Hausa NovelsTantiriya a Gidan Yari Book 2 complete Hausa Novel

Tantiriya a Gidan Yari Book 2 Page 36-40

Paid group 300

ACCNT NO
0175487861
ASMAU GARBAt MUHAMMAD GTBANK

YAN NIGER
+22790795939

TANTIRIYA
A GIDAN YARI

BOOK2
~YARAN JAURO~

36-40

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM

Page naki ne
Aminatu Yusuf Bawale

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Lro2cmYgE0588BKELFJhbf
Assalamu alaikum matan kwarai munkawomuku magungunan mata masu kyauda inganci munada maganin sanyi original muna hadin 3ster hajiyata kizamo star agurin oga hajiyata karkimanta shima ogan akwainashi muna nan asokoto muna aikawa kowane gari harma damokotan kasashenmu babu inda bama kai kaya ⭐⭐⭐3 Alkhairice garemu yan uwamata
Gamai bukatar lambar kira gata 09039320715 sai munjiku siyannagari maidakudi gida
3⭐⭐⭐alkhairice

 

Hashimu Dolo shigar sa gida ke nan,Kubra taci gayu cikin shadda fara da adon blue tayi kyau,yarta wacce tayi wayo itama an mata gayu cikin kaya kanana tana Saman cinyarta,tace sannu da zuwa,Abba ya shugo Yana cewa Kai Yar Inna yau mun gaji mun Sha zama,Kubra tayi murmushi tace sannu to,Abba yace uhm tunda nace zanyi kishiya kika yi hankali Kubra,da abinci ma bakya bani sai an min wulakanci a gaban yarana,amma wlh tunda nace zan Kara aure shike nan kika canja,Ashe Kuna sani kuke wani abin ,da ance za a muku kishiya sai ku wani nutsu da ba ayi dan Allah ba sai an ji kishiya ko ance za a Karo kishiya,Kubra tace hankali nayi yanzu,a gidan uwar wa,kice da ashe da mahaukaciya nake zaune ban sani ba,Kubra harda shagwaba tace to ai yanzu na canja na gane kurena Kuma gashi na gyara,ni da na aurar da yara har jika ce Dani,Hashimu ya Kalli Kubra yace ai duk dadin Baki kin iya ya zanyi,sai da kika yi maganar jika ma kika tuna min ko Naila ta samu ciki oho na gaji da jika daya tal,in banda irin Hanan Amal bani da kowa,Umma tace to ai Hanan taka ce fa mene da irinta,Abba yace na daina kaunarta.

Dariya Kubra tayi tace ai Kai da wai na gari,Abba yace Ina nima na kama gabana,Kubra babyn dake hannunta ta bashi tace riketa na kawo maka abinci,Ina yaran gidan ne yau? Kubra ta furta suna makaranta ka manta yanzu ma kafin Hidaya ta fita sai da muka yi fada da ita, na ci mata Kai Abban Mohsin,kika ci Ubanta kenan? tace ae wlh bata da kunya wai lallai sai na bata kudinta da take Tarawa zata dinka anko,Abba dolo yace to da kika ci mata Uba ya ban ji bani Ina can gidan Jauro banji dadin komai ba har na dawo,Dariya ya bawa Kubra taje ta kawo Masa abincin ya fara ci kenan sai ga Naila ta kira wayar Kubra.

Kubra ta daga tace dazu fa ta kirani maybe Kai take nema,Abba yace wayata kuwa ba charge,Kubra ta daga Naila tace Umma ba ke nake nema ba, Abba yana nan? wayarsa a kashe,ba charge amma gashi bari na bashi.
Abba ya karba yayi Sallama,Naila ta amsa tare da gaida Abba ya amsa.
Tace Abba addua na bugo ka tayani na fadawa Umma ma shine ta dinga fada wai mene abin na fada,Abba yace mene ne ya faru Kuma Ina ta cewa kina can kalau kalau,Naila tace Abba kalau nake Kuma muna zaune lafiya amma dazu muka je asibiti gwajin lafiya sai aka gano min wai kwayayen Haihuwa ta sun mutu tun Ina kauye,wai wani sinadari ne a nonon saniya idan ba a dafa ba yake kashe su wai saura kadan, na haihu a duniya da yawa na haifi yara uku ko hudu,Kuma Abba har yau wlh shuru ban samu cikin ba,Abba yace shi Dan ubansa mijin me yakeyi duk nacin sa? Shi yasa nake birge kaina ni Hashimu,Naila tace Kai Abba dan Albarka zaka ce karka zage shi,Abba yace to ai shike nan ki kwantar da hankalinki zaki samu, ki rabu da maganar likitoci Yan karya nasara ya koya musu karya,Allah duk Wanda ya rubuta zaizo duniya sai yazo damuwarki ko rashinta Bai sawa ki samu Abu,ni Banga ma abin damuwa ba wata nawa kwata kwata da auren baki karasa 3mnths ba fa a dakin miji amma har zaki damu kanki,Wanda Allah Bai bashi ba fa sai ya kashe kansa kenan? Ki godewa Allah da an gano miki ance bakya haihuwa fa ya zaki yi Kuma kin San aure zai Kara ya zama dole,ko nine akace bakya haihuwa ai har gida zanzo na bashi shawara nace ya Kara aure, Naila tace Abba ni din? Abba yace ai ni duk Inda gaskiya take Ina Nan ko uwata ce cewa zanyi a Kara mata Kuma wlh na zama Dan Amarya kullum Ina wajen Amarya sai dai tayi ta kishinta,dariya Naila tayi tace shike nan Abba ai shima yace yana mana addua Allah ya kawo na gari masu Albarka.

Abba yace a’a karki yarda namiji ya dinga addua a boye yayita a fili kina ji da kunnenki,idan ba haka ba kina can kina Jin dadi Yana addua kina amsa Masa da Ameen Ameen shegen Ashe matar aure yake nema ya Kara ta biyu,Yana Allah ka bani mace ta kirki na Kara aure,idan talaka ne ya dinga addua kenan Allah ya bashi kudi ya Kara mata, ke baki sani ba kina Ameen Ameen, wani Kuma dama yaga wata Yana so wata yar Fatima karki yarda,Naila dariya tayi tace to Abba.

Abba yace Kinga Naila a yanzu duk da cewa ke kinyi dace Alhmdllh amma da yawan mutane da aure Yana Expire kamar Passport ko driver’s license mutane da yawa baza su sake sabuntawa ba,to za a samu wasu dai su canja miji suyi sabo amma indai da matar farko ce ko mijin da matar to da yawa baza ayi wani ba.
Nima badan Kubra ta canja ba Ina cikin Wanda basu sake sabuntawa ba,amma yanzu duk kina Amarya baza mu yarda da shi ba sai kin haihu tukun zamu yarda da Spark a lokacin za a gane Ina ya nufa,idan farkon aure ne ba a ganewa kullum wannan jarabar kiran Baby da Baby,Yana Baby zo nan kwanta a kirjina kina Jin dadi nan gaba Billahillazi sai kiji yace Maman Kandala da Allah Kalli Jikin bango ni munsharinki ya dame ni,Naila ta dinga sheka dariya tace Abba sai kace tsofaffi, Maman Kandala Allah rabani da Kandala wlh,mu Yan gayu ne,Abba yace to shike nan Naila ai bana so nima ya zama haka nafi so har tsufa Kuna Nan haka,gaskiya dai na fada miki.
Abba ya dade Yana bawa Naila dariya har suka yi sallama,ta kashe wayar ta kira Mohsin.

Yana dagawa tace Yaya ka daina so na yanzu,dariya yayi yace Ina sonki mana,ka samu matar so an watsar dani yanzu gashi kwayayen haihuwa ta sun mutu saura hudu ko uku baka sani ba ma,Mohsin yace ta ya kika sani,Naila ta yi kalar tausayi tace sun mutu tun a kauye ba a sani ba,madarar shanu ta kashe su,yanzu ance Bai fi na haifi yara uku ba jiya muka je asibiti,Kuma Yaya wlh kwana Nan na gama period kaga ba a samu komai ba,Kuma kullum sai mun girgiza bed yafi sau nawa shuru kake ji,dariya ta bawa Mohsin yace wato ke har yanzu baza ki daina iskanci ba? Naila tace gaskiya ce ai ko Kai baka girgiza bed din ne,ni na manta ma ban tambayeka ba ya maganin kayi amfani da shi yanzu? Ai yanzu ta Saba matar taka,haka tace miki ta Saba? Mohsin ya tambaya,Naila tace ae tace ta Saba har zuwa take tana gode min tace yayana ya hadu kullum salo salo babu missionary,zanci ubanki Beauty ce zata fada miki haka karya kike,Naila tace tun yaushe ta fitsare tace kullum sai kayi sau biyar wai Kaine ka lalata ta,Dariya yayi yace daga ji karya kike sau biyar fa mahaukaci ne ni,maganin nan ya hadu Naila ashe da gaske kike yi yana da kyau na zauna Ina ta walagigi,Har naje Kauye na karbo wasu,har Beauty na karbo mata,Naila tace da ka rainani na fada maka kaki yarda,yanzu na yarda ai,Hidaya tace zata zo wai idan sunyi hutu,Naila tace sai yanzu taga dama,dama tayi zamanta ta bari sai na samu ciki idan na fara laulayi sai tazo ta dinga yi min aiki,Mohsin dariya ta bashi sosai yace ke wai yaushe zaki hankali ne Naila,yaushe kika San Allah zai baki cikin ma? Idan sai nan da Shekara biyar fa? Naila tace wlh kuka zanyi,daga aure kin damu mutane da ciki,ki bari bawan Allah yaci amarcinsa ya more ai ni murna nake taya shi wlh Inama nine,au yaya Kai an gamu ne? yace uhm gashi nan dai da alama ciki ne da ita,wani ihu da Naila tayi sai da Spark ya fito daga toilet Inda yake wanka ya leko bedroom din ya gani ko lafiya,Mohsin yace mene abin ihu ta dinga Jin dadi sai kace itace ta samu,Mohsin wayarsa ya kashe yana dariyar Naila,yace wannan yarinyar zanga ranar da zata yi hankali.

1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected