DA’IMAN Complete Hausa Novel
Copied B
⚜DA’IMAN Complete Hausa Novel⚜
Na
MAMUH GEEE
☆dedicated to☆
Husnah bbchoudiallo
BISMILLAHIR-RAHMANR-RAHEEM.
Ina mika dukkanin godiata ga masoyana masu
son novels dina,
Kuma akoyaushe ina samun sakon fatar
alkhairanku…ngd allah yabar kauna.
1→5
Sallama take kwadowa tun akofar gidan harta
shigo dan karamin tsakar gidan.
Sanye takeda atampha `yar leda kalar kore shar
wato kalar asalin `dan `kauye..sai wani gyale
fari data yafo mai bakin lesi da `yar jakar
hannunta `baka data farfashe alamar tsufa duk
da itace tafi kowa wayewa akauyen tunda itake
zuwa birni.
Shekarunta xasu kai talatin da takwas zuwa da
arba’in zuwa da sama.
Wata sallamar takuma kwadawa tana fadin,
Wai duka gidan bakowane nake sallama ba’a
amsawa?
Daga bayanta taji an amsa mata cikin wata yar
siririyar murya.
Juyowa tayi adan tsorace tana ganinta ta hade
fuska tareda watsa mata harara tace,
Lallai na yarda da kinsamu sake a wurin
ladingo.
Munafuka mai kamada mayyar uwarta ace kina
cikin gidan nan naketa rangada sallama amma
kikayi lukus a daki.
Toma wai uwar me kike adakin ne.
Sunkuyar da kanta tayi muryarta na `dan rawa
tace,
Kiyi hkr iya jummai wlh kainane yake ciwo
banjiba.
To dama ina zakiji ladingo ta daure miki gindin
iya shege.
Ladingon ce tafito daki cikin sauri tana daurawa
guiguyayen kanta dankwali murya cikeda masifa
tace,
Wai hayaniyar me nakejine a gidan?
Washe jajayen hakoranta tayi dasuka dafe tana
fadin,
Aa jummai lfy daga zuwanki kike fada,badai
wannan mai kamada muciyarce ta tabakiba
yanxu nasa buba ya yayi mata dukan shanu ba.
Aa kyaleta ai dagayau kuma andaina dukanta
dan nazo mana da mafita akanta kuma wllh ba
karamin samu zamuyiba ke wlh har makka sai
munje.
Washe baki ladingo tayi cikeda farin ciki tace,
Haba jummai yanxu naji zanje,
Nidai idan xamu samu kudin aiko gidan cire
kaine xan bada ita na huta da ganin wannan
shegiyar fuskar tata mai kama da jariran aljanu.
`Dakin ladingo suka shige.
Tadan leko tace,
Kuma wlh kafin nafito ki tabbatarda kinyi wanke
wanke kin dora mun abincin saidawata na
rana.munafuka dangin ifiritu.
Sum sum tawuce tafara hada kayan wanke
wanke dan ita tarigada tasaba da xagi,cin
zarafi,duka da wahalar babah ladingo da
`yayanta buba da idi dakuma babbar aminiyarta
wato iya jummai.
○○○○○○○○
Gyara zama tayi takalli aminiyar tata tace,
Ladingo wani alherine nagani nace to lallai kece
kika cancanta dashi.
Wato can gidan hajiyar danake zuwa birni kai
mata yan aiki.
Da sauri ladingo ta kada kai tace inajinki
jummai.
Wato wani alhajine mai shegen kudi a acan
habuja, `dansa dayafiso fiyeda komai
aduniyarnan yasamu matsala ta tabin
kwakwalwa ta sanadin shan ko menene ma
sunan?ni namanta sunan abun.
Mahaifiyar yaron ta rasu tun yana yaro ta a
kasar turawa yatashi acan yakoyi shan abun har
yasamu matsala.
Matar alhajin ita tace bazata iyaba shinefa
akayi takai masu aiki duk wadda aka kai giduwa
suke basu iyawa sbd.
Mahaifin yaron kuma bai cika zamaba.
Anyi na asibin tarsun gaji shine aka kira malami
yace sammu ne akayiwa yaron.
Atakaice dai baasamu me iya zama dashiba
shine malamin yace ayi masa aure sbd matarsa
bazata gujesaba.
Anyi neman matar dazaa aura masa babu sbd
kowa tsoro yake.
To matar alhajin saita bugowa hajiyar danake
zuwa gurinta tace asamo masa koda yar
kauyece idan yaso inya warke sai ya
saketa.kuma ta bada kyautar miliyan daya ga
duk wanda yabada ‘yarsa aka daurawa yaron.
Shine naga wannan mai kamada masillar kitson
batada wani amfani agareki ba gwara ki badata
ki hutada dangin mayuba.
Wani irin fitsarine yakusa kufcewa ladingo ta
waro ido jikinta na rawa tace,
Jummai miliyan daya?
Yazamuyi dasu?
Kwantar da hankalinki
Miliyan daya dinnan rabawa zamuyi muda
‘yayanmu tunda duk babu mai abinyi acikinsu
sai sace sace kinga kuwa mun huta.
Wata irin guda ladingo tasaki tana shewa tace,
Wllh jummai idan kinje yau kice nabasu ita ko
gobe sukeso suxo adaura nabasu……..
⚜DA’IMAN⚜
Na
MAMUH GEEE
☆dedicated to☆
Husna bbchoudiallo
6→10
Cikeda farin ciki tareda kwarin gwiwa ta isa kano gidan haj salamatu ta zayyane mata ansamu yarinyar daza’a daura auren da ita.
Cikin farin ciki itama haj salamatu takira matar alhajin haj zeenat tafada mata ansamu.
Murna tayi sosai tareda cewa,
To shikenan yanxu zan aiko da kudi dubu dari biyar asiyawa yarinyar kaya,
Kuma akoya mata abubuwan daya kamata dan nan dataxo babu me lokacin koya mata yanda zatayi aiki da abu kuma inson tadanyi clean kafin nanda sati sbd daddynsa dayazo za’azo adaura auren aranar juma’a.
So banason yazo yaganta kaca kaca yace anfasa dan gskia baxan iya cigaba da wahalar nema masa masu kula dashi.
Kuma inason tazo nan kano gidanki ace kece uwarta dan banasan yasan ‘yar kauyece.
Kin gane zance kuwa.
Cikin rawar jiki tace,
Ai duk abunda kika fada kamar angamane haj.
Yauwa to sai anjimanku.
Tana datse kiran haj salamatu takalli jummai tace,
To jummai kindai ji abunda tace dan haka ya kike ganin xaayi da iyayen yarinyar?
Cikin washe baki jummai tace,
Ai haj ita yarinyar batada kowa sai matar mahaifinta data bada ita wato aminiyata sbd uwar yarinyar tarasu kuma batada dangi sbd buxuwace daga nijar ta tsallako wai iyayenta gobara ta cinyesu shinefa mijin aminiya ta ladingo ya aureta suka haifi yarinyar.
Bayan haihuwar yarinyar awuein haihuwa ta biyu ta rasu batareda ta haihun ba.
Bayan rasuwarta da shekara bakwai shima malam din yarasu sai yarinyar ta taso hannun aminiyata ladingo.
Kuma haj yarinyar shegen kyau ne da ita kamar jikar aljanu ga gashi kamar ka ara kayi kitso dashi,sannan duk kauyen nan ita kadai tayi karatu dan malam kafin yarasu dakansa yake kaita yadaukota.
Wata irin dariyar farin ciki haj salamt tayi tace,
Gaskia shiyasa nake yaba miki jummai dan kin iya xaben kwarai
Ta shekarar yarinyar nawa?kuma yaya sunanta?
Shekararta goma sha shida kuma sunanta NAZLI.
********
Karfe uku a kauyen takai tayi musu cikin gidan babah ladingo.
Kudi masu yawa kimanin dubu hamsin haj salamatu ta zubewa ladingo agabanta tace,
Wannan somin tabine na abani yarinyar naje da ita nafara shiryata kafin sati saiku samemu acan kano sai a daura auren acan suwuce da ita.
Idi ne yayi saurin waftar kudin yace,
Ai dama ko bakizo yau daukartaba mun shirya kaita gobe dan kawai ayi auren mu musamu kudin shanawa.
Buba yace,
Nidai kubani kasona na wannan daaka kawo natafi dan inada gurin xuwa kafin akawo masu yawar.
Ladingo kuwa kwalawa nazli dake tsakar gidan tana jibgar wankin ladingo hardana buba da idi kira tayi tana xuwa ta durkusa kofar dakin cikin nutsuwa da sanyin murya tace,
Gani.
Maza je kihada tsummanki birni xamu yanxu.
Rass gabanta ya buga dan tasan abunda suke niyar yi mata na aura mata mai tabin hankali dantayi jinyarsa akan kudi sbd taji firarsu lkcin datake fadawa su buba jia.
Kwana tayi tana kuka dan ta kara tabbatarda rashin gatanta amma bazata bijire mataba dan kota bijire din to ta tabbatarda korarta zasuyi a gidan data rasa gurin zuwa gwara tabi umarninsu ko kashe tane marar lfyar yayi ta huta da bakin ciki da azabar datake ciki.