Dabi'ar Zuciya 46
46
“Ki kira jawahir mu wuce,saiki zauna da hajiyan” shine abinda yace da ita sanda ta bude motar xata fita,yayin da yake zaune a nan wajen ba tare daya motsa ba
“To” ta amsashi dashi,sannan ta wuce zuwa cikin gidan.
Ta taras jawahir harta kwanta abinta,sai mubina dake zaune,idanunta sun dan canza kala,bata sani ba kuka tayi kome tayi oho.
Hajiya qaramar ta nuna jin dadi sosai da taji kaltum din zata zauna da ita,saidai tace dama yabar jawahir din ta kwana kawai
“Gwara naje gidan hajiya,gobe da makaranta,kuma ban debo komai na zuwa makarantar ba,amma kafin ki warware zan dawo na kwana idan kaltum ta kusa komawa,saimu koma tare…..hajiya kindai daukemin qawartawa da take debemin kewa” jawahir ta fada tana ɓata fuska
“Yo basai ki hanata zama ba?”
“Ni na’isa hajjaju,Allah ya huci zuciyarki,aro amma na baki ita” tayi maganar tana roller mayafinta,dai dai nan kira ya shigo wayarta,ta duba da sauri ta suri jakarta
“Ya saraki,babu jira”
“Dakata,zaku sauke mubina gida,jikin hajara ya motsa zata kula da ita” hajiya qarama ta fada,dai dai sanda mubina ta fito dauke da qaramae jakarta,idanunta har yanzu a jirkice suke
“Khairan in sha Allah,ki daina wannan damuwar,haka zakije kina daga mata hankali maimakon ki kwantar mata da hankali ki bata qwarin gwiwa,haba….banason irin wannan sakarcin” kai mubinan ta daga tana dan goge fuskarta,ita kadai ce tasan irin tashin hankalin da takeji cikin qirjinta tun sanda taji daga bakin jawahir cewa an kusa kai kudin aure da sanya rana na samir din da wata wai ita jauhar,duk da umminta bata da lpy amma batakai ta koma gida ba,ta yanke ta shawarar gwara ta koma gidan qila tafi samun nutsuwar tunanin da zaya kawo mata mafita,kafin ta waiwayo ta dawo gidan,don tunda ta fuskanci alaqarshi da gidan taci alwashin sai inda qarfinta ya qare.
*********Washegari da wuri ta tashi ta kammalawa hajiya qarama komai daya kamata ayi cikin gidan,hatta da abincin da zataci,sannan tayi shirin makaranta,wanda already tun kafin su kwanta hajiyan ta gaya mata wanda zai dinga kaita din,don haka ta fice zuwa farfajiyar gidan inda yake jiranta.
Harta shiga ta manta batasha maganinta ba ta dawo ta dauko,ta ballosu tana kallonsu a tafin hannunta,murmushi ya qwace mata saboda tuna abinda ya faru a jiyan da tayi.
Can wani bari na zuciyarta taji yana burgeta,a caring person,sunan ya dace dashi qwarai,da alama ya damu da damuwar wasu,ba iya kanshi ya sani ba,she never expected akwai mutum irinsa a yanzu,a rich and handsome man,amma bai dauki rayuwarshi da wani zurfi ba,saita afa qwayoyin da sauri ta bisu da ruwa a gurguje ta fito saboda tunawa da tayi tabar mai kaitan yana jiranta.
A lokaci irin wannan ba kasafai malamai ke shigowa aji ba,saboda shirye shiryen fara exam na qualifying da sukeyi,koda sun shigo din ma revision ne kawai akeyi.
Yauma kusan ajin ba malami,masu hira nayi,masu wayo kamarta sun kama litattafansu suna dubawa.
Duka wadanda seat dinsu ke kusa da nata wadanda suke komai tare idan ya kama ta bawa hannu suka gaisa,suka dan taba hira da bata wuce ta minti biyar ba,sannan ta karbi note book din saliha ahmad da zata kwafi wani note,ta koma seat dinta ta zauna bayan ta ciro nata littafin ta fara kwafa.
Tana aikin tana sauraren hirarrakinsu,wanda dama idan suka hadu basa gajiya,kusan dukka hirar tasu kan samarinsu ne da kuma aure,kowacce burinta data gama nan tayi aure,wani abun ta girgiza kai,wani tayi murmushi,tsahon lokaci har suka cika mata ciki,saita rufe note din da takeyi ta dubesu tana murmushi
“Wai nikam….duk cikinku babu wanda yake sha’awar yin karatu ne sai aure aure kawai?” Dukka suka waiwayo suka kalleta,sai suka sanya dariya,saliha ahmad ce ta amsa
“Wa yake ta wani karatu?,ai idan ka dace da gidan mijin qwarai karatu duk wahala ce,wanda akayi ma Allah ya amfana,tunda duk tsiya da secondary School certificate ba wanda ya isa ya kalleka ya kiraka da sunan jahili”
“Kulsum fa batasan dadin aure ba” madina ta fada tana dariya,sai kaltum din ta jefeta da harara
“Sannu uwar masu gida,keda kikayi ai kin sani” dariya suka sake yi
“Ba haka nake nufi ba,ko hirar akefa shuru kike ki zuba mana ido,iyaka naki sauraro,baki bada naki gudun mawar” littafinta taci gaba da budawa da sunan ci gaba da rubutunta sannan ta bata amsa
“To me na sani bare na samu ta cewa a kai,kudai da kuketa naci Allah ya bada sa’a,nikam karatu zanyi”
“Aure ai baya hana karatu,malama ki tsaya ki saurari ni’imar aure,da kanki zaki canza ra’ayi,kinsan dadin soyayya kuwa da auren masoyi?” Bakinta ta tabe bata kuma tanka musu ba,saidai kunnenta yana tare dasu sanda take rubutun.
Abubuwa da yawa da suke fadi yatsaya mata a rai game da soyayya,itadai ta sani taso nasuru kuma sunyi soyayya,amma abubuwan da suke fada din sai take ganin kamar qarya ce kawai,don duka bata ji wannan akan nasurun ba.
Sun jima suna hirar tana dauke wasu abubuwa daga ciki,har zuwa sanda malaminsu na maths ya shigo,kowa kuma ya koma hankalinsa ya bashi hankalinsa.
Sanda ta koma ta samu hajiya qarama parlor,ita da baqi da alama masu dubiya ne.
A ladabce ta gaidasu sannan ta sake duba jikin hajiya qarama
“Da sauqi kaltum,kinsha hidima,na tashi na tarar har kin gama komai,Allah yayi albarka” murmushi ta sake kana ta amsa da amin,amma itakam bataji wata wahala ko wani abu ba,dadin jikinta ma taji sosai a yau din,saboda tayi irin ayyukan data saba sanda tana gida,sai takeji jikinta yayi dadi.
Dakin da hajiya qarama ta bata ta shiga,dakine dabam ba wanda mubina ke zaune ba,shima wannan din akwai komai a ciki,tana mamakin yadda suke ajiyar dakuna haka da komai a ciki amma kuma babu wanda yake zaune a ciki.
Uniform dinta ta cire ta duba kayanta data tarar an kawo mata,duk da basu wuce kala biyu ba ta sanya wata atamfa riga da zani,saita daura alwala tayi sallar azahar,sannan ta dawo parlor ta tambayi hajiya qarama abinda za’a dafa
“Na bar miki zabi kaltum,nasan ba zakiyi zabin banza ba” murmushi tayi ta juya zuwa kitchen din.
A nutse kasancewar babu kowa cikin kitchen din ta fara duba abubuwan da suke ciki,kafin daga bisani ta yanke abinda zata dafa din.
Koda ta kammala la’asar liqis,har yanzu baqin hajiya qarama basu tafi ba,saita koma daki ra jirayi sallar magariba,wadda bayan ta idar dinma taji sabuwar hayaniya,da alama wasu baqin tayi,saitayi xamanta a dakin,har tayi sallar isha’i tanajin motsin ‘yan dubiyar,tasan babu abinda hajiyan zata buqata,don ta riga data hada mata komai,kuma itama bata jin yunwa,don haka saita bude school bag dinta,ta ciro wani novel da saliha ta bata ta fara karantawa.
Tun batayi nisa ba taji karatun ya fara gundurarta,saboda wannan shine lokaci na farko data fara karanta novel a rayuwarta,yadda suketa maganar yasa ta dinga kushe abun,saidai yadda suka raja’a kan don bata karantawa ne yasa abun bai burgeta,amma ta gwada ta gani,akwai qaruwa sosai a ciki,duk wanda kuma yayi winning su ko shi to akwai wani abu da za’a sashi yayi,kuma dole yayi accepting koma mene,ta yarda ta kuma karba din.


