Dabi'ar Zuciya 35
“Saraki….wai me kake shirin aikatawa ne?,are you in your sense?” Aamir daya riqo samir a rude ya furta yana duban qwayar idanun samir din.
Hannunsa ya zame daga cikin ma Aamir yana dubansa shima
“So kake nace bazan karbeta ba?,so kake nace musu na saketa?,so kake na gayawa wannan rarraunar uwar cewa na saki diyarta kwana daya tal da daura mata aure?,wannan uwar data karbi dukkan qaddarar auren diyarta ga wanda bata san ainihin koshi waye ba?,ko kuma so kake na gayawa wannan dattijon kawun cewa na saki ‘yar ‘yar uwarsa?,aurenta baya nufin komai…hakanan bazai sauya komai ba”
“Duk da haka…..ta yaya zaia fuskanci daddy prof ka gaya masa ka daura aure ba tare da sani ko yardarsa ba?” Qaramin murmushin da iyakarsa lebe ya saki,don shi kansa yasan murmushin bai kai qasan zuciyarsa ba,shi da kansa yake gina tunanin abubuwan tashin hankalin da xasu biyo baya ya kuma yi musu fenti su fito radau kamar gaske,ciki kuwa harda sake tabarbarewar soyayya da fahimtar junan da yake tattali,wanda tayi qaranci tsakaninsa da mahaifinsa,sakamakon bambance banbamce na abubuwa masu yawa a tsakaninsu,wani sabanin ma baya sanin ainihin abinda ya haifar musu da shi,yakan zo ne haka siddan a wadansu lokutan
“Kada ka damu a abinda zan gaya masa, just wait and see what will happen”. Kanshi amiru ya dafe
“Me yasa nayi coursing maka wannan matsalar?,why?” Gajeran murmushi ya sake fiddawa
“Bawa baya wucewa qaddararsa,dama qaddarar tawa ce” itace amsar daya bashi,kafin amirun ya juya zuwa bigiren da kaltume ta wanzu akai tana biye dasu,har yanzu fuskarta shafe da hawaye da qananun majina
“Tana bayanmu ne fa saraki”
“Garinsu ne,ba zata bata ba” ya amsa masa a gajarce.
Shuru ne ya zamar musu babban dan rakiya,har suka riski motocinsa guda biyu dake dakon jiran dawowarsa,tunda taga sun nufi motar ta fara takawa a hankali,cikin tsoro da fargaba,mamaki kuma ya maye gurbinsu gaba daya sanda taga amiru ya bude murfin motar ya shige,shima samir din ya bude daya bangaren da niyyar shiga,sai taga ya fasa,ya waiwayo yana dubanta,xuwa sannan ta tsaya cak maqale da kayanta tana qare musu kallo
“Zoki shiga”yayi maganar yana bude murfin daya motar da tafi kusa dashi,sannan ya sake maida dubansa ga baqar fuskarta,wadda tsabar tashin hankali gami da kuka ya qara mata shining,ga kuma hasken rana dake dukan fuskar tata.
Kanta ta girgiza alamun a’ah,don tanq jin cewa koda sama da qasa zasu hadu ba zata yarda ta shiga wannan abar da taji suna kira da sunan mota ba,hasalima wajen gudu take nema,mutanen da bata taba ganinsu suna yawo dako keke ba a karkarar tasu,amma su suka bude wannan abar mai suna motq zasu shiga?,to shin waima ina suka samota?.
“Ki shiga mu tafi,lokaci yana qure mana” ya fada wannan karon yana dan dava murya.
Da qarfi ta girgiza masa kanta,donta fuskanci kamar bai fahimci na daxu ba,amiru wanda yake kallon duk abinda ke faruwa ta mirror,yana kuma qoqarin boye dariyarsa,kasancewarsa ma’abocin dariya koda yaushe,ya leqo da kansa ta window sanda yaga ta fara takawa da baya da baya alamun barin wajen.
“Saika mata dabara,da alama batasan irin wadan na motocin ba” dauke kansa yayi daga duban amiru,ya maida ga kaltume data fara ja baya sosai da inda suke,ya fara takawa a hankali zuwa wajenta,yana mata bayani ta yadda yake saka ran zata fahinceshi,saidai ko kusa ko alama babu alamun hakan,bisa dukkan alamu ma takowarsa zuwa inda take din qara tsoratata yakeyi,don sai qara hanzari kawai take wajen ja da bayan,daga bisani ma data lura ya fita hanzari,saita juya da sauri zata take,hakan yasa ya rufa mata baya cikin zafin nama.
