VENNETE
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi'ar Zuciya 21

A daren ranar suna zaune a tsakar gida saboda yanayin zafi,ummansu na qofar dakinta,haka babansu na nashi qofar dakin qarqashun rumafarsa ta bunu,yaci ya qoshi da abincin da bashi ya nemo ba,yana zaune kuma ya kunna radio gamida kasa idanunsa a tsakaninsu,yana neman wani dan qaramin dalilin da zai sanyashi ya bude faifan bala’insa,dole ce ta sanya kaltum itama zama qofar nata dakin,dukkaninsu ba’a sake suke ba,saboda zamansa a tsakaninsu babu abinda yake haifarwa sai da mara idanu,da zarar ya gansu a zaune tare zaice sun hada kai suna munafuncinsa ita da ‘yarsa,don haka matuqar yana nan din sun gwammace su raba wajen zama.

Addu’a kaltum take cikin ranta kada Allah ya shigo da bilalu,ta tabbatar idan har ya shigo din sai baban nasu ya samu abun fada.

Sallamar munzali ce ta ratso tsakar gidan,ya shigo hannunsa dauke da buhu,ummansu ta amsa masa tana miqewa ta zauna sosai daga jingina bayanta da tayi.

Fuska babu fara’a ya gaidata ta amsa masa cikin kulawa,idan da sabo ta saba da wannan halayya da dabi’a tasu,kai bakace itace ta rainesu ba a sanda mahaifiyarsu ta fita tabar gidan ba,sam babu wani halacci kara ko kunya a tsakaninsu,duk da cewa da wayonsu ta samesu,amma duk sauran hidima da yaro ke buqata kafin zamowarsa cikakken mutum ita ta dauki gabarar yi musu ita har zuwa sanda sukayi aure.

Ta gaban kaltum ya wuce,wadda take ta gaidashi yayi watsin tsiya da gaisuwarta,saima harara daya balla mata,ya qarasa gaban baban nasu,yaja kujerar mata ta tsuguno ya zauna akai ya soma gaidashi
“Ya akayi munxali?” Baice komai ba sai zazzage kayan dake cikin buhun da yayi,ya soma ware wasu gefe wasu kuma yana miqawa baban.

Sai daya ware jallabiya kala hudu,takalmi da agogo,da hular tashi ka fiya naci da kudi ‘yan dubu dubu guda hudu ya miqawa baban
“Gashinan inji innarmu tace a baka”
“Allahu akbar kabiran,hajjaju mutan saudiyya,ta dawo ne?” Ya fadi cikin wata madaukakiyar fara’a data baiwa kaltum mamaki,ta kuma sanyata kallon ummansu,saboda ita dai bata saba ganin hakan ba,saidai suna hada idanu ta dauke kanta,saima ta janyo wani dan abun hannu na duwatsu me kyau nata daya katse dazu taci gaba da gyarashi,kanta yana kallon qasa
“Bata dawo ba,ta dai yo aikene,ni da muzammilu da sani da muka ce mata muna son jari” ya fada yana jin haushin baban nasu can qasan ransa,saboda har yanzu bai manta yadda babar tasu tasha wahala hannunsa ba kafin ya saketa ta tsallake zuwa saudiyya neman kudi
“Ma sha Allahu,kai Allah ya saka da alheri”
“Wata shekarar take saka ran zuwa,zata tafi damu muyo umara”
“To madalla alhaji munzali,ince dai baku manta dani ba?” Sai daya miqe tsaye sannan ya bashi amsa,saboda ya soma gajiya da yadda yake fidda son zuciyarsa quru quru,baya ma tuna abinda shi ya aikata a baya
“Idan Allah ya kiraka kaima sai kaga ta biya maka ai”
“To Allah amin” ya fada yana jujjuya kayan hannunsa,wanda ba’a taba masa kyauta irin haka ba tunda yake.

Har munzalin ya gota kaltum saiya dawo da baya
“Ke kattume” ya kirayeta sa qarfi
“Na’am yaya” ta amsa tana daga kai da hanzari
“Rannan nazo nemanki ban sameki ba,bansan me kika yiwa fiddau ba,nayi nayi ta gayamin taqi,wallahi ki kuka da kanki duk randa ta shaidan naji rashin mutunci kikayi mata”
“Kaga yaya fa ba…..”
“Rufemin baki!” Ya dakata mata tsawa,sannan ya shura takalmansa yayi gaba abinsa,saita bishi da kallo,a lokacinne kuma baban nasu ya dira nasa
“Wani diban albarkar hala kika yi musu?,ke wai me yasa kike da daukar magana kamar ‘yar Allah ya bani?,to wallahi indai kuwa taba munzali ko ahalinsu kikayi nima ba qyaleki zanyi ba,shashasha mara lissafi,shi yasa qanwarki ta tafi dakin miji ta barki ke gododo a zaune” shuru tayi harya kammala jafa’insa ya koma kan murnar kayansa,yanata yada magana da habaici,kanzail ummansu batace masa ba,sai kaltum ta fara tattare shimfidarta jin ya koma kan umman tasu daya fuskanci bata da niyyar kulashi
“Wato saboda tsabaragen baqin hali da kishin banza,kin kasa yiwa uwar yaron nan godiya….a gabanki ya kawo kayan nan,kuma koda ya tafi ma kin gaza daga kai ki tayani murna” a hankali ta daga kanta ta dubeshi sau daya
“Allah ya sanya alheri,a kashe lafiya” daga haka ta maida haka ta maida kanta taci gaba da abinda takeyi,saidai duk da haka shi hakan baiyi masa ba,haka yaci gaba da qananun mitocinsa kafin ya tattara ya shige daki yana yiwa kayan boyo na musamman,tare da qiyasta sanda zai sanyasu.

*********Jawahir najwa da jauhar ne tsaye a farfajiyar gidan,sai saraki dake tsaye gefe guda sanye da wasu qananun kaya da sukayi masifar fitar da kyau da kuma kwarjininsa,hannunayensa gaba daya zube cikin aljihun wandonsa,ya zubawa motarsa a aka gama wankewa ana gogeta idanu.

Fita zasuyi zuwa gidan hajiya qarama,wanda mummy ce ta shirya fitar,da sunan yaje ya kaisu su gaidata,a gaban idanun daddy ne,don haka bashi data cewa,bama wannan ce damuwarsa ba,yadda yaji suna tsiro da zancan zuwa azare,abinda sam sam yakejin bada shi xa’ayi ba,zuwansa azare tare da jauhar kamar ya bada lasisin dake nuna amincewarsa da aurenta,saboda tafiyar zata zamana tamkar tattakine na nuna jauhar ga dangin mahaifinsa.

Horn ake saki a bakin gate din,wanda hakan yaja hankalin samir,saboda yadda ake danne horn din babu qaqqautawa,hannuwansa ya sauke yana duban gate din sanda malam salahu ke rawar jikin budewa,kauda kansa yayi sanda motar ta shigo,ba kowa bane sai fawwaz,don haka ya taka zuwa gaba,ya bude motar kafin ya qarasa gabanta,ta bada wata ‘yar qata ta security,hakan yaja hankalinsu jawahir suka matso suma sannan ya saka key ya bude.

Dakatawa yayi daga qoqarin shigar da yakeyi saboda jiyo muryar fawwaz cikin fada yana yiwa malam salahu fada,wanda a qalla ya kusa haifarshi idanma bai haifeshin ba,qafarsa daya zura cikin motar ya cire,yaja rigarsa qasa ya gyara ta sanna ya fara takawa zuwa inda suke tsayen
“……..dukka alamu sun nuna bakasan aikinka ba” kalmar qarshe da samir din yaji daga bakin fawwaz kenan,wanda ke tsaye gab da malam salahu,kamar me shirin gabza masa mari
“Baba” samir ya kira malam salahu cikin nutsuwa,waiwayowa yayi cike da girmamawa
“Na’am dana”
“Lafiya….meya faru?” Fuskar cike da alhini da alamun rashin jin dadin cin fuskar da fawwaz din ke yawan yi musu matuqar zai tako qafarsa cikin gidan ya shaida masa cewa,yana bayan gida yana fitsari ne sanda ya iso,kuma yana fitowa yazo ya bude masa,ya masa bayanin dalilin jinkirin nasa amma yace bai yarda ba.

Idanunsa samir ya dauke daga kan malam salahu zuwa kan fawwaz,wanda duba daya zaka masa ka hangi yanda ransa ya sosu dajin abinda fawwaz din yakeyi,idan bai manta ba shi akaran kansa wannan ba shine karon farko da fawwaz din ya aikata haka a gabansa ba,amma a yau din yakai maqurar da bazai iya qyaleshi ba
“Kayi haquri baba don Allah kaji?” Cewar samir da sassanyar muryarsa bayan ya maida.ganinsa ga malam salahu
“Babu komai dana,ba komai” ya amsa masa cikin nuna girmamawa yana cakude tafukan hannayensa waje daya,sannan ya motsa ya bar wajen,samir ya bishi da kallo cike da tausasawa.

“Ji mana” samir ya fadi sanda fawwaz ya gyara kwalar rigarsa yana shirin barin wajen zuwa cikin gida,dakatawa yayi fuskarsa a daure ya waiwayo yana duban samir din
“Kayi qoqari wannan ya zama karo na qarshe da irin haka zata sake faruwa takaninka da duk wani ma’aikaci na gidan nan,don mu muna girmamasu…..saboda daraja ta fifiko da tazarar shekaru da Allah ya bamu tsakaninmu dasu,banason na sake ji ko na sake gani,nan gidan akwai ɗa’a” ya qarashe maganar yana gyada kanshi,sannan ya taka zuwa wajen motarsa ya barshi a nan,cikin zuciyarsa yana jin zafi,saboda ya fuskanci maganarsa ta qarshe tamkar baqar magana yake gaya masa,gugar xana yake masa kenan?,qwafa yaja cikin ranshi yana fadin
“Idan kere na yawo,zabo na yawo…..” Yasa kai zuwa cikin gidan da sassarfa,samir dake qoqarin tada motar ya bishi da kallo,abubuwa masu tarin yawa suna kaiwa da kawowa cikin qwaqwalwarsa.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected