asirinta zai jawo scandal a Jihar nan sannan da wani idon kike so Nana da Mahirah su kalle ta? Abinda kika yiwa mahaifinta bai isheki ba? Mi kuma kike so Asiya? Mi kike so?"
maganar da suka yi da mahaifiyar Bilkisu ya dawo mata sabo.
Gwammna ya katse shirunta da cewa "Ba zan nemi takara ba a karo na biyu, bayan na bar Gwamnati zamu yi nisa da jahar nan, na tabbata Bilki..."
"Na yi iya nawa Excellency. Ruwanka ne ka yi abinda ya dace ko kuma ka ɓuya bayan uwar 'ya'yan ka. Sai dai abu ɗaya na ke so ka tuna, a ranan gobe matsayinka ko matsayinta a wajenka ba zai tseratar da ita daga azabar Allah ba"
Daga haka ta juya ta bar masa falon. Tana shiga ɗaki ta zauna gefen gado ta ɗau waya ta fara daddannawa, chan kuma ta cillar da wayar ta fashe da kuka. Kuka sosai take yi tana tuno abubuwan da suka faru saboda rai ɗaya, Bilkisu Kachallah.
Matar nan bata chanchanci ta cigaba da rayuwa bama balle har a kalleta da idon tausayi, wai kuma shine yake ƙoƙarin kareta saboda kawai matar sa ce uwar 'ya'yansa. Tabbas zai ce haka mana tunda dai ita ɗin bata haifa masa ba.
*
Washegari ko da ta gaya masa za ta je umura bai musa ma ta ba, ta lura ma a rikice yake.
Cikin kwanaki biyu aka kammala shirin tafiyarta ta wuce Saudiyya. A Riyadh ta fara sauka ta gana da likitan mata kafin ta wuce Makkah dan ta yi umura.
Likita na huɗu kenan da ta ke gani gameda rashin haihuwarta. Ta ga Likita a Sudan lokacin da ta raka Mahira makaranta sannan ta gani a America da ma a ƙasarta Nigeria.
Wai ma shekara nawa ne ya kamata mace ta kai a gidan miji kafin ta fara damuwa da rashin haihuwa?. Bata san amsar ba, abu ɗaya da ta sani shine tana son haihuwa.
Halima Kachallah wata goma da aurenta da Yaya Bello ta haihu. Itama kenan da ta yi aure tana shekaru talatin da shida. Idan haka ne ai tana da ƙarancin shekaru fiye da Halima, bata kai talatin ba, tana kula da lafiyarta tana samun isashshen hutu tun lokacin da aka kama Mr Lamara Damana.
Duk wannan tunani ta yi shi ne bayan ganawarta da likita wanda ya jaddada mata lafiyarta ƙalau zata iya samun ciki a kowanni lokaci.
Bayan ta isa ɗakin Allah ta maida hankalinta kan ibada da kuma addu'ar samun haihuwa mai albarka, tareda yiwa Gwamna addu'ar Allah ya bashi ikon yin adalci a ragowar wa'adinsa.
***
Ba ta yi tsammani za ta dawo ta samu Gwamna yana nan riƙe da shaidun da ta bashi ba tareda ya miƙa su ga hukuma ba.
Kallo ɗaya ta masa ta san har yanzu yana kokonton yin abinda ya dace.
Idanu ta zuba masa dan itakam ta yi iya nata, ruwansa ne ya bari a hukunta Bilkisu ko kuma ya bari a sake ta ba tareda wani hukunci ba.
Abu ɗaya ta sa a ranta. Duk ranan da kotu ta sake Bilkisu ba tareda hukunci ba to aurensu ya ƙare. In dai zai rufe ido akanta to tabbas ya tabbata Azzalumi ita kuma ba zata zauna da Azzalumi ba...
Daga ɓangaren Gwamna ya fara samun matsin lamba daga jam'iyya akan indai ba zai sayi form ɗin takara ba to ya bari mataimakinsa ya siya. Duk da akwai mutane uku da suka sayi form ɗin amma shine candidate ɗin da idan ya fito takara babu makawa mutane zasu zaɓe shi.
Idan ya dawo gida sai ya ga gidan ya masa faɗi. Asiya ta ƙi zama a gidan Gwamnati. Ya sani fushi take da shi saboda maganar da yai ranan da securities suka je fitar da Bilkisu daga gidan. Ga Nana nan kullum cikin roƙonsa take akan yasa a sako mommynsu.
Yana jin kunyar haɗuwa da Asiya dan ya sani bashi da bakin da zai mata bayani kan dalilinsa na rashin miƙa shaidun da za su sa a hukunta Bilkisu ga kotu.
Cikin kwanakin nan yana tunani da kuma dana sani. Inama ace bai amince yayi takara ba bayan ya cinye wa'adin Gwamna mai rasuwa.
Ba wai baya son a hukunta Bilkisu bane sai dai ya kasa gaskata abubuwan daya gani. Ya kasa yarda cewa Bilkisu ce ta aiwatar da dukkan abubuwan da ake tuhumarta da su.
A wani ɓangare kuma yana ɗaura laifin abinda ya faru a kansa. Kamar yadda Bilkisu ta faɗa masa shine silar komai, shine silar maida ita abinda ta zamo yau. Sau tari idan ya zauna yana tunani sai yaga ai Bilkisu gaskiya ta faɗa. Saboda shi duk waɗannan abubuwan suka faru.
To bari zai yi a hukunta Bilkisu bayan shine sanadin lalacewarta haka. To da wani ido zai dinga kallon Nana da Mahirah idan har aka yankewa mahaifiyarsu hukuncin kisa?...
***
"Har yanzu Gwamna bai ce miki komai ba?"
"Ni dai na zuba masa ido ne naga iya gudun ruwansa"
"Abin kam ba daɗi. Zai dinga gani kamar ya ci amanar mahaifinta ne"
"Amanar banza. Duk tarin laifuffukan da ta yi ace har akwai wata amana da zata hana ai mata hukunci"
"Calm down ba ni ne Gwamna Saifuddeen ba"
Badawiyya ta ɗauki kofi ta tsiyayawa kanta 5alive Berryblast mai sanyi ta kurɓa a hankali.
"Kin ga kar ki sa wata damuwa a ran ki. Ke kin yi naki kin gama. Ki bari shima yai nashi, na tabbata zai yi abinda ya dace. Give him some time"
Asiya ta girgiza kai itama ta tsiyayi juice ɗin ta fara sha.
Ta kalli Badawiyya ta yi murmushi a ranta. Gaskiya aure ni'ima ne idan kayi dacen miji. Tana yiwa ƙawartata addu'ar samun zaman lafiya mai ɗaurewa dan farin ciki da nitsuwa duk sun bayyana a tattare da ita...
Yau safiyar Monday Asiya tana gyara gadonta ta ji wayarta na ringing. Kan dresser ta ɗauko wayar ta ƙara a kunne.
"Madam Bintu ta mutu"
Asiya ta yi saurin duba wayar dan ta tabbatar Badawiyyar ce ke magana
"An ce jiya da daddare ta dinga bubbuga kanta a jikin bango, kafin a zo a dubata ta jikata kuma ta zubar da jini sosai. Ba za ki so ganin gawarta ba Asiya, ni da na gani har yanzu na kasa samun nitsuwa. Allah ka sa mu yi ƙarshe mai kyau, Allah mun tuba"
Asiya ta yi shiru tana jin sheshsheƙar kukan Badawiyya bata san mi zata ce ba, bata san wani addu'a ya kamata ta yi ba. Ba ta san irin lallashin da zata mata ba.
*
Ƙaton dogon gate ɗin gidan kurkukun Congo ya buɗe lokacin da wata baƙar mota mai lambar Gwamnati ta yi horn yayinda wasu motoci biyu duka baƙaƙe suke biye da ita.
Security ya fito da sauri ya buɗe ƙofar motan dake tsakiya. Wata ƙasaitacciyar mace ta fito fiskarta ɗauke da murmushi, sai dai murmushin yafi kama da ta 'yan wasan kwaikwayo dan kuwa bai kai zuci ba.
Duk inda ta wuce gaisheta ake yi hakan ya tabbatar da cewa ita ɗin macece mai daraja a idon mutane. Macece mai lamba ta ɗaya a duk cikin matan dake faɗin jihar Congo.
Rayuwa juyi-juyi. Yau ga Asiya zaune da 'yancinta ita kuma Bilkisu Kachallah zaune da kayan firsina tana jiran hukunci.
"Kin zo dan ki min dariya ne?"
Kaico mutum yai rayuwan zalunci da rashin imani. Mutum ba komai bane.
Yau gashi duniya ta juyawa Bilkisu Kachallah. Fiskarta yanƙwane kamar wata tsohuwa ga wasu ƙananan ƙuraje da suka feso mata suka ƙarawa fiskarta muni.
"Kin san dai har yanzu ina da damar da zan iya sanyawa a hallakaki a hallaka banza"
Ta katse shirun Asiya.
"Hmmm. Duniya kenan. Ni ban zo dan na miki dariya ba domin ke abar tausayi ce ba abar dariya ba"
"Allah ya tsinewa tausayi. Na fi ƙarfin ki ji tausayina, zan fito nan bada jimawa ba kuma Alkali ne zai wanke sunana. All of you will pay for what you did to me. Idan na zama Gwamna kan ki zan sa a fara fillewa"
"Ke mahaukaciya ce Bilkisu. Ki tuba ga Allah ko zaki samu sauƙi"
Bilkisu ta kwashe da dariya sai da ofishin da suke ciki ya amsa.
"Kin san dana sani ɗaya nayi a rayuwata"
"Na yi dana sanin kashe ki da banyi ba da hannuna"
"Na zo in miki nasiha ne Bilkisu. Ki tuba ga Allah sannan ki amsa laifukan ki, idan baki yi dan kowa ba kiyi dan yaran ki. Kin sani su mata ne kuma duk abinda kika aikata zai iya shafar rayuwarsu nan gaba. Wai shin ma ba kya tunanin mutuwar ki ne?"
Wata dariyar Bilkisu ta sake yi. Asiya ta shiga girgiza kai. Duk yadda ta tsani matar nan, chan cikin zuciyarta tana addu'ar Allah ya shiryar da ita. Tana matuƙar tausayin mutuwarta a haka. Ko jiya sai da Nana ta zo roƙonta wai Dan Allah ta sa baki a sako mahaifiyarsu. Nana bata san girman laifukan mahaifiyarta ba, dan da ta sani da ba za ta nemi a sake ta ba.
Babu ɗa na gari da zai so ganin uwarsa a irin wannan hali.
Ganin ɓata lokaci kawai take akan Bilkisu yasa ta miƙe tsaye.
"Ki yi tunani Bilkisu, abinda kike ba zai fishshe ki ba"
Bilkisu ta miƙe tsaye itama duk da Asiyar ta fita tsayi, ta ɗaga kai ta kalleta ido cikin ido tace "baki isa ki ga bayana ba Asiya. I will always rule this state. Wannan da kike gani temporary ne, zan fito, kuma zan shiga takara kuma zan ci zaɓe. Duk wannan da kike taƙama da shi"
Ta nunata sama da ƙasa, idonta ya sauka kan cikin Asiya
"Jiƙar mai ƙusumbi sai sun dawo tsumma a jikin ki"
Idanunta suka kasa motsawa daga cikin Asiya. Doguwar rigar Atamfa ta saka tareda babban mayafi daya tafi dai dai da kalar Atamfar wanda yafi kama da kalar ruwan goro
"Wani cikin kika sake samu?"
Asiya ta kalleta cikin rashin fahimta. "Ban gane ba?"
"Well, ki yi ta ɗaukan ciki kina wahalar da kan ki dan kuwa yadda wancan ya tafi wannan ma binsa zai yi. Ba za ki taɓa haihuwa da Saifuddeen ba. NEVER" ta faɗa da wani irin tsawa wanda ya sa Asiya ta firgita, kalamanta suka fi tsawan firgitata.
Dariya ne ya biyo bayan haka dan har aka zo aka tafi da ita bata bar dariya ba.
Mamaki ne da tambayoyi suka cikawa Asiya kwanya.
Mi Bilkisu ke nufi? Ko dai haukan kanta ne ke saka ta maganar shirme.
Shugaban kurkukun ne ta shigo ofishin tana yiwa Asiya sannu tareda fatan Bilkisu bata ba ta wata matsala ba. Da kyar Asiya ta iya amsa mata sama-sama kafin ta fice daga office ɗin.
Waje ɗaya ne za ta samu amsa, kuma nan ta nufa
32
***
Matar Gwamna tana da damar zuwa ofishin Gwamna a kowanni lokaci. Asiya za ta iya irga sau nawa ta taka taje ofishin Gwamna tun lokacin tana ƙaramar 'yar jarida zuwa yanzu da matsayinta ya kasance daraja ta ɗaya a wannan jiha.
Ofishin Gwamna bai taɓa mata nisa ba irin na yau, dan tunda ta fito daga mota take ganin ga kowanni taku ɗaya da ta yi ofishin na ƙara nisan taku goma.
Ta ko'ina gaishe ta ake amma damuwar dake tattare da ita ya hanata sakewa ta gaisa da mutane. Ba za ta iya cewa ga amsar da take basu ba amma abu ɗaya ta iya daurewa a kai shine murmushi. Murmushin nata da ya tsaya iya fatar baki.
Ba bu wani shamaki daya hanata shiga ofishin Gwamna kai tsaye dan kowa buɗa mata hanya yake domin ita da mai ofishin sun zamo ɗaya.
Shi kaɗai ne a office ɗin kuma rubutu yake, zaka gane rubutun na da mahimmanci a gareshi dan hatta eye glass ɗinsa da bai cika amfani da shi ba sai dare yana manne a fiskarsa ya duƙufa yana rubutu.
Sai da ta iso gabansa sannan ya iya ɗaga kai ya kalleta. Wani murmushi ne ya suɓuce masa. Ko dan bai yi tunanin ganinta a ofishinsa ba, ko kuma dan kewanta da yake yi, ko kuma duka
"Akwai abinda kake ɓoye min ne?"
Ta yi maganar cike da fatan babu gaskiya cikin abinda Bilkisu ta faɗa.
A cikin mota ta gama tunanin yiwuwar maganar Bilkisu kuma abu biyu ta iya hangowa. Tabbas ba ta ga jininta ba lokacin Azumi sannan komai zai iya faruwa a hatsarin da suka yi a hanyar su ta zuwa Congo bayan sallah.
Bai san inda maganarta ya dosa ba dan haka ya ajiye biron hannunsa ya haɗa hannunsa biyu ya ɗaura haɓarsa a kansu ya zuba mata ido yana jiran ƙarin bayani.
"Lokacin da muka yi hatsari" ta tsaya da maganar dan bata san wasu kalmomi za ta yi amfani da su ba.
Ta ɗan ja numfashi a hankali " akwai abinda na rasa lokacin da na yi hatsari ne? Akwai abinda Likita ya faɗa maka ka ɓoye min?"
"Asya" ya miƙe daga kujerarsa ya zagayo inda take tsaye. Hannunta biyu ya kamo ya haɗasu ya manna musu kiss murya a sanyaye yace "mi kike nufi? Abinda ya faru lokacin ba abune daya kamata ace kina tunawa da shi ba tunda Alhamdulillahi dukkanku uku kuna nan lafiya"
"Har ɗan cikin nawa ma sai an siyasantar da shi"
"Asya"
Ta kwace hannunta daga cikin nasa. Yanayin yadda ya kira sunanta, yadda idanunsa suka rikiɗa zuwa roƙo su suka fahimtar da ita cewa gaskiya ne abinda Bilkisu ta faɗa.
"So, ni bani da gata kenan a rayuwarka. Bilkisu za ta iya yi mini komai kuma a zauna lafiya, har za ka iya ɓoye min gaskiyar daya kamata na sani"
"Asya ba abinda kike tunani bane"
Hannu ta ɗaga masa tareda ja baya idanunta tuni sun kawo ruwa.
"Lokacin da Lamara Damana yace min Bilkisu ce ta sa aka buga mana mota raina yayi mugun ɓaci amma na danne domin bani da shaida kuma ba zan tuhumeta bisa zargi ba. Ko ka kasan cewa ita ta maida mahaifina makaho. Ko ka san cewa tanada niyyar kashe min mahaifi ba dan nayi amfani da wani abu da take tsoro na hanata idda nufinta ba. Ban taɓa gaya maka ba, ban taɓa cewa ka ɗau min fansa ba. Duk cikin abinda na baka shaidu ne akan abinda ta aikata wa jahar nan ba wai abinda ta aikata mini ba. Amma ni bani da ko 'yanci na san cewa ta kashe min ɗa, my baby, wanda ban ma san da zaman shi a jikina ba" ta rufe bakinta tana mai fashewa da kuka.
" Shahidah please listen to me, na ɓoye miki ne saboda idan kika sani zaki tada hankalinki. Na san kina son haihuwa, na san lokacin da kika je ganin Likita kan maganar haihuwa.
"Tunda na tabbatar baki san da cikin ba na hana Likita ya gaya miki. Saboda bana son abinda zai sa ki cikin damuwa. Ban yi haka dan Bilkisu ba. I did it for you, because i love you. Ba ki san yadda nake ji ba idan na tuna abinda ya faru da kika je ganin Likita, na ga test strips ɗin a banɗaki kuma Likitan da kansa ya kira ni ya min bayani. I don't want you to be depressed saboda ɓari da kika yi. I'm sorry na..."
" idan aka zo maganar Asiya duk abinda ka ga dama kake yi saboda Asiya bata da gata. After all ni jiƙar mai ƙusumbi ce ko. Na tabbata idan Bilkisu ce tayi ɓari, ni zaka fara zargi. Amma saboda ni ce , shiru ka yi da maganar ka ɓoye kamar ba abinda ya faru"
"What are you saying? Asya kin san irin son da nake miki"
"Ba zan iya ba Saifuddeen, na gaji da zama second best ɗinka, na gaji da komai. Na gaji da halin ko in kula da kake da lamurra na. Na bar mata kai, ka bata state pardon, ka maida ta gidan ka, ka bata kujerar ka, ka mata duk abinda kake so, i don't care"
"Asya, Asya" ya bi ta yana ƙoƙarin kamata. Sai da ta kai bakin ƙofa sannan ta tsaya. Shima tsayawa yai yana jiran mi za ta yi, mi kuma za ta faɗa.
"Zan koma gidanmu, ka turomin takardata chan"
"As...ya" ta riga ta rufe ƙofa.
Ba abinda yake nufi ba kenan. Ya damu da yadda ta damu da rashin haihuwa shiyasa ya rufe mata komai.
Badawiyya ya kira ranan a Asibiti ya tambayeta ko ta san Asiya na da ciki. Tace masa a'a kuma in har Asiya ta san tana ɗauke da ciki to ba zata ɓoye mata ba. Itama shawaran daya riga ya ɗauka ta faɗa masa. "Dan Allah kar ka sanar da ita yanzu sai komai ya lafa idan ba haka ba hankalinta zai tashi"
Bai san laifi bane ɓoye mata da yai. Daya san manufar da za ta ɗauka kenan da ya sanar da ita tuntuni. Ya sauke ajiyar zuciya yana fata ba ta nufin maganarta na ƙarshe.
***
Tun daga falo ya fahimci Asiya bata gidan. Akwai wani turaren wuta da ta ke kunnawa indai tana nan amma yau babu shi, akwai ƙanshin turaren kaɗan-kaɗan saboda yawan kunnawa da ake amma ba kamar idan aka kunna ba. Ya taɓa faɗa mata cewa yana son ƙanshin turaren shiyasa ta dage da kunna shi.
Yana tura ƙofar ɗakinta ya ga duhu. Ya sa hannu ya kunna wutan ɗakin. Da alama ta sha wahala kafin ta iya haɗa kayan da ta ɗauka. Akwai sauran kayanta a kan gado, ga tarin kaya birjik a closet data bari a buɗe. Ya kai dubansa ga wajen madubinta nan ma 'yan tsirarun abubuwa ta ɗauka a wajen.
Ya zauna bakin gado yana ƙarewa ɗakin kallo. Idanunsa suka kai wani night dress ɗinta da ke dai-dai ƙafarsa, ba sabo bane, ya shaƙi ƙanshinta, rigar da ta saka ne a haɗuwarsu ta ƙarshe. Idan ba wai sanyi ba tafi saka irin waɗannan ƙananan nightie ɗin wanda baya shan wahala wajen cire su lokaci guda. Amma ba lokaci guda yake cirewan ba, ya kan ɗau lokaci yana ƙoƙarin ja, yana ja yana wasa da dukkanin ilahirin jikinta. Wasu lokuta hannu yake sawa ta ciki yai wasa da ita a haka ba tareda ya yi yunƙurin cire rigan ba.
Ya lumshe ido yana saƙe shaƙar rigar yana wani jin daɗi kamar ya shaƙi daddaɗan iska bayan anyi ruwan sama.
Maganarta na ƙarshe ya faɗo masa
"Zan koma gidanmu, ka turomin takardata chan"
Allah ya kiyaye ya rubuta mata takarda idan ba takardar soyayya ba. Taya zai rayu babu ita kusa da shi. Taya zai gyara lamurransa idan bata tareda shi. Duk wani abu na jin daɗi da talakawa suka samu yau a mulkinsa ta hanyar jajircewanta ne. Taya zai rabu da matan da ta yi sanadiyyar sada shi da 'yanuwan mahaifiyarshi. Ta ya zai yi tunanin rabuwa da wacce soyayyarta yake maƙale da shi a kowanni bugun ƙirjinshi.
Zai bata lokaci sannan ya je ya nemi gafararta, ya je ya dawo da ita. Amma kafin nan sai ya samu matsaya akan maganar Bilkisu.
Bilkisu tana da matsayi a rayuwarsa amma abubuwa sun faru dayawa wanda ba zai iya cewa har yanzu akwai sauran matsayi na musamman da take da shi a rayuwarsa ba sama da cewa ita ɗin uwar 'ya'yansa ne.
Asiya kuma yana mata soyayyar da shi kansa bai san adadinsa ba. Matsayi kuwa tun ma kafin ta kasance mata a gareshi take da wani matsayi na musamman a gunsa, balle yanzu da ya rayu da ita ya gane ko ita wacece, ya bata matsayi na musamman da bai taɓa bawa wata mace ba a rayuwarsa.
Ya jima a ɗakinta, kafin ya miƙe riƙe da rigan baccin ya fice daga ɗakin.
***
Satinta ɗaya a gida Ale yasa aka kira masa ita. Yana sane du da yadda take wuni kuka da rashin cin abinci. Da farko ɓoye masa tayi kan ainihin abinda ke damunta amma daya matsa mata sai ta buɗe masa komai, har dalilin cire mishi ido da aka yi.
Yai shiru na tsawon lokaci. Chan kuma sai yace mata.
"Da kika zo kika tare a nan kin haƙura da auren kenan?"
"Baba"
"Dawowar ki nan zai maida miki abinda kika rasa ne? Ko kuma dai hakan zai dawo min da idanuna?.
"Allah ya baki haƙuri Asiya. Ni ba zan tursasa miki ki koma gidan ki ba. Na sani a baya na aurad da ke ne ga Gwamna saboda kwaɗayi da son zuciya, dan haka yanzu ba zan miki zaɓi ba. Ni dai ina miki nasiha da cewa abinda haƙuri bai bada shi ba, rashin haƙuri ba zai bayar ba"
Daga haka bai ƙara cewa komai ba, itama ɗin bata samu bakin magana ba dan gaba ɗaya ya kashe mata jiki.
Washegari da suka yi maganar ne kuma Tabawa mahaifiyar Ale ta fara zazzaɓi mai tsanani. Dama ta jima tana jinya dan ko fita bata iya yi. Tun wancan karan da Asiya ta zo gida kafin Azumi take so a kaita babban Asibiti a cikin gari amma Tabawa tace babu inda zata a barta ta ɗanɗana azabar duniya ko Allah zai yafe mata abubuwan da ta aikata a ƙuriciyarta. Da ƙyar take bari Likita ya zo dubata duk bayan kwana biyu.
Suna Asibitin ne kuma Badawiyya ta kira Asiya.
"Dama ba kya gida kika sa na ɗebi ƙafa na je"
"Sorry ban san zaki je ba ai"
"Asiya miya faru? Mai aikinki tace min kin fi sati ba kya gida"
"Iyi. Na bar masa gidan ai"
"Akan me?. Saboda ya ƙi miƙa takardun da kika bashi?"
Asiya ta sauke ajiyar zuciya. "Saboda Bilkisu ta kashe min ɗa bai yi komai a kai ba. Badawiyya kin san a lokacin hatsarin nan i had a miscarriage amma..."
"Nina hana ya faɗa miki?"
"Rabi'ah?"
"Faɗa miki a lokacin ba shi da amfani dan na san halin ki sarai, kuma na san ciwon da kike fama da shi akan rashin haihuwa. Kiyi haƙuri amma laifina ne ba laifin Gwamna ba"
"Badawiyya i deserve to know, duk min ɗacin gaskiya gara a faɗa min da a ninke ni cikin ƙarya"
"Ki yi haƙuri, Dan Allah Asiya"
Asiya ta cire wayar daga kunnenta ba tareda ta ce komai ba...
***
Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah yana zaune a office ɗinsa ya tsurawa ceiling ido aka kira wayansa.
Ya ɗauki wayan ya ƙara a kunne.
"Na sani. Zaku samu amsana yau"
Ya ajiye wayar ya cigaba da kallon ceiling.
Chan ya sauke idonsa tareda ɗaukan wata takarda dake gabansa, tun daren jiya ya typing takardar amma har yanzu ya kasa saka wa takardar hannu.
Ya sake karanta abinda ke cikin takardar wannan karan yana yi yana tuna lokutan da yai ta kamfen. Shin na cika alƙawurran dana ɗaukar mu su?.
"Shin kama taɓa tunanin yin amfani da damar ka wajen yiwa talakawa aiki? Kama taɓa yin wani huɓɓasa a karan kan ka wajen yiwa talakawa aiki?"
Ya tuno kalaman Asiya.
Ya ɗauki biro zai saka hannu a takardar amma sai hannunsa ya fara rawa. Muryan Asiya ke masa yawo a kai. "You are a COWARD Saifuddeen"
Yai saurin rufe kunnensa da hannu bibbiyu yana jin bugun ƙirjinsa na ƙaruwa.
Tabbas idan ya ajiye aiki Asiya ba zata yafe masa ba, kuma ta tabbata cewa shi ɗin coward ne kamar yadda ta ke faɗa masa a baya.
Ya kamata yanzu kam yai huɓɓasa a karan kansa da niyyar sake mulkin jihar nan bisa gaskiya da adalci.
Ya kai minti goma yana saƙa da warwara a zuciyarsa kafin ya samu ƙarfin kekketa takardar barin aiki daya rubuta jiya.
Bayan ya gama da ayyukan office ya wuce gida, yai ɓadda kama ya fita daga gida daga shi sai Direba.
An san da zuwansu dan haka babu ɓata lokaci aka buɗe musu dogon gidan.
Ta ƙara lalacewa fiye da farkon kawota gidan. Zuciyarsa ya motsa da tausayinta. Yau kwana uku kenan da cikan aurensu shekara ishirin, sai da zai taho ne lissafin anniversary ɗinsu ya faɗo masa. Ya tuna buri da Bilkisu ta sha lokacin anniversary na cikar aurensu shekara goma. Idan suka cika shekara ishirin da aure za ta yi bikin da ba a taɓa yi ba a ƙasar nan. Yau gashi ranan ya zo har ya wuce, auren na su kuma yana lilo igiyar na gab da tsinkewa.
Ya dubi fiskarta dai dai zata zauna. Lokacin da ya aureta fara ce amma ba sosai ba. A gidansa ta fara shafa mai ta mayar da kanta farar balarabiya ƙarfi da yaji. Ba zai iya tuna ya ainihin gashin kanta yake ba saboda sun rayu ne da gashin da take chanjawa akai-akai wanda ya mantar da shi kala ko kuma tsayin ainihin gashinta.
"Mr Governor da kansa. Na ji ance har yanzu ba ka sayi form ɗin takara ba, good for you, dan ko ka siya asara za ka yi"
"Ki zauna Bilkisu, we need to talk"
"Ka fara dana sanin abinda ka min ne?"
Tambaya ɗaya ya zo yi mata, tambayar da ta tsaya masa a rai watanni da dama da suka wuce.
"My son, Sa'ad Junior, ke kika kashe shi?"
"How dare you!" Ta miƙe a fusace.
"Shima kin kashe shi ne saboda kujerar Gwamna?"
"Kar ka gaya min maganar banza. Ni ba muguwar uwa bace. I love him, I love my son. Taya zan kashe ɗana, "
Hawaye suka fara zubo mata tunowa da ta yi da yadda ta ga gawar Junior.
Shri Malaminta na India ya faɗa mata ɗaukan fansa macijiya tayi akan ɗanta saboda ta sabunta alkawari. Amma duk da haka bata ganin laifinta a cikin wannan lamari sai laifin Saifuddeen.
Shima ɗin idanunsa ne suka ciko da hawaye saboda abinda yake shirin faɗa mata na cinsa
"Bilkisu" ya kira sunanta da sigar jan hankali
Ta tattaro nitsuwarta ta bashi.
"Na sake ki saki ɗaya"
Zuba masa ido tayi kamar ba ta ji mai yace ba.
"Gobe za a gabatar da shaidu a kan ki, ban san wani hukunci za a yanke miki ba. Amma Dan Allah kafin nan ki tuba wa Allah, laifukan ki suna da girma Bilkisu"
Dariya ta ƙwace mata. Tana yi tana nuna shi da yatsa.
"Ba ka isa ba. Ba ka isa ba Saifuddeen. Baka isa ka min haka ba"
Ta miƙe ta cakumo shi " Ba zan yarda ba. Ba zan yarda ba Saifuddeen"
A lokacin ya rasa wanne ne ya fi daminta sakin da yai mata ko kuma asirinta dake daf da tonuwa.
Ranan daya koma gida zama yai a ƙasan ɗaki yai ta kuka kamar ƙaramin yaro, jikinsa har ɓari yake saboda har yanzu yana gani kamar shine dalilin da ya sa Bilkisu ta zamo haka.
Washegari kamar yadda ya tsara ya miƙa takardun da Asiya ta bashi ga hukuma.
Tun bai bar office ba Nana ta kira shi tana kuka. Bai san mi zai ce mata ba kawai ya kashe wayar ya kwantar da kansa a kan kujera. Inama Asiya tana kusa da shi da zai ji sauƙi koda kaɗan ne a ransa.
Da sauran ƙarfi daya rage masa ya rubuta mata text ya tura, nan kuma ya kwanta yana numfashi sama sama har kuma numfashin ya tsaya...
33
Yau ne ukun rasuwan Tabawa dan haka har yanzu gidan su akwai mutane. Mutanen ne ma yasa ta koma gidan Baffa Malam dan bata jin daɗin jikinta tun kafin rasuwan.
Tana kwance Mama ta zo ta tasheta hannunta ɗauke da wayarta.
"Tun ɗazu aketa kira inaga an kira ya fi sau ishirin. Ki duba dai ko lafiya"
Asiya ta amshi wayar tana yin hamma dan baccin bai isheta ba.
Nambobin da suka yi ta kiranta ne yasa hankalinta ya tashi baccin da ke idonta ya washe. Nana, Badawiyya, Likitan Gwamna, Hajiya Umma, Halima Kachallah.
To miyake faruwa?
Ta ma rasa wa zata kira. Ganin text da aka turo guda huɗu yasa ta shiga wajen message da sauri.
*kina ina ne Asiya?. Wallahi idan baki zo ba wani abu ya same shi zaki yi dana sanin taurin kan ki.....* Badawiyya
*Direba yana hanya zai ɗauko ki, ki bar komai ki taho tareda shi....* Haj. Umma
*Daddy ba lafiya please ki zo Asibiti...* Nana
*"I need you....* Saifuddeen
Likita ta fara kira dan gaba ɗaya zuciyarta ya bata wani mummunan abu ya samu Saifuddeen.
Jin ba a amsa wayar ba ta sake shiga tashin hankali.
"Badawiyya ya mutu ko?" Ta faɗa cikin muryan kuka.
"Idan ya mutu ke kika kashe ai"
"Na shiga uku"
"Kwantar da hankalinki yana da rai amma gaskiya a yadda Abban Fadilah ya gaya min yana jin jiki. Asiya ki je Asibiti ki duba shi"
Ko wanka bata yi ba ta chanja kaya ta saka dogon hijabi. Tana shirin neman wanda zai zo ya kaita ne ma sai ga Direban da aka turo ya iso...
Likita yace suma yake yana farfaɗowa, kusan sau uku yana haka kuma a duk farfaɗowan da zai yi sai ya kira sunan Asya wannan yasa suke ta kiran numbarta
"Yana coma yanzu haka, zamu bashi awa ashirin da huɗu zuwa awa saba'in da biyu idan bai farfaɗo ba zamu ɗau wani mataki"
Ta rufe baki da hijabinta ta fara kuka. Idan Saifuddeen bai farfaɗo ba ba zata taɓa yafewa kanta ba.
*
Kwana biyu suna jira ya farfaɗo amma shiru. Gaba ɗaya sun tsorata da lamarin, Asiya har ta fara maganar ko waje za a fita da shi Likita yace a'a ba za a iya fita dashi a haka ba.
Allah da ikonsa a rana ta uku sai gashi ya farfaɗo. Asiya tana ɗakin itada Nana suna karatun ƙur'ani suka ji kaman gadonsa ya motsa.
Asiya tayi saurin juyawa aikuwa suka yi ido huɗu da shi.
Ita da Nana suka shiga rige-rigen ƙarisawa gadonsa.
Idan Allah bai rubuta lokacinka ya ƙare ba duk abinda zai sameka ba za ka mutu ba.
Gwamna yana jinya a Asibiti aka siya masa form ɗin takara a karo na biyu. Kasancewar Asiya na kusa da shi tana bashi kulawa ya sa yake samun sauƙi da sauri.
Kwanansa biyar da sallamoshi daga Asibiti aka yi zaɓen primary aka fidda sunan shi a matsayin wadda zai yi takara a jam'iyyarsu. Babban abokin adawarsa wannan karan ma Alhaji Umaru Kwom ne wanda yake ganin zai yi kamfen da abubuwan da Bilkisu ta yi ya yaƙi kamfen ɗin Saifuddeen.
A ɗaukaka ƙara da aka yi, an yankewa Mr Lamara Damana hukuncin zaman gidan yari har ƙarshen rayuwarsa. Sauran muƙarrabansa da aka rafka kuwa wasun su sun samu shekaru bakwai wasu kuma shekaru sha huɗu a gidan yari. Mr Paul kaɗai ne ya samu hukuncin shekaru ashirin a kurkuku...
Kafin ayi shari'ar Bilkisu Asiya ta baiwa Gwamna shawara dan haka shi da iyalinsa har ma da Mahirah dake Sudan suka tattara suka tafi ƙasar Gambia ganin 'yanuwan Mahaifinsu na wajen uwa.
Wannan tafiyar ta ɗan sanyayawa yaran rai musamman Nana da tafi kowa damuwa da halin da mahaifiyarsu ke ciki. Mahirah kam kullum addu'arta shine Allah ya shiryar da mahaifiyarsu kada ta mutu da tarin laifuffukanta.
Sati biyu suka yi a Gambia kafin nan suka dawo gida. Duk da Asiya tana da labarin hukuncin da aka yankewa Bilkisu da kuma abinda ya biyo bayan hakan bata faɗawa Gwamna ba sai da suka dawo.
Sai da suka kwana biyu da dawowa kafin Asiya ta faɗa masa. Suma yaran shiru suka yi amma sun riga sun gani a social media tun ranar da suka dawo.
Asiya ce ta musu nasiha akan su kwantar da hankalinsu sannan su dinga yi mata addu'a.
Hukuncin kisa a kaiwa Bilkisu Kachallah amma a gaban Alkalin ta ɓingire da haukar ƙarya wanda yasa aka tsaida hukuncin har sai ta samu lafiya.
Wannan samun lafiyar yaƙi ci ya ƙi cinyewa kuwa dan Bilkisu gwana ce a irin haukar da take yi.
Lokacin da Mahirah zata koma makaranta ita da Nana suka tafi gidan mahaukata inda aka kai mahaifiyarsu. Ba tareda sanin kowa ba suka je. Sun je ne su mata nasiha amma kalaman da suka dinga fitowa daga bakin mahaifiyar su ya kashe musu jiki. Ko dai da gaske mahaifiyar su ta haukace ko kuma dai mahaifiyarsu tayi nisan da ba zata ji kira ba.
Nana ta sha kuka amma Mahirah gagara kukan ta yi, ta dinga lallashin yayarta akan su cigaba da yiwa mahaifiyarsu addu'a kawai.
"Na kusa fita daga wannan gida. Kar ku damu a zaɓen bana ni zan lashe zaɓe. Mommynku zata zamo Gwamna mace ta farko a jihar nan. Zaku gani. Amma kafin nan ku gayawa party Chairman idan ya fitar dani daga nan zan bashi 99% na dukkan abinda na tara"
"Nana, ki gaya masa kin ji?" Ta faɗa lokacin da yaran suka miƙe suna shirin tafiya.
Har suka fito daga gidan Nana bata bar kuka ba. Itama Mahiran sai da suka fito ta fara hawaye.
***
"Asya miƙo min hula" Gwamna Saifuddeen Kachallah kenan daya fito daga ɗakinsa yana ƙoƙarin gyara babbar rigansa.
Asiya ta fito daga ɗaki hannunta ɗauke da hula tabi bayansa. A tsakiyar falo ta same shi ta saka masa hular.
"Kayi kyau"
Ya ɗan ja hannunta ya manna mata kiss a goshi yace " Ki min addu'a"
Ta riƙe goshinsa ta fara karanto masa addu'o'in tsari. Da ta gama ya ɗan sunkuyar da kansa dai dai cikinta ya manna mata kiss a wajen, ya shafa cikin yace " Daddy zai je taron rufe kamfen ka masa addu'a"
"Macece fa" Asiya ta faɗa tana murmushi.
"Ni na san Sa'ad Junior zai dawo Insha Allah"
Bayan fitansa daga falon itama ta sa hannu ta shafa cikinta ɗan wata huɗu daya fara tasowa kaɗan.
Tunda ta tabbatar masa tanada ciki wata biyu da suka wuce ya hanata yawon Kamfen.
Shi kaɗai yake kamfen ɗinsa yayinda ayyukan da yai aka gani a ƙasa musamman Project Tomatonion da har yanzu ana cin moriyarsa a jihar ya zamo masa abin ƙarfafawa mutane gwiwa dan su zaɓe shi.
Nana ta samu admission itama a Sudan dan haka su biyu kaɗai ne a gidan suna cin soyayyarsu suna kula da junansu.
*
Yau ne ranan zaɓe. Dan haka kowanni rumfar zaɓe ka gani zaka ga jama'a sun cika a wajen maƙil kowa yana dangwalawa gwaninsa.
Sai dai duk da kashe kuɗi da Alhaji Umaru Kwom yai hakan bai sa mutane sun yi zaɓen tumun dare ba.
Asiya na tare da Gwamna lokacin da aka kira aka tabbatar masa shi ya lashe zaɓe, kusan ya bawa abokin tazararsa rata mai yawa na ban mamaki.
Maimakon hakan ya saka shi farin ciki sai ya tashi ya wuce ɗaki ya rufe kansa. Bai fito ba sai lokacin sallar magariba.
Ta sani sarai Bilkisu ya tuno. Duk da sun faɗawa junansu cewa ba za su bari abinda ya samu Bilkisu ya shigo rayuwar aurensu ba amma ganin yadda ya shiga wani yanayi yasa dole ta ɗaura aniyar yi masa magana.
Bayan sallar isha daya dawo daga masallaci ta same shi a ɗaki.
"Congratulations Excellency"
Yai mata murmushin yaƙe ya kauda kai.
"Ba ka ji daɗin nasaran da ka samu bane?"
Shiru yai na ɗan wasu seconds kafin yace " a kan wannan kujerar mutane da dama sukan rasa imaninsu. Ana kisa akan wannan kujerar. Ana yin shirka duk saboda kujerar Gwamna. Ana haukacewa akan muƙamin Gwamna"
"To ka godewa Allah tunda babu ko ɗaya daka yi Allah ya baka wannan kujera a karo na biyu"
"Ba zaki gane ba"
"Gaskiya ne ba zan gane ba"
Miƙewa ta yi za ta bar masa ɗakin ya riƙo hannunta.
" ki yi haƙuri, ba wai na faɗa dan na ɓata miki rai bane"
"Na sani" ta faɗa tana ƙaƙaro murmushin dole.
Wani lokaci tana ji a jikinta kamar har yanzu yana zarginta da abinda ya faru da Bilkisu. Har ga Allah tana yiwa Bilkisu fatan shiriya musamman ma da ta yi wani mummunan mafarki a kanta. Tunda tayi mafarkin kuwa ta sa wani malami ya dinga zuwa gidan mahaukata yi mata nasiha. Sai dai har yau babu wani chanji da aka samu.
Wani lokaci idan ta tuna cewa shekara ashirin suka yi tare kafin rabuwarsu sai ta yi masa uzuri akan maganar Bilkisu. Babu yadda za ayi ya manta da lamarinta lokaci guda, musamman tunda akwai 'ya'ya tsakaninsu.
" haɗo min tea Dan Allah" ya katse mata tunani.
***
Rana ba ta ƙarya yau ake shirin naɗa Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah a wa'adinsa na biyu.
Asiya ta shirya cikin wata Malaysian gown mai kyau kalar teku, ƙasan rigan da hannun rigan lace design ne a jiki . Cikinta ya kai wata takwas amma idan ka ganta zaka ce haihuwa ko yau ko gobe. Babu wani kwalliya a fiskarta dan yanzu ta tsani kallon fiskar ta ma a madubi saboda kumbura da ta yi ta ko'ina.
A hankali ta dinga takowa daga stairs har ta sauko hannunta ɗauke da gyalen riganta da kuma purse, kanta ko comb bai gani ba balle ya san wani abu wai taje kai. Ta de ɗaure gashin kam amma gaba ɗaya ta gefe yayi wani buzu-buzu da shi.
"Anty ki rolling gyalen mana" Nana ta faɗa tana karɓan purse ɗin hannunta. "Bar shi kawai yafawa zan yi, ban ga pins ɗina ba ko ɗaya"
Nana ta karɓi gyalen ta shiga yi mata rolling.
"Ni dana sani ma hijabi na sa. Mahirah ko zaki ɗauko min hijab a ɗakinku"
"Anty ki bari yanzu zan gama"
Gwamna ne ya shigo falon ya sha ado cikin fararen manyan kaya.
"Kun gama?"
"Yes Daddy" Nana ta amsa masa.
Cikin mota babu wanda yai magana. Tun jiya yake fargaban wannan rana. Rana ce da zai sake ɗaukan amanar jihar Congo.
Asiya ta riƙe hannunsa tana murzawa a hankali. Ita ɗinma tana fargaban yadda za su sake shekara huɗu a gidan Gwamnati. Tana fargaban kada kwaɗayin mulki ya ruɗeta, kada mulki ya sakata saɓon Allah ko kuma ya sakata rashin godiyan Allah. Bata fata ta kasance irin Bilkisu.
Ta dinga addu'a a zuciyarta Allah ya sa su gama shekaru huɗun nan lafiya bisa adalci da amana.
*
Idan kayi mai kyau duniya zata tuna da kai har bayan ranka, idan kayi tsiya duniya za ta mance da kai.
Duniya ta mance da Bilkisu Kachallah. Tun ana damuwa da rashin zartar mata da hukunci har aka manta da sha'aninta.
Hauka da ta ƙirƙira ta ajiyewa kanta dan ta tsira daga hukuncin kisa shi ya zauna mata a ka har ya zamto gaskiya duk da kuwa a karan kanta tana ganin kanta a matsayin mai hankali. To dama ai mahaukaci baya kiran kansa mai hauka.
Kusan damuwa da muradin zama Gwamna sun birkita mata ƙwaƙwalwa da tunani. A duk abinda take yi a Asibitin tana yi ne da sanin cewa ita ɗin fa ta kusa zama Gwamna. Daga baya da aka ga shirmenta ya fara ƙaruwa sai ya zamana ana kulleta kowanni lokaci sai idan Likita zai dubata.
Kaɗaici da alhakin mutane ya dirar mata a kwanya. A idanunta ta fara ganin mutanen da ta salwantar, daɗin daɗawa kuma ɗanta Junior da yake yawan mata gizau. Wasu lokaci cikin mafarkanta tana yawan ganin macizai wannan sai ya hanata bacci. Rashin bacci a karan kansa damuwa ne ga ƙwaƙwalwa balle kuma.
A lokacin da take da damarta ta manta rabon da tayi cikakkun salloli na khamsu salawat balle karatun ƙur'ani ko addu'a. Ta gina zuciyarta da cewa idan ta nema sai ta samu, kuma ko ta ƙaƙa ne za ta samu duk abinda take so.
Tun ƙuruciyarta karatun addini bai yi tasiri a ranta ba sannan a hankali zuciyarta ya lalace da cewa idan tana ciyar da marayu kuma tana tura malamai zuwa Makkah shikenan tayi abin kirki a ɓangaren addini, ita ai ba sai ta sha wata wahalar ba.
Malamin dake zuwa yi mata nasiha yana yawan cewa ta dinga yin istigfari sannan ta tuba wa Allah, ta ji aranta ta aikata laifuka kuma tana neman yafiyar Ubangiji. Sai dai har wa yau bata ji a ranta tayi laifi ba, balle har ta fara neman tuba.
Ranar wata laraba da dare tana bacci wani ƙaton maciji ya lalabo ta jikin gini ya zo ya sareta, jikinta ya shanye gaba ɗaya.
*
Labarin mutuwar Bilkisu ya zo dai-dai Asiya na labour. Tun daren laraba suka je Asibiti amma bata haihu ba.
A wayar wata nurse da ta kunna radio tajiyo sanarwar mutuwar wanda hakan ya sa ta sake rikicewa, chan kuma haihuwa ya taho mata gadan-gadan.
