VENNETE
Ajiya A Duhu BOOK 1 Na Billyn Abdul

Ajiya a Duhu Na Billyn Abdul Page 43

????4??3??

______________

……..Shima da gaba ?aya kansa ke juya masa, al’amura masu nauyi da suke lullu?e a zuciyarsa na sake zaburowa, a hankali ya saki mata yatsan yana rumtse idanunsa da ?arfi. Wani irin ratsa zuciyarsa da ?argo kukan nata yake yi. Sai dai bazaka ta?a fahimtar hakan a fuskarsa ba idan ka cire idanunsa da sukai matu?ar ka?awa. Tawani fannin kuma zai iya cewa kukan yake so tayi, dan zai rage mata nauyin zuciya dana zafinsa da yasan take ji. Fin mintuna biyar suna a haka kafin ya mi?e a wajen, veil ?inta dake yashe a ?asa ya ?auka, ?amshinsa na sake ratsa hancinsa, kanta ya ?an rankwafo ya yafa mata veil ?in a saman kanta batare da yace komai ba ya wuce ainahin office chair ?insa, batare daya zauna ba ya ciri ?aramar pepper yay ?an rubutu, sai kuma ya ?auka shopping bag ?arama dake a saman desk ?in. Rigar suit ?insa dake a hanger ya cire itama tare da tattare wayoyinsa. Gabanta yaje ya ajiye shopping bag ?in nan da shot note ?in da yayi batare da yace mata komai ba ya nufi ?ofa. Sai da ya kai hannu zai danna ma?allin bu?e ?ofar batare daya jiyo ba ya furta, “Ki tabbatar kin shiga restroom kin gyara fuskarki”. Daga haka yay ficewarsa cike da takunsa na nutsuwa da ?asaita.
Da wani irin sauri Huznah dake zaune cikin takaici da damuwa ta mi?e. Hakama AS ?insa daya san wannan ba lokacin fitowarsa bane mi?ewa yayi. Baiko kalla inda Huznah take ba, sai Assistant ?in nasa ya kalla. “Zanje airport ?aukar su Mamy. Take care of everything”.
“Okay Sir ALLAH ya tsare”.
Kansa kawai ya jinjina masa yay wucewarsa. Har kuma yayi taku uku sai ya tsaya cak jin ana binsa a baya. ?an waiwayowa yay tamkar mai jin ciwon wuya ya zuba mata ?asaitattun idanunsa da gaba ?aya suka sauya kala da launinsu. Dan farin gilashin fuskarsa bai zam ya ?oye komai ba daga garesu. Kasa jure kallonsa Huznah tayi, sai ma jikinta dake neman fara rawa. Amma tai ?o?arin ri?e kanta da tsiya, sai dai muryarta na ?an rawa ta ce, “A zahiri bakayi kama da mai wula?anta mutane ba, why ni nake neman zama ?as?antacciya a yayin zuwa ganinka? Please ka duba ni, ka bani dama muyi magana dan ALLAH”..
Karo na farko ya lumshe idanun nasa da bu?esu. Hakan tuni ya zame masa ?abi’a musamman a yayin son yin magana. Cikin cool voice ?insa mai fidda ?aramin amo da kasancewa ?asa-?asa tamkar ba namiji ba ya furta, “Mi kike bu?ata?”.
“Kai! Kai nake bu?ata AA. Ina son yin magana da kai Please”.
Lips ?insa ya ?an ciza sai kuma ya janye idanunsa daga kanta. ?o?arin wucewa yay batare daya tanka mata ba yana kallon Designer agogonsa da sai ka gama kara?ewa baka samo sa ba, dan shi duk wani agogon sakawarsa ana masa shi a companynsa kuma shi ka?ai, sai idan wani ne yace yana so ayi irinsa daga nan shi kuma yabar saka Design ?in sai kuma wani. Da sauri ta bi bayansa suka shige cikin elevator daya bu?e. Anan ?in ma dubansa tayi da son yin magana sai dai ta gagara sakamakon ganin fuskarsa babu alamun wasa. A haka suka fito tanata ?o?arin ganin ta daidaita tafiyarsu. Aiko hakan yaja hankalin ma’aikatansa matu?a. Dan duk inda suka gitta idanu yuuu akansu. Masu ?us-?us nayi masu jinjina kai nayi. Yayinda zukatan mafi yawansu suka sake yarda da eh lallai da gaske itace boss ?in nasu zai aura kuwa. Dan abune da basu ta?a gani ba boss da mace kamar haka. Ina dai ka gansu da wata to lallai abokiyar kasuwanci ce, dan shi hatta a cikin family baya kula ?ar kowa, in dai kina sama da shi zai yi respecting ?inki. Suna gama ficewa sai ?us-?us ?in ya ?aru, yayinda wasu suka maida hankalinsu ga hotunan dake akowacce kusurwa ta Company ?in na mace mai ni?ab da hijjab. Wadda da yawansu sun gagara tantance hoto ne ko zane ne. So suke su tantance ko wadda suka fita taren ce. Sai dai sam babu wani alamu ko kamanni daya nuna hakan. Dan baka isa tantance ainahin wacece a hoton ba tako ina….

Yana fitowa drivern sa dake can wajen securitys suna hira ya mi?e da sauri. Sai dai koda ya iso garesa sai ya mi?a masa hannu murya ?asa-?asa yana fa?in, “Don’t worry, give me the key, I want to drive myself”.
Babu musu driver ya rissina ya mi?a masa key ?in. Sai kuma ya bu?e masa motar da sauri.
“Ka sama mata taxi”.
Ya sake fa?a yana ?o?arin shiga motar, kallon Huznah driver yayi, sai kuma ya amsa da sauri cike da girmamawa. Huznah kam dake tsaye kamar zata saki kuka kallonsu kawai takeyi, tana ji tana gani a gabanta ya birka motarsa ya fice cike da ?warewar iya tu?i na nutsuwa da cikar kamala….
Lallai yau taga madarar wula?anci da babu ko gauraye a cikinta, wato mutumin nan cikin ruwan sanyi yake tsula maka tsiya babu hayaniya babu hargowa ko yawan magana. Dole ne ta koma Kaduna su sake shiri kam, amma zata fara bari ta ha?u da mahaifiyar tasa dan taga yaya nata takun itama, hakan zai sa susan irin shirin da zasu musu su duka.. da wannan tunanin ta ballama drivern harara ta fice da ?afarta…..

???

Maanal ta jima a wajen tana kuka, sai da ta fara jin zuciyarta na mata nauyi a cikin ?irjinta kafin ta ?ago kanta da ?yar, office chair ?insa ta zubama ido sosai tamkar shine a wajen, har yanzu hawayen na cigaba da ziraro mata. Tunanin dake neman tasiri a ranta ta ture da ?arfin tsiya tare da mi?ewa ta nufi restroom ?in kamar yanda ya fa?a, dan itama tasan ko giyar wake tasha bazata fita a haka ba ai. Sosai restroom ?in ya ha?u, gashi ?al-?al sai ?amshi yake zubawa kamar ba toilet ba. Ta jima tsaye tana kallon kanta a mirror ?in bayin tana hawaye kafin ta wanke fuskar tata ta fito bayan ta gogeta da ?aramin towel fari tas dake a bayin. Harta nufi ?ofa ta koma da baya, shopping bag ?in daya ajiye a gabanta ta ?auka kasancewar ganin abinda ya rubuta a takardar daya ajiye a sama, sai kuma ta maida ta ajiye. Nan ma ta juya zata tafi idonta suka sake sauka a novel ?in nan nasa. Baki ta tura gaba sannan ta ?auka shi dai ta ficewarta..
Koda ta fito bata kula kowa ba a wajen ta shiga ha?a ?an tarkacen kayanta, kallonta kawai su Zaharadeen suke cike da gulma. Sai Yaqub ne daya mi?e tsaye yana kallonta tun shigowarta ya furta, “Sister Maanal are you okay?”.
Kanta kawai ta jinjina masa batare da dace komai ba. Kafin ya samu damar sake magana ta kwashi kayanta zata wuce. Cikin sauri ya bita yana fa?in, “Ina zaki je?”.
“Gida”.
Ta bashi amsa a takaice. Cikin tashin hankali ya bu?e baki zai sake magana a fusace ta ce, “Please Yakub! Nace ba komai. Leave me alone”. Daga haka tai gaba abinta fuuuu. Shiru yay kawai yana kallonta, gaba ?aya fuskarsa ta nuna tsantsar damuwa da tashin hankali. Shin mike faruwa? Mi akai mata? A office na CEO fa aka kirata! Miya faru acan ?in?”. Rashin mai bashi amsa ya sashi juyawa jiki a sanyaye ya koma ciki. Sai kuma ya sake tadda wani abun takaicin, su Zaharadeen ne suke bu?e babin gulmar Maanal ?in. Wai maybe ta fa?ama CEO tana sonshi ne shine ya koreta a aiki, sai ALLAH ya ?ara suke mata da kiranta mai girman kai da fa?in rai. Takaicinsu ya saka Yakub ko kulasu baiyi ba……

