Dabi'ar Zuciya 11
11
A mararrabar hanya suka rabu da nasirun,shi yabi hanyar da zata sadashi da gonakinsu,ita kuma tabi hanyar da zata kaita gidan matar da zata kaiwa kudin kabewa.
Tun daga nesa ta hangi sashen da tsohuwar makarantarsu take da al’umma a tsaitsaye,wasu manyan lafiyayyun kyawawan motoci guda uku fake a gefe,saita dauke kanta ta wuce zuwa gidan mari mai Saida kayan miya,ta shiga suka gama magana ta bata kudin ta fito.
Idanunta sake sauka yayi ta gefan makarantar,har yanzun mutane ne a tsaye a wajen suna zagaya makarantar,zuwa yanzu jama’ar dake cika wajen sun dadu,don an samu dadin ‘yan kallo,wadanda kallon motocin dake wajen da kuma aikin da taga kamar ana danyi ya kawo,cikin masu kallon kuwa harda manya.
Baki ta tabe tana dannjan tsaki,mutane suna bata mamaki,komai qanqantar abu abun kallo ne a wajensu
“yaya”taji kamar muryar bilal tana qwalla mata kira,saita dakata da tafiyar sannan ya waiwaya.
Bilal dinne kuwa,ta zuba masa idanu tana jiran qarasowarshi,kamar ko yaushe fututu dashi,da wahala kaga bila din tsatsaf dashi,idan ba ranaku irin na juma’a ba ko kuma ranakun idi, saboda koda yaushe cikin aikin wahala da neman kudi yake.
“kai kuma me kakeyi a nan?,Allah dai yasa ba fada ake ba”dariya ya danyi
“ni bana tsokana ai yaya saidai a tsokaneni….ba fada ake ba,wasu ne wai suka turo a sake ginin makarantar me tafasa,sannan a gina mata masallaci babba nayin sallah,shine na maqale a wajen ko Alla zaisa a sakani cikin masu aikin ginin”tsaiwa tayi tana kallonsa sosai,kamar kowanne lokaci shi.bilal din tunaninsa daban,ba kasafai yake hango wani abu ba,saidai shi a hango masa
“kai wato samun aiki ne ya dameka,bama ka tunanin shiga sahun daliban da za’a dauka ida an gama gyaran makarantar ko?”dariya ya danyi
“karatu fa yaya?….tabdi ba yanzu ba”
“au bazakayi ba kenan”sai yayi murmushi
“zanyi amma ba yanzu ba”
“Allah ya shiryeka”ta fada tana yin gaba,ya biyota a baya yana ci gaba da bata labarin irin mutanen da sukazo wajen,’yan birni sosai ‘yan gayu,kowa sai kallonsu yake,harda cewa
“yaya motarsu kamar madubi,idan ka tsaya a gabanta Allah har kanka kana iya gani,da guduwa fa aka dinga yi,kowa yana tsoron kada ya bace”murmushi ta saki kawai
“naji,kaidai ka kula,ba ruwanka da kowa,ka kiyaye”
“ni dama yaya meye nawa?,kawai aiki nake nema”shiya rakata har gida suna hira,sannan ya zauna yaci abinci ya sake ficewa.
Da yammacin ranar aka kama habiba,kuma shima abun ya qayatar kamar dai jiyan,komai a tsare akayi lafiya aka gama lafiya,saidai rashin ganin mutum biyu ya baiwa kaltum mamaki qwarai da gaske inna da kuma suwaiba,babu su babau labarinsu har akayi aka gama.
Washegari akayi wuni da daurin aure,wata washegaein kuma aka dauki habiba zuwa gidanta,ranar sun sha kuka dukkaninsu,sai kaltum ta dinga jin kadaici sosai,ta dinga jinta wani iri tun a ranar,ta tabbatar wani sabon zaman ke sake fuskantota,wanda batasan da wacce fuska zaizo mata ba,ta dawo gida jiki a sanyaye bayan sun baro habiba da tsohuwar da zata zauna mata kafin gobe suje ayi mata budar kai.
Washegari da safe suna tsakar gida suna karyawa saiga sallamar inna,abinda ya bawa dukkaninsu mamaki, tare da tambayar kansu dalilin zuwan innar,tunda dai har akaci aka cinye innar bata koda rabo dangar gidan ba,hakanan sisinta da sunan gudunmawa ga bikin jikarta bai ratsa hannun umman ba,sai yau a rana ta qarshe da za’a gama komai kuma sai innar tazo?.
