Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Ikraam 18

Ikraam~ By Khaleesat Haiydar. 18..... Da sauri Mami ta fito daga kitchen tana tambayarsu me ya faru, shi kam Khaleel hanyar stairs yyi da sauri bayan ya dauki briefcase dinsa, Ikram ta bi sa da gudu ta fixgo hannunsa tana hararansa tace "meyasa xaka bani tsoro kai" Mami ta karasa stairs din tana kallon Khaleel tace "magana nake son kuma kana wucewa" ya fixge hannunsa daga rikon da Ikram tayi masa yana mata mugun kallo yace "xan take kanki ne" ta xaro manyan idonta tayi gun Mami da sauri tace "Mami kina jinsa ko, wae xae taka min kai, wllh kai ma sae na taka maka naka" Kwafa yyi ya haura sama, Mami na kallon Ikram tace "me ya sauko da ke?" Ikram ta wara ido tace "ji nayi wani abu yyi wani irin kara sae na sauko da gudu in gani" Mami ta kamo hannun Ikram tace "kar ki kuma saukowa falon nn idan bani na sauko dake ba" ikram kmr xata yi kuka tace "sbda me" Mami bata tanka ta ba suka haura sama ta shiga dakinta da ita, sae da Mami tasa ta je ta sake wanka don jikinta duk yaukin shower gel yake, Mami ta shafa mata mai bayan ta fito snn ta bata wani riga da wando ta sa, Ikram tace "to ina wnn abokin nawa yake ban gansa ba" Mami tace "ki jira ni in dauko maki abinci" tana kai wa nn ta fice, Ikram ta dinga bin dakin da kallo, a hankali ta bude kofar dakin ta tsaya daga bakin kofar tana kare ma corridors din dakin kallo, kofofi sun fi biyar ta gani, ta fito ta shiga bude duka kofofin bbu wanda bata ga makeken gado ciki da tv ba, kofar dakin dake kallon na Mami ta bude suka yi ido hudu da Khaleel yana goge kansa da towel da alamar daga wanka ya fito, bude baki yyi da mamaki yana kallonta cikin tsawa yace "ohh my God, Mami wae wacece wnn 4 Heaven sake" ko kallonsa Ikram bata yi ba ta gama kalle kallenta ta juya xata wuce sae ga Mami, Mami ta hade rae tace "me ya fito dake Ikram, ba ki jin magana ko?" Ikram ta daga hannunta sama tace "wllh ina ji Anty, kawae fa don ina kallon ko ina shine xae dinga ihu yana kiranki" cikin damuwa Khaleel yace "don Allah ki gaya min wacece wnn Mami, me take xuwa yi a nn" Ikram tace "sunana Rabi'a, amma Ammi da Abba da yan anguwarmu suna kirana Ikram, Ammi tace min kawu Na lado ne yace a...." janta Mami tayi suka fice daga dakin ta kullo masa kofa tana kallon Ikram tace "idan ina gaya maki magana baki ji Ikram wllh xa mu bata" ikram ta xumburo baki Mami ta bude dakinta ta turata ciki tace "kar ki sake fitowa" Ikram bata ce komai ba Mami ta jawo kofar ta koma kitchen, bude kofar Ikram ta kuma yi tace "to ae ban gama gaya masa sunana ba" ta murguda baki tayi hanyar dakinsa kuma ta bude kofar, wnn karan jallabiya yake sa wa, kasa karasa xura jallabiyan yyi, Ikram tace "kawu na lado ne yace wae a sa min Rabia wae sunan kanwarsa ce kuma....." fixgota yyi a fusace ya kulle kofar dakin da makulli.

Post a Comment for "Ikraam 18"