Taku biyar kyawawa ya cafkota,ya damqi hannunta sosai ya fara tafiya,saita turje tana zubar hawaye tare da roqarsa ya barta ta koma wajen ummanta,kada ya cutar da ita,saiya waiwayo ya kalleta,a yadda tayin,babu wani bayani da zata gane,bata masa lokaci kawai takeyi,ya kalli siriein hannunta,ko ba’a gaya masa ba bazatayi nauyi ba ko na sisin kwabo,saboda haka ya dagata cilak ita da qullin kayanta ya nufi bakin motar yana dauke kai gamida riqe numfashinsa,saboda fargabar kada ya shaqi wani abu da zai sanyashi amai ko ya yamutsa masa ‘ya’yan hanjinsa.
Ihu ta saki sanda ya sakata a motar,ya tabbatar idan ya canza mota ya barta a nan hauka kawai zata musu,don haka shima ya shiga bayan ya bada umarnin qara qarfin sanyin ACn dake aiki.
Tsawa ya daka mata wadda ta sanyata curewa waje daya,ya fidda dukka idanunsa waje yana dora yatsansa saman lips dinsa alamun tayi masa shuru,ta kasa koda qwaqwqwaran motsi kuwa,sai kanta data cusa tsakanin cinyoyinta tana rawar dari na tsoro daya cakuda da kuka da kuma sanyin da aka balbalawa motar,tana jin a ranta tata ta qare,ita kuma ta wannan hanyar ce sanadin barinta duniya?,ashe babu nisan tazara tsakaninta da bilalunta.
Wayarsa ya fidda ya kira amiru ya gaya masa su wuce gaba a wannan motar zai tafi,ya kashe wayar ya ajjiye ya fidda iska daga bakinsa
“Inason mu isa gida da wuri” ya bawa drivern umarni
“An gama yallabai” ya fada yana tayar da motar cikin sauri.
Shuru ne ya ratsa cikin motar,babu abinda yake tashi sai sheshsheqar kukanta can qasa,tsahon wasu mintuna,yaja qaramin tsaki yana gyara zamanshi,saboda yana jin kukan a matsayin wani abu da zai sake takurashi.
Tafiyar awa guda da wasu mintuna motarsu tayi parking a parking lot na gidan,ya sanya hannunsa zai bude qofar motar,saiya tuna da ita,ya waiwaya ya dubeta,har yanzu tana zaune a cure waje guda,saika dauka cewa a saman wuta aka azata
“Fito” ya ambata sanda ya bude mata murfin motar,ta daga kai da sauri,idanuwanta suka kan ginin da idan a mafarki ne,banda a zahiri take sai tace gidanta ne na aljanna,aljannar da ake bata labari,to amma wannan kuwa babu ko tantama duniya ce,cikin gidan masu yanka kan mutane,saita fashe da kuka,ta san cewa kwananta ya riga ya qare
“Don Allah kayi haquri karka yankemin kai,wallahi ba laifina bane” ta fada jikinta yana rawa,idanunsa ya lumshe ganin tana neman bashi wani ciwon kan,wannan wanne irin xallar qauyanci ne,saiya bude idanunsa bayan ya saki dogon tsaki
“Kinga….ki fito nace miki,bakiga mutane ba gasunan suna wucewa?,ta yaya za’ayi yankan kai kamar haka?” Sam taqi yarda da zancansa,har sai da amiru ya qaraso wajen,cikin hikima da hilata irin tasa ya fiddota,tana qanqame da kayanta tabi bayan samir,yayin da amiru ya wuce sashensu kai tsaye.
Duk tafiyar second daya ko biyu sai ya waiwayo ya jirayeta,da qyar take daga qafafunta tana saukesu,kai kace tana tafiya ne saman qaya,qafafunta babu takalmi,duk wani motsi tsoranta yake nunawa muraran.
Kallo daya zakayi mata ka hangi zallar isa izza mulki da kuma iko a tattare da ita,dukkansu sun bayyana kansu ta yanayin shigarta,uwa uba kuma yanayin fuskarta dake a hade.
A zahiri jarida take karantawa,yayin da kuma a badini tayi nisa cikin duniyar tunani da kuma lissafe lissafenta da bata so su kaucewa qa’idarta kosu subuce mata,tayi wannan zaman ne mintuna kadan bayan sun gama waya da mahaifiyar jauhar hajiya na’ima,gefanta najwa ce data nutse cikin luntsuma luntsuman kujerun falon,hannunta dake da wayarta tana latsawa,ba kamar sauran lokutan da zaka sameta dauke da tarin takardu ba,wadanda take jin sune tamkar makwafin rayuwarta.



