Dabi'ar Zuciya 51
51
D/Z
Tana sake matsawa kanta da tambayar tana sake jin maqogoronta yana bushewa,wanda ya sake tabbatar mata da cewa ruwa take da buqatar sha,cusa hoton ta kuma yi qasan filon,ta miqe jikinta na rawa a hankali cikin sanda ta doshi falon.
A hankali ya murda qofar falon ya turata kana ya shigo,jikinsa ko ina yana fidda zufa saboda mafarkin da yayi,babu abinda yake da buqatar sha illa ruwa,sanda ya niyyaci shan ruwan,saiya taras babu komai a fridge din sashen sai drinks,wadanda ba zasu kashe qishirwar da yakeji ba sam.
Idanu ya zuba mata daga nesa cikin mamakin ganinta a dai dai wannan lokacin,duk da cewa babu wadatar haske sosai a falon amma ya ganeta sosai,baqin gashinta daya ware ya sauka a bayanta yanata qyalli,ci gaba yayi da takowa a hankali yana nannade hannayen rigarsa ko zaiji raguwar zufar dake sauka a jikinsa.
Da hanzari take zuba ruwan cikin cup tana daga tsaye a bakin fridge din bayan ta budeshi,alamun takun sawayen da taji ya sanyata firgita sosai,hakan ya sabbaba mata tsoron daya tilasta ruwan da robar faduwa gaba daya a qasa ruwan ya soma malalala a qafafunta,sannan ta waiwayo tana duban bayanta.
Fararen idanunta sun fito tarwai wadanda suka cika da tsoro,tsoron daya bashi mamaki,saiya qarasa gabanta a nutse,ya sunkuya ya dauke ruwan kana ya dago yana duban tsakiyar idanunta,fuskarta tayi wani fayau, fresh babu komai saman fatarta,gab suke da juna har suna iya musayar numfashi,still yana kallonta a tausashe muryarsa can qasa maqoshinsa yace
“Wannan tsoron fa?” Qas tayi da kanta tana son dai daita kanta,tana kuma jin nauyin yadda yake tsaye gab da ita,ta fahimci kuma idanunsa na yawo ne a kanta,har zuwa qirjinta da maballan rigarta guda biyu na sama suke a bude,hakan ya bawa qirjin nata damar fitowa kadan ta saman
Ganin ta kasa cewa komai saiya dauki wani cup din daga saman fridge din,a hankali taji ya kama hannayenta,ya sanya mata cup din a hannu days,daya hannun kuma robar ruwan bayan ya budeta,dora hannayenshi shima yayi saman nata hannayen,ya tayata riqe cup din da robar ruwan,suka fara tsiyaya ruwan a tare,kowannensu idanunshi na ka robar da cup din,saidai kowa da abinda zuciyarsa ke saqa masa.
Sai daya cika shi da ruwan sannan ya tayata daga cup din zuwan bakinta ta hanyar ci gaba da dafe bayan hannunshi cikin tafi hannunta,a hankali take aika ruwan daga bakinta zuwa maqogoranta cikin wani yanayi,sanyin ruwan na kai mata ko ina,jikinta na mutuwa saboda wanzuwarsa a wajen.
Rabi tasha tadan janye shi daga bakinta,ta tsammaci zai sake mata hannu ne amma sai taga ya sake sauke hannun nata tare da sake zuba ruwan ya kuma cika cup din,wannan karon bakinsa yakai ruwan,ya fara sha shima a hankali, Adams apple dinsa na sama da qasa,yayin da idanunsa masu haske da girma ke zube cikin nashi,qas tayi da kanta,tana ji ya gama shan ruwan,ya zare hannunsa cup din da kuma gorar ruwan gaba daya ya ajjiye.
Bata ankara ba taji ya kama tsintsiyar hannunta,haka kawai.mafarkin ya birkita shi,yaji yana da buqatar wani abu da zai daidaira bugun numfashinsa,yana buqatar wanda zaiji yadda zuciyarsa take bugawa,sai ya sake taku sosai ya hade jikinsa da nata,hakan bai masa ba,sai daya dora qafafunta saman nashi,hakan ya qara mata tsaho,sai taji ya zagaya hannayensa zuwa bayanta ya rungumeta gaba daya cikin jikinsa.
Qamshin turarensa laushin fatarsa da dumin dake fita daga jikinsa da kuma ba zatar da yayi mata yaso tafiya da numfashinta gaba daya,bugun zuciyarsu ya cakuda waje daya,kowanne a cikinsu yana iya jin yadda zuciyar dan uwansa ke bugawa da wani irin gudu.
Numfashi mau nauyi ya dunga saukewa ajere,a hankali a hankali har zuwa wani lokaci,cikin jikinta ta karan kanta ta dinga jin wata nutsuwa,kamar yadda shima nutsuwar ta dinga ratsashi ta kowanne sassa na jikinsa,nutsuwar da bai taba jin kamarta ba duk sanda yayi irin wannan mafarkin
“Me ya tsorataki?” Ya kuma jefa mata tambayar cikin wata murya dako a falon kake baka isa kaji abinda ya fada ba,saboda wani feelings dake tsarashi,yana iya jin tudun komai na jikinta a jikinsa
“Mafarki nayi”
“Na umma?,ko na bilal?” Tambayar data sosa mata wani tabkeken miki dake danqare a zuciyarta,wanda dare da rana taketa qoqarin ganin ta sayashi,kiran sunan da yayi ya shiga sosai cikin kunnenta,ya kuma motsa zuciyarta,duk da mafarkinta bashi da alaqa da umman,amma sai taji a take hankalinta ya karkata zuwa gareta,hakan ya bawa hawaye damar taruwa cikin idanunta,cikin qanqanin lokaci kuma suka fara sauka saman fuskarta.
Batasan yadda akayi ya fahimci ta soma kuka ba,saidai hannunsa data ji saman fuskarta yana share mata,batasan cewa yaji sauyin fitar numfashinta da bugun zuciyarta ba,yana sharemata yana runtse idonsa,akwai wani abu daya sanyashi ya zama qwararre wajen gane fitar hawaye ba tare daya kalli fuska ba matuqar a jikin mutum yake,hawayen AMMAnsa,daya daga cikin abinda yasa ya tsani kukan mace,abu guda daya dake sanya rauninsa bayyana.
Yana da burin kaita gida,a yadda aqarta take da yan uwanta da mahaifiyarta yasan cewa tayi namijin qoqarin zama har zuwa wannan lokacin bataga kowa nata ba,bayan an daukota a lokacin da take tsaka da jinyar rashin dan uwanta,to amma a wanne matsayi take?,wacce amsa ce gareshi na matsayinta a wajensa?,MATA KO QANWA?.
**********Tunda drivern ya daukota takejin wani farinciki cikin ranta,kammaluwar jarabawarta cike da alamun sa’a da nasara,nan bada wani jimawa ba zata tsinci kanta a ajin qarshe na secondary,abinda bata taba mafarkin kasancewarsa kaf tsayin rayuwarta,tafi mafarkin gata can gidan nasuru,gatacan a matsayin matar nasurun,sai gata yau cikin wata mota da take hange a baya daga can qololuwar nesa,bata taba sha’awar hawanta bama saboda tasan ba zata hau ba.
Abu daya ne a yazu yake dan motsa mata,daga sanda ta fara karatun litattafan nan ta gane meye aure?,meye ma’ana da manufar aure?,tun daga ranar daya fara rungumeta cikin jikinsa yabar mata wani abu,ya kuma dauki wani abu daga zuciyarta yayi gaba dashi,to amma ta ina zata fara yaqi da qoqarin karbarwa kanta matsayinta?,wannan shine matsalar da takeji lokaci zuwa lokaci tana motsi a zuciyarta.
Yana tsaida motar ta fito zuwa cikin gida,tana da masaniyar gobe zasu wuce azare kamar yadda ya shaida mata cikin wancan daren data yi masa kyakkyawar ajiya a zuciyarta,don haka tana son hada komai nata aka tsari,ta ciri kayan da take da buqata cikin siyayyar da yayi mata wancar ranar.
Ta saba duk sanda zata shiga waje tayi sallama koda babu kowa,yauma sallamar tayi,duk da tasan mawuyacine ta samu masu aikin cikin falon.
Ga mamakinta sai taji an amsa mata,abinda ya daure mata kai kenan,ta maida dubanta ga wajen da taji an amsata din,sai suka hada ido da mubina tana sakar mata murmushi
“Sonshi nake da gaske jawahir,ko zaki taimaka min?” Kalaman mubina a ganinta da ita na qarshe ya dawo mata,hakanan taji yawan farashin fara’ar da takeson maida mata ya ragu,yaqe taji tana mata,amma duk da haka saita dakata suka gaisa kamar yadda suka saba
“Hajiyan suna azare gaba daya” kaltum ta gayawa mubina tana miqewa bayan ta dauki takardunta
“Eh na sani,ai har mama itama tana can,tare suka tafi,kinsan mama aisha kishiyar yayata ce,ni kuma a hannun yayar tawa nake” dan dubanta kaltum tayi ta gyada kai kawai



