Dabi'ar Zuciya 47
47
D/Z
A gaba ta zauna kamar yadda tsarinsa yake,suna shiga motar jauhar na kiransa a waya,saiya hada wayar da speaker din motar yana amsa wayar.
Duk yadda taso dauke hankalinta daga hirar tasu hakan ya gagareta,saita samu kanta da bibiyar duk wata hira da jauhar din ke masa,shi kuma yana qoqarin amsata,wanda kana jin yadda yake amsawar dauriya kawai yakeyi da qoqarin tursasawa kansa,don hirarma batayi tsaho ba yace mata
“Am on my way to office,i will call you when I’m back”
“Ok honey,byeeee” ta fada da wani baby voice da take amfani dashi wajen ganin taja hankalinsa.
Shuru ne yaci gaba da wanzuwa,wanda mintunan da suka qara basu wuce biyar ba ya tsaida motar bakin makaranta,ta dauki jakarta ta fita tana cewa
“Na gode” ta maida murfin ta rufe bayan tabar masa sauran qamshin turaren data durfafa a yanzu.
Yana motsa motar zuwa gaba yana hangen sanda ta shige makarantar ta madubi,saiya dauke idonsa ya maida hankalinsa sosai ga tuqinsa,yana qoqarin daga wayar amiru data shigo.
Shaida masa yayi yana nan dawowa da yammacin yau,amma zai dan zauna gidan hajiya qaraman kafin ya qaraso nan gida,yaji dadin dawowar tasa wannan karon da wuri,sabida amirun shi daya ne amini ga samir,wanda yake iya tattauna matsala ko damuwarsa dashi,hakanan yakan samu courage na aiki a duk sanda amirun ke cikin kamfani,saidai dole wani lokaci akan rashi a kusa,sabida shike kula da dukiyar da mahaifinsa ya rasu ya barmusu shida ‘yan uwansa mata biyu dake aure a wata qasar.
Yau din tana aiki tana duba novel din,don da qagu taga qarshensa,sosai labarin yake dibanta gami da tafiya da ita,batasan sam haka soyayya take ba sai yanzu,batasan haka rayuwar auren masoya take ba sai data karanta littafin,saita tsinci kanta tana hasaso kanta da gina rayuwar soyayya irin ta cikin littafin,amma kuma dawa?,a yiwa kanta tambayar data katse dukka zaran tunaninta.
Idan ta dauko soyayyar da tayi a qauye sai taga ashe badan badamarsu kawai sukeyi,basusan meye ma ainihin soyayyar ba,kawai wani abu suke mai kama da wasan kwaikwayo.
Zamantakewar aure a karkararsu kuwa dama ta jima da sanin cewa ana yinta ne illegally ,abubuwan dake faruwa kwata kwata basuyi kama da zaman aure ba.
Ita kadai a kitchen tana aikin abinci tana sakin murmushi a duk sanda ta tuna da labaran novel din,sun sanyata nishadi ba kadan ba,abinda kuma ya jawo mata delay kenan,tayi nawar gama girkin da takeyi,har akayi kiran sallar magariba.
Ajjiyewa tayi taje tayi sallar sannan ta dawo tana duba abinda ya rage din,a hankali tanayi tana duba sabon novel din data karbo din.
Bakwai na dare motar tayi parking a parking lot na gidan,zaratan samarin guda biyu suka fito daga cikin motar,fuskokinsu wasai,suna taba hira har suka qaraso qawataccen parlour din hajja.
Tana daga zaune taji sallamarsu,murmushi ya wadata a fuskarta,farincki ya cika zuciyarta,ta bisu da kallo tana musu fatan dacewa da samun mataye na gari,a yanzu babban burinta shine taga dukkaninsu sunyi aure,sabida tsakanin ita da yayan nata yara maza biyune rak dasu,sai mata,ita uku shi biyu,tana fatan wadan nan da Allah ya basu yaci gaba da albarkacesu,su kuma tara musu zuri’a me dumbin yawa.
Waje suka samu suka zauna cikin nuna mata kulawa,amiru ya zamo ya gaidata yana mata sannu da jiki,yayin da samir shima ke sake mata sannu kamar ba daxu yabar gidan ba.
Hira suka fara tabawa kadan kadan,wadda ta shafu tafiyar tasa,da kuma abubuwan da suka faru bayan bashi nan.