______________?

“Alhamdullahi ranka ya da?e aiki ya kammala. Wannan shine cikakken bayani akan ainahin mahaifinta dama zuri’arta baki ?aya”. Rabilu ne mai maganar fuskarsa washe da murmushi yana mi?ama Sen.. Bukar bayani akan Maanaal daya binciko kamar yanda ya bu?ata. Sosai fuskar sa ta washe da murmushi. Dan shi ka?ai yasan yanda yake azabtuwa da so da ?aunar yarinyar nan data mamaye dukkan illahirin jinin jikinsa. Yanzu haka yau har gaban Mawaad company yasa drivern sa yaje ya faka mota har Maanal ta iso. Fitarta a motar Shahidah da dukkan abinda ya faru a wajen kan idonsa ne. Ji ya dingayi kamar ya sato ta saboda yanda tai matu?ar ?yawu a cikin kwalliyar ta yau.
Rabilu ya cigaba da fa?in, “Su ?in asalin su ?an jihar Kebbi ne, ?aramar hukumar suru a wani ?auye da ake kira giro. Mahaifin nata ?an sanda ne, dan har ya kai matakin DPO amma yanzu ya ajiye aiki sakamakon doguwar jiyyar da yayi. Ita kuma mahaifiyarta bata tare da shi a yanzu, dan sun rabu shekaru kusan takwas kenan, a yanzu haka tana auren wani Alhaji Usman Chalawa ne anan kaduna, yana ri?e da su kuma tamkar mahaifin nasu koma fiye da shi.”
Cike da zumu?i ya furta, “Rabilu kaje wajen Oler ka amshi key ?in motar ka sabuwa dal, zuwa dare zan nemeka idan na koma gida”.
Cikin matu?ar washe baki Rabilu ya shiga godiya harda ?an zamowa daga visitors chair da yake zaune ta office ?in Sen.. Aifa cike da zumu?i ya bar office ?in. Kai tsaye gidan Sen.. Bukar ya nufa domin amsar al?awarinsa dan yasan baya magana biyu akan alkawari irin wannan daya shafi mata. Zai iya cewa dukan matan alhajin idan ka cire uwargidansa duk shine ya masa bincike akan sauran biyun. Ya kuma taka rawar gani akan samuwar auren fiye da zaton mai zato. Sai dai ya fahimci kamar Senator ?in yafi sakin ku?i da ?oki akan wannan ?ar shilar. To ?ar shila mana. Akan matan Alhaji ai manaal ?ar shila ce. Dan ko jikansa na farko ya girmi Maanal sosai. Aiko ina sha ALLAHU zai yi iya ?o?arinsa dan ganin tako ina Alhaji bai samu matsala ba, ya kuma mallaki yarinyar da gaggawa. Dan yasan irin wannan kari?ujin arzi?in da ire-irensa sunta zuwa kenan. Zama kuwa ai ba nashi bane ba….

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected