Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Ikraam 9

~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 9..... Mami tace "dawo inda kike kar mu bata ynxun nn" ba musu ta dawo, shi kam tada motar kawae yyi yana murmushi suka bar wajen, tana jikin Mami suka iso dae dae inda Mami ke shiga mota idan ta fito daga kasuwa Mami na kallonta tace "ina ne hanyar gidan naku Ikram" Ikram tace "A'a a nn xaku ajiye ni ae" Mami tace "aa gun mamarki xan je Ikram," da sauri Ikram tace "A'a ni dae a nn xan sauka nace maki bbu kowa a gidanmu" Mami tayi shiru tana kallonta snn cikin lallami tace "to Ikram ae Mamanki dukanki xata yi idan kika koma gida ynxu ke kadae, kinga dare ya kusa, xata ce daga ina kike" ikram ta girgixa kai alamar bata yrda ba tace "A'a ae a xaure xan tsaya har Abbana ya dawo, baxae bari ta dokeni ba" Mami ta rasa me kuma xata ce mata, can dae tace "baki son in mayar da ke gidana ki xauna dani ina sa maki cartoon ina baki naman nn mae dadi muna tafiya yawo kuma ina siya maki sabon kaya" da sauri Ikram tace "ehh ehh ina so" Mami tayi murmushi tace "to ae sae naje na gaya ma mamarki kar ayi ta nemanki" Ikram ta girgixa kai tana tabe baki alamar bata yrda ba tace "A'a ni dae baxan kai ki ba dukana Ammi xata yi da waya ko muciyan tuwo maman altine ta taya ta, kinsan maman Altinen nan bata sona" Aliyu da ya tsura mata ido har lkcn yyi murmushi yana kallon mami cikin harshen turanci yace "bar ta kawae ta tafi Mami, xan rakata da kafa sae in ga gidan nasu, idan yaso ko gobe ne sae in kawo ki" Mami ta galla masa harara tace "sannunka, to ban yrda ba" yyi murmushi yace "to ae dats d only option ynxu Mami" ya maida dubansa ga Ikram yace "to ni in raka ki gidanku Ikram" Ikram ta juya tana kallonsa xata yi magana yace "to ae ba shiga xanyi ba, kawae raka ki xanyi" tace "to" snn ta shiga tura motar xata bude, a hankali Mami ta bude mata motar snn ta sakar mata murmushi tace "to ki gaida min mamanki Ikram" kai kawae Ikram ta gyada mata ta fice, shi ma ya fito, Mami ta mika masa ledan tsarabar da tayi mata ya karba snn ya bi bayan Ikram, ita ko ta dawo driver seat tana binsu da kallo, tafiya suke yana rike da hannunta yace "wani class kike Ikram" Ikram tace "ae primary 5 nake ynxu, amma fa da a primary 4 nake kawae sae naga an mayar dani 5, kuma ina son makarantar mu ssae don ana siyar da alawa da madara da ice cream, Ammi tace baba ne yace a sa ni a makaranta don shafa da altine ma sun fara xuwa, amma ynxu shafa ta daina xuwa wae babanta kawu na lado bashi da kudi, nima kasan wa ke biya min, to ba babana ke biya min ba don shima ba shi da kudi, malam habu ne ke biya min," matse hannunta da ta ji yyi yasa tayi shiru, yace "ca nayi wani class kika ban ce ki ban lbri ba" ta fixge hannunta tana huci tace "shine xaka cunkule ni baka san akwae xafi ba" yyi yar dariya yace "to rama" ta dago hannunsa ta dage ta shiga yi masa abinda yyi mata, sae taga dariya kawae yake, bae ankara ba yaji ta gatsa masa wani mugun cixo, yyi yar kara ya fixge hannunsa ya saki ledan hannunsa yana yarfe hannun yana kallonta da mamaki, ta fashe da dariya ta kanne ido tace "gashi nn na rama" ya daga hannun yana kallon inda ta cije shi, ta duka ta shiga kwashe abinda ya xubar snn ta mika masa ledan tace "ungo" ya fixge yace "wllh ba ruwana dake daga yau" tayi narai narai da ido kmr xata yi kuka ta mika masa hannunta tace "to rama" ya kama hannun ya durkusa gabanta ya daura hakoransa kan yatsunta, ta rumtse ido tana yarfe dayan hannun ya gatsa mata cixo shi ma snn ya sake, ihu ta fasa ta shiga yarfe hannun ta fashe da kuka tace "wllh sae na gaya ka da babana" ya fashe da dariya yace "to ae ke kika ce in rama" rikota yyi ganin guduwa take son yi tana kuka, don ba karamin xafi cixon yyi mata ba, da sauri yana dariya yace "srrry kanwata kema rama kuma" ta fixgo hannunsa ta gatsara masa wani shegen cixo, yyi kara yana yarfe hannun ya mike ya dauki ledan yace "to mu tafi" suka ci gaba da tafiya tana tsotsan inda ya cije ta sae kallonta yake har suka iso anguwarsu, ta juya tana kallonsa tace "oya ka tafi to ga gidanmu can" yace "baki son in gaida mama Ikram" kmr xata yi kuka tace "to ae dukan mutane take yi, nima ynxu nasan dukana xata yi" ya tsura mata ido yace "mu je in roketa kar ta dokeki" da sauri tace "A'a ae sae ta dokeni, ta bayi na yi tsalle na fita daga gida daxu don ta rufe kofar xaure wae baxan fita ba ni kuma ina son in fita" ya xare ido yana kallonta da mamaki, kan yace komai tace "lahhh ga Abbana can ya dawo" da gudu ba tare da ta kuma kallonsa ba tayi gaba, ya shiga kiranta ta karbi abinda mami ta siya mata amma ina, dae dae kofar xaure suka ci karo da Abbanta ta rungumesa tana masa oyoyo yace "daga ina kike Mamata" tana washe hakori tace "can" jan ta yyi ba tare da ya lura da kayan jikinta ba suka shiga ciki, Aliyu yyi murmushi ya juya ya bar wajen don Magrib yyi. Suna shiga tsakar gida Ammi ta fito da wayar rediyonta Ikram tayi waje da gudu tana ihu, Abba yace "wae meye hka kike Aisha me tayi maki" Ammi tace "ae wlh ta koma ta shigo gidan nn ta inda ta fita idan ba hka ba wllh sae na faffasa mata jiki yau"

Post a Comment for "Ikraam 9"