Jahilci Ko Al’ada Complete Hausa Novel
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
‘ Complete Hausa Novel️
Uwar batooler ️
Bismillahirrah manirraheem
Duk abunda da zan rubuta wanda yake dede Allah alfarman Rasulullahi Sallallahu Alaihi laihi Wasallama Rabbi kaban ladan masu karantawama kabasu ladan wanda yake badede ba astagfirullah allah kayafeni kayafemu duka
Allah karabamu da abun da zai ruɗemu dazamubar ibadanmu danshi
Inkina karanta littafina aka qira sallah baki tashi kinyi ba, nide ban yafeba indai har hakan ya shafeni
Mijinki
Iyayenki
Yayanki
Baqonki
Dukwani mai haqqi akanki dan darajar Allah kada sanadin littafina ki tauye masa wannan haqqin plsss
banyardaba asauyamun littafi kokuwa asayarmun dan wannan nacikin don haka inma ance na sayarwa ne ba da yamun ba
Ayi karatu lafiya
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw
!! !! !!
‘
.
– / . ‘
‘
– 250 – 2
– 5 – 500
– 75 – 750
– 25 – 25
– 50 – 5
– 75 – 75
bashi ( )
/
.
……
امى بتولة
️ 1_2
Yarinyace qarama wacce ataqaice ba zata haura shekara 14 da haihuwa ba, take ta aikin kwarara amai a tsakiyar ɗan madedecin gidan nasu.
Gidane madedeci mai ɗauke da ɗakuna huɗu 4 sai kuma ɗan rumfa haka da alama na dabbobinsune sai madafi(kitchen) a gefe sai kuma bayi(toilet).
Amai take kan yi, wata mata ce naga ta futo daga banɗakin nasu, ta ajiye butan dake hanunta sai ta wuce ɗaya daga cikin ɗakunan gidan, tayi kaman ba taga yarinyar dake ta kakarin amai ba. can wata mata a ɗaya ɗakin ta ɗaga labule ta leqo, da taga shigewan wannan matar ɗaki sai ta taɓe baki tace “dangin jarababbu kawai haka zaku fama ta mutu ma kece da asara” sauqe labulen tayi ta koma cikin ɗalibta.
Wata yarinyace yar shekara 12 ta shigo gidan tana ɗan tsallenta da alama daga aika take, ganin ƴar uwar tata a halin da take a saba’in ta yasar da ledan hanunta tayo wajan yar uwar tata tana cewa “Addah me ya sameki? ina Inna da Mama? Sai ta fashe da kuka ganin yacce ƴar uwar tan ta galabaita, ɗakin Innar tasu ta shiga na wacce ta futo daga bayi amma ba jimawa can ta fito tana kuka tayi ɗakin ɗaya matar.
Muryar matar naji tana cewa “ta mutu mana ina ruwana ita uwar ta bata kallonta ne dangin jarababbu kawai ba zan fito ba, ke hassu zaki ficemun a ɗaki ko sai na ɗau samira nayo kanki dashi” sai yarinyar ta fito tana kuka wanda qarshe ficewa tayi a gidan gaba ɗaya tana kuka.
Wannan yarinya mai aman kuwa sulalewa tayi qasa ta faɗi dan da alama suma tayi dan ta jikkita sosai.
Ba jimawa wannar yarinya da matar tacewa hassun ta shigo gidan ita da wata stohuwa, Salati wannan tsohuwan tayi ta ɗaura hanu akai tace “na shiga uku ni merama daso uwar isa, yanzu dan tsabar rashin kirki da mutanen gidan nan ke fama dashi ace akwai mutane a gidan amma akabar mun jika zata mutu” sai ta nufi wajan yarinyar da ta jima da sumewa.
Mama ce ta futo ɗaki tana cewa “baabaa sannu da zuwa yanzu nima nakeson fitowa dubata naga ko lafiya ina sallah naji kaman ana amai”
Kota kanta stohuwar bata bi ba tace “ke hansai zoki kamamun ita mu kaita ɗakinku” hassu tazo ta tallafawa stohuwar suka kaita cikin ɗakin nasu jikinta gaba ɗaya ya sake kaman babu rai ajikinta, ita dai hassu sai hawaye ita kuwa stohuwa sai masifa take yi”
Shigowa ɗakin Mama take qoqarin yi ita kuwa stohuwan na qoqarin fita, kallonta tayi tace “kinsan Allah da girma yake lami in kika shiga ɗakin nan sai na gwada maki ke qaramar ƴar daba ce, munafuka kawai wato indai ita indon bata san zafin haihuwa ba ke da aka bawa yarinyan bakisan zafin rashin ɗa ba, kuna gidan nan amma jikata na qoqarin mutuwa”
Sanin halin stohuwar ya sanyata ja da baya bata ce komi ba.
Ruwa ta ɗebo a randa tazo ta wuce Mama lami a qofan, qwafa tayi ta shige ɗakin.
Yayyafa mata ruwan tayi tana cewa “ke takwara tashi kinji ta Allah ba tasu ba, tambaɗaɗɗun iyaye kawai”.
Dogon numfashi yarinyar taja, ganin haka sai stohuwar taji sanyi a zuciyar ta tace da Hassu “ke kuma kin wani tasamu gaba kina hawaye kaman ance maki ta mutu tom takwarata ba mai mutuwa yanzu bace kema aniyar ki ta biki, tashi ki kawo mun ruwa a roba me ɗumi maza-maza yi saura”.
Tashuwa tayi ta fice a ɗakin, inda tayi sa’an samun tukunya cike da ruwa akan murhu wanda har ya tafasa, roba ta duba ta ɗiba ruwan ta surka sannan ta kaiwa kakar tasu a ɗaki.
Gefen kayansu stohuwan taje ta jawo wani ɗan-kwali babba, ta cirewa jikar nata kayan jikinta ta lullubeta da wannan ɗan-kwalin. Share mata jikinta tayi tass duk inda ya ɓaci da aman da tayin, ta goge ta tass sannan ta ɗauko wani kayan hassu na taimaka mata suka sanya mata.
Yarinyar ko ido bata buɗe ba, dan tana jin jiki gashi jikinta yayi zafi jau-jauu kaman wuta.
Stohuwar tace “ke hansai tashi kije ki qiramun malam ko magaji duk wanda kika gani nan qofa, kice yazo ya ɗauka mun ita muje gidana tunda nan gidan neman ranta suke basa sonta, to ya isa ni bazan iya ba ina sonta, in su suna gani zasu barta ta mutu to ni duk wata marar mutuncin da ta cika zan nuna mata nawa yafi nata, tambaɗaɗɗun iyaye kawai”.
Fita Hassu tayi ta nufi qofan gidan, cikin sa’a ta haɗu da Magaji, tana ganinsa tace masa “Hamma wai inji baabaa Mero kazo” amsa mata yayi suka shigo cikin gidan tare, suka nufi ɗakin su Hassun.
Jin shigowan Magaji gidan Mama Lami da sauri tayi dakinta ta turo qofar.
Da sallama ya shiga ɗakin, ganin kakar tasu tsaye kan yarinyar da mamaki yace “baabaa me yasami Innai kuma?
Cikin hasala stohuwar tace “to ubana Magaji zaka tsaya tambaya na ne ko zakamun abunda naqira kamun?”
Sanin masifar stohuwar sai yace “Allah baki haquri stohuwa” harara ta aika masa da shi tace “nace in ya bani kabi dare ka kwace, ɗan bokon tsiya kawai ni ka ɗauka mun jika mu tafi da ita gidana ba lafiyane da ita ba kuma in nabarta a gidan nan duka maqiyantane kashemun ita zasu yi ɗan gwanda hansai ma abunka da ƴar uwa har da qwalla tayi na tausayin Addan ta”
Qafa tsohuwar ta kuma yi tace “Magaji ina dalili in haifi abu in kasa ko kallonsa balle kulawa da shi, ko mutuwa zai yi, amma nide matar nan Indo abunda take yi yana cimun tuwo a qwarya aradu ji nake wataran inbi dare inshaqeta kowa ya huta da wannan kayan ciwon zuciyan, wai dan Allah ka haifi ɗa kai ga shugaban masu kunyan ɗan farko sai kaqi kula dashi tun yaushe akabar wannan jahilcin ai al’adar ma taci qaniyar ta, mu dai a zamanin mu ba wannan tambaɗewan zagewa ake a kula da ɗa in baka kula dashi ba ubanwa ya maka naqudan sa da zai kula maka da shi? Allah dai ya bawa takwara miji nagari tayi aure ko ta huta da taqaicin wannan tambaɗaɗɗiyar uwa da Allah ya bata”
“Ameen” Hassu da Magaji suka amsa wa baabaa Mero.
Ɗaukanta Magaji yayi kaman baby suka fita a gidan suka kama hanyan gidan baabaa da yake basu da nisa stakaninsu, suna tafiya sai sababi take har suka isa gidan nata ɗan madedeci, ɗakin ta Magaji ya shige da Innai ya kwantar da ita a ɗan qaramin gadon ciyawan dake ɗakin wanda dama na Innai ne dan mutuniyar baabaa Mero ce.
Baabaa tace “nagode ɗan nan Allah dai ya maka albarka duk da dai dama ba wani nauyin kirki ne da ita ba, yo to yaushe ma ta samu kwanciyan hankali da farincikin da zata yi nauyi yarinya kaman a hure ta faɗi, watarana ma aka yi iska mai qarfi inba sa’a ba sai ya ɗauke ta, Allah ya saka miki takwara”
Magaji yace “Allah qara sauqi baabaa bari muje lokacin salllah yayi”
Tace “to angode, kema hansai jeki gidan kigyara ɗakin naku ko da yake ke ai ɗiyar so ce, takwarata ce ba’a son ta” qwafa tsohuwar tayi ta ɗauki buta ta shige ban ɗaki”.
Hassu kaman ba taso haka ta kama hanyan gidan nasu ita kanta da take yarinya qarama abun na damun ta yacce mahaifiyar tasu ke nuna halin ko inkula akan ƴar uwar tata haka ma Mama Lami, “Allah baki lafiya Adda” cewar Hassu tana share ƙwalla ta shige gidan.
Ta samu mahaifiyarta ta idar da alwala kenan ta shiga ɗaki, Mama Lami ce ta fito dan itama tayi alwalan. Kallon Hassu tayi tace “munafuka ƴar munafukai dangin jarababbu hankalinki ya kwanta ke gaki me ƴar uwa ba kin qira tsohuwar nan ta zage mutane burin ki ya cika, Ita uwar taku bata kula da ƴar ta ba sai ni a gayyan soɗi da shishishigi mtswwww” ɗaga murya tayi dan mahaifiyar su Hassu ta jiyo ta “wai shi mutum gashi bafulatani a haka dai ƴar mutum za ta mutu indai nice zan kula da ita aikin banza anjiqa ba’a tsame ba” Buta ta ɗauka tayi bantdaki tana ta mita dan taji zafin faɗan baabaa Mero.
Ita dai Hassu ba tace komai ba ta nufi inda Addan nata tayi aman ta kwashe ta gyara gurin taje ɗakinsu ta gyara ta ɗauko kayan da aka cire wa Addan nata ta wanke su, Aikin da take kai kace ba yarinya ce ba.
Bayan ta kammala gyara komai ta ɗau buta tai alwala ta shige ɗakinsu dan itama tayi sallahn