Kanwar Maza Hausa Novel

Kanwar Maza 42

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau’in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Tsayawa yayi cak ya ƙura mata ido, sai yayi mata kwarjini sosai da sosai, hakan ya tilasata yin gum da bakinta tana cigaba da bin sa da kallo.

Hannu ya saka ya ɗauko jaririn daga kusa da rumaisa, ai kuwa ta tashi zaune sosai ta tsatstsasreshi da ido, ko ƙiftawa ba ta yi, dan kar ya shammaceta ya gudar mata da jariri.

Ya nemi wuri ya zauna, ya ɗan tsurawa yaron ido, a hankali ya kai bakinsa kunnen yaron, yayi masa huɗuba da Mahmud kamar yadda ammi ta buƙata, ba kuma dan yayi niyyar sanya sunan ba.

Ya sauke yaron a hankali yana cigaba da kallonsa, ya ɗaga kai ya kalli rumaisa ya ce “A karo na babu adadi, ina sake tambayarki ina aisha take? Bana son ki kai ni bango, in yi miki abun da ba shikenan ba, ki bani amsar tambayoyin da nayi miki, matata na cikin hatsari dole na san in da take”

Kawar da kanta ta yi gefe, ta ƙi kallonsa.

“Am talking to you” yayi maganar cikin tsawa ganin yadda take nema ta mayar da shi mahaukaci.

Sake kawar da kanta gefe ta yi, ta dafe kanta da hannayenta, tana ƙunƙuni.

“Da ke nake, ki bani amsa” ya sake maganar kamar zai kai mata duka.

“Wai dan Allah me kake so na ce maka, ni na san a in da take? Nima fa saceni a kai, ko garinmu ne da zan san ina ne, ka je da kanka mana ka duba, ni na san sunan wurin ne? Kuma wallahi kar sake yi mini tsawa bana so”

Ya yinƙura zai sake magana mama ta yi sallama. Ya haɗiye maganar ya waiwaya ya kalli in da mama take.

Cikin girmamawa suka gaisa, mama ta ce “Ashe ka zo, na je sayo mata magani ne a waje”

Adam ya ce “Eh na zo, ban jima ba, amma ku din ga kai takardar pharmacy zasu baku ba wani abu”.

Mama ta ce “A’a basu da shi ne, ai yakamata muma mu din ga taɓukawa, masu shagunan ne ma basu fito ba, saboda haƙarƙarin da take kuka da shi, ya sanya na fita dubawa”.

Adam ya karɓi takardar hannun mama, ya ɗau hotonta, ya kalli mama ya ce “In anjima Bashir zai zo, zai taho da maganin sannan ya kai ku wurin X-ray ɗin”.

Mama ta girgiza kai ta ce “A’a, mun gode ɗawainiyar ta yi yawa, hakan ma Allah ya saka da alkhairi yayi maka albarka, ka bari kawai wannan zamu yi ba zai gagara ba da yardar Allah”

“Nima ɗan ki ne, ba zan ji daɗi ba idan ki ka nuna ba kya son na yi muku abu”

Tsidik ruma ta sanya baki ta ce “A’a bama so, yaya Abubakar zai zo su kai ni, idan ma wayo kake yi mini na fika wayo in gaya maka” ta yi maganar tana harare-harare.

Da ido ɗaya yayi mata wani irin kallo, mama kuma ta yi mata daƙuwa ta ce “Ke bana ciki da rashin hankalinki, sa’anki ne ko wani ya saka baki da ke? Kin ma taɓa yi masa godiyar ɗawainiyar da yake da ke?”

Ruma ta yi shiru tana basarwa, kar mama ta cigaba da yi mata faɗa a gabansa ya rainata.

Huzaifa ne yayi sallama da kwandon kayan abinci, suka amsa masa bayansa kuma Gwaggo ce da lawisa.

Nan suka zauna suna gaggaisawa, Huzaifa ya ƙarasa ya karɓi Mahmud a hannun takawa ya riƙe hannun jaririn ya ce “Mai sunan babanmu, kana lafiya?” Yayi maganar kamar jaririn zai amsa masa.

Takawa kuwa bin su yake da ido, lawisa ma ta bi Huzaifa tana cewa ya bata ta ɗauke shi.

Adam ya tashi yayi musu sallama ya fice, tabbas ranar da zai karɓi jaririn nan akwai daru, mussaman a wurin uwar riƙonsa rumaisa, yarinyar da ta riga ta fara shi kai bango saboda halinta.

***
“Ammi kin yi shiru baki ce mana komai ba”

Ammi ta ce “To Nusaiba me zan ce muku?”

Iman ta ce “Ammi kina ɓoye mana abun da yake faruwa, amma gaba ɗaya yanayinki da na takawa a ‘yan kwanakin nan ya tabattar da akwai wani abu a ɓoye, bama jin daɗin yanayin nan sam”.

Nusaiba ta ce “Ni fa ina daf da sanarwa Anty laila, wataƙila ki gaya mata meke damunku ku ka ƙi gaya mana”

Ammi ta numfasa ta ce “Kar ki kuskura ki haɗa ni da laila, koma menene dole zaku ji, amma ba yanzu ba”

“Yanzu Ammi haka zamu cigaba da kallonku a haka, ba fa haka muka saba rayuwa a tsakaninku ba, taya zamu yi adopting hakan lokaci guda, ammi walwalarki ce fa tamu” Nusaiba tayi maganar kamar za ta yi kuka.

Iman kuwa tuni idonta ya tara hawaye ta ce ‘Ammi ko dai nice, idan saboda ni ne, ki kai ni Gombe can family house ɗin ku, zan zauna, kuma duk wanda ki ka zaɓa mini zan aure shi, amma dan Allah ki cigaba da walwala muna ganin murmushin ki”

Tausayin Iman ya kama Ammi, ya kamo hannun iman ta ce “Haba iman ɗina, ki na tunanin akwai wani ƙalubale da zai ta so na rabu da ke ne? Kar ki kuma wannan maganar, wani abu ne yake faruwa daban, amma komai zai daidaita in sha Allah”.

“Ammi wai muma ‘ya’yanki baki yadda da mu ba, muma munafukai ne kenan yaya takawa ne kawai mai iya riƙe sirrinki?” Nusaiba ta yi maganar har cikin zuciyarta.

Duk da halin da Ammi ke ciki, sai da Nusaiba ta bata dariya, ta girgiza kai ta ce “Ba abun da ku ke tunani bane ba Nusaiba, wata yarinya aka tsinto a katsina da jariri” sai kuma ta yi shiru.

“Ammi to meye haɗin hakan da damuwar da kuke ciki?”

Ammi ta ce “Ɗan takawa ne”

Nusaiba cikin rashin fahimta ta ce “Wane takawan? Ta ina za a tsinto yaro a katsina kuma ya zama ɗan sa?”

“Ɗan sa ne” Ammi ta basu amsa.

Iman ta ce ‘Amma Ammi, ta yaya?”

“Ɗan Aisha ne, ta kawo ɗan kwalinta da gwala-gwalanta”

Nusaiba ta ɗan dafe goshi a rikice ta ce “Ammi kin hargitsani ban gane ba, ta yaya Anty Aisha da take Saudiyya za’a tsinto ɗan ta da ɗan kwalinta a Nigeria kuma a katsina, anya ba ƙarya yarinyar take yi ba, ko wani abun ake shiryawa ba”

Hawaye ya cika idon ammi, ta ɗauki wayarta, ta buɗe ta nemo hoton jaririn ta miƙa musu.

Cikin tsananin mamaki suke kallon hoton, babu in da yaron ya bar Adam saboda kamanni.

Iman ta ce “Ammi, ni fa haryanzu ban gane ba, a ssudiyyan ta haihu ko kuma yaushe ta dawo Nigeria har aka tsinci jaririnta, ita tana ina?”

Nan Ammi ta warware musu komai, kamar yadda takawa yayi mata bayani.

Nusaiba ta dafe kai ta fashe da kuka ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Ammi yanzu mai za’a cewa mai girma turaki, tayaya za’a warware wannan lamari? Anty Aisha a hannun ‘yan bindiga tsawon wannan lokaci babu wanda ya sani? Kuma Ammi ki ke ɓoyewa, idan zancen ya ɓullo ta wani wurin daban fa, kar ki manta ba’a san da cikin nan ba, kuma cewa aka yi zata ƙaro karatu, aka yi ta surutu a kai, tayaya za a dawo ace ba ƙaro karatu ta tafi ba, har ta je ta dawo an saceta ya haihu sai ɗa da ɗankwalinta da gwala-gwalanta, ana ma da tabbacin tana raye?”

Gaban Ammi ne ya sake faɗuwa, jin abubuwan da Nusaiba ta faɗa, take hawaye ya fara gangarowa daga cikin idon Ammi.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected