Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Ikraam 3

[12/30, 8:39 PM] ‪+234 706 135 1072‬: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 3...... A hanya ikram ta hadu da su Altine kawarta suna dawowa daga islamiyya, Altine tace "ina xaki Ikram," Ikram tace "kasuwa xanje na ga ko xan ga matar daxu ta kuma bani Ayaba xo ki raka ni," Altine tace "wace mata?" Ikram tace "wata babban mata ce ta bani ayaba da kudi da apple matar na da katuwar mota da katon yaro har ya xama baba shi ma" Altine da ta bude baki uwa sokuwa tana kallon ikram tace "aa ni gida xan tafi kar baba tayi man duka," Ikram ta murguda mata baki tace "shine kika tsayar da ni," tayi kwafa tare da jan tsaki ta ci gaba da tafiyarta, Altine tace "malam yace me yasa kika daina xuwa makaranta fa," Ikram na ci gaba da tafiyarta tace "Ammi tace baxan kuma xuwa ba," Altine da sauran kawayenta suka tabe dan bakinsu suka ci gaba da tafiyarsu. Ammi na fitowa ta nemi ikram ta rasa tsakar gidan, ta leka dakinta bata ciki, ta fito tana haska tsakar gidan ko xa ta ga takalminta ta ga bbu, ta rike habarta tana girgixa kai cikin damuwa tace "na shiga uku ni Aisha ina yarinyar nn tayi kuma" Hijabinta ta figa tayi gun me treda don nan daya daga wajajen xuwanta, yace ae ikram bata yo gun sa ba, tayi gidansu Altine mamar Altine na daki ta fito, tace lah ae ikram ko bata shigo ba, Ammi tace "to su Altine fa," matar ta kwala ma Altine kira ta fito, Ammi tace "kinga ikram altine," nn Altine ta labarta ma Ammi abinda ikram ta gaya mata, Ammi ta fita daga gidan da sauri tana cewa "nashiga uku na lalace, kashe ni ikram ke son yi, kasuwa da daddaren nn?" Mamar altine ta bi ta suka fita ita ma tana salati, nan suka shiga neman ikram gida gida a anguwar ko karya tayi ma altine, amma duk inda suka shiga sae ace bata je ba, hnklin Ammi duk ya bi ya tashi, mamar altine sae ca take xa su ganta. Ikraam bata taba xuwa kasuwa da daddare ba, tana isa ta tarar duk an kulle kofofin shiga cikin kasuwar nan ita wae gun mae fruit din xata je ta tambayesa ko matar ta sake dawowa, wani mutumi dake xaune yana xukar wiwi da yan uwansu su kusan hudu kan benci taje ta sama tana kallonsa tace "kai meyasa aka rufe kofofin nn, waye kuma ya rufe gashi ina son shiga," mutumin ya daga jajayen idonsa yana kallonta da mamaki yace "shiga xa ki yi?" tace "eh mana gun mai Ayaba nake son xuwa," duk suka bushe da dariya ta dinga binsu da kallo baki a sake, wani daga cikinsu ya fixgota yace "xo mu je in nuna maki idan xaki bi ki je gun me ayaba yarinya," sauran duk suka kuma kwashewa da dariya ta fixge hannunta tana murguda masa dan karamin bakinta tace "dan iska kawae," ya buda ido ssae yana kallonta yace "ni kika ce ma dan iska?" tace "eh mana ae ku duk yan iska ne nasani, dama Ammina tace min duk masu shan sigari yan iska ne kuma basu da mama da baba," ta kuma murguda masu baki tana jujjuya mnyan idanunta ta ja wani dogon tsoki ta koma jikin karfen kasuwar ta shiga hawa wae xata dura ciki, har ta kai tsakiya gnin ynda suke ta dariya yasa ta sauka ta juya xata bar wajen, mutum biyu suka fixgota a tare, wani kuma ya shake wuyarta, ihu ta fasa, wani ya mike ya daga ta sama da katon muryarsa yace "ku xo mu je," duk suka mike, ta dinga ihu tana shure shure, wani bawan Allah ya xo wucewa ya bisu da gudu yace "ina xaku kai yarinyar," ikraam tace "wllh yanka ni xasu je suyi yan iska ne su, sigari suke sha," gabansu ya shige yace "maxa ku ajiyeta," duk suka bushe da dariya wani yace "kama gabanka malam," wani wawan naushi ya kai ma wnda ke rike da ita ba shiri ya saketa ta fadi kasa, ta mike a guje ta bar wajen, mutane biyu suka bita da gudu, sauran suka rufe mutumin da duka, kan kace me har ta bace masu don lungu lungu ta dinga bi gashi ta iya gudu, tana mayar da numfashi ta iso anguwarsu duk ta jefar da takalman kafarta da hula, anguwar tsit gun mai treda ta nufa tana kallon kofar gidansu kmr munafuka, bata tarar da shi ba amma shagon a bude yake, ta xauna kan benci ta kara fitilar da ya rage snn ta dauki sweet daya ta jefa bakinta, ta kai minti kusan talatin xaune a gun, jifa jifa tana ganin mutane da fitila suna wucewa sae ta buya, ashe nn duk nemanta ake, muryar mai treda taji da wasu maxa guda hudu suna cewa "idan Allah ya yrda ma xa'a ganta, bbu abinda ya sameta," mai tredan yace "to Allah yasa hka, ban jin ma xan iya xama shago ynxu bari na rufe kawae na tafi gidan wllh rashin ganin yarinyar nn ya tsaya min a rai," ya karaso cikin shagon xae kashe fitila ya rufe ya ga ikraam xaune tana kallonsu, sae da ya koma baya da sauri da mugun mamaki yace "ikraam" ta washe hakora tana kkrin boye sweet din hannunta, yyi waje da sauri cikin daga murya yake cewa "jama'ah ku xo ga ikram a shagona," baban altine ne ya fara iso wa da sauri snn sauran makwabtansu, me treda dae na tsaye baki bude yana kallon ikram, baban altine ne ya hade rae yace "daga ina kike Rabi," ta dan marairaice tace "kaga baban altine a nn kofar gida ne wasu masu shan sigari suka daga ni sama shine na shigo shagon baba Habu da gudu, amma sun tafi," Ammi ce da su maman altine suka karaso wajen da sauri, Ammi ta ci kuka har ta gode Allah.

Post a Comment for "Ikraam 3"