KWARKWARAH Complete Hausa Novel

KWARKWARAH Complete Hausa Novel

[6/11, 12:55 PM] My Zahrah:
*K’WARK’WARAH Complete Hausa Novel*

”'{ITAMA MATAR SARKI CE}”’

_LOVE TRIANGLE♥️_

1️⃣

1987-October- 23
Sintiri yake hannun goye a bayan shi, tsakanin zauren gidan shi sanye yake da janfa! Shigowa da sauri wata dattijuwa tayi ta zub’e akan gwiwarta cikin hakki, sai da ta dai-daita nutsuwarta sannan tace.
“Allah Ya taimaki me martaba! Ubangiji ya kare takawa lafiya! Allah ya bawa takawa Abinda yake nima! A gafarce Ni da kitsen  da nayi!”

Shiru zauren ya dauka! Kafin yayi magana cikin sansanyar murya yace..
“Ina jinki Jakadiya!”

Sake risinawa tayi sosai sannan tace.
“Allah taimaki Sarki Jalaludeen! Adalin Sarkin mu! Me kaunar Al’ummar shi!”

Shiru tayi sannan ta had’iye yawu kafin ta cigaba da cewa.
“Allah ya karama nisan kwana! K’wark’waranka Ummu Rumana tana kan gwiwa! Ita da Fulani Hasiyah”

Shiru yayi kamar bayi zauren, sannan ya d’aga mata hannu!
Mik’ewa tayi cikin sauri tace.
“Na Barka lafiya! Allah ya kawo maganin Izza lafiya”

Tunda ta bashi labarin Rumana tana kan gwiwa yaji duk wata nutsuwar shi ya kwace,
Ajiyar zuciya ya sauke Kafin ya koma kan shimfid’ar shi da yasha kwalliya da dardumai tare da kilisai, ya zauna a yanzun a halin da yake ciki mutum d’aya yake bukatar gani a cikin wannan yanayin! Wato tsohon amininshi Magaji!

Mik’ewa yayi tare da nufar cikin d’akin shi, ya sauya kayan shi ya b’adda kama, sannan ya nufi kofar dake cikin Zauren shi wanda zai fidda ka wajen masarautar Daura.

——
A hanyar fita Jakadiya suka yi karo da Shamaki!
“A’ah Jigal kazamin tsuntsu,”

“A’ah me abu da abinsu kura da kalabin kitse daga ina haka”

Murmushi tayi da alamun abinda ya gaya mata yayi mata dad’i tace.
“Hmm! Maraba da gasheshe kura taga bakin jaki”

Gyara tsayuwar yayi sosai dan ya fahimci akwai magana a bakinta.
Juyawa yayi hagu da dama yace.
“Da kukan kura, da bacewar akuya duk d’aya ce! Meke tafe dake”

Mika hannunta tayi cikin muzurai tace.
“Da babbar rowa gara karamar kyauta”

Zuba mata ido yayi aikuwa ta kauda kanta, kamar ba ita tayi maganar ba. Jinjina kai yayi sannan ya sanya hannu a cikin aljuhun shi ya ciro kud’i ya mika mata.

Murmushi tayi sannan ta kirga kuɗin kafin tace.
“Cinikin duniya, diban nono!”

“Hmm me tsegumi bashi rabuwa da waiwaya! Meke faru”

Juyar da kai tayi sannan tace.
“Bikin farar kaza! Su balbala gayyar sod’i ce, Fulani Hasiyah da K’wark’warar Sarki suna bisa gwiwarsu! Amma wannan karon zakarar dawaki ne kukanshi bana Alkhairin bane, zan koma ciki.”

“Kina nufin!”

“Gyaran hanci, yafi gyaran gona! Koma me nake nufi kasan baza a nunawa ringing wata ba, dan da alamu cikin su dole asami d’aya ta”

Shiru yayi bai tanka mata ba ya kad’e saka tarar shi yayi gaba, yana magana.
“Tab bashi yuwa, an san da wuyar biri ake d’aura shi a k’ugu! Dole mu hana haihuwar d’a namiji a cikin wannan masarautar!”

“Assalamu alaikum!”
Da sauri ta zub’e akan gwiwarta, tace.
“Allah Ya taimaki! Fulani Sakonki ya isa ga sarki Jalaludeen!”

Juya bayanta tayi tana kallon yan tsuntsayen da suke shawagi a cikin kejinsu! Sannan ta mai da idanunta kan jaririyar da take nad’e cikin kunshi zani.

“Kije ki duba min Rumana! Ki nemi amintacciyar baiwa ki bata gadin Rumana, idan ta haihu kar a kai ga fad’a takawa”

Gyad’a kai kawai Jakadiya tayi, sannan ta mik’e da sauri tare da barin d’akin. Tana murmushi sannan tace.
“Mutanen duniya kudan doki ne, dole abisu a hankali! Muje zuwa”

Da sauri ta wuce zuwa hanyar da zai kaita shashin k’wark’wara Rumana, tana shiga kamar wacce yazo da haihuwar. Korar unguwar zoman tayi, takira wata cikin bayin ta turata Katanga bayi, sai gasu tare da wata baiwa dattijuwa itama.
“Larai ki gyara abinda aka haifa, naga kamar ta sume kar labarin haihuwar ya isa ga takawa! Duba min ma tukun me ta haifa”

Dake k’wark’wara Rumana a durkushe take, d’aga zanin Baiwa Larai tayi, ta janyo abinda aka samu. A d’imauce ta d’ago kanta tana kallon Jakadiya, bakinta na rawa tace.
“Ranki shi dad’e! Ai magajin masarauta aka samu.”

Wata irin zabura Jakadiya tayi cikin mamaki tare da lekawa, taga abinda aka samu d’a namiji ne kyakyawa dashi, kaman shi da sarki Jamaluddin ya b’aci, hasken fatar uwar shi.
Takowa tayi ta d’ago kan Rumana wacce take sume bayan haihuwar ta, tace.
“Ki nad’e jaririn ki tabbatar kin yanke cibiya”

Tana gama fad’ar haka tabar cikin dakin da sauri, kallon unguwar zomar tayi, sannan tace.
” Zaku iya tafiya, dan ta sauka lafiya kuma.”

Sai tayi shiru sannan ta wuce bayan taga barin su gurin, b’ata nufi shashin Fulani ba, fita tayi daga masarautar,

Wani gida ta nuna sannan ta wuce zauren gidan, babu sallama ta akfa musu.
“Toh tauraruwa mai wutsiya! Meke tafe dake!”

Murmushi tayi sannan tace.
“An kawo kare dan haushi, ya buge da kukan akuya!”

Zubur ya mik’e jikin shi na rawa,
“Karya ne Jakadiya! Masallacin kura kare bashi limancin”

“Allah sarki! Harbi ga wutsiya kuskure ne” Inji Jakadiya.

“Me haka ke nufi?”
Ya wurgata mata tambaya,

“Eh hakan yana nufin duk matan sarki babu wacce tayi nasarar da Rumana tayi,”

“Aikin banza kiba a kunne! Sani ake zance.”
“Na Barka lafiya”
Ta ficce da sauri, daga cikin gidan ta nufi masarautar tana juyawa murmushi tayi sannan tace.

“Komi gaggawar hasara dole ta jira samu”

Shashin Fulani ta nufa, cikin sauri ko sallama ba tayi ba ta zub’e a gaban fulani, cikin hali ta sunkuyar da kai zuciyarta cike da fargaba, dan duk wata munakisa da kutungwailarta bata kamo kafar Fulani Hasiyah ba.
“Me Rumana ta samu?!”
Tambayar da Fulani ta wurgo mata ya katse mata tunanin da take.
“Ranki shi dad’e! Ina niman afuwarki, Allah ya huci zuciyarki! Hmm ta sami abinda Takawa yake mafarkin samu ne”

Murmushi Fulani Hasiyah ta sake, har sai da Jakadiya ta d’ago kanta tana mamakinta sannan tace.
“Allah ya huci zuciyarki! Farin ciki kike na gani!”

“Ki dauki y’ar ki kaita inda Rumana take! Sannan wacce kika bari a gurin! Ki sanya Bak’o ya aikata inda bazata dawo ba! Gawar sai ku mata sutura a tabbatar da Rumana ce ta haihuwa Y’a mace! sauran bayanin kin fahimta, ina yaso Jaririyar ki san hikimar da zaki kara!”
Takowa tayi gaban Jakadiya tana kallon cikin idanunta, ta cigaba da cewa.
“Abinda wancan yace, shi nace kirarin me tsoro kin fahimta”

Gyad’a kai Jakadiya tayi cikin tsantsar tsoro tace.
“Uwar d’akina aka mutu ma balle lalacewa! Ai zancenki kamar an binne Rumana da ranta ne, balle Larai”

“Muguwar aniya bata karewa tukunya,” Inji Fulani.

Sunkuyar da kai Jakadiya tayi dan ta fahimci sakon Fulani, a hankali tace.
“Allah kad’ai ke kaunar kura”

Fita Jakadiya tayi bayan ta dauki jaririyar sannan tace.
” Duk inda jirgi yaje, inda hakuri wata rana kunkuru zashi sai dai ya jima bai isa ba! Fulani dani kike zancen”

Tana shiga inda Rumana take ta kori larai sannan ta dauki d’an Rumana ta ajiye mata yar da tazo da ita, sannan ta fita da Yaron da Rumana ta haifa.

Bayan Sa’a d’aya aka fidda sanarwar mutuwar Rumana bayan ta haihu, sai mutuwar Baiwar da ta amshi haihuwar sakamakon gubar da tasha.
——

Tun bayan fitar Mai martaba Sarki Jalaludeen, ya nufi gidan abokin shi, sun jima suna tattaunawa kafin ya bar gidan, zuwa masarautar a cikin shigar shi na tsofi tukuf ya isa shashinsa, yana cire kayan. Ya tsinkayo Muryar Jakadiya.
Gaban shine yayi mugun Fad’uwa ya fito daga d’akin yana kallonta.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected