Tsutsar Nama Book 2 page 14
*_Typing_*
*_TSUTSAR NAMA….!!_*
_(Itama nama ce)_
_ _
_ _
_ _
…….Cak numfashina ya tsaya, illahirin jikina ya saki gaba ɗaya. Da ga ni har shi muka zubama juna ido. Yamutsawa kaina ya farayi saboda wani sinadari mai ƙarfi dake fitowa daga cikin cat ayes ɗinsa yana shiga cikin nawa. Wani irin kallo yake min mai kama da gargaɗi koma tsanace ban sani ba. Dan duk yanda naso dakewa hakan ya gagara. Tuni naji wani irin kwarjininsa ya gama mamayeni da cikani tamkar mu kaɗaine a wani matsatsen lungu. Hatta da iska ma ta fara min wuyar shaƙa neman komawa fisgar numfashi nake yi. Wani matsiyacin kallo daya dalla min tare da ƙoƙari janye jikinsa daga nawa ya sani tafiya gaba ɗayana baya zan faɗi. Bamma san na fasa ƙara ba da komawa gaba ɗaya jikin nashi na ƙanƙamesa tamkar zan huda shi na shige ciki…
Kusan kowa dake a wajen sai da ya sake waro idanu. Yayinda tuƙuƙin baƙin ciki da kishi mai tsanani ya gama mamaye zuciya da ruhin Azizat. A yanda take jin bawan ALLAHn nan a ranta ko macen sauro ta tsani ta taɓa mata shi, ai tuni idanunta sun sake rufewa. Batama san lokacin data isa gabansu ba. “Wlhy sai na kasheki ƴar iska. Bayan maita ma harda bin mazan mutane”. ta faɗa cikin ihu mai ƙaraji tana damƙo hannun Samraah da ƙoƙarin janta baya daga jikin Maash. Wani mugun kallo ya watsa mata. Sai kawai ta fashe da kuka tare da sakar min hannun tana ƙoƙarin kaimin mari. Nima tamkar wadda aka farkar a barci dai-dai nan na dawowa a hayyacina, Cikin wani irin sauri da shiga tsananin tashin hankali na sakesa gaba ɗaya tare da turashi. Sai da me ko gezau, yana nan a tsayensa ƙyam saman ƙafafunsa tamkar dasashiyar bishiyar data kafu a muhallin daya dace da ita. Kallo ɗaya yay min da shegun idanun nan nasa kalar na maguna ya janye tamkar wanda ba’ai komai ba ma. Ga fuskar tsamm babu alamun rahama ko sassauci balle ma kai tunanin ya taɓa sanin mai kama dani a rayuwarsa. Duk yanda naso janye nawa idanun daga kansa na gagara hakan saboda tsabagen shiga ƙololuwar baƙin ciki, ruɗani da mamakin makirci da mugun halin mutumin nan, kenan da gaske shi MAASH ɗin ake nufi da sunan gidan nan?. Tayaya ma to hakan ta kasance?, farkon labarin a kano, cigabansa a Abuja, ƙarashensa a Lagos. Duka a ƙarƙashin ikonsa, kenan da gaske yayi winning kamar yanda yake iƙirari da cika bakin shi ba’a game da shi baiyi winning ba. Kai impossible…
Mugun zagin da Azizat ta lailayo min da sake yo kaina ya maidoni a hayyacina, raina a dugunzume na janye idanuna a kansa na dawo da shi gareta, dan wlhy tana sake taɓani duk haushi da takaicin mugun nan saina juyesu a kanta yanzun nan. Tana gab da kai hannunta jikina aka kira sunanta da ɗan faɗa-faɗa. “Azizat minene haka wai?!”. Mu dukanmu kalon Aunty Mama da tayi maganar mukayi, yayinda itama ta dakata tana hararata da famar huci sai kace wata kububuwa. Cikin sake bada umarni daga inda take tsaye ta dubi Mama Balki. “Kuje inda na turaku”.
“Godiya muke ranki ya daɗe, ALLAH ya ƙara girma”. Mama Balki ta faɗa tana risinawa tare da kama hannuna. Tamkar wadda aka zarema illahirin lakar jiki na shiga binta zuciyata na wata kalar suya da raɗaɗi mai zafi. Yayinda idanuna ya kasa daina kallonsa, nama rasa wana kalar tunani kuma ya dace nayi. Muna gab da fita muka haɗa ido, wani irin lumshe nasa yay da yamutse fuska ya motsa lips ɗinsa a hankali, (First Game) sai kuma ya cije gefen lips ɗin da wani salo ya ɗauke kansa gaba ɗaya daga garemu.
Da ƙarfi na rumtse idanuna dake cikowa da ƙwalla. Cikin ɓacin rai na shiga ƙoƙarin son fisge hannuna daga na Mama Balki. Dan bazan iya haƙuri ba sai na maida masa murtani. Kai yau ma duk abinda za’ayi sai dai ayi wlhy. Sake damƙe min hannu Mama Balki tayi tare da jawoni gaba ɗaya daga cikin falon muka fito cikin main falo, sai da muka fito anan ma gaba ɗaya wajen compaund sannan. Cikin lallashi da ɗan faɗa ta furta, “Ya isa mana. Ki ƙyaleta. Banda abinki ina ke ina faɗa da ƴar masu gida. Kin san kuwa fitinar Azizat musamman akan bawan ALLAHn nan. Zuciya ba taki bace ba ɗiyata, anan a ƙarƙashinsu muke dole muyi haƙuri da koma mi zamu gani. Kima godema ALLAH Alhaji ƙarami yazo wajen da wlhy abinda zai faru ALLAH kaɗai ya sanshi. A hakan ma ALLAH ya taƙaita duk barci jama’ar gidan suke. Ita kuma Aunty Mama tana da sauƙi a cikinsu da ko gidan nan bazaki sake kwana ba. Kema dai na lura akwai ƙarfin hali, ki daure ki sauke wannan zuciyar taki kada ki sake kwatanta abinda kikayi yau”.
Zantukan Mama Balki sake ƙona min rai suke. Dan haka na sakar mata kuka kawai tare da faɗawa a jikinta na ƙanƙameta. Itama sai ta riƙeni hannu bibbiyu tana lallashi na…..
Su Samraah na gama ficewa a falon Azizat tayo kansa. “Yaya Please kace afitar mana da ita a gida. ALLAH yarinyar nan mayya ce. Tun jiya da aka shigo da ita gidan nan naji na tsaneta, jinake kamar ma na kashe banza. Dan bazan taɓa yafe mata rungumar da tayi maka b…..”
Ko kallon inda take baiyi ba, sai ma motsa lips ɗinsa da yay a hankali cikin silent voice ɗin nan tasa ya furta, “Good Morning Aunt” yay wucewarsa. Wani irin tsayawa tayi cak jikinta na tsuma. Duk da ba yau ne farau ɗin hakan ba a tsakaninsu sai take jin na yau ɗin ya mata zafi. Da kallo ta bisa idanunta nayin narai-narai alamar gab take da sakin kuka. Murmushi Aunty Mama tayi da ɗan girgiza kanta tana binsa da kallo. Har sai da ya ɓacema ganinsu ta janye idanun, ganin Azizat ta zabura zata bisa ta sakko ta kama hannunta batare da tace komai ba ta jata suka koma saman dan tasan bin nasa bazai haifar da ɗa mai ido ba. Dama ga wata wutar dake neman tasowa akan matsalarsun….
★★★
Cike da nishaɗi Abba ya koma gida. Sai dai me, yana shiga ya samu Mom na jibgar Halime har Bibaa na tayata. Yayinda Baby ke kwance a kujera wanwar alamar tasha kayan nata. Tuni yay wata irin zabura batare daya sani ba ya hankaɗesu su duka. Sannan ya ɗauke fuskar Bibaa da mari. “Kinci gidanku Habiba. Dan uwarki wannan ɗin sa’arki ce?”.
Kafin Habiba dake kuka ta bada amsa Mom data sake shiga cikin matsanancin ɓacin rai ta hayayyaƙo masa. “Mitai maka zaka daketa. Akan ƴar aiki wulaƙantacciya da iyayenta ma suka sallama ma duniya saboda baƙin talauci”.
Wani irin ɓacin rai ne ya tasoma Abba. Cikin rufewar ido ya furta, “Jalilah! Halimatussa’adiyyar ce wulaƙantacciya?”.
“Kuturun ubancan! Imamu harma sunanta ka sani? Harda ƙara masa wani ƙaimi. To ko dai kana zagayowa ne ban sani ba ta zama karuwarka. No wander yanzu kullum sai ka dawo gida da rana. Idan ka zauna kuma kata waige-waige kenan…”
“You are vary stupid Jalilah! Ni kike dangantawa da fasiƙanci?”.
“Yo in ba fasiƙin ba minene kai? Taya akai kasan wannan tsinanniyar yariyar anan gidan ma? Bayan na mata gargaɗi kaima kuma nayi maka. To wlhy kuwa zaku mutu yau ku duka…” ta ƙare maganar da rarumo flower base tai kan Halime dake maƙure gefe tana kuka. Damƙota Abba yayi da masifar ƙarfi, aiko ta juyo gaba ɗayanta ta buga masa abin a kai. Lokaci ɗaya Bibaa da Halime da Baby da hayaniyarsu ta sakata buɗe ido suka ƙwalla wata irin masifaffiyar ƙara da duk maƙwaftansu sai da suka jiyo. Yayinda fuskar Abba ta gama wankewa da jini. A take ya faɗi wanwar ƙasa. Ai sai su Bibaa suka sake ƙwala wata ƙarar da tafi ta farko. Itama Mom ta yadda guntun flawer base ɗin daya rage a hannunta tayi wani uban tsalle gefe tana ware idanu. Halime kuwa tuni ta gigice tazura waje a guje…….