Ba ai minti goma ba ta haiho ƙaton jaririnta.
A wajen Gwamna ranan rana ce ta baƙin ciki da kuma farin ciki. Har yanzu wani ɓangarensa yana ganin kamar duk abinda Bilkisu tayi laifinsa ne, ya shiga dana sanin sakaci da yai tayi da lamurranta, ƙila daya tsawata mata da za ta gyara, ƙila da ba za a zo wannan wajen ba.
Sai dai mutuwa dole ce ko da ace baya raye idan an rubuta irin mutuwar da Bilkisu za ta yi kenan to tabbas sai ta yi.
Kusan har aka yi suna aka watse bai iya sake jikinsa ba. Ba dan ma magani daya ke sha akai akai ba ƙila da hawan jininsa ya sake tashi, ƙila ba lallai ya surviving heart attack irin wancan karan ba.
Asiya da ta ga yanayinsa ya ƙi sauƙi damuwarsa ya fara shafe farin cikin haihuwa da aka masa sai kawai ta tattara ta tafi wanka gidan su. Sai bayan ta tafi ta kira shi ta faɗa masa, ya dinga masifa wai miyasa za ta tafi da Ayan ko sati biyu bai yi ba.
Ta bashi amsa da cewa ai ta ga an masa rasuwa ne gara su bashi waje yai zaman makoki iya son ransa.
Ya gane fushi take da shi dan haka ya saukar da kai ya shiga lallashinta. Gaskiyar magana haihuwar Sa'ad Ayan kaɗai ya hana shi samun matsala da kansa lokacin da ya ji mutuwar Bilkisu. Mutuwar ya affecting ɗinsa matuƙa haka ma haihuwar ɗansa ya sanyaya masa rai kuma ya ƙara bashi ƙarfin gwiwar jajircewa a lamurransa. Ya dena yin sako-sako da duk abinda ya faru.
Tunda dai Asiya ta tafi dole ya haƙura zuwa ta gama wanka ta dawo gida amma yace mata duk weekend zai zo ya ga ɗansa...
***
Ayan na da shekara ɗaya gidan talabijin na Hill TV suka gayyaci tsohuwar ma'aikaciyarsu kuma matar Gwamnan jihar Congo zuwa wani shiri na su sabo da suka fara inda za'a dinga tattaunawa da manyan mata masu faɗa aji a jihar,. za su fito su ba da haske gameda tarihinsu, fafutukar da suka yi da kuma gudummawa da suke bayarwa al'ummansu.
CY ne camera man ɗin. Ya jima da barin aiki da Hill TV tun lokacin daya koma America wajen mahaifiyarsa da zama. Sai dai kamar yadda aka gayyaci Asiya haka shima aka gayyace shi kasancewar yana ƙasar a wannan lokaci. Ƙila sun kira shi ne saboda sun taɓa aiki da shi da Asiya, ko kuma Asiyar ce ta nemi hakan
Yarinyar da za ta gabatar da shirin budurwace da ba zata wuce shekara Ashirin da huɗu ba. Lokacin da ake shirye-shiryen haɗa na'urori Asiya ta samu damar gaisawa da CY dan sun fi shekara suna waya amma basu haɗu ba.
"C Y ga chan P Y fa "
CY ya kalli Asiya ya kuma maida dubansa ga 'yar jaridar dake tsaye riƙe da madubi tana gyara gashinta. Wani abu ya ɗarsu masa a zuciya. Itace yarinyar da Asiyar ta tura masa hotonta kwanan baya, bai san miyasa ya kasa goge hoton ba duk da ya san haɗa su Asiya ke son yi kuma shi bai shirya hakan ba.
" Princess Yakubu sunanta. Na ji ance ita ce star reporter na Hill TV yanzu"
C Y yai murmushi a dai dai lokacin da itama Princess ta ɗago ido suka yi ido huɗu da shi. Ta ɗan tura baki sannan ta kauda kai ta cigaba da duba fiskarta.
Bayan an gama shirya komai aka fara shirin.
Gwamna Saifuddeen Kachallah yana zaune gaban TV yana kallon shirin yayinda Ayan ke zaune akan cinyarsa yana wasa da mota.
"Ko zaki faɗawa masu kallonmu sunan ki duk da dai na san sunan ba baƙo bane ga duk wani ɗan jihar nan." Princess 'yar jarida ta tambaya.
Asiya ta yi murmushi. Murmushi ne mai ɗauke da darussa na rayuwa, murmushi ne mai cike da ƙalubale da nasarori, murmushi ne da ya wanzu bayan an jima ana fafatawa kuma ake kan fafatawa.
"Sunana Asiya Shahidah Faruƙ Baba, MATAR GWAMNA"
***
Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah!
Ina miƙa godiya ga ilahirin mutanen da suka jure zaman jiran littafin nan. Wata goma ba wasa bane.
Ina neman yafiya ga duk wanda ya biya kuɗin labarin nan kuma bai same shi akan lokaci ba. Dan Girman Allah, Dan darajar Manzon Allah (SAW) ku yafe min. Ban tsaida rubutun littafin nan haka kawai dan son raina ba. Abubuwa da dama sun faru wanda baki ba zai iya furta su ba. Alhamdulillah tunda muna nan da rai.
Mutanen da suka bibiyeni a lokuta da dama ina baku haƙuri. Mutanen da suka tuntuɓeni amma ban samu damar amsa musu ba ina bada haƙuri. Chats, text ko kira da ban amsa ba dan Allah ku yi haƙuri ku yafe min, Musamman marubuciya Shatuu da Anty Hauwa Jidda.
Ilahirin members na groups ɗina ina godiya a gareku tareda neman afuwa na musamman daga wajen ku.
Masoya littattafaina ina godiya a gareku. Yanzu na fara rubutu Insha Allah amma daga yanzu duk wani littafina na kyauta (free book) zan dinga sake shi ne page by page, amma idan littafin kuɗi ne (Paid book) ba zai zo ba sai na kammala shi gaba ɗaya saboda gudun abinda ya faru a Matar Gwamna book 3.
Allah yasa ina da nisan rai rubutun littafi yanzu na fara kuma Insha Allah zan yi ƙoƙari na ga na rubuta labarin da ko a gaban Allah zan iya bada shaida akai. Insha Allah littattafaina kamar kullum zasu faɗakar, su nishaɗantar, su ƙayatar, sannan su zo da salon soyayya tsabtacacciya mai ƙayatarwa.
Littafina mai taken MISS NIGERIA zai fara zuwa Insha Allah ranan laraba 1/6/2022 za'a same shi a wattpad a duk lokacin da na yi posting.
Please please please idan kun hau youtube ku subscribing a channel ɗina mai suna *Azi's Corner*
NAGODE
Taku
©AzizatHamza
Post a Comment for "Governor's Wife Book 3 Complete Hausa Novel"