Daga umma altine,yakumbo indo kowa fuskarsa cike da mamaki take,hakanan babu watq cikakkiyar fara’a jin dadi ko walwala suka tarbeta,saimw umman ce daya yunqura cikinnzallae farinciki ta shimfida mata sabuwar tabarma wadda ta habiban ce da aka manta ba’a tafi da ita ba,yau za’a tafi da ita,jikin umma na rawa tasa aka zuba mata kunu da qosai da sukayi aka aje ma innar,sannan ta tsugunna gefanta tana gaidata,bayan umma altine da yakumbo indo sun gaidata,sai kaltum wadda ke zaune gefe,ta zubawa sarautar Allah idanu,ta kasa ta tsare taqi tashi,don itama tana son taji dame innar taxo.
Badai tace komai ba har aka gama gaisawar,hakanan bataqi jan kwanon kunu da qosai ba ta fara kaiwa baka,har zuwa lokacin da masu tafiya suka fara da taruwa.
Tsaf kaltum itama ta shirya cikin daya daga cikin atamfofin da nasuru ya siya mata,wadda ta saka shekaran jiya,yau din sai tayi maimaice,zata shiha dakinsu ta debo ragowar kayan sawar habiba taji innar na cewa
“Wannan saqar tabarmar tayi kyau….irinta naketa nema zan siya ba’a samomin ba”tasan halin innar sarai,don haka saota fasa shiga dakin,ta waiwayo tana cewa
“Kuma gata na ko ina a kasuwar darimi,idan kina so ajjiye kudinki jibi naje da kaina na siyo miki” harara ta balla mata
“Naqi na bayar din,wannan din da kika dawo dominta ita zan dauke dan uwaki,shegiya manna’il lil khairi”baki kaltum ta tabe,sannan tayi gaba,dama tasan abinda innar keso kenan,ita akuwa bataga dalioin da zaia bata kawo komai ba sannan ta dauki wani abu sabo na amarya ta tafi dashi ba,Allah ba zata bar mata ba,saida duk yadda za’ayi ayi.
Tana tsaye bakin window tana fakon innar,har Allah yasa ta tashi zata shiga bayi,da sauri kaltum ta fito,taja tabarmar ta nade tsaf tayi dakinsu da ita,ta daga shimfidarta ta fara shimfida tabarmar daga qasa,sannan ta maida kayan kai,ta yadda babu yadda zaka gani kace tabarmar tana qasan,sannan ta fito tsakar gidan,tana ci gaba da hada abinda take da buqata.
Tana jin sanda innar ta fito tana neman shimfidar tata,neman duniya anata juyayi amma kaltum tayi fir da ita,umma ta kirata taja mata kunnen indai ita ta dauka ta fito da ita amma tace batasan zance ba,daga qarshe ma da innar ta soma zarginta tana antayo mata zagi saita dauka mayafinta ta fice
“Shegiya mai baqin hali,gadon tsiya da talauci,shi yasa gashinan ubanku har yau jiya iyau”haka ta dinga gayaqa kaltum din,darajar ummansu kawai taci ta fita bata tanka mata ba.
Bata dawo cikin gidan ba sai data daidaici lokacin tafiya yayi,ta dawo kuwa a dai dai,don an gama haduwa,an fito da sauran kayan da za’a tafin dasu.
Dai dai sanda ta shigo ta ji inna na fadin
“To zuwaira…..ina kayan garar ne?”muryar umman a tausashe tace
“Babu inna,ba’a samu yi mata ba” haba innar ta kama
“La’ilaha illallahu,yanzu zuwaira garar ma saita gagari yarinya?,haba wannan wanne irin abun kunya ne?,ace kun kasa yiwa yarinya gara fisabilillahi?,yo ko bashi bakwaci kuyi mata ita ba ku fidda ita kunya?,wallahi ba don na riga nazo ba,kuma banason surutu kada ace banzo ba da babu inda zani,haba” tsit wajen yayi,aka koma kallon kallo na mamaki,yayin da umma ta samu waje ta zauna jin yadda mahaifiyarta ke shirin kwance mata zani a kasuwa,yakumbo indo ce ta karba
“Haba inna wannan aikinki ne ai dama a matsayinki na kakar yarinya,ke ya kamata kiyi,basu da suka gama hidimar biki qarfinsu ya qare ba” shalele ce tayi magana,shi yasa innar yin shuru bata sake cewa komai ba baya ga
“To naji uwar iyawa”da haka aka tattaru aka dunguma gidan amarya habiba.
Ba shakka habiban tayi sa’a,don kwana daya tal a gidan yusufa amma sun sameta tare da tarin alkhairansu,ita kanta ‘yar tayin zaman yabonsu take,anan akayi budar kai cikin karamci,aka sake tattarawa kuma biki ya qare akabar amarya ita da angonta,daga nan kowa ya wuce gida,na nesa ma suka je suka kintsa kayansu suka yiwa umma sallama suka wuce,umman nata godiya a garesu saboda tarin karamci zumunci da kuma karar da suka nuna mata.