Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 29

29
Zaman shirun yake sake girmama tinani da burikan Ababa game da lamarin komai ya sauya na lissafinsa Kuma,
A yanzu baida burin daya wuce su karba cikin kawai ya Dora sharidansa kai tsaye ba batawa juna lokaci.

Dd babba zuwa lokacin jininsa yafara kokarin Hawa Amma dayake jajirtaccen mutum ne Mai qarfin zuciya da Iko sai ya danne ya Hana Kansa karban zancen Tako Ina daga zuciyarsa har cikin Kansa.

Bilal kawai yake jira a datse zancen ya sallami mutumin tareda gargadin ko sunansu karya sake shiga cikin zancen ko gun Bada labari ne na yayi sabanin fahimtar zuwa gurinsu.

Knocking kofar da akai yasa gaban Ababa daka tsalle zuciyarsa na tsinkewa take shakku da fargaba Kuma Mai tsanani yashigesa na abinda Bilal zai fada akan cikin yanzu shine zai tabbatarda matsayin samunsa da rashinsa yanzu kam,

Dan idan Bilal Yace Bai san sumayyah ba kokuma cikin to tabbas ta tabbata daga yau yakoma Nobaba,
Idan Kuma Yace yasan da sumayyahn ko Bai san cikin ba wlh sai sun karba Dan ko ba nasa bane sai ya maqala musu kafin ya koma gida su fuskanci juna shi da sumayyahn Harma da uwarta da Benazir.

Shi kansa Dd babba sai daya sauke numfashi ahankali Mai sanyi kafin ya Bada izinin shigowar.

Kaman yanda suka tsammata Bilal dinne
Gabaki dayansu idanuwansu akansa suna kallansa a tare kowannensu da fata da abinda yake buqatan Bilal din ya tabbatar.

Shi kuwa Bilal hankalinsa akan Dd babban yake sbd baisan Ababan ba Dan Bai taba ganinsa ba sai so daya Kuma da yamma ne daga nesa Dan haka Bai qarar da kamanninsa ba dan haka Yana shigowa cikeda nutsuwa da ladabi ya qarasa ciki ya Isa gaban Dd ya zauna ya gaidasa cikin girman da nutsuwa kaman yanda ya saba.

Numfashi Dd ya sake saukewa kafin ya amsa gaisuwar cikin kulawa ya masa barka da dawowa.

Amsawa yayi Yana kokarin danne tasa damuwar da tashin hankalin dayake ciki na zancen sumayyahn sbd baisan ta inda zai bullo ba Dan yasani Babu maganar karban wannan qaddararriyar maganar a cikin dictionaryn Kaantes din Dan haka yake cikin tsaka me wuyan da baisan Ina zai Saka Kansa Harma da sumayyahn ba.

Gyara murya Dd babba yayi da kyau cikin nutsuwa kafin ya fara da cewa

“Ga bako Nan a bayanka zaune ka duba da kyau ko ka Sansa Dan bakon kusan na ke.”

Juyawa yayi cikin nutsuwa ya kalli Ababa ya gaidasa jiki a mace tareda dawo da kallansa ka Dd babba Yace

“Ban Ganesa ba gaskia sai an tinatar Dani.”

Magana Ababa zaiyi Dd babba ya daga masa hannu fuskarsa ba sauki ko sakewa ko kadan
Take kwarjininsa ya cika masa Ido gabaki daya dan haka dole yayi shiru zuciyarsa na sake tsinkewa da zancen da Bilal yafara dashi.

“BILAL” Dd ya kirasa Yana kallansa Kai tsaye da son tabbatar masa mahimmanci maganar da zaiyi masa.

“Na’am”
Shima ya amsa cikin nutsuwa da jikinsa dayake bayyanarda sanyinsa a yanzu.

“Bilal wannan bawan Allah gashi Nan yazo tin safe Yace Yana son ganina bai samu damar ba sai da magrib ya Dana fita ya sameni a masallaci da wani babban zancen daya sami yarsa,

Magana yakeyi akan ‘yarsa ta hadu da tsautsayin qaruwa ta juna biyu Kuma Wanda yakeda alhakin hakan sunansa Bilal.,

Yazo ne Nan akan Kai Bilal din yake zargi da hakan kokuma Nace yazo ne kan ‘yar tasa ta basa tabbacin ka Bilal kaante din ne yayi mata wannan cin mutuncin.

Tinda Dd yafara maganar maqoshin Ababa ke motsi kaman ya karbi zancen ya qarasa sbd ganin Dd babban yakasa fitowa ka tsaye yai maganar data Tara su din sai alokacin da yakai qarshen maganar Ababan ya saki ajiyar zuciya a boye Yana zubawa Bilal idanuwansa kirjinsa na harbawa da jiran amsar dazai Bada.

Sunkuyar da Kai Bilal yayi ahankali a karo na farko dayaji kunyar Kansa data Dd babba Harma data iyayensa da basa gurin,
idan har wannan shine Ababa mahaifin sumayyah to tabbas komai ya Riga ya bayyana gaban Dd Babu sauran tsimi Babu dabara.

“Sumayyah sunanta,nine Ababa mahaifinta”…suka Ji muryar Ababan Yana fada Shima muryasa na rawa sbd matsiwa da fargaba.

Wata sabuwar kunya da damuwa Mai qarfin gaske Ce ta lullube Bilal a gurin Dan kuwa ya tabbata dai Ababan ne yazo gurin Dd babba da zancen.

“Innalillahi wainna ilayhi rajiun”
Wannan shine iya Kalmar da ya iya furtawa cikin zuciyarsa Dake harbawa da karfi.

Jin shirun Bilal da yanayinsa daya bayyanar da tsananin kunya,Dana sani da baqin ciki ya kasa dagowa ya kallesa yasa Dd babba tsayar da kallan sa akansa Yana jiran amsarsa.

Cikin kame murya fiyeda farko wannan Karan dan sirkin zafi kadan a sautin Yace

“Kayi magana a sallamesa ba zancen batawa Kai lokaci tinani bane,
Idan baka sansuba ba buqatan tsayawa nazari ko wani tinanin
ka fada Kai tsaye a sallamesa.”

A karo na biyu ya sake Jin hawaye game da kaddara sun ciko idanuwansa duk da kasancewarsa babba bame qananun shekaru ba Amma Kuma tinda komai ya zo a qaddarawan ubangiji baida kaucewa bayan fadan gaskiar.

Ba iya dago Kansa ba yakalli Dd babba ya Bude bakinsa cikin Rauni Yace

“Na Santa,Kuma qaddara Ce ta gifta Banda niyar cutatarwa ko keta mutuncinta,
Da niyar zan aureta na bibiyeta tin farko,Ina matiqar Dana sani da Bada hakuri ga wannan qaddarar data shigo.

A jejjere Ababa ya ringa jero ajiyar zuciya a boye Yana hamdala kala kala ga ubangiji Yana Jin wani farin ciki da sanyi na mamaye ransa.

Bai taba sakawa sumayyahn albarka ba sai yau din yaji zuciyarsa na Saka mata albarka da Bata fada masa karya ba,
Tinda dai Bilal ya tabbatarda ciki nasa ne ai komai ba zai zo da sauki.

Dd babba kuwa shiru yai Bai iya cewa komaiba
Suma duk sukai tsit gurin ya dauke sauti ko motsi Babu.

Minti kusan hudu a hakan kafin Dd ya motsa ahankali ya dauki wayarsa ya Saka kiran Abbakar yaransa tin na shekaru har yanzu.

Abbakar din na dagawa Dd Yace yazo yanzun nan.

Ajiye wayar yai Yana kokarin Hana Kansa bayyanarda attack din daya riskesa take a gurin Saidai daga muryarsa Bilal yagane ya samu attack take ya miqe da sauri yai Kansa Yana Kiran sunansa cikin kulawa
kafin wani yunqurin tini numfashin Dd din ya fara kokarin daukewa saiga Abbakar Yana ganin hakan hankali tashe yayo Kansa Shima.

Ababa ma hankalinsa tashi yayi ya miqe tsaye Yana fatan kada komai ya samu Dd babban a samu matsala Dan haka dashi aka hau yi masa firfita Bilal kuwa likita ya fara kokarin Kira hankalinsa a matiqar tashe.

Cikin mitinan da Basu wuce qalilan ba tsohon yake Neman rasa ransa Dan haka kasa jira sukai take Akai kaante specialist dashi.

Ababa kuwa silalewa yayi dole ya tafi gida bayan an dakatar da kowa shiga Inda Dd babban yake.

 

Kai tsaye gida ya wuce Baima samu biyawa asibitin ba Dan jikinsa koina ciwo yake Shima yau din yaci wuya Amma tinda dai buqata kusan ta samu shiga komai yazo da sauki.

Anne data kusan haukacewa a kwana daya da wuni biyu sbd rashin ganinsu benazir da rashin sanin wane Hali sike ciki yasa gabaki daya Bata hayyacinta gashi Ababan yaqi fada mata komai bare taji dan sanyi aranta.

Dan haka ma da Daren yana shigowa ya shigewarsa ko abinci Bai samu damar ci ba ya kwanta sbd gobe sammako zaiyi zuwa asibiti da Kansa zaiyi jinyar sumayyahn shi da Benazir.

******A asibiti kuwa sumayyah da Benazir sun Dan samu sassaucin zuciya Dana jiki tinda basa aikin komai sai zama da bacci,

Tinanin Anne ne kawai yake tsananin damun benazir ita datasan halin data barota
Amma koma yayane tinda bataji Ababa Yace ta mutu ba to tasan tasamu tsira kenan.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected