Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Ikraam 88

88..... Karfe bakwae Khaleel ya shigo dakin har lkcn Ikram na baccin da bata yi jiya ba, ya xauna kan gadon ya tsura mata ido yana kallonta, can yyi murmushi ya kauda kansa a xuciyarsa yace Alhmdllh na samo cure din rashin kunyar yarinyar nn, dawowa kusa da ita yyi ya shiga tada ta, ta farka a tsorace ya hade rae ya daura yatsunsa biyu a lips dinsa alamar kar tayi masa kara, suna hada ido ta sunkuyar da kanta da sauri, yace "kin yi sllh ne" girgixa masa kai tayi ta mike ba tare da ta kallesa ba kmr munafuka ta nufi bathroom, ko da ta fito baya dakin, dogon hijab dinta ta sa don yin sllh, tana idarwa ta dauki brush dinta ta shiga bayin ta wanke baki, snn ta fito tayi maxa ta sa kayanta tunda tayi wanka, ta koma can karshen gado ta xauna ta rakube, da breakfst Khaleel ya dawo dakin, ya ajiye mata nata yace "hurry up xamu kama hanya ynxu" ba tare da ta kallesa ba kanta a kasa kmr munafuka ta jawo breakfst din ta shiga budewa a hankali, ya kafa mata ido, karfe takwas da minti goma suka bar hotel din suka kama hanyar Abuja, ba su suka isa Abuja ba sae kusan yamma, duk Ikram ta jigata ssae tayi amai har ta gode Allah, Mami bata nn sae Jummai, ta shiga dakin Mami ta cire gown din jikinta ta daura xani ta xube kan gado sae baccin wahala. Karfe shidda kishin ruwa tare da bude kofar da aka yi suka farkar da ita daga baccin da take, Aliyu ta gani tsaye bakin kofa ya kafa mata ido, suna hada ido ya juya da sauri ya fice daga dakin, da har ta bude baki xata ce yayana kawae ta toshe bakin da sauri sae hawaye. tana xaune ita daya a daki tun bayan fitan Aliyu tayi jigum duk ta rasa me ke damunta, ssae xata baka tausayi idan ka ganta a wnn lkcn, bude kofar da aka yi yasa ta daga idonta da sauri Mami ta shigo dakin, Ikram ta sakko daga kan gado tana kirkiran murmushi tace "Mami sannu da dawowa" Mami ta karaso dakin ta ajiye handbag din hannunta tace "Ina Khaleel" Ikram tace "ban sani ba nima Mami, daga bacci na tashi" Mami bata kuma cewa komai ba, ganin Mood din Mami yasa Ikram a hankali tace "Mami baki da lfya ne" Mami ta girgixa mata kai ba tare da ta kalleta ba, ta ciro wayarta tayi dailn nmbrsa ta kara a kunne sae da ya kusa katsewa snn ya daga, Mami tace "ina neman ka Khaleel" bata jira me xae ce ba ta katse wayar, ta juya tana kallon Ikram kmr bata son mgna tace "kinyi sllh ne" Ikram ta girgixa mata kai snn ta nufi bathroom don yin alwala, Mami na xaune ta fito tayi sllh, snn tace taje ta karba abinci gun Jummai, a stairs suka hadu da Khaleel bata ko kallesa ba ta sauka abunta ya nufi dakin Mami, da sallamarsa amma can kasa ya shiga dakin, suna hada ido da Mami ya sunkuyar da kansa ya xauna kasan tiles yace "ina yini Mami" Mami bata amsa ba idonta a kansa, ya daga kai yana kallonta sae kuma ya maxa ya sunkuyar da kai ganin kallonsa take. Mami ta mike ta nufi window a hankali ta tsaya tana kallon waje snn ta fara mgna a nutse. 2 mins · Khaleesat Haiydar...

Post a Comment for "Ikraam 88"