Tsutsar Nama 7
*_Typing_*
*_TSUTSAR NAMA….!!_*
_(Itama nama ce)_
_ _
_ _
…….Ina shiga ɗaki kukan da banyi ba a gabansu ya kufce min. Ban yarda nai zaman yinsa ba, na zame kayan jikina kawai na nufi bathroom. Tsayawa kawai nai ina kallon bayin raina a matuƙar ɓace. An masa kaca-kaca tamkar banyi wahalar gyaransa ba kafin na wuce. Nasan Bibaa ce tai masa haka. Dan tsabar iskanci har pad data cire guda biyu ta yasar a bayin da pants ɗinta. Inada ƙyanƙyami sosai a rayuwata, dan abu kaɗan ke ɗagamin hankali, shiyyasa ma nake bugar jikina na tsaftace gidan yanda ta kamata batare da jin ƙyashi ba. Hawaye tab da idona na shiga gyaran bayin, sai da na maidashi ƙal na tattara trash ɗin data tarama mutane na fitar. Har lokacin suna a falon zaune suna kallo har Mum ɗin, kai kace basu ji sallar magrib da akeyi ba. Na jima da fahimtar Mum saita gadama take salla, shiyyasa ƴaƴan nata ma dai gasu nan sai a hankali babu wanda ya damu da ibadar. A da Hafizzullah har ya fara ɗaukar ɗabi’ar, sai da na miƙe kansa ni da Yaya Musaddiq tamkar bama ƙaunarsa sannan. Sake zuwa nai na wucesu na koma ciki. Sai da nayi wanka na saka doguwar riga mara nauyi nai salla. Bayan na idar zaman yin karatun Alkur’ani nayi, ban ɗaga a wajen ba sai da akai isha’i, har lokacin kuma ina jiyo hayaniyarsu a falon, sallar dai bazasu tashi suyi ba. Falon na fito na wuce dan ɗaukar abinci na, amma sai na samu wayam. Banyi ƙasa a gwiwa ba na dawo ina tambayar Bibaa. Wani kallon banza yarinyar ta watsa min duk da kuwa na bata kusan shekara bakwai zuwa takwas, dan kwata-kwata yanzu take a shekara ta goma sha uku, a gadarance ta ce, “Kin bani ajiya ne. Ka jimin rainin wayo dan ALLAH mtsowww!!” ta maida kanta ta cigaba da abinda take yi. Bance komai ba na juya na koma ɗaki, dan hakan da tai na nufin yau banda abinci a gidan tunda na tafi aiki ban kammala miya ba, bayan kuma nayi komai har abinda ba’a sakani ba, miyar ma na barta ne kawai ta gama fidda mai dan karna makara tunda ta soyu. Wajen kwanciyata nakai zaune ina hawaye, dan haka kawai yau naji zafin abinda akai min ɗin duk da bawai yau ɗinne farko ba, amma kasancewar na dawo da yunwa sai abin ya zafeni. Tun muna yara idan Mum ta bushi iska takan hanamu abinci, haka Hafizzullah zaita kukan yunwa dan ni da Yaya Musaddiq mukan daure, ko zaiyi kukan mutuwa kuma bazata bashi ba sai dai Yaya Musaddiq ya fita ya samo masa a waje koda da bara ne, yanzu kam da muka girma idan aka hanamu zai sayo ya jamu ɗakinsa muci mu ƙoshi muna hirarmu. Sai kuma hakan ke ba Mum haushi take kai ƙararmu ga Abba wai muna haɗe kai muyita zaginta a ɗakin Yaya Musaddiq. Wani lokacin Abban kan mana faɗa, wataran kuma ya mata shiru, sai dai ta ƙaraci masifarta ita kaɗai. Ganin zaman bazai amfaneni da komai ba na miƙe ina share hawayena. Ƙaramin hijjab ɗina na zaman gida na ɗauka na saka, na ɗauki jakata dana fita aiki da ita na fito. Suna a falon har yanzu suna kallo, banko kalla kowa ba a cikinsu na fita zuwa ɗakin Yaya Musaddiq. Sai da na ƙwanƙwasa tare da yin sallama ya bani izinin shiga sannan na shiga. Tashi yay daga kwancen da yake a tabarmar barcinsa, dan koya sayi katifa amshewa Mum take ta bama su Bibaa su kasheta da fitsari ko a bama su Abbas. Kusan sau uku tana yin hakan shiyyasa ma ya bar saya shima. Murmushi yay min yana mai bina da kallo, na ɗan tura baki gaba ina zama a gefensa da ajiye jakar kamar a yanayin gajiye. Yaya Musaddiq mutum ne mai sauƙin kai sosai, da wahala ka iya ganin fushinsa a zahiri. Cike da kulawa ya ce, “Kandala miya faru kuma ake kumbura wannan cat face ɗin?”.
Sake tura bakin nayi da faɗin, “Ni ba komai, yunwa nake ji”.
Ɗan jimm yay yana kallona, sai kuma ya ɗauke kansa da sauke ajiyar zuciya ya miƙe. Rigarsa ya ɗauka ya saka a saman singlate ɗin jikinsa. “Ki jirani ina zuwa”.
Kaina na jinjina masa ina kaiwa kwance a tabarmar tasa. Yana fita na ɗan lumshe idona. Kusan minti huɗu ina a haka sai kuma na miƙe zaune. Jakar tawa na jawo gabana, tare da zuge zip na ciro mujallar nan da MD ya bani ɗazun. Yanzu kam kai tsaye na zubama mujallar ido, sosai nama mutumin kallon ƙurilla a karo na biyu, badan baiyi haske dau irin na larabawa da indiyawa ba da tabbas zan iya cewa daga cikinsu ya fito. Dan daga suffar jiki har zuwa ta halitta fuska bai yi kama da ƴan Nigeria ba. Sai dai kuma abin mamaki fatarsa zamu iya cewa irin tamu ce. Duk da kuwa ba baƙi bane wulik, idan ma za’a kira farare za’a iya nunashi mu anan Africa, sai dai kuma farin nashi yasha banban, koda yake maybe camara ce ta maida shi hakan. Sake maida idanuna akan kitson kansa dake ɗaure a tsakkiyar kai kamar wani mace, sai kawai naja sirrin tsaki, banda ƙarshen duniya dai ace namiji da kitso da ɗan kunne. Kai ALLAH ya ƙyauta, inaga dai ɗan daudu ne gaskiya. Dangwarar da mujallar nayi gefe na sake komawa nai kwanciyata. A dai-dai nan Yaya Musaddiq ya shigo ɗakin da sallama. Amsa masa nai ina tashi zaune. Ya ajiye min ledar hannunsa yana faɗin, “Oya tashi kici”.
Babu musu na tashi zaune, ina ƙoƙarin buɗe ledar shima yana kaiwa zaune ya ɗauki mujallar. “Tofa! Ke kuma ina kika samo _Maash_ haka kandala?”.
Baki na taɓe da fara kai lokar indomie ɗina. Kafin na ce, “MD ɗinmu ne ya bani yau wai zanyi aiki a kansa”.
“Aiki kuma?”.
“Eh Yaya, so suke wai nayi hira da shi a ranar bikin buɗe Companyn sa”.
“Kai lallai sun haɗaki da aiki. Amma ALLAH ya bada nasara”.
“Amin” na amsa masa ina sake jin karaya. Sai kuma na kallesa, batare da nasan ya akai bakina ya suɓuce ba na ce, “Yaya amma dai shi ba musulmi bane ba ko? Sannan ba ɗan Nigeria bane?”.
Sosai ya waro idanu waje da faɗin, “Kai! K waye ya gaya miki ba musulmi bane?”.
“To Yaya wane musulmi ne zai zauna ai masa kitso a saman kai ya ɗaure haka kamar wani mace. Ga ɗan kunne kuma a kunne ga tattoo a wuyansa. Sannan kalli idonsa kamar na mage fa. Ni wlhy banji ya birgeni ba abu kamar ɗan daudu”.
Dariya Yaya Musaddiq ya saki yana girgiza kansa. Ya ce, “Banda abinki Samraah dan mutum yayi duk wannan sai a fiddashi a musulunci ko a kirashi ɗan daudu. Wannan abun da kika gani yanzu shine samari suka ɗauka matsayin gayu da wayewa wai, baki ganin kuma shi ɗin mai lokaci ne da duniya ke ji da gani. Idan kuɗi na ɗibar mutum ai komai ma sai ya yi ba komai bane. Sannan shi ɗin kamar ance ruwa biyu ne. Tsakanin kakansa da kakarsa akwai wadda ba ɗan Nigeria ba, anan ma ya kwaso waɗan nan kamannin da kowa ke ganin ba ɗan 9ja ɗin bane ba. Amma asalin mahaifinsa ɗan kwanar Mashi ne ma, Kinga kuwa shi cikakken bakano ne, anan ma aka haifesa shi”.
Baki na taɓe akan maganar yaya ta kusan ƙarshe, sai kuma na ce, “Humm, to ALLAH ya rabamu da irin wannan kuɗin masu mantar da bawa shi waye kuwa. Ni yanzu Yaya yaya zanyi to. Wlhy duk kaina ya gama kullewa fa?”.
“Karki damu in sha ALLAHU zamu samo mafita. Ke dai kawai ki saka a zuciyarki zaki iya. In dai shi ba aljani bane nasan duk taurin kan Maash bazai gagari Kandalata ba ai. Dan itama tauriƙiƙin kantace ga naci akan abinda tasa gaba”.
Dariya na ƙyalƙyale da shi da faɗin “Kai yaya?”
Ya ce, “ALLAH ai nasanki ne fiye da yunwar cikina kandala”.
Nanma dariyar nayi shima yana tayani, tuni Yaya ya mantar dani baƙin halin mutanen gidanmu. Ya kuma bani ƙwarin gwiwa sosai data bani karsashi akan tunkarar wannan aiki da MD ya bani, ban baro ɗakin ba sai da na fara hammar barci….
