Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi'ar Zuciya 60

60

A hankali bibi ta sulale a wajen saboda kasa qarasawa da tayi zuwa wajen momma raihanan,duk da burin hakan da takeyi,amma sam qafafunta sun kasa daukarta,ganin abun take kamar almara,kamar cikin irin mafarkan data saba yi,idanunta suna iya hango mata sanda samir da momman suma suka durqushe zuwa qasa,sai giftawa kaltum da amiru suna qoqarin dagata.

*******. *****. *****. *****

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke bayan dawowa da yayi daga dogon tunani,yau babu kowa a parlor din nasa,samir da amiru sun fita sun shaida masa zasu wani waje,jawahir dinsa ta shiga makaranta,mommy ta tafi asibiti a duba mata bayanta dake ciwo,najwa kuwa dama sau daya tal take shigowa dubashi……sau dayan da idan zai yiwu da ya hanata shigowa ma,saboda wasu tarin dalilai,da kuma rashin alfanun zuwa dubiyar tasa ma gaba daya.

Ko sau daya yaga gilmawarta kota mahaifiyarta sai yaji wani abu yana motsa ranshi,abun da har yanzu yake masa zafi da ciwo a qirji,kullum addu’a yake dare da rana,tun daga wancan lokaci kam rabbus samawati ya warware dukkan wani qulli dake cikin rayuwarsa.

Wannan zaman da yake a yanzu yana yinsa ne badon bai warke ba,a’ah,yana yinsa ne saboda jinyar zuciyarsa,a duk sanda ya tuna irin musgunawa da miyagun kalaman da yake jifan samir dasu a baya sai yaji zuciyarsa ta quntata,babban abun tambayar shine……a koda yaushe jidda bata hanashi jifan samir din da miyagun kalamai,saidai kawai fa nuna a fuskarta,bata taba tursasa samir dai dai da rana daya yayi abinda yakeso ba,koda kuwa shi baya so,inda raihana ce zata bar haka ta faru?……

Gabansa yayi wani muguj faduwa da tuna raihanan da yayi,a hankali tunaninsa ya koma baya,zuciyarsa ta shiga tuna masa wace raihana?,tun daga haduwarsu har zuwa rayuwarsu…….

“Daddy……kayi baquwa” muryar najwa ta katse masa dogon tunanin da ya fada,ya daga kai yana duban yarinyar,duba me kama dana qurilla,sai ya buda bakinsa a hankali

“Wacece?”
“Hajiya shuwa,…..maman fawwaz,tace saqo tazo kawo maka” mamaki sosai ya kamashi,a iya tsahon saninsa da hajiya shuwan aminiyar matarsa ce,tun suna da jajayen sawayensu kawo yanzu,babu kuma abinda yake hadasu da ita illa gaisuwar mutunci,to amma,baisan wanne irin saqo bane wannan

“Ki rakota ta shigo” ya fada yana gyara zamansa saman kujera,sai ta juya da saurinta ta fice,tana addu’ar Allah yasa maganar nemawa fawwaz aurenta ne,saboda tasan indai hakan ta faru tofa burinta ya cika,daddynta bashi da matsala,yana qaunarta,hakanan yafi mummyn sauqin kai.

Daga kai yayi yana amsa sallamarsu ita da fawwaz sannan yayi musu izinin zama,suka gaisa sukayi masa sannu da jiki,sannan najwa ta juya tana cewa

“Hajiya bari na kawo muku abun motsa baki” daga haka tayi gaba tana jin dadi cikin ranta,shuru ya ratsa wajen na wasu sakanni sannan hajiya shuwa ta fara magana

“Nasan zakayi mamakin jin cewa gurinka nazo…..nazo kawo maka saqo ko?” Kai ya gyada yana dubanta

“Qwarai kuwa” saita motsa jakar hannunta me dan fadi da yalwa

“To ba abun mamaki bane,duba da cewa…..jidda ta buqaci duk wani abu nata dake hannunmu na dawo mata dashi…..to…..kasan mu da riqon amana da kuma cika alqawari,nazo na taras bata nan,to banason baiwa diyarta kayanta tunda da alama diyar halin mahaifinta tayo…..kayi haquri,bakai nake nufi ba,domin kai din ba mahaifinta ba,kai ubanta ne,uba kuma irin na riqo,wanda ya dauki nauyin dukkan wasu nauye nauyen na diyoyin daba nashi ba har zuwa sanda suka zama mutane……” Takai qarshen maganar tana ciro wasu takardu daga jakarta,sannan ta dora idanunta ga daddy wanda ya zuba mata ido sosai,yana son gaya alamun hauka ko tabin hankali tattare da haj shuwa da take furta wadan nan kalaman

“Nasan ka shiga mamaki ko?,to ina tafe da hujjata ta gaya maka haka,ungo wadan na takardun guda biyu” ta fada tana miqawa fawwaz su,shi kuma ya miqawa daddyn sannan ta dora

“Takardar farko takarda ce ta asibitin daka taba kwanciya jinya sanda ka samu hadari shakaru talatin baya,a lokacin da danka samir bai wuce shekara uku a duniya ba,baya nine na cewa wata jijiya cikin jikinka da zata iya bayuwa ga samun cikin matarka ta tabu,saidai daga shekara uku zuwa hudu zata iya komawa kan aikinta,matarka zata iya daukan ciki harma ta haihu…..,a wannan lokacin raihana cikin gidanka bata da wani amfani,saboda siddabaru da kissa da jidda tayi amfani dasu ta shiga tsakaninku…..don haka jidda ita ta karba takardar.

Da ganin bayanan jiki hankalinta yayi matuqar tashi,tayimin bayanin cewa indai haka ta kasance shikenan bata da wani riba a aurenka,saboda raihana nada da namiji,ita kuwa bata da qwai ko guda daya,yaushe zata yita zama har sai ka warke?,warkewar da babu tabbas?ita data shigo da burin tayita haifa maka yara,dalilin da ya sanya duk cikin da raihana ta dinga samu bayan samir ta dinga lalata mata shi kenan ba tare da saninku ba gaba dayanku….” Daga kai daddy yayi da sauri ya dubeta,kai ta gyada masa alamun tabbatarwa sannan kuma taci gaba

Da wannan dalilin jidda ta boye wannan takardar bata bari kowa ya gani ba,qarshe ma saboda gudun bacin rana ta bani ajiyarsu,tun daga ranar jidda ta shiga neman hanyar da zata samu ciki,dalilin da yasa ta komawa ainihin saurayinta daya fara yi mata ciki har sau biyu a duniya.

DAGE cikakken dan sara suka,kuma tantiri,wanda ya taso a gidan da babu cin yau babu na gobe,bangar siyasa da daba sata da shaye shaye shine aikinsa,ba wani jimawa kuwa ta samu cikin NAJWA dashi,ta kuma haife maka,ka amsheta a matsayin ‘yarka…….,bayan wannan tasan yadda ta hada masa TARKON da ya kashe mutum aka kaishi gidan kurkuku,daurin rai da rai,yanzu haka yana can.

“La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin” daddy ya furta kansa a qasa,hawaye na qoqarin saukowa daga idanunsa

“Bayan ta haifa najwa tun kafin takai dage gidan kurkuku dama tace ba zata koma masa ba,da alama yara mata iya baiwa mahaifar mace,don duk cikinta na baya guda biyu data zubda mata ne,saita koma kan lecturer dinta data qyalla idanu ta gani,ta kuma samu labarin ‘ya’ya maza gareshu guda hudu rigis,burinta bai cika akanshi ba,sai satoshi tasa akayi,ta kuma bashi abun gusar da hankali yayi mata yadda takeso,tsahon wata biyu yana aje a wajenta tana yadda takeso dashi ba dare ba rana,bata sakeshi ba sai data tabbatar ta samu abinda take da buri,wanda bayan komai ya kammala ya shiga baqinciki da takaici,abinda kusan yayi ajalinsa kenan,ya hadu da hawan jini,wannan shine mahaifin jawahir”

Kamar ta buga masa guduma aka da qahon zuciya haka yaji,saboda bai taba tsammatar hakan akan jawahir ba,yarinyar da tayi matuqar shiga ransa,yarinya mai hankali da nutsuwa….tausayi da kuma sanin ya kamata,har gwara najwa….tun daga ranar da yaji bala na waya da ita….tana bashi umarnin ya watsar da daddyn bisa titi bayan an tsinke musu burki yasha jinin jikinsa,jikinsa yake bashi tabbas ba diyarsa bace ta halak,saboda abune mai matuqar wuya ɗa na tsantsar halaliya,dan da aka auri mahaifiyarsa bisa tafarkin shari’a,aka haifeshi bisa tafarkin shari’a ya iya kashe mahaifansa

“Sanda raihana ta sake samun ciki abun yayi matuqar daga hankalin jidda,kuma ya tabbatar mata da cewa lallai ka samu sauqi,tana tsoron kada raihana ta sake haihuwa ta samu da namiji ita tana zaune,abinda yasa ta yanke shawarar kau da ita,ta kuma yita qoqarin ta samu haihuwa da kai koda sau daya ne…..saidai inaa,bata samu wannan rabon ba har yau……..

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected