Tsutsar Nama 3
.
*_Typing_*
*_TSUTSAR NAMA….!!_*
_(Itama nama ce)_
_ _
_ _
……Tun dai muna shashshare juna har abinda ke cikin zuciya ya bayyana, domin kuwa Mansoor ya fito fili ya nuna min shifa sona yake. Tom kun san dai halin mutuniyar taku, ban gusa ba na balbalesa da masifar da zuwa yanzu wasu sun fara kallona da sumumu kasau macijin sari ka noƙe. Maimakon yaji haushi sai ya dinga sakar min murmushi, wannan shine karo na farko da nabar zuwa cafeteria da tunanin ai Mansoor zai ƙyaleni na huta, dan ni kam burina karatu ba soyayya ba. Sai dai kuma ba hakan bane ba, dan kuwa dai shima salo ya canja ta hanyar nuna ba soyayyar za’aiba yanzu karatu ne gaba, idan komai ya daidaita nan gaba sai soyayyar ta koma gaba. Tun ina shashsha masa ƙamshi harna miƙa wuya. Kafin wani dogon lokaci kowa yasan soyayyar mu da Mansoor kasancewar sa mutum popular a cikin makarantar, duk da dai kamar yanda ta faɗa karatune gaba ba soyayya muke ba, dan da wahala ma kaji ya saka min batun soyayya, sai yayta amfani da hakan shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tdakaninmu. Komai ya cigaba da tafiya yanda ya kamata, Mansoor na taimaka min matuƙa a ɓangaren karatu ni da ƙawata Joy. Hakan kuma ya sake fiddo ƙwazona. Sannan soyayyarsa na bani kariya sosai daga tsagerun ɗalibai harma da malamai ƴan bani gishiri na baka manda. Tun sauran ɗalibai na ɗaukar soyayyar yaudara ko wata manufa har suka yarda ɗari bisa ɗari da gaske muke, saboda komai muna gudanar da shi a tsaftace.
Tafiya tai tafiya, shekaru sunja abubuwa sun canja. Su Mansoor sun kammala karatunsu, sai dai kuma muna nane da juna ta waya. Yana kuma zuwa gida duk da ban taɓa yarda kowa yasan da batunsa ba bayan Yaya Musaddiq. Koda yake su Baby sun sani, dan nasha jin ma wai ai Baby ta jima tana son shi, sai dai bansan minene ya faru koya katangeta da sanarwa a gida ina soyayya da wani ba, sannan ita bata taɓa tarata da batun Mansoor ba kai tsaye, sai dai tai habaici a wasu lokutan ko shaguɓe, ni kuma sai ban taɓa kulata ba ko nuna na fahimta. Ina zangon ƙarshe na kammala karatuna na fahimci ashe Yaya Musaddiq shike biyamin kuɗin makaranta babu wani scholarship dama. Ya haɗa baki da malamin namune kawai, dan a yanzu haka shima Hafizzullah yana a level 100 a jami’ar Umaru Musa ƴar-aduwa dake Katsina. Shima kuma dai da batun scholarship ɗin nan aka rufe bakunan su Uncle Imam duk da an kwashi tashin hankali sosai fiye da nawa lokacin kasancewar shi Nabil bai samu ya tafi ba har yanzu. Ranar da nasan wannan sirrin nasha kuka a gaban Yaya Musaddiq. Shiko ya dinga lallashina yana murmushi, a ranar ya sanar min da komai bai ɓoye min ba. Dan yace bazai taɓa iya zama bamuyi karatu ba, dan haka ya zaɓi bi ta wannan hanyar domin gina gobenmu. Shiko aikin kanikancinsa ya ishesa in sha ALLAHU. Na nuna masa ban yarda ba, shima dole ne musam yanda zamuyi ya koma karatu, dan kuwa zuwa yanzu yana samun kuɗi sosai, sai dai duk a hidimar gidanmu da karatunmu suke tafiya, dan har yanzu bai tsinanama kansa komai na rayuwa ba irin burin matasa na son gina gida da sauransu, hatta budurwa ma baida ita shi sam. Ya min alƙawarin idan lokacin komawar yayi zai koma in sha ALLAHU.
Alhmdllh na kammala karatu cikin nasara, yayinda na riga Abbas da Baby da suka rigani farawa kammalawa saboda su sun saka wasa a karatun nasu. Bakuma su da niyyar gama school ɗin da alama, maybe sai an korosu su shiga hankalinsu oho, dan gasu nan koda yaushe cikin maimaita shekara suke. Bayan kammala karatuna da wasu watanni Mansoor yay uwa yay maɗaukiya ya sama min aiki a wani gidan tv da rediyo dake tashe a wannan lokacin. Hakan ya saka Yaya Musaddiq farin ciki, yayinda ran su Abba yay baƙi har suka kasa ɓoye hassadarsu a fili musamman ma Mom, dan da farko ma tuburewa tai akan tunda na gama karatu aure kawai ya kamata Abba yay min, wai akwai wani ɗan yayarta ya jima da cewa yana so na. Abba har ya ɗauki zancenta da muhimmanci niko na tibire nace wlhy idan aka aura min shi kashesa zanyi, dan ni ban shirya aure ba sai na fara aiki na. Ganin fa da gaske nake kuma sun san tsurin idona dan randa yaron yazo hira wajena zagin ƙare dangi na masa, hakan yasa Abba ya kashe maganar, sai dai ban san yaya sukai da matar tashi ba a ɓoye, a zahiri dai yace ya kashe wannan batu naje nai aiki na. Amma ya bani nan da ƙarshen shekarar nan na kawo miji. Oho ban wani damu dasu ba na fara aiki na, dan nasan dai inada Mansoor ɗina a hannu. Cikin nasara kafin kace mi na samu karɓuwa, albashina na farko dana biyu dana uku na haɗa da shi na sayama Yaya Musaddiq fili da taimakon Mansoor. Lokacin dana damƙa masa takardun sai kawai ya fashe da kuka. Nima kukan na fashe da shi tare riƙe hannunsa ina roƙonsa dan ALLAH ya daina, shifa uba ne a garemu yanzu, idan bamu masa hidima da abinda ALLAH ya azurtamu da shi ba wa zamuyimawa. Da ƙyar dai mukai shiru dan dama a wajen aikinsa na samesa, gudun kada na bashi a gida wani yaji a ƙwace. Tom Alhmdllh, yanzu dai a taƙaice watanni na shida kenan da fara aiki na, ina kuma matuƙar jin daɗin da nuna kwazo matuƙa. Dan bada ƙwaƙwalwa kawai nake aikin nan ba, harda zuciyata da ƙwanjina gaba ɗaya. Gashi ALLAH ya bani farin jinin mutane, dan tunda na fara gabatar da wani shiri akan matasa shikenan kamar nayi kiranyen masoya, dan da a iya rediyo ne kawai, amma wata guda kenan da fara gabatar da shi a television saboda yanda oganmu yaga shirin ya amsu yana sake jawo hankalin mutane ga channel ɗin tamu sai abin yay matuƙar birgesa. Dan haka aka sake ƙarfafa shirin ta hanyar fiddoshi a fanninmu na television ma, Alhmdllh kuma komai na tafiya fiye ma da yanda akai zato da tsammaninsa…….✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
