YAR ME MAGANI COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR ME MAGANI COMPLETE HAUSA NOVEL

[7/17, 11:23 AM] OUM HAIRAN: *YAR ME MAGANI COMPLETE HAUSA NOVEL*

 

*Story and writing*
*Oum Hairan*

 

Lullumin gari na damuna iska me ɗauke da ƙananun yayyafi tana kaɗawa alamun ruwa na shirin tsinkewa daga Indallahi shine yasa daukacin jama’ar wannan karkara fara guje guje domin nemawa kai mafaka yayin da shikuma hadarin yake ƙara gangamowa yana curewa waje guda domin isar da saƙon mahalicci.
Iska ce ta fara tashi dalilin ya ya sanya gari ɗaukar duhu kenan kafin kace wane wannan ruwa ya kece me ƙarfin gaske.
Cikin ruwan wata yarinya ce tafe take sanye da riga da zani haɗin gambiza taci uwar ɗammara da gyalenta tana tafe cikin nutsuwa me nuna alamar batada wata damuwa da ruwan da yake dukanta, kanta ɗauke da tulu alamun ruwa ta ɗebo.
Bata kara sauri daga saurin da takeyi ba a nutse take tafe har ta isa ga wani gidan kasa matsakaici ta tura kofar ta shiga tana ambata sallama wani dattijo dake cikin wani daki ya amsa da cewa “Hinde Ina kikaje tun dazu nake nemanki guri-guri” ajiye tulun tayi ta kwance dammararta ta shiga dakin tana cewa “ruwan ne ban samu na debo ba Saida Matin Saude yazo shine ya debomin” jinjina Kai yayi yana daga kwance yace.

“Ga alkaki da kindirmo nan Kisha maganin yunwa idan kin tashi Sha ki zuba wancan rubutun a ciki Sai Kisha kinji” daukar alkakin tayi ta fara ci tana Shan nonon sukaji ana taba kofar gidan ga ruwa da ake makawa ta kalli mahaifin nata Shima ita ya kalla yace “waye ke taba Mana kofa yanzu Hinde aje a gani” tashi tayi ta fito duk ta jike da ruwan sama ta bude gidan wasu karti majiya karfi ne suka shigo gidan su takwas Suka angajeta suna cewa “ke yar maye Ina uban naki yau mu aikashi barzahu tunda baiji kashedi ba an hanashi fita cikin mutane shine ya fito har ya Kama Mana gyatuma to qur’anin Allah kodai ya sakar mata kurwa ko kuma mu kasheshi kowa ya huta”
Kallonta Mal Nuhu dake zaune saman buzunsa da carbi a hannunsa yayi mata nuni da kansa alamar ta fice Babu musu duk da cewa tana da abin fada ga bakin na babanta ta fice.

 

Can cikin gidan wajen tuke shanu ta nufa ta fara binsu tana dubawa a nutse gabanta na faduwa lokacin da maigari ya banko kofar ya shigo yanata tsine tsine da zage zage fadi yakeyi Hadi idan bazai saketa ba ku aikashi barzahu Mana ni nagaji da wannan masifa duk garin nan shi kadaine matsalarmu kullum cikin yiwa mutane dauki daidai yake”
Ihu da salatin mahaifin nata data jiyo shine ya sata sakin kwaryar data dauka don tatso nonon ta nufo dakin da gudu batasan ya akayi ba itadai tajita a rike a hannun wani kato da bazata iya kwatar kanta ba.
Wani kuma Sai bal yakeyi da Mal Nuhu ta rintse idanunta tayi wani kukan kura da nufin kwacewa hannun wannan mutum daya riketa rintse idanunta ta kumayi ta saki kuka me gunji tana cewa “Na shiga uku zasu kashemin Baba shikenan sun kasheshi wlh mu ba mayu bane babana ba maye bane kada ku kasheshi ku dauki hakkinsa ya rataya a kanku…..”

 

Dukan bakinta akayi ta kuma sakin kara tana kuka me gunji idanunta kan mahaifinta dake kwance cikin jini Babu alamun rayuwa a jikinsa tana kuka tana cewa “Don Allah Baba Mal karka mutu ka barni na shiga uku ni Hindatu Ina zansa kaina waye zai jinbanci lamurana waye zai kula da rayuwata Baba Mal kayi hkr karka mutu ka tashi mu tafi mu bar garin mu tsallake boorder mu shiga Nigeria ko mu koma Niger nasan su sunada Imani zasu fahimcemu”
Shigowar wani bakon mutum ne ya sanyasu sakinta suka tsallake zasu fice ta nufi mahaifinta da sauri ta janyoshi tana jijjigashi tana Kiran sunansa tare da tofa masa addu’o’i tana kuka me cin zuciya tana cewa “Idan ka mutu bansan ya zanyi ba Allah shine yake da rayuwa amma Baba Mal gara ni na mutu” dagowa tayi ta kalli mutumin dake tsaye a kansu wani matashin magidanci ne dogo kyakkyawa duk da kasancewarsa ba fari ba kuma bazaka kirashi baki ba da ganinsa kasan hutu ya hudashi.
Cikin muryarta me sanyi tace “Ka taimakeni kada Baba Mal ya mutu nasan zaka iya” da muguwar kasala da mutuwar jiki ya isa garesu ya daga Baba Mal dake kwance cikin jini ya fita dashi yasashi a mota ya juyo ya dubeta kanta na kasa dogon gashin kanta ya rufe mata fuska ya motsa bakinsa a hankali yace “Ina asibiti yake?” Cikin in’ina tace “Bansani ba nima” shiga motar yayi yace “Ki shigo mu duba”
Shiga tayi Suka dauki hanya sunyi tafiya me tsayin gaske kafin su fito birnin Chadin suka tsaya jikin wani asibitin kudi ya fita bai jima ba ya dawo da ma’aikata Suka kinkimi Baba Mal Suka shiga dashi ciki itama tabi bayansu a reception sukayi matsugunni ita da mutumin daya kawosu yana share gumi wayarsa ta buga ya dagota ya kara a kunnensa duk da cewa batajin abinda yake cewa domin turanci yakeyi ta fahimci da wani mutum me muhimanci yake waya.

 

Yana gamawa ya Mike yace “sun shiga dashi ciki za suyi masa duk abinda ya dace” yana fadin haka ya fice tabi bayansa da kallo har ya fice daidai lokacin da likitan ya fito yace “Ina Hindatu Nuhu?” Mikewa tayi tace “gani” numfashi ya sauke yace “Mara lafiyarku ne yakeson ganinki” yana maganar yana tafiya tabi bayansa cike da son ganin mahaifin nata dakin ya nuna mata ta bude ta shiga domin tasan kofofin irin na makarantarsu ne.
Zubawa Baba Mal idanu tayi hawaye ya tsiraro mata Shima ita yake kallo duk an nadeshi da bandeji saboda ba karamin duka yaci gurin su Hadi ba ga kuma tsufa dama kuma ga lalura tunda dama ba lafiya ce dashi ba.
Bin hannunsa tayi har ta isa gareshi ta tsugunna jikin gadon tace “Baba ya jikin?” Muryarsa Bata fita sosai yace “Ki daina kuka Hindu tawa tayi kyau saura tasu damuwata ke Ina zan barki? Hindatu Ina kika samu kudin kawoni asibiti?” Sunkuyar da kanta tayi kas tace “bani na kawoka ba Baba wani bako ne Allah ya aikoshi dan ya kawo Mana dauki….”
Karar bude kofar ce ta sanyasu juyawa sukayi ido hudu da bakon tayi kas da nata daidai lokacin daya karaso yace “Sannu Mal ya jikin naka?” Numfashi Mal ya sauke yayi ajiyar zuciya yace “Da sauki yaro daga Ina ka kawo Mana agaji?” Ajiyar zuciya ya sauke yana duban Hindatu yace “Nazo ne daga Abujan Nigeria domin neman maganin matsalata saina ishe matsalar me magani tafi ta me karbar magani Allah gafarta Mal meye ya hadaka da wadannan azzaluman mutanen suke neman ganin bayanka?” Lumshe idanu Baba Mal yayi ya Kama hannun Hindu ya rike cikin nasa yace “Sudin dangina ne Amma basa kaunata tun Ina yaro sunce gyatuma ta mayyace duk da bansan meyece maita ba Amma mun karba sun koreni a cikinsu mun koma bayan gari.

 

Sun hanani fita ko kofar gida Muna rayuwa ta kunci sha’ani na yaro in ni na jure Hindu bazata jure ba shine dalilin da yasa na kaita makarantar kwana saidai irin wannan lokacin na hutu Hindu ita kadai na mallaka a duniya mahaifiyarta ta rasu dalilin haihuwarta ko fuskarta bata gani ba duk yan’uwana su tara mata uku Maza biyar ban samu Wanda ya dauketa ba ni nayita dawainiya da Hindu tun tana jaririya kawo yanzu.
Dakyar Baba ya zayyanewa bako komai bakon ya kafa mata idanu itako ta kwantar da kanta jikin Baba Mal tana kuka ya dafa kanta yace “Ba mutuwa nake tsoro ba ke nake tausayi ko bayan kasa ta rufe idanuna Ina shawartarki da rike mutumcinki ki rike maraicinki kiji tsoron Allah aduk inda kike karki zamo me amfani da dama wajen wulakanta wani idan tazo miki ki dauki kowa naki zakiyi farin jini Allah zai kaunaceki mutane zasu soki” sakin hannunta yayi ya dubi bakon yace “Zaka iya bawan Allah ga amanar Hindu nan in ta samu miji ka auradda ita ga mutum na gari…”
Yana kaiwa nan tare ya turnuke shi ya rinkayi yana dafe kirjinsa dukkansu har likitan dake shigowa Suka rufu a kansa Amma Ina dan aike yazo hanun Hindu cikin na Mal Nuhu rai yayi halinsa ta rinka bin likitan da wannan bakon da kallo ganin bakon ya sanya hannu ya shafe masa idanunsa tayi zaman yan bori agurin tana girgiza Kai tana karanto innanillahi wa inna ilaihirraji’un hawaye wani na bin wani a kuncinta”
Bakon ne ya iso gareta jikinsa duk yayi sanyi idanunsa ya kada yayi jawur ya tsugunna gabanta ya zaro tsumman goge gumi ya mika mata yace “Kiyi hkr Allah ya jikan Baba Mal”
Kukanta ta sawa jiniya ta rike kafarsa tace “shikenan ya sun kasheshi nima zasu kasheni bako karka barni su kasheni ko na rinka yima iyayena addu’a”…..

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected