Namijin Zuma 31
U……31
Zaks Yaga nan da nan fuskar tasa ta hade baki kirin kmr hadari, be taba ganinsa a yanayin da yakansa ba yanzu, har wani duhu fuskarsa tayi saboda zallar azabar matsifa da jaraba dasuka masa dirar mikiya a zuciya, ya Kure su nabeelah da Alhaji Sadi da ido, se huci yakeyi kmr kumurcin maciji mesa a rami. “Da Aurena,,,,da Aurena take tsayuwa da wani namiji,,,wallahi wallahi Zaks yau sena kashe wancan tsinannen! Wlhi yau nine ajalinsa,! Zan nuna masa waye ni, dan mecin uwar ubansa, shege tsinanne kawai!” Aeezad ya fadi da muryarsa wadda ke barazanar tarwatsa motar da dodon kunnen Zaks din. Laluba aljihunsa yashigayi domin yaji akwai Karamar bindiga ciki, yaji babu , nan take duk yabi ya rikice idanuwansa sun rufe, lalubar gaban motar yashigayi tako ina yasan baza a rasa bindiga a motar tasa ba, ko gani bayayi sbda bacin rai,ji yake kmr zuciyarsa zata buga ta tarwatse, Zaks kam ya rasama yazeyi ya kasa cewa komi , shide yasan be isa ya dakatar da Aeezad daga aikata abinda yaga dama ba, Gashi da alama mommy Ma ta gansu danse kallonsu takeyi, gaskiy mommy bata kyauta ba, Zaks be taba ganin lefin mommy ba se yau, tasan da Aurensa a kanta kuma ta tsaya da wani namiji, ta gansu yanzu taga motar tasan sune a ciki koda motar ba a ganin na ciki, amma ai kaf motocin Aeezad tasani kodan lambar motar jiki, amma ta kallah ta dauke kai, taci gaba da sakarma Alhaji sadin murmushi, inside kam ba karamin bugu zuciyarta keyi ba, tinda taga ba ayi packing dai-dai ba, hkn ya tabbatar mata da yau akwai matsala, ta sadakar yau zatasha marirrika, kawai tunano irin Marin daya mata a asibitin tashigayi,.”yau natashi aiki!” Ta fadi a zuciyarta, dukda iskar dake kad’awa amma seta Kama zufa, kawai murmushi takeyi a zahiri, amma ko abinda Alhaji sadin kecewa bata fahimta. Ba bata lokaci Aeezad yaga bindiga karama a gaban motar, ganin yaga bindigar yasa Zaks shiga tashin hankali sbda yasan komi na iya faruwa. “Dan Allah Aboki karka Aikata abinda be dace ba in rai ya baci hankali ke nemosa…” Zaks ya fadi yana RIKO hannun Aeezad me lafiya wanda ke rike da bindigar yana kokarin ficewa a motar. Ina Ai Aeezad bebi takanma me Zaks ke kokarin sanar dashi ba, ko gani bayayi sosai, ya fito daga cikin motar, Zaks ma ya fito, nabeelah na ganin Aeezad ya fito daga cikin motar kuma taga bindiga a hannunsa, taga yana tinkarosu gadan-gadan da bindigar, zumbur ta tashi tsaye, Tana fadin “Alhaji kashiga mota ka gudu,,,kashiga motarka ka gudu! Nashi uku yau!!!” A rikice take mgnr, Alhaji Sadi shima mikewa tsayen yayi ba tare daya fahimci me nabeelah ke nufi ba, yashiga tambayarta “kamarya? Bangane ba?” Kasancewar ya bawa Aeezad baya Sam be Gansu ba, shifa bemaga shigowarsu da motar ba, in yana gaban nabeelah baya fahimtar komi kyaunta na makantar dashi, shifa Allah yasani dan kyaunta ze Aureta, (kunsan cikakkun kanawa dasan mata masu kyau, musammanma in farar mace ce) “kashiga motarka ka gudu dan Allah Alhaji!” Nabeelah ta fadi cikin magiya still idanuwanta na kan Aeezad da Zaks dasuke tinkarosu. Ganin inda ta tsurewa ido sannan ga alamar fitar hayyaci ya bayya kan fuskarta, yasa Alhaji Sadi juyawa yaga me take kallo ne daga bayansa, daya gigita ta har haka. Juyawar dazeyi yaga Aeezad da Zaks , ganin ya juyo Yana kallonsa yasa Aeezad dago hannunsa dake dauke da bindiga sama , ya shigo nuno Alhaji Sadi da bindigar yana kokarin sakin harsashin Zaks ya rike kan bindigar. “Ka barni in kashe shi, wlhi yau nine ajalinsa, daga kan matata baze kara marmarin kusantar wata mace ba in har matan Aure ce,…karamin mazinaci neshi,, wlhi sena zama ajalinsa yau!” Sune kalaman dake fitowa daga bakin Aeezad, Alhaji Sadi ya shiga firgici, Jin kalaman bakin Aeezad Sam be fahimci me yake nufi ba, sbda shide yasan nabeelah ba matar Aure bace, Alhajin ya fara tunanin Anya bayan ciwon hannun da yakeyi ciwon hauka be shafi Aeezad dinba, tini ya ganesa tinda ya daura idanuwansa a kansa ya fahimci kanin matar baban noor ne. “Ka fita a gidannan dan Allah’’ Cewar nabeelah da hankalinta ya kara mummunar tashi, ta shiga ture Alhaji Sadin da hannayenta biyu, ko gezau Alhajin beyi ba, sbda shi kansa ma ya kulle. “Bura ubannan!” Aeezad ya fadi a bayyane ganin nabeelah na ture Alhaji Sadi da hannayenta , hannayenta nasa na Auren sunnah, shine take taba jikin wani d’ana miji dashi yau garjejen kato. Hankalinsa da zuciyarsa da lissafinsa suka kuma baci, sbda tsabar bacin rai ko ganin gabansa bayayi sosai,. “Ka kyaleni Zaks , ka sakar min bindigata, in baka sakarminba na kashe mutuminnan to tabbas Kai zan kashe!’” Aeezad ya fadi cikin kunar zuciya, Zaks ya kara rike bingidar sosai da hannayensa biyu yace “Naji aboki zan dauka ka kasheni ,…” da karfi Aeezad ya fisge bindigar daga hannun Zaks yana fadin “Ka kyaleni ba ruwanka!!!” Ya fadi hadi da nufar kam Alhaji sadi da firgici ya hanasa tafiya, nabeelah sece masa takeyo ya wuce amma yaki wucewa se tambayarta yakeyi meke faruwa. Cikin hanzari Zaks ya kara binsa ya rikesa yayinda sukazo daf da Alhaji sadin, Aeezad na kokarin harbin Alhaji Sadi Zaks ya rike kan bindigar again, saura kiris a hannun Zaks din Dan Allah ya rufa asiri zaks din ya maida kunamar bindigar ciki. “Ka kyaleni!! Wlhi ka kyaleni in kashesa ko kai in kasheka,! Wlhi sena kashesa koda Nima daga hk za a kasheni!” Aeezad ya sake fadi cikin fitar hayyaci kishi ya rufe masa idanuwa, idanuwan nasa na kan Alhaji sadi. Zaks ya kalli Alhaji Sadi da zufa keta keto masa bakinsa se rawa yakeyi sbda tsoro ya kasa guduwa duk yabi ya firgice Gashi ga mutuwa real aini dole ya rude ya rasa uwar ubansa. “Ka bar gidannan !inba haka ba wlhi ze harbeka….” Cewar Zaks da yayi mgnr da Alhaji sadi, se kokawa yakeyi da Aeezad wanda ke kokarin amshe bindigarsa daga rikon da Zaks din yayi mata, so Zaks yakeyi ya amshe bindigar daga hannun Aeezad amma ina ya kasa, ya tabbatar da ace Aeezad nada lafiyar Dayan hannu da Zaks be isa ya iya masa ba, a haka ma ya kasa amsar bindigar a hannunsa, dukda shi hannu biyu garesa shi kuma hannu daya garesa, se zufa kawai Zaks keyi, gogan kam jikinsa har kyarma yakeyi idanuwa nan nasa sunyi ja-jawur kmr jan gauta. Nabeelah kam tini ta fara kuka sbda tashin hnkli , maaikata gidan na ganin abinda ke faruwa amma ba wanda ya isa ya we uffan ko gurin basu isa su karaso ba , baban noor na part dinsa ya kule a karshen bedroom dinsa yana wayar iskanci da karuwarsa. (Kaima baban noor Allah baze barka ba, ana nan ana maka talala,,) aunty hafsat na saman upstairs Tana dakinta ita da yaranta suna wasan yaushe gamo, big hajiya kam na dakin kasa tana baccin asara na bayan la,asar ta hangame baki, duk ba wanda yasan meke faruwa a tsakar gidan, kowa nacan yana sabgar gabansa.
Ba bata lokaci alhaji sadi ya isa ga motarsa jiki na rawa ya shiga, ya tada motar ya isa bakin get da motar da kyar sam hnklinsa baya jikinsa yake driving din ya raba motar Aeezad da akayi packing dinta ba dai-dai ba, yana kokarin ficewa a gidan Aeezad ya sakarma Zaks bindigar ya isa ga motar Alhaji Sadi dake kokarin ficewa a gidan a guje, already daman glashing motar tasa a bude yake ta fannin me tuki, wani irin mahaukacin naushi Aeezad yakai masa ta Cikin window din motar dai dai a saitin bakin Alhaji sadin. “Bakina !” Alhaji Sadi ya fadi a gigice sbda zafin dayaji a bakinsa ya matukar kara rud’asa nan da nan jini ya Balle daga bakin Alhaji sadin dai dai hakoransa guda biyu suka fito daga bakin nasa na gaba, suka fado gaban rigarsa, nan hnklin sadin ya kuma tashi, ya tabbatar Aeezad de mahaukaci ne. Aeezad na kokarin kara Kai masa wani naushin Zaks ya karaso a guje ya rikesa nan yaga Alhaji Sadi baki na jini. “Kaga abinda mahaukacin nan yamin kou ?” Alhaji Sadi ya fadi nan take wawulon bakinsa ya bayyana na gaba wanda keta jini. “Innalillahi! Ka gudu dan Allah …” cewar zaks dake kici kicin rike Aeezad, wanda keso ya kara kwacewa ya farma Alhaji sadin danya tabbatar shidin mahaukacin gaskene bana wasa ba. Ganin Zaks ya rikesa a guje Alhaji Sadi ya fice a gidan ya Danna motarsa kan titi ya shiga sharara gudu sbda gani yake kmr Aeezad din ze biyosa ne ya kashesa, Gashi ba a shara’ah da mahaukaci.

