Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Ikraam 12

~ By Khaleesat Haiydar 12..... Washegari da Asuba Ammi ta sa Ikram tayi shirin makaranta bayan sun yi sllh don Abba yace shi xae dinga sauke ta a makaranta idan xa shi gun aikinsa, idan an tashi kuma Ammi taje ta daukota, tana saka uniform dinta tace "Ammi ae safiya bae gama yi ba kina son a sace ni ne a hanya," Ammi ta galla mata harara tace "ae da xan samu mai sace ki ma ni da na huta" ikram ta xumburo baki ta tsallake tean da Ammi ke hadawa taje dauko safarta da takalmi a dakin Ammi, Ammi ta daka mata tsawa "wae ke don ubanki wace irin yarinya ce shi tean kike tsallakewa" kmr xata yi kuka tace "to kin tare min hanyar" da gudu ta dawo dakin bayan fitar ta tana cewa "Ammi ni banga books dina cikin jakata ba" Ammi tace "to kina ban ajiyar book ne" ta fasa ihu tare da doka uban tsalle lkci daya ta kwabar da tean gaban Ammi tana cewa "wayyoo wllh ni baxan je ba Aunty xata min duka" Ammi ta mike da sauri tana salati ita ko tayi waje da gudu, Ammi ta bi ta ta cafkota ta mammaketa snn ta hada ta da biredin taci shi hka, shi dae Abba bae ce masu komai ba, karfe bakwae saura suka fita gida yana rike da Ikram da bata daina kukan dukan da Ammi tayi mata ba, har cikin makaranta ya shiga da ita snn yace da malamar ko an tashi kar ta bari ta fita mamarta xata xo daukarta, dariya malamar tayi don su kansu Ikram ta ishesu a makarantar. Ammi na kwashe taliyar da ta dafa ma Ikram na rana kafin taje daukota a sch, don ikram na son taliya ssae taji ana sallama a bakin xaure, sae da ta gama xuba taliyar a kula snn ta shiga da shi daki ta dauko Hijabi, a tsakar gida ta hadu da kanin Altine usman, tace "A'a usman daga ina, baka je makarantar bane yau" yaron yace "mama tace bani da lfya shi yasa ban je ba, wae wasu mutane suka ce in ce suna sallama da ke a waje" da mamaki Ammi tace "mutane kuma, mata ne ko maxa" yaron yace "mama guda biyu da mutumi guda daya ne" hankalin Ammi ya tashi a xuciyarta tace shknn Ikram ta kuma dauko mata magana kila, yaron ya juya xae wuce Ammi tayi maxa tace "usman an tashi daga makaranta ne, su Altine sun dawo ne?" ya girgixa kai yace "A'a basu dawo ba kuma ban ga yan makaranta na tafiya ba" Ammi tace "to je kace masu gani nan xuwa" yaron ya fita da gudu, Ammi tayi jigum a tsakar gidan gabanta sae faduwa yake, ganin bata ma masu jiran nata lkci take yasa tayi kofar gidan, tsaye Mami take har lkcin da wata mata da alamar kawarta ce, driver na xaune cikin motar da suka xo da, Ammi na ganinsu gabanta yyi mugun faduwa ganin irin shigar da suka yi, ta dake tace "ina yinin mu" Mami tayi murmushi tace "har ina tunanin ma ko masu gidan basa ciki ne" Ammi tace "ina ciki wllh" Mami tace "to sae dae kuma maganar da ta kawo mu ba ta tsayuwa bace" Ammi da gaba daya hankalinta baya jikinta tace "to ku shigo mana" Mami tace "to mungode" snn suka bi bayan Ammi suka shiga gidan, Ammi ta shimfida masu tabarma tsakar gidan suka xauna, snn ta dauko kujera yar tsugunno ta xauna tana kallonsu tace "ina fata dae lfya Hajiya" Mami tayi murmushi tace "lfya qlau wllh, nima dae ina fatan da maman Ikram muke mgana" gaban Ammi yace dass, ta shiga uku maganarta ya tabbata knn wani maganar kuma ikram ta dauko mata, Mami ta katse mata tunaninta tace "kin yi shiru kuma" Ammi tace "ehh ni ce, Allah yasa ba wani abun tayi maku ba nasan ma baxae wuce hka ba amma don Allah ku yi hkuri wllh na gaji da yarinyar ban san ynda xan yi da ita ba" dariya Mami tayi tace "ko daya wllh, wata alfarma naxo kuyi min maman Ikram, babanta na nn ne?" kai kawae Ammi ta sami kanta da girgixa mata, mami tace "duk da nasan baki san ni ba amma kisa a ranki ni din musulma ce kmr ku kuma me tsoran Allah ce" Ammi tayi shiru tana kallonta da mamaki, to wace alfarma matar nn ke so daga gareta ita da ba kowa ba, Mami ta katse mata tunanin da take cikin nutsuwa tace "Ikram nake son ku bani na rike don Allah ba don ni ba, kuma nayi maku alkawari xan rike maku ita amana, xan kuma bata tarbiyar da ya kamata snn xata yi karatu ssae, wllh Allah ya dora min son yara mata kuma sae gashi bae bani ba, kuyi ma Allah da Annabi ku bani ita na rike maku ita" tun da mami ta fara magana Ammi ta saki baki tana kallonta.

Post a Comment for "Ikraam 12"