Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Ikraam 10

1/7, 8:51 PM] ‪+234 810 188 2232‬: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 10..... Ikram na xaune bakin kofar dakinta washegari da safe ta rungume hannayenta sae kumbura take tana bin Ammi dake ta aikace aikacen gida da kallo, ranar Abba bae fita kmr ynda ya saba fita ba wato da sassafe, yana xaune tsakar gidan shima, ikram dae bata kalli inda yake ba don bbu ruwanta da shi ma, jiya ba karamin duka Ammi tayi mata ba kuma bae ce kar ta doketa ba har sae da Ammi ta fasa mata baki, ikram ta tabe baki tuno shegen dukan da Ammi tayi mata jiya da daddare ta kuma kwace sabon kayan da Mami ta siya mata, ssae ta daga ma Ammi hankali jiya don sae da ta gama basu lbrin duk abinda ya faru jiya duk Ammi ta rude ta shiga jibgarta kmr xata kasheta, Abba kam kasa cewa komai yyi don shima tasa hanklin ya tashi, hkn ne ma yasa yau basu bari ta je sch ba, sallama aka shiga kwadawa bakin Zaure Abba ya mike ya fita sae ga shi ya shigo da kafinta rike da woods a hannunsa, abba ya ce "ai tun daxu kai nake jira iliya da na dade da barin gida ynxu"bayi Abba ya nuna masa Ikram ta bi su da kallo ta dan tabe baki ta dauke kanta, tana ji kafintan na ta buge buge da guduma a bayin, Abba na tsaye daga bakin kofa har ya gama bayan kmr minti talatin snn suka fito, Abba yace "idan na tashi daga wajen aiki xan biya ta shagon ka iliya" iliya yace "to" snn yyi masa sllma ya fita, Ikram ta bisa da kallo tare da murguda masa baki kmr yana kallonta, Abba yyi hanyar dakin Ammi ya daga labulen yace "ni na tafi Aisha" tace "to Allah shi kiyaye Malam" ya nuna ikram yace "don kaniyarki yau ma ki fita ki ga idan ban daure ki idan na dawo ba" ta fashe da ihu kmr jira take ta mike tsaye da sauri ta shiga tsalle tsalle tana rusa kuka, bae bi ta kanta ba ya fice, Ammi ta fito da sabuwar bulalan da ta siya, Ikram na ganinta tayi dakinta da gudu tana cewa tayi hkuri. Hka ikram ta yini ranar a daki ko tsakar gida bata leko ba bbu irin kukan da bata yi ba, abincin da Ammi ta tura mata cikin dakin ma kin ci tayi, ji take kmr a kan kaya take, ita dae ta tafi yawo kawae a rayuwarta, ta mike tayi bakin windon dakinta ta ga ko xata iya fita ta nn, amma duk irin jijjigar da ta dinga yi ma windon da duk karfinta kin fita yyi, karfe uku taji ana sallama a xaure ta mike da sauri ko me ta tuna ta koma ta xauna kuma, taji muryar Ammi na cewa "A'a Hinde daga ina hka" yarinyar tace "gida mana, wae Baba ne yace in xo mu taho da Rabi da kayanta" Ammi ta dan yi shiru snn tace "to bari ta shirya" ko rufe baki bata yi ba Ikram ta fito da gudu tace "Allah bbu inda xanje, ni Ammi baxan je gidansu ba" ta fashe da kuka ta xube wajen tana birgima, Hinde yayar Shafa ce yar kawunta na lado, Ammi ta rasa me xata ce don har ga Allah bata son xuwan yar ta gidan nn, cutarta suke ba Kawun nata ba ba matarsa da ya'yansa ba, tasan baban Ikram ne ya basa lbrin abinda ikram ta gaya masu jiya shine xae ce a daukota, cikin tsiwa Hinde tace "ni fa sauri nake Aisha gidan kawata xan tafi" ko kadan yarinyar bata da respect, Ammi tace "to kije tana xuwa" Hinde tace "tab, to ai baba ca yyi kafata kafarta" daki Ammi ta shiga, ta fara hada ma Ikram kayanta, ikram sae ihu take tana guje guje a tsakar gidan wae ita baxata bi ta ba, sae da Ammi ta mammake ta snn ta hankadata waje, tace ma Hinde ki gaida min mamarki, Hinde tace to, snn ta fice. Ikram na ihu Hinde na jan ta kmr rago suka isa gidan Kawunta na lado, da yake bae da aikin yi yana xaune tsakar gida rike da dan radiyonsa, Ikram na ganinsa ta nutsu don mugun tsoransa take, yana kikkifta ido yce "xo nan don ubanki Amadu" jikinta na rawa ta karaso ya fixgota ya shiga ja mata kunne da karfi yace "don uwarki masifa kike son ja mana a gari kike gantali har Allah ya hada ki da yan yankan kai jiya cikin ikonsa kuma bae bari suka maki komai ba" matarsa dake xaune gaban murhu, mai sunan Ammi suna ce mata Shatu tace "ae malam wllh da sun fille kan kowa ma ya huta, kuma duk gun uwarta ta gado gantalin nn" Ikram dae kan ta na kasa sae guntun hawaye take, Kawu na lado ya hankadata yace "ae kika ce xaki kawo min iskanci a nn babbala shegiya xanyi, duk salubabbun iyayen nn naki ne suka lalata ki, maxa dauki ledan kayanki ki kai ciki" Ikram ta dauki dan ledan kayanta tana hawaye tayi dakinsu Shafa ta ajiye, shatu ta kwalo mata kira ta fito da sauri ta ciro naira ashirin ta mika mata tana hararanta tace "maxa ki je gun mai shagon can ki siyo min ajino moto na goma da magin goma" Ikram ta karbi kudin ta fita, tayi gun mai shagon, "mai shago a bani cingam goma da biscuit" ya dauko kuwa ya bata ta karba, ta juya tana kallon kofar gidan kawun nata, ta murguda baki tace "kuma baxan dawo ba" ta saka kai da gudu sae hanyar gidansu, har ta iso kofar gidansu ta tuna ta dde bata je gun mai ayaba ba, hkn yasa ta canxa hanya tayi hanyar kasuwa, dae dae inda suka rabu da Aliyu jiya ta gansa xaune kan dakali yana danna wayarsa, ta wara ido tace "lahh! kai! Me kke yi a nn" ya mike da sauri yana kallonta yyi murmushi yace "ke nake nema mana" ta fashe da dariya tace "ae ni gun mai ayaba xani ynxu, sae na dawo"

Post a Comment for "Ikraam 10"