VENNETE
SO DA BURI HAUSA NOVEL

SO DA BURI HAUSA NOVEL

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K’AI.

So da Buri
Free Book
01.

3 years ago…..
A cikin garin kano,a unguwar gandun albasa,cikin wani d’an matsakaicin gida…
kana ganin gidan kai tsaye za ka kirashi da na mai k’aramin k’arfi…daga waje k’ofa ce idan ka shigeta zaka biyo ta wani k’aramin soro,a soron akwai k’ofar d’aki mai band’aki a cikinsa kafin ka karaso cikin tsakar gidan wanda babu ko siminti rairayi ne a malale
wanda ya ke nan a share dukda yanada d’an girma amman hakan bai hana an share shi tsaf ba! Daga gefe guda akwai d’akuna guda hud’u a jere,daga chan ta wajen k’arshen tsakar gidan kuma akwai bayi wanda aka sakaye shi da k’ofar langa langa duk tayi tsatsa,sai kuma opposite d’inshi kitchen ne da ko k’ofar langa langar ma shi babu amman baka iya hango cikin kitchen d’in saboda duhunsa sakamokon bangon da duk yayi bak’i wuluk ta dalilin girki da itace.
Wata y’ar matashiyar budurwa da ba zata gaza shekaru 14 ba ce a tsakar gidan sai uban zufa takeyi,ta yi kneel down ta d’aga hannayenta sama,a kan tafukan hannayen nata kuwa wasu maka makan takalman ball ne d’aya a kowanne hannu…
D’an motsi ta yi wanda hakan ya sanya takalmin dake kan hannun hagun ta ya kusan fad’uwa,tsabar yadda duk ta rikice ta fita a hayyacin ta ga rana ga tsoron bulala ne ya sanya ba ta san lokacin da ta yar da na hannun daman nata tai saurin rik’e na hannun hagun nata ba…
ai kuwa bata k’arasa rik’ewa ba ya d’aga zabgegiyar bulalar dake rik’e a hannunsa ya zabga mata a kan hannayen nata,hakan yasanya ta k’arasa zubar da takalmin itama ta zub’e a nan k’asan saboda ba kad’an ba dukan ya shigeta.
Kamar jira yake yi kuwa ya rufeta ta duka! Babu ji babu gani…
ihu takeyi sosai tana kwala kiran
“Mama!, mama!!,mama!!!”
Mama da ke a d’aki,wadda tun farawar abun take jin su, ta runtse idanunta hawaye na gangaro mata tana adduan Allah ya kawo wanda zai ceci y’ar tata.
Kamar daga sama ya ji an fizge bulalar,juyowa yayi a fusace zai yi masifa suka had’a ido da wani kyakkyawan saurayi!mai manyan idanuwa..yanada cikar gashin kai da na gira da dogon hanci sannan bakinsa bai cika girma ba…skin colour d’insa chocolate ne me d’an haske da shek’i,dan ko kad’an ba za ka kira sa da Bak’i ba…..

cikin b’acin rai Junaidu yake kallon yayan nasa wanda suke mugun kama da juna bambancin kawai Junaidun ya fi yayan nasa kyau da manyan idanuwa da haske,sannan lips d’insa bai yi duhu ba kamar na yayan nasa da suka yi bak’ik’irin instead nasa shi light pink ne…..
tun cikin bacci yake jin hayaniyarsa a tsakar gida sama sama har ya kaiga farkawa ya watstsake yafara jiyosu sosai.
Kallon kwayar idanunsa Junaidun yayi…a zuciye ya yar da bulalar a k’asa kafin ya doka wani uban tsaki sannan yace”yanzu fisabillillahi ya Ja’afar abinda kake yi ya dace kenan??idan za ka hukunta Yarinyar nan ka dinga hukunta ta a lokutan da kake cikin haiyyacinka mana!!!
kalla fa idanunka!
ka je ka yi high!!kawai ka zo sai jubgar y’ar mutane ka ke yi so kake ka illatata??
kuma zan iya dafa Qur’ani akan cewa ba wani laifin kirki ta yi maka ba…a kan laifin da bai taka kara ya karya ba ka zo kanata dukanta haka!
me ta yi maka??”
Ya yi masa tambayar still yana tsare shi da manyan idanuwansa.

Mitsi misi ya Ja’afar d’in yayi da idanuwansa da suka yi jazir sannan ya yi baya kad’an ya d’an yi tangal tangal kamar zai fad’i sai kuma ya dawo daf da Junaidun ya tsaya ya zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa sannan ya zuba masa idanuwa kafin yace
“Kai,dan uwarka ni sa’anka ne?”

Shiru Junaidun ya yi yana kallon shi kafin a hankali ya d’an sassauta murya yace
“yi hak’uri,mai tai maka??”

Tsaki ya Ja’afar d’in ya yi sannan yace
“Akan gyaran d’akin da suke yi mini it da Jalila ne,Jalila ta yi mini bayanin ta ta wuce,
Ita wannan makirar sai ta tsaya shara wai Umma ce ta sakata sharar tsakar gida, abun haushin da na shiga d’akin nawa fa ko tsinke ba’a d’aga ba komai yana nan a yadda na barshi…”

shiru Junaidu yayi don in dai zai iya tunawa to jiya da shekaran jiya duk ya ganta tana gyaran d’akin ya Ja’afar,kuma a ka’idarsa shi ya Ja’afar d’in kwana bibbiyu sukeyi itada jalilan…to ya za a yi kuma yau ma yace still itace zatai mishi gyaran d’aki…
Juyawa yai yana kallon hanyar d’akunan gidan kmr yana neman wani abun kafin da k’arfi ya fara kwala kiran
“Jalila!Jalila!!Jalila!!!”
Ya jafar ne ya d’an tab’o hannunsa sannan yace masa
“kai ta tafi jarabawa fa”
juyawa Junaidu ya yi ya kalle sa kafin yace
“ya Ja’afar yau a ka’ida waye zai yi maka gyaran d’aki???”
shiru yayi kafin cikin maganarsa ta y’an shaye shaye yace
“Kagane ko!
a k’a’ida Jalila ce,to ita wannan makirar sharar da ta yi jiya da shekaran jiya duk basu fita ba kai gyaran ma kwata kwata bai yi ba shiyasa yau sai d’akin yayi kmr ba a tab’a gyarawa ba sannan Jalila jarabawa ta tafi,shine na shigo na ganta tana shara kuma Jalila ta sameni a waje ta ce mini ta rok’eta ta gyara d’akin ita ta makara amman ta zazzageta har da marin ta fa tayi!!!
ita dan uwarta a gidan ubanta ba a alfarma ne eh? Shine fa na shigo na sameta tana kwashe shara,ni kuma na d’auki alwashin sassama mata kamanni a yau d’innan tunda ta raina ni,ai ba Jalila ta zaga ba ni ta zaga tunda d’akina ne,kai marin ma ni ta mara tunda ai dai duk akan d’aki na ne”

Junaidu da ya fara fahimta makirci ne kawai Umma da Jalila suka had’a saboda sunga an kwana biyu ba a jibgi baiwar Allah n ba,sannan su Baba ya hana su dukanta shine suka biyo ta hannun ya Ja’afar tunda sunga shi in dai ya bugu to ba iya gane gaskiya da k’arya yake yiba sannan ko baya ga hakama daman chan shi ya tsani Yarinyar….

Sunkuyawar da ya ga ya Ja’afar nayi yana k’ok’arin sake d’auko bulalar ne ya dawo dashi daga nazarin daya tafi,da sauri ya rik’e hannun ya Ja’afar ya shiga lallab’asa akan ya yi hak’uri ya barta za a gyara masa d’akin nasa,amman fur ya k’i hak’ura…
k’arshe dai naira ashirin Junaidu ya d’auko daga aljihu ya basa tukunna ya hak’ura ya karb’a yana murmushi yace ta bar gyaran d’akin ma gobe sai ta yi,idan kuma Jalila bata da jarabawa goben sai ta bari jibi ta karb’i aikinta.
Juyawa ya Ja’afar ya yi yai hanyar fita daga gidan
shikuma Junaidu ya juyo yana kallonta anan a durk’ushe tana kuka tana ajiyar zuciya ta kifa kanta a k’asa….
A hankali ya sunkoyo kanta,kafad’unta ya kama duka biyu ya juyo da ita sannan ya sa hannunsa a hab’arta ya d’ago fuskarta.

Da sauri ta runtse idanuwanta da suka yi luhu luhu fuskarnan tayi jawur tsabar kukan dataci..shiruu ya yi yana kallon ta..tun daga kan lafiyayyan gashin gaban goshinta wanda suka kwanta sukai lub lub akan farar fatar ta,zuwa kan gashin girarta masu kyau da shape kamar ta yi cavn da madaidaitan idanuwanta, zuwa kan dogon hancinta wanda yai kmr M daga k’arshe amman ba sosaiba da dan mitsitsin bakinta….
Cikin seconds d’in da ba su fi uku ba ya yi mata wannan kallon..a hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya kira sunanta“HUDAN”saurin bud’e idanunta tayi ta kallesa!
kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai ta yi saurin ture hannunsa daga jikinta ta tashi da gudu tai hanyar d’akin Mama.

Shiru ya d’an yi,chan kuma a hankali ya mik’e tsaye, ya juya da niyyar komawa d’akinsa.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected