Rainon Soja Hausa Novel

Rainon Soja 11

*️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*

 

Free page 11

 

*To masoya na mun kusa muce free page ya ƙare A page 12 Inshallah zamu ƙare na ƙyauta wato book 1 masu buƙatar Cigaban littafin Rainon soja ga yanda process ɗin namu yake…..Regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 ko katin MTN…a next page book 1 zaiyi ending*

“Babu ma’eesha? , Kamar ya kenan bata nan? . Mami tayi maganan cike da rawar murya tare da fiddo da idanun ta waje tana zuba su ga Drivan da yayi ƙasa da kan sa yana mai labarta mata yanda Abun ya faru tsakanin Jidderh da ma’eesha. Yanzu Bala ka sauke mun yarinya ana ruwa a tsakiyar hanya? Yarinya yar shekaru goma sha ɗaya? Tabbas yau sai nayi maganin Jidder a cikin gidan nan….Ta furta zancen jikin ta ko ina rawa yake yi kar-kar-kar . Duk ruwan dake sauka a kan ta bata jin sanyin sa , kallon Bala ta sake yi wanda shi kan sa Jikin sa kyarma yake yi na tsoro . Tabbas yasan ya aikata kuskuren biye ma Jidder da yayi ,amma kuma idan aka duba bashi da laifi Masifar Jidder yake gudu yasa ka yayi mata yanda tace ” .

“Buɗe moton tayi tana Furta maza ka kaini inda kuka sauke mun yarinya , Shashancin Banza da wofi ” . Jikin Bala driva na rawa yayi saurin shigewa Moton yana yin horn da sauri Sojojin suka Wangale masa Gate yana ficewa da Mami daga cikin gidan General Saleh Yelwa.

**
Yanda take tafiya a gadarance haka komai nata harta halayyar nata yake , a shirye take da ko wani hukunci Yau Mami zata yi mata a cikin gidan . Turusss tayi ganin Aliyu Haidar zaune bisa Resting chair ɗin dake ƙayataccen falon, idanun sa na bisa hanyar shigowa wato inda take. Tsayawa tayi tana kafe shi da ido zuciyar ta na harbawa da ƙarfi lokaci guda , don bata san mene zata ce masa idan ya tambaye ta ina Ma’eeshan nasa ba?”. Ɗan rufe idanun ta tayi tana ware su kana tayi saurin kallon stairs ɗin da Khalil ke saukowa hannun sa Ɗauke da Laptop da alama wani Abin zaiyi mai muhimmanci ko yana kan yi. “Hummmm….Dogon Numfashi ta sauke tana maida kallon ta ga Ali Haidar, da yake sakin mata murmushin nan nasa, fuskar sa ya tara ƙasumba tamkar ba Daga Aikin soja yake ba. Duk wata cikar zati na Cikakken Namiji saurayi ya gama bayyana masa, Don a wannan lokaci yakai 27 . Yana sanye cikin ƙananun kaya na Hutawa da shan iska , White t.shirt da boxer wani Black mai yarfin kakin Soja…He looks neat and breathtaking Bin ta yake da innocent face ɗin sa kana taga ya ware hannun sa yana furta “ taho mana Jidder na”.

Murmushi Tayi cike da jin dadin ganin nasu don bata yi tsammanin Dawowan su ba ta nufi Aliyu tana zama tare da shigewa jikin sa tana furta “ Oyoyo Ya Haidar ”….Kee ina Ma’eesha ? ” .

Muryar Khalil ya katse su , Wanda a hankali ta ɗago tana kallon sa kana ta kalli Aliyu sai ta fara kame-kame tana cuno bakin ta gaba . Ya Khalil bakayi kyawata ba ne kake tambayar Ma’eesha ita kaɗai? . Zama yayi a kujeran dake fuskantar nasu kana yace“ Nayi kyawar ku duka, yau aka yi Hutu ina result din ki ? Ina kuma nata nasan ta she is talented, Shiyasa na ƙagu naga na nawa tayi ?”. Hummmm Ai ba tare muke ba ….kaman ya ba tare kuke ba ? Yess tana hanya zata shigo yanzu. Kamin Khalil ya ƙara magana tuni ta miƙe tana faɗin “ Lemme go and take shower , idan na dawo sai ka duba result din nawa ”. Bin ta da kallo Khalil yayi , kana ya kalli Aliyu wanda yake shan Lemun tsamin da yasa aka yi masa juise nashi. Shan Lemon sa yake tamkar baya jin mene suke faɗi.

Takaici ne ya kama khalil tabbas shi jikin sa bai bashi ba , Miƙewa yayi yana furta “ Ali baka ji menake cema jidderh ba? Wai kai wannan lemon amfanin me yake maka?. Kallon sa Aliyu yayi a Miskilance kana ya kalli Ruwan lemon hannun sa , motsa laɓɓan sa yayi tare da cewa“ Baka taɓa sanin mene lemon tsami ke sawa ba ko ragewa? , Tsayawa Khalil yayi kana yace “ Ban sani ba ”. Aje cup ɗin yayi yana kallon sa tare da gyara zaman sa kamin yace “Alright rage sha’awa , don Ni fa bana tsammanin Zan koma Bakin Aiki ba tare da Aure ba , da matata zan koma. “Wani irin kallo Khalil yayi masa idan da sabo ya saba da iskancin Aliyu baya ɗaukar sa da mutunci ko yaji kunyar sa na yayan sa ,ya dauke sa tamkar aboki ….mtswwwww Bad behavior, ya furta yana hararan Aliyu tare da Cigaba da cewa “ Na tsani wannan Ɗabi’ar naka Haidar, idan kaso ka Auri Huɗu a lokaci daya.

Wani irin dariya Aliyu yayi wanda sai da na ƙara kallon sa , gaba ɗaya ya sauya ya wani koma Arrogant har a Muryar sa. Dariya yayi irin ta Basawan soja “Hahahaha…”! Ai shikenan Ya Khalil dama na faɗa maka Ni mace ɗaya ba zan iya rayuwa da ita ba ,don ba zan samu biyar buƙatan…….Ɗaga masa hannu khalil yayi yana dakatar dashi kana yace “ Ka bari idan Daddy yazo sai kayi masa bayanin Aure kake buƙata , Ni Bara na leƙa naga Ma’eesha, na ƙosa naga yanda yanzu ta girma shekaru uku bamu ganta ba”.
Ok Ali ya furta yana kauda kan sa gyefe , yayin da Khaleel cikin sauri ya fice daga Falon ”.

**
Bayan mami sun fita ba daɗewa ruwan ya fara tsagaitawa, Ya zama sai dai yayyafi irin mai ƙarfin nan. Titin babu kowa kaman an share ko abun hawa babu masu wucewa kowa ya fake a mafakarsa. Ma’eesha ta hanga ita kaɗai tana tafiya tana rungume da hannayen ta alamar sanyi na kaɗata. Gaba ɗaya ta jiƙe sharɓammm sai tafiya take , komai nata a salɓi take yin shi alamu har ta gaji da tafiya. Fitowa Mami tayi daga moton jikin ta a mace zuciyar ta na kuka ta fara takawa ixuwa inda Ma’eesha take. Ɗan nesa da ita ta tsaya tana ƙare ma kyaƙyƙyawar fuskar ta kallo wanda kan ta ke ƙasa sam bata lura da Mami ba , har ta tako zuwa gaban ta .

Ƙafafun mami ta gani a gaban ta ,wannan yasa ma’eesha saurin Ɗagowa suna haɗa ido da Mami dake zubda Wasu irin ƙwallah…Cikin Sanyin murya tana Wangale mata baki cike da fara’ar nan nata ta furta “ Mami…”! Lumshe ido Mami tayi wasu hawayen na sauko mata kana cikin sauri ta furta “ Na’am Babyn Mami taho gare ni”. Da gudu Ma’eesha ta faɗa jikin mami data rage Tsawon ta itama tana Rungume Ta tsammmmm….Ina sonki Ma’eesha na , tayi maganan tana ƙara mannata da jikin ta . Ina sonki Nima mami. Caaakkk ta ɗauki Ma’eesha tana murmushi tare da cewa“ Yau Ali da Khalil sun dawo fa”.

Yeeeeee Mami muyi sauri Uncle sun dawo? Daddy fa? Moton suka shige kana Mami tace “ Jidderh ce tace ki fita ? Me Yasa baki fake a wani wurin ba? Yau sai na hukunta Jidder, yanzu zan kira Doctor Isma’il ya taho ya duba ki , za kisha magani ko Ma’eesha na?

Murmushi Ma’eesha tayi kana ta gyaɗa mata kai cike da yarinta ta furta “Eh mami amma kar ki ma Anti jidderh komai , laifi nayi mata ” . A’a nafa sanki bakya laifi Ma’eesha . To mami na kiyi Haƙuri ki yafe ma Anti Jidder.

Tsayawa Mami tayi tana kallon ta kana ta kai hannu tana kwantota bisa ƙirjin ta . A hankali take shafa bayan Ma’eesha tana cije laɓɓanta ita kaɗai tasan halin baƙin cikin da zuciyar ta ke ciki a halin yanzu .

**
Fitowa tayi daga Bedroom ɗin ta tare da isowa tsakiyar falon, sai ƙamshi take yi tana hura hanci …..Sanye take cikin rigar Atampha doguwa mai ƙaramar hannu an mata ɗinkin da ya kama jikin ta sosai . Dama ba gwanar saka Kallabi Bace haka ta fito Attachment ɗin kan ta na reto har tsakiyar baya , Wanda yake ɗauke da launin milk don ba bama baƙi ta sanya ba . Kunnen ta ɗaya cikin ear phone yayin da hannun ta ke ɗauke da Wayar ta. Plate shoe ta sanya tana mai isowa zuwa Tsakiyar falon Nasreen tayi tana wannan yauƙi tare da caɓe baki tana bin Ma’aikatan dake falon da Wani irin wulaƙantaccen kallo . “Barka da wannan lokaci Hajiya ”.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected