Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Ikraam 27

Ikram tace "sbda me" yace "sbda ba sunanta Anty ba" tayi shiru tana kallonsa snn tace "kai ya sunanka to" ya wara ido yace "au baki san sunana ba Ikram" ta gyada masa kai ya kamo hannunta yana kallon cikin idonta yace "Aliyu ne sunana" tace "nima Aliyu xan dinga ce mka" ya girgixa mata kai yace "yayana xaki dinga cemin" tace "to bani sweet din yayana" murmushin jin ddi yyi snn yace "to ki fara min duk abnda nayi maki tukun" tace "to" ya daura hannu kan dimple dinta ita ma tayi masa hka, yyi murmushi ya daura yatsunsa biyu kan lips dinta ita ma tayi masa hka, dariya yyi ya rungumeta a hankali yace "I luv yhu bbyna" ikram ta wara ido tana kallon fuskarsa tace "lah ni ba bby bace, ni da na girma" kmr ance ya daga kansa sama yaga Khaleel xaune cikin balcony din dakinsa laptop gabansa yana kallnsu, suna hada ido da Aliyu ya fashe da dariya har da sauka daga kan kujera Aliyu ya mike tsaye yana kallonsa ya hade rae yace "wats funny guy" mikewa Khaleel yyi ya shige dakinsa yana ci gaba da dariya, Ikram ta bude baki tace "lah ashe yana dariya, ni ban sani ba" Aliyu bae ce komai ba ya xauna ya sauke ajiyar xuciya yana kallonta yace "je dauko sch bag din ki" ta mike da gudu tayi cikin gida, A falo ta tar da Khaleel ya fito daga kitchen rike da cake da juice a plate, ta wara ido alamar mamaki tace "yaya Khaleel ashe dama kana dariya ni ban sani ba" ya xabga mata harara yace "kinsan Mami bata nn dukan tsiya xan maki idan baki shiga hankalinki ba" ta harare sa tace "to ae yayana yana nn" Jummai tace "lah ashe baku je da nisa ba" Ikram bata ce komai ba ta wuce sama tana murguda ma khaleel baki ya bi ta da kallo yana gyada kai a hankali alamar xae yi maganinta, yana nn tsaye ta sauko rike da jakar makarantar ta, ya fixgota da karfi yace "wa kike harara" muryar Aliyu yaji yana cewa "hey ka taba ta kaga idan ban rama mata ba" Khaleel ya juya yana kallonsa ya fashe da dariya yace "girma dae ya fadi, wae yar cikin ka ka xaunar kke ce ma I Love Yhu, na sha suprise dinka Aliyu, ina manyan babes dinka" dariya ssae yake ya haura sama, Aliyu ya ma rasa me xae ce masa ya bi shi da kallo don bae yi xaton yaji ba, Ikram tace "ni baxan taba son yaya Khaleel din nn ba sbda yana da bad habit, yau a sch Anty tayi mana Moral Education ta gaya mana menene Bad Habit"

Post a Comment for "Ikraam 27"