Karo na kusan hudu wayar samir tayi tsuwwa yasa hannu yayi rejecting kamar yadda yakeyi tun dazu,hajiya qarama ta dubeshi
“Ka daga mana ba kiranka akeyi ba?” Saiya jinjina kai
“Barsu hajiya,idan na gama komai zan kira” maganar amiru ta katse zancan
“Nifa tunda na shigo nakejin qamshin girki hajiya,kuma anmin fuska,a amatsayina na baqo yaci ace an tarbeni da wani kyakkyawan girki nan” kallonsa tayi ta tabe baki
“Idan abun bai maka dadi ba kayi zuciya ka kawomin mata qarshen watan nan,ni dama na gaji da ganinku wallahi a gabana,shi wannan kamae bashi da idanu saida aka zaba masa mata,wadda har yanzu nikam ban gama yarda da ingancinta ba,kai kuma har yanzu shuru,to gwanda gwanda shi da kai ma” gyara zamansa yayi sosai yana duban hajiyan
“Wato hajiya kada ki damu,tana qarasa NYSC zan gabatar miki da ita in sha Allah” baki ta sake tabewa
“Zuwa yaushe kenan?”
“Nan da wasu ‘yan watanni ne,tana dawowa” kai ta dauke haushi yana cikata,badon sanin halin yaran zamani ba,da tuni kowanne ta zaba masa mata sun aurar dashi an huta,to amma ita kanta tana adawa da auren dole
“Data gama abincin da tuni ta kawo,amma yanzu ma nasan tana dab da gamawa” ta amsa musu,sai samir ya miqe,don da gasken shikam yunwa yakeji,wunin yau banda baqin coffee babu abinda ke cikinsa,sai cake guda biyu
“Bari na samo wani abun”
“Yauwa mutumina,ka hado dani please” hara rarsa yayi
“Idan ka matsu kaje ka dauka da kanka,yaron gidanka ne ni?” Dariya ya saki
“Ban isa ba,ataimaka min” bai sake ce masa komai ba ya wuce cikin kitchen din.
Bai lura da ita ba sai daya isa cikin kitchen din daga bakin qofa,saiya dakata a hankali da tafiyar da yakeyi din,tana tsaye riqe da littafin tana karantawa,fuskarta na fitar da wani murmushi dake nuna nishadin da zuciyarta ke ciki.
Sanye take da daya daga cikin kayan da jawahir ta bata,high tummy skert me wata belt a jikinsa me fadi wadda gabanta ke dauke da tambarin kamfanin DG daya bayyana asirin shafaffen cikinta,daga baya kuma mazaunai da qugunta da suka fara bajewa suka bayyana,sai long sleeves t.shirt turtle neck wadda ta dace da kalar peach din skert din me adon green,dan kwalin kanta shima peach ne me santsi sosai,wanda ya hadu da santsin gashinta ya hana dankwalin zama yadda ya kamata,hakan yasa ya zame daga kanta ba tare data sani ba.
Fuskarta yabi da kallo,fatarta data koma chocolate colour ta haska sosai cikin peach color kayan data sanya,daga gaban goshinta gashin kanta ya kwanta sosai ya sauka zuwa kafadunta.
Wani motsi yaji zuciyarsa nayi,yabita da kallo sanda ta furta
“Yes,anzo wajen” qasa qasa bada wani qarfi ba,saboda laushi da zaqin murya da Allah ya bata daya dade da sani tun a qauyen dinya,saita kife littafin,ta tafi ta juya miyarta ta kuma dan dana.
Fararen idanunta da suka qara girma da gaske ta dinga rarrabawa bayan ta gama dandanar miyar taji da sauran tsami,saita ajjiye ludayin,ta matsa gaba kadan gaban wata locker ta jikin bango dake sama,inda hajiya ta nuna mata nan suke ajjiye kanwa koda akwai buqatar amfani da ita,tasa hannunta ta bude locker tana fatan Allah yasa tsahonta yakai,saboda ta kere mata sosai.
Hannunta ta sanya ta laluba sosai,saidai bataju komai ba,saboda gwangwanayen sun shige can ciki,don haka ta duba hagu da damanta ko akwai abinda zata taka takai saidai babu,abinda yasa ta fara yin dage kenan tana tana ta zura hannu amma a banza.
Murmushi ya qwace masa saboda yadda yaga tana yin dagen,gami da tsalle duka,ya sauke hannayensa daya rungume a qirji,ya fara takawa a hankali zuwa inda take tsayen.
