Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi'ar Zuciya 8

08
*zafafa biyar na kudine,tuntubi wadan nan numbers din don samun naki copy din ki karanta cikin aminci*

08184017082
Ko
09134848107

*_follow us @ instagram_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1h9y2qgfg67x5&utm_content=nj79azb

Or facebook
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

___________________________

Dan kwantar da kujarar yayi kana ya miqe sosai Samanta yana jin yadda gajiya take bin jikinsa,don gaba daya wunin yau bai shirya fita ba,ya shirya zama ya huta sosai a gida,saboda satin gaba daya cikin aiki ya yisu,babu dare babu raba,har inda ma a tsarinsa babu schedule na zuwansa sai daya ratso masa a sannan din.

hannayensa saman kansa yayin da idanuwansa suke a rufe,yayi nisa a tunaninsa sosai,busy busy ne dashi irin wanda mutane da yawa ke mamakinsa,sam bai bawa kansa hutu ba.

a qalla ya kusa minti ashirin a zaune a haka,wanda hakanan yaji zaman yayi masa dadi,ko ba komai ya dan samu break na wasu mintuna.

Dan waiwayawa yayi gefansa,a sannan ya hango tahowar professor shi da wasu mutane hudu,saiya miqe ya gyara zamansa,ya kuma kunna motar yana jiran qarasowarsa.

yana jin sanda ya shiga yana sallama da mutanen,suka maida murfin motar suka rufe masa,don haka saiya tashi motar,dai dai sanda professor ya furta
“alhamdulillah”yana sauke ajiyar numfashi.

A nutse yake tuqin har suka fita daga airport din,a hankali professor rashid yace
“lawan….ko ka sake koyon sabon salon tuqi ne?”raba idanu samir yayi hagunsa da damansa,saiya lanqwashe murya yace
“eh alhaji”dan jim professor yayi sannan yace
“to yayi kyau”daga haka bai sake cewa komai ba,zaman shuru yaci gaba da ratsawa a tsakaninsu.

“Daka sani ai baka wahalar da kanka ba samir…..”yaji abban nashi ya fada bayan tsahon wani lokaci,ya ganeshi kenan,qyaleshi yayi kamar bai gane ba,qaramin murmushi ya subuce a kuncinsa,jerarrun fararen haqoransa suka bayyan,har yayi kamar bazaice komai ba sai kuma ya tanka
“yau daya dai abba….ai nima na samu ladan yau din”wayar hannunsa professor ya ajjiye,ya tsurawa gaban motar idanu,kamar anan fuskar samir din take,baisan me yasa a kullum shi da tilon dan nasa komai nasu yasha banban ba,komai nasu ba iri daya bane,abinda yake sam ba cikin tsari da burinsa ba,ya jima da sanin cewa ba haka yakeso ya kasance ba,ba haka tsarinsa yaso ya zama ba,to amma duk ta inda yake tunanin zai gyarota babu wani sauran dama data rage masa,don haka a maimakon yayi magana,saiya buge da hade yatsunsa waje daya,yana maida tunaninsa wani waje daban.

Duk sanda yayi tafiya irin wannan ya dawo iyalansa dama ma’aikatan gidan kan cika da murna,kamar yanzun,da samir ke biye dashi dauke da wata qawatacciyar qaramar jaka mai zubin akwati,yana biye da professor har zuwa cikin qawataccen falon gidan,mai yalwa da kuma burgewa,wanda ya wadata da dukkan wani nau’in kayan alatun rayuwa.

mutum uku ne ke dakonsa zaune cikin falon,biyu daga cikinsun matasan yammata ne,daya tafi daya tsaho da haske,kamar yadda daya tafi daya shekaru da basu wani taka kara sun karya ba,don dukkansu ba zasu gaza shekara sha tara da ashirin ba.

Daga wata kujera kuma mai mazaunin mutum biyu,macace xaune itama wadda ta mallaki shekaru ɗai ɗai har shekara hamsin,saidai idan har kai mai kallo xa’a qyaleka kayi mata ƙiyasin shekaru,to ba shakka zaka ce dauka cewa bata wuce shekara talatin da biyar ba.

Tun a kallon farko xaka bata sunan HAMSHAQIYA saboda ta cancanci sunan,fara ce sol,shekarunta sam basu boye hasken fatarta ba,tana da matsakaicin kyau wanda ya cakuda da tarin ado da qawar da take qawata kanta dashi kullum kwanan duniya,kallon farko zai gaya maka ta saba da ado ya zame mata jiki,salon irin abun nan da hausawa suke cewa WANKA YABI JIKI,tun daba hannayenta zuwa wuyanta kayan ado ne na mata,fuskarta wadace take da murmushi kamar bakinta zai yage,idanunta qur bisa saman fuskar wadan nan halittu guda biyu,wato samir da professor,tana dubansu da wani irin kallo me nauyi da zurfi.

Dukkaninsu suka miqe kowanne fuskarsa na nuna tsantsar farinciki,daya daga cikin matasan yammatan nan wadda da alama batakai shekarun daya ba ita ta tako da sauri zuwa inda professor yake
“Abba…..sannu da dawowa”ta fada da ‘yar siga ta shagwaba,da alama kuma hakan habit dinta ne,tana dora kanta saman kafadarsa,kamar marayan daya samu tallafi,murmushi ya saka yadan dora kansa saman kanta
“barka kadai auta….na sameku lafiya?”
“lafiya qalau abba,saidai munyi missing dinka”murmushin yakuma saki
“gani na dawo ai jauhar,duk wata kewa ta qare ko?”kai ta gyada,sai dayar itama ta matso,tasa hannu kadan tana gyara eye glasses dinta,fuskarta itama murmushinne kwance
“barka da zuwa abba”
“barka kadai lelen abba…..na sameku lafiya?”
“lafiya lau abba ya hanya?”
“alhmdlh,ya karatu?”saida ta saki wani ni’imtacce murmushi,tana jin wani dadi na ratsata,ta daga idanun a hankali ta maida gashi,samir…….wanda har yanzu yake tsaye a bayan abban nasu tamkar wani dogari,hannayensa zube cikin aljihun wandonsa yana kallon dukkan abinda ke faruwa, inside him yana jin tsaiwarsa a wajen cikin abubuwan da suke gundurarsa nan da nan,ya qagu duka a gama wadan nan gaishe gaishen.

dauke idanunta tayi ta maida kan abban,a duniya tana jin dadi tana alfahari abban nasu ya tambayeta karatunta,tana jin wani qwarin gwiwa yana shigarta aduk sanda ya tambayeta wani abu daya danganci karatunta,takanji burinta kwadayinta da qwarim gwiwarta yana daduwa
“alhmdlh abba….komai lafiya”
“ma sha Allah”ya fada yana maida dubansa xuwa gareta,har yanzu bata matsa daga inda take tsaye ba,amma hankalinta idanuwanta da hankalinta dukka yana kansu
“sarautar mata…….yada tsaiwa a nan?”murmushi ta saki
“to ai naga hankalinka duka yana kan yaranka,kaga gwara na barku ku gama tukunna…..barka da dawowa”
“barka kadai…..na sameku lafiya?”
“alhmdlh”ta fada taba jifansa da wani murmushin,saita tako a hankali ta raba ta gefansa,idanunta saman fuskar samir,suna hada idanu ya kauda kansa ya miqa mata jakar professor dake riqe a hannunsa,hannu ta miqa zata amsa tana cewa
“ka kyauta samir”ya fahimci abinda take nufi,saiya saki qaramin murmushi yana juyawa kadan zai fita
“ya da haka son…ka bari daddy ya kintsa muci abincin rana tare mana”ta furta cikin nuna zallar kulawa,kansa ya girgiza yana sosa kan mashi da tsinin key din mota,shida yakeson tsallakewa fadan professor,yayi imanin idan ya zauna suci abin tare zai tono laifin da shi yaketa qoqarin bunnewa ne
“akwai abubuwa da yawa dana bari,zanje na rage wasu,bazan jima yau a waje ba zan dawo gida” sanda yake maganar shima professor ya nufi hanyar da zata sadashi da sassansa da suka qunshi bedrooms manya guda biyu,da.katafaren falo guda daya
“da zaki daina wahalar da kanki wajen tsaidashi,ki barshi ya tafi kawai, saboda haka yakeso,hakan ya tsarawa kansa kamar ko yaushe” sarai samir yasan magana ce mai harshen damo yayi masa,sai data waiwayo ya kalli samir
“ohk….saika dawo,Allah ya tsare” kansa ya gyada sannan ya juya zai fice,itama ta rufawa professor baya.

“ya saraki”kiran da aka masa shine abu na biyu daya shiga kunnensa daga hirar professor da matarshi,sai yaja tunga ya tsaya sannan ya waiwayo a hankali sanda take tasowa a shagwabe ta riskeshi